Hausa: Unlocked Literal Bible - Hausa

Littafin Farawa
Littafin Farawa
Sura 1

1 A cikin farko, Allah ya hallici sammai da duniya. 2 Duniya bata da siffa, sarari ce kawai. Duhu kuma ya rufe dukkan zurfafa. Ruhun Allah kuma yana kewayawa a bisa fuskar ruwaye. 3 Allah yace, "Bari haske ya kasance, haske kuwa ya kasance." 4 Allah kuma ya ga hasken, ya kuma ƙayatar. Sai ya raba haske da duhu. 5 Allah ya kira haske "yini," duhu kuma ya ce da shi "dare." Wannan shi ne safiya da dare, a rana ta ɗaya. 6 Allah yace, "Bari a sami fili tsakanin ruwaye, Sai ya rarraba tsakanin ruwaye." 7 Allah yayi tsakani ga ruwayen dake ƙarƙas da kuma ruwayen dake sammai. Haka kuma ya kasance. 8 Allah ya kira tsakanin "sararin sama." Wannan shi ne maraice da safiya, rana ta biyu kenan. 9 Allah yace, ruwayen dake ƙarƙashin sammai su tattaru wuri ɗaya, kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana," haka kuma ya faru. 10 Allah ya kira sandararriyar ƙasa "duniya," ruwayen da suka tattaru kuma ya kira su "tekuna" ya kuma ga suna da kyau. 11 Allah yace, "Duniya ta fitar da ciyayi da itatuwa masu fitar da iri da kuma 'ya'ya waɗanda ke cikin 'ya'yan, kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance. 12 Ƙasa ta fitar da ganyayyaki, da itatuwa masu bada iri kowanne bisa ga irinsa, da kuma itatuwa masu bada 'ya'ya dake cikinsu, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau. 13 Wannan ce safiya da maraice, rana ta uku. 14 Allah yace, "Haske ya kasance a sararin sama domin ya raba tsakanin haske da duhu, su kuma zama alamu na yanayi, domin ranaku da shekaru. 15 Sai su zama haske a sararin sama domin su haskaka duniya." Haka kuwa ya kasance. 16 Allah yayi manyan haskoki guda biyu, babban hasken yayi mulkin yini, ƙaramin hasken kuma yayi mulkin dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya shirya su a sama domin su bada haske ga duniya, 18 su kuma yi mulki kan yini da kuma dare, su kuma raba tsakanin haske da duhu. Allah kuma ya ga yana da kyau. 19 Wannan ce safiya da yammaci, rana ta huɗu. 20 Allah yace, "Ruwaye su kasance da manyan halittu masu rai, ya kuma bar tsuntsaye suyi ta firiya a saman duniya a sararin sama." 21 Allah ya hallici manyan hallittu na tekuna, da kuma sauran halittu kowanne bisa ga irinsa, da masu tafiya da kuma waɗanda suka cika ruwaye a ko'ina, da kuma dukkan tsuntsaye masu fukafukai, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau. 22 Allah ya albarkace su, cewa, "Ku ruɓanɓanya, ku hayayyafa, ku cika ruwaye a cikin tekuna. Ya ce tsuntsaye su ruɓanɓanya a duniya." 23 Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta biyar. 24 Allah yace, "Ƙasa ta bada hallittu masu rai, kowanne bisa ga irinsa, dabbobin gida, masu rarrafe dana daji kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance. 25 Allah kuma ya yi dabbobin duniya kowanne bisa ga irinsu, dabbobin gida kowanne bisa ga irinsa da duk masu jan jiki a ƙasa kowanne bisa ga irinsa. Ya kuma ga suna da kyau. 26 Allah yace "Bari muyi mutum cikin kamanninmu, bisa surarmu. Su yi mulkin kifaye na tekuna, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da kuma dukkan duniya, da dukkan abu mai rarrafe a bisa duniya." 27 Allah ya hallici mutum cikin kamanninsa. Cikin kamanninsa ya hallice shi. Mace da namiji ya hallice su. 28 Allah ya albarkace su ya ce da su,"Ku hayayyafa ku kuma ruɓaɓɓanya. Ku cika duniya ku nome ta. Kuyi mulkin kifaye na tekuna da tsuntsayen sama, da kuma duk abu mai rai dake tafiya bisa duniya." 29 Allah yace, "Duba na baka kowanne tsiro dake bada iri wanda yake a fuskar duniya, da dukkan bishiyoyi dake da iri a cikinsu. za su zama abinci a gare ku. 30 Ga kowacce dabba ta duniya, da kuma dukkan tsuntsaye na sammai, da kowanne abu mai rarrafe a doron duniya, da kuma dukkan halittu masu numfashin rai na baku kowanne irin koren ganye domin abinci." Haka kuma ya kasance. 31 Allah kuma ya ga dukkan abin da ya halitta na da kyau. Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta shida.

Sura 2

1 To an kammala sammai da duniya, da duk abubuwa masu rai da suka cika su. 2 A rana ta bakwai Allah ya kammala aikinsa da ya yi, domin haka sai ya huta a rana ta bakwai daga dukkan aikinsa. 3 Allah ya albarkaci rana ta bakwai ya kuma tsarkaketa, domin a cikinta ya huta daga dukkan aikinsa na halitta da ya yi. 4 Waɗannan sune al'amuran da suka shafi sammai da duniya, a lokacin da aka hallice su, a ranar da Yahweh ya yi sammai da duniya. 5 Ba wani filin daji kuma a duniya, ba tsire-tsire kuma a cikin filaye, domin Yahweh bai sa a yi ruwa ba tukuna a duniya, kuma ba mutumin da zai nome ƙasa. 6 Amma raɓa ta sauka a ƙasa ta jiƙe dukkan ƙasar. 7 Yahweh Allah ya halitta mutum daga cikin ƙasa, ya kuma hura masa numfashin rai a cikin kafafen hancinsa, sai mutum ya zama rayayyen taliki. 8 Yahweh ya yi lambun itatuwa a bangon gabas a cikin Aidan, a can ya sa mutumin daya halitta. 9 Daga cikin ƙasa Yahweh Allah ya sa ko waɗanne irin itatuwa masu ƙayatarwa da abinci su tsiro. Wannan ya haɗa da itacen rai wanda ke a tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta. 10 Rafi ya bi ta tsakiyar lambun Aidan domin ya jiƙa lambun. Daga can ne ya rabu ya zama rafuka huɗu. 11 Sunan na farko shi ne Fishon. Shi ne wanda ya malala a dukkan ƙasar Habila, inda akwai zinariya. Zinariyar wannan ƙasar tana da kyau. 12 Akwai kuma itatuwa masu ƙamshi da kyawawan duwatsu. 13 Sunan rafi na biyun shi ne Gishon. Wannan shi ne wanda ya malala zuwa Kush. 14 Sunan rafi na ukun shi ne Tigris, wanda ya malala gabashin Asshur. Rafi na huɗu shi ne Yufaretis. 15 Yahweh Allah ya ɗauki mutumin ya sa shi a lambun Aidin domin ya nome shi ya kula da shi. 16 Yahweh Allah ya umarci mutumin, da cewa, "Daga kowanne irin 'ya'yan itace na cikin lambun kana da 'yancin ci. 17 Amma ba za ka ci daga cikin itace na sanin nagarta da mugunta ba, domin ranar daka ci daga cikinsa, tabbas za ka mutu." 18 Yahweh Allah yace, "ba shi da kyau mutumin ya zauna shi kaɗai. Zan yi masa mataimakiyar da ta dace da shi." 19 Daga cikin ƙasa ne Yahweh Allah ya siffatta kowacce irin dabba ta saura da kuma tsuntsun sararin sama. Sai ya kawo su wurin mutumin domin ya ga yadda zai kira su. Duk abin da mutumin ya kira kowacce halitta sunanta kenan. 20 Mutumin ya ba dukkan dabbobi suna da kuma dukkan tsuntsayen sararin sama. Amma ga mutumin ba a sami mataimakin da ya dace da shi ba. 21 Yahweh Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin domin haka mutumin ya yi barci. Yahweh Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya yi mace ya kuma kawo ta ga mutumin 22 Da haƙarƙarin da Yahweh ya ciro daga jikin mutumin, ya yi mace da shi ya kuma kawo ta ga mutumin. 23 Sai mutumin yace, "A wannan lokacin, wannan ƙashi ne na ƙasusuwana, tsoka ce daga tsokata. Za a kira ta 'mace,' saboda daga jikin mutum aka ciro ta." 24 Domin haka mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, zai zama haɗe da matarsa, kuma za su zama jiki ɗaya. 25 Dukkan su biyu tsirara suke, mijin da matar, amma ba su jin kunya.

Sura 3

1 To maciji ya fi dukkan sauran dabbobin saura da Yahweh yayi wayau. Sai ya ce da macen, "Ko da gaske ne Allah yace ba zaku taɓa ci daga kowanne 'ya'yan itacen dake cikin lambun ba?" 2 Sai matar ta ce da macijin, "Ma iya ci daga cikin itatuwan lambun, 3 amma game da itacen dake tsakiyar lambun, Allah yace, 'Ba zaku ci shi ba, ba kuma zaku taɓa shi ba, in ba haka ba, zaku mutu."' 4 Sai maciji yace da macen, "Hakika ba zaku mutu ba. 5 Domin Allah ya san cewa a ranar da kuka ci idanunku zasu buɗe, zaku kuma zama kamar Allah, kuna sanin nagarta da mugunta." 6 Da matar ta duba ta ga itacen yana da kyau domin abinci, yana kuma ƙayatar da idanu, kuma itacen abin marmari ne yana sa mutum ya zama mai hikima, sai ta tsinki waɗansu daga cikin 'ya'yan ta ci shi. Sai ta bada waɗansu ga mijinta, shi kuma ya ci. 7 Idanun dukkan su biyun suka buɗe, sai suka gane tsirara su ke. Sai suka ɗinka ganyayyakin ɓaure suka yi wa kansu sutura. 8 Sai suka ji motsin Yahweh Allah ya na tafiya cikin lambun da sanyin yamma, domin haka mijin da matar suka ɓuya a cikin itatuwan lambun daga fuskar Yahweh Allah. 9 Sai Yahweh Allah ya kira mutumin yace da shi, "Ina ka ke?" 10 Mutumin yace "Na ji ka a cikin lambun, na kuma ji tsoro, domin tsirara na ke. Domin haka na ɓoye kaina." 11 Allah yace, "Wane ne ya faɗa maka cewa tsirara ka ke? Ko ka ci 'ya'yan itacen da na dokace ka kada ka ci daga cikinsa ne?" 12 Sai mutumin yace, "Macen daka ba ni ta kasance tare da ni, ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci shi." 13 Yahweh Allah yace da matar, "Me ki ka yi kenan?" Sai macen ta ce, "Maciji ne ya yi mini ƙarya, na kuwa ci." 14 Yahweh Allah yace da maciji, "Saboda ka yi wannan, kai kaɗai ne la'ananne a cikin dukkan dabbobin saura da dukkan dabbobin sama. A kan cikinka za ka yi tafiya, kuma ƙasa za ka ci dukkan kwanakin ranka. 15 Zan sa magaftaka tsakaninka da matar, da kuma tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje diddigensa." 16 Ga macen yace, "Zan ninka shan wuyarki sosai a samun 'ya'ya; a cikin shan wuya za ki haifi 'ya'ya. Duk marmarinki zai zama domin mijinki, amma zai yi mulkin ki." 17 Ga Adamu yace, "Domin ka saurari muryar matarka, ka ci daga cikin itacen da na dokace ka cewa, 'Kada ka ci daga cikinsa,' saboda kai na la'anta ƙasa; ta wurin aiki mai zafi za ka ci daga cikinta dukkan kwanakin ranka. 18 Za ta fitar da ƙaya da sarƙaƙƙiya domin ka, za ka kuma ci tsire-tsiren ƙasar. 19 Ta wurin zufarka za ka ci gurasa, har sai randa ka koma turɓaya, domin daga cikinta aka ciro ka. Domin kai ƙura ne, ƙura kuma za ka koma." 20 Mutumin ya kira sunan matarsa Hauwa ita ce mahaifiyar dukkan rayayyu. 21 Yahweh Allah ya yi wa Adamu da matarsa sutura ta fatu ya rufe su. 22 Yahweh Allah yace, "Yanzu mutumin ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, yana sane da mugunta da nagarta. To yanzu ba za mu taɓa barinsa ya sa hannunsa, ya tsinka daga itacen rai ba, ya ci, ya kuma rayu har abada." 23 Saboda haka Yahweh Allah ya fitar da shi daga cikin lambun Aidin, domin ya noma ƙasa wanda daga ita aka ciro shi. 24 To sai Allah ya kori mutumin daga lambun, ya sa kerubim a gabashin lambun Aidin da kuma takobi mai walƙiya dake jujjuyawa ta kowanne fanni, domin su yi tsaron hanya ta zuwa itacen rai.

Sura 4

1 Mutumin ya kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi Kayinu. Ta ce,"Na haifi mutum da taimakon Yahweh." 2 Sai ta sake haifar ɗan'uwansa Habila. Sai Habila ya zama makiyayi, amma Kayinu ya zama manomi. 3 Sai ya zamana wata rana Kayinu ya kawo wani sashe daga cikin amfanin gonar da ya noma daga ƙasa a matsayin baiko ga Yahweh. 4 Shi kuma Habila, sai ya kawo waɗansu 'ya'yan fari daga cikin garkensa da kuma sashe na kitse. Yahweh ya karɓi Habila da baikonsa, 5 amma Kayinu da baikonsa bai karɓa ba. Domin haka Kayinu ya fusata sosai, ya kuma ɓata fuska. 6 Yahweh yace da Kayinu, "Meyasa ka yi fushi meyasa fuskarka ta ɓaci haka? 7 In da ka yi abin dake nagari, da ba a karɓe ka ba? Amma in ba ka yi abin dake nagari ba, zunubi na ƙwanƙwasa ƙofa kuma marmarinsa shi ne ya mallake ka, amma dole ne ka yi mulkinsa." 8 Sai Kayinu ya yi magana da ɗan'uwansa Habila. Sai ya zamana a lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya kashe shi. 9 Daga nan Yahweh yace da Kayinu, "Ina ɗan'uwanka Habila?" Ya ce, "Ban sani ba. Ni makiyayin ɗan'uwana ne?" 10 Yahweh yace, "Me ka yi kenan? Jinin ɗan'uwanka yana kira na daga ƙasa. 11 Yanzu kai la'ananne ne daga ƙasar da ta buɗe baki ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka. 12 Daga yanzu duk lokacin daka noma ƙasa, ba za ta baka issashen amfaninta ba. Za ka zama mai yawo barkatai a cikin duniya." 13 Kayinu yace da Yahweh, "Horona ya yi girma fiye da yadda zan iya ɗauka. 14 Hakika ka kore ni waje yau daga wannan ƙasa, zan kuma riƙa ɓuya daga fuskarka. Zan zama mai yawo barkatai a cikin duniya, kuma duk wanda ya same ni zai kashe ni." 15 Yahweh yace da shi, In har wani ya kashe Kayinu za ayi masa ramako har niki bakwai." Daga nan Yahweh ya sa alama a jikin Kayinu, domin in wani ya gan shi kada wannan mutumin ya kai masa hari. 16 Sai Kayinu ya tafi daga fuskar Yahweh ya zauna a ƙasar Nod, a gabashin Aidin. 17 Kayinu ya kwana da matarsa sai ta yi ciki ta haifi Enok. Ya gina birni ya bashi sunan ɗansa Enok. 18 Ga Enok sai aka haifa masa Irad. Irad ya zama mahaifin Mehuyawel. Mehuyawel ya zama mahaifin Metushawel. Metushawel ya zama mahaifin 19 Lamek. Lamek ya aura wa kansa mata biyu: sunan ɗayar Ada, ɗayar kuma sunanta Zilla. 20 Ada ta haifi Yabal. Shi ne mahaifin masu zama a cikin rumfuna waɗanda ke da dabbobi. 21 Ɗan'uwansa shi ne Yubal. Shi ne mahaifin makaɗan molo da algaita. 22 Ita kuma Zilla, ta haifi Tubal Kayinu, shi ne mai samar da kayayyaki na jan ƙarfe. 'Yar'uwar Tubal Kayinu ita ce Na'ama. 23 Sai Lamek yace da matansa, Ada da Zilla, ku saurari muryata; ku matan Lamek, ku saurari abin da na ce. Domin na kashe mutum saboda ya yi mani rauni, saurayi domin ya ƙuje ni. 24 In an saka wa Kayinu sau bakwai, to za a saka wa Lamek sau saba'in." 25 Sai Adamu ya sake kwana da matarsa, sai ta sake haifar wani ɗan. Sai ta kira sunansa Set, ta kuma ce, "Allah ya bani wani ɗan a madadin Habila, domin Kayinu ya kashe shi." 26 Aka haifa wa Set ɗa, sai ya kira sunansa Enosh. A wancan lokacin ne mutane suka fara kiran bisa sunan Yahweh.

Sura 5

1 Wannan shi ne lissafin zuriyar Adamu. A ranar da Allah ya hallici mutum, ya yi su a cikin kamanninsa. 2 Namiji da mace ya hallice su. Ya albarkace su ya basu suna mutane a lokacin da ya hallice su. 3 Da Adamu ya yi shekaru130 sai ya zama mahaifin ɗa a cikin kamanninsa sai ya kira sunansa Set. 4 Bayan Adamu ya haifi Set, ya yi rayuwa tsawon shekaru ɗari takwas. Sai ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa. 5 Adamu ya yi rayuwa har shekaru 930 daga nan ya mutu. 6 Da Set ya yi shekaru 105, sai ya haifi Enosh. 7 Bayan ya haifi Enosh, ya rayu har tsawon shekaru 807 ya zama mahaifin 'ya'ya maza da mata da yawa. 8 Set ya rayu har shekaru 912 daga nan ya mutu. 9 Bayan Enosh ya rayu na tsawon shekaru tasa'in, sai ya haifi Kenan. 10 Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya rayu na tsawon shekaru 815. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa. 11 Enosh ya rayu tsawon shekaru 905 daga nan ya mutu. 12 Da Kenan ya yi shekaru saba'in, sai ya haifi Mahalalel. 13 Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekaru 840. Sai ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 14 Kenan ya rayu na tsawon shekaru 910, daga nan ya mutu. 15 Mahalalel ya rayu shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Yared, 16 Mahalalel yana da shekaru 830. Sai ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata masu yawa. 17 Mahalalel ya rayu na tsawon shekaru 895, daga nan ya mutu. 18 Da Yared ya yi shekaru 162, sai ya haifi Enok. 19 Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru ɗari takwas. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 20 Yared ya rayu na tsawon shekaru 962, daga nan ya mutu. 21 Da Enok ya yi shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Metusela. 22 Enok ya yi tafiya tare da Allah shekaru ɗari uku daga nan ya haifi Metusela, ya kuma haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 23 Enok ya yi shekaru ɗari uku da sittin da biyar. 24 Enok ya yi tafiya tare da Allah, daga bisani ya tafi, domin Allah ya fyauce shi. 25 Da Metusela ya yi shekaru 187, ya haifi Lamek. 26 Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 27 Metusela ya rayu na tsawon shekaru 965 daga nan ya mutu. 28 Bayan ya yi shekaru182, sai ya haifi ɗa. 29 Sai ya kira sunansa Nuhu, yana cewa, "Wannan zai bamu hutu daga aikinmu daga kuma aikin hannuwanmu mai wuya, da zamu yi saboda Allah ya la'anta ƙasa." 30 Lamek ya yi shekaru 595 daga nan ya haifi Nuhu. Daga nan ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata. 31 Lamek ya rayu na tsawon shekaru 777, daga nan ya mutu. 32 Bayan Nuhu ya yi shekaru ɗari biyar, sai ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

Sura 6

1 Sai ya zamana da mutane suka fara ruɓamɓanya a duniya aka kuma haifa masu 'ya'ya mata, 2 sai 'ya'yan Allah suka ga 'ya'yan mutane na da ban sha'awa. Sai suka auri mata daga cikinsu, dukkan su da suka zaɓa. 3 Yahweh yace "Ruhuna ba zai dawwama a cikin mutum ba har abada, domin su jiki ne. Za su rayu shekaru 120 ne." 4 A waɗancan kwanakin akwai ƙarfafan mutane sosai, kuma haka ya faru ne bayan 'ya'yan Allah sun auri 'ya'ya mata na mutane, sun kuma sami 'ya'ya tare da su. Waɗannan sune manyan mutanen dã can, mutane masu jaruntaka. 5 Yahweh ya ga muguntar mutum ta haɓaka a duniya, kuma dukkan tunane-tunanen zuciyarsa kullum mugunta ce. 6 Yahweh ya yi takaicin halitar mutum a duniya, kuma abin ya dame shi a zuciyarsa. 7 Domin haka Yahweh yace,"Zan shafe mutum wanda na halitta daga fuskar duniya; mutum da manyan dabbobi, da abubuwa masu rarrafe da tsuntsayen sammai, domin na yi takaici dana halicce su." 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a idanun Yahweh. 9 Waɗannan sune abubuwa game da Nuhu. Nuhu adalin mutum ne, kuma ba shi da abin zargi a cikin mutanen kwanakinsa. 10 Nuhu yayi tafiya tare da Allah. Nuhu ya haifi 'ya'ya uku: Wato Shem da Ham da Yafet. 11 Duniya ta ƙazanta a gaban Allah, ta kuma cika da hargitsi. 12 Allah ya ga duniya; duba, ta gurɓanta, domin dukkan mutane sun ɓata tafarkinsu a duniya. 13 Allah yace da Nuhu, Na ga cewa lokacin ƙarshen dukkan hallita ya yi domin duniya ta cika da hargitsi ta wurin su, hakika, zan hallaka su tare da duniya. 14 Ka yi wa kanka jirgi da itacen sida ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka rufe shi ciki da waje. 15 Ga fasalin yadda zaka yi shi: tsawon jirgin kamu ɗari uku, faɗinsa kamu hamsin, bisansa kamu talatin. 16 Ka yi wa jirgin rufi, ka kuma kammala shi ka dalaye shi daga sama har ƙasa. Ka sa ƙofa ta gefen jirgin, ka yi masa matakala, ƙarama, da ta biyu, da kuma matakala ta uku. 17 Ka saurara, Na kusa kawo ambaliyar ruwa a duniya domin in hallakar da dukkan masu rai dake da numfashi rai dake a ƙarƙashin sama. Duk abin dake a duniya zai mutu. 18 Amma zan kafa alƙawarina da kai. Zaka shiga cikin jirgin, da kai da 'ya'yanka da matarka da matan 'ya'yanka tare da kai. 19 Da dukkan hallitu masu rai, kowanne iri biyu dole ne kuma ka shigar dasu cikin jirgin, ka ajiye su, su tsira tare da kai, dukkan su namiji da mace. 20 Da tsuntsaye bisa ga irinsu, da manyan dabbobi bisa ga irinsu, dukkan wani abu mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu, biyu daga cikin kowanne iri daga cikinsu za su zo tare da kai, domin ka tsirar da rayukansu 21 Ka kuma yi wa kanka tanadin kowanne irin abinci na ci ka adana shi, domin ya zamar maka abinci da kuma dominsu." 22 Sai Nuhu ya yi wannan. Bisa yadda Allah ya umarce shi, haka ya yi.

Sura 7

1 Yahweh yace da Nuhu, "Ka zo, da kai da dukkan gidanka, zuwa cikin jirgin, domin na ga kai mai adalci ne a gabana a wannan tsara. 2 Da dukkan dabbobi masu tsarki tare da kai, maza bakwai mata bakwai. Daga dukkan dabbobi marasa tsarki ka ɗauko biyu-biyu. 3 Hakanan daga tsuntsayen sararin sama, ka kawo maza bakwai da mata bakwai daga cikinsu, domin a tanadi irinsu a faɗin duniya. 4 Domin a rana ta bakwai zan sa a yi ruwa a dukkan duniya har kwana arba'in dare da rana. Zan hallakar da dukkan masu rai dana halitta daga fuskar duniya" 5 Nuhu ya yi dukkan abin da Yahweh ya umarce shi. 6 Nuhu yana da shekaru ɗari shida a lokacin da aka yi ruwan tsufana a duniya. 7 Da Nuhu, da 'ya'yansa maza, da matarsa, da matan 'ya'yansa maza suka shiga jirgin saboda ruwan tsufana. 8 Dabbobi masu tsarki da tsuntsaye da duk abu mai rarrafe a ƙasa, 9 biyu-biyu, namiji da mace, suka zo wurin Nuhu suka shiga akwatin, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu. 10 Sai ya zamana bayan kwanaki bakwai, ruwan tsufana ya sauko a duniya. 11 A shekaru ɗari shida na Nuhu, a wata na biyu, a ranar sha bakwai ga wata, a dai wannan ranar, sai dukkan taskoki na zurfafa suka buɗe suka fashe, sakatun sama suka buɗe, 12 Ruwa ya fara sauka a duniya har kwanaki arba'in dare da rana. 13 A wannan ranar dai Nuhu da 'ya'yansa, Shem da Ham da Yafet da matar Nuhu, da matan 'ya'yan Nuhu uku na tare da su, suka shiga jirgin. 14 Suka shiga tare da dukkan dabbobin jeji kowanne bisa ga irinsa, da kuma kowacce irin dabba ta gida bisa ga irinta, da kuma duk abu mai rarrafe da kowaɗanne irin tsuntsaye bisa ga irinsu, da dukkan wata hallitta mai fuka-fukai. 15 Biyu daga dukkan hallitar dake da numfashin rai suka shiga jirgin tare da Nuhu. 16 Dabbobi da dukkan hallitun da suka shiga sun shiga ne kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Yahweh ya kulle ƙofar bayan sun shiga. 17 Sai ruwan tsufana ya sauko a duniya kwanaki arba'in, ruwan kuma ya ƙaru ya ɗaga akwatin sama da ƙasa. 18 Ruwa ya rufe duniya gaba ɗaya jirgin kuma yana ta lilo a saman ruwa. 19 Ruwa ya tumbatsa sosai a duniya har ya rufe dukkan duwatsu dake ƙarƙashin sama. 20 Ruwan ya kai har taki shida a bisa duwatsu 21 Dukkan halittu dake motsi bisa duniya suka mutu; tsuntsaye, da dabbobin gida dana daji, dukkan dabbobi dake da yawa waɗanda ke duniya da kuma dukkan mutane. 22 Da dukkan hallitun dake bisa ƙasa, waɗanda ke da numfashin rai a hancinsu, suka mutu. 23 Kowanne abu mai rai dake bisa duniya an shafe su, daga mutane ya zuwa manyan dabbobobi, da duk masu rarrafe, ya zuwa tsuntsayen sama. Dukkan su an hallakar da su daga duniya. Sai Nuhu da waɗanda ke tare da shi ne suka rage. 24 Ruwan bai janye daga ƙasa ba har kwanaki ɗari da hamsin.

Sura 8

1 Sai Allah ya yi la'akari da Nuhu, da dukkan dabbobin jeji, da dukkan dabbobin gida dake tare da shi a cikin jirgin ruwan. Allah ya sa iska ta hura a kan ƙasa, sai ruwaye suka fara sauka ƙasa. 2 Maɓuɓɓugai na ƙarƙas da sakatun sama aka rufe su, ruwa kuma ya ɗauke. 3 Ambaliyar ruwa kuma ta kwanta sannu a hankali daga ƙasa, bayan kuma kwanaki ɗari da hamsin, sai ruwa ya yi ƙasa. 4 Sai jirgin ruwan ya sami sauka a wata na bakwai, a ranar sha bakwai ga wannan watan, a kan duwatsun Ararat. 5 Ruwan ya ci gaba da sauka har wattanni goma. A rana ta farko ta watan, sai ƙonƙolin duwatsu suka bayyana. 6 Sai ya zamana bayan kwanaki arba'in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin ruwan da ya yi. 7 Ya aiki hankaka ya yi ta kai da komowa har sai da ruwa ya tsane daga duniya. 8 Daga nan sai ya aiki kurciya ta ga yadda ruwan ya tsane daga ƙasa, 9 amma kurciyar ba ta sami wurin sauka ba, sai ta koma gare shi cikin jirgin ruwan, domin har ya zuwa lokacin ruwa na rufe da ƙasa baki ɗaya. Sai ya miƙa hannunsa ya kamo ta ya shigar da ita cikin jirgin ruwan tare da shi. 10 Sai ya jira na tsawon ƙarin kwanaki bakwai, sa'an nan sai ya sake aiken kurciyar daga cikin jirgin ruwan. 11 Kurciyar ta koma wurinsa da yamma. Duba! a cikin bakinta ta tsinko sabon ganyen zaitun. Daga nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga ƙasa 12 Sai ya ƙara jira na waɗansu kwanaki bakwai, sai ya sake aiken kurciyar. Ba ta sake komawa wurinsa ba. 13 Sai ya zamana a shekara ta ɗari shida a farkon shekara, a wata na farko, a ranar farko ta wata, sai dukkan ruwa ya bushe daga dukkan ƙasa. Nuhu ya buɗe rufin jirgin ruwan, ya dudduba ya ga ƙasa ta bushe. 14 A cikin wata na biyu, a ranar ashirin da bakwai ga wata, ƙasa ta bushe. 15 Sai Allah yace da Nuhu, 16 "Ka fito daga cikin jirgin ruwan da kai da matarka da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai. 17 Ka kuma kwaso kowacce halitta mai rai dake tare da kai, da tsutsaye, da dabbobi da duk abin da ke rarrafe a doron ƙasa - domin su hayayyafa, su zama babbar runduna ta masu rai a ko'ina a duniya, su hayayyafa, su ruɓamɓanya a cikin duniya." 18 Sai Nuhu ya fita tare da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa. 19 Da kowacce irin hallitta dake tare da shi da dukkan masu rarrafe da dukkan tsuntsaye da duk wani abu mai motsi bisa duniya, bisa ga irinsu, suka fito daga cikin jirgin ruwan. 20 Nuhu ya gina bagadi ga Yahweh. Ya ɗauki waɗansu daga cikin dabbobi masu tsarki da tsuntsaye masu tsarki ya miƙa hadaya ta ƙonawa da su akan bagadin. 21 Yahweh ya shaƙi ƙanshin hadayar sai ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zan sake la'anta ƙasa saboda mutum ba, koda yake nufe-nufen mutane a zukatansu mugunta ne tun daga yarantakarsu. Ba zan ƙara hallakar da duk masu rai ba kamar yadda na yi. 22 Muddin duniya tana nan, lokacin iri da lokacin girbi, sanyi, da zafi, bazara da damuna, dare da rana ba za su taɓa ƙarewa ba."

Sura 9

1 Sai Allah ya albarkaci Nuhu da 'ya'yansa, ya ce da su, "Ku ruɓanɓanya ku hayayyafa, ku cika duniya. 2 Tsoronku da tsoratarwarku za ta zama a kan dukkan dabbobi masu rai dake duniya, da kowanne tsuntsu dake sararin sama, da duk wani abu dake motsi bisa ƙasa, da dukkan kifayen teku. An bada su a hannunka. 3 Dukkan wani abu mai motsi dake rayuwa zai zama abinci a gare ku. Na baku koren ganyayyaki, yanzu na ba ku kowanne abu. 4 Amma ba za ku ci naman da jininsa da ransa ke cikinsa ba. 5 Amma a bisa jininka, da ran dake cikin jininka, zan bukaci diyya. Daga dukkan dabbobi zan bukace ta. Daga hannun kowanne mutum, wato, mutumin da ya aikata kisan kai ga ɗan'uwansa, 6 zan bukaci bada lissafi na wannan mutum. Duk wanda ya zubar da jinin mutum ta wurin mutum za a zubar da jininsa, domin cikin kammanin Allah aka hallici mutum. 7 Ku kuma, ku hayayyafa, ku ruɓanɓanya, ku warwatsu a ko'ina a duniya, ku ruɓanɓanya a cikinta." 8 Sai Allah ya yi magana da Nuhu da 'ya'yansa dake tare da shi cewa, 9 Amma, "Ka saurara! Zan tabbatar da alƙawarina da ku da zuriyarku dake biye da ku, da kuma 10 dukkan halittu masu rai dake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da kowacce halitta ta duniya dake tare da ku, da kuma duk abin da ya fito daga cikin jirgin, da kuma dukkan halittu masu rai dake duniya. 11 Na tabbatar da alƙawarina da ku, cewa ba zan ƙara hallakar da dukkan halittu da ruwa ba, ba za a sake yin ruwan da zai hallaka duniya ba." 12 Allah yace, "Wannan ce alamar alƙawarin da nake yi tsakanina da ku da dukkan halittun dake tare da ku, domin kuma dukkan tsararraki masu zuwa: 13 Na sa bakangizona a cikin girgije, zai kuma zama alamar alƙawarina da ku da kuma duniya. 14 Zai kuma zamana a lokacin da na sauko da girgije a kan duniya aka kuma ga bakangizo a cikin girgijen, 15 to zan tuna da alƙawarina da ku da dukkan halitta mai rai. Ruwaye ba zasu ƙara zama abin hallakarwa ga mutane ba. 16 Bakangizon zai kasance a cikin girgije, zan kuma gan shi, domin in tuna da alƙawarina madawwami, tsakanin Allah da dukkan halittu masu rai a duniya. 17 "Sai Allah yace da Nuhu, "Wannan ita ce alamar alƙawarin da na tabbatar tsakanina da dukkan masu rai na duniya." 18 'Ya'ya maza na Nuhu da suka fito daga cikin jirgin sune Shem, Ham, da kuma Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana. 19 Waɗannan guda uku sune 'ya'yan Nuhu, daga waɗannan ne aka sami dukkan mutanen duniya. 20 Nuhu ne ya fara zama manomi, ya kuma shuka garkar inabi. 21 Sai ya sha waɗansu 'ya'yan inabin, ya kuma bugu. Yana kwance a cikin rumfarsa tsirara. 22 Sai Ham mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya kuma faɗawa 'yan'uwansa guda biyu a waje. 23 Sai Shem da Yafet suka ɗauki mayafi suka ɗora a kafaɗunsu, suka tafi da baya suka rufe tsiraicin mahaifinsu. Fuskokinsu na fuskantar wani bangon, domin haka ba su ga tsiraicin mahaifinsu ba. 24 Da Nuhu ya tashi daga mayensa, sai ya gane abin da ɗansa ƙarami ya yi masa. 25 Domin haka ya ce, "Kan'ana zai zama la'annanne. Ya zama baran barorin 'yan'uwansa." 26 Hakan nan ya ce, "Yahweh Allah na Shem, ya zama da albarka, Kan'ana kuma ya zama baransa. 27 Allah ya faɗaɗa abin mulkin Yafet, ya kuma sa gidansa a cikin rumfunan Shem. Kan'ana kuma ya zama baransa." 28 Bayan ruwan tsufana, Nuhu ya yi shekaru ɗari uku da hamsin. 29 Dukkan kwanakin Nuhu shekaru ɗari tara ne da hamsin, daga nan ya mutu.

Sura 10

1 Waɗannan sune zuriyar 'ya'yan Nuhu maza, wato Shem da Ham da Yafet. An haifa masu 'ya'ya maza bayan ruwan tsufana. 2 'Ya'yan Yafet maza sune Gomar, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras. 3 'Ya'yan Gomar maza sune Ashkenaz, Rifhat da Togarma. 4 'Ya'yan Yaban maza sune Elisha, Tarshish, Kittim da Dodanim. 5 Daga waɗannan ƙasashe mutane suka watsu suka tafi ƙasashensu, kowanne da nasu harshe bisa ga kabilarsu, da kuma janhuriyunsu. 6 'Ya'yan Ham maza sune Kush, Mizraim, Fut da Kan'ana. 7 "Ya'yan Kush maza sune Seba, Habila, Sabta, Ra'ama da Sabteka. 'Ya'ya maza na Ra'ama sune Sheba da Dedan. 8 Kush ya zama maihaifin Nimrod, wanda shi ne ya fara mamaye duniya. 9 Shi riƙaƙƙen maharbi ne a fuskar Yahweh. Wannan ya sa ake cewa "Kamar Nimrod riƙaƙƙen maharbi a fuskar Yahweh." 10 Wurin mulkinsa na farko shi ne Babila, Erek, Akkad, da Kalne a ƙasar Shinar. 11 Daga cikin ƙasar ya fita zuwa Assiriya ya gina Nineba da Rehobot Ir, Kala, 12 da Resen wadda take a tsakanin Nineba da Kalash. Ita babban birni ce. 13 Mizraim ya zama mahaifin Ludatiyawa, Anamitiyawa, da Lehabiteyawa, Naftuhitawa, 14 Fatrusitiyawa da Kasluhiyatawa (waɗanda daga cikinsu ne Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftoriyawa. 15 Kan'ana ya zama mahaifin Sidom, ɗansa na fari, da kuma Het, 16 har kuma da Yebusawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, 17 Hibiyatawa, da Arkittawa, da Sinitawa, 18 da Arbaditiyawa, da Zemaritiyawa, Hammatiyawa. Bayan haka kabilar Kan'aniyawa ta yaɗu waje. 19 Kan iyakar Kan'ana tana daga Sidon, wajen Gerar har zuwa Gaza da kuma kamar mutum zai yi wajen Sodom, da Gomara, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha. 20 Waɗannan sune 'ya'yan Ham bisa ga kabilarsu, da kuma harsunansu, a cikin ƙasarsu, da al'ummarsu. 21 Hakanan an haifawa Shem 'ya'ya maza, babban ɗan'uwan Yafet. Shem shi ne kãkan dukkan mutanen Eber 22 'Ya'yan Shem maza sune Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da kuma Aram. 23 'Ya'yan Aram maza kuwa sune Uz, Hul, Gezar, da Meshek. 24 Arfakshad ya zama mahaifin Shela, Shela kuma ya haifi Eber. 25 Eber na da 'ya'ya biyu sunan ɗayan shi ne Feleg, domin a cikin kwanakinsa aka raba duniya. Ɗan'uwansa shi ne Yoktan. 26 Yoktan ya zama mahaifin Almodad, Shelef, Hazamabi, Yerah, 27 Hadoram, Uzal, Diklah 28 Obal, Abimawel, Sheba, 29 Ofir, Habila, da Yobab. Duk waɗannan 'ya'ya maza ne na Yoktan. 30 Iyakarsu ta kama daga Mesha, har ya zuwa hanyar Sefhar da tsauni na gabas. 31 Waɗannan sune 'ya'yan Shem maza, bisa ga kabilarsu da harsunansu, a cikin ƙasashensu, bisa ga al'ummarsu. 32 Waɗannan sune kabilar 'ya'yan Nuhu, bisa ga ƙididdigar asali, ta hanyar janhuriyarsu. Daga waɗannan janhuroriyoyi suka rarrabu suka shiga ko'ina a duniya bayan ruwan tsufana.

Sura 11

1 To dukkan duniya sun yi magana da harshe ɗaya, kalmominsu kuma ɗaya ne. 2 Da suka yi tafiya zuwa gabas a hayin filin Shinar suka zauna a can. 3 Suka ce da juna, "Zo mu yi tubula mu gasa su sosai." Suka yi aiki da tubali a madadin dutse, katsi kuma a maimakon yunɓu, 4 "Suka ce, "Ku zo, mu gina wa kanmu birni da kuma hasumiya wadda tsawonta zai kai har sararin sama, kuma mu yi wa kanmu suna. In ba mu yi ba, za a warwatsu mu a fuskar duniya dukka." 5 Sai Yahweh ya zo daga sama domin ya ga birnin da hasumiyar da zuriyar Adamu suka gina. 6 Yahweh yace "Duba su mutane ɗaya ne da harshe ɗaya, kuma sun fara yin wannan! Ba da jimawa ba zasu iya yin duk wani abin da suka yi niyya, ba abin da zai gagare su. 7 Zo, mu sauka mu rikirkitar da harshensu a can, domin kada su fahimci juna." 8 Sai Yahweh ya warwatsa su daga can zuwa ko'ina a duniya, sai kuma suka dena ginin birnin. 9 Domin haka sunansa ya zama Babila, domin a can ne Yahweh ya rikirkitar da harsunan duniya baki ɗaya, kuma daga can ne Yahweh ya watsa mutane ko'ina a sararin duniya. 10 Waɗannan sune zuriyar Shem, Shem na da shekaru ɗari, sai ya zama mahaifin Arfakshad shekaru biyu bayan ruwan tsufana. 11 Shem ya rayu har shekaru ɗari biyar bayan ya haifi Arfakshad. Hakanan ya haifi 'ya'ya maza da mata ma su yawa. 12 Da Arkfashad ya yi shekaru talatin da biyar, sai zama mahaifin Shela. 13 Arkfashad ya rayu na tsawon shekaru 403 bayan ya haifi Shela. Hakanan ya haifi waɗansu sauran 'ya'ya maza da mata. 14 Da Shelah ya kai shekaru talatin, ya haifi Ebar. 15 Shelah ya rayu har shekaru 403 bayan ya haifi Ebar. Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 16 Da Ebar ya yi shekaru talatin da huɗu sai ya haifi Felag. 17 Ebar ya yi shekaru 430 bayan ya haifi Felag, Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 18 Da Felag ya yi shekaru talatin, sai ya haifi Reu, 19 bayan Felag ya haifi Reu ya rayu har shekaru 209, ya kuma haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 20 Da Reu ya kai shekaru 32 sai ya haifi Serug. 21 Reu ya yi shekaru 207 bayan ya haifi Serug. Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 22 Da Serug ya kai shekaru talatin sai ya haifi Nahor. 23 Bayan Serug ya haifi Nahor, ya rayu na tsawon shekaru ɗari biyu sai kuma ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 24 Bayan Nahor ya rayu shekaru ashirin da tara, sai ya zama mahaifin Tera. 25 Nahor ya rayu shekaru 119 bayan ya haifi Tera. Hakanan ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da mata. 26 Bayan Tera ya rayu na tsawon shekaru saba'in sai ya zama mahaifin Abram, da Nahor, da Haran. 27 To waɗannan sune zuriyar Tera, Tera ya haifi Ibram, Nahor, Haran, Haran kuma ya haifi Lot. 28 Haran ya mutu a fuskar mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa. 29 Ibram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Ibram Sarai matar Nahor kuma sunanta Milka, 'yar Haran wanda shi ne mahaifin Milka da Iskah. 30 To Sarai bakarariya ce; ba ta da ɗa. 31 Tera ya ɗauki ɗansa, da Lot ɗan ɗansa Haran, da kuma surukarsa Sarai matar ɗansa Ibram, tare suka bar Ur ta Kaldiyawa, zuwa ƙasar Kan'ana. Amma suka zo Haran suka zauna a can. 32 Tera ya rayu shekaru 205 daga nan ya mutu a Haran.

Sura 12

1 Sai Yahweh yace da Ibram "Ka tashi ka bar ƙasarka da danginka, da kuma ƙasar mahaifinka, zuwa ƙasar da zan nuna maka, 2 zan maishe ka babbar al'umma, zan albarkace ka in kuma sa sunanka ya yi girma, kuma za ka zama albarka. 3 Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, zan kuma la'anta duk wanda ya tozarta ka. Ta wurin ka dukkan al'ummar duniya za ta sami albarka." 4 To Ibram ya tafi, kamar yadda Yahweh ya faɗa masa ya yi, Lot kuma ya tafi tare da shi. Ibram yana da shekaru saba'in da biyar a lokacin da ya tafi ya bar Haran. 5 Ibram ya ɗauki matarsa Sarai, da Lot ɗan ɗan'uwansa da dukkan mallakarsu da suka tara, da kuma dukkan mutanen da suka samu a Haran. Suka tafi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa isa ƙasar Kan'ana. 6 Ibram ya wuce ƙasar har zuwa Shekem, zuwa al'ul na Moreh. A wancan lokacin Kan'aniyawa na zaune a ƙasar. 7 Yahweh ya bayyana ga Ibram, ya ce, "Ga zuriyarka Zan ba da wannan ƙasa." Daga nan Ibram ya gina bagadi domin Yahweh, wanda ya bayyana a gare shi. 8 Daga can ya tafi zuwa ƙasar duwatsu a gabashin Betal, inda ya kafa rumfarsa, ga Betal a yammaci, Ai kuwa a gabashi. A can ya kafa bagadi domin Yahweh, ya kuma yi kira bisa sunan Yahweh. 9 Daga nan Ibram ya ci gaba da tafiya, zuwa wajen Negeb. 10 A kwai yunwa a cikin ƙasar, don haka Ibram ya gangara zuwa Masar ya zauna domin yunwar ta tsananta sosai a cikin ƙasar. 11 Da ya kusa shiga Masar sai ya ce da matarsa Sarai, "Duba na san ke mace ce kyakkyawa. 12 In Masarawa suka gan ki za su ce, 'Wannan matarsa ce; za su kuma kashe ni, amma za su bar ki da rai. 13 Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin komai ya yi mani dai-dai saboda ke, don a bar ni in rayu saboda ke." 14 Sai ya zamana bayan Ibram ya shiga cikin Masar, Masarawa suka ga cewa Sarai kyakkyawa ce. 15 'Ya'yan sarki suka gan ta, suka kuma yaba mata a gaban Fir'auna, sai aka ɗauki matar zuwa gidan sarki. 16 FIr'auna ya kyautatawa Ibram saboda ita, ya ba shi tumaki, takarkarai, da jakai maza da mata da bayi maza da mata da kuma raƙuma. 17 Sai Yahweh ya bugi gidan Fir'auna da annoba mai zafi saboda Sarai matar Ibram. 18 Fir'auna ya kira Ibram ya ce da shi me kenan ka yi mini? Meyasa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ba ce? 19 Meyasa ka ce ita 'yar'uwarka ce; don in ɗauke ta ta zama matata? To yanzu ga matarka nan. Ka ɗauke ta ku tafi." 20 Sai Fir'auna ya bada umarni game da shi daga nan suka sallame shi ya tafi, tare da matarsa da duk abin da yake da shi.

Sura 13

1 Sai Ibram ya bar Masar ya tafi Negeb, shi da matarsa da duk abin da ya mallaka. Lot ya tafi tare da su. 2 Ibram ya wadata sosai ta fannin dabbobi da zinariya da azurfa. 3 Ya ci gaba da tafiya daga Negeb har zuwa wurin da ya kafa rumfarsa a dã baya, tsakanin Betal da Ai. 4 Ya tafi har zuwa inda ya kafa rumfa a baya. A nan ya fara kiran sunan Yahweh. 5 To Lot wanda ke tare da Ibram shi ma yana da garke da sauran bisashe da rumfuna. 6 Ƙasar kuma ta yi masu kaɗan, su da mallakarsu domin suna da mallaka da yawa, saboda haka ba su iya tsayawa a wuri ɗaya ba. 7 Hakanan akwai rashin jituwa tsakanin makiyayan dabbobin Ibram da kuma makiyayan dabbobin Lot. Feriziyawa da Kan'aniyawa ne ke zama a wannan ƙasar a wancan lokacin. 8 Sai Ibram yace da Lot, "bai kamata a sami rashin jituwa tsakanina da kai ba, ko kuma tsakanin makiyayan dabbobina da makiyayan dabbobinka. 9 Fiye ma da haka mu dangi ne, duba ba fili ne nan gabanka ba? Ka zaɓi duk inda kake so, in ka zaɓi hagu, ni sai in zaɓi dama, in ka zaɓi dama ni sai in zaɓi hagu" 10 Sai Lot ya duba yankin Yodan, ya kuma gan shi kore shar har zuwa yankin Zowar, kamar lambun Yahweh, kamar kuma ƙasar Masar. Haka yake kafin a hallaka Sodom da Gomora. 11 Sai Lot ya zaɓi wannan filin na Yodan ya tafi gabas, dangin suka rabu da juna. 12 Ibram ya zauna a ƙasar Kan'ana Lot kuma ya zauna a biranen filin ƙasa. Ya kakkafa rumfunansa har zuwa Sodom, 13 To mutanen Sodom miyagu ne sosai, masu yi wa Yahweh zunubi ne. 14 Yahweh yace da Ibram bayan Lot ya rabu da shi. "Duba daga inda kake tsayuwa zuwa arewa, kudu da gabas da yamma. 15 Dukkan wannan ƙasar da ka ke gani, na bada ita ga zuriyarka har abada. 16 Zan haɓaka zuriyarka ta zama kamar turɓayar ƙasa, domin in har mutum zai iya ƙirga turɓayar ƙasa to zai iya ƙirga zuriyarka. 17 Tashi ka kewaya faɗin ƙasar da tsawonta, domin zan bada ita gare ka. 18 Sai Ibram ya tashi ya ɗauki rumfarsa ya je ya zauna kusa da itatuwan rimayen Mamre, wanda ke a Hebron. A can ya kafa bagadi domin Yahweh.

Sura 14

1 Sai ya zamana a kwanakin Amrafel, sarkin Shinar, Ariyok sarkin El'asar, Kedorlaoma sarkin Elam, da Tidal sarkin Goyim, 2 suka kai yaƙi kan Bera sarkin Sodom, Birsha, sarkin Gomora, Shinab, sarkin Adma, Shemebar, Sarkin Zeboyim, da sarkin Bela (wato wanda ake kira Zowar). 3 Waɗancan sarakuna na baya suka taru a kwarin Siddim (wanda kuma ake kira Tekun Gishiri). 4 Suka bautawa Kedorlawoma shekaru sha biyu, amma a shekara tasha uku suka yi tayawe. 5 A shekara ta sha huɗu kuma, da sarakunan dake tare da shi suka zo suka kawo hari kan Rafaim a Ashterot Karnaim, da Zuzim a Ham, na Emim a Shaba Kiriataim, 6 da Horitiyawa a ƙasar duwatsu ta Se'ir, har zuwa El Faran dake kusa da hamada. 7 Daga nan sai suka juyo suka zo En Mishfat (wadda kuma ake kira Kadesh), suka cinye dukkan ƙasar Amelikawa, da kuma ta Amoriyawa waɗanda ke zama a Hazazon Tamar. 8 Daga nan sai sarkin Sodom, da sarkin Gomora, da sarkin Admah da sarkin Zeboim da sarkin Bela (da ake kira Zowar) suka je suka yi shirin yaƙi 9 găba da Kedorlawomar sarkin Elam, Tidal, sarkin Goim, Amrafel sarkin Shinar, Ariok, sarkin Ellasar; sarakuna huɗu găba da biyar. 10 To kwarin Siddim ya cika da ramukan yaƙi, da sarakunan Sodom da Gomora suka gudu sai suka faɗa cikinsu a can. Waɗanda suka rage suka gudu kan duwatsu. 11 Domin haka maƙiya suka kwashe dukkan kayayyakin Sodom da Gomora suka tafi abin su 12 Da suka tafi, suka kame Lot, ɗan ɗan'uwan Ibram, wanda ke zama a Sodom tare da dukkan malakarsa. 13 Wani da ya tsira ya zo ya gaya wa Ibram Ba'ibirane. Yana zama a gefen rimin Mamre Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, Waɗanda dukkansu abokan Ibram ne. 14 To da Ibram ya ji maƙiya sun kame ɗan'uwansa, sai ya jagoranci horarrun mazajensa guda 318 waɗanda aka haifa a gidansa ya bi su har zuwa Dan. 15 Ya rarrraba mazajensa găba da su a wannan daren ya kai masu hari, ya bi su har zuwa Hoba wadda ta ke arewa da Damaskus. 16 Daga nan ya dawo da dukkan mallakar, ya kuma dawo da ɗan'uwansa Lot da duk kayansa, da mataye da sauran mutane. 17 Bayan Ibram ya dawo daga yin nasara da Kedorlawoma da sarakunan dake tare da shi, sarkin Sodom ya tafi ya tare shi a kwarin Shabe (Wanda kuma ake kira Kwarin Sarki) 18 Melkizedek, sarkin Salem ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki. 19 Ya albarkace shi cewa, Mai albarka ne Ibram ta wurin Allah Mafi Ɗaukaka, Mahallicin sama da duniya. 20 Albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka, wanda ya bada maƙiyanka a hannunka." Sai Ibram ya ba shi kaso ɗaya bisa goma na komai. 21 Sarkin Sodom yace da Ibram, "Ka bani mutane, ka ɗauki kayayyakin domin kanka. 22 "Ibram yace da sarkin Sodom, "Na ɗaga hannunna sama zuwa ga Yahweh, Allah Maɗaukaki, Mahallicin sama da duniya, 23 cewa ba zan ɗauki koda tsinkin zare ko takalmi ko dukkan wani abu dake naka ba, domin kada ka ce, 'Na sa Ibram ya azurta,' 24 Ba zan ɗauki komai ba sai abin da matasa samari suka ci da kuma rabon mazajen dake tare da ni. Let Aner, Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu kason."

Sura 15

1 Bayan waɗannan abubuwa sai maganar Yahweh ta zo wurin Ibram a wahayi, cewa, "Ibram kada ka ji tsoro ni ne garkuwarka da kuma babban ladanka." 2 Ibram yace, ya Ubangiji Yahweh, me za ka bani tunda yake har yanzu bani da ɗa. Magajin gidana kuma Eliyazar ne daga Damaskus," 3 Ibram yace, da yake baka bani zuriya ba, duba, ɗan aikin gida ne ya zama magajina. 4 Sai ga maganar Yahweh ta zo gare shi, cewa "Ba wannan mutumin ne zai gaje ka ba, amma wanda zai fito daga cikin jikinka ne zai zama magajinka." 5 Daga nan sai ya fito da shi waje ya ce, "Duba sama, ka kuma ƙidaya taurari, in za ka iya ƙirga su. Daga nan ya ce da shi, haka zuriyarka za ta zama." 6 Ya yi imani da Yahweh, sai ya lisafta masa shi a matsayin adalci. 7 Ya ce da shi, "Ni ne Yahweh, wanda ya fito da kai daga Ur ta Kaldiyawa, domin in baka wannan ƙasar ka gãje ta." 8 Ya ce ya Ubangiji Yahweh, ta yaya zan sani cewa zan gãje ta?" 9 Daga nan ya ce da shi, "Ka kawo mini bijimi ɗan shekara uku da kuma akuya 'yar shekara uku da kurciya, da tantabara." 10 Ya kawo masa dukkan waɗannan ya kuma datsa su biyu-biyu ya kuma ajiye kowanne tsagi a gefen ɗayan, amma bai raba tsuntsayen ba. 11 Lokacin da tsuntsayen dake yawo suka zo wurin mushen sai Ibram ya kore su. 12 Daga nan bayan rana ta kusa faɗuwa, Ibram ya yi barci mai nauyi, sai ga wani babban duhu mai ban razana ya sha kan shi. 13 Daga nan Yahweh yace da Ibram, hakika ka san cewa zuriyarka zasu yi baƙunci a ƙasar da ba tasu ba, za a kuma bautar da su, a tsananta musu har tsawon shekaru ɗari huɗu. 14 Zan hukunta waccan al'ummar da zasu bauta wa, bayan haka kuma zasu fita da mallaka mai yawa. 15 Amma za ka je wurin ubanninka da salama, kuma za a yi maka jana'iza a shekaru ma su kyau. 16 A cikin tsara ta huɗu zasu sake zuwa nan kuma, saboda muguntar Amoriyawa ba ta kai iyakarta ba tukuna." 17 Da rana ta faɗi dare kuma ya yi, sai ga hayaƙin wuta da kuma harshen wutar tukunya da tartsatsi suka wuce a tsakanin yankin naman. 18 A wannan lokaci Yahweh ya yi yarjejeniya da Ibram cewa ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa tun daga kogin Masar zuwa babban kogin Yuferetis- 19 da Kan'aniyawa da Kanizitawa 20 da Hitiyawa da Feriziyawa da Refatiyawa, 21 da Amoriyawa da Kan'aniyawa da Girgashiyawa da Yebusiyawa."

Sura 16

1 To Sarai, matar Ibram, ba ta haifa masa 'ya'ya ba tukuna, amma tana da baiwa, mutumiyar Masar, sunanta Hajara. 2 To sai Sarai ta ce da Ibram, "Duba Yahweh ya hana mani 'ya'ya, ka je ka kwana da baiwata. Watakila na sami 'ya'ya ta wurinta." Ibram ya saurari muryar Sarai. 3 Bayan Ibram ya yi shekaru goma a Kan'ana ne Sarai ta miƙa baiwarta Hajara ga Ibram a matsayin mata. 4 Sai ya yi tarayya da Hajara ta kuwa yi juna biyu. Da taga ta yi juna biyu sai ta fara duban uwargijiyarta da reni. 5 Daga nan Sarai ta ce da Ibram, "Wannan kuskuren a kaina saboda kai ne. Na bada baiwata gare ka, kuma bayan ta ga ta yi juna biyu, sai aka sayar da ni a idonta. Bari Ubangiji ya shari'anta tsakanina da kai." 6 Amma Ibram yace da Sarai, "Duba ita baiwarki ce, tana ƙarƙashin ikonki, ki yi mata abin da kike tunanin ya fi kyau," Sai Sarai ta takura mata sosai, sai ta gudu daga gare ta 7 Sai mala'ikan Yahweh ya same ta a maɓulɓular ruwa a jeji, wannan maɓulɓular dake kan hanya zuwa Shur. 8 Ya ce da ita, Hajara baiwar Sarai daga ina ki ka zo kuma ina za ki? sai ta ce "ina gujewa uwargijiyata ne Sarai." 9 Mala'ikan Yahweh yace da ita, "Ki koma wurin uwargiyarki, ki miƙa kai ga shugabancinta." 10 Sai mala'ikan Yahweh yace da ita, "Zan ruɓanɓaya zuriyarki sosai, domin su zama da yawa, su wuce ƙirge." 11 Hakanan mala'ikan Yahweh yace da ita, Duba kina ɗauke da juna biyu na ɗa namiji, kuma za ki kira sunansa Isma'ila, saboda Yahweh ya ji ƙuncinki. 12 Zai zama jakin jeji, zai yi magaftaka da dukkan mutane, dukkan mutane kuma na gãba da shi, zai kuma zauna a ware da 'yan, uwansa." 13 Sai ta bada wannan sunan ga Yahweh wanda ya yi magana da ita, "Kai Allah ne mai ganina," domin ta ce, "Ko zan ci gaba da gani, bayanda ya gan ni?" 14 Saboda haka ake kiran rijiyar Beyer Lahai Roi; tana nan tsakanin Kadesh da Bered. 15 Hajara ta haifa wa Ibram ɗa namiji ta ba shi suna Isma'ila. 16 Ibram na da shekaru tamanin da shida a lokacin da Hajara ta haifi Isma'ila.

Sura 17

1 Da Ibram ya kai shekaru tasa'in da tara, lokacin da Yahweh ya bayyana a gare shi ya kuma ce masa, "Ni ne Allah mai iko dukka. Ka yi tafiya a gabana ka zama da rashin laifi. 2 Daga nan zan cika alƙawarina tsakani na da kai, zan kuma kuma ruɓanɓanya ka sosai." 3 Ibram ya sunkuyar da fuskarsa ƙasa sai Allah ya yi magana da shi cewa, 4 "Ni kam, duba, alƙawarina na tare da kai. Zaka zama uban al'ummai masu yawa. 5 Ba za a ƙara kiran sunanka Ibram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim - domin na zaɓe ka ka zama uban al'ummai masu yawa. 6 Zan sa ka ruɓanɓanya sosai, daga cikinka kuma zan samar da al'ummai, daga cikinka kuma za a sami sarakuna. 7 Zan kafa alƙawarina tsakanina da kai da kuma zuriyarka dake biye da kai, a dukkan tsararrakinsu domin alƙawari na har abada, in zama Allah a gare ka da kuma zuriyarka dake biye da kai. 8 Zan bada ƙasar da kake zama gare ka da kuma zuriyarka, dukkan ƙasar Kan'ana domin ta zama mallakarka ta har abada, zan kuma zama Allahnsu." 9 Sai Allah yace wa Ibrahim, "Amma kai dole ka kiyaye alƙawarina, da kai da zuriyarka dake biye da kai a dukkan tsararrakinsu. 10 Wannan shi ne alƙawarina da dole zaka kiyaye, tsakanina da kai da dukkan tsararrakin dake biye da kai: 11 Dole ka yi wa kanka kaciya, kuma wannan nan zai zama alamar alƙawarina da kai. 12 Kowanne ɗa namiji a cikinku da ya kai shekaru takwas, dole ne a yi masa kaciya, a dukkan tsararrakin mutanenka. Wannan ya haɗa da wanda aka haifa a gidanka, da kuma wanda aka saya da kuɗinka daga kowanne irin bãƙo wanda ba ya cikin zuriyarka. 13 Da wanda aka haifa maka da wanda ka saya dole ne ayi masa kaciya. Da haka alƙawarina zai kasance a jikinka domin zama alƙawari na har abada. 14 Duk wani namiji wanda ba shi da kaciya za a fitar da shi daga cikin mutanensa. Ya karya alƙawarina." 15 Allah yace da Ibrahim, "Game da Sarai matarka kuma Kada ka ƙara kiranta Sarai. A maimakon Sarai za a kira sunanta Saratu. 16 Zan albarkace ta, kuma za ta zama uwar al'ummai. Sarakunan mutane za su fito daga cikinta." 17 Daga nan sai Ibrahim ya sunkuyar da fuskarsa ƙasa ya yi dariya, a cikin zuciyarsa ya ce, "Ko za a haifa wa ɗan shekara ɗari ɗa? Ta yaya Saratu wadda ta kai shekaru tasa'in za ta iya haifar ɗa?" 18 Ibrahim yace da Allah, "Ah Isma'ila zai zauna tare da kai!" 19 Allah yace, "A 'a, amma Saratu matarka za ta haifa maka ɗa, kuma za ka ba shi suna Ishaku. Zan kafa alƙawarina da shi wato alƙawari na har abada da zuriyarsa dake biye da shi. 20 Shi kuma Isma'ila na ji ka. Duba na sa masa albarka, zan kuma ruɓaɓɓanya shi zan wadata shi sosai. Zai zama uban kabilu goma sha biyu. Zan kuma mai da shi babbar al'umma. 21 Amma alƙawarina zan kafa shi da Ishaku, wanda Saratu za ta haifa maka baɗi war haka." 22 Da ya gama yi masa magana, sai Allah ya rabu da Ibrahim. 23 Sai Ibrahim ya ɗauki Isma'ila ɗansa, da duk waɗanda aka haifa a cikin iyalinsa, da duk waɗanda ya saya da kuɗinsa da dukkan mazaje na mutanensa duk suka yi kaciya a rana ɗaya kamar yadda Allah ya faɗa masa. 24 Ibrahim yana da shekaru tasa'in da tara lokacin da ya yi kaciya. 25 Ɗansa Isma'ila kuma yana da shekaru sha uku a lokacin da aka yi masa kaciya. 26 A wannan ranar aka yi wa Ibrahim da ishaku kaciya a rana ɗaya. 27 Aka yi masa kaciya tare da dukkan mazajensa, da waɗanda aka haifa masa da waɗanda ya saya da kuɗi daga bãƙi.

Sura 18

1 Yahweh ya bayyana ga Ibrahim a gefen itatuwan rimi na Mamre a lokacin da yake zaune a ƙofar rumfa da tsakar rana. 2 Ya duba sama, sai ga mutane uku na tsaye kewaye da shi. Da ya gan su, sai ya ruga daga ga ƙofar rumfar domin ya gamu da su, ya sunkuya ƙasa. 3 Ya ce, "Ubangiji, in na sami tagomashi a wurin ka, kada ka wuce ka rabu da bawanka. 4 Sai a kawo maku ɗan ruwa, ku wanke ƙafafu, ku kuma shaƙata a ƙarƙashin itace. 5 Sai in kawo maku abinci domin ku sami ƙarfi tun da kun zo wurin bawanku. "Suka amsa, Ka yi kamar yadda ka ce." 6 Sai Ibrahim ya yi hanzari ya shiga rumfa wurin Saratu, ya ce, "Hanzarto ki samo awo uku na gãri ki cuɗa shi ki yi gurasa." 7 Sai Ibrahim ya ruga garke ya ɗauko ɗan maraƙi ƙosasshe ya ba bayinsa su yi sauri su gyara shi. 8 Ya ɗauki curin da madara da maraƙin da aka gyara ya kai musu ya tsaya a gefensu a lokacin da suke ci. 9 Suka ce da shi, "Ina Saratu matarka?" Ya amsa, Ta na can, cikin rumfa," 10 Ya ce, hakika zan komo wurinka baɗi war haka, kuma duba, Saratu matarka za ta sami ɗa." Saratu tana ji a bakin ƙofa cikin rumfa dake bayansa. 11 To Ibrahim da Saratu sun tsufa, shekarunsu sun yi nisa sosai, Saratu kuma ta wuce lokacin da mata ke iya haifar 'ya'ya. 12 Domin haka Saratu ta yi wa kanta dariya, tana cewa da kanta, "Bayan na tsufa, shugabana kuma ya tsufa, ko zan sami wannan jin daɗin?" 13 Yahweh yace da Ibrahim, "Meyasa Saratu ta yi dariya ta kuma ce, "Ko hakika zan iya haifar ɗa Yanzu dana tsufa"? 14 Ko akwai abin da ke da wuya ne ga Yahweh? A daidai lokacin dana sa, kamar war haka, zan komo wurinka a shekara mai zuwa Saratu za ta sami ɗa," 15 Sai Saratu ta yi musu, ta ce "Ban yi dariya ba domin tana jin tsoro. Ya amsa mata ya ce, "A'a, kin yi dariya." 16 Sai mutanen suka tashi suka tashi suka duba wajen Sodom. Sai Ibrahim ya tafi tare dasu ya raka su a kan hanyarsu. 17 Amma Yahweh yace "Ko zan ɓoye wa Ibrahim abin da zan aikata, 18 da yake Ibrahim zai zama babbar al'umma kuma dukkan al'umman duniya zasu sami albarka ta wurinsa? 19 Domin na zaɓe shi domin ya umarci 'ya'yansa da gidansa dake biye da shi domin su bi tafarkin Yahweh, su aikata adalci da aikin adalci, domin Yahweh ya cika abin da ya faɗa wa Ibrahim zai aikata a gare shi." 20 Daga nan sai Yahweh yace, "Saboda kukan Sodom da Gomora ya yi yawa, kuma zunubinsu ya haɓaka, 21 Yanzu zan sauka in ga kukan da ake yi a kan su wanda ya zo gare ni, ko hakika sun aikata al'amarin. In ba haka ba zan sani." 22 To sai mazajen suka juya daga can, suka nufi wajen Sodom, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Yahweh. 23 Sai Ibrahim ya matso ya ce "Ko zaka share adalai tare da mugaye? 24 In a ce za a sami adalai hamsin a cikin birnin. Ko zaka hallaka shi ba tare da la'akari da adalan nan hamsin ba dake can? 25 Ba zai yiwu ba ka yi haka wato ka kashe adalai tare da miyagu, domin a hori adalai kamar yadda aka hori miyagu. Ba zai yiwu ba mai hukunta duniya ya yi abin da ke dai-dai?" 26 Yahweh yace, "In na sami adalai hamsin a cikin birnin Sodom, to zan kuɓutar da dukkan birnin saboda su." 27 Ibrahim ya amsa ya ce, "Duba na jawo wa kaina magana da Ubangijina, koda yake ni ƙura ne kawai da toka! 28 To in ace adalan sun gaza hamsin ba mutum biyar? Zaka hallaka birnin saboda rashin biyar?" Daga nan sai ya ce, "Ba zan hallaka shi ba, in na sami mutane arba'in da biyar." 29 Sai ya sake yi masa magana, ya ce "To a ce za a sami arba'in a can fa?" Ya amsa, "Saboda mutane arba'in ɗin ba zan yi ba." 30 "Ya ce, "Har yanzu dai ina roƙo Ubangiji kada ka yi fushi in na yi magana. To in a ce za a sami talatin a can fa." Ya amsa ba zai yi hakan ba, in a kwai mutane talatin a can." 31 Ya ce "Ga shi na dage in yi magana da Ubangijina! In a ce za a sami ashirin a can fa." Ya amsa "Saboda mutane ashirin ɗin ba zan hallakar da shi ba." 32 Ya ce, "Ina roƙo kada ka yi fushi, Ubangiji, zan sake faɗin wannan karo na ƙarshe. In a ce za a sami goma fa a can." Sai ya ce, "Ba zan hallaka shi ba saboda mutane goman nan." 33 Sai Yahweh ya tafi a lokacin da ya gama yin magana da Ibrahim, shi kuma Ibrahim ya koma gida.

Sura 19

1 Mala'ikun guda biyu suka zo Sodom da yamma, a lokacin da Lot ke zaune a ƙofar Sodom. Da Lot ya gan su sai ya tashi ya tare su, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa. 2 "Ya ce, "Ya shugabannina, ina roƙon ku daku biyo ta gidan baranku, ku kwana ku wanke ƙafafunku. Da safe sai ku tashi ku yi tafiyarku." Suka amsa, "A'a za mu je mu kwana a kwararo." 3 Amma ya yi ta roƙon su, sai suka tafi tare da shi, suka shiga gidansa. Ya shirya musu abinci ya kuma soya musu gurasa marar gami suka ci. 4 Amma kafin su kwanta, mazajen birnin, wato mazajen Sodom, suka kewaye gidan, da tsofaffinsu da matasansu, da dukkan mazajen birnin. 5 Suka kira Lot, suka ce da shi, "Ina mutanen da suka zo gidanka yanzu? Fito da su gare mu, domin mu kwana da su." 6 To sai Lot ya fita wajen ƙofa ya kulle ƙofar a bayansa. 7 Ya ce da su, "Ina roƙon ku 'yan'uwana, kada ku yi aikin mugunta irin wannan. 8 Duba ina da 'ya'ya mata guda biyu da ba su taɓa kwana da maza ba. Ina roƙon ku in kawo muku su, ku yi duk abin da kuka so da su. Amma kada ku yi wa mazajen nan komai, domin suna nan ne a ƙarƙashin kulawata 9 Suka ce, "Ka tsaya can!" Haka kuma suka ce, "Shi da ya zo baƙunta, yanzu kuma ya zama alƙalinmu! Yanzu za mu ci mutuncika fiye da yadda za mu yi musu." Suka matsa wa Lot da kuma mutanen, suka zo kusa da ƙofar domin su ɓarke ta. 10 Amma sai mutanen suka miƙa hannuwansu suka shigo da Lot ciki suka kulle ƙofar. 11 Sai bãƙin na Lot suka bugi mutanen da makanta, wato mutanen dake wajen ƙofar gidan, duk da matasansu da tsofaffinsu duk ƙarfinsu ya ƙare a lokacin da suke ƙoƙarin ɓarke ƙofar 12 Sai mutanen suka ce da Lot, "Ko kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko 'ya'ya maza da mata da duk wanda kake da shi a cikin birnin, ka fitar da su daga birnin nan. 13 Domin mu na gab da hallaka wannan wurin, saboda zargin da ake yi wa birnin a gaban Yahweh ya yi yawa shi ya sa ya aiko mu domin mu hallaka shi." 14 Sai Lot ya tafi ya yi magana da surukansa, wato mazajen da suka yi alƙawari zasu auri 'ya'yansa mata, ya ce "Ku hanzarta, ku fita daga wannan wurin, domin Yahweh na gab da hallaka birnin." Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi. 15 Da safiya ta yi, mala'ikun suka hanzarta Lot, "Ka fito da kai da matarka da 'ya'yanka mata guda biyu dake a wannan wuri, domin kada a share ku tare a cikin wannan hukunci na birni." 16 Amma ya yi jinkiri. Sai mazajen suka kama hannuwansa, da hannun matarsa, da hannuwan 'ya'yansa mata guda biyu, saboda Yahweh ya yi masa jinƙai. Suka fitar dasu bayan birnin. 17 Da suka fitar dasu waje, ɗaya daga cikin mazajen ya ce, "Ku tserar da rayukanku! Kada ku waiga baya, ko kuma ku tsaya a wannan filin. Ku gudu kan duwatsu domin kada a hallakar da ku." 18 Lot yace da su, "A'a shugabannina ina roƙon ku! 19 Baranku ya sami tagomashi a wurinku, kuma kun nuna mini kirki sosai da kuka ceci raina, amma ba zan iya kai wa kan duwatsu ba, masifar za ta same ni, kuma zan mutu. 20 Duba ga wani birni can, ya isa in je can domin tsira, kuma ƙarami ne, ina roƙo ku bar ni in je can in tsira (ba ɗan ƙarami ba ne?), rayuwata kuma za ta cetu." 21 Ya ce da shi, "Shikenan, na biya maka wannan buƙata, kuma ba zan hallaka birnin da ka faɗa ba. 22 Ka yi hanzari ka gudu can, domin ba zan yi wani abu ba sai ka isa can." Shi ya sa ake kiran wurin Zowar. 23 Rana ta ɗaga bisa duniya a lokacin da Lot ya isa Zowar. 24 Sai Yahweh ya saukar da ruwan wuta da matsanancin zafi bisa Sodom da Gomora. 25 Ya hallaka waɗannan biranen, da filayen, da duk mazauna biranen da tsire-tsire da suka yi girma a ƙasa. 26 Amma matar Lot dake bayansa, ta waiwaya baya, sai ta zama umudin gishiri. Ibrahim ya tashi da sassafe ya je wurin da ya tsaya tare da Yahweh. 27 Ya duba wajen Sodom da Gomora da kuma dukkan filayen. 28 Da ya duba sai ya ga hayaƙi na tashi daga filin kamar na hayaƙin matoya. 29 To lokacin da Allah ya hallakar da biranen da filayen, Allah ya tuna da Ibrahim Ya fitar da Lot daga wannan hallakarwar a lokacin da ya hallaka biranen da Lot ya zauna. 30 Amma Lot ya fita daga Zowar zuwa duwatsu tare da 'ya'yansa mata guda biyu, domin yana jin tsoron zama a Zowar. Sai ya zauna a cikin kogon dutse, shi da 'ya'yansa mata guda biyu. 31 Babbar ta ce da ƙaramar, "Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wanda zai kwana damu bisa ga tsarin dukkan duniya. 32 Ki zo, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi ya bugu, sai mu kwana da shi, domin mu wanzar da sunan mahaifinmu." 33 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi ya bugu a wannan daren. Sai babbar ta je ta kwana da mahaifinta, bai ma san lokacin da ta kwanta ba, bai kuma san lokacin da tashi ba. 34 Washegari Sai babbar ta ce da ƙaramar, "Kin ga, jiya na kwana da mahaifina. Yau kuma sai mu sa shi ya sake buguwa da ruwan inabi, ke kuma sai ki je ki kwana da shi, domin mu wanzar da sunan mahaifinmu." 35 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi ya bugu, sai ƙaramar ta je ta kwana da shi. Bai san lokacin da ta kwanta ba haka kuma bai san lokacin da ta tashi ba. 36 Ta haka 'ya'yan Lot guda biyu suka yi juna biyu ta wurin mahaifinsu. 37 Ta farin ta haifi ɗa namji ta sa masa suna Mowab. Shi ne ya zama uban Mowabawa a yau. 38 Ita ma ƙaramar 'yar ta haifi ɗa namiji sai ta ba shi suna Ben Ammi. Shi ne ya zama uban mutanen Ammon na yau.

Sura 20

1 Ibrahim ya bar wurin ya gangara zuwa Negeb, ya zauna tsakanin Kadesh da Shur. Shi baƙo ne mazaunin Gerar. 2 Ibrahim yace game kuma da Saratu matarsa, "Ita 'yar'uwata ce" Sai Abimelek sarkin Gerar ya aika mazajensa suka ɗauko Saratu. 3 Amma Allah ya zo wurin Abimelek a mafarki da duhu, ya ce da shi, "Duba kai mataccen mutum ne saboda matar daka ɗauko, domin ita matar mutumin ce." 4 Abimelek kuma bai kusance ta ba ya ce, "Ubangiji ko zaka kashe har ma al'umma mai adalci? Ashe ba shi da kansa ne ya ce da ni 'ita 'yar'uwataba ce?' 5 Har ma ita da kanta ta faɗa, cewa 'Shi ɗan'uwana ne.' Na yi wannan bisa nagartar zuciyata, da kuma rashin laifofin hannuwana." 6 Sai Allah yace da shi a cikin mafarki, I nima na sani ka yi haka ne bisa ga nagartar zuciyarka, Ni ma kuma na hana ka yi mini zunubi. Saboda haka ne ban bar ka ka taɓa ta ba. 7 Saboda haka ka mayar wa mutumin matarsa domin shi annabi ne. Zai yi maka addu'a kuma za ka rayu. Amma in ba ka mayar da ita ba, ka sani tabbas kai da dukkan abin da ke naka zaku hallaka." 8 Abimelek ya tashi da asuba ya kira dukkan bayinsa gare shi. Ya faɗa musu duk waɗanna abubuwa, sai mazajensa suka firgita. 9 Sai Abimelek ya kira Ibrahim yace da shi, "Me kenan ka yi mana? Yaya nayi maka laifi, da ka jawo wa mulkina da ni kaina wannan zunubi? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba." 10 Abimelek yace da Ibrahim, "Meyasa ka yi wannan abin?" 11 Ibrahim yace, domin na yi tsammanin cewa hakika babu tsoron Allah a wannan wurin, kuma zasu kashe ni saboda matata.' 12 Bayan haka kuma hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina ce, amma ba 'yar mahaifiyata ba, sai kuma ta zama matata. 13 Lokacin da Allah ya sa na bar gidan mahaifina in yi tafiya daga wannan wuri zuwa wancan wuri, na ce da ita dole ne ki nuna mini wannan aminci a matsayin matata: A duk inda muka je ki faɗi haka game da ni, "Shi ɗan'uwana ne."" 14 Sai Abimelek ya kwashi tumaki da takarkari da maza da mata na bayi ya bada su ga Ibrahim. Daga nan ya mayar da Saratu, matar Ibrahim a gare shi. 15 Abimelek yace, "Duba, wannan ƙasar tawa tana gabanka. Ka zauna a duk inda ya yi maka kyau." 16 Ga Saratu kuma ya ce, duba, na ba ɗan'uwanki azurfa dubu. Wannan domin ya shafe duk wani laifi dana yi maku ne a fuskarku dukka, da kuma a gaban kowa da kowa, hakika kun yi abin da ke dai-dai." 17 Sai Ibrahim ya yi addu'a sai Allah ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata domin su iya haifar 'ya'ya. 18 Domin Yahweh yasa dukkan matan gidan Abimelek su zama marasa haihuwa baki ɗaya, Saboda Saratu matar Ibrahim.

Sura 21

1 Yahweh ya saurari Saratu kamar yadda ya ce zai yi, Yahweh kuwa ya yi wa Saratu kamar yadda ya alƙawarta. 2 Saratu kuwa ta yi juna biyu ta haifa wa Ibrahim ɗa a cikin kwanakin tsufansa, a daidai lokacin da Yahweh ya yi masa magana. 3 Ibrahim kuma ya raɗa wa ɗansa suna, wato wannan ɗa da aka haifa masa, wannan da Saratu ta haifa masa wato Ishaku. 4 Ibrahim ya yi wa ɗansa Ishaku kaciya da yayi kwana takwas, kamar dai yadda Allah ya umarce shi. 5 Ibrahim na da shekaru ɗari a lokacin da aka haifa masa Ishaku. 6 Saratu ta ce, "Allah ya sa ni dariya, duk wanda ya ji zai yi dariya tare da ni." 7 Wane ne zai ce da Ibrahim cewa Saratu za ta yi masa renon 'ya'ya, kuma duk da haka na haifa masa ɗa a kwanakin tsufansa!" 8 Yaron ya yi girma aka yaye shi, Ibrahim ya yi babbar liyafa a ranar da aka yaye Ishaku. 9 Saratu ta ga ɗan Hajara Bamasariya, da ta haifa wa Ibrahim, na ba'a. 10 Saboda haka ta ce da Ibrahim, "Ka kori wannan baiwar matar da ɗanta: domin ɗan wannan baiwar ba zai ci gãdo, tare da ɗana Ishaku ba." 11 Wannan abin ya yi wa Ibrahim zafi a rai saboda ɗansa. 12 Amma Allah yace da Ibrahim, "Kada ka damu saboda yaron, da kuma saboda wannan matar baiwarka. Ka saurari kalmominta kan duk abin da ta faɗa maka kan wannan al'amari, saboda ta wurin Ishaku ne za a kira zuriyarka. 13 Hakanan zan sa ɗan baiwar matar ya zama al'umma, domin shi zuriyarka ne." 14 Ibrahim ya ta shi da asuba, ya ɗauki gurasa da goran ruwa, ya ba da shi ga Hajara ya ɗora shi a kafaɗarta. Ya ba ta ɗan ya sallame ta ta tafi. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Beyersheba. 15 Da ruwan da ke cikin goran ruwan ya ƙare, sai ta yashe da ɗan a gindin wasu ciyayi. 16 Sai ta tafi ta zauna can nesa dai-dai harbin kibiya, domin ta ce, "Kada in ga mutuwar ɗana." Da ta zauna daura da shi sai ta ta da murya ta yi kuka. 17 Allah ya ji kukan ɗan, sai mala'ikan Allah ya kira Hajara daga can sama, ya ce da ita, "Me ke damun ki, Hajara? Kada ki ji tsoro, domin Allah ya ji kukan ɗan a inda yake. 18 Tashi ki ɗauki yaron, ki ƙarfafa shi, domin zan maishe shi babbar al'umma." 19 Sai Allah ya buɗe idanunta, sai ta ga rijiyar ruwa. ta je ta cika gorar da ruwa, ta ba ɗan ya sha. 20 Allah na tare da ɗan, ya kuma yi girma. Ya yi rayuwa cikin jeji sai ya zama mafarauci. 21 Ya yi rayuwa a jejin Faran, mahaifiyarsa kuma ta aura masa mata daga ƙasar Masar 22 Sai ya zamana a lokacin da Abimelek da Fikol shugaban sojojinsa ya yi magana da Ibrahim, cewa, "Allah na tare da kai a cikin dukkan al'amuranka. 23 Yanzu sai ka rantse mini cewa ba zaka yi mini ƙarya ba, haka kuma 'ya'yana, da zuriyata. Ka nuna mini da kuma ƙasar da kake zaune a ciki irin wannan alƙawari mai aminci da na nuna gare ka." 24 Ibrahim yace "Na rantse." 25 Ibrahim kuma ya miƙa kukansa ga Abimelek game da rijiyar ruwa da bayin Abimelek su ka ƙwace daga wurinsa. 26 Abimelek yace "Ban san wanda ya yi wannan abu ba. Ba ka faɗa mini ba tuntuni; Ban ji al'amarin ba sai yau." 27 Sai Ibrahim ya ɗauki tumaki da shanu ya ba Abimelek, su biyun suka yi yarjejeniya. 28 Sai Ibrahim ya ware raguna bakwai na garken da kansu. 29 Abimelek yace da Ibrahim, "Mene ne ma'anar waɗannan matan tumakin daka shirya su da kansu?" 30 Ya amsa, waɗannan matan tumakin guda bakwai zaka karɓa daga hannuna, domin su zama shaida domina, cewa ni na haƙa wannan rijiya." 31 Sai ya kira wannan wurin Biyasheba, saboda a can ne dukkan su suka yi rantsuwa. 32 Suka yi yarjejeniya, Daga nan sai Abimelek da Fikol, shugaban sojojinsa, ya koma ƙasar Filistiyawa. 33 Ibrahim ya dasa itacen sabara a Biyasheba. a can ya yi sujada ga Yahweh, Allah madawwami. 34 Ibrahim ya zauna a matsayin baƙo a ƙasar filistiyawa na kwanaki masu yawa.

Sura 22

1 Sai ya zamana bayan waɗannan abubuwa Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce da shi, "Ibrahim" Ibrahim yace, "Ga ni nan," 2 Sai Allah yace, "Ka ɗauki ɗanka, tilon ɗanka, wanda kake ƙauna, Ishaku, sai ku je ƙasar Moriya. A can za ka miƙa shi baiko na ƙonawa akan ɗaya daga cikin duwatsun dake can, wanda zan faɗa maka game da shi." 3 Sai Ibrahim ya tashi da asuba ya ɗaura wa jakinsa sirdi, ya kuma ɗauki biyu daga cikin matasan mazajensa tare da shi, haɗe kuma da Ishaku ɗansa. Ya sassari itace domin baiko na ƙonawa, daga nan ya kama hanyarsa zuwa inda Allah ya faɗa masa. 4 A rana ta uku Ibrahim ya duba sama sai ya hangi wurin daga nesa. 5 Sai Ibrahim yace da matasansa, "Ku tsaya nan da jakin, ni da yaron zamu haura can. Za mu yi sujada daga nan sai mu dawo wurinku." 6 Sai Ibrahim ya ɗauki itace domin hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa Ishaku ɗansa. Sai ya ɗauki wuƙa da wuta a hannunsa; sai kuma suka tafi tare. 7 Ishaku ya yi magana da Ibrahim mahaifinsa ya ce, "Babana," sai ya ce, "Ga ni nan ɗana." Ya ce, Ga wuta anan da itace, amma ina ɗan ragon baikon ƙonawa?" 8 Ibrahim yace, "Ɗana Allah da kansa zai tanada ɗan rago domin baikon ƙonawa." Sai suka ci gaba da tafiya tare su dukka. 9 Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, Sai Ibrahim ya gina bagadi a can ya zuba itace a kansa. Sai ya ɗaure ɗansa Ishaku, ya ɗora shi akan bagadin bisa itacen. 10 Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauko wuƙa domin ya yanka ɗansa. 11 Sai mala'ikan Yahweh ya kira shi daga sama ya ce, "Ibrahim, Ibrahim!" sai ya ce, "Ga ni nan." 12 Ya ce, "Kada ka ɗora hannunka a kan yaron, kar ka yi duk wani abu da zai cutar da shi, domin yanzu na sani kana tsoron Allah, ganin cewa ba ka hana mini ɗanka ba, tilon ɗanka." 13 Ibrahim ya duba sama, sai ga ɗan rago a sarƙafe da ƙahonsa. Ibrahim ya ɗauki ɗan ragon ya miƙa shi baiko na ƙonawa a maimakon ɗansa. 14 Saboda haka Ibrahim ya kira wurin, "Yahweh zai tanada," haka kuma ake kiran wurin har yau,"A kan tsaunin Yahweh za a tanada shi." 15 Mala'ikan Yahweh ya kira Ibrahim daga sama a karo na biyu 16 ya ce - wannan shi ne furcin Yahweh - na yi rantsuwa da kaina cewa da yake ka yi wannan abu, ba ka hana ɗanka ba tilon ɗanka, 17 Hakika zan albarkace ka zan kuma ruɓanɓanya zuriyarka kamar taurarin sammai, kamar kuma yashin dake gaɓar teku; zuriyarka kuma zasu mallaki ƙofar maƙiyansu. 18 Ta wurin tsatsonka za a albarkaci dukkan al'ummar duniya, saboda ka yi biyayya da muryata." 19 Sai Ibrahim ya koma wurin barorinsa, suka tafi Beyarsheba tare sai ya zauna a Beyarsheba. 20 Ya zamana bayan waɗannan abubuwa sai, aka ce da Ibrahim "Milka ta haifi 'ya'ya, haka kuma ɗan'uwanka Nahor." 21 Su ne Uz ɗansa na fari, Buz shi ne ɗan'uwansa, Kemuwal shi ne mahaifin Aram, da 22 Kesed da Hazo, da Fildash da Yidlaf da Betuwel. 23 Betuwel ya haifi Rebeka. Waɗannan sune 'ya'ya takwas da Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim. 24 Ƙwarƙwararsa mai suna Reuma ita ma ta haifi Tebah da Gaham Tahash da Ma'aka.

Sura 23

1 Saratu ta rayu tsawon shekaru ɗari da ashirin da bakwai. Waɗannan sune shekarun Saratu. 2 Saratu ta mutu a Kiriyat Arba wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim ya yi makoki da kuka domin Saratu. 3 Sai Ibrahim ya tashi ya bar wurin da matarsa ta mutu, ya yi magana da 'ya'yan Het, cewa. 4 "Ni bãƙo ne a cikin ku Ina roƙo ku bani mallakar wurin maƙabarta a cikinku domin in bizne matattuna." 5 Sai 'ya'yan Het suka amsa wa Ibrahim cewa, 6 "Ka saurare mu shugabana. Kai yariman Allah ne a cikin mu. Bizne matattunka a duk inda ka zaɓa a maƙabartunmu, ba wanda zai hana maka maƙabartarsa domin ka bizne matattunka." 7 Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna wa mutanen ƙasar, ga "ya'yan Het. 8 Ya yi musu magana cewa, "In kun yarda cewa in bizne matacciyata, sai ku saurare ni ku roƙi Ifron ɗan Zohar domi na. 9 Ku tambaye shi ya sayar mini da kogon Makfela, wadda ya mallaka, wadda yake a ƙarshen filinsa. Domin cikakken farashi ya kuma sayar mini da shi a gaban mutane domin ya zama mallakata, da maƙabarta." 10 Ifron kuma na zaune a cikin 'ya'yan Het, sai Ifron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan 'ya'yan Het maza da kuma duk waɗanda suka zo ƙofar birninsa, cewa, 11 "A'a shugabana, ka saurare ni. Na baka filin da kuma kogon dake cikinsa. Na baka shi a gaban 'ya'yan mutanena maza. Na baka shi domin bizne matacciyarka." 12 Sai Ibrahim ya sunkuyar da kansa ƙasa a gaban mutanen ƙasar. 13 Ya yi magana da Ifron a kunnen mutanen ƙasar cewa. "Amma in ka amince, inka yarda ka saurareni. Zan biya kuɗin filin. Ka karɓi kuɗi daga wuri na, ni kuma zan bizne mattaciyata a can." 14 Ifron ya amsa wa Ibrahim, da cewa, 15 "Ina roƙo, ya shugabana, ka saurare ni.‌ Ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu na azurfa, mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka bizne mamaciyarka." 16 Ibrahim ya saurari Ifron, ya auna shekel ɗari huɗu kamar yadda Ifron ya ambata a kunnuwan dukkan 'ya'yan Het maza, mudu ɗari huɗu na zinariya, bisa ga mizanin ma'aunin fatake. 17 Domin haka filin Ifron dake a Makfela wanda ke gaban Mamre, wato da filin da kogon dake cikinsa, da duk itatuwan dake cikin filin, da dukkan iyakarsa, 18 aka ba Ibrahim tawurin sayarwa a gaban 'ya'yan Het maza, da kuma duk waɗanda suka zo ƙofar birninsa. 19 Bayan wannan Ibrahim ya bizne Saratu matarsa a cikin kogon filin Makfela, wanda ke gaba da Mamre wato Hebron, a cikin ƙasar Kan'ana. 20 Domin haka da filin da kogon dake cikinsa aka miƙa su ga Ibrahim daga 'ya'yan Het maza domin ya zama maƙabarta.

Sura 24

1 Ya zamana kuma Ibrahim ya tsufa ainun, kuma Yahweh ya albarka ce shi a cikin komai. 2 Sai Ibrahim yace da baransa, wanda ya fi daɗewa da kuma ke kula da komai da ya mallaka, ya ce "Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, 3 zan sa ka ka rantse da Yahweh, Allah na sama da kuma Allah na duniya, cewa ba zaka auro wa ɗana mata daga cikin Kan'aniyawan da nake zama a cikinsu ba. 4 Amma zaka je cikin ƙasata da dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata daga can." 5 Sai baran yace da shi, "To yaya kenan, in matar ta ce ba za ta biyo ni zuwa wannan ƙasar ba fa? Ko ya zama tilas in mayar da ɗanka zuwa ƙasar da ka baro?" 6 Ibrahim yace da shi, "Ka tabbata cewa ba ka komar da ɗana can ba! 7 Yahweh Allah na sama, wanda ya ɗauko ni daga gidan mahaifina da kuma ƙasar dangina, wanda kuma ya yi mini tabbataccen alƙawari cewa, 'Ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa,' zai aiko mala'ikansa a gabanka, kuma zaka samo wa ɗana mata daga can. 8 Amma in matar ba ta son ta biyo ka, to ka kuɓuta daga rantsuwata, kada ka komar da ɗana can," 9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyoyin Ibrahim shugabansa, ya yi masa rantsuwa game da wannan al'amari. 10 To sai baran ya ɗauki raƙuma goma na shugabansa ya tafi. Haka nan ya ɗauki duk waɗansu kyaututtuka da suka kamata daga wurin shugabansa ya tafi da su yankin Aram Naharaim zuwa birnin Nahor. 11 Ya sa raƙuman suka kwakkwanta a gefen rijiyar ruwa. Da yamma ne daidai lokacin da mata ke fita ɗiban ruwa. 12 Daga nan sai ya ce, "Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, ka ba ni nasara a yau ka kuma nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim. 13 Duba yanzu ina tsaye a bakin ƙoramar ruwa, kuma 'yan'matan mutanen birnin suna fitowa domin su ɗibi ruwa. 14 Ka sa abin ya kasance kamar haka. In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha; sai kuma ta ce da ni, ka sha, zan kuma shayar da raƙumanka ma; to bari ta zama matar daka nufa ta zama matar bawanka Ishaku. Da haka zan sani cewa ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana." 15 Sai ya zamana kafin ma ya gama magana sai ga Rebeka ta zo da abin ɗiban ruwanta a kafaɗarta. Rebeka 'yar Betuwel ce ɗan Milka, matar Nahor, ɗan'uwan Ibrahim. 16 Budurwar kyakkyawa ce kuma ba ta ɓata budurcinta ba. Ba mutumin da ya taɓa kwana da ita. Sai ta tafi ƙoramar ta cika abin ɗiban ruwanta, ta hauro. 17 Sai baran ya yi gudu domin ya gamu da ita ya ce, "Ina roƙo ki sam mani ruwa in ɗan sha daga cikin abin ɗiban ruwanki." 18 Ta ce ya shugabana ka sha sai ta yi sauri ta sauke abin ɗiban ruwan ƙasa a hannunta ta ba shi ya sha. 19 Bayan ta gama ba shi ya sha, sai ta ce, "Zan ɗebowa raƙumanka ma su sha har sai sun kammala sha." 20 Sai ta yi sauri ta juye abin ɗebo ruwan, ta yi gudu ta sake komawa rijiyar domin ta ɗebo ruwa domin dukkan raƙumansa. 21 Sai mutumin ya dube ta a natse domin ya gani ko Yahweh ya ba tafiyarsa nasara ko kuwa a'a. 22 Bayan raƙuman sun gama shan ruwan, sai mutumin ya ciro zoben zinariya na hanci mai nauyin rabin ma'auni, da ƙarau guda biyu na azurfa na sawa a dantse wanda ya kai nauyin ma'auni goma, 23 sai ya tambaya, "Ke "yar wane ne? Ina roƙon ki ki faɗa mini, ko akwai masauki a gidan mahaifinku da za mu kwana?" 24 Ta ce da shi, "Ni 'yar Batuwel ce ɗan Milka wanda ta haifawa Nahor." 25 Ta kuma ce da shi muna kuma da ciyawa da abincin dabbobi da kuma ɗaki domin ku kwana." 26 Sai mutumin ya sunkuya ƙasa ya yi sujada ga Yahweh. 27 Ya ce, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, wanda bai yashe da alƙawarinsa mai aminci ba da kuma amincinsa ga shugabana. Ni da kaina Yahweh ya bi da ni kai tsaye zuwa gidan dangin shugabana." 28 Sai budurwar ta yi gudu ta je ta faɗa wa iyalin gidan mahaifiyarta duk abin da ya faru dangane da waɗannan al'amura. 29 Rebeka kuma tana da ɗan'uwa, sunansa Laban. Sai Laban ya ruga zuwa wurin mutumin wanda ke can kan hanyar ƙoramar. 30 Da ya ga wannnan zobe na hanci da ƙarau na dantse a dantsen 'yar'uwarsa, kuma bayan ya ji duk abin da Rebeka 'yar'uwarsa ta faɗa, "Wannan shi ne abin da mutumin ya ce da ni," sai ya tafi wurin mutumin, sai ga shi a tsaye a gefen raƙuma a wurin ƙoramar. 31 Sai Laban yace, "Zo, kai mai albarka na Yahweh. Meyasa kake tsayuwa a waje? Na shirya gida da kuma wuri domin raƙuman." 32 Sai mutumin ya zo gidan ya kuma sauke wa raƙuman kaya. Sai aka ba raƙuman ciyawa da abincin dabbobi aka kuma tanadi ruwa domin ya wanke ƙafafunsa da kuma na mutanen dake tare da shi. 33 Suka kawo masa abinci domin ya ci, amma ya ce, "Ba zan ci ba sai na faɗi abin da zan faɗa. "Sai Laban yace to faɗi abin da zaka faɗa." 34 Ya ce, "Ni baran Ibrahim ne. 35 Yahweh ya albarkaci shugabana sosai ya kuma yi girma sosai. Ya ba shi garkuna da dabbobi da zinariya da azurfa, da bayi maza da mata da raƙuma da jakuna. 36 Saratu matar shugabana ta haifi ɗa ga shugabana a lokacin da ya tsufa, ya kuma bayar da duk abin da ya mallaka gare shi. 37 Shugabana ya sa na rantse, cewa, 'Ba za ka auro wa ɗana mata daga cikin 'yanmatan Kan'aniyawa ba, waɗanda a ƙasarsu na yi gidana. 38 Maimakon haka dole ka je wajen dangin mahaifina, cikin 'yan'uwana ka samo wa ɗana matar aure.' 39 Na ce da shugabana, in a ce matar ba zata biyo ni ba fa.' 40 Amma ya ce da ni, Yahweh wanda nayi tafiya a gabansa, zai aiko mala'ikansa ya kasance tare da kai ya kuma baka nasara bisa tafiyarka, domin ka auro wa ɗana mata daga cikin dangina da kuma iyalin mahaifina. 41 Amma zaka kuɓuta daga rantsuwata in ka zo wurin 'yan'uwana in ba su baka ita ba. To zaka kuɓuta daga rantsuwata.' 42 To da na kawo wurin ƙorama, na ce, 'Ya Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, ina roƙon ka, in har ka so ka ba tafiyata nasara- 43 gani nan a tsaye a bakin ƙorama-ka sa budurwar da ta zo ɗiban ruwa, wato macen da zan ce, "Ina roƙo ki ɗan san mani ruwa in sha daga abin ɗiban ruwanki," 44 macen da ta ce da ni, "Sha, zan kuma shayar da raƙumanka"_Bari ta zama macen da kai, Yahweh, ka zaɓa domin ɗan shugabana.' 45 Tun ma kafin in gama magana a cikin zuciyata, sai ga, Rebeka ta zo da abin ɗiban ruwanta a kafaɗarta sai ta gangara ƙoramar ta ɗebo ruwa. Sai na ce da ita, 'Ina roƙo ki bani ruwa in sha.' 46 Sai ta yi sauri ta sauko da abin ɗiban ruwan daga kafaɗarta ta ce, 'Ka sha, zan kuma shayar da raƙumanka.' Sai na sha, ta kuma shayar da raƙuman. 47 Na tambaye ta cewa, 'Ke 'yar wane ne?' Ta ce, 'Yar Betuwel, ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.' Daga nan sai na sa zoben a hancinta da kuma ƙarau a damtsenta. 48 Sai na sunkuya na yi sujada ga Yahweh, na albarkaci Yahweh Allah na shugabana Ibrahim, wanda ya bishe ni a madaidaiciyar hanya domin in sami 'yar dangin shugabana domin ɗansa. 49 Yanzu kuma, in kuna shirye ku nuna zumunci mai aminci da amana, ku faɗa mini. Amma in ba haka ba, ku faɗa mini, domin in bi dama ko hagu." 50 Sai Laban da Betuwel suka amsa suka ce, Al'amarin daga Yahweh ya zo; ba zamu iya ce maka ya yi kyau ko bai yi kyau ba. 51 Duba Rebeka na gabanka. Ɗauke ta ku tafi, domin ta zama matar ɗan shugabanka, kamar yadda Yahweh ya faɗa." 52 Da baran Ibrahim ya ji maganarsu, sai ya sunkuyar da kansa ƙasa ga Yahweh. 53 Sai baran ya fito da kayayyaki na zinariya da azurfa da sutura ya miƙa su ga Rebeka. Hakanan ya bada kyautai masu daraja ga ɗan'uwanta da kuma mahaifiyarta. 54 Daga nan shi da mazajen dake tare da shi suka ci, suka sha. Suka kwana har gari ya waye, bayan sun tashi da safe, ya ce "Ku sallame ni zuwa gun shugabana." 55 Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, "Bari budurwar ta ɗan yi waɗansu 'yan kwanaki kamar goma tukuna. Bayan nan za ta iya ta tafi." 56 Amma ya ce da su kada ku hana ni da yake Yahweh ya sa tafiyata ta yi nasara. Ku sallame ni domin in koma wurin shugabana." 57 Suka ce za mu kira budurwar mu tambaye ta." 58 Sai suka kira Rebeka suka tambaye ta, "Za ki tafi tare da wannan mutumin?" Ta amsa "zan tafi." 59 Sai suka aika 'yar'uwarsu Rebeka, tare da baranyarta, a cikin tafiyarta tare da baran Ibrahim da mazajensa. 60 Suka albarkaci Rebeka, suka ce da ita, "Yar'uwarmu, muna addu'a ki zama uwar dubun dubbai goma, da ma zuriyarki ta mallaki ƙofar maƙiyansu." 61 Sai Rebeka ta tashi, ita da barorinta mata suka hau raƙuma, suka bi mutumin. Da haka baran ya ɗauki Rebeka ya yi tafiyarsa. 62 Ya zamana Ishaku na zama a Negeb, ya dawo kenan daga Beyerlahairoi. 63 Ishaku ya fita domin yin nazari a saura da yammaci. Da ya duba tudu, ya hanga, sai ya ga raƙuma na tafe! 64 Rebeka ta duba, da ta ga Ishaku sai ta diro daga kan raƙumin. 65 Ta ce da baran, "Wane ne wancan dake tafiya a cikin saura domin ya tarbe mu?" Baran yace, "'Shugabana ne." Sai ta ɗauki gyale ta yi lulluɓi. 66 Baran ya zaiyana wa Ishaku dukkan abin da ya yi. 67 Sai Ishaku ya kawo ta rumfar mahaifiyarsa Saratu ya ɗauki Rebeka, ta zama matarsa, ya kuma ƙaunace ta. Da haka Ishaku ya ta'azantu bayan mutuwar mahaifiyarsa.

Sura 25

1 Sai Ibrahim ya auro wata mata mai suna Ketura. 2 Ta haifa masa Zimra, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak, da Shuwa. 3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Asiriya, da mutanen Letush, da mutanen Leyum. 4 'Ya'yan Midiyan sune Efa, Efer, Hanok, Abida, da Elda'ah. Duk waɗannan sune zuriyar Ketura. 5 Ibrahim ya mallaka duk abin da yake da shi ga Ishaku. 6 Duk da haka, a lokacin da yake raye ya ba da kyautai ga 'ya'yan ƙwaraƙwaransa ya aika su ƙasar gabas nesa da ɗansa Ishaku. 7 Waɗannan sune kwanakin shekarun rayuwar Ibrahim da ya yi shekaru, 175. 8 Ibrahim ya yi numfashinsa na ƙarshe ya mutu a cikin kyakkyawan tsufa, tsohon mutum mai cike da kuzari, sai aka tattara shi ga mutanensa. 9 Ishaku da Isma'ila, 'ya'yansa suka bizne shi a kogon Makfela, a filin Ifron ɗan Zohar Bahitte, wadda ke kusa da Mamre. 10 Wannan filin Ibrahim ya saya daga'ya'yan Het maza. A can aka bizne Ibrahim da matarsa Saratu. 11 Bayan mutuwar Ibrahim Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku, Ishaku ya zauna kusa da Beyer Lahai Roi. 12 To Waɗannan sune zuriyar Isma'ila ɗan Ibrahim, da Hajara Bamasariya baiwar Saratu, ta haifa wa Ibrahim. 13 Waɗannan sune sunayen 'ya'yan Isma'ila bisa ga tsarin haihuwarsu: Nebaiyot - shi ne ɗan fari na Isma'ila, da Kedar, da Adbe'el, da Mibsam, 14 da Mishma, da Massa, 15 Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema. 16 Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ila, kuma waɗannan sune sunayensu bisa ƙauyukansu, suna kuma da sarakuna sha biyu bisa ga kabilarsu. 17 Waɗannan su ne shekarun rayuwar Isma'ila, shekaru, 137 ya yi numfashinsa na ƙarshe sa'an nan ya mutu, sai aka tattara shi ga mutanensa. 18 Sun yi rayuwa daga Habila zuwa Ashur, wadda take kusa da Masar, ɗaya kuma ya nufi Asiriya. Sun yi zaman tankiya da juna. 19 Waɗannan su ne al'amura game da Ishaku, ɗan Ibrahim: Ibrahim ya haifi Ishaku. 20 Ishaku nada shekaru arba'in a lokacin da ya ɗauki Rebeka a matsayin matarsa, 'yar Betuwel mutumin Aramiya ta Faddan Aram, 'yar'uwar Laban na Aramiya. 21 Ishaku ya yi addu'a ga Yahweh domin matarsa saboda ba ta da ɗa, Yahweh kuma ya amsa addu'arsa, Rebeka matarsa kuma ta yi juna biyu. 22 'Ya'yan na ta fama tare tun daga cikinta, sai ta ce, "Meyasa wannan ke faruwa da ni?" Ta je ta tambayi Yahweh game da haka. 23 Yahweh yace da ita, "Al'umma biyu ce a mahaifarki, mutane biyu kuma zasu rabu daga gare ki. Ɗaya jama'ar za ta fi ɗayar ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin." 24 Da lokacin haihuwarta yayi, sai ta kasance da 'yan biyu a mahaifarta. 25 Na farkon ya fito da gargasa a ko'ina kamar tufafin gashi. Suka kira sunansa Isuwa. 26 Bayan haka, ɗan'uwansa ya fito hannuwansa na‌ riƙ‌e da diddigen Isuwa. Sai aka kira shi Yakubu. Ishaku na da shekaru sittin lokacin da matarsa ta haifa masa su. 27 Samarin suka yi girma, Isuwa ya zama shahararren mafarauci mai yawo a saura; amma Yakubu mai shiru-shiru ne, wanda ya kashe lokacinsa cikin runfofi. 28 Sai ishaku ya ƙaunaci Isuwa domin yakan ci namomin jejin da ya harbo, amma Rebeka ta ƙaunaci Yakubu. 29 Yakubu ya shirya ɗan dage-dage. Isuwa ya zo daga saura, ya kuma raunana saboda yunwa. 30 Isuwa yace da Yakubu, "Ka ciyar da ni da dage-dagenka mana. Ina roƙonka ƙarfina ya ƙare!" Shiyasa aka kira sunansa Idom. 31 Yakubu yace, "Da farko ka sayar mani da matsayinka na ɗan fari tukuna." 32 Isuwa yace, "Duba, Na kusa mutuwa. Wanne amfani ne matsayin ɗan fari ke da shi a gare ni?" 33 Yakubu yace, "Da farko sai ka rantse mani" ta haka Isuwa ya yi rantsuwa kuma ta haka Isuwa ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yakubu. 34 Yakubu ya ba Isuwa dage-dagen wake da gurasa. Ya ci ya sha, daga nan ya tashi ya tafi abinsa. Ta wannan hali Isuwa ya banzantar da matsayinsa na ɗan fari.

Sura 26

1 Sai aka yi yunwa a ƙasar, bayan wacce aka yi ta fari a kwanakin Ibrahim, Ishaku ya tafi wurin Abimelek, sarkin Filistiyawa a Gerar. 2 Sai Yahweh ya bayyana gare shi ya ce, "Kada ka gangara Masar; ka zauna a ƙasar dana ce ka zauna a ciki. 3 Ka zauna a wannan ƙasar, zan kasance tare da kai, in kuma albarkace ka; domin a gare ka da zuriyarka ne zan bayar da ƙasashen al'ummai, kuma zan cika alƙawarin dana yi wa Ibrahim mahaifinka. 4 Zan ruɓanɓanya zuriyarka kamar taurarin sama zan kuma bada waɗannan ƙasashe ga zuriyarka. Ta wurin al'ummarka dukkan ai'umman duniya zasu sami albarka. 5 Zan yi wannan domin Ibrahim ya yi biyayya da muryata ya kuma kiyaye dokokina, da farillaina, da shari'una. da ka'idodina." 6 Don haka Ishaku ya zauna a Gerar. 7 Da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, "Ita 'yar'uwata ce". Ya ji tsoro ya ce, "Ita matata ce," saboda ya yi tunanin cewa, mutanen zasu kashe ni su ɗauke Rebeka domin ita kyakkyawa ce." 8 Bayan Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba ta taga. Sai ya ga Ishaku na shafa Rebeka, matarsa. 9 Abimelek ya kira Ishaku gare shi ya ce, "Duba hakika ita matarka ce. Don me ka ce, ita 'yar'uwata ce'?" Ishaku yace da shi, "Saboda na yi tsammanin wani zai iya ya kashe ni don ya same ta." 10 Abimelek yace, "Me kenan ka yi mana? Da kuwa wani ya kwana da matarka cikin sauƙi, da kuma ka jawo mana laifi." 11 Sai Abimelek ya gargaɗi mutene ya ce, "Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa hakika za a kashe shi." 12 Ishaku ya shuka hatsi a waccan ƙasar, ya kuma yi girbi a wannan shekara, ya sami riɓi ɗari, saboda Yahweh ya albarkace shi. 13 Mutumin ya azurta, ya dinga bunƙasa sosai har sai da ya yi girma sosai. 14 Yana da tumakai masu yawa da dabbobi, da iyalai masu yawa. Filistiyawa suka yi kishinsa. 15 To dukkan rijiyoyin da barorin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin Ibrahim mahaifinsa, Filistiyawa suka cike su da ƙasa. 16 Abimelek yace da Ishaku, "Ka tafi ka ba mu wuri, domin ka fi mu ƙarfi." 17 Sai Ishaku ya bar garin ya koma Kwarin Gerar ya zauna a can. 18 Haka kuma Ishaku ya tone rijiyoyi na ruwa waɗanda aka haƙa a kwanakin Ibrahim mahaifinsa. Filistiyawa suka ɓata su bayan mutuwar Ibrahim. Ishaku ya kira rijiyoyin da ainihin sunan da mahaifinsa ya kira su. 19 Bayan barorin Ishaku sun yi tono a cikin kwarin, sai suka sami wata rijiya mai fitar da ruwa a can. 20 Makiyayan Gerar suka yi faɗa da makiyayan Ishaku suka ce, "Wannan ruwan namu ne." Domin haka Ishaku ya kira rijiyar "Esek" wato rikici, saboda sun yi rikici da shi. 21 Sai suka sake haƙa wata rijiyar, sai suka sake yin rikici akan itama wannan rijiyar, sai ya ba ta suna "Sitnah." 22 Sai ya bar wurin ya ƙara haƙa wata rijiyar, amma ba su yi rikici kan wannan ba. Don haka ya kira ta Rehobot, ya ce, "Yanzu Yahweh ya samar mana masauki, kuma za mu wadata a cikin ƙasar." 23 Sai Ishaku ya haura daga can zuwa Bayersheba. 24 Yahweh ya bayyana a gare shi a cikin wannan daren ya ce, "Ni ne Allah na Ibrahim mahaifinka. Kada ka ji tsoro, domin ina tare da kai zan kuma albarkace ka in ruɓanɓanya zuriyarka, saboda barana Ibrahim." 25 Ishaku ya gina bagadi ya yi kira bisa sunan Yahweh. A can ya kafa rumfarsa, barorinsa kuma suka haƙa rijiya. 26 Sai Abimelek ya je wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzat, abokinsa, da Fikol, jagoran sojojinsa. 27 Ishaku yace da su, "Meyasa kuke zuwa gare ni, tun da yake kun ƙi ni, kun kuma kore ni daga wurinku?" 28 Sai suka ce, "Zahiri mun ga Yahweh na tare da kai. Shi yasa muka ga ya fi kyau a sami rantsuwa tsakaninmu, i, tsakaninmu da kai, To in ka yarda sai mu yi yarjejeniya da kai, 29 cewa ba zaka wahalshe mu ba, kamar yadda muka yi maka muka sallame ka cikin lumana, hakika Yahweh ya albarkace ka." 30 Sai ishaku ya shirya liyafa domin su, suka ci suka sha. 31 Suka tashi da asuba suka yi rantsuwar alƙawari da juna. Daga nan Ishaku ya sallame su, suka bar shi cikin salama. 32 A wannan ranar dai barorin Ishaku suka zo suka ba shi labari game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, Mun sami ruwa." 33 Ya kira rijiyar da suna Shiba, shi ya sa a ke kiran wannan birni da suna Bayersheba har ya zuwa yau. 34 Da Isuwa ya kai shekaru arba'in, ya auri mata mai suna Yudit 'yar Be'eri Bahitte, da kuma Basemat "yar Elon Bahitte. 35 Suka kawo baƙinciki ga Ishaku da Rebeka.

Sura 27

1 Da Ishaku ya tsufa har ta kai ga ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa, babban ɗansa, ya ce da shi, "Ɗana." Ya ce da shi "Ga ni." 2 Ya ce, "Gashi yanzu, na tsufa. Ban kuma san ranar mutuwata ba. 3 Domin haka, ka ɗauki kwarinka da bakanka da makamanka, ka je daji ka yiwo mini farauta. 4 Ka yi mani dage-dage, irin wanda nake ƙauna, ka kawo shi gare ni domin in ci in albarkace ka kafin in mutu." 5 Sai Rebeka ta ji lokacin da Ishaku ke magana da Isuwa ɗansa. Isuwa ya tafi daji domin ya yiwo farauta ya kawo. 6 Sai Rebeka ta yi magana da Yakubu ɗanta ta ce, "Duba, na ji mahaifinka ya yi magana da Isuwa ɗan'uwanka. Ya ce, 7 'Ka farauto mani nama ka shirya mani dage-dage domin in ci in albarkace ka a gaban Yahweh kafin mutuwata.' 8 Yanzu fa ɗana, ka yi biyayya da muryata kamar yadda zan umarce ka. 9 Ka je garke, ka kawo mini "yan awaki guda biyu; zan kuma shirya dage-dage mai daɗi da su domin mahaifinka, kamar yadda yake ƙauna. 10 Zaka kai shi wurin mahaifinka, domin ya ci, ya albarkace ka kafin ya mutu." 11 Yakubu yace da Rebeka mahaifiyarsa, "Gashi, Isuwa ɗan'uwana gargasa ne, ni kuma sulɓi ne. 12 In mahaifina ya taɓa ni, na kuma zama mayaudari a gare shi. Zan jawo wa kaina la'ana ba albarka ba." 13 Mahaifiyarsa ta ce da shi, "Ɗana, bari duk wata la'ana ta auko mani. kai dai ka yi biyayya da muryata, ka je ka kawo su wurina." 14 Sai Yakubu ya tafi ya samo 'yan awaki guda biyu ya kawo su ga mahafiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya dage-dage, kamar yadda mahaifinsa ke ƙauna. 15 Sai Rebeka ta ɗauki tufafin Isuwa babban ɗanta, mafi kyau, wanda ke tare da ita a gida, sai ta sa wa Yakubu, ƙaramin ɗanta. 16 Sai ta sa fatar 'yan awaki a hannunsa da kuma tattausan sashen wuyansa. 17 Sai ta sa dage-dagen mai daɗi da gurasar da ta shirya a hannun ɗanta Yakubu. 18 Sai Yakubu ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, "Mahaifina." Ya ce,"Ga ni nan; Wane ne kai ɗana?" 19 Yakubu yace da mahaifinsa, "Ni ne Isuwa ɗanka na fari; Na yi kamar yadda ka ce da ni. Yanzu sai ka tashi ka zauna ka ci ɗan dage-dagen, domin ka albarkace ni." 20 Ishaku yace da ɗansa, "Ɗana yaya aka yi ka samo shi da sauri haka?" Ya ce, "Domin Yahweh Allanka ya kawo su wurina". 21 Ishaku yace da Yakubu, "Ɗana ka matso kusa da ni, domin in taɓa ka, domin in san ko kai ɗana ne." 22 Yakubu ya matsa ga Ishaku mahaifinsa, Ishaku kuma ya taɓa shi ya ce, "Muyar kamar ta Yakubu ce, amma jikin na 23 Isuwa ne." Ishaku bai iya gane shi ba, domin hannuwansa gargasa ne kamar na hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, domin haka Ishaku ya albarka ce shi. 24 Ya ce "Kai ne ɗana Isuwa kuwa?" Ya amsa "Ni ne." 25 Ishaku yace, "Kawo abincin wurina, zan ci in kuma albarkace ka. Yakubu ya kawo abincin gare shi. Ishaku ya ci, Yakubu kuma ya kawo masa ruwan inabi, ya kuwa sha. 26 Sai babansa Ishaku yace da shi, "Ɗana ka zo nan kusa ka sumbace ni." 27 Yakubu ya matso kusa ya sumbace shi' ya sunsuni ƙamshin suturarsa ya albarkace shi. Ya ce, "Duba, ƙamshin ɗana yana kama da ƙamshin ganyayyakin da Yahweh ya sa wa albarka. 28 Allah ya baka rabo na raɓar sama, rabo na sashin ƙasa mafi dausayi, ya baka hatsi da ruwan Inabi mai yawa. 29 Mutane da al'ummai kuma su rusuna maka. Ka zama shugaban 'yan'uwanka maza, 'ya'yan mahaifiyarka maza kuma su rusuna maka. Duk kuma wanda ya la'ance ka ya zama la'annanne, duk wanda kuma ya albarkace ka ya zama mai albarka." 30 Ishaku na gama sa wa Yakubu albarka kenan, bayan ya fita daga wurin mahaifinsa Ishaku, sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya shigo daga wurin farautarsa. 31 Shi ma ya shirya dage-dagen, abinci mai daɗi ya kawo shi wurin mahaifinsa. Ya ce da mahaifinsa, "Mahaifina, ka tashi ka ci irin dage-dagen ɗanka, domin ka albarkace ni." 32 Ishaku mahaifinsa ya ce da shi, "Kai wane ne?" Ya ce, "Ni ne ɗan farinka, Isuwa. 33 Ishaku ya gigice sosai ya ce, "Wane ne ya yiwo farauta ya kawo mani dage-dage? Na ci a gabanin zuwanka, na kuma albarkace shi. Hakika, zai zama da albarka." 34 Bayan Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, ya yi kuka da baƙinciki matuƙa, ya ce da mahaifinsa, "Ni ma ka albarkace ni mana, mahaifina." 35 Ishaku yace, "Ɗan'uwanka ya zo cikin yaudara ya karɓe albarkarka." 36 Isuwa yace, "Ashe ba haka ta sa aka ba shi suna Yakubu ba? Domin ya zambace ni sau biyu. Ya karɓe matsayina na ɗan fãri, kuma duba yanzu ya karɓe albarkata." Daga nan ya ce, "Ba ka rage wata albarka domina ba?" 37 Ishaku ya amsa ya ce da Isuwa, "Duba, na maishe shi ya zama shugabanka, kuma na ba shi dukkan 'yan'uwansa maza su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Me kuma zan yi maka, ɗana?" 38 Isuwa yace da mahaifinsa, "Ko albarka ɗaya ba ka rage mani ba mahaifina? Ka albarkace ni nima mahaifina." Isuwa yayi kuka da ƙarfi. 39 Ishaku mahaifinsa ya amsa masa cewa, "Duba, wurin da zaka zauna zai zama da nisa daga wadatar duniya, nesa kuma da raɓar sararin sama. 40 Ta wurin takobinka zaka rayu, kuma zaka bautawa ɗan'uwanka. Amma lokacin da kayi tayarwa, zaka kawar da karkiyarsa daga wuyanka." 41 Isuwa ya ƙi Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya ba shi. Isuwa yace a cikin zuciyarsa, "Kwanakin makokin mahaifina sun kusa wucewa, bayan wannan zan kashe ɗan'uwana Yakubu." 42 Sai aka faɗa wa Rebeka kalmomin da babban ɗanta ya faɗa. Domin haka ta aika a kira Yakubu ƙaramin ɗanta ta ce da shi, "'Duba, ɗan'uwanka na tunanin yadda zai kashe ka. 43 Saboda haka, ɗana, yanzu sai ka yi biyayya da muryata, ka gudu wurin Laban ɗan'uwana a Haran. 44 Ka zauna tare da shi na ɗan lokaci, 45 har sai fushin ɗan'uwanka ya huce daga gare ka, ya kuma manta abin da kayi masa. Daga nan zan aika a dawo da kai daga can. Don me zan rasa ku dukka a rana ɗaya? 46 Rebeka ta ce, "Na gaji da rayuwa saboda 'ya'yan Het. In Yakubu ya auri 'yanmata irin waɗannan mataye, waɗansu daga cikin 'yan matan ƙasar, wanne abu ne mai kyau zai zama a rayuwata?"

Sura 28

1 Ishaku ya kira Yakubu, ya albarkace shi, ya kuma dokace shi, "Tilas ba zaka ɗauki mata daga cikin matan Kan'aniyawa ba. 2 Ka tashi, ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan Betuwel mahaifin mahaifiyarka, ka kuma ɗauki mata daga can, ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Laban, ɗan'uwan mahaifiyarka. 3 Bari Allah mai iko dukka ya albarkace ka, yasa kayi 'ya'ya, ka kuma ruɓanɓanya, yadda zaka zama mutane tururu. 4 Bari ya bada albarkar Ibrahim, gare ka, da zuriyarka a bayanka, domin ka iya gãdon ƙasa inda ka ke zama, wadda Allah ya ba Ibrahim." 5 Sai Ishaku ya sallami Yakubu, Yakubu ya tafi Faddan Aram, zuwa ga Laban ɗan Betuwel Ba'aramiye, ɗan'uwan Rebeka, mahaifiyar Yakubu da Isuwa. 6 Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya albarkaci Yakubu ya kuma sallame shi zuwa Faddan Aram, ya ɗauko mata daga can. Ya kuma ga cewa Ishaku ya albarkace shi ya kuma dokace shi, cewa, "Tilas ba za ka ɗauki mata daga matan Kan'aniyawa ba." 7 Isuwa kuma ya ga cewa Yakubu ya yi biyayya da mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya kuma tafi Faddan Aram. 8 Isuwa ya ga cewa matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba. 9 Sai ya tafi wurin Isma'ila, ya ɗauko, baya ga matan da yake da su, Mahalat ɗiyar Isma'ila, ɗan Ibrahim, 'yar'uwar Nebayot, ta zama matarsa. 10 Yakubu ya bar Bayesheba ya tafi zuwa Haran. 11 Ya iso daidai wani wuri ya kuma tsaya wurin dukkan dare, saboda rana ta fãɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun wurin, ya sa ƙarƙashin kansa, ya kuma kwanta a wurin domin ya yi barci. 12 Ya yi mafarki ya kuma ga hawan bene an kafa bisa duniya. ‌Ƙololuwarsa ta kai cikin sama kuma mala'ikun Allah suna hawa suna sauka a kansa. 13 Duba, Yahweh ya tsaya a bisansa ya kuma ce, "Ni ne Yahweh, Allah na Ibrahim mahaifinka, da Allah na Ishaku. ‌Ƙasar inda kake kwance, zan bayar gare ka ga kuma zuriyarka. 14 Zuriyarka zasu zama kamar turɓayar ƙasa, kuma zaka bazu nesa zuwa yamma, zuwa gabas, zuwa arewa, zuwa kuma kudu. Ta wurin ka da ta wurin zuriyarka dukkan iyalan duniya zasu yi albarka. 15 Duba, Ina tare da kai, kuma zan kiyaye ka ko'ina ka tafi. Zan sake kawo ka cikin wannan ƙasa; gama ba zan barka ba. Zan yi dukkan abin dana yi alƙawari a gare ka." 16 Yakubu ya tashi daga barci, ya kuma ce, "Tabbas Yahweh yana wannan wurin, kuma ban sani ba." 17 Ya ji tsoro ya kuma ce, "Wurin nan mai ban tsoro ne! Wannan ba wani wuri ba ne wanda ya wuce gidan Allah. Wannan ƙofar sama ce." 18 Yakubu ya tashi da sassafe ya kuma ɗauki dutsen da ya sa ƙarƙashin kansa. Ya kafa shi a matsayin ginshiƙi ya kuma zuba mai a kansa. 19 Ya kira sunan wannan wuri Betel, amma asalin sunan wannan birni Luz ne. 20 Yakubu ya yi wa'adi, cewa, "Idan Allah zai kasance tare da ni ya kuma kiyaye ni a cikin wannan hanya dana ke tafiya, ya kuma ba ni gurasa in ci, da suturar sanya wa, 21 yadda zan dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, daga nan Yahweh zai zama Allah na. 22 Daga nan wannan dutse dana kafa a matsayin ginshiƙi zai zama tsarkakakken dutse. Daga kowanne abin da ka bani, babu shakka zan bayar da kashi ɗaya cikin goma a gare ka."

Sura 29

1 Daga nan Yakubu ya kama tafiyarsa ya zo cikin ƙasar mutanen gabas. 2 Yayin da ya duba, sai ya ga rijiya a saura, kuma, duba, garkunan tumaki uku na kwance a gefen ta. Domin daga wannan rijiyar za su yi wa garkunan ban ruwa, kuma dutsen dake bakin rijiyar ƙato ne. 3 Sa'ad da dukkan garkunan suka taru a nan, makiyayan zasu gangarar da dutsen daga bakin rijiyar su kuma yi wa tumakin ban ruwa, sai kuma su mai da dutsen bakin rijiyar, daidai wurinsa. 4 Yakubu yace masu, "Yan'uwana, daga ina ku ke?" Suka maida amsa, "Daga Haran muke." 5 Ya ce masu, "Kun san Laban ɗan Nahor?" Suka ce, "Mun san shi." 6 Ya ce masu, "Yana nan lafiya?" Suka ce, "Yana nan lafiya, kuma, duba can, Rahila ɗiyarsa na zuwa tare da tumaki." 7 Yakubu yace, "Duba, yanzu rana tsaka ne. Lokaci bai yi ba da za a tattara garkuna tare. Kuyi wa tumakin ban ruwa daga nan ku tafi ku kai su kiwo." 8 Suka ce, "Ba za mu iya yi masu banruwa ba har sai dukkan garkunan sun tattaru tare. Daga nan mazan zasu gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, sai kuma mu yi wa tumakin banruwa." 9 Yayin da Yakubu ke magana tare da su, Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, domin ita ke kiwon su. 10 Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, ɗiyar Laban, ɗan'uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, ɗan'uwan mahaifiyarsa, Yakubu ya zo kusa, ya gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma yi wa garken Laban ɗan'uwan mahaifiyarsa banruwa. 11 Yakubu ya sumbaci Rahila ya yi kuka da ƙarfi. 12 Yakubu ya gaya wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne, kuma cewa shi ɗan Rebeka ne. Daga nan ta ruga ta gaya wa mahaifinta. 13 Sa'ad da Laban ya ji labarin Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, ya ruga domin ya same shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kuma kawo shi cikin gidansa. Yakubu ya gaya wa Laban dukkan waɗannan abubuwa. 14 Laban yace masa, "Tabbas kai ƙashina ne da namana." Daga nan Yakubu ya zauna tare da shi har wajen wata ɗaya. 15 Daga nan Laban ya cewa Yakubu, "Kã bauta mani a banza saboda kai ɗan dangina ne? Gaya mani, mene ne zai zama ladanka?" 16 Yanzu dai Laban na da 'ya'ya mata biyu. Sunan babbar Liya, sunan ƙaramar kuma Rahila. 17 Idanun Liya tausasa ne amma Rahila na da kyakkyawar siffa. 18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, "Zan bauta maka shekaru bakwai domin Rahila, ƙaramar ɗiyarka." 19 Laban yace, "Gwamma in bayar da ita a gare ka, maimakon in bayar da ita ga wani mutumin. Ka yi zamanka da ni." 20 Sai Yakubu ya yi bauta shekaru bakwai domin Rahila; sai kuma suka yi masa kamar kwanaki kaɗan, domin ƙaunar da yake yi mata. 21 Daga nan Yakubu ya cewa Laban, "Ka bani matata, domin kwanakina sun kammalu - domin in aure ta!" 22 Sai Laban ya tattara dukkan mutanen wurin ya kuma yi biki. 23 Da maraice ya yi, Laban ya ɗauki ɗiyarsa Liya ya kuma kawo wa Yakubu, wanda ya kwana da ita. 24 Laban ya ɗauki baiwarsa Zilfa ya ba ɗiyarsa Liya, ta zama baiwarta. 25 Da safe, da ya duba, sai ya ga ashe Liya ce! Yakubu ya cewa Laban, "Mene ne wannan ka yi mani? Ba domin Rahila na bauta maka ba? To me ya sa ka yaudare ni?" 26 Laban yace, "Ba al'adarmu ba ce mu bayar da ƙaramar ɗiya kafin ta fãrin. 27 Ka kammala satin amarcin wannan ɗiyar, za mu kuma baka ɗayar a sakamakon sake bauta mani na wasu shekarun bakwai." 28 Yakubu ya yi haka, ya kammala satin Liya. Daga nan Laban ya ba shi Rahila ɗiyarsa a matsayin matarsa. 29 Laban kuma ya bayar da Bilha ga ɗiyarsa Rahila, ta zama baiwarta. 30 Haka kuma Yakubu ya kwana da Rahila, amma ya ƙaunaci Rahila fiye da Liya. Sai Yakubu ya bauta wa Laban na wasu shekaru bakwai. 31 Yahweh ya ga cewa ba a ƙaunar Liya, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ba ta da ɗa. 32 Liya ta ɗauki ciki ta haifi ɗa, ta kuma kira sunansa Ruben. Domin ta ce, "Saboda Yahweh ya dubi azabata; babu shakka yanzu mijina zai ƙaunace ni." 33 Daga nan ta sake ɗaukan ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Saboda Yahweh ya ji cewa ba a ƙauna ta, saboda haka ya bani wannan ɗan kuma," ta kuma kira sunansa Simiyon. 34 Daga nan ta sake ɗaukan ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Yanzu a wannan lokacin mijina zai haɗe da ni, saboda na haifa masa 'ya'ya maza uku." Saboda haka a ka kira sunansa Lebi. 35 Ta sake ɗaukar ciki ta kuma haifar ɗa. Ta ce, "Wannan lokacin zan yabi Yahweh." Saboda haka ta kira sunansa Yahuda; Daga nan ta tsaya da haihuwar 'ya'ya.

Sura 30

1 Da Rahila ta ga cewa ba ta haifa wa Yakubu 'ya'ya ba, sai Rahila ta ji kishin 'yar'uwarta. Ta ce wa Yakubu, "Ba ni 'ya'ya, ko in mutu." 2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna gãba da Rahila. Ya ce, "Ina a madadin Allah ne, wanda ya hana ki samun 'ya'ya?" 3 Ta ce, "Duba, wannan baiwata ce Bilha. Ka kwana da ita, saboda ta haifi 'ya'ya bisa gwiwoyina, kuma in sami 'ya'ya ta wurin ta." 4 Sai ta bayar da baiwarta Bilha a matsayin mata, Yakubu kuma ya kwana da ita. 5 Bilha ta ɗauki ciki ta haifa wa Yakubu ɗa. 6 Daga nan Rahila ta ce, "Allah ya baratar da ni, ya kuma ji muryata ya kuma bani ɗa." Domin wannan dalili ta kira sunansa Dan. 7 Bilha, baiwar Rahila, ta sake ɗaukar ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 8 Rahila ta ce, "Da kokowa mai girma na yi kokowa da 'yar'uwata na kuma yi nasara." Ta kira sunansa Naftali. 9 Sa'ad da Liya ta ga cewa ta tsaya da haihuwar 'ya'ya, ta ɗauki Zilfa, baiwarta, ta bayar da ita ga Yakubu a matsayin mata. 10 Zilfa, baiwar Liya, ta haifa wa Yakubu ɗa. 11 Liya ta ce, "Wannan rabo ne!" Sai ta kira sunansa Gad. 12 Daga nan Zilfa, baiwar Liya, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 13 Liya ta ce, "Na yi murna! domin 'ya'ya mata zasu kira ni murna." Sai ta kira sunansa Asha. 14 Ruben ya fita a lokacin yankan alkama ya kuma samo 'ya'yan itacen manta'uwa daga saura. Ya kuma kawo su wurin mahaifiyarsa Liya. Daga nan Rahila ta ce wa Liya, "Ki ba ni daga cikin 'ya'yan itacen manta'uwa na ɗanki." 15 Liya ta ce mata, "‌Ƙaramin al'amari ne a gare ki, cewa kin ɗauke mani miji? Ki na so yanzu ki ɗauke 'ya'yan manta'uwa na ɗana, kuma?" Rahila ta ce, "To zai kwana dake a daren nan, a matsayin musanya domin 'ya'yan manta uwa na ɗanki." 16 Yakubu ya dawo daga gona da yamma. Liya ta fita ta same shi ta ce, "Tilas ka kwana da ni a daren nan, domin nayi hayar ka da 'ya'yan manta'uwa na ɗana." Sai Yakubu ya kwana da Liya a wannan daren. 17 Allah ya saurari Liya, ta kuma ɗauki ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar. 18 Liya ta ce, "Allah ya bani ladana, saboda na bayar da baiwata ga mijina." Sai ta kira sunansa Issaka. 19 Liya ta sake ɗaukan ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na shida. 20 Liya ta ce, "Allah ya bani kyauta mai kyau. Yanzu mijina zai girmama ni, saboda na haifa masa 'ya'ya maza shida." Ta kira sunansa Zebulun. 21 Daga baya ta haifi ɗiya ta kuma kira sunanta Dina. 22 Allah ya tuna da Rahila ya kuma saurare ta. Ya sa ta ɗauki ciki. 23 Ta ɗauki ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Allah ya ɗauke kunyata." 24 Ta kira sunansa Yosef, cewa, "Yahweh ya ƙara mani wani ɗan." 25 Bayan da Rahila ta haifi Yosef, sai Yakubu yace wa Laban, "Ka sallame ni saboda in tafi nawa gidan da ƙasata. 26 Ka bani matayena da 'ya'yana waɗanda domin su na yi maka bauta, bari kuma in tafi, gama ka san hidimar dana yi maka." 27 Laban yace masa, "Idan yanzu na sami tagomashi a gaban ka, ka jira, saboda ta wurin amfani da sihiri na gane cewa Yahweh ya albarkace ni saboda kai." 28 Daga nan ya ce, "Ka faɗi ladanka, zan kuma biya su." 29 Yakubu yace masa, "Ka san dai yadda na bauta maka, da yadda dabbobinka suka kasance tare da ni. 30 Domin 'yan kaɗan kake da su kafin in zo, kuma sun ƙaru a yalwace. Yahweh ya albarkace ka a duk inda na yi aiki. Yanzu yaushe zan samar wa nawa gidan shi ma?" 31 Sai Laban yace, "Me zan biya ka?" Yakubu yace, "Ba zaka bani komai ba. Idan zaka yi wannan domina, zan sake ciyar da dabbobinka in kiwata su kuma. 32 Bari in ratsa cikin dukkan dabbobinka a yau, zan ware daga cikin su duk wasu tumaki dabbare-dabbare da masu ɗigo, da waɗanda ke baƙaƙe daga cikin tumakin, da masu ɗigo da kyalloli daga cikin awakin. Waɗannan ne zasu zama ladana. 33 Amincina zai yi shaida game da ni daga bisani, sa'ad da zaka zo ka duba ladana. Duk wadda ba kyalla ba ce ko mai ɗigo daga cikin awaki, da baƙa daga cikin tumaki, duk wadda a ka samu a wurina, a ɗauke shi a matsayin sata." 34 Laban yace, "Na yarda. Bari ya kasance bisa ga maganarka." 35 A wannan rana Laban ya ware dukkan bunsurai masu zãne da masu ɗigo, da dukkan awaki kyalloli da masu ɗigo, duk wata mai fari a jikinta, da dukkan baƙaƙe daga cikin tumaki, ya kuma bayar da su cikin hannun 'ya'yansa. 36 Laban kuma ya sa tafiya ta kwana uku tsakaninsa da Yakubu. Sai Yakubu ya ci gaba da kiwon sauran dabbobin Laban. 37 Sai Yakubu ya ɗauko ɗanyun tsabgun auduga, da rassan itacen almond da rassan itacen durumi, ya kuma fera fararen zãne a kan su, ya sanya fararen itatuwan dake cikin ƙiraren su bayyana. 38 Daga nan ya jera ƙiraren da ya feffere a gaban dabbobin, a gaban kwamamen ruwa in da suke zuwa su sha. Suna ɗaukar ciki sa'ad da suka zo shan ruwa. 39 Dabbobin suka yi ta barbara a gaban ƙiraren; dabbobin kuma suka yi ta haihuwar 'ya'yai masu zãne, da kyalloli, da masu ɗigo. 40 Yakubu ya ware waɗannan 'yan raguna, amma ya sanya sauran su fuskanci dabbobin masu zãne da dukkan baƙaƙen tumaki a garken Laban. Daga nan sai ya ware nasa dabbobin domin kansa kaɗai ba ya kuma haɗa su tare da dabbobin Laban ba. 41 A duk sa'ad da ƙarfafan tumakin ke barbara, sai Yakubu ya shimfiɗa ƙiraren nan a cikin kwamamen ruwan nan a gaban idanun dabbobin, saboda su ɗauki ciki a tsakiyar ƙiraren. 42 Amma idan dabbobi marasa ƙarfi daga cikin garken suka zo, ba ya sanya ƙiraren a gabansu. Sai ya zama dabbobin marasa ƙarfi na Laban ne, ƙarfafan kuma na Yakubu ne. 43 Mutumin ya zama wadatacce sosai. Yana da manyan garkuna, bayi mata da bayi maza, da raƙuma da jakuna.

Sura 31

1 Yanzu Yakubu ya ji maganganun 'ya'yan Laban maza, cewa sun ce, "Yakubu ya ɗauke dukkan abin dake na mahaifinmu, kuma daga mallakar mahaifinmu ne ya samo dukkan wannan dukiyar." 2 Yakubu ya kalli yanayin fuskar Laban. Ya ga cewa halinsa zuwa gare shi ya canza. 3 Daga nan Yahweh ya cewa Yakubu, "Ka koma ƙasar ubanninka da danginka, zan kuma kasance tare da kai." 4 Yakubu ya aika a ka kira Rahila da Liya zuwa saura a garkensa 5 ya kuma ce masu, "Na ga halin mahaifinku zuwa gare ni ya canza, amma Allah na mahaifina yana tare da ni. 6 Kun san cewa da dukkan karfina ne na bautawa mahaifinku. 7 Mahaifinku ya ruɗe ni ya canza ladana sau goma, amma Allah bai ba shi damar cutar da ni ba. 8 Idan ya ce, "Dabbobin kyalloli zasu zama ladanka,' daga nan dukkan garken suka haifi jarirai kyalloli. Idan ya ce, "Ma su zãne zasu zama ladanka,' daga nan dukkan garken suka haifi 'ya'ya masu zãne. 9 Ta wannan hanya Allah ya ɗauke dabbobin mahaifinku ya kuma bayar da su a gare ni. 10 Sau ɗaya a lokacin yin barbara, na gani a mafarki cewa bunsuran na barbara da dabbobin. Bunsuran masu zãne ne, da kyalloli, da masu ɗigo. 11 Mala'ikan Allah yace da ni a cikin mafarkin, 'Yakubu.' Na ce, 'Ga ni nan.' 12 Ya ce, 'Ka ɗaga idanunka ka ga dukkan bunsuran dake barbara da dabbobin. Masu zãne ne, da kyalloli, da masu ɗigo, gama na ga dukkan abin da Laban yake yi maka. 13 Ni ne Allah na Betel, in da ka yi wa ginshiƙi shafewa, in da ka ɗaukar mani wa'adi. Yanzu ka tashi ka bar wannan ƙasar ka kuma koma ƙasar haihuwarka."' 14 Rahila da Liya suka amsa suka ce masa, "Akwai kuma wani rabo ko gãdo dominmu a gidan mahaifinmu? 15 Ba kamar bãre ya maida mu ba? Gama ya sayar da mu kuma ya lanƙwame kuɗinmu gabaɗaya. 16 Domin dukkan arzikin da Allah ya ɗauke daga wurin mahaifinmu yanzu na mu ne da 'ya'yanmu. To yanzu duk abin da Allah yace maka, sai ka yi." 17 Daga nan Yakubu ya tashi ya ɗora 'ya'yansa da matayensa bisa raƙumma. 18 Ya kora dukkan dabbobinsa gaba da shi, tare da dukkan kaddarorinsa, har da dabbobin da ya samu a Faddan Aram. Daga nan ya kama tafiya zuwa wurin mahaifinsa Ishaku a cikin ƙasar Kan'ana. 19 Sa'ad da Laban ya tafi yi wa tumakinsa sausaya, Rahila ta ɗauke allolin gidan mahaifinta. 20 Yakubu shi ma ya ruɗi Laban Ba'aramiye, ta wurin ƙin gaya masa cewa zai tashi. 21 Sai ya tsere da dukkan abin da yake da shi, nan da nan kuma ya wuce ƙetaren Kogi, ya kuma doshi zuwa ƙasar tudu ta Giliyad. 22 A rana ta uku a ka gaya wa Laban cewa Yakubu ya gudu. 23 Sai ya ɗauki danginsa ya kuma bi shi na tsawon tafiyar kwana bakwai. Ya sha kansa a ƙasar tudu ta Giliyad. 24 Sai Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye a cikin mafarki da dare ya kuma ce masa, "Ka yi hankali kada kayi magana da Yakubu mai kyau ko marar kyau." 25 Laban ya sha kan Yakubu. Yanzu Yakubu ya kafa rumfarsa a ƙasar tudu. Laban shi ma ya kafa sansani tare da danginsa a ƙasar tudu ta Giliyad. 26 Laban ya cewa Yakubu, "Mene ne ka yi, da ka ruɗe ni ka kuma ɗauke 'ya'yana mata kamar kamammun yaƙi? 27 Meyasa ka tsere a asirce ka kuma yi mani dabara ba ka kuma gaya mani ba? Da na sallame ka da biki da waƙe-waƙe, tare da tambari da garayu. 28 Ba ka bar ni na yi sumbar sallama ga jikokina da 'ya'yana ba. Yanzu ka aikata wawanci. 29 A cikin ikona ne in cutar da kai, amma Allah na mahaifinka ya yi magana da ni a daren da ya wuce ya ce, 'Ka yi hankali kada ka yi magana da Yakubu mai kyau ko marar kyau.' 30 Yanzu ka gudu saboda kana marmarin ka koma gidan mahaifinka. Amma me ya sa ka sace allolina?" 31 Yakubu ya amsa kuma ya ce wa Laban, "Saboda na ji tsoro kuma na yi tunanin za ka karɓe 'ya'yanka mata da ƙarfi daga gare ni sai na gudu a asirce. 32 Duk wanda ya sace allolinka ba zai ci gaba da rayuwa ba. A gaban dangoginmu, ka tantance abin da ke naka tare da ni ka ɗauka." Gama Yakubu bai san cewa Rahila ta sace su ba. 33 Laban ya shiga cikin rumfar Yakubu, cikin rumfar Liya, da cikin rumfar bayi matan biyu, amma bai gan su ba. Ya fita daga rumfar Liya ya shiga cikin rumfar Rahila. 34 A she Rahila ta ɗauki allolin gidan, ta sanya su a sirdin raƙumi, ta kuma zauna a bisansu. Laban ya bincike rumfar gabaɗaya, amma bai same su ba. 35 Ta ce wa mahaifinta, "Kada ka ji haushi, shugabana, cewa ba zan iya tashi ba a gabanka, domin ina cikin al'adata." Sai ya bincike amma bai ga allolin gidansa ba. 36 Yakubu ya husata ya yi gardama da Laban. Ya ce masa, "Mene ne laifi na? Mene ne zunubi na, da ka runtumo ni da zafi? 37 Gama ka duba dukkan mallakata. Me ka samu daga dukkan kayayyakin gidanka? Ka fito da su yanzu a gaban dangoginmu, sai su shar'anta a tsakanin mu biyu. 38 Shekaru ashirin ina tare da kai. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuma ci wani rago ba daga garkunanka. 39 Abin da bisashe suka yayyage ban kawo maka ba. Maimako, na ɗauki asararsa. Ko yaushe kana sa in biya duk wata dabbar da ta bace, ko wadda a ka sace da rana ko wadda a ka sace da dare. 40 Nan ni ke; da rana zafi na cinye ni, da dare cikin sanyin dusar ƙanƙara; na yi tafiya kuma babu barci. 41 Waɗannan shekaru ashirin ina cikin gidanka. Na yi maka aiki shekaru sha huɗu domin 'ya'yanka biyu mata, shekaru shida kuma domin dabbobinka. Ka canza ladana sau goma. 42 Idan ba domin Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim, da wanda Ishaku ke tsoro, yana tare da ni ba, tabbas da yanzu ka kore ni hannu wofi. Allah ya dubi tsanantawata da aiki tuƙuru dana yi, ya kuma tsauta ma ka a daren jiya." 43 Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, "'Ya'yan mata 'ya'yana ne, jikokin jikokina ne, dabbobin kuma dabbobina ne. Dukkan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan iya yi a yau game da waɗannan 'ya'ya matan nawa, ko kuma game da 'ya'yansu da suka haifa? 44 To yanzu, bari mu ɗauki alƙawari, kai da ni, bari kuma ya zama domin shaida tsakanin kai da ni." 45 Sai Yakubu ya ɗauki dutse ya kuma dasa shi a matsayin ginshiƙi. 46 Yakubu ya cewa danginsa, "Ku tattara duwatsu." Sai suka ɗebo duwatsu suka tattara su. 47 Laban ya kira shi Yagar Saha Duta, amma Yakubu ya kira shi Galid. 48 Laban yace, "Wannan tarin shaida ne tsakani na da kai a yau." saboda haka a ka kira sunansa Galid. 49 A na kuma kiransa Mizfa, saboda Laban yace, "Bari Yahweh ya duba tsakanin ka da ni, yayin da muka ɓace daga juna. 50 Idan ka wulaƙanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wasu matan baya ga 'ya'ya na, ko da yake babu wanda ke tare da mu, duba, Allah ne shaida tsakanin ka da ni." 51 Laban ya cewa Yakubu, "Dubi wannan tarin, ka kuma dubi ginshiƙin, wanda na kafa tsakanin ka da ni. 52 Wannan tarin shaida ne, ginshiƙin kuma shaida ne, cewa ba zan ƙetare gaba da wannan tarin ba zuwa gare ka, kai kuma ba zaka ƙetare gaba da wannan tarin ba da wannan ginshiƙin zuwa gare ni ba, domin cutarwa. 53 Bari Allah na Ibrahim, da allahn Naho, da allolin mahaifinsu, su shar'anta tsakaninmu." Yakubu ya rantse da tsoron mahaifinsa Ishaku. 54 Yakubu ya miƙa hadaya a bisa tsaunin ya kuma kira danginsa su ci abinci. Suka ci suka zauna tsawon dare a tsaunin. 55 Tun da sassafe Laban ya tashi, ya sumbaci jikokinsa da 'ya'yansa mata ya albarkace su. Daga nan Laban ya tafi ya koma gida.

Sura 32

1 Yakubu shima ya tafi hanyarsa, mala'ikun Allah suka same shi. 2 Sa'ad da Yakubu ya gan su, ya ce, "Wannan sansanin Allah ne." sai ya kira sunan wannan wuri Mahanayim. 3 Yakubu ya aiki manzanni gaba da shi zuwa ga ɗan'uwansa Isuwa a cikin ƙasar Seyir, a cikin lardin Idom. 4 Ya dokace su, cewa, "Ga abin da zaku cewa shugabana Isuwa: Ga abin da bawanka Yakubu yace: 'Ina zaune tare da Laban, na kuma yi jinkirin dawowata har zuwa yanzu. 5 Ina da shanu, da jakkai, da garkunan tumaki, da awaki, bayi maza da bayi mata. Na aiko da wannan saƙon ga shugabana, domin in sami tagomashi a idanunka."' 6 Manzannin suka dawo wurin Yakubu suka kuma ce, "Munje wurin ɗan'uwanka Isuwa. Yana zuwa ya same ka, da mutane ɗari huɗu tare da shi." 7 Daga nan Yakubu ya tsorata kuma ya ji haushi. Sai ya raba mutanen dake tare da shi ya yi sansani biyu, da garkunan tumaki, da awaki, da garkunan shanu, da raƙumma. 8 Ya ce, "Idan Isuwa ya zo ga sansani ɗaya ya kawo mana hari, daga nan sansanin da ya rage zasu kuɓuce." 9 Yakubu yace, "Allah na mahaifina Ibrahim, da Allah na mahaifina Ishaku, Yahweh, wanda ya ce mani, 'Ka koma ga ƙasarka da danginka, zan kuma wadata ka,' 10 Ban cancanci dukkan ayyukanka na alƙawarin aminci ba da dukkan yarda da ka yi domin bawanka ba. Domin da sandana kawai na ƙetare wannan Yodan, yanzu kuma na zama sansanai biyu. 11 Ina roƙonka ka cece ni daga hannun ɗan'uwana, daga hannun Isuwa, domin ina jin tsoronsa, cewa zai kawo mani hari tare da iyaye matan da 'ya'yan. 12 Amma ka ce, 'Babu shakka zan sa ka wadata. Zan maida zuriyarka kamar rairayin teku, waɗanda ba za a iya lissafawa ba domin yawansu."' 13 Yakubu ya zauna nan a wannan daren. Ya ɗauki wasu daga cikin abin da yake da su a matsayin kyauta domin Isuwa, ɗan'uwansa: 14 awaki ɗari biyu da bunsuru ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin, 15 raƙuma talatin masu shayarwa da 'ya'yansu, shanu arba'in, bijimai goma, jakkai mata ashirin da jakkai maza goma. 16 Waɗannan ya bayar dasu cikin hannun bayinsa, kowanne garke daban. Ya cewa bayinsa, "Ku tafi gaba da ni, ku sanya tazara tsakanin kowanne garken." 17 Ya umarci bawa na farko, cewa, "Idan Isuwa ɗan'uwana ya gamu da kai ya tambaye ka, cewa, 'Kai na wane ne? Ina za ka je? Dabbobin wane ne waɗannan da ke gabanka?' 18 Daga nan za ka ce, 'Na bawanka ne Yakubu. Kyauta ce a ka aiko wa shugabana Isuwa. Duba, shi ma yana zuwa bayanmu."' 19 Yakubu ya sake bada umarnai ga ƙungiya ta biyu, ta uku, da dukkan mutanen da suka bi garkunan. Ya ce, "Zaku faɗi abu iri ɗaya ga Isuwa idan kuka same shi. 20 Tilas kuma ku ce, 'Bawanka Yakubu yana zuwa bayanmu."' Gama ya yi tunani, "Zan tausar da shi da kyaututtukan da nake aikawa da su a gabana. Sai daga baya, sa'ad da zan gan shi, wataƙila zai karɓe ni." 21 Sai kyaututtukan suka tafi gaba da shi. Shi kuwa da kansa ya tsaya a wannan daren a cikin sansani. 22 Yakubu ya tashi da daddare, ya kuma ɗauki matayensa biyu, da matayensa barori su biyu, da 'ya'yansa maza sha ɗaya. Ya aika da su ƙetaren kududdufin Yabbok. 23 Ta wannan hanyar ya aika da su ƙetaren rafin tare da dukkan mallakarsa. 24 A ka bar Yakubu shi kaɗai, wani mutum kuwa ya yi kokowa da shi har wayewar gari. 25 Sa'ad da mutumin ya ga cewa ba zai kayar da shi ba, sai ya mazge shi a kwankwaso. Sai kwankwason Yakubu ya goce sa'ad da yake kokowa da shi. 26 Mutumin yace, "Bari in tafi, domin gari yana wayewa." Yakubu yace, "Ba zan bar ka ka tafi ba sai ka albarkace ni." 27 Mutumin yace masa, "Yayã sunanka?" Yakubu yace, "Yakubu." 28 Mutumin yace, "Ba za a sake kiran sunanka Yakubu ba, amma Isra'ila. Gama ka yi gwagwarmaya tare da Allah tare da mutane ka kuma yi nasara." 29 Yakubu yace masa, "Ina roƙon ka, ka faɗi mani sunanka." Ya ce, "Meyasa kake tambayar sunana?" Daga nan ya albarkace shi a wurin. 30 Yakubu ya kira sunan wurin Feniyel, gama ya ce, "Na ga Allah fuska da fuska, kuma rayuwata ta kuɓuta." 31 Rana ta taso bisa Yakubu sa'ad da yake wuce Feniyel. Yana ɗangyashi saboda kwankwasonsa. 32 Shi ya sanya har wa yau mutanen Isra'ila ba su cin jijiyoyin kwankwaso waɗanda suke mahaɗin kwankwaso, saboda mutumin ya yi wa jijiyoyin rauni sa'ad da ya sa kwankwason Yakubu ya goce.

Sura 33

1 Yakubu ya hango, kuma, duba, Isuwa na zuwa, tare da shi kuma mutane ɗari huɗu. Yakubu ya raba 'ya'yan tsakanin Liya, Rahila, da matayen biyu barori. 2 Daga nan ya sanya matayen barori da 'ya'yansu a gaba, a biye kuma Liya da 'ya'yanta, a biye kuma Rahila da Yosef na ƙarshen su dukka. 3 Shi da kansa kuma ya tafi gaba da su. Ya rusuna zuwa ƙasa sau bakwai, har sai da ya zo kusa da ɗan'uwansa. 4 Isuwa ya rugo ya same shi, ya rungume shi, ya rungumi wuyansa, ya sumbace shi kuma. Daga nan suka yi kuka. 5 Sa'ad da Isuwa ya hanga, sai ya ga matayen da 'ya'yan. Ya ce, "Su wane ne waɗannan mutanen tare da kai?" Yakubu yace, "'Ya'yan da Allah ta wurin alherinsa ya ba bawanka ne." 6 Daga nan bayi matan suka zo gaba tare da 'ya'yansu, suka kuma rusuna. 7 Sai Liya ita ma da 'ya'yanta suka zo gaba suka rusuna. A ƙarshe kuma Yosef da Rahila suka zo gaba suka rusuna. 8 Isuwa yace, "Mene ne kake nufi da dukkan waɗannan ƙungiyoyi da na tarar?" Yakubu yace, "Domin in sami tagomashi a gaban shugabana ne." 9 Isuwa yace, "Ina da isassu, ɗan'uwana. Ka ajiye abin da kake da shi domin kanka." 10 Yakubu yace, "A'a, ina roƙon ka, idan na sami tagomashi a idanunka, to ka karɓi kyautata daga hannuna, gama babu shakka, na ga fuskar ka, kuma kamar ganin fuskar Allah ne, kuma ka karɓe ni. 11 Ina roƙon ka ka karɓi kyautata da a ka kawo maka, saboda Allah ya aiwatar da alheri zuwa gare ni, saboda kuma ina da isassu." Haka nan Yakubu ya lallashe shi, Isuwa kuma ya karɓe su. 12 Daga nan Isuwa yace, "Mu kama hanya. Zan tafi gaba kafin kai." 13 Yakubu yace masa, "Shugabana yasan cewa yaran ƙanana ne, kuma tumakin da garken dabbobin suna renon ƙananansu. Idan a ka kora su da ƙarfi a rana ɗaya, dukkan dabbobin zasu mutu. 14 Ina roƙon ka bari shugabana ya tafi gaba da bawansa. Zan yi tafiya a hankali, bisa ga saurin dabbobin dake a gabana, bisa kuma ga saurin yaran, har sai na zo ga shugabana a Seyir." 15 Isuwa yace, "Bari in bar maka wasu daga cikin mutane na dake tare da ni." Amma Yakubu yace, "Meyasa zaka yi haka? Bari in sami tagomashi a idanun ubangijina." 16 Sai Isuwa a wannan ranar ya fara tafiya bisa hanyarsa ta komawa Seyir. 17 Yakubu ya tafi Sukkot, ya gina wa kansa gida, ya yi wa dabbobinsa kuma wurin zama. Saboda haka sunan wannan wuri ana kiransa Sukkot. 18 Sa'ad da Yakubu ya zo daga Faddan Aram, ya isa lafiya a birnin Shekem, wanda ke a cikin ƙasar Kan'ana. Ya kafa sansani kusa da birnin. 19 Daga nan ya sayi filin da ya kafa rumfarsa daga hannun 'ya'yan Hamo, mahaifin Shekem, a kan jimillar azurfa ɗari. 20 A nan ya kafa bagadi, ya kuma kira shi El Elohi Isra'ila.

Sura 34

1 Sai Dinah, ɗiyar Liya wadda ta haifawa Yakubu, ta fita ta tafi wurin 'yanmatan ƙasar. 2 Shekem ɗan Hamo Bahibiye, yariman ƙasar, ya ganta ya kuma cafke ta, ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita. 3 Ya shaƙu da Dinah, ɗiyar Yakubu. Ya ƙaunaci yarinyar, ya kuma yi mata magana mai taushi. 4 Shekem ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Ka samo mani wannan yarinyar a matsayin mata." 5 Yanzu Yakubu ya ji cewa ya lalata ɗiyarsa Dina. 'Ya'yansa kuma na tare da dabbobinsa a saura, sai Yakubu ya kame bakinsa har sai da su ka zo. 6 Hamo mahaifin Shekem ya tafi wurin Yakubu domin ya yi magana da shi. 7 'Ya'yan Yakubu suka dawo daga saura sa'ad da suka ji batun al'amarin. Mutanen ransu ya ɓaci. Suka fusata sosai saboda ya kunyatar da Isra'ila ta wurin tilasta kansa bisa ɗiyar Yakubu, domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba. 8 Hamo ya yi magana da shi, cewa, "‌Ɗana Shekem na ƙaunar ɗiyarka. Ina roƙon ka. ka bayar da ita a gare shi a matsayin mata. 9 Ku yi auratayya da mu, ku bayar da 'ya'yanku mata a gare mu, ku kuma ɗauki 'ya'yanmu mata domin kanku. 10 Zaku zauna tare da mu, za a buɗe ƙasar kuma a gare ku domin ku zauna ku kuma yi sana'a a ciki, ku kuma mallaki kaddarori." 11 Shekem yace wa mahaifinta da 'yan'uwanta maza, "Bari in sami tagomashi a idanunku, duk kuma abin da kuka ce mani zan bayar. 12 Ku tambaye ni komai yawan sadakin da kyautar da kuke so, kuma zan bayar da duk abin da kuka ce, amma dai ku bani yarinyar a matsayin mata." 13 'Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da Hamo mahaifinsa tare da zamba, saboda Shekem ya ɓata Dina 'yar'uwarsu. 14 Suka ce masu, "Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu bayar da 'yar'uwarmu ga duk wani wanda ba shi da kaciya; domin zai zama abin kunya a gare mu. 15 Sai dai a kan wannan matakin kaɗai za mu yarda da ku: Idan zaku zama masu kaciya kamar mu, idan kowanne namiji a cikin ku an yi masa kaciya. 16 Daga nan ne za mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare ku, mu kuma zamu ɗauki 'ya'yanku mata a gare mu, mu kuma zauna daku mu zama mutane ɗaya. 17 Amma idan baku saurare mu ba kuka zama masu kaciya, daga nan zamu ɗauki 'yar'uwarmu kuma za mu tashi." 18 Maganganunsu suka gamshi Hamo da ɗansa Shekem. 19 Saurayin bai ɓata lokaci ba wurin yin abin da suka ce, saboda yana jin daɗin ɗiyar Yakubu, saboda kuma shi ne taliki mafi daraja a dukkan gidan mahaifinsa. 20 Hamo da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu suka kuma yi magana da mutanen birninsu, cewa, 21 "Mutanen nan suna zaman salama da mu, bari su zauna cikin ƙasar su kuma yi sana'a a ciki domin, tabbas, ƙasar na da isasshen girma domin su. Bari mu ɗauki 'ya'yansu mata a matsayin matayen aure, bari kuma mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare su. 22 A wannan matakin kaɗai mutanen za su yarda su zauna da mu kuma mu zama mutane ɗaya. Idan a ka yi wa kowanne namiji a cikin mu kaciya, kamar yarda suke da kaciya. 23 Ba dukkan dabbobinsu da kaddarorinsu - dukkan dabbobinsu zasu zama namu ba? Don haka mu yarda da su, zasu kuma zauna a cikinmu." 24 Dukkan mutanen birnin suka saurari Hamo da Shekem, ɗansa. Kowanne namiji a ka yi masa kaciya. 25 A rana ta uku, sa'ad da suke cikin zafi tukuna, 'ya'yan Yakubu biyu (Simiyon da Lebi 'yan'uwan Dina), kowannen su ya ɗauki takobinsa suka kuma kai hari ga birnin dake da tabbacin tsaro, suka kuma kashe dukkan mazajen. 26 Suka kashe Hamo da ɗansa Shekem ta kaifin takobi. Suka ɗauke Dina daga gidan Shekem suka yi tafiyar su. 27 Sauran 'ya'yan Yakubu suka zo wurin gawawwakin suka washe birnin, saboda mutanen sun ɓata 'yar'uwarsu. 28 Suka ɗauki garkunan tumakinsu dana awaki, da garkunan shanunsu, da jakkansu, da duk wani abu dake cikin birnin da gonakin dake kewaye tare da 29 dukkan dukiyarsu. Dukkan 'ya'yayensu da matayensu, suka kame. Suka ma ɗauke kowanne abu dake cikin gidajen. 30 Yakubu ya cewa Simiyon da Lebi, "Kun kawo mani matsala, domin kun sa in yi ɗoyi ga mazaunan ƙasar, da Kan'aniyawa da Feriziyawa. Ni kima ne a lissafi. Idan suka tattara kansu tare gãba da ni, su kuma kawo ma ni hari, daga nan zan hallaka, ni da gidana." 31 Amma Simiyon da Lebi suka ce, "Ya kamata Shekem ya yi da 'yar'uwarmu kamar karuwa?"

Sura 35

1 Allah ya cewa Yakubu, "Ka tashi, ka nufi sama zuwa Betel, ka kuma zauna a can. Ka ginawa Allah bagadi a wurin, wanda ya bayyana a gare ka sa'ad da kake gujewa Isuwa ɗan'uwanka." 2 Daga nan Yakubu ya cewa gidansa da dukkan waɗanda ke tare da shi, "Ku fitar da bãƙin alloli dake a tsakaninku, ku tsarkake kanku, ku kuma canza suturarku. 3 Daga nan mu bar nan, mu nufi sama zuwa Betel. Zan ginawa Allah bagadi a can, wanda ya amsa mani a ranar ƙuncina, kuma ya kasance tare da ni dukkan inda na nufa." 4 Sai suka ba Yakubu dukkan bãƙin alloli da suke a hannunsu, da zobban da suke a kunnuwansu. Yakubu ya bizne su a ƙarƙashin rimi dake kusa da Shekem. 5 Yayin da suke tafiya, Allah ya sanya tsoronsu ya fãɗo a bisa biranen dake kewaye da su, domin haka waɗannan mutane ba su runtumi 'ya'yan Yakubu ba. 6 Sai Yakubu ya iso Luz (wato, Betel), wadda ke cikin ƙasar Kan'ana, shi da dukkan mutanen dake tare da shi. 7 Ya gina bagadi a nan ya kira sunan wurin El Betel, saboda a wurin ne Allah ya bayyana kansa a gare shi, sa'ad da yake gudu daga ɗan'uwansa. 8 Debora, mai kula da Rebeka, ta mutu. A ka bizne ta a gangare daga Betel ƙarƙashin itacen rimi, domin haka ana kiran wurin Allon Bakut. 9 Sa'ad da Yakubu ya zo daga Faddan Aram, Allah ya sake bayyana a gare shi ya kuma albarkace shi. 10 Allah yace masa, "Sunanka Yakubu, amma ba za a sake kiran sunanka Yakubu ba. Sunanka zai zama Isra'ila ne." Sai Allah ya kira sunansa Isra'ila. 11 Allah yace masa, "Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka hayayyafa ka kuma ruɓanɓanya. ‌Ƙasa da ƙungiyar ƙasashe zasu fito daga gare ka, kuma sarakuna zasu kasance cikin zuriyarka. 12 ‌Ƙasar dana bayar ga Ibrahim da Ishaku, zan bayar a gare ka. Ga zuriyarka bayanka kuma zan bayar da ƙasar." 13 Allah ya tafi daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi. 14 Yakubu ya kafa ginshiƙi a wurin da Allah ya yi magana da shi, ginshiƙin dutse. Ya zuba baikon sha a bisansa ya kuma zuba mai a kansa. 15 Yakubu ya kira sunan wurin inda Allah ya yi magana da shi, Betel. 16 Suka kama tafiya daga Betel. Yayin da suke da 'yar tazara daga Efrat, Rahila ta fãra naƙuda. Ta yi naƙuda mai wuya. 17 Yayin da take cikin azabar naƙuda, unguwar zomar ta ce mata, "Kada ki ji tsoro, domin yanzu za ki sami wani ɗan." 18 Yayin da take mutuwa, da numfashinta na mutuwa ta raɗa masa suna Ben-Oni, amma mahaifinsa ya kira shi da suna Benyamin. 19 Rahila ta mutu a ka kuma bizne ta a kan hanyar zuwa Efrat (wato, Betlehem). 20 Yakubu ya kafa ginshiƙi bisa kabarinta. Shi ne shaidar kabarin Rahila har ya zuwa yau. 21 Isra'ila ya ci gaba da tafiya ya kafa rumfarsa a gaba da hasumiyar tsaron garke. 22 Yayin da Isra'ila ke zaune a wannan ƙasa, Ruben ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra'ila kuma ya ji labari. Yakubu dai na da 'ya'ya maza sha biyu. 23 'Ya'yansa maza daga Liya su ne Ruben, ɗan fãrin Yakubu, da Simiyon, Lebi, Yahuda, Issaka, da Zebulun. 24 'Ya'yansa maza daga Rahila su ne Yosef da Benyamin. 25 'Ya'yansa maza daga Bilha, baiwar Rahila, sune Dan da Naftali. 26 'Ya'ya maza na Zilfa, baiwar Liya, su ne Gad da Asha. Dukkan waɗannan 'ya'yan Yakubu ne waɗanda a ka haifa masa a Faddan Aram. 27 Yakubu ya zo wurin Ishaku a Mamri a Kiriyat Arba (ita ce dai Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna. 28 Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin. 29 Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, a ka kuma tattara shi ga kakanninsa, tsohon mutum cike da kwanaki. Isuwa da Yakubu, 'ya'yansa, suka bizne shi.

Sura 36

1 Waɗannan ne zuriyar Isuwa (wanda kuma a ke kira Idom). 2 Isuwa ya ɗauki matayensa daga Kan'aniyawa. Waɗannan ne matayensa: Ada ɗiyar Elon Bahittiye; Oholibama ɗiyar Ana, jikar Zibiyon Bahibbiye; 3 da Bashemat, ɗiyar Isma'il, 'yar'uwar Nebayot. 4 Ada ta haifi Elifaz da Isuwa, Bashemat kuma ta haifi Ruwel. 5 Oholibama kuma ta haifi Yewish, Yalam da Kora. Waɗannan ne 'ya'yan Isuwa waɗanda a ka haifa masa a ƙasar Kan'ana. 6 Isuwa ya ɗauki matayensa, da 'ya'yansa maza, da 'ya'yansa mata, da mutanen dake gidansa, da dabbobinsa - dukkan dabbobinsa, da dukkan mallakarsa, wadda ya tattara a ƙasar Kan'ana, ya tafi cikin wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu. 7 Ya yi haka ne saboda mallakarsu ta yi yawan da ba zasu iya zama tare ba. ‌Ƙasar da suka zauna ba za ta iya ɗaukar su ba saboda yawan dabbobinsu. 8 Sai Isuwa, wanda kuma a ka sa ni da Idom, ya zauna a ƙasar tudu ta Seyir. 9 Waɗannan ne zuriyar Isuwa, kakan Idomawa a ƙasar tudu ta Seyir. 10 Waɗannan ne sunayen 'ya'ya maza na Isuwa: Elifaz ɗan Ada, matar Isuwa; Ruwel ɗan Bashemat, matar Isuwa. 11 'Ya'ya maza na Elifaz sune Teman, Omar, Zefo, Gatam, da Kenaz. 12 Timna, wata ƙwarƙwarar Elifaz, ɗan Isuwa, ta haifi Amalek. Waɗannan ne jikoki maza na Ada, matar Isuwa. 13 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Ruwel: Nahat, Zera, Shamma, da Mizza. Waɗannan ne jikoki maza na Bashemat, matar Isuwa. 14 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Oholibama, matar Isuwa, wadda ita ce ɗiyar Ana da jikar Zibiyon. Ta haifa wa Isuwa Yewish, Yalam, da Kora. 15 Waɗannan ne kabilu a cikin zuriyar Isuwa: Zuriyar Elifaz, ɗan fãrin Isuwa: Teman, Omar, Zefo, Kenaz, 16 Kora, Gatam, da Amalek. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga Elifaz a ƙasar Idom. Su ne jikoki maza na Ada. 17 Waɗannan ne dangogi daga Ruwel, ɗan Isuwa: Nahat, Zera, Shamma, Mizza. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga Ruwel a cikin ƙasar Idom. Su ne jikokin Bashemat, matar Isuwa. 18 Waɗannan ne dangogin Oholibama, matar Isuwa: Yewish, Yalam, Kora. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga matar Isuwa Oholibama, ɗiyar Ana. 19 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Isuwa (wanda a ka sa ni da Idom), kuma waɗannan ne hakimansu. 20 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Seyir Bahorite, mazauna ƙasar: Lotan, Shobal, Zibiyon, Ana, 21 Dishon, Eza, da Dishan. Waɗannan ne dangogin Horitiyawa, mazauna Seyir a cikin ƙasar Idom. 22 'Ya'ya maza na Lotan su ne Hori da Heman, kuma Timna 'yar'uwar Lotan ce. 23 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Shobal: Alban, Manahat, Ebal, Shefo, da Onam. 24 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Zibiyon: Aiya da Ana. Wannan Ana shi ne ya gano maɓulɓular ruwa mai zafi a jeji, yayin da yake kiwon jakkan Zibiyon mahaifinsa. 25 Waɗannan ne 'ya'yan Ana: Dishon da Oholibama, ɗiyar Ana. 26 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Dishon: Hemdan, Eshban, Itran, da Keran. 27 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Eza: Bilhan, Za'aban, da Akan. 28 Waɗannan ne "ya'ya maza na Dishan: Uz da Aran. 29 Waɗannan ne dangogin Horitiyawa: Lotan, Shobal, Zibiyon, da Ana, 30 Dishon, Eza, Dishan: Waɗannan ne dangogin Horitiyawa, bisa ga dangoginsu da aka lissafa a ƙasar Seyir. 31 Waɗannan ne sarakunan da suka yi mulki a ƙasar Idom kafin wani sarki ya yi mulki a bisa Isra'ilawa: 32 Bela ɗan Beyor, ya yi mulki a Idom, sunan birninsa kuma Dinhaba ne. 33 Sa'ad da Bela ya mutu, daga nan Yobab ɗan Zera da Bozra, ya yi mulki a gurbinsa. 34 Sa'ad da Yobab ya mutu, Husham wanda ke daga ƙasar Temanawa, ya yi mulki a gurbinsa. 35 Sa'ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Midiyanawa da yaƙi a ƙasar Mowab, ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Abit ne. 36 Sa'ad da Hadad ya mutu, daga nan Samla na Masreka ya yi mulki a gurbinsa. 37 Sa'ad da Samla ya mutu, daga nan Shawul na Rehobot ta gefen kogi ya yi mulki a gurbinsa. 38 Sa'ad da Shawul ya mutu, daga nan Ba'al Hanan ɗan Akbor ya yi mulki a gurbinsa. 39 Sa'ad da Ba'al-hanan ɗan Akbo, ya mutu, daga nan Hadar ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Fawu ne. Sunan matarsa Mehetabel, ɗiyar Matred, jikar Me Zahab. 40 Waɗannan ne sunayen shugabannin kabilu daga zuriyar Isuwa, bisa ga dangoginsu da lardunansu, bisa ga sunayensu: Timna, Alba, Yetet, 41 Oholibama, Ela, Finon, 42 Kenaz, Teman, Mibzar, 43 Magdiyel, da Iram. Waɗannan ne shugabannin dangogin Idom, bisa ga mazaunansu a cikin ƙasar da suka mallaka. Wannan ne Isuwa, mahaifin Idomawa.

Sura 37

1 Yakubu ya zauna ƙasar da mahaifinsa ke zama, a cikin ƙasar Kan'ana. 2 Waɗannan ne al'amura game da Yakubu. Yosef, wanda ke saurayi ɗan shekaru sha bakwai, yana kiwon tumaki da awaki tare da 'yan'uwansa. Yana tare da 'ya'yan Bilha da 'ya'yan Zilfa, matan mahaifinsa. Yosef yana kawo labarai marasa daɗi game da su wurin mahaifinsu. 3 Isra'ila dai yana ƙaunar Yosef fiye da dukkan 'ya'yansa maza saboda shi ɗan tsufansa ne. Ya yi masa wata riga mai kyau. 4 'Yan'uwansa suka ga cewa mahaifinsu na ƙaunarsa fiye da dukkan 'yan'uwansa maza. Suka ƙi jininsa, kuma ba su maganar alheri da shi. 5 Yosef ya yi wani mafarki, ya kuma gaya wa 'yan'uwansa game da mafarkin. Suka ƙara ƙin jininsa. 6 Yace masu, "Ina roƙon ku da ku saurari wannan mafarkin da na yi. 7 Duba, muna ta ɗaurin dammunan hatsi a gona, gashi kuwa, sai damina ya tashi ya kuma tsaya a tsaye, sai kuma, dammunanku suka zo a kewaye suka rusuna wa damina." 8 'Yan'uwansa suka ce masa, "Lallai zaka yi sarauta a kanmu? Lallai kuwa zaka yi mulki a kanmu?" Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkansa saboda kuma maganganunsa. 9 Ya sake yin wani mafarkin ya gaya wa 'yan'uwansa. Yace, "Duba, Na yi wani mafarkin: Rana da wata da taurari sha ɗaya sun rusuna mani." 10 Ya gaya wa mahaifinsa kamar yadda ya gaya wa 'yan'uwansa, mahaifinsa kuma ya tsauta masa. Yace masa, "Wanne irin mafarki ne ka yi haka? Ko hakika mahaifiyarka da Ni da 'yan'uwanka maza za mu zo mu rusuna ƙasa a gare ka?" 11 'Yan'uwansa suka yi kishin sa, amma mahaifinsa ya ajiye al'amarin a rai. 12 'Yan'uwansa suka tafi kiwon dabbobin mahaifinsu a Shekem. 13 Isra'ila ya cewa Yosef, "Ba 'yan'uwanka na kiwon dabbobin a Shekem ba? Zo, zan kuma aike ka wurin su." Yosef yace masa, "Na shirya." 14 Yace masa, "Ka tafi yanzu, ka duba ko 'yan'uwanka na lafiya ko dabbobin kuma na lafiya, sai ka kawo mani magana." Sai Yakubu ya aike shi daga Kwarin Hebron, Yosef kuma ya tafi Shekem. 15 Wani mutum ya sami Yosef. Duba, Yosef yana ta gararanba a saura. Mutumin ya tambaye shi, "Me kake nema?" 16 Yosef yace, "Ina neman 'yan'uwana ne. Ka gaya mani, ina roƙon ka, inda suke kiwon dabbobin." 17 Mutumin yace, "Sun bar nan wurin, domin na ji suna cewa, 'Bari mu tafi Dotan."' Yosef ya bi bayan 'yan'uwansa ya kuma same su a Dotan. 18 Suka hange shi daga nesa, kafin kuma ya iso kusa da su, suka shirya makirci gãba da shi su kashe shi. 19 'Yan'uwansa suka ce wa junansu, "Duba, mai mafarkin nan yana tafe. 20 Ku zo yanzu, saboda haka, bari mu kashe shi mu kuma jefa shi cikin ɗaya daga cikin ramukan. Za mu ce, 'Naman jeji ya cinye shi.' Za mu ga abin da zai fãru da mafarkansa." 21 Ruben ya ji labari, kuma ya ceto shi daga hannunsu. Ya ce, "Kada mu ɗauki ransa." 22 Ruben yace masu, "Kada ku zubar da jini. Ku jefa shi cikin wannan ramin dake cikin jeji, amma kada ku ɗora hannu a kansa" - domin ya ceto shi daga hannunsu ya maida shi wurin mahaifinsa. 23 Sai ya kasance da Yosef ya iso wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa kyakkyawar rigarsa. 24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin ramin. Ramin ba komai a ciki babu ma ruwa a ciki. 25 Suka zauna, su ci abinci. Suka ɗaga idanuwansu suka duba, kuma, duba, zangon Isma'ilawa na tafe daga Giliyad, tare da raƙummansu ɗauke da kayan yaji da man ƙanshi da kayan ƙanshi. Suna tafiya zasu kai su Masar. 26 Yahuda ya cewa 'yan'uwansa, "Ina ribar da ke ciki idan muka kashe ɗan'uwanmu muka kuma rufe jininsa? 27 Ku zo, mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada dai mu ɗora hannunmu a kansa. Gama shi ɗan'uwanmu ne, jikinmu." 'Yan'uwansa suka saurare shi. 28 Midiyawan fatake suna wuce wa. 'Yan'uwan Yosef suka jawo shi, suka fito da shi daga rijiyar. Suka sayar da Yosef ga Isma'ilawa a kan azurfa ashirin. Isma'ilawa suka ɗauki Yosef zuwa cikin Masar. 29 Ruben ya dawo ga ramin, kuma, duba, Yosef ba shi cikin ramin. Ya yage tufafinsa. 30 Ya dawo wurin 'yan'uwansa ya ce, "Yaron ba shi a wurin! Ni kuma, ina zan tafi?" 31 Suka yanka akuya, daga nan kuma suka ɗauki rigar Yosef suka tsoma a cikin jinin. 32 Sa'an nan suka kawo ta wurin mahaifinsu suka ce, "Mun tsinci wannan. Muna roƙon ka, ka duba ko rigar ɗanka ce ko a'a." 33 Yakubu ya gane ta ya ce, "Rigar ɗana ce. Naman daji ya cinye shi. Babu shakka an yayyaga Yosef gutsu-gutsu." 34 Yakubu ya yayyage tufafinsa, ya sanya tsummokara a kwankwasonsa. Ya yi makokin ɗansa kwanaki da yawa. 35 Dukkan 'ya'yansa maza da 'ya'yansa mata suka tashi domin su ta'azantar da shi, amma ya ƙi ya ta'azantu. Ya ce, "Tabbas zan gangara zuwa Lahira cikin makoki domin ɗana." Mahaifinsa ya yi kuka domin sa. 36 Midiyawa kuwa suka saida shi a Masar ga Fotifa, wani maƙaddashin Fir'auna, hafsan masu tsaro.

Sura 38

1 Sai ya kasance a wannan lokaci Yahuda ya bar 'yan'uwansa ya je ya zauna da wani Ba'addulmiye, mai suna Hira. 2 Ya haɗu da wa ta ɗiyar wani mutum Bakananiye mai suna Shuwa. Ya aure ta ya kuma kwana da ita. 3 Ta ɗauki ciki ta sami ɗa, a ka sa masa suna Er. 4 Ta sake ɗaukar ciki ta sami ɗa. Ta kira sunansa Onan. 5 Ta sake samun wani ɗan ta kira sunansa Shela. A Kezib ne wurin da ta haife shi. 6 Yahuda ya samar wa Er mata, ɗan fãrinsa. Sunanta Tama ne. 7 Er, ɗan fãrin Yahuda, mugu ne a idanun Yahweh. Yahweh ya kashe shi. 8 Yahuda ya cewa Onan, "Ka kwana da matar ɗan'uwanka. Ka yi aikin ɗan'uwan miji a gare ta, ka samar wa ɗan'uwanka ɗa." 9 Onan ya san cewa ɗan ba zai zama na shi ba. Duk lokacin da ya kwana da matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyin a ƙasa domin kada ya samar wa ɗan'uwansa ɗa. 10 Abin nan da ya yi kuwa mugunta ce a idanun Yahweh. Yahweh ya kashe shi shima. 11 Daga nan Yahuda ya cewa Tama, surukarsa, "Ki yi zaman gwauruwa a gidan mahaifinki har sai Shela, ɗana, ya girma." Gama ya ji tsoro, "Shi ma wataƙila ya mutu, kamar 'yan'uwansa." Tama ta tashi ta kuma koma da zama gidan mahaifinta. 12 Bayan lokaci mai tsawo, ɗiyar Shuwa, matar Yahuda, ta mutu. Yahuda ya ta'azantu ya kuma tafi wurin sausayar tumakinsa a Timna, shi da abokinsa Hira Ba'addulmiye. 13 Aka gaya wa Tama, "Duba, surukinki zai tafi Timna domin sausayar tumakinsa." 14 Sai ta tuɓe tufafin gwaurancinta ta rufe kanta da gyale ta kuma lulluɓe jikinta. Ta zauna a ƙofar Enayim, wadda ke kan hanyar zuwa Timna. Domin ta ga Shela ya girma, amma ba a bayar da ita ba a gare shi a matsayin mata. 15 Sa'ad da Yahuda ya ganta ya zaci cewa karuwa ce saboda ta lulluɓe fuskarta. 16 Ya je wurin ta a bakin hanya ya kuma ce, "Zo, ina roƙon ki bari in kwana da ke" - domin bai san cewa surukarsa ba ce - sai kuma ta ce, "Mezaka bani domin ka kwana da ni?" 17 Ya ce, "Zan aiko maki da 'yar akuya daga garke." Ta ce, "Zaka bani diyya har sai ka aiko da ita?" 18 Ya ce, "Wacce irin diyya zan ba ki?" Ta maida amsa, "Zoben hatiminka da ɗamararka, da sandar dake a hannunka." Ya bayar dasu a gare ta ya kuma kwana da ita, sai ta sami ciki daga gare shi. 19 Ta tashi ta yi tafiyarta. Ta tuɓe lulluɓinta ta sanya tufafin gwaurancinta. 20 Yahuda ya aika da 'yar akuyar ta hannun abokinsa Ba'addulmiye saboda ya karɓo diyyar daga hannun matar, amma bai same ta ba. 21 Sai Ba'addulmiyen ya tambayi mutanen dake wurin, "Ina karuwar asiri dake zaune a Enayim a bakin hanya?" Suka ce, "Babu wata karuwar asiri dake zaune a nan." 22 Ya dawo wurin Yahuda yace, "Ban same ta ba. Kuma, mutanen wurin sun ce, 'Babu wata karuwar asiri dake zaune a nan."' 23 Yahuda yace, "Bari ta ajiye abubuwan, domin kada mu sha kunya. Tabbas, na aika da 'yar akuyar nan, amma ba ka same ta ba." 24 Sai ya kasance bayan wajen wata uku, sai a ka gaya wa Yahuda, "Tama surukarka ta aikata karuwanci, kuma tabbas, ta sami ciki ta haka." Yahuda yace, "Ku kawo ta nan bari a ƙona ta kuma." 25 Sa'ad da aka fito da ita, sai ta aika wa surukinta da saƙo, "Ta wurin mutumin dake da waɗannan nake da ciki." Ta ce, "Ina roƙon ka da ka gano mani waɗannan na waye, zoben tambarin da ɗamarar da sandar." 26 Yahuda ya gane su ya kuma ce, "Ta fi ni adalci, tunda ban bayar da ita ba a matsayin mata ga Shela, ɗana." Bai sake kwana da ita ba kuma. 27 Sai ya kasance da lokacin haihuwarta ya kai, duba, tagwaye ne ke cikin mahaifarta. 28 Sai ya kasance a lokacin da take haihuwar ɗaya ya fito da hannunsa waje, unguwar zomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura masa a hannu ta kuma ce, "Wannan ne ya fãra fitowa." 29 Amma daga nan sai ya maida hannunsa, kuma, duba, sai ɗan'uwansa ya fito farko. Unguwar zomar ta ce, "Ya ya ka faso waje!" Sai aka sa masa suna Ferez. 30 Daga nan ɗan'uwansa ya fito, wanda yake da jan zare a hannu, aka kuma sa masa suna Zera.

Sura 39

1 Aka kawo Yosef zuwa Masar. Fotifa, maƙaddashin Fir'auna kuma hafsan masu tsaro kuma Bamasare, ya sawo shi daga Isma'ilawa, waɗanda suka kawo shi nan. 2 Yahweh yana tare da Yosef ya kuma zama wadataccen mutum. Yana zaune cikin gidan ubangidansa Bamasare. 3 Ubangidansa ya ga cewa Yahweh na tare da shi kuma Yahweh na wadata kowanne abu da ya yi. 4 Yosef ya sami tagomashi a idanunsa. Ya bautawa Fotifa. Fotifa ya maida Yosef shugaban gidansa, da kowanne abu da ya mallaka, ya sanya ƙarƙashin lurarsa. 5 Sai ya kasance tun lokacin da ya maida shi shugaba bisa gidansa da bisa kowanne abu da ya mallaka, sai Yahweh ya albarkaci gidan Bamasaren saboda Yosef. Albarkar Yahweh tana bisa kowanne abu da Fotifa yake da shi a cikin gida da gona. 6 Fotifa ya sanya kowanne abu da yake da shi a ƙarƙashin lurar Yosef. Ba ya buƙatar ya yi tunani game da komai sai dai kawai abincin da zai ci. Shi dai Yosef kyakkyawa ne gwanin sha'awa kuma. 7 Sai ya kasance bayan wannan matar ubangidansa ta yi sha'awar Yosef. Ta ce, "Ka kwana da ni." 8 Amma ya ƙi, ya kuma ce wa matar ubangidansa, "Duba, ubangidana ba ya kulawa da abin da nake yi a cikin gidan nan, kuma ya sanya kowanne abu da yake da shi a ƙarƙashin lura ta. 9 Babu wanda ya fi ni girma a cikin gidan nan. Bai hana mani komai ba sai dai ke, saboda ke matarsa ce. Ta yaya daga nan zan yi wannan irin babbar mugunta da zunubi gãba da Allah?" 10 Ta dinga magana da Yosef rana bayan rana, amma ya ƙi ya kwana da ita ko ya kasance tare da ita. 11 Sai ya kasance wata rana, Yosef ya shiga cikin gidan domin ya yi aikinsa. Babu ko ɗaya daga cikin mutanen gidan dake cikin gidan. 12 Ta kama shi ta tufafinsa ta ce kuma, "Ka kwana da ni." Ya bar tufafinsa a hannunta, ya tsere, ya fita waje kuma. 13 Sai ya kasance, sa'ad da taga cewa ya bar tufafinsa a cikin hannunta ya kuma tsere waje, 14 sai ta kira mutanen gidanta ta ce masu, "Duba, Fotifa ya kawo Ba'ibraniye ya wulaƙanta mu. Ya shigo wurina ya kwana da ni, na kuwa yi ihu. 15 Sai ya kasance sa'ad da ya ji ina ihu, sai ya bar tufafinsa tare da ni, ya tsere, ya kuma fita waje." 16 Ta ajiye tufafinsa a kusa da ita har sai da ubangidansa ya zo gida. 17 Ta faɗi masa wannan bayyani, "Ba'ibraniyen nan bawa wanda ka kawo mana, ya shigo domin ya wulaƙanta ni. 18 Sai ya kasance sa'ad da nayi ihu, ya bar tufafinsa tare da ni ya kuma tsere waje." 19 Sai ya kasance, sa'ad da ya ji bayanin da matarsa ta faɗi masa, "Wannan ne abin da bawanka ya yi mani," sai ya fusata sosai. 20 Ubangidan Yosef ya ɗauke shi ya saka shi cikin kurkuku, wurin da a ke tsaron 'yan kurkukun sarki. Ya na nan a cikin kurkukun. 21 Amma Yahweh na tare da Yosef ya kuma nuna alƙawarin aminci a gare shi. Ya kuma ba shi tagomashi a idanun shugaban kurkukun. 22 Shugaban kurkukun ya bayar da dukkan 'yan kurkukun dake cikin kurkukun cikin hannun Yosef. Duk abin da suka yi a nan, Yosef ne ke shugabancin sa. 23 Shugaban kurkuku ba ya kulawa da kowanne abu dake cikin hannunsa, saboda Yahweh na tare da shi. Duk abin da ya yi Yahweh na wadatar da shi.

Sura 40

1 Sai ya kasance bayan waɗannan abubuwa, mai riƙon ƙoƙon sha na sarkin Masar da mai toye-toye na sarki suka ɓata wa ubangidansu, sarkin Masar rai. 2 Fir'auna ya ji haushin ofisoshinsa biyu, da shugaban ma su riƙon ƙoƙon sha da shugaban masu toye-toye. 3 Ya sa aka tsare su a cikin gidan shugaban masu tsaro, a cikin wannan kurkuku inda aka tsare Yosef. 4 Shugaban masu tsaron ya miƙa Yosef a gare su, ya kuma yi masu hidima. Suka ci gaba a tsare na wani lokaci. 5 Dukkan su biyu sai suka yi wani mafarki - mai riƙon ƙoƙon sha da mai toye-toye na sarkin Masar waɗanda ke tsare a kurkukun - kowanne mutum ya yi nasa mafarki a dare ɗaya, kuma kowanne mafarkin da tasa fassarar. 6 Yosef ya zo wurin su da safe ya kuma gan su. Duba, suna cikin baƙinciki. 7 Ya tambayi ofisoshin Fir'auna waɗanda ke tare da shi a tsare a cikin gidan ubangidansa, ya ce, "Meyasa kuke baƙinciki a yau?" 8 Suka ce masa, "Dukkan mu biyu munyi wani mafarki kuma babu wanda ya iya fassara su." Yosef yace masu, "Fassarori ba ta Allah ba ce?" Ku faɗa mani, ina roƙon ku." 9 Shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ya gaya wa Yosef mafarkinsa. Ya ce masa, "A cikin mafarkina, duba, itacen inabi na gabana. 10 A itacen inabin akwai rassa uku. Suka tsiro, suka yaɗu da 'ya'ya nan da nan inabin kuma suka nuna. 11 ‌Ƙoƙon Fir'auna yana hannuna. Na ɗauki 'ya'yan inabin na matse su cikin ƙoƙon Fir'auna, sai kuma na miƙa ƙoƙon cikin hannun Fir'auna." 12 Yosef yace masa, "Wannan ce fassarar sa. Rassan uku kwanaki uku ne. 13 A cikin kwanaki uku Fir'auna zai ɗaga kanka ya kuma mai da kai wurin aikinka. Za ka sanya ƙoƙon Fir'auna cikin hannunsa, kamar dai sa'ad da kake mai riƙon ƙoƙon shansa. 14 Amma ka tuna da ni sa'ad da komai ya tafi lafiya da kai, ina roƙon ka kuma ka nuna mani alheri. Ka ambace ni wurin Fir'auna a fito da ni daga wannan kurkuku. 15 Domin tabbas an sato ni ne daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma banyi wani abu ba da zai sanya su su sani cikin wannan rami ba." 16 Sa'ad da shugaban masu toye-toye ya ga cewa fassarar ta yi daɗi, ya cewa Yosef, "Ni ma nayi mafarki, kuma, duba, kwanduna uku na gurasa suna bisa kaina. 17 A cikin kwandon na sama akwai kowanne irin kayan toye-toye domin Fir'auna, amma tsuntsaye suka cinye su daga cikin kwandon a bisa kaina." 18 Yosef ya amsa ya ce, "Wannan ce fassarar sa. Kwandunan uku kwanaki uku ne. 19 A cikin kwanaki uku Fir'auna zai ɗaga kanka daga gare ka zai kuma sarƙafe ka bisa itace. Tsuntsaye kuma zasu cinye namanka daga gare ka." 20 Sai ya kasance a rana ta uku ranar tunawa da haihuwar Fir'auna ce. Sai ya yi wa dukkan bayinsa biki. Sai ya ɗaga kan shugaban masu riƙon ƙoƙon sha da shugaban masu toye-toye, daga cikin bayinsa. 21 Ya maido da shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ga hidimarsa, ya kuma sake sanya ƙoƙon cikin hannun Fir'auna. 22 Amma ya sargafe shugaban masu toye-toye, kamar yadda Yosef ya yi masu fassara. 23 Duk da haka shugaban masu riƙon ƙoƙon shan bai tuna da Yosef ba, amma ya manta da shi.

Sura 41

1 Sai ya kasance bayan shekaru biyu cur Fir'auna ya yi wani mafarki. Duba, yana tsaye bakin Nilu. 2 Duba, sai ga wasu shanu bakwai sun fito daga Nilu, masu ban sha'awa da ƙiba, suna kuma kiwo a cikin iwa. 3 Duba, ga wasu shanun bakwai sun fito bayan su daga cikin Nilu, marasa ban sha'awa ramammu kuma. Suka tsaya gefen waɗancan shanun a bakin kogin. 4 Daga nan shanun marasa ban sha'awa ramammu kuma suka cinye shanun masu ban sha'awa da ƙiba. Daga nan Fir'auna ya farka. 5 Daga nan kuma ya sake yin barci ya kuma sake yin mafarki karo na biyu. Duba, kawunan hatsi bakwai sun fito bisa kara ɗaya, cikakku masu kyau kuma. 6 Gashi, kawuna bakwai, ƙanana waɗanda kuma iskar gabas ke kakkaɓewa, suka fito bayan su. 7 ‌Ƙananan kawunan suka haɗiye kawunan cikakku masu kyau kuma. Fir'auna ya farka, kuma, duba, ashe mafarki ne. 8 Sai ya kasance da safe ruhunsa ya damu. Ya aika aka kira dukkan 'yan dabo da masu hikima na Masar. Fir'auna ya gaya masu mafarkansa, amma babu wani da ya iya fassara su ga Fir'auna. 9 Daga nan shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ya ce wa Fir'auna, "A yau ina tunani game da laifuffukana. 10 Fir'auna ya yi fushi da bayinsa, ya kuma sanya ni cikin tsaro a cikin gidan shugaban masu tsaro, shugaban masu tuya tare da ni. 11 Muka yi mafarki a cikin dare ɗaya, shi da ni. Muka yi mafarki kowanne mutum bisa ga fassarar mafarkinsa. 12 Tare da mu a can akwai wani saurayin mutum Ba'ibraniye, bawan shugaban masu tsaro. Muka faɗi masa kuma ya fassara mana mafarkanmu. Ya fassara wa kowannen mu bisa ga mafarkinsa. 13 Sai ya kasance kamar yadda ya fassara mana, haka ya faru. Fir'auna ya maido ni bisa aikina, amma ɗayan ya sarƙafe shi." 14 Daga nan Fir'auna ya aika aka kuma kirawo Yosef. Nan da nan suka fito da shi daga ramin. Ya kuma yi aski, ya canza sutura, ya kuma fito zuwa wurin Fir'auna. 15 Fir'auna ya cewa Yosef, "Na yi mafarki, amma babu mai fassara. Amma na ji labarinka, cewa idan ka ji mafarki kana iya fassara shi." 16 Yosef ya amsawa Fir'auna, cewa, "Ba ni ba ne. Allah zai amsawa Fir'auna da tagomashi." 17 Fir'auna ya yi magana da Yosef, "A cikin mafarkina, duba, ina tsaye a bakin Nilu. 18 Gashi, shanu bakwai suka fito daga cikin Nilu, masu ƙiba da ban sha'awa, suna kuma kiwo cikin iwa. 19 Gashi, wasu shanun bakwai suka fito bayan su, marasa ƙarfi, marasa ban sha'awa, ramammu kuma. A cikin dukkan ƙasar Masar ban taɓa ganin wani abin rashin ban sha'awa ba kamar su. 20 Shanun marasa ƙiba da rashin ban sha'awa suka cinye shanun na farko masu ƙiba. 21 Sa'ad da suka cinye su, ba za a ma san cewa sun cinye su ba, domin sun kasance marasa ban sha'awa kamar dã. Daga nan na farka. 22 Na duba a cikin mafarkina, kuma, duba, kawuna bakwai na hatsi suka fito bisa kara ɗaya, cikakku masu kyau. 23 Gashi kuwa, ƙarin kawuna bakwai - busassu, ƙanana, waɗanda kuma iskar gabas ke kakkaɓewa - suka fito bayansu. 24 ‌Ƙananan kawunan suka haɗiye kawunan bakwai masu kyau. Na faɗi waɗannan mafarkai ga masu dabo, amma babu wani da zai yi bayyanin su a gare ni." 25 Yosef ya cewa Fir'auna, "Mafarkan Fir'auna ɗaya ne. Abin da Allah ke gaf da aiwatar wa, ya bayyana wa Fir'auna. 26 Shanun masu kyau guda bakwai shekaru bakwai ne, kawunan hatsin bakwai kuma shekaru bakwai ne. Mafarkan iri ɗaya ne. 27 Shanun bakwai ramammu marasa ban sha'awa da suka fito bayan su shekaru bakwai ne, haka nan kuma kawunan hatsin ƙanana da iskar gabas ke kakkaɓe wa shekaru ne bakwai na yunwa. 28 Wannan batun ne na faɗawa Fir'auna. Abin da Allah ke gaf da aiwatar wa ya bayyana wa Fir'auna. 29 Duba, shekaru bakwai na yalwa zasu zo cikin dukkan ƙasar Masar. 30 Shekaru bakwai na yunwa zasu zo bayan su, za a kuma manta da dukkan yalwar da aka yi a ƙasar Masar, kuma yunwar za ta lalata ƙasar. 31 Ba za a tuna da yalwar ba a cikin ƙasar saboda yunwar da za ta biyo baya, domin za ta zama da tsanani sosai. 32 Cewa an maimaita wa Fir'auna mafarkin saboda Allah ya tabbatar da al'amarin ne, kuma Allah zai aiwatar ba da daɗewa ba. 33 Yanzu bari Fir'auna ya nemi wani mutum mai fahimta da hikima, ya kuma ɗora shi bisa ƙasar Masar. 34 Bari Fir'auna ya zaɓi shugabanni bisa ƙasar, bari kuma su ɗauki kashi biyar na dukkan amfanin Masar a cikin shekaru bakwai na yalwa. 35 Bari su tattara dukkan abincin waɗannan shekaru masu kyau dake zuwa su kuma ajiye hatsi a ƙarƙashin ikon Fir'auna, domin abincin da za a yi amfani da shi a cikin biranen. Su adana shi. 36 Abincin zai zama abin wadatar wa domin ƙasar domin kuma shekaru bakwai na yunwa da zasu kasance a ƙasar Masar. Ta wannan hanyar ƙasar ba zata lalace ba ta wurin yunwar." 37 Wannan shawara ta yi kyau a idanun Fir'auna da idanun dukkan bayinsa. 38 Fir'auna ya cewa bayinsa, "Za mu iya samun wani mutum kamar wannan, wanda Ruhun Allah ke cikinsa?" 39 Sai Fir'auna ya cewa Yosef, "Tunda Allah ya nuna maka dukkan waɗannan abubuwa, babu wani mafi fahimta da hikima kamar kai. 40 Zaka kasance bisa gidana, kuma bisa ga maganar ka za a yi mulkin dukkan mutanena. A bisa kursiyi ne kawai zan fi ka girma." 41 Fir'auna ya cewa Yosef, "Duba, na sanya ka bisa dukkan ƙasar Masar." 42 Fir'auna ya cire zoben hatiminsa daga hannunsa ya sanya a hannun Yosef. Ya yi masa sutura da suturar linin mai laushi, ya kuma sanya sarƙar zinariya a wuyansa. 43 Ya sanya shi ya tuƙa karusarsa ta biyu da ya mallaka. Mutane suka yi sowa a gabansa, "Gwiwa a durƙushe." Fir'auna ya sanya shi bisa dukkan ƙasar Masar. 44 Fir'auna ya cewa Yosef, "Ni ne Fir'auna, baya gare ka kuma, babu mutumin da zai ɗaga hannunsa ko ƙafarsa a cikin dukkan ƙasar Masar." 45 Fir'auna ya kira Yosef da suna "Zafenat-Faniya." Ya ba shi Asenat, ɗiyar Fotifera firist na On, a matsayin mata. Yosef ya fita bisa ƙasar Masar. 46 Yosef yana da shekaru talatin sa'ad da ya tsaya a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Yosef ya fita daga gaban Fir'auna, ya kuma tafi cikin dukkan ƙasar Masar. 47 A cikin shekaru bakwai na yalwa ƙasar ta fitar da amfani a yalwace. 48 Ya tattara dukkan abinci na shekaru bakwai dake cikin ƙasar Masar ya kuma sanya abincin a cikin biranen. Ya sanya a cikin kowanne birni abincin gonakin dake kewaye da shi. 49 Yosef ya ajiye hatsi kamar rairayin teku, da yawan gaske har ya daina ƙirgawa, saboda ya zarce ƙirgawa. 50 Yosef ya haifi 'ya'ya biyu kafin zuwan shekarun yunwa, waɗanda Asenat, ɗiyar Fotifa firist na On, ta haifa masa. 51 Yosef ya kira sunan ɗan fãrinsa Manasse, domin ya ce, "Allah ya sa na manta da dukkan damuwata da dukkan gidan mahaifina." 52 Ya kira sunan ɗan na biyu Ifraim, domin ya ce, "Allah ya maida ni mai bada 'ya'ya a cikin ƙasar wahalata." 53 Shekaru bakwai na yalwa da suka kasance a ƙasar Masar suka kawo ƙarshe. 54 Aka fãra shekaru bakwai na yunwa, kamar yadda Yosef ya faɗa. Aka yi yunwa a cikin dukkan ƙasashen, amma a cikin dukkan ƙasar Masar akwai abinci. 55 Sa'ad da dukkan ƙasar Masar suka fãra yunwa, mutanen suka kira ga Fir'auna da ƙarfi domin abinci. Fir'auna ya cewa dukkan Masarawa, "Ku je wurin Yosef ku kuma yi abin da ya ce." 56 Yunwa tana bisa dukkan fuskar ƙasar. Yosef ya buɗe dukkan gidajen ajiya ya sayar wa da Masarawa. Yunwa ta yi tsanani a ƙasar Masar. 57 Dukkan duniya na zuwa Masar su sayi hatsi daga wurin Yosef, saboda yunwar ta yi tsanani a dukkan duniya.

Sura 42

1 Yanzu Yakubu ya sami sani cewa akwai hatsi a Masar. Ya ce wa 'ya'yansa maza, "Meyasa kuke kallon juna?" 2 Ya ce, "Ku saurara, Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sawo domin mu dagacan domin mu rayu kada kuma mu mutu." 3 'Yan'uwan Yosef goma suka gangara domin su sawo hatsi daga Masar. 4 Amma Benyamin, ɗan'uwan Yosef, Yakubu bai aike shi ba tare da 'yan'uwansa, saboda ya ji tsoron cewa wani bala'i na iya afko masa. 5 'Ya'yan Isra'ila na cikin waɗanda suka zo saye, domin akwai yunwa a cikin ƙasar Kan'ana. 6 Yanzu dai Yosef shi ne gwamna a ƙasar. Shi ne ke saida wa dukkan mutanen ƙasar. 'Yan'uwan Yosef suka zo suka kuma rusuna masa da fuskokinsu ƙasa. 7 Yosef ya ga 'yan'uwansa ya kuma gãne su, amma ya ɓadda masu kamarsa ya kuma yi magana da su da zafi. Ya ce masu, "Daga ina kuka fito?" Suka ce, "Daga ƙasar Kan'ana domin mu sayi abinci." 8 Yosef ya gãne 'yan'uwansa, amma su basu gãne shi ba. 9 Daga nan Yosef ya tuna da mafarkan da ya yi game da su, ya kuma ce masu, "Ku 'yan leƙen asirin ƙasa ne! kun zo ku ga sassan ƙasar da basu da tsaro." 10 Suka ce masa, "A'a, shugabana. Bayinka sun zo sayen abinci ne. 11 Dukkan mu 'ya'yan mutum ɗaya ne. Mu mutane ne masu gaskiya. Bayinka ba 'yan leƙen asirin ƙasa ba ne." 12 Ya ce masu, "A'a, kun zo ku ga sassan ƙasar da ba su da tsaro." 13 Suka ce, "Mu bayinka 'yan'uwa sha biyu ne, 'ya'yan mutum ɗaya a cikin ƙasar Kan'ana. Duba, ƙaramin mu a yau yana tare da mahaifinmu, ɗayan ɗan'uwan kuma baya da rai." 14 Yosef yace masu, "Abin da na ce maku ke nan; ku 'yan leƙen asirin ƙasa ne. 15 Ta haka za a gwada ku. Da ran Fir'auna, ba zaku bar nan ba, sai idan ƙaramin ɗan'uwanku ya zo nan. 16 Ku aiki ɗaya daga cikin ku ya je ya zo da ɗan'uwanku. Zaku zauna a kurkuku, domin a gwada maganganunku, ko akwai gaskiya a cikin ku." 17 Ya sa dukkan su a ka kulle su har kwana uku. 18 A rana ta uku Yosef yace masu, "Ku yi haka kuma ku rayu, domin ina tsoron Allah. 19 Idan ku mutane ne masu gaskiya, bari ɗaya daga cikin 'yan'uwanku a tsare shi a kurkuku, amma ku ku tafi, ku ɗauki hatsi domin yunwar gidajenku. 20 Ku kawo mani ƙaramin ɗan'uwanku domin a tabbatar da maganganunku kuma ba za ku mutu ba." Sai suka yi haka. 21 Suka cewa juna, "Babu shakka mun yi laifi game da ɗan'uwanmu yadda muka ga ƙuncin ransa sa'ad da ya roƙe mu, amma muka ƙi sauraron sa. Saboda haka wannan ƙunci ya zo bisanmu." 22 Ruben ya amsa masu, "Ban gaya maku ba, 'Kada kuyi zunubi game da saurayin, amma baku saurare ni ba? Yanzu, duba, ana neman jininsa daga hannunmu." 23 Basu san cewa Yosef ya fahimce su ba, domin akwai mai fassara a tsakanin su. 24 Ya juya daga gare su ya yi kuka. Ya kuma dawo gare su ya yi magana da su. Ya ɗauki Simiyon daga cikin su ya ɗaure shi a gaban idanunsu. 25 Daga nan Yosef ya umarci bayinsa su cika buhunan 'yan'uwansa da hatsi, kuma su maida wa kowa kuɗinsa cikin buhunsa, su kuma basu kayan masarufi domin tafiyarsu. A ka yi haka domin su. 26 Suka ɗora wa jakunansu hatsi suka kuma yi tafiyar su daga wurin. 27 Yayin da ɗaya daga cikin su ya buɗe buhunsa domin ya ciyar da jakinsa a wurin hutawar su, ya ga kuɗinsa. Duba, suna bakin buhunsa. 28 Ya cewa 'yan'uwansa, "An maida mani kuɗina, ku dube su; suna bakin buhuna." Zukatansu suka nitse, suka kuma juya suna rawar jiki ga junansu, suna cewa, "Mene ne haka da Allah ya yi mana?" 29 Suka tafi wurin Yakubu, mahaifinsu a cikin ƙasar Kan'ana suka kuma gaya masa dukkan abin da ya faru da su. Suka ce, 30 "Mutumin, ubangijin ƙasar, ya yi magana da mu da zafi ya zaci cewa mu 'yan leƙen asirin ƙasa ne. 31 Muka ce masa, "Mu mutane ne masu gaskiya. Ba 'yan leƙen asirin ƙasa bane. 32 Mu 'yan'uwa ne sha biyu, 'ya'ya maza na mahaifinmu. ‌Ɗaya baya da rai, ƙaramin kuma yau yana tare da mahaifinmu a ƙasar Kan'ana.' 33 Mutumin, ubangijin ƙasar, ya ce mana, 'Ta haka zan sani cewa ku mutane ne masu gaskiya. Ku bar ɗaya daga cikin 'yan'uwanku tare da ni, ku ɗauki hatsi domin yunwar dake gidajenku, ku kuma yi tafiyarku. 34 Ku kawo ƙaramin ɗan'uwanku wuri na. Daga nan zan sani cewa ku ba 'yan leƙen asirin ƙasa ba ne, amma ku mutane ne masu gaskiya. Daga nan zan saki ɗan'uwanku a gare ku, kuma zaku yi sana'a a ƙasar."' 35 Sai ya kasance yayin da suka zazzage buhunansu, duba, kowanne mutum jakkar azurfarsa na cikin buhunsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga jakkunan azurfarsu, sai suka tsorata. 36 Yakubu mahaifinsu ya ce masu, "Kun salwantar mani da 'ya'yana. Yosef ba shi da rai, Simiyon kuma ya tafi, kuma zaku ɗauke Benyamin. Waɗannan abubuwa dukka gãba suke da ni." 37 Ruben ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Kana iya kashe 'ya'yana biyu idan ban maido maka da Benyamin ba. Ka sanya shi cikin hannuwana, kuma zan sake maido maka da shi." 38 Yakubu yace, '‌Ɗana ba zai tafi tare da ku ba. Domin ɗan'uwansa ya mutu shi kaɗai kuma ya rage. Idan wani bala'i ya zo masa a hanyar da zaku tafi, daga nan zaku kawo furfurata da baƙinciki zuwa Lahira."

Sura 43

1 Yunwa ta yi tsanani a ƙasar. 2 Sai ya kasance sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce masu, "Ku sake komawa; ku sayo mana ɗan abinci." 3 Yahuda yace masa, "Mutumin ya yi mana kashedi sosai, 'Ba za ku ga fuskata ba har sai ɗan'uwanku na tare da ku.' 4 Idan ka aika ɗan'uwanmu tare da mu, to za mu gangara mu je mu sayo maka abinci. 5 Amma idan ba ka aika da shi ba, ba za mu tafi ba. Domin mutumin ya ce mana, 'Ba za ku ga fuskata ba har sai ɗan'uwanku na tare da ku."' 6 Isra'ila yace, "Meyasa kuka yi mani mummunan abu haka ta wurin gaya wa mutumin cewa kuna da wani ɗan'uwan?" 7 Suka ce, "Mutumin ya yi tambaya dalla-dalla game da mu da iyalinmu. Ya ce, 'Mahaifinku yana nan da rai? Kuna da wani ɗan'uwan? Muka amsa masa bisa ga waɗannan tambayoyi. Ta yaya zamu san cewa zai ce, 'Ku kawo ɗan'uwanku nan?"' 8 Yahuda ya cewa Isra'ila mahaifinsa, "Ka aiki saurayin tare da ni. Zamu tashi mu tafi domin mu rayu kada kuma mu mutu, dukkanmu, da kai, da kuma 'ya'yanmu dukka. 9 Ni zan tsaya domin sa. Zaka riƙe ni hakkinsa. Idan ban dawo maka da shi ba na kuma tsaida shi a gabanka ba, daga nan bari in ɗauki laifin har abada. 10 Domin idan da ba mu yi jinkiri ba, tabbas da yanzu mun dawo karo na biyu. 11 Mahaifinsu Isar'ila yace masu, "Idan haka abin yake, yanzu kuyi haka. Ku ɗauki mafi kyau daga cikin amfanin ƙasar a cikin jakkunanku. Ku tafi da su kyauta ga mutumin - su man shafawa da zuma, kayan yaji da ƙaro, tsabar 'ya'yan itace dana almond. 12 Ku ɗauki kuɗi ka shi biyu a hannunku. Kuɗaɗen da aka maido maku da aka buɗe buhunanku, ku ɗauka a cikin hannunku. Wataƙila kuskure ne. 13 Ku ɗauki ɗan'uwanku kuma. Ku tashi ku sake tafiya wurin mutumin. 14 Bari Allah maɗaukaki ya baku jinƙai a gaban mutumin, domin ya sakar maku ɗaya ɗan'uwanku da Benyamin. Idan na rasa 'ya'yana, na rasa su." 15 Mutanen suka ɗauki kyautar, a hannunsu kuma suka ɗauki kuɗi kashi biyu, tare da Benyamin. Suka tashi kuma suka tafi suka gangara zuwa Masar suka je suka tsaya kuma a gaban Yosef. 16 Sa'ad da Yosef yaga Benyamin tare da su, ya cewa ma'aikacin gidansa, "Ka kawo mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya ta, domin mutanen zasu ci tare da ni da rana." 17 Ma'aikacin ya yi yadda Yosef ya ce. Ya kawo mutanen cikin gidan Yosef. 18 Mutanen suka tsorata saboda an kawo su cikin gidan Yosef. Suka ce, "Saboda kuɗaɗen da aka maido mana cikin buhunanmu a zuwanmu na farko aka kawo mu ciki, domin ya sami zarafin gãba da mu. Zai iya ɗaure mu ya ɗauke mu a matsayin bayi, ya kuma karɓe jakkunanmu." 19 Suka kusanci ma'aikacin gidan Yosef, 20 suka kuma yi magana da shi a bakin ƙofar gidan, cewa, "Shugabana, mun zo karo na farko sayen abinci. 21 Sai ya kasance, da muka isa wurin hutawa, sai muka buɗe buhunanmu, kuma, duba, kuɗin kowanne mutum na bakin buhunsa, kuɗaɗenmu kuma nada nauyinsu dai-dai. Mun sake kawo su a hannuwanmu. 22 Mun sake kuma kawo wasu kuɗaɗen domin mu sayi abinci. Ba mu san wanda ya sanya kuɗaɗenmu cikin buhunanmu ba." 23 Ma'aikacin yace, "Salama a gareku, kada ku ji tsoro. Allahnku da Allahn mahaifinku ne ya sanya kuɗaɗenku a buhunanku. Na karɓi kuɗaɗenku." Daga nan ma'aikacin ya fito da Simiyon wurinsu. 24 Ma'aikacin ya kai mutanen cikin gidan Yosef. Ya basu ruwa, suka kuma wanke ƙafafunsu. Ya ciyar da jakkunansu. 25 Suka shirya kyaututtukan domin zuwan Yosef da rana, domin sun ji cewa zasu ci abinci a nan. 26 Sa'ad da Yosef ya zo gida, suka kawo kyaututtukan dake hannuwansu cikin gidan, suka kuma rusuna a gabansa har ƙasa. 27 Ya tambayi lafiyarsu ya kuma ce, "Mahaifinku na nan lafiya, tsohon da kuka yi maganar sa? Har yau yana nan da rai?" 28 Suka ce, "Bawanka mahaifinmu yana nan lafiya lau. Har yau yana nan da rai." Suka kwanta kuma suka rusuna har ƙasa. 29 Sa'ad da ya ɗaga idanunsa ya kalli Benyamin ɗan'uwansa, ɗan mahaifiyarsa, sai ya ce, "Wannan ne ƙaramin ɗan'uwanku da kuka yi mani maganarsa?" Daga nan ya ce, "Allah ya yi maka alheri, ɗana." 30 Yosef ya yi hanzari ya fita daga ɗakin, saboda ya motsu sosai game da ɗan'uwansa. Ya nemi wurin da zai yi kuka. Ya tafi ɗakinsa ya yi kuka a can. 31 Ya wanke fuskarsa ya kuma fito. Ya kame kansa, ya ce, "A raba abincin." 32 Bayin suka yi wa Yosef hidima shi kaɗai, suka kuma yi wa 'yan'uwan hidima su kaɗai. Masarawan suka ci tare da shi su kaɗai, saboda Masarawa ba zasu ci abinci tare da Ibraniyawa ba, domin yin haka abin ƙyama ne ga Masarawa. 33 'Yan'uwan suka zauna a gabansa, na farko bisa ga matsayin haihuwarsa, ƙaramin kuma bisa ga samartakarsa. Mutanen suka yi mamaki tare. 34 Yosef ya aika masu kaso daga abincin dake gabansa. Amma kason Benyamin ya yi sau biyar fiye dana 'yan'uwansa. Suka sha suka kuma yi murna tare da shi.

Sura 44

1 Yosef ya umarci ma'aikacin gidansa, ya ce, "Ka cika buhunan mutanen da abinci, iya yadda zasu iya ɗauka, ka kuma maida wa kowannen su kuɗinsa cikin bakin buhunsa. 2 Ka sanya kofina, kofin azurfa, cikin bakin buhun ƙaramin, da kuɗinsa na hatsi." Ma'aikacin ya yi yadda Yosef ya ce. 3 Da asuba, aka kuma sallami mutanen, su da jakkunansu. 4 Sa'ad da suka fice daga birnin ba su riga sun yi nisa ba, Yosef ya cewa ma'aikacinsa, "Tashi, ka bi bayan mutanen, idan kuma ka sha kansu, ka ce masu, 'Meyasa kuka maida mugunta domin nagarta? 5 Wannan ba kofin da maigidana ke sha bane, kofin da yake amfani da shi domin sihiri? Kun yi mugunta, wannan abin da kuka yi."' 6 Ma'aikacin ya sha kansu ya kuma faɗi waɗannan maganganu a gare su. 7 Suka ce masa, "Meyasa shugabana yake faɗin waɗannan maganganu haka? Bari ya yi nesa daga bayinka da zasu aikata irin wannan. 8 Duba, kuɗaɗen da muka samu a bakin buhunanmu, mun sake kawo maka su daga ƙasar Kan'ana. Ta yaya daga nan zamu yi sãtar azurfa ko zinariya daga gidan shugabanmu? 9 Duk wanda aka same shi a wurinsa daga cikin bayinka, bari ya mutu, mu kuma zamu zama bayin shugabana." 10 Ma'aikacin yace, "Yanzu kuma bari ya kasance bisa ga maganganunku. Shi wanda aka sami kofin a wurinsa zai zama bawana, ku kuma sauran zaku fita daga zargi." 11 Daga nan kowanne mutum ya yi hanzari ya sauko da buhunsa ƙasa, kowanne mutum kuma ya buɗe buhunsa. 12 Ma'aikacin ya bincike. Ya fãra da babban ya kuma ƙarashe da ƙaramin, aka kuma sami kofin a buhun Benyamin. 13 Daga nan suka kece tufafinsu. Kowanne mutum ya ɗora kaya a jakinsa suka kuma dawo cikin birni. 14 Yahuda da 'yan'uwansa suka zo gidan Yosef. Har yanzu yana nan, suka kuma rusuna a gabansa har ƙasa. 15 Yosef yace masu, "Mene ne kuka yi haka? Ba ku san cewa mutum kamar ni ina aikata sihiri ba?" 16 Yahuda yace, "Me za mu cewa shugabana? Me za mu faɗa? Ko yaya zamu baratar da kanmu? Allah ya gãno laifin bayinka. Duba, mu bayin shugabana ne, dukkan mu da wanda aka iske kofin a hannunsa." Yosef yace, 17 "Bari yayi nesa da ni da in aikata haka. Mutumin da aka iske kofin a hannunsa, wannan taliki zai zama bawana, amma game da ku sauran, ku tafi cikin salama ga mahaifinku." 18 Daga nan Yahuda ya matso kusa da shi ya kuma ce, "Shugabana, na roƙe ka bari bawanka ya faɗi magana cikin kunnuwan shugabana, bari kuma fushinka ya yi ƙuna gãba da bawanka, domin kamar dai Fir'auna kake. 19 Shugabana ya tambayi bayinsa, cewa, 'Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?' 20 Muka cewa shugabana, 'Muna da mahaifi, tsohon mutum, kuma da ɗan tsufansa, ƙarami ne. Amma ɗan'uwansa ya mutu, shi kaɗai kuma ya rage ga mahaifiyarsa, kuma mahaifinsa na ƙaunarsa.' 21 Daga nan ka cewa bayinka, 'Ku kawo shi nan a gare ni domin in gan shi.' 22 Bayan haka, muka cewa shugabana, 'Yaron ba zai iya barin mahaifinsa ba. Domin idan har ya bar mahaifinsa to mahaifinsa zai mutu.' 23 Daga nan ka cewa bayinka, 'Har sai ƙaramin ɗan'uwanku ya zo tare da ku, ba zaku sake ganin fuskata ba.' 24 Daga nan ya kasance sa'ad da muka tafi wurin bawanka mahaifina, muka faɗi masa maganganun shugabana. 25 Mahaifinmu yace, 'Ku sake komawa, ku sawo mana ɗan abinci.' 26 Daga nan muka ce, 'Ba za mu iya komawa ba. Idan ƙaramin ɗan'uwanmu yana tare da mu, daga nan zamu gangara mu tafi, domin ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba har sai ƙaramin ɗan'uwanmu yana tare da mu.' 27 Bawanka mahaifina ya ce mana, 'Kun san cewa matata ta haifa mani 'ya'ya maza biyu. 28 ‌Ɗaya daga cikin su ya fita daga gare ni kuma na ce, "Tabbas an yage shi gutsu-gutsu, ban sake ganin sa ba kuma tuni." 29 Yanzu idan kuka sake ɗauke wannan daga gare ni, kuma bala'i ya zo masa, zaku gangarar da furfurata da baƙinciki zuwa Lahira.' 30 Yanzu, saboda haka, sa'ad dana koma wurin bawanka mahaifina, kuma saurayin baya tare da mu, tun da rayuwarsa ɗaure take da rayuwar yaron, 31 zai kasance, sa'ad da ya ga yaron ba ya tare da mu, zai mutu. Bayinka zasu gangara da furfurar bawanka mahaifinmu da baƙinciki zuwa Lahira. 32 Gama bawanka ya zama wanda ya tsaya domin yaron ga mahaifina na kuma ce, 'Idan ban maido maka da shi ba, daga nan zan ɗauki laifin ga mahaifina har abada." 33 Saboda haka yanzu, ina roƙon ka bari bawanka ya tsaya a maimakon yaron a matsayin bawan shugabana, bari kuma yaron ya tafi tare da 'yan'uwansa. 34 Gama ta yaya zan tafi wurin mahaifina idan yaron ba ya tare da ni? Ina tsoron in ga mugun abin da zai zo bisa mahaifina."

Sura 45

1 Daga nan Yosef bai iya kame kansa ba a gaban dukkan bayin dake tsaye a gefensa. Ya ce da ƙarfi, "Kowa ya bar ni tilas. "Babu bawan da ya tsaya a gefensa sa'ad da Yosef ya sanar da kansa ga 'yan'uwansa. 2 Ya yi kuka da ƙarfi, Masarawa suka ji, gidan Fir'auna kuma suka sami labari. 3 Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ni ne Yosef. Har yanzu mahaifina nada rai?" 'Yan'uwansa ba su iya amsa masa ba, domin sun gigice a gabansa. 4 Daga nan Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ku zo kusa da ni, ina roƙon ku." Suka zo kusa da shi. Ya ce, "Ni ne Yosef ɗan'uwanku, wanda kuka sayar zuwa cikin Masar. 5 Kada kuyi baƙinciki ko kuji haushin kanku saboda kun sayar da ni zuwa nan, domin Allah ya aiko ni ne gaba da ku saboda a ceci rai. 6 Domin shekaru biyu kenan yunwa na cikin ƙasar, har yanzu kuma akwai shekaru biyar inda ba za a yi huɗa ko girbi ba. 7 Allah ya aiko ni gaba da ku domin ya adana ku a matsayin ragowa a duniya, ya kuma ajiye ku da rai ta wurin babbar kuɓutarwa. 8 Saboda haka yanzu ba ku ne kuka aiko ni nan ba amma Allah ne, kuma ya maida ni uba ga Fir'auna, shugaban dukkan gidansa, kuma mai mulki a cikin dukkan ƙasar Masar. 9 Ku yi hanzari ku tafi wurin mahaifina ku ce masa, 'Wannan ne abin da ɗanka Yosef yace, "Allah ya maida ni shugaban dukkan Masar. Ka gangaro zuwa gare ni, kada ka yi jinkiri. 10 Zaka zauna a ƙasar Goshen, zaka kuma kasance kusa da ni, kai da 'ya'yanka da 'ya'yan 'ya'yanka, da garkunan tumakinka dana awaki da garkunan shanunka, da dukkan abin da kake da shi. 11 Zan biya buƙatunka a can, domin har yanzu akwai shekaru biyar na yunwa, domin kada ku kai ga talaucewa, kai, da gidanka, da dukkan abin da kake da shi."' 12 Duba, idanunku sun ga ni, da idanun ɗan'uwanku Benyamin, cewa bakina ne ya yi magana da ku. 13 Zaku gayawa mahaifina game da dukkan ɗaukakata a Masar da dukkan abin da kuka gani. Zaku yi hanzari ku kawo mahaifina a nan." 14 Ya rungume wuyan ɗan'uwansa Benyamin ya kuma yi kuka, Benyamin kuma ya yi kuka a wuyansa. 15 Ya sumbaci dukkan 'yan'uwansa kuma ya yi kuka a kansu. Bayan wannan 'yan'uwansa suka yi magana da shi. 16 Aka faɗi labarin al'amarin a gidan Fir'auna: "'Yan'uwan Yosef sun zo." Abin ya gamshi Fir'auna da bayinsa sosai. 17 Fir'auna ya cewa Yosef, "Ka cewa 'yan'uwanka, 'Ku yi haka: Ku yi wa dabbobinku kaya ku kuma tafi ƙasar Kan'ana. 18 Ku ɗauko mahaifinku da gidanku dukka ku kuma zo wurina. Zan baku nagartar ƙasar Masar, kuma zaku ci dausayin ƙasar.' 19 Yanzu an umarce ku, 'Ku yi haka, ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'ya'yanku domin matayenku kuma. Ku kuma ɗauko mahaifinku ku zo. 20 Kada ku damu da mallakokinku, domin nagartar dukkan ƙasar Masar taku ce."' 21 'Ya'ya maza na Isra'ila suka yi haka. Yosef ya basu kekunan shanu, bisa ga dokar Fir'auna, ya kuma basu guzuri domin tafiyar. 22 Ga dukkan su ya ba kowanne mutum canjin tufafi, amma ga Benyamin ya bayar da azurfa ɗari uku da canjin tufafi biyar. 23 Ya aika wannan domin mahaifinsa: jakuna goma ɗauke da kyawawan abubuwan Masar; da matan jakuna goma ɗauke da hatsi, gurasa, da sauran kayan masarufi domin mahaifinsa domin tafiyar. 24 Sai ya sallami 'yan'uwansa suka kuma yi tafiyarsu. Ya ce masu, "Ku tabbatar cewa ba ku yi faɗa ba a kan hanya." 25 Suka tafi daga Masar suka zo ƙasar Kan'ana, ga Yakubu mahaifinsu. 26 Suka gaya masa cewa, "Yosef yana nan da rai, kuma shi ne shugaba bisa dukkan ƙasar Masar." Zuciyarsa ta yi mamaki, domin bai gaskata da abin da suka faɗa masa ba. 27 Suka gaya masa dukkan maganganun Yosef da ya faɗi masu. Sa'ad da Yakubu ya ga kekunan shanun da Yosef ya aiko su da su, ruhun Yakubu mahaifinsu ya farfaɗo. 28 Isra'ila yace, "Ya isa. Yosef ɗana yana nan da rai. Zan tafi in gan shi kafin in mutu."

Sura 46

1 Isra'ila ya kama hanyarsa da dukkan abin da yake da shi, ya kuma tafi Bayersheba. A can ya miƙa hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku. 2 Allah ya yi magana da Isra'ila a cikin wahayi da dare, cewa, "Yakubu, Yakubu." Ya ce, "Ga ni nan." 3 Ya ce, "Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron gangarawa zuwa Masar, domin a can zan maida kai babbar al'umma. 4 Zan gangara da kai zuwa cikin Masar, kuma tabbas zan sake hawo da kai kuma Yosef zai rufe idanunka da hannunsa." 5 Yakubu ya taso daga Bayersheba. 'Ya'yan Isra'ila suka tafi da Yakubu mahaifinsu, 'ya'yansu, da matayensu, a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aiko a ɗauke shi. 6 Suka ɗauki dabbobinsu da mallakarsu da suka tattara a ƙasar Kan'ana. Suka zo cikin Masar, Yakubu da dukkan zuriyarsa tare da shi. 7 Ya taho Masar tare da 'ya'yansa maza da 'ya'yan 'ya'yansa maza, da 'ya'yansa mata da 'ya'yan 'ya'yansa mata, da dukkan zuriyarsa. 8 Waɗannan ne sunayen 'ya'yan Isra'ila waɗanda suka zo Masar: Yakubu da 'ya'yansa, Ruben, ɗan fãrin Yakubu; 9 'ya'yan Ruben, Hanok, Fallu, Hezron, da Karmi; 10 'ya'yan Simiyon, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar, da Shawul, ɗan Bakan'aniya; 11 'ya'yan Lebi kuma, Gashon, Kohat, da Merari. 12 'Ya'yan Yahuda su ne Er, Onan, Shela, Ferez, da Zera, (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Ferez su ne Hezron da Hamul. 13 'Ya'yan Issaka su ne Tola, Fuwa, Lob, da Shimron; 14 'ya'yan Zebulun sune Sered, Elon, da Yalil 15 Waɗannan ne 'ya'yan Liya waɗanda ta haifa wa Yakubu a Faddan Aram, tare da ɗiyarsa Dina. Lissafin 'ya'yansa maza da mata talatin da uku. 16 'Ya'yan Gad su ne Zefon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi, da Areli. 17 'Ya'yan Asha su ne Imna, Ishba, Ishbi, da Beriya; kuma Sera ce 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya su ne Heba da Malkiyel 18 Waɗannan ne 'ya'yan Zilfa, wadda Laban ya bayar ga ɗiyarsa Liya. Waɗannan 'ya'ya ta haifa wa Yakubu - sha shida dukka dukkansu. 19 'Ya'yan Rahila matar Yakubu su ne Yosef da Benyamin. 20 A Masar Asenat ɗiyar Fotifera firist na On, ta haifa wa Yosef Manasse da Ifraim. 21 'Ya'yan Benyamin su ne Bela, Beka, Ashbel, Gera, Na'aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim, da Ard. 22 Waɗannan ne 'ya'yan Rahila da aka haifa wa Yakubu - sha huɗu dukkan su. 23 ‌Ɗan Dan shi ne Hushim. 24 'Ya'yan Naftali su ne Yaziyel, Guni, Yeza, da Shillem. 25 Waɗannan ne 'ya'yan da Bilha ta haifa wa Yakubu, wadda Laban ya bayar ga Rahila ɗiyarsa - bakwai dukka dukkansu. 26 Dukkan waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, waɗanda ke zuriyarsa, ba a ƙidaya da matayen 'ya'yan Yakubu ba, su sittin da shida ne dukkansu. 27 Tare da 'ya'yan Yosef maza biyu da aka haifa masa a Masar, yawan iyalinsa da suka tafi Masar su saba'in ne dukkansu. 28 Yakubu ya aiki Yahuda zuwa ga Yosef saboda ya nuna masa hanya a gabansa ta zuwa Goshen, suka kuma zo ƙasar Goshen. 29 Yosef ya shirya karusarsa ya kuma tafi domin ya sami Isra'ila mahaifinsa a Goshen. Ya gan shi, ya rungumi wuyansa, ya kuma yi kuka na dogon lokaci bisa wuyansa. 30 Isra'ila yace wa Yosef, "Yanzu bari in mutu, tunda na ga fuskarka, cewa kana nan da rai." 31 Yosef ya cewa 'yan'uwansa da gidan mahaifinsa, "Zan tafi in gaya wa Fir'auna, cewa, "Yan'uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina. 32 Mutanen makiyaya ne, domin suna kiwon dabbobi ne. Sun kawo garkunan tumakinsu dana awakinsu, da garkunan shanunsu, da dukkan abin da suke da shi.' 33 Zai kasance, sa'ad da Fir'auna zai kira ku ya yi tambaya, 'Mene ne sana'arku?' 34 To zaku ce masa, 'Bayinka masu kiwon dabbobi ne tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yanzu, dukkanmu, da ubanninmu.' Ku yi haka domin ku zauna a ƙasar Goshen, domin kowanne makiyayi haramtacce ne ga Masarawa."

Sura 47

1 Daga nan Yosef ya shiga ya gaya wa Fir'auna, "Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunan tumakinsu da na awaki, da garkunan shanunsu, da dukkan abin da ke nasu, sun iso daga ƙasar Kan'ana. Duba, suna ƙasar Goshen." 2 Ya ɗauki biyar daga cikin 'yan'uwansa ya kuma gabatar da su ga Fir'auna. 3 Fir'auna ya cewa 'yan'uwansa, "Mene ne sana'arku?" Suka cewa Fir'auna, "Bayinka makiyaya ne, kamar kakanninmu." 4 Daga nan suka cewa Fir'auna, "Mun zo ɗan zama ne a ƙasar. Babu makiyaya domin garkunan bayinka, saboda yunwar ta yi tsanani a ƙasar Kan'ana. To yanzu, muna roƙonka bari bayinka su zauna a ƙasar Goshen." 5 Daga nan Fir'auna ya yi magana da Yosef, ya ce, "Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka. 6 ‌Ƙasar Masar na gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a lardi mafi kyau, ƙasar Goshen. Idan ka san maza ƙwararru daga cikinsu, ka sanya su kiwon dabbobi na." 7 Daga nan Yosef ya shigo da Yakubu mahaifinsa ya kuma gabatar da shi ga Fir'auna. Yakubu ya albarkaci Fir'auna. 8 Fir'auna ya cewa Yakubu, "Tsawon rayuwarka nawa?" 9 Yakubu ya cewa Fir'auna, "Shekarun yawace-yawace na ɗari ne da talatin. Shekarun rayuwata kima ne kuma cike da wahala. Ba su kai yawan na kakannina ba." 10 Daga nan Yakubu ya albarkaci Fir'auna ya kuma fita daga gabansa. 11 Daga nan Yosef ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa. Ya ba su gunduma a ƙasar Masar, yankin ƙasar mafi kyau, a ƙasar Ramesis, kamar yadda Fir'auna ya umarta. 12 Yosef ya wadata abinci domin mahaifinsa, da 'yan'uwansa, da dukkan gidan mahaifinsa, bisa ga lissafin masu dogara da su. 13 Yanzu dai babu abinci a dukkan ƙasar; domin yunwar ta yi tsanani. ‌Ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka lalace saboda yunwar. 14 Yosef ya tattara dukkan kuɗaɗen dake ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana, ta wurin sayar da hatsi ga mazaunan. Daga nan Yosef ya kawo kuɗaɗen fãdar Fir'auna. 15 Sa'ad da aka gama kashe dukkan kuɗaɗen dake ƙasashen Masar da Kan'ana, dukkan Masarawa suka zo wurin Yosef suka ce, "Ka bamu abinci! Ya ya zamu mutu a gabanka saboda kuɗaɗenmu sun ƙare?" 16 Yosef yace, "Idan kuɗaɗenku sun ƙare, ku kawo dabbobinku ni zan kuma baku abinci misanya domin dabbobinku." 17 Sai suka kawo dabbobinsu wurin Yosef. Yosef ya basu abinci misanya domin dawakai, domin garkunan tumaki da awaki, domin garkunan shanu, domin kuma jakuna. A wannan shekarar ya ciyar dasu da abinci a misanyar dukkan dabbobinsu. 18 Sa'ad da shekara ta ƙare, suka zo wurinsa a shekara ta gaba suka kuma ce masa, "Ba zamu ɓoye ba daga shugabanmu cewa kuɗaɗenmu sun tafi, kuma garkunan shanun na shugabanmu ne. Babu abin da ya rage a idanun shugabana, sai jikkunanmu kawai da ƙasarmu. 19 Yaya zamu mutu a gaban idanunka, dukkanmu da ƙasarmu? Ka saye mu da ƙasarmu a musanya domin abinci, mu da ƙasarmu mu zama bayi ga Fir'auna. Ka bamu iri domin mu rayu kada mu mutu, kada kuma ƙasar ta zama kufai." 20 Saboda haka Yosef ya saye wa Fir'auna dukkan ƙasar Masar. Domin kowanne Bamasare ya sayar da gonarsa, saboda yunwar ta yi tsanani sosai. Ta wannan hanya, ƙasar ta zama ta Fir'auna. 21 Game da mutanen, ya mayar dasu bayi daga ƙarshen kan iyakar Masar zuwa ɗaya ƙarshen. 22 ‌Ƙasar firistoci ce kawai Yosef bai saya ba, saboda ana ba firistocin albashi. Suna ci daga kason da Fir'auna yake ba su. Saboda haka basu sayar da gonarsu ba. 23 Daga nan Yosef ya cewa mutanen, "Duba, na saye wa Fir'auna ku da ƙasarku. Yanzu ga iri domin ku, zaku kuma noma ƙasar. 24 Da kaka tilas ku bada kaso biyar ga Fir'auna, kashi huɗu kuma zai zama naku, domin iri na gonaki domin kuma abinci domin gidajenku da 'ya'yanku." 25 Suka ce, "Ka ceci rayukanmu. Bari mu sami tagomashi a idanunka. Zamu zama bayin Fir'auna." 26 Sai Yosef ya maida haka doka mai aiki har wayau a ƙasar Masar, cewa kashi biyar na Fir'auna ne. ‌Ƙasar firistoci ce kawai ba ta zama ta Fir'auna ba. 27 Saboda haka Isra'ila ya zauna a ƙasar Masar, a ƙasar Goshen. Mutanensa suka sami mallakar wurin. Suka hayayyafa suka ruɓanɓanya sosai. 28 Yakubu ya zauna a ƙasar Masar shekaru sha bakwai, saboda haka shekarun rayuwar Yakubu ɗari da arba'in da bakwai ne. 29 Sa'ad da lokaci ya kusato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yosef yace masa, "Yanzu idan na sami tagomashi a idanunka, ka sanya hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka kuma nuna mani aminci da yarda. Ina roƙon ka kada ka bizne ni a Masar. 30 Sa'ad da na yi barci da ubannina, zaka ɗauke ni ka fitar da ni daga Masar ka kuma bizne ni a maƙabartar kakannina." Yosef yace, "Zan yi yadda ka ce." 31 Isra'ila yace, "Ka rantse mani," Yosef kuma ya rantse masa. Daga nan Isra'ila ya rusuna a bisa kan gadonsa.

Sura 48

1 Sai ya kasance bayan waɗannan abubuwa, sai wani ya cewa Yosef, "Duba, mahaifinka bai da lafiya." Sai ya ɗauki 'ya'yansa maza biyu tare da shi, Manasse da Ifraim. 2 Sa'ad da aka gaya wa Yakubu, "Duba, ɗanka Yosef ya iso ya ganka," Isra'ila ya ƙoƙarta kuma ya zauna bakin gado. 3 Yakubu ya cewa Yosef, "Allah maɗaukaki ya bayyana a gare ni a Luz cikin ƙasar Kan'ana. 4 Ya albarkace ni ya kuma ce mani, 'Duba, zan sa ka hayayyafa, ka kuma ruɓanɓanya. Zan maida kai taron al'ummai. Zan bayar da wannan ƙasar ga zuriyarka a matsayin madawwamiyar mallaka.' 5 Yanzu 'ya'yanka biyu maza, waɗanda aka haifa maka a ƙasar Masar kafin in zo wurinka a Masar, nawa ne. Ifraim da Manasse zasu zama nawa, kamar yadda Ruben da Simiyon suke nawa. 6 'Ya'yan da zaka haifa bayan su zasu zama naka; za a lissafa su ƙarƙashin sunayen 'yan'uwansu a cikin gãdonsu. 7 Amma game da ni, sa'ad dana zo daga Faddan, cikin baƙincikina Rahila ta mutu a ƙasar Kan'ana a kan hanya, yayin da da sauran tazara a isa Ifrat. Na bizne ta a nan a kan hanyar zuwa Ifrat" (wannan ce, Betlehem). 8 Sa'ad da Isra'ila ya ga 'ya'yan Yosef maza, ya ce, "Na wane ne waɗannan?" 9 Yosef yace wa mahaifinsa, "'Ya'yana ne, waɗanda Allah ya bani a nan." Isra'ila yace, "Kawo su wurina, domin in sa masu albarka." 10 Yanzu dai idanun Isra'ila na kasawa saboda shekarunsa, har baya iya gani. Sai Yosef ya kawo su kusa da shi, kuma ya sumbace su ya kuma rungume su. 11 Isra'ila ya cewa Yosef, "Banyi tsammanin zan sa ke ganin fuskarka ba, amma Allah ya bar ni inga 'ya'yanka ma." 12 Yosef ya fito da su daga tsakanin guiwoyin Isra'ila, Daga nan kuma ya rusuna da fuskarsa ƙasa. 13 Yosef ya ɗauke su biyun, Ifraim a hannun damansa zuwa hannun hagun Isra'ila, Manasse kuma a hannun hagunsa zuwa hannun damar Isra'ila, ya kuma matso da su kusa da shi. 14 Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama ya kuma ɗora bisa kan Ifraim, wanda shi ne ƙarami, hannun hagunsa kuma bisa kan Manasse. Ya gitta hannuwansa, domin Manasse shi ne ɗan fãri. 15 Isra'ila ya albarkaci Yosef, yana cewa, "Allah wanda a gabansa ubannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allah wanda ya lura da ni har ya zuwa yau, 16 mala'ikan da ya kiyaye ni daga dukkan bala'i, bari ya albarkaci waɗannan samari. Bari a raɗa sunana a sunansu, da sunan ubannina Ibrahim da Ishaku. Bari su yaɗu su yi tururu a bisa duniya." 17 Sa'ad da Yosef ya ga cewa mahaifinsa ya ɗora hannunsa na dama bisa kan Ifraim, bai ji daɗi ba. Ya ɗauke hannun mahaifinsa domin ya matsa da shi daga bisa kan Ifraim zuwa bisa kan Manasse. 18 Yosef yace wa mahaifinsa, "Ba haka ba, babana; domin wannan shi ne ɗan fãrin. Ka ɗora hannunka na dama bisa kansa." 19 Mahaifinsa ya ƙi ya kuma ce, "Na sani, ɗana, Na sani. Shi ma zai zama jama'a, shima kuma zai zama babba. Duk da haka ƙanensa zai fi shi girma, kuma zuriyarsa zasu zama al'ummai tururu." 20 Isra'ila ya albarkace su a wannan rana da waɗannan maganganu, "Mutanen Isra'ila zasu furta albarku da sunayenku suna cewa, 'Bari Allah ya maida ku kamar Ifraim kamar Manasse kuma'." Ta wannan hanya, Isra'ila ya sanya Ifraim gaba da Manasse. 21 "Isra'ila ya cewa Yosef, "Duba, ina gaf da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku, zai kuma maida ku ƙasar ubanninku. 22 Game da kai, a matsayin wanda aka ɗora sama da 'yan'uwansa, Na baka gangaren tsaunin dana karɓe daga hannun Amoriyawa da takobina da kuma bakana."

Sura 49

1 Daga nan Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya kuma ce: "Ku tattara kanku tare, domin in gaya maku abin da zai faru daku a gaba. 2 Ku tattara kanku ku kuma saurara, ku 'ya'yan Yakubu. Ku saurari Isra'ila, mahaifinku. 3 Ruben, kai ne ɗan fãrina, ƙarfina, da farkon ƙarfina, ka yi fice wajen jamali, ka kuma yi fice wajen iko. 4 Marar kamewa kamar ruwan dake ambaliya, ba zaka yi muhimmanci ba, saboda ka hau bisa gadon mahaifinka. Daga nan ka gurɓata shi; ka hau bisa gadona. 5 Simiyon da Lebi 'yan'uwa ne. Makaman ta'addanci ne takubbansu. 6 Ya raina, kada ka zo cikin shawararsu; kada ka shiga cikin taruwarsu, domin zuciyata ta fi haka daraja sosai. Domin cikin fushinsu sun kashe mutane. Saboda annashuwa ne suka turke shanu. 7 Bari fushinsu ya la'ana, domin mai zafi ne - hasalarsu kuma domin mai tsanani ce. Zan rarraba su a Yakubu in kuma warwatsa su a Isra'ila. 8 Yahuda, 'yan'uwanka zasu yabe ka. Hannunka zai kasance bisa wuyan maƙiyanka. 'Ya'yan mahaifinka za su rusuna a gabanka. 9 Yahuda ɗan zaki ne. ‌Ɗana, ka haura daga kamammunka. Ka duƙa, ka rarrafa kamar zaki, kamar zakanya. Wa zai kuskura ya tada kai? 10 Sandan sarauta ba za ta fita daga Yahuda ba, ko sandar mulki daga tsakanin ƙafafunsa, har sai Shilo ya zo. Al'ummai zasu yi masa biyayya. 11 Yana ɗaure jakinsa ga kuringar inabinsa, da ɗan jakinsa ga zaɓaɓɓiyar kuringar inabinsa, ya wanke tufafinsa cikin ruwan inabi, da alkyabbarsa cikin jinin inabi. 12 Idanunsa zasu yi duhu kamar ruwan inabi, haƙoransa kuma farare kamar madara. 13 Zebulun zai zauna a gaɓar teku. Zai zama masaukin jiragen ruwa, kuma kan iyakarsa za ta zarce har zuwa Sidon. 14 Issaka jaki ne mai ƙarfi, yana zaune a tsakiyar turakun tumaki. 15 Yana ganin wurin hutawa mai kyau da ƙasa mai gamsarwa. Zai sunkuyar da kafaɗarsa domin kaya ya kuma zama bawa domin hidimar. 16 Dan zai hukunta mutanensa a matsayin ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila. 17 Dan zai zama maciji a gefen hanya, maciji mai dafi a tafarki dake cizon kofaton doki, saboda mahayinsa ya fãɗi ta baya. 18 Ina jiran cetonka, Yahweh. 19 Gad - mahaya zasu kai masa hari, amma zai kai masu hari ta diddigensu. 20 Abincin Asha zai zama wadatacce, zai kuma bayar da girke-girken sarauta. 21 Naftali sakakkiyar barewa ce; zai haifi kyawawan 'ya'ya. 22 Yosef mai hayayyafa ne, mai bayar da 'ya'ya ne, mai bayar da 'ya'ya dake gefen ƙorama wanda rassansa ke hawan katanga. 23 Maharba zasu kai masa hari, su kuma harbe shi, su firgita shi. 24 Amma bakansa zai tsaya dai-dai, kuma hannayensa zasu ƙware saboda hannayen Mai Iko na Yakubu, saboda sunan Makiyayi, Dutsen Isra'ila. 25 Allah na mahaifinka zai taimakeka kuma Allah Mai Iko Dukka zai albarkace ka da albarkun sararin sama, albarkun zurfafa dake kwance ƙarƙashin ƙasa, da albarkun nonna da mahaifa. 26 Albarkun mahaifinka sun fi albarkun duwatsun zamanin dã ko abubuwan marmari na tuddan dã. Bari su kasance bisa kan Yosef, har bisa rawanin dake kan yariman 'yan'uwansa. 27 Benyamin damisa ne mayunwaci. Da safe zai lanƙwame kamammensa, da yamma kuma zai raba ganimarsa." 28 Waɗannan ne kabilu sha biyu na Isra'ila. Wannan ne abin da mahaifinsu ya ce masu sa'ad da ya albarkace su. Kowannen su ya albarkace shi bisa ga albarkar da ta dace. 29 Daga nan ya umarce su ya ce masu, "Ina gaf da tafiya ga mutanena. Ku bizne ni tare da kakannina a kogon dake cikin gonar Ifron Bahittiye, 30 a cikin kogon dake cikin gonar Makfela, wadda ke kusa da Mamri a ƙasar Kan'ana, gonar da Ibrahim ya saya a matsayin maƙabarta daga hannun Ifron Bahittiye. 31 A nan ne aka bizne Ibrahim da matarsa Saratu; a nan ne suka bizne Ishaku da matarsa Rebeka; a nan ne kuma na bizne Liya. 32 Gonar da kogon dake cikin ta an saye su ne daga mutanen Het." 33 Da Yakubu ya gama waɗannan umarnai ga 'ya'yansa, ya ja ƙafafunsa cikin gadonsa, ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma tafi wurin mutanensa.

Sura 50

1 Daga nan Yosef ya rikice, ya faɗi bisa fuskar mahaifinsa, ya kuma yi kuka a bisansa, ya kuma sumbace shi. 2 Yosef ya umarci bayinsa masu ilimin magani su nannaɗe mahaifinsa. Masu ilimin maganin suka nannaɗe Isra'ila da maganin hana ruɓewa. 3 Suka ɗauki kwana arba'in, domin wannan ne tsawon lokaci idan an naɗe gawa. Masarawa suka yi masa kuka na kwana saba'in. 4 Da kwanakin makoki suka cika, Yosef ya yi magana da gidan Fir'auna, cewa, "Idan yanzu na sami tagomashi a idanunku, ina roƙonku ku yi magana da Fir'auna, ku ce, 5 'Mahaifina yasa in yi rantsuwa, cewa, "Duba, ina gaf da mutuwa. Ka bizne ni a kabarin dana gina domin kaina a ƙasar Kan'ana. A can zaka bizne ni." Yanzu bari in haye in tafi, in kuma bizne mahaifina, daga nan kuma zan dawo."' 6 Fir'auna ya amsa, "Ka tafi ka bizne mahaifinka, kamar yadda yasa ka yi rantsuwa." 7 Yosef ya haye ya tafi bizne mahaifinsa. Dukkan 'yan majalisar Fir'auna suka tafi tare da shi - dattawan gidansa, dukkan manyan masu gari na ƙasar Masar, 8 tare da dukkan gidan Yosef da 'yan'uwansa, da gidan mahaifinsa. Amma 'ya'yansu, da garkunan tumakinsu, dana awaki, da garkunan shanunsu aka bari a ƙasar Goshen. 9 Karusai da mahaya dawaki suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiyar mutane ce sosai. 10 Sa'ad da suka iso bakin masussukar Atad a ɗayan gefen Yodan, suka yi makoki da babban makoki da baƙinciki mai tsanani. A can Yosef ya yi makokin kwana bakwai domin mahaifinsa. 11 Sa'ad da mazauna ƙasar, Kan'aniyawa, suka ga makokin a masussukar Atad, suka ce, "Wannan taro ne na baƙinciki sosai ga Masarawa." Shi yasa ake kiran wurin da suna Abel Mizrayim, wanda ke tsallaken Yodan. 12 Daga nan 'ya'yan Yakubu suka yi masa kamar yadda ya umarta. 13 'Ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana suka kuma bizne shi a kogon cikin gonar Makfela, kusa da Mamri. Ibrahim ya sayi kogon tare da gonar a matsayin maƙabarta. Ya saya ne daga Ifron Bahittiye. 14 Bayan da Yosef ya bizne mahaifinsa, sai ya koma cikin ƙasar Masar, shi, tare da 'yan'uwansa, da dukkan waɗanda suka raka shi bizne mahaifinsa. 15 Sa'ad da 'yan'uwan Yosef suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, suka ce, "To idan Yosef ya riƙe mu da fushi gãba da mu fa, kuma yana so ya yi mana cikakkiyar sakayya domin dukkan muguntar da muka yi masa?" 16 Sai suka umarci kasancewar Yosef, suka ce, "Mahaifinka ya bada umarni kafin ya mutu, cewa, 17 'Ku gaya wa Yosef haka, "Mu na roƙonka ka gafarta laifin 'yan'uwanka da zunubinsu sa'ad da suka yi maka mugunta."' Yanzu muna roƙonka ka gafartawa bayin Allah na mahaifinka. Yosef ya yi kuka sa'ad da suka yi masa magana. 18 'Yan'uwansa kuma suka zo suka kwanta fuska ƙasa a gabansa. Suka ce, "Duba, mu bayinka ne." 19 Amma Yosef ya amsa masu, "Kada ku ji tsoro. Ina gurbin Allah ne? 20 Game da ku, kun yi niyyar mugunta a gare ni, amma Allah ya yi niyyar alheri ne, saboda a adana rayuwar mutane da yawa, kamar yadda kuka gani a yau. 21 Saboda haka, yanzu kada ku ji tsoro. Zan tanada maku da ƙananan 'ya'yanku." Ya ta'azantar dasu ta wannan hanyar ya kuma yi maganar mutunci ga zukatansu. 22 Yosef ya zauna a Masar, tare da iyalin mahaifinsa. Ya yi rayuwa shekaru ɗari da goma. 23 Yosef ya ga 'ya'yan Ifraim har zuwa tsara ta uku. Ya kuma ga 'ya'yan Makir ɗan Manasse, waɗanda aka sanya a gwiwoyin Yosef. 24 Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ina gaf da mutuwa; amma tabbas Allah zai zo gare ku, ya kuma bida ku hayewa daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse zai ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu." 25 Daga nan Yosef ya sa mutanen Isra'ila suka rantse da alƙawari. Ya ce, "Tabbas Allah zai zo gare ku. A wannan lokacin tilas ku ɗauki ƙasusuwana daga nan." 26 Sai Yosef ya mutu, da shekaru 110. Aka nannaɗe shi da maganin hana ruɓa, kuma aka ajiye shi cikin akwati.

Littafin Fitowa
Littafin Fitowa
Sura 1

1 Ga sunanyen 'ya'yan Isra'ila da suka zo cikin Masar tare da Yakubu, kowannen su tare da iyalansa: 2 Ruben, da Simiyon, da Lebi, da kuma Yahuda, 3 da Issaka, da Zebulun da kuma Benyamin, 4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Asha. 5 Dukkan zuriyar Yakubu su saba'in ne. Yosef yana nan a Masar. 6 Sai Yosef, dukkan 'yan uwansa, da duk wannan tsãra suka mutu. 7 Isra'ilawa suka yi albarka, suka riɓaɓɓanya, da kuma ƙara ƙarfi sosai; ƙasar kuma ta cika da su. 8 Yanzu dai sai wani sabon sarki ya taso a Masar, wanda bai san da Yosef ba. 9 Ya cewa mutanensa, "Ku duba, Isra'ilawan sun fi mu yawa da kuma ƙarfi. 10 Ku zo, bari mu bi da su cikin hikima, idan ba haka ba za su ci gaba da haɓɓaƙa, idan yaƙi ya taso, za su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su kuma bar ƙasar." 11 Sai suka ɗora shugabannin aikin tilas a bisansu domin su wahalshe su da bauta mai zafi. Isra'ilawan suka gina wa Fir'auna biranen ajiya: Fitom da Ramesis. 12 Amma sa'ad da Masarawan suke ƙuntata masu, da haka Isra'ilawa ke ƙaruwa suna kuma yaɗuwa. Don haka Masarawan suka fara tsorata da Isra'ilawa. 13 Masarawan suka sa Isra'ilawa su yi aiki mai tsanani. 14 Suka sa rayukan su suka yi ɗaci cikin hidimarsu a kwaɓa ƙasa da ginin tubali, da kuma dukkan ayyuka a cikin filaye. Dukkan aikin da ake so suyi masu wuya ne. 15 Sai sarkin Masar ya yi magana da mataye unguwarzoma na Ibraniyawa; ɗaya sunanta Shifra, ɗayan kuma Fuwa. 16 Ya ce, "Lokacin da kuke taimaka wa matan Ibraniyawa a kujeran haihuwa, ku kula da lokacin da suka haihu. Idan ɗa namiji ne, to sai ku kashe shi; amma idan mace ce, to tana iya rayuwa." 17 Amma matan unguwarzoma suka ji tsoron Allah ba su kuma aikata yadda sarkin Masar ya umarce su ba; a maimakon haka, suka bar 'ya'ya maza su rayu. 18 Sarkin Masar ya kirawo mataye unguwarzoman ya ce masu, "Don me kuka yi haka, da kuka bar 'ya'ya maza su rayu?" 19 Unguwarzoman suka ce wa Fir'auna, "Matayen Ibraniyawa ba kamar matayen Masar ba ne. Suna da ƙarfi kuma kamin mu iso gare su sun rigaya sun haihu." 20 Allah kuma ya tsare waɗannan mata unguwarzoma. Mutanen kuma suka riɓaɓanya suka zama da ƙarfi sosai. 21 Domin mataye unguwarzoman sun ji tsoron Allah, sai ya ba su iyalai. 22 Sai Fir'auna ya ba dukkan mutanensa doka, "Dole ku jefa kowanne ɗan da aka haifa cikin kogi, amma kowacce ɗiya ku bar ta da rai."

Sura 2

1 To akwai wani mutum daga kabilar Lebi wanda ke auren wata mace mutumiyar Lebi. 2 Macen ta yi juna biyu ta kuma haifi ɗan yaro. Da ta ga cewa yaron lafiyayye ne, sai ta ɓoye shi har wata uku. 3 Amma da ya kai wani lokacin da ta ga ba za ta iya ɓoye shi ba, sai ta ɗauki kwandon iwa ta dalaye shi da katsi da ƙaro. Sai ta sanya jaririn ciki ta kuma saka shi cikin ruwan a cikin ciyayin bakin teku. 4 'Yar'uwarsa na tsaye daga nesa don ta ga abin da zai faru da shi. 5 Ɗiyar Fir'auna ta gangaro zuwa kogin domin ta yi wanka yayin da kuyanginta na tafiya a gefen kogin. Sai ta hango kwandon cikin ciyayi sai ta aika kuyanginta su kawo shi. 6 Da ta buɗe, sai ta ga jaririn. Duba, jaririn na kuka. Sai ta yi juyayinsa ta kuma ce, "Wannan lallai ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne." 7 Sai 'yar uwar jaririn ta ce ma ɗiyar Fir'auna, "In je in nemo maki mai reno daga cikin matan Ibraniyawa?" 8 Sai ɗiyar Fir'auna ta ce ma ta, "Je ki." Sai yarinyar ta tafi ta kuma samo uwar jaririn. 9 Sai ɗiyar Fir'auna ta cewa uwar jaririn, "Ɗauki jaririn nan ki yi mani renon sa, ni kuma zan biya ki albashi." Sai matar ta ɗauki jaririn ta yi renon sa. 10 Da jaririn ya yi girma, sai ta kawo shi wurin ɗiyar Fir'auna, sai ya zama ɗanta. Ta raɗa masa suna Musa ta kuma ce, "Domin na tsamo shi daga ruwa." 11 Da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa ya kuma lura da nawayarsu. Sai ya ga wani Bamasare na bugun Ba'ibrane, ɗaya daga cikin mutanensa. 12 Sai ya waiga nan da can, da ya ga babu kowa a wurin, sai ya kashe Bamasaren ya kuma binne jikinsa cikin yashi. 13 Washegari ya sake fita, kuma, gashi kuwa, biyu daga cikin mazajen Ibraniyawa suna faɗa da juna. Ya cewa wanda shi ke da rashin gaskiya, "Me ya sa kake dukan ɗan'uwan ka?" 14 Amma mutumin yace, "Waye ya sanya ka shugaba da mai shari'a bisanmu? Ko kana shirin kashe ni kamar yadda ka kashe wancan Bamasaren?" Sai Musa ya ji tsoro ya kuma ce, "Abin da na yi tabbas ba a ɓoye yake ga sauran ba." 15 Ya zama kuma da Fir'auna ya ji abin da ya faru, sai ya yi ƙoƙarin kashe Musa. Amma Musa ya tsere daga gaban Fir'auna zuwa ƙasar Midiyan. A nan ya zauna a bakin wata rijiya. 16 Ya zama cewa firist na Midiyan na da 'yan mata guda bakwai. Suka zo, su ɗebi ruwa, su cika kwamayensu don su shayar da garkunan mahaifinsu. 17 Sai wasu makiyaya suka zo suka yi ƙoƙarin korar su, amma Musa ya tashi ya taimake su. Sai kuma ya shayar da dabbobinsu. 18 Da 'yan matan suka komo wurin Ruwel mahaifinsu, ya ce, "Me ya sa kuka yi saurin dawo wa gida yau?" 19 Suka ce, "Wani Bamasare ne ya kuɓutar da mu daga hannun makiyayan. Har ma ya jawo mana ruwa ya shayar da garken." 20 Sai ya ce da 'yan matansa, "To ina yake? Don me kuka bar mutumin? Ku kira shi domin ya ci abinci tare da mu." 21 Sai Musa ya yarda da ya zauna tare da mutumin, shi ma sai ya ba shi ɗiyarsa Ziffora ya aura. 22 Ta haifa masa ɗan yaro, sai Musa ya kira shi da suna Gashom; yana cewa, "Na zama mai baƙonci a cikin baƙuwar ƙasa." 23 Bayan lokaci mai tsawo, sai sarkin Masar ya mutu. Isra'ilawa suka yi nishi saboda aikin bautarsu. Suka yi kukan neman taimako, sai kuma roƙon su ya kai ga Allah saboda bautarsu. 24 Sa'ad da Allah ya ga ƙuncinsu, Allah ya tuna da alƙawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu. 25 Allah ya ga Isra'ilawa, ya kuma fahimci matsalarsu.

Sura 3

1 Yanzu dai Musa yana ta kiwon garken Yetro surukinsa, firist na Midiyan. Musa ya kai garken har iyakar sashen hamada ya kuma iso Horeb, tsaunin Allah. 2 A nan mala'ikan Yahweh ya bayyana gare shi cikin harshen wuta mai ci a kurmi. Sai Musa ya duba, ga shi, kurmin na ci da wuta, amma kurmin bai ƙone sarai ba. 3 Sai Musa yace, "Zan juya nan inga wannan abin ban mamaki, don me kurmin bai cinye ƙurmus da wutar ba." 4 Sa'ad da Yahweh ya ga cewa ya juya garin ya duba, sai Allah ya yi kira gare shi daga cikin kurmin ya ce, "Musa, Musa." Musa yace, "Ga ni nan." 5 Allah yace, "Kada ka iso nan! Ka kwaɓe takalmanka daga kafafun ka, gama inda kake tsaye ƙasa ce keɓaɓɓiya a gare ni." 6 Ya kuma ce, "Ni ne Allahn mahaifinka, Allahn Ibrahim, da na Ishaku, da kuma na Yakubu." Sai Musa ya rufe fuskarsa, gama yana tsoron duban Allah. 7 Yahweh yace, "Na ga azabar mutanena da suke a Masar. Na ji kururuwarsu sabili da shugabanninsu na aikin tilas, gama ina sane da wahalarsu. 8 Na sauko domin in kuɓutar da su daga ikon Masarawa in kuma fito da su daga wannan ƙasa zuwa ƙasa mai kyau, mai girma, ƙasa mai ɓulɓulo da madara da zuma; zuwa ƙasashen Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa. 9 Yanzu dai kururuwar mutanen Isra'ila ta hau zuwa gare ni. Fiye da haka, na ga zaluncin da Masarawa suke gwada masu. 10 Ga shi yanzu, zan aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da mutanena, Isra'ilawa, daga cikin Masar." 11 Amma Musa ya cewa Allah, "Ni, wane ne, har da zan tafi wurin Fir'auna in kuma fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?" 12 Allah ya amsa, "Ni zan kasance tare da kai tabbas. Wannan zai zama maka alama da cewa Ni na aike ka. Yayin da ka fito da mutanen daga Masar, za ku yi mani sujada a kan wannan n." 13 Sai Musa ya cewa Allah, "Sa'ad da na tafi wurin Isra'ilawa na kuma ce masu, 'Allah na kakanninku ya aiko ni gare ku,' in kuma suka ce mani, 'Mene ne sunansa?' to me zan amsa masu?" 14 Sai Allah ya cewa Musa, "NI NE DA NAKE NI NE." Allah yace, "Dole ka faɗi wa Isra'ilawa, 'NI NE ya aiko ni gare ku."' 15 Allah ya kuma ce wa Musa, "Dole ka gaya wa Isra'ilawa, 'Yahweh, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu, ya aiko gare ku. Wannan ne sunana har abada, kuma da haka za a tuna da ni cikin dukkan tsararraki. 16 Ka tafi ka tara shugabannin Isra'ila tare. Ka ce masu, 'Yahweh, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, na Ishaku, kuma da na Yakubu, ya bayyana gare ni ya ce, "Lallai na kula da ku na kuma ga abin da aka yi maku a Masar. 17 Na yi alƙawarin in fito da ku daga zaluncin Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa, ƙasa mai zubo da madara da kuma zuma."' 18 Za su saurare ka. Da kai da shugabannin Isra'ila dole ku je wurin sarkin Masar, dole kuma ku faɗi masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya gamu da mu. Saboda haka yanzu bari mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji, domin mu yi hadaya ga Yahweh Allahnmu.' 19 Amma na san da cewa sarkin Masar ba zai bar ku ku tafi ba, sai in an tilasta hannunsa. 20 Zan miƙa hannuna in kuma kai wa Masarawa farmaki da dukkan al'ajiban da zan aikata a tsakaninsu. Bayan haka, zai ƙyale ku ku tafi. 21 Zan bai wa mutanen nan tagomashi daga Masarawa, don haka lokacin da kuka fito, ba za ku fita hannu wofi ba. 22 Kowacce mace za ta roƙi ƙarafan azurfa da zinariya da kuma tuffafi daga maƙwabtansu Masarawa da kuma kowacce mace dake zama gidan maƙwabtanta. Za ku sanya su bisa 'ya'yanku maza da mata. Da haka za ku washe Masarawa."

Sura 4

1 Sai Musa ya amsa, "Amma idan basu gaskata da ni ko su saurare ni ba amma suka ce a maimako, 'Yahweh bai bayyana gare ka ba'?" 2 Yahweh yace masa, "Menene wannan a hannunka?" Musa yace, "Sanda ce. 3 Yahweh yace, "Jefa ƙasa." Sai Musa ya jefar da ita ƙasa, sai ta zama maciji. Sai Musa ya guje masa. 4 Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannu ka riƙe wutsiyar." Sai ya miƙa hannu ya kuma kama macijin. Sai ta sake zama sanda cikin hannunsa. 5 "Wannan ya faru domin su gaskata da Yahweh, Allahn kakanninsu, Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yakubu, ya bayyana gare ka." 6 Yahweh ya sake ce masa, "Yanzu ka sanya hannun ka cikin rigarka." Sai Musa ya sanya hannunsa a cikin rigarsa. Da ya fito da shi, gashi kuwa, hannunsa ya kama kuturta, fari fat kamar ƙanƙara. 7 Yahweh yace, "Ka sake maida hannunka cikin riga, kuma da ya fito da shi, sai ya ga cewa an maido da lafiyarsa kuma, kamar sauran sashen fatarsa. 8 Yahweh yace, "Idan basu gaskanta da kai ba - idan har basu kula da alama ta ikona na farko ba ko su gaskanta da ita ba, to za su gaskanta da alama ta biyun. 9 Idan kuma basu gaskanta da dukka waɗannan alamu biyu na ikona ba, ko su saurare ka, sai ka ɗebo ruwa daga kogi ka kuma tsiyaye shi a busasshiyar ƙasa. Ruwan daka ɗebo zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasar." 10 Sai Musa ya cewa Yahweh, "Ubangiji, ban taɓa iya magana da kyau ba, ko a dã ko tun lokacin daka yi magana da bawanka. Ni ba mai magana da sauri ba ne kuma harshena mai nauyi ne." 11 Yahweh yace dashi, "Wanene ya yi bakin mutum? Wa ke maida mutum bebe ko kurma ko mai gani ko makaho? Ba Ni ba ne, Yahweh? 12 Saboda haka yanzu ka tafi, Ni kuma zan kasance da kai in kuma koya maka abin da za ka faɗi." 13 Amma Musa yace, "Ubangiji, na roƙe ka ka aika da wani, duk wanda ka so ka aika." 14 Sai Yahweh ya yi fushi da Musa. Yace, "To Haruna fa, ɗan'uwanka, Ba'lebi? Na san da cewar ya iya magana da kyau. Ga shi ma, yana fitowa don ya tarye ka, kuma sa'ad da ya ganka, zai yi murna cikin zuciyarsa. 15 Za ka yi magana dashi ka kuma sanya maganganun da zai faɗi a bakinsa. Zan kasance da bakinka da kuma bakin sa, kuma zan bayyana maku ku biyun abin da za ku yi. 16 Shi za ya yi magana ga mutanen a madadin ka. Zai zama bakinka, kai kuma za ka zama gareshi kamar ni, Allah. 17 Za ka ɗauki wannan sanda a hannunka. Da ita za ka aiwatar da alamun." 18 Sai Musa ya komo wurin Yetro surukinsa ya kuma ce dashi, "Bari in tafi domin in koma ga dangina da su ke a Masar in kuma ga ko suna nan da rai." Sai Yetro ya cewa Musa, "Ka tafi cikin salama." 19 Yahweh ya cewa Musa cikin Midiyan, "Tafi, ka koma Masar, gama dukkan mazajen dake neman su ɗauke ranka sun mutu." 20 Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya ɗora su bisa jaki. Ya dawo zuwa ƙasar Masar, ya kuma ɗauki sandar Allah cikin hannunsa. 21 Yahweh ya cewa Musa, "Lokacin da ka iso Masar, ka tabbata ka aikata a gaban Fir'auna dukkan abubuwan banmamaki da na sanya cikin ikonka. Amma zan taurare zuciyarsa, ba kuwa zai bar mutanen su tafi ba. 22 Dole ka cewa Fir'auna, 'Ga abin da Yahweh yace: Isra'ila ɗana ne, ɗan fãrina, 23 kuma ina ce maka, "Ka bar ɗana ya tafi, domin ya yi mani sujada." Amma tunda ka ƙi ka bar shi ya tafi, lallai zan kashe ɗanka, ɗanka na fãri.'" 24 Yayin da suke kan hanya, da suka tsaya don su kwana a daren nan, Yahweh ya gamu da Musa ya kuma yi ƙoƙarin ya kashe shi. 25 Sai Ziffora ta ɗauki wuƙa mai kaifi ta yanke loɓar fatar ɗanta, ta taɓa shi da ita ga sawayensa. Sai ta ce, "Tabbas kai ango ne a gare ni ta wurin jini." 26 Sai Yahweh ya ƙyale shi. Ta ce, "Kai angon jini ne" sabili da kaciyar. 27 Yahweh yace da Haruna, "Tafi cikin jeji ka gamu da Musa." Haruna ya tafi, ya gamu dashi a tsaunin Allah, ya yi masa sumba. 28 Sai Musa ya faɗa wa Haruna dukkan maganganun Yahweh da ya aike shi ya faɗi da dukkan alamu na ikon Yahweh da ya umarce shi ya aikata. 29 Sai Musa da Haruna suka tafi suka tãra dukkan dattawan Isra'ila. 30 Haruna ya faɗi dukkan maganganun da Yahweh ya faɗa wa Musa. Ya kuma yi alamun na ikon Yahweh a gaban mutanen. 31 Mutanen suka gaskanta. Lokacin da suka ji cewa, Yahweh ya lura da Isra'ilawa kuma da cewa ya ga ƙuncinsu, sai suka sunkuyar da kansu suka kuma yi masa sujada.

Sura 5

1 Bayan waɗannan abubuwan sun faru, sai Musa da Haruna suka je wurin Fir'auna suka kuma ce, "Ga abin da Yahweh, Allah na Isra'ila, yace: 'Ka bar mutane na su tafi, domin suyi ma ni biki a cikin jeji.'" 2 Fir'auna yace, "Wane ne Yahweh? Don me zan saurari muryarsa har da zan bar Isra'ila ya tafi? Ban san Yahweh ba; don haka, ba zan bar Isra'ila ya tafi ba." 3 Suka ce, "Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji mu kuma yi hadaya ga Yahweh Allahnmu domin kada ya kawo mana farmaki da annoba ko takobi." 4 Amma sarkin Masar yace ma su, 'Musa da Haruna, don me kuke ɗauke mutanen nan daga aikinsu? Ku koma ga aikinku." 5 Ya kuma ce, "Gashi yanzu akwai mutane Ibraniyawa dayawa a cikin ƙasarmu, kuma kuna sasu su daina aikinsu." 6 A wannan ranar, Fir'auna ya bada umarni ga shugabannin aikin tilas da masu jagorar mutanen. Ya ce, 7 Ba kamar dã ba, ba za ku bada tattaka ga mutanen ba domin yin tubula. Bari su tafi su tarawa kansu budu. 8 Duk da haka, za ka buƙaci tubula daga garesu dai dai kamar yadda ka buƙata a dã. Kada ku karɓi abin da ya gaza yadda aka sãba, domin ƙyuya gare su. Shi yasa suke kira da cewar, 'Bari mu je mu yi hadaya ga Allahnmu.' 9 Ku ƙara wa mazajen aiki don su duƙufa cikinsa har da ba za su saurari maganganun yaudara ba." 10 Sai shugabannin aikin tilas da masu jagorar mutanen suka fita suka yi magana da mutane. Suka ka ce, "Ga abin da Fir'auna yace: 'Ba zan ƙara baku wani budu ba. 11 Ku da kanku dole ku je ku kuma samo budu duk inda ake samunsa, amma aikin ku ba zai ragu ba.'" 12 Don haka sai mutanen suka barbazu a ko'ina cikin ƙasar Masar domin su tãra yayi don budu. 13 Sai 'yan gandu suka ci gaba da tsananta masu suna cewa, "Ku gama aikin ku, kamar yadda dã ake baku tattaka." 14 Shugabannin aikin tilas na Fir'auna suka dinga bugun masu jagorar Isra'ilawa, waɗanda aka sanya bisa sauran ma'aikata. Shugabannin aikin tilas suka dinga tambayarsu, "Don me yasa baku yi dukkan ãdadin tubula da ake buƙata ba, ko na jiya da kuma na yau, kamar yadda kuka sãba a baya?" 15 Sai masu jagora na Isra'ilawa suka shiga wurin Fir'auna da kuka gare shi. Suka ce, "Meyasa kake yi da bayinka haka? 16 Babu wata tattakar da ake ba bayin ka kuma, duk da haka suna ce mana, 'Ku yi tubula!' Mu ma, bayin ka, yanzu bugun mu ake yi, duk da haka laifin mutanen ka ne." 17 Amma Fira'auna yace, "Kuna da ƙyuya! Kuna da ƙyuya! Kun ce, 'Ka barmu mu je mu yi hadaya ga Yahweh.' 18 Saboda haka yanzu ku koma ga aiki. Ba za a ba ku tattaka ba, amma dole ne ku cika ãdadin tubulan ku." 19 Sai masu jagorar Isra'ilawa suka ga cewa suna cikin matsala lokacin da aka ce da su, "Ba za ku rage tubula na kowace rana ba." 20 Sai suka sami Musa da Haruna, a wannan lokaci suna tsaye a wajen fãdar, sa'ad da suke fitowa daga wurin Fir'auna. 21 Suka cewa Musa da Haruna, 'Bari Yahweh ya dube ku ya kuma hore ku, domin kunsa mun zama abin kyama a gaban Fir'auna da kuma bayinsa. Kun sanya takobi a hannunsu don su kashe mu." 22 Sai Musa ya komo ga Yahweh ya kuma ce, "Ubangiji, meyasa ka kawo wahala ga mutanenka? Meyasa ka aiko ni tun da farko? 23 Tun lokacin da na iso wurin Fir'auna domin in yi magana da shi a sunanka, ya jawo wa mutanen nan wahala, kuma baka ƙubutar da mutanenka ba sam-sam."

Sura 6

1 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Yanzu ne za ka ga abin da zan yi wa Fir'auna. Za ka ga wannan, gama zai barsu su tafi sabili da hannuna mai ƙarfi. Sabili da hannuna mai ƙarfi, zai kore su daga ƙasarsa." 2 Allah ya yi magana da Musa ya kuma ce masa, "Ni ne Yahweh. 3 Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku, ga Yakubu kuma a matsayin Allah Mai Iko Dukka; amma da sunana, Yahweh, basu san Ni ba. 4 Na kuma kafa alƙawari na da su, domin in ba su ƙasar Kan'ana, ƙasar da suka zauna a matsayin baƙi, ƙasar da suka yi yawo a ciki. 5 Bugu da ƙari, na ga ƙuncin 'ya'yan Isra'ila waɗanda Masarawa suka bautar, kuma na tuna da alƙawarina. 6 Saboda haka, ka gaya wa Isra'ilawa, 'Ni ne Yahweh. Zan fito da ku daga bautar Masarawa, kuma zan fishe su daga ƙarƙashin ikon su. Zan kuɓutar da ku ta wurin nuna ikona, tare da manyan ayyukan hukunci. 7 Zan ɗauke ku a gare ni a matsayin mutane na, zan kuma zama Allahnku. Za ku sani Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga bautar Masarawa. 8 Zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse in ba Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu. Zan bada ita gareku abin mallaka. Ni ne Yahweh."' 9 Da Musa ya faɗi wannan ga Isra'ilawa, sai suka ƙi su saurare shi saboda karayar zucinsu sabili da bautarsu mai zafi. 10 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 11 "Tafi ka faɗi wa Fir'auna, sarkin Masar, ya bar mutanen Isra'ila su tafi daga ƙasarsa." 12 Sai Musa ya cewa Yahweh, "To idan har Isra'ilawa ba su saurare ni ba, don me Fir'auna zai saurare ni, tunda ban ƙware a magana ba?" 13 Yahweh ya yi magana da Musa da kuma Haruna. Ya ba su umarni domin Isra'ilawa domin kuma Fir'auna, sarkin Masar, su fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar. 14 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu: 'Ya'yan Ruben, ɗan fari na Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hezron, da kuma Karmi. Waɗannan su ne kakannin kabilar Ruben. 15 'Ya'yan Simiyon su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da kuma Shawul - ɗan wata mace Bakan'aniya. Waɗannan su ne kakannin kabilar Simiyon. 16 Ga jerin sunayen 'ya'yan Lebi, tare da zuriyarsu. Sune Gashon, da Kohat, da kuma Merari. Lebi ya yi rayuwa har shekaru 137. 17 'Ya'yan Gashon su ne Libni da Shimei. 18 'Ya'yan Kohat su ne Amram, da Izhar, da Hebron, da kuma Uzziyel. Kohat ya yi rayuwa har ya kai shekaru 133. 19 'Ya'yan Merari su ne Mahli da Mushi. Waɗannan suka zama kakannin kabilar Lebiyawa, tare da zuriyarsu. 20 Amram ya auri Yokebeb, 'yar'uwar mahaifinsa. Ta haifar masa Haruna da Musa. Amram ya yi rayuwa har tsawon shekaru 137 sai kuma ya mutu. 21 'Ya'yan Izhar su ne Korah, da Nefeg, da Zikri. 22 'Ya'yan Uzziyel su ne Mishyel, da Elzafan, da kuma Sitri. 23 Haruna ya auri Elisheba, ɗiyar Amminadab, 'yar uwar Nahshon. Ta haifar masa Nadab da Abihu, da Eliyeza da kuma Itamar. 24 'Ya'yan Kora su ne Assir, da Elkana, da kuma Abiyasaf. Waɗannan su ne kakannin kabilar Korahawa. 25 Eliyeza, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya matan Futiyel. Ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanni a cikin Lebiyawa, tare da zuriyarsu. 26 Waɗannan mutanen biyu su ne Haruna da Musa a gare su ne Yahweh yace, "Ku fito da 'ya'yan Isra'ilawa daga ƙasar Masar, bisa ga ƙungiyoyinsu na mayaƙa." 27 Sai Haruna da Musa suka yi magana da Fir'auna, sarkin Masar, da ya barsu su fito da Isra'ilawa daga Masar. Waɗannan dai Musa da Harunan ne. 28 Da Yahweh ya yi magana da Musa a cikin ƙasar Masar, 29 ya ce masa, "Ni ne Yahweh. Ka ce wa Fir'auna, sarkin Masar, dukkan abin da zan faɗa maka." 30 Amma Musa ya cewa Yahweh, "Ban ƙware ba wurin magana, don haka ta yaya Fir'auna zai saurare ni?"

Sura 7

1 Yahweh ya cewa Musa, "Duba, Na maishe ka kamar wani allah ga Fir'auna. Haruna ɗan'uwanka zai zama annabi dominka. 2 Za ka faɗi dukkan abin da na dokace ka ka faɗa. Haruna ɗan'uwanka zai yi magana da Fir'auna don ya bar mutanen su tafi daga ƙasarsa. 3 Amma zan taurare zuciyar Fir'auna, kuma zan bayyana alamu masu yawa na iko na, abubuwa masu ban mamaki, cikin ƙasar Masar. 4 Amma Fir'auna ba zai saurare ku ba, saboda haka zan saukar da hannuna bisa Masar in kuma kawo ƙungiyoyin mayaƙana, mutanena, zuriyar Isra'ila, daga cikin ƙasar Masar da manyan ayyuka na shara'antawa. 5 Masarawa zasu sani Ni ne Yahweh sa'ad da na miƙa hannuna bisa Masar na kuma fito da Isra'ilawa daga cikin su." 6 Sai Musa da Haruna suka aikata haka; suka yi dai-dai kamar yadda Yahweh ya dokace su. 7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku a lokacin da suka yi magana da Fir'auna. 8 Yahweh ya cewa Musa da Haruna, 9 "Idan Fir'auna yace maku, 'Ku yi abin al'ajibi,' sai ka ce wa Haruna, 'Ka ɗauki sandarka ka kuma jefa ta ƙasa a gaban Fir'auna, domin ta zama maciji.'" 10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, sai kuma suka yi kamar yadda Yahweh ya umarce su. Haruna ya jefar da sandarsa ƙasa a gaban Fir'auna da bayinsa, sai ta zama maciji. 11 Sai Fir'auna shima ya kira masu hikimarsa da masu duba. Sai su ma suka yi haka ta wurin sihiri. 12 Kowanne mutum ya jefar da sandarsa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sai macijin Haruna ya haɗiye macizansu. 13 Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar yadda Yahweh ya faɗa tun dã. 14 Yahweh ya cewa Musa, "zuciyar Fir'auna ta yi tauri, kuma ya ƙi ya bar mutanen su tafi. 15 Ka tafi wurin Fir'auna da safe lokacin da ya fita wurin ruwan. Ka tsaya daga bakin kogin don ka tarye shi, ka kuma ɗauki sandarka a hannunka sandar da ta zama maciji. 16 Ka ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya aike ni gare ka in ce maka, "Ka bar mutanena su tafi, don su yi mani sujada cikin jeji. Har yanzu baka saurara ba." 17 Yahweh ya faɗi wannan: "Ta haka zaka sani Ni ne Yahweh. Zan bugi ruwa na Kogin Nilu da sandar dake a hannuna, sai kuma ruwan ya zama jini. 18 Kifayen da suke a cikin kogin za su mutu, kuma kogin zai yi ɗoyi. Masarawa ba za su iya shan ruwa daga kogin ba.'"" 19 Sai Yahweh yace da Musa, "Ka ce wa Haruna, 'Ka ɗauki sandarka ka miƙa ta zuwa ga ruwayen Masar, da kuma zuwa ga kogunansu, da rafufukansu, da kududdufansu, da kuma dukkan tafkunansu, domin ruwayensu sun zama jini. Ka yi wannan domin a sami jini cikin dukkan ƙasar Masar, har ma da randunan itace da na duwatsu.'" 20 Sai Musa da Haruna suka yi kamar yadda Yahweh ya umarta. Haruna ya miƙa sandar ya kuma bugi ruwan kogin, a gaban Fir'auna da bayinsa. Sai dukkan ruwaye na kogunan suka zama jini. 21 Kifayen kogin suka mutu, sai kogin ya fara ɗoyi. Masarawa ba su iya shan ruwa daga kogin ba, kuma sai jinin ya bazu ko'ina a cikin ƙasar Masar. 22 Amma masu sihiri na Masar suka yi haka dai-dai da dabonsu. Amma zuciyar Fir'auna an taurare, sai kuma ya ƙi ya saurari Musa da Haruna, kamar yadda Yahweh ya faɗi zai faru. 23 Sai Fir'auna ya juya ya koma gidansa. Bai ma ba da hankalinsa ga wannan ba. 24 Dukkan Masarawa suka haƙa rami a gefen kogin don su sami ruwa su sha, amma ba su iya shan ruwan kogin da kansa ba. 25 Kwana bakwai suka wuce bayan da Yahweh ya kai farmaƙi ga kogin.

Sura 8

1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, "Ka tafi wurin Fir'auna ka kuma ce masa, 'Yahweh ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada. 2 Idan ka ƙi ka barsu su tafi, zan azabtar da dukkan ƙasarka da ƙwaɗi. 3 Kogunan za su cika da kwaɗi. Za su fito su shiga gidajenku, da ƙuryar ɗakinku, da kan gadonku. Za su shiga cikin gidajen bayinku. Za su kai ga mutanenka, cikin murhunka, da kuma cikin makwaɓan ƙullunka. 4 Kwãɗin za su hau kanka, da mutanenka, da kuma dukkan bayinka.""' 5 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ce wa Haruna, 'Miƙa hannun ka tare da sandarka bisa kogunan, da rafufuka, da kuma kududdufai, ka kawo kwãɗi bisa ƙasar Masar."' 6 Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwayen Masar, sai kwãɗin suka zo suka rufe dukkan ƙasar Masar. 7 Amma bokayen suka aikata irin haka da dabonsu; suka kawo kwãɗi bisa ƙasar Masar. 8 Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya kuma ce, "Ku yi addu'a ga Yahweh don ya kawar da kwãɗin daga gare ni da mutanena. Sa'an nan zan bar mutanen su tafi, domin su yi masa hadaya." 9 Musa ya cewa Fir'auna, "Kana iya samun zarafin gaya mani in yi maka addu'a, da bayinka, da kuma mutanenka, don a kawar da kwãɗin daga gare ku da gidajenku su kuma tsaya a cikin kogin kawai." 10 Fir'auna yace, "Gobe." Musa yace, "Bari shi zama yadda ka faɗa, don ka san cewa babu wani kamar Yahweh, Allahnmu. 11 Kwãɗin za su bar ka, da gidajenka, da bayinka, da kuma mutanenka. Za su tsaya cikin kogi ne kawai." 12 Sai Musa da Haruna su ka fito daga gaban Fir'auna. Sai Musa ya yi kuka ga Yahweh game da kwãɗin da ya kawo bisa Fir'auna. 13 Yahweh ya aikata kamar yadda Musa ya roƙa: Sai kwãɗin suka mutu cikin gidajen, daga shirayi, da filaye. 14 Sai mutanen suka tara su tuli-tuli, sai kuma ƙasar ta yi ɗoyi. 15 Amma da Fir'auna ya ga cewa akwai sauƙi, sai ya taurare zuciyarsa bai kuma saurari Musa da Haruna ba, kamar yadda Yahweh yace zai yi. 16 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ce da Haruna, 'Ka miƙa sandarka ka bugi ƙurar ƙasa, don ta zama kwarkwata cikin dukkan ƙasar Masar."' 17 Suka aikata haka: Haruna ya miƙa hannunsa da sandarsa. Ya bugi ƙura a ƙasa. Sai kwarkwata masu yawa suka zo bisa mutum da dabba. Dukkan ƙurar ƙasa ta zama kwarkwata cikin dukkan ƙasar Masar. 18 Sai bokayen su ma suka gwada da sihirinsu domin su fito da kwarkwata, amma ba su iya yin haka ba. Aka sami kwarkwata a bisa mutane da kuma dabbobi. 19 Sai bokayen suka ce wa Fir'auna, "Wannan yatsan Allah ne." Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, don haka bai saurare su ba. Dai-dai ne ga yadda Yahweh ya faɗi cewa Fir'auna zai yi. 20 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tashi da sauri da safe ka kuma tsaya a gaban Fir'auna yayin da ya fito zuwa kogi. Ka ce da shi, 'Yahweh ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi don suyi mani sujada. 21 Amma idan baka bar su sun tafi ba, zan aiko da cin-cirindon ƙudaje gareka, zuwa ga bayinka, da kuma mutanenka, da kuma cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da cin-cirindon ƙudaje, har ma da ƙasar da suke tsayawa za ta cika da ƙudaje. 22 Amma a wannan ranar zan bambanta ƙasar Goshen, ƙasar da mutanena suke zama, don kada a sami wani cin-cirindon ƙudaje a nan. Wannan zai faru domin ka san cewa Ni ne Yahweh da nake tsakiyar wannan ƙasa. 23 Zan bambanta tsakanin mutanena da mutanenka. Wannan alama ce ta ikona zai faru gobe.""' 24 Yahweh ya yi haka, sai kuma cin-cirindon ƙudaje mai kauri suka aukawa gidan Fir'auna da kuma gidajen bayinsa. Cikin dukkan ƙasar Masar, ƙasar ta lalace ta dalilin cin-cirindon ƙudajen. 25 Sa'an nan Fir'auna ya kira Musa da Haruna yace, "Ku tafi, ku yi hadaya ga Allahnku a cikin ƙasarmu." 26 Musa yace, "Bai yi dai-dai ba muyi haka, gama hadayar da muke yi ga Yahweh Allahnmu abar ƙyama ce ga Masarawa. Idan muka miƙa hadayar suna gani abin ƙyama ga Masarawa, ba zasu jejjefemu ba? 27 Ba haka ba, tafiyar kwana uku ce cikin jeji da ya kamata muyi, domin muyi hadaya ga Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya umurce mu." 28 Fir'auna yace, "Zan bar ku don ku tafi ku yiwa Allahnku hadaya cikin jeji. Sai dai kada ku tafi da nisa sosai. Ku yi mani addu'a. 29 Musa yace, "Da zarar na fita daga gare ka, zan yi roƙo ga Yahweh domin cin-cirindon ƙudaje su bar ka, Fir'auna, da bayinka da kuma mutanenka gobe. Amma kada ka ƙara yin yaudara ta wurin ƙin barin mutanenmu su tafi su yiwa Yahweh hadaya." 30 Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna ya kuma yi roƙo ga Yahweh. 31 Yahweh ya yi yadda Musa ya roƙa; ya kuma janye cin-cirindon ƙudaje daga Fir'auna, da bayinsa, da mutanensa. Babu wanda ya rage 32 Amma Fir'auna ya taurare zuciyarsa wannan lokaci kuma, ya kuma ƙi barin mutanen su tafi.

Sura 9

1 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Jeka wurin Fir'auna ka ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: "Bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada." 2 Amma idan baka yarda ka bar su ba, idan ka hana su, 3 daganan hannun Yahweh zai kasance bisa garken shanunka cikin filaye da kuma bisa dawakai, da jakuna, da raƙuma, garkunan dabbobi, da garkunan tumaki da awaki, kuma zai yi sanadiyar cuta mai banrazana. 4 Yahweh zai bambanta garken Isra'ilawa da ta Masarawa kuma babu dabbar dake ta Isra'ilawa da za ta mutu. 5 Yahweh ya tsayar da lokaci; ya riga yace, "Gobe ne zan aikata wannan abin cikin ƙasar.""' 6 Yahweh ya yi wannan washegari: Dukkan garkunan shanun Masar suka mutu, amma babu dabbar da ke ta Isra'ila da ta mutu, ko dabba ɗaya. 7 Fir'auna ya yi bincike, kuma, duba, ko da ɗaya na dabbar Isra'ilawa bata mutu ba. Amma zuciyarsa ta taurare, don haka bai yadda mutanen su tafi ba. 8 Sai Yahweh ya cewa Musa da Haruna, "Ku ɗebo toka daga murhu. Kai, Musa, dole ka watsa tokar sama cikin iska yayin da Fir'auna na gani. 9 Za su zama ƙura mai laushi bisa dukkan ƙasar Masar. Za su yi sanadiyar gyambuna da kuma marurai su addabi mutane da dabbobi cikin dukkan ƙasar Masar." 10 Sai Musa da Haruna suka ɗebo toka daga murhu suka kuma tsaya a gaban Fir'auna. Sai Musa ya watsar da tokar cikin iska. Tokar ta yi sanadiyar gyambuna da marurai da suka addabi mutane da dabbobi. 11 Bokayen ba su iya tsayayya da Musa ba sabili da gyambunan, domin gyambunan sun kama su da sauran Masarawa. 12 Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, don haka Fir'auna bai saurari Musa da Haruna ba. Wannan kamar yadda Yahweh ya riga ya gaya wa Musa ne cewa Fir'auna zai yi. 13 Sai Yahweh yace wa Musa, "Ka tashi da sassafe, ka tsaya a gaban Fir'auna, ka kuma ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada. 14 Gama a wannan karon zan aiko da dukkan annobaina a kanka, a bisa bayinka da mutanenka. Zan aikata wannan domin ka san cewa babu wani mai kama da ni cikin dukkan duniya. 15 Ko a yanzu da na miƙa hannuna in kai maka farmaki da mutanenka da cuta, kuma da yanzu an kawar da kai daga ƙasar. 16 Amma sabili da wannan dalili ne na bar ka ka tsira: Domin in nuna maka ikona, domin a shaida sunana a cikin dukkan duniya. 17 Har yanzu kana ɗaukaka kanka gãba da mutanena da har yanzu baka barsu su tafi ba. 18 Ka saurara! Gobe warhaka zan kawo ruwa da ƙanƙara mai ƙarfi, irin wadda ba a taɓa gani ba a cikin ƙasar Masar ba tun lokacin da aka kafa ta zuwa yau. 19 Yanzu dai, ku aika mazaje su dawo da garken ku da dukkan abin da kuke da shi a cikin gonaki zuwa ga mafaka. Kowanne mutum da dabba dake a gona da ba a shigo da su gida ba - ƙanƙarar zata faɗo masu, za su kuma mutu.""' 20 Sa'an nan wasu daga cikin bayin Fir'auna waɗanda suka gaskanta da saƙon Yahweh suka yi hanzari suka dawo da bayinsu da kuma garkensu cikin gidaje. 21 Amma waɗanda ba su ɗauki maganar Yahweh da wani mahimmanci ba suka bar bayinsu da garken su cikin gonaki. 22 Sai Yahweh yace wa Musa, "Miƙa hannunka zuwa sararin sama don a yi ƙanƙara cikin dukkan ƙasar Masar, bisa mutane, bisa dabbobi, da kuma dukkan itatuwan cikin gonaki a dukkan ƙasar Masar." 23 Sai Musa ya miƙa sandarsa zuwa sararin sama, sai Yahweh ya aiko da aradu, ƙanƙara, da walkiya a ƙasar. Ya kuma kwararo ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar. 24 Saboda haka aka yi ƙanƙara da walƙiya gauraye da ƙanƙarar, mai tsananin gaske, irin da ba a taɓa yi ba cikin dukkan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma. 25 A dukkan ƙasar Masar kuwa, ƙankaran ta bugi kowanne abu cikin gonaki, da mutane da kuma dabbobi. Ta bugi kowacce shuka dake a gonaki ta kuma karya kowanne itace. 26 A ƙasar Goshen ne kaɗai, inda Isra'ilawa ke zama, babu ƙanƙara. 27 Daga nan sai Fir'auna ya aika da mutane su kawo Musa da Haruna. Ya ce masu, "Na yi zunubi dai yanzu. Yahweh mai adalci ne, ni kuwa da mutanena mugaye ne. 28 Ku yi addu'a ga Yahweh, domin waɗannan tsawa mai ƙarfi da kuma ƙanƙara sun yi yawa. Zan barku ku tafi, ba kuma zaku zauna nan ba." 29 Musa yace masa, "Da zarar na fita daga birnin, zan buɗe hannuwana ga Yahweh. Tsawar aradun zata tsaya, kuma babu sauran ƙanƙara. Ta haka zaka sani cewa duniyar ta Yahweh ce. 30 Amma game da kai da bayinka, Na san da cewa har yanzu baka rigaya ka girmama Yahweh Allah ba da gaske." 31 Yanzu dai da hatsi da kuma riɗi an lallatar da su, gama riɗi ta yi ido, hatsi kuma tana fidda kai. 32 Amma alkama da gero ba a ji masu rauni ba domin ba su yi girma ba tukuna. 33 Bayan da Musa ya bar Fir'auna da kuma birnin, ya miƙa hannuwansa ga Yahweh; tsawa da ƙanƙara suka tsaya, sai kuma ruwan sama bai sake saukowa ba. 34 Sa'ad da Fir'auna ya ga cewa ruwan sama ya tsaya, da ƙanƙarar, da tsawar aradun sun tsaya, sai ya sake yin zunubi ya taurare zuciyarsa, duk da bayinsa. 35 Zuciyar Fir'auna ta taurare, don haka bai bar mutanen Isra'ila su tafi ba. Yadda Yahweh ya riga ya faɗa wa Musa cewa Fir'auna zai aikata.

Sura10

1 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi wurin Fir'auna, gama na taurare zuciyarsa da zuciyar bayinsa. Na yi haka ne domin in nuna waɗannan alamun ikon ƙarfina a cikin su. 2 Na kuma yi haka ne domin ku gaya wa 'ya'yanku da jikokinku abubuwan dana yi, yadda na fusata bisa Masar, da kuma yadda na nuna alamu daban-daban na ƙarfin ikona a tsakaninsu. Da haka zaku sani Ni ne Yahweh." 3 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna suka kuma ce masa, "Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: 'Har yaushe zaka ƙi ka ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada. 4 Amma idan ka ƙi ka bar mutanena su tafi, ka saurara, gobe zan kawo fãri cikin ƙasarka. 5 Za su rufe fuskar ƙasa har babu wanda zai iya ganin ƙasa. Za su chinye kowanne abin da ya tsira daga ƙanƙara. Za su kuma cinye kowanne itacen da ya tsiro domin ka cikin gonaki. 6 Za su cika gidajenka, da na bayinka, da na dukkan Masarawa - abu ne wanda mahaifinka da kakanka basu taɓa gani ba, abin da ba a taɓa gani ba tun daga ranar da suke cikin duniya har wa yau.'" Daga nan Musa ya fita ya kuma bar Fir'auna. 7 Sai bayin Fir'auna suka ce masa, "Har yaushe wannan mutum zai zama mana bala'i? Ka bar Isra'ilawan su tafi domin su yi wa Yahweh Allahnsu sujada. Ko ba ka fahimci cewa an hallakar da Masar ba?" 8 Aka kawo Musa da Haruna kuma a gaban Fir'auna, sai yace masu, "Ku tafi ku yiwa Yahweh Allahnku sujada. Amma waɗanne mutane ne za su tafi?" 9 Musa yace, "Za mu tafi tare da ƙanananmu da kuma tsofofinmu, tare da 'ya'yanmu maza da 'ya'ya mata. Zamu tafi da tumakanmu da garkenmu, gama dole ne muyi buki ga Yahweh." 10 Fir'auna yace masu, "Bari Yahweh lallai ya kasance tare da ku, idan har na barku ku tafi tare da 'yan ƙanananku. Duba, kana da wata mugunta a cikin zuciya. 11 Ba haka ba! Ku tafi, mazaje kawai na cikinku, ku yiwa Yahweh sujada, gama abin da kuke so kenan." Sa'an nan aka kori Musa da Haruna daga fuskar Fir'auna. 12 Sai Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannunka bisa ƙasar Masar zuwa ga fãrin, domin su abko wa ƙasar Masar su kuma cinye dashe-dashen cikin ta, dukkan sauran abubuwan da ƙanƙara ta rage." 13 Musa ya miƙa sandarsa bisa Masar, Yahweh kuwa ya aiko da iskar gabas bisa ƙasar dukkan wannan rana da dare. Sa'ad da safiya ta yi, iskar gabas ta riga ta kawo fãrin. 14 Fãrin suka shiga dukkan ƙasar Masar suka kuma cutar da dukkan sassanta. Ba a taɓa yin irin wannan cin-cirindon fãri cikin ƙasar ba, ba kuma za a sake mai kamannin haka ba. 15 Suka rufe fuskar dukkan ƙasa har wuri ya yi duhu. Suka cinye dukkan dashe-dashe da ke cikin ƙasa da dukkan 'ya'yan itatuwan da ƙanƙara ta rage. A cikin dukkan ƙasar Masar, babu koren tsiro mai rai da ta ragu, ko wani itace ko dashe a cikin gonaki. 16 Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya kuma ce, "Na yi zunubi ga Yahweh Allahnku, da gare ku kuma. 17 Yanzu dai, ku gafarta zunubi na wannan kãron, kuyi addu'a ga Yahweh Allahnku don ya ɗauke wannan mutuwa daga gare ni." 18 Don haka Musa ya fita daga gaban Fir'auna ya yi addu'a ga Yahweh. 19 Yahweh ya kawo babbar iskar yamma mai ƙarfi da ta kwashe fãrin ta kora su cikin Jan Teku; babu fãrar da ta rage cikin dukkan lardunan Masar. 20 Amma Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, kuma Fir'auna bai bar Isra'ilawa su tafi ba. 21 Sai Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannunka zuwa sararin sama, don a yi duhu bisa ƙasar Masar, duhun da za a iya taɓawa." 22 Sai Musa ya miƙa hannunsa zuwa sama, sai aka yi wani gaggarumin duhu bisa dukkan ƙasar Masar har na kwana uku. Babu wanda ya iya ganin wani; 23 Babu wanda ya bar gidansa har kwana uku. Duk da haka, dukkan Isra'ilawa suna da haske a wurin da suke zaune. 24 Sai Fir'auna ya aika aka kawo Musa sai yace, "Ku tafi ku yi wa Yahweh sujada. Har da iyalanku na iya tafiya tare da ku, amma garkunan ku na tumaki dole ku bar su nan." 25 Amma Musa yace, "To dole ka ba mu dabbobin da zamu yi hadaya ga Yahweh Allahnmu. 26 Garkunan mu dole mu tafi da su; babu ko ƙofaton su da zai rage a baya, gama dole ne mu tafi da su domin yin sujada ga Yahweh Allahnmu. Gama ba mu san da mene ne za mu yi sujada ga Yahweh ba, sai mun isa can." 27 Amma sai Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, har da ba zai bar su su tafi ba. 28 Fir'auna ya cewa Musa, "Ka fita daga gare ni! Kayi hankali da abu ɗaya, cewa kada ka ƙara gani na, gama duk ranar da ka ga fuskata, za ka mutu." 29 Sai Musa yace masa, "Kai da kanka ka faɗa. Ba zan ƙara ganin fuskarka ba."

Sura 11

1 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Akwai sauran annoba guda ɗaya da zan kawo bisa Fir'auna da Masar. Bayan wannan, zai barku ku tafi daga nan. Sa'ad da a ƙarshe ya barku kuka tafi, zai kore ku gaba ɗaya. 2 Ka umarci mutanen cewa kowanne mutum da kowacce mace su roƙi maƙwabcinsa ko maƙwabciyarta kayayyakin azurfa da kayayyakin zinariya." 3 Yanzu dai Yahweh ya sa Masarawa suyi ɗokin farantawa Isra'ilawa rai. Bugu da ƙari, mutumin nan Musa ya birge sosai a gaban barorin Fir'auna da mutanen Masar. 4 Musa yace, "Yahweh ya faɗi wannan: 'Wajen tsakar dare zan ratsa cikin dukkan Masar. 5 Dukkan 'ya'yan fãri cikin ƙasar Masar za su mutu, daga ɗan fãrin Fir'auna, wanda ke zaune bisa kursiyinsa, zuwa ɗan fãrin baiwa wanda ke bayan dutsen niƙa tana niƙa, da dukkan 'ya'yan fãrin dabbobi. 6 Daga nan za a yi babban makoki cikin dukkan ƙasar Masar, irin wanda ba a taɓa yi ba kuma ba za a ƙara yi ba. 7 Amma babu ko kare da zai yi haushi ga ko ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila, ko ga mutum ko dabba. Ta wannan hanya za ku sani cewa ina nuna bambanci tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.' 8 Dukkan waɗannan bayin naka, Fir'auna, za su sauko zuwa gare ni su rusuna mani. Za su ce, 'Ka tafi, kai da dukkan mutanen da suka biyo ka!' Bayan wannan zan fita." Daga nan ya fita daga wurin Fir'auna da babban fushi. 9 Yahweh ya cewa Musa, "Fir'auna ba zai saurare ka ba. Wannan ya zama haka ne domin in aiwatar da abubuwan ban mamaki masu yawa a cikin ƙasar Masar." 10 Musa da Haruna suka yi dukkan waɗannan al'ajibai a gaban Fir'auna. Amma Yahweh ya kangarar da zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuma bai bar mutanen Isra'ila suka fita daga ƙasarsa ba.

Sura 12

1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna a cikin ƙasar Masar. Ya ce, 2 "Game da ku, wannan wata zai zama farawar watanni, watan farko na shekara a gare ku. 3 Ka faɗa wa taron Isra'ila, 'A ranar goma ga wannan watan dole ne kowannen su ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya domin kansu, kowanne iyali na yin wannan, ɗan rago domin kowanne gida. 4 Idan gidan ya yi ƙanƙanta sosai domin ɗan rago, mutumin da makwabcinsa zasu ɗauki naman ɗan rago ko ɗan akuya wanda zai isa domin adadin mutanen. Ya kasance ya isa domin kowanne mutum ya ci, saboda haka dole su ɗauki isasshen nama domin dukkan su su ci. 5 ‌Ɗan ragonku ko ɗan akuyan dole ya zama marar aibi, ɗan shekara ɗaya m. Kuna iya ɗaukar ɗaya daga cikin tumaki ko awaki. 6 Tilas ku ajiye ta har sai ranar sha huɗu ga wata. Daga nan dukkan taron Isra'ila tilas su yanka waɗannan dabbobi da hasken asuba. 7 Tilas ku ɗiba daga cikin jinin ku kuma sanya a dokin ƙofa gefe biyu da saman ginshiƙan ƙofofin gidajen inda zaku ci naman. 8 Tilas ku ci naman a wannan daren, bayan an gasa da farko a bisa wuta. A ci shi da gurasa da akayi ba da gami ba, tare da ganye mai ɗaci. 9 Kada ku ci shi ɗanye ko dafaffe cikin ruwa. A maimako, ku gasa shi bisa wuta tare da kansa, kafafunsa da kayan cikinsa. 10 Tilas ba za ku bar wani daga cikinsa ba ya rage har safiya. Tilas ku ƙone duk abin da ya rage har safiya. 11 Ga yadda tilas zaku ci shi: tare da ɗamararku a ɗaure, takalmanku bisa tafin ƙafarku, da sandarku a hannunku. Tilas ku ci shi da hanzari. ‌Ƙetarewa ne na Yahweh. 12 Yahweh ya faɗi wannan: zan ratsa ta cikin ƙasar Masar a wannan dare zan kuma kai hari ga dukkan 'ya'yan fãri na mutum da na dabba a cikin ƙasar Masar. Zan kawo horaswa ga dukkan allolin Masar. Ni ne Yahweh. 13 Jinin zai zama alama ne bisa gidajenku domin zuwa na a gare ku. Idan naga jinin, Zan ƙetare ku sa'ad da na kai hari ga ƙasar Masar. 14 Wannan annoba ba za ta zo bisan ku ba ta kuma hallaka ku. Wannan rana zata zama abar tunawa domin ku, wadda tilas ku kiyaye a matsayin bikin Yahweh. A koyaushe zai kasance shari'a a gare ku, cikin dukkan tsararrakin mutanenku, cewa tilas ku kiyaye wannan rana. 15 Zaku ci gurasa ba tare da gami ba a lokacin kwanakin bakwai. A rana ta farko zaku cire gami daga gidajenku. Duk wanda yaci gurasa mai gami daga ranar farko zuwa rana ta bakwai, wannan taliki tilas a datse shi daga Isra'ila. 16 A rana ta farko za ayi taro da za a keɓe a gare ni, a rana ta bakwai kuma za a sake yin wani irin wannan taron. Babu wani aikin da za ayi a cikin waɗannan kwanaki, sai dai girki domin kowa ya ci. Wannan ne kaɗai aikin da tilas ya zama mai yiwuwa a gare ku. 17 Tilas ku kiyaye wannan biki na gurasa marar gami saboda a wannan rana ce na fito da mutanenku, ƙungiya, ƙungiya na mayaƙa, daga cikin ƙasar Masar. Saboda haka tilas ku kiyaye wannan rana cikin dukkan tsararrakin mutanenku. Wannan a koyaushe zai zama shari'a a gare ku. 18 Tilas ku ci gurasa marar gami tun daga hasken asuba na ranar sha huɗu ga watan farko na shekara, har zuwa hasken asuba na ranar ashirin da ɗaya ga watan. 19 A lokacin waɗannan kwanaki bakwai, tilas kada a sami wani gami cikin gidajenku. Duk wanda ya ci gurasa da aka yi da gami tilas a datse shi daga cikin gundumar Isra'ila, koda wannan taliki baƙo ne ko kuma wanda aka haifa a cikin ƙasar. 20 Tilas ba zaku ci wani abin da akayi da gami ba. Duk inda kuka zauna, tilas ku ci gurasa da akayi ba tare da gami ba."' 21 Daga nan Musa ya yi sammace ga dukkan dattawan Isra'ila ya kuma ce masu, "Kuje ku zaɓi 'yan raguna ko 'yan awaki waɗanda za su isa ku ciyad da iyalanku sai ku kuma yanka su a matsayin ɗan ragon ‌Ƙetarewa. 22 Daga nan sai ku ɗauki curin soso ku tsoma cikin jinin da zai kasance cikin kwano. Sai ku shafa jinin a bisa ginshiƙin ƙofa da dokin ƙofofi biyu. Kada waninku ya fita daga ƙofar gidansa har sai da safe. 23 Domin Yahweh zai ratsa ta ciki ya kai hari ga Masarawa. Idan yaga jinin a bisa ginshiƙin ƙofar da dokin ƙofa biyun, zai ƙetare ƙofarku kuma ba zai bada izini ga mai lalatarwa ba ya shigo cikin gidajenku ya kawo maku hari. 24 Tilas ku kiyaye wannan al'amari. Wannan a koyaushe zai zama shari'a domin ku da zuriyarku. 25 Idan kuka shiga ƙasar da Yahweh zai baku, kamar yadda ya yi alƙawari zai yi, tilas ku kiyaye wannan aikin sujada. 26 Idan 'ya'yanku suka tambaye ku, 'Mene ne ma'anar wannan aikin sujada?' 27 daganan tilas ku ce, 'hadayar ‌Ƙetarewa ce ta Yahweh, saboda Yahweh ya ƙetare gidajen Isra'ilawa a Masar sa'ad da ya kai hari ga Masarawa. Ya 'yantar da gidajenmu."' Daga nan mutanen suka rusuna suka kuma yi sujada ga Yahweh. 28 Isra'ilawa suka tafi suka yi dai-dai yadda Yahweh ya umarci Musa da Haruna. 29 Ya kuwa faru a tsakar dare Yahweh ya kai hari ga dukkan 'ya'yan fãri dake cikin ƙasar Masar, daga ɗan fãrin Fir'auna, wanda ya zauna bisa kursiyi, har ya zuwa ɗan fãrin talikin dake cikin kurkuku da dukkan 'ya'yan fãrin dabbobi. 30 Fir'auna ya tashi da dare - shi, dukkan bayinsa, da dukkan masarawa. Akwai makoki mai ƙara a Masar, domin babu wani gida inda ba wanda ba a rasa wani da ya mutu ba. 31 Fir'auna ya yi sammace ga Musa da Haruna da dare ya kuma ce, "Ku tashi, ku fita daga cikin mutanena, ku da Isra'ilawa. Ku tafi, kuyi sujada ga Yahweh, kamar yadda kuka ce kuna so kuyi. 32 Ku ɗauki garken tumakinku dana awakinku da garken shanunku, kamar yadda kuka ce, ku kuma tafi, sai ku kuma albarkace ni." 33 Masarawa suna cikin babban hanzari su fitar dasu daga ƙasar, gama sun ce, "Dukkanmu zamu mutu." 34 Sai mutanen suka ɗauki ƙullinsu ba tare da sun ƙara wani gami ba. Kwanonin markaɗensu sun riga sun ɗaure cikin kayansu da bisa kafaɗunsu. 35 Yanzu mutanen Isra'ila sun yi yadda Musa yace masu. Suka roƙi Masarawa domin kayayyakin azurfa, da kayayyakin zinariya, da sutura. 36 Yahweh yasa Masarawa ɗokin farantawa Isra'ilawa rai. Sai masarawa suka basu komai game da abin da suka roƙa. Ta wannan hanyar, Isra'ilawa suka washe Masarawa. 37 Isra'ilawa suka yi tafiya daga Remasis zuwa Sukkot. Lissafinsu kimanin mazaje 600,000, baya ga ƙarin mataye da yara. 38 Gaurayen taron waɗanda ba Isra'ilawa ba ma suka tafi tare da su, tare da garkunan tumaki da awaki da na shanu, babban lissafin dabbobi. 39 Suka gasa gurasa marar gami daga cikin ƙullin da suka kawo daga Masar. Ya zama marar gami ne saboda an kore su daga Masar ba zasu kuma yi jinkirin shirya abinci ba. 40 Isra'ilawa sun yi zama a cikin Masar har shekaru 430. 41 A ƙarshen shekaru 430, a dai-dai wannan rana, dukkan ƙungiyoyin mayaƙan Yahweh suka fita daga ƙasar Masar. 42 Wannan dare ne na tsayawa a faɗake, domin Yahweh ya fito da su daga ƙasar Masar. Wannan daren Yahweh ne da za a kiyaye ga dukkan Isra'ilawa cikin dukkan tsararrakin mutanensu. 43 Yahweh ya cewa Musa da Haruna, "Wannan ne ka'ida domin ‌Ƙetarewa: babu wani bare da mai yiwuwa yaci daga cikin sa. 44 Duk da haka, kowanne bawan Ba-isra'ile, da aka sawo da kuɗi, yana iya ci bayan kun yi masa kaciya. 45 Bare da bayin haya tilas ba za su ci wani daga cikn abincin ba. 46 Tilas a ci abincin cikin gida ɗaya. Tilas ba za ku ɗauki wani daga cikin abincin ba ku fita da shi waje, tilas kuma ba za ku karya wani ƙashi ba daga cikin sa. 47 Dukkan gundumar Isra'ila tilas su kiyaye wannan biki. 48 Idan bare yana zaune tare daku kuma yana so ya kiyaye ‌Ƙ‌etarewar ga Yahweh, dukkan danginsa maza tilas a yi masu kaciya. Daga nan zai yiwu su zo su kuma kiyaye shi. Zai zama kamar mutanen da aka haifa cikin ƙasar, Duk da haka, babu wani taliki marar kaciya da mai yiwuwa ya ci wani abu daga cikin abincin. 49 Wannan irin dokar za a zartar ga haifaffen garin da kuma bare dake zaune cikin ku. 50 Sai dukkan Isra'ilawa suka yi dai-dai yadda Yahweh ya umarci Musa da Haruna. 51 Sai ya kasance a dai-dai wannan rana ce Yahweh ya fito da Isra'ila daga ƙasar Masar a ƙungiyoyin mayaƙansu.

Sura 13

1 Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce, 2 "Ka keɓe mani dukkan 'ya'yan fãri, kowanne ɗan fãri namiji daga cikin Isra'ilawa, duk da na mutane da dabbobi. 'Ya'yan fãrin nawa ne." 3 Musa ya cewa mutanen, "Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, domin ta hannun Yahweh mai ƙarfi ya fito daku daga nan wurin. Babu wata gurasa mai gami da zai yiwu a ci. 4 Za ku fita daga Masar a wannan ranar, a cikin watan Abib. 5 Sa'ad da Yahweh ya kawo ku cikin ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hibbiyawa, da kuma Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai baku, ƙasar dake malala da madara da zuma - daganan tilas ku kiyaye wannan aikin sujada a cikin wannan watan. 6 Gama kwanaki bakwai tilas za ku ci gurasa marar gami; a ranar kwana na bakwai za ayi bikin girmama Yahweh. 7 Gurasa marar gami tilas za a ci cikin dukkan kwanakin bakwai; babu wata gurasa mai gami da zai yiwu a gani a cikin ku. Babu wani gami da zai yiwu a gani tare daku a cikin kowanne kan iyakokinku. 8 A wannan rana zaku cewa 'ya'yanku, 'Wannan saboda abin da Yahweh ya yi domina ne sa'ad da na fito daga Masar.' 9 Wannan zai zama abin tunawa domin ka a bisa hannu, abin tunawa kuma a bisa goshi. Wannan saboda shari'ar Yahweh ta kasance a bakinka, domin tare da hannu mai ƙarfi Yahweh ya fito da kai daga Masar. 10 Saboda haka tilas ka kiyaye wannan shari'a a lokacin da aka zaɓa daga shekara zuwa shekara. 11 Sa'ad da Yahweh ya kawo ku cikin ƙasar Kan'aniyawa, kamar yadda ya rantse maku da kakanninku zai yi, kuma sa'ad da ya bayar da ƙasar a gare ku, 12 tilas ku keɓe ga Yahweh kowanne yaro ɗan fãri da ɗan farko na dabbobinku. Mazajen dukka za su zama na Yahweh. 13 Kowanne ɗan fãrin jaki tilas ku saye shi da ɗan rago. Idan baku saye shi ba, daga nan tilas ku karya wuyansa. Amma kowanne ɗan fãri namiji daga cikin dukkan 'ya'yanku maza - tilas ku sake sayen su. 14 Idan ɗan ka yayi maka tambaya daga bisani, 'Mene ne ma'anar wannan?' Daga nan sai ka gaya ma shi, 'Ta wurin hannun Yahweh mai ƙarfi ne aka fito damu daga Masar, daga gidan bauta. 15 Sa'ad da Fir'auna da taurin kai ya ƙi ya bar mu mu tafi, Yahweh ya kashe dukkan 'ya'yan fãri na ƙasar Masar, duk da 'ya'yan fãrin mutane da 'ya'yan fãrin dabbobi. Shi ya sa nake hadaya ga Yahweh na ɗan fãri namiji na kowacce dabba, shi yasa kuma nake sake sayen 'ya'yan fãri na mazaje.' 16 Wannan zaya zama abin tunawa a hannunku, abin tunawa kuma a bisa goshinku, domin ta hannu mai ƙarfi Yahweh ya fito damu daga Masar." 17 Sa'ad da Fir'auna ya bar mutanen su tafi, Allah bai bida su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, koda yake wannan ƙasar tana kurkusa. Domin Allah yace, "Watakila mutanen za su canza ra'ayinsu sa'ad da suka fuskanci yaƙi daganan kuma su koma Masar." 18 Sai Allah ya bi da mutanen su kewaya ta cikin jeji zuwa Tekun Iwa. Isra'ilawa suka fita daga ƙasar Masar shirye domin yaƙi. 19 Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yosef tare da shi, domin Yosef yasa Isra'ilawa suka yi rantsuwa ya kuma ce, "Babu shakka Allah zai ceto ku, kuma tilas ku ɗauke ƙasusuwana tare daku." 20 Isra'ilawa suka yi tafiya daga Sukkot suka kuma yi sansani a Itam a bisa gaɓar jeji. 21 Yahweh ya shiga gabansu da rana ta inuwar girgije domin ya bida su ta hanyar da zasu bi. Da dare ya tafi ta inuwar wuta domin ya basu haske. Ta wannan hanyar suna iya tafiya da rana da kuma dare. 22 Yahweh bai ɗauke kuma daga gaban mutanen da rana inuwar girgije ba da dare kuma inuwar wuta ba.

Sura 14

1 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Ka gaya wa Isra'ilawa cewa su juya su kuma yi sansani kafin Fi Hahirot, tsakanin Magdol da teku, kafin Ba'al Zifon. Za ku yi sansani a gefen teku akasi da Fi Hahirot. 3 Fir'auna zai ce game da Isra'ilawa, 'Su na yawo a cikin ƙasar. Jeji ya rufe bisan su.' 4 Zan taurare zuciyar Fir'auna, kuma zai runtume su. Zan sami girmamawa saboda Fir'auna da dukkan mayaƙansa. Masarawa zasu sani cewa Ni ne Yahweh." Sai Isra'ilawa suka yi sansani kamar yadda aka umarce su. 5 Sa'ad da aka gaya wa sarkin Masar cewa Isra'ilawa sun tsere, sai ra'ayin Fir'auna da bayinsa suka juya gãba da mutanen. Suka ce, "Me muka yi? Mun saki Isra'ila daga bauta ma na?" 6 Daga nan sai Fir'auna ya shiryo karusansa ya kuma ɗauki mayaƙansa tare da shi. 7 Ya ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shidda da dukkan sauran karusan Masar, da shugabanni a bisa dukkansu. 8 Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, sarkin Masar, sarkin kuma ya runtumi Isra'ilawa. Yanzu dai Isra'ilawa sun yi tafiyarsu cikin nasara. 9 Amma Masarawa suka runtume su, tare da dukkan dawakansa da karusai, mahayan dawakansa, da mayaƙansa. Suka sha kan Isra'ilawa da suka yi sansani a gefen teku a gefen Fi Hahirot, kafin Ba'al Zifon. 10 Sa'ad da Fir'auna ya iso kusa, Isra'ilawa suka duba sama suka kuma yi mamaki. Masarawa suna tattaki bayan su, suka kuma firgita. Isra'ilawa suka yi kuka ga Yahweh. 11 Suka ce wa Musa, "Saboda babu kaburbura ne a Masar, shi yasa ka ɗauko mu domin mu mutu a jeji? Meyasa ka yi haka da mu, ka fito da mu daga Masar? 12 Ba wannan muka gaya maka ba a Masar? Muka ce maka, 'Ka ƙyale mu, domin mu yiwa Masarawa aiki.' Ya gwammace mana muyi aiki domin su maimakon mu mutu cikin jeji." 13 Musa ya cewa mutanen, "Kada kuji tsoro. Ku tsaya cik ku kuma ga ceton da Yahweh zai wadata domin ku a yau. Domin ba zaku sake ganin Masarawan da kuka gani ba a yau. 14 Yahweh zai yi yaƙi domin ku, kuma tsayawa kawai za kuyi cik." 15 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Meyasa kai, Musa, ka ke ci gaba da kira a gare ni? Ka gaya wa Isra'ilawa su tafi gaba. 16 Ka ɗaga sandarka, ka miƙa hannunka bisa tekun ka kuma raba ta biyu, saboda mutanen Isra'ila su bi ta tekun bisa busasshiyar ƙasa. 17 Ka sani cewa zan taurare zukatan Masarawa saboda su biyo bayansu. Zan sami daraja saboda Fir'auna da dukkan mayaƙansa, karusansa, da mahaya dawakansa. 18 Daga nan Masarawa zasu sani cewa Ni ne Yahweh sa'ad da Na samo daraja saboda Fir'auna, karusansa, da mahaya dawakansa." 19 Mala'ikan Allah, wanda ya tafi gaban Isra'ilawa, ya matsa ya kuma je bayansu. Inuwar girgijen ta matsa daga gabansu ta kuma koma ta tsaya bayansu. 20 Girgijen ya zo tsakanin sansanin Masar da sansanin Isra'ila. Girgije mai duhu ne ga Masarawa, amma ya haska daren domin Isra'ilawa, sai gefe ɗaya basu zo kusa da ɗayan ba dukkan dare. 21 Musa ya miƙar da hannunsa bisa tekun. Yahweh ya maida tekun baya da babbar iskar gabas dukkan wannan dare ya kuma maida tekun zuwa busasshiyar ƙasa. Ta haka ruwayen suka rabu. 22 Isra'ilawa suka tafi ta cikin teku bisa busasshiyar ƙasa. Ruwayen suka yi katanga domin su a hannun dama da hannun hagu. 23 / Masarawa suka runtume su. Suka tafi bayansu cikin tsakiyar teku - dukkan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahaya dawakai. 24 Amma a sa'o'in farkon safiya, Yahweh ya duba ƙasa bisa mayaƙan Masarawa ta wurin umudin wuta da girgije. Ya sanya firgita tsakanin Masarawa. 25 Keken karusansu suka cije, mahayan dawakan suka yi tuƙi da wahala. Sai masarawa suka ce, "Bari mu tsere daga Isra'ila, gama Yahweh yana yaƙi domin su gãba da mu." 26 Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙar da hannunka bisa tekun domin ruwayen su dawo bisa Masarawa, karusansu, da mahaya dawakansu." 27 Sai Musa ya miƙar da hannunsa bisa tekun, kuma ya koma yadda ya ke da safiya ta bayyana. Masarawa suka tsere cikin teku, Yahweh kuma ya kora Masarawa zuwa cikin tsakiyarsa. 28 Ruwayen suka dawo suka rufe karusan Fir'auna, mahayan dawakai, da dukkan mayaƙansa dasu ka bi karusan zuwa cikin teku. Babu wanda ya tsira. 29 Duk da haka, Isra'ilawa suka yi tafiya bisa busasshiyar ƙasa cikin tsakiyar teku. Ruwayen suka zama katanga domin su a hannun damansu da hagunsu. 30 Sai Yahweh ya ceto Isra'ila a wannan rana daga hannun Masarawa, Isra'ila kuma suka ga matattun Masarawa bisa gaɓar teku. 31 Sa'ad da Isra'ila suka ga babban iko da Yahweh ya yi amfani da shi gãba da Masarawa, mutanen suka girmama Yahweh, suka kuma amince da Yahweh da kuma bawansa Musa.

Sura 15

1 Daga nan Musa da mutanen Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Yahweh. Suka raira, "Zan raira ga Yahweh, gama ya yi ɗaukakakkiyar nasara; doki da mahayinsa ya watsar cikin teku. 2 Yahweh ne ƙarfina da waƙata, ya kuma zama mai cetona. Wannan ne Allahna, kuma zan yabe shi, Allah na mahaifina, zan kuma ɗaukaka shi. 3 Yahweh mayaƙi ne; Yahweh ne sunansa. 4 Ya watsar da karusan Fir'auna da mayaƙansa cikin teku. Zaɓaɓɓun hafsoshin Fir'auna sun nutse cikin Tekun Iwa. 5 Zurfafa sun rufe su; sun tafi ƙasa cikin zurfafa kamar dutse. 6 Hannunka na dama, Yahweh, ɗaukakakke ne cikin iko; hannunka na dama, Yahweh, ya rugurguza maƙiyi. 7 Cikin babban girma ka kayar da waɗanda suka taso gãba da kai. Ka aika da hasalarka; ta cinye su kamar haki. 8 Da hucin kafofin hancinka ruwaye suka jera; ruwayen dake malala suka tsaya tsaye suka yi tsibi; ruwa mai zurfi ya daskare a cikin zuciyar teku. 9 Maƙiyi yace, 'Zan runtuma, zan sha kai, zan rarraba ganima; marmarina zai ƙoshi a kansu; zan zaro takobina; hannuna zai hallakar dasu.' 10 Amma ka busa da iskarka, teku kuma ya rufe su; suka nutse kamar baƙin ƙarfe cikin manyan ruwaye. 11 Wane ne kamar ka, Yahweh, a tsakanin alloli? Wane ne kamar ka, girma cikin tsarki, daraja cikin yabo, mai aikata al'ajibai? 12 Ka miƙa hannun damanka, ƙasa kuma ta haɗiye su. 13 A cikin alƙawarin amincinka ka bida mutanen ka ceto su. A cikin ƙarfinka ka bida su zuwa wuri mai tsarki inda kake zaune. 14 Mutane zasu ji, zasu kuma yi rawar jiki; fargaba zai afko wa mazaunan Filistiya. 15 Daga nan shugabannin Idom zasu ji tsoro; sojojin Mowab zasu girgiza; dukkan mazaunan Kan'ana zasu narke. 16 Tsoro da fargaba zai fãɗo masu. Saboda ikon damtsenka, zasu tsaya cik kamar dutse har sai mutanenka sun wuce, Yahweh - har sai mutanen da ka ceto sun wuce. 17 Za ka kawo su ka dasa su bisa tsaunin gãdonka, wurin da, Yahweh, ka yi domin ka zauna a ciki, wuri mai tsarki, Ubangijinmu, wanda hannuwanka suka gina. 18 Yahwah zai yi mulki har abada abadin." 19 Gama dawakan Fir'auna suka tafi tare da karusansa da mahaya dawakansa cikin teku. Yahweh ya maido da ruwayen teku bisansu. Amma Isra'ilawa suka yi tafiya bisa busasshiyar ƙasa a tsakiyar teku. 20 Miriyam annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kacau-kacau, dukkan mataye kuma suka fita da kacau-kacau, suna rawa tare da ita. 21 Miriyam ta raira masu waƙa: "Ku raira ga Yahweh, domin ya yi ɗaukakakkiyar nasara. Doki da mahayinsa ya jefar cikin teku." 22 Daga nan Musa ya bida Isra'ila gaba daga Tekun Iwa. Suka tafi zuwa cikin jejin Shur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jeji basu kuma sami ruwa ba. 23 Daga nan suka iso Mara, amma basu iya shan ruwan wurin nan ba saboda yana da ɗaci. Sai suka kira sunan wannan wuri Mara. 24 Sai mutanen suka yi gunaguni ga Musa suka kuma ce, "Me zamu sha?" 25 Musa ya yi kuka ga Yahweh, sai Yahweh ya nuna masa wani itace. Musa ya jefa shi cikin ruwan, ruwan kuma ya zama da daɗin sha. A wannan wurin ne Yahweh ya basu shari'a mai tsauri, a wannan wurin ne kuma ya gwada su. 26 Ya ce, "Idan a hankali kuka saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kuma yi abin dake dai-dai a idanunsa, idan kuma kuka kasa kunne ga umarninsa kuka kuma yi biyayya da dukkan shari'unsa - ba zan sanya maku ko ɗaya daga cikin cututtukan dana sanya wa Masarawa ba, gama Ni ne Yahweh dake warkar da ku." 27 Daga nan mutanen suka iso Elim, inda akwai maɓuɓɓugan ruwa sha biyu da itatuwan dabino saba'in. Suka yi sansani a nan bakin ruwa.

Sura 16

1 Mutanen suka kama hanya daga Elim, kuma dukkan taron jama'ar Isra'ila suka iso jejin Sin, wanda ke tsakanin Elim da Sinai, a ranar sha biyar ga watan biyu bayan barowarsu daga ƙasar Masar. 2 Dukkan taron jama'ar Isra'ila suka yi gunaguni gãba da Musa da Haruna a cikin jejin. 3 Isra'ilawa suka ce masu, "Da ma kawai mun mutu ta hannun Yahweh a ƙasar Masar sa'ad da muke zama gefen tukwanen nama muke kuma cin gurasa mu ƙoshi. Domin ka fito da mu cikin wannan jeji ka kashe dukkan taron jama"armu da yunwa." 4 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Zan yi ruwan gurasa daga sama domin ku. Mutanen zasu fita su tattaro ta yini ɗaya kowacce rana saboda in gwada su in gani ko zasu yi ko kuwa ba zasu yi tafiya cikin shari'a ta ba. 5 Za ya kasance a rana ta shida, zasu tattaro riɓi biyu na yawan yadda suke tattarawa kowacce rana a baya, sai kuma su dafa abin da suka ɗebo." 6 Daga nan Musa da Haruna suka cewa dukkan mutanen Isra'ila, "Da maraice zaku sani cewa Yahweh ne ya fito da ku daga ƙasar Masar. 7 Da safe zaku ga ɗaukakar Yahweh, domin ya ji gunaguninku gãba da shi. Mu su wane ne da zaku yi gunaguni gãba da mu?" 8 Musa ya sake cewa, "Zaku san wannan sa'ad da Yahweh ya baku nama da maraice da gurasa da safe ku ƙoshi - domin ya ji gunagunan da kuka furta gãba da shi. Su wane ne Haruna da ni? Gunagunanku ba gãba damu ba ne; gãba da Yahweh ne." 9 Musa ya cewa Haruna, "Ka cewa dukkan taron jama'ar mutanen Isra'ila, 'Ku zo kusa a gaban Yahweh, domin ya ji gunagunanku."' 10 Sai ya kasance, yayin da Haruna yake magana da dukkan taron jama'ar mutanen Isra'ila, sai suka kalli zuwa jeji, kuma, duba, ɗaukakar Yahweh ta bayyana a girgije. 11 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 12 "Na ji gunagunan mutanen Isra'ila. Ka yi magana dasu ka ce, 'Da maraice zaku ci nama, da safe kuma zaku cika da gurasa. Daga nan zaku sani cewa Ni ne Yahweh Allahnku."' 13 Sai ya kasance da maraice makwarwai suka taso suka rufe sansanin. Da safe raɓa ta kwanta kewaye da sansanin. 14 Da raɓar ta tafi, a nan birbishin jejin sai ga wasu falle-falle kamar dusar ƙanƙara a ƙasa. 15 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gan ta, suka ce da juna, "Mene ne wannan?" Ba su san ko mene ne ba. Musa yace masu, "Gurasar da Yahweh ya baku ce ku ci. 16 Wannan ne umarnin da Yahweh ya bayar: 'Tilas ku tattaro, kowannen ku, adadin da kuke buƙata ku ci, awon kowanne taliki bisa ga lissafin mutanenku. Ga yadda zaku tattara ta: Ku tattara isasshe domin ci ga kowanne taliki dake zaune a rumfarku."' 17 Mutanen Isra'ila suka yi haka. Wasu suka tãra da yawa, wasu suka tãra kaɗan. 18 Sa'ad da suka auna da awon gwangwani, waɗanda suka tãra da yawa basu rage komai ba, waɗanda kuma suka tãra kaɗan basu rasa komai ba. Kowanne taliki ya tãra dai-dai da biyan buƙatarsu. 19 Daga nan Musa yace masu, "Dole ba wanda zai bar komai daga cikin ta har safiya." 20 Duk da haka, basu saurari Musa ba. Waɗansu suka rage daga cikin ta har safiya, sai ta haifar da tsutsotsi ta kuma yi wãri. Daga nan Musa ya fusata da su. 21 Suka tattara ta safiya bayan safiya. Kowanne taliki ya tãra isassar wanda zai ci domin wannan ranar. Sa'ad da rana ta yi zafi, ta narke. 22 Sai ya kasance a rana ta shida kowannensu ya tãra riɓi biyu na gurasar, gwangwani biyu domin kowanne taliki. Dukkan shugabannin jama'ar suka zo suka faɗi wa Musa. 23 Ya ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh yace: 'Gobe hutun nadama ne, Asabar mai tsarki cikin girmama Yahweh. Ku gasa abin da kuke so ku gasa, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Duk abin da ya rage, sai ku ajiye shi gefe domin kanku har sai da safe."' 24 Sai suka ajiye ta gefe har sai da safe, kamar yadda Musa ya bada umarni. Ba ta zama da wãri ba, ko kuma a sami wata tsutsa a cikinta. 25 Musa yace, "Ku ci wannan abin cin yau, domin yau rana ce wadda aka keɓe a matsayin Asabaci na girmama Yahweh. Yau ba zaku same ta ba a gonaki. 26 Zaku tattara ta cikin kwanaki shida, amma rana ta bakwai Asabaci ce. A ranar Asabar babu manna." 27 Sai ya kasance a rana ta bakwai waɗansu mutane suka fita su tattaro manna, amma ba su sami komai ba. 28 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Har yaushe zaku ƙi kiyaye umarnai na da shari'u na? 29 Duba, Yahweh ya baku Asabaci. Don haka a rana ta shida yana baku gurasa domin kwanaki biyu. Kowannen ku tilas ya tsaya a wurinsa; tilas babu wanda zai fita daga wurin shi a rana ta bakwai." 30 Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai. 31 Mutanen Isra'ila suka kira wannan abinci "Manna." Ita fara ce kamar tsabar riɗi, ɗanɗanon ta kuma kamar wainar da aka yi da zuma. 32 Musa yace, "Wannan ne Yahweh ya umarta: 'A ajiye gwangwanin manna cikin dukkan tsararrakin mutanenku saboda zuriyarku su ga gurasar dana ciyar da ku a jeji, bayan da na fito daku daga ƙasar Masar."' 33 Musa ya cewa Haruna, "Ka ɗauki tukunya ka sa gwangwani ɗaya na manna a cikin ta. Ka adana ta gaban Yahweh domin a ajiye ta cikin dukkan tsararrakin mutanen." 34 Kamar yadda Yahweh ya umarci Musa, Haruna ya ɓoye ta bayan alƙawarin dokoki a cikin akwatin alƙawari. 35 Mutanen Isra'ila suka ci manna shekaru arba'in har sai da suka zo ƙasar dake da mazauna. Ita suka ci har sai da suka zo kan iyakokin ƙasar Kan'ana. 36 Yanzu dai gwangwanin kashi ɗaya ne cikin goma na mudu.

Sura 17

1 ‌Ɗaukacin taron jama'ar Isra'ilawa suka yi tafiya daga jejin Sin, biye da umarnan Yahweh. Suka yi sansani a Refidim, amma babu ruwa domin mutane su sha. 2 Sai mutanen suka ba Musa laifi saboda halin da suke ciki suka kuma ce, "Ka ba mu ruwa mu sha." Musa yace, "Meyasa kuke faɗa da ni? Meyasa kuke gwada Yahweh?" 3 Mutanen suna jin ƙishi sosai, suka kuma yi gunaguni gãba da Musa. Suka ce, "Meyasa ka fito da mu daga Masar? Don ka kashe mu da 'ya'yanmu da kuma dabbobinmu da ƙishi?" 4 Daga nan Musa ya yi kuka ga Yahweh, "Me zanyi da waɗannan mutanen? Sun kusa shirya jifa na." 5 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi gaba da mutanen, ka tafi kuma tare da wasu dattawan Isra'ila. Ka ɗauki tare da kai sandar daka buga kogi, ka kuma tafi. 6 Zan tsaya a gabanka can a dutsen Horeb, zaka kuma bugi n. Ruwa zai fito daga cikin sa domin mutanen su sha." Daga nan Musa ya yi haka a gaban dattawan Isra'ila. 7 Ya kira wannan wuri Massa da Meriba saboda gunagunin Isra'ilawa, saboda kuma sun gwada Ubangiji ta wurin cewa, "Yahweh yana cikinmu ko a'a?" 8 Daga nan mayaƙan mutanen Amalekawa suka fita suka kuma kai hari ga Isra'ila a Refidim. 9 Sai Musa ya cewa Yoshuwa, "Ka zaɓi wasu mutane ka fita. Ka yi faɗa da Amalekawa. Gobe zan tsaya bisa tudu tare da sandar Allah a hannuna." 10 Sai Yoshuwa ya yi faɗa da Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, yayin da Musa, Haruna, da Hor suka hau saman tudu. 11 Yayin da Musa ke riƙe da hannayensa sama, Isra'ila suna nasara; idan ya sauke hannayensa su huta, sai Amalekawa su fãra yin nasara. 12 Sa'ad da hannayen Musa suka zama da nauyi, Haruna da Hor suka ɗauki dutse suka sanya ƙasansa domin ya zauna a kai. A dai-dai wannan lokaci, Haruna da Hor suka riƙe hannayensa sama, mutum ɗaya a gefensa ɗaya, mutum ɗaya kuma a ɗayan gefensa. Haka aka riƙe hannayen Musa a tallafe har faɗuwar rana. 13 Haka Yoshuwa ya kayar da mutanen Amalekawa da takobi. 14 Yahweh ya cewa Musa, "Ka rubuta wannan cikin littafi ka kuma karanta shi cikin kunnuwan Yoshuwa, saboda da zan share tunawa da Amalekawa kakaf daga ƙarƙashin sammai." 15 Daga nan Musa ya gina bagadi ya kira shi "Yahweh ne tuta ta." 16 Ya ce, "Gama an ɗaga hannu sama zu wa kursiyin Yahweh - cewa Yahweh zai ja dagar yaƙi da Amalekawa daga tsara zuwa tsara."

Sura 18

1 Yetro, firist na Midiyan, surukin Musa, ya ji dukkan abin da Allah ya yi domin Musa domin kuma Isra'ila mutanensa. Ya ji cewa Yahweh ya fito da Isra'ila daga Masar. 2 Yetro, surukin Musa, ya ɗauki Ziffora, matar Musa, bayan da ya tura ta gida, 3 da 'ya'yanta maza biyu; sunan ɗan ɗaya Gashom, domin Musa yace, "Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa." 4 Sunan ɗayan Eliyeza, domin Musa yace, "Allah na kakannina ne taimako na. Ya cece ni daga takobin Fir'auna." 5 Yetro, surukin Musa, ya zo tare da 'ya'yan Musa da matarsa a wurin Musa a cikin jeji inda ya yi sansani a tsaunin Allah. 6 Ya cewa Musa, "Ni, surukinka Yetro, ina zuwa tare da matarka da 'ya'yanta maza biyu." 7 Musa ya tafi domin ya tarbi surukinsa, ya rusuna ƙasa, ya kuma sumbace shi. Suka tambayi lafiyar juna daganan kuma suka tafi cikin rumfa. 8 Musa ya gaya wa surukinsa dukkan abin da Yahweh ya yi wa Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ila, game da dukkan wahalhalun da suka afko masu a kan hanya, da yadda Yahweh ya cece su. 9 Yetro ya yi farinciki game da dukkan nagartar da Yahweh ya yi wa Isra'ila, yadda ya cece su daga hannun Masarawa. 10 Yetro yace, "Bari a yabi Yahweh, domin ya cece ka daga hannun Masarawa daga kuma hannun Fir'auna, ya kuma kuɓutar da mutanen daga hannun Masarawa. 11 Yanzu na sani cewa Yahweh babba ne fiye da dukkan alloli, saboda sa'ad da Masarawa suka wulaƙanta Isra'ilawa da gadara, Allah ya ceci mutanensa." 12 Yetro, surukin Musa, ya kawo baikon ƙonawa da hadayu ga Allah. Haruna da dukkan dattawan Isra'ila suka zo su ci abinci a gaban Allah tare da surukin Musa. 13 Washegari Musa ya zauna domin yi wa mutane hukunci. Mutane suka tsaitsaya kewaye da shi daga safe har yamma. 14 Sa'ad da surukin Musa yaga dukkan abin da ya yi domin mutanen, ya ce, "Mene ne haka kake yi tare da mutanen?" Meyasa kake zaunawa kai kaɗai kuma dukkan mutanen ke tsayawa kewaye da kai daga safe har yamma?" 15 Musa ya cewa surukinsa, "Mutanen suna zuwa wurina ne su tambayi bishewar Allah. 16 Sa'ad da suka sami saɓani, suna zuwa wurina. Ina ɗaukar matsayi tsakanin taliki ɗaya da wani, kuma ina koyar da su farillan Allah da shari'unsa." 17 Surukin Musa yace masa, "Abin da kake yi bai da kyau sosai. 18 Tabbas zaka gajiyar da kanka, kai da mutanen dake tare da kai. Wannan ƙangi ya yi maka nauyi sosai. Ba zaka iya yin shi ba kai kaɗai. 19 Ka saurare ni. Zan baka shawara, kuma Allah zai kasance tare da kai, saboda kai ne a madadin mutane ga Allah, kuma kai ke kawo rikice-rikicensu gare shi. 20 Dole ka koya masu farillansa da shari'unsa. Dole ka nuna masu hanyar da zasu yi tafiya da kuma aikin da zasu yi. 21 Gaba da haka, dole ka zaɓi mutane tsayayyu daga cikin mutanen, mutane masu girmama Allah, mutane masu gaskiya masu ƙin ƙazamar riba. Dole ka sanya su bisa mutane su zama shugabannin dubbai, da ɗarurruka, da hamsin-hamsin, da goma-goma. 22 Za su yi hukunci tsakanin mutane a dukkan al'amuran yau da kullum, amma al'amura masu wuya sai su kawo maka. Game da dukkan ƙananan al'amura kuwa, zasu hukunta waɗannan da kansu. ta wannan hanyar zai yi maka sauƙi, za su kuma ɗauki nauyin tare da kai. 23 Idan ka yi wannan, idan kuma Allah ya umarce ka kayi haka, daganan zaka iya jurewa, kuma dukkan mutanen zasu iya tafiya gida a barace." 24 Sai Musa ya saurari maganganun surukinsa ya kuma yi dukkan abin da ya ce. 25 Musa ya zaɓi tsayayyun mutane daga dukkan Isra'ila ya kuma maida su shugabannin mutanen, shugabanni masu lura da dubbai, da ɗarurruka, da hamsin-hamsin, da goma-goma. 26 Suka hukunta mutane a al'amura masu sauƙi, al'amura masu wuya kuma suka kawo wa Musa, amma su da kansu suka hukunta dukkan ƙananan al'amura. 27 Daga nan Musa ya bar surukinsa ya tafi, Yetro kuma ya koma cikin ƙasarsa.

Sura 19

1 A cikin wata na uku bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar, a wannan ranar, suka zo jejin Sinai. 2 Bayan da suka bar Refidim suka kuma zo jejin Sinai, suka yi sansani a jejin a gaban tsaunin. 3 Musa ya hau zuwa wurin Allah. Yahweh ya kira shi daga tsaunin ya kuma ce, "Tilas ka gaya wa gidan Yakubu, mutanen Israi'la; 4 Kunga yadda na yiwa Masarawa, yadda na ɗauko ku bisa fikafikan gaggafa na kuma kawo ku a gare ni. 5 To yanzu, idan da biyayya kuka saurari muryata kuka kuma kiyaye alƙawarina, daganan zaku zama mallakata ta musamman daga cikin dukkan mutane, domin dukkan duniya tawa ce. 6 Zaku zama masarautar firistoci da al'umma mai tsarki domina. Waɗannan maganganun ne tilas ka faɗe su ga mutanen Isra'ila." 7 Daga nan Musa ya zo ya sammaci shugabannin mutanen. Ya faɗi a gabansu dukkan waɗannan maganganun da Yahweh ya umarce shi. 8 Dukkan mutanen suka amsa tare suka ce, "Za muyi dukkan abin da Yahweh yace." Daga nan Musa ya zo ya kawo rahoton maganganun mutanen ga Yahweh. 9 Yahweh ya cewa Musa, "Zan zo gare ka cikin girgije mai kauri saboda mutanen su iya ji sa'ad da zan yi magana tare da kai, su kuma gaskata da kai har abada." Daga nan Musa ya faɗi maganganun mutanen ga Yahweh. 10 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi wurin mutanen. Yau da gobe Tilas ka keɓe su a gare ni. ka kuma sanya su su wanke tufafinsu. 11 Ku shirya domin rana ta uku, gama a rana ta uku Yahweh zai sauko bisa Tsaunin Sinai. 12 Tilas ka sanya kan iyakoki domin mutanen a dukkan kewayen tsaunin. Ka ce masu, 'Ku kula da cewa baku hau zuwa tsaunin ba koku taɓa kan iyakarsa. Duk wanda ya taɓa tsaunin tabbas za a kashe shi.' 13 Kada hannun wani ya taɓa irin wannan taliki. A maimako, babu shakka tilas za a jefe shi ko a harbe shi. Ko mutum ne ko dabba tilas a kashe shi. Sa'ad da aka busa ƙaho mai dogon amo, suna iya zuwa gindin tsaunin." 14 Daga nan Musa ya tafi ya gangara daga tsaunin zuwa ga mutanen. Ya keɓe mutanen ga Yahweh suka kuma wanke tufafinsu. 15 Ya cewa mutanen, "Ku shirya a rana ta uku; kada ku kusanci matayenku." 16 A rana ta uku, sa'ad da safiya ta yi, aka yi cida da wurge-wurgen walƙiya da girgije mai kauri a bisa tsaunin, da ƙarar kaho mai ƙarfi sosai. Dukkan mutanen dake cikin sansanin suka yi rawar jiki. 17 Musa ya fito da mutanen daga cikin sansanin su gamu da Allah, suka kuma tsaya a gindin tsaunin. 18 Tsaunin Sinai kuwa an lulluɓe shi ɗungum da hayaƙi saboda Yahweh ya sauko bisa kansa cikin wuta da hayaƙi. Hayaƙin kuwa ya yi sama kamar hayaƙin tanderu, tsaunin kuma gabaɗaya ya yi mummunar girgiza. 19 Da ƙarar ƙahon ta ci gaba da ƙaruwa bisa ƙaruwa, Musa ya yi magana, Allah kuma ya amsa masa da murya. 20 Yahweh ya sauko bisa Tsaunin Sinai, bisa ƙololuwar tsaunin, ya kuma sammaci Musa zuwa sama. Sai Musa ya haye sama. 21 Yahweh ya cewa Musa, "Ka gangara ka dokaci mutanen da kada su faso gareni su kalla, ko dayawa daga cikin su su hallaka. 22 Bari firistocin suma dake kusantata su keɓe kansu - su shirya kansu domin zuwa na - saboda kada in kai masu hari." 23 Musa ya cewa Yahweh, "Mutanen ba zasu iya zuwa har Tsaunin Sinai ba, domin ka dokace mu: 'Ku sanya kan iyakoki kewaye da tsaunin ku kuma keɓe shi ga Yahweh."' 24 Yahweh yace masa, "Tafi, ka gangara daga tsaunin, ka kuma kawo Haruna tare da kai, amma kada ka bar firistocin da mutanen su faso shingen su hawo zuwa gare ni, ko in kai masu hari." 25 Sai Musa ya gangara zuwa ga mutanen ya yi magana da su.

Sura 20

1 Allah ya furta dukkan waɗannan maganganu, 2 "Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 3 Tilas ne ba zaku yi wasu alloli ba baya ga ni. 4 Ba zaku yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa ba ko kamannin wani abu dake can cikin sama, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a cikin ruwaye. 5 Dole ne ba zaku rusuna masu ba koku yi masu sujada, gama Ni, Yahweh Allahnku, Allah ne mai kishi. Ina horon muguntar kakanni ta wurin sauko da horo bisa zuriyarsu, har zuwa tsararraki na uku da na huɗu na waɗanda ke ƙi na. 6 Amma ina nu na alƙawarin aminci ga dubban waɗanda ke ƙaunata suke kuma kiyaye dokokina. 7 Dole ne ba zaku ɗauki sunan Yahweh Allahnku ba, a wofi, domin ba zan riƙe shi marar laifi ba duk wanda ya ɗauki sunana a wofi. 8 Ku tuna da ranar Asabaci, ku keɓe ta domina. 9 Dole kuyi aiki tuƙuru ku kuma yi dukkan aikinku a ranaku shida. 10 Amma rana ta bakwai Asabaci ce ga Yahweh Allahnku. A wannan rana baza kuyi wani aiki ba, koku, ko 'ya'yanku maza, ko 'ya'yanku mata, ko bayinku maza, ko bayinku mata, ko garken shanunku, ko baƙon da yake cikin ƙofofinku. 11 Domin a cikin ranaku shida Yahweh ya yi sammai da duniya, da teku, da dukkan abin dake cikin su, sai kuma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Yahweh ya albarkaci ranar Asabaci ya kuma keɓe ta. 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, saboda ka rayu na dogon lokaci a cikin ƙasar da Yahweh Allahnka yake baka. 13 Tilas ba zaka kashe kowa ba. 14 Tilas ba zaka yi zina ba. 15 Tilas ne ba zaka yi sata ba daga wani. 16 Tilas ne ba zaka bada shaidar ƙarya ba gãba da maƙwabcinka. 17 Tilas ne ba zaka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba; tilas ne ba zaka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, bawansa namiji, baiwarsa mace, sansa, jakinsa, ko dukkan wani abu dake na maƙwabcinka." 18 Dukkan mutanen suka ga cidar da walƙiyar, suka kuma ji muryar ƙahon, suka kuma ga tsaunin na hayaƙi. Sa'ad da mutanen suka ga haka, suka firgice suka kuma tsaya daga nesa. 19 Suka cewa Musa, "Ka yi magana da mu, zamu kuma saurara; amma kada ka bari Allah ya yi magana da mu, ko kuwa za mu mutu." 20 Musa ya cewa Mutanen, "Kada kuji tsoro, domin Allah ya zo ya gwada ku saboda girmamawarsa ya kasance cikin ku, saboda kuma kada kuyi zunubi." 21 Sai mutanen suka tsaya nesa, Musa kuma ya kusanci duhun mai kauri inda Allah ya ke. 22 Yahweh ya cewa Musa, "Wannan ne tilas ka gayawa Isra'ilawa: 'Ku da kanku kunga cewa nayi magana da ku daga sama. 23 Kada ku yiwa kanku wasu alloli tare da ni, allolin azurfa ko allolin zinariya. 24 Tilas ku gina mani bagadin ƙasa, dole kuma ku yi hadayar baye-baye na ƙonawa a kansa, baye-baye na zumunta, tumaki, da shanu. A cikin dukkan inda nasa a girmama sunana, zan zo gare ku in albarkace ku. 25 Idan kuka yi mani bagadin dutse, ba zaku gina shi ba da dutsen da aka yanko, domin idan kuka yi amfani da kayan aikinku a kansa, kun riga kun gurɓata shi. 26 Tilas ne ba za ku hau bisa bagadina ta matakala ba, saboda kada tsirancinku ya bayyana."'

Sura 21

1 To waɗannan su ne sharuɗan da zaka sa a gabansu: 2 Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a ta bakwai zai tafi 'yantacce ba tare da ya biya kome ba. 3 Idan shi kaɗai ya zo, sai ya tafi shi kaɗai, idan kuma ya zo da mata, zata zama 'yantarta ta tafi tare da shi. 4 Idan ubangijinsa ne ya yi masa aure, da matar da 'ya'yanta zasu zama na ubangijinsa, shi kuwa zai zama 'yantacce ya tafi shi kaɗai. 5 Amma idan bawan da kansa ya ce, "Ina ƙaunar ubangijina da matata da 'ya'yana; ba zan zama 'yantacce in tafi ba," 6 Dole ubangijinsa ya kawo shi wurin Yahweh, dole ubangijinsa zai kawo shi ƙofa ko bakin ƙofa, kuma dole ubangijinsa zai huda kunnensa da allura. Daga nan zai zama bawa har iyakar rayuwarsa. 7 Idan mutum ya sayar da ɗiyarsa mace ta zama baiwa, ba zata tafi haka nan kamar yadda bayi maza suke yi ba. 8 Idan ba ta gamshi ubangijinta wanda ya ajiye ta domin kansa ba, to dole ne a fanshe ta. Ba zai sayar da ita ga waɗan su baƙin mutane ba. Ba shi da wannan damar saboda ya yaudare ta. 9 Idan ubangijinta ya bada ita ga ɗansa ta zama matarsa, sai ya ɗauke ta kamar ɗiyarsa. 10 Idan ya ɗauko wata matar, kada ya hana ta abinci ko tufafi ko kuwa 'yancinta na aure. 11 Amma idan bai ba ta waɗannan abubuwa uku ba, to sai ta tafi a matsayin 'yantarta, ba tare da ta biya wasu kuɗi ba. 12 Ko wane ne ya doki wani mutum har ya mutu, shima sai a kashe shi. 13 Idan mutumin bada manufa ya yi ba, amma ya yi da kuskure ne, zan tanada wurin da zai gudu. 14 Idan wani mutum ya kaiwa maƙwabcinsa hari, ya yaudare shi har ya kashe shi, zaka ɗauke shi, koda yana kan bagadin Yahweh, domin a kashe shi. 15 Dukkan wanda ya doki mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole za a kashe shi. 16 Dukkan wanda ya yi garkuwa da mutum - ko wanda ya yi garkuwa da mutumin ya sayar da shi, ko kuwa an same shi a hannun mai garkuwar - dole ne a kashe mai yin garkuwar. 17 Dukkan wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole za a kashe shi. 18 Idan mutane suka yi faɗa, ɗaya ya bugi ɗayan da dutse ko ya naushe shi, kuma mutumin bai mutu ba, amma ya kwanta saboda dukan da ya yi masa; 19 idan mutumin ya samu ya tashi, har yana tafiya yana dogara sanda, shi wanda ya doke shi zai biya shi diyyar lokacin da ya ɓata; dole mutumin ya biya kuɗin jinyar sa har ya warke. Amma mutumin bai tserewa laifin kisan kai ba. 20 Idan mutum ya doki bawansa ko baiwarsa da sanda, har bawan ya mutu sanadiyar wannan duka, dole ne za a hori mutumin. Duk da haka, 21 idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, ba za a hori mutumin ba, saboda ya sha wuyar rashin bawansa. 22 Idan mutane suka yi faɗa suka yi wa mace mai ciki rauni, har ta yi ɓari amma ba wani rauni a jikinta, mai laifin zai biya tara yadda mijinta ya bukata, dole ya biya abin da alƙali ya ce ya biya. 23 Amma idan akwai rauni mai muni, sai a bada rai maimakon rai, 24 ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙiri, hannu naimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa, 25 ƙuna maimakon ƙuna, rauni maimakon rauni, ƙujewa maimakon ƙujewa. 26 Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya mutu, bawan zai zama 'yantacce ya tafi maimakon idonsa ko idonta. 27 Idan ya buge wa bawansa ko baiwarsa haƙori har ya cire, bawan ko baiwar zai zama 'yantacce ya tafi maimakon haƙorinsa ko haƙorinta. 28 Idan să ya soki mutum namiji ko mace har ya mutu, dole za a jejjefe san, kuma ba za a ci namansa ba; amma mai san zai zama baratacce. 29 Amma idan san ya kan soki mutane dama, kuma an yi wa mai san gargaɗi bai kuwa ɗaure san ba, idan san ya soki wani mutum ko wata mace har ga mutuwa, za a jejjefe san, mai san ɗin shima za a kashe shi. 30 Idan kuwa an ce a biya diyya domin ransa, to, dukkan abin da aka bukata a biya haka zai biya. 31 Idan san ya soki ɗan wani ko ɗiyar wani, mai san zai yi kamar yadda wannan ka'ida ta bukaci ya yi. 32 Idan san ya soki bawan wani mutum na miji ko mace, mai san zai biya azurfa talatin, san kuma za a jejjefe shi. 33 Idan mutum ya buɗe rami ko ya gina rami bai rufe shi ba, idan să ko jaki ya faɗa cikin sa, 34 wanda ya yi ramin zai biya diyya. Dole zai biya mai dabbar kuɗi, matacciyar dabbar kuma za ta zama asararsa. 35 Idan san wani ya yi wa san wani rauni har ya mutu, za a sayar da san mai rai sai su raba kuɗin, su kuma raba san wanda ya mutu. 36 Amma idan dama san ya saba yin haka, kuma an yiwa mai san gargaɗi amma bai ɗaure sansa ba, zai biya să maimakon să matacciyar dabbar kuma za ta zama ta sa.

Sura 22

1 Idan mutum ya saci bijimi ko tinkiya, ya kashe ko ya sayar, zai biya da bijimai biyar a kan bijimi ɗaya, ko tinkiya huɗu a kan tinkiya ɗaya. 2 Idan aka kama ɓarawo yana fasa gida, aka buge shi har ya mutu, ba za a kama kowa da laifin kisan kai a kansa ba. 3 Amma idan rana ta fito kamin ya fasa ya shiga, za a kama wanda ya kashe shi da laifin kisan kai. Dole ɓarawo ya biya diyya. Idan kuwa ba shi da komi, sai a sayar da shi saboda satar sa. 4 Idan an sami dabbar da ya sata a wurin sa, ko bijimi ne ko jaki ko tinkiya, dole ya biya riɓi biyu na abin da ya sata. 5 Idan mutum yana kiwo, ya bar dabbarsa ta kwance ta yi kiwo a gonar wani, dole ya biya diyya daga gonarsa mafi kyau ko daga garkarsa mafi kyau. 6 Idan wuta ta ƙwace ta shiga cikin ƙayoyi har ta tarar da hatsi, ko an girbe ko kuwa yana tsaye har ta cinye gonar, dole wanda ya kunna wutar ya biya diyya. 7 Idan mutum ya ba maƙwabcinsa ajiyar kuɗi ko kaya, sai aka sace abin a gidansa, idan aka kama ɓarawon dole zai biya diyyar abin da ya sata riɓi biyu. 8 Amma idan ba a kama ɓarawon ba, sai mai gidan ya zo wurin alƙali a gani ko ya ɗauki wani abu cikin kayan maƙwabcinsa. 9 Gama kowacce jayayya game da wani abu, ko bijimi ko jaki ko tinkiya ko kayan sawa, ko kowanne abin da ya ɓace wani ya ce, "Wannan nawa ne," dole a zo wurin alƙali da masu jayayyar. Wanda a ka samu da laifi zai biya maƙwabcinsa diyya riɓi biyu. 10 Idan mutum ya ba maƙwabcinsa ajiyar jaki ko bijimi ko tinkiya ko kowacce irin dabba, sai ta mutu ko aka ji mata rauni ko aka ɗauke ta ba wanda ya gan ta, 11 dole su biyun suyi rantsuwa domin a gane wani bai ɗauki kayan maƙwabcinsa ba. Sai mai abin ya yarda da haka kuma ɗayan ba zai biya diyya ba. 12 Amma idan sacewa aka yi, sai mutumin ya biya diyya ga mai shi. 13 Idan kuma an yayyaga dabbar ne, sai mutumin ya kawo dabbar shaida. Ba zai biya dabbar da aka yayyaga ba. 14 Idan mutum ya yi aron dabba a wurin maƙwabcinsa, sai aka yi wa dabbar rauni ko ta mutu ba a wurin mai ita ba, dole ɗaya mutumin ya biya diyya. 15 Amma idan dabbar tana wurin mai ita, ɗaya mutumin ba zai biya ba; idan hayar dabbar aka yi sai a biya kuɗin hayar. 16 Idan mutum ya ruɗi budurwa wadda ba a yi riƙon ta ba, har ya kwana da ita, dole yasa ta zama matarsa ta wurin biyan dukiya yadda aka bukaci ya biya. 17 Idan mahaifinta ya ƙi ba shi ita, to dole ya biya dukiya dai-dai da ta budurwa. 18 Dole ne ba zaka bar mayya ta rayu ba. 19 Dukkan wanda ya kwana da dabba dole za a kashe shi. 20 Dukkan wanda ya yi hadaya ga wani allah in ba Yahweh ba dole za a hallaka shi. 21 Dole ne ba zaku yi wa baƙo laifi ba ko kuwa ku ƙware shi, domin dă ku baƙi ne a Masar. 22 Kada ka wulaƙanta gwauruwa ko maraya. 23 Idan ka ƙware su, suka yi kira gare ni, babu shakka zan ji kiran su. 24 Fushina zai yi, ƙuna kuma zan kashe ka da kaifin takobi; matanka zasu zama gwauraye, 'ya'yanka kuma su zama marayu. 25 Idan ka bada rancen kuɗi cikin mutanena matalauta, kada ka zama kamar mai bada kuɗi da ruwa, ba zaka sa riba ba. 26 Idan ka karɓi rigar maƙwabcinka da alƙawari, dole ka dawo masa da ita kafin rana ta faɗi, 27 gama ita kaɗai ce abin rufarsa; ita ce rigar da zai sa jikinsa. Da me zai rufa? Sa'ad da ya kira gare ni, zan ji kiransa gama ni mai tausayi ne. 28 Kada ka yi mani saɓo, Allah, ko ka zagi mai mulkin mutanenka. 29 Kada ku hana baye-baye daga amfanin gonarku ko ruwan inabinku. Dole ku bani nunar fari ta 'ya'yanku. 30 Dole kuma ku yi haka da bijimanku da tumakinku. Gama kwana bakwai za su yi da iyayensu, a rana ta takwas za ku bada su gare ni. 31 Za ku zama mutane keɓaɓɓu gare ni. Kada ku ci kowanne abin da naman daji ya kashe a gona. Sai dai, ku jefa wa karnuka shi.

Sura 23

1 Kada ku ba da shaidar ƙarya game da wani. Kada ku haɗa kai da mai mugunta ku zama maƙaryatan shaidu. 2 Kada ku bi rububi domin ku yi mugunta, ko ku goyi bayan rububi ku yi shaida domin ku ɓata adalci. 3 Kada ku nuna wa matalauci fifiko idan a na yi ma sa shari'a ko kaɗan. 4 Idan ka gamu da bijimin maƙiyinka ko jakinsa ya ɓace, dole ka dawo masa da shi. 5 Idan ka ga jakin wanda yake ƙin ka ya faɗi, kaya ya danne shi, kada ka bar shi shi kaɗai. Dole ka taimake shi ka tada jakinsa. 6 Kada ka yar da adalci gefe sa'ad da ake yi wa matalaucinka shari'a. 7 Kada ka haɗa kai da waɗan su ku yi zargi a kan ƙarya, kada ku kashe marar laifi ko mai adalci, gama ba zan 'yantar da mai mugunta ba. 8 Kada ku karɓi toshi ko kaɗan, gama toshi ya kan sa masu gani su makance, ya hana maganar masu aminci aiki. 9 Kada ku cuci baƙo, da yake ka san rayuwar baƙo, gama da kuma baƙi ne a Masar. 10 Shekaru shida za ka shuka iri a gonakinka ka sami amfaninsa. 11 Amma a shekara ta bakwai za ka bar ta ba za ka noma ba, domin matalauta na cikin ku su ci abinci. Abin da suka rage namun daji za su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku da garkunan inabinku. 12 Cikin kwanaki shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai dole za ku huta. Ku yi haka domin bijimanku da jakinku su huta, domin 'ya'yan bayinka da kowanne baƙo ya huta ya wartsake. 13 Ku yi lura da dukkan abin da na gaya maka. Kada ku ambaci sunayen waɗansu alloli, ko ku bari a ji sunayensu daga bakinku. 14 Dole ku je ku yi mani biki sau uku a kowacce shekara. 15 Za ku yi bikin gurasa marar gami. Kamar yadda na umurce ku, za ku ci gurasa marar gami kwana bakwai. A wannan lokaci, za ku zo gabana a watan Abib, wanda aka tsaida domin yin haka. A cikin wannan wata ne kuka fito daga Masar. Amma kada ku zo gabana hannu wofi. 16 Dole za ku yi Bikin Kaka, na nunar fari na irin da kuka shuka a gonakinku. Kuma dole ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa'ad da kuka tattara amfanin gonakinku gida. 17 Dole mazajenku dukka su zo gaban Ubangiji Yahweh sau uku a shekara 18 Dole ba za ku miƙa mani jinin hadayunku da gurasa wadda take da gami ba. Kitsen hadayun idodina ba zai wuce dukkan dare ya kai safiya ba. 19 Dole ku kawo zaɓaɓɓar nunar fari na gonakinku gidana, gidan Yahweh Allahnka. Ba za ka dafa 'yar burguma mai shan nonon uwarta ba. 20 Zan aiko da mala'ika ya yi maku jagora a kan hanya, ya kawo ku wurin da na shirya. 21 Ku saurare shi ku yi masa biyayya. Kada ku cakune shi domin ba zai gafarta laifofinku ba. Sunana yana kansa. 22 Idan kuka yi biyayya da muryarsa kuka yi dukkan abin da na faɗa maku, zan zama maƙiyi ga maƙiyanku in tayar wa masu tayar maku. 23 Mala'ikana zai shiga gabanku ya kawo ku wurin Amoriyawa da Hittiyawa da Firizziyawa da Kan'aniyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa. Zan hallaka su. 24 Kada ku rusuna wa allolinsu, ku yi masu sujada, ko ku yi kamar yadda suke yi. Maimakon haka, dole ku kaɓantar da su dukka, ku ragargaza ginshiƙan duwatsunsu rugu--rugu. 25 Dole Yahweh Allahnku za ku yiwa sujada, kuma zai albarkaci gurasarku da ruwanku. Zan kawar da ciwo daga cikin ku. 26 Ba matar da za ta zama bakarariya ko ta yi ɓarin jariri a ƙasarku. Zan baku tsawancin kwana. 27 Zan sa tsoro a cikin waɗanda kuke shiga ƙasarsu. Zan kashe dukkan mutanen da kuka gamu da su. Zan sa dukkan maƙiyanku su juya maku baya a wurin yaƙi. 28 Zan aiko da zirnaƙo ya kori Hibiyawa da Kan'aniyawa da Hittiyawa daga gabanku. 29 Ba zan kore su a cikin shekara ɗaya ba domin kada ƙasar ta zama ba kowa, kada namun daji su yi maku yawa ƙwarai. 30 Maimakon haka zan kore su da kaɗan-kaɗan har ku yi yawa ku gaji ƙasar. 31 Zan sa iyakokinku daga Tekun Iwa zuwa Tekun Filistiyawa, kuma daga jejin Kogin Yuferatis. Zan baku nasara a kan dukkan mazunan ƙasar. Za ku kore su daga gabanku. 32 Kada ku yi amana da su koda allolinsu. 33 Kada su zauna a ƙasarku, domin kada su sa ku yi zunubi a gare ni. Idan kuka yi sujada ga allolinsu, babu shakka zai zama tarko a gare ku."'

Sura 24

1 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Ku hawo wuri na-kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila, ku yi mani sujada daga nesa. 2 Musa kaɗai ne zai zo kusa da ni. Sauran ba zasu zo kusa ba, mutanen ba zasu hawo tare da shi ba." 3 Musa ya je ya faɗa wa mutanen Isra'ila dukkan maganganun Yahweh da farillai. Dukkan mutanen suka amsa da murya ɗaya suka ce, "Za mu yi dukkan abin da Yahweh yace," 4 Sa'an nan Musa ya rubuta dukkan maganganun Yahweh. Tun da sassafe, Musa ya gina bagadi a kusa da tsaunin ya shirya duwatsu goma sha biyu, domin duwatsun goma sha biyu su zama a madadin kabilu goma sha biyu na Isra'ila. 5 Ya aiki waɗansu samarin Isra'ila su miƙa baye-baye na ƙonawa da hadaya ta baye-bayen zumunta na bijimai ga Yahweh. 6 Musa ya ɗauki rabin jinin ya sa cikin darurruka; ya yayyafa sauran rabin a bisa bagadin. 7 Ya ɗauki littafin Alƙawarin ya karanta shi da murya ga mutanen. Suka ce, "Za mu yi dukkan abin da Yahweh ya faɗi. Za mu zama masu biyayya." 8 Sa'an nan Musa ya ɗauki jinin ya yayyafa shi a kan mutanen. Ya ce, "Wannan shi ne jinin alƙawarin da Yahweh ya yi daku sa'ad da ya baku alƙawari da dukkan waɗannan maganganun." 9 Sa'an nan Musa da Haruna da Nadab da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila suka hau bisa tsaunin. 10 Suka ga Yahweh na Isra'ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa a kwai wani dakali wanda aka yi kamar da n safire, yana sheƙi kamar sararin sama. 11 Yahweh bai ɗora hannu don fushi a kan dattawan Isra'ila ba. Suka ga Yahweh, suka ci suka sha. 12 Yahweh yace da Musa, "Ka hawo wurina a kan tsaunin ka tsaya a can. Zan baka alluna na dutse da doka da dokokin da na rubuta, domin ka koya masu." 13 Sai Musa ya shirya, shi da mataimakinsa Yoshuwa suka hau tsaunin Yahweh. 14 Musa yace da dattawan, "Ku tsaya nan ku jira har sai mun dawo wurin ku. Haruna da Hor suna tare da ku. Idan wani yana da damuwa, ya je wurin su." 15 To sai Musa ya hau tsaunin, girgije ya rufe tsaunin. 16 Darajar Yahweh ta sauko a kan Tsaunin Sinai, girgije ya rufe shi har kwana shida. A rana ta bakwai ya kira Musa daga cikin girgijen. 17 Baiyanuwar darajar Yahweh ta yi kama da wuta mai ci a idanun Isra'ilawa a kan tsaunin. 18 Musa ya shiga cikin girgijen ya hau kan tsaunin. Yana can kan tsaunin har kwana arba'in da yini arba'in.

Sura 25

1 Yahweh yace da Musa, 2 "Ka ce da Isra'ilawa, duk mutumin da ya ji yana da niyya a zuciyarsa ya kawo mani baiko. Sai ka karɓi waɗannan baye-baye domi na. 3 Ga baye-bayen da za ka karɓa daga wurin su: zinariya, da azurfa, da tagulla; 4 da shuɗi, da shunayya, da jăn kaya; da leshe mai kyau; da gashin awaki; 5 da fatar rago da aka yiwa jan rini da fatar ragon ruwa; da itacen ƙirya; 6 da mai domin fitilu na haikali; da kayan yaji saboda mai na shafewa da turare mai ƙanshi da duwatsun 7 oniks da sauran duwatsu masu daraja da za a manna a alkyabba da ɗamara ta ƙirji. 8 Sai su yi mani haikali domin in zauna a cikin su. 9 Sai ka yi dai-dai yadda zan nuna maka tsarinsa da dukkan kayayyakinsa. 10 Za su yi akwati na itacen ƙirya. Ratarsa za ta zama kamu biyu da rabi; faɗinsa zai zama kamu ɗaya da rabi; tsayinsa zai zama kamu ɗaya da rabi. 11 Sai ka shafe shi da zinariya tsantsa ciki da waje, dole ka kewaye shi da rawanin zinariya a bisansa. 12 Sai ka yi ƙawanyu huɗu na zubi da zinariya domin sa, kasa su a ƙafafu huɗu na akwatin, da ƙawanyoyi biyu a ɗaya gefen. 13 Sai ka yi sanduna na itacen ƙirya ka shafe su da zinariya. 14 Sai kasa sandunan a cikin ƙawanyoyi na gefen akwatin alƙawarin, yadda za a iya ɗaukar sa. 15 Za a bar sandunan jikin akwatin; kada a cire su. 16 Sai ka sa ka'idodi na alƙawarin da zan baka a cikin akwatin. 17 Sai ka yi marfi na zinariya tsantsa. Ratarsa za ta zama kamu biyu da rabi, faɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18 Sai ka yi sifofi biyu na kerubim da gogaggiyar zinariya saboda gefe biyu na marfin kafara. 19 Ka yi kerub ɗaya saboda gefe ɗaya na marfin kafara, ɗaya kerub ɗin kuma saboda ɗaya gefen. Za ka yi su dai-dai kamar abu ɗaya da marfin kafara. 20 Fukafukan kerubobin su miƙe tsaye su yi sama su yiwa marfin kafara inuwa. Kerubobin su dubi juna su kalli tsakiyar marfin kafara. 21 Sai ka sa marfin kafara a kan akwatin, kuma kasa ka'idodi na alƙawari da zan ba ka a ciki. 22 A wurin akwatin ne zan sadu da kai. Zan yi magana da kai a inda nake a bisa marfin kafara. Zai zama daga tsakanin kerubobin biyu a bisa akwatin na shaida zan yi magana da kai game da dukkan ka'idodi da zan baka domin Isra'lawa. 23 Sai ka yi teburi na itacen ƙirya. Ratarsa za ta zama kamu biyu; faɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa zai zama kamu ɗaya da rabi. 24 Sai ka shafe shi da zinariya tsantsa ka yi masa ado da dajiya ta zinariya a sama kewaye da shi. 25 Sai kayi dajiya ta kewaye shi mai faɗin tafin hannu ɗaya, ka kuma yiwa bakinsa ado da bugaggen zinariya. 26 Sai ka yi masa ƙawanyoyi na zinariya guda huɗu ka liƙa ƙawanyoyin a kusurwoyinsa huɗu, inda ƙafafun nan huɗu suke. 27 Sai ka liƙa ƙawanyoyin a wuri domin sandunan, yadda za a iya ɗaukar teburin. 28 Sai ka yi sandunan da itacen ƙirya ka shafe su da zinariya domin a iya ɗaukar teburin tare da su. 29 Sai ka yi tasoshinsa da cokulansa da butocinsa da akusoshinsa domin zuba baye-baye na sha. Sai ka yi su da zinariya zalla. 30 Za ka riƙa ɗora gurasa ta kasancewa a bisa teburin a gabana. 31 Sai ka yi wurin ɗora fitila da gogaggiyar zinariya. Wurin ɗora fitilar za kayi da wurin zamansa. Kofinansa da leɓunansa da furanninsa za kayi su tare kamar abu ɗaya. 32 Rassa shida za su fito daga gefunansa-rassa uku daga gefe ɗaya, rassa uku kuma na wurin ɗora fitilar su zarce a ɗaya gefen. 33 Reshe na farko zai zama da kofuna uku kamar an yi su da lingaɓin itacen almond, da baki mai kamar ganye da fure, kofuna uku kuma an yi su kamar lingaɓin itacen almond a ɗaya reshen, da baki kamar ganye da fure. Dukkan su shida za su zama dai-dai da juna, su zarce daga abin ɗora fitilar. 34 A kan abin ɗora fitilar kansa, a tsakiyarsa, zai kasance da kofuna huɗu masu kama da lingaɓin itacen almond, da kamannin ganye da furanni. 35 Tagwayen rassa biyu na farko za su zama da baki kamar ganye-an yi su tare kamar abu ɗaya, tagwayen rassa na biyu kuma an yi su da kamar ganye abu ɗaya tare. Haka kuma tagwayen rassa na uku za a yi su da kamannin ganye sai ka ce abu ɗaya. Haka dukkan rassan shida za su zama su zarce wurin ɗora fitilar. 36 Bakunansu masu kama da ganye za su zama abu ɗaya, an yi shi da bugaggiyen aikin curin zinariya tsantsa. 37 Za ka yi abin ɗora fitilar da fitulunsa guda bakwai, kasa fitilun a bisansa domin su bada haske daga wurinsa. 38 Hantsukan da tasoshin a yi su da zinariya tsantsa. 39 A yi amfani da awo ɗaya na zinariya a yi wurin ɗora fitilar da kayayyakinsa. 40 Ka tabbata ka yi su kamar yadda aka nuna maka a kan tsaunin.

Sura 26

1 Rumfar taruwa kuma za ka yi ta da labule goma da aka yi su da lilin mai kyau da shuɗi da shunayya da jan ulu mai zanen cerubim. Wanda gwanin mai aikin hannu ya yi. 2 Tsawon kowanne labule zai zama kamu ashirin da takwas, faɗi kuma kamu huɗu. Labulen dukkan su su kasance girmansu ɗaya. 3 Labule biyar su zama haɗe da juna, sauran biyar kuma su zama haɗe da juna. 4 Kashi ɗaya na labulen za ka yi masa abin ratayewa na shuɗi daga ƙarshensa. Kashi na biyu ma haka za ka yi masu daga ƙarshe. 5 Kashi na farko za ka yi masu wurin ratayewa hamsin, kashi na biyu ma za ka yi masu wurin ratayewa hamsin. Ka yi haka domin wurin ratayewar labulen su dubi junansu. 6 Sai ka yi kayan adon labule na zinariya guda hamsin ka haɗa labulen tare da juna domin rumfar sujadar ta zama a haɗe. 7 Za ka yi labule na gashin awaki domin rumfa ta bisan rumfar sujada. Za ka yi labule guda goma sha ɗaya. 8 Tsawon kowanne labule zai zama kamu talatin, faɗin kowanne labule kuma kamu huɗu. Labulen nan goma sha ɗaya girmansu ya zama ɗaya. 9 Labule biyar sai ka haɗa su da juna sauran shida kuma ka haɗa su da juna. Sai ka gwama labule na shida wanda yake a gaban rumfar. 10 Sai ka yi maratayi hamsin a gefen labule jeri na farko, maratayi hamsin kuma a gefen labulen da ya haɗa jeri na biyu. 11 Sai ka yi abin maƙalawa hamsin na tagulla ka sa su a maratayin. Sa'an nan ka haɗa rumfar tare ta zama abu ɗaya. 12 Rabin labulen da ya rage, wato wanda ya zarce ya ragu daga labulen rumfar, sai ka bar shi yana lilo a bayan rumfar sujada. 13 Zai zama kamu ɗaya na labulen a gefe ɗaya, kamu ɗaya kuma na labulen a ɗaya gafen-wato abin da ya ragu na labulen rumfar a bar shi ya na lilo a gefen rumfar sujada a sashi ɗaya domin ya rufe ta. 14 Sai ka yi wa rumfar sujadar abin rufewa da fatun rago waɗanda a ka jeme mai rinin jă, wani marfin kuma na fata mai kyau ka sa ya rufe wannan. 15 Sai ka yi wa rumfar sujadar diraku na itacen ƙirya a kafa su a tsaye. 16 Ratar kowacce dirka zai zama kamu goma, faɗin ta kuma kamu ɗaya da rabi. 17 Sai a yi wa dirakun turaka biyu na katako domin su haɗa su da juna. Haka za ka yi dukkan dirakun rumfar sujada. 18 Sa'ad da ka yi dirakun rumfar sujadar, sai ka yi guda ashirin saboda sashi na kudu. 19 Sai ka yi darurruka arba'in na azurfa a ƙarƙashin dirakun nan ashirin. Darurruka biyu za su zama matashin dirka ta farko, darurruka biyu kuma za su zama matashin dirakun guda biyu. 20 Sashi na biyu na rumfar sujada, wato daga arewa, za ka yi masa diraku ashirin 21 da darurrukansu guda arba'in na azurfa. Dirka ta farko za ta kasance da darurruka biyu, biyu kuma a ta gaba, har a gama su dukka. 22 Bayan rumfar sujada kuma daga sashin yamma, sai ka yi ma sa diraku shida. 23 Sai ka yi diraku biyu saboda kusurwar rumfar sujada ta baya. 24 Waɗannan dirakun ba za a haɗa su daga ƙasa ba, amma daga sama za a haɗa su da ƙawanya ɗaya. Haka kusurwoyi biyu na baya za su zama. 25 Za su zama diraku takwas, tare da darurrukansu na azurfa. Za a sami darurruka goma sha shida, darurruka biyu a ƙarƙashin dirka ta farko, darurruka biyu kuma a ta gaba, har a gama. 26 Dole ka shirya katakai da zasu gitta da itacen ƙirya-biyar saboda sashi ɗaya na dirakun rumfar sujada, 27 katakai biyar na gittawa kuma saboda ɗaya sashin na dirakun rumfar sujada, katakai biyar na gittawa kuma saboda dirakun sashin rumfar sujada na baya wajan yamma. 28 Katakon da yake tsakiyar dirakun, zai kai daga wannan ƙarshe zuwa wancan ƙarshen. 29 Sai ka shafe dirakun da zinariya. Za kuma ka yi zobbansu da zinariya, domin su riƙe katakan da aka gitta, na gittawar ma za ka shafe su da zinariya. 30 Dole ka tsara rumfar sujada ta wurin bin yadda aka nuna maka a kan tsaunin. 31 Sai ka kayi labule na shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da leshe mai kyau da zanen kerubim, wanda ƙwararren mai aikin hannu zai yi. 32 Sai dole ka rataye shi a kan ginshiƙai na itacen ƙirya shafaffu da zinariya. Waɗannan ginshiƙai za a yi ma su ƙugiyoyi na zinariya a kan darurruka huɗu na azurfa. 33 Sai kuma dole ka sa labulen a wurin ratayewarsa, sai kuma ka kawo akwatin a ciki. Labulen zai raba tsakanin wuri mai tsarki da wuri mafi tsarki. 34 Sai kasa marfi na kafara a bisa akwatin shaida, wanda yake a cikin wuri mafi tsarki. Sai kasa teburin a waje daga labulen. 35 Sai kasa wurin ɗora fitilar ya dubi teburin daga sashin kudu na rumfar sujada. Teburin ya kasance daga sashin arewa. 36 Sai kuma dole ka yi maratayi a ƙofar shiga rumfar. Sai kuma dole ka yi shi da shuɗi, da shunayya, da jan ƙyalle, da leshe mai kyau, murɗaɗɗe wanda mai iya zane a kan tufa ya yi. 37 Wurin ratayewar za ka yi masa ginshiƙai biyar na ƙirya shafaffu da zinariya. Ƙugiyoyinsu su zama na zinariya, ka yi darurruka biyar na zubi da tagulla.

Sura 27

1 Sai ka yi bagadi na itacen ƙirya, ratarsa kamu biyar faɗinsa ma kamu biyar. Bagadin zai kasance kamu dai-dai kowanne gefe da tsawonsa kamu uku. 2 Za ka sa kusurwoyinsa su zarce da kamannin ƙahonin bijimi. Bagadin da ƙahonin za su zama tare kamar abu ɗaya, zaka shafe su da tagulla. 3 Za ka yi kayan aiki domin bagadin: wato tukunya saboda zuba toka da kuma cebur da darori da cokulan tsamo nama da kasake na tuya. Dukkan waɗannan kayan aikin za kayi su da tagulla. 4 Za ka yiwa bagadin makari na tagulla da răgă. Za ka yi zobba na tagulla guda huɗu domin kowacce kusurwa. 5 Za ka sa makarin ƙasa da bagadin, ya kai rabin sa daga ƙasa. 6 Za ka yiwa bagadin sanduna na itacen ƙirya, ka shafe su da tagulla. 7 Sandunan za ka sa su shiga cikin zobban, a sassa biyu na bagadin, domin a iya ɗaukar sa. 8 Za kayi bagadin ba kome a cikinsa, da katakai. Za kayi shi kamar yadda a ka nuna maka a kan tsaunin. 9 Za ka yi wa rumfar sujada haraba. Za a yi wuraren rataye-rataye a harabar a sashin kudu, ragayu na leshe mai kyau saƙaƙƙe mai ratar kamu ɗari. 10 Za ka yi diraku ashirin domin ragayun, da darori ashirin na tagulla. Za a yi ƙugiyoyi liƙe da dirakun da sanduna na azurfa. 11 Haka kuma a sashin arewa, za ka yi ragayu guda ɗari tare da diraku ashirin da darori ashirin na tagulla da ƙugiyoyi liƙe da dirakun da sandunan azurfa. 12 A sashin yamma na harabar za ka yi labule kamu hamsin. Za ka yi diraku goma da darori goma. 13 Haraba za ta zama kamu hamsin daga sashin gabas. 14 Ragayoyi na wurin shiga ratarsa za su zama kamu hamsin. Za su zama da diraku uku da darori uku. 15 Ɗaya sashin ma zai zama da ragayu kamu goma sha biyar. Da dirakunsu uku da darorinsu uku. 16 Ƙofar shigowa harabar za ta zama da labule mai ratar kamu ashirin. Za a yi labulen da shuɗi da shunaiya da jăn ƙyalle da saƙaƙƙen leshe mai kyau, wanda ƙwararren mai aikin hannu ya yi. Zai zama da diraku huɗu da darori huɗu. 17 Dukkan dirakun harabar za su zama da sandunan azurfa da ƙugiyoyin azurfa da darorin tagulla. 18 Ratar harabar za ta zama kamu ɗari, da faɗin kamu hamsin da tsawon kamu biyar da ragaya ta saƙaƙƙen leshe mai kyau da darori na tagulla. 19 Dukkan kayan aikin rumfar sujada, da abubuwan kamawar na harabar za a yi su da tagulla. 20 Za ka umurci mutanen Isra'ila su kawo man zaitun, mai tsabta, domin fitilun su yi ta ci ba fasawa. 21 A rumfa ta taruwa, bayan labulen rumfar sujada inda akwatin shaida ya ke, Haruna da 'ya'yansa za su sa fitilun suyi ta ci tun daga yamma har zuwa safiya a gaban Yahweh. Mutanen Isra'ila za su lura da wannan ka'idar a dukkan zamanu.

Sura 28

1 Ka kira Haruna ɗan'uwanka da 'ya'yansa maza- wato, Nadab, da Abihu, da Eliyeza, da Itama - daga cikin Isra'ilawa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci. 2 Ka yi wa Haruna, ɗan'uwanka rigunan keɓaɓɓu gare ni. Waɗannan riguna za su zama domin ya fita da kyau da kwarjini. 3 Ka yi magana da mutane masu hikima a zuciya, waɗanda na cika su da ruhun hikima, domin su yi wa Haruna riguna a keɓe shi domin ya yi mani hidima a matsayin firist. 4 Rigunan da za suyi su ne, ɗamara ta sawa a ƙirji da alkyabba, da taguwa, da riga mai aiki, da rawani, da ɗamara. Za su yi waɗannan tufafi keɓaɓɓu gare ni. Za su zama saboda Haruna ɗan'uwanka da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci. 5 Ma su aikin hannu za su yi amfani da leshe mai kyau mai launin zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jã. 6 Sai su yi alkyabba da launin zinari, da shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da leshe mai kyau mai aiki. gwani ne zai yi aikin. 7 A kusurwoyi biyu za ta kasance da ƙyallayen da za'a sa a kafaɗa. 8 A yi mata saƙa mai kyau ɗamarar ta zama kamar alkyabbar; kuma a yi su tare da falmarar, ayi su da leshe mai kyau mai aiki da launin zinari da shuɗi da shunaiya da ja. 9 Ka ɗauki duwatsu biyu na oniks ka rubuta sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu. 10 Sunaye shida a kan dutsen ɗaya, sauran shidan kuma a kan ɗaya dutsen, bisa ga yadda aka haife su. 11 Mai iya rubutu a kan dutse ne zai yi rubutun kamar yadda ake rubuta hatimi, ka rubuta sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsun guda biyu. Ka ɗora duwatsun a kan kasko na zinariya. 12 Za ka ɗora duwatsun biyu a ƙyallen kafaɗa na falmara, su zama duwatsun tuna wa Yahweh da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai ɗauki sunayensu a gaban Yahweh bisa kafaɗunsa biyu su zama abin tunawa a gare shi. 13 Sai kayi kasake na zinariya 14 za kayi sarƙoƙi biyu na zinariya kamar tsarkiyoyi, ka liƙa sarƙoƙin a jikin kasaken. 15 Za ka yi ƙyalle na ƙirji domin yin shawara, ka sami gwani ya tsara shi kamar alkyabba. A yi shi na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da linin mai kyau. 16 Ya zama murabi'i. Ƙyallen na ƙirji za ka sa shi riɓi biyu. Ratarsa za ta zama taki ɗaya faɗinsa ma taki ɗaya. 17 Ka yi jere huɗu na duwatsu masu daraja a jikinsa. Dole jeri na farko a sa rubi, da tofez, da kuma ganet.. 18 A jeri na biyu kuma dole a sa emerald, da saffiya, da lu'u-lu'u. 19 Jeri na uku kuma dole kasa yasint, da agat, da kuma ametis. 20 Jeri na huɗu za ka sa beril da oniks, da yasfa. A sa su a kan kasaken zinariya. 21 Za a jera duwatsun bisa ga sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu, bi da bi a jere. A zana su kamar yadda a ke yin hatimi da zobe, kowanne suna ya zama a madadin kabilu goma sha biyu. 22 Ƙyalle na ƙirjin ya zama sarƙa kamar tsarkiya, saƙaƙƙe na zinariya tsantsa. 23 Za ka yi wa ƙyallen zobba biyu liƙe da juna a kusurwoyinsa biyu. 24 Ka liƙa sarƙoƙin nan biyu a jikin ƙyalle na ƙirji. 25 Za ka liƙa ƙarshen sarƙoƙin nan biyu a jikin kasaken. Sa'an nan ka liƙa su a jikin ƙyallen kafaɗa na falmara a gaba. 26 Za ka yi zobba na zinariya guda biyu, ka sa su a ɗaya gefe na ƙyallen na ƙirjin, a ƙarshen kalmasa ta ciki kusa da haɓar. 27 Dole zaka yi waɗansu zobba na zinariya guda biyu, ka liƙa su jikin ƙyalle na kafaɗar falmara daga ƙasa, a bisa ɗamarar nan ta kyakkawan leshe na falmarar. 28 Su haɗa ƙyallen nan na ƙirji da zobban falmarar nan masu launin shuɗi, domin su haɗu saƙaƙƙiyar ɗamarar nan ta falmarar. Domin kada ƙyallen na ƙirji ya zama a ware da falmarar. 29 Sa'ad da Haruna yake shiga cikin wuri mai tsarki, zai ɗauki sunayen mutanen Isra'ila a bisa zuciyarsa cikin ƙyallen nan na ƙirji domin ɗaukar shawara, za ayi ta yin haka domin ya zama abin tunawa a gaban Yahweh. 30 Zaka sa Urim da Tummim a cikin ƙyalle na ƙirjin domin ɗaukar shawara, domin su zama a bisa zuciyar Haruna sa'ad da yake shiga gaban Yahweh. Ta haka Haruna zai riƙa ɗaukar abin ɗaukar shawara domin mutanen Isra'ila bisa zuciyaarsa a gaban Yahweh. 31 Rigar wato falmara zaka yi ta duka da shuɗi. 32 Za a yi mata wurin sa kai a tsakiya. Dole ayi wa wurin sa kai ɗin saƙa domin kada ya yage. Dole a sami mai saƙa ya yi aikin. 33 Za ka yi wa haɓar rigar, ado na 'yan tutoci da shuɗi, da shunayya, da jan ulu ya kewaye dukka. 34 Ka yi ƙararrawa ta zinariya ta zagaya dukka a tsakanin tutocin. A sa ƙararrawa ta zinariya da tuta, sai kuma ƙararrawa ta zinariya sai kuma tuta - da sauransu - kewaye tufar dukkan ta. 35 Haruna zai sa wannan tufar sa'ad da zai yi hidima, domin a iya jin ƙararta sa'ad da yake shiga wuri mai tsarki gaban Yahweh da sa'ad da yake fita. Wannan domin kada ya mutu ne. 36 Dole ka yi faranti na zinariya ka yi zane a kan sa, kamar zanen hatimi, "Tsarki ga Yahweh." 37 Za ka liƙa wannan farantin da shuɗiyar iggiya a jikin rawanin. 38 Haruna zai sa shi a kansa; zai ɗauki laifi da ake yi game da baye-baye masu tsarki na Isra'ilawa waɗanda aka keɓe domin Yahweh. Dole rawanin ya kasance a kansa domin Yahweh ya karɓi baye- bayensu. 39 Dole ka yi alkyabba da linin mai kyau, da rawani na linin mai kyau. Kuma zaka sa mai zane ya yi masa ado. 40 Zaka yi riguna saboda 'ya'yan Haruna, da ɗammaru, da abin ɗaurawa a kansu saboda daraja da kwarjini. 41 Dole ka suturta Haruna ɗan'uwanka, da 'ya'yansa. Dole ka shafe su, ka naɗa su, ka keɓe su domi na, domin su yi mani hidima a matsayin firistoci. 42 Dole ka yi masu wuyan wanduna na sawa a ciki domin su rufe tsiraicin jikinsu, ya rufe su daga kwankwaso zuwa cinya. 43 Haruna da 'ya'yansa za su riƙa sa waɗannan tufafi sa'ad da suke shiga wurin taruwa da sa'ad da suke fuskantar bagadi su yi hidima a wuri mai tsarki. Dole su yi haka domin kada su zama da kuskure in ba haka ba za su mutu. Wannan zaunanniyar doka ce domin Haruna da zuriyarsa a bayansa.

Sura 29

1 Ga abin da za ka yi domin ka keɓe su yadda za su iya yi mani hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa cikas da, 2 gurasa marar gami, da waina marar gami gauraye da mai. Ka kuma ɗauki wainar alkama marar gami ka shafe da mai. wadda aka yi da kyakkyawar alkama. Wadda ake ci da zuma. 3 Dole ka sa su a cikin kwando ɗaya, ka kawo su a cikin kwandon, ka miƙa su tare da bijimin da ragunan nan biyu. 4 Dole ne ka miƙa Haruna da 'ya'yansa a ƙofar shiga rumfar ta taruwa. Za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa wanka da ruwa. 5 Dole ka ɗauki rigunan da alkyabba ka sa wa Haruna da maratayin falmara da falmara da ƙyalle na ƙirjin da ɗamara ta leshe mai kyau tare da falmara ka yafa masa. 6 Ka naɗa rawanin a kansa da kambi na tsarki a bisa rawanin. 7 Sa'an nan ka ɗauki mai na shafewa ka zuba a kansa, da haka za ka shafe shi. 8 Dole ka kawo 'ya'yansa su ma ka sa masu alkyabbobi. 9 Za ka sa wa Haruna da 'ya'yansa ɗammaru da ƙyalle na ado a kansu. Aikin firist zai zama nasu kullum bisa ga doka. Ta haka za ka tsarkake Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima. 10 Dole dukkan ku za ku kawo bijimin a wurin rumfa ta taruwa, Haruna da 'ya'yansa za su sa hannayensu a kan bijimin. 11 Zaka yanka bijimin a ƙofar rumfar ta taruwa a gaban Yahweh. 12 Dole ka ɗauki jinin bijimin da yatsarka ka sa a kan ƙahon bagadin, sai ka ɗauki sauran jinin ka zubar da shi a dakalin bagadin. 13 Dole ka ɗauki kitse na marfin ciki da wanda ya lulluɓe hantar da ƙodojin biyu da kitsen da yake kansu; ka ƙona a kan bagadin. 14 Amma naman bijimin da fatarsa da sauran abin da ya rage jikinsa, dole ka ƙone su a waje. Za ya zama baiko na zunubi. 15 Dole ka kuma ɗauki rago ɗaya, Haruna da 'ya'yansa su ɗora hannuwansu a kansa. 16 Dole ka yanka ragon, ka yayyafa jininsa a kowanne sashi na bagadin. 17 Dole ka yanka ragon gunduwa--gunduwa da ƙafafunsa, ka sa 'yancikinsa tare da gunduwoyin tare da kansa, 18 a bisa bagadin. Sa'an nan ka ƙone ragon dukkan sa. Zai zama baiko na ƙonawa ga Yahweh, baiko mai daɗin ƙanshi wanda aka yi domin Yahweh. 19 Sa'an nan dole ka ɗauki ɗaya ragon, Haruna da 'ya'yansa su ɗora hannuwansu a kansa. 20 Sa'an nan dole ka yanka ragon ka ɗauki jininsa. Ka sa shi a bisa kunnen Haruna na dama, da bisa kan kunnuwan 'ya'yansa na dama, da kan babban yatsansu na dama, da babban yatsan kowannen su na dama na ƙafa. Sa'an nan ka yayyafa jinin a jikin bagadin a kowanne sashe. 21 Dole ka ɗauka daga jinin da yake kan bagadi da mai na shafewa, ka yayyafa a kan Haruna da tufafinsa, da kuma kan 'ya'yansa da tufafinsu. Sa'an nan Haruna zai zama keɓaɓɓe domi na, da kuma tufafinsa da 'ya'yansa da tufafinsu tare da shi. 22 Dole ka ɗauki kitsen ragon da kitsen bindin da kitsen da ya rufe kayan cikin da wanda ya lulluɓe hantar, da ƙodojin biyu da kitsen dake kansu, da cinyar dama-wannan ragon na keɓewar firistoci ne a gare ni. 23 Ka ɗauki dunƙule ɗaya na gurasa da wainar da aka yi da mai, guda ɗaya da wainar alkama ɗaya daga cikin kwandon wadda bata da gami wadda ke gaban Yahweh. 24 Dole ka sa waɗannan a cikin hannuwan Haruna da hannuwan 'ya'yansa ka ɗaga su a gabana domin baiko na ɗagawa a gaban Yahweh. 25 Sa'an nan dole ka ɗauke abincin daga hannuwansu ka ƙone shi a kan bagadin tare da baiko na ƙonawa. Zai kawo ƙanshi mai daɗi a gare ni; zai zama baikon da aka yi mani da wuta. 26 Dole ka ɗauki haƙarƙarin ragon da aka yanka saboda keɓe Haruna ka ɗaga shi ka karkaɗa shi sama domin ya zama baiko na ɗagawa ga Yahweh, shi ne kuma zai zama rabonka. 27 Dole ka keɓe ƙirjin da aka karkaɗa a sama domi na, cinyar da firistoci suka kawo gudummuwa-ƙrjin da aka karkaɗa da cinyar da aka kawo gudummuwa saboda Haruna da 'ya'yansa. 28 Wannan zai zama zaunanniyar ka'ida saboda Haruna da 'ya'yansa. Zai zama gudummuwar da mutanen Isra'ila suka ba Yahweh baye-baye na salama. 29 Za a ajiye tufafin Haruna masu tsarki saboda 'ya'yansa a bayansa. Za a shafe su a cikin waɗannan tufafi a keɓe su gare ni a cikin su. 30 Firist ɗin da ya gaje shi daga cikin 'ya'yansa, wanda ya zo rumfa ta taruwa domin ya yi mani hidima a wuri mai tsarki, zai sa waɗannan tufafi har kwanaki bakwai. 31 Dole ka ɗauki ragon na rantsar da firistoci ka dafa namansa a cikin wuri mai tsarki. 32 Haruna da 'ya'yansa ne za su ci naman ragon da gurasar dake cikin kwando a ƙofar shiga rumfa ta taruwa. 33 Dole su ci naman da gurasar da aka bayar domin a yi masu kafara a kuma naɗa su, domin a keɓe su domina. Ba wanda zai ci wannan abincin, saboda zai zama abin da aka tsarkake saboda ni. 34 Idan naman keɓewar da aka bayar ko gurasar sun rage har sun kai safiya, za ka ƙone shi. Ba za a ci shi ba saboda an riga an keɓe shi saboda ni. 35 Haka za ka yi, ka bi umarnin dana baka, ka yi wa "ya'yan Haruna haka. Ka shirya su har kwana bakwai. 36 Kowacce rana zaka miƙa bijimi domin baiko na zunubi damin kafara. Dole ka tsarkake bagadin ta wurin yin kafara domin sa, zaka shafe shi domin ya zama a keɓe domi na. 37 Dole ka yi kwana bakwai kana yin hadaya saboda bagadin kana keɓe shi saboda Yahweh. Sa'an nan bagadin zai zama keɓaɓɓe saboda ni. Dukkan abin da ya taɓa bagadin zai zama keɓaɓɓe na Yahweh. 38 Dole ka riƙa miƙa ɗan rago bana ɗaya kowacce rana. 39 Dole ka miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya ɗan ragon kuma ka miƙa shi da yamma. 40 Tare da ɗan rago na fari, za a miƙa mudu biyu na garin alkama mai laushi wanda aka kwaɓa da man zaitun kwalba biyu, da ruwan inabi shi ma kwalba biyu baiko na sha. 41 Rago na biyu tilas ka miƙa shi da faɗuwar rana. Dole ka sa gari kamar yadda ka sa da safe, haka kuma baiko na sha. Waɗannan za su zama da ƙamshi mai daɗi a gare ni; za su zama baiko da aka yi mani da wuta. 42 Waɗannan za su zama baiko na ƙonawa a cikin dukkan tsararrakinku, a ƙofar shiga rumfa ta taruwa a gaban Yahweh, inda zan sadu da kai in yi magana da kai a can. 43 A nan ne zan sadu da Isra'ilawa; darajata za ta keɓe rumfar. Zan keɓe rumfar ta taruwa da bagadin domin su nawa ne ni kaɗai. 44 Zan kuma keɓe Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci. 45 Zan zauna a cikin Isra'ilawa zan zama Allahnsu. 46 Za su sani Ni ne Yahweh, Allahnsu wanda ya fito da su daga Masar domin in zauna a cikin su. Ni ne Yahweh Allahnsu.

Sura 30

1 Tilas ka yi bagadi na ƙona turare. Tilas ka yi shi da itacen ƙirya. 2 Ratarsa za ta zama kamu ɗaya, faɗinsa kamu ɗaya. Tilas ka yi shi murabbi'i, tsawonsa kamu biyu. Tilas ka yi shi tare da ƙahonninsa. 3 Tilas ka shafe bagadin da zinariya tsantsa-bisansa, da sassansa, da ƙahoninsa. Tilas ka kewaye gefensa da zinariya. 4 Tilas ka yi zobba biyu na zinariya liƙe da shi a kusa da shi daga ƙasa suna duban sa a sassa biyu. Zobban za su zama wurin zura sandunan riƙewa da za a iya ɗaukar bagadin. 5 Tilas ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka shafe su da zinariya. 6 Tilas ka sa bagadin turaren a gaban labulen dake kusa da akwatin shaida. Zai zauna a gaban marfin kafara na zunubi a bisa akwatin shaida, inda zan sadu da kai. 7 Tilas Haruna ya ƙona turare mai ƙamshi kowacce safiya. Zai ƙona shi sa'ad da yake gyara fitilun, 8 da yamma kuma Haruna zai kunna fitilun domin turaren ya riƙa ƙonewa koyaushe a gaban Yahweh, a dukkan tsararraki. 9 Amma kada ka miƙa wani turaren a kan bagadin turaren, ko wani baiko na ƙonawa ko baiko na hatsi. Kada ka zuba wani baiko na sha a kansa. 10 Tilas Haruna ya yi hadaya ta zunubi a kan ƙahonninsa sau ɗaya a shekara. Da jinin baikon na zunubi zai yi hadaya ta zunubi sau ɗaya a shekara a dukkan tsararrakinku. Keɓaɓɓe ne sarai saboda Yahweh." 11 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 12 "Sa'ad da ka ƙidaya Isra'ilawa, kowanne mutum zai kawo abin fansa domin ransa ga Yahweh. Sa'ad da ka ƙidaya su dole ne ka yi haka. Domin kada annoba ta auko a cikin su sa'ad da kake ƙidaya su. 13 Dukkan wanda aka ƙidaya cikin yin ƙidayar zai biya rabin awo na azurfa, bisa ga kuɗin da ake amfani da su a wuri mai tsarki (awon dai-dai yake da abin da ake auna nauyin ƙaramin abu). Wannan rabin awo baiko ne domin Yahweh. 14 Dukkan wanda aka ƙidaya, daga shekara ashirin zuwa gaba, dole ya bada wannan baikon gare ni. 15 Lokacin da mutane suke bada wannan baiko domin fansar rayukansu, masu arziki ma ba zasu bada fiye da rabin awon nan ba, matalauta kuma ba zasu bada abin da bai kai rabin awon nan ba. 16 Dole ka karɓi wannan kuɗin fansa daga Isra'ilawa ka sa su cikin aikin rumfa ta taruwa. Dole ya zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gare ni, su miƙa abin kafara domin rayukansu. 17 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 18 "Zaka yi babban bangaji na tagulla da wurin zamansa na tagulla, bangajin wanke-wanke. Tilas ka sa shi tsakanin rumfa ta taruwa da bagadi, ka zuba ruwa a cikin sa. 19 Haruna da 'ya'ansa za su wanke hannuwansa da ƙafafunsu da ruwan dake cikin sa. 20 Sa'ad da suke shiga rumfa ta taruwa da sa'ad da suke zuwa kusa da bagadi su yi mani hidima ta ƙona baiko, dole su wanke da ruwa domin kada su mutu. 21 Dole su wanke hannuwansu da ƙafafunsu domin kada su mutu. Dole wannan ta zama dawwamammar doka ga Haruna da zuriyarsa a dukkan tsararrakin mutanensa. 22 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 23 "Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau: da murr mai zubowa na awo ɗari biyar, da sinamon mai ƙanshi mai daɗi na awo 250, da kayan yaji mai ƙanshi na awo 250, 24 da kayan yaji mai ƙanshi na kasiya na awo ɗari biyar, wanda aka auna bisa ga ma'aunin wuri mai tsarki, da kwalba ɗaya ta man zaitun. 25 Dole da waɗannan kayan haɗi za ka sa maiyin turare ya yi mai na shafewa mai tsarki. Zai zama man tsarki na shafewa, ajjiyayye saboda ni. 26 Dole da wannan mai na shafewa za ka shafe rumfa ta taruwa da akwati na shaida, 27 sai kuma teburin da kayan aikinsa da abin ɗora fitilar da kayanta da sanduƙin turare, 28 sai kuma bagadin ƙona baye--baye da dukkan kayansa da bangajin da wurin ɗora shi. 29 Tilas ka keɓe su saboda ni su zama masu tsarki domi na. Dukkan abin da ya taɓa su zai zama mai tsarki. 30 Tilas ka keɓe Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci. 31 Dole kace da Isra'ilawa, 'Wannan mai na shafewa ne da aka keɓe domin Yahweh a dukkan tsararrakin mutanenku. 32 Dole mutane ba za su shafa shi a jikinsu ba, kuma ba za ka yi wani mai da kamar yadda ka yi shi ba, saboda keɓaɓɓe ne saboda Yahweh. Dole ka lura da shi ta wannan hanya. 33 Dukkan wanda ya yi turare irin sa, ko ya shafa wa wani shi, za a datse shi daga cikin mutanensa."' 34 Yahweh yace da Musa, "Ka ɗauki kayan yaji - wato su-stakte da onika da galbanum-kayan yaji masu ƙanshi tare da lubban tsantsa, ka auna su dai-dai wa daida. 35 Ka yi su kamar turaren yadda maiyin turare ya haɗa, gyararre da gishiri, mai tsafta keɓaɓɓe. 36 Ka yi masa haɗi mai kyau ka niƙa. Ka ɗiba cikinsa ka sa a shaida, wanda yake a cikin rumfa ta taruwa, inda zan sadu da kai. Ka ɗauke shi da tsarki sosai a gare ni. 37 Wannan turaren da zaka yi, ba zaka yi wani irin sa domin kanka ba. Zai zama mai tsarki sosai a gare ka. 38 Dukkan wanda ya yi turare irin sa ya yi anfani da shi za a datse shi daga cikin mutanensa."

Sura 31

1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 2 "Duba, na kira sunan Bezalel ɗan Uri ɗan Hour, daga kabilar Yahuda. 3 Na kuma cika Bezalel da Ruhuna, ya ba shi hikima, basira da ilimi, da dukkan kayayyakin ayyukan hannuwa, 4 don ya yi fasalin abubuwa da aikin zinariya da azurfa da tagulla; 5 ya kuma yanka da jera duwatsu da sassaƙa itace -- ya yi kowanne irin aikin fasahar hannu. 6 Tare da shi, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan. Na sa fasaha a zukatan dukkan masu hikima don su yi dukkan abin dana umarce ka. Wannan ya haɗa da 7 rumfar taruwa, da akwatin shaida, da abin tuba da yake kan akwatin, da dukkan kayayyakin dake cikin rumfar- 8 teburi da kayayyakinsa da tsantsa alkuki tare da dukkan kayayyakinsa, da turaren bagadi da 9 bagadin hadayar konawa da dukkan kayayyakinsa da babbar kwatarniya tare da mazaunin ta. 10 Wannan ya haɗa da ƙyakkyawan - sakakkun riguna - tsarkakkun tufafin domin Haruna firist da 'ya'yansa maza, na ajiye su domin na, saboda su yi aikin firistoci. 11 Wannan ya haɗa da man shafewa da turare domin wuri mai tsarki. Waɗannan masu sana'ar hannu dole ne su yi dukkan waɗannan abubuwa kamar yadda na umarce ku." 12 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 13 "Faɗa wa Isra'ilawa: 'Dole ku kiyaye ranakun Asabar na Yahweh, domin dukkan waɗannan za su zama alama tsakanin shi da ku acikin dukkan zuriyar mutanenku har abada don ku sani shi ne Yahweh, wanda ya keɓe ku domin kansa. 14 Saboda haka dole ku kiyaye Asabar, don ku lura da ita da tsarki, ya keɓe ta dominsa. Duk wanda ya tozarta ta babu shakka kashe shi za a yi. Duk wanda ya yi aiki ranar Asabar, wannan mutum babu shakka za a yanke shi daga mutanensa. 15 Ku yi aiki a kwana shida kaɗai, amma a rana ta bakwai ranar Asabar ce ku huta, tsattsarka ga Yahweh. Duk wanda ya yi aiki a ranar Asabar babu shakka za a kashe shi. 16 Saboda haka Isra'ilawa dole su kiyaye Asabar. Dole su kiyaye ta a dukkan tsararrakin mutanensu za ta zama dawwamammar doka. 17 Asabar za ta zama a kullum alama tsakanin Yahweh da Isra'ilawa, gama a cikin kwana shida Yahweh ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya huta da yin komai.'" 18 Sa'ad da Allah ya gama magana da Musa a kan Tsaunin Sinai, ya ba shi alluna biyu na alƙawarin ka'idodi, da aka yi da dutse, rubutattu da hannunsa.

Sura 32

1 Da mutanen suka ga Musa ya yi jinkirin dawowa daga tsaunin, sai suka taru kewaye da Haruna, suka ce masa, "Zo, ka yi mana gunki da zai wuce gaban mu. Domin wannan Musa, mutum wanda ya fito damu daga ƙasar Masar, bamu san abin da ya faru da shi ba." 2 Sai Haruna yace masu, "Ku tuttuɓe zobbanku na zinariya waɗanda suke a kunnuwan matayenku da kunnuwan 'ya'yanku maza da mata ku kawo su gare ni." 3 Dukkan jama'a suka tuttuɓe zobban da suke a kunnuwansu, suka kawo su wurin Haruna. 4 Ya karɓi zinariyar daga wurinsu, ya narkar da su, ya mai da shi siffa ta ɗan maraki. Sai mutanen suka ce, "Isra'ila, wannan shi ne allahnku wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar." 5 Sa'ad da Haruna ya ga wannan, ya gina bagadi a gaban siffar marakin ya yi shela; ya ce, "Gobe akwai bikin girmama Yahweh." 6 Mutane suka tashi da asussuba kashegari suka miƙa hadayu na konawa da bayarwar zumunta. Sai suka zauna suka ci suka sha, sa'an nan suka tashi suna shagalin shashanci. 7 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, "Tafi da sauri, gama mutanenka, waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar, sun ƙazantar da kansu. 8 Sun yi saurin ƙyale hanyar dana umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraki suna yi masa sujada, suna miƙa masa hadaya. Sun kuma ce, Isra'ila, wannan shi ne allahnka wanda ya fito daku daga ƙasar Masar.'" 9 Sai Yahweh ya faɗa wa Musa, "Na ga wannan jama'ar. Duba, mutanen nan suna da taurinkai. 10 Yanzu dai, kada ka yi ƙoƙarin hana ni. Fushina ya yi ƙuna a kansu, saboda haka zan hallaka su. Sai in yi wata babbar al'umma daga gare ka." 11 Amma Musa ya yi ƙoƙarin roƙon Yahweh Allahnsa. Ya ce, "Yahweh, me ya sa ka husata da mutanenka, waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar da ƙarfin iko da babban hannu? 12 Me ya sa za ka sa Masarawa su ce, 'Ya sa su sun fito da mugun nufi, don ya kashe su cikin duwatsu ya kuma shafe su daga fuskar duniya?' Ka janye daga zafin fushinka, ka ji tausayi daga wannan hukunci a kan mutanenka. 13 Ka tuna da Ibrahim da Ishaku da Isra'ila, bayinka, waɗanda kai da kanka ka rantse ka ce, 'Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sammai, in kuma ba zuriyarku dukkan wannan ƙasa wanda na yi maganar ta. Za ku gaje ta har abada.'" 14 Sai Yahweh ya huce ya janye daga hukuncinsa da ya ce zai sa masifa a kan mutanensa. 15 Musa kuwa ya juyo ya sauko daga kan tsaunin, yana ɗauke da allunan biyu na shaidar ka'idodi a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da waje, gaba da baya. 16 Allunan kuma aikin Allah ne, rubutun kuwa na Allah ne, da ya zana a kan allunan. 17 Sa'ad da Yoshuwa ya ji hayaniyar mutane kamar suna ihu, ya cewa Musa, "Akwai hargowar yaƙi a zangon." 18 Amma Musa yace, "Ai ba amon nasara ba ce, ba kuma amon mutanen da aka ci nasara a kansu bane, amma hayaniyar waƙa nake ji." 19 Sa'ad da Musa ya kusato zangon ya ga siffar ɗan maraki mutane kuma na ta rawa. Ya harzuka da haushi. Ya watsar da allunan da suke hannunwansa suka farfashe a gindin tsaunin. 20 Ya ɗauki siffar ɗan marakin da mutane suka yi, ya kone ta, ya nike ta zama gari, ya barbada a cikin ruwa. Sa'an nan ya sa mutanen Isra'ila su sha ta. 21 Musa ya cewa Haruna, "Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo babban zunubi a kansu?" 22 Haruna yace, "Kada ka bar fushinka ya yi ƙuna, ya shugabana. Ka san waɗannan mutane, yadda suke a kan yin mugunta. 23 Sun ce da ni, 'Ka yi mana allah wanda zai wuce gabanmu. Gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga ƙasar Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.' 24 Ni kuwa nace da su, 'Duk wanda yake da zinariya, bari ya tuɓe ya kawo ta.' Suka ba ni zinariya ni kuwa na zuba su cikin wuta, daganan wannan maraki ya fito." 25 Musa ya ga mutanen sun gagara (gama Haruna ya barsu sun fi karfin a shawo kansu, suna sa abokan gãbarsu su yi masu ba'a). 26 Sai Musa ya tsaya a ƙofar zango ya ce, "Duk wanda yake wajen Yahweh, ya zo wurina." Dukkan Lebiyawa suka tattaru a wurinsa. 27 Ya ce masu, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: 'Bari kowanne mutum ya rataya takobinsa a gefensa da bayansa ya tafi ya dawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango kowa kuma ya kashe ɗan'uwansa, ya kashe abokinsa da kuma makwabcinsa.'" 28 Lebiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarta. A ranan nan mutane dubu uku suka mutu. 29 Musa ya cewa Lebiyawa, "Ku bada kanku cikin aikin Yahweh yau, gama kowannenku ya yi gãba da ɗansa da ɗan'uwansa, saboda Yahweh ya iya baku albarka yau." 30 Washegari Musa ya cewa mutanen, "Kun aikata babban zunubi. Yanzu zan tafi wurin Yahweh. Watakila zan iya yin kafara domin zunubanku." 31 Musa ya koma wurin Yahweh yace, "Aiya, waɗannan mutane sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya. 32 Amma yanzu, idan ka yarda ka gafarta zunubansu; amma idan ba za ka yi ba, ka shafe sunana daga cikin litafin daka rubuta." 33 Yahweh ya cewa Musa, "Duk wanda ya yi mani zunubi, shi ne kuwa zan shafe sunansa daga cikin littafina. 34 Saboda haka yanzu ka tafi, ka bida mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka. Duba, mala'ikana zai wuce gabanka. Amma a ranar da zan hukuntasu, zan hukuntasu saboda zunubinsu." 35 Yahweh ya aika da annoba ga mutanen domin sun yi ɗan marakin, da Haruna ya yi.

Sura 33

1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. "Tafi, daganan, kai da mutane waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar. Tafi zuwa ƙasar dana rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da na ce, 'Zan bada ita ga zuriyarku.' 2 Zan kuma aiki mala'ika a gabanka, zan kori Kan'aniyawa, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hibiyawa, da Yebusiyawa. 3 Tafi zuwa ƙasar, wanda ke fitar da madara da zuma, amma ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurinkai. Don zan iya hallaka ku a hanya." 4 Sa'ad da mutane suka ji waɗannan maganganu masu tada hankali, suka damu suka yi nadama babu wanda ya sa kayan ado. 5 Yahweh yace da Musa, "Faɗa wa Isra'ilawa, 'Ku mutane ne masu taurin kai. Idan na tafi tare daku ɗan lokaci kaɗan, zan hallaka ku. Domin haka yanzu, ku tuɓe kayan adonku don zan iya yin abin dana shawarta da ku.'" 6 Saboda haka Isra'ilawa ba su sa kayan ado daga Tsaunin Horeb ba har zuwa gaba. 7 Musa ya ɗauki rumfar ya kafa ta a bayan zango. Ya kuma kira ta da suna rumfar taro. Duk wanda yake neman Yahweh da kowanne abu sai ya tafi rumfar taruwa, wajen zangon. 8 Duk sa'ad da Musa ya fita daga zango, dukkan mutane nan za su tashi tsaye a ƙofar rumfarsu su kalli Musa har sai ya shiga ciki. 9 Duk sa'ad da Musa ya shiga rumfa, al'amudin girgije yakan sauko ya tsaya bisa ƙofar rumfar, Yahweh kuwa ya yi magana da Musa. 10 Duk lokacin da dukkan mutane suka ga al'amudin girgijen nan na tsaye a kofar rumfar, sai su tashi su yi sujada, kowanne mutum a ƙofar rumfarsa. 11 Yahweh kuwa zai yi magana da Musa fuska da fuska, kamar mutum ne ke magana da abokinsa. Musa kuwa zai koma cikin zango, amma baransa Yoshuwa ɗan Num, saurayin mutum, zai tsaya a rumfar. 12 Musa ya cewa Yahweh, "Duba, ka faɗa mani cewa, 'Ka fita da mutanen nan a tafiyarsu,' amma ba ka bar ni in san wanda za ka aika tare da ni ba. Ka ce, 'Na san ka ta wurin sunanka, ka kuma sami tagomashi a idanuwana.' 13 Yanzu idan har na sami tagomashi a idanunka, ka nuna mani hanyoyinka domin in san ka in kuma cigaba da samun tagomashi a idanunka. Ka tuna wannan al'umma mutanenka ne." 14 Yahweh kuwa ya amsa, "Zan tafi tare da kai, zan kuma baka hutawa." 15 Musa yace da shi, "Idan ba za ka tafi tare da mu ba, kada ma ka ɗaga mu daga nan. 16 Domin in ba ta haka ba, ƙaƙa za a sani na sami tagomashi a idanunka, ni da mutanenka? Ba sai ka tafi tare da mu ba, domin ni da mutanenka a ga bambanci daga dukkan sauran jama'ar da suke fuskar duniya?" 17 Yahweh ya cewa Musa, "Zan kuma yi wannan abu yadda ka roƙa, gama ka sami tagomashi a idanuna, na kuma san ka da suna." 18 Musa kuwa ya ce, "Idan ka yarda ka nuna mani darajarka." 19 Yahweh yace, "Zan sa dukkan ɗaukakata ta wuce a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda na yi wa alheri, zan kuma nuna jinkai ga wanda na yi wa jinkai. 20 Amma Yahweh yace, "Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama babu wanda zai gan ni ya rayu." 21 Yahweh yace, "Duba, a nan ga wani wuri kusa da ni; inda za ka tsaya bisa wannan dutsen. 22 Sa'ad da ɗaukakata take wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hunnuna har sai na wuce. 23 Sa'an nan zan ɗauke hannuna, za ka ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba."

Sura 34

1 Yahweh ya cewa Musa, "Ka datse allunan biyu na dutse kamar allunan farkon. Zan rubuta kalmomin a kan waɗannan allunan yadda suke cikin allunan farkon, allunan da ka farfasa. 2 Ka yi shiri da safe, ka zo kan Tsaunin Sinai, ka gabatar da kanka gare ni a kan saman tsaunin. 3 Babu wani da zai zo tare da kai. Kada ka bari a ga wani a ko'ina a kan tsaunin. Kada a bar garken tumaki ko awaki, su yi kiwo a gaban tsaunin." 4 Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau kan Tsaunin Sinai, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. Musa ya rike allunan na dutse a hannunsa. 5 Yahweh kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da Musa a can, ya yi shelar sunansa "Yahweh." Yahweh ya wuce ta gabansa ya yi shelar Yahweh, 6 Yahweh, Allah mai jinkai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan kauna, mai gaskiya, 7 mai kiyaye alƙawarin aminci ga dubban tsarraraki, mai gafarta mugunta da laifuffuka da zunubai. Gama ba zai kuɓutar da mai mugunta ba. Zai hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da tsara ta hudu saboda zunubin iyaye." 8 Musa ya hanzarta ya sukunyar da kansa ƙasa ya yi sujada. 9 Sai ya ce, "Idan na sami tagomashi a idanunka, Ubangijina, ina roƙonka ka tafi tare da mu, gama waɗannan mutanen suna da taurinkai. Gafarta mana laifinmu da zunubinmu, ka ɗauke mu abin gãdonka." 10 Yahweh yace, "Duba na kusan yin alƙawari. Gaban dukkan mutanenka, zan aikata al'ajabi irin wanda ba a taba yi ba a cikin dukkan duniya ko a cikin wata al'umma. Dukkan mutanen dake cikinku za su ga aikina, gama abin bantsoro nake yi da ku. 11 Ku kiyaye abin dana umarce ku yau. Na kusa korar maku Amoriyawa da Kan'aniyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa. 12 Ku lura da kada ku yi alƙawari tare da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, ko su zama tarko a cikinku. 13 A maimakon haka dole ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu na dutse, ku sassare gumakansu. 14 Gama ba za ku yi wa wani allah sujada ba, domin Yahweh, wanda sunansa mai Kishi, Allah mai kishi ne. 15 Saboda haka kuyi hankali kada ku ƙulla alƙawari tare da mazaunan ƙasar, domin sun karuwantar da kansu ga allolinsu, kuma suka miƙa hadaya ga allolinsu. Sa'an nan wani daga cikinsu zai gayyace ku kuma za ku ci daga cikin hadayarsa, 16 sa'an nan kuma za ku ɗauka daga cikin 'ya'yansa mata domin "ya'yanku maza, 'ya'yansa mata za su karuwantar da kansu ga allolinsu, za su kuma sanya 'ya'yanku maza su karuwantar da kansu ga allolinsu. 17 Kada ku yi wa kanku alloli na zuɓi. 18 Dole ku kiyaye Bukin Abinci Marar Gami. Kamar yadda na umarce ku, ba za ku ci gurasa marar gami ba har kwana bakwai a kan lokacin da aka sa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito daga cikin Masar. 19 Dukkan ɗan farin nawa ne, koda ɗan farin mutum ne ko na dabba, dukkan 'ya'yan farin dabbobinku, wato na saniya da tunkiya. 20 Za ku fanshi ɗan farin jaki da ɗan rago, amma idan kuwa ba za ku fanshi ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Dole za ku fanshi kowanne ɗan fari 'ya'ya mazanku. Kada wani ya zo gabana da hannu wofi. 21 Za ku iya yin aiki kwana shida, amma a kan rana ta bakwai dole sai ku huta. Koda lokacin noma ne da lokacin girbi dole ku huta. 22 Dole ku kuma kiyaye Bukin Makwanni tare da amfanin fari na alkama da kuka cire, kuma dole ku kiyaye bukin Tattarawa a karshen shekara. 23 Sau uku a cikin shekara dukkan mazajenku dole su hallara a gaban Ubangiji Yahweh, Allah na Isra'ila. 24 Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in faɗaɗa kan iyakokinku. Babu wani da zai yi ƙyashin ƙasarku kamar na su a lokatan da kuka tafi ku bayyana a gaban Yahweh Allahnku sau uku a shekara. 25 Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da wani abu mai gami ba, ko wani nama daga hadaya ta Bikin Ƙetarewa wanda za a bari har zuwa safiya. 26 Dole ku kawo mai kyau ta nunar farin amfanin gonakinku a cikin gidana. Kada ku yarda ku dafa ɗan akuya da yake shan nonon uwarsa." 27 Yahweh ya cewa Musa, "Rubuta waɗannan maganganu, gama dai-dai suke da maganganu alƙawarin da ni na ɗauka da Isra'ila." 28 Musa kuwa yana tare da Yahweh yini arba'in da dare arba'in; bai ci kowanne abinci ba ko ya sha ruwa ba. Ya rubuta maganganun alƙawarin a kan allunan, Dokoki Goma. 29 Lokacin da Musa ya sauko daga Tsaunin Sinai tare da alluna biyu na alƙawarin a hannunsa, bai sani ba, fuskarsa tana annuri lokacin da yake magana tare da Allah. 30 Sa'ad da Haruna da Isra'ilawa suka ga fatar fuskar Musa tana annuri, sai suka ji tsoro suka ka sa zuwa kusa da shi. 31 Amma Musa ya yi magana da Haruna da dukkan shugabannin jama'a su zo gare shi. Musa kuwa ya yi magana da su. 32 Bayan wannan, dukkan mutanen Isra'ila suka zo wurin Musa, ya faɗa masu dukkan umarnin da Yahweh ya ba shi a Tsaunin Sinai. 33 Sa'ad da Musa ya gama magana tare da su, sai ya sa mayafi ya rufe fuskarsa. 34 Duk lokacin da Musa ya je gaban Yahweh ya yi magana da shi, sai ya cire lullubin, har sai ya fito. Idan ya fito, zai faɗawa Isra'ilawa abin da aka umarce shi ya faɗa. 35 Da Isra'ilawa suka ga fuskar Musa tana haske, sai ya lullube fuskarsa kuma har sai ya koma don ya yi magana tare da Yahweh.

Sura 35

1 Musa ya tattara dukkan jama'ar Isra'ilawa ya ce da su, "Waɗannan su ne abubuwan da Yahweh ya umarce ku da yi. 2 A rana ta shida za ku yi aiki, amma dominku, rana ta bakwai za ku maida ita rana mai tsarki, ranar Asabar ce ku huta sosai, mai tsarki ta Yahweh. Duk wanda ya yi wani aiki a ranar lalai zai mutu. 3 Ba za a hura wuta a kowanne gida ba a ranar Asabar." 4 Musa kuwa ya yi magana da dukkan jama'ar Isra'ilawa, cewa, "Wannan shine abin da Yahweh ya umarta. 5 Ku karɓi baiko domin Yahweh, dukkan ku wanda ya yi niyya a zuciya. Ku kawo baikon ga Yahweh--zinariya da azurfa da tagulla 6 da zane shudi da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin da gashin awaki da 7 fatun raguna da aka rina suka zama ja da fatun awaki da itacen kirya 8 da man fitila da kayan yaji domin man keɓewa da turaren konawa 9 da duwatsu masu tamani da duwatsun da za a mammanne a alkyabba da kyallen makalawa a kirji." 10 Kowanne mutum da yake da fasaha a cikinku ya zo ya yi wani abu ga Yahweh ya umarta- 11 rumfar sujada da rumfarta, da murfinta da maratayai da katakanta da sandunanta da dirkokinta da kwasfanta 12 da kuma akwati da sandunansa, da marfin kafara, da labule domin rufewa. 13 Suka kawo tebur da sandunansa da dukkan kayayyakinsa, kuma da gurasa ta kasancewa, 14 da alkuki don haske, tare da kayayyakinsa da fitilunansa da man fitilu 15 da bagadin turaren ƙonawa da sandunansa da man keɓewa mai ƙanshi da turaren ƙonawa da labulen ƙofar rumfa ta sujada 16 bagadin baye-baye na ƙonawa da ragarsa ta tagulla da sandunansa da kuma kayayyakinsa da babban daro da gammonsa. 17 Suka kawo labulen domin harabar tare da dirkokinsa da kwasfansu da labulen don ƙofar harabar 18 da kuma turakun maratayin rumfar da turakun farfajiyar tare da igiyoyinsu. 19 Suka kawo saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a wuri mai tsarki da tsarkakkun tufafi domin Haruna firist da tufafin 'ya'yansa maza na aikin firistoci." 20 Sai dukkan kabilun Isra'ila suka tashi daga gaban Musa. 21 Kowanne zuciyarsa ta kada shi da wanda ruhunsa ya iza shi ya yi niyya kawo wa Yahweh baiko domin yin rumfa ta sujada, da dai dukkan ayyuka cikinta da kuma tsarkakkun tufafi. 22 Suka zo, maza da mata, dukkan waɗanda suke da niyya a zuciya. Suka kawo kayayyakin ƙawanya wato su 'yan kunne da ƙawane da mundaye da kayayyakin dukkan zinariya iri iri. Dukkansu suka bada baikon zinariya kamar su baye-bayen kaɗawa ga Yahweh. 23 Kowanne mutum da yake da shuɗi ko shunayya ko mulufi ko lallausan lilin ko gashin awaki ko fatun raguna da aka rina suka zama ja ko fatun awaki ya kawo su. 24 Kowanne ne wanda ya iya yin baikon azurfa da tagulla ga Yahweh, da kowanne wanda aka same shi yana da itacen ƙirya wanda zai zama da amfani a cikin aikin ya kawo shi. 25 Kowace mace mai fasaha da ta kaɗa zare da hannuwanta ta kawo zaren da ta kaɗa na shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin. 26 Dukkan mataye waɗanda zukatansu suka iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki. 27 Shugabanai suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan alkyabba da kyallen makalawa a kirji; 28 suka kuma kawo kayan yaji da mai don fitilu da mai domin keɓewa da turare mai kanshi don ƙonawa. 29 Sai Isra'ilawa suka kawo bayarwar yardar rai ga Yahweh; kowanne mutum da mace waɗanda zuciyarsu ta iza su da niyya suka kawo kayayyaki domin dukkan aikin da Yahweh ya umarta ta wurin Musa aka yi shi. 30 Musa ya cewa Isra'ilawa, "Duba Yahweh ya kira Bezalel ɗan Uri ɗan Hur da sunansa, daga kabilar Yahuda. 31 Ya cika Bezalel da Ruhunsa, domin ya ba shi hikima da basira da sani da ilimi, don ya iya dukkan kowanne irin aiki, 32 ya ƙirƙiro zane-zane da aikin zinariya da azurfa da tagulla 33 da kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa da sassaƙar itace-ya yi dukkan kowanne irin zane-zane na gwaninta. 34 Ya sa masa a cikin zuciyarsa ya koyar, shi da Oholiyab dan Ahisamak, daga kabilar Dan. 35 Ya cika su da fasaha ta yin kowanne irin aiki, da aiki kamar na sassaƙa dana zane-zane dana yin ɗinke-ɗinke da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin dana yin saƙa. Sun iya yin kowanne irin aiki da yin zane-zane.

Sura 36

1 Bezalel da Oholiyab da kowanne mutum mai fasaha waɗanda Yahweh ya ba su fasaha da basira na sanin yin kowanne irin aikin wuri mai tsarki bisa ga dukkan yadda Yahweh ya umarta." 2 Musa ya kirawo Bezalel da Oholiyab da kowanne mutum mai fasaha wanda Yahweh ya ba shi fasaha a zuciya da dai dukkan wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo ya yi aikin. 3 Su kuwa sun karɓa daga wurin Musa dukkan baye-bayen da Isra'ilawa suka kawo domin aikin wuri mai tsarki. Duk da haka mutane suna kawo baye-bayen yardar ransu kowacce safiya ga Musa. 4 Sai dukkan mutane masu fasaha suke yin aiki a wuri mai tsarki suka zo daga aikin da suke ta yi. 5 Masu aikin hannu suka faɗa wa Musa, "Mutane suna ta kawo wa fiye da abin da ake buƙata domin aikin da Yahweh ya umarta a yi." 6 Sai Musa ya umarce su kada wani a cikin zango ya sake kawo baiko don aikin wuri mai tsarki. 7 Saboda haka mutane suka dena bada waɗannan kyaututtuka. Sun bada fiye da kayayyakin da ake buƙata domin yin dukkan aikin. 8 Sai dukkan gwanayen mutane a cikin ma'aikatan suka yi rumfa da labule goman da aka yi daga lallausan zanen lilin da shudi da shunayya da mulufi da kuma zanen kerubim. Wannan shine aikin Bezalel, mai babbar fasahar sassaƙa. 9 Tsawon kowanne labule kamu ashirin da takwas, faɗinsa kuma kamu hudu ne. Dukkan labule girmansu ɗaya ne. 10 Bezalel ya haɗa labule biyar ga kowanne ɗayan, sa'an nan kuma ɗayan labule biyar ya kuma haɗa kowanne da ɗan'uwansa. 11 Ya sa maratayai shuɗi a gefen karshen labule na layin, ya sake yin haka har sau biyu. 12 Ya sake sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Saboda haka dukkan maratayan suna daura da juna. 13 Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labulen da juna da maɗauran saboda rumfar sujadar ta zama ɗaya. 14 Bezalel ya yi labulai da gashin awaki domin a rufe rumfar; ya yi waɗannan labulai goma sha ɗaya. 15 Tsawon kowanne labule kamu talatin, faɗinsa kuma kamu huɗu ne. Kowanne ɗaya daga cikin labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne. 16 Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, labule shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya da juna. 17 Sai ya yi hantuna hamsin ya sa a gefe na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa maratayai hamsin a gefen sama na labule na biyu. 18 Bezalel ya yi hamsin maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa maratayan da su domin rumfar ta zama ɗaya. 19 Ya yi wa rumfar marufi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma sake yin wani abin rufewa na fata mai kyau ya hau sama da shi. 20 Bezalel ya yi katakan rumfar da itacen ƙirya. 21 Tsawon kowanne katako kamu goma ne, kaurinsa kuwa kamu ɗaya da rabi ne. 22 Kowanne katako an feƙe bakinsa biyu domin a harhaɗa su tare. Ya yi wannan domin dukkan katakan rumfar. 23 Ya yi katakan rumfar ne ta wannan hanya: ya kafa katakai ashirin domin gefen kudu. 24 Bezalel ya yi kwasfa arba'in da azurfa su shiga ƙarƙashin katakai ashirin. Akwai kuma katako da yana da kwasfa biyu don bakinsa biyu da aka feƙe. 25 Gama na biyun yana wajen arewa da rumfar, ya kafa katakai ashirin, 26 kwasfa arba'insu na azurfa. Akwai katako da yake da kwasfa biyu a ƙarƙashin katakon gaba. 27 Domin bayan rumfar a gefen yamma, Bezalel ya yi tsaikoki shida. 28 Ya yi kuma katakai biyu don kusurwar baya ta rumfar. 29 Waɗannan katakai an raba su tun daga ƙasa, amma an haɗa su a sama a ƙawanya ta fari. Haka ya yi da su kusurwoyin nan biyu. 30 Akwai katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida dukkansu, kowanne katako yana ƙarƙashin na fari, katakai biyu kuma suna ƙarƙashin kwasfa ta gaba. 31 Bezalel ya yi sanduna na itacen ƙirya-sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na rumfar, 32 sanduna biyar kuwa don katakan ɗaya gefen na rumfar, biyar kuma domin katakan da yake bayan rumfar wajen yamma. 33 Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga ƙarshe zuwa ƙarshe. Ya dalaye katakan da zinariya. 34 Ya yi masu ƙawanne na zinariya, don su yi aikin riƙe sarƙafa sandunan, ya kuma dalaye sandunan da zinariya. 35 Bezalel ya yi labule da shuɗi, da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zanen kerubim na aikin gwaninta. 36 Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya, sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi masu maratayai da zinariya don dirkokin kwasfa huɗu da azurfa. 37 Ya yi wa ƙofar rumfar labule da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin ya yi wa labulen ado sosai. 38 Ya kuma haɗa labulen da dirkokinsa biyar. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya. Kwasfansu guda biyar an dalaye su da tagulla.

Sura 37

1 Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, faɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 2 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye har sama. 3 Ya sa ƙawanya huɗu ta zinariya domin kafafunsa huɗu, kawanne biyu a gefensa ɗaya, biyu kuma a ɗaya gefen. 4 Ya yi sandunan da itacen ƙirya ya kuma dalaye su da zinariya. 5 Ya zura sandunan cikin ƙawayun da suke a gefen akwatin don ɗaukarsa. 6 Ya yi murfin kafara da zinariya tsantsa. Tsawonsa kamu biyu da rabi faɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 7 Bezalel ya ƙera siffofin kerubobin biyu da zinariya domin ƙarshen kafara biyu. 8 Kerub ɗaya don ƙarshen kafara, ɗaya kerub kuma domin ƙarshen gefen. An yi su kamar guntu ɗaya ne na murfin. 9 Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwanta murfin da fikakansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kallon tsakiyar murfin kafara. 10 Bezalel ya yi tebur da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu biyu, faɗinsa kamu ɗaya ne, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 11 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya kuma yi masa dajiya da zinariya tsantsa a kewayan samansa. 12 Ya yi masa dajiya mai faɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya a kewaye da ita. 13 Ya yi ƙawanye huɗu na zinariya, ya kuma manna kowanne a kursuwoyi huɗu na ƙafafunsa. 14 Kowannensu na kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin. 15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya, ya kuma dalaye su da zinariya domin ɗaukar teburin. 16 Ya yi kayan da za a ɗora a kan teburin-kwanonin da cokula da kwanonin tuya da butoci waɗanda za ayi baye-baye da su. Ya yi su da zinariya tsantsa. 17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. Ya yi alkuki a gindinsa da gorar jikinsa, ƙoƙunan da mahaɗansa da furanninsa dukkansu a haɗe aka yi da ita. 18 Akwai rassa guda shida daga cikin kowanne gefen-rassa uku daga cikin ɗaya gefen, sa'an nan rassa uku na alkukin daga wancan gefen. 19 Reshe na fari ya yi da ƙoƙuna uku an yi su kamar tohon almond tare da mahaɗai da furanni da kofuna guda uku wanda aka yi kamar almond ya yi fure a kan reshe da mahaɗan furannin. Tana kamar dukkan rassa shidan daga wajen alkuki. 20 A bisa alkukinsa, a tsakiyar ƙyauran, akwai kofuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond da mahaɗai da furanni. 21 Akwai mahaɗi a ƙarƙashin kowanne reshe biyu biyu-an yi su kamar ɗaya da ita, a ƙarƙashin rassa na biyu biyu-haka nan kuma an yi kamar guda ɗaya a haɗe. Ta wannan hanyar akwai mahaɗi a ƙarƙashin rassa na uku, an yi da maɗauri ɗaya. Haka aka yi don dukkan rassa shida daga cikin alkukin. 22 Ganyensu da rassan an yi dukka a maɗauri ɗaya, da ƙerarriyar zinariya tsantsa aka yi kome. 23 Bezalel ya yi alkuki da fitilunsa bakwai da hantsuka da farantansa da zinariya tsantsa. 24 Ya yi alkuki da kayayyakinsa tare da talanti ɗaya da zinariya tsantsa. 25 Bezalel ya yi bagadin ƙona turare. Ya yi ta da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu ɗaya, faɗinsa kamu ɗaya, murabba'i tsayinsa kuma kamu biyu. Ƙahoninsa an yi su kamar ɗaya ne da shi. 26 Ya dalaye bagadin da zinariya tsantsa-bisansa da gefensa da ƙahoninsa. Ya kuma kewaye shi da dajiya ta zinariya. 27 Ya yi masa ƙawanne biyu wanda za a haɗa su da ita a ƙarƙashin dajiya daura da juna. Kowannen su yana riƙe da sandunan da za a ɗauki bagadin. 28 Ya kuma yi sanduna na itacen ƙirya, ya kuma dalayesu da zinariya. 29 Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma tsantsa turare mai ƙanshi yadda mai yin turare ya kan yi.

Sura 38

1 Bezalel ya yi bagadin ƙona baye-baye da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu biyar faɗinsa kamu biyar - murabba'i ne nan - tsayinsa kuwa kamu uku ne. 2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu siffar kamar ƙahonnin takarkari. An yi ƙahonnin su haɗe tare da bagadin, ya dalaye shi da tagulla. 3 Ya yi dukkan kayayyakin domin bagadin-tukwane da cokula da daruna da cokula masu yatsotsi da farantan wuta. Ya kuma yi dukkan kayayyakin da tagulla. 4 Ya yi raga domin bagadin, an yi aikin ne da tagulla aka sa a ƙarƙashin kanta, yasa ta daga ƙasa zuwa sama. 5 Ya sa ƙawanyoyi huɗu domin kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sandunan. 6 Bezalel ya yi sanduna da itacen kirya ya kuma dalaye su da tagulla. 7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawanne na gefen bagadin, don ɗaukar shi. Ya yi bagadin da itace sa'an nan ya raba cikinsa. 8 Bezalel ya yi daron wanka da tagulla da gammonsa na tagulla. Ya yi gammuna daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar rumfar taro. 9 Ya kuma yi haraba. Ya yi labulenta na gefen kudun harabar da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne. 10 Labulai suna da dirkokinsu ashirin, tare da tagulla a ƙarƙashin kwasfan ashirin. Akwai maratayan dirkoki, da maɗaurai da aka yi da azurfa. 11 Kamar yadda yake gefen arewa, akwai labule kamu ɗari da sanduna masu kamu ashirin na tagulla, maɗauran sanduna ƙarafuna na azurfa. 12 Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne. Maɗaurai da dirkokin ƙarafuna na azurfa ne. 13 Tsawon harabar kamu hamsin ne wajen gabas. 14 Labulai na gefe ɗaya na ƙofar kamu goma sha biyar ne. Suna da dirkoki guda uku tare da kwasfan dirkoki uku. 15 A gefen ƙofar farfajiyar akwai labule masu tsawo kamu goma sha biyar da dirkoki uku da kuma kwasfan uku. 16 Dukkan labulai da suke kewaye da harabar an yi su da lallausan zaren lilin. 17 An yi kwasfan dirkoki da tagulla. Maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su ne da azufa. Dukkan dirkokin farfajiyoyin an dalaye su da azurfa, kuma marufan dirkokin suma an yi su da azurfa. Dukkan harabar dirkokan an dalaye su da azurfa. 18 Labulan ƙofar harabar kamu ashirin tsayinsa. Labulen an yi su da shudi da na shunayya da na mulufi da na lallausan zaren lilin. 19 Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar dai-dai da labulen haraba. An yi dirkokin labulen guda huɗu da kwasfan dirkoki na azurfa. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa. 20 Dukkan turakun rumfa da harabar an yi su da tagulla, 21 Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi na rumfa, rumfar alƙawarin ka'idodi, kamar yadda aka yi bisa ga yadda Musa ya yi umarni. Wannan aikin Lebiyawa ne a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna firist. 22 Bezalel ɗan Uri ɗan Hur daga kabilar Yahuda, an yi dukkan abin da Yahweh ya umarci Musa. 23 Oholiyab ɗan Ahisamak daga kabilar Dan, wanda ya yi aiki tare da Bezalel gwani ne, cikakken ma'aikacin zane-zane da ɗinki na shuɗi, da na shunayya da na mulufi da na lallausan zaren lilin. 24 Dukkan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita don wannan aiki, a cikin dukka aikin wanda ya haɗa da wuri mai tsarki - zinariya daga baikon bankwana - talanti ashirin da tara ne da awo 730 bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 25 Azurfar da aka samu ta wurin taron mutane awonsa talanti ɗari ne da awo 1,775, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, 26 ko kowanne mutum da aka ƙidaya ya bada rabin awo. Wannan adadin abin da aka samu bisa kowanne mutum wanda aka ƙidaya ta ƙasa, waɗanda sun kai 603,550 daga shekara ashirin zuwa gaba manya da tsoffafi na dukkan maza. 27 An yi amfani da azurfa talanti ɗari domin yin kwasfa don wuri mai tsarki da labule-an yi kwasfa ɗari da talanti ɗaya don kowanne kwasfa. 28 Sauran 1,775 na awon azurfa, Bezalel yayi maratayan dirkokin, ya dalaye saman maratayan dirkoki ya kuma yi da ƙarafuna dominsu. 29 Tagulla daga abin da aka bayar kuwa talati saba'in da awo 2,400. 30 Tare da wannan ya yi kwasfa domin ƙofar rumfar taruwa, da tagullar bagadi, da tagulla aka yi ragarsa, da dukkan kayayyakin bagadin, 31 Kwasfa domin harabar, da kwasfa don ƙofar harabar, da dukkan turakun don rumfar sujada da na dukkan turakun harabar.

Sura 39

1 Tare da shuɗi da shunayya da mulufi, suka ɗinka tufafi masu kyau domin aiki a wuri mai tsarki. Sun yi wa Haruna tsarkakun tufafi domin wuri mai tsarki, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 2 Bezalel ya yi falmarar da zinariya, da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin. 3 Suka buga zinariya falle-falle, suka yanyanka ta zare-zare don su yi aikin saƙa da ita tare da zane na shuɗi da shunayya da mulufi da kuma na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha ne. 4 Suka yi aikin kafaɗu domin falmara, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama. 5 An yi anfani da ɗamarar falmarar ta saƙa mai kyau; da irin kayan da aka saƙa falmara ne aka saƙa su da zinariya da shuɗi da shunayya da mulufi da zane lallausan lilin, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 6 Sun gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su a tsaiko, aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu. 7 Bezalel ya sa a kan kafaɗun falmarar don su zama duwatsun tunawa da Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 8 Ya kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, an yi amfani da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmarar. Ya yi ta da zinariya da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin. 9 Tana nan murabba'i. An yi ƙyallen maƙalawa a kirji riɓi biyu. tsawonsa da faɗinsa kamu ɗaya ne. 10 Suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. Jeri na fari aka sa yakutu da tofaz da ganat. 11 A jeri na biyu aka sa emeral da saffir da lu'u-lu'u. 12 A jeri na uku aka sa yakinta da idon mage da ametis. 13 A jeri na huɗu aka sa beril da onis da yasfa. Duwatsun an yi masu maɗauki da zinariya. 14 An jera duwatsun bisa sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu, kowanne bisa ga yadda sunansa yake. Suna kamar yadda a kan yi hatimin zoɓe, kowanne suna ya tsaya domin ɗaya daga cikin kabilu goma sha biyu. 15 A kan kirjin sai suka yi tukakkun sarƙoƙi kamar igiyoyin amara da aikinsa zinariya tsantsa. 16 Sai suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawanyu biyu na zinariya, suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 17 Suka kuma zura sarkokin nan biyu na zinariya a kowannen biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 18 Sai suka maƙala waɗancan a bakin sarƙoƙin biyu. Sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmarar daga gaba. 19 Suka yi ƙawanne biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na kyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran. 20 Suka yi waɗansu ƙawanne biyu na zinariya, suka maƙala su kusa a gaban kafaɗu biyu na falmarar kusa da mahaɗin a bisa abin damarar falmarar. 21 Sai suka ɗaure ƙawanyun kyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanyun falmarar da shuɗiyar igiya saboda kyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin damarar. An yi wannan don kada falmarar ya kwance daga ƙirjin falmarar. Wannan ya faru ne kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 22 Bezalel ya saka taguwa ta falmaran da shuɗi ga baki ɗaya, aikin masaƙi ne. 23 An yi wa taguwar wuya wurin sa kai a tsakiya. An yi wa wayan saƙa saboda kada ta yage. 24 A ƙasan taguwar, sai suka yi fasalin 'ya'yan rumman da shuɗi, shunayya, da mulufi da lallausan lilin. 25 Suka yi kararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin rumman dukka kewaye a ƙasa da bakin igiyar, tsakanin rumman -- 26 an sa ƙararrawa da rumman, ƙararrawar da rumman -- a bakin igiya domin Haruna ya yi hidima a ciki. Wannan bisa ga yadda Yahweh ya umarci Musa. 27 Suka saƙa janfofi da lallausan zaren lilin saboda Haruna da 'ya'yansa. 28 Suka kuma yi rawani da lallausan lilin, da huluna da mukura da lallausan lilin, da mukurai da lallausan lilin. 29 Sun kuma yi abin damara da lallausan lilin mai launin shuɗi da shunayya da mulufi, an yi mata dinkin ado. Wannan an yi shi kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zana rubutu a kan ta, irin na hatimi a kanta, "Mai Tsarki ga Yahweh." 31 Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin. Wannan an yi shi yadda Yahweh ya umarci Musa. 32 Haka kuma aka yi aikin rumfar sujada, da rumfar taruwa, kuma an gama ta. Mutanen Isra'ila suka yi shi dukka. Suka bi dukkan umarnin da Yahweh ya ba Musa. 33 Suka kawo wa Musa rumfar sujada - rumfar da dukkan kayayyakinta, maratayanta da katakanta da sandunanta da dirkokinta da kwasfanta 34 da murfi na jan fatun raguna da na awaki da labulen rufewa 35 da akwatin alƙawari da sandunansa da murfin kafara. 36 Suka kawo tebur da dukkan kayayyakinsa da gurasar ajiyewa 37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa, tare da kayayyakinsa da mai domin fitilu 38 da bagadin zinariya da mai na keɓewa da turare mai ƙanshi da labulen ƙofar rumfar sujada 39 da bagadin tagulla da ragarsa ta tagulla da sandunansa da kayayyakinsa da daro da gammonsa. 40 Suka kawo labulen harabar da dirakunta da kwasfanta da labulen ƙofarta da igiyoyinta da turakunta da dukkan kayayyaki don aiki a rumfar sujada da rumfar taruwa. 41 Suka kawo tufafin ado na aiki a wuri mai tsarki da tsarkakan tufafin domin Haruna firist da tufafin 'ya'yansa maza, domin su yi aiki a matsayin firistoci. 42 Mutanen Isra'ila suka yi dukkan wannan aiki yadda Yahweh ya umarci Musa. 43 Musa ya duba dukkan aikin, duba, sun yi shi dai-dai. Yadda Yahweh ya umarta, ta wannan hanya suka yi shi. Sai Musa ya sa masu albarka.

Sura 40

1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "A kan rana ta fari a wata na fari a sabuwar shekara dole ka kafa rumfar sujada, rumfar taruwa. 3 Ka sa akwatin alƙawari a cikin ta sa'an nan ka kare akwatin da labule. 4 Ka shigar da tebur, ka shirya shi yadda ya kamata da kayayyakinsa dai-dai. Ka kuma shigar da alkukin da fitilu a bisansa. 5 Ka ajiye bagadi na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alƙawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar rumfar sujada. 6 Ka ajiye bagadi na yin baikon ƙonawa a gaban ƙofar rumfar taruwa. 7 Ka kuma ajiye daro tsakanin rumfar taruwa da bagadin sa'an nan ka zuba ruwa a cikin shi. 8 Ka yi harabar ka kewaye ta, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar harabar. 9 Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa rumfar sujada da kome dake cikinta. Ka tsarkake ta da dukkan kayayyakinta gare ni, ta kuma zama tsarkakkiya. 10 Ka shafe bagadin domin ƙona hadaya da dukkan kayayyakinsa. Za ka tsarkake bagadin a gare ni, zai zama mafi tsarki gare ni. 11 Ka shafa wa daron tagulla da mazauninsa man keɓewa a gare ni. 12 Ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar rumfar taruwa, kuma dole ka yi masu wanka da ruwa. 13 Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi masu tsarki ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mani aikin firist. 14 Ka kawo 'ya'yansa maza, ka kuma sa masu taguwoyi. 15 Sa'an nan ka shafe su da mai kamar yadda ka shafe mahaifinsu saboda su yi mani aiki a matsayin firistoci. Shafe su da man zai sa su zama firistoci din-din din cikin dukkan tsararrakin mutanen su. 16 Wannan shine abin da Musa ya yi; ya bi dukkan umarnin da Yahweh ya ba shi. Ya yi dukkan waɗannan abubuwa. 17 Sai aka kafa rumfar sujadar a kan rana ta fari a wata na fari a sheka ta biyu. 18 Musa ya kafa rumfar sujadar, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta. 19 Sa'an nan ya baza shinfiɗa a bisa rumfar sujadar ya sanya rumfa a bisan ta, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 20 Sai ya ɗauki dokokin alƙawaran ka'idodi ya sa a cikin akwatin. Ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin kafara a bisansa. 21 Ya kawo akwatin a cikin rumfar sujada. Sa'an nan ya sa labulen domin kare akwatin alƙawari yadda Yahweh ya umarce shi. 22 Ya sa teburin cikin rumfar taruwa, a wajen gefen arewa na rumfar sujada, a wajen labulen. 23 Sai ya jera gurasa a kan teburin a gaban Yahweh, yadda Yahweh ya umarce shi. 24 Ya kuma sa alkukin a cikin rumfar taruwa, daura da gaban tebur, a wajen kudu na rumfar sujada. 25 Ya kunna fitilu a gaban Yahweh, yadda Yahweh ya umarce shi. 26 Sai ya sa zinariyar turaren bagadi a cikin rumfar taruwa a gaban labule. 27 Ya ƙona turare a kanta, yadda Yahweh ya umarce shi. 28 Ya sa labule a ƙofar rumfar sujada. 29 Ya kuwa sa bagadi domin ƙona hadaya a ƙofar rumfar sujada da rumfar taruwa. Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa da hadayar gari, yadda Yahweh ya umarce shi. 30 Ya sa daro a tsakanin rumfar taruwa da rumfar sujada, ya kuma sa ruwa a cikinta domin wankewa. 31 Musa da Haruna da 'ya'yansa maza su kan wanke hannuwansu da ƙafafuwansu daga daron, 32 sa'ad da suke shiga cikin rumfar taruwa, da sa'ad da su kan tafi bisa bagadi, yadda Yahweh ya umarci Musa. 33 Musa kuwa ya yi haraba kewaye da rumfar sujada da bagadin. Ya sa labulen ƙofar harabar. Ta wannan hanya, Musa ya gama aikin. 34 Sa'ad da girgije ya rufe rumfar taruwar, sai ɗaukakar Yahweh ta cika rumfar sujada. 35 Musa kuwa bai iya shiga rumfar taruwa ba gama girgijen yana zaune a bisanta, kuma saboda ɗaukakar Yahweh ta cika rumfar sujadar. 36 Duk lokacin da aka ɗauke girgijen daga kan rumfar sujadar, mutanen Isra'ila su kan kama hanya domin tafiya. 37 Amma idan girgijen bai tashi daga rumfar sujadar ba, mutanen ba za su iya tafiya ba. Za su tsaya har ranar da ya tashi. 38 Gama girgijen Yahweh yana bisa kan rumfar sujada da rana, haka nan wutarsa ta na bisan shi da dare, wannan ya sa dukkan mutanen Isra'ila suka yi tafiyarsu ko'ina.

Littafin Lebitikus
Littafin Lebitikus
Sura 1

1 Yahweh ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin rumfar taruwa, ya ce, 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana ka gaya masu cewa, 'Sa'ad da waninku ya kawo baiko ga Yahweh, sai ya kawo baikon dabbar daga cikin dabbobinsa, daga garken shanu ko kuma na tumaki. 3 Idan baikonsa baiko ne na ƙonawa daga garken shanu, dole ya miƙa namiji marar lahani. Zai miƙa shi a ƙofar rumfar taruwa, domin ya zama karɓaɓɓe a gaban Yahweh. 4 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko na ƙonawar, sa'an nan za a karɓa daga gare shi a yi masa kaffara domin shi kansa. 5 Dole ne ya yanka bijimin a gaban Yahweh. 'ya'yan Haruna maza, firistoci, zasu miƙa jinin su yayyafa shi a kan bagadi wanda ya ke a bakin ƙofar rumfar taruwa. 6 Sa'an nan dole ya feɗe baikon ƙonawar ya kuma yanyanka shi gunduwa-gunduwa. 7 Sa'an nan 'ya'ya maza na Haruna firist zasu kunna wuta a kan bagadin su sa itace domin iza wutar. 8 'Ya'yan Haruna maza, firistoci zasu jera gunduwa-gunduwar nan, za su sa kan da fari sa'an nan kitsen a jere haka a kan itacen da ke bisa wutar da ke kan bagadi. 9 Amma kayan cikinsa da ƙafafuwansa dole ya wanke su da ruwa. Sa'an nan firist zai ƙona dukka a kan bagadi a matsayin baiko na ƙonawa. Zai ba da ƙamshi mai daɗi a gare ni; zai zama baikon da aka yi mani da wuta. 10 Idan baikonsa domin baiko na ƙonawa ne daga cikin garke, ɗaya daga cikin tumaki ko ɗaya daga cikin awaki, dole ya miƙa namiji marar lahani. 11 Dole ya yanka shi a arewacin bagadin a gaban Yahweh. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, zasu yayyafa jinin a kowanne gefen bagadin. 12 Sa'an nan dole zai yanka shi gunduwa-gunduwa, tare da kansa, da kuma kitsensa, firist zai jera su dai-dai akan itace da ke kan wuta, wadda take kan bagadi, amma kayan ciki da ƙafafun dole ya wanke su da ruwa. 13 Sa'an nan firist zai miƙa dukka, ya ƙona shi a kan bagadin. baiko na ƙonawa ne, zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta. 14 Idan baikonsa ga Yahweh zai zama baiko na ƙonawa na tsuntsaye, to dole ya kawo baikon kurciya ko 'yar tantabara. 15 Dole firist ya kawo shi ga bagadi, ya murɗe kansa, ya ƙona shi a kan bagadin. Sa'an nan dole a tsiyaye jininsa a gefen bagadin. 16 Dole ya cire ƙururunsa da abin da ke cikinsa, ya jefar da shi a gabashin bagadin a gefe, wurin da ake zuba toka. 17 Dole ya tsaga shi biyu ya buɗe shi daga fukafukansa, amma ba zai raba shi biyu ba. Sa'an nan firist zai ƙona shi a kan bagadin, a kan itacen da ke kan wuta. Zai zama baiko na ƙonawa, kuma zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baiko da aka yi masa da wuta.

Sura 2

1 Sa'ad da wani ya kawo baikon hatsi ga Yahweh, dole ne baikonsa ya zama na gari mai laushi, kuma ya zuba mai a kai ya sa turare a kai. 2 Zai kai baikon ga 'ya'yan Haruna maza firistoci, a can firist zai ɗibi tafi guda na garin mai laushi tare da mai da turare da ke kansa. Sa'an nan firist zai ƙona baikon a kan bagadin baiko na tunawa kenan. Zai ba da ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta. 3 Duk ragowar baiko na garin hatsi zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza. Mafi tsarki ne sosai ga Yahweh domin daga baye-baye ne da aka yi wa Yahweh da wuta. 4 Sa'ad da kuka miƙa baiko na garin hatsi da babu gami da aka toya a tanda, dole ya zama waina mai laushi da aka yi da lallausar gari cuɗe da mai, ko waina mai tauri da bata da gami, da aka yayyafa mata mai. 5 Idan baikonku na garin hatsi an toya shi a tandar ƙarfe ne, dole ya zama gari mai laushi marar gami cuɗaɗɗe da mai. 6 Za ku yanyanka shi gunduwa-gunduwa a zuba mai a kai. Wannan shi ne baiko na hatsi. 7 Idan baikonku na garin hatsi an dafa a tukunyar tuya ne, dole a yi shi da gari mai laushi da mai. 8 Dole ku kawo baiko na garin hatsi da aka yi su daga waɗannan abubuwa ga Yahweh, za a kuma miƙa su ga firist, wanda zai kawo su wurin bagadi. 9 Sa'an nan firist zai ɗauki wasu daga baiko na garin hatsin domin ya zama baikon madadi, zai kuma ƙona su a kan bagadin. Zai zama baikon da aka yi da wuta, zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. 10 Ragowar baikon garin hatsi zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza. Abu ne mafi tsarki ga Yahweh daga cikin baye-baye da aka yi ga Yahweh da wuta. 11 Kada baiko na garin hatsi da za ku miƙa wa Yahweh ya zama da gami, gama ba za ku ƙona gami ba, ko zuma, a baikon da aka yi da wuta ga Yahweh. 12 Za ku miƙa su ga Yahweh a madadin baikon nunar fari, amma ba za a yi amfani da su don su bada ƙamshi mai daɗi a kan bagadi ba. 13 Dole kowanne baye-bayenku na garin hatsi a sa masa ɗanɗanon gishiri. Kada ku fasa sa gishiri na alƙawari na Allahnku a cikin baikonku na garin hatsi. Cikin dukkan baye-bayenku dole ku miƙa gishiri. 14 Idan kuka miƙa baikon hatsin nunar fari ga Yahweh, ku miƙa sabon hatsi wanda aka gasa da wuta sa'an nan aka ɓarza, 15 Sai ku sa mai da turare a kai. Wannan shi ne baiko na garin hatsi. 16 Sa'an nan firist zai ƙona wasu daga cikin ɓarzajjen hatsin da mai da turare sun zama baiko na madadi. Wannan baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh.

Sura 3

1 Idan wani ya miƙa hadayarsa wanda baiko ne na zumunta na dabba daga garken shanu, ko namiji ko mace, dole ya miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Yahweh. 2 Zai ɗibiya hannusa a kan baikonsa ya yanka ta a ƙofar rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza firistoci zasu yayyafa jinin kewaye da bagadin. 3 Mutumin zai miƙa hadayar baiko na zumunta da wuta ga Yahweh.‌ Ƙitsen da ya rufe ko kuma da ke haɗe da kayan ciki, 4 da ƙodoji biyu, da ƙitsen da ya ke kansu a wajen kwiɓi, da na taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai cire dukkan waɗannan. 5 'Ya'yan Haruna maza zasu ƙona wannan a kan bagadi tare da baiko na ƙonawa, wanda ya ke a kan itacen da ya ke kan wuta. Wannan zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta. 6 Idan hadayar mutumin baikon zumunta ne ga Yahweh daga cikin garken tumaki; namiji ko mace, dole ya miƙa hadaya marar lahani. 7 Idan ya miƙa ɗan rago domin hadaya, to dole ya miƙa shi a gaban Yahweh. 8 Zai ɗibiya hannunsa a kan hadayar ya yanka shi a gaban rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza zasu yayyafa jinin kewaye da bagadin. 9 Mutumin zai miƙa hadayar baye-bayen zumunta domin baiko da aka yi da wuta ga Yahweh. Kitsen, dukkan kitse na wajen wutsiya da aka yanke kusa da ƙashin baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki da dukkan kitsen da ke kusa da kayan ciki, 10 da kuma ƙodojin biyu da kitsen da ke tare da su, wanda ke kusa da kwiɓi, da na taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai cire duk waɗannan. 11 Sa'an nan firist zai ƙona su dukka a kan bagadi ya zama baiko na ƙonawa na abinci ga Yahweh. 12 Idan baikon mutumin akuya ce, to zai miƙa ta a gaban Yahweh. 13 Dole ya ɗibiya hannunsa a kan akuyar ya yanka ta a gaban rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza za su yayyafa jinin kewaye da bagadi. 14 Mutumin zai miƙa hadayarsa da ya yi da wuta ga Yahweh. Zai cire kitsen da ya rufe kayan ciki, da kuma dukkan kitsen da ke kusa da kayan cikin. 15 Zai kuma cire ƙodojin biyu da kitsen da ke tare da su, wanda ke wajen kwiɓi, da wajen taiɓar hanta tare da ƙodoji. 16 Firist zai ƙona dukkan waɗannan a kan bagadi ya zama baiko na ƙonawa na abinci, da zai bada ƙamshi mai daɗi. Duk kitsen ya zama na Yahweh. 17 Zai zama madawwamin farilla ga dukkan tsararrakin jama'arku a ko'ina da kowanne wuri da kuka maida shi mazauninku, cewa ba za ku ci kitse ba ko jini.'"

Sura 4

1 Yahweh ya yi wa Musa magana, ya ce, 2 "Ka gaya wa mutanen Isra'ila, 'Lokacin da wani ya yi zunubi ba da niyyar yin zunubi ba, ya yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya dokata kada a yi, idan ya yi abin da aka hana, ga abin da dole za a yi. 3 Idan babban firist ne ya yi zunubin har ya kawo laifi a kan jama'a, domin zunubinsa da ya aikata sai ya miƙa ɗan maraƙi marar lahani ga Yahweh baiko don zunubi kenan. 4 Dole ya kawo bijimin ƙofar rumfar taruwa a gaban Yahweh, ya ɗibiya hannunsa a kansa, ya yanka shi a gaban Yahweh. 5 Keɓaɓɓen firist zai ɗiba daga jinin bijimin ya kai rumfar taruwa. 6 Firist zai tsom‌a ɗan yatsansa cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Yahweh, a gaban labulen wuri mafi tsarki. 7 Sa'an nan firist zai sa daga jinin a ƙahonnin bagadin na turare mai ƙamshi a gaban Yahweh, wanda ya ke cikin rumfar taruwa, zai kuma zuba dukkan sauran jinin bijimin a gindin bagadi domin baye-baye na ƙonawa, wanda ya ke a ƙofar rumfar taruwa. 8 Zai yaɗe dukkan kitsen bijimin baiko don zunubi; kitsen da ya rufe kayan ciki, da dukkan kitsen da ke manne da kayan ciki, 9 da ƙodojin biyu da kitsen da ke bisansu, wanda ke wajen kwiɓi, da taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai yanke duk wannan. 10 Zai yanke shi dukka, kamar yadda ya yanke shi daga bijimi na hadayar baye-baye ta salama. Sa'an nan firist zai ƙona waɗannan ɓangare akan bagadin baye-bayen ƙonawa. 11 Fatar bijimin da duk sauran naman, da kan da ƙafafunsa da kayan cikinsa da kashinsa, 12 da dukkan sauran sashen bijimin - zai ɗauki dukkan waɗannan ya kai bayan sansani wurin da aka tsarkake domina, inda ake zuba toka; zasu ƙona waɗannan a bisa itace. Dole su ƙona waɗannan ragowar bijimin inda suke zubar da toka. 13 Idan dukkan taron Isra'ila suka yi zunubin da ba na ganganci ba, kuma taron ba su san sun yi zunubi ba idan suka yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya umarta kada su yi, idan sunyi laifin, 14 sa'annan, yayin da zunubin da suka aikata ya zama sananne, dole taron su miƙa ɗan bijimi baiko wato baiko don zunubi a kuma kawo shi gaban rumfar taruwa. 15 Dattawan taro zasu ɗibiya hannuwansu a bisa kan bijimin a gaban Yahweh, za a yanka bijimin a gaban Yahweh. 16 Keɓaɓɓen firist zai kawo daga jinin bijimin zuwa rumfar taruwa, 17 firist kuma zai tsoma yatsansa cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Yahweh, a gaban labule. 18 Zai sa daga jinin a ƙahonnin bagadin da ke gaban Yahweh, wanda ya ke cikin rumfar taruwa, zai kuma zuba jinin dukka a gindin bagadin baye-baye na ƙonawa, wanda ya ke a kofar rumfar taruwa. 19 Zai ɗebe dukkan ƙitsen daga gare shi ya ƙona a kan bagadi. 20 Wannan shi ne abin da zai yi dole da bijimin. Kamar yadda ya yi da bijimin baiko don zunubi, haka kuma zai yi da wannan bijimin, firist kuma zai yi kaffara domin mutane, za a kuma gafarta masu. 21 Zai ɗauki bijimin ya kai shi bayan zango ya ƙona kamar yadda ya ƙona bijimi na farko. Wannan shi ne baiko don zunubi saboda taron. 22 Sa'ad da shugaba ya yi zunubi ba dagangan ba, har ya yi ɗaya daga cikin dukkan abubuwan da Yahweh Allahnsa ya umarta ka da a yi, kuma ya yi laifin, 23 sai aka sanar da shi a kan zunubin da ya aikata, dole ya kawo hadayarsa ta akuya, bunsuru marar lahani. 24 Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun ya yanka shi inda aka yanka baiko na ƙonawa a gaban Yahweh. Wannan shi ne baiko domin zunubi. 25 Firist zai tsoma ɗan yatsansa cikin jinin baiko domin zununbi ya sa shi a ƙahonnin bagadin domin baye-baye na ƙonawa, sai ya kuma zuba jinin a gindin bagadin baiko na ƙonawa. 26 Zai ƙona dukkan kitsen a kan bagadi, dai-dai kamar na kitsen hadayar baye-baye na salama. Firist zai yi kafara domin shugaban game da zunubinsa, za a kuwa gafarta wa shugaban nan. 27 Idan wani talaka ya yi zunubi ba dagangan ba, sai ya yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya umarta kada a yi, idan ya gane laifinsa, 28 sa'an nan za a bayyana masa zunubinsa, sai ya kawo akuya domin hadayarsa, ta mace marar lahani, domin zunubin da ya aikata. 29 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko domin zunubi ya kashe baikon don zunubin a wurin yin baiko na ƙonawa. 30 Firist zai lakuto daga jinin a yatsansa ya sa a ƙahonnin bagadi domin baye-baye na ƙonawa. Zai zuba dukkan sauran jinin a gindin bagadin. 31 Zai yaɗe dukkan kitsen, dai-dai kamar yadda ya yaɗe kitsen da ke kan hadayar baye-baye na salama. Firist zai ƙona su a kan bagadi domin ya bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Firist zai yi kaffara domin mutumin, za a kuwa gafarta masa. 32 Idan mutumin ya kawo ɗan rago domin hadayarsa ta baiko domin zunubi, zai kawo mace marar lahani. 33 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko domin zunubi sai kuma a yanka ta saboda baiko domin zunubi a inda aka yanka baiko na ƙonawa. 34 Firist zai ɗiba daga jinin baiko domin zunubi a ɗan yatsansa yasa su a kan ƙahonnin bagadi domin baye-baye na ƙonawa, zai zuba dukkan jinin a gindin bagadi. 35 Zai yaɗe dukkan kitsen, kamar yadda aka yaɗe kitsen ɗan rago daga hadayar baye-bayen salama, firist zai ƙona shi a kan bagadi a bisa baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta. Firist zai yi kaffara saboda shi domin zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin.

Sura 5

1 Idan wani ya yi zunubi domin bai bada shaida ba sa'ad da ya ga wani abu game da abin da yakamata ya yi shaida, ko ya gani, ko kuwa yaji akan abin, za a kama shi da laifi. 2 Ko wani ya taɓa wani abin da Allah ya haramta shi marar tsarki, ko mushen haramtacciyar dabbar jeji ko ta gida da ta mutu, ko dabba mai rarrafe, ko da mutumin bai yi niyyar taɓa ta ba, ya ƙazamtu, ya kuma zama da laifi. 3 Ko kuma idan ya taɓa ƙazamtar wani mutum, ko ma mene ne ƙazamtar, idan har bai sani ba, zai zama da laifi bayan an sanar da shi. 4 Ko kuma wani ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa zai yi mugunta, ko ya yi nagari, ko mene ne mutum ya rantse da garaje, ko ma dai da rashin saninsa, idan an sanar da shi, zai zama da laifi a cikin abubuwan nan. 5 Idan wani yana da laifi ko da guda ɗaya ne daga cikin waɗannan abubuwa, dole ya furta kowanne zunubi da ya aikata. 6 Dole ya kawo wa Yahweh baiko na laifi domin zunubin da ya aikata, dabba mace daga cikin garke ko ɗan rago ko akuya, domin baiko na zunubi, firist kuma zai yi kaffara dominsa game da zunubinsa. 7 Idan ba zai iya sayan ɗan rago ba, sai ya kawo baikonsa na laifi domin zunubinsa kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu ga Yahweh, ɗaya domin baiko na laifi ɗaya kuma domin baiko na ƙonawa. 8 Dole ya kawo su ga firist, wanda zai miƙa ɗaya domin baiko domin zunubi da fari - zai murɗe kan daga wuya amma ba zai cire shi ɗungum daga jikinsa ba. 9 Sa'an nan zai yayyafa kaɗan daga cikin jinin baikon domin zunubi a gefen bagadi, sauran jinin zai tsiyayar a gindin bagadi. Wannan shi ne baiko domin zunubi. 10 Sa'an nan dole ya miƙa tsuntsu na biyu domin baiko na ƙonawa, kamar yadda aka bayyana a cikin farillai, sai firist kuma ya yi masa kaffara domin zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin. 11 In kuwa ba zai iya sayan kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu ba, sai dole ya kawo hadaya domin zunubinsa tiya biyu na gari mai laushi saboda baiko domin zunubi. Ba zai sa mai ko turare a kai ba, saboda baiko ne domin zunubi. 12 Dole ne ya kawo shi ga firist, firist kuma zai ɗiba dai-dai tafin hannu ya zama baiko domin tunawa Sa'an nan zai ƙona shi a kan bagadi, a bisa baye-baye da aka yi da wuta domin Yahweh. Wannan baiko domin zunubi kenan. 13 Firist zai yi kaffara domin kowanne zunubin da mutumin ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin nan. Duk ragowa daga baikon zai zama rabon firist, kamar dai baiko na hatsi.'" 14 Sa'an nan Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa, 15 "Idan wani ya yi zunubi ya aikata rashin aminci game da abubuwan da ke na Yahweh, amma ba dagangan ba, to dole ya kawo baiko domin laifi ga Yahweh. Wannan baiko dole ya zamana rago marar lahani daga garken tumaki; za a lisafta tamaninsa da ma'aunin azurfar - ma'auni na masujada - domin baiko na laifi. 16 Dole ya gamshi Yahweh domin abin da ya yi marar kyau game da abu mai tsarki, dole kuma ya ƙara kashi ɗaya cikin biyar a kai domin ya ba firist. Sa'an nan firist zai yi masa kafara da ragon baiko na laifi, za a kuwa gafarta wa mutumin nan. 17 Idan wani ya yi zunubi har ya yi wani abin da Yahweh ya bada doka kada a yi, idan ma bai ankara da yinsa ba, duk da haka ya yi laifi dole ne ya amsa laifinsa. 18 Dole ya kawo rago marar lahani daga cikin garke, dai-dai tamanin kuɗinsa a yanzu, domin baiko domin laifi ga firist. Sa'an nan firist zai yi masa kaffara game da zunubin da ya aikata, wanda ya yi da rashin sani, za a kuwa gafarta masa. 19 Baiko ne domin laifi, kuma hakika yana da laifi a gaban Yahweh."

Sura 6

1 Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa, 2 "Idan wani ya yi abin rashin aminci gãba da Yahweh ta wurin yaudarar makwabcinsa game da wani abin da aka bashi riƙon amana, ko game da wani abin da aka sace, ko dai ya yi ta zaluntar makwabcinsa, 3 ko ya tsinci abin da makwabcinsa ya ɓatar ya yi musu a kansa, ya kuma rantse a kan ƙaryar, ko duk dai cikin abubuwa makamantan haka da mutane ke zunubi, 4 idan ya zamana ya yi zunubi, har aka same shi mai laifi ne, dole ne ya mayar da abin da ya karɓe da ƙwace ko ta hanyar zalunci, ko ta ajiyar da aka bashi riƙon amana ko ta abin da ya ɓace ya kuma tsinta. 5 Bugu da ƙari, a cikin kowanne al'amari da ya rantse a kan karya, dole ya mayar cif yadda ya ke ya kuma ƙara kashi ɗaya cikin biyar na tamanin abin da ya biya dukka ga mai ita a ranar da aka kama shi da laifi. 6 Sa'an nan zai kawo wa Yahweh baiko na laifinsa, rãgo marar lahani daga cikin garke wanda tamaninsa haka ya ke a kasuwa, domin baiko na laifi ga firist. 7 Firist zai yi masa kaffara a gaban Yahweh, za a kuma gafarta masa game da duk wani laifi da ya yi." 8 Sa'an nan Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa, 9 "Ka dokaci Haruna da 'ya'yansa maza, cewa, 'Wannan ita ce dokar baiko na ƙonawa: Dole baiko na ƙonawa ya kasance a kan garwashin wutar bagadi dukkan dare har safiya, kuma wutar bagadin za a dinga izata tayi ta ci. 10 Firist zai sanya rigunansa na lilin, zai kuma sa ƙananan kaya 'yan ciki na lilin. Zai kwashe tokar da ta rage bayan wuta ta cinye baiko na ƙonawa da ke kan bagadi, zai kuma sa tokar a gefen bagadin. 11 Zai tuɓe rigunansa ya sa wasu rigunan domin ya kai tokar bayan zango a wuri mai tsabta. 12 Wutar da ke kan bagadi za a dinga iza ta. Ba za a barta ta mutu ba, firist zai yi ta ƙona itace a kanta kowacce safiya. Zai shirya baiko na ƙonawa yadda ya kamata a bisansa, a kansa zai ƙona kitsen baye-baye na salama. 13 Dole a sa wuta ta yi ta ci a kan bagadin ba fasawa. Kada a bari ta mutu. 14 Wannan ita ce shari'a ta baiko na hatsi. 'Ya'yan Haruna maza zasu miƙa shi a gaban Yahweh a gaban bagadi. 15 Firist zai ɗibi tafin hannu na lallausar gari daga cikin baiko na garin hatsi da na mai da kuma turare wanda ya ke a kan baiko na garin hatsi, zai ƙona shi a kan bagadin domin ya bada ƙamshi mai daɗi domin baiko na madadi. 16 Haruna da 'ya'yansa maza zasu ci duk abin da ya rage daga baikon. Dole a ci shi ba gami a wuri mai tsarki. Za su ci shi a harabar rumfar taruwa. 17 Ba za a toya shi da gami ba. Na ba su wannan kason ya zama nasu rabon daga nawa baye-baye da aka yi mani da wuta. Abu ne mafi tsarki, kamar baiko domin zunubi da baiko domin laifi. 18 Domin dukkan lokatai masu zuwa dukkan tsararrakin mutanenku, kowanne ɗa namiji daga zuriyar Haruna zai iya cin rabonsa, daga baye-baye ga Yahweh da aka yi da wuta. Duk wanda ya taɓa su zai tsarkaka.'" 19 Sai Yahweh ya sake yin magana da Musa, cewa, 20 "Wannan shi ne baikon Haruna da 'ya'yansa maza, wanda zasu miƙa wa Yahweh a ranar da aka keɓe kowanne ɗa: kashi ɗaya cikin goma na garwar lallausar gari domin baiko na hatsi koyaushe, rabinsa da safe rabi kuma da maraice. 21 Za a yi shi da mai a kaskon tuya. Sa'ad da aka jiƙa shi, za ku kawo shi ciki. A toye curi-curi za ku miƙa baiko na garin hatsi domin ya bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. 22 ‌Ɗan babban firist wanda zai gaji babban firist daga cikin 'ya'yansa zai miƙa shi. Kamar yadda aka umarta har abada, za a ƙona shi dukka ga Yahweh. 23 Kowanne baiko na garin hatsi na firist za a ƙona shi ƙurmus. Ba za a ci shi ba." 24 Yahweh ya sake yin magana da Musa, cewa, 25 "Ka yi wa Haruna da 'ya'yansa maza magana, cewa, "Wannan ita ce dokar baiko domin zunubi: Dole a kashe baiko domin zunubi inda aka kashe baiko na ƙonawa a gaban Yahweh. Abu ne mafi tsarki. 26 Firist da ya miƙa shi don zunubi zai ci shi. Dole a ci shi a wuri mai tsarki a harabar rumfar taruwa. 27 Duk abin da ya taɓa naman zai zama da tsarki, kuma idan aka yayyafa jinin akan wata riga, dole ku wanke ta, wannan shashen da ya ɗiga a kai, a wuri mai tsarki. 28 Amma tukunyar yunɓun da aka dafata a ciki dole a fashe ta. Idan an dafa ne a tukunyar ƙarfe, dole ne a kankare ta a ɗauraye ta cikin ruwa mai tsabta. 29 Kowanne ɗa namiji daga cikin firistoci zai iya ci daga ciki domin mafi tsarki ne. 30 Amma kowanne baiko domin zunubi wanda aka kawo jininsa a rumfar taruwa domin a yi kaffara a wuri mai tsarki ba za a ci shi ba. Dole ne a ƙona shi.

Sura 7

1 Wannan ita ce dokar baiko domin laifi. Mafi tsarki ne. 2 Dole a kashe baiko domin laifi a mayankarsa, dole kuma su yayyafa jininsa a kowanne gefen bagadi. 3 Dukkan kitsen da ke cikinsa za a miƙa shi: kitsen wutsiya, da kitsen da ke a kan kayan ciki, 4 da ƙodojin biyu da kitsen da ke bisan su, wanda ke kusa da kwiɓi, da wanda ya rufe hanta, tare da ƙodoji - duk wannan dole a cire su. 5 Dole firist ya ƙona waɗannan sassa a kan bagadin shi ne baikon da aka yi da wuta ga Yahweh. Wannan shi ne baiko domin laifi. 6 Kowanne namiji daga cikin fistoci zai iya ci daga wannan baikon. Dole ne a ci shi a wuri mai tsarki domin mafi tsarki ne. 7 Baiko domin zunubi kamar baiko domin laifi ya ke. Doka guda ce domin su biyun. Za su zama na firist wanda ya ke yin kaffara da su. 8 Firist wanda ya miƙa wa wani baikonsa na ƙonawa zai iya ɗaukar wa kansa fatar wannan baikon. 9 Kowanne baiko na garin hatsi da aka toya a cikin tanda, da kowanne makamancin baiko da aka dafa a tukunya ko a kaskon tuya zai zama na firist da ya miƙa baikon. 10 Kowanne baiko na garin hatsi, ko busasshe ko kwaɓaɓɓe da mai, za su zama rabon dukkan zuriyar Haruna dai-dai wa dai-da. 11 Wannan ita ce shari'ar hadayar baye-baye na salama wadda mutane za su miƙa ga Yahweh. 12 Idan wani ya miƙa shi domin ya yi godiya, to dole ya miƙa shi da hadayar waina da aka yi ba a sa gami ba, amma kwãɓe da mai, waina da aka yi ba gami, amma an shafa masu mai, waina da aka yi ta da lallausar gari da aka kwaɓa da mai. 13 Kuma domin dalilin miƙa godiya, dole ya miƙa baikonsa na salama tare da wainar gurasa da aka yita da gami. 14 Zai miƙa guda ɗaya na kowanne irin waɗannan hadayu ya zama baikon da aka miƙa ga Yahweh. Zai zama rabon firist wanda ya yayyafa jinin baye-baye na salama a kan bagadi. 15 Mutumin da ke miƙa baiko na salama domin nuna godiya dole ya ci naman baikonsa a ranar yin hadayar. Kada ya bar ragowar har kashegari da safe. 16 Amma idan hadayar baikonsa domin wa'adi ne, ko kuma domin bayarwar yardar rai, dole a ci naman a ranar da ya miƙa hadayar, amma duk abin da ya rage a ciki za a iya cinsa kashegari. 17 Amma, kowanne ragowar naman hadaya a rana ta uku dole a ƙone shi. 18 Idan aka ci naman hadayar wani na baikon salama a rana ta uku, ba za a karɓa ba, ba kuma za a lisafta shi ga mai miƙa wa ba. Zai zama abin ƙyama, kuma mutumin da ya ci shi zai ɗauki laifin zunubinsa. 19 Duk naman da ya taɓa abin da ba tsarki ba za a ci shi ba. Dole a ƙona shi. Game da sauran naman, duk wanda ya ke da tsarki zai iya cin shi. 20 Amma fa, mutum marar tsarki wanda ya ci wani nama daga hadayar baiko na salama wanda ya ke na Yahweh ne- wannan mutum dole a datse shi daga mutanensa. 21 Idan wani mutum ya taɓa wani abu marar tsarki - ko ƙazamtar mutum ne, ko na ƙazamin dabba, ko na wani abu marar tsarki na ban ƙyama, sa'an nan kuma ya ci daga naman hadayar baiko na salama wanda ya ke na Yahweh ne, wannan mutumin dole a datse shi daga mutanensa.'" 22 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 23 "Yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, 'Ba za ku ci kitsen sã ko na tunkiya ko na akuya ba. 24 Kitsen dabba mushe da ba a yi hadaya da ita ba, ko kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin amfani da su domin wani abu, amma kada ku kuskura ku ci su. 25 Ko wane ne ya ci kitsen dabbar da mutane zasu iya miƙa ta hadaya ta ƙonawa ga Yahweh, wannan mutumin dole a datse shi daga mutanensa. 26 Ba za ku ci jini ba daɗai a gidajenku, ko daga tsuntsu ya ke ko dabba. 27 Duk wanda ya ci jini, dole a datse wannan mutum daga mutanensa.'" 28 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 29 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, 'Wanda duk ya ke miƙa hadayar baiko na salama ga Yahweh dole ya kawo wani sashen hadayar ga Yahweh. 30 Baiko domin Yahweh da za a yi da wuta, mai ita ne zai kawo da hannunsa. Dole ya kawo kitsen tare da ƙirjin, saboda a kaɗa ƙirjin ya zama baiko don kaɗawa a gaban Yahweh. 31 Dole ne firist ya ƙona kitsen a kan bagadi, amma ƙirjin zai zama na Haruna da zuriyarsa. 32 Dole a bada cinyar ƙafar dama ga firist a matsayin baikon da aka miƙa daga cikin hadayarku ta baye-baye na salama. 33 Firist, ɗaya daga cikin dangin Haruna, wanda ya miƙa jinin baye-baye na salama da kitsen - shi zai ɗauki cinyar ƙafar dama rabonsa kenan na baikon. 34 Gama na ɗauka daga mutanen Isra'ila, ƙirjin baiko na kaɗawa, da cinya su zama bayarwarsu, an rigaya an ba Haruna firist da 'ya'yansa maza waɗannan su zama rabonsu koyaushe. 35 Wannan ne rabon Haruna da zuriyarsa daga baye-bayen da aka yi wa Yahweh da wuta, a ranar da Musa ya miƙa su su yi wa Yahweh hidima a cikin aikin firist. 36 Wannan rabon ne da Yahweh ya umarta a ba su daga mutanen Isra'ila, a ranar da ya keɓe firistoci. Kullum zai zama rabonsu har dukkan tsararraki. 37 Wannan shi ne shari'ar baiko na ƙonawa, da baiko na hatsi, da baiko domin zunubi, da baiko domin laifi, da baiko na keɓewa, da na hadayar baye-baye na salama, 38 wanda Yahweh ya ba da umarnai ga Musa a kan Tsaunin Sinai a ranar da ya umarci mutanen Isra'ila su miƙa hadayunsu ga Yahweh a jejin Sinai.'"

Sura 8

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa' 2 "Ka ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza tare da shi, da riguna, da man ƙeɓewa, da bijimi domin baiko na zunubi, da raguna biyu, da kwandon waina marar gami. 3 Ka tara dukkan taron a ƙofar rumfar taruwa." 4 Sai Musa ya yi yadda Yahweh ya umarce shi, dukkan taron suka tattaru a ƙofar rumfar taruwa. 5 Sai Musa ya cewa taron, "Ga abin da Yahweh ya umarta a yi." 6 Musa ya kawo Haruna da 'ya'yansa maza ya wanke su da ruwa. 7 Ya sa wa Haruna riga 'yarciki ya ɗaura masa ɗamara a ƙugunsa, ya sa masa taguwa ya kuma sa masa falmara, sa'an nan ya ɗaura masa falmarar da wata ƙasaitacciyar ɗamara mai kyan ɗinki ya zagaya ƙugunsa da ita ya ɗaure. 8 Ya sa masa ƙyallen ƙirji, a kan ƙyallen kuma ya sa Urim da Tumim. 9 Ya naɗa masa rawani a kansa, a kan rawanin, a goshi, ya kafa masa tasar zinariya, kambi mai tsarki, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 10 Musa ya ɗauki man ƙeɓewa, ya keɓe rumfar da dukkan abin da ke cikinta ya keɓe su ga Yahweh. 11 Ya yayyafa man a kan bagadi sau bakwai, ya shafe bagadin da dukkan kayan aikinta, da daron wanki da maɗorinta, saboda a keɓe su domin Yahweh. 12 Ya zuba wasu man keɓewa akan Haruna ya shafe shi don a keɓe shi. 13 Musa ya kawo 'ya'yan Haruna maza ya suturta su da su riguna 'yanciki. Ya ɗaura masu ɗamara kewaye da ƙugunsu ya ɗaura masu rawanin ƙyallen lilin a kawunansu, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 14 Musa ya kawo bijimin na baiko domin zunubi, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan bijimin da suka kawo saboda baiko domin zunubi. 15 Ya yanka shi, sai ya ɗauki jinin ya sa a kan ƙahonnin bagadin da ɗan yatsansa, ya tsarkake bagadin, ya zuba jinin a ƙarƙashin bagadin, ya keɓe shi ga Yahweh domin ya yi kaffara domin shi. 16 Ya ɗauki dukkan kitsen da ke kan kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, da ƙodojin biyu da kitsensu, sai Musa ya ƙona su dukka a kan bagadi. 17 Amma bijimin, da fatarsa, da namansa, da kashinsa ya ƙona su a bayan sansani, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 18 Musa ya miƙa rãgon domin baiko na ƙonawa, kuma Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan rãgon. 19 Ya yanka shi ya yayyafa jininsa a kowanne gefen bagadin. 20 Ya yanka rãgon gunduwa gunduwa ya ƙona kan da yankakkun naman da kuma kitsen. 21 Ya wanke kayan cikin da ƙafafun da ruwa, ya kuma ƙona rãgon ɗungum a kan bagadi. Baiko ne na ƙonawa mai bada ƙamshi mai daɗi, baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 22 Sa'an nan Musa ya miƙa ɗaya ragon, ragon tsarkakewa, Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan rãgon. 23 Sai Haruna ya yanka shi, Musa kuma ya ɗiba daga jinin ya sa su a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun damansa da bisa babban yatsan ƙafarsa ta dama. 24 Ya kawo 'ya'yan Haruna maza, ya sa daga jinin a kan leɓatun kunnuwansu na dama, da kan manyan yatsan hannuwansu na dama, da kan manyan yatsansu na ƙafafun dama. Sa'an nan Musa ya yayyafa jinin a kowanne gefen bagadin. 25 Ya ɗauki kitsen, kitsen wutsiya, dukkan kitsen da ke bisa kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, da ƙodojin biyu da kitsensu, da cinyar dama. 26 Daga cikin kwandon gurasa da bata da gami da ke gaban Yahweh, ya ɗauki curi guda na marar gami, da curi guda na gurasa da aka shafe ta da mai, da waina guda, sai ya ɗibiya su bisa kitsen da kuma kan cinyar dama. 27 Ya sa su dukka a hannuwan Haruna da kuma hannuwan 'ya'yansa maza kuma ya kaɗa su a gaban Yahweh domin baiko na kaɗawa. 28 Sa'an nan Musa ya karɓe su daga hannunsu ya ƙona su a kan bagadi domin baiko na ƙonawa. Baiko ne na keɓewa ya kuma bada ƙamshi mai daɗi. Baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh. 29 Musa ya ɗauki ƙirjin ya kaɗa su don su zama baikon kaɗawa ga Yahweh. Wannan shi ne rabon Musa daga rãgon domin naɗa firist, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 30 Musa ya ɗiba daga man keɓewa da jinin da ke kan bagadi; ya yayyafa su a kan Haruna, da kan rigunansa, da kan 'ya'yansa maza, da kan rigunan 'ya'yansa maza tare da shi. Da haka ne ya keɓe Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu ga Yahweh. 31 Sai Musa ya cewa Haruna da 'ya'yansa maza, "Ku dafa naman a ƙofar shiga rumfar taruwa, ku ci a can da gurasar da ke cikin kwandon tsarkakewa, kamar yadda na umarta, cewa, 'Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi.' 32 Duk abin da ya rage daga naman da gurasar dole a ƙona. 33 Ba za ku fita daga ƙofar rumfar taruwa ba har kwana bakwai, sai kwanakin naɗinku sun cika. Domin Yahweh zai tsarkake ku kwana bakwai. 34 Mene ne aka rigaya aka yi yau - Yahweh ya umarta a yi domin a yi maku kaffara. 35 Za ku zauna dare da rana har kwana bakwai a ƙofar rumfar taruwa, ku yi biyayya da umarnin Yahweh, domin kada ku mutu, domin wannan ne aka umarce ni. 36 Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukkan abubuwan da Yahweh ya umarce su ta wurin Musa.

Sura 9

1 A rana ta takwas Musa ya kira Haruna da 'ya'yansa maza da dattawan Isra'ila. 2 Ya cewa Haruna, "Ka ɗauki ɗan maraƙi daga garke domin baiko na zunubi, da rago marar lahani domin baiko na ƙonawa, ka miƙa su a gaban Yahweh. 3 Dole ka yi wa mutanen Isra'ila magana ka ce, 'Ku ɗauki bunsuru domin baikon zunubi da kuma ɗan maraƙi da ɗan rãgo, dukka biyun bana ɗaya kuma marasa lahani, domin baiko na ƙonawa; 4 kuma ka ɗauki sã da rãgo domin baiko na salama a yi hadaya ga Yahweh, da baiko na garin hatsi cuɗaɗɗe da mai, domin yau Yahweh zai bayyana a gare ku.'" 5 Sai suka kawo dukkan abin da Yahweh ya umarta zuwa rumfar taruwa, sai dukkan taron Isra'ila suka matso suka tsaya a gaban Yahweh. 6 Sai Musa ya ce, "Wannan shi ne Yahweh ya umarce ku kuyi domin ɗaukakarsa ta bayyana a gare ku," 7 Musa ya cewa Haruna, "Ka matso kusa da bagadi ka miƙa baikonka domin zunubi da na ƙonawa, ka yi wa kanka kaffara domin mutane kuma, ka kuma miƙa hadaya domin mutane domin a yi masu kaffara kamar yadda Yahweh ya umarta." 8 Sai Haruna ya tafi kusa da bagadi ya yanka ɗan maraƙin domin baikon zunubi wanda domin kansa ne. 9 'Ya'yan Haruna suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa cikinsa ya sa a ƙahonnin bagadin; sa'an nan ya zuba jinin a gindin bagadin. 10 Amma, ya ƙona kitsen, da ƙodojin da wanda ya rufe hanta a kan bagadi domin baikon zunubi, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 11 Da naman da fatar ya ƙona su a bayan sansani. 12 Haruna ya yanka baiko na ƙonawa, 'ya'yansa maza suka bashi jinin, wanda ya warwatsa a kowanne gefen bagadi. 13 Sa'an nan suka miƙa masa baiko na ƙonawa, gunduwa-gunduwa, tare da kan, sai ya ƙona su a kan bagadi. 14 Ya wanke kayan cikin da ƙafafuwan ya ƙona su a kan baiko na ƙonawa a kan bagadi. 15 Haruna ya miƙa hadayar mutanen - bunsuru, sai ya ɗauke shi domin hadayar zunubansu ya yanka shi; ya miƙa hadayar ne domin zunubi, kamar yadda ya yi da bunsuru na fari. 16 Ya miƙa baiko na ƙonawa ya miƙa kamar yadda Yahweh ya umarta. 17 Ya miƙa baiko na garin hatsi; ya cika tafin hannunsa da ita ya ƙona ta a kan bagadi, tare da baikon ƙonawa na safe. 18 Ya kuma yanka san da rãgon, hadaya domin baiko na salama, saboda mutanen. 'Ya'yan Haruna maza suka ba shi jinin, wanda ya yayyafa a kowanne gefen bagadi. 19 Amma, suka yanke kitsen bijimin da na rãgon, da kitsen wutsiyar, da kitsen da ya rufe kayan ciki, da ƙodoji, da wanda ya rufe hanta. 20 Suka ɗauki sassan da aka yanka suka ɗibiyasu a kan ƙirjin, sa'an nan Haruna ya ƙona kitsen a kan bagadi, 21 Haruna ya kaɗa ƙirjin da cinyar ƙafar dama domin baiko na kaɗawa a gaban Yahweh, kamar yadda Musa ya umarta. 22 Sa'an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa yana fuskantar mutane ya albarkace su; sai ya dawo daga miƙa baiko na zunubi, baiko na ƙonawa, da baiko na salama. 23 Musa da Haruna suka shiga rumfar taruwa, suka sake fitowa kuma suka albarkaci mutanen, sai ɗaukakar Yahweh ta bayyana ga dukkan mutane. 24 Wuta ta fito daga Yahweh ta cinye baikon ƙonawar da kitsen da ke kan bagadin. Da dai dukkan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suka kwanta fuskokinsu a ƙasa.

Sura 10

1 Sai Nadab, da Abihu 'ya'yan Haruna maza, kowannensu ya ɗauki farantinsa ya sa wuta a ciki, da kuma turare. Sa'an nan suka miƙa haramtacciyar wuta a gaban Yahweh, wanda bai dokace su su miƙa ba. 2 Saboda haka wuta ta fito daga gaban Yahweh ta hallaka su, suka kuwa mutu a gaban Yahweh. 3 Sai Musa ya cewa Haruna, "Wannan shi ne Yahweh ya ke magana a kai sa'ad da ya ce, "Zan bayyana tsarkina ga waɗanda suka matso gare ni. Za a ɗaukaka ni a gaban dukkan mutane.'" Haruna bai ce komai ba. 4 Musa ya kira Mishayel da Elzafan, 'ya'ya maza na Uziyel kawun Haruna, ya ce masu, "Ku zo nan ku ɗauki 'yan'uwanku daga cikin sansani daga gaban rumfar taruwa." 5 Sai suka matso kusa suka ɗauke su, suna saye da rigunansu na firistoci, zuwa bayan sansani, kamar yadda Musa ya umarta. 6 Sai Musa ya ce da Haruna da Eliyazar da kuma Itamar 'ya'yansa maza, "Kada ku bar gashin kanku da tsawo, kada kuma ku kekketa tufafinku, domin kada ku mutu, kuma domin kada Yahweh ya yi fushi da dukkan taro. Amma ku bari 'yan'uwanku wato dukkan gidan Isra'ila, su yi makoki domin waɗanda wutar Yahweh ta babbake. 7 Ba za ku fita daga ƙofar rumfar taruwa ba, ko kuwa ku mutu, gama man shafewa na Yahweh yana kanku." Sai suka aikata bisa ga umarnin Musa. 8 Yahweh ya yi magana da Haruna, cewa, 9 "Kada ka sha ruwan inabi ko barasa, da kai, da 'ya'yanka maza da ke tare da kai, yayin da kuka shiga rumfar taruwa, domin kada ku mutu. Wannan zai zama tsayayyar ka'ida dukkan tsararrakin mutanenku, 10 domin a faiyace mai tsarki da marar tsarki, tsakanin ƙazamtacce da tsarkakke, 11 domin ka koyar da mutanen Isra'ila dukkan farillan da Yahweh ya umarta ta wurin Musa." 12 Musa ya yi magana da Haruna da Eliyazar da kuma Itamar, 'ya'yansa maza da suka rage, "‌Ku ɗauki baiko na hatsi da ya ragu daga baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta, ku ci bada gami ba kusa da bagadi, gama mafi tsarki ne. 13 Dole ka ci shi a wuri mai tsarki, domin rabonku ne da kuma rabon 'ya'yanku maza baye-bayen da aka yi wa Yahweh da wuta, gama wannan ne aka umarce ni in faɗa maku. 14 Ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka miƙa wa Yahweh, dole ku ci a wuri mai tsabta karɓaɓɓe ga Yahweh. Da kai da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata tare da kai za ku ci waɗannan rabon, gama an bada su domin su zama rabonka da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayu na baye-baye na zumunta na mutanen Isra'ila. 15 Cinyar da aka miƙa da ƙirjin da aka kaɗa, dole ne su kawosu da baye-baye na kitse da aka yi da wuta, domin a kaɗa su a gaban Yahweh. Za su zama naka da na 'ya'yanka maza rabonku ne har abada, kamar yadda Yahweh ya umarta." 16 Sa'an nan Musa ya tambaya game da bunsurun baiko na zunubi, sai ya ga an ƙone shi kurmus. Saboda haka ya yi fushi da Eliyazar da Itamar, sauran 'ya'ya maza na Haruna; ya ce, 17 "Me ya sa ba ku ci baiko na zunubi a harabar rumfar sujada ba, tunda shike mafi tsarki ne, kuma tun da Yahweh ya bada shi gare ku domin a ɗauke laifin taro, domin a yi masu kaffara a gabansa? 18 Duba, ba a kawo jininsa cikin rumfar sujada ba, yakamata lallai da kun ci shi a harabar rumfar sujada, kamar yadda na umarta." 19 Sai Haruna ya amsa wa Musa, "Duba, yau sun miƙa baikonsu na zunubi da baiko ta ƙonawa a gaban Yahweh, kuma ga wannan abu ya faru da ni yau. In da na ci baiko na zunubi yau, da zai zama da kyau kenan a idon Yahweh?" 20 Da Musa ya ji wannan, sai ya gamsu.

Sura 11

1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa, 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana, ka ce, 'Waɗannan su ne masu rai da za ku ci daga cikin dukkan dabbobin da ke a duniya. 3 Za ku ci kowacce dabba da ke da rababben kofato tana kuma tuƙa. 4 Amma fa, wasu dabbobin suna tuƙa, ko kuma suna da rababbun kofatai, ba za ku ci su ba, dabbobi kamar su raƙumi, domin yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato. Saboda haka raƙumi marar tsarki ne a gare ku. 5 Haka ma rema, domin tana tuƙa amma ba ta da rababben kofato, ita ma marar tsabta ce a gare ku. 6 Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, saboda haka marar tsabta ne a gare ku. 7 Alade, koda shike yana da rababben kofato, ba ya tuƙa, marar tsabta ne a gare ku. 8 Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawakinsu. Marasa tsabta ne a gare ku. 9 Dabbobin da ke zaune cikin ruwa da za ku ci su ne duk waɗanda ke da ƙege ko kamɓori, ko a cikin teku ko cikin koguna. 10 Amma duk rayayyun hallitu da ba su da ƙege ko kamɓori a cikin teku da koguna, har da ma dukkan masu yawo a ruwa da dukkan hallitu da ke cikin ruwa - dole za su zama abin ƙyama a gare ku. 11 Tun da ya zama dole ku ƙyamace su, ba za ku ci daga namansu ba; kuma, dole ku ƙyamaci gawawakinsu. 12 Dukkan abin da ba shi da ƙege ko kamɓori a cikin ruwa dole ku ƙyamace su. 13 Ga tsuntsayen da za ku ji ƙyama kuma ba za ku ci su ba su ne: gaggafa, da ungulu, 14 da shirwa, da kowacce irin mikiya, 15 da kowanne irin hankaka, 16 jimina, da mujiyar dare, da shaho, da kowacce irin shirwa. 17 Za ku kuma ƙyamaci mujiya, da babba da ƙarama, da zalɓe, 18 da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu, 19 da shamuwa, da jinjimi, da burtu, da jemage. 20 Dukkan ƙwari masu fukafukai da ke tafiya a kan ƙafa huɗu abin ƙyama ne a gare ku. 21 Amma za ku iya cin ƙwari masu tashi suna kuma tafiya a kan ƙafafu huɗu idan ƙafafunsu suna da mahaɗi don tsalle a ƙasa. 22 Za ku iya cin kowacce irin fara, da gara mai fukafukai da gyare, ko fara. 23 Amma duk ƙwari masu tashi masu ƙafa huɗu abin ƙyama ne a gare ku. 24 Za ku ƙazantu har faɗuwar rana ta wurin waɗannan dabbobi idan kun taɓa mushen ɗaya daga cikinsu. 25 Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawakinsu dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har ya zuwa faɗuwar rana. 26 Duk dabbar da ke da rababben kofato kuma bata tuƙa zai zama ƙazantacce a gare ku. Duk wanda ya taɓa ta zai ƙazantu. 27 Duk abin da ke tafiya a kan daginsa a cikin dukkan dabbobi da suke tafiya a kan ƙafafu huɗu, ƙazantattu ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu zuwa maraice. 28 Duk wanda ya ɗauki gawarsa dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har ya zuwa maraice. Waɗannan dabbobi za su zama ƙazantattu a gare ku. 29 Cikin dabbobi masu rarrafe a ƙasa, waɗannan dabbobi za su zama ƙazantattu a gare ku: da murɗiya, da ɓera, da kowanne irin babban ƙadangare, 30 da tsaka, guza, da ƙadangare, da damo da hawainiya.. 31 A cikin dukkan dabbobi masu rarrafe, waɗannan ne dabbobin da za su zama ƙazantattu a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har maraice. 32 Idan waninsu ya mutu ya kuma faɗi a kan wani abu, wannan abin ya ƙazantu, ko an yi shi da itace, ƙyalle, fata, ko tsumma, Ko mene ne shi kuma ko mene ne ake amfani da shi, dole a sa shi cikin ruwa; zai zama ƙazamtacce har maraice. Sa'an nan zai zama tsarkakakke. 33 Duk tukunyar yumɓun da ƙazantacciyar dabbar ta faɗa ciki, duk abin da ke cikin tukunyar ya ƙazanta, dole ku fasa tukunyar. 34 Duk abinci da za a iya ci amma yana da ruwa a bisansa wannan tukunya ba ta da tsabta. Duk abin sha da ya ke cikin tukunyar ya ƙazantu. 35 Duk abin da mushe ya faɗi a kansa ya ƙazantu; ko tanderu ne ko ƙaramin murhu ne, dole a farfasa su mitsi-mitsi. Ba su da tsarki kuma dole su kasance marasa tsarki a gare ku, 36 Maɓuɓɓugar ruwa ko daron ɗibar ruwa zai zama da tsabta; amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu. 37 Idan wani shashen mushen ya faɗa kan iri domin shuka, waɗannan irin yana da tsabta. 38 Amma idan an zuba ruwa akan wannan iri, kuma wani sashe na mushen ya faɗi a kansa, za ya zama ƙazantattu a gare ku. 39 Idan dabbar da ya kamata ku ci ta mutu, sai shi wanda ya taɓa gawar ya ƙazantu har sai maraice. 40 Duk wanda ya ci wannan mushen dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har faɗuwar rana. Wanda duk ya ɗauki wannan gawa zai wanke tufafinsa ya ƙazantu har maraice. 41 Kowacce dabba da ke rarrafe a ƙasa za ku ƙyamace ta; ba za ku ci su ba. 42 Duk abin da ke jan ciki, da duk abin da ke tafiya akan ƙafafu huɗu, ko mai ƙafafu da yawa - dukkan dabbobi masu rarrafe a ƙasa, ba za ku ci waɗannan ba, domin abin da za a ji ƙyama ne. 43 Ba za ku ƙazantar da kanku da kowacce hallita mai rai wanda ya ke jan ciki ba; ba za ku ƙazantar da kanku da su ba, har da za ku zama marasa tsarki da su. 44 Gama ni ne Yahweh Allahnku. Za ku ƙeɓe kanku da tsarki, saboda haka, kuma ku zama da tsarki, domin ni mai tsarki ne. Ba za ku ƙazantar da kanku da kowacce irin dabbar da ke tafiya a fuskar ƙasa ba. 45 Domin ni ne Yahweh, wanda ya fitar daku daga ƙasar Masar, domin in zama Allahnku. Saboda haka dole ne ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne, 46 Wannan ita ce dokar da ta shafi dabbobi, da tsuntsaye, da dukkan rayayyun hallitu da ke yawo cikin ruwaye, da kowacce hallita da ke rarrafe a fuskar ƙasa, 47 waɗanda za a sa bambanci tsakanin marasa tsarki da masu tsarki, da tsakanin abubuwa masu rai da za a iya ci, da abubuwa masu rai da ba za a ci su ba.'"

Sura 12

1 Yahweh ya cewa Musa, 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana, cewa, "Idan mace ta yi ciki ta haifi ɗa namiji, za ta ƙazantu har kwana bakwai, kamar yadda ta ƙazantu a kwanakin watan hailarta. 3 A rana ta takwas dole a yi wa ɗan yaron kaciya. 4 Sa'an nan tsarkakewar uwar daga zubar jini zai ci gaba har kwana talatin da uku. Ba zata taɓa wani abu mai tsarki ba ko ta shiga harabar haikali har sai kwanakin tsarkakewarta sun cika. 5 Amma idan ta haifi 'ya mace, za ta ƙazantu sati biyu, kamar yadda take kwanakin hailarta. Sa'an nan kwanakin tsarkakewar uwar zai ci gaba har kwana sittin da shida. 6 Lokacin da kwanakin tsarkakewarta suka cika, domin ɗa na miji ko mace, dole ta kawo ɗan tunkiya bana ɗaya, domin baiko na ƙonawa, da ɗan kurciya ko tattabara domin baiko na zunubi, zuwa ƙofar rumfar taruwa, zuwa ga firist. 7 Sa'an nan zai miƙa shi a gaban Yahweh ya yi kaffara domin ta, sa'an nan za ta tsarkaka daga zubar jininta. Wannan ita ce doka game da matar da ta haifi ɗa ko ɗiya. 8 Idan ba ta iya ba da tunkiya ba, to sai ta ɗauko kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu, ɗaya domin baikon ƙonawa, ɗayan domin baiko na zunubi, sa'an nan firist zai yi kaffara domin ta; sa'an nan za ta tsarkaka.'"

Sura 13

1 Yahweh ya yi magana da Musa da kuma Haruna, ya ce, 2 "Sa'ad da wani yana da kumburi ko ɓamɓaroki ko tabo mai haske a fatar jikinsa, har ya kamu da cuta kuma akwai cutar fata a jikinsa, dole a kawo shi ga Haruna babban firist, ko ga ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza firistoci. 3 Firist zai dudduba cutar a fatar jikinsa. Idan gashin da ke cikin cutar ya zama fari, kuma idan an ga cutar ta yi zurfi fiye da fatar jiki, to cuta ce mai yaɗuwa. Bayan da firist ya dudduba shi, dole ya furta shi marar tsarki. 4 Idan tabon mai haske a jikinsa fari ne, kuma ba aga cutar ta yi zurfin data zarce fatar jikin ba, kuma idan gashin da ke cikin cutar bai rikiɗa fari ba, to dole firist ya ware wannan mai cutar shi kaɗai har kwana bakwai. 5 A rana ta bakwai, dole firist ya duba shi idan a ganinsa cutar ba ta ƙara muni ba, in kuma ba ta bazu a cikin fatar ba. Idan ba ta bazu ba, sai dole firist ya ƙara tsare shi wasu kwanaki bakwai kuma. 6 Firist zai sake bincike shi a rana ta bakwai ya ga ko cutar ta yi sauƙi, bata kuma ƙara bazuwa a fatar ba. Idan bata bazu ba, sai firist ya furta shi tsarkakakke.‌ Ƙuraje ne. Dole ya wanke tufafinsa, sai ya tsarkaka. 7 Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar bayan ya nuna kansa ga firist domin tsarkakewarsa, sai dole ya sake nuna kansa ga firist kuma. 8 firist zai sake duba shi ya ga ko ɓamɓarokin ya ƙara yaɗuwa a fatar jikin. Idan ya yaɗu, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cutar fata ce mai bazuwa. 9 Idan cutar fata mai yaɗuwa tana jikin wani, dole a kawo shi wurin firist. 10 Firist zai duba shi ya ga ko akwai farin kumburi a fatar jikinsa, idan gashin ya rikiɗa ya zama fari, ko kuma akwai buɗaɗɗen ƙurji a kumburin. 11 Idan akwai, to lallai akwai riƙaƙƙiyar cutar fata mai yaɗuwa, dole firist ya furta shi marar tsarki. Ba zai ware shi ba kaɗai, gama ya rigaya ya ƙazantu. 12 Idan cutar ta bazu barkatai a cikin fata kuma ta mamaye duk fatar jikin mutumin daga kansa har zuwa kafafunsa, bisa ga ganin firist, 13 sai dole firist ya dudduba shi domin ya ga ko cutar ta rufe dukkan jikinsa. Idan kuwa haka ne, sai firist dole ya furta cewa mutumin nan mai cutar tsarkakke ne. Idan ta rikiɗa ta zama fari, to tsarkakakke ne. 14 Amma idan akwai buɗaɗɗen ƙurji a kansa, to ya ƙazantu. 15 Dole firist ya duba miƙin jikin ya furta cewa ya ƙazantu domin miƙin fatar ƙazantacce ne. Cuta ce mai yaɗuwa. 16 Amma idan miƙin fatar ya koma kuma ya zama fari, dole mutumin ya tafi wurin firist. 17 Firist zai dudduba shi ya ga ko fatar ta koma fari. Idan ya koma, sai firist ya furta wannan mutum tsarkakke ne. 18 Idan mutum yana da maruru a fatar jikinsa amma ya warke, 19 kuma a tabon marurun nan sai ga wani farin kumburi ko fata mai ƙyalli, ja da fari, to fa dole a nuna wa firist. 20 Firist zai dudduba ya ga ko ya shiga cikin fata sosai, kuma idan gashin wurin ya rikiɗa ya zama fari. Idan haka ne, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce ta fata mai saurin yaɗuwa, idan ya girma a inda kumburin ya ke. 21 Amma idan firist ya dudduba ya ga ba farin gashi a ciki, kuma zurfin bai zarce fata ba amma ya dushe, dole firist ya ware shi da bam har kwana bakwai. 22 Idan ta bazu ta mamaye fatar, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa. 23 Amma idan fata mai haske ta kassance wuri guda bai bazu ba, to tabon maruru ne, dole kuma firist ya furta shi tsarkakakke. 24 Idan fata tana da ƙuna kuma wani buɗaɗɗen ƙurji ya fito a wurin da launi jaja-jaja fari-fari ko farin ɗigo, 25 sai firist ya dudduba shi ya ga ko gashin wurin ya zama fari, in kuma zurfinsa ya wuce fata. Idan haka ne, to cuta ce mai yaɗuwa. Ya ɓullo ne akan tabo, dole ne firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa. 26 Amma idan firist ya dudduba shi ya ga babu farin gashi a wurin, kuma bai zarce fata ba amma ya dushe, sai dole firist ya ware shi shi kaɗai har kwana bakwai. 27 Sa'an nan ɗole firist ya dudduba shi a rana ta bakwai. Idan ya yaɗu ya mamaye fatar, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa. 28 Idan cutar ta tsaya wuri guda ba ta yaɗu cikin fatar ba amma ta dushe, to kumburi ne daga ƙuna, dole firist ya furta shi tsarkakakke, saboda ba wani abu ba ne, sai dai tabo ne daga ƙuna. 29 Idan namiji ko mace na da cuta mai yaɗuwa a kã ko a haɓa, 30 sai dole firist ya dudduba mutumin saboda cutar da ke yaɗuwa domin a ga ko ta zarce fatar jikin, idan aka ga gashi ruwan ɗorowa, kuma siriri a cikinsa. Idan akwai shi, to dole firist ya furta shi marar tsarki.‌ Ƙaiƙai ne. Cuta ce mai yaɗuwa a kã ko a haɓa, 31 Idan firist ya dudduba cuta mai ƙaiƙayi ya ga babu ita ƙarƙashin fata, kuma ba baƙin gashi a ciki, to sai firist ya ware mutumin nan mai cutar ƙaiƙayi shi kaɗai har kwana bakwai. 32 A rana ta bakwai firist zai duba cutar ya ga ko ta bazu. Idan babu gashi mai kalar ruwan ɗorowa, kuma idan cutar ba ta zarce zurfin fata ba, sai dole a yi masa aski, 33 amma ba za a aske wajen cutar ba, kuma dole firist ya ware mutumin nan mai cutar ƙaiƙayi shi kaɗai kimamin wasu kwana bakwai. 34 A rana ta bakwai firist zai dudduba cutar ya ga ko ta dena bazuwa a cikin fatar, Idan an ga bata zarce zurfin fata ba, sai dole firist ya furta shi tsarkakakke. Dole mutumin ya wanke tufafinsa, sa'an nan za ya zama tsarkakakke, 35 Amma idan cutar ƙaiƙayin ta bazu da yawa a cikin fatar bayan firist ya ce ya tsarkaka, 36 sai dole firist ya sake dudduba shi kuma. Idan cutar ta bazu a cikin fatar, firist bai buƙatar ya nemi gashi mai launin rawaya. Mutumin ya kazantu. 37 Amma idan a ganin firist cutar ƙaiƙayi ta dena bazuwa kuma baƙin gashi ya toho a wurin, to cutar ta warke. Ya zama tsarkakakke, dole firist ya furta shi tsarkakakke. 38 Idan namiji ko mace na da farin tabbuna a fata, 39 sai dole firist ya dudduba mutumin ya ga ko tabbunan ba farare sosai ba ne, wannan ƙuraje ne kawai da suka farfashe a cikin fatar. Shi tsarkakakke ne. 40 Idan gashin namiji ya zube daga kansa, yana da saiƙo, amma yana da tsarki. 41 Idan gashinsa suka zube daga gaban kansa, idan goshinsa na da saiƙo, shi tsarkakakke ne. 42 Amma idan akwai wani ƙurji jaja-jaja fari-fari akan saiƙonsa ko goshinsa, wannan cuta ce mai yaɗuwa da ta faso. 43 Saboda haka dole firist ya dudduba shi ya ga ko kumburin cutar inda take a kan saiƙo ko goshinsa ya yi jaja-jaja fari-fari, da kuma kamannin cuta mai yaɗuwa ce a cikin fata. 44 Idan ita ce, to yana da cuta mai yaɗuwa kuma ba shi da tsarki. Tabbas kuma dole ne firist ya furta shi marar tsarki saboda cutarsa da ke a kansa. 45 Mutumin da ke da cuta mai yaɗuwa dole ya sa yagaggun tufafi, ya bar gashin kai ba gyara, dole kuma ya rufe fuskarsa har hanci yana kira da ƙarfi, 'Marar tsarki, marar tsarki.' 46 Dukkan kwanakin da ya ke da wannan cuta mai yaɗuwa zai kasance marar tsarki. Domin ya ƙazantu da cuta mai yaɗuwa, dole ya zauna shi kaɗai. Dole ya zauna a bayan sansani. 47 Rigar data ƙazantu da kuturta ko ta ulu ce ko rigar lilin ce, 48 abin da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko lilin, ko fata, ko mene ne dai da aka yi shi daga fata - 49 idan akwai wani kore-kore ko jaja-jajar ƙazanta a taguwar, fatar, da saƙa ko ɗinkakken yadi, ko mene ne dai da aka yi daga fata, to wannan kuturta ce data yaɗu; dole a nuna wa firist. 50 Dole firist ya dudduba kayan don kuturta; dole ne ya kulle duk abin da ke da kuturta har kwana bakwai. 51 Zai sake duba kuturtar nan a rana ta bakwai. Idan ta bazu a tufar da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko yadin lilin ko fata ko wani abu da aka yi amfani da fata, to wannan kuturta ce mai cutarwa, wannan abu ya ƙazantu. 52 Dole ya ƙona wannan tufar, ko sakakkiya ko ɗinkakkiyar abin da aka yi da ulu ko yadin lilin, ko fata, ko wani abin da aka yi daga fata, dukkan abin da aka sami kuturta mai cutarwa a ciki, gama zai iya kaiwa ga cuta, Dole a ƙona wannan abin ƙurmus. 53 Idan firist ya dudduba abin ya ga kuturta amma bata bazu cikin tufa ba ko cikin abin da aka ɗinka da yadi ko aka saƙa da ulu ko lilin, ko kayayyakin da aka yi su da fata, 54 sa'an nan zai umarce su su wanke kayan da aka sami kuturta a ciki, dole kuma zai kulle shi wasu kwana bakwai kuma. 55 Sa'an nan firist zai duba abin bayan an wanke wannan kayan mai kuturta. Idan kuturtar bata sauya launin ba, koda shike bata bazu ba, ƙazamtacce ne. Dole a ƙona wannan abin, ko ma a ina kuturtar ta ƙazamtar da shi. 56 Idan firist ya duba wannan abin, idan kuturtar ta dushe bayan an wanke ta, dole ya yage wannan ƙazantaccen wuri daga tufar ko fatar, ko daga saƙaƙƙe ko ɗinkakken yadi. 57 Idan kuturta ta sake bayyana a taguwar ko a cikin saƙaƙƙe ko ɗinkakken yadi, ko wani abin da aka yi da fata, bazuwa take yi. Dole ku ƙona duk wani abin da ke da kuturta. 58 Riga ko wani abin da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko yadin lilin, ko fata, ko wani abin da aka yi da fata - idan kun wanke abin kuma kuturtar ta fita, sai kuma dole ku wanke wannan abin karo na biyu, sa'an nan zai zama da tsarki. 59 Wannan ita ce shari'a game da kuturta a tufar ulu ko lilin, ko kowanne abin da aka saƙa ko ɗinka daga ulu ko yadin lilin, ko fata ko ko mene ne da aka yi shi da fata, domin ku furta shi mai tsarki ko marar tsarki."

Sura 14

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Wannan ce shari'a domin mutum mai cuta a ranar tsarkakewarsa. Dole ne a kawo shi ga firist. 3 Firist zai fita daga cikin zango domin ya dudduba mutumin ya ga ko cutar mai yaɗuwa a fata ta warke. 4 Sa'an nan firist zai bada doka cewa wanda za a tsarkake ya ɗauki tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen sida. da jan zare, da ɗaɗɗoya. 5 Firist zai umarce shi ya kashe ɗaya daga cikin tsuntsayen a kan ruwa mai tsabta da ke cikin tukunyar yumɓu. 6 Firist zai ɗauki tsuntsun mai rai da itacen sida, da jan zare da ɗaɗɗoyar, yatsoma dukkan waɗannan abubuwa, har ma da tsuntsun nan mai rai, a cikin jinin tsuntsun da aka kashe a kan ruwa mai tsabta. 7 Sa'an nan firist zai yayyafa wannan ruwa sau bakwai a kan mutumin da za a tsarkake daga cutar, sa'an nan firist zai furta cewa ya tsarkaka. Sa'an nan firist zai saki tsuntsun mai rai ya yi tafiyarsa jeji. 8 Mutumin da ake tsarkakewa zai wanke tufafinsa, ya aske dukkan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan zai tsarkaka. Bayan wannan dole ya dawo cikin zango. amma ba zai zauna a cikin rumfarsa ba sai bayan kwana bakwai. 9 A rana ta bakwai dole ya yanke dukkan gashin kansa, kuma dole ya aske gemunsa da girar idonsa. Dole ya aske dukkan gashinsa, kuma dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa; sa'an nan zai zama da tsarki. 10 A rana ta takwas dole ya ɗauki 'yan raguna biyu marasa lahani, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da kashi uku bisa goma na mudun lallausar gari cuɗaɗɗe da mai domin baiko ta hatsi, da moɗar mai ɗaya. 11 Firist da ya tsarkake shi zai tsaida wanda za a tsarkake, tare da waɗannan abubuwa, a gaban Yahweh a ƙofar rumfar taruwa. 12 Firist zai ɗauki ɗaya daga cikin 'yan ragunan ya miƙa shi baiko domin laifi, tare da moɗar mai; zai kaɗa su domin baiko na kaɗawa a gaban Yahweh. 13 Dole ya yanka ɗan ragon a inda suke yanka baye-baye na zunubi da baye-baye na ƙonawa, a harabar haikali, domin baiko na zunubi rabon firist ne, haka ma baiko na laifi, domin mafi tsarki ne. 14 Firist zai ɗauki kaɗan daga cikin jinin baikon domin laifi ya sa shi a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun damansa, da kan babban yatsan ƙafarsa ta dama. 15 Sa'an nan firist zai ɗauki mai daga moɗar ya zuba shi a tafin hannun hagunsa, 16 ya tsoma yatsansa na dama a cikin man da ke tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa daga man da yatsansa sau bakwai a gaban Yahweh. 17 Firist zai sa ragowar man a hannunsa a kan leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a kan babban yatsan hannunsa na dama, da a kan babban yatsan ƙafarsa ta dama. Dole ya sa wannan mai a kan jinin baiko domin laifi. 18 Game da sauran man da ke hannun firist, zai sa shi a kan mutumin da za a tsarkake, firist kuma zai yi kaffara dominsa a gaban Yahweh. 19 Sa'an nan firist zai miƙa baiko na zunubi ya yi kaffara domin wanda za a tsarkake saboda rashin tsarkinsa, bayan wannan zai yanka baiko na ƙonawa. 20 Sa'an nan firist zai miƙa baiko na ƙonawa da kuma baiko na hatsi a kan bagadi. Firist zai yi kaffara domin wannan mutumin, sa'an nan zai zama da tsarki. 21 Amma, idan mutumin matalauci ne har ba zai iya ba da waɗannan hadayu ba, to sai ya ɗauki ɗan rago ɗaya domin baiko na laifi saboda a kaɗa shi, a yi kaffara dominsa, da awon garwa na gari mai laushi da aka kwaɓa da mai domin baiko na hatsi, da mai a moɗa, 22 tare da kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu, iyakar dai abin da ya iya samu; tsuntsu ɗaya zai zama na baikon zunubi ɗayan kuma baiko na ƙonawa. 23 A rana ta takwas dole ya kawo su domin tsarkakewarsa ga firist, zuwa ƙofar shiga rumfar taruwa, a gaban Yahweh. 24 Firist zai ɗauki ragon domin baiko, zai ɗauke shi tare da moɗar man zaitun, sai ya ɗaga su sama sosai sa'ad da ya ke miƙa wa Yahweh. 25 Zai yanka ɗan ragon baiko domin laifi, zai ɗauki ɗan jinin baiko domin laifi ya sa su a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun dama, da kan babban yatsan ƙafar damansa. 26 Sa'an nan firist zai zuba daga cikin man a tafin hannunsa na hagu, 27 kuma ya yayyafa da ɗan yatsansa na dama daga cikin man da ke tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Yahweh. 28 Firist zai sa daga man da ke tafin hannunsa a kan leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun damansa, da kuma kan babban yatsan ƙafar damansa, a nan wuraren da ya sa jinin baiko domin laifi. 29 Zai sa sauran man da ke hannunsa a kan wanda za a tsarkake, domin a yi kaffara dominsa a gaban Yahweh. 30 Dole ya miƙa ɗaya daga cikin 'yan kurciyoyin ko 'yan tantabarai, gwargwadon abin da mutumin ya iya samowa - 31 ɗaya domin baikon zunubi ɗaya kuma domin baiko na ƙonawa, tare kuma da baiko na garin hatsi. Sai firist ya yi kaffara domin wanda za a tsarkake a gaban Yahweh. 32 Wannan ita ce doka domin mutumin da ke da cutar fata mai yaɗuwa, wanda ya gaza bayarwa bisa ga ka'idodin baye-baye domin tsarkakewarsa." 33 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa, 34 "Sa'ad da kuka shiga cikin ƙasar Kan'ana wanda na ba ku ta zama mallakarku, idan na sa kuturta mai yaɗuwa a cikin gida cikin ƙasar mallakarku, 35 sai dole mai wannan gida ya tafi ya faɗa wa firist. Dole ne ya ce, 'Ni a gani na akwai wani abu kamar kuturta a cikin gidana.' 36 Sa'an nan firist zai umarta a fitar da komai daga cikin gidan kafin ya shiga ya duba ya tabbatar akwai kuturtar, domin kada a ƙazamtar da dukkan abin da ke gidan. Bayan wannan firist zai shiga ya duba cikin gidan. 37 Dole ya dudduba kuturtar ya ga ko tana bangayen gidan, ya duba ko yana da kore-koren launi ko jaja-jaja cikin zurfin bangayen. 38 Idan akwai kuturta a gidan, sai firist ya fita daga gidan ya rufe ƙofar gidan har kwana bakwai. 39 Sa'an nan firist zai sake dawowa a rana ta bakwai ya dudduba shi domin ya ga ko kuturtar ta bazu a bangayen gidan. 40 Idan ta bazu, sai firist ya umarta a cire duwatsun da aka tarar da kuturta a jefar da su a wuri marar tsabta a bayan birni. 41 Zai sa a kankare dukkan bangayen cikin gidan, dole kuma a kwashe dukkan ƙazamtattun kayayyakin da aka kankare a kai su can bayan birni a zuba su a wuri marar tsabta. 42 Dole su ɗauki wasu duwatsu su cike gurbin waɗancan duwatsun da aka cire, dole kuma su yi amfani da sabuwar ƙasa su yaɓe gidan. 43 Idan kuturta ta sake ɓullowa cikin gidan da aka ciccire duwatsun bangayen aka kakankare su aka kuma yi sabon shafe, 44 sai dole firist ya shiga ciki ya dudduba gidan ya ga ko kuturtar ta bazu a cikin gidan. Idan ta bazu, to kuturtar mai cutarwa ce, gidan kuma ya ƙazantu. 45 Dole ne a rushe gidan nan. Da duwatsun, da katakan, da dukkan shafen cikin gidan dole a kwashe su daga cikin birni zuwa wuri marar tsabta. 46 Bugu da ƙari, duk wanda ya shiga cikin gidan a lokacin da aka kulle gidan zai zama marar tsarki har maraice. 47 Duk wanda ya kwana a cikin gidan dole ya wanke tufafinsa, kuma duk wanda ya ci a cikin gidan dole ya wanke tufafinsa. 48 Idan firist ya shiga domin ya dudduba ya ga ko kuturtar ta yaɗu a cikin gidan bayan an yi wa gidan yaɓe, sa'an nan, idan kuturtar ta tafi, sai ya furta wannan gida tsarkakakke. 49 Sai dole firist ya ɗauki tsuntsayen biyu domin tsarkake gidan, da itacen sida, da shuɗin zare, da ɗaɗɗoya. 50 Sai ya kashe ɗaya tsuntsun a bisa ruwa mai tsabta cikin tukunyar yumɓu. 51 Zai ɗauki itacen sida, da ɗaɗɗoyar, da shuɗin zaren da kuma tsuntsun mai rai, ya tsoma su cikin jinin ɗaya tsuntsun da aka kashe, cikin ruwan nan mai tsabta, ya yayyafa gidan sau bakwai. 52 Zai tsarkake gidan da jinin tsuntsun da ruwan nan mai kyau, tare da tsuntsun nan mai rai, da itacen sida, da ɗaɗɗoya, da kuma jan zare. 53 Amma zai bar tsuntsun mai rai ya fita daga cikin birni ya tafi jeji. Ta haka ne dole zai yi kaffara domin gidan, zai kuma zama da tsarki. 54 Wannan ita ce shari'a domin dukkan irin cutar fata mai yaɗuwa, da abubuwan da ke sa irin wannan cuta, ko ƙaiƙayi, 55 da kuma kuturta a cikin tufafi da cikin gida, 56 da kumburi, da ƙuraje, da kuma tabo, 57 domin a tabbatar da lokacin da makamantan haka ba tsarki ko da tsarki. Wannan ita ce shari'a a kan cututtukan fatar jiki mai yaɗuwa da kuma kuturta.

Sura 15

1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa, 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, ka ce masu, "Yayin da kowanne mutum ya ke da ruwan da ke fitowa daga cikin jikinsa, ya zama ƙazantacce. 3 Ƙazantarsa sakamakon wannan cutar ruwan ce. Ko jikinsa yana zubar da ruwan ko ya tsaya, kazantacce ne. 4 Kowanne gadon da ya kwanta akai zai ƙazantu, duk abin da ya zauna akansa kuma zai ƙazantu. 5 Duk wanda ya taɓa gadonsa dole ya wanke tufafinsa kuma ya yi wanka cikin ruwa, kuma ya ƙazantu har yamma. 6 Duk wanda ya zauna akan kowanne abin da da mutum mai cutar zubar ruwan nan ya zauna akai, wannan mutum dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa, kuma zai zama marar tsabta har yamma. 7 Duk wanda ya taɓa jikin mai cutar zubar ruwa dole ya wanke tufafinsa kuma ya yi wanka cikin ruwa, ya ƙazantu har yamma. 8 Idan mutumin nan mai cutar zubar ruwa ya tofa miyau a bisa wani mai tsabta, daga nan wannan mutumin dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka cikin ruwa, kuma ya ƙazantu har yamma tayi. 9 Kowanne sirdi da mai zubar ruwan ya hau kai zai zama ƙazantacce. 10 Duk wanda ya taɓa kowanne abin da ke ƙarƙashin mutumin zai ƙazantu har yamma, kuma wanda ya ɗauki waɗannan abubuwan dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka cikin ruwa; ya ƙazantu har yamma ta yi. 11 Duk wanda mai cutar zubar ruwan ya taɓa ba tare da ya ɗauraye hannuwansa da farko cikin ruwa ba, mutumin da aka taɓa dole ya wanke tufafinsa ya yiwa kansa wanke cikin ruwa, kuma zai zama marar tsabta har yamma ta yi. 12 Kowacce tukunyar yumɓun da mai irin wannan zubar ruwan ya taɓa dole a fasata, kuma kowanne akushin itace dole a ɗauraye shi cikin ruwa. 13 Sa'ad da shi mai zubar ya tsarkaka daga zubar tasa, daga nan sai ya ƙirgawa kansa kwana bakwai domin tsarkakewarsa; daga nan dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa mai gudu. Daga nan zai tsarkaka. 14 A rana ta takwas dole ya ɗauki "yan kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai guda biyu ya zo gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa; a can dole ya bada tsuntsayen ga firist. 15 Dole firist ɗin ya miƙa su, ɗaya a matsayin hadayar zunubi ɗaya a matsayin ƙonanniyar hadaya, kuma dole firist ya yi kaffara domin sa a gaban Yahweh domin zubarsa. 16 Idan kowanne mutum yana da fitaccen maniyyi, daga nan dole ya wanke dukkan jikinsa cikin ruwa; zai zama marar tsabta har yamma. 17 Kowacce riga ko tufar fata inda akwai maniyyin dole a wanke ta da ruwa; zata zama marar tsarki har yamma. 18 Idan mace da miji suka kwanta tare kuma akayi canjin maniyyi zuwa gare ta, dole dukkansu su yi wanka cikin ruwa; zasu zama marasa tsarki har yamma. 19 Idan mace tana haila, rashin tsarkinta zai ci gaba har kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓata zai ƙazantu har yamma ta yi. 20 Kowanne abin data kwanta akai lokacin al'adarta zai zama marar tsarki; kowanne abin data zauna akansa kuma zai zama marar tsarki. 21 Duk wanda ya taɓa gadonta dole ya wanke tufafinsa kuma ya wanke kansa cikin ruwa; wannan mutumin zai zama marar tsarki har yamma. 22 Duk wanda ya taɓa kowanne abin data zauna a kansa dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa; wannan mutumin zai ƙazantu har yamma. 23 Ko akan gado ko akan kowanne abin da ta zauna akai, idan ya taɓa shi, wannan mutumin zai zama marar tsarki har yamma. 24 Idan kowanne mutum ya kwana da ita, kuma idan zubar rashin tsarkinta ya taɓa shi, zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowanne gadon da ta kwanta kai zai zama marar tsarki. 25 Idan mace tana zubar jini kwanaki da yawa wanda ba cikin kwanakin hailarta bane, ko idan tana zuba fiye da kwanakin hailarta, lokacin dukkan kwanakin zubar rashin tsarkinta, zata zama kamar tana cikin kwanakin hailarta. Marar tsarki ce. 26 Kowanne gadon data kwanta akai dukkan kwanakin zubar jininta zai zama a gareta kamar gadon data kwanta akai lokacin hailarta, kuma duk abin data zauna akai zai ƙazantu, kamar rashin tsarkin ta na haila. 27 Duk wanda ya taɓa kowanne ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai zama marar tsarki; dole ya wanke tufafinsa ya kuma wanke kansa cikin ruwa, kuma ya zama marar tsarki har yamma tayi. 28 Amma idan ta tsarkaka daga zubar jininta, daga nan sai ta lisafta wa kanta kwanaki bakwai, bayan wannan ta tsarkaka. 29 A rana ta takwas za ta ɗauki 'yan'kurciyoyi guda biyu ko 'yan' tantabarai guda biyu za ta kawo su wurin firist a ƙofar rumfa ta taruwa. 30 Firist zai miƙa tsuntsu ɗaya a matsayin hadaya ta zunubi, ɗayan kuma domin ƙonanniyar hadaya, kuma zai yi kaffara domin ta a gaban Yahweh domin zubar jininta. 31 Ta haka za ku keɓe mutanen Isra'ila daga ƙazantarsu, domin kada su mutu ta wurin ƙazantarsu, ta wurin ɓata rumfar sujadata, in da nake zama a tsakiyar su. 32 Waɗannan su ne ka'idodi domin duk wanda ya ke zubar ruwa, domin kowanne mutum da maniyinsa ya fita daga gare shi ya sa shi ya zama marar tsarki, 33 ga kowacce mace da ke haila, da duk wanda ya ke zubar ruwa, ko namiji ko mace, da kuma duk wanda ya kwana da matar da ta ƙazanta.'"

Sura 16

1 Yahweh ya yi magana da Musa -- wannan bayan mutuwar 'ya'yan Haruna guda biyu, lokacin da suka kusato Yahweh kuma suka mutu. 2 Yahweh ya ce da Musa. "Ka yi magana da Haruna ɗan'uwanka ka ce masa kada kowanne lokaci ya riƙa shiga wuri mai tsarki cikin labule, a gaban mazaunin jinƙai wanda ke bisa kan akwatin al̀ƙawari. Idan ya yi haka, zai mutu, saboda ina bayyana cikin girgije a bisa mazaunin jinƙai. 3 Don haka ga yadda Haruna zai shiga wuri mafi tsarki. Dole ya shiga da ɗan bijimi domin hadaya ta zunubi, da rago domin hadaya ta ƙonawa. 4 Dole ya sanya riga mai tsarki, kuma dole ya sa riga 'yarciki a jikinsa, kuma dole ya sa ɗamarar linin da rawanin linin. Waɗannan su ne riguna masu tsarki. Dole ya wanke jikinsa cikin ruwa daga nan ya shirya kansa da waɗannan rigunan. 5 Dole ya karɓi bunsura biyu daga taron jama'ar Isra'ila a matsayin baikon zunubi da rago ɗaya domin ƙonanniyar hadaya. 6 Daga nan dole Haruna ya miƙa bijimi domin baikon zunubi, wanda ya ke domin kansa, zai yi kaffara domin kansa da iyalinsa. 7 Daga nan dole ya ɗauki bunsura biyun ya ajiye su gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa. 8 Daga nan dole Haruna ya jefa ƙuri'a domin bunsuran biyu, ɗaya domin Yahweh, ɗaya a matsayin refataccen bunsuru. 9 Daga nan dole Haruna ya miƙa bunsurun da ƙuri'a ta faɗa wa ga Yahweh, kuma ya miƙa bunsurun a matsayin baikon zunubi. 10 Amma bunsurun da ƙuri'a ta faɗa wa a matsayin refataccen bunsuru dole a kawo shi da rai gaban Yahweh, domin kaffara ta wurin aikar da shi a matsayin refataccen bunsuru cikin jeji. 11 Daga nan dole Haruna ya miƙa bijimi domin baikon zunubi, wanda zai zama domin kansa. Dole ya yi kafara domin kansa da kuma domin iyalinsa, dole ya yanka bijimi a matsayin baikon zunubi domin kansa. 12 Dole Haruna ya ɗauki kasko cike da garwashin wuta daga bisa bagadi gaban Yahweh, hannuwansa kuma cike da gyararren garin turare mai ƙanshi, ya kuma kawo waɗannan abubuwan cikin labule. 13 A can dole ya ɗibiya turare akan wuta gaban Yahweh domin hayaƙi daga turaren ya rufe marfin kaffara a bisa dokokin alƙawarin. Dole ya yi haka domin kada ya mutu. 14 Daga nan dole ya ɗauki jinin bijimi ya yayyafa shi da yatsansa a gaban marfin kaffara. Dole ya yayyafa sauran jinin da yatsansa sau bakwai gaban mazaunin jinƙai. 15 Sa'an nan dole ya yanka bunsuru domin hadayar zunubi wanda ya ke domin jama'a ya kawo jininsa cikin labule. A can dole ya yi da jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin: Dole ya yayyafa shi a bisa murfin kafara da kuma gaban murfin kafara. 16 Dole ya yi kafara domin wuri mai tsarki saboda ƙazantar ayyukan mutanen Isra'ila, da kuma domin tayarwarsu da dukkan zunubansu. Dole kuma ya yi haka kuma domin rumfar taruwa, inda Yahweh ke zama cikinsu, a gaban ƙazantattun ayyukansu. 17 Ba wanda zai kasance a rumfar taruwa sa'ad da Haruna ya shiga domin ya yi kaffara cikin wuri mafi tsarki, har lokacin da ya fito ya kuma gama yin kaffara domin kansa da kuma iyalinsa, da kuma dukkan taron Isra'ila. 18 Dole ya fita zuwa bagadin da ke gaban Yahweh domin ya yi kaffara domin sa, kuma dole ya ɗibi jinin bijimi da jinin akuyar ya sa shi a bisan ƙahonnin bagadi ko'ina kewaye. 19 Dole ya yayyafa daga cikin jinin a kai da yatsansa sau bakwai ya tsabtace shi ya keɓe shi ga Yahweh, nesa daga ƙazantar ayyukan mutanen Isra'ila. 20 Sa'ad da ya gama yin kaffara domin wuri mafi tsarki, rumfar taruwa, da bagadi, dole ya miƙa bunsurun mai rai. 21 Dole Haruna ya ɗibiya hannayensa a kan bunsurun mai ran ya furta dukkan muguntar mutanen Isra'ila, dukkan tayarwarsu, da dukkan zunubansu. Daga nan dole ya sa zunubansu a kan bunsurun ya sallami bunsurun ta wurin kulawar mutumin da ya shirya ya jagoranci bunsurun zuwa cikin jeji. 22 Dole bunsurun ya ɗaukarwa kansa dukkan muguntar mutane zuwa wurin da ba kowa. A can cikin jeji, mutumin zai saki bunsurun ya tafi hakanan. 23 Daga nan dole Haruna ya koma cikin rumfar taruwa ya tuɓe rigunansa na linin waɗanda ya sa kafin ya shiga wuri mafi tsarki, kuma dole ya bar rigunan can. 24 Dole ya wanke jikinsa a cikin ruwa cikin wuri mai tsarki, ya sa tufafinsa da ya saba; daga nan dole ya fito ya miƙa baikonsa na ƙonawa da baikon ƙonawa domin jama'a, ta haka zai yi kaffara domin kansa kuma domin jama'a. 25 Dole ya ƙone kitsen baikon zunubi a bisa kan bagadi. 26 Mutumin da ya bar refataccen bunsuru ya tafi dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa; bayan haka, zai iya dawowa cikin sansani. 27 Bijimi domin baikon zunubi da bunsurun domin baikon zunubi, wanda aka kawo jininsu domin kaffara cikin wuri mai tsarki, dole a ɗauke su waje bayan sansani. A can dole su ƙone fatarsu, namansu, da kashinsu. 28 Mutumin da ya ƙone waɗannan sassan dole ya wanke tufafinsa ya wanke jikinsa cikin ruwa; bayan haka, zai iya dawowa cikin sansani. 29 Zai zama farilla a gare ku kullum a cikin wata na bakwai, a bisa rana ta goma, dole ku ƙasƙantar da kanku kada ku yi aiki, ko wanda aka haifa ɗan gari ko bãƙo wanda ya ke zama a cikinku. 30 Saboda a ranar nan za ayi kaffara domin ku, a tsarkake ku daga dukkan zunubanku domin ku tsarkaka a gaban Yahweh. 31 Assabat ta musamman ta hutawa domin ku, dole kuma ku ƙasƙantar da kanku kada ku yi wani aiki. Wannan zai zama farilla a gare ku kullum. 32 Babban firist, wanda za a zuba masa mai a keɓe shi ya zama babban firist a madadin mahaifinsa, dole ya yi wannan kaffarar ya sa tufafin linin, wato, tufafi masu tsarki. 33 Zai yi kaffara domin wuri mafi tsarki; dole ya yi kaffara domin rumfar taruwa da kuma domin bagadi, kuma dole ya yi kaffara domin firistoci kuma domin dukkan taron jama'a. 34 Wannan zai zama farilla a gare ku koyaushe, a yi kaffara domin mutanen Isra'ila saboda dukkan zunubansu, sau ɗaya a cikin shekara." An yi haka kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.

Sura 17

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa, da dukkan mutanen Isra'ila. Ka faɗa masu abin da Yahweh ya umarta: 3 'Duk mutumin da ke daga gidan Isra'ila wanda ya kashe sã, rago ko akuya a cikin sansani, ko wanda ya kashe shi a bayan sansani, domin ya miƙa shi hadaya - 4 idan bai kawo shi a ƙofar rumfar taruwa ya miƙa shi hadaya ga Yahweh a gaban mazaunin sa ba, wannan mutum ya zama da laifin zubar da jini. Ya zubar da jini, wannan mutum dole a datse shi daga cikin jama'arsa. 5 Dalilin wannan dokar shi ne domin mutanen Isra'ila su kawo hadayunsu ga Yahweh a ƙofar rumfar taruwa, wurin firist domin hadaya a matsayin baikon zumunta ga Yahweh, maimakon baikon hadayun da suke miƙawa a fili. 6 Firist zai yayyafa jinin a bisa bagadin Yahweh a ƙofar rumfar taruwa, zai ƙona kitsen domin ya bada ƙanshi mai daɗi domin Yahweh. 7 Nan gaba mutanen ba za su ƙara miƙa hadayunsu ga gumakan bunsuru ba, domin sun aikata kamar karuwai. Wannan zai zama farilla ta din-din din a gare su ga dukkan tsararsu.' 8 Dole ka ce masu, 'Kowanne mutumin Isra'ila, ko kowanne baƙon da ke zaune a cikinsu, wanda ya miƙa baikon ƙonawa ko hadaya 9 kuma bai kawo ta a ƙofar rumfar taruwa domin a miƙa ta ga Yahweh ba, wannan mutumin dole a fitar da shi daga jama'arsa. 10 Idan wani mutumin gidan Isra'ila, ko wani baƙon da ke zaune a cikin su ya sha kowanne irin jini, zan sa fuskata gãba da wannan mutum da ya sha jini kuma zan datse shi daga cikin jama'arsa. 11 Gama ran dabba yana cikin jininsa. Na bada jininsa gare ku domin ku yi kaffara a bisa bagadi domin rayukanku, saboda jini ne ke yin kaffara, gama jini ke yin kaffara domin rai. 12 Domin wannan na ce da mutanen Isra'ila ba wani a cikinku da zai ci jini, ko kowanne bãƙo da ke zaune a cikinku ya ci jini. 13 Kowanne mutumin Isra'ila, ko baƙin da ke zaune a cikinsu, wanda ya yi farauta ya kashe dabba ko tsuntsun da za a iya ci, dole wannan mutumin ya zubar da jinin sa'an nan ya rufe jinin da ƙasa. 14 Gama ran dukkan halitta yana cikin jininta. Shi ya sa na ce da mutanen Isra'ila, "Ba za ku ci jinin kowacce halitta ba, gama ran kowacce halitta yana cikin jininta. Duk wanda ya ci ya zama dole a datse shi." 15 Kowanne mutumin da ya ci dabbar data mutu ko wadda namomin jeji suka yayyaga, ko mutumin nan haifaffen gida ne ko baƙon da ke zama a cikinku, dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har yamma. Sa'an nan zai tsarkaka. 16 Amma idan bai wanke tufafinsa ba ko ya wanke jikinsa ba, daga nan dole ya ɗauki alhakin laifinsa.'"

Sura 18

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Ni ne Yahweh Allahnku. 3 Ba za ku yi abubuwan da mutane ke yi a Masar ba, in da kuka taɓa zama. Ba za ku yi abubuwan da mutane ke yi a Kan'ana ba, ƙasar da nake kai ku. Kada ku bi al'adunsu. 4 Shari'una su ne za ku yi dole, dokokina kuma su ne za ku kiyaye dole, domin ku yi tafiya cikinsu, saboda ni ne Yahweh Allahnku. 5 Don haka dole ku kiyaye umarnaina da shari'una. Idan mutum ya yi biyayya da su, zai rayu saboda su. Ni ne Yahweh. 6 Ba wanda zai kwanta da kowanne dangi na kusa domin ya buɗe tsiraicinsa. Ni ne Yahweh. 7 Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwanciya da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce! Kada ka ƙasƙantar da ita. 8 Kada ka kwana da kowacce matar mahaifinka; kada ka ƙasƙantar da mahaifinka kamar haka. 9 Kada ka kwana da kowacce 'yar'uwarka, ko ita ɗiyar mahaifinka ce ko ɗiyar mahaifiyarka, ko a gidan ku ta girma ko a wani gida na nesa da kai. Kada ka kwana da 'yan'uwanka mata. 10 Kada ka kwana da ɗiyar ɗanka ko ɗiyar 'yarka. Wannan zai zama abin kunya gare ka. 11 Kada ka kwana da ɗiyar matar mahaifinka, wadda mahaifinka ya haifa. Ita 'yar'uwarka ce, kuma kada ka kwana da ita. 12 Kada ka kwana da 'yar'uwar mahaifinka, Ita 'yar'uwar mahaifinka ce ta kusa. 13 Kada ka kwana da 'yar'uwar mahaifiyarka. Ita 'yar'uwar mahaifiyarka ce ta kusa. 14 Kada ka ƙasƙantar da ɗan'uwan mahaifinka ta wurin kwana da matarsa. Kada ka yi kusa da ita akan wannan dalili; ita bãbarka ce. 15 Kada ka kwana da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ce; kada ka kwana da ita. 16 Kada ka kwana da matar ɗan'uwanka; kada ka ƙasƙantar da shi ta wurin yin haka. 17 Kada ka kwana da mace da ɗiyarta kuma, ko ɗiyar ɗanta ko ɗiyar 'yarta. Su danginta ne na kusa, kwana da su zai zama mugunta. 18 Ba zaka auri 'yar'uwar matarka a matsayin kishiyarta ba kuma ka kwana da ita yayin da matarka ta farko na da rai. 19 Kada ka kwana da mace a lokacin hailarta. Ba ta da tsarki a wannan lokacin. 20 Kada ka kwana da matar maƙwabcinka kuma ka ƙazantar da kanka da ita ta wannan hanya. 21 Kada ka bada ko ɗaya daga cikin 'ya'yanka a sa su cikin wuta, domin ka miƙa su hadaya ga Molek, saboda ba za ka tozarta sunan Allahnka ba. Ni ne Yahweh. 22 Kada ka kwana da wasu maza kamar yadda ake yi da mace. Wannan zai zama mugunta. 23 Kada ka kwana da kowacce dabba ka kuma ƙazantar da kanka da ita. Ba wata mace da zata kwana da kowacce dabba. Wannan zai zama keta doka. 24 Kada ka ƙazantar da kanka ta kowanne irin waɗannan hanyoyi, gama ta cikin irin waɗannam hanyoyi ne al'ummai suka ƙazantu, al'umman da na kora daga gaban ku. 25 ƙasar ta ƙazantu, na hukunta zunubansu, ƙasar ta amayar da mazaunanta. 26 Domin haka, ku, dole ku kiyaye dokokina da umarnaina, kuma ba za ku aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan banƙyama ba, ko haifaffen Ba - Isra'ile ko bãƙon da ke zaune a cikinku. 27 Gama wannan ita ce muguntar da mutanen cikin ƙasar da suka rigaye ku suka aikata, waɗanda suka zauna nan kafin ku, yanzu kuma ƙasar ta ƙazantu. 28 Don haka sai ku yi hankali don kada ƙasar ta amayar da ku bayan da kun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da mutanen da suka rigaye ku. 29 Duk wanda ya aikata kowanne ɗaya daga cikin abubuwan banƙyamar nan, mutanen da suka yi waɗannan za a datse su daga cikin jama'arsu. 30 Don haka dole ku kiyaye dokata kada ku aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan al'adun mãsu banƙyama waɗanda aka aikata a nan a gaban ku, domin kada ku ƙazantar da kanku ta wurin su. Ni ne Yahweh Allahnku.'"

Sura 19

1 Yahweh ya yi magana da Musa cewa, 2 "Ka yi magana ga dukkan taron jama'ar Isra'ila ka ce masu, "Dole ku zama da tsarki, gama ni Yahweh Allahnku mai tsarki ne. 3 Kowanne dole ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, kuma dole ku kiyaye assabataina. Ni ne Yahweh Allahnku. 4 Kada ku juya ga gumakai marasa amfani, ko ku yi wa kanku alloli na ƙarfe. Ni ne Yahweh Allahnku. 5 Sa'ad da ka miƙa hadaya ta zumuntar baye-baye ga Yahweh, dole ka miƙa ta yadda za a karɓe ka. 6 Dole a cinye ta a ranar da aka miƙa ta, ko kuma washegari. Idan wani abu ya rage har rana ta uku, dole a ƙone shi da wuta. 7 Idan anci ta ko kaɗan a kan rana ta uku, naman ya zama marar tsarki; ba za a karɓe ta ba, 8 kuma duk wanda ya ci dole ya ɗauki alhakin laifinsa saboda ya ƙazantar da abin da ke mai tsarki na Yahweh, wannan mutum dole a datse shi daga jama'arsa. 9 Sa'ad da kuka girbe amfanin ƙasarku, ba za ku girbe kusurwowin gonarku dukka ba, ba kuma za ku tattara dukkan amfanin girbin ku ba. 10 Ba za ku tattara kowanne inabi daga garkar inabin ba, ko ku tattara inabin da ya faɗi a ƙasa cikin garkar. Dole ku bar su domin matalauta kuma domin bãƙi. Ni ne Yahweh Allahnku. 11 Kada ku yi sata. Kada ku yaudari juna. 12 Kada ku rantse da sunana kan ƙarya kuma ku tozarta sunan Allahnku. Ni ne Yahweh. 13 Kada ka zalunci makwabcinka ko ka yi masa fashi. Haƙin bawan da aka yi hayarsa kada ya kwana wurinka har safiya. 14 Kada ka la'anta kurma ko ka sa abin tuntuɓe gaban makaho. Maimakon haka, dole ku ji tsoron Allah. Ni ne Yahweh. 15 Kada ka aikata rashin gaskiya cikin shari'a. Kada ka nuna tãra ga wani saboda shi talaka ne, kuma kada ka nuna tãra ga wani saboda muhimmancinsa. Maimakon haka, ka shari'anta makwabcinka bisa ga adalci. 16 Kada ka yi tafiyar yawon ɓatanci a cikin mutanenka, amma ka nemi kare ran makwabcinka. Ni ne Yahweh. 17 Kada ka ƙi ɗan'uwanka a zuciyarka. Dole ka tsauta wa maƙwabcinka akan gaskiya domin kada zunubinsa ya shafe ka. 18 Kada ka ɗaukar wa kanka fansa ko ka riƙe shi da ƙiyayya gãba da wani cikin mutanenka, amma maimakon haka sai ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Yahweh. 19 Dole ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da wasu irin dabbobi dabam. Kada ku cuɗa iri biyu lokacin da kuke shuka a gonarku. Kada ku sa tufafin da aka yi da ke da haɗe-haɗe iri biyu tare. 20 Duk wanda ya kwana da yarinyar da take baiwa wadda aka alƙawarta wa miji, amma ba a fanshe ta ba ko 'yanta ta ba, dole a hukunta su. Ba za a kashe su ba saboda ba a 'yanta ta ba. 21 Sai mutumin ya kawo baikon laifinsa ga Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa - rago domin hadayar laifi. 22 Daga nan firist zai yi kaffara domin sa da rago domin baikon laifi a gaban Yahweh, domin zunubin da ya aikata. Daga nan za a gaffarta masa zunubin da ya yi. 23 Sa'ad da kuka zo cikin ƙasar kuma kuka dasa ko waɗanne irin itatuwa domin abinci, sai ku maida 'ya'yan itatuwansu haramtattu gare ku har shekaru uku. Ba za ku ci su ba. 24 Amma a cikin shekara ta huɗu dukkan amfaninsu za su zama mãsu tsarki, baikon yabo ga Yahweh. 25 A cikin shekara ta biyar za ku iya cin amfanin, domin kun jira saboda itatuwan su ƙara ba da 'ya'ya da yawa. Ni ne Yahweh Allahnku. 26 Kada ku ci kowanne irin nama tare da jininsa a cikinsa. Kada ku tuntuɓi ruhohi game da abin da zai faru nan gaba, kada ku nemi ku mulki waɗansu ta wurin manyan ikoki ko duba. 27 Ba za ku aske gashin kanku a kewaye ko ku aske ƙarshen gemunku ba. 28 Kada ku yanke jikinku domin matattu ko ku yi tsaga a jikinku. Ni ne Yahweh. 29 Kada ka kunyatar da ɗiyarka ta wurin sa ta karuwanci, ko ƙasar ta faɗa cikin karuwanci ƙasar kuma ta cika da mugunta. 30 Dole ku kiyaye Assabataina ku girmama mazaunina mai tsarki. Ni ne Yahweh. 31 Kada ku juya wurin waɗanda suke magana da matattu ko da ruhohi, kada ku neme su, domin za su ƙazantar da ku. Ni ne Yahweh Allahnku. 32 Dole ku tashi tsaye gaban wanda ya ke da furfura kuma ku gimama kasancewar dattijo. Dole ku ji tsoron Allah. Ni ne Yahweh. 33 Idan bãƙo na zaune a wurinku cikin ƙasarku, kada ku cutar da shi. 34 Bãƙon da ke zaune tare da ku dole ya zama kamar haifaffen Ba-Isra'ile wanda ya ke zama a cikin ku, kuma dole ka ƙaunace shi kamar kanka, saboda dã ku bãƙi ne a cikin ƙasar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku. 35 Kada ku yi awo da ma'aunin ƙarya lokacin auna tsawo, nauyi ko yawa. 36 Dole ku yi amfani da ma'auni, madaidaici, kwanon gaskiya kofi na gaskiya. Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fitar da ku daga ƙasar Masar. 37 Dole ku kiyaye dukkan farillaina da dokokina, kuma ku aikata su. Ni ne Yahweh.'"

Sura 20

1 Yahweh ya yi magana da Musa cewa, 2 "Ka faɗa wa mutanen Isra'ila 'Duk wanda ke daga cikin jama'ar Isra'ila, ko bãƙon da ke zaune a cikin Isra'ila ya miƙa ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga gunkin nan Molek, dole a kashe shi. Dole mutanen cikin ƙasar su jejjefe shi da duwatsu. 3 Zan kuma sa fuskata gãba da wannan mutumin in kuma datse shi daga cikin mutanensa domin ya miƙa ɗansa ga Molek, domin ya ƙazantar da wurina mai tsarki ya kuma muzanta sunana mai tsarki. 4 Idan jama'ar ƙasar suka kulle idanunsu ga wannan mutumin a lokacin da ya ke miƙa ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, Idan suka ƙi kashe shi, 5 Sa'an nan Ni da kaina zan sa fuskata gãba da wannan mutumin da danginsa, zan kuma datse shi da kuma dukkan wanda ya shiga karuwanci domin ya aikata karuwaci tare da Molek. 6 Mutum wanda ya juya ga wa‌ɗ‌anda suke magana da matattu, ko ga waɗanda ke magana da ruhohi don ya yi karuwanci tare da su, Zan sa fuskata gãba da wannan mutumin; Zan datse shi daga cikin mutanen sa. 7 Don haka ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni ne Yahweh Allahnku. 8 Dole ku kiyaye umarnaina ku kuma aikata su. Ni ne Yahweh wanda ya ke‌ɓe ku a matsayin tsarkaka. 9 Duk wanda ya la'anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi. Ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, to ya yi laifi kenan ya kuma cancanci mutuwa. 10 Mutumin da ya yi zina da matar wani, wato, dukkan wanda ya yi zina da matar maƙwabcinsa - mazinacin da mazinaciyar dole ne a kashe su. 11 Idan mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya buɗe tsiraicin mahaifinsa. Da ɗan da matar mahaifinsa dole a kashe su. Alhakin jininsu na kansu. 12 Idan mutum ya kwana da matar ɗansa, dukkan su dole ne a kashe su, sun aikata abin ƙyama. Masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa. 13 Idan mutum ya kwana da namiji, yadda ake yi da mace, dukkansu sun aikata mummunan abin ƙyama. Hakika tilas ne a kashe su. Masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa. 14 Idan mutum ya auri mace ya kuma auri mahaifiyarta, wannan mugunta ce. Dole ne a ƙone su, shi da matar dukka, domin ya zama babu mugunta a tsakiyarku. 15 Idan mutum ya kwana da dabba, dole ne a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar. 16 Idan mace ta kusanci kowacce dabba domin ta kwana da ita, dole ku kashe macen da dabbar. wajibi ne ku kashe su. masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa. 17 Idan mutum ya kwana da 'yar'uwarsa, ɗiyar mahaifinsa ko ɗiyar mahaifiyarsa, ya kuma buɗe tsiraicinta, ita kuma ta ga tsiraicinsa, abin kunya ne. Dole a datse su daga gaban jama'arsu, saboda ya kwana da ƴar'uwarsa. Dole ya ɗauki alhakin sa. 18 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin jinin al'adarta har ya kwana da ita, har ya buɗe jinin da ke gudanowa daga jikinta, maɓulɓular jininta. Da mutumin da matar dole a datse su daga cikin jama'arsu. 19 Ba za ka kwana da 'yar'uwar mahaifiyarka ba, ko kuma da 'yar'uwar mahaifinka, domin zaka ‌ƙas‌ƙantar da danginka na kusa. Wajibi ne ka ɗauki alhakinka. 20 Idan mutum ya kwana da bãbarsa, ya ƙasƙantar da kawunsa. Za su ɗ‌auki hakkin zunubinsu, za su kuma mutu babu 'ya'ya. 21 Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa sa'ad da ɗan'uwansa ke da rai, wannan ƙasƙanci ne. Ya ƙasƙantar da ‌ɗan'uwansa, kuma zan ɗauke wa 'ya'yansu duk wata mallaka da suka gada daga iyayensu. 22 Saboda haka wajibi ne ku kiyaye dukka farillaina da dukkan dokokina; Dole ku yi biyayya da su domin kada ƙasar da Na ke kai ku domin ku zauna a ciki ta amayar da ku daga cikinta. 23 Ba za ku yi tafiya cikin al'adun al'umman da nake kora daga gabanku ba, domin sun aikata duk waɗannan abubuwan, kuma na ƙyamace su. 24 Na faɗa maku, "Za ku gãji ƙasarsu; Zan ba ku ita ku mallaketa, ƙasa mai ɓulɓulo da madara da zuma. Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran mutane. 25 Dole ne ku bambanta tsakanin dabbobi masu tsarki da marasa tsarki, da kuma tsakanin tsuntsaye marasa tsarki da masu tsarki. Wajibi ne ku ƙaurace wa ƙazantar da kanku da dabbobi ko tsuntsaye ko da kowacce irin halitta mai rarraffe akan ƙasa, wanda Na keɓe su a matsayin ƙazamtattu daga gare ku. 26 Dole ne ku zama da tsarki, gama Ni, Yahweh, Mai Tsarki ne, kuma Na keɓe ku daga sauran mutane, saboda ku nawa ne. 27 Mutum ko matar da ke yin magana da matacce ko suke yin magana da ruhohi dole ne a kashe su. Dole jama'a su jejjefe su da duwatsu. masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa.'"

Sura 21

1 Yahweh ya cewa Musa: "Ka yi magana da firistoci, 'ya'ya maza na Haruna, ka ce masu, 'Kada a sami wani a cikinku da zai ƙazantar da kansa da gawar wanda ya mutu daga cikin mutanensa, 2 sai dai idan shi dangi ne na kusa - mahaifiyarsa, mahaifinsa, ɗansa, 'yarsa, ɗan'uwansa, 3 ko 'yar'uwarsa budurwa wadda ya ke rike da ita, tunda ya ke bata da miji - saboda ita yana iya ƙazantar da kansa. 4 Amma kada ya ƙazantar da kansa saboda wa‌ɗansu dangi ta haka ya kuma ‌ɓata kansa. 5 Firistoci ba za su aske kansu ko su aske gefen gemun su, ko su yanka jikkunnansu ba. 6 Dole su zama tsarkaka ga Allahnsu, kada kuma su ƙasƙantar da sunan Allahnsu, gama firistoci ke mi‌ƙa hadayun Yahweh na abinci, gurasa ta Allahnsu. Don haka wajibi ne firistoci su zama da tsarki. 7 Ba za su auri kowacce mace wadda take karuwa ba da wadda aka ɓata, Kuma ba za su auri mace wadda mijinta ya sake ta ba, domin su keɓaɓɓu ne ga Allahnsu. 8 Za ku keɓe shi, domin shi ne mai miƙa gurasa ga Allahnku. Dole ya zama da tsarki gare ku, domin Ni, Yahweh wanda ya tsarkake ku, Mai Tsarki ne. 9 Duk wata ɗiya ta firist da ta ƙazantar da kanta ta wurin zama karuwa ta ƙasƙantar da mahaifinta. Dole a ƙone ta. 10 Wanda ya ke shi ne babban firist daga cikin "yan'uwansa, wanda aka zuba mai na keɓewa a kansa, wanda kuma aka tsarkake domin ya sa rigar babban firist, ba zai kwance gashin kansa ko ya keta tufafinsa ba. 11 Ba zai je wurin da akwai gawa ba ya kuma ƙazantar da kansa, ko da mataccen mahaifinsa ne ko mahaifiyarsa ce. 12 Babban firist ba zai bar harabar haikali ko ya ƙazantar da haikalin Allahnsa ba, domin an keɓe shi a matsayin babban firist ta wurin man keɓewa na Allahnsa. Ni ne Yahweh. 13 Wajibi ne babban firist ya auri budurwa a matsayin matarsa. 14 Ba zai auri gwauruwa, ko sakakkiyar mace, ko mace wadda take karuwa ba. Ba zai auri irin waɗannan matan ba. Zai iya auren budurwa daga cikn jama'arsa, 15 domin kada ya ƙazantar da 'ya'yansa daga cikin jama'arsa, domin Ni ne Yahweh, wanda ya maishe shi tsarkakakke.'" 16 Yahweh ya yi magana da Musa, ya ce, 17 "Ka yi magana da Haruna ka faɗa masa, 'Dukkan wanda aka samu da wata nakasar jiki cikin zuriyarka a dukkan tsararrakinsu, ba zai matso kusa domin ya miƙa abinci ga Allahnsa ba. 18 Kowanne mutum da ke da nakasa a jiki kada ya kusanci Yahweh, irin wannan makahon ko mutumin da bai iya tafiya, shi da ya ke da nakasa a jiki ko fuskar, 19 mutumin da ke da nakasa a hannu ko a ƙafa, 20 mutumin da ke da ƙusumbi a bayansa ko shanyayye ko wãda, ko mutumin da ke da hãkiya a idanunsa, ko ya ke da cuta, gyambo, ƙurji, ko rauni a mazakutta. 21 Ba wani mutum daga cikin zuriyar Haruna firist mai nakasa a jikinsa da zai matso kusa domin ya miƙa baye-bayen da ake miƙawa da wuta ga Yahweh. Irin wannan mutumin mai naƙasa a jiki; kada ya zo kusa domin ya miƙa gurasar Allahnsa. 22 Ya iya cin abincin Allahnsa, ko daga cikin mafi tsarki ko kuma daga cikin mai tsarki. 23 Duk da haka, Ba zai shiga daga cikin labulen ko ya zo kusa da bagadi ba, saboda yana da naƙasa a jikinsa, domin kada ya ƙazantar da tsattsarkan wurina, gama Ni ne Yahweh, wanda ya tsarkake su."' 24 Haka Musa ya fa‌ɗawa Haruna wa‌ɗ‌annan maganganu, ga 'ya'yansa, da kuma ga dukkan mutanen Isra'ila.

Sura 22

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza, ka fa‌ɗa masu su kiyaye kansu daga kayayyaki masu tsarki na mutanen Isra'ila, waɗanda suka keɓe gare ni. Ba za su ƙasƙantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Yahweh. 3 Ka faɗa masu, 'Idan wani daga cikin zuriyarku cikin dukkan tsararrakinku ya kusanci kayayyaki masu tsarki da jama'ar Isra'ila suka keɓe ga Yahweh, a sa'ad da ya ke marar tsarki, wannan mutumin dole a datse shi daga gabana: Ni ne Yahweh. 4 Kada wani daga cikin zuriyar Haruna wanda ke da cutar fata, ko mai miki da ke zubar da ruwa daga jikinsa, ya ci ko ɗaya daga wa‌ɗannan hadayun da aka miƙa ga Yahweh har sai ya tsarkaka. Dukkan wanda ya taɓa wani abu marar tsarki ta wurin taɓa gawa, ko ta wurin taɓa mutum mai zub da maniyyi, 5 ko kowacce dabba mai rarrafe data ƙazantar da shi, ko kowanne mutum ɗaya maida shi marar tsarki, ko dai kowacce irin ƙazanta ta zama- 6 daga nan firist wanda ya taɓa kowanne abu marar tsarki zai zama marar tsarki har maraice. Ba zai ci duk wani abu mai tsarki ba, har sai ya wanke jikinsa a cikin ruwa. 7 Sa'ad da rana ta fa‌ɗi, zai zama tsarkakakke. Bayan rana ta faɗi ya iya ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa, domin su abincinsa ne. 8 Ba zai ci duk abin da aka same shi matacce ba ko abin da naman jeji ya kashe, wanda ta wurin haka zai ƙazantar da kansa. Ni ne Yahweh. 9 Wajibi ne firistoci su bi umarnaina, domin kada su yi zunubi, su mutu domin muzanta ni. Ni ne Yahweh wanda ke tsarkake su. 10 Kada wanda ba daga iyalin firist ya ke ba, duk da baƙon da ya sauka a gidan firist ko barorinsa, ya ci duk abin da ya ke tsatstsarka. 11 Amma idan firist ya sayi wani bawa da ku‌ɗinsa, wannan bawan na iya ci daga cikin abin da aka keɓe ga Yahweh. Iyalan gidan firist da kuma bayin da aka haifa a gidansa, za su iya cin waɗannan abubuwan tare da shi. 12 Idan ɗiyar firist ta auri wani mutum wanda ba firist ba, ba za ta ci ko ‌ɗaya daga cikin baye-bayen gudunmuwa mai tsarki ba. 13 Amma idan ɗiyar firist ɗin gwauruwa ce, ko kuma sakakkiya, kuma idan bata da ɗa, kuma idan ta koma ta zauna a gidan mahaifinta kamar a lokacin ƙuruciyarta, za ta iya ci daga cikin abincin mahaifinta. Amma kada wani wanda ba daga cikin iyalin firist ya ke ba yaci abincin firist. 14 Idan mutum yaci abinci mai tsarki ba da sani ba, dole ya biya firist abin da ya ci; wajibi ne ya ƙara kashi ɗaya bisa biyar akan abin ya kuma maida wa firist. 15 Mutanen Isra'ila ba za su ƙazantar da abubuwa masu tsarki waɗanda suka ‌ɗaga sama suka miƙa ga Yahweh ba. 16 Su jawowa kansu ɗaukar zunubin da zai sa su yi laifin cin abinci mai tsarki, gama Ni ne Yahweh wanda ya ke tsarkake su." 17 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 18 "Ka yi magana da Haruna shi da 'ya'yansa maza, da dukkan mutanen Isra'ila. Ka fa‌ɗ‌a masu, 'Duk Ba-Israi'le, ko bãƙon da ke zaune cikin Isra'ila, lokacin da suka kawo hadaya- kodai ta cika wa'adi, ko ta bayarwar yadda rai, ko idan sun kawo hadayar ƙonawa ga Yahweh, 19 Idan za ta zama karɓaɓɓiya, dole su miƙa dabba namiji marar aibu daga cikin garken shanu, tumaki, ko awaki. 20 Amma kada ku miƙa duk wani abu mai aibu. Ba zan karbe su a maimakon ku ba. 21 Kowanne mutum da ya miƙa hadaya ta salama daga cikin garke ko tumaki ga Yahweh don cika wa'adi, ko a matsayin bayarwar yardar rai, dole ta zama marar aibu kafin a kar‌ɓe ta. Kada a sami nakasa cikin dabbar. 22 Ba zaku miƙa mani dabbobi makafi ba, ko guragu, ko naƙasassu, ko masu kirci, ko masu ƙuraje, ko tabbai. Ba za ku miƙa waɗannan ga Yahweh a matsayin hadaya ta ƙonawa a kan bagadi ba. 23 Zaku iya miƙa bayarwar yardar rai da sã, ko da ‌ɗ‌an rago da ke da naƙasa ko ƙanƙane, amma bayarwa irin wannan ba za ta karɓu domin cika wa'adi ba. 24 Kada ku miƙa wa Yahweh kowacce dabbar da ke da ƙurji, gurzajje, yayyagagge, ko dandaƙaƙƙe ba. Ba za ku yi wannan a cikin ƙasarku ba. 25 Kada kubar baƘo ya miƙa maku gurasa ga Allahnku. Wa‌ɗannan dabbobin naƙasassu ne suna kuma da aibu a cikin su, ba za'a karɓe su a madadinku ba." 26 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 27 "Sa'ad da aka haifi ɗan maraki, ko ɗan tunkiya ko ɗan akuya, dole ya zauna tare da mahaifiyarsa har kwana bakwai. A kwana na takwas, a iya karbar shi a matsayin hadayar ƙonawa da wuta ga Yahweh. 28 Ba za ku kashe saniya ko tunkiya tare da ƙananunsu, dukka a rana ‌ɗ‌aya ba. 29 Duk sa'ad da kuke miƙa hadaya ta godiya ga Yahweh, dole ku miƙa ta ta karɓaɓɓiyar hanya. 30 Dole ku cinye naman hadayar a ranar da aka miƙa ta. Ba za ku rage komai daga ciki zuwa safiya ba. Ni ne Yahweh. 31 Dole ne ku kiyaye dokokina ku kuma aikatasu dukka. Ni ne Yahweh. 32 Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole ne a san ni a matsayin mai tsarki ta wurin jama'ar Isra'ila. Ni ne Yahweh mai tsarkake ku, 33 wanda ya fishsheku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku: Ni ne Yahweh.

Sura 23

1 Yahweh ya fa‌ɗa wa Musa: 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, kace masu, 'wa‌ɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwanku ga Yahweh, wa‌ɗ‌anda dole ku shaida su a matsayin tattaruwa mai tsarki; su ne bukukuwana na yau da kullum. 3 Za ku iya yin aiki kwanaki shida, amma rana ta bakwai asabar ce ta cikakken hutu, tattaruwa mai tsarki. Ba za ku yi wani aiki ba domin asabar ce ta Yahweh a cikin dukkan wuraren da kuke zaune. 4 Wa‌ɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwa na Yahweh, tattaruwa mai tsarki da dole ku sanar a ƙayyadaddu lokuttansu: 5 A wata na farko, a rana ta goma sha hu‌ɗ‌u ga wata washegari, ranar bukin ƙetarewa ne na Yahweh. 6 A rana ta goma sha biyar ga wannan watan ranar za ta zama ranar bukin gurasa marar gami ga Yahweh. Dole za ku ci gurasa marar gami har tsawon kwana bakwai. 7 A rana ta farko za ku keɓe kanku domin ku taru wuri ‌ɗaya; ba za ku yi kowanne irin aiki da kuka saba yi ba. 8 Za ku miƙa bayarwar abinci ga Yahweh har kwana bakwai. Kwana na bakwai tattaruwa ce keɓaɓɓiya ga Yahweh, kuma a wannan rana wajibi ne ba za ku yi kowanne aiki da kuka saba yi ba. 9 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 10 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Lokacin da kuka shiga cikin ƙasar da zan ba ku, Sa'ad da kuka yi girbi, wajibi ne ku kawo dami na nunar fari na hatsin ga firist. 11 Shi zai ‌ɗ‌aga damin hatsin a gaban Yahweh ya kuma miƙa shi gare shi, domin a karɓe shi a maimakon ku. A kwana ‌ɗaya bayan assabacin firist zai ‌ɗaga abin ya kuma gabatar da shi gare ni. 12 A ranar da kuka ɗaga damin hatsin kuka kuma miƙa shi gare ni, wajibi ne ku miƙa ɗan rago mai shekara ɗaya kuma marar naƙasa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh. 13 Hadaya ta gari wajibi ne ta zama kashi biyu bisa goma na lallausan gari da aka gauraya da mai, bayarwar da aka yi da wuta ga Yahweh. Domin ta bada ƙamshi mai da‌ɗi, kuma tare da ita hadaya ta abin sha, awo hu‌ɗ‌u na ruwan inabi. 14 Ba za ku ci gurasa, ko gasashshen nama, ko ‌ɗanyen hatsi ba, har sai ranar da kuka kawo sadakar ga Allahnku ta kewayo. Wannan farilla haka zata zama din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku, a cikin dukkan wurin da kuke zaune. 15 Tun daga kwana ‌ɗaya bayan ranar asabaci-Wannan ce ranar da ku ka kawo damin hatsi a matsayin sadaka ta ‌ɗagawa - ku ƙirga makonni bakwai cikakku. 16 Dole ku ƙirga kwanaki hamsin, wanda zai kasance rana bayan asabar ta bakwai. Wajibi ne ku miƙa bayarwar sabon hatsi ga Yahweh. 17 Dole ku ‌ɗibo curi biyu daga cikin gidajenku da aka yi da kashi biyu bisa goma na garwa. Wajibi ne a yi su da lallausan gari da aka yi da gami; zasu zama bayarwar nunar fari ta ɗagawa ga Yahweh. 18 Za ku miƙa gurasar tare da 'yan raguna bakwai masu shekara ‌ɗ‌aya marasa aibu, ‌ɗan maraƙi ɗaya, da raguna biyu. Dole su zama hadaya ta ƙonawa ga Yahweh, tare da hadayar garin da hadaya ta sha, bayarwar da aka yi da wuta mai kuma bada ƙanshi ga Yahweh. 19 Za ku miƙa bunsuru ɗaya domin hadaya ta zunubi, ku kuma miƙa 'yan raguna biyu masu shekara ‌ɗaya hadaya, a matsayin hadaya ta zumunci. 20 Wjibi ne firist ya ka‌ɗa su tare da gurasar nunar fari a gaban Yahweh, ya kuma miƙa su gare shi a matsayin bayarwa tare da 'yan raguna biyu. Za su zama baye-baye masu tsarki na Yahweh domin firist. 21 Dole kayi shaida a wannan ranar. Za'a ha‌ɗa taro mai tsarki, kuma kada kuyi aikin da kuka saba yi. Wannan zai zama farilla na din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku a cikin dukkan wuraren da kuke zaune. 22 Lokacin da kuka girbe amfanin gonarku, baza ku girbe har ƙurewar gonakinku ba, ba kuma za ku yi kalar gonakinku ba. Dole ne ku rage wa matalauta da baƙi su. Ni ne Yahweh Allahnku'". 23 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 24 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka faɗi masu, 'A wata na bakwai, ranar farko ta wannan watan zata zama ranace ta cikakken hutu gare ku, ranar tunawa tare da busa sarewa, da kuma ranar taro mai tsarki. 25 Ba za ku yi wani aiki ba, kuma dole ne ku miƙa hadaya da wuta ga Yahweh."' 26 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa 27 "Yanzu ranar goma ga wannan wata na bakwai ita ce Ranar Kaffara. Za ta kasance tattaruwa mai tsarki, kuma dole ku ƙasƙantar da kanku ku kuma miƙa baiko da wuta ga Yahweh. 28 Ba za ku yi wani aiki a wannan rana ba gama Ranar Kaffara ce, ku yi kaffara domin kanku a gaban Yahweh Allahnku. 29 Dukkan wanda bai ƙasƙantar da kansa a wannan rana ba dole a datse shi daga cikin mutanensa. 30 Dukkan wanda ya yi wani aiki a wannan rana, Ni, Yahweh, zan hallakar da shi daga cikin mutanensa. 31 Ba za ku yi kowanne irin aiki a wannan rana ba. Wannan zai zama farilla ta din-din din cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan wuraren da kuke zama. 32 Ranar nan zata zama Assabat ta cikakken hutu gare ku, kuma dole ku ƙasƙantar da kanku a rana ta tara ga watan da maraice. Daga maraice zuwa maraice za ku kiyaye Assabacinku." 33 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 34 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, cewa, 'Rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai zata zama ranar bukukuwan bukkoki ga Yahweh. Za ku kiyaye shi har kwanaki bakwai. 35 Za ku yi tattaruwa mai tsarki a rana ta fari. Ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba. 36 Tsawon kwana bakwai za ku miƙa hadaya ta wurin wuta ga Yahweh. A rana ta takwas za ku yi taro mai tsarki, kuma dole ne ku miƙa hadaya ta wuta ga Yahweh. Wannan babban taro ne, kuma ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba. 37 Waɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwa ga Yahweh, waɗanda zaku shaida a matsayin tattaruwa mai tsarki ku miƙa hadayu na wuta ga Yahweh, bayarwar ƙonawa da kuma bayarwar gari, hadaya da kuma bayarwar abin sha, kowacce a ranar ta. 38 Waɗannan bukukuwa ƙari ne ga Assabar ta Yahweh da kuma kyaututtukanku, dukkan alƙawuranku, da kuma dukkan baye-bayenku na yardar rai da kuka ba Yahweh. 39 Dangane da bukukuwan bukkoki, a ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, lokacin da kuka gama tattara albarkun ƙasar, Dole ku kiyaye wannan bukukuwa ga Yahweh har kwana bakwai. Ranar farko zata zama ta cikakken hutu, haka rana ta takwas ma zata kasance ranar cikakken hutu. 40 A rana ta fari za ku ‌ɗauka daga cikin mafi kyau na 'ya'yan itatuwanku, rassan itatuwan dabino, da rassa masu ganyayyaki na itatuwa masu ƙarfi, d‌a ciyayi masu yaɗo daga rafuka, zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku har kwana bakwai. 41 Tsawon kwana bakwai a kowacce shekara, wajibi ne ku yi wannan buki ga Yahweh. Wannan zai zama farilla gare ku cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan wuraren da kuke zama. Dole ne ku yi bukin nan a wata na bakwai. 42 Wajibi ne ku zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Dukkan haifaffen gidan Isra'ila dole ya zauna cikin ƙananan bukkoki tsawon kwana bakwai, 43 domin zuriyarku, daga tsara zuwa tsara, su koyi yadda nasa mutanen Isra'ila suka zauna a cikin irin waɗannan bukkokin lokacin da na jagorance su daga cikin ƙasar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku."' 44 Ta haka fa, Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila ƙayyadaddun bukukuwa ga Yahweh.

Sura 24

1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 2 "Ka umurci mutanen Isra'ila su kawo maka mai mai tsabta da aka tatso daga zaitun don a riƙa amfani dashi cikin fitilu, domin su yi ta bada haske ba yankewa. 3 A wajen labulen a gaban akwatin alƙawari cikin rumfar taruwa, wajibi ne ga Haruna daga maraice zuwa safiya, ya sa fitila ta yi ta ci a gaban Yahweh. Wannan zai zama farillanku na din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku. 4 Dole babban firist ya sa fitilu su yi ta ci a gaban Yahweh, fitilun za su kasance a kan ma‌ɗ‌orin da aka yi da zinariya tsantsa. 5 Ka ‌ɗauki lallausan gari ka yi curin gurasa goma sha biyu dashi. Kowanne curi a yi shi da adadin kashi biyu bisa goma na garwa. 6 Sa'an nan wajibi ne ku jera su a layi biyu, shida a kan kowanne layi, a kan tebur na zinariya mai tsabta a gaban Yahweh. 7 Wajibi ne ku sa turare mai tsabta a kan kowanne jerin gurasa a maimakon baiko. Wannan turaren za a ƙone shi domin Yahweh. 8 Kowacce Assabar babban firist ya ajiye gurasa a gaban Yahweh a maimakon mutanen Isra'ila, a matsayin alama ta alƙawari na har abada. 9 Wannan bayarwar zata zama domin Haruna da 'ya'yansa maza, kuma za su ci gurasar a wurin da ya ke mai tsarki, domin rabo ne daga baye-baye ga Yahweh da aka miƙa ta wuta." 10 Ya zama fa ɗan wata mata Ba-isra'iliya, wanda mahaifinsa Ba-masare ne, ya tafi tare da mutanen Isra'ila. Wannan ɗan matar Ba-isra'iliya ya yi faɗa da mutumin Isra'ila a cikin zango. 11 Wannan ɗan matar Ba-isra'iliya ya zagi sunan Yahweh ya kuma la'anta Allah, domin haka jama'a suka kawo shi gaban Musa. Sunan mahaifiyarsa Shelomit, ɗiyar Dibri, daga kabilar Dan. 12 Suka tsare shi a kurkuku har sai sun ji abin da Yahweh da kansa zai furta nufinsa a kansu. 13 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa, 14 "Ka ɗauki mutumin da ya la'anta Allah bayan sansani. dukkan wanda ya ji shi dole su ɗibiya hannayensu a kansa, daga nan dukkan taron jama'a su jejjefe shi. 15 Dole ka bayyanawa mutanen Isra'ila ka ce, "Duk wanda ya la'anci Allahnsa dole ya ɗauki alhakin laifinsa. 16 Shi wanda ya saɓi sunan Yahweh hakika dole a kashe shi. Dukkan taron jama'a dole su jejjefe shi da dutse, ko shi baƙo ne ko haifaffen Ba-Isra'ile. Duk wanda ya yi saɓon sunan Yahweh, dole a kashe shi. 17 Duk wanda ya bugi wani mutum har ya mutu, lallai dole shi ma a kashe shi. 18 Idan wani ya bugi dabbar wani har ta mutu, dole ya mayar, rai maimakon rai. 19 Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa rauni, dole ayi masa yadda ya yi wa maƙwabcinsa: 20 tsaga maimakon tsaga, ido domin ido, haƙori domin haƙori. Kamar yadda ya jawo lahani ga mutum, to haka shi ma za'a yi masa. 21 Duk wanda ya kashe dabba dole ya biya, kuma duk wanda ya kashe mutum dole shi ma a kashe shi. 22 Dole ku kasance da doka iri ɗaya domin baƙo da wanda ya ke haifaffen Ba-Isra'ile, gama Ni ne Yahweh Allahnku.'" 23 Sai Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila, mutanen kuma suka fito da mutumin wajen sansani, wanda ya la'anta Yahweh. Suka jejjefe shi da duwatsu. Mutanen Isra'ila suka aiwatar da dokar Yahweh ta hannun Musa.

Sura 25

1 Yahweh ya yi magana da Musa akan tsaunin Sinai, cewa, 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, "Sa'ad da kuka zo cikin ƙasa wadda na ba ku, daga nan dole ƙasar za ta kiyaye Assabat domin Yahweh. 3 Dole ku shuka gonarku shekaru shida, shekaru shida kuma dole ku gyara gonarku ta inabi ku tattara amfaninta. 4 Amma a cikin shekara ta bakwai, dole a kula da Assabat mai saduda ta hutu, Assabat domin Yahweh. Ba za ku shuka gonar ba ko ku gyara gonar inabinku ba. 5 Ba za ku shirya girbe duk abin da ya tsiro don kansa ba, kuma ba za ku shirya girbin inabin da ya tsiro a kuringar da baku gyara ba. Wannan za ta zama shekara mai saduda ta hutawa domin ƙasar. 6 Duk tsiron da ƙasar da baku aikata ba ta bayar lokacin Assabat na ƙasar zai zama abinci domin ku. Ko, 'ya'yanku maza, da bayinku mata, da bayin da aka yi hayarsu, da baƙi da ke zaune tare da ku za ku iya tattara abinci, 7 dabbobinku kuma da bisashenku za su iya cin amfanin da ƙasar ta bayar. 8 Dole ku lisafta Assabat guda bakwai na shekaru, wato, bakwai sau shekaru bakwai, wato akwai Assabat bakwai na shekaru, jimilla duka shekaru arba'in da tara ke nan. 9 Sa'an nan za ku busa ƙaho da ƙarfi ko'ina a rana ta goma a watan bakwai. A ranar kaffara dole ku busa ƙaho ko'ina a cikin ƙasarku. 10 Dole ku keɓe shekara ta hamsin ga Yahweh kuma ayi shelar 'yanci ko'ina a ƙasar ga dukkan mazaunanta. Zata zama ranar mayarwa domin ku, inda kowacce mallaka da bayi dole za su koma wurin iyalinsu. 11 Shekara ta hamsin zata zama shekarar mayarwa a gare ku. Ba za ku shuka ko shirya girbi. Ko cin duk abin da ya tsiro da kansa ba, kuma ba za ku tattara inabi da ya tsiro a kuringai da baku gyara ba. 12 Gama Shekarar 'Yanci ce, wadda za ta zama mai tsarki domin ku. Dole kuci amfanin da ya tsiro don kansa a gonaki. 13 Dole ku mayar wa da kowanne mutum mallakarsa a shekarar 'Yanci. 14 Idan ka sayar da gona ga maƙwabcinka ko ka sayi gona a wurin maƙwabcinka, kada ku cuci ko ku zalunci juna. 15 Idan ka sayi gona daga maƙwabcinka, sai ka yi la'akari da shekaru da amfanin da za a girbe har zuwa shekarar gaba ta 'Yanci. Maƙwabcinka da ke sayar maka da gonar dole ya kula da wannan shi ma. 16 Yawan shekarun har zuwa shekarun 'Yanci zai ƙara tamanin ƙasar, gwargwadon ƙarancin shekarun za a rage tamanin ta, saboda yawan girbin da ƙasar zata bayar domin sabon mai gonar yana alaƙa da yawan shekaru kafin shekarar 'Yanci ta gaba. 17 Ba za ku cuci ko ku zalunci juna ba; maimakon haka dole ku girmama Allahnku, gama Ni ne Yahweh Allahnku. 18 Domin wannan dole ku kiyaye umarnaina, ku kiyaye dokokina, kuma ku aiwatar da su. Daga nan za ku zauna cikin ƙasar lafiya. 19 ƙasa za ta bada amfaninta, kuma za ku ci ku ƙoshi kuma ku zauna can cikin tsaro. 20 Za ku iya cewa, "Me zamu ci cikin shekara ta bakwai? Duba, ba dama mu shuka ko mu tattara amfaninmu ba." 21 Zan umarci albarkata ta zo bisanku a cikin shekara ta shida, kuma zata bada isasshen amfani har shekaru uku. 22 Za ku shuka cikin shekara ta takwas kuma ku ci gaba da cin abincin da kuka ajiye a shekarun baya. Har lokacin girbi na shekara ta tara ta zo, za ku ci daga tanajin ajiyar da kuka yi a shekarun baya. 23 Ba za a sayar da ƙasa ga wani ya zama sabon mai ita ta din-din din ba, saboda ƙasa tawace. Dukkanku bãƙi ne masu zama na ɗan lokaci a ƙasa ta. 24 Dole ku kula da haƙin fansa domin dukkan ƙasar da kuka mallaka; dole ku bari a sake sayen ƙasar ga iyalin daga wanda ya saye ta. 25 Idan ɗan'uwanka Ba-Isra'ile ya zama talaka kuma akan wannan dalili ya sayar da wata mallaka tasa, daga nan danginsa na kusa zai iya zuwa ya fanshi mallakar da ya sayar maka. 26 Idan mutum ba shi da ɗan'uwa da zai fãnshi mallakarsa, amma idan ya azurta har zai iya fãnsar ta, 27 daga nan zai iya lissafta shekaru tun lokacin da aka sayar da ƙasar sai ya biya sauran ga mutumin da ya sayar wa. Daga nan zai iya dawo wa ga mallakarsa. 28 Amma idan bai iya dawo da ƙasar domin kansa ba, daga nan ƙasar da ya sayar za ta kasance cikin mallakar shi wanda ya saye ta har zuwa lokacin shekarar 'Yanci. A shekarar 'Yanci, ƙasar zata koma ga mutumin da ya sayar da ita, ainihin mai ita kuma zai koma ga mallakarsa. 29 Idan mutum ya sayar da gidansa a cikin birni mai ganuwa, daga nan zai iya ya fãnshar sa cikin dukkan shekara bayan ya sayar. Gama a cikin cikar shekara yana da 'yancin fãnsa. 30 Idan ba a fãnshi gidan kamin cikar shekara ba, daga nan gidan da ke cikin birni mai ganuwa zai zama mallaka ta din-din din ga wanda ya saya shi da zuriyarsa. Ba za a mayar da shi cikin shekara ta 'Yanci ba. 31 Amma gidajen ƙauyukan da ba su da gãnuwa kewaye da su za a yi lissafinsu a matsayin filin ƙasa. Za a iya fãnsarsu kuma dole a dawo da su a shekarar 'Yanci. 32 Amma, gidajen da Lebiyawa suka mallaka cikin birane za su iya fãnsarsu a kowanne lokaci. 33 Idan ɗaya daga cikin Lebiyawa bai fãnshi gidan da ya sayar ba, daga nan gidan da aka sayar a cikin birni a inda ya ke dole a dawo da shi cikin shekarar 'Yanci, gama gidajen biranen Lebiyawa mallakarsu ne a cikin mutanen Isra'ila. 34 Amma filayen da ke kewaye da biranen ba za a sayar da su ba saboda mallakar Lebiyawa ne na din-din din. 35 Idan ɗan ƙasarku ya zama talaka, yadda ba zai iya biyan buƙatar kansa ba, daga nan dole ka taimake shi kamar yadda za ka taimaki bãƙo ko wani dabam da ke zaune kamar na waje a cikinku. 36 Kada ka caje shi da ruwa ko ka yi ƙoƙarin samun riba daga gare shi ta kowacce hanya, amma ka girmama Allahnka domin ɗan'uwanka ya ci gaba da zama tare da kai. 37 Kada ka bashi bashin kuɗi da ruwa, ko ka sayar masa abinci don samun riba. 38 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, domin in baku ƙasar Kan'ana, kuma in zama Allahnku. 39 Idan ɗan ƙasarku ya zama talaka har ya sayar da kansa gare ka, kada kasa shi ya yi aiki kamar bawa. Ka kula da shi kamar baran haya. 40 Dole ya zama kamar wanda ya ke zama da kai na ɗan lokaci. Zai yi hidima tare da kai har zuwa shekarar 'Yanci. 41 Daga nan zai tafi daga gare ka, shi da 'ya'yansa tare da shi, zai koma wurin iyalinsa da mallakar kakanninsa. 42 Gama su bayina ne waɗanda na kawo daga ƙasar Masar. Ba za a sayar da su kamar bayi ba. 43 Kada ku mallake su da tsanani, amma dole ku girmama Allahnku. 44 Ga zancen bayinku maza da mata, waɗanda za ku samu daga al'umman da ke kewaye da ku, za ku iya sayen bayi daga gare su. 45 Za ku iya sayen bayi daga bãƙin da ke zaune a wurin ku, wato, daga iyalin da ke tare da ku, 'ya'yan da aka haifa cikin ƙasarku. Sun zama mallakarku. 46 Za ku iya tanada wa 'ya'yanku irin waɗannan bayi su zama gãdo bayan ku, su riƙe su a matsayin mallaka, su kuma za su zama bayi har abada, amma baza ku yi mulkin 'yan'uwanku cikin mutanen Isra'ila da tsanani ba. 47 Idan bãƙo ko wani da ke zama cikinku na ɗan lokaci ya azurta, ɗan'uwanku kuma Ba-Isra'ile ya talauce ya sayar da kansa ga bãƙon, ko ga wani cikin iyalin bãƙon, 48 bayan da an sayi Ba-Isra'ilenku, za a iya fãnsarsa. Wani daga cikin iyalinsa zai iya fãnsar sa. 49 Zai iya zama kawun mutumin ko ɗan kawunsa, wanda ya fanshe shi, ko wani wanda ya ke kusa da iyalinsa. Ko, idan ya azurta, zai iya fãnsar kansa. 50 Dole ya yi ciniki da wanda ya saye shi; dole su lisafta shekarun daga shekarar da ya sayar da kansa ga wanda ya saye shi har zuwa shekarar 'Yanci. Farashin da aka fãnshe shi zai zama dai-dai da yawan wanda aka biya baran da akayi hayar sa, zai iya ci gaba da yin aiki har wasu shekaru ga wanda ya sawo shi. 51 Idan har yanzu akwai sauran shekaru da yawa kafin shekarar 'Yanci, dole ya biya kuɗin domin fãnsarsa bisa ga adadin waɗannan shekaru. 52 Amma idan shekarun sun ragu kaɗan ga shekarar 'Yanci, daga nan dole ya yi ciniki tare da mai sayensa ya nuna yawan shekarun da suka ragu kafin shekarar 'Yanci, kuma dole ya biya domin fãnsarsa bisa ga yawan shekarun. 53 Dole a kula da shi kamar mutumin da aka yi hayarsa shekara bayan shekara. Dole ku tabbatar ba a tsananta masa da tsanani ba. 54 Idan ba a fãnshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, daga nan zai ci gaba da bauta har zuwa shekarar 'Yanci, shi da 'ya'yansa tare da shi. 55 A gare ni mutanen Isra'ila bayi ne. Bayi na ne waɗanda na fisshe su daga ƙăsar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku.'"

Sura 26

1 "Ba za ku yi gumakai ba, kuma ba za ku ɗaga sassaƙaƙƙiyar siffa ko keɓaɓɓen ginshiƙin dutse, kuma ba za ku kafa kowacce irin sassaƙaƙƙiyar siffa ta dutse a cikin ƙasarku da za ku durƙusa masa ba, gama ni ne Yahweh Allahnku. 2 Dole ku kiyaye assabataina ku girmama rumfar sujadata. Ni ne Yahweh. 3 Idan kuka yi tafiya cikin umarnaina kuka kiyaye dokokina kuma kuka yi biyayya da su, 4 daga nan zan ba ku ruwan sama a lokacinsa; ƙasar kuwa zata bada amfaninta, itatuwan gonaki kuma za su bada 'ya'yansu. 5 Za ku yi ta girbi har lokacin girbin 'ya'yan inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuka. Za ku ci abincinku ku ƙoshi kuma ku zauna lafiya inda kuka yi gida a cikin kasarku. 6 Zan bada salama cikin ƙasar; za ku kwanta ba abin da zai tsoratar da ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar, takobi kuma ba zata ratsa ta ƙasarku ba. 7 Za ku runtumi maƙiyanku, kuma za su faɗi a gaban ku ta wurin takobi. 8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi ɗari, mutum ɗarinku kuma za su runtumi mutum dubu goma; maƙiyanku za su faɗi a gabanku ta wurin takobi. 9 Zan dube ku da idon rahama in sa ku hayayyafa in riɓanɓanya ku; zan tabbatar da alƙawarina tare da ku. 10 Za ku ci abinci ku ajiye shi tsawon lokaci. Za ku fitar da abincin da kuka ajiye saboda kuna buƙatar ɗaki domin ku ajiye sabon hatsi. 11 Zan kafa mazaunina a tsakiyar ku, ba kuwa zan ƙi ku ba. 12 Zan yi tafiya tare da ku in kuma zama Allahnku, kuma za ku zama mutanena. 13 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, domin kada ku zama bayinsu. Na karya sandunan karkiyarku na sa ku yi tafiya madaidaiciya. 14 Amma idan ba za ku saurare ni ba, kuma ba za ku yi biyayya da dukkan dokokin nan ba, 15 idan kuma kuka yi watsi da dokokina kuma kuka ƙi umarnaina, domin kada ku yi biyayya da dukkan dokokina, amma kuka karya alƙawarina - 16 - idan kuka yi waɗannan abubuwa, daga nan nima zan yi wannan a gare ku: Zan sa tsõro a kan ku, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idanunku rayuwa zata zama da wahala. Za ku shuka irinku a banza, amma maƙiyanku ne za su ci amfaninsu. 17 Zan sa fuskata gãba da ku, maƙiyanku za su fi ƙarfinku. Mutanen da suke ƙin ku za su mallake ku. Za ku yi gudu ko da wani bai kore ku ba. 18 Idan bayan dukkan wannan baku saurare ni ba, daga nan zan ƙara hukunta ku da tsanani sau bakwai domin zunubanku. 19 Zan karya gimanku cikin ikonku. Zan sa sama da ke kanku ta zama kamar ƙarfe ƙasarku kuma kamar tagulla.‌ 20 Ƙ‌arfinku zai zama ba amfani, saboda ƙasarku ba zata bada amfaninta ba, itatuwan ‌ƙasar kuma ba za su bada 'ya'yansu ba. 21 Idan kuka yi tafiya gãba da ni ba ku saurare ni ba, Zan kawo nushi sau bakwai akan ku, bisa ga yawan zunubanku. 22 Zan aiko maku da mugayen namomin jeji gãba da ku, waɗanda za su sace 'ya'yanku, su hallaka dabbobinku, su sa ku zama kaɗan. Hanyoyin kuma za su zama ba masu gilmawa. 23 Idan baya ga waɗannan duk da haka ba ku karɓi gyara na ba kuka ci gaba da tafiya cikin yin adawa da ni, 24 daga nan ni ma zan yi tafiya cikin yin adawa da ku, kuma Ni da kaina zan hukunta ku sau bakwai saboda zunubanku. 25 Zan kawo takobi a kanku a kashe ku da ramuwa domin karya alƙawari. Za a tattara ku tare cikin biranenku, can zan aikar da cuta a wurin, za a miƙa ku cikin hannun maƙiyanku. 26 Idan na datse abincin da kuka tanada, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, kuma za su rarraba abincinku bisa ga ma'auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba. 27 Idan ba ku saurare ni ba duk da waɗannan abubuwan, amma kuka ci gaba da tafiya gãba da ni, 28 daga nan ni ma zanyi tafiya gãba da ku cikin fushi, kuma zan hukunta ku har sau bakwai sosai saboda zunubanku. 29 Za ku ci naman 'ya'yanku maza; za ku ci naman 'ya'yanku mata. 30 Zan lalatar da wurarenku masu tsayi, in datse bagadan ƙona turarenku, in jefar da gawarwakinku akan gawarwakin gumakanku, kuma ni da kaina zan ji ƙyamar ku. 31 Zan juyar da biranenku su zama kufai in lalatar da masujadanku. Ba zan ji daɗin ƙamshin baye-bayenku ba. 32 Zan lalatar da ƙasar. Maƙiyanku da ke zaune a ƙasar za su yi mamaki da irin lalatarwar. 33 Zan warwatsaku cikin ƙasashe, kuma zan zare takobina in fafareku. ‌Ƙ‌asarku za a yashe ta, biranenku kuma za su zama kangaye. 34 Daga nan ƙasar zata ji daɗin hutunta muddin tana kwance yasasshiya kuma ku kuna ƙasashen maƙiyanku. A wannan lokaci, ƙasar zata huta zata ji daɗin hutunta. 35 Muddin ƙasar tana kwance kango, zata huta, zai zama hutun da bata samu ba tare da assabatunku, lokacin da kuka zauna cikinta. 36 Amma ga waɗansun ku da suka ragu cikin ƙasashen maƙiyanku, Zan aikar da tsoro cikin zukatansu yadda motsin kaɗawar ganye cikin guguwa ma zai razanar da ku, za ku sheƙa a guje kamar kuna gujewa takobi. Za ku faɗi, koda ba wanda ke korar ku. 37 Za ku yi ta karo da juna kamar kuna gujewa daga takobi, kodashike ba mai korar ku. Ba za ku sami ikon tsayawa gaban maƙiyanku ba. 38 Za ku hallaka cikin al'ummai, ƙasar maƙiyanku kanta za ta haɗiye ku. 39 Waɗanda suka ragu a cikinku za su lalace cikin zunubansu, a can cikin ƙasashen maƙiyanku, saboda zunubin kakanninsu kuma za su lalace kamar su. 40 Duk da haka idan suka furta zunubansu da zunubin kakanninsu, da cin amanar su da suka zama da rashin aminci a gare ni, da tayarwar da suka yi mani -- 41 wanda ya sa ni na juya gãba da su na kawo su cikin ƙasar maƙiyansu - idan suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, kuma suka karɓi hukunci domin zunubansu, 42 daga nan zan tuna da alƙawarina da Yakubu, alƙawarina da Ishaku, da kuma alƙawarina tare da Ibrahim; kuma, zan tuna da ƙasar. 43 Za su yashe da ƙasar, za ta ji daɗin hutunta yayin da take kwance yasasshiya ba tare da su ba. Za su biya alhakin zunubansu saboda su da kansu sun yi watsi da umarnaina suka yi ƙyamar dokokina. 44 Duk da haka bayan dukkan waɗannan, sa'ad da suke cikin ƙasar maƙiyansu, ba zan ƙi su ba, ko in ƙyamace su domin in hallaka su gaba ɗaya har in karya alƙawarina da su ba, Gama Ni ne Yahweh Allahnsu. 45 Amma saboda su zan tuna da alƙawarina tare da kakanninsu, waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai, domin in zama Allahnsu. Ni ne Yahweh." 46 Waɗannan dokoki, umarnai da shari'u waɗanda Yahweh ya yi tsakaninsa da mutanen Isra'ila a Tsaunin Sinai ta hannun Musa.

Sura 27

1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Idan wani ya yi alƙawari na musamman ga Yahweh, yi amfani da waɗannan tamanin. 3 Darajar misalin abin da za ka biya domin maza daga shekara ashirin zuwa sittin dole ya zama awo hamsin na tagulla, bisa ga awo na wuri mai tsarki. 4 Ga mataye masu shekaru iri ɗaya darajar abin da za a biya dole ya zama awo talatin. 5 Daga shekara biyar zuwa shekara ashirin darajar abin da za a biya domin maza dole ya zama awo ashirin, mataye kuma awo goma. 6 Daga wata ɗaya zuwa shekara biyar darajar abin da za a biya domin maza dole ya zama awo biyar na tagulla, ga mata awo uku na tagulla. 7 Daga shekaru sittin zuwa sama ga maza tamanin abin da za a biya dole ya kai awo goma sha biyar, mata kuma awo goma. 8 Amma idan mutumin da ya yi wa'adi ba zai iya biyan tamanin ba, daga nan mutumin da aka bayar dole a kawo shi gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamanin abin da mutumin da ya yi wa'adin zai iya biya bisa ga ƙarfinsa. 9 Idan wani yana son miƙa hadayar dabba ga Yahweh, kuma idan Yahweh ya karɓe ta, daga nan wannan dabbar za a keɓe ta dominsa. 10 Kada mutumin ya musanya irin wannan dabbar, mai kyau da marar kyau ko marar kyau da mai kyau. Idan ya musanya ko canza dabbar da wata, daga nan dukkan su biyu da aka musanya da wadda aka musanyar za su zama masu tsarki. 11 Duk da haka, idan abin da mutumin ya yi wa'adi zai ba Yahweh ta zama marar tsarki, don haka Yahweh ba zai karɓe ta ba, daga nan dole mutumin ya kai dabbar wurin firist. 12 Firist zai kimanta tamanin ta, bisa ga darajar dabbar. Duk yadda firist ya kimanta dabbar, haka darajarta zata zama. 13 Idan mai ita yana so ya fãnshe ta, sai ya yi ƙarin kashi biyar na farashin fãnsa. 14 Idan mutum ya keɓe gidansa a matsayin kyauta mai tsarki ga Yahweh, daga nan sai firist ya kimanta tamaninsa ko da kyau ko ba kyau. Duk yadda firist ya kimanta darajarsa, haka zai zama. 15 Amma idan mai gidan wanda ya keɓe gidan yana so ya ƒãnshe shi, dole ya ƙara kashi ɗaya cikin biyar na tamanin farashin fansa, gidan kuwa zai zama nasa. 16 Idan mutum ya keɓe wani sãshe na gonarsa, daga nan tamaninta zai zama kimanin dai-dai da yawan irin da ya kamata a shuka - tiyar bãli tamaninta zai zama a bakin shekel hamsin na azurfa. 17 Idan ya keɓe gonarsa lokacin shekarar 'Yanci, haka tamaninta zai tsaya. 18 Amma idan ya keɓe gonarsa bayan shekarar 'Yanci dole firist ya lisafta yawan tamanin ƙasar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa shekarar 'Yanci, kuma dole a rage tamaninta. 19 Idan shi mutumin da ya keɓe gonar yana so ya fãnshe ta, daga nan dole ya ƙara kashi biyar na tamanin, kuma sai ta zama ta sa. 20 Idan bai fãnshi gonar ba, ko idan ya rigaya ya sayar da gonar ga wani mutum, ba za ta fãnsu ba faufau. 21 Maimakon haka, idan gonar, an sake ta cikin shekarar 'Yanci, zata zama kyauta mai tsarki ga Yahweh, kamar gonar da aka bayar gaba ɗaya ga Yahweh. Zata zama mallakar firist. 22 Idan mutum ya keɓe gonar da ya saya, amma wannan gonar bata cikin ƙasar gãdon iyalinsa, 23 daga nan firist zai kimanta tamaninta har zuwa shekarar 'Yanci, daga nan dole mutumin ya biya tamaninta a ranar a matsayin kyauta mai tsarki ga Yahweh. 24 A cikin shekarar 'Yanci, sai gonar ta koma ga mutumin wanda daga wurinsa aka saye ta, ga ainihin mai gonar. 25 Dukkan kowanne tamani dole ya zama bisa ga nauyin awo na wuri mai tsarki. ‌Ƙaramin awo ashirin da ke matsayin awo ɗaya. 26 Ba wanda zai keɓe ɗan fãri cikin dabbobi, da shike dama na Yahweh ne; ko sã ko tunkiya, na Yahweh ne. 27 Idan dabbar marar tsarki ce, daga nan mai ita zai iya fãnsar ta bisa ga tamanin, dole ya ƙara kashi biyar akan tamanin. Idan ba'a fãnshi dabbar ba, daga nan sai a sayar da ita bisa ga tamanin da aka sanya. 28 Amma ba abin da mutum zai bayar ga Yahweh, daga dukkan abin da ya ke da shi, ko mutum ko dabba, ko ƙasar gãdonsa, da za a sayar ko a fãnsar. Duk abin da aka keɓe ya zama mai tsarki na Yahweh. 29 Ba za a biya kuɗin fãnsa ba ga mutumin da aka keɓe domin hallakarwa. Wannan mutumin dole a kashe shi. 30 Dukkan zakkar ƙasa, ko ta hatsin da aka noma a ƙasa ko 'ya'yan itatuwa, na Yahweh ne. Mai tsarki ne ga Yahweh. 31 Idan mutum ya fãnshi kowanne abu na zakkarsa, dole ya ƙara ɗaya bisa biyar na tamaninta. 32 Ga kowanne ɗaya bisa goma na makiyaya ko dabbobi, ko mene ne ya wuce ta ƙarƙashin sandar makiyaya, dole a keɓe ɗaya bisa goma ga Yahweh. 33 Kada makiyayin ya nemi mai kyau ko munanan dabbobi, kada ya musanya da wata. Idan har ya canja, daga nan dukkansu da wadda ya canja za su zama tsarkakku ga Yahweh. Ba za a fãnshe su ba.'" 34 Waɗannan su ne dokokin da Yahweh ya bayar a tsaunin Sinai ga Musa domin mutanen Isra'ila.

Littafin Lissafi
Littafin Lissafi
Sura 1

1 Yahweh ya yi magana da Musa a runfar taruwa a cikin jejin Sinai. Wannan ya fãru ne a rana ta farko a wata na biyu a shekara ta biyu bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar. Yahweh yace, 2 "Ka yi ƙidayar dukkan mutanen Isra'ila daga kowanne dangi, a cikin iyalan ubanninsu. Ka ƙidaya su bisa ga sunaye. Ka ƙidaya kowanne namiji, kowanne mutum 3 wanda ke shekaru ashirin ko fiye. Ka ƙidaya dukkan waɗanda ke iya faɗa a matsayin sojoji domin Isra'ila. Kai da Haruna tilas ku rubuta lissafin dukkan mazaje a rukunonin mayaƙansu. 4 Mutum daga kowacce kabila, kan dangi, tilas ya yi hidima tare da ku a matsayin shugaban kabilarsa. Kowanne shugaba tilas ya shugabanci mazajen da zasu yi faɗa kabilarsa. 5 Waɗannan ne sunayen shugabannin waɗanda tilas su yi faɗa tare da ku: Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur; 6 daga kabilar Simiyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai; 7 daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab; 8 daga kabilar Issaka, Netanel ɗan Zuwar; 9 daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon; 10 daga kabilar Ifraim ɗan Yosef, Elishama ɗan Ammihud; daga kabilar Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur; 11 daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gidiyoni; 12 daga kabilar Dan, Ahiyeza ɗan Ammishaddai; 13 daga kabilar Asha, Fagiyel ɗan Okran; 14 daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Duwel; 15 kuma daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan." 16 Waɗannan ne mazajen da aka zaɓa daga mutanen. Suka bida kabilun kakanninsu. Sune shugabannin kabilun a Isra'ila. 17 Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane, waɗanda aka lissafa da sunayensu, 18 tare da waɗannan mutanen tattaro dukkan mutanen Isra'ila a rana ta farko na wata na biyu. Daga nan kowanne mutum ɗan shekaru ashirin da sama ya tantance asalinsa. Dole ya bada suna ga dangi da iyalan zuriyar daga kakanninsa. 19 Daga nan Musa ya rubuta lissafinsu a cikin jejin Sinai, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi. 20 Daga zuriyar Ruben, haihuwar fãrin Isra'ila, an yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 21 Suka ƙidaya mutane 46,500 daga kabilar Ruben. 22 Daga zuriyar Simiyon kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu. 23 Suka ƙidaya mutane 59,300 daga kabilar Simiyon. 24 Daga zuriyar Gad kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 25 Suka ƙidaya mutane 45,650 daga kabilar Gad. 26 Daga zuriyar Yahuda kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 27 Suka ƙidaya mutane 74,600 daga kabilar Yahuda. 28 Daga zuriyar Issaka kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 29 Suka ƙidaya mutane 54,400 daga kabilar Issaka. 30 Daga zuriyar Zebulun kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 31 Suka ƙidaya mutane 57,400 daga kabilar Zebulun. 32 Daga zuriyar Ifraim kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 33 Suka ƙidaya mutane 40,500 daga kabilar Ifraim. 34 Daga zuriyar Manasse kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu. 35 Suka ƙidaya mutane 32,200 daga kabilar Manasse. 36 Daga zuriyar Benyamin kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu. 37 Suka ƙidaya mutane 35,400 daga kabilar Benyamin. 38 Daga zuriyar Dan kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu. 39 Suka ƙidaya mutane 62,700 daga kabilar Dan. 40 Daga zuriyar Asha kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu. 41 Suka ƙidaya mutane 41,500 daga kabilar Asha. 42 Daga zuriyar Naftali kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu. 43 Suka ƙidaya mutane 53,400 daga kabilar Naftali. 44 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan waɗannan mutane, tare da mutanen sha biyu waɗanda ke shugabancin kabilun sha biyu na Isra'ila. 45 Haka dukkan mazajen Isra'ila daga 'yan shekaru ashirin zuwa sama, dukkan waɗanda ke iya faɗa a yaƙi, aka ƙidaya su a kowanne iyalansu. 46 Suka ƙidaya mutane 603,550. 47 Amma mazajen da suka fito daga zuriyar Lebi ba a ƙidaya su ba, 48 saboda Yahweh ya cewa Musa, 49 "Tilas baza ka ƙidaya kabilar Lebi ba ko ka haɗa da su cikin jimillar mutanen Isra'ila. 50 A maimakon haka, ka sa Lebiyawa lura da runfar alƙawarin dokoki, su kuma lura da dukkan kayayyakin adon runfar da kowanne abu dake cikinta. Tilas Lebiyawa su ɗauki runfar, kuma tilas su ɗauki kayayyakin adon runfar. Tilas su lura da runfar, su kuma yi wa kansu sansani kewaye da ita. 51 Sa'ad da za a matsa da runfar zuwa wani wuri, tilas Lebiyawa su sauke ta. Sa'ad da za a kafa runfar, tilas Lebiyawa su kafa ta. Duk wani baƙo da ya zo kusa da runfar tilas a kashe shi. 52 Sa'ad da mutanen Isra'ila zasu kafa runfunansu, kowanne mutum tillas ya yi haka kusa da tutar da take ta ƙungiyar mayaƙansa. 53 Duk da haka, Lebiyawa tilas su kafa runfunansu kewaye da runfar alƙawarin dokoki kada fushina ya sauko bisa mutanen Isra'ila. Tilas Lebiyawa su lura da runfar alƙawarin dokoki." 54 Mutanen Isra'ila suka yi dukkan waɗannan abubuwa. Suka yi kowanne abin da Yahweh ya umarta ta wurin Musa.

Sura 2

1 Yahweh ya sake magana da Musa da Haruna. Ya ce, 2 "Kowanne Ba'isra'ile dole ya yi sansani wajen matsayinsa, tare da tutocin gidan ubanninsa. Za su yi sansani kewaye da rumfar taruwa ta kowanne gefe. 3 Waɗanda za su yi sansani gabas da rumfar taruwa, inda rana ke fitowa, su ne sansanin Yahuda kuma suna sansani a ƙarƙashin matsayinsu. Nashon ɗan Amminadab shi ne shugaban mutanen Yahuda. 4 Lissafin mutanen Yahuda 74,600 ne. 5 Kabilar Issaka tilas su yi sansani a gaba da Yahuda. Netanel ɗan Zuyar tilas ya shugabanci mayaƙan Issaka. 6 Lissafin bataliyar mutane 54,400 ne. 7 Kabilar Zebulun tilas su yi sansani a gaba da Issaka. Eliyab ɗan Helon tilas ya shugabanci mayaƙan Zebulun. 8 Lissafin bataliyarsa 57,400 ne. 9 Dukkan lissafin sansanin Yahuda 186,400 ne. Sune za su fãra tafiya. 10 Gefen kudu zai zama sansanin Ruben a wajen matsayinsu. Shugaban sansanin Ruben shi ne Elizur ɗan Shedewur. 11 Lissafin dake bataliyarsa 46,500 ne. 12 Simiyon zai yi sansani a gaba da Ruben. Shugaban mutanen Simiyon shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai. 13 Lissafin bataliyarsa shi ne 59.300. 14 Kabilar Gad su ne gaba. Shugaban mutanen Gad shi ne Eliyasaf ɗan Deuyel. 15 Lissafin bataliyarsa shi ne 45,650. 16 Lissafin dukkan mutanen da aka bayar ga sansanin Ruben, bisa ga bataliyarsu, shi ne 151,450. 17 Na gaba, rumfar sansanin tilas ta fita daga sansanin tare da Lebiyawa a tsakiyar dukkan sansanan. Tilas su fita daga sansanin bisa ga tsarin yadda suka shiga sansanin. Kowanne mutum tilas ya tsaya a wurinsa, gefen tutarsa. 18 Rabe-raben zangon sansanin Ifraim a ƙarƙashin matsayinsu. Shugaban mutanen Ifraim shi ne Elishama ɗan Ammihud. 19 Lissafin bataliyarsa shi ne 40,500. 20 Gaba dasu su ne Kabilar Manasse. Shugaban Manasse shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur. 21 Lissafin bataliyarsa shi ne 32,200. 22 Gaba da su zai kasance kabilar Benyamin. Shugaban Benyamin shi ne Abidan ɗan Gidiyoni. 23 Lissafin dake bataliyarsa 35,400 ne. 24 Dukkan waɗanda aka lissafa a sansanin Ifraim 108,100 ne. Su ne na ukun fita. 25 Daga arewa zai kasance bataliyoyin sansanin Dan. Shugaban mutanen Dan shi ne Ahiyeza ɗan Ammishaddai. 26 Lissafin dake bataliyarsa 62,700 ne. 27 Mutanen kabilar Asha suka yi sansani gaba da Dan. Shugaban Asha shi ne Fagiyel ɗan Okran. 28 Lissafin bataliyarsa 41,500 ne. 29 Kabilar Naftali su ne gaba. Shugaban Naftali shi ne Ahira ɗan Enan. 30 Lissafin dake bataliyarsa 53,400 ne. 31 Dukkan waɗanda aka lissafa a sansanin tare da Dan 157,600 ne. Sune na ƙarshen fita daga sansanin, a ƙarƙashin tutarsu." 32 Waɗannan ne Isra'ilawa, an lissafa su bisa ga iyalansu. Dukkan waɗanda aka ƙidaya a sansanansu, bisa ga bataliyoyinsu, 603,550 ne. 33 Amma Musa da Haruna ba su ƙidaya Lebiyawa ba a cikin mutanen Isra'ila. Wannan bisa ga yadda Yahweh ya umarci Musa ne. 34 Mutanen Isra'ila suka yi kowanne abu da Yahweh ya umarci Musa. Suka yi sansani bisa ga tutocinsu. Suka fita daga sansanin bisa ga dangoginsu, bisa ga tsarin iyalan kakanninsu.

Sura 3

1 Yanzu wannan ne tarihin zuriyar Haruna da Musa sa'ad da Yahweh ya yi magana da Musa a Tsaunin Sinai. 2 Sunayen 'ya'yan Haruna maza su ne Nadab haihuwar farko, da Abihu, Eliyeza, da Itama. 3 Waɗannan ne sunayen 'ya'yan Haruna maza, firistoci waɗanda aka shafe aka kuma naɗa su yi hidima a matsayin firistoci. 4 Amma Nadab da Abihu sun fãɗi sun mutu a gaban Yahweh sa'ad da suka miƙa masa wuta marar karɓuwa a cikin jejin Sinai. Nadab da Abihu ba su da 'ya'ya, sai Eliyeza da Itama ne kawai suka yi hidima a matsayin firistoci tare da Haruna mahaifinsu. 5 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 6 "Ka kawo kabilar Lebiyawa ka gabatar da su ga Haruna firist domin su taimake shi. 7 Tilas su aiwatar da ayyuka a madadin Haruna da dukkan jama'a a gaban rumfar taruwa. Tilas su yi hidima a rumfar sujada. 8 Tilas su lura da dukkan kayan ado na cikin rumfar taruwa, kuma tilas su taimaki kabilun Isra'ila su aiwatar da hidimar rumfar sujada. 9 Tilas ka bayar da Lebiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza. An bayar da su ɗungun su taimaka masa ya yi hidima ga mutanen Isra'ila. 10 Tilas ka naɗa Haruna da 'ya'yansa maza a matsayin firistoci, amma duk wani bãre da yazo kusa tilas a kashe shi." 11 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 12 "Duba, na ɗauki Lebiyawa daga tsakanin mutanen Isra'ila. Na yi haka ne a maimakon ɗaukar kowanne haihuwar fãri namiji wanda aka haifa a cikin mutanen Isra'ila. Lebiyawa nawa ne. 13 Dukkan haihuwar fãri nawa ne. A ranar dana kai hari ga dukkan haihuwar fãri na ƙasar Masar, na keɓewa kaina dukkan haihuwar fãri cikin Isra'ila, mutane duk da dabbobi. Nawa ne su. Ni ne Yahweh." 14 Yahweh ya yi magana da Musa a jejin Sinai. Ya ce, 15 "Ka ƙidaya zuriyar Lebi a kowanne iyali, cikin dangoginsu. Ka ƙidaya kowanne namiji daga wata ɗaya zuwa sama. 16 "Musa ya ƙidaya su, yana bin maganar Yahweh, kamar yadda dai aka umarce shi ya yi. 17 Sunayen 'ya'yan Lebi maza su ne Gashon, Kohat, da Merari. 18 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Gashon maza su ne Libni da Shimai. 19 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Kohat maza su ne Amram, Izhar, Hebron, da Uzziyel. 20 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Merari maza su ne Mahli da Mushi. Waɗannan ne dangogin Lebiyawa, aka rubuta dangi zuwa dangi. 21 Dangin Libniyawa da Shimaiyawa sun fito daga Gashon. Waɗannan ne dangogin Gashonawa. 22 Dukkan mazaje daga wata ɗaya zuwa sama an ƙidaya su, jimilla 7,500. 23 Kabiluin Gashonawa tilas su yi sansani gefen yamma da rumfar sujada. 24 Eliyasaf ɗan Layel tilas ya shugabanci kabilun zuriyar Gashonawa. 25 Iyalin Gashon tilas su lura da rumfar taruwa duk da rumfar sujada. Tilas su lura da rumfar, da abin rufewar ta, da labulen da ake amfani da shi a shiga rumfar taruwar. 26 Tilas su lura da masagalen labulen harabar, labulen dake ƙofar harabar - harabar dake kewaye da tsattsarkan wuri da bagadi. Tilas su lura da igiyoyin rumfar taruwa kuma domin kowanne abu dake cikinta. 27 Waɗannan kabilun sun zo daga Kohat: kabilar Amramiyawa, dangin Izrahiyawa, kabilar Hebroniyawa, da kabilar Uzziyeliyawa. Waɗannan kabilar Kohatawa ne. 28 Mazaje 8,600 an ƙidaya su shekaru daga wata ɗaya zuwa sama su lura da abubuwan dake na Yahweh. 29 Dangogin Kohat tilas su yi sansani a gefen kudu da rumfar sujada. 30 Elizafan ɗan Uzziyel tilas ya shugabanci dangogin Kohatawa. 31 Tilas su lura da akwatin, da teburin, da abin ajiyar fitila, da bagadai, da abubuwa masu tsarki da ake amfani da su wajen hidimarsu, labule, da dukkan aiki dake kewaye da shi. 32 Eliyeza ɗan Haruna firist tilas ya shugabanci mutanen dake shugabantar Lebiyawa. Tilas ya kula da mutanen dake lura da wuri mai tsarki. 33 Dangogi biyu suka zo daga Merari: Dangin Mahliyawa da dangin Mushiyawa. Waɗannan dangogi sun zo daga Merari. 34 Mazaje 6,200 aka ƙidaya shekara daga wata ɗaya zuwa sama. 35 Zuriyel ɗan Abihayil tilas ya shugabanci dangogin Merari. Tilas su yi sansani a gefen arewa da rumfar sujada. 36 Zuriyar Merari tilas su lura da katakan rumfar sujada, da sandunan gittawa, dana dirkoki, dana kafa harsashe, dukkan kaya masu ƙarfi, da duk wani abu da yake tattare dasu, duk da 37 ginshiƙai da dirkokin harabar dake kewaye da rumfar sujada, tare da kwasfofinsu, turkuna, da igiyoyin. 38 Musa da Haruna da 'ya'yansu maza tilas su yi sansani a gefen gabas na rumfar sujada, a gaban rumfar taruwa, zuwa tasowar rana. Sune ke da nauyi domin cika ayyukan tsattsarkan wuri da ayyukan mutanen Isra'ila. Duk wani bãre da ya gabato tsattsarkan wuri tilas a kashe shi. 39 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan mazajen dake cikin dangogin Lebi masu shekaru daga wata ɗaya zuwa sama, kamar dai yadda Yahweh ya umarta. Suka ƙidaya maza dubu ashirin da biyu. 40 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ƙidaya dukkan mazaje haihuwar fãri na mutanen Isra'ila masu shekaru daga wata ɗaya zuwa sama. Ka lissafa sunayensu. 41 Tilas ka ɗauki Lebiyawa domina - Ni ne Yahweh - maimakon dukkan haihuwar fãri na mutanen Isra'ila, da dabbobin Lebiyawa maimakon haihuwar fãri na dabbobin zuriyar Isra'ila." 42 Musa ya ƙidaya dukkan haihuwar fãri na mutanen Isra'ila yadda Yahweh ya umarce shi ya yi. 43 Ya ƙidaya sunan dukkan mazaje haihuwar fãri, shekara daga wata ɗaya zuwa sama. Ya ƙidaya maza 22,273. 44 Yahweh, ya sake magana da Musa. Ya ce, 45 "Ka ɗauki Lebiyawa a maimakon dukkan haihuwar fãri daga cikin mutanen Isra'ila, ka kuma ɗauki dabbobin Lebiyawa a maimakon dabbobin mutanen. Lebiyawa nawa ne - Ni ne Yahweh. 46 Tilas ne ka karɓi shekel biyar domin fansar kowanne ɗaya daga cikin 273 haihuwar fãri na mutanen Isra'ila da suka zarce lissafin Lebiyawa. 47 Tilas ka yi amfani da shekel na tsattsarkan wuri a matsayin adadin awo. Shekel na dai-dai da awo ashirin na gera. 48 Tilas ku bayar da kuɗin fansa da kuka biya ga Haruna da 'ya'yansa maza." 49 Sai Musa ya karɓi biyan fansar daga wurin waɗanda suka zarce lissafin waɗanda Lebiyawa suka fansa. 50 Musa ya karɓi kuɗin daga haihuwar fari na mutanen Isra'ila ya karɓi shekel 1,365 an auna da shekel na tsattsarkan wuri. Musa ya bayar da kuɗin fansa ga Haruna da 'ya'yansa maza. 51 Musa ya yi kowanne abu da aka ce masa yayi ta maganar Yahweh kamar yadda Yahweh ya umarce shi.

Sura 4

1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce, 2 "Ka yi ƙidayar mazaje zuriyar Kohat daga cikin Lebiyawa, bisa ga dangoginsu da iyalansu. 3 Ka ƙidaya dukkan mazan dake shekaru talatin zuwa hamsin. Waɗannan mutane tilas su shiga ayarin hidima a cikin rumfar taruwa. 4 Zuriyar Kohat tilas su lura da abubuwa mafi tsarki da aka keɓe domina a cikin rumfar taruwa. 5 Sa'ad da sansanin ya shirya matsawa gaba, Haruna da 'ya'yansa maza tilas su shiga cikin rumfar, su sauke labulen da ya raba tsakanin wuri mafi tsarki da wuri mai tsarki su kuma rufe akwatin alƙawari da shi. 6 Tilas su rufe akwatin da fãtun saniyar teku. Tilas su baza shuɗiyar sutura a kai. Tilas su sãƙa dirkokin don su ɗauke shi. 7 Za su baza shuɗiyar sutura bisa teburin gurasa da ke gabansa. A bisan sa tilas su sa kwanonin, da cokulan, da langunan, da kwalaben zubawa. Tilas koyaushe gurasa ta kasance a teburin. 8 Tilas su rufe ta da jar sutura kuma tare da fãtar saniyar teku. Tilas su sãƙa dirkoki na ɗaukar teburin. 9 Tilas su ɗauki shuɗiyar sutura su rufe mazaunin fitilar, tare da fitilun, da mamurɗan, da tururrukan, da dukkan kwalaben mai domin fitilun. 10 Tilas su sanya mazaunin fitilar tare da kayayyakinsa a cikin abin rufewar da aka yi da fãtar saniyar teku, tilas su sanya shi cikin katakon ɗauka. 11 Tilas su baza sutura shuɗiya bisa bagadin zinariya. Tilas su rufe shi da abin rufewar da aka yi da fãtun saniyar teku, daga nan kuma a sãƙa dirkokin ɗauka. 12 Tilas su ɗauki dukkan kayayyakin aikin wuri mai tsarki a kuma rufe su da shuɗiyar sutura. Tilas su rufe shi da fãtun saniyar teku a sanya kuma kayayyakin cikin katakon ɗauka. 13 Tilas su ɗebe toka daga bagadi su kuma shimfiɗa sutura shunayya bisa bagadin. 14 Tilas su sanya dukkan kayayyaki da suka yi amfani da su wurin aikin bagadi bisa katakon ɗauka. Waɗannan kayayyaki su ne kaskunan wuta, cokula masu yatsu, cebura, kwanuka, da dukkan sauran kayayyaki domin bagadi. Tilas su rufe bagadin da fãtun saniyar teku Daga nan kuma su sãƙa dirkokin ɗauka. 15 Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka kammala rufe wuri mai tsarki da dukkan kayayyakinsa, sa'ad da kuma sansani ya matsa gaba, Daga nan zuriyar Kohat tilas su zo su ɗauki wuri mai tsarki. Idan suka taɓa kayayyakin aikin masu tsarki, tilas su mutu. Wannan ne aikin zuriyar Kohat, su ɗauki kayayyakin ado na cikin rumfar taruwa. 16 Eliyeza ɗan Haruna firist zai shugabanci lura da mai domin haskakawa, turare mai daɗi, baikon hatsi da aka saba yi, da mai na shafewa. Zai shugabanci lura da rumfar sujadar gaba ɗaya da dukkan abin dake cikin ta, wuri mai tsarki da kayayyakinsa." 17 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce, 18 "Kada ku bari a cire kabilar dangogin Kohatawa daga cikin Lebiyawa. 19 Ku kãre su, domin su rayu kada kuma su mutu, ta wurin yin haka. Sa'ad da suka kusanci abubuwa mafi tsarki 20 tilas ba za su je su duba wuri mai tsarki ba ko dana ɗan taƙi, ko kuwa tilas su mutu. Haruna da 'ya'yansa maza tilas su shiga ciki, Daga nan kuma Haruna da 'ya'yansa maza tilas su sanya kowanne daga cikin Kohatawa ga aikinsa, ga aikinsa na musamman." 21 Yahweh ya sake magana da Musa, ya ce, 22 "Ka yi ƙidayar zuriyar Gashon kuma, bisa ga iyalan kakanninsu bisa ga dangoginsu. 23 Ka ƙidaya waɗanda suke shekaru talatin zuwa shekaru hamsin. Ka ƙidaya dukkan waɗanda za su shiga ayarin su yi bauta a rumfar taruwa. 24 Wannan ne aikin kabilun Gashonawa sa'ad da suka yi bauta da abin da suka ɗauka. 25 Tilas su ɗauki labulan rumfar sujada, da rumfar taruwa da abin rufe ta, abin rufe ta na fãtar saniyar teku, da labulan hanyar shiga rumfar taruwa. 26 Tilas su ɗauki labulan harabar, labule domin hanyar ƙofa ta ƙofar harabar, wadda ke kusa da rumfar sujada kusa kuma da bagadi, igiyoyinsu, da dukkan kayayyakin aiki domin hidimarsu. Duk abin da ya kamata a yi da waɗanan abubuwa, tilas su yi shi. 27 Haruna da 'ya'yansa maza tilas su bida dukkan hidimar zuriyar Gashonawa, a cikin dukkan abin da suka ɗauko, a cikin kuma dukkan hidimarsu. 28 Tilas ka sanya su ga dukkan ayyukansu. Wannan ne hidimar dangogin zuriyar Gashonawa domin rumfar taruwa. Itama ɗan Haruna firist tilas ne ya bida su cikin hidimarsu. 29 Tilas ka ƙidaya zuriya Merari bisa ga dangoginsu, ka kuma shirya su bisa ga iyalan kakanninsu, 30 daga shekaru talatin zuwa sama har shekaru hamsin. Ka ƙidaya dukkan waɗanda za su shiga ayari su kuma yi bauta a rumfar taruwa. 31 Wannan ne hakkinsu da aikinsu a cikin dukkan hidima domin rumfar taruwa. Tilas su lura da katakan rumfar sujada, da sandunan gittawa, dirkoki, da mahaɗai, 32 tare da dirkokin filin harabar dake kewaye da rumfar sujada, mahaɗansu, turkuna, da igiyoyinsu, tare da dukkan kayayyakinsu. Ka lissafa bisa sunan kayayyakin da tilas su ɗauka. 33 Wannan ne aikin kabilun zuriyar Merari, abin da za su yi domin rumfar taruwa, ƙarƙashin bishewar Itama ɗan Haruna firist." 34 Musa da Haruna da shugabannin jama'a suka ƙidaya zuriyar Kohatawa bisa ga dangogin iyalan kakanninsu. 35 Suka ƙidaya su daga shekaru talatin zuwa sama har shekaru hamsin. Suka ƙidaya kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a rumfar taruwa. 36 Suka ƙidaya mazaje 2,750 bisa ga dangoginsu. 37 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan mazaje a cikin dangogi da iyalan Kohatawa waɗanda suke bauta a rumfar taruwa. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa. 38 Aka ƙidaya zuriyar Gashon a cikin dangoginsu, ta wurin iyalan kakanninsu, 39 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin, kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a rumfar taruwa. 40 Dukkan mazaje, da aka ƙidaya ta wurin dangogi da iyalan kakanninsu, lissafi 2,630 ne. 41 Musa da Haruna suka ƙidaya dangogin zuriyar Gashon waɗanda za su yi bauta a cikin rumfar taruwa. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa. 42 Aka ƙidaya zuriyar Merari a cikin dangoginsu ta wurin iyalan kakanninsu, 43 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin, kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a cikin rumfar taruwa. 44 Dukkan mazaje, da aka ƙidaya ta wurin dangoginsu da iyalan kakanninsu, lissafi 3,200 ne. 45 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan waɗannan mazaje, zuriyar Merari. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa. 46 Sai Musa, Haruna, da shugabannin Isra'ila suka ƙidaya dukkan Lebiyawa ta wurin dangoginsu cikin iyalan kakanninsu 47 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin. Suka ƙidaya kowanne da zai yi aiki a cikin rumfar sujada. 48 Suka ƙidaya mazaje 8,580. 49 Ta umarnin Yahweh, Musa ya ƙidaya kowanne mutum, yana ajiyar ƙidayar kowanne bisa ga irin aikin da aka ba shi ya yi. Ya ƙidaya kowanne mutum bisa ga irin hakkin da aka ɗora masa ya ɗauka. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su su yi ta wurin Musa.

Sura 5

1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila su kori kowanne mutum daga sansani wanda ke da cutar fãta da ake ɗauka, da kowanne dake da ƙurjin dake fitar da ruwa, da duk wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa. 3 Ko namiji ko mace, tilas ka kore su daga sansanin. Tilas ne ba za su gurɓata sansanin ba, saboda ina zaune a cikin sa." 4 Mutanen Isra'ila suka yi haka. Suka kore su daga sansanin, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. Mutanen Isra'ila suka yi biyayya da Yahweh. 5 Yahweh ya sa ke magana da Musa. Ya ce, 6 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Sa'ad da wani mutum ko wata mata suka aikata zunubi irin wanda mutane ke aikatawa ga junansu, kuma ya yi rashin aminci a gare ni, wannan mutum ya yi laifi. 7 Daga nan tilas ya furta zunubin da ya yi. Tilas ya biya farashin laifinsa gaba ɗaya ya kuma ƙara akan farashin kashi ɗaya cikin biyar. Tilas ya bayar da wannan ga wanda ya yiwa laifin. 8 Amma idan wanda aka yiwa laifin bai da ɗan'uwa na kusa da zai karɓi biyan, tilas ya biya farashin laifinsa gare ni ta wurin firist, tare da rago na yin kaffara domin sa. 9 Kowanne baiko na mutanen Isra'ila, abubuwan da aka keɓe aka kuma kawo ga firist ta wurin mutanen Isra'ila, zai zama nasa. 10 Baye-bayen kowanne taliki zai zama domin firist; idan wani ya bayar da wani abu ga firist, zai zama nasa." 11 Bugu da ƙari, Yahweh yayi magana da Musa. Ya ce, 12 "Kayi magana da mutanen Isra'ila. Ka ce da su, 'Ga misali idan matar wani ta kauce hanya ta kuma yi zunubi gãba da mijinta. 13 Misali a ce wani mutum ya kwana da ita. A wannan al'amari, ta ƙazantu. Ko da mijinta bai gani ba ko kuma ya san da hakan, kuma ko da ba wanda ya kama ta cikin aikata hakan kuma ba bu wanda zai bada shaida gãba da ita, 14 duk da haka. ruhun kishi zai sanarwa mijin cewa matarsa ta ƙazamtu. Ko da yake, ruhun kishi na ƙarya na iya sauko wa mutum alhali matarsa ba ta ƙazantu ba. 15 A cikin irin waɗannan al'amura, tilas mutumin ya kawo matarsa ga firist. Tilas mutumin ya zo da baikon da ake buƙata a madadin ta, kashi goma na awon garin bali. Tilas ne kuma ba zai zuba mai a kai ba ko kuma ya zuba turaren ƙonawa a kai ba, saboda baikon hatsi ne na kishi, baikon hatsi domin tunawa, a matsayin abin tunawa da laifin. 16 Tilas firist ya kawo ta kusa ya miƙa ta gaban Yahweh. 17 Tilas firist ya ɗauki gorar ruwa mai tsarki ya kuma ɗibi ƙurar ƙasan rumfar sujada. Tilas ya zuba ƙurar cikin ruwan. 18 Firist zai sa matar gaban Yahweh kuma zai kwance gashin dake kan matar. Zai sanya cikin hannuwanta baikon hatsi na tunawa, wanda shi ne baikon hatsi na zato. Firist zai riƙe a hannunsa ruwa mai ɗaci da zai iya kawo la'ana. 19 Firist zai sanya matar ƙarƙashin rantsuwa ya kuma ce mata, 'Idan babu mutumin da yayi saduwar jima'i dake, idan kuma baki fita iskanci ba kika kuma aikata rashin tsarki, to zaki 'yantu daga wannan ruwa na ɗaci da zai iya kawo la'ana. 20 Amma idan ke, mace ƙarƙashin mijinta, kin fita iskanci, idan kin ƙazantu, idan kuma wani mutum daban ya kwana da ke, 21 daga nan, (tilas firist ya sa matar ta ɗauki rantsuwar da za ta sauko mata da la'ana, daga nan kuma tilas ya ci gaba da magana da matar) 'Yahweh zai maida ke la'ana da za a nuna wa mutanenki ya kasance haka. Wannan zai kasance idan Yahweh ya sa cinyarki ta ruɓe kuma mararki ta kumbura. 22 Wannan ruwan da zai kawo la'ana zai shiga cikin cikinki ya sa mararki ta kumbura cinyoyinki kuma su ruɓe.' Matar kuma za ta maida amsa, 'I, bari haka ya kasance idan ina da laifi.' 23 Firist tilas ne ya rubuta waɗannan la'anoni cikin naɗaɗɗen littafi, Daga nan kuma tilas ya wanke rubutattun la'anonin cikin ruwa mai ɗaci. 24 Tilas firist ya sa matar ta sha ruwa mai ɗaci da zai kawo la'ana. Ruwan dake kawo la'ana zai shiga cikinta ya zama ɗaci. 25 Firist tilas ya ɗauke baikon hatsi na kishi daga hannun matar. Dole ya riƙe baikon hatsin a gaban Yahweh ya kuma kawo shi zuwa bagadi. 26 Firist tilas ya ɗibi tafin hannu na baikon hatsin a matsayin baikon madadi, ya kuma ƙonashi bisa bagadi. Daga nan tilas ya ba matar ruwa mai ɗaci ta sha. 27 Sa'ad da ya ba ta ruwan ta sha, idan ta ƙazantu saboda ta aikata zunubi gãba da mijinta, to ruwan dake kawo la'ana zai shiga cikinta, ya kuma zama ɗaci. Mararta za ta kumbura kuma cinyarta ta ruɓe. Matar za ta zama la'ananna a cikin mutanenta. 28 Amma idan matar ba ta ƙazantu ba kuma da tsabtarta, to tilas ta 'yantu. Za ta iya haihuwar 'ya'ya. 29 Wannan ce shari'ar kishi. Shari'a ce domin matar da ta fita iskanci daga wurin mijinta ta kuma ƙazantu. 30 Shari'a ce domin mutumin da ka tare da ruhun kishi sa'ad da yake kishin matarsa. Tilas ya kawo matar a gaban Yahweh, kuma firist tilas ya yi mata dukkan abin da shari'ar kishi ta tsara. 31 Mutumin zai 'yantu daga laifi domin kawo matarsa da ya yi a gaban firist. Tilas ne matar ta ɗauki nauyin kowanne laifi da take da shi."

Sura 6

1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Ka ce masu, 'Idan namiji ko mace ya keɓe kansa ga Yahweh tare da alƙawari na musamman na zama Nazari, 3 ba zai taɓa shan ruwan inabi da abin sha mai ƙarfi ba. Ba zai taɓa shan abin sha mai tsami da aka yi daga ruwan inabi ba ko daga abin sha mai ƙarfi. Ba zai taɓa shan abin da aka matso daga inabi ba ko ya ci sabobbin 'ya'yan inabi ko busassun 'ya'yan inabi ba. 4 A cikin dukkan kwanakin keɓewarsa gare ni, ba zai ci wani abin da aka yi da inabi ba, tare da dukkan abin da aka yi daga tsabar inabin zuwa fãtunsa. 5 A cikin dukkan lokacin alƙawarinsa na keɓewa, ba za a yi amfani da aska ba a bisa kansa har sai kwanakin keɓewarsa ga Yahweh sun cika. Tilas a ware shi ga Yahweh. Tilas ya bar gashinsa ya yi tsawo a bisa kansa. 6 A cikin dukkan lokacin da ya keɓe kansa ga Yahweh, tilas ne ba zai zo kusa da gawa ba. 7 Tilas ne ba zai mai da kansa marar tsarki ba ko da domin mahaifinsa, mahaifiyarsa, ɗan'uwansa, da 'yar uwarsa ba, idan suka mutu. Wannan kuwa saboda an keɓe shi ga Allah, kamar yadda kowa zai gani ta wurin dogon gashinsa. 8 A cikin dukkan lokacin keɓewarsa mai tsarki ne shi, ajiyayye domin Yahweh. 9 Idan wani da gaske farat ɗaya ya mutu a gefensa, ya kuma ɓãta keɓaɓɓen kansa, Daga nan tilas ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa - a rana ta bakwai tilas ya aske shi. 10 A rana ta takwas tilas ya kawo kurciyoyi biyu ko tantabaru 'yan shila biyu ga firist a ƙofar shiga rumfar taruwa. 11 Firist kuma tilas ya miƙa tsuntsuwa ɗaya a matsayin baikon zunubi, ɗaya kuma a matsayin baikon ƙonawa. Waɗannan za su yi masa kafara saboda ya yi zunubi ta wurin kasancewa kusa da gawa. Tilas ya sake keɓe kansa kuma a wannan rana. 12 Tilas ya kiyaye kansa ga Yahweh domin kwanakin keɓewarsa. Tilas ya kawo ɗan rago ɗan shekara ɗaya a matsayin baikon laifi. Kwanakin da ya yi kafin ya ƙazantar da kansa tilas ba za a lissafa su ba, domin keɓewarsa ta ƙazantu. 13 Wannan ce shari'a game da Nazari domin sa'ad da lokacin keɓewarsa ya cika. Tilas a kawo shi ƙofar shiga rumfar taruwa. 14 Tilas ya gabatar da baikonsa ga Yahweh. Tilas ya miƙa a matsayin baikon ƙonawa ɗan rago ɗan shekara ɗaya kuma marar aibi. Tilas ya miƙa a matsayin baikon zunubi 'yar tunkiya 'yar shekara ɗaya kuma marar aibi. Tilas ya kawo rago a matsayin baikon zumunta wanda yake marar aibi. 15 Tilas ya kawo kwandon gurasa da aka yi ba tare da gami ba, dunƙule-dunƙule na gari mai laushi da aka gauraya da mai, waina marar gami da aka shafe da mai, tare da baikon hatsinsu da baye-baye na sha. 16 Tilas ne firist ya gabatar da su a gaban Yahweh. Tilas ya miƙa baikon zunubinsa da baikon ƙonawa. 17 Tare da kwandon gurasa marar gami, tilas ya miƙa ragon a matsayin hadaya, baikon zumunta ga Yahweh. Firist kuma tilas ya gabatar da baikon hatsi da baikon abin sha. 18 Nazirin tilas ya aske kansa don a nuna cewa an keɓe shi ga Allah a ƙofar shiga rumfar taruwa. Tilas ya ɗauki gashin dake daga kansa ya kuma sanya a cikin wutar dake ƙarƙashin hadayar baye-bayen zumunta. 19 Tilas firist ya ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, curin gurasa ɗaya marar gami daga cikin kwandon, da waina ɗaya marar gami. Tilas ya ɗora su cikin hannuwan Banazaren bayan ya aske kansa nuna keɓewa. 20 Tilas firist ya wurga su a matsayin baiko a gaban Yahweh, kaso mai tsarki domin firist, tare da ƙirgin da aka wurga da kuma cinyar da aka gabatar domin firist. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi. 21 Wannan ce shari'a domin Nazari wanda ya yi alƙawarin baikonsa ga Yahweh domin keɓewarsa. Kowanne abu kuma da zai iya bayarwa, tilas ya kiyaye ka'idodin alƙawarin da ya ɗauka, ya kiyaye alƙawarin da aka nuna ta wurin shari'a domin Banazare."' 22 Yahweh ya sake magana da Musa. Ya ce, 23 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza. Cewa, 'Tilas ku albarkaci mutanen Isra'ila ta wannan hanya. Tilas ku ce masu, 24 "Bari Yahweh ya albarkace ku ya kuma kiyaye ku. 25 Bari Yahweh ya sa fuskarsa ta haskaka a bisanku ya kuma yi maku alheri. 26 Bari Yahweh ya kalle ku da tagomashi ya kuma ba ku salama."' 27 Ta wannan hanya ce tilas za su bayar da sunana ga mutanen Isra'ila. Daga nan zan albarkace su.

Sura 7

1 A ranar da Musa ya kammala rumfar sujadar, sai ya shafe ta ya kuma keɓe ta ga Yahweh, tare da dukkan kayan adonta. Ya yi haka kuma domin bagadin da dukkan kayayyakinsa. Ya shafesu ya kuma keɓe su ga Yahweh. 2 A wannan rana, shugabannin Isra'ila, shugabannin iyalan kakanninsu, suka miƙa hadayu. Waɗannan mutane ne ke shugabancin kabilun. Sun shugabanci lissafin mazajen a ƙidaya. 3 Suka kawo baye-bayensu gaban Yahweh. Suka kawo kekunan noma rufaffu guda shida da shanu sha biyu. Suka kawo kowanne keken noma ɗaya domin shugabanni biyu, kuma kowanne shugaba ya kawo sã ɗaya. Suka gabatar da waɗannan abubuwa a gaban rumfar sujada. 4 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 5 "Ka karɓi baye-bayen daga garesu ka kuma yi amfani da baye-bayen domin aikin rumfar taruwa. Ka bayar da baye-bayen ga Lebiyawa, ga kowannen su bisa ga yadda aikinsa ke buƙatarsu." 6 Musa ya ɗauki kekunan noman da shanun, ya kuma bayar da su ga Lebiyawa. 7 Ya bayar da kekunan noma biyu da shanu huɗu ga zuriyar Gashon, saboda abin da aikinsu ke buƙata. 8 Ya bayar da kekunan noma huɗu da shanu takwas ga zuriyar Merari, cikin kulawar Itama ɗan Haruna firist. Ya yi wannan ne saboda abin da aikinsu ya ke buƙata. 9 Amma bai ba da ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ba ga zuriyar Kohat, saboda nasu zai kasance aikin dake da dangantaka da abubuwan dake na Yahweh wanda za su ɗauka bisa kafaɗunsu. 10 Shugabannin suka miƙa kayayyakinsu domin keɓewar bagadi a ranar da Musa ya shafe bagadi. Shugabannin suka miƙa hadayunsu a gaban bagadin. 11 Yahweh ya cewa Musa, "Kowanne shugaba a ranarsa zai miƙa hadayarsa domin keɓewar bagadi." 12 A rana ta farko, Nashon ɗan Amminadab, na kabilar Yahuda, ya miƙa tasa hadayar. 13 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awo na rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 14 Ya bayar da kwanon zinariya guda ɗaya mai nauyin awo goma cike da turaren ƙonawa. 15 Ya bayar da bijimi ɗaya domin baiko na ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 16 Ya bayar da bunsuru ɗaya domin baikon zunubi. 17 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab. 18 A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuyar, shugaban Issaka, ya miƙa hadayarsa. 19 Ya miƙa a matsayin hadaya tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa ɗaya mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 20 Ya kuma bayar da kwanon zinariya guda ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 21 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 22 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 23 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuyar. 24 A rana ta ukku, Eliyab ɗan Helon, shugaban zuriyar Zebulun, ya miƙa hadayarsa. 25 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130, da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 26 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 27 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 28 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon sujada. 29 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon. 30 A rana ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban zuriyar Ruben, ya miƙa hadayarsa. 31 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 32 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 33 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya. 34 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 35 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur. 36 A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban zuriyar Simiyon, ya miƙa hadayarsa. 37 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 38 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 39 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya. 40 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 41 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar, a matsayi hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai. 42 A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deuyel, shugaban zuriyar Gad, ya miƙa hadayarsa. 43 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi. 44 Ya kuma bayar da kwanon azurfa ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 45 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya. 46 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 47 Ya bayar da shanu biyu, roga biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deuyel. 48 A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban zuriyar Ifraim, ya miƙa hadayarsa. 49 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi. 50 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 51 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 52 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 53 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud. 54 A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban zuriyar Manasse, ya miƙa hadayarsa. 55 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 56 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 57 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 58 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 59 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur. 60 A rana ta tara, Abidan ɗan Gidiyoni, shugaban zuriyar Benyamin, ya miƙa hadayarsa. 61 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 62 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 63 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 64 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 65 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gidiyoni. 66 A rana ta goma, Ahiyeza ɗan Ammishaddai, shugaban zuriyar Dan, ya miƙa hadayarsa. 67 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi. 68 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 69 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya. 70 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 71 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Ahiyeza ɗan Ammishaddai. 72 A rana ta sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban zuriyar Asha, ya miƙa hadayarsa. 73 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi. 74 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 75 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 76 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 77 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran. 78 A rana ta sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban zuriyar Naftali, ya miƙa hadayarsa. 79 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi. 80 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa. 81 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya. 82 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi. 83 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan. 84 Shugabannin Isra'ila suka keɓe dukkan waɗannan a ranar da Musa ya shafe bagadi. Suka keɓe tirirrikan azurfa sha biyu, bangajin azurfa sha biyu, da kwanukan zinariya sha biyu. 85 Kowanne tire nauyin awo 130 kowanne bangaji kuma nauyin awo saba'in. Dukkan kayan azurfar nauyin su awo 2,400 ne, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. 86 Kowanne kwanukan zinariya sha biyu, cike da turaren ƙonawa, nauyin awo goma bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan kwanukan zinariyar nauyin awo 120 ne. 87 Suka keɓe dukkan dabbobi domin baye-baye na ƙonawa, bijimai sha biyu, rago sha biyu, 'yan raguna sha biyu 'yan shekara ɗaya. Suka bayar da baikon hatsinsu. Suka bayar da bunsuru sha biyu a matsayin baikon zunubi. 88 Daga dukkan garken dabbobinsu, suka bayar da bijimai ashirin da huɗu, rago sittin, bunsuru sittin, da 'yan raguna sittin 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan domin keɓewar bagadi ne bayan an shafe shi. 89 Sa'ad da Musa ya shiga cikin rumfar taruwa domin ya yi magana tare da Yahweh, ya ji muryarsa ya na magana da shi. Yahweh ya yi magana da shi daga bisan marfin kafara dake a kan akwatin alƙawari., daga tsakanin kerubim biyu. Ya yi masa magana.

Sura 8

1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Ka yi magana da Haruna. Ka ce da shi, 'Fitilun nan guda bakwai su bada haske a gaban wurin ɗora fitilar idan ka kunna su."' 3 Haruna kuwa ya yi haka. Ya kunna fitilun yadda za su ba da haske wajan gaban inda a ke ɗora fitilun, kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa. 4 Haka a ka yi wurin ɗora fitilun yadda Yahweh ya nuna wa Musa. Ya zama bugaggiyar zinariya tun daga ƙasa har sama, da bugaggun koffuna kamar furanni. 5 Yahweh, ya sake yin magana da Musa. Ya ce, 6 "Ka ɗebi Lebiyawa daga cikin mutanen Isra'ila ka tsarkake su. 7 Ga yadda za ka tsarkake su: Ka yayyafa ruwan kafara a kansu. Ka sa su aske jikinsu dukka, su wanke tufafinsu ta haka za su tsarkake kansu. 8 Ka sa su sami ɗan bijimi da baikonsa na gari wanda a ka gauraya da mai. Su kuma sami wani ɗan bijimin domin baiko na zunubi. 9 Ka kawo Lebiyawan gaban rumfa ta taruwa ka kuma tattara dukkan mutanen Isra'ila. 10 Sa'ad da ka kawo Lebiyawan gaban Yahweh, sai dukkan mutanen Isra'ila su ɗora hannuwansu a kan Lebiyawan. 11 Sai Haruna ya miƙa Lebiyawan a gaban Yahweh, kamar bayarwa ta ɗagawa daga mutanen Isra'ila domin su yi wa Yahweh hidima. 12 Sai Lebiyawan su ɗora hannuwansu a bisa kawunan bajiman. Sai ka miƙa bijimi ɗaya baiko na zunubi, ɗaya bijimin kuma baiko na ƙonawa gare ni, sai a yi wa Lebiyawan kafara. 13 Sai ka gabatar da Lebiyawan ga Haruna da 'ya'yansa, ka ɗaga su kamar baiko na ɗagawa a gare ni. 14 Ta haka za ka keɓe Lebiyawan daga cikin mutanen Isra'ila. Lebiyawan za su zama nawa. 15 Bayan wannan sai Lebiyawan su shiga su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa. Dole ne ka tsarkake su. Dole kuma ka miƙa su kamar baikon na ɗagawa. 16 Ka yi haka, saboda sun zama nawa ɗungum daga cikin mutanen Isra'ila. Su za su zama kamar kowanne ɗă namiji da aka fara haifuwa, ɗa na fari daga kowacce zuriya ta Isra'ila. Na ɗauki Lebiyawa domin kaina. 17 Kowanne ɗă na fari na mutanen Isra'ila nawa ne, na mutum dana dabba. A ranar dana ɗauke dukkan rayukan 'ya'yan fari cikin ƙasar Masar, na keɓe su gare ni. 18 Na ɗauki Lebiyawa daga cikin mutanen Isra'ila a madadin dukkan 'ya'yan fari. 19 Na bayar da Lebiyawa kyauta ga Haruna da 'ya'yansa. Na ɗauke su daga cikin mutanen Isra'ila domin su yi aikin mutanen Isra'ila a cikin rumfa ta taruwa. Na bayar da su domin su yi kafara saboda mutanen Isra'ila domin kada annoba ta same su sa'ad da suka zo kusa da wuri mai tsarki." 20 Musa da Haruna da dukkan taron mutanen Isra'ila suka yi haka da Lebiyawa. Suka yi dukkan abin da Yahweh ya ummurci Musa game da Lebiyawa. Mutanen Isra'ila suka yi haka da su. 21 Lebiyawan su ka tsarkake kansu suka wanke tufafinsu, Haruna ya gabatar da su kamar baiko na ɗagawa ga Yahweh kuma ya yi kafara domin su ya tsaftace su 22 Bayan haka, sai Lebiyawan suka shiga domin su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa a gaban Haruna da 'ya'yansa. Wannan ya zama kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa game da Lebiyawa. Haka suka yi da dukkan Lebiyawa. 23 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce, 24 "Dukkan wannan saboda Lebiyawan da suka kai shekara ashirin da biyar ne zuwa gaba. Za su haɗu da sauran su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa. 25 Za su dena yin hidima sa'ad da suka kai shekara hamsin. A waɗannan shekarun ba za su ƙara yin hidima ba. 26 Za su iya taimakon 'yan'uwansu waɗanda suke ci gaba da yin hidima a rumfa ta taruwa, amma su ba za su ƙara yin hidima ba. Sai ka jagoranci Lebiyawa cikin dukkan waɗannan al'amura.

Sura 9

1 Yahweh ya yi magana da Musa a cikin jejin Sinai, a cikin wata na biyu bayan sun fito daga ƙasar Masar. Ya ce, 2 "Sai mutanen Isra'ila su kiyaye idin Ƙetarewa a lokacin da aka ayyana cikin shekara. 3 A kan rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da yamma, dole ne ku kiyaye idin Ƙetarewa a lokacin da aka ayyana shi a shekara. Ku kiyaye shi ku bi dukkan ka'idodi, ku yi biyayya da dukkan farillan da aka ayyana domin sa." 4 Haka, Musa ya gaya wa mutanen Isra'ila ya wajaba su riƙa kiyaye Idin Ƙetarewa. 5 Haka suka kiyaye Idin Ƙetarewa a cikin wata na fari a kan rana ta goma sha huɗu ga watan, da yamma, a cikin jejin Sinai. Mutanen Isra'ila suka kiyaye dukkan abin da Yahweh ya ummarci Musa ya yi. 6 Akwai waɗansu mutanen da suka zama ƙazamtattu ta wurin taɓa gawa. Ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a wannan ranar ba. 7 Waɗannan mutane suka ce da Musa, "Mun ƙazamtu ta wurin taɓa gawar wani mutum. Meyasa hana aka mu miƙa hadaya ga Yahweh tare da sauran mutanen Isra'ila a lokacin da a ka ayyana na shekara?" 8 Musa yace da su, "Ku jira in ji umarnin da Yahweh zai bani saboda ku." 9 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 10 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Cewa, 'Idan wani a cikin ku, ko zuriyarku ya ƙazamtu ta wurin taɓa gawa, yana cikin tafiya mai nisa, zai iya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Yahweh.' 11 A cikin wata na biyu a kan rana ta goma sha huɗu da yamma, za su iya cin abincin Idin Ƙetarewa. Za su ci ragon Idin Ƙetarewa da gurasa marar gami da ganyaye masu ɗăci. 12 Kada su rage shi har zuwa safiya, ko su karya ƙasusuwan. Dole ne su kiyaye dukkan ka'idodin da aka ayyan na Idin Ƙetarewar. 13 Amma dukkan mutum mai tsarki kuma ba tafiya ya ke yi ba, amma bai yi Idin Ƙetarewar ba, wannan mutum za a datse shi daga cikin mutanensa saboda bai miƙa hadaya ga Yahweh yadda ake bukata a lokacin da aka ayyana a shekara ba. Wannan mutum zai ɗauki zunubinsa. 14 Idan akwai baƙo a cikin ku yana kiyaye Idin Ƙetarewa domin ya ba Yahweh girma, sai ya kiyaye dukkan abin da aka umarta, da ka'idodinsa, da dukkan dokokinsa. Dokoki ɗaya ne za su shafi wanda aka haifa a ƙasar da kuma baƙo." 15 A ranar da aka kafa alfarwar, sai girgije ya sauka ya rufe ta, wato rumfar ta alƙawari. Da yamma girgijen yana bisan alfarwar. Ya zama kamar wuta har zuwa safiya. 16 Haka ya ci gaba. Da dare girgijen ya rufe alfarwar kamar wuta. 17 Duk lokacin da aka ɗauke girgijen daga bisa rumfar, sai mutanen Isra'ila su ci gaba da tafiyarsu. Dukkan sa'adda girgijen ya tsaya wuri ɗaya, sai mutanen su yi zango. 18 Idan Yahweh ya bada ummurni, sai mutanen Isra'ila su tafi, idan ya bada ummurni sai su yi zango. Sa'ad da girgijen ya tsaya a bisan alfarwar, sai su tsaya a zangonsu. 19 Idan girgijen ya tsaya a bisan alfarwar kwanaki da yawa, sai mutanen Isra'ila su yi biyayya da ka'idodin Yahweh ba za su tafi ba. 20 Wani lokaci girgijen yakan tsaya a bisa alfarwar har 'yan kwanaki. A wannan lokaci, sai su yi biyayya da umarnin Yahweh--sai su yi zango sai in ya bada umarni sai su tafi. 21 Wani lokacin sai girgijen ya kasance a bisa zangon tun daga yamma har safiya. Idan girgijen ya tashi da safe sai su tafi. Idan kuma ya ci gaba da tsayawa dare da rana, sai sa'ad da girgijen ya tashi za su tafi. 22 Duk sa'ad da girgijen ya tsaya a bisa alfarwar kwana biyu ko wata ɗaya ko shekara, idan dai girgijen yana tsaye a nan, mutanen za su tsaya a zangonsu ba za su tafi ba. Amma duk lokacin da aka ɗauke girgijen sai su kama tafiyarsu. 23 Za su yi zango sa'adda Yahweh ya bada umarni, kuma su tafi bisa ga umarninsa. Sun yi biyayya da umarnin da Yahweh ya ba Musa.

Sura 10

1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Ka yi kakaki biyu na azurfa. Ka yi su da bugaggiyar azurfa. Ka yi amfani da ƙahonin domin ka kira ƙungiyoyin jama'a su zo su taru kuma domin ka kira ƙungiyoyin jama'a su zakuɗa da zangunansu. 3 Fristoci su busa kakakin domin su kira dukkan ƙungiyoyin jama'a su taru a gaban rumfa ta taruwa. 4 Idan firistoci suka busa kakaki ɗaya, sai shugabanni da shugabannin iyalai na Isra; ila, su zo su taru. 5 Idan ka busa alama mai ƙara, sai zangon gabas su fara tafiyarsu. 6 Idan ka busa alama mai ƙara ta biyu, sai zanguna na zangon kudu su fara tafiyarsu. Suma sai su busa alama mai ƙara domin su tafi. 7 Sa'anda jama'a suka taru wuri ɗaya sai ka busa ƙahonin, amma ba da ƙarfi ba. 8 'Ya'yan Haruna da firistoci ne za su busa kakakin. Wannan za ta zama ka'ida a gare ka dukkan zamanun mutanenka. 9 Idan kuka tafi yaƙi cikin ƙasarku da maƙiyi wanda yake găba da ku, sai ku busa alama da kakakin. Ni, Yahweh Allahnku, zan tuna daku in cece ku daga maƙiyanku. 10 Kuma, lokacin bukukuwa, da bukukuwanku na yau da kullum ko na farkon wata, sai ku busa kakaki saboda baye--bayenku na ƙonawa da hadayinku da baye--bayenku na zumunci. Waɗannan abubuwa za su sa in tuna da ku, Ni Allahnku. Ni ne Yahweh Allahnku." 11 A cikin shekara ta biyu, a cikin wata na biyu, a rana ta ashirin ga watan, sai aka ɗauke girgijen daga bisa rumfar taruwa ta umarnin alƙawari. 12 Sai mutanen Isra'ila suka ci gaba da tafiyarsu daga jejin Sinai. Sai girgijen ya tsaya a jejin Faran. 13 Suka yi tafiyarsu ta fari, suna bin umarnin da Yahweh ya ba Musa. 14 Sai zangon dake ƙarƙashin tutar zuriyar Yahuda suka fara tafiya, suka fara gusawa da sojojinsu. Nashon ɗan Amminadab ya jagoranci sojojin Yahuda. 15 Netanel ɗan Zuyar ya jagoranci sojojin zuriyar Issaka. 16 Eliyab ɗan Helon ya jagoranci sojojin zuriyar Zebulun. 17 Zuriyar Geshon da Merari, waɗanda ke lura da alfarwa, suka ɗauki alfarwar suka tafi. 18 Na biye su ne sojojin dake ƙarƙashin tutar zangon Ruben suka shirya suka tafi. Elizur ɗan Shedur ya jagoranci sojojin Ruben. 19 Shenumiyel ɗan Zurishaddai ya jagoranci sojojin zuriyar Simeyon. 20 Eliyasaf ɗan Dewuyel ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Gad. 21 Sai Kohatiyawa suka shirya fita. Suka ɗauki kayayyaki masu tsarki na wurin sujada. Waɗansu za su shirya alfarwa kafin Kohatiyawa su zo zango na gaba. 22 Sojoji na ƙarƙashin tutar zuriyar Ifraim su ne na gaba. Elishama ɗan Amihud ya jagoranci sojojin Ifraim. 23 Gamaliyel ɗan Fedazur ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Manasse. 24 Abidan ɗan Gidiyoni ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Banyami. 25 Sojojin da suka yi zango a ƙarƙashin tutar zuriyar Dan su ne suka tashi daga ƙarshe. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ya jagoranci sojojin Dan. 26 Fagiyel ɗan Okran ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Asha. 27 Ahira ɗan Inan ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Naftali. 28 Wannan shi ne yadda sojojin mutanen Isra'ila suka shirya suka fita tafiyarsu. 29 Musa ya yi magana da Hobab ɗan Rewuyel mutumin Midiya. Rewuyel ne mahaifin matar Musa. Musa ya yi magana da Hobab ya ce, "Za mu tafi wurin da Yahweh ya bayyana. Yahweh yace, 'Zan baku shi.' Ka biyo mu zamu kyautata maka. Yahweh ya yi alƙawari zai kyautatawa Isra'ila." 30 Amma Hobab yace da Musa, "Ba zan bi ku ba. Zan tafi ƙasata wurin mutanena." 31 Sai Musa ya amsa, "Idan ka yarda kada ka rabu da mu. Ka san yadda a ke yin zango a cikin jeji. Sai ka kula da mu. 32 Idan ka biyo mu, zamu kyautata ma ka kamar yadda Yahweh zai kyautata mana." 33 Suka yi tafiya ta kwana uku daga tsaunin Yahweh. Akwatin alƙawari na Yahweh ya tafi a gabansu kwana uku domin ya samar masu wurin da za su huta. 34 Girgijen Yahweh yana bisansu da rana inda suke tafiya. 35 Dukkan lokacin da akwatin alƙawari ya tashi, Sai Musa yace, "Yahweh, tashi ka watsar da maƙiyanka. Ka sa masu ƙin ka su gudu daga wurinka." 36 Duk sa'ad da akwatin alƙawari ya tsaya, sai Musa yace,"Yahweh ka dawo wurin Isra'ila masu yawa dubbai."

Sura 11

1 Sai mutanen suka yi kuka game da matsalolinsu Yahweh kuwa yana ji. Yahweh ya ji ya yi fushi. Sai wuta ta fito daga wurin Yahweh ta kama a cikinsu har ta ƙone gefunan wasu bayan wani zangon. 2 Sai mutanen suka yi kira ga Musa, sai Musa ya yi addu'a ga Yahweh, sai wutar ta mutu. 3 Aka kira wannan wurin da suna Tabera, saboda wutar Yahweh ta yi ƙuna a wurin. 4 Sai waɗansu baƙi suka fara sauka a zangon zuriyar Isra'ila. Suka so su ci abinci mai kyau. Daga nan mutanen Isra'ila suka fara kuka suka ce, "Wane ne zai ba mu nama mu ci? 5 Mun tuna da kifin da muka ci a Masar kyauta, da kukumba da kabewa da albasa da kankana da tafarnuwa. 6 Yanzu har ma bamu da marmari, saboda wannan mannar kaɗai muke iya gani." 7 Manna dai tana kama da ƙwayar riɗi. Launinta kuma kamar ƙaro. 8 Mutanen suka zagaya suka ɗebo ta. Suka niƙa ta a dutse, suka daka ta a turmi, su ka dafa ta a tukwane, suka yi waina da ita. Sai ɗanɗanonta ya zama kamar na sabon man zaitun. 9 Sa'ad da raɓa ta sauko a kan zangon da dare, manna kuma ta faɗo. 10 Musa ya ji mutanen suna ta kuka cikin iyalansu, kowanne mutum ya fito ƙofar rumfarsa. Sai Yahweh ya yi fushi ƙwarai, Musa kuwa yana ganin koken-koken nasu bai yi dai-dai ba. 11 Musa yace da Yahweh, "Me yasa ka yiwa mutanenka mummunan abu haka? Me yasa baka yarda da ni ba? Ka sa na ɗauki nawaiyar mutanen nan dukka. 12 Ni na ɗauki cikin dukkan mutanen nan? Ni na haife su da zaka ce dani, 'Ka ɗauke su a ƙirjinka kamar yadda uba yake ɗaukar jariri?' Ni zan ɗauke su in kai su ƙasar da ka rantse wa kakaninsu cewa za ka ba su? 13 A ina zan sami naman da zan ba dukkan mutanen nan? Suna ta kuka a gabana suna cewa, 'Ka bamu nama mu ci.' 14 Ba zan iya da mutanen nan ba ni kaɗai. Sun yi mani yawa. 15 Tun da haka kake yi da ni, gara ka kashe ni yanzu--Idan na sami tagomashi a idanunka -- kada ka bari in ga takaicina." 16 Sai Yahweh yace da Musa, "Ka kawo dattawan Isra'ila guda saba'in a wurina. Ka tabbatar su dattawa ne kuma shugabannin jama'a. Ka kawo su rumfa ta taruwa su tsaya nan tare da kai. 17 Zan sauko in yi magana da su a can. Zan ɗauka daga Ruhun da yake a kanka in sashi a kansu. Za su ɗauki nawayar mutanen tare da kai. Ba za kayi ta fama da su kai kaɗai ba. 18 Ka ce da mutanen, 'Ku tsarkake kanku, gama gobe za ku ci nama sosai, gama kun yi kuka kuma Yahweh ya ji. Kun ce, "Wane ne zai ba mu nama mu ci? Gama dã abincinmu ne a Masar." Yahweh zai ba ku nama, kuma za ku ci shi. 19 Ba wai zaku ci nama yini ɗaya ko biyu ko biyar ko goma ko ma ashirin ba, 20 amma zaku yi wata guda kuna cin nama har sai ya fito maku a ƙofar hancinku. Sai ya ginshe ku, gama kun ƙi Yahweh, wanda ke cikin ku. Kun yi kuka a gabansa. Kun ce, "Meyasa muka baro Masar""' 21 Sa'an nan Musa yace, "Mutane 600,000 ne ke tare dani, kuma ka ce, 'Zan ba su nama su yi ta ci har wata guda ɗungum.' 22 Garkunan shanu dana tumaki za a yanka har ya ƙosar da su?" 23 Sai Yahweh yace da Musa, "Hannuna ya kasa ne? Yanzu zaka gani ko maganata gaskiya ce ko a'a." 24 Musa ya fita ya faɗawa mutanen maganar Yahweh. Ya tattara dattawan su saba'in ya sa suka kewaye rumfar. 25 Yahweh ya zo cikin girgije ya yi magana da Musa. Yahweh ya ɗauka daga cikin Ruhun da yake kan Musa ya sa a kan dattawan su saba'in. Sa'ad da Ruhun ya sauko a kansu, sai suka yi anabci, amma a wannan lokacin ne kaɗai ba su ƙara yi ba kuma. 26 Sai mutane biyu suka rage a zangon, su ne Eldad da Medad. Su ma Ruhun ya sauko a kansu. An rubuta sunayensu, amma basu fita sun je rumfa ta taruwa ba. Duk da haka, sun yi anabci a cikin zangon. 27 Wani saurayi ya ruga daga cikin zangon ya gaya wa Musa cewa, Ga Eldad da Medad suna yin anabci a cikin zango." 28 Sai ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun mutanensa Yoshuwa mataimakin Musa, ya ce da Musa, "Shugabana Musa, ka hana su." 29 Musa yace da shi, "Kana jin kishi saboda ni ne? So na ne dukkan mutanen Yahweh su zama annabawa ya kuma sawa dukkan su Ruhunsa!" 30 Daga nan sai Musa da dattawan Isra'ila suka koma cikin zango. 31 Daga nan sai iska ta taso daga wurin Yahweh ta kawo makware daga teku. Suka faɗo kusa da zangon, misalin kusan tafiyar yini ɗaya a wannan sashi, haka kuma a ɗaya sashin. Makwaren suka kewaye zangon wajen kamu ɗaya daga bisa suka kere ƙasa. 32 Mutanen suka yi ta tara makware a wannan yini dukka da wannan daren dukka da kuma washe gari dukka. Kowanne mutum ya kama makware da yawan gaske. Suka raba makwaren cikin zangon dukka. 33 Sa'anda naman ke tsakankanin haƙoransu, suna tauna shi, Sai Yahweh ya yi fushi da su. Ya sa wani ciwo mai zafi ya auko masu. 34 Aka kira sunan wannan wurin Kibrot Hattãba, saboda sun rufe mutanen da suka yi zarin cin nama. 35 Daga Kibrot Hattãba mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, suka tsaya a can.

Sura 12

1 Sai ya zama Miriyam da Haruna suka yi gunaguni a kan Musa saboda wata mace Bakushiya da ya aura. 2 Suka ce, "Kai kaɗai ne Yahweh ya yi magana da kai? Mu ma bai yi magana da mu ba ne?" Sai Yahweh ya ji abin da suka ce. 3 Musa kuwa mutum ne mai tawali'u, fiye da kowa a duniya. 4 Nan take Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna da Miriyam: "Ku uku ɗin, ku fito, ku zo rumfa ta taruwa." Sai su uku ɗin suka fito suka je. 5 Sa'an nan Yahweh ya sauko ta cikin umudin girgije. Ya tsaya a ƙofar rumfa ta taruwa ya kira Haruna da Miriyam. Sai suka matso. 6 Sai Yahweh yace, "Sa'ad da annabina ke tare da ku, zan bayyana kaina a wurinsa ta wurin ruya in yi magana da shi cikin mafarkai. 7 Bawana Musa ba haka yake ba. Shi mai aminci ne a cikin dukkan gidana. 8 Na kan yi magana da shi kai tsaye, ba a zaurance ko da ruya ba. Ya kan ga zatina. Me yasa ba ku ji tsoron yin gunaguni a kan bawana Musa ba?" 9 Fushin Yahweh ya yi ƙuna a kansu, kana ya bar su. 10 Girgijen ya tashi daga bisa rumfar, nan da nan Miriyam ta zama kuturwa--ta yi fari kamar auduga. Da Haruna ya juya sai ya ga Miriyam ta zama kuturwa. 11 Sai Haruna yace da Musa, "Ya shugabana, idan ka yarda kada ka riƙe mu a kan wannan abu. Mun yi magana cikin wawanci, kuma mun yi zunubi. 12 Idan ka yarda kada ka barta ta zama kamar jaririn da naman jikinsa ya lalace sa'ad da yake fitowa daga cikin mahaifar uwarsa." 13 Sai Musa ya yi kira zuwa ga Yahweh. Ya ce, "Idan ka yarda ka warkar da ita, Ya Allah, idan ka yarda." 14 Sai Yahweh yace da Musa, "Idan ubanta ya tofa mata yau a fuska, za a ƙasƙantar da ita har kwana bakwai. Ka rufe ta a bayan zango har kwana bakwai. Bayan haka sai ka dawo da ita." 15 Haka aka rufe Miriyam har kwana bakwai a bayan zango. Mutanen ba su tafi ba sai da ta dawo zangon. 16 Bayan haka, mutanen suka tafi daga Hazerot suka yi zango a cikin jejin Faran.

Sura 13

1 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Ka aiki waɗansu mutane su dubo ƙasar Kan'ana, wadda na ba mutanen Isra'ila. Ka aiki mutum ɗaya daga kowacce kabila ta ubanninsu. Kowanne ya zama shugaba ne a cikinsu." 3 Musa ya aike su daga jejin Faran, domin su yi biyayya da ummarnin Yahweh. Dukkan su shugabanni ne a cikin mutanen Isra'ila. 4 Ga sunayensu: daga kabilar Ruben, Shammuya ɗan Zakkur; 5 daga kabilar Simiyon kuma, Shafat ɗan Hori; 6 daga kabilar Yahuda, kuma Kaleb ɗan Yefunne; 7 daga kabilar Issakar kuma, Igal ɗan Yosef; 8 daga kabilar Ifraim kuma, Hosheya ɗan Nun; 9 daga kabilar Benyamin kuma, Falti ɗan Rafu; 10 daga kabilar Zebulun kuma, Gaddiyel ɗan Sodi; 11 daga kabilar Yosef kuma, (wato daga kabilar Manasse), Gaddi ɗan Susi; 12 daga kabilar Dan kuma, Ammiyel ɗan Gemalli; 13 daga kabilar Asha kuma, Shetur ɗan Mikayel; 14 daga kabilar Naftali kuma, Nãbi ɗan Bofsi; 15 daga kabilar Gad kuma, Gewuyel ɗan Maki. 16 Waɗannan su ne sunyen mazajen da Musa ya aika su dubo ƙasar. Musa ya kira Hosheya ɗan Nun da suna Yoshuwa. 17 Musa ya aike su domin su dubo ƙasar Kan'ana. Ya ce da su, "Ku bi ta Negeb ku hau ta ƙasar kan tudu. 18 Ku dubo ƙasar ku ga yadda ta ke. Ku yi la'akari da irin mutanen da suke zauna a can, ko suna da ƙarfi ko kuwa raunana ne, kuma ko suna da yawa ko 'yan kaɗan ne. 19 Ku ga yadda ƙasar ta ke inda suke zaune. Ta na da kyau ko ba ta da kyau? Yaya biranen suke? Kamar zango--zango suke, ko kuwa ƙayatattun birane ne? 20 Ku gano yadda ƙasar ta ke, ko shuka za ta iya yin girma da kyau ko babu, ko akwai itatuwa ko babu. Ku yi ƙarfin hali ku kawo abin misali daga irin amfanin ƙasar." Lokacin kuwa na nunar fari na inabi ne. 21 Sai mazajen suka je suka duba ƙasar tun daga jejin Zin zuwa Rehob, kusa da Lebo Hamat. 22 Suka hau ta Negeb suka ɓullo Hebron. Ahiman da Sheshayi da Talmai, waɗanda jinsinsu ya fito daga Anak, suna nan. Ya zama an gina Hebron shekaru bakwai kafin Zowan ta cikin Masar. 23 Sa'ad da suka kawo kwarin Eshkol, suka yanki reshe da kurshen zaitun. Suka sagalo shi a jikin sanda tsakanin ƙungiyoyinsu biyu. Suka kawo rumman da ɓaure kuma. 24 Wannan wurin a ka kira da suna kwarin Eshkol, saboda kurshen zaitun da mutanen Isra'ila suka yanko daga can. 25 Bayan kwana arba'in, suka dawo daga dubo ƙasar. 26 Suka dawo wurin Musa da Haruna da dukkan taron jama'ar Isra'ila a cikin jejin Faran a Kadesh. Suka kawo masu labari tare da dukkan jama'a, suka nuna masu irin amfanin ƙasar. 27 Suka ce da Musa, "Mun kai ƙasar daka aike mu. Gaskiya ne tana zubo da madara da zuma. Ga irin amfanin wurin. 28 Duk da haka, mutanen da suka yi gidajensu a can ƙarfafa ne. Biranen ƙayatattu ne manya ne kuma. Mun kuma ga kabilar Anak a can. 29 Amelekawa na zaune a Negeb. Hitiyawa da Yebusawa da Amoriyawa na da gidajensu a ƙasar kan tudu. Kan'aniyawa na zama a bakin teku kusa da Kogin Yodan." 30 Kaleb ya sa mutanen suka yi shiru a gaban Musa yace, '"Bari mu je mu karɓe ƙasar, gama ba shakka za mu iya cin nasara da ita." 31 Amma mazajen da suka je tare da shi suka ce, "Ba za mu iya kai wa mutanen nan hari ba domin sun fi mu ƙarfi." 32 Sai suka kai rahoton karya gwiwa ga mutanen Israila game da ƙasar da suka je suka dubo. Suka ce, "Ƙasar da muka je muka dubo cinye mazauna ƙasar su ke yi. Dukkan mazajen da muka gano a can dogaye ne ƙwarai. 33 Mun gano jarumawa a can, zuriyar Anak, waɗanda dama jarumawa ne. Idan a ka kwatanta mu da su, mu kamar fara mu ke, haka kuma suka gan mu."

Sura 14

1 A wannan daren al'ummar dukka ta yi kuka da ƙarfi. 2 Dukkan mutanen suka ba Musa da Haruna laifi. Dukkan al'ummar suka ce da su, "Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko nan cikin jeji! 3 Meyasa Yahweh ya kawo mu wannan ƙasar mu mutu ta wurin takobi? Matayenmu da ƙanananmu za su cutu. Ba zai fi kyau a gare mu mu koma Masar ba?" 4 Suka cewa junansu, "Bari mu zaɓi wani shugaba, mu koma Masar." 5 Sai Musa da Haruna suka kwanta a gaban taron mutanen Isra'ila da fuskokinsu a ƙasa. 6 Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne, waɗanda ke cikin waɗanda aka aika dubo ƙasar, suka tsage tufafinsu. 7 Suka yi magana da al'ummar mutanen Isra'ila. Suka ce, "Ƙasar da muka ratsa muka dubo muka wuce, ƙasa ce mai kyau ƙwarai. 8 Idan Yahweh ya ji daɗin mu, zai kai mu cikin wannan ƙasa ya ba mu ita. Ƙasar tana zubowa da madara da zuma. 9 Amma kada ku bijire wa Yahweh, kuma kada ku ji tsoron mutanen ƙasar, gama su gurasa ne a gare mu. Tsaronsu zai rabu da su, saboda Yahweh na tare da mu. Kada ku ji tsoron su." 10 Sai dukkan taron suka ce a jejjefe su da duwatsu. Amma sai ga darajar Yahweh ta bayyana ga dukkan mutanen Isra'ila a rumfar taruwa. 11 Yahweh yace da Musa, "Har yaushe waɗannan mutane za su rena ni? Har yaushe za su kasa gaskatawa dani, su rena dukkan alamu da ikon dana yi a cikin su? 12 Zan sa annoba ta auko masu, ba za su zama gãdona ba kuma, in sa kabilarka ta zama babbar al'ummar da za ta fi su girma." 13 Musa yace da Yahweh, "Idan ka yi haka Masarawa za su ji labari, saboda ka kuɓutar da waɗannan mutane da ikonka daga wurinsu. 14 Za su gaya wa mazaunan wannan ƙasar. Sun ji labarinka, Yahweh, kana tare da waɗannan mutane ne saboda ana ganin ka fuska da fuska. Girgijenka yana tsayawa a bisa mutanenka. Kana tafiya a gabansu da umudin girgije da rana da dare kuwa da umudi na wuta. 15 Yanzu idan ka kashe mutanen nan kamar mutum ɗaya, sa'an nan al'umman da suka ji labarin jaruntakarka zasu ce, 16 'Saboda Yahweh ya kăsă kai mutanen nan ƙasar da ya rantse zai ba su, sai ya kashe su a cikin jeji.' 17 Ina roƙon ka, ka yi amfani da ikonka mai girma. Gama ka ce, 18 'Yahweh mai jinkirin fushi ne kuma mai yalwar jinƙai. Yakan gafarta mugunta da laifofi. Ba zai yafe mugunta ba sa'ad da ya kawo horon zunubin kakanni a kan zuriyarsu, har zuwa zuriya ta uku da ta huɗu.' 19 Ka yafe, zunubin mutanen nan, ina roƙon ka, saboda alƙawarin jinƙanka mai girma, kamar yadda kake ta gafarta wa mutanen nan tun daga cikin Masar har zuwa yanzu." 20 Sai Yahweh yace, "Na yafe masu saboda roƙonka, 21 amma gaskiya, kamar yadda nake a raye, dukkan duniya zata cika da ɗaukakata, 22 dukkan mutanen nan da suka ga ɗaukakata da alamu na ikon da na yi a cikin Masar da cikin jeji--har yanzu suna jarabta ta sau goma kenan ba su saurari muryata ba. 23 Babu shakka ba za su ga wannan ƙasar da nayi wa ubanninsu alƙawari ba. Waɗannan da suka rena ni ba ko ɗaya a cikin su da zai gan ta, 24 sai bawana Kaleb kaɗai, saboda da ruhunsa daban yake. Ya bini da gaske; zan kai shi ƙasar da ya je ya dubo. Zuriyarsa zasu gaje ta. 25 (To Amelikawa da Kan'aniyawa suna zaune a cikin kwari.) Gobe ka juya ka tafi jejin ka bi ta Teku na Iwa." 26 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce, 27 "Har yaushe zan jure da muguntar mutanen nan da suke ta ganin laifina? Na ji gunagunin mutanen Isra'ila game da ni. 28 Ka ce da su, 'Yahweh yace, 'kamar yadda nike a raye, 'kamar yadda kuka yi magana ina ji, ga abin da zan yi ma ku: 29 Dukkan ku da kuka yi gunaguni a kaina zaku mutu a cikin jeji, ku da aka ƙirga cikin lissafi, dukkan ma su shekara ashirin zuwa gaba. 30 Babu shakka ba zaku shiga ƙasar dana yi alƙawari zan yi maku gida ba. Sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun. 31 Amma ƙanananku da kuka ce abin zai shafe su, su zan kai cikin ƙasar. Za su ji yadda ƙasar da kuka ƙi ta ke! 32 Ku kuwa jikkunanku za su faɗi su mutu a cikin jeji. 33 'Ya'yanku za su zama makiyaya a cikin jeji har shekara arba'in. Dole ne za su sha sakamakon aikinku na bijirewa a cikin jeji har sai gawarwakinku sun ƙare. 34 Kamar yadda kuka yi kwana arba'in kuna dubo ƙasar, Haka zaku yi shekara arba'in kuna ɗaukar alhakin zunubanku-- kowanne kwana ɗaya a matsayin shekara ɗaya, zaku gane abin da zai faru da ku idan na yi găba da ku. 35 Ni, Yahweh ne na faɗa. Babu shakka haka zan yi wa wannan al'umma mai mugunta da suka haɗa kai gãba dani. Za a datse su gaba ɗaya, a nan za su mutu." 36 Haka mazajen da Musa ya aika su gewayo ƙasar, waɗanda suka dawo suka kawo rahoton da ya sa dukkan taron jama'a suka yi gunaguni a kan Musa game da ƙasar-- 37 Waɗan nan mazaje da suka kawo rahoto marar daɗi aka hallaka su da annoba daga wurin Yahweh suka mutu. 38 A cikin mazajen da suka gewaya ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne ne kaɗai suka rage da rai. 39 Sa'ad da Musa ya bada wannan rahota ga mutanen Isra'ila dukka, sai suka yi baƙinciki ƙwarai. 40 Suka fita tun da sassafe suka hau bisa kan tsauni suka ce, "Dubã, ga mu nan, kuma za mu tafi wurin da Yahweh ya yi alƙawari, gama mun yi zunubi." 41 Amma Musa yace, "Meyasa kuke wulakanta ummarnin Yahweh? Ba za ku yi nasara ba. 42 Kada ku tafi, saboda Yahweh ba ya tare da ku, domin ya kare ku, don kada abokan gãbarku su yi nasara a kanku ba. 43 Su Amelekawa da Kan'aniyawa suna can, kun zo ku mutu da kaifin takobi saboda kun dena bin Yahweh. Saboda haka ba zai kasance tare da ku ba." 44 Amma sai suka yi taurin kai suka tafi ƙasar kan tudu; amma kuma, ko Musa ko akwatin alƙawarin Yahweh ba wanda ya bar zangon. 45 Sai Amelekawa suka sauko, Kan'aniyawa ma suka sauko daga tuddai. Suka kai hari a kan Isra'ilawa suka kuma ci nasara a kansu har zuwa Horma.

Sura 15

1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Kayi magana da mutanen Isra'ila ka ce dasu, 'Sa'ad da kuka shiga ƙasar da zaku zauna, wadda Yahweh zai ba ku, 3 sai ku shirya baiko da wuta domin Yahweh, ko baiko na ƙonawa ko hadaya domin a cika alƙawarin baiko na yardar rai, ko baiko na idodinku, domin ku kawowa Yahweh baiko na ƙamshi mai daɗi daga garkenku ko daga dangwalinku. 4 Dole ku kawo wa Yahweh baiko na ƙonawa da baiko na gari da hadaya ta sha ta gari mai kyau wanda aka gauraya da mai kwalba bakwai. 5 Kuma za ku haɗa baiko na ƙonawar ko hadayar da ruwan inabi saboda sha domin kowanne ɗan rago. 6 Idan rago ne ake miƙawa, sai kuma a shirya baiko na gari awo uku wanda aka gauraya da mai kwalba biyar. 7 Domin baiko na sha kuwa sai a bada ruwan inabi kwalba biyar. Zai bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. 8 Idan kuka shiya bijimi domin baiko na ƙonawa ko hadaya domin ku cika alƙawari, ko baiko na zumunci ga Yahweh, 9 sai ku miƙa bijimin tare da baiko na hatsi, gari mai kyau awo uku wanda aka gauraya da mai kwalba biyu. 10 Dole kuma ku ba da baiko na ruwan inabi kwalba biyu, baikon da aka yi da wuta, da zai bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. 11 Haka za ayi wa kowanne bijimi da kowanne rago da kowanne ɗan rago da 'yan awaki. 12 Kowacce hadaya za ku shirya ku miƙa haka za ku yi ta kamar yadda aka bayyana a nan. 13 Dukkan 'yan ƙasa da aka haifa a Isra'ila haka za su yi waɗannan abubuwa, sa'adda wani ya kawo baikon da za ayi da wuta, domin ya kawo ƙanshin da zai gamshi Yahweh. 14 Idan baƙo na zaune wurinku, ko duk wanda zai zauna a cikin ku a dukkan zamanin mutanenku, dole ne ya yi baikon da za ayi da wuta domin ya bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. Dole ne shi ma ya yi kamar yadda kuke yi. 15 Dokar da ta shafi taron jama'arku ita ce za ta shafi baƙon da yake zaune a wurinku, wannan zaunanniyar doka ce gare ku dukkan zamanin jama'arku. Kamar yadda kuke haka ma wanda ya zo wurin ku zai zama. Dole ne ya yi kamar yadda kuke yi a gaban Yahweh. 16 Doka da ka'idar da ta shafe ku ita ce kuma za ta shafi baƙon da yake tare da ku.'" 17 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce, 18 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce da su, 'Idan kuka zo ƙasar da zan kai ku, 19 idan kuka ci abincin da aka yi a ƙasar, sai ku yi baiko ku miƙa shi gare ni. 20 Cikin abin da za ku fara ɓarzawa sai ku yi dunƙule da shi ku ɗaga shi kamar baiko na ɗagawa a masussuka. Ga yadda za ku ɗaga shi. 21 Daga abin da kuka ɓarza da fari sai ku yi bayarwa ta ɗagawa a dukkan zamanin mutanenku. 22 Wani lokaci za ku yi zunubi ba tare da saninku ba, idan ba ku yi biyayya da dukkan umarnin dana gaya wa Musa ba-- 23 dukkan abin dana umarce ku ta wurin Musa tun daga ranar dana fara baku umarni har zuwa zamanin mutanenku dukka. 24 A lamarin zunubin da aka yi ba tare da niyya ba kuma jama'a ba su sani ba, sai dukkan jama'a kowa ya yi baiko na ƙonawa da bijimi domin ya bada shessheƙi na ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. Tare da wannan sai a yi baiko na hatsi dana sha, kamar yadda aka umarta a ka'idodi, da baiko na ɗan akuya ɗaya domin baiko na zunubi. 25 Sai firist ya yi kafara domin dukkan taron jama'ar Isra'ila. Za a gafarta masu saboda zunubin kuskure ne. Sun kawo hadayarsu, baikon da aka yi da wuta zuwa gare ni. Sun kawo baiko na zunubi gare ni gama kuskure ne. 26 Sa'an nan za a gafartawa dukkan taron jama'ar Isra'ila, da dukkan baƙin da suke zaune tare da su, saboda dukkan taron jama'ar sun yi zunubin ba tare da sanin su ba, 27 Idan wani mutum ya yi zunubi cikin rashin sani, sai ya miƙa baiko na ɗan akuya bana ɗaya saboda zunubinsa. 28 Sai firist ya yi kafara a gaban Yahweh saboda mutumin da ya yi zunubi ba tare da saninsa ba. Idan aka yi kafara za a gafarta wa wannan mutum. 29 Sai ku kasance da doka iri ɗaya ga duk wanda ya yi wani abu ba tare da saninsa ba. Doka ɗaya da ta shafi ɗan ƙasa da aka haifa a Isar'ila ita ce kuma za ta shafi baƙin dake zaune a cikin su. 30 Amma idan mutum ya yi ba dai--dai ba cikin sanin sa, ko ɗan ƙasa ne ko baƙo, ya yi mani zunubi. Wannan mutum za a datse shi daga cikin mutanensa. 31 Saboda ya rena maganata ya karya dokokina, wannan mutum za a datse shi sarai. Zunubinsa zai zauna a kansa. 32 Sa'ad da mutanen Isra'ila ke a cikin jeji, sai suka tarar da wani mutum na tattara itace ranar Asabaci. 33 Waɗanda suka tarar da shi suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukkan taron jama'ar Isra'ila. 34 Sai suka sa shi a cikin kurkuku saboda ba a yanke abin da za a yi masa ba. 35 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Sai a kashe wannan mutum. A kai shi bayan zango, dukkan jama'a su jejjefe shi da duwatsu. 36 Haka dukkan jama'ar suka kawo shi bayan zango suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 37 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce, 38 "Kayi magana da 'ya'yan Isra'ila ka umarce su da su yi tutoci su maƙala a kafaɗun rigunansu, su maƙala su a kowacce kafaɗa da shuɗin zare. Za su yi haka a dukkan zamanin mutanensu. 39 Idan kuka dube su za su zama abin tunawa da dukkan dokokina na musamman a gare ku. Ku ɗauke su a wurinku domin kada ku dubi zuciyarku da idanunku ku yi karuwanci da su. 40 Ku yi wannan domin ku tuna ku yi biyayya da dukkan dokokina, kuma domin ku zama da tsarki, keɓaɓɓu domina Allahnku. 41 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, ya zama Allahnku. Ni ne Yahweh Allahnku."

Sura 16

1 Ana nan sai Korah ɗan Izhar ɗan Kohat ɗan Lawi, tare da Datan da Abiram 'ya'yan Eliyab da On ɗan Felet, zuriyar Ruben, suka taru da waɗansu mutane. 2 Suka tayar wa Musa, tare da waɗansu daga cikin mutanen Isra'ila, su ɗari biyu da hamsin shugabannin jama'a sanannu sosai a cikin jama'a. 3 Suka tattaro kansu domin su fuskanci Musa da Haruna. Suka ce da su, "Fankamarku ta yi yawa! Dukkan mutanen keɓaɓɓu ne, kowanne ɗayan su, kuma Yahweh na tare da su. Meyasa kuke ɗaukaka kanku fiye da sauran mutanen Yahweh?" 4 Sa'ad da Musa ya ji haka, sai ya kwanta da fuskarsa ƙasa. 5 Ya yi magana da Korah da dukkan waɗanda ke tare da shi, "Gobe da safe Yahweh zai nuna wanda ke nasa, da wanda ya keɓe domin kansa. Zai kawo wannan mutum kusa da shi. Zai kawo wanda ya zaɓa kusa da shi. 6 Korah, kai da ƙungiyarka ga abin da za ku yi. 7 Gobe ku ɗauki turare ku sa wuta a gaban Yahweh. Wanda Yahweh ya zaɓa, zai zama keɓaɓɓe na Yahweh. Fankamarku ta yi yawa, ku 'ya'yan Lebi." 8 Musa ya ƙara cewa da Korah, "Ka saurara, kai zuriyar Lebi: 9 ƙaramin abu ne a wurin ka da Allah na Isra'ila ya keɓe ka daga cikin mutanen Isra'ila, ya kawo ka kusa da shi, domin ka yi aiki cikin alfarwar Yahweh, kuma ka tsaya a gaban jama'a ka yi masu hidima? 10 Ya kawo ku kusa da dukkan 'ya'uwanka, zuriyar Lebi, tare da kai, kuma kana nema ka zama firist! 11 Wannan ne yasa kai da ƙungiyarka kuka taru ku yiwa Yahweh tayarwa. Meyasa kake gunaguni a kan Haruna, wanda ya yi biyayya da Yahweh?" 12 Sai Musa ya kira Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, "Ba za mu hawo ba. 13 Ƙaramin abu kayi daka fito da mu daga ƙasa mai zubo da madara da zuma, ka kashe mu a cikin jeji? Yanzu kana so ka maida kanka mai mulki a kan mu! 14 Bugu da ƙari, baka kai mu ƙasar dake zubowa da madara da zuma ba, ko ka bamu gonaki da lambuna su zama gadonmu. Yanzu kana so ka makantar da mu da alƙawuran wofi? Ba zamu zo wurin ka ba." 15 Musa ya yi fushi ƙwarai ya ce da Yahweh, "Kada ka karɓi baikonsu. Ban ɗauki ko jaki ɗaya daga wurin su ba, kuma ban ji wa ko ɗaya a cikin su ba. 16 Sa'an nan Musa yace da Korah, "Gobe kai da mutanenka za ku je gaban Yahweh--kai da su, da Haruna. 17 Kowannen ku ya ɗauki tasa ya sa turare a ciki. Kuma dole kowanne mutum ya kawo tasarsa gaban Yahweh, tasoshi ɗari biyu da hamsin. Kai da Haruna kuma kowa ya kawo tasarsa," 18 Sai kowanne mutum ya ɗauki tasarsa, yasa wuta a ciki, yasa turare a cikin ta, suka tsaitsaya a ƙofar rumfa ta taruwa tare da Musa da Haruna. 19 Sai Korah kuma ya tattara dukkan mutanen da suke tayarwa Musa da Haruna a ƙofar rumfa ta taruwa, sai ɗaukakar Yahweh ta bayyana ga dukkan jama'a. 20 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna: 21 "Ku ware kanku daga cikin wannan taron domin in hallaka su yanzun nan." 22 Musa da Haruna suka kwanta da fuskokinsu a ƙasa suka ce, "Ya Allah, Allah na ruhohin dukkan mutane, idan mutum ɗaya ya yi zunubi, ka yi fushi da dukkan mutane?" 23 Yahweh ya amsa wa Musa. Ya ce, 24 "Ka faɗawa taron jama'ar. Ka ce, 'Ku gudu daga rumfar Kora da Datan da Abiram."' 25 Sai Musa ya tashi ya je wurin Datan da Abiram; dattawan Isra'ila suka bi shi. 26 Ya yi magana da taron ya ce, "Sai ku gudu daga rumfunan waɗannan mugayen mutane kada ku taɓa kome nasu."Idan ba haka ba zunubinsu zai cinye ku dukka." 27 Haka jama'ar dake cikin rumfunan su Korah da Datan da Abiram suka rabu da su. Datan da Abiram suka fito suka tsaya a ƙofar rumfunansu, tare da matansu da 'ya'yansu da ƙananansu. 28 Sa'an nan Musa yace, "Ta wurin wannan za ku sani Yahweh ne ya aiko ni in yi dukkan waɗannan ayyuka, gama ba domin kaina nake yin su ba. 29 Idan mutanen nan suka yi mutuwa irin ta kowanne mutum, kamar yadda abu yakan sami kowanne mutum, ba Yahweh ne ya aiko ni ba. 30 Amma idan Yahweh ya halitto wani sabon abu, idan ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su, tare da dukkan abin da suke da shi, suka tafi cikin lahira da rai, sa'an nan za ku gane waɗannan mutane sun rena Yahweh." 31 Da dai Musa ya gama faɗin wannan magana, ƙasa ta buɗe a ƙarƙashin waɗannan mutane. 32 Ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su, da iyalinsu da dukkan jama'ar dake na Korah, tare da dukkan abin da suka mallaka. 33 Haka su da dukkan abin da suka mallaka suka tafi lahira da ransu. Ƙasa ta rufe a kan su, suka lalace daga wurin taron jama'a. 34 Dukkan mutanen Isra'ila dake kewaye da su suka gudu daga biranensu. Suka yi kururuwa, watakila mu ma ƙasa za ta haɗiye mu!" 35 Sa'an nan wuta ta walƙato daga wurin Yahweh ta haɗiye mutane 250 da suka miƙa turare. 36 Yahweh ya ƙara yin magana da Musa ya ce, 37 Ka yi magana da Eliyeza ɗan Haruna firist bari ya ɗauke tasoshin daga cikin wuta, gama tasoshin keɓaɓɓu ne a gare ni. Sa'an nan ya barbaza garwashin daga nesa. 38 Ɗauke tasoshin waɗanda suka rasa rayukansu saboda zunubinsu. A bubbuge su su zama marfin bagadinsu. Waɗancan mutanen sun miƙa su a gabana, don haka sun zama keɓaɓɓu a gare ni. Za su zama alamar kasancewata ga mutanen Isra'ila." 39 Sai Eliyeza firist ya ɗauki tasoshi na tagulla da mutanen da suka ƙone suka yi amfani da su, aka bubbuga su, suka zama marfin bagadin, 40 domin su zama abin tunawa ga mutanen Isra'ila, domin ya zama ba wani baƙo wanda ba a cikin kabilar Haruna yake ba da zai zo ya ƙona turure a gaban Yahweh, domin kada su zama kamar Korah da ƙungiyarsa--kamar yadda Yahweh ya bada umarni ta wurin Musa. 41 Amma da safiya ta yi sai dukkan taron jama'ar suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna. Suka ce, "Kun kashe mutanen Yahweh." 42 Sai ya zama, sa'ad da mutanen suka taru gãba da Musa da Haruna, da suka duba wajen rumfa ta taruwa, duba sai gashi girgije ya rufe ta. Darajar Yahweh ta bayyana, 43 sai Musa da Haruna suka zo gaban rumfar ta taruwa. 44 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 45 "Ka gudu daga gaban wannan taron domin in hallaka su yanzu--yanzu." Sai Musa da Haruna suka kwanta da fuskokinsu a ƙasa. 46 Musa yace da Haruna, "Ka ɗauki tasa, ka sa wuta a ciki ba a kan bagadin ba, ka sa turare a cikin ta, ka kai ta wurin taron jama'ar, da sauri ka yi kafara saboda su, saboda fushi na zuwa daga wurin Yahweh. Annobar ta fara." 47 Sai Haruna ya yi kamar yadda Musa ya ummurce shi. Ya ruga cikin tsakiyar taron jama'ar. Annobar ta fara bazuwa a cikin mutanen, sai ya sa turaren a ciki ya yi kafara saboda mutanen. 48 Haruna ya tsaya a tsakanin matattu da masu rai; ta haka annobar ta tsaya. 49 Waɗanda annobar ta kashe sun kai 14,700, ban da waɗanda suka mutu cikin lamarin Korah. 50 Haruna ya dawo wurin Musa a ƙofar rumfa ta taruwa, sai annobar ta ƙare.

Sura 17

1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce, 2 "Faɗa wa mutanen Isra'ila, su ɗauki sanduna daga gare su, kowanne ɗaya domin kabilar kakanni, sanduna goma sha biyu. Rubuta sunan kowanne mutum a kan sandarsa. 3 Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lebi. A kan kowacce sanda domin shugaban kabilar kowanne kakanninsa. 4 Ka ajiye sandunan a cikin alfarwar taro a gaban ka'idodi alƙawari, wurin da nakan sadu da kai. 5 Zai zamana sandan mutumin dana zaɓa za ta yi toho. Zan sa ƙorafe-ƙorafe daga mutanen Isra'ila ya tsaya, waɗanda suke magana a kanka." 6 Sai Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila. Dukkan shugabannin kabilu suka ba shi sandunan, sanda ɗaya daga kowanne shugaba, da aka zaɓa daga dukkan kabilun kakanin, sanduna goma sha biyu dukka. Sandan Haruna na cikinsu. 7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Yahweh cikin alfarwar ka'idodin alƙawari. 8 Kashegari Musa ya tafi cikin alfarwar ka'dodin alƙawari, sai ga shi, sandar Haruna ta kabilar Lebiyawa ta yi toho. Ta tuko tayi toho ta bada 'ya'yan almon nunannu! 9 Musa kuwa ya fito da dukkan sandunan a gaban Yahweh zuwa ga dukkan mutanen Isra'ila, sai kowanne mutum ya ɗauki sandansa. 10 Yahweh yace da Musa, "Sa sandan Haruna a gaban ka'idodin alƙawari. Ka ajiye ta alama ce a kan mutane waɗanda ke tawaye saboda ka kawo ƙarshen gunaguni a kaina, ko kuwa za su mutu. 11 Musa kuwa ya yi kamar yadda Yahweh ya umarce shi. 12 Mutanen Isra'ila suka yi magana da Musa suka ce, "Za mu mutu a nan. Dukkan mu zamu lalace! Duk wanda ya zo nan, kowa ya kusanci alfarwar Yahweh, zai mutu. 13 Mu dukka za mu lalace?"

Sura 18

1 Yahweh yace da Haruna, "Kai, da 'ya'yanka, da kabilar kakanninka za ku ɗauki hakkin dukkan zunubai da za ayi game da alfarwar sujada. Amma kai da 'ya'yanka ne kaɗai za ku ɗauki hakkin dukkan zunuban da ya shafi kowanne firist. 2 Kuma sauran 'yan'uwan kabilar Lebi, kakanninka, ka kawo su tare da kai saboda su kasance tare da kai don su taimake ka da 'ya'yanka aiki a gaban alfarwa ta ka'idodin alƙawari. 3 Su yi maka dukkan ayyukan alfarwa. Amma ba za su zo su kusanci kowanne abu dake a wuri mai tsarki, ko wani abu da ya shafi bagaɗi ba, ko su da kai dukka ku mutu. 4 Su haɗu da kai, don su lura da alfarwar taruwa, domin dukkan aikace-aikace na alfarwar. Kada wani baƙo ya zo kusa da ku. 5 Ku ɗauki nauyin ayyukan wuri mai tsarki da kuma bagaɗi saboda kada fushina ya zo a kan mutanen Isra'ila kuma. 6 Duba, ni da kaina na zaɓi 'yan 'uwan Lebiyawa daga cikin zuriyar Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, an bani su don su yi aikin lura da alfarwar taro. 7 Amma da kai da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagaɗi da dukkan aiki na bayan labule. Kune da kanku za ku yi waɗannan aikace-aikace. Ina baku aikin firist a matsayin kyauta. Duk wani baƙo wanda ya matso zai mutu." 8 Sai Yahweh ya cewa Haruna, "Duba, na baka aikin, kula da baikon ɗagawa a gare ni, da dukkan baye -baye masu tsarki da mutanen Isra'ila suka bani. Na bada dukkan baye-bayen a gare ka da 'ya'yanka maza har abada. 9 Wannan zai zama rabonka daga abubuwa masu tsarkin gaske da za a ajiye daga wuta. Daga kowanne baiko nasu--kowacce bayarwar hatsi, da kowacce bayarwa don zunubi da bayarwar laifi--za su ajiye su gare ka da 'ya'yanka. 10 Waɗannan baye-baye suna da tsarki sosai, kowanne namiji ya ci shi, domin suna da tsarki a gare ka. 11 Waɗannan su ne baye-bayen da za su zama naka: sun zama da tsarki daga dukkan bayarwar ɗagawa daga mutanen Isra'ila. Na bada su a gare ka da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata, a matsayin naka har abada. Duk wanda yake da tsarki a iyalinka zai iya cin kowanne daga waɗannan baye-bayen. 12 Dukkan mai mai kyau, dukkan sabon ruwan inabi da hatsi da nunar fari masu kyau da mutane suka bada gare ni--dukkan waɗannan abubuwa na bada su a gare ka. 13 Nunan fari na dukkan amfanin gonarsu, wanda suke kawo wa gare ni, za su zama naka. Duk wanda yake da tsarki a iyalinka zai iya cin waɗannan abubuwa. 14 Iyakar abin da aka keɓe a Isra'ila zai zama naka. 15 Dukkan abin da aka haifa, dukkan nunar fari wadda jama'a suka bayar ga Yahweh, mutum ko dabba, zai zama naka. Duk da haka, mutane dole su fanshi kowanne haihuwar fari na mutum, su kuma fanshi ɗan fari na dabba namiji da ba shi da tsarki. 16 Waɗanda mutane za su fansa dole sai sun kai wata ɗaya da haihuwa. Sa'an nan mutane zasu iya fansar su, gama kuɗinsu shekel biyar ne bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi na shekel, wanda ya ke dai dai da awo ashirin na gerah. 17 Amma haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya ko ta akuya--ba za ka fanshi waɗannan dabbobi ba; keɓaɓɓu ne a gare ni. Sai ka yayyafa jininsu a kan bagaɗi, ka ƙona kitsensu a matsayin baiko na ƙonawa, abin ƙanshi mai gamsarwa ga Yahweh. 18 Namansu zai zama naka. Kamar ƙirjin da aka ɗaga da cinyar dama, namansu zai zama naka. 19 Dukkan baye--baye masu tsarki da mutanen Isra'ila suka bayar ga Yahweh, na bada su gare ka da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata tare da kai, yadda za ku ci gaba da samun rabo ke nan. Wannan alƙawarin gishiri mara ƙarewa ne, alƙawarin yana nan har abada, a gaban Yahweh domin ka da zuriyarka. 20 Yahweh yace da Haruna, "Ba za ka sami gãdo a cikin ƙasar mutane ba, ko ka sami rabon kaya a cikin mutane. Ni ne rabonka da gãdonka a cikin mutanen Isra'ila. 21 Duba, ga zuriyar Lebi, na ba su dukkan zakar Isra'ila a matsayin gãdonsu saboda hidimar da suke yi a cikin rumfa ta taruwa. 22 Daga yanzu mutanen Isra'ila za su zo kusa da rumfa ta taruwa, ko su ɗauki alhakin wannan zunubi, su mutu. 23 Lebiyawa ne za su yi aikin da ya shafi rumfa ta taruwa. Za su ɗauki alhakin kowane zunubi dangane da shi. Wannan zai zama doka ta din-din-din a dukkan zamanan mutanenka. A cikin mutanen Isra'ila ba za su sami gãdo ba. 24 Gama zakkar mutanen Isra'ila, wadda za su miƙa a matsayin gudummuwarsu gare ni-- waɗannan ne na bayar ga Lebiyawa a matsayin gãdonsu. Wannan shi yasa na ce da su, 'Baza su sami gãdo ba a cikin mutanen Isra'ila.'" 25 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 26 "Dole ka yi magana da Lebiyawa ka ce da su, 'Sa'ad da suka karɓi kashi goma daga mutanen Isra'ila wanda na basu gãdo, sai ku bada gudummuwa daga cikin ta ga Yahweh, kashi goma na zakkar. 27 dole ku ɗauke ta kamar kashi goma na hatsinsu ne daga masussuka ko kuma kamar amfani daga wurin matsewar inabinku. 28 Haka kuma dole ku miƙa gudummuwa ga Yahweh daga dukkan zakkar da kuke karɓa daga wurin mutanen Isra'ila. Daga ciki dole za ku bayar da gudummuwa ga Haruna firist. 29 Daga dukkan kyaututtukan da kuke karɓa, dole ku bada kowacce gudummuwa ga Yahweh. Dole ku yi wannan daga dukkan abu mafi kyau mafi tsarki da aka ba ku.' 30 Saboda haka dole ka ce da su, 'Sa'ad da kuka bada mafi kyau daga ciki, sai ya zama na Lebiyawa kamar amfanin da ya fito daga masussuka da wurin matsewar inabi. 31 Za ku iya cin sauran kyaututtukanku a kowanne wuri, ku da iyalinku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a rumfa ta taruwa. 32 Ba kuwa za ta zama maku sanadin laifi ba ta wurin cinta da shanta, in dai har kuka bada ga Yahweh mafi kyau daga cikin abin da ku ka karɓa. Amma ba za ku ɓata tsarkakakken baye-bayen na mutanen Isra'ila ba, ko ku mutu.'"

Sura 19

1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. 2 Ya ce, "Wannan ita ce ka'ida, da doka wadda nake umartar ku: Ka faɗawa mutanen Isra'ila dole su kawo maka jar karsana marar lahani ko wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba. 3 Sai ka ba Eliyeza firist karsanar. Dole ya kawo ta a wajen zango, kuma dole wani zai yanka ta a gabansa. 4 Dole Eliyeza, firist, ya ɗibi jininta da yatsansa ya yayyafa sau bakwai a gaban rumfa ta taruwa. 5 Dole sai wani firist ya ƙone karsanar a idonsa. Dole zai ƙone fatarta da namanta da jinin tare da ƙashinta. 6 Dole firist ya ɗauki itacen al'ul da abin tsaftacewa da mulufi ya jefa su dukka a cikin tsakiyar wutar da take ƙone karsanar. 7 Sa'an nan dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka a cikin ruwa. Sa'an nan zai zo ya shiga zangon, a wurin zai zama da ƙazamta har zuwa maraice. 8 Shi kuwa wanda ya ƙone karsanar zai wanke tufafinsa a cikin ruwa, ya yi wanka a cikin ruwa. Zai zama da ƙazamta har zuwa maraice. 9 Mutumin dake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya sa ta wajen sansani a wuri mai tsabta. Za a adana tokar saboda jama'a mutanen Isra'ila. Za su riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi, tun da yake tokar daga bayarwar zunubi ce. 10 Shi kuwa wanda ya tara tokar karsanar sai ya wanke tufafinsa. Zai zama ƙazantacce har maraice. Wannan doka ce ta har abada domin mutanen Isra'ila da baƙin dake zama tare da su." 11 Duk wanda ya taɓa jikin gawar mutum zai ƙazantu har kwana bakwai. 12 Wannan mutum zai tsarkake kansa a rana ta uku da rana ta bakwai. Sa'an nan zai tsarkaka. Amma in a rana ta uku bai tsarkake kansa ba, ba zai zama da tsarki ba a rana ta bakwai. 13 Duk wanda ya taɓa jikin gawar mutum wanda ya mutu, bai tsarkake kansa ba--wannan mutum zai kazantar da alfarwar Yahweh. Wannan mutum za a yanke shi daga cikin Isra'ila domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba. Zai kasance ƙazantacce; ƙazancewarsa za ta kasance a kansa. 14 Wannan ita ce doka a kan wanda ya rasu a cikin alfarwa. Duk wanda ya shiga alfarwar da wanda ke cikin alfarwar za su ƙazantu har kwana bakwai. 15 Kowanne buɗaɗɗen akwati da ba a rufe ba, zai ƙazantu. 16 Hakanan ma duk wanda ke wajen alfarwar ya taɓa jikin mamacin wanda aka kashe da takobi, ko kowacce gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari--wannan mutumin zai ƙazantu har kwana bakwai. 17 A yi wannan domin mutumin da ya ƙazantu: A ɗibi toka daga cikin bayarwar ƙonawa a haɗa su a cikin tulu tare da sabon ruwa. 18 Duk wanda ke da tsarki zai ɗauki abin tsaftacewar ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar da dukkan kayayyakin dake cikin alfarwar, da mutanen dake a wurin, da wanda ya taɓa ƙashin ko wanda aka kashe ko wanda ya mutu, ko kabari. 19 A kan rana ta uku da ta bakwai kuma wanda yake da tsarki zai yayyafa wa mutum marar tsarkin ruwa. A rana ta bakwai mutum mara tsarki zai tsarkake kansa. Zai wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa. Da maraice kuwa zai tsarkaka. 20 Amma duk wanda ya kasance da rashin tsarki, wanda ya ƙi ya tsarkake kansa--wannan mutum za a datse shi daga jama'a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Yahweh. Kuma ba a yayyafa masa ruwan da ake yayyafa wa marasa tsarki ba. 21 Wannan zai zama doka a gare su a kan abubuwa kamar haka. Wanda ya yayyafa ruwan don tsarkakewa, zai wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan don tsarkakewa zai zama marar tasrki har maraice. 22 Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa, zai ƙazantu. Duk wanda kuma ya taɓa abu marar tsarki, zai ƙazantu har maraice."

Sura 20

1 Sai mutanen Isra'ila da dukkan taron jama'a suka zo jejin Zin a wata na fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta rasu, a nan kuma aka bizne ta. 2 Babu ruwa domin jama'a, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna. 3 Mutane kuwa suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, "Zai fi kyau idan da mun mutu yadda 'yan'uwanmu Israilawa suka mutu a gaban Yahweh! 4 Donme ka fito da taron jama'ar Yahweh a cikin wannan jeji mu mutu a nan, mu da dabobbinmu? 5 Donme kuma ka sa muka fito daga Masar ka kawo mu a wannan mugun wuri? A nan babu hatsi, ko ɓaure ko inabi ko rumman ko ruwan da za a sha." 6 Sai Musa da Haruna suka tafi daga gaban taron. Suka shiga alfarwar taro, suka faɗi rub da ciki. A wurin ɗaukakar Yahweh ta bayyana a gare su. 7 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 8 "ɗauki sandarka ka tara jama'a, kai da Haruna ɗan'uwanka. Yi magana da dutse a gaban idanunsu, ya bada ruwan dake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo daga dutsen domin su, ka bada ruwan ga jama'ar da garkunansu su sha." 9 Musa ya ɗauki sandar daga gaban Yahweh, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi. 10 Sai Musa da Haruna suka tara dukkan jama'ar, a gaban dutsen. Musa yace da su, "Ku saurara yanzu, ku 'yan tawaye. Za mu fito da ruwa daga cikin dutsen nan domin ku? 11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandarsa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Jama'a kuwa suka sha, dabobbi ma suka sha. 12 Sai Yahweh yace da Musa da Haruna, "Tun da yake baku gaskata ni ba, baku kuwa ɗaukaka ni akan ni mai tsarki bane a idon mutanen Isra'ila, to, baza ku kai wannan taron a cikin ƙasar dana ba su ba." 13 Wannan wuri ne aka kira shi ruwan Meriba domin mutanen Isra'ila suka yi wa Yahweh gunaguni a wurin, inda shi kuma ya nuna masu shi kansa mai tsarki ne. 14 Musa ya aika da manzanni daga Kadesh zuwa ga sarkin Idom: Yan'uwanka Israila sun faɗi wannan: "Ka san dukkan wahalun da suka same mu. 15 Ka san yadda kakanninmu suka tafi can Masar, suka zauna a Masar da daɗewa. Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu. 16 Sa'ad da muka yi kira ga Yahweh, ya ji muryarmu, ya aiko da mala'ikansa, ya fishe mu daga Masar. Duba, muna nan a Kadesh, birni dake kan iyakar ƙasarka. 17 Ina roƙonka ka yardar mana mu ratsa ƙasarka. Za mu bi ta cikinta mu wuce gona, ko gonar inabi, ba za mu sha ruwa daga cikin rijiyarka ba. Za mu bi ta gwadaben sarki. Ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka." 18 Amma sarkin Idom ya amsa masa, "Ba za ku ratsa ta nan ba. Idan kuwa kuka yi, zan fita tare da takobi, za mu ci ku da yaƙi." 19 Sai mutanen Isra'ila suka ce da shi, "Za mu bi gwadabe ne kawai. Idan kuwa mu da dabobbinmu mun sha ruwanku, za mu biya. Mu dai, a yardar mana mu wuce a ƙafafunmu, ba tare da yin wani abu ba kuma." 20 Amma sarkin Idom ya sake amsa masu da cewa, "Ba mu yarda ba. "Sai sarkin Idom ya fito gãba da Isra'ila da runduna mai yawa. 21 Sarkin Idom ya ƙi ya bar Isra'ila su ratsa a kan iyakarsu. Domin wannan, Isra'ila suka juya daga ƙasar Idom. 22 Sai mutane suka kama tafiya daga Kadesh. Mutanen Isra'ila da dukkan jama'a suka zo Tsaunin Hor. 23 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna a Tsaunin Hor, a iyakar Idom. Ya ce, 24 "Dole ne Haruna ya tarar da mutanensa, don ba zai shiga ƙasar dana ba mutanen Isra'ila ba. Wannan domin ku biyun kun yi mani tawaye a kan maganata a kan ruwan Meriba. 25 Ka ɗauki Haruna da Eliyeza ɗansa, ka zo da su bisa Tsaunin Hor. 26 Ka ɗauki rigar firistanci ta Haruna, ka sawa ɗansa Eliyeza. Haruna zai mutu, za a tara shi ga mutanensa a can. 27 Musa kuwa ya yi yadda Yahweh ya umarta. Suka hau bisa Tsaunin Hor a idon dukkan jama'a. 28 Musa ya ɗauki rigar Haruna ta firist ya sawa Eliyeza ɗansa. Haruna kuwa ya rasu a bisa tsaunin. Sa'an nan Musa da Eliyeza suka sauko ƙasa. 29 Sa'ad da dukkan jama'a suka ga Haruna ya rasu, sai dukkan jama'a suka yi kuka da makoki domin Haruna har kwana talatin.

Sura 21

1 Sa'ad da sarkin Kan'ana na Arad wanda ke zaune a Negeb, ya ji Isra'ila na zuwa ta hanyar Atarim, sai ya yi faɗa da Isra'ila ya ɗauki waɗansu a matsayin kamammun yaƙi. 2 Isra'ila suka yi wa'adi ga Yahweh cewa, "Idan zaka ba mu nasara a kan waɗannan mutane, sai mun hallakar da su da biranensu." 3 Yahweh ya saurari muryar Isra'ila, ya kuma ba su nasara a kan Kan'aniyawa. Suka hallaka su da biranensu. Shiyasa ake kiran wurin Horma. 4 Suka yi tafiya daga Tsaunin Hor ta hanya zuwa Tekun Iwa a kewayen ƙasar Idom. Sai mutane suka kusan fitar da zuciya a hanya. 5 Mutane suka yi gunaguni da Allah da Musa: "Meyasa kuka fitar da mu daga Masar don mu mutu a cikin jeji? Babu abinci, babu ruwa kuma bamu son irin wannan abinci mai gundura." 6 Sai Yahweh ya aika da macizai masu zafin dafi a cikin mutane. Suka kuwa sassari mutane, har mutane da yawa suka mutu. 7 Mutane suka zo wurin Musa suka ce, "Mun yi zunubi gama mun yi wa Yahweh gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Yahweh domin ya ɗauke macizan daga gare mu." Musa kuwa ya yi addu'a saboda mutanen. 8 Yahweh ya cewa Musa, "Ka yi maciji ka sa shi a sanda, zai zamana duk wanda macijin ya sare shi idan ya dubi macijin tagulla zai tsira." 9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla ya sarƙafa shi a bisa dirka. Idan kuwa maciji ya sari mutum, in dai ya dubi macijin tagulla sai ya tsira. 10 Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya suka yi zango a Obot. 11 Sun yi tafiya daga Obot, suka yi zango a Iye Abarim a cikin jeji suna fuskantar Mowab wajen gabas. 12 Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered. 13 Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda ke cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Kogin Arnon shi ne kan iyakar Mowab, tsakanin Mowab da Amoriyawa. 14 Saboda haka aka faɗa a littafin Yaƙoƙi na Yahweh,"--"Waheb ta cikin yankin Sufa da kwaruruka na kogin Arnon, 15 da gangaren kwaruruka wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab." 16 Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, rijiya wadda Yahweh yace da Musa, "Ka tattara mutane wuri ɗaya domi na, zan kuwa ba su ruwa." 17 Sai Isra'ila suka raira waka: "Ƙorama ki, ɓuɓɓugo yadda ya kamata! Rera waƙa a game da ita, 18 a game da rijiyar da shugabanninmu suka gina, rijiyar da mutanenmu masu daraja suka gina, da sandan sarauta da kuma sandunansu." Daga cikin jeji suka tafi har zuwa Mattana. 19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel, daga can kuma suka tafi Bamot, 20 daga Bamot kuma suka tafi kwarin dake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda ke duban hamada. 21 Sai Israila suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon sarkin Amoriyawa suna cewa, 22 "Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu ratsa ta cikin gonaki ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai har mu fita daga iyakarka." 23 Amma sarkin Sihon bai yarda wa Isra'ila su ratsa ta kan iyakarsa ba. Maimakon haka, sai ya tattara dukkan sojojinsa don su kaiwa Isra'ila hari a cikin jeji. Ya zo Yahaz, wurin da ya yi yaƙi da Isra'ila. 24 Sojojin Isra'ila suka faɗa su da karkashewa da kaifin takobi suka karɓe ƙasar daga Arnon zuwa kogin Yabbok, har ma zuwa ƙasar mutanen Ammonawa. To sai aka ƙayata iyakar mutanen Amonawa. 25 Isra'ila kuwa su ka ci dukkan biranen Amoriyawa da dukkan waɗanda su ke zama da su, ya haɗa da Heshbon da dukkan kauyukanta. 26 Heshbon ita ce birnin Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi yaƙi da sarkin Mowab a dã. Sihon ya ƙwace dukkan ƙasarsa daga yakinsa zuwa Kogin Arnon. 27 Don haka shi ya sa waɗanda suka yi magana suke misali cewa, "Ku zo Heshbon. Bari birnin Sihon a sake gina shi, ya kuma tabbata. 28 Wuta daga Heshbon, hasken wuta daga birnin Sihon ya lanƙwame Ar ta Mowab, da mazaunan tuddan wuraren Arnon. 29 Kaitonki, Mowab! Kin lalace, mutanen Kemosh. Ya sa 'ya'yansa maza na gudu, an kama 'ya'yansa mata sun zama 'yan kurkukun Sihon sarkin Amoriyawa. 30 Amma yanzu an ci nasarar Sihon. Heshbon ta lalata dukkan hanya zuwa Dibon. Mun ci nasararsu a dukkan hanya zuwa Nofa, wadda ta kai kusa da Medeba." 31 Sai Isra'ila suka fara zama a ƙasar Amoriyawa. 32 Musa ya aika mutane su leko asirin Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawa daga cikinta waɗanda ke a can. 33 Sa'an nan suka juya suka tafi su haura ta hanyar Bashan. Og sarkin Bashan ya fita gãba da su, shi da dukkan sojojinsa su yi yaƙi da su a Edirai. 34 Sai Yahweh yace da Musa, "Kada ka ji tsoronsa, gama na baka nasara a kansa, da dukkan sojojinsa da ƙasarsa. Ka yi masa yadda ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, waɗanda suka zauna a Heshbon." 35 Haka fa suka kashe shi da 'ya'yansa maza da dukkan sojojinsa, har babu wani a mutanensa da ya rage a raye. Sai suka mallaki ƙasarsa.

Sura 22

1 Mutanen Isra'ila suka kama tafiya har suka yi zango a filayen Mowab kusa da Yeriko, a ɗaya gefen a Kogin Yodan daga birnin. 2 Balak ɗan Ziffor ya ga dukkan abin da Isra'ila suka yi wa Amoriyawa. 3 Mowab sun firgita kwarai saboda mutanen, domin suna da yawa. Mowab sun ji tsoron mutanen Isra'ila kwarai. 4 Sarkin Mowab ya cewa dattawan Midiyanawa, "Wannan taro zai cinye dukkan abin da ke kewaye da mu, kamar yadda sã ya kan cinye ciyawar saura" Yanzu Balak ɗan Zippor wanda ke sarkin Mowab a wancan lokacin. 5 Ya aika da manzanni zuwa wurin Balaam dan Beyor, a Fetor wadda ke kusa da Kogin Yuferatis, a cikin ƙasar al'ummar mutanensa. Ya kira shi ya ce, "Duba, mutane sun zo nan daga Masar. Sun rufe fuskar duniya, ga shi suna zaune kusa da ni. 6 Ina roƙonka ka zo, ka la'anta mutanen nan domi na, gama suna da ƙarfi sosai fiye da ni. Ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar. Na sani duk wanda ka sawa albarka zai albarkatu, wanda kuwa ka la'anta zai zama la'ananne." 7 Sai dattawan Mowab da dattawan Midiyanawa suka tafi, suka ɗauki ladar duba tsibbu. Suka tafi wurin Balaam suka faɗa masa saƙon Balak. 8 Balaam yace da su, "Ku kwana a nan. Ni kuwa zan baku abin da Yahweh ya faɗa mani." Shugabannin Mowab suka tsaya suka kwana tare da Balaam. 9 Allah kuwa ya zo wurin Balaam yace, 10 "Su wane ne mutanen dake tare da kai? Balaam ya amsa wa Allah, Balak ɗan Zippor, sarkin Mowab, ya aiko su gare ni. Ya ce, 11 'Duba, mutanen da suka zo daga Masar suka cika fuskar ƙasata. Yanzu zo ka la'anta su domi na. Watakila zan iya faɗa da su, har in kore su.'" 12 Allah ya amsa wa Balaam, "Ba za ka tafi tare da mutanen ba, ba kuwa za ka la'anta mutanen Isra'ila ba domin masu albarka ne." 13 Balaam ya tashi da safe ya yi magana da shugabannin Balak, "Ku koma ƙasarku gama Yahweh ya hana ni in tafi tare da ku." 14 Shugabannin Mowab suka koma wurin Balak. Suka ce, "Balaam ya ƙi ya taho tare da mu." 15 Sai Balak ya sake aiken shugabannin, kuma masu yawa masu daraja fiye dana fari. 16 Suka zo wurin Balaam suka ce da shi, "Balak ɗan Zippor ya faɗi wannan, 'Idan ka yarda kada ka bar wani ya hana ka zuwa gare ni, 17 gama zan biya ka sosai, za a ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mani in yi, zan yi. Ka zo ka la'anta wannan jama'a domi na.'" 18 Balaam ya amsa, yacewa mutanen Balak, "Ko da a ce Balak zai bani fadarsa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Yahweh, Allahna ba, ba zan ƙara wani abu ko in rage ba sai dai abin da ya faɗa mani. 19 Amma yanzu, ina rokonku ku kwana a nan, har in san abin da Yahweh zai sake faɗa mani." 20 Allah ya zo wurin Balaam da dare, ya ce masa, "Tun da mutanen nan sun zo kiran ka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin dana umarce ka kaɗai za ka yi." 21 Balaam ya tashi da safe, ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da shugabannin Mowab. 22 Amma saboda ya tafi, fushin Allah ya yi zafi. Mala'ikan Yahweh ya tsaya a hanya kamar wani ya tarye Balaam, wanda ya ke bisa jakarsa. Barorin Balaam biyu na tare da shi. 23 Jakar kuwa ta ga mala'ikan Yahweh na tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa. Sai jakar ta kauce daga hanya ta shiga saura. Balaam ya bugi jakar don ta juyo a kan hanyar. 24 Sai mala'ikan Yahweh ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi, bango a gefen damarsa da bango gefen hagunsa. 25 Jakar ta ga mala'ikan Yahweh kuma. Sai ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Balaam ga bangon. Balaam ya sake bugunta. 26 Mala'ikan Yahweh kuma ya sha kanta ya tsaya a ƙuntataccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu. 27 Jakar ta ga mala'ikan Yahweh, sai ta kwanta a ƙafafun Balaam. Sai Balaam ya husata ya bugi jakar da sandarsa. 28 Sa'an nan Yahweh ya buɗe bakin jakar har ta yi magana. Ta ce da Balaam, "Me nayi maka da ka buge ni har sau uku?" 29 Balaam ya amsa wa jakar, "Domin kin shashantar da ni. Dama a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki." 30 Jakar ta ce wa Balaam, "Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukkan lokacin rayuwarka har zuwa wannan ranar ba? Na taɓa yi maka haka? Balaam ya ce, "A'a." 31 Sa'an nan Yahweh ya buɗe idanun Balaam, ya ga mala'ikan Yahweh na tsaye a hanya da takobi zare a hanunsa. Balaam ya sunkuyar da kansa, ya faɗi rubda ciki. 32 Mala'ikan Yahweh yace da shi, "Meyasa ka bugi jakarka har sau uku? Duba, na fito ne kamar wani abokin gãba don ayyukanka a wuri na mugunta ne. 33 Jakar ta gan ni, ta kauce mani har sau uku. Da a ce bata kauce mani ba, lallai da na kashe ka, in bar ta da rai." 34 Balaam ya cewa mala'ikan Yahweh, "Na yi zunubi. Ban san ka tsaya gãba da ni a hanya ba. To yanzu, idan ka ga mugun abu ne, sai in koma." 35 Amma mala'ikan Yahweh ya cewa Balaam, "Tafi tare da mutanen. Amma abin da na faɗa maka shi kaɗai zaka faɗa." Sai Balaam ya tafi tare da shugabannin Balak. 36 Sa'ad da Balak ya ji Balaam ya zo, ya fita ya tarye shi a birnin Mowab a Arnon, wadda ke kan iyaka. 37 Balak yace wa Balaam, "Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Meyasa baka zo wurina ba? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?" 38 Sai Balaam ya amsa wa Balak yace, "Ga shi, na zo gare ka. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Zan iya faɗin maganar da Allah ya sa a bakina ne kawai." 39 Balaam ya tafi tare da Balak, suka je Kiriyat Huzot. 40 Sai Balak ya yi hadaya da sã da tunkiya ya aika wa Balaam da shugabannin da ke tare da shi. 41 Washegari, Balak ya ɗauki Balaam ya kai shi kan tudu wurin Ba'al. Daga wurin Balaam ya ga wasu daga mutanen Isra'ilawa a zangonsu.

Sura 23

1 Balaam ya cewa Balak, "Ka gina mani bagadai guda bakwai a nan, ka shirya bijimai bakwai da raguna bakwai." 2 Balak ya yi yadda Balaam ya bukace shi ya yi. Sai Balak da Balaam suka miƙa bijimi da rago a kan dukkan bagadan. 3 Balaam yace da Balak, "Tsaya kusa da bayarwar ƙonawa, ni kuwa zan tafi can. Watakila Yahweh zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mani zan faɗa maka." Ya kuwa tafi wani fako a kan tudu wurin da ba itatuwa. 4 A lokacin da yake a kan tudu, Allah ya sadu da shi, Balaam yace da shi, "Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimai guda da rago guda a kan kowanne bagadi." 5 Yahweh ya sa magana a bakin Balaam yace, "Koma wurin Balak, ka yi magana da shi." 6 Sai ya koma wurin Balak, wanda ke tsaye kusa da hadayar ƙonawarsa, da dukkan shugabannin Mowab tare da shi. 7 Balaam kuwa ya fara maganarsa ta annabci ya ce, "Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab daga duwatsun gabas. 'Zo, la'anta Yakubu domi na,' ya ce, 'Zo, ka tsine wa Isra'ila.' 8 Ƙaƙa zan iya la'anta waɗanda Allah bai la'antar ba? Ƙaƙa zan iya tsine wa waɗanda Yahweh bai tsine wa ba? 9 Gama daga kan duwatsu na gan shi, daga bisa kan tuddai na hange shi. Duba, akwai mutane waɗanda ke zama su kaɗai, ba su ɗauki kansu a bakin kome ba a cikin jama'a. 10 Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yakubu ko ya iya yin lissafin ɗaya bisa hudu na Isra'ila? Ka sa in mutu mutuwar adalin mutum, ka sa in mutu cikin salama kamar irin mutuwarsa." 11 Balak ya cewa Balaam, "Me kenan ka yi mani? Na kawo ka ka la'anta abokan gãbana amma ga shi sai albarka kake sa masu." 12 Balaam ya amsa ya ce, "Ba zan yi hankali da abin da zan ce abin da Yahweh ya sa a bakina ba? 13 Balak yace da shi, "Idan ka yarda zo tare da ni zuwa wani wuri inda za ka gan su. Za ka gansu a kurkusa, ba dukkansu ba. A can sai ka la'anta su domi na." 14 Ya kuwa ɗauki Balaam a cikin filin Zofim, a bisa Dutsen Fisga, ya gina bagadai bakwai. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowanne bagadi. 15 Sai Balaam yace da Balak, "Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Yahweh a can. 16 Yahweh kuwa ya sadu da Balaam, ya sa masa magana a bakinsa. Ya ce, "Koma wurin Balak ka faɗa masa maganata." 17 Balaam ya koma wurinsa, ga shi a tsaye kusa da bayarwarsa ta ƙonawa, shugabannin Mowab na tare da shi. Balak yace da shi, "Me Yahweh ya ce?" 18 Balaam ya fara annabcinsa. Ya ce, "Tashi, Balak, ka ji. Ka saurare ni, ya ɗan Ziffor. 19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, ko kuwa mutum ne, da zai canza tunaninsa. Ya yi wani alƙawarin da bai cika shi ba? Ko ya ce zai yi wani abu kuma bai yi shi ba? 20 Duba, an umarce ni in sa albarka. Allah ya bada albarka, ba zan iya janye ta ba. 21 Ya ga babu mugunta a Yakubu ko wahala a Isra'ila. Yahweh Allahnsu na tare da su, suna sowa domin sarkinsu na cikinsu. 22 Allah ne ya fishe su daga Masar da ƙarfi kamar kutunkun ɓauna. 23 Babu wata maitar da zata cuci Yakubu, ba sihirin da zai cuci Isra'ila. Maimakon haka dole ace da, Yakubu da Isra'ila, 'Duba abin da Allah ya yi!' 24 Duba, mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfan zaki, yadda zai fito ya hallakar. Ba ya kwantawa har sai ya cinye ganimarsa, ya lashe jinin abin da ya kashe." 25 Sai Balak ya cewa Balaam, "Kada ka la'anta su ko ka albarka ce su dukka." 26 Amma Balaam ya amsa ya ce da Balak, "Ban faɗa maka ba, zan faɗi dukkan abin da Yahweh ya ce da ni shi zan ce?" 27 Balak ya amsa wa Balaam, "Ka zo yanzu, zan ɗauke ka zuwa wani wuri. Watakila Allah zai yarda ka la'anta su a can domi na." 28 Balak kuwa ya kai Balaam a ƙwanƙolin Dutsen Feyor, wanda ke fuskantar hamada. 29 Balaam yace da Balak, "Gina mani bagadai bakwai a nan ka shirya bijimai bakwai da raguna bakwai." 30 Balak ya yi yadda Balaam ya ce ya yi; ya miƙa hadayar bijimi da rago a kan kowanne bagadi.

Sura 24

1 Da Balaam ya ga Yahweh ya ji daɗin da aka sawa Isra'ila albarka, bai tafi ba, kamar waɗancan lokutan, don ya yi aiki da tsafi. Maimakon haka, sai ya duba wajen jeji. 2 Ya tada idanunsa, ya ga Isra'ila sun yi zango, kowa a cikin kabilarsu, Ruhun Allah ya sauko masa. 3 Ya karɓi wannan annabci, ya ce, "Balaam ɗan Beyor ne ke magana, mutumin da idanuwansa a buɗe suke. 4 Ya faɗa, an ji maganar Allah. Ya ga wahayi daga wurin Maɗaukaki. A gaban wanda ke durƙushe tare da idanuwansa a buɗe. 5 Yaya kyan alfarwarka, Yakubu, a wurin da ka zauna, Isra'ila! 6 Kamar kwarurruka suka bazo, kamar gonaki a gefen kogi, kamar itatuwan aloyes da Yahweh ya dasa, kamar itatuwan al'ul a gefen ruwaye. 7 Ruwa na malalowa daga bokatansu, iri ya jiƙu sosai. Sarkinsu zai fi Agag girma, za a ɗaukaka mulkinsu. 8 Allah ne ya fisshe su daga Masar da iko kamar kutunkun ɓauna. Zai cinye al'ummai waɗanda suka yi faɗa gãba da shi. Zai kakkarya ƙasusuwansu gutsu gutsu. Zai harbe su da kibiyoyinsa. 9 Zai laɓe a ƙasa kamar zaki, kamar zakanya. Ba bu wanda zai dame shi? Bari duk wanda ya albarka ce shi ya yi albarka; duk wanda ya la'anta shi ya zama la'ananne." 10 Balak ya husata da Balaam, ya tafa hannunsa a cikin fushi. Balak yace da Balaam, "Na kirawo ka ka la'anta maƙiyana, amma ga shi har sau uku kana sa masu albarka. 11 Yanzu sai ka tafi gidanka. Na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi Yahweh ya hana ka samun wani lada." 12 Sai Balaam ya amsa wa Balak, "Na faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni. 13 Idan Balak ya ba ni fadarsa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Yahweh ba, da wani mugun abu ko mai kyau ne, kai kowanne irin abu ne zan so in yi. Zan faɗi abin da Yahweh ya faɗa mani shi zan ce.' Ban faɗa masu haka ba? 14 Saboda haka yanzu, ga shi, zan koma ga mutanena. Amma da farko bari in gargaɗe ka abin da waɗannan mutane za su yiwa mutanenka a ranaku masu zuwa." 15 Balaam ya fara wannan annabci. Ya ce, "Balaam ɗan Beyor ya faɗa, mutumin da idanunsa ke buɗe. 16 Wannan shi ne annabcin wanda yake jin magana daga Allah, wanda ke da ilimi daga wurin Maɗaukaki, wanda ke da wahayi daga Mai Iko Dukka, A gaban wanda yake durƙurshe tare da idannunsa a buɗe. 17 Na gan shi, amma baya nan yanzu. Ina hangensa, amma baya kusa. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, kendir zai fito daga cikin Isra'ila. Za ya ragargaje shugabannin Mowab ya hallaka dukkan zuriyar Shitu. 18 Sai Idom ta zama mallakar Isra'ila, Seyir kuma za ta zama mallakarsu, abokan gãbar Isra'ila, waɗanda Isra'ila zasu ci da ƙarfi. 19 Daga cikin Yakubu sarki zai zo wanda zai yi mulki, zai hallaka waɗanda suka ragu a birninsu." 20 Sai Balaam ya dubi Amalek ya fara annabcinsa. Ya ce, "Amalek mafi girma ne cikin al'ummai, amma ƙarshensa zai kasance hallaka." 21 Sai Balaam ya duba zuwa wajen Kan'aniyawa, ya fara annabcinsa. Ya ce, "Wurin da kuke zama mai ƙarko ne, gidajenku kuma na cikin duwatsu. 22 Duk da haka ku Kan'aniyawa za a lalatar da ku da wuta idan Asiriyawa suka ɗauke ku bayi." 23 Sai Balaam ya fara annabcinsa na ƙarshe. Ya ce, "Kaito! Wa zai rayu sa'ad da Allah ya yi wannan 24 Jiragen ruwa kuwa za su zo daga gaɓar tekun Kittim; za su faɗawa Asiriya, zasu ci Eber, amma kuma, ƙarshensu hallaka ce." 25 Sai Balaam ya tashi ya tafi. Ya koma gidansa, Balak ma yayi tafiyarsa.

Sura 25

1 Isra'ila ta zauna a Shittim, maza suka fara yin karuwancinsu da matan Mowab, 2 domin Mowabawa sun gayyaci mutane zuwa wajen hadayar allolinsu. Saboda haka mutane suka ci suka durƙusa wa allolin Mowabawa. 3 Mutanen Isra'ila suka shiga bautawa gumakun Ba'al na Feyor, Yahweh ya yi fushi da Isra'ila. 4 Yahweh yace da Musa, "Kashe dukkan shugabannin mutanen, ka rataye su a gabana a nuna su a fili, don in huce daga fushi da nake yi da Isra'ila." 5 Musa kuwa ya cewa shugabanin Isra'ila, "Kowannen ku dole ya kashe mutanensa waɗanda suka shiga bautar gumakun Ba'al Feyor." 6 Sai ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila ya zo, ya kawo mace Bamidiyaniya cikin iyalinsa. Wannan ya faru ne a idannun Musa da dukkan jama'ar mutanen Isra'ila, a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwar taro. 7 Finehas ɗan Eliyeza ɗan Haruna firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin jama'a, ya ɗauki mãshi a hannunsa. 8 Ya bi Ba'isra'ilen cikin alfarwa, ya soke dukkansu biyu, Ba'isra'ilen da macen. Da haka aka tsaida annobar da Allah ya aiko wa mutanen Isra'ila. 9 Waɗanda suka mutu saboda annobar sun kai jimilar mutane dubu ashirin da hudu. 10 Yahweh ya faɗa wa Musa ya ce, 11 "Finehas ɗan Eliyeza ɗan Haruna firist, ya kawar da fushina daga mutanen Isra'ila gama yayi kishi irin nawa a cikinsu. Saboda haka ba zan hallakar da mutanen Isra'ila da fushina ba. 12 Saboda haka ne, 'Yahweh ya faɗa, "Duba, ina ba Finehas alƙawarin salamata. 13 Dominsa da zuriyarsa zasu bi shi, alƙawarin da ba zai taɓa ƙarewa ba daga firistoci gama yana da kishi domin, Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin mutanen Isra'ila.'"' 14 Yanzu sunan Ba'isra'ilen da aka kashe tare da Bamidiyar, Zimri ɗan Salu, shugaban zuriyar iyalin Simiyonawa. 15 Sunan Bamidiyar wanda aka kashe, ita ce Kozbi 'ɗiyar Zur, wanda yake shi ne shugaban wata kabila na iyalin Midiyan. 16 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 17 "Ku fãɗa wa Midiyanawa abokan gãbarku, ku hallaka su, 18 gama sun yi maku kamar abokan gãbanku da makircinsu. Sun kai ku cikin mugun abu a kan Feyor da na Kozbi 'yar'uwarsu, ɗiyar shugaban Midiyan, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor."

Sura 26

1 Ya zamana bayan annobar sai Yahweh ya yi magana da Musa da Eliyeza ɗan Haruna firist. Ya ce, 2 "Ku ƙidaya dukkan taron mutanen Isra'ila, daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, bisa ga zuriyar kakanninsu, da dukkan waɗanda za su iya zuwa yaƙi domin Isra'ila." 3 Musa da Eliyeza firist suka yi masu magana a filayen Mowab daura da Yodan a Yeriko, suka ce, 4 "A ƙidaya mutane daga mai shekaru ashirin zuwa gaba kamar yadda Yahweh ya umarci Musa da mutanen Isra'ila, waɗanda suka fito daga ƙasar Masar." 5 Ruben shi ne ɗan fari na Isra'ila. Daga ɗansa Hanok kabilar Hanokiyawa ta zo. Daga Fallu kabilar Falluniyawa ta zo. 6 Daga Hesruna har zuwa kabilar Hezaroniyawa. Daga Karmi har zuwa kabilar Karmiyawa. 7 Waɗannan su ne kabilun Ruben, waɗannan yawansu ya kai jimilar mutane 43,730. 8 Eliyab shi ne ɗan Fallu. 9 'Ya'yan Eliyab su ne Nemuwel da Datan da Abiram. Waɗannan su ne Datan da Abiram waɗanda suka bi Korah a lokacin da suka yi wa Musa da Haruna ƙalubale, suka kuma yi tawaye ga Yahweh. 10 Ƙasa kuwa ta buɗe bakinta ta haɗiye su tare da Kora da dukkan mabiyansa suka mutu. A wancan lokaci, wuta kuma ta cinye mutane 250, waɗanda suka zama abin faɗakarwa. 11 Amma iyalin Kora ba su mutu ba. 12 Kabilar zuriyar Simiyon su ne waɗannan: Ta wurin Nemuwel, aka sami kabilar Nemuwelawa, ta wurin Yamin, kabilar Yaminawa, ta wurin Yakin, kabilar Yakinawa, 13 ta wurin Zera, kabilar Zerawa, ta wurin Shawul, kabilar Shawulawa. 14 Waɗannan su ne kabilun zuriyar Simiyon, waɗanda aka ƙidaya jimilar mutane 22,200. 15 Kabilar zuriyar Gad su ne waɗannan: Ta wurin Zifon, aka sami kabilar Zifonawa, ta wurin Haggi, kabilar Haggiyawa, ta wurin Shuni, kabilar Shuniyawa 16 ta wurin Ozni, kabilar Oziniyawa, ta wurin Eri, kabilar Eritiyawa, 17 ta wurin Arod kabilar Arodiyawa, ta wurin Areli, aka sami kabilar Areliyawa. 18 Waɗannan su ne kabilar zuriyar Gad sun kai jimilar mutane 40,500. 19 'Ya'yan Yahuda su ne Er da Onan, amma waɗannan mutane sun rasu a ƙasar Kan'ana. 20 Sauran kabilar zuriyar Yahuda su ne: ta wurin Shela, kabilar Shelatawa, ta wurin Feresa, kabilar Feresawa, da ta wurin Zera, kabilar Zerawa. 21 Zuriyar Ferez su ne: Ta wurin Hezron, kabilar Hezronawa, ta wurin Hamul, kabilar Hamulawa. 22 Waɗannan su ne zuriyar kabilar Yahuda sun kai jimilar mutane 76,500. 23 Kabilar zuriyar Issaka su ne: Ta wurin Tola, kabilar Tolawa, ta wurin Fuwa, kabilar Fuwayawa, 24 ta wurin Yashub, kabilar Yashubawa, ta wurin Shimron, kabilar Shimronawa. 25 Waɗannan su ne kabilun Issaka, waɗanda sun kai jimilar mutane 64,300. 26 Zuriyar kabilar Zebulun su ne waɗannan: Ta wurin Sered, kabilar Seredawa, ta wurin Elon, kabilar Elonawa, ta wurin Yaleyel, kabilar Yaleyawa. 27 Waɗannan su ne kabilun Zebulun, sun kai jimilar mutane 60,500. 28 Zuriyar kabilar Yosef su ne Manasse da Ifraim. 29 Zuriyar Manasse su ne waɗannan: ta wurin Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Giliyad), ta wurin Giliyad, kabilar Gilidiyawa. 30 Zuriyar Giliyad su ne waɗannan: Ta wurin Leza, kabilar Lezawa, ta wurin Helek, kabilar Helekawa, 31 ta wurin Asriyel, kabilar Asrilawa, 32 ta wurin Shekem, kabilar Shekemawa, ta wurin Shemida, kabilar Shemidawa, ta wurin Hefer, kabilar Heferawa. 33 Zelofehad ɗan Hefer ba shi da 'ya'ya maza, amma sai 'ya'ya mata kaɗai. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka daTirza. 34 Waɗannan su ne kabilar Manasse, sun kai jimilar mutane 52,700. 35 Zuriyar kabilar Ifraim su ne waɗannan: Ta wurin Shutela, kabilar Shutelawa, ta wurin Beker, kabilar Bekerawa, ta wurin Tahat, kabilar Tahatawa. 36 Zuriyar Shutela su ne, ta wurin Eran, kabilar Eraniyawa. 37 Waɗannan su ne zuriyar kabilar Ifraim, sun kai jimilar mutane 32,500. Waɗannan su ne zuriyar Yosef an lissafta kowanne bisa ga kabilunsu. 38 Zuriyar kabilar Benyamin su ne waɗannan: Ta wurin Bela, kabilar Belayawa, ta wurin Ashbel, kabilar Ashbelawa, ta wurin Ahiram, kabilar Ahiramawa, 39 ta wurin Shefufam, kabilar Shefufamawa, ta wurin Hufam, kabilar Hufamawa. 40 'Ya'yan Bela maza su ne Ard da Na'aman. Daga Ard aka sami kabilar Ardawa, daga Na'aman aka sami kabilar Na'amawa. 41 Waɗannan su ne zuriyar Benyamin. Yawan mutane 45,600 ne. 42 Zuriyar kabilar Dan su ne, ta wurin Shuham, aka sami kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne zuriyar kabilun Dan. 43 Dukkan kabilun Shuhamawa sun kai yawan mutane 64,400. 44 Zuriyar kabilar Asha su ne waɗannan: Ta wurin Imna, kabilar Imnawa, ta wurin Ishbi, kabilar Ishabawa, ta wurin Beriya, kabilar Beriyawa. 45 Zuriyar Beriya su ne waɗannan: Ta wurin Hebar, kabilar Hebarawa, ta wurin Malkiyel, kabilar Malkiyawa. 46 Sunan 'yar Asha Sera. 47 Waɗannan su ne zuriyar kabilun Asha, sun kai jimilar mutane 53,400. 48 Zuriyar kabilar Naftali su ne waɗannan: Ta wurin Yazeyel, kabilar Yazelawa, ta wurin Guni, kabilar Guniyawa, 49 ta wurin Yezer, kabilar Yezerawa, ta wurin Shilem, kabilar Shilemawa. 50 Waɗannan su ne zuriyar kabilun Naftali sun kai jimilar mutane 45,400. 51 Wannan shi ne cikakken lissafin maza a cikin mutanen Isra'ila: 601,730. 52 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 53 "Dole a raba ƙasar ga waɗannan mutane gãdo bisa ga yawan sunayensu. 54 Za ka ba babbar kabila babban rabon gãdo, ka ba karamar kabila karamin rabon gãdo. Kowacce kabila za a ba ta gãdo bisa ga yawan mutanenta da aka lissafta. 55 Amma za a rarraba ƙasar ta wurin kuri'a. Za su gaji ƙasar yadda aka raba a tsakanin kabilun kakanninsu. 56 Za a rarraba gãdo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a." 57 Kabilar Lebiyawa da aka ƙidaya bisa kabila kabila, su ne waɗannan: Ta wurin Gershon, kabilar Gershawa, ta wurin Kohat, kabilar Kohatiyawa, ta wurin Merari, kabilar Merariyawa. 58 Kabilar Lebi su ne waɗannan: kabilar Lebiyawa da kabilar Hebroniyawa da kabilar Maliyawa da kabilar Mushiyawa da kabilar Koriyawa. Kohat shi ne kakan Amram. 59 Sunan matar Amram ita ce Yokabed, zuriyar Lebi, wanda ya haifi Lebiyawa a Masar. Ta haifa wa Amram 'ya'yansu, su ne Haruna da Musa da Miriyam 'yar uwarsu. 60 Haruna ya haifi Nadab da Abihu, Eliyeza da Itamar. 61 Nadab da Abihu sun rasu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Yahweh. 62 Mazan da aka ƙidaya daga cikinsu sun kai dubu ashirin da uku, dukkansu maza daga wata ɗaya zuwa sama. Amma ba a ƙidaya su ba cikin zuriyar Isra'ila domin ba a ba su gãdo a cikin mutanen Isra'ila ba. 63 Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eliyeza firist suka ƙidaya. Suka ƙidaya mutanen Isra'ila a kwarin Mowab Yodan a Yeriko. 64 Gama a cikin waɗannan babu mutum wanda Musa da Haruna firist ba su ƙidaya ba a zuriyar Isra'ila da aka ƙidaya a jeji Sinai. 65 Gama Yahweh ya ce da dukkan waɗannan mutane lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

Sura 27

1 Sai Musa ya zo wurin 'ya'ya mata na Zelofehad ɗan Hefer ɗan Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse, kabilar Manasse ɗan Yosef. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yansa mata: Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza. 2 Suka tsaya a gaban Musa da Eliyeza firist, da shugabanni, da dukkan jama'a a ƙofar shiga rumfar taro. Suka ce, 3 "Mahaifinmu ya rasu a cikin jeji. Ba ya cikin waɗanda suka tayar wa Yahweh a ƙungiyar Kora. Ya mutu saboda alhakin zunubinsa, ga shi ba shi da 'ya'ya maza. 4 Donme za a cire sunan mahaifinmu daga cikin kabilar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? Ka ba mu gãdo tare da 'yan'uwan mahaifinmu" 5 Musa ya kai maganarsu a gaban Yahweh. 6 Yahweh ya yi magana da Musa, ya ce, 7 "Ya'ya mata na Zelofehad suna magana dai dai. Ka ba su ƙasa a matsayin gãdo a cikin 'yan'uwansu, za ka tabbatar sun sami gãdon mahaifinsu. 8 Ka yi magana da mutanen Isra'ila, ka ce, 'Idan mutum ya rasu, ba shi da ɗa, sai ka sa gãdon mahaifinsa ya koma kan 'yarsa. 9 Idan ba shi da 'ya, sai ka bada gãdon ga 'yan'uwansa. 10 Idan kuma ba shi da 'yan'uwa maza, sai ka bada gãdonsa ga 'yan'uwan mahaifinsa maza. 11 Idan kuwa ba shi da 'yan'uwa maza, sai ka bada gãdonsa ga 'yan'uwansa na kusa a kabilarsa, zai ɗauke ta don kansa. Wannan ita ce doka da aka tabbatar da ka'ida saboda mutanen Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya umarce ni.'" 12 Yahweh yace da Musa, "Tafi bisa duwatsun Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba mutanen Isra'ila. 13 Bayan daka ganta, kai ma, za a tara ka ga mutanenka, kamar Haruna ɗan'uwanka. 14 Wannan zai kasance domin ku biyun kun yi tawaye akan umarnina cikin jejin Zin. A can, lokacin da ruwa ke kwararowa daga dutse, a cikin fushi baku girmama ni kamar mai tsarki a gaban idannun dukkan jama'a ba." Waɗannan su ne ruwayen Meriba dana Kadesh a jejin Zin. 15 Sai Musa ya yi magana da Yahweh, ya ce, 16 "Bari kai, Yahweh, Allah na ruhohin dukkan 'yan adam, ya naɗa mutum bisa kan jama'a, 17 mutum wanda zai tafi, ya dawo a gabansu, ya shugabance su ya fita, ya dawo, saboda jama'arka ba kamar tumakin da ba makiyayi suke ba." 18 Yahweh yace da Musa, "Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutum wanda Ruhuna yake raye a cikinsa, ka sa hannunka a kansa. 19 Sa shi a gaban Eliyeza firist da gaban dukkan jama'a, ka umarce shi a gaban idanunsu ya shugabance su. 20 Ka danka masa ikonka a kansa, don dukkan jama'ar mutanen Isa'ila su yi masa biyayya. 21 Zai wuce gaban Eliyeza firist ya nemi nufina domin sa, ta wurin yanke shawarar Urim. Zai zama bisa ga umarninsa da mutane za su tafi waje su kuma komo ciki, shi da dukkan mutanen Isra'ila tare da shi, da kuma dukkan jama'a." 22 Sai Musa ya yi kamar yadda Yahweh ya umarce shi. Ya ɗauki Yoshuwa ya sa shi a gaban Ele'yazar firist da dukkan jama'a. 23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya umarce shi ya yi shugabanci, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.

Sura 28

1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila, ka ce da su, 'Za ku miƙa hadaya gare ni a ayyanannun lokatai, ta abincin baye-baye na ta wurin wuta mai daɗin ƙanshi domi na.' 3 Ka kuma ce da su, 'Wannan bayarwa da za a yi da wuta, za ku bayar ga Yahweh--ɗan tunkiya shekara ɗaya wanda babu lahani a gare shi, guda biyu kowacce rana, matsayin bayarwar ƙonawa. 4 Dan tunkiya ɗaya za ku bayar da safe, ɗaya kuma da maraice. 5 Za ku bayar da mudun lallausan garin filawa matsayin bayarwar hatsi, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa. 6 Wannan zata zama ta bayarwar ƙonawa da za ku riƙa yi yadda an umarta a Tsaunin Sinai baiko mai daɗin ƙanshi, da aka yi da wuta ga Yahweh. 7 Bayarwar sha zata zama ɗaya bisa huɗu na moɗa don ɗaya ɗan rago. Za a kwarara a wuri mai tsarki baiko na sha mai ƙarfi ga Yahweh. 8 Ɗaya ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice tare da baiko na gari kamar baiko na safe. Dole ne kuma a miƙa wani na sha tare da shi, baikon ƙonawa da wuta, mai daɗin ƙamshi ga Yahweh. 9 A ranar Asabaci kuwa za a miƙa 'ya'yan raguna biyu kowanne bana ɗaya marasa lahani, da mudu biyu na lallausan gari a matsayin baiko, kwaɓaɓɓe da mai, da baiko na sha tare da shi. 10 Wannan shi ne baikon ƙonawa domin kowacce Asabaci, a kan kowanne baiko na ƙonawa da baiko na sha tare da shi. 11 A farkon kowanne wata, za a miƙa baikon ƙonawa ga Yahweh. Za a miƙa 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya da kuma 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya, marasa lahani. 12 Za a kuma miƙa kwaɓaɓɓen gari kashi uku bisa ɗaya na garwa da man zaitun don kowanne bijimi, da gari kashi biyu bisa goma na garwa don rago ɗaya. 13 Za a kuma miƙa humushin lallausan gari za a haɗa shi da mai kamar baikon hatsi don kowanne rago. Wannan zai zama baikon ƙonawa, domin ya bayar da ƙamshi mai daɗi, baiko da aka yi da wuta ga Yahweh. 14 Baiko na sha na mutane dole ya zama rabin moɗa na ruwan inabi don bijimi, da ɗaya bisa uku na moɗa don rago da ɗaya bisa huɗu na moɗa don ɗan rago. Wannan shi ne baiko na ƙonawa a kowanne wata a dukkan watannin shekara. 15 Dole kuma a miƙa bunsuru ɗaya a matsayin baiko na zunubi ga Yahweh. Wannan zai zama ƙarin baiko na ƙonawa da baiko na sha da za a riƙa yi da su. 16 A cikin wata na farko, a rana ta goma sha huɗu ga watan, idin Ƙetarewa ga Yahweh. 17 A kan rana ta goma sha biyar ga wannan watan kuwa za a yi idi. Gama kwanaki bakwai na cin abinci mara gami ne. 18 A rana ta fari, za ku yi tsarkakakken taron girmama Yahweh. Ba za ku yi aikin da kuka saba yi a ranar ba. 19 Duk da haka, dole ku miƙa baiko da aka yi da wuta, a baiko na ƙonawa ga Yahweh. Dole ku miƙa 'yan bijimai biyu da rago ɗaya, da 'yan tumaki bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani. 20 Tare da bijimi, za ku miƙa lallausan gari kashi uku na garwa wanda aka kwaɓa da mai tare da rago, kashi biyu bisa uku. 21 Tare da kowanne 'yan raguna bakwai, za ku miƙa lallausan gari haɗe da mai, 22 da ɗan akuya ɗaya a matsayin baikon zunubin ƙafara domin kanku. 23 Dole ku miƙa waɗannan a kan bayarwar ƙonawa da kuke miƙawa kowacce safiya. 24 Kamar yadda aka nuna a nan, za ku miƙa waɗannan hadayu kullum, saboda ranaku bakwai na Idin ‌Ƙetarewa, za ku yi baikon abincin da aka yi da wuta mai daɗin kamshi ga Yahweh. Za a miƙa a kan bayarwar ƙonawa da kuke yi da baiko na sha. 25 A rana ta bakwai za ku yi tsattsarkan taro na girmama Yahweh, ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba a ranar. 26 Haka nan a ranar nunar fari, da kuke miƙa baikon sabon hatsi ga Yahweh a Bikin Makonni, za ku yi tsattsarkan taro na girmama Yahweh, ba za ku yi aikin da kun saba yi ba a ranar. 27 Dole ne ku miƙa baikon ƙonawa mai dadin ƙamshi ga Yahweh. Dole ne ku miƙa 'yan bijimai biyu da rago ɗaya da 'yan tumakai maza guda bakwai bana ɗaya ɗaya. 28 Kuma ku miƙa baikon gari tare da su: gari haɗe da mai, gari kashi uku bisa uku da aka haɗa da mai domin kowanne bijimi da kashi biyu don rago ɗaya. 29 Ku miƙa kashi goma na garwa da aka haɗa da mai don kowanne 'yan raguna bakwai, 30 da ɗan akuya na ƙafara domin kanku. 31 Idan kuka miƙa waɗannan dabobbin marasa lahani, tare da baye bayenku na sha, wannan zai zama a kan baye-bayen ƙonawa, da hatsi da kuke bayarwa tare su.'"

Sura 29

1 A cikin wata na bakwai, a rana ta farko ta watan, za ku yi taro mai tsarki na girmama Yahweh. Tilas ba za ku yi wani aikin da aka saba a koda yaushe ba a wannan rana. Dole ne ta zama ranar da za ku busa ƙahonni. 2 Za ku miƙa ƙonannen baiko domin abin daɗi da ƙamshi ga Yahweh. Dole ku miƙa ɗan bijimi, rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai masu shekara ɗaya, mara aibi. 3 Dole ne ku miƙa su tare da baikonsu na hatsi, gari mai laushi cuɗaɗɗe da mai, uku cikin goma na efa domin bijimi, biyu cikin goma domin ragon, 4 ɗaya cikin goma kuma domin kowanne cikin raguna bakwai. 5 Dole ne ku miƙa bunsuru ɗaya domin baiko na zunubi don a yi maku kafara. 6 A miƙa waɗannan baye-baye a cikin wata na bakwai a bisa kan sauran dukkan baye-bayen da za ku bayar a ranar farko ta kowanne wata: ƙonannen baiko na musamman da kuma baiko na hatsi a haɗa da shi. Waɗannan dole za a miƙa su zama ƙãri bisa ga ƙonannen baikon da aka sãba, baiko hatsin, da kuma baye-bayensa na sha. Sa'ad da kuka miƙa waɗannan baye-bayen, za ku yi biyayya da abin da aka umurtar don ya bãda ƙamshi mai daɗi, baiko na wurin wuta ga Yahweh. 7 A rana ta goma ga watan bakwai za ku yi taro mai tsarki don girmama Yahweh. Dole ku ƙasƙantar da kanku ba za ku yi wani aiki ba. 8 Dole ku miƙa baiko na ƙonawa mai bãda ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Dole ku miƙa ɗan bijimi ɗaya, da ɗan rago ɗaya, da kuma 'yan raguna 'yan shekara ɗaya guda bakwai. 9 Dole ku miƙa tare da su baiko na hatsi, gãri mai laushi gauraye da mai, 10 uku cikin goma na efa domin bijimi, biyu cikin uku domin tunkiya guda ɗaya, da kuma kashi goma na efa domin dukkan raguna bakwai ɗin. 11 Dole ku miƙa ɗan akuya ɗaya don baikon na zunubi. Wannan zai zama ƙãri bisa baikon zunubi na kaffara, da baye-bayensu na sha. 12 A rana ta sha biyar ga watan bakwai za ku yi taro mai tsarki don girmama Yahweh. Ba za ku taɓa yin wani aiki yadda kuka sãba a kodayaushe a wannan rana ba, kuma za ku yi buki gare shi kwana bakwai. 13 Dole ku miƙa baiko na ƙonawa, hadaya da aka miƙa ta wurin wuta domin abin ƙamshi da daɗi ga Yahweh. Dole ku miƙa 'yan bijimi guda sha uku, tumaki guda biyu, da kuma tumakai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya. Kowanen su ya zama mara aibi. 14 Dole ne ku miƙa tare da su baiko na hatsi, niƙaƙƙen gari harɗe da mai, kashi uku na efa don kowanne rago na raguna sha ukun, kashi biyu domin kowanne rago na raguna biyun, 15 da kashi ɗaya na efa domin dukkan tumaki guda sha huɗun. 16 Dole ku miƙa baiko na zunubi namijin akuya ɗaya ƙãri bisa ƙonannun baiko na kodayaushe, baikon hatsin, tare da shi kuma da baikon abin sha. 17 A rana ta biyu na taruwa, dole ne ku miƙa 'yan raguna guda sha biyu, tumaki biyu, da awakai maza goma sha huɗu 'yan shekara ɗaya, kowanne mara aibi. 18 Dole ku miƙa su tare da baikon hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku. 19 Dole ne ku miƙa baiko na zunubi ɗan rago ɗaya ƙãri bisa baiko na ƙonawa a kodayaushe yaushe, da kuma baye-bayensu na shã. 20 A rana ta uku na taruwan, dole ne ku miƙa raguna shaɗaya, tumaki biyu, da bunsurai sha huɗu 'yan shekara ɗaya, kowanne mara aibi. 21 Dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da baye-baye na abin shã domin ragunan, domin su tumakin, da kuma don su awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku. 22 Dole ne ku miƙa namijin tunkiya ɗaya baiko na zunubi ƙãri bisa baiko na ƙonawa na kodayaushe, baikon hatsinta, da kuma baye-bayensu. 23 A rana ta huɗu ta taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda goma, tumaki guda biyu, da mazajen awakai 'yan shekara ɗaya guda shahuɗu, kowannensu marasa aibi. 24 Dole ne ku yi tare da su baiko na hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, da kuma domin awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku. 25 Dole ne ku miƙa bunsuru ɗaya baiko na zunubi ƙãri bisa baiko na ƙonawa na kodayaushe, baiko na hatsinsa, da baye-bayensu na shã. 26 A rana ta biyar ta taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda tãra, tumaki biyu, da bunsurai 'yan shekara ɗaya guda sha huɗu, marasa aibi. 27 Dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da kuma baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, domin kuma awakan, ana miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurta. 28 Dole ne ku miƙa namijin tunkiya ɗaya na baikon domin zunubi ƙari bisa ƙonannen baiko na kodayaushe, baikon hatsin, da baye-baye na shãnsu. 29 A rana ta shida ta taruwar, dole ne ku miƙa raguna takwas, tumaki biyu, da mazajen awakai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya, marasa aibi. 30 dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da kuma baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakan, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurce ku. 31 dole ne ku miƙa bunsuru guda ɗaya baiko na zunubi, baikon hatsi, da baye-bayensu na shã. 32 A rana ta bakwai na taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda bakwai, tumakai biyu, da kuma bunsurai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya, marasa aibi. 33 Dole ne ku miƙa tare da su baiko na hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakan, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurce ku. 34 Dole ne ku miƙa namijin akuya domin baiko na zunubi don ƙari bisa ga baiko na ƙonawa kamar na kodayaushe, domin baiko na hatsin, da kuma baye-bayensu na shã. 35 A rana ta takwas zaku sake yin wani taron mai tsarki. Kar ku kuskura ku yi wani aiki kamar yadda kuka saba a wannan rana. 36 Dole ne ku miƙa hadaya na ƙonawa, baiko da aka yi da wuta domin a miƙa abin ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Za ku miƙa ɗan bijimi guda ɗaya, akuya ɗaya, da kuma 'yan raguna guda bakwai masu shekara ɗaya, kowanne mara aibi. 37 Dole ne ku miƙa baikon hatsinsu da kuma baikon abin sha domin bijimi, domin ɗan akuya, kuma domin 'yan raguna, kuna miƙa baye-baye kamar yadda aka umurta. 38 Dole ne ku miƙa bunsuru guda ɗaya baiko na zunubi ƙari bisa ƙonannen baikon da aka sãba kodayaushe, baikon hatsinsu, da kuma baye-bayensu na shã. 39 Waɗannan su ne dole ku miƙa ga Yahweh a tsayayyun bukukuwanku. Waɗannan za su zama ƙãri ne bisa alƙawaranku da kuma baye-bayenku na yardan rai. Dole ne ku miƙa waɗannan a matsayin baye-bayenku na ƙonawa, baye-baye na hatsi, baye-baye na shã, da baye-baye na zumunci." 40 Sai Musa ya gaya wa mutanen Isra'ila dukkan abin da Yahweh ya umurce shi ya faɗa.

Sura 30

1 Musa ya yi magana da shugabannin ƙabilun mutanen Isra'ila. Ya ce, "Ga abin da Yahweh ya umarta. 2 Idan wani ya yi wa'adi ga Yahweh, ko ya yi rantsuwa don ya riƙe kansa ga alƙawari, kada ya karya maganarsa. Dole ya cika alƙawarinsa ya aikata duk abin da ya fito daga bakinsa. 3 Idan 'yar matashiya mace mai zama cikin gidan mahaifinta ta yi wa'adi ga Yahweh ta ɗaure kanta ga alƙawari, 4 idan mahaifinta ya ji wa'adin da kuma alƙawarin da ta daukar wa kanta, kuma idan bai ce komai ba domin ya hana ta ba, to dukka wa'adodinta za su tsaya. Kowanne alƙawarin da ta ɗaukar wa kanta zai tsaya. 5 Amma idan mahaifinta ya ji game da wa'adinta da alƙawarinta, idan kuma bai ce da ita komai ba, to dukkan wa'adodinta da alƙawaranta da ta ɗaukar wa kanta za su tsaya. 6 Amma, idan mahaifinta ya ji dukkan wa'adodin da ta yi da kuma alƙawura masu tsarki da ta ɗaukar wa kanta, idan kuma ya sọke abin da ta yi a wannan ranar, to ba za su tsaya ba. Yahweh zai gafarta mata domin mahaifinta ya sọke abin da ta yi. 7 Idan ta auri mutum yayin da ta ke ƙarƙashin waɗannan wa'adodin, ko kuma idan ta furta alƙawarai cikin garaje da ta ɗaukar wa kanta nawaya, wannan nawayar tilas ta tsaya. 8 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji game da zancen, sa'an nan ya hana alƙawarin da ta ɗauka, maganar gangancin da ta yi ta fita daga leɓunanta da ta ɗaure kanta. Yahweh zai sãke ta. 9 Amma game da gwauruwa ko sakakkiyar mace, dukkan abin da ta ɗaure kanta da shi zai tsaya a kanta. 10 Idan mace ta ɗauki alƙawari a cikin gidan mijinta ko ta yi wa kanta hani ta wurin yin rantsuwa, 11 sai kuma maigidanta ya ji game da wannan, amma bai ce mata komai ba, to sai dukkan abin da ta alƙawarta su tsaya. 12 Amma idan maigidanta ya hana su a wannan ranar da ya ji game da su, to duk abin da ya fito daga leɓunanta game da wa'adodinta ko alƙawaranta baza su tsaya ba. Mijinta ya hana su. Yahweh zai sãke ta. 13 Kowanne wa'adi ko rantsuwar da mace ta yi da suka ɗaure ta har ta hana wa kanta wani abu maigidanta na iya tabbatarwa ko ya hana. 14 Amma idan bai ce mata komai a ranar ba, to ya tabbatar da dukkan wa'adodi da zaunannun alƙawarai wadanda ta ɗauka. Ta haka ya tabbatas da su domin bai ce da ita komi ba a ranar da ya ji game da su. 15 Idan mijinta yayi ƙoƙarin hana alƙawarin da matarsa ta ɗauka da daɗewa bayan ya ji shi, don haka zai ɗauki laifinta." 16 Waɗannan su ne farillan da Yahweh ya umarci Musa da ya sanar - da farillai game da abin dake tsakanin mutum da matarsa da kuma tsakanin mahaifi da ɗiyarsa a matashiyarta sa'ad da take tare da iyalin mahaifinta.

Sura 31

1 Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce, 2 "Ka ɗauki fansa a bisa Midiniyawa kan abin da suka yi wa Isra'ilawa. Bayan ka yi wannan, za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka." 3 Sai Musa ya yi magana da mutanen. Ya ce, "Ku shirya wasu daga cikin mazajenku don yaƙi gãba da Midiyan, ku kuma yi ramako na Yahweh a bisanta. 4 Kowacce kabila cikin dukkan Isra'ila dole ta aika da sojoji dubu zuwa yaƙi." 5 Saboda haka cikin dubban mazajen Isra'ila, aka aika da dubu ɗaya daga kowacce kabila, mazaje dubu sha biyu shiryayyu don yaƙi. 6 Sai Musa ya aika da su zuwa yaƙi, daga kowacce kabila dubu ɗaya, tare da Finehas ɗan Eliyeza firist, da kuma wasu kayayyaki daga cikin wuri mai tsarki da kuma su ƙahonni dake a hannunsa don busawa ta alamar yaƙi. 7 Suka yi yaƙi da Midiya, kamar yadda Yahweh ya bada umarni ga Musa. Suka karkashe kowanne mutum. 8 Suka kashe sarakunan Midiyan tare da sauran matattunsu: Ebi, da Rekem, da Zur, da Hur, da kuma Reba, sarakuna guda biyar na Midiyan. Suka kuma kashe Bala'am ɗan Beyor, da takobi. 9 Rundunar Isra'ila suka kwashe bayi matayen Midiyan, da yaransu, da dukkan shanunsu, da garkunansu, da dukkan dukiyarsu. Suka kwashe su ganima. 10 Suka ƙone dukkan biranensu inda suke zama da dukkan sansaninsu. 11 Suka kwashe dukkan ganimar da kuma 'yan sarƙoƙi, da mutane da dabbobi. 12 Suka dawo da 'yan sarƙoƙin, da ganimar, da abubuwan da aka ƙwace wurin Musa, ga Eliyeza firist, zuwa kuma ga jama'ar Isra'ila. Suka kawo su zuwa cikin sansani cikin kwarurukan Mowab, wanda ke bakin Yodan kurkusa da Yeriko. 13 Musa, da Eliyeza firist, da dukkan shugabannin jama'a suka fito domin su tarye su a wajen sansani. 14 Amma Musa ya yi haushi da shugabannin rundunar, kwamandojin na dubbai da kuma na ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga yaƙi. 15 Musa yace masu, "Kun bar dukkan matayen su rayu ko? 16 Duba, waɗannan mataye sun jawo wa mutanen Isra'ila, ta wurin shawarar Bala'am, su aikata zunubi ga Yahweh ga zancen Feyor, yayinda annoba ta bazu cikin mutanen Yahweh. 17 Yanzu fa, sai ku kashe kowanne namiji cikin dukkan ƙananan, ku kuma kashe kowacce macen da ta taɓa kwana da namiji. 18 Amma ku ɗaukar wa kanku dukkan 'yan matan da ba su taɓa kwana da namiji ba. 19 Dole ku yi sansani can a wajen sansani na Isra'ila har na kwana bakwai. Dukkan ku da kuka kashe wani da kuma ko kuka taɓa duk wani matacce -dole ku tsarkake kanku a rana ta uku a rana ta bakwai kuma- ku da bayinku. 20 Dole ku tsarkake kowacce tufa da kowanne abin da aka yi da fatar dabba da gashin akuya, da kuma kowanne abin da aka yi da itace." 21 Sai Eliyeza yace da sojoji waɗanda suka tafi yaƙi, "Wannan shi ne umarnin shari'a da Yahweh ya bayar ga Musa: 22 Zinariyar, da azurfa, da jangaci, da tama, da kuza, da dalma, 23 da kuma kowanne abin da ya jimre ma wuta, sai ka saka shi ta wurin wuta, za shi kuma yi tsabta. Dole daga nan ka tsarkake waɗannan abubuwa da ruwan tsarkakewa. Duk abin da ba za shi shiga ta wuta ba sai ka tsarkake da ruwa. 24 Dole ku wanke tufafinku a rana ta bakwai, daga nan zaku zama da tsabta. Daga nan kuna iya shigowa cikin sansanin Isra'ila." 25 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce, 26 "Ka ƙirga dukkan abin ganimar da aka kawo, da mutane da dabbobi. Kai, da Eliyeza firist, da kuma shugabanni na gidajen ubanni na mutane 27 za a raba ganimar gida biyu. Ka raba a tsakanin sojojin da suka tafi yaƙi da kuma dukkan sauran mutanen. 28 Sa'an nan za ka sa a karɓi haraji domina daga wurin sojojin da suka tafi yaƙi. Wannan harajin dole ya zama ɗaya daga cikin kowanne ɗari biyar, ko na mutane, ko na dabbobi, ko na jakuna, ko na awakai, ko tumakai. 29 Ka ɗauki wannan haraji daga rabinsu ka kuma bada su ga Eliyeza firist abin baikon da za a miƙa gare ni. 30 Haka kuma daga rabin mutanen Isra'ila, sai ka karɓi ɗaya daga cikin kowanne hamsin - daga wurin mutane, ko shanu, ko jakai, ko awakai, da kuma tumaki. Ka miƙa su ga Lebiyawa ma su lura da mazamnina. 31 Sai Musa da Eliyeza firist suka yi kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 32 To yanzu dai ganimar da ta rage daga cikin abin da sojojin suka ɗauka su ne tumaki 675,000, 33 shanu dubu saba'in da biyu, 34 jakuna dubu sittin da ɗaya, 35 da kuma 'yan mata dubu talatin da biyu waɗanda ba su taɓa kwana da wani namiji ba. 36 Rabin da aka ajiye domin sojoji tumaki 337,000 ne. 37 Tumaki waɗanda suke na Yahweh kuma 675 ne. 38 Shanu dubu talatin da shida ne waɗanda harajin Yahweh saba'in da biyu ne. 39 Jakunan 30,500 ne, waɗanda daga ciki na Yahweh sittin da ɗaya ne. 40 Mutum dubu sittin ne daga ciki kuwa na harajin Yahweh talatin da biyu ne. 41 Sai Musa ya ɗauki harajin da za a miƙa ta baiko ga Yahweh. Ya bayar ga Eliyeza firist, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. 42 Game da rabi na mutanen Isra'ila waɗanda Musa ya karɓa daga sojojin da suka tafi yaƙi - 43 rabi na mutane kuwa, tumaki 337,500 ne, 44 shanu dubu sittin ne, 45 jakai 30,500 ne, 46 mata kuma dubu sha shida. 47 Daga cikin rabi na mutanen Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga kowanne hamsin, da na mutane da kuma dabbobi. Ya bayar da su ga Lebiyawa waɗanda ke lura da mazaunin Yahweh, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi. 48 Sai shugabannin runduna, da na dubu dubu da kuma na bisa ɗari ɗari, suka zo wurin Musa. 49 Suka ce masa, "Bayinka sun lisafta sojojin dake a ƙarƙashinsu, kuma babu mutum ɗaya da ya ɓace. 50 Mun kawo baiko na Yahweh, abin da kowanne mutum ya samu, kayayyakin ado na zinariya, ƙarafu na ƙafa da na hannu, zoben hannu, da zoben kunne, da kayan ado na wuya, domin a yi kafara domin mu kanmu a gaban Yahweh." 51 Sai Musa da Eliyeza firist suka karɓa daga garesu zinariyar da dukkan kayayyaki na aikin gwaninta. 52 Dukkan baiko na zinariya da suka miƙa ga Yahweh - baye-baye daga shugabanni na dubbai daga kuma shugabanni na ɗari ɗari - an auna shekel 16,750. 53 Kowanne soja ya ɗauki ganima, kowanne mutum domin kansa. 54 Musa da Eliyeza firist suka karɓi zinariyar daga shugabanni na dubbai da na ɗari ɗari. Suka kai zuwa cikin alfarwa ta taruwa domin tunawa ta mutanen Isra'ila ga Yahweh.

Sura 32

1 A wannan lokacin zuriyar Ruben da ta Gad suna da garkunan shanu masu yawan gaske. Da suka lura cewa ƙasar Yaza da Giliyad, ƙasa ce mai kyaun gaske domin kiwon shanu. 2 Saboda haka zuriyar Gad da ta Ruben suka zo suka yiwa Musa magana, ga Eliyeza firist, ga kuma shugabannin jama'a. Suka ce, 3 "Ga lissafin wuraren da muka yi bincike: Atarot, Dibon, Yaza, Nimra, da Heshbon, Eliyele, Sebam, Nebo, da kuma Beyon. 4 Waɗannan su ne ƙasashen da Yahweh ya yaƙa a gaban shugabannin Isra'ila, kuma suna da kyau domin kiwon shanu. Mu, bayinka muna da shanu masu yawa." 5 Suka ce, "Idan mun sami tagomashi a wurinka, bari a bamu wannan ƙasa, mu bayinka, abin mallaka. Kada a ƙetare Yodan da mu." 6 Sai Musa ya amsa wa zuriyar Gad da ta Ruben, "To 'yan'uwanku sun tafi yaƙi, ku kuma kwa zauna a nan? 7 Don me kuke karya zuciyar mutanen Isra'ila daga shiga cikin ƙasar alƙawarin da Yahweh ya ba su? 8 Haka ubanninku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh Barniya su yi duban ƙasa. 9 Suka tafi zuwa kwarin Eshkol. Suka ga ƙasar amma suka karya zukatan mutanen Isra'ila har da ba su yarda su shiga ƙasar da Yahweh ya basu ba. 10 Fushin Yahweh ya yi ƙuna a wannan rana. Ya kuma yi rantsuwa ya ce, 11 'Hakika babu wani daga cikin mazajen da suka fito daga cikin Masar, daga mai shekara ashirin da fiye da haka, da zai ga ƙasa wadda na yiwa Ibrahim, da Yakubu, da Ishaku alƙawari, domin basu bi ni da dukkan yadda ya kamata ba, sai dai 12 Kaleb ɗan Yefunne Bakeniziye, da kuma Yoshuwa ɗan Nun. Kaleb da Yoshuwa kaɗai suka bi ni yadda ya kamata.' 13 Fushin Yahweh kuma ya yi ƙuna a bisa Isra'ila. Ya sa suka yi watangaririya a cikin jeji na tsawon shekaru arba'in har sai da wannan tsãra ta waɗanda suka aikata wannan mugunta a fuskarsa suka hallaka. 14 Duba, kun tashi a cikin mazaunin ubanninku, haka kuma kuke mazaje masu zunubi, domin ku daɗa fushin Allah mai ƙuna gãba da Isra'ila. 15 Idan kuka juya daga binsa, shi kuma zai ƙara barinsu a cikin jeji, ku kuma da kun gama hallaka dukkan mutanen nan." 16 Sai suka zo wurin Musa suka kuma ce, "Ka barmu mu gina ganuwa ta shimge a nan domin dabbobinmu da kuma birane domin iyalanmu. 17 Duk da haka, mu da kanmu za mu shirya mu ɗauki makamai mu tafi tare da rundunar Isra'ila har sai mun tafi da su zuwa wurarensu. Amma iyalanmu za su zauna a birane masu ganuwa saboda sauran mutanen dake zama cikin ƙasar. 18 Ba zamu dawo ba har sai dukkan mutanen Isra'ila kowa ya karɓi gãdonsa. 19 Ba zamu ci gãdon ƙasan tare da su a ƙetaren Yodan ba, domin gãdonmu na a nan yamma da Yodan." 20 Sai Musa ya amsa masu, "Idan kuka yi abin da kuka faɗa, idan kuka ɗauki makamai don ku wuce gaban Yahweh don yaƙi, 21 don haka kowanne mutum daga cikin mayaƙanku za shi ƙetare Yodan a gaban Yahweh, har sai ya kori maƙiyansa daga gabansa, 22 ƙasar kuma a ci mulkinta a gabansa. Sa'an nan daga baya ku komo. Za ku zama marasa laifi a gaban Yahweh da kuma wurin Isra'ila. Wannan ƙasa za ta zama abin mallaka a gaban Yahweh. 23 Amma idan ba ku yi haka ba, duba, da ko za ku yi wa Yahweh zunubi. Ku kuma san da cewa lallai za a bayyana zunubinku a fili. 24 Ku gina birane domin iyalanku, shimgayen kuwa domin dabbobinku; sai ku yi abin da kuka faɗi." 25 Sai zuriyar Gad da na Ruben suka yi magana da Musa suka kuma ce, "Bayinka za su yi kamar yadda kai, shugabanmu, ka umarta. 26 Da ƙanananmu, da matayenmu, da garkunan tumakinmu, da dukkan shanunmu za su zauna can cikin biranen Giliyad. 27 Amma, mu, bayinka, za mu ƙetare a gaban Yahweh zuwa ga yaƙi, kowanne mutum a shirye domin yaƙi, yadda kai, ubangidanmu, ka faɗi." 28 Don haka sai Musa ya yi umarni game da su zuwa ga Eliyeza firist, zuwa ga Yoshuwa ɗan Nun, da kuma zuwa ga shugabanni na ubannin kabilun mutanen Isra'ila. 29 Musa yace masu, "Idan zuriyar Gad da na Ruben suka ƙetare Yodan tare da ku, kowanne mutum da ya yi shirin yaƙi a gaban Yahweh, idan kuwa aka sarayyar da ƙasar a gabanku, to, sai ku ba su ƙasar Giliyad abin mallaka. 30 Amma idan har basu ƙetare da ku da shirin yaƙi ba, don haka za su sami ta su mallakar tare da ku a cikin ƙasar Kan'ana." 31 Sai zuriyar Gad da ta Ruben suka amsa suka ce, "Kamar yadda Yahweh ya faɗa mana, mu bayinka, wannan ita za mu yi. 32 Za mu ƙetare da shirin yaƙi a gaban Yahweh zuwa cikin ƙasar Kan'ana, amma namu gãdon mallakar za su zauna da mu a wannan sashe na Yodan." 33 Don haka ga zuriyar Gad da na Ruben, da kuma ga rabin kabilar Manasse ɗan Yosef, Musa ya ba su masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da na Og, sarkin Bashan. Ya ba su ƙasar, ya kuma raba masu dukkan biranenta da iyakokinta, da biranen dake kewaye da su. 34 Sai zuriyar Gad suka sãke gina Dibon, Atarot, Arowa, 35 da Atrot Shofan, Yaza, Yogbeha, 36 Bet Nimra, da Bet Haran birane masu ganuwa da shimgaye domin tumaki. 37 Zuriyar Ruben kuma suka gina Heshbon, da Eleyale, da Kiriyatayim, 38 da Nebo, da Ba'al Meyon - daga baya aka canza sunayensu, da kuma Sibma. Suka bada wasu sunaye ga biranen da suka sãke ginawa. 39 Zuriyar Makir ɗan Manasse ya tashi ya tafi Giliyad, ya kuma ɗauke ta daga Amoriyawa waɗanda ke cikinta. 40 Sai Musa ya bãda Gilyad ga Makir ɗan Manasse, mutanen sa kuma suka zauna nan. 41 Yayir ɗan Manasse ya tashi ya tafi ya ci garuruwanta, ya kuma kira su da suna Habbot Yayir. 42 Noba ya tafi ya kuma cinye Kenat da kauyukanta, ya kuma kirata da suna Noba, bisa ga sunansa.

Sura 33

1 Waɗannan su ne zangon mutanen Isra'ila bayan da suka bar ƙasar Masar da runduna bayan runduna a ƙarƙashin shugabancin Musa da Haruna. 2 Musa ya rubuta duk inda suka baro da inda suke kaiwa, yadda Yahweh ya umarta. Ga yadda zangon suka kasance, tashi bayan tashi. 3 Suka yi tafiya daga Ramesis cikin wata na farko, da suka taso a rana ta sha biyar ga wata na farko. Da safe bayan Bikin ‌Ƙetarewa, sai mutanen Isra'ila suka fito a fili, dukkan Masarawa na gani. 4 Wannan ya faru ne sa'ad da Masarawa ke binne dukkan 'ya'yan farinsu matattu, waɗanda Yahweh ya kashe a cikinsu, gama ya kawo hukunci a bisa allolinsu. 5 Sai mutanen Isra'ila suka tashi daga Ramesis suka kuma yi zango a Sukkot. 6 Suka tashi daga Sukkot suka yi zango a Etam, a gacin jejin. 7 Suka tashi daga Etam suka juya baya zuwa Fi Hahirot, wadda take kallon Ba'al Zefon, inda suka yi zango fuska da fuskar Migdol. 8 Sai suka shirya tashi domi tafiya daga gaban Fi Hahirot suka kuma wuce ta tsakiyar teku zuwa cikin jeji. Sun yi tafiyar kwana uku zuwa cikin jejin Etam suka kuma yi zango a Mara. 9 Suka shirya tafiya daga Mara suka kuma isa Elim. A Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa da kuma itatuwan dabino. A nan ne suka kafa zango. 10 Sai suka tashi daga Elim suka kafa zango a bakin Tekun Iwa. 11 Sai suka tashi daga bakin Tekun Iwa suka yi zango a cikin jejin Sin. 12 Suka tashi daga jejin Sin suka yi zango a Dofka. 13 Suka tashi daga Dofka suka kuma yi zango a Alush. 14 Suka tashi daga Alush suka yi zango a Refidim, inda ba a sami ruwan da mutane zasu sha ba. 15 Suka tashi daga Rafidim suka yi zango a cikin jejin Sinai. 16 Suka tashi daga jejin Sinai suka kuma yi zango a Kibrot Hattaba. 17 Suka tashi daga Kibrot Hattaba suka yi zango a Hazerot. 18 Suka tashi daga Hazerot suka kuma yi zango a Ritma. 19 Suka tashi daga Ritma suka kuma yi zango a Rimmon Ferez. 20 Su ka tashi daga Rimmon Ferez suka kuma yi zango a Libna. 21 Suka tashi daga Libna suka kuma yi zango a Rissa. 22 Suka tashi daga Rissa suka kuma yi zango a Kehelata. 23 Suka tashi daga Kehelata suka kuma yi zango a Tsaunin Shefa. 24 Suka tashi daga Tsaunin Shafa suka yi zango a Harada. 25 Suka tashi daga Harada suka kuma yi zango a Makhelot. 26 Suka tashi daga Makhelot suka yi zango a Tahat. 27 Suka tashi daga Tahat suka kuma yi zango a Tera. 28 Suka tashi daga Tera suka kuma yi zango a Mitka. 29 Suka tashi daga Mitka suka kuma yi zango a Hashmona. 30 Suka tashi daga Hashmona suka kuma yi zango a Moserot. 31 Suka tashi daga Moserot suka kuma yi zango a Bene Ya'akan. 32 Suka tashi daga Bene Ya'akan suka kuma yi zango a Hor Haggidgad. 33 Suka tashi daga Hor Haggidgad suka kuma yi zango a Yotbata. 34 Suka tashi daga Yotbata suka kuma yi zango a Abrona. 35 Suka tashi daga Abrona suka kuma yi zango a Ezion Geba. 36 Suka tashi daga Ezion Geba suka kuma yi zango a cikin jejin Zin a Kadesh. 37 Suka tashi daga Kadesh suka kuma yi zango a Tsaunin Hor, a bakin iyakar ƙasar Idom. 38 Sai Haruna firist ya haura bisa Tsaunin Hor ga umarnin Yahweh ya kuma mutu can a cikin shekara ta arba'in bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar, a cikin wata na biyar, a rana ta farko ga watan. 39 Haruna na da shekaru 123 lokacin da ya mutu a Tsaunin Hor. 40 Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda ke zama cikin kudancin jeji a ƙasar Kan'ana, ya ji game da isowar mutanen Isra'ila. 41 Suka tashi daga Tsaunin Hor suka kuma yi zango a Zalmona. 42 Suka tashi daga Zalmona suka kuma yi zango a Funon. 43 Suka tashi daga Funon suka kuma yi zango a Obot. 44 Suka tashi daga Obot suka kuma yi zango a Iye Abarim, a bakin iyakar Mowab. 45 Suka tashi daga Iye Abarim suka kuma yi zango a Dibon Gad. 46 Suka tashi daga Dibon Gad suka kuma yi zango a Almon Diblatayim. 47 Suka tashi daga Almon Diblatayim suka kuma yi zango a cikin duwatsu na Abarim, fuska da Nebo. 48 Suka tashi daga duwatsun na Abarim suka kuma yi zango a cikin kwarrurukan Mowab a bakin Yordnn a Yeriko. 49 Suka yi zango a bakin Yodan, daga Bet Yeshimot zuwa Abel Shittim cikin filayen Mowab. 50 Yahweh ya yi magana da Musa a cikin filayen Mowab a bakin Yodan a Yeriko ya kuma ce, 51 "Ka yi magana da 'ya'yan Isra'ila ka kuma ce masu, 'Yayin da kuka ƙetare Yodan zuwa cikin ƙasar Kan'ana, 52 dole ne ku kori dukkan mazauna ƙasar daga gareku. Dole ku hallakar da dukkan sassaƙaƙƙun siffofinsu. Dole ku hallakar da siffofinsu na zubi ku kuma farfasa dukkan tuddan wurarensu. 53 Dole ku mallaki ƙasar ku kuma zauna cikinta, domi na baku ƙasar abin mallaka. 54 Dole ne ku yi gãdon ƙasar yanki-yanki, bisa ga kowacce kabila. Dole ne ku bada yanki mai girma zuwa kabilar da tafi kowacce kabila, ga kabila mafi ƙanƙata kuwa ƙaramin yankin ƙasar. Duk sa'ad da yankin ya fãɗa ga kowacce kabila, wannan ƙasa zata zama tata. Za ku gãji ƙasar bisa ga kabilar ubanninku. 55 Amma idan baku kori mazaunan ƙasar a gaban ku ba, sa'an nan mutanen da kuka bari su tsaya, za su zama maku kamar wani abu cikin idanunku da kuma ƙaya a kwiɓinku. Za su wahalshe da rayukanku cikin ƙasar da kuka zauna. 56 Sa'an nan zai zama kuma duk abin da na yi niyyar yi wa waɗannan mutanen, zan yi maku shi."'

Sura 34

1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila ka kuma ce ma su, 'Sa'ad da kuka shiga cikin ƙasar Kan'ana, ƙasar da zata zama taku, ƙasar Kan'ana da iyakokinta, 3 iyakarku daga yamma zata kai har cikin jejin Zin kusa da iyakar Idom. Gabashin ƙarshe na yamma za shi zama kan layin da ya kai ƙarshe a yammancin ƙarshe na Tekun Gishiri. 4 Iyakarku zata juya zuwa yamma daga dutsen Akrabbim ta wuce ta jejin Zin. Daga nan, zata tashi zuwa gabas da Kadesh Baniya har ta kai Harza Adda zuwa ga Azmon. 5 Daga nan, iyakar zata juya daga Azmon zuwa wajen rafin Masar ta kuma bi zuwa teku. 6 Iyaka ta Kudu za ta zama kan iyakar Babban Teku. Wannan zai zama iyaka gareku ta yammanci. 7 Iyakarku ta Arewa zata tashi daga kan layin da zaku sa alama daga Babban Teku zuwa Tsaunin Hor, 8 daga Tsaunin Hor zuwa Lebo Hamat, daga nan zuwa Zedad. 9 Daga nan iyakar zata ci gaba zuwa Zifuron ta tsaya a Hazar Enan. Wannan zata zama iyakarku ta arewa. 10 Zaku saka alama mai nuna iyakarku ta gabas daga Hazar Enan kudu da Shefam. 11 Daga nan iyaka ta gabas za ta kai daga Shefam zuwa Ribla, gabas da Ain. Iyakar za ta gangaro ta wajen gabas gefen Teku na Kinneret. 12 Iyakar kuma za ta gangaro zuwa ga Kogin Yodan zuwa ga Tekun Gishiri ta kuma gangaro zuwa iyaka ta gabashin Tekun Gishiri. Wannan za ta zama ƙasarku, da dukkan iyakokinta dake zagaye da ita. 13 Sai Musa ya umarci mutanen Isra'ila ya ce, "Wannan ce ƙasar da zaku yi gãdonta ta wurin rabo, wanda Yahweh ya umarta a bayar ga sauran kabilu tãre da kuma rabin kabilar. 14 Kabila ta zuriyar Ruben, bisa ga rabon gãdo ga ubannin kabilunsu, da kuma kabila ta zuriyar Gad, bisa ga rabon gãdo ga ubannin kabilunsu, da kuma rabin kabilar Manasse dukkansu suka karɓi tasu ƙasar. 15 Kabilun biyu da kuma rabin kabilar suka karɓi tasu gãdon na ƙasar a ƙetaren Yodan a sashen Gabashin Yeriko, wajen fitar rana." 16 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 17 "Ga sunayen mazajen da zasu raba maku ƙasar domin gãdonku: Eliyeza firist da kuma Yoshuwa ɗan Nun. 18 Za ku zaɓi shugaba daga kowanne kabila don ya raba ƙasar domin zuriyarsu. 19 Ga sunayen mazajen: Daga kabilar Yahuda, Kaleb ɗan Yefunne. 20 Daga kabilar zuriyar Simiyon, Shemuwel ɗan Ammihud. 21 Daga kabilar Benyamin, Elidad ɗan Kislon. 22 Daga kabila ta zuriyar Dan aka sami shugaba, Bukki ɗan Yogli. 23 Daga cikin zuriyar Yosef, daga kabila ta zuriyar Manasse shugaba, Hanniyel ɗan Efod. 24 Daga kabila ta zuriyar Ifraim aka sami shugaba, Kemuwel ɗan Shiftan. 25 Daga kabila ta zuriyar Zebulun aka sami shugaba, Elizafan ɗan Farnak. 26 Daga kabila ta zuriyar Issaka aka sami shugaba, Faltiyel ɗan Azzan. 27 Daga kabila ta zuriyar Asha aka sami shugaba, Ahihu ɗan Shelomi. 28 Daga kabila ta zuriyar Naftali aka sami shugaba, Fedahel ɗan Ammihud." 29 Yahweh ya umarci waɗannan mutanen su raba ƙasar Kan'ana su kuma raba wa kowanne kabila na Isra'ila gãdonsu.

Sura 35

1 Yahweh ya yi magana da Musa a kwarin Mowab kusa da Yodan a Yeriko ya kuma ce, 2 "Ka umarci jama'ar Isra'ila su baiwa Lebiyawa kaɗan daga gãdonsu na ƙasar. Zasu basu birane su zauna ciki da kuma wuraren kiwo zagaye da waɗannan birane. 3 Su Lebiyawan zasu sami waɗannan biranen su zauna a ciki. Wuraren kiwon za su zama domin garkunansu na shanu, da na tumaki, da na dukkan dabbobinsu. 4 Wuraren kiwon zagaye da birnin da zaku baiwa Lebiyawan zai tashi daga bangon birnin kãmu dubu ɗaya a kowanne sashi. 5 Dole ka auna kãmu dubu biyu daga wajen birnin a sashen gabas, kãmu dubu biyu zuwa sashen kudu, kãmu dubu biyu zuwa sashen yamma, kãmu dubu biyu kuma zuwa ga sashen arewa. Wannan za shi zama wuraren kiwo domin biranensu. Biranen zasu kasance a tsakiya. 6 Birane shida da zaku ba Lebiyawa zasu zama biranen mafaka. Zaku ku yi tanadin waɗannan wurare domin duk wanda ya kashe wani na iya guduwa can. Haka kuma za ku yi tanadin wasu birane arba'in da takwas. 7 Biranen da zaku bai wa Lebiyawa gaba ɗaya zai zama arba'in da takwas. Dole ku basu tare da wuraren kiwonsu. 8 Manyan kabilu na jama'ar Isra'ila, kabilar da take da yawan ƙasa, zata tanada birane fiye da kowa. 'Yar ƙaramar kabila kuwa zata tanadi birane kaɗan. Kowacce kabila zata tanada wa Lebiyawa dai-dai bisa ga gãdon da ta karɓa. 9 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 10 "Ka yi magana da 'ya'yan Isra'ila ka ce masu, 'Idan kuka ƙetare Yodan zuwa ƙasar Kan'ana, 11 sa'an nan zaku zaɓi birane su zama biranen mafaka dominku, wurin da idan mutum ya kashe wani ba da gangan ba, yana iya guduwa can. 12 Waɗannan biranen zasu zama mafakarku daga mai ramako, domin kada a kashe mai kisa ba tare da ya gurfana gaban shari'a a gaban jama'ar ba. 13 Za ku zaɓi birane shida a matsayin birnin mafaka. 14 Dole ku shirya birane uku a ƙetaren Yodan, uku kuma a cikin ƙasar Kan'ana. Za su zama birane na mafaka. 15 Domin jama'ar Isra'ila, domin baƙi, domin kowanne mai zama tare da ku, waɗannan birane shida zasu zama maku mafaka ga duk wanda ya kashe wani ba da gangan ba yana iya gudu can. 16 Amma idan mutumin mai kisan ya bugi wani da ƙarfe, idan kuma mutumin ya mutu, to mutumin tabbas mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi. 17 Idan wani mutum ya bugi wani da dutse cikin hannunsa dake iya kashe wani, idan kuma mutumin ya mutu, to tabbas wannan mutumin mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi. 18 Idan mutum mai kisa ya bugi wani mutum da makami na sanda dake iya kashe wani mutumin, idan kuma mutumin ya mutu, to tabbas wannan mutumin mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi. 19 Mai ramakon jini zai kashe mai kisan. Idan ya same shi, mai ramakon jini sai ya kashe shi. 20 Idan ya bugi wani da ƙiyayya ko ya wurga masa wani abu, yayin da yake ɓuya domin ya yi masa kwanto, har mutumin ya mutu, 21 ko idan ya buge shi ƙasa da ƙiyayya da hannunsa har mutumin ya mutu, to mai kisan da ya buge shi dole za a kashe shi. Shi mai kisan kai ne. Mai ramakon jini na iya kashe mai kisan kan idan ya gãmu da shi. 22 Amma idan mutumin mai kisan ya bugi wani nan da nan ba tare da ya shirya ƙiyayya ko ya wurga wani abin da ya buge shi ba tare da ya yi niyar yin hakan ba 23 ko ya wurga dutsen dake iya kashe shi ba tare da ya gan shi ba, don haka mai kisan bai zama maƙiyin sa ba; ba ƙoƙarin cutar da mutumin ya yi ba. Amma ga abin da za a yi idan mutumin ya mutu har wa yau. 24 Idan haka ne, jama'ar zasu yi shari'a tsakanin mai kisan da mai ramakon jinin da waɗannan sharuɗa. 25 Jama'ar zasu kuɓutar da mai kisan daga ikon mai ramakon jinin. Su jama'ar zasu komo da mai kisan kan zuwa birnin ramakon wanda asali ya guje daga gare shi. Za ya zauna a wurin har sai bayan mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai-tsarki. 26 Amma idan mai kisan ya fita daga iyakar birnin mafakan da ya gudu zuwa gare ta, 27 idan kuma mai ramakon jini ya gamu da shi a wajen iyakar birninsa na mafaka, idan kuma ya kashe mutumin mai kisan, mai ramakon jini ba zai zama mai laifi game da kisan kai ba. 28 Dalili kuwa shi ne mutumin mai kisan kai da bai fito daga cikin birnin mafaka ba har sai babban firist ya mutu. Bayan mutuwar babban firist, mai kisan kan na iya komawa ƙasarsa inda gãdonsa yake. 29 Waɗannan dokokin zasu zama maku farillai dominku cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan inda kuka zauna. 30 Duk wanda ya kashe wani, za a kashe mai kisan, kamar yadda aka yi shaida daga shaidu. Amma shaidar mutum ɗaya baza ta iya sa a kashe mutum ba. 31 Haka kuma, ba zaku karbi ɗiyya domin ran mai kisa wanda aka iske shi da laifin kisa ba. Dole a kashe shi. 32 Ba zaku karbi ɗiyya domin wanda ya gudu zuwa birnin mafaka ba. Da haka ba zaku yardar ma sa ya zauna bisa gãdonsa ba har sai babban firist ya mutu. 33 Kada ku ƙazantar da wannan ƙasar da kuke zama a cikinta ta yin haka, gama jinin da aka zubar ta hanyar kisa na ƙazantar da ƙasa. Babu kafarar da za a iya yi domin ƙasar yayin da aka zubar da jini bisanta, sai dai da jinin shi wanda ya zubas da jinin. 34 Don haka baza ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama cikinta ba domni ina zama cikinta. Ni, Yahweh, ina zaune cikin mutanen Isra'ila."'

Sura 36

1 Sa'an nan shugabanni na gidajen kakannin iyalai na zuriyar Giliyad ɗan Makir (wanda shi ne ɗan Manasse), waɗanda suke daga zuriyar Yusufu, suka iso suka yi magana da Musa da a gaban shugabanni waɗanda ke kan gaba daga gidajen kakanni na mutanen Isra'ila. 2 Suka ce, "Yahweh ya umarce ka, ubangidanmu, ka bada rabon ƙasa bisa ga ƙuri'a ga mutanen Isra'ila. Yahweh ya umarce ka da ka bada rabon Zelofehad ɗan'uwanmu ga 'ya'yansa mata. 3 Amma idan 'ya'yansa mata suka yi aure zuwa wata ƙabilar mutanen Isra'ila, sai gãdonsu na ƙasa a cire daga gãdon dake na ubanninmu. Za a ƙara bisa gãdon dake na ƙabilar da dã suka shiga. Don haka, za a cire daga namu gãdon. 4 Don haka, idan shekarar Yubili na mutanen Isra'ila ta zo, sai a harɗa gãdonsu da gãdon kabilar da suka yi aure. Ta haka, za a cire gãdonsu daga gãdon kabilar kakanninmu." 5 Sai Musa ya ba da umarni ga mutanen Isra'ila, bisa ga maganar Yahweh. Ya ce, "Abin da kabilar zuriyar Yosef suka ce dai-dai ne. 6 Wannan ne abin da Yahweh ya faɗa game da 'ya'ya mata na Zelofehad. Ya ce, 'Bari su auri duk wanda ya yi masu dai-dai, amma dole ne su yi aure daga cikin zuriyar iyalin mahaifinsu.' 7 Kada a canza gãdon wata kabilar mutanen Isra'ila zuwa ga wata kabilar. Duk mutumin Isra'ila dole ya ci gaba da zama da nasa gãdo na kabilar ubanninsa. 8 Kowacce ɗiya ta mutanen Isra'ila wadda take da gãdo cikin kabilarta za ta auri wani daga zuriyar mahaifinta. Wannan zai zama haka domin dukkan mutanen Isra'ila su ajiye abin gãdonsu daga ubanninsu. 9 Babu gãdon da za a ɗauka daga kabila ɗaya zuwa wata kabilar. Kowacce kabila ta mutanen Isra'ila za ta riƙe nata abin gãdon. 10 Sai 'ya'ya ɗiyan Zelofehad suka aikata kamar yadda Yahweh ya umarce Musa. 11 Mahal, Tirza, Hogla, Milka, da Nowa, 'ya'ya mata na Zelofehad, suka auri zuriyar Manasse. 12 Suka yi aure cikin dangin iyalin Manasse ɗan Yosef. Ta haka, gãdonsu ta kasance tare da kabilar da mahaifinsu ya fito. 13 Waɗannan su ne umarnai da shari'un da Yahweh ya bai wa mutanen Isra'ila ta bakin Musa a cikin kwarurukan Mowab a bakin Yodan a Yeriko.

Littafin Maimaitawar Shari'a
Littafin Maimaitawar Shari'a
Sura 1

1 Waɗannan ne maganganun da Musa ya gaya wa dukkan Isra'ila a ƙetaren Yodan a cikin jeji, a sararin kwarin Kogin Yodan daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da kuma Di Zahab. 2 Tafiyar kwana sha ɗaya ce daga Horeb ta hanyar Dutsen Seyir zuwa Kadesh Barniya. 3 Ya kasance a shekara ta arba'in, a wata na sha ɗaya, a kan ranar farko na watan, Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila, yana gaya masu dukkan abin da Yahweh ya umarce shi game da su. 4 Wannan kuwa bayan da Yahweh ya kai hari ga Sihon sarkin Amoriyawa ne, wanda ke zama a Heshbon, da Og sarkin Bashan, wanda ke zama a Ashtarot a Edrayi. 5 A ƙetaren Yodan, ƙasar Mowab, Musa ya fara sanar da waɗannan umarnai, cewa, 6 "Yahweh Allahnmu ya yi magana da mu a Horeb, cewa, 'Dogon zaman da kuka yi a wannan ƙasar tudu ya isa. 7 Ku juya ku kama tafiyarku, ku kuma tafi ƙasar tudu ta Amoriyawa da dukkan wurare kusa da sararin kwarin Kogin Yodan, a cikin ƙasar tudu, a cikin ƙasar kwari, a cikin Negeb, da bakin teku - ƙasar Kan'aniyawa, da cikin Lebanon har ya zuwa babban kogi, wato Yufiretis. 8 Duba, na sanya ƙasar a gaban ku; ku tafi ciki ku kuma mallaki ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku - ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu - ya basu da kuma zuriyarsu a bayansu.' 9 Na yi magana da ku a wancan lokacin, cewa, 'Bazan iya ɗaukarku da kaina ni kaɗai ba. 10 Yahweh Allahnku ya riɓanɓanya ku, kuma, duba, a yau kun riɓanɓanyu kamar taurarin sama. 11 Bari Yahweh, Allahn ubanninku, ya maida ku fiye da yadda kuke sau dubu, ya kuma albarkace ku, kamar yadda ya yi maku alƙawari! 12 Amma ta yaya ni da kaina ni kaɗai zan ɗauki nawayoyinku, karkiyoyinku, da saɓananku? 13 Ku ɗauki mutane masu hikima, mutane masu fahimta, da mutane masu kyakkyawar shaida daga kowacce kabila, zan kuma sanya su shugabanni a bisan ku.' 14 Kuka amsa mani kuka ce, ' Abin da ka faɗa ya yi mana kyau mu yi.' 15 Sai na ɗauki shugabanni daga cikin kabilunku, mutane masu hikima, mutane kuma masu kyakkyawar shaida, na kuma mai da su shugabanni a bisan ku, hafsoshin dubbai, hafsoshin ɗaruruwa, hafsoshin hamsin-hamsin, hafsoshin goma-goma, da ofisoshi, kabila bayan kabila. 16 Na umarci alƙalanku a wancan lokaci, cewa, 'Ku saurari saɓanai tsakanin 'yan'uwanku, ku kuma yi hukuncin adalci tsakanin mutum da ɗan'uwansa, da bãre wanda ya ke tare da shi. 17 Ba zaku nuna sonkai ga kowa ba a cikin saɓani; zaku saurari ƙarami da babba bai ɗaya. Ba zaku ji tsoron fuskar mutum ba, domin hukuncin na Allah ne. Saɓanin da yafi ƙarfinku, zaku kawo a gare ni, zan kuma saurare shi.' 18 Na umarce ku a wancan lokaci dukkan abubuwan da zaku yi. 19 Muka yi tafiyarmu daga Horeb muka kuma tafi ta cikin dukkan babban jeji da ban razana da kuka gani, a kan hanyarmu ta zuwa ƙasar tudu ta Amoriyawa, kamar yadda Yahweh Allahnmu ya umarce mu; kuma muka zo Kadesh Barniya. 20 Na ce maku, 'Kun zo ƙasar tudu ta Amoriyawa, wadda Yahweh Allahnmu ya ke bamu. 21 Duba, Yahweh Allahnku ya sanya ƙasar a gaban ku; ku tafi, ku mallaketa, kamar yadda Yahweh, Allah na ubanninku, ya faɗi maku; kada ku ji tsoro, ko ku karaya.' 22 Kowannenku ya zo gare ni ya kuma ce, 'Bari mu aika da mutane gaba da mu, saboda suyi binciken ƙasar domin mu, su kuma kawo mana magana game da hanyar da zamu bi mu kai hari, game kuma da biranen da zamu je.' 23 Shawarar ta gamshe ni sosai; na ɗauki mutanenku sha biyu, mutum ɗaya domin kowacce kabila. 24 Suka juya suka tafi zuwa cikin ƙasar tudu, suka isa kwarin Eshkol, suka kuma yawace shi. 25 Suka ɗauko daga cikin amfanin ƙasar a cikin hannuwansu, suka kuma kawo mana. Suka kuma kawo mana magana suka kuma ce, '‌Ƙasa ce mai kyau da Yahweh Allahnmu ya ke bamu.' 26 Duk da haka kuka ƙi kai hari, amma kuka yi tawaye gãba da dokar Yahweh Allahnku. 27 Kuka yi gunaguni a rumfunanku kuka kuma ce, "Saboda Yahweh ya ƙi mu ne ya fito da mu daga ƙasar Masar, ya bayar da mu cikin hannun Amoriyawa su hallaka mu. 28 Ina zamu iya zuwa yanzu? 'Yan'uwanmu sun sa zuciyarmu ta narke, cewa, 'Waɗannan mutane masu girma ne da tsayi fiye da mu; biranensu kuma manya ne kuma da garu har cikin sammai; bugu da ƙari, munga 'ya'ya maza na Anakim a wurin."' 29 Daganan nace maku, 'Kada ku firgita, ko ku ji tsoronsu. 30 Yahweh Allahnku, wanda ya ke tafiya a gaban ku, zai yi yaƙi domin ku, kamar dukkan abin da ya yi domin ku a Masar, a gaban idanunku, 31 da kuma a cikin jeji, inda kuka ga yadda Yahweh Allahnku ya ɗauke ku, kamar yadda mutum ke ɗaukar ɗansa, dukkan inda kuka tafi har sai da kuka zo wannan wuri.' 32 Amma duk da wannan magana baku gaskata da Yahweh Allahnku ba, 33 wanda ya tafi a gaban ku a bisa hanya don ya sami wuri domin kuyi sansani, cikin wuta da dare cikin kuma girgije da rana. 34 Yahweh ya ji ƙarar maganganunku ya kuma yi fushi; ya yi rantsuwa ya ce, 35 'Tabbas babu ko ɗaya daga cikin waɗannan mutane na wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba kakanninku, 36 sai Kaleb ɗan Yefunne; zai gan ta. A gare shi zan bayar da ƙasar da ya taka akai, ga 'ya'yansa kuma, saboda ya bi Yahweh ɗungum.' 37 Sa'an nan Yahweh ya fusata da ni saboda ku, cewa, 'Kai ma baza ka je cikin wurin ba; 38 Yoshuwa ɗan Nun, wanda ke tsayawa a gaban ka, shi zai je cikin wurin; ka ƙarfafa shi, domin zai bida Isra'ila su gãje ta. 39 Haka kuma, ƙananan yaranku, waɗanda kuka ce zasu hallaka, waɗanda a yau basu da sanin nagarta ko mugunta - zasu je cikin wurin. A gare su zan bayar da ita, kuma zasu mallake ta. 40 Amma game da ku, ku juya ku kama tafiyarku zuwa cikin jeji ta gefen hanyar zuwa Tekun Iwa.' 41 Daganan kuka amsa kuka ce mani, 'Mun yi zunubi gãba da Yahweh; zamu tafi mu yi yaƙi, kuma zamu bi dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya umarce mu mu yi.' kowanne mutum a cikin ku ya sanya makaman yaƙinsa, kuma kuka shirya ku kai hari ga ƙasar tudu. 42 Yahweh ya ce mani, 'Ka ce masu, "Kada ku kai hari kuma kada ku yi yaƙi, gama bazan kasance tare da ku ba, kuma zaku sha kaye daga maƙiyanku.' 43 Na yi magana da ku ta wannan hanya, amma baku saurara ba. Kuka yi tawaye gãba da dokar Yahweh; kuka kangare kuma kuka kai hari ga ƙasar tudu. 44 Amma Amoriyawa, waɗanda ke zaune a ƙasar tudu, suka fito gãba da ku kuma suka kore ku kamar zuma, suka kuma mãke ku ƙasa a Seyir, har nesa zuwa Horma. 45 Kuka dawo kuma kuka yi kuka a gaban Yahweh; amma Yahweh bai saurari muryarku ba, ko kuma ya kula da ku ba. 46 Sai kuka dakata a Kadesh na kwanaki da yawa, dukkan kwanakin da kuka dakata a can.

Sura 2

1 Daga nan muka juya muka ɗauki tafiyarmu ta hanyar cikin jeji ta wajen Tekun Iwa, kamar yadda Yahweh ya yi magana da ni; muka tafi kewaye da Dutsen Seyir na kwanaki da yawa. 2 Yahweh ya yi magana da ni, cewa, 3 'Tafiyarku kewaye da wannan dutse ya isa; ku juya arewa. 4 Ka umarci mutanen, cewa, "Zaku bi ta cikin kan iyakar 'yan'uwanku, zuriyar Isuwa, waɗanda ke zaune a Seyir; zasu ji tsoronku. Saboda haka ku kiyaye 5 kada ku yi yaƙi da su, domin ba zan baku ko ɗaya daga cikin ƙasarsu ba, a'a, bama wadda ta isa tafin ƙafarku ya taka ba; gama na bayar da Dutsen Seyir ga Isuwa a matsayin mallaka. 6 Za ku sayi abinci daga gare su da kuɗi, domin ku ci; zaku kuma sayi ruwa daga gare su da kuɗi, domin ku sha. 7 Gama Yahweh ya albarkace ku a cikin dukkan aikin hannunku; ya san tafiyarku cikin wannan babban jeji. Cikin waɗannan shekaru arba'in Yahweh Allahnku yana tare daku, kuma baku rasa komai ba."' 8 Sai muka ratsa ta wurin 'yan'uwanmu, zuriyar Isuwa da ke zaune a Seyir, nesa da hanyar Araba, daga Elat daga kuma Eziyon Gebar. Daganan muka juya muka kuma ratsa ta jejin Mowab. 9 Yahweh ya ce mani, 'Kada ku matsawa Mowab, kada kuma ku yi faɗa da su a yaƙi. Domin ba zan bayar da ƙasarsa ba a gare ku domin mallakar ku, saboda na bayar da Ar ga zuriyar Lutu, domin mallakar su,' 10 (Emiyawa suka yi zama a wurin a dã, mutane manya, masu yawa, masu tsayi kuma kamar Anakimawa; 11 su kuma waɗannan ana ɗaukar su 'yan Refayim, kamar Anakimawa; amma Mowabawa suna kiransu Emiyawa. 12 Horitawa su kuma sun yi zama a Seyir a dã, amma zuriyar Isuwa suka gaje su. Suka hallakar da su a gabansu suka kuma zauna a wurin su, kamar yadda Isra'ila ya yi da ƙasar mallakarsa wadda Yahweh ya basu.) 13 Yanzu ku tashi ku tafi tsallaken kwarin Zered.' Sai muka tafi tsallaken rafin Zered. 14 Yanzu daga kwanakin da muka zo daga Kadesh Barniya har muka ketare rafin Zered, shekaru talatin da takwas ne. A wannan lokacin ne dukkan tsarar mazajen da suka isa yaƙi aka kawar da su daga mutanen, kamar yadda Yahweh ya rantse masu. 15 Haka nan kuma, hannun Yahweh ya yi gãba da wannan tsara domin a lalatar da su daga mutanen har sai da suka ƙare. 16 Sai ya kasance, sa'ad da dukkan mazajen da suka isa yaƙi suka mutu suka kuma ƙare daga cikin mutanen, 17 sai Yahweh ya yi magana da ni, cewa, 18 'A yau ne zaku ƙetare Ar, kan iyakar Mowab. 19 Sa'ad da kuka zo kusa daura da mutanen Ammon, kada ku matsa masu ko ku yi yaƙi da su; gama ba zan baku ko ɗaya daga cikin ƙasar mutanen Ammon ba a matsayin mallaka; saboda na bayar da ita ga zuriyar Lutu a matsayin mallaka."' 20 (Wannan ita ma an ɗauke ta ƙasar Refayim. Refayim ne suka yi zama a wurin a dã - amma Ammoniyawa suna kiransu Zamzumiyawa - 21 mutane manya, masu yawa, masu tsayi kuma kamar Anakimawa. Amma Yahweh ya hallakar da su a gaban Ammoniyawa, suka kuma gaje su suka zauna a wurin su. 22 Wannan kuma Yahweh ya yi domin mutanen Isuwa, waɗanda ke zaune a Seyir, da ya hallakar da Horinawa a gabansu, zuriyar Isuwa kuma suka gaje su suka zauna a wurin su har ya zuwa yau. 23 Amma game da Abibiyawa waɗanda ke zaune a ƙauyuka har nesa zuwa Gaza, Kaftorimawa, waɗanda suka zo daga Kafto, suka hallakar da su suka zauna a wurin su.) 24 Yanzu ku tashi, ku kama tafiyarku, ku kuma ratsa ta kwarin Arnon; duba, Na bayar cikin hannunku Sihon Ba'amoriye, sarkin Heshbon, da ƙasarsa. Ku fara mallakarta, ku kuma yi faɗa da shi a yaƙi. 25 A yau zan fara sanya tsoronku da fargabanku a bisa mutanen da ke dukkan ƙarƙashin sama; zasu ji labari game da ku zasu kuma yi rawar jiki su kuma kasance cikin ƙunci sabili da ku.' 26 Na aika da manzanni daga jejin Kedemot ga Sihon, sarkin Heshbon, da maganar salama, cewa, 27 Bari in ratsa ta cikin ƙasarka; zan bi ta kan titi; bazan juya ko zuwa hannun dama ba ko zuwa na hagu. 28 Za ka sayar mani da abinci domin kuɗi, saboda in ci; ka bani ruwa domin kuɗi, saboda in sha; ka dai bar ni kawai in ratsa ta ciki bisa sawaye na; 29 kamar zuriyar Isuwa da ke zaune a Seyir, da Mowabawa da ke zaune a Ar; har sai na ketare Yodan zuwa cikin ƙasar da Yahweh Allahnmu ya ke bamu.' 30 Amma Sihon, sarkin Heshbon, ba zai barmu mu ratsa ta wurinsa ba; domin Yahweh Allahnku ya taurare tunaninsa ya kuma sa zuciyarsa ta kafe, domin ya kayar da shi ta wurin ƙarfinku, wanda yanzu ya yi shi a yau. 31 Yahweh ya ce mani, 'Duba, Na fara miƙa Sihon da ƙasarsa a gaban ku; ku fara mallakar ta, domin ya zama kun gaji ƙasarsa.' 32 Daganan Sihon ya fito gãba da mu, shi da dukkan mutanensa, su yi faɗa a Yahaz. 33 Yahweh Allahnmu ya bayar da shi a gare mu muka kuma kayar da shi da 'ya'yansa maza da dukkan mutanensa. 34 Muka ɗauki dukkan biranensa a wancan lokaci muka kuma hallakar da kowanne birni ɗungum - maza da mata da ƙanana; bamu bar mai tsira ba. 35 Garken dabbobi ne kawai muka ɗauka a matsayin ganima domin mu, tare da ganimar biranen da muka ɗauka. 36 Daga Arowa, wadda ke gefen kwarin Arnon, daga kuma birnin da ke cikin kwarin, dukkan hanya har Giliyad, babu birnin da ya fi ƙarfin mu. Yahweh Allahnmu ya bayar da su cikin hannuwanmu. 37 ‌Ƙasar zuriyar Ammon ce kawai baku je ba, har ma dukkan gefen kogin Yabbok, da biranen ƙasar tudu - kowanne wurin da Yahweh Allahnmu ya hana mu zuwa.

Sura 3

1 Daga nan muka juya muka tafi hanyar Bashan. Og, sarkin Bashan, yazo kuma ya kawo mana hari, shi da dukkan mutanensa, ya yi faɗa a Edrai. 2 Yahweh ya ce mani, "Kada ka ji tsoronsa; gama na baka nasara a kansa kuma na sanya dukkan mutanensa da ƙasarsa a ƙarƙashin mulkinka. Zaka yi masa yadda kayi wa Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda ya zauna a Heshbon.' 3 Sai Yahweh Allahnmu ya bamu nasara a bisa Og sarkin Bashan, dukkan mutanensa kuma aka sanya su ƙarƙashin mulkinmu. Muka fyaɗe su har ba ko ɗaya daga cikin mutanensa da ya rage. 4 Muka ɗauki dukkan biranensa a wancan lokaci. Babu ko ɗaya daga cikin biranen nan sittin da bamu karɓe ba daga gare su - dukkan lardin Argob, masarautar Og a Bashan. 5 Dukkan waɗannan birane tsararru ne da dogayen ganuwoyi, ƙofofi, da ƙarafuna; waɗannan kuwa baya ga ƙauyuka marasa ganuwa masu yawan gaske. 6 Muka hallakar da su ɗungum, kamar yadda muka yi da Sihon sarkin Heshbon, muka hallakar da kowanne birni ɗungum - maza da mata da ƙanana. 7 Amma dukkan garken dabbobin da ganimar biranen, muka ɗauka a matsayin ganima domin mu. 8 A wannan lokacin muka ɗauke ƙasar daga hannun sarakunan Amoriyawa biyu, waɗanda ke ƙetaren Yodan, daga kwarin Arnon zuwa dutsen Hamon 9 (Sidoniyawa na kiran dutsen Hamon Siriyon, Amoriyawa kuma na kiran sa Senir) 10 da dukkan biranen sarari, dukkan Giliyad, da dukkan Bashan, har ya zuwa Saleka da Edrai, biranen masarautar Og a Bashan." 11 (Game da ragowar Refayim, Og sarkin Bashan ne kaɗai ya rage. Duba! gadonsa gadon ƙarfe ne. Ba yana a Rabba ba, inda zuriyar Ammon suka zauna? tsawonsa kamu tara ne fãɗinsa kuma kamu huɗu, bisa ga yadda mutane ke gwaji.) 12 Wannan ƙasa muka ɗauka mallaka a wannan lokaci - daga Arowa, wato ta gefen kwarin Arnon, da rabin ƙasar tudu ta Giliyad, da biranenta - Na bayar ga Rubenawa ga kuma Gadanawa. 13 Sauran Giliyad da dukkan Bashan, masarautar Og, Na bayar ga rabin kabilar Manasse. (Dukkan lardin Argob, da dukkan Bashan. Wannan gundumar ce ake kira ƙasar Refayim. 14 Yayir, wata zuriyar Manasse, suka ɗauki dukkan lardin Argob zuwa kan iyakar Geshurawa da Ma'akatawa. Ya kira lardin, wato Bashan, da sunansa, Habbot Yayir, har ya zuwa yau.) 15 Na bayar da Giliyad ga Makir. 16 Ga Rubenawa ga kuma Gadawa na bayar da gunduma daga Giliyad zuwa kwarin Arnon - tsakiyar kwarin shi ne kan iyakar gundumar - zuwa kuma kogin Yabbok, wanda ke kan iyaka tare da zuriyar Ammon. 17 Wasu kan iyakokinta kuma su ne sararin kwarin Kogin Yodan, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) zuwa gangarowar Dutsen Fisga maso gabas. 18 Na dokace ku a wancan lokaci, cewa, 'Yahweh Allahnku ya baku wannan ƙasa ku mallake ta; ku, dukkan ku mazajen yaƙi, zaku ƙetare shirye da makamai a gaban 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila. 19 Amma matayenku, da ƙanananku, da garken dabbobinku (nasan kuna da garken dabbobi masu yawa), zasu tsaya a biranen da na baku, 20 har sai Yahweh ya bayar da hutawa ga 'yan'uwanku, kamar yadda ya yi a gare ku, har su ma sai sun mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ke bayarwa a gare su a ƙetaren Yodan; daganan za ku dawo, kowanne mutum a cikinku, ga kaddararku da na bayar a gare ku.' 21 Na dokaci Yoshuwa a wancan lokacin, cewa, 'Idanunka sun ga dukkan abin da Yahweh Allahnka ya yi ga waɗannan sarakuna biyu; Yahweh zai yi irin haka ga dukkan masarautun da za ku je a ƙetare. 22 Ba za ku ji tsoronsu ba, gama Yahweh Allahnku shi ne zai yi yaƙi dominku.' 23 Na yi roƙo da naciya ga Yahweh a wancan lokaci, cewa, 24 'Ya Ubangiji Yahweh, ka fãra nuna wa bawanka girmanka da ƙarfin hannunka; gama wanne allah ne a sama ko a duniya da zai yi irin ayyukan da ka aiwatar, kuma dai-dai irin manyan ayyukan? 25 Ka barni in ƙetare, na roƙe ka, in kuma kalli ƙasar mai kyau da ke ƙetaren Yodan, wannan ƙasar tudu mai kyau, da kuma Lebanon.' 26 Amma Yahweh ya yi fushi da ni saboda ku; bai saurare ni ba. Yahweh ya ce mani, 'Bari wannan ya ishe ka - kada ka ƙara yi mani magana game da wannan al'amari: 27 ka hau zuwa ƙwalƙolin Fisga ka kuma ɗaga idanunka zuwa yamma, zuwa arewa, zuwa kudu, da zuwa gabas; ka duba da idanunka, domin ba zaka je ƙetaren Yodan ba. 28 A maimakon haka, ka umarci Yoshuwa ya ƙarfafa ka kuma ƙarfafashi, gama zai shiga gaban waɗannan mutane ya ƙetare, zai kuma sa su gãji ƙasar da za ka gani.' 29 Sai muka tsaya a kwari daura da Bet Feyo.

Sura 4

1 Yanzu, Isra'ila, ku saurari shari'o'i da dokoki da nake gab da koya maku, ku aikata su; saboda ku rayu ku kuma shiga ku kuma mallaki ƙasar da Yahweh, Allah na ubanninku, ya ke baku. 2 Ba zaku ƙara bisa ga maganganun dana umarce ku ba, ko kuma ku rage su, saboda ku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku wanda na ke gab da umartar ku. 3 Idanunku sun ga abin da Yahweh ya yi saboda Ba'al Feyo; domin dukkan mutanen da suka bi Ba'al na Feyo; Yahweh Allahnku ya lalatar da su a tsakaninku. 4 Amma ku da kuka manne wa Yahweh Allahnku kuna raye a yau, kowannen ku. 5 Duba, na koya maku shari'u da dokoki, kamar yadda Yahweh Allahna ya umarce ni, cewa kuyi haka a tsakiyar ƙasa inda kuke tafiya ciki domin ku mallake ta. 6 Saboda haka ku kiyaye su ku kuma aikata su; domin wannan shi ne hikimarku da fahimtarku a idanun mutanen da zasu ji dukkan waɗannan farillai su kuma ce, 'Tabbas wannan babbar al'umma mutane ne masu hikima da fahimta.' 7 Gama wacce al'umma ce da suke da allah da ke kusa da su sosai, kamar yadda Yahweh Allahnmu ya ke a duk sa'ad da muka yi kira a gare shi? 8 Wacce babbar al'umma ce da ke nan da take da shari'u da dokoki masu adalci sosai kamar dukkan shari'a da nake shiryawa a gaban ku a yau? 9 Kawai dai ku lura ku kuma jagoranci kanku a hankali, domin kada ku manta da abin da idanunku suka gani, saboda kada su bar zukatanku domin dukkan kwanakin rayuwarku. A maimakon haka, ku sanar da su ga 'ya'yanku da 'ya'yan 'ya'yanku. 10 A ranar da kuka tsaya a gaban Yahweh Allahnku a Horeb, sa'ad da Yahweh ya ce mani, 'Ka tattara mani mutanen, zan kuma sa su su ji maganganuna, domin su koyi jin tsorona dukkan kwanakin da suke raye a duniya, domin kuma su koyawa 'ya'yansu.' 11 Kuka zo kusa kuka tsaya a gindin dutsen. Dutsen na ƙonewa da wuta har tsakiyar sama, tare da duhu, girgije, da duhu mai kauri. 12 Yahweh ya yi magana daku daga cikin tsakiyar wuta; kuka ji muryar tare da maganganunta, amma baku ga wata siffa ba; murya kaɗai kuka ji. 13 Ya furta maku alƙawarinsa da ya umarceku ku aikata, Dokoki goma. Ya rubuta su a allunan duwatsu biyu. 14 Yahweh ya dokace ni a wannan lokaci da in koya maku farillai da shari'u, saboda ku aikata su a cikin ƙasar da kuke ƙetarawa ku ɗauki mallaka. 15 Saboda haka ku yi hankali da kanku - domin baku ga wata siffa ba a ranar da Yahweh ya yi magana daku a Horeb daga tsakiyar wuta - 16 domin kada ku lalata kanku ta wurin yin sassaƙaƙƙen siffa bisa ga siffar wani abu, a cikin kamannin namiji ko mace, 17 a cikin kamannin kowacce irin dabba a duniya, kamannin kowanne irin tsuntsu mai fukafukai da ke shawagi a sammai, 18 kamannin kowanne irin abu da ke rarrafe a bisa ƙasa, ko kamannin kowanne irin kifi da ke cikin ruwa a ƙarƙashin duniya. 19 Ba zaku ɗaga idanunku zuwa sammai ba ku dubi rana, wata, ko taurari ba - dukkan rundunar sammai - kuma ku janye zuwa yi masu sujada ku kuma girmama su - waɗannan abubuwa waɗanda Yahweh Allahnku ya bada kaso ga dukkan mutanen ƙarƙashin sararin sama baki ɗaya. 20 Amma Yahweh ya ɗauko ku ya kawo ku kuma daga tanderun ƙarfe, daga Masar, ku zama a gare shi mutanen gãdonsa, kamar yadda kuke a yau. 21 Yahweh yaji haushina saboda ku; ya yi rantsuwa cewa bazan ƙetare Yodan ba, da cewa kada in tafi cikin wannan ƙasa mai kyau, ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke bayarwa a gare ku a matsayin gãdo. 22 A maimako, tilas in mutu a wannan ƙasa; tilas ba zan tafi ƙetaren Yodan ba; amma ku zaku ƙetare ku kuma mallaki ƙasar mai kyau. 23 Ku lura da kanku, domin kada ku manta da alƙawarin Yahweh Allahnku, wanda ya yi tare daku, ku kuma yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa a cikin siffar wani abu wanda Yahweh Allahnku ya hanaku ku yi. 24 Gama Yahweh Allahnku wuta ne mai lanƙwamewa, Allah ne mai kishi. 25 Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya da 'ya'yan 'ya'ya, sa'ad da kuma kuka kasance a ƙasar na dogon lokaci, idan kuma kuka lalata kanku kuka kuma yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa bisa ga siffar kowanne abu, kuka kuma aikata abin da ke na mugunta a idanun Yahweh Allahnku, domin ku tunzura shi zuwa fushi - 26 na kira sama da duniya suyi shaida gãba da ku a yau cewa ba da daɗewa ba zaku lalace daga ƙasar da kuke ƙetare Yodan domin ku mallaka; ba zaku tsawonta kwanakinku ba a cikin ta, amma ɗungum zaku rushe. 27 Yahweh zai warwatsa ku cikin mutane, kuma zaku zama 'yan kaɗan a cikin al'ummai, inda Yahweh zai aika da ku. 28 A can zaku yi bautar wasu alloli, ayyukan hannuwan mutane, katako da dutse, waɗanda basu gani, ji, ci, ko sunsunawa. 29 Amma daga can zaku biɗi Yahweh Allahnku, kuma zaku same shi, sa'ad da kuka neme shi da dukkan zuciyarku da dukkan ranku. 30 Sa'ad da kuke cikin ƙunci, sa'ad da kuma dukkan waɗannan abubuwa suka zo kanku, cikin waɗannan kwanakin ƙarshe zaku dawo ga Yahweh Allahnku kuma ku saurari muryarsa. 31 Gama Yahweh Allahnku Allah ne cike da jinƙai; ba zai gaza maku ba ko ya rusa ku, ko kuwa ya manta da alƙawarin ubanninku wanda ya rantse masu. 32 Ku yi tambaya yanzu game da kwanakin da suka wuce, waɗanda suke kafin lokacinku, tun ranar da Allah ya halitta mutum a duniya, ku yi tambaya daga ƙarshen sama zuwa ɗaya ƙarshen sama, ko an taɓa yin wani abu babba kamar wannan, ko an taɓa jin wani abu kamar wannan? 33 Ko an taɓa yin wasu mutane da suka ji muryar Allah na magana daga cikin wuta, kamar yadda kuka ji, kuka kuma rayu? 34 Ko kuwa Allah ya taɓa ɗaukar wani mataki yaje ya ɗaukarwa kansa al'umma daga cikin wata al'ummar, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu, da ta wurin al'ajibai, da ta wurin yaƙi, da ta wurin hannu mai ƙarfi, da ta wurin miƙaƙƙen damtse, da ta wurin babbar razana, kamar dukkan abin da Yahweh Allahnku ya yi domin ku a Masar a gaban idanunku? 35 A gare ku aka nuna waɗannan abubuwa, saboda ku sani cewa Yahweh shi ne Allah, kuma da cewa babu wani baya gare shi. 36 Daga sama ya sa kuka ji muryarsa, saboda ya umarce ku; a duniya ya sa kuka ga babbar wutarsa; kuka ji maganganunsa daga cikin tsakiyar wutar. 37 Saboda yana ƙaunar ubanninku, ya zaɓi zuriyarsu bayansu, ya kuma fito daku daga Masar tare da bayyanuwarsa, tare da babban ikonsa; 38 domin ya kore daga gabanku al'ummai da suka fi ku girma da ƙarfi, saboda ya kawo ku ciki, saboda ya baku ƙasarsu a matsayin gãdo, kamar a yau. 39 Saboda haka ku sani a yau, ku kuma ajiye shi a zukatanku, cewa Yahweh shi ne Allah a sama can da duniya a ƙarƙashi; babu wani kuma. 40 Zaku kiyaye farillansa da dokokinsa waɗanda ya dokace ku a yau, domin lafiya ta tafi tare da ku da 'ya'yanku a bayanku, saboda kuma ku tsawonta kwanakinku a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku har abada." 41 Daganan Musa ya zaɓi birane uku daga sashen gabas da Yodan, 42 saboda wani yana iya gudu zuwa ɗaya daga cikinsu idan ya kashe wani taliki cikin kuskure, wanda ba maƙiyinsa bane a dã. Ta wurin tserewa zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane, zai iya tsira. 43 Su ne: Bezar a jeji, ƙasar sarari, domin Rubenawa; Ramot a Giliyad, domin Gadawa; da Golan a Bashan, domin Manasawa. 44 Wannan ita ce shari'ar da Musa yasa a gaban mutanen Isra'ila; 45 waɗannan ne dokokin alƙawari, shari'u, da sauran dokoki daya faɗi ga mutanen Isra'ila sa'ad da suka fito daga Masar, 46 sa'ad da suke a gabas da Yodan, a kwari daura da Bet Feyo, a ƙasar Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda ya zauna a Heshbon, wanda Musa da mutanen Isra'ila suka kayar sa'ad da suka fito daga Masar. 47 Suka ɗauki ƙasarsa a matsayin mallaka, da ƙasar Og sarkin Bashan - waɗannan, sarakuna biyu na Amoriyawa, waɗanda ke ƙetaren Yodan zuwa gabas. 48 Wannan gunduma ta tafi daga Arowa, a gaɓas Kwarin Arnon, zuwa Dutsen Sihiyona (ko Dutsen Hamon), 49 ya kuma haɗa da dukkan sararin kwarin Kogin Yodan, maso gabas a ƙetaren Yodan, zuwa Tekun Araba, zuwa gangaren Dutsen Fisga.

Sura 5

1 Musa ya yi kira ga dukkan Isra'ila ya ce masu, "Ku saurara, Isra'ila, ga farillai da dokoki da zan faɗa cikin kunnuwanku a yau, domin ku koye su ku kuma kiyaye su. 2 Yahweh Allahnmu ya yi alƙawari tare da mu a Horeb. 3 Yahweh bai yi wannan alƙawari tare da kakanninmu ba, amma tare da mu, dukkan mu da muke a raye a nan a yau. 4 Yahweh ya yi magana daku fuska da fuska a dutse daga tsakiyar wuta 5 (na tsaya tsakanin Yahweh daku a wancan lokaci, in bayyana maku maganarsa; domin kuna jin tsoro saboda wutar, kuma baku hau zuwa tsaunin ba). Yahweh ya ce, 6 'Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 7 Ba za ku yi wasu alloli ba a gabana. 8 Ba za kuyi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa ba ko kamannin wani irin abu da ke sama can, ko da ke a duniya a ƙasa, ko da ke a cikin ruwa a ƙarƙashi. 9 Ba zaku russuna masu ba ko ku bauta masu, domin Ni, Yahweh Allahnku, ni Allah ne mai kishi. Ina hukunta muguntar kakanni ta wurin sauko da hukunci bisa 'ya'yan, har zuwa tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni, 10 da nuna alƙawarin aminci ga dubbai, ga waɗanda ke ƙaunata da kiyaye dokokina. 11 Ba zaku ɗauki sunan Yahweh Allahnku ba a banza, gama Yahweh ba zai riƙe shi marar laifi ba shi wanda ya ɗauki sunansa a banza. 12 Ka lura da ranar Asabaci ka kiyaye ta da tsarki, kamar yadda Yahweh Allahnka ya dokace ka. 13 Gama cikin kwana shida zaka yi aikin ƙarfi kayi kuma dukkan ayyuka; 14 amma rana ta bakwai Asabaci ce ga Yahweh Allahnka. A cikin ta ba za ka yi wani aiki ba - ban da kai, ko ɗanka, ko ɗiyarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko san ka, ko jakinka, ko wani daga cikin garken dabbobinka, ko wani baƙo daga cikin ƙofofinka. Wannan kuwa haka ne domin bawanka da baiwarka su huta kamar yadda za ka huta. 15 Za ka tuna da cewa kaima bawa ne a ƙasar Masar, kuma Yahweh Allahnka ya fito da kai daga can da hannu mai ƙarfi da miƙaƙƙen damtse. Saboda haka Yahweh Allahnka ya dokace ka da ka kiyaye ranar Asabaci. 16 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kamar yadda Yahweh Allahnka ya dokace ka kayi, domin ka zauna na dogon lokaci a cikin ƙasar da Yahweh Allahnka ya ke baka, domin kuma ya kasance lafiya tare da kai. 17 Ba za kayi kisa ba. 18 Ba zaka aikata zina ba. 19 Ba zaka yi sata ba. 20 Ba zaka bada shaidar zur ba gãba da maƙwabcinka. 21 Ba zaka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ba zaka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba, ko gonarsa, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko wani abu da ke na maƙwabcinka.' 22 Waɗannan maganganu Yahweh ya faɗi da babbar murya ga dukkan taronku a bisa dutse daga tsakiyar wuta, daga gizagizai, daga kuma duhu mai kauri; baiyi ƙarin wasu maganganu ba. Ya rubuta su bisa allunan dutse ya kuma bani su. 23 Sai ya kasance, da kuka ji muryar daga tsakiyar duhu, yayin da dutsen ke ƙonewa, sai kuka zo kusa da ni - dukkan dattawanku da shugabannin kabilunku. 24 Kuka ce, 'Duba, Yahweh Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da girmansa, kuma mun ji muryarsa daga tsakiyar wuta; mun gani a yau cewa sa'ad da Yahweh ya yi magana da mutane, za su iya rayuwa. 25 Amma me yasa zamu mutu? gama wannan babbar wuta zata cinye mu; idan muka ƙara jin muryar Yahweh Allahnmu, zamu mutu. 26 Gama banda mu wane ne a cikin nama da jini, ya taɓa jin muryar Allah mai rai daga tsakiyar wuta ya kuma rayu, kamar yadda muka yi? 27 Game da kai, ka tafi ka saurari dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya ce; ka maimaita mana dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya ce maka; zamu saurara kuma mu yi biyayya.' 28 Yahweh yaji maganganunku sa'ad da kuka yi zance da ni. Ya ce mani, 'Na ji maganganun waɗannan mutane, abin da suka ce maka. Abin da suka ce mai kyau ne. 29 Oh, ace ma akwai irin wannan zuciyar a cikinsu, cewa zasu girmama ni kuma koyaushe zasu kiyaye dokokina, domin ya tafi lafiya tare da su tare kuma da 'ya'yansu har abada! 30 Ka je kace masu, "Ku koma rumfunanku." 31 Amma game da kai, ka tsaya nan gefe na, zan kuma gaya maka dukkan dokokin, farillai, da shari'u da zaka koya masu, saboda su kiyaye su a cikin ƙasar da zan ba su su mallaka.' 32 Saboda haka, zaku kiyaye, abin da Yahweh Allahnku ya dokace ku; ba zaku kauce ba zuwa hannun dama ko hagu. 33 Zaku yi tafiya cikin dukkan hanyoyi da Yahweh Allahnku ya dokace ku, domin ku rayu, domin kuma ya tafi lafiya tare da ku, ku kuma tsawonta kwanakinku a cikin ƙasar da zaku mallaka.

Sura 6

1 Yanzu waɗannan ne dokoki, da farillai, da kuma shari'un da Yahweh Allahnku ya dokace ni in koya maku, domin ku kiyaye su a cikin ƙasar da kuke tafiya ƙetaren Yodan ku mallaka; 2 saboda ku iya girmama Yahweh Allahnku, saboda ku kiyaye dukkan farillansa da dokokinsa waɗanda nake dokatarku a yau - ku, da 'ya'yanku, da 'ya'yan 'ya'yanku, dukkan kwanakin rayuwarku, saboda kwanakinku su yi tsawo. 3 Saboda haka ku saurare su, Isra'ila, ku kuma kiyaye su, saboda ya tafi lafiya tare daku, saboda ku yi babbar ruɓanɓanya, a cikin ƙasar da ke malalowa da madara da zuma, kamar yadda Yahweh, Allah na ubanninku, ya yi maku alƙawari zai yi. 4 Ku saurara, Isra'ila: 5 Yahweh Allahnmu ɗaya ne. Zaku ƙaunaci Yahweh Allahnku tare da dukkan zuciyarku, tare da dukkan ranku, tare kuma da dukkan ƙarfinku. 6 Maganganun da nake umartarku a yau za su kasance a zukatanku; 7 da ƙwazo kuma zaku koyar da su ga 'ya'yanku; zaku yi magana game da su sa'ad da kuke zaune cikin gida, sa'ad da kuke tafiya akan hanya, sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 8 Za ku ɗaura su a matsayin alama a bisa hannunku, zasu kuma zama kamar 'yan goshi a tsakanin idanunku. 9 Zaku rubuta su a ginshiƙan gidajenku da ƙofofinku. 10 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya yi rantsuwa ga ubanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu, cewa zai baku, da birane manya-manya kyawawa da baku gina ba, 11 da gidaje cike da dukkan abubuwa iri-iri masu kyau da baku yi ba, tankunan ruwa da baku gina ba, garkunan inabi da itatuwan zaitun da baku dasa ba, zaku ci ku ƙoshi - 12 daganan ku lura saboda kada ku manta da Yahweh, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan ƙunci. 13 Zaku girmama Yahweh Allahnku; shi ne zaku yi wa sujada, kuma zaku yi rantsuwa da sunansa. 14 Ba zaku bi waɗansu alloli ba, allolin mutanen da suke kewaye daku kakaf - 15 domin Yahweh Allahnku da ke tsakiyarku Allah ne mai kishi - idan kuka yi, fushin Yahweh Allahnku zai kunnu gãba daku kuma zai hallakar daku daga fuskar duniya. 16 Ba zaku gwada Yahweh Allahnku ba kamar yadda kuka gwada shi a Massa. 17 Zaku yi ƙwazo ku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku, dokokinsa natsastsu, da farillansa, waɗanda ya dokace ku. 18 Zaku yi abin da ke dai-dai mai kyau kuma a idanun Yahweh, saboda ya kasance lafiya a gare ku, ku kuma iya zuwa ku mallaki ƙasa mai kyau da Yahweh ya rantse wa ubanninku, 19 ya kori dukkan maƙiyanku daga gare ku, kamar yadda Yahweh ya faɗa. 20 Sa'ad da ɗanku ya tambaye ku a lokaci mai zuwa, cewa, 'Waɗanne ne dokokin alƙawari da farillai da sauran dokoki da Yahweh Allahnmu ya umarce ku? 21 daganan zaku cewa ɗanku, 'Mu bayin Fir'auna ne a Masar; Yahweh ya fito da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi, 22 ya kuma aiwatar da alamu, da al'ajibai, manya masu tsanani, a bisa Masar, a bisa Fir'auna, a kuma bisa dukkan gidansa, a gaban idanunmu; 23 ya kuma fito da mu daga wurin, saboda ya kawo mu ciki, ya ba mu ƙasar da ya rantse wa ubanninmu. 24 Yahweh ya dokace mu da a koyaushe mu kiyaye waɗannan farillai, mu ji tsoron Yahweh Allahnmu domin kyaunmu, domin ya iya kiyaye mu a raye, kamar yadda muke a yau. 25 Idan muka kiyaye dukkan waɗannan dokoki a gaban Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya dokace mu, wannan ne zai zama adalcinmu.'

Sura 7

1 Lokacin da Yahweh Allahnku ya kawo ku zuwa ƙasar da kuke shiga domin ku mallake ta, za ya kori al'ummai masu yawa - su Hittiyawa, da Girgashawa da Amoriyawa da Kan'aniyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa da kuma Yebusawa - al'ummai guda bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku. 2 Yahweh Allahnku ne ya miƙa su cikin hannunku lokacin da kuka ci su da yaƙi, haka nan kuma dole ne ku hallaka su dukka. Ba zaku ɗauki alƙawari da su ba, kada kuma ku nuna masu jinƙai. 3 Kada kuma ku shirya aurayya da su. Ba zaku miƙa 'ya'yanku mata aure ga 'ya'yansu maza ba, kuma ba zaku ɗauko 'ya'yansu mata domin 'ya'yanku maza ba. 4 Gama zasu juyar da hankalin 'ya'yanku maza daga bina, domin su yi sujada ga wasu alloli. Da haka fushin Yahweh za shi yi ƙuna gãba daku, kuma za ya hallaka ku da sauri. 5 Ga yadda zaku yi da su: Zaku rushe har ƙasa bagadansu, ku farfashe umudansu, ku datse Asherim da mazamninta, ku kuma ƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu. 6 Gama ku al'umma ce da aka keɓe ga Yahweh Allahnku. Ya zaɓe ku ku zama mutane domin ya mallaka, gaba da dukkan sauran mutanen da ke fuskar duniya. 7 Yahweh bai ɗora ƙaunarsa bisanku ko ya zaɓe ku domin kun fi sauran mutane yawa bane - gama kun zama ƙalilan cikin dukkan mutane - 8 amma domin ya ƙaunace ku, kuma yana kiyaye alƙawarinsa da ya yi wa ubanninku. Wannan shi ne dalilin da yasa Yahweh ya fito daku da hannu mai girma ya kuma fanshe ku daga gidan bauta, daga hannun Fir'auna, sarkin Masar. 9 Saboda haka ku san cewa Yahweh Allahnku - shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alƙawari da kuma aminci ga dubban tsararraki da waɗanda suke ƙaunarsa suna kuma kiyaye dokokinsa, 10 amma yana saka wa waɗanda suka ƙi shi a fuskarsu, domin ya hallaka su; ba za ya tausaya wa duk wanda ya ƙi shi ba; zai yi masa sakamako yana ji yana gani. 11 Don haka zaku kiyaye dokoki, da farillai, da kuma umarnai dana dokace ku yau, domin ku aikata su. 12 Idan kuka saurari waɗannan umarnai, kuka kiyaye ku kuma aikata su, za shi zama kuma Yahweh Allahnku za ya kiyaye ku da alƙawari da kuma amincin da ya rantse wa ubanninku. 13 Za ya ƙaunace ku, ya albarkace ku, ya kuma riɓanɓanya ku; za ya kuma albarkaci 'ya'yan jikinku da kuma na ƙasarku, hatsinku, da sabuwar inabinku, da kuma mai da ke naku, da ƙaruwar garkunanku da 'ya'yan garkunanku, a cikin ƙasan da ya rantse wa ubanninku zai baku. 14 Zaku yi albarka fiye da dukkan sauran mutane; ba za a samu bakararre ko bakararriya cikinku ba ko a cikin garkunanku. 15 Yahweh zai ɗauke dukkan ciwo daga gare ku; babu ko ɗaya daga cikin mugayen cututtuka na Masarawa da kuka sani da zai sa a bisanku, amma zai sa su bisa dukkan waɗanda suka ƙi ku. 16 Zaku hallaka dukkan mutanen da Yahweh Allahnku za ya bada su cikin hannunku, kuma idanunku ba zasu tausaya masu ba. Kada ku yi sujada ga allolinsu, gama wannan tarko ne a gare ku. 17 Idan kun ce cikin zuciyarku, 'Waɗannan al'ummai sun sha ƙarfinmu da yawa; yaya zan ci ƙarfinsu in kore su?' - 18 kada ka ji tsoronsu; ka tuna da abin da Yahweh ya yi ma Fir'auna da dukkan Masarawa; 19 anobai masu girma da idanuwanka suka gani, alamu, da al'ajibai, hannu mai ƙarfi, da kuma miƙaƙƙiyar hannu wadda Yahweh Allahnku ya fito daku. Yahweh zai yi haka kuma ga dukkan mutanen da kuke tsoron su. 20 Bayan wannan kuma, Yahweh Allahnku zai aika zirnaƙo a cikinsu, har sai duk waɗanda suka rage da waɗanda suka ɓoye kansu daga gare ku sun hallaka daga fuskarku. 21 Ba zaku razana ta dalilinsu ba, gama Yahweh Allahnku na cikinku, Allah mai girma mai ban razana. 22 Yahweh Allahnku zaya kori waɗannan al'ummai daga gabanku kaɗan-kaɗan. Ba zaku iya hallaka su dukka a lokaci ɗaya ba, don kada namomin jeji su yi yawa kewaye daku. 23 Amma Yahweh Allahnku zaya baku nasara bisansu sa'ad da kuka gamu da su a dagar yaƙi; za ya rikitar da su matuƙa har sai sun lalace sarai. 24 Za ya sanya sarakunansu a ƙalƙashin ikonku, kuma zaku sa sunansu ya hallaka daga doron ƙasa. Babu wanda zaya iya tsayayya daku, har sai kun hallaka su sarai. 25 Zaku ƙona sassaƙaƙƙun siffofin allolinsu - kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da ta dalaye su ku kuma ɗauke ta domin amfaninku, don in kun yi haka, zai zama tarko gare ku - gama abin kyama ne ga Yahweh Allahnku. 26 Ba zaku kawo kowanne ƙazamtaccen abu cikin gidanku ba har da zaku yi masa sujada. Amma zaku yi matuƙar ƙyama ku kuma tsane su, gama keɓaɓɓe ne domin hallakarwa.

Sura 8

1 Dole ku kiyaye dukkan dokokin da nake baku yau, domin ku rayu ku kuma riɓaɓɓanya, ku kuma fita ku mallaki ƙasar da Yahweh ya rantse ga ubanninku. 2 Zaku tuna da dukkan hanyoyin da Yahweh Allahnku ya bi daku waɗannan shekaru arba'in cikin jeji, domin ya ɗauke girman kai daga gare ku, domin ya gwada ku ya kuma san mene ne ke cikin zuciyarku, ko zaku kiyaye dokokinsa ko a'a. 3 Ya ɗauke girman kanku, ya sa kun ji yunwa, ya kuma ciyar daku da manna, wadda ba ku taɓa sani ba wadda kuma ubanninku ba u sani ba. Ya yi haka ne domin ya koya maku da cewa bada gurasa kaɗai mutane ke rayuwa ba; sai dai, ta kowacce abin da ke fitowa daga bakin Yahweh mutane ke rayuwa. 4 Tufafinku basu koɗe su kuma faɗi daga jikinku ba, kuma sawayenku basu kumbura cikin shekarun nan arba'in ba. 5 Zaku yi tunani cikin zuciyarku, ta yaya, kamar yadda mutum ke horon ɗansa, haka Yahweh Allahnku ya ke horonku. 6 Zaku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku, domin ku yi tafiya cikin tafarkunsa ku kuma girmama shi. 7 Gama Yahweh Allahnku yana kawo ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka, da ɓulɓulai da zurfafa da masu gangarowa daga tuddai, suna gudu zuwa cikin kwarurrukai da tuddai; 8 ƙasa mai alkama da bali, na inabi, itacen ɓaure, dana rumana; ƙasar da akwai man zaitun da kuma zuma. 9 ́‌‌Ƙ‌asa ce inda zaku ci gurasa babu rashi, kuma inda zaku tafi ba da rashin komai ba; ƙasa wadda duwatsunta tama ce, kuma daga cikin tsaunukanta kana iya haƙa jan ƙarfe. 10 Zaku ci ku kuma ƙoshi, ku kuma albarkaci Yahweh Allahnku domin ƙasa mai kyau da ya baku. 11 Ku kula kada ku manta da Yahweh Allahnku, kuma kada kuyi banza da dokokinsa, farillansa, da umurnansa da nake dokace ku yau, 12 in ba haka ba, lokacin da kuka ci kuka kuma ƙoshi, kuka kuma gina gidaje kuka kuma zauna cikinsu, zuciyarku za ta yi kumburi. 13 Ku kula sa'ad da garkunanku na shanu dana tumaki suka ƙaru kuma lokacin da azurfanku da zinariyarku suka ƙaru, da dukkan mallakarku suka yawaita, 14 sai zuciyarku ta kumbura har ku manta da Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 15 Kada ku manta da shi wanda ya bishe ku ta cikin jeji babba da mai ban-razana, tare da macizai masu masifa da kunamai da ƙasa mai ƙishi inda babu ruwa, wanda ya fito maku da ruwa daga dutse fa. 16 Ya ciyas da ku cikin jeji da manna abin da ubanninku basu taɓa sanin ta ba, domin ya ɗauke fahariya daga gare ku ya kuma gwada ku, domin ya yi maku alheri a ƙarshe, 17 amma zaku ce a zuciyarku, 'Ai ƙarfina ne da ikon hannuna ne suka bani wannan dukkan dukiyar.' 18 Amma zaku tuna da Yahweh Allahnku, domin shi ne ke baku iko don ku wadata; domin ya kafa alƙawarinsa da ya yi wa ubanninku, kamar yadda ya ke a yau. 19 Haka za shi zama, idan zaku manta da Yahweh Allahnku ku kuma bi wasu alloli, kuyi masu sujada, ku kuma girmamasu, nayi shaida gãba daku yau da cewa zaku hallaka. 20 Kamar al'ummai da Yahweh ke sasu hallaka a gaban ku, haka kuma zaku hallaka, domin kun ƙi ku saurari muryar Yahweh Allahnku.

Sura 9

1 Ku saurara, Isra'ila; kuna gab da ƙetare Yodan yau, ku shiga ciki ku kaɓantar da al'ummai waɗanda suka fi ku girma da kuma ƙarfi, da kuma birane ƙarfafa da ganuwa na tsaro da ke kaiwa har sama, 2 mutane masu girma da tsawo, 'ya'yan Anakim, waɗanda kuka sani, kuma waɗanda kuka ji mutane ke cewa game da su, 'Waye zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?' 3 Saboda haka yau ku sani cewa Yahweh Allahnku shi ne wanda ya ke tafiya a gabanku kamar wuta mai cinyewa; zaya hallakar da su, kuma zaya ci ƙarfinsu a gabanku; da haka zaku kore su ku kuma sasu hallaka da sauri, kamar yadda Yahweh ya gaya maku. 4 Kada ku faɗi a zuciyarku, bayan da Yahweh Allahnku ya ture su waje a gabanku, 'Saboda adalcina ne Yahweh ya kawo ni ciki domin in mallaki wannan ƙasa; gama sabili da muguntar waɗannan al'ummai ne yasa Yahweh ya ke korarsu a gabanku. 5 Ba saboda adalcinku ko dai-daituwa ta zuciyarku ne yasa zaku shiga ku mallaki ƙasarsu ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne yasa Allahnku ke koran su waje daga gabanku, kuma domin ya cika maganarsa da ya rantse wa ubanninku, ga Ibarahim, da Ishaku, da kuma Yakubu. 6 Don haka ku san cewa, Yahweh Allahnku ba yana baku wannan ƙasa mai kyau domin ku mallake ta don adalcin ku bane, gama ku mutane ne masu taurin zuciya. 7 Ku tuna kada kuma ku manta yadda kuka tozarta Yahweh Allahnku ga fushi a cikin jeji; daga ranar da kuka baro ƙasar Masar har kuka iso wannan ƙasa, kun yi ta tayarwa gãba da Yahweh. 8 Haka ma a Horeb kuka tozarta Yahweh ga fushi, har Yahweh ya yi fushin da har zai iya hallaka ku. 9 Da na tafi kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, alluna na alƙawarin da Yahweh ya yi da ku, na zauna a dutsen har kwanaki arba'in da dare arba'in; ban ci gurasa ba ban kuma sha ruwa ba. 10 Yahweh ya ba ni allunan dutse guda biyu da ya yi rubutu da yatsansa; a cikinsu kuma aka rubuta dukkan maganganun da Yahweh ya shaida maku a kan dutse daga cikin tsakiyar wuta a ranan taro. 11 Haka ya zama a ƙarshen waɗannan yini arba'in da dare arba'in da Yahweh ya bani allunan duwatsu guda biyu, alluna na alƙawari. 12 Yahweh ya ce da ni, 'Tashi, sauka ƙasa da sauri daga nan, gama mutanen ka, waɗanda ka fito da su daga Masar, sun ƙazamtar da kansu. Sun yi hamzari daga juyawa daga tafarkin dana dokace su. Sun yi ma kansu sassaƙaƙƙen siffa.' 13 Gaba da wannan, Yahweh ya yi mani magana ya ce, 'Na ga waɗannan mutanen; mutane ne masu taurin zuciya. 14 Ka bar ni, don in hallaka su in shafe sunansu daga ƙarƙashin sama, sai kuma in maishe ka al'umma mafi ƙarfi da girma fiye da su.' 15 Sai na juya na kuma sauko daga dutsen, dutsen kuma na ci da wuta. Allunan alƙawari guda biyu a cikin hannuwana. 16 Sai na duba, ai kuwa, kun rigaya kun saɓa wa Yahweh Allahnku. Kun yi wa kanku siffar gumaka. Kun juya da sauri daga tafarkin da Yahweh ya dokace ku. 17 Sai na ɗauko alluna biyun na jefar da su daga hannuwana. Na karya su a idanunku. 18 Sai na sake kwantawa da fuska a ƙasa a gaban Yahweh yini arba'in da dare arba'in; ban ci ko burodi ko in sha ruwa ba, saboda zunubinku da kuka yi, na aikata abin da ke na mugunta a gaban Yahweh, domin ku tozarta shi ga fushi. 19 Gama na ji tsoron fushi da rashin jin daɗi mai zafi irin wadda Yahweh ya yi gãba daku da ya isa har ya hallaka ku. Amma Yahweh ya saurare ni a wannan lokaci kuma. 20 Yahweh ya yi matuƙar fushi da Haruna har da zai hallaka shi; Na yi ma Haruna addu'a shi ma a wannan sa'a. 21 Na ɗauki zunubinku, siffar ɗan maraƙin da kuka yi, na ƙone shi, na tattake shi, na kuma niƙa su gaba ɗaya, har ya zama kamar ƙura. Na zubas da ƙurar cikin rafin da ke gangarowa daga dutsen. 22 A Tabera, a Massa, da kuma Kibrot Hatta'aba, kuka cakuni Yahweh ya fusata. 23 Lokacin da Yahweh ya aike ku daga Kadesh Barniya ya kuma ce, 'Ku haura ku mallaki ƙasar dana rigaya na baku,' sai kuka yi tawaye da dokokin Yahweh Allahnku, baku kuma gaskanta da shi ba koku saurari muryarsa ba. 24 Kun daɗe kuna tayaswa gãba da Yahweh tun daga ranar dana sanku. 25 Sai na faɗi da fuskata ƙasa a gaban Yahweh a waɗannan yini arba'in da dare arba'in, domin ya ce zai hallaka ku. 26 Na yi addu'a ga Yahweh na kuma ce, 'Ya Ubangiji Yahweh, kada ka hallakar da mutanenka ko abin gãdon ka daka fanshe su ta wurin girmanka, waɗanda ka fitar daga Masar da hannu mai iko. 27 Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu; kada ka kula da taurin kan waɗannan mutane, ba kuma ga muguntarsu ba, ko ga zunubinsu ba, 28 domin kada ƙasar daka fito da mu su ce, "Domin Yahweh bai iya ya kai su zuwa cikin ƙasar da ya yi alƙawari garesu ba, kuma domin ya ƙisu, sai ya fito da su zuwa jeji domin ya kashe su a nan." 29 Duk da haka su mutanenka ne da kuma abin gãdonka, wanda ka fito da su da girman ƙarfinka da kuma ta wurin bayyana aikakkiyar ikonka.'

Sura 10

1 A wannan lokaci Yahweh ya ce da ni, 'Kayi sassakan alluna guda biyu kamar na farko, sai ka hauro wurina kan dutsen, kayi akwatin alƙawari na itace. 2 Zan yi rubutu a cikin allunan maganganun da suke cikin alluna na farkon daka farfasa, zaka kuma sanya su cikin akwatin.' 3 Sai na yi akwatin alƙawari daga itacen maje, sai na sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, sai kuma na haura zuwa saman dutse, riƙe da allunan biyu a hannuna. 4 ya yi rubutu a bisa allunan, kamar rubutu na farko, Dokoki Goma wanda Yahweh ya yi maku magana a kan dutse daga cikin tsakiyar wuta a ranar taruwa; sai Yahweh ya miƙa mani su. 5 Sai na juyo na sauko daga dutsen, na kuma sanya allunan cikin akwatin alƙawarin dana yi; a nan suke, kamar yadda Yahweh ya umarce ni." 6 (Jama'ar Isra'la suka yi tafiya daga Birot Bene Ya'akan zuwa Mosera. A nan ne Haruna ya rasu, a nan kuma aka binne shi; Eleyaza, ɗansa, ya yi hidima na firist a matsayinsa. 7 Daga can suka yi tafiya zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma zuwa Yotbata, ƙasa mai rafuffuka na ruwa. 8 A wannan lokaci sai Yahweh ya zaɓi ƙabilar Lebi don su ɗauki akwatin alƙawari na Yahweh, domin su tsaya a gaban Yahweh su yi masa hidima, su kuma albarkaci mutane a cikin sunansa, kamar yau. 9 Don haka Lebi ba shi da rabo ko gãdon ƙasa tare da 'yan'uwansa; Yahweh ne gãdonsa, kamar yadda Yahweh Allahnka ya yi masa magana.) 10 "Na zauna a kan dutsen kamar yadda nayi da farko, yini arba'in dare arba'in. Yahweh ya saurare ni wannan lokaci kuma; Yahweh ba shi da niyyar hallaka ku. 11 Yahweh ya ce mani, 'Ka tashi, ka sha gaban mutanen domin ka shugabance su a kan hanyarsu; za su shiga ciki su kuma mallaki ƙasar dana rantse wa ubanninsu in ba su.' 12 Yanzu, Isra'ila, mene ne Yahweh Allahnka ke buƙata daga gare ka, sai dai ka ji tsoron Yahweh Allahnka, kayi tafiya cikin dukkan tafarkunsa, ka ƙaunace shi, ka kuma yi sujada ga Yahweh Allahnka da dukkan zuciyarka da kuma dukkan ranka, 13 don ka kiyaye dokokin Yahweh, da farillansa, waɗanda nake umartan ka yau domin lafiyarka? 14 Duba, sama da kuma sama ta sammai na Yahweh Allahnka ne, duniyan, da dukkan abin da ke cikinta. 15 Yahweh ne kawai ya ji daɗin ubanninku da har ya ƙaunace su, ya kuma zaɓe ku, zuriyarsu, a bayansu, fiye da kowanne sauran mutane, kamar yadda ya ke yi yau. 16 Don haka kuyi wa loɓan zuciyarku kachiya, kuma kada ku ƙara taurin kai kuma. 17 Gama Yahweh Allahnku, shi ne Allahn alloli da kuma Ubangijin iyayengiji, Allah Alƙadiru, mai girma mai bantsoro, wanda baya nuna sonkai baya kuma karɓan toshi. 18 Yana aikata adalci domin marayu da gwamraye, kuma yana nuna ƙauna ga wanda ke baƙo ta yadda ya ke ba shi abinci da tufafi. 19 Saboda haka ka ƙaunaci wanda ya ke baƙo; gama ku da kanku dã baƙi ne a ƙasar Masar. 20 Zaka ji tsoron Yahweh Allahnku; shi ne zaka yi masa sujada. Gare shi dole zaka manne, kuma da sunansa zaka yi rantsuwa. 21 Shi ne yabonka, kuma shi ne Allahnka, wanda ya aikata domin ka waɗannan al'amura masu girma da kuma ban-tsoro, waɗanda idanunku suka gani. 22 Ubanninku suka tafi cikin Masar su mutum saba'in ne; yanzu Yahweh Allahnka ya maishe ka dayawa kamar taurarin sammai.

Sura 11

1 Saboda haka zaka kaunaci Yahweh Allahnka ka kuma kiyaye umarnansa, da farillansa, da shari'unsa, da dokokinsa koyaushe. 2 Ku yi la'akari da cewa ba da 'ya'yan ku nake magana ba, waɗanda basu sani ko suka ga hukuncin Yahweh Allahnku, da girmansa, hannunsa mai iko, ko miƙaƙƙiyar zira'assa, 3 da alamomi da kuma ayyukan da ya yi cikin Masar ga Fir'auna, sarkin Masar, ga kuma dukkan ƙasarsa. 4 Ba su kuma ga abin da ya yi wa rundunar Masarawa ba, ko ya yi wa karusansu, yadda ya sa ruwayen Jan Teku suka haɗiye su yayin da suke bin bayansu, da kuma yadda Yahweh ya hallakar da su har wa yau, 5 ko abin da ya yi maku cikin jeji har kuka zo wannan wuri. 6 Ba su ga abin da Yahweh ya yi wa Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab ɗan Ruben ba, yadda ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su dukka, da danginsu, da rumfarsu, da kowanne abu mai rai da ya biyo su, a tsakiyar dukkan Isra'ila. 7 Amma idanunku sun ga dukkan manyan ayyukan Yahweh da ya aiwatar. 8 Don haka ku kiyaye dukkan dokokin da nake baku yau, domin ku yi ƙarfi, ku kuma shiga ku mallaki ƙasa inda kuke shigowa don ku mallake ta, 9 don kuma kwanakinku ya daɗe cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku domin ya basu da kuma zuriyarsu, ƙasa mai zubowa da madara da zuma. 10 Gama ƙasar, inda kuke shiga don ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar ba ne, inda kuka fito, wurin da kuka yi shukin irinku kuka kuma yi ban-ruwa da kafafunku, kamar lambun baƙulai; 11 amma ƙasar, da zaku shiga don ku mallake ta, ƙasa ce mai tuddai da kwaruruka, suna kuma shanye ruwan sama na sammai, 12 ƙasa wacce Yahweh Allahnku ke kula da ita; idanun Yahweh Allahnku na bisan ta koyaushe, daga farkon shekara har zuwa ƙarshen shekara. 13 Zai faru haka, idan kuka saurara da aniya ga dokokina da nake dokace ku yau, cewa ku ƙaunaci Yahweh Allahnku ku kuma bauta masa da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku, 14 sa'an nan zan bada ruwan sama na ƙasarku a kan lokaci, ruwa na farko dana ƙarshe, domin ku tara hatsinku, da sabuwar inabinku, da kuma manku. 15 Zan bada ciyawa cikin filayenku domin garkunanku, kuma zaku ci ku kuma ƙoshi. 16 Ku lura da kanku don kada a ruɗar da zuciyarku, har da zaku kauce ku yi sujada ga wasu alloli ku kuma russuna masu; 17 har fushin Yahweh shi yi ƙuna gãba daku; kuma har kada ya kulle sammai da baza a yi ruwan sama ba, kuma ƙasa ta ƙi bada amfaninta, da kuma har ku hallaka da gaggawa daga cikin ƙasa mai kyau da Yahweh ya ke baku. 18 Saboda haka ku ajiye waɗannan maganganuna a cikin zuciyarku da ranku, ku ɗaura su kamar alama a hannunku, kuma bari su zama kamar layu a tsakiyar idanunku. 19 Zaku koyar da su ga 'ya'yanku ku kuma yi zancensu lokacin da kuka zauna a gidanku, sa'ad da kuke tafiya kan hanya, da lokacin da kuke kwance, da kuma sa'ad da kuka tashi. 20 Zaku rubuta su kan kofofin gidanku da kuma bisa kofofin biranenku, 21 don kwanakinku dana 'ya'yanku shi riɓaɓɓanya cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku ya ba su har iyakar tsawon yadda sammai ke bisa duniya. 22 Domin idan kuka yi himma ga kiyaye dukkan waɗannan dokokin da nake dokatan ku, don ku aikata su, kuna ƙaunar Yahweh Allahnku, kuna tafiya cikin dukkan tafarkunsa, ku kuma manne masa, 23 sa'annan Yahweh zai kori dukkan waɗannan al'ummai a gabanku, kuma zaku washe al'umman da suka fi ku yawa da kuma ƙarfi. 24 Duk inda tafin sawunku zasu taka zasu zama naku; daga jeji zuwa Lebanon, daga kogin, Kogin Yufiretis, zuwa gabashin teku zasu zama iyakarku. 25 Babu mutumin da za ya iya tsayayya da ku. Yahweh Allahnku zai sa tsoronku da kuma razanarku bisa dukkan ƙasan da kuka taka, kamar yadda ya gaya maku. 26 Duba, na sa a gabanku yau albarka da kuma la'ana: 27 albarkan, idan kuka yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku dana dokace ku yau, 28 la'anar kuma, idan baku yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku ba, amma kuka juya daga hanyar dana dokace ku yau, don ku bi wasu allolin da baku sani ba. 29 Zai zama kuma, sa'ad da Yahweh Allahnku ya kawo ku zuwa ƙasar da kuke shiga domin ku mallake ta, zaku aza albarka bisa Dutsen Gerizim, la'ana kuma a bisa Dutsen Ebal. 30 Ba a ƙetaren Yodan suke ba, ta faɗuwar rana kan hanya, cikin ƙasar Kan'aniyawa waɗanda suke zama cikin Araba, gaba da Gilgal, daura da itatuwa na More? 31 Gama zaku ƙetare Yodan domin ku shiga ciki ku mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kuma za ku mallaketa ku kuma zauna cikinta. 32 Za ku kiyaye dukkan farillai da umarnan dana shirya a gabanku yau.

Sura 12

1 Waɗannan su ne farillai da dokoki da zaku kiyaye cikin ƙasar da Yahweh, Allahn ubanninku, ke baku domin ku mallaka, dukkan kwanakin da zaku rayu a duniya. 2 Tabbas zaku lallata dukkan wuraren da al'umman da zaku kora suka bauta wa allolinsu, a bisa duwatsu masu tsawo, a bisa tsaunuka, da kuma ƙarƙashin kowanne koren itace. 3 Dole ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje ginshiƙansu na dutse, ku ƙone dogayen sandunansu na Ashera. Dole ku sassare sassaƙaƙƙun siffofin allolinsu ku hallaka sunayensu daga wurin nan. 4 Ba zaku yi sujada ga Yahweh Allahnku haka ba. 5 Amma wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa daga cikin dukkan kabilunku ya sa sunansa, wannan zai zama wurin da zai zauna kuma wurin ne zaku tafi. 6 A can ne zaku kawo baye-bayenku na ƙonawa, hadayunku, zakkarku, da baye-bayenku da kuka bayar da hannunku, baye-bayenku na wa'adodi, da baye-bayenku na yaddar rai, da 'ya'yan fari na garkunanku na shanu dana tumaki. 7 A can ne zaku ci a gaban Yahweh Allahnku ku yi murna akan kowanne abin da kuka sa hannunku a gare shi, ku da iyalanku, wurin da Yahweh Allahnku ya albarkace ku. 8 Ba zaku yi dukkan abubuwan da muke yi anan ba yau; yanzu kowanne yana yin abin da yaga ya dace a gare shi; 9 gama baku zo wurin hutawa ba tukuna, ga abin gãdo da Yahweh Allahnku ya ke baku. 10 Amma idan kuka haye Yodan kuka kuma zauna cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku ita gãdo, kuma zai baku hutu daga dukkan maƙiyanku da ke kewaye da ku, domin ku zauna lafiya. 11 Daga nan zuwa wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa yasa sunansa ya zauna a wurin -- a can ne zaku kawo kowanne abin da na umarce ku: baye-bayenku na ƙonawa, da hadayunku, da zakkarku, da baye-bayen da kuka bayar da hannunku, da dukkan baye-bayen da kuka zaɓa domin wa'adodi da zaku yi wa'adi ga Yahweh. 12 Zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da bayinku maza, da bayinku mata, da Lebiyawan da ke zama tare da ku, saboda ba shi da rabo ko gãdo a cikin ku. 13 Ku kula da kanku kada ku miƙa baye-bayenku na ƙonawa a kowanne wurin da kuka gani; 14 amma a wurin da Yahweh zai zaɓa a cikin ɗaya daga cikin kabilunku zaku miƙa baye-bayenku na ƙonawa, kuma a can ne zaku yi kowanne abin da na dokace ku. 15 Duk da haka, zaku iya yanka dabbobi ku kuma ci a ko'ina cikin biranenku, kamar yadda kuke so, kuna karɓan albarkar Yahweh Allahnku domin dukkan abin da ya baku; mutane marasa tsarki da masu tsarki dukkansu za su iya ci, dabbobi kamar gada da barewa. 16 Amma ba zaku ci jinin ba; zaku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. 17 Ba zaku ci waɗannan a garuruwanku ba daga zakkar hatsinku, sabon inabinku, man ku, ko 'ya'yan farin shanunku, ko tumakinku; ba zaku ci kowanne nama da kuka yi hadaya tare da kowanne wa'adodinku da kuka yi, ko kuma baye-bayenku na yaddar rai, ko baikon da kuka bayar da hannunku. 18 Maimakon haka, sai ku ci su a gaban Yahweh Allahnku a wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku maza, da barorinku mata, da Balebi wanda ke zaune a garuruwanku; zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku game da kowanne abin da ya sa a hannunku. 19 Ku lura da kanku domin kada ku manta da Lebiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku. 20 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya fãɗaɗa iyakokinku, kamar yadda ya alƙawarta maku, sa'annan kuka ce, 'Zan ci nama,' saboda ƙãwar cin nama, zaku iya cin nama, yadda ranku ya ke so. 21 Idan wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa ya yi maku nisa sosai, daganan sai ku yanka wasu daga garken shanunku da tumaki da Yahweh ya baku, kamar yadda na umarce ku; zaku iya ci a garuruwanku, kamar yadda ranku ya ke so. 22 Kamar gada da barewa zaku ci, sai ku ci su, mutane marasa tsarki da masu tsarki za su iya ci su ma. 23 Sai dai ku tabbata baku ci jinin ba, gama jinin shi ne ran; ba zaku ci rai da nama ba. 24 Kada ku ci shi, zaku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. 25 Ba zaku ci shi ba, domin kome ya tafi lafiya tare da ku, tare da 'ya'yanku a bayan ku, idan kuka yi abin da ke dai dai a gaban Yahweh. 26 Amma abubuwan da ke na Yahweh da kuke da su da baye-bayen wa'adodinku -- zaku ɗauki waɗannan zuwa wurin da Yahweh ya zaɓa. 27 A can ne zaku miƙa baye-bayenku na ƙonawa, naman da jinin, akan bagadin Yahweh Allahnku; za a zubar da jinin hadayunku akan bagadin Yahweh Allahnku, kuma zaku ci naman. 28 Ku lura kuma ku saurara ga dukkan kalmomin da na dokace ku da su, don ku sami zaman lafiya tare da 'ya'yanku a bayanku har abada, yayin da kuke yin abin da ke mai kyau da yin dai-dai a gaban idanun Yahweh Allahnku. 29 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya datse al'umman daga gabanku, sa'ad da kuka je kuka kore su, kuka mallake su, kuka zauna cikin ƙasarsu, 30 ku yi hankali da kanku kada ku faɗa cikin tarkon bin su, bayan da an hallaka su a gabanku -- kada ku faɗa cikin tarkon binciko allolinsu, cikin tambayar, 'Ta yaya waɗannan al'ummai suka yi wa allolinsu sujada? Zan yi kamar yadda suka yi.' 31 Kada ku yi wa Yahweh Allahnku sujada ta irin wannan hanya, gama kowanne abin ƙyama ga Yahweh, abubuwan da ya ƙi -- sun yi waɗannan abubuwa tare da allolinsu; har sun ƙona 'ya'yansu maza da mata cikin wuta domin allolinsu. 32 Iyakar abin dana dokace ku, ku aikata shi, kada ku ƙara masa ko ku rage daga gare shi.

Sura 13

1 Idan wani annabi ya tashi daga cikinku ko mai mafarkin mafarkai, kuma idan ya baku wata alama ko mu'ujiza, 2 kuma idan alamar ko mu'ujizar ta faru, wanda ya yi maku magana ya ce, 'Bari mu bi waɗansu allolin, da baku sani ba, kuma bari muyi masu sujada,' 3 kada ku saurari maganganun annabin nan, ko mai mafarkin mafarkan; gama Yahweh Allahnku yana gwada kune ya sani ko kuna ƙaunar Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku tare da dukkan ranku. 4 Zaku bi Yahweh Allahnku, ku girmama shi, ku kiyaye dokokinsa, kuyi biyayya da muryarsa za kuyi masa sujada kuma ku manne masa. 5 Wannan annabin ko wannan mai mafarkin mafarkai za a kashe shi, saboda ya yi maganar tayarwa gãba da Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, da wanda ya fãnshe ku daga gidan bauta. Wannan annabi yana so ya karkatarda ku daga hanyar da Yahweh Allahnku ya dokace ku ku yi tafiya a kanta. Don haka sai ku kawar da mugunta daga cikinku. 6 Idan ɗan'uwanka, ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko ɗiyarka, ko matar da ke ƙirjinka, ko abokinka wanda ke ƙaunar ranka, a asirce ya lallasheka ya ce, 'Bari muje mu bauta wa wasu allolin da baku sani ba, ko ku ko kakanninku -- 7 kowanne allolin mutanen da ke kewaye daku, ko kusa daku, ko nesa can daku, daga wannan iyakar duniya zuwa ƙarshen waccan iyakar duniya,' 8 Kada ku yarda da shi ko ku saurare shi, kada ku bari idonku ya ji tausayinsa, kada ku barshi koku ɓoye shi. 9 Maimakon haka, ku tabbata kun kashe shi; hannunku ne zai zama na farko wajen kisan sa, daga nan sai hannun dukkan jama'a. 10 Zaku jejjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi ƙoƙarin janye ku daga Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 11 Dukkan Isra'ila zasu ji kuma suji tsoro, kuma ba zasu ci gaba da yin irin wannan mugun abu a cikin ku ba. 12 Idan kuka ji wani ya ce wani abu game da ɗaya daga cikin biranenku, da Yahweh Allahnku ya baku ku zauna ciki: 13 Waɗansu mugaye sun fita daga cikinku har sun janye mazaunan birnin suka ce, 'Bari muje muyi sujada ga allolin da baku sani ba.' 14 Daganan sai ku yi nazarin shaidar, ku bincika, ku tabbatar da kyau. Idan kun gãne cewa gaskiya ne kun haƙiƙance cewa abin ƙyama irin wannan ya faru a cikinku, daganan sai ku ɗauki mataki. 15 Ku tabbatar kun kai wa mazaunan birnin hari da kaifin takobi, ku hallaka shi da dukkan mutanen da ke zaune ciki, tare da dabbobinsa, da kaifin takobi gaba ɗaya. 16 Zaku tattara dukkan ganimar daga gare shi zuwa cikin tsakiyar tituna zaku ƙone birnin, da dukkan ganimar -- domin Yahweh Allahnku. Birnin zai zama tsibin kufai har abada; ba za a ƙara gina shi ba. 17 Ba ɗaya daga cikin abubuwan da aka keɓe domin hallakarwa da zai liƙe cikin hannunku. Dole haka ya faru, domin Yahweh ya juya daga zafin fushinsa, ya nuna maku jinkai, ya ji tausayinku, yasa ku riɓanɓanya, kamar yadda ya rantse wa kakanninku. 18 Zai yi wannan saboda kuna sauraron muryar Yahweh Allahnku, kuna kiyaye dukkan dokokin dana dokace ku da su yau, kuna yin abin da ke dai-dai a gaban Yahweh Allahnku.

Sura 14

1 Ku mutanen Yahweh Allahnku ne. Kada ku tsãge kanku, ko ku aske kowanne sashi na fuskarku domin matacce. 2 Gama ku al'umma ce keɓaɓɓiya ga Yahweh Allahnku, Yahweh kuma ya zaɓe ku ku zama mutane abin mallaka, fiye da dukkan al'umman da ke a fuskar duniya. 3 Ba zaku ci kowanne abin da ke haram ba. 4 Waɗannan su ne dabbobin da zaku iya ci: saniya, da tunkiya, da akuya, 5 da mariri, da barewa, da mazo, da bunsurun daji, da makwarwa, da gada, da ragon dutse. 6 Zaku iya cin kowacce dabbar da ke da rababben kofato, wato, wadda kofatonta sun rabu kashi biyu, kuma tana tuƙa. 7 Duk da haka, ba zaku ci waɗansu dabbobin da suke tuƙa kuma suke da rababben kofato ba misali: raƙumi, da zomo, da reman dutse; saboda suna tuƙa amma ba su da rababben kofato, marasa tsarki ne a gare ku. 8 Alade ma ba shi da tsarki a gare ku saboda yana da rababben kofato amma ba ya yin tuƙa; haram ne a gare ku. Kada kuci naman alade, kada kuma ku taɓa mushensu. 9 Daga irin waɗannan da suke cikin ruwa zaku iya ci: duk abin da ke da ƙege da ɓanɓaroki; 10 amma duk abin da ba shi da ƙege da ɓanɓaroki kada ku ci su; marasa tsarki ne a gare ku. 11 Zaku iya cin dukkan tsarkakakkun tsuntsaye. 12 Amma waɗannan tsuntsayen da ba zaku ci ba: Mikiya, da Ungulu, da ƙwaƙwa, 13 da jar shirwa da baƙar shirwa, da kowanne irin shaho. 14 Kada ku ci kowanne irin hankaka, 15 da jimina, da ƙururu, da harbiyar ruwa, kowanne irin shaho, 16 ƙaramar mujiya da babbar mujiya, da farar mujiya, 17 da zalben ruwa, da ungulu, da agwagwar daji. 18 Ba zaku ci zalɓe ba, da kowanne irin jinjimi, bunburwa da jemage. 19 Dukkan abin da ke da fiffike da masu rarrafe marasa tsarki ne a gare ku; ba zaku ci su ba. 20 Zaku iya cin dukkan tsarkakakkun abubuwan da suke shawagi. 21 Kada ku ci kowanne abin da ya mutu da kansa; za ku iya ba baƙon da ke cikin garuruwanku, domin ya ci; ko ku sayar da shi ga baƙo. Gama ku al'umma ce keɓaɓɓiya ga Yahweh Allahnku. Ba zaku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa ba. 22 Dole ku tabbata kun fitar da zakkar dukkan amfanin irin da kuka shuka, wanda ke tsirowa a gona kowacce shekara. 23 Dole ku ci a gaban Yahweh Allahnku, a wurin da zai zaɓa a matsayin wuri mai tsarki, zakkar hatsin ku, da sabon inabi, dana manku, da 'ya'yan farin shanunku dana dabbobinku; domin kullum ku koyi girmama Yahweh Allahnku. 24 Idan tafiyar ta yi maku nisa kwarai da baza ku iya kai ta ba, saboda wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa a matsayin wurin sa mai tsarki ya yi maku nisa, daganan, idan Yahweh ya albarkace ku, 25 sai ku sayar da zakkar ku mai da ita kuɗi, sai ku ƙulle kuɗin cikin hannunku, ku tafi wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa. 26 A can ne zaku kashe kuɗin akan duk abin da kuke marmari: domin sã, ko domin tunkiya, ko domin ruwan inabi, ko domin abin sha mai ƙarfi, ko domin duk abin da kuke so; zaku ci a can a gaban Yahweh Allahnku, kuma ku yi murna, kuda iyalin gidanku. 27 Balebi wanda ya ke cikin garuruwanku -- kada ku yashe shi, gama ba shi da rabo ko gãdo tare da ku. 28 A ƙarshen kowacce shekara uku za ku kawo dukkan zakkar amfaninku cikin wannan shekarar, zaku ajiye ta cikin ƙofofinku; 29 Balebi kuma, saboda ba shi da rabo ba shi da gãdo tare daku, da baƙo, da maraya, da gwamruwa waɗanda ke cikin ƙofofinku, za su zo su ci su ƙoshi. Ku yi haka domin Yahweh Allahnku ya albarkace ku cikin dukkan aikin da hannuwanku ke yi.

Sura 15

1 A ƙarshen kowacce shekara bakwai, dole ku yafe basussuwa. 2 Ga yadda za a yi yafiyar: Kowanne mai bin bashi zai yafe abin da ya rantawa maƙwabcinsa; ba zai neme shi daga wurin maƙwabcinsa ba ko ɗan'uwansa saboda an yi shelar yafe basussuwa ta Yahweh. 3 Zaka iya nema daga wurin baƙo; amma duk abin da ke naka ya ke tare da ɗan'uwanka ba za ka nemi a biya ka ba. 4 Har yanzu, ba za a sami matalauci a cikinku ba (gama lallai Yahweh zai albarkace ku a cikin ƙasar da ya ke baku ita a matsayin gãdo ku mallaka), 5 muddin kuka saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye dukkan waɗannan dokoki da nake umartarku da su yau. 6 Gama Yahweh Allahnku zai albarkace ku, kamar yadda ya alƙawarta maku; zaku ba al'ummai da yawa rance, amma ba zaku ranta ba; zaku yi mulkin al'ummai da yawa, amma ba zasu yi mulkin ku ba. 7 Idan akwai wani mutum matalauci a cikinku, ɗaya daga cikin 'yan'uwanku, a tsakanin kowacce ƙofofinku cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kada ku taurare zuciyarku koku rufe hannunku daga ɗan'uwanku matalauci; 8 amma lallai sai ku buɗe hannunku gare shi kuma ku ranta masa issashe domin biyan bukatarsa. 9 Ku lura kada ku kasance da mugun tunani a cikin zuciyarku, kuna cewa, 'Ai shekara ta bakwai, shekarar yafewa, ta kusa,' domin kada ku zama da maƙo game da ɗan'uwanku ku kuma ƙi bashi kome; zai iya yin kuka ga Yahweh game daku, kuma ya zama zunubi a gare ku. 10 Lallai dole ku bashi, zuciyarku kuma ba zata da mu ba idan kuka bashi, saboda wannan Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin dukkan aikinku da kuma dukkan abin da kuka sanya cikin hannunku ku yi. 11 Gama ba za a rasa matalauta a cikin ƙasar ba; saboda haka na dokace ku cewa, 'Dole ku zama da hannu sake ga ɗan'uwanku, ga mabuƙatanku, da kuma matalauci a cikin ƙasarku.' 12 Idan aka sayar maku da ɗan'uwanku, Ba'ibrane ko mace ko namiji sai ya bauta maku shekara shida, daga nan a cikin shekara ta bakwai dole ku 'yantar da shi daga gare ku. 13 Idan kuka 'yantar da shi daga gare ku, ba zaku barshi ya tafi hannun wofi ba. 14 Dole ku bashi kyauta a yalwace daga cikin tumakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Kamar yadda Yahweh Allahnku ya albarkace ku, dole ku ba shi. 15 Dole ku tuna cewa dã ku bayi ne a cikin ƙasar Masar, kuma Yahweh Allahnku ya fãnshe ku; don haka nake umartarku yau ku yi haka. 16 Idan kuma ya ce maku, 'Ba zan tafi daga gare ku ba,' saboda yana ƙaunarku da gidanku, kuma yana jin daɗin zama tare da ku, 17 daganan sai ku ɗauki bisilla ku huda kunnensa har dogaran ƙofa, zai zama bawanku har iyakar rayuwa. Haka kuma zaku yi da mace baiwa. 18 Kada ya zama da damuwa a gare ku idan kuka 'yantar shi daga gare ku, saboda ya yi maku bauta shekaru shida darajar bautarsa ta ninka biyu da ta mutumin da aka yi hayarsa. Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin dukkan abin da kuke yi. 19 Dukkan 'ya'yan farin a cikin garkunan shanunku dana tumaki dole ku keɓe su ga Yahweh Allahnku. Kada ku yi aiki da 'ya'yan farin shanunku, koku yi sausayar ɗan farin tumakinku. 20 Dole ku ci ɗan farin a gaban Yahweh Allahnku kowacce shekara a wurin da Yahweh ya zaɓa, ku da iyalinku. 21 Idan tana da wani cikas -- misali, gurguntaka, ko makanta ko tana da wani cikas ta kowanne iri -- kada ku miƙa ta hadaya ga Yahweh Allahnku. 22 Zaku ci ta a garuruwanku; mutane marasa tsarki da masu tsarki su ma dole su ci, kamar mariri ko barewa. 23 Sai dai kada ku ci jinin; dole ku zubar da jinin a ƙasa kamar ruwa.

Sura 16

1 Ku kiyaye watan Abib, kuma ku kiyaye Bukin Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku, gama a watan Abib ne Yahweh Allahnku ya fito daku daga Masar da daddare. 2 Zaku miƙa hadayar Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku tare da wasu garkunan tumakinku dana shanu a wurin da Yahweh zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. 3 Ba zaku ci abinci mai gami tare da ita ba; kwana bakwai zaku ci abinci mara gami tare da hadayar, abincin wahala ne; gama kun fito daga ƙasar Masar da gaggawa. Kuyi haka dukkan kwanakinku domin ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar. 4 Kada a ga gami a cikinku a dukkan iyakokinku a lokacin kwanaki bakwai; kada kowanne naman da kuka miƙa hadaya da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya. 5 Kada ku miƙa hadayar Ƙetarewa a kowanne garin da Yahweh ya ke baku. 6 Maimakon haka, ku miƙa ta a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. A can zaku miƙa hadayar Ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, a dai-dai lokacin da shekarar da kuka fito daga Masar. 7 Dole ku gasa shi kuma ku ci shi a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa; da safe zaku juya ku koma zuwa rumfunanku. 8 Kwana shida zaku yi kuna cin abinci mara gami; a rana ta bakwai sai kuyi muhimmin taro domin Yahweh Allahnku; a wannan ranar kada kuyi aiki. 9 Zaku ƙirga mako bakwai domin kanku; daga lokacin da kuka fara sa lauje ga hatsinku da ke tsaye dole ku fara ƙirga makonni bakwai. 10 Dole ku kiyaye Bikin Makonni domin Yahweh Allahnku tare da bada gudunmuwa ta yaddar rai daga hannunku da zaku bayar, gwargwadon yadda Yahweh Allahnku ya albarkace ku. 11 Zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku - ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku maza, da barorinku mata, da Balebiyen da ke zaune a ƙofofin garinku, da baƙo, da marayu, da gwamruwa waɗanda ke tare da ku, a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa domin wurinsa mai tsarki. 12 Ku tuna dã ku bayi ne a Masar; dole ku kiyaye kuma ku aikata waɗannan farillai. 13 Dole ku kiyaye Bikin Bukkoki kwanaki bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku da wurin matsewar ruwan inabinku. 14 Zaku yi murna a lokaci bikin -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku mata, da Balebiye, da baƙo, da maraya da gwamruwa waɗanda ke a garuruwanku. 15 Kwana bakwai zaku kiyaye biki ga Yahweh Allahnku a wurin da Yahweh zai zaɓa, saboda Yahweh Allahnku zai albarkace ku a cikin dukkan aikin hannuwanku, kuma dole ku zama da cikakkiyar murna. 16 Sau uku a shekara dole dukkan mazajenku su hallara a gaban Yahweh Allahnku a wurin da zai zaɓa: a lokacin Bikin Abinci Marar Gami, da lokacin Bikin Makonni, da kuma lokacin Bikin Bukkoki. Kada wani ya hallara gaban Yahweh hannu- wofi; 17 maimakon haka, kowanne mutum zai bayar gwargawdon abin da zai iya, domin ku san albarkar da Yahweh Allahnku ya bayar gare ku. 18 Dole ku naɗa alƙalai da shugabannai a dukkan ƙofofin garuruwanku da Yahweh Allahnku ya ke baku; za a ɗauko su daga kowacce kabilarku, dole su shari'anta jama'a da shari'a ta adalci. 19 Kada ku ɗauke adalci da ƙarfi; kada ku nuna son kai koku karɓi cin hanci, gama cin hanci yana makantar da idanun mai hikima ya karkatar da maganganun adali. 20 Dole kubi adalci, bayan adalci kaɗai, domin ku rayu ku iya gãdon ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku. 21 Kada ku sanya wa kanku Asherah, kowanne irin itace, kusa da bagadin Yahweh Allahnku da zaku yi domin kanku. 22 Kada kuma ku gina wa kanku al'amudin dutse, wanda Yahweh Allahnku ya ke ƙi.

Sura 17

1 Kada ku miƙa wa Yahweh Allahnku hadaya ta sã ko tunkiya da ke da kowanne lahani ko duk abin da bashi da kyau, gama wannan zai zama abin ƙyama ga Yahweh Allahnku. 2 Idan aka sami wani, a tsakanin kowaɗanne ƙofofin garinku da Yahweh Allahnku ya ke baku, kowanne mutum ko mace, wanda ya aikata abin da ke mugu a gaban Yahweh Allahnku yana karya alƙawarinsa, 3 duk wanda yaje ya yi sujada ga waɗansu alloli ya kuma russuna masu, ko rana, ko wata, ko kowacce rundunar sama - ba abin dana umarce ku ba - 4 idan aka faɗa maku game da wannan, ko kuka ji labarinsa, daganan dole kuyi bincike a hankali. Idan gaskiya ne kuma an tabbatar da anyi irin wannan abin ƙyamar a Isra'ila, wannan shi ne abin da zaku yi. 5 Dole ku kawo wannan mutum ko macen, wanda ya aikata wannan mugun abu, ga ƙofofin garuruwanku, wannan mutumin ko macen, dole ku jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. 6 Bisa ga shaidu biyu ko shaidu uku, za a kashe shi; amma ba za a kashe mutum bisa ga shaidar mutum ɗaya ba. 7 Hannun shaidun zasu fara jifansa ga mutuwa, daganan sauran dukkan jama'a; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku. 8 Idan wani abu ya taso da ya zama da wahala a gare ku ku shari'anta - watakila zancen kisankai ko haɗarin mutuwa, ta zancen 'yancin wani da ta wani, ko tambaya akan wani irin lahani da aka yi, ko dai wani al'amari, al'amura masu wahalarwa a cikin ƙofofin garinku -- daga nan dole ku tafi wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. 9 Dole ku je wurin firist, zuriyar Lebi, da kuma wurin alƙali da zai yi hidima a lokacin; zaku nemi shawararsu, zasu baku mafita. 10 Dole ku bi shari'ar da aka baku a wurin da Yahweh zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. Dole ku lura ku yi dukkan abin da suka jagorance ku ga yi. 11 Kubi shari'ar da suka koya maku, ku kuma yi bisa ga shawarwarin da suka baku. Kada ku kauce daga abin da suka faɗa maku, zuwa hananun dama ko zuwa hannun hagu. 12 Duk wanda ya yi isgilanci, ta wurin ƙin sauraron firist wanda ke tsaye ya bauta wa Yahweh Allahnku, ko ta ƙin sauraron alƙali - wannan mutum zai mutu; dole ku kawar da mugunta daga Isra'ila. 13 Dukkan mutane dole suji kuma suji tsoro, ba zasu ƙara yi isgilanci ba. 14 Sa'ad da kuka zo ƙasar da Yahweh Allahnku ya ba ku, kuma idan kuka mallake ta kuka fara zama cikinta, sa'an nan kuka ce, 'Zan sanya sarki a bisa kaina, kamar dukkan al'umman da suke kewaye da ni,' 15 daga nan dole ku tabbatar kun naɗa wa kanku sarki wanda Yahweh Allahnku zai zaɓa. Dole ku naɗa wa kanku sarki wanda ke daga cikin 'yan'uwanku. kada ku sanya baƙo, wanda ba ɗan'uwanku ba, a bisa kanku. 16 Amma kada ya ƙara wa kansa dawakai, kada ya sa mutane su koma Masar don su ƙaro masa dawakai, gama Yahweh ya ce maku, 'Kada ku ƙara komawa can.' 17 Kada ya ɗauki mata da yawa domin kansa, domin kada zuciyarsa ta karkace. Kada ya tattara wa kansa tulin kuɗin azurfa da zinariya. 18 Sa'ada da ya zauna kan gadon sarautar mulkinsa, dole ya rubutawa kansa a cikin naɗaɗɗen kwafin littafi shari' an nan, daga shari'a da ke gaban firist, waɗanda suke Lebiyawa. 19 Naɗaɗɗen littafin zai kasance tare da shi, kuma dole ya karanta shi cikin dukkan kwanakin ransa, domin ya koyi girmama Yahweh Allahnsa, domin ya kiyaye dukkan kalmomin shari'ar da waɗannan farillai, ya kiyaye su. 20 Dole ya yi haka domin kada zuciyarsa ta kumbura bisa kan 'yan'uwansa, domin kada ya kauce daga bin dokokin, zuwa dama ko hagu; domin ya sami dalilin daɗewa cikin mulkinsa, shi da 'ya'yansa, a cikin Isra'ila.

Sura 18

1 Firistoci, da suke Lebiyawa, da dukkan kabilar Lebi, ba za su sami rabo ko gãdo tare da Isra'ila ba; dole su ci baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta a matsayin gãdonsu. 2 Ba zasu sami gãdo tare da 'yan'uwansu ba; Yahweh shi ne gãdon su, kamar yadda ya faɗa masu. 3 Wannan shi ne rabon da aka ba firistoci, aka basu daga mutanen da suka miƙa hadaya, ko ta sã ne ko tunkiya ce: kafaɗar, kumatu biyu, da kuma kayan ciki. 4 Sai nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabi, da manku, da gashin tumakinku da kuka fara sausaya, dole ku ba shi. 5 Gama Yahweh Allahnku ya zaɓe shi da ga cikin kabilunku su tsaya su yi hidima a cikin sunan Yahweh, shi da 'ya'yansa har abada. 6 Idan Balebiye ya fito daga kowanne garinku na dukkan Isra'ila daga inda ya ke zama, kuma ya yi marmari da dukkan ransa ya zo wurin da Yahweh ya zaɓa, 7 daganan dole ya yi hidima a cikin sunan Yahweh Allahnsa kamar yadda dukkan 'yan'uwansa Lebiyawa suke yi, waɗanda ke tsayawa a can a gaban Yahweh. 8 Dole su sami rabo iri ɗaya su ci, banda abin da ke zuwa daga abin da iyalinsa suka sayar na gãdo. 9 Sa'ad da kuka zo cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kada kuyi kwaikwayon ayyukan banƙyama na waɗannan al'ummai. 10 Kada a sami wani a cikinku da zai miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya cikin wuta, duk wanda ke amfani da maita ko mai faɗin gaibu, ko mai sihiri, ko ya shiga maita, 11 duk mabiya, ko mai sha'ani da ruhohi ko mai surkulle, mai magana da ruhohin matattu. 12 Gama duk mai yin waɗannan abubuwa abin ƙyama ne ga Yahweh; saboda waɗannan abubuwan ban ƙyama ne Yahweh Allahnku ya ke korarsu daga gaban ku. 13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Yahweh Allahnku. 14 Gama waɗannan al'ummai da zaku kora suna sauraran masu aikata maita da masu duba; amma ku, Yahweh Allahnku bai yaddar maku ku yi haka ba. 15 Yahweh Allahnku zai tayar maku da wani annabi daga cikinku, ɗaya daga cikin 'yan'uwanku, kama ta. Dole ku saurare shi. 16 Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Yahweh Allahnku a Horeb a ranar taron, cewa, 'Kada ka barmu mu ƙara jin muryar Yahweh Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don zamu mutu.' 17 Yahweh ya ce mani, 'Abin da suka ce yana da kyau. 18 Zan tayar masu da wani annabi daga cikin 'yan'uwansu, kamar ka. Zan sa maganganuna cikin bakinsa, zai faɗa masu dukkan abin da na dokace shi. 19 Zai kasance kuwa duk wanda bai saurari maganganuna da zai faɗa a cikin sunana ba, Zan nemi haƙƙinta a gareshi. 20 Amma annabin da ya faɗi maganar isgilanci cikin sunana, maganar da ban umarce shi ba ya faɗa, ko wanda ya yi magana cikin sunan waɗansu alloli, wannan annabin dole ya mutu.' 21 Wannan shi ne abin da zaku ce a cikin zuciyarku: 'Ta yaya zamu san saƙon da Yahweh bai faɗi ba?' 22 Zaku gane saƙon da Yahweh ya faɗa idan annabi ya yi magana a cikin sunan Yahweh. Idan wannan abin bai zo ba, ko bai faru ba, daganan wannan shi ne abin da Yahweh bai faɗa ba kuma annabin ya faɗe shi ne cikin isgilanci, kada ku ji tsoronsa.

Sura 19

1 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya datse al'ummai, waɗannan waɗanda Yahweh Allahnku zai baku ƙasarsu, sa'ad da kuka zo bayansu kuka zauna a cikin garuruwansu da gidajensu, 2 sai ku zaɓi birane uku domin kanku a tsakiyar ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke ba ku ku mallaka. 3 Sai ku gina hanyoyi ku kuma raba iyakokin ƙasarku kashi uku, ƙasar da Yahweh Allahnku ke saku gãda, domin duk wanda ya kashe wani mutum sai ya gudu zuwa can. 4 Wannan itace doka domin wanda ya kashe wani da wanda ya gudu can don ya tsira - duk wanda ya kashe maƙwabcinsa ba don ya yi niyya ba, kuma bai ƙi shi ba a dã. 5 Misali, idan mutum ya tafi cikin jeji tare da maƙwabcinsa domin su saro itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar ya sari maƙwabcinsa ya kashe shi - daganan wannan mutumin dole ya gudu zuwa ɗaya daga biranen domin ya tsirar da ransa. 6 Idan ba haka ba mai bin haƙƙin jini zai iya bin shi wanda ya ɗauki ran, cikin zafin fushinsa ya cim masa, idan nisan ya yi yawa sosai, ya cim masa ya kashe shi, koda shike mutumin nan bai cancanci mutuwa ba, tunda shike bai ƙi shi ba a dã. 7 Don haka na dokace ku ku keɓe wa kanku birane uku. 8 Idan Yahweh Allahnku ya fãɗaɗa iyakokinku, kamar yadda ya alƙawarta wa kakanninku zai yi, ya baku dukkan ƙasar da ya alƙawarta ya ba kakanninku; 9 idan kuka kiyaye dukkan waɗannan dokoki kuka aikata su, waɗanda nake dokatarku da su yau - dokokin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku kullum kuyi tafiya cikin hanyoyinsa, daganan sai ku ƙara birane uku domin kanku, akan waɗannan ukun kuma. 10 Kuyi haka domin kada a zubar da jinin mara laifi a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku domin gãdo, domin kada alhakin jini ya kasance a kanku. 11 Amma idan wani yana ƙin maƙwabcinsa, ya yi kwanto yana jiransa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, idan ya gudu zuwa cikin ɗaya daga cikin biranen nan - 12 daganan dattawan garinsu dole su aika a kawo shi daga can, daganan su miƙa shi a hannun ɗan'uwan mai bin hakƙin jini domin a kashe shi. 13 Kada idannunku su tausaya masa; maimakon haka dole ku kawar da alhakin zubar da jini daga Isra'ila, domin ku sami zaman lafiya. 14 Kada ku kawar da iyakar maƙwabcinka da kakanninku suka kafa tuntuni, a cikin gãdon da zaku gãda, a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka. 15 Shaidar mutum ɗaya ba zata isa a tabbatar da cewa mutum ya yi kowanne irin laifi ba, ko kowanne zunubi, a kan kowanne zunubin da ya yi; sai an ji a bakin shaidu biyu ko uku, kafin a tabbatar da kowanne abu. 16 Alal misali idan mashaidi marar adalci ya tashi gãba da kowanne mutum ya shaida sharri game da laifinsa. 17 Daganan sai dukkansu mutanen, waɗanda rashin jituwar ta faru tsakaninsu, dole su tsaya gaban Yahweh, a gaban firistoci da alƙalai masu yin hidima akwanakin nan. 18 Dole alƙalan suyi bincike sosai; su duba, idan mai shaidar mai shaidar zur ne, ya yi shaidar ƙarya game da ɗan'uwansa, 19 daganan sai ku yi masa, kamar yadda ya so ayi wa ɗan'uwansa; kuma zaku kawar da mugunta daga cikinku tawurin yin haka. 20 Daganan sauran da suka ragu zasu ji su ji tsoro, kuma daganan ba zasu ƙara aikata irin wannan mugunta a cikinku ba. 21 Kada idannunku su tausaya; rai maimakon rai, ido mai makon ido, haƙori mai makon haƙori, hannu mai makon hannu, ƙafa mai makon ƙafa.

Sura 20

1 Sa'ad da kuka tafi yaƙi gãba da maƙiyanku, idan kunga dawakai, karusai, da mutanen da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu; Gama Yahweh Allahnku yana tare daku, shi wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. 2 Sa'ad da kuke gab da shiga cikin yaƙi, sai firist ya kusato ya yi magana da mutane. 3 Dole ya ce masu, 'Ku saurara, Isra'ila, zaku tafi yaƙi gãba da maƙiyanku. Kada ku bari zukatanku su karaya. Kada kuji tsoro ko ku firgita. Kada kuji tsoronsu. 4 Gama Yahweh Allahnku shi ne mai tafiya tare daku ya yi yaƙi domin ku gãba da maƙiyanku ya cece ku kuma.' 5 Dole shugabanni suyi magana da mutane su ce, 'Ko akwai wani mutum wanda ya gina sabon gida da bai buɗe shi ba? Bari ya koma gidansa, domin kada ya mutu cikin yaƙi sa'an nan wani mutum dabam ya yi bikin buɗewarsa. 6 Ko akwai wani daya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Bari ya koma gida, domin kada ya mutu a cikin yaƙi wani mutum dabam yaci amfaninta. 7 Wanne mutum ne ya ke tashin mace amma bai aure ta ba tukuna? Bari ya koma gida domin kada ya mutu a cikin yaƙi sa'an nan wani mutum dabam ya aure ta.' 8 Shugabannin zasu ci gaba da yiwa mutane magana su ce, 'Ko a kwai wani mutum a nan da ya ke jin tsoro ko mai karyayyar zuciya? Bari ya koma gidansa, domin kada zuciyar 'yan'uwansa su narke kamar yadda zuciyarsa ta narke.' 9 Sa'ad da shugabanni suka gama yin magana da mutane, dole su naɗa hafsoshi a kansu. 10 Sa'ad da kuka kusanci wani birni don ku kai masa hari, ku ba mutanen birnin kyautar salama. 11 Idan suka karɓi kyautar ku har suka buɗe maku ƙofofinsu, dukkan mutanen da kuka sãmu a cikinsa dole suyi maku aikin gandu kuma su bauta maku. 12 Amma idan ya ƙi yin salama daku, maimakon haka sai ya yi yaƙi daku, daganan sai ku kewaye shi da yaƙi, 13 idan kuma Yahweh Allahnku ya baku nasara ya sa su ƙarƙashin sarrafawar ku, dole ku kashe kowanne mutum a cikin garin. 14 Amma mata da ƙanana, da dabbobi, da kowanne abin da ke cikin birnin, da dukkan ganimarsu, zaku ɗauka a matsayin ganima domin kanku. Zaku ci ganimar maƙiyanku, wadda Yahweh Allahnku ya baku. 15 Haka zaku aikata ga dukkan biranen da ke nesa daku sosai, biranen da ba biranen waɗannan al'ummai ba. 16 A cikin biranen al'umman nan da Yahweh Allahnku ya ke baku a matsayin gãdo, kada ku bar kowanne abin da ke numfashi da rai. 17 Maimakon haka zaku hallakar da su ƙarƙaf: Su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da Yebusiyawa, kamar yadda Yahweh Allahnku ya dokace ku. 18 Ku yi haka domin kada su koya maku ku aikata kowanne abin banƙyamarsu kamar yadda suka yi tare da allolinsu. Idan kuka yi, zaku yi zunubi ga Yahweh Allahnku. 19 Sa'ad da kuka daɗe da kewaye birni, yayin da kuke yaƙi da shi domin ku ci shi, kada ku hallaka itatuwansa da gatari ta wurin saransu. Gama zaku iya ci daga gare su, don haka kada ku sare su ƙasa. Gama itacen gona mutum ne da zaku kewaye shi da yaƙi? 20 Itatuwan kaɗai da kuka sani ba itatuwan da ake ci ba, zaku iya hallakarwa ku sare su ƙasa; zaku gina kagara da su gãba da birnin da ke yaƙi daku, har sai ya faɗi.

Sura 21

1 Idan aka iske an kashe wani a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka, a kwance cikin gona, kuma ba a san wanda ya kai masa hari ba; 2 daganan sai dattawanku da alƙalanku su fita, dole su auna zuwa garuruwan da ke kewaye da shi wanda aka kashe. 3 Daganan dattawan garin da ke kusa da gawar mataccen dole su ɗauki karsana daga garke, wadda ba a taɓa aiki da ita ba, kuma ba a taɓa sa mata karkiya ba. 4 Daganan dole su jagoranci karsanar zuwa kwari inda ruwa ke gudu, kwarin da ba a noma ko shuka ba, kuma a can cikin kwarin zasu karya wuyar karsanar. 5 Sai firistoci, zuriyar Lebi, dole su zo gaba, domin Yahweh Allahnku ya zaɓe su su hidimta masa su kuma sa albarka a cikin sunan Yahweh su kuma dai-dai ta kowacce matsalar jayayya da cin mutunci ta wurin maganarsu. 6 Dukkan dattawan birni da ya fi kusa da mutumin da aka kashe dole su wanke hannuwansu a kan karsanar wadda aka karya wuyanta a cikin kwari; 7 kuma dole su amsa ga matsalar su ce, 'Hannayenmu ba su zubar da wannan jinin ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba. 8 Yahweh, ka gafarta, wa mutanenka Isra'ila, waɗanda ka fansa, kuma kada ka ɗora alhakin jinin mara laifin nan a tsakiyar mutanenka Isra'ila.' Daganan za a yafe masu zubar da jinin. 9 Ta haka zaku kawar da alhakin jinin mara laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh. 10 Sa'ad da kuka fita yaƙi gãba da maƙiyanku Yahweh Allahnku kuwa ya baku nasara yasa su ƙarƙashin sarrafawarku, kuka kuwa ɗauke su a matsayin bayi, 11 idan a cikin bayinka akwai kyakkyawar mace, wadda ka yi sha'awarta kuma kana so ka ɗauke ta domin ta zama matarka, 12 daganan sai ka kawo ta gidanka; za ta aske kanta ta kuma yanke farshenta. 13 Daganan zata tuɓe tufafinta da take sawa sa'ad da aka ɗauko ta bauta zata kasance cikin gidanka tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta wata guda cif. Bayan haka zaka iya kwana tare da ita ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka. 14 Idan ka ji baka jin daɗinta, daganan sai ka barta ta tafi wurin da ta ga dama. Amma kada ka yarda ka sayar da ita domin kuɗi, kada kuma ka wahalsheta kamar baiwa, saboda ka ƙasƙantar da ita. 15 Idan mutum yana da mata biyu sai ya nuna yana son ɗayar kuma ya ƙi ɗayar, kuma dukkansu sun haifa masa 'ya'ya - dukka da wadda ya ke ƙauna da wadda ya ke ƙi - idan ɗan farin na wadda ya ke ƙi ce, 16 daganan a ranar da zai sa 'ya'yansa su gãji abin da ya mallaka, kada yasa ɗan matar da ya ke ƙauna ya zama ɗan fari gaban ɗan matar da ya ke ƙi, wanda shi ne ainihin ɗan farin. 17 Maimakon haka, dole ya amince da wanda ya ke ɗan farin, wato ɗan matar da ya ke ƙi, ta wurin bashi kaso biyu na dukkan abin da ya mallaka; gama wannan ɗan shi ne farkon ƙarfinsa; haƙin ɗan fari nasa ne. 18 Idan mutum yana da gagararren ɗa kuma mai tayaswa wanda ba ya biyayya da maganar mahaifinsa ko maganar mahaifiyarsa, kuma wanda, koda shike sun kwaɓe shi, ba ya sauraron su; 19 daganan sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su cafke shi su kawo shi waje wurin dattawansu na birni kuma zuwa ƙofar birninsa. 20 Dole su ce da dattawan birnisa, 'Wannan ɗanmu ne gagararre ne kuma ɗan tayarwa; baya biyayya da maganar mu; shi mai zarin ci ne kuma mashayi.' 21 Daganan dukkan mutanen birni dole su jejjefeshi da duwatsu har ya mutu; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku. Dukkan Isra'ila zasu ji suji tsoro. 22 Idan mutum ya aikata zunubin da ya isa mutuwa kuma aka kashe shi, kuma aka rataye shi a bisa itace, 23 daganan kada abar jikinsa ya kwana dukkan dare a kan itace, amma, dole ku tabbatar kun bizne shi a ranar; gama duk wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Allah. Ku yi biyayya da dokar nan domin kada ku ƙazantar da ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku a matsayin gãdo.

Sura 22

1 Kada ku kalli sã ko tunkiyar ɗan'uwanku Ba-isra'ile yana ɓacewa ku ƙyale su; dole ku tabbatar kun dawo da su ga maishi. 2 Idan ɗan'uwanku mutumin Isra'ila ba ya kusa daku, ko idan baku sanshi ba, daganan dole ku kawo dabbar wurinku a gidanku, za ta kasance tare daku har lokacin da ya zo neman ta, daganan dole ku mayar masa da ita. 3 Dole kuyi irin haka da jakinsa, dole kuyi haka ga rigarsa; dole kuyi haka da kowanne abin da ya ɓace na ɗan'uwanku Ba-isra'ile, duk abin da ya ɓata kuka tsinta; lallai ba zaku ɓoye kanku ba. 4 Ba zaku ga jaki ko san ɗan'uwanku Ba-isra'ile ya faɗi a hanya ku ƙyale su ba; dole ku tabbatar kun taimake shi tawurin sake ɗaga shi sama. 5 Kada mace ta sanya abin da ya shafi suturar maza, kuma kada namiji ya sanya suturar mata; gama duk wanda ya yi waɗannan abubuwa abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku. 6 Idan kuna tafiya a kan hanya sai kuka ga sheƙar tsuntsu, a kan kowanne itace, ko a ƙasa, da 'ya'yansa ko ƙwayaye a ciki, uwar kuma na kwance a kan 'ya'yan ko a kan ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan. 7 Ku tabbatar uwar ta tafi, amma zaku iya kwashe 'ya'yan domin kanku. Ku yi biyayya da dokar nan domin ku sami zaman lafiya ta haka kuma zaku tsawaita kwanakinku. 8 Sa'ad da kuka gina sabon gida, daganan dole ku ja rawani a rufin domin kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya faɗi daga can. 9 Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku, domin kada wuri mai tsarki ya karɓe dukkan amfaninku, irin da kuka shuka da kuma amfanin gonar inabinku. 10 Kada ku haɗa sa da jaki suyi huɗa tare. 11 Kada ku sanya rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin. 12 Dole kuyi wa kanku geza a kusurwoyi huɗu na suturar da kuke suturta kanku. 13 Idan mutum ya ɗauki mace, ya kwana da ita, daga nan ya ƙi ta, 14 kuma yana zarginta da yin abubuwan kunya ya sanya mummunar shaida akan ta, ya ce, 'Na ɗauki wannan mace, amma sa'ad da na yi kusa da ita, Na iske babu shaidar budurci a cikinta.' 15 Daganan sai mahaifinta da mahaifiyar yarinyar su kawo shaidar budurcinta gaban dattawa a ƙofar birni. 16 Mahaifin yarinyar zai cewa dattawan, 'Na bada 'yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta. 17 Duba, ya zarge ta da abubuwan kunya har ya ce, 'Ban sami ɗiyarka da shaidar budurci ba.' Amma ga shaidar budurcin 'yata.' Daganan zasu shimfiɗa ƙyalle a gaban dattawan birni. 18 Sai dattawan garin su kama wannan mutumin su hukunta shi; 19 kuma zasu yi masa tarar awo ɗari na azurfa, su bada su ga mahaifin yarinyar, saboda mutumin ya bada mummunar shaida ga budurwa a Isra'ila. Dole ta zama matarsa; ba shi da iko ya sallame ta dukkan kwanakin ransa. 20 Amma idan wannan gaskiya ne, cewa ba a ga shaidar budurci a cikin yarinyar ba, 21 daganan dole su kawo yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, daganan mutanen garin dole su jejjefeta da duwatsu har ta mutu, saboda ta aikata abin kunya a cikin Isra'ila, ta aikata karuwanci a cikin gidan mahaifinta; ta haka za ku kawar da mugunta a cikinku. 22 Idan aka iske mutum yana kwana da matar wani, dukkansu biyu dole su mutu, wato mutumin da ke kwana da matar da matar kanta; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku. 23 Idan akwai yarinyar da ke budurwa, da wani ke tashinta, sai wani mutum ya iske ta cikin gari ya kwana da ita, 24 ku ɗauki dukkansu biyun zuwa ƙofar birni, a jejjefe su su mutu. Dole ku jejjefe yarinyar da duwatsu, saboda bata yi kururuwa ba, koda shike tana cikin gari. Dole ku jejjefe mutumin, saboda ya ɓata matar maƙwabcinsa; kuma dole ku kawar da mugunta daga cikinku. 25 Amma idan mutumin ya iske yarinyar a cikin gona, idan ya ɗauke ta da ƙarfi ya kwana da ita, daga nan mutumin kaɗai daya kwana da ita za a kashe. 26 Amma ga yarinyar ba za ayi mata kome ba; domin bata yi zunubin da ya cancanci mutuwa ba. Gama wannan matsalar na dai-dai da mutumin da ya fãɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi. 27 Gama ya same ta a cikin gona; ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta. 28 Idan mutum ya iske yarinya wadda take budurwa amma ba a tashinta, idan ya kama ta da ƙarfi ya kwana da ita, idan aka gane su, 29 shi mutumin da ya kwana da ita dole ya biya shekel hamsin na azurfa ga mahaifin yarinyar, kuma dole ta zama matarsa, saboda ya ƙasƙantar da ita. Ba zai sallame ta ba dukkan kwanakin ransa. 30 Kada mutum ya ɗauki matar mahaifinsa a matsayin matarsa; kada kuma ya ɗauke 'yancin auren mahaifinsa.

Sura 23

1 Ba mutumin da aka yi wa rauni ta wurin dandaƙa ko yanke gabansa da zai shiga taron jama'ar Yahweh. 2 Shegen ɗa ba zai shiga taron jama'ar Yahweh ba; har tsara ta goma ta zuriyarsa, ba mutum a cikinsu da zai kasance a taron jama'ar Yahweh. 3 Ba'ammone ko Bamowabe ba zai zama cikakken mutum a taron jama'ar Yahweh ba; har tsara ta goma ta zuriyarsu, ba wani a cikinsu da zai shiga taron jama'ar Yahweh ba. 4 Saboda basu zo sun tarye ku da abinci da ruwa ba sa'ad da kuke kan hanyarku lokacin da kuka fito daga Masar, kuma suka yi hayar Bala'am ɗan Beyor daga Fetor cikin Aram Naharayim, ya la'anta ku. 5 Amma Yahweh Allahnku bai saurari Bala'am ba; sai Yahweh Allahnku ya juyar da la'anar ta zama albarka dominku, saboda Yahweh Allahnku yana ƙaunarku. 6 Kada ku taɓa nemar musu zaman lafiya ko wadata, lokacin dukkan kwanakinku. 7 Kada kuji ƙyamar Ba'idome, gama shi ɗan uwanku ne; kada ku ƙi Bamasare, domin kunyi baƙunci a cikin ƙasarsa. 8 Zuriyarsu tsara ta uku da aka haifa masu zasu iya shiga taron jama'ar Yahweh. 9 Sa'ad da kuka fita domin ku kafa sansani gãba da maƙiyanku, daganan dole ku kiyaye kanku daga kowanne mugun abu. 10 Idan a cikinku akwai wani mutum daya ƙazantu saboda abin da ya faru da shi da dare, daganan dole ya fita daga cikin sansanin; kada ya komo cikin sansanin. 11 Sa'ad da yamma ta yi, dole ya yi wanka cikin ruwa; sa'ad da rana ta faɗi, sai ya dawo cikin sansani. 12 Dole ku kasance da wani wuri kuma a bayan sansani in da zaku je; 13 kuma sai ku kasance da wani abu cikin kayanku da zaku yi gini da shi; sa'ad da kuka tsuguna domin kuyi bayan gari, dole kuyi gini da shi daganan sai ku mayar da ƙasar ku rufe bayan garin da kuka yi. 14 Gama Yahweh Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku ya baku nasara ya kuma bada maƙiyanku cikin hannunku. Domin haka dole sansaninku ya kasance da tsarki, domin kada ya ga abu mara tsarki a cikinku ya juya daga gare ku. 15 Kada ku bada bawan da ya tsere daga ubangijinsa. 16 Ku bar shi ya zauna tare daku, a cikin kowanne garin da ya zaɓa. Kada ku tsananta masa. 17 Kada a sami ko ɗaya daga cikin 'yan'matan Isra'ila, ko 'ya'yansu maza a cikin ƙungiyar karuwanci na addini. 18 Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci ko kuɗin da aka samu tawurin yin luɗu a cikin haikalin Yahweh Allahnku domin cika kowanne wa'adi; gama dukkan wannan abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku. 19 Kada ku bada bashi da ruwa ga danginku Ba-isra'ile - ribar kuɗi, ribar abinci, kona kowanne irin abu da akan bada shi da ruwa. 20 Ga wanda ya ke baƙo zaku iya bashi rance da ruwa, domin Yahweh Allahnku yasa maku albarka a kan dukkan abin da kuka sa hannunku ga yi, a cikin ƙasar da zaku shiga ku mallake ta. 21 Sa'ad da kuka yi wa'adi ga Yahweh Allahnku, kada kuyi jinkirin cikawa, gama Yahweh Allahnku lallai zai neme shi gare ku; zai zama zunubi a gare ku idan baku cika shi ba. 22 Amma idan kuka nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba. 23 Duk abin da ya fita daga cikin leɓunanku dole ku kula ku aikata; bisa ga yadda kuka alƙawarta ga Yahweh Allahnku, duk abin da kuka alƙawarta da yaddar ranku da bakinku. 24 Sa'ad da kuka shiga cikin gonar inabin maƙwabcinku, zaku iya cin inabin 'ya'yan inabin yadda kuke so har ku ƙoshi, amma kada ku sa ko ɗaya a cikin kwandonku. 25 Sa'ad da kuka shiga cikin hatsin maƙwabcinku daya nuna, zaku iya tsinke kawunan hatsin da hannunku, amma kada ku sa lauje ku yanki hatsin maƙwabcinku da ya nuna.

Sura 24

1 Idan namiji ya ɗauki mata ya aure ta, idan bata sami tagomashi a idanunsa ba saboda ya sami wani abin aibatarwa da ita, sai dole ya rubuta mata takardar saki, yasa a hannunta, ya sallame ta daga gidansa. 2 Sa'ad da ta fita daga gidansa, zata iya ta tafi ta zama matar wani. 3 Idan mijinta na biyun ya ƙi ta ya kuma rubuta mata takardar saki, yasa mata a hannunta, ya kuma sallame ta daga gidansa; ko kuma mijinta na biyun ya rasu, wato mutumin daya ɗauke ta ta zama matarsa - 4 sai mijinta na dã, wannan na farko wanda ya fara sallamar ta, ba zai koma ya ɗauke ta ta zama matarsa kuma ba, bayan ta rigaya ta ƙazamtu; domin wannan zai zama abin ƙyama ga Yahweh. Ba zaku sa ƙasar ta zama da laifi ba, ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku abin gado. 5 Lokacin da namiji ya ɗauki sabuwar mata, ba zai tafi yaƙi da sauran mayaƙa ba, ba za a kuma umarce shi ya tafi ya yi aikin ƙarfi da yaji ba; yana da 'yanci ya zauna a gida har shekara guda ya faranta wa matarsa da ya aura rai. 6 Kada wani ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, domin wannan zai zama karɓar ran mutum ne jingina. 7 Idan an kama wani ya saci ɗan'uwansa daga cikin mutanen Isra'ila, ya mai da shi kamar bawa ya saida shi, wannan ɓarawon dole ya mutu; haka zaku kawar da mugunta daga tsakaninku. 8 Ku kula game da annobar kuturta, domin ku aikata dai-dai a kowace ka'ida da aka baku, wanda firistoci, da lebiyawa, suka koya maku; kamar yadda na umarce su, haka zaku yi. 9 Ku tuna da abin da Yahweh Allahnku ya yi wa Maryamu sa'ad da kuke fitowa daga Masar. 10 Sa'ad da ka ranta wa makwabcinka wani irin abu, ba zaka shiga cikin gidansa ka ɗauko jinginar ba. 11 Zaka tsaya a waje, sa'an nan mutumin nan daka ba shi rance zai fito waje ya baka jinginar. 12 Idan mutumin matalauci ne, kada jinginarsa ta kwana a hannunka. 13 Hakika dole zaka mayar masa da jinginarsa kafin faɗuwar rana, domin ya yi barci cikin mayafinsa yasa maka albarka; zai zama adalci dominka a gaban Yahweh Allahnka 14 Ba zaka zalumci bawanka ɗan ƙwadago matalauci fakiri ba, ko shi ɗan'uwanka Ba'isra'ile, ko daga baƙi waɗanda ke cikin ƙasarku cikin ƙofofin biranenku; 15 Dole kowacce rana ka bashi albashinsa; kada rana ta faɗi baka cika wa'adin nan ba, domin matalauci ne zuciyarsa tana kan hakinsa. Kayi wannan domin kada ya yi kuka gãba da kai ga Yahweh, kuma domin kada ya zama zunubin daka aikata. 16 Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, haka ma 'ya'ya ba za a kashe su saboda iyayensu ba. Maimakon haka, dole ne kowa ya mutu domin nasa zunubin. 17 Ba zaka fizgi adalci daya cancanta karfi da yaji daga baƙo ba, ko maraya, ko ka ɗauki mayafin gwauruwa don jingina. 18 Maimakon haka, zaku tuna ku bayi ne dã a Masar, kuma Yahweh Allahnku ya kuɓutar daku daga can. Saboda haka ina umartar ku kuyi biyayya da wannan doka. 19 Sa'ad da kuka girbe amfaninku daga gonakinku, idan kuka manta da dami guda a gonar, kada ku koma domin ku ɗauko shi; dole zai zama domin baƙo, domin marayu, domin gwauruwa, saboda Yahweh Allahnku ya albarkace ku a cikin dukkan aikin hannuwanku. 20 Sa'ad da kuka kakkaɓe itacen zaitunku, kada ku koma ku rore rassansu, zai zama domin baƙo, da marayu da, kuma gwauruwa. 21 Sa'ad da kuka tattara 'ya'yan inabin garkarku, ba zaku yi kalarta kuma ba. Abin da aka bari baya zai zama na baƙo, na marayu, dana gwauruwa. 22 Dole ne ku tuna dã ku bayi ne a cikin ƙasar Masar. Saboda haka ina umartarku kuyi biyayya da wannan doka.

Sura 25

1 Idan akwai jayayya tsakanin mutane sai suka tafi kotu, sai al'ƙalai suka shari'anta su, zasu kuɓutar da mai adalci su hukunta mugun. 2 Idan mai laifi ya cancanci dukã, sai al'ƙali yasa shi ya kwanta ayi masa bulala a gabansa iya ƙididdigar bugun, daya dace da laifinsa. 3 Al'ƙali zai iya yi masa bulala arba'in, amma ba zai zarce wannan lambar ba; gama idan ya zarce lambar nan ya bulale shi da abin da yafi haka yawa, to za a ƙasƙantar da ɗan'uwanku Ba'isra'ile a kan idanunku. 4 Ba zaku sa wa san da ke casar hatsi takunkumi ba. 5 Idan 'yan'uwa maza suna zaune tare sai ɗayan ya rasu, kuma bashi da ɗa, ba za a aurar da matar marigayin ba ga wani a waje wanda baya cikin iyalin. Maimakon haka, dole ɗan'uwan miji marigayi ya kwana da ita ya ɗauke ta ta zama matarsa, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi mata. 6 Wannan ya zama haka domin ɗan farin da zata haifa zai ci gaba da sunan ɗan'uwa marigayi, domin kada sunansa ya ɓace a Isra'ila. 7 Amma idan mutumin baya so ya ɗauki matar ɗan'uwansa, sai matar ɗan'uwan ta tafi ƙofa wurin dattawa ta ce, '‌Ɗan'uwan mijina yaƙi ya wanzar da sunan ɗan'uwansa a Isra'ila; ba zai yi abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi mani ba.' 8 Dole sai dattawan birnin su kira shi suyi masa magana. Amma idan yaƙi ya ce, 'bana so in ɗauke ta.' 9 Dole matar ɗan'uwansa ta je wajensa a gaban dattawa, ta cire takalminsa daga ƙafarsa, ta tofa masa miyau a fuskarsa. Zata amsa masa ta ce, 'Wannan shi ne abin da ake yi wa wanda yaƙi gina gidan ɗan'uwansa.' 10 Za a kira sunansa a Isra'ila, 'Gidan wandan aka saluɓe takalminsa.' 11 Idan mutane suka yi faɗa da junansu, sai matar ɗaya daga cikinsu ta zo ta kuɓutar da mijinta daga hannun wanda ya mare shi, idan ta miƙa hannuta ta kama gabansa, 12 sai dole a yanke hannunta; kada idonku ya ji tausayi. 13 Ba zaku riƙe ma'aunan nauyi iri biyu a jakarku ba, da babba da ƙarami. 14 Ba zaku ajiye a cikin gidanku ma'aunai iri biyu ba, da babba da ƙarami. 15 Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da ya ke dai dai; mudu na adalci zaku kasance da shi, domin kwanakinku suyi tsawo a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku. 16 Domin duk masu yin irin abubuwan nan, duk waɗanda ke aikata rashin gaskiya, abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku. 17 Ku tuna da abin da Amalek suka yi maku a hanya sa'ad da kuka fito daga Masar, 18 yadda suka gamu daku a hanya suka fãɗa wa na bayanku, dukkan marasa ƙarfi na bayanku, sa'ad da kuka some kuka gaji; bai girmama Allah ba. 19 Saboda haka, sa'ad da Yahweh Allahnku zai baku hutawa daga dukkan maƙiyanku da kewaye, a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka abin gado, ba zaku manta cewa dole ku shafe tunawa da Amalek daga ƙarƙashin sama ba.

Sura 26

1 Sa'ad da kuka zo ƙasar da Yahweh Allahnku ke ba ku abin gãdo, kuma lokacin da kuka mallaƙeta kuka zauna cikinta, 2 sai dole ku ɗauki nunan farinku na dukkan girbin ƙasar wanda kuka kawo cikin gida daga ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku. Dole kusa shi a kwando ku je inda Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin haikalinsa. 3 Dole za ku je wajen firist wanda shi ne mai hidima a kwanakin nan kuce masa, 'Ina shaida yau ga Yahweh Allahnka cewa nazo ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninmu zai bamu.' 4 Dole firist zai karɓi kwandon daga hannunsa ya ajiye shi a gaban bagadin Yahweh Allahnku. 5 Dole ku faɗi haka a gaban Yahweh Allahnku, 'Kakana mayawacin Ba'aramiye ne. Ya gangara zuwa cikin Masar ya zauna a can, kuma mutanensa kima ne. A can ya yi girma, ya ƙasaita, kuma ya zama al'umma mai jama'a. 6 Masarawa suka wulaƙanta mu ainun suka tsananta mana. Suka bautar da mu. 7 Muka yi kuka ga Yahweh, Allah na ubanninmu, ya kuma ji muryarmu, ya dubi azabarmu da wahalarmu, da zalumtarmu da aka yita yi. 8 Yahweh ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi, da damtsensa miƙaƙƙe, da babbar razanarwa, da alamu da kuma al'ajibai; 9 ya kuma kawo mu nan wajen ya kuma bamu wannan ƙasar, ƙasa wacce take zuba da madara da zuma. 10 Duba yanzu, na kawo maka nunan fari na girbin ƙasar da kai, Yahweh, ka bani.' Dole ka ajiye shi a gaban Yahweh Allahnka kayi sujada a gabansa; 11 kuma dole kayi farinciki cikin dukkan abubuwa nagari da Yahweh Allahnka ya yi dominka, da kuma gidanka - da kai. da kuma Lebiyawa, da baƙon da ke tsakiyarku. 12 Bayan kun gama bada dukkan zakkarku ta girbi a shekara ta uku, wato, shekara ta zakka, dole ne kuba Lebiyawa, da baƙo, da maraya, da kuma gwauruwa, domin su ci a ƙofofin biranenku su kuma ƙoshi. 13 Dole ku ce a gaban Yahweh Allahnku, 'Na kawo waɗannan daga cikin gidana abubuwan da suke na Yahweh, na kuma ba Lebiyawa, da baƙo da maraya, da kuma gwauruwa, bisa ga dukkan umarnai waɗanda ka bani. Ban kuskure ko kaɗan ba daga umarnanka, ban kuma manta da su ba. 14 Ban ci ko kaɗan daga cikinsu a cikin baƙin cikina ba, ban kuma aje su a wani wuri marar tsarki ba, ko in miƙa su don girmama matacce. Na saurari muryar Yahweh Allahna; Nayi biyayya da dukkan abin da ka umarce ni in yi. 15 Ka duba daga wuri mai tsarki inda kake zaune, daga sama, ka albarkaci mutanenka Isra'ila, da ƙasar daka bamu, kamar yadda ka rantse wa ubanninmu, ƙasa wadda take zuba da madara da zuma.' 16 Yau, Yahweh Allahnku yana umartarku kuyi biyayya da ka'idodinsa da dokokinsa; saboda haka za ku kiyaye su zaku yi biyayya da su da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku. 17 Kun furta yau cewa Yahweh shi ne Allahnku, zaku kuma yi tafiya a tafarkunsa ku kuma kiyaye ka'idodinsa, da umarnansa da dokokinsa, cewa kuma zaku kasa kunne da muryarsa. 18 Yau Yahweh ya furta cewa ku mutane ne waɗanda mallakarsa ce, kamar yadda ya alƙawarta maku, cewa zaku yi biyayya da dukkan umarnansa, 19 zai fifita ku sama da dukkan sauran al'umman da ya yi, zaku kuma sami yabo, da suna, da daraja. Zaku zama mutanen da aka keɓe su ga Yahweh Allahnku, kamar yadda ya faɗi."

Sura 27

1 Musa da dattawan Isra'ila suka umarci mutanen suka ce, "Ku kiyaye dukkan umarnan dana umarce ku yau. 2 A ranar da zaku tsallake Yodan zuwa ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku, sai dole ku kafa manyan duwatsu ku shafe su da farar ƙasa. 3 Dole ne ku rubuta a kansu dukkan maganganun dokokin nan sa'ad da kuka rigaya kuka ƙetare; domin ku tafi cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku, ƙasa mai zubar da madara da zuma, kamar yadda Yahweh, Allahn kakanninku ya yi maku alƙawari. 4 Sa'ad da kuka ƙetare Yodan, ku kafa waɗannan duwatsu da nake umartanku yau, a kan Dutsen Ibal, ku shafe su da farar ƙasa. 5 A can zaku gina bagadi ga Yahweh Allahnku, bagadi na duwatsu; amma ba zaku yi amfani da alatu na ƙarfe ku sassaƙa duwatsun ba. 6 Dole ku gina wa Yahweh Allahnku bagadin da ba a sassaƙa duwatsun ba. Dole ku miƙa baye-baye na ƙonawa a kansa ga Yahweh Allahnku, 7 zaku miƙa hadayar baye-baye na zumunci ku kuma ci a can; zaku yi farinciki a gaban Yahweh Allahnku. 8 Zaku rubuta dukkan waɗannan maganganu na wannan dokoki a kan duwatsu su fita a fili sosai." 9 Musa da firistoci, da Lebiyawa, suka yi magana da dukkan Isra'ilawa suka ce, 10 "Kuyi shuru ku saurara, ya Isra'ila: Yau kun zama mutanen Yahweh Allahnku. Saboda haka dole kuyi biyayya da muryar Yahweh Allahnku ku kuma yi biyayya da umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartan ku yau." 11 Musa ya umarci mutanen a ranan nan ya ce, 12 "Waɗannan kabilu dole su tsaya a kan Dutsen Gerizim su albarkaci mutane bayan kun ƙetare Yodan: Simiyon, da Lebi, da Yahuda, da Isakar, da Yosef, da kuma Benyamin. 13 Waɗannan su ne kabilun da dole su tsaya a kan Dutsen Ibal su furta la'anu: Ruben, da Gad, da Ashar, da Zebulun, da Dan da kuma Naftali. 14 Lebiyawa zasu amsa su cewa dukkan mutanen Isra'ila da murya mai ƙafi: 15 Bari mutumin ya zama la'ananne wanda ya siffanta ko ya yi zubin ƙarfe, abin ƙyama ga Yahweh, aikin hannun gwanin masassaƙi, wanda ya kafa shi a asirce.' Dole ne dukkan mutane su amsa su ce, 'Amin.' 16 'Bari mutumin ya zama la'ananne wanda bai girmama mahaifinsa da mahaifiyarsa ba.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.' 17 'Bari mutumin ya zama la'ananne wanda ya cire shaidar iyakar makwabcinsa.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.' 18 Bari mutumin ya zama la'ananne wanda yasa makaho ya saki hanya.' Sai dole mutanen su ce,; Amin.' 19 Bari mutumin ya zama la'ananne wandan karfi da yaji ya ƙwace adalci daga baƙo, maraya, ko gwauruwa.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce. 'Amin.' 20 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, domin ya karɓe hakkin mahaifinsa.' Daganan sai dukkan mutane su ce, 'Amin.' 21 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da kowacce irin dabba.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.' 22 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, ɗiyar mahaifinsa, ko ɗiyar mahaifiyarsa.' Daganan dukkan mutane dole su ce, 'Amin.' 23 'Bari mutumin nan da zai kwana da surukarsa ya zama la'ananne.' Daganan dukkan mutane dole su ce, 'Amin.' 24 Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kashe makwabcinsa a ɓoye.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.' 25 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda zai karɓi toshiya domin ya kashe da mutum marar laifi.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.' 26 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ba zai yi biyayya da shariɗun nan ba.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.'

Sura 28

1 Idan kuka saurari muryar Yahweh Allahnku da kirki domin ku kiyaye dukkan dokokin nan da nake umartan ku yau, Yahweh Allahnku zai fifita ku fiye da dukkan sauran al'umman duniya. 2 Dukkan waɗannan albarku zasu zo bisanku har ma suyi amabaliya, idan kuka saurari muryar Yahweh Allahnku. 3 Zaku zama da albarka cikin birni, kuma zaku zama da albarka a jeji. 4 'Ya'yanku zasu zama da albarka, ƙasarku zata zama da albarka wajen bada amfani, da'ya'yan dabbobinku, shanunku zasu yi yabanya, haka ma 'ya'yan tumakinku. 5 Kwandunanku zasu zama da albarka, haka ma wurin kwaɓar wainarku. 6 Zaku shiga da albarka, ku fita da albarka. 7 Yahweh zai sa maƙiyanku da suka tashi gãba daku a buge su a gaban ku; zasu tasar maku ta gefe guda amma zasu gudu daga gaban ku ta hanyoyi bakwai. 8 Yahweh zai umarta albarka ta zo bisanku a cikin rumbunanku, kuma da cikin dukkan abin da kuka sa hannunku; zai albarkace ku a cikin ƙasar da ya ke ba ku. 9 Yahweh zai kafa ku a matsayin mutanen daya keɓe domin kansa, kamar yadda ya rantse maku, idan kuka kiyaye umarnan Yahweh Allahnku, kuma kuka yi tafiya a hanyoyinsa. 10 Dukkan al'umman duniya zasu ga ana kiranku da sunan Yahweh, zasu kuwa ji tsoronku. 11 Yahweh zai azurta ku ainun, da 'ya'yan jikinku, da 'ya'yan shanunku, da amfanin ƙasa, a ƙasar da ya rantse wa ubanninku zai baku. 12 Yahweh zai buɗe maku rumbunsa na sammai ya baku ruwa domin ƙasarku a dai-dai lokaci, ya kuma albarkaci dukkan aikin hannuwanku; zaku ranta wa al'ummai da yawa, amma ku ba zaku karɓi rance ba. 13 Yahweh zai saku zama kai, ba wutsiya ba; zaku kasance kullum a bisa, ba a ƙasa ba, idan kun kasa kunne ga umarnan Yahweh Allahnku da nake umartanku yau., domin ku lura ku yi su, 14 kuma idan baku juya daga waɗannan maganganu da nake umartanku a yau, ga hannun dama ko hagu ba, har da zaku bi waɗansu alloli ku bauta masu. 15 Amma idan baku saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye dukkan umarnansa da ka'idodinsa da nake umartan ku yau ba, to dukkan waɗannan la'anu zasu afka maku su mamayeku. 16 La'anannu zaku zama cikin birni, la'anannu zaku zama a jeji. 17 La'ana za ta bi kwandonku da kuma makwabar wainarku. 18 'Ya'yanku zasu zama la'anannu, amfanin gonakinku zasu zama la'anannu, da 'yan maruƙanku da 'ya'yan garken tumakinku. 19 La'anannu ne ku sa'ad da kuka shiga, la'anannu ne ku sa'ad da kuka fita. 20 Yahweh zai aiko maku la'ana, ruɗewa, da kwaɓa a dukkan abin da kuka ɗibiya hannunku, har sai kun lalace har sai kun hallaka nan da nan sabili da miyagun ayyukanku ta yadda kuka yashe ni. 21 Yahweh zai sa annoba ta manne maku har sai ya hallaka ku daga ƙasar da kuke tafiya zuwa cikin ta ku mallaka. 22 Yahweh zai buge ku da annobai masu yaɗuwa, zazzaɓi, da marurai, da fãri, da zafin rana, da iska mai ƙuna, da kuturta. Waɗannan zasu runtume ku har sai kun hallaka. 23 Samaniyar da ke kanku zata zama tagulla, ƙasar kuma da ke ƙarƙashinku zata zama ƙarfe. 24 Yahweh zai maida ruwan saman ƙasarku gari da ƙura; daga sammai zasu sabko kanku, har sai kun hallaka. 25 Yahweh zai sa a buge ku a gaban maƙiyanku; za ku fita ta hanya guda gãba da su zaku guje daga gabansu ta hanyoyi bakwai. Za a yi ta kora ku gaba da baya cikin dukkan mulkokin duniya. 26 Gawawakinku za su zama abinci ga dukkan tsuntsayen sama da dabbobin duniya; ba wanda zai tsorata su su gudu. 27 Yahweh zai far maku da maruran Masar da gyambuna, da ƙusumbi, da ƙaiƙayi wanda ba za a iya warkar daku daga su ba. 28 Yahweh zai buge ku da ciwon hauka, da makamta, da rikicewar hankali. 29 Zaku yita lalubawa da tsakar rana kamar yadda makaho ya ke yi a duhu, ba zaku azurta ba a ayyukanku; kullum za ayi ta zalumtarku ana maku ƙwace, ba kuma wanda zai cece ku. 30 Zaku yi tashin matã, amma wani namiji zai ƙwace ta ya yi mata fyaɗe. Zaku gina gida amma ba zaku zauna a ciki ba; zaku noma garkar inabi amma ba zaku ji daɗin 'ya'yansa ba. 31 Za a yanka san nomanku a kan idanunku; amma ba zaku ci namansa ba; za a karɓe jakinku ƙiri ƙiri ƙarfi da yaji ba za a kuma mayar maku ba. Za a bada tumakinku ga magabtanku, ba ko ɗaya da zaku samu ya taimaka maku. 32 Za a bada 'ya'yanku maza da mata ga wasu mutane; idanunku zasu neme su dukkan rana, amma za su gaji da sa zuciya. Hannuwanku zasu yi rauni. 33 Girbin ƙasarku da dukkan wahalarku - wata al'ummar da baku santa ba zata cinye su; kullum za a zalumce ku a murƙushe ku, 34 haka zaku haukace tawurin abin da ya zama dole ku ga ya faru. 35 Yahweh zai bugi gyiwowinku da ƙafafunku da marurai wanda ba za a iya warkar daku daga su ba, daga tafin kafafunku har ƙolƙolin kanku. 36 Yahweh zai ɗauke ku da sarkin da zaku naɗa bisa kanku zuwa wata al'umma da baku santa ba, koku ko kakanninku; a can zaku yi sujada ga allolin itace da duwatsu. 37 Zaku zama ban tsoro, da karin magana, da gatse, cikin dukkan mutane inda Yahweh zai kora ku. 38 Zaku kai hatsi da yawa gona, amma zaku sami amfanin hatsin kaɗan, gama fãri zasu cinye su. 39 Zaku dasa garkunan inabi ku kuma noma su, amma ko kaɗan ba zaku sha ruwansu ba, ba ma zaku girbi 'ya'yansu ba, gama tsutsotsi zasu cinye su. 40 Zaku kasance da itatuwan zaitun a dukkan yankinku, amma ba zaku shafa ko ɗan man a jikinku ba, gama itatuwan zaitunku zasu zubar da 'ya'yansu. 41 Zaku haifi 'ya'ya maza da mata, amma ba zasu zama naku ba, gama zasu tafi bautar talala. 42 Dukkan itatuwanku da amfanin ƙasarku - fãri za su mamayesu. 43 Baƙon da ke tsakiyarku zai yi ta ƙaruwa fiye daku gaba gaba; amma ku zaku yi ta komawa baya baya. 44 Zai ranta maku, amma ku ba za ku ranta masa ba; shi zai zama kai, ku kuwa zaku zama wutsiya. 45 Dukkan waɗannan la'anu zasu afko kanku su bi ku su chafke ku har sai sun hallaka ku. Wannan zai faru domin ba ku saurari muryar Yahweh Allahnku ba, da zaku kiyaye umarnansa da farillansa daya umarce ku. 46 Waɗannan la'anu suna kanku a matsayin alamu da al'ajibai, da kuma kan zuriyarku har abada. 47 Saboda baku yi sujada ga Yahweh Allahnku tare da murna da farin cikin zuciya lokacin yalwarku ba, 48 domin wannan fa, zaku bauta wa maƙiyan da Yahweh zai aiko gãba da ku; zaku bauta masu da yunwa, cikin ƙishirwa, cikin tsiraici, da cikin talauci. Zai ɗibiya maku karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku. 49 Yahweh zai aiko da wata al'umma gãba daku daga nesa, daga ƙarshen duniya, kamar yadda gaggafa takan fyauce abincinta, al'ummar da baku fahimci harshenta ba; 50 al'umma da fuskarta abin ban razana ne waɗanda bata ganin kwarjinin tsoffi ko ta nuna alfarma ga matashi. 51 Zasu cinye 'yan maruƙanku da amfanin ƙasarku har sai sun hallaka ku. Ba zasu bar maku hatsi ba, ko sabon ruwan inabi, ko mai, ko 'yan maruƙanku na shanu ko na tumaki, har sai sun saku ku lalace. 52 Zasu yi maku kwanto a dukkan ƙofofin biranenku, har sai tsararrun ganuwowinku masu tsayi sun faɗi a koina a ƙasarku, garu waɗanda kuka dogara a gare su. Zasu kafa maku dãga a dukkan ƙofofin biranenku a dukkan iyakar ƙasar da Yahweh Allahnku ya baku. 53 Zaku ci 'ya'yan da kuka haifa, naman 'ya'yanku maza da na 'ya'ya mata, waɗanda Yahweh Allahnku ya baku, a cikin kwanto da wahalai waɗanda maƙiyanku zasu ɗibiya maku. 54 Mutum mai taushin zuciya kuma mai kula da ke tare daku-zai ji kyashin ɗan'uwansa da matarsa da ya ke ƙauna, da dukkan yaransa da suka rage. 55 Ba zai ba ko ɗayansu naman 'ya'yan jikinsa da zai ci ba, domin ba abin da zai rage ya ci don kansa a cikin kwanto da wahalai da maƙiya suka ɗibiya maku a dukkan ƙofofin biranenku. 56 Mace mai taushin zuciya mai kula da ke a cikinku, wanda ba za ta kuskura ta aje tafin sawunta a ƙasa saboda taushin zuciya da kyakkyawan hali - zata ji kyashin mijinta da take ƙauna, da ɗanta, da ɗiyarta, 57 da sabon jaririnta da ya fito ta tsakanin ƙafafunta, da 'ya'ya waɗanda zata haifa. Zata cinye su a ɓoye domin babu abinci, a cikin kwanto da wahalai waɗanda maƙiyanku zasu ɗibiya maku a ƙofofin biranenku. 58 Idan ba ku kiyaye dukkan maganganun dokokin da aka rubuta cikin wannan littafi ba, domin ku girmama wannan suna mai ɗaukaka da banrazana, Yahweh Allahnku, 59 sai Yahweh ya tsananta annobarku, dana zuriyarku; za a yi maku manyan annobai, masu tsawon lokaci, cututuka masu azabtarwa, na dogon lokaci. 60 Zai sake maido da dukkan cututukan Masar bisa kanku waɗanda kuka ji tsoronsu; zasu manne maku. 61 Kuma kowacce cuta da annoba da ba a rubuta a wannan littafin shari'a ba, su kuma Yahweh zai kawo bisa kanku har sai kun hallaka. 62 'Yan kaɗan zaku ragu, koda shike dã kuna kamar taurarin sammai a yawa, saboda baku saurari muryar Yahweh Allahnku ba. 63 Kamar yadda dã Yahweh ya yi farinciki da yi maku kirki, ya riɓaɓɓanya ku, haka ma zai yi farinciki da saku ku lalace da kuma hallakar daku. Za a tumbuƙe ku daga ƙasar da kuke tafiya ku mallaka. 64 Yahweh zai warwatsar daku cikin dukkan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan bangon duniya; a can za ku yi sujada ga allolin da baku taɓa sani ba, ko ku, ko kakanninku, allolin itace da dutse. 65 Ba zaku sami sakewa wurin waɗannan al'umman ba, kuma babu hutawa ga tafin ƙafafunku; maimakon haka, Yahweh zai baku a can zuciya mai fargaba, idanu marasa gani, da rai mai makoki. 66 Ranku zai kasance cikin shakka a gabanku; zaku zauna cikin tsoro kowanne dare da rana baku da tabbas ko kaɗan a dukkan rayyuwarku. 67 Da safe zaku ce, 'Ina ma maraice ne!' da maraice zaku ce, 'Ina ma safiya ce!' saboda da tsoro a zukatanku da abubuwan da dole idanunku su gani. 68 Yahweh zai dawo daku cikin Masar a jiragen ruwa, ta hanyar dana riga na faɗa maku, 'Ba zaku ƙara ganin Masar ba.' A can zaku miƙa kanku domin saye ga maƙiyanku bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku."

Sura 29

1 Waɗannan su ne maganganun da Yahweh ya umarta wa Musa ya faɗi wa 'ya'yan Isra'ila a ƙasar Mowab, maganganu da aka ƙara a kan alƙawarin da ya yi da su a Horeb. 2 Musa ya kira dukkan Isra'ila ya ce masu, "Kun dai ga dukkan abin da Yahweh ya yi a kan idanunku a ƙasar Masar ga Fir'auna, da dukkan barorinsa da dukkan ƙasarsa - 3 manyan wahalai da idanunku suka gani, da alamu, da waɗannan dukkan al'ajibai. 4 Har wa yau Yahweh bai baku zuciya ta sani ba, idanu domin a gani, ko kunnuwa domin ji. 5 Na bisheku a jeji shekaru arba'in, rigunanku basu tsufa a jikinku ba, takalmanku ma basu tsufa a ƙafafunku ba. 6 Baku ci waina ba, baku sha ruwan inabi ba, ko barasa mai sa maye, domin ku sani nine Yahweh Allahnku. 7 Sa'ad da kuka zo wannan wurin, Sihon, sarkin Hesbon, da Og sarkin Bashan, suka fito suyi yaƙi gãba daku, muka buga su. 8 Muka karɓe ƙasarsu muka ba Rubenawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manasa. 9 Saboda haka, ku kiyaye waɗannan maganganun alƙawari ku aikata su, domin ku azurta cikin dukkan abubuwan da zaku yi. 10 Kuna tsaye yau, dukkanku, a gaban Yahweh Allahnku, da sarkinku, da kabilunku, da dattawanku, da shugabanninku-da dukkan mazajen Isra'ila, 11 da 'yan ƙanananku, da matanku, da baƙi waɗanda suke zaune a tsakiyarku cikin zangonku, da shi wanda ke saro maku itace da mai‌ ɗibar maku ruwa. 12 Kuna nan domin ku ƙulla alƙawari da Yahweh Allahnku da rantsuwa da Yahweh Allahnku ya ke yi da ku yau, 13 domin ya maishe ku yau mutane na kansa, domin kuma ya zama Allahnku, kamar yadda ya yi maku magana, kamar kuma yadda ya rantse wa kakanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu. 14 Domin bada ku kaɗai nake yin wannan alƙawari da rantsuwa ba - 15 da kowannenku da ke tsaye tare da mu yau a gaban Yahweh Allahnmu - amma da kuma waɗanda basa nan tare da mu a yau. 16 Kun sani mun zauna a ƙasar Masar, da yadda muka biyo ta tsakiyar al'ummai waɗanda kuka wuce. 17 Kun ga allolinsu masu banƙyama da aka yi su da itace da dutse, azurfa da zinariya, da ke tsakiyar su. 18 Ku tabbata ba wani a cikinku, wani mutum, mata, iyali, ko kabila da zuciyarsa take juyawa daga Yahweh Allahnmu, ya tafi ya yi sujada ga allolin waɗancan al'umman. Ku tabbata ba wani tushe a cikinku mai ba da ɗaci da dafi. 19 Lokacin da mutumin nan yaji maganganun la'anan nan, zai albarkaci kansa ya ce a zuciyarsa, "Zan sami salama koda shike zan yi tafiya cikin taurin zuciyata.' Wannan zai haddasa hallaka mai adalci tare da mugu. 20 Yahweh ba zai gafarta masa ba, fushin Yahweh da kishinsa zai auka wa mutumin nan, kuma dukkan la'anan da aka rubuta a littafin nan zasu bi ta kansa, Yahweh zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama. 21 Yahweh zai ware shi domin bala'i daga dukkan kabilun Isra'ila, domin kiyaye dukkan la'ana na alƙawari da aka rubuta cikin wannan littafin dokoki. 22 Tsara mai zuwa, yaranku da zasu tashi a bayanku da baƙon da zai zo daga ƙasa mai nisa, zasu yi magana sa'ad da suka ga annobai a kan ƙasannan da cututukan da Yahweh yasa mata ciwo - 23 sa'ad da suka ga dukkan ƙasar ta zama wuta da ƙibiritu, inda ba shuki ko ya bada 'ya'ya, inda ba tsiro, kamar sa'ad da aka kaɓar da Soduma da Gomarata, Adma da Zeboyim, waɗanda Yahweh ya hallakar cikin fushinsa da hasalarsa. - 24 zasu ce tare da dukkan wasu al'ummai, 'Meyasa Yahweh ya yi wa ƙasar nan haka? Mene ne ma'anar zafin hasalar nan?' 25 Sa'annan mutane zasu ce, 'Domin sun watsar da alƙawarin Yahweh, Allahn kakanninsu, da ya yi da su lokacin daya fitar da su daga ƙasar Masar, 26 kuma domin sun tafi sun bauta wa wasu alloli suka russuna masu, allolin da basu sani ba ba kuma shi ya basu ba. 27 Saboda haka fushin Yahweh ya yi ƙuna akan wannan ƙasa, har ya kawo a kanta dukkan la'anar da aka rubuta a littafin nan. 28 Yahweh ya tumbuƙe su daga ƙasarsu cikin fushi, da hasala, da fushi mai ƙuna, ya kuma jefar da su cikin wata ƙasa, har wa yau.' 29 Sanin abubuwan asiri na Yahweh Allahnmu ne kaɗai; amma abubuwan da aka bayyana su namu ne har abada mu da kuma zuriyarmu, domin mu aikata dukkan maganganun waɗannan dokoki.

Sura 30

1 Sa'ad da dukkan waɗannan abubuwa suka zo kanku, albarku da la'ana dana sa a gabanku, kuma sa'ad da kuka tuna da su yayin da kuna cikin dukkan al'ummai inda Yahweh Allahnku ya kora ku, 2 sa'ad da kuma kuka koma ga Yahweh Allahnku kuka yi biyayya da muryarsa, kuna yin dukkan abin da na umarce ku yau - ku da 'ya'yanku, - da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku, 3 sa'an nan Yahweh Allahnku zai komo daku daga bautar talala ya yi juyayinku; zai juya ya tattaroku daga cikin dukkan al'ummai da Yahweh Allahnku ya warwatsa ku. 4 Idan korarrun mutanenku suna cikin manisantan wuraren ƙasa da sammai, daga can Yahweh Allahnku zai tattara ku, kuma daga can zai kawo ku. 5 Yahweh Allahnku zai kawo ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, kuma zaku sake mallakarta; zai yi maku alheri ya riɓaɓɓanya ku fiye da yadda ya yi da kakanninku. 6 Yahweh Allahnku zai yi wa zuciyarku kaciya da ta zuriyarku, domin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku da dukkan ranku, domin ku rayu. 7 Yahweh Allahnku zai sa dukkan waɗannan la'ana a kan maƙiyanku da kan waɗanda suke ƙin ku, waɗanda suka tsananta maku. 8 Zaku juyo kuyi biyayya da muryar Yahweh, kuma zaku aikata dukkan umarnansa da nake umartar ku yau. 9 Yahweh Allahnku zai yalwata dukkan aikin hannunku, da 'ya'yan jikinku, da 'yan maruƙanku, da amfanin gonakinku, domin wadata; gama Yahweh zai sake yin farin ciki a kanku ya azurta ku, kamar yadda ya yi farinciki da ubanninku. 10 Zai yi wannan idan kuka yi biyayya da muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye umarnansa da sharuɗansa da ke rubuce cikin littafin dokokin nan, idan kuka juyo ga Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku da dukkan ranku. 11 Domin wannan umarni da nake umartan ku yau baifi ƙarfin ku ba, kuma bai yi nisa har da ba zaku kama ba. 12 Ba a sama ya ke ba, har da zaku ce, 'Wa zai je can sama domin mu ya sauko mana da ita yasa mu iya jinta, domin mu yi ta?' 13 Kuma ba a ƙarshen ruwaye ya ke ba, da zaku ce, 'Wa zai haye ruwaye domin mu ya kawo mana ita yasa mu mu jita, domin mu aikata ta?' 14 Amma maganar tana kurkusa da kai, a bakinka da kuma zuciyarka, domin ka aikata ta. 15 Duba, yau nasa a gabanku rai da nagarta, mutuwa da mugunta. 16 Idan kun yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku, waɗanda nake umartanku yau ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, ku yi tafiya a tafarkunsa, ku kuma kiyaye umarnansa, da ka'idodinsa da kuma farillansa, zaku rayu ku riɓaɓɓanya, kuma Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin ƙasar da kuke shigarta domin ku mallaka. 17 Amma idan zuciyarku ta juya, baku saurara ba a maimako kuka janye kuka russuna wa waɗansu alloli kuka yi masu sujada, 18 to yau ina maku shela cewa ba shakka zaku lalace; ba zaku yi tsawon kwanaki ba cikin ƙasar da kuke ƙetare Yodan domin ku shiga cikinta ku mallaka. 19 Na kira sama da ƙasa suyi shaida gãba daku yau, cewa na ajiye a gabanku rai da mutuwa, albarku da la'ana; saboda haka ku zaɓi rai domin ku rayu, daku da zuriyarku. 20 Kuyi wannan don ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, kuyi biyayya da muryarsa, ku kuma manne masa. Gama shi ne ranku da tsawon kwanakinku; kuyi haka domin ku zauna cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga Yakubu kuma, zai ba su."

Sura 31

1 Musa ya tafi ya faɗa wa Isra'ila waɗannan maganganu. 2 Ya ce masu, "Yanzu ina da shekaru ɗari da ashirin bana iya shiga in fita; Yahweh ya ce mani, 'Ba zaka ƙetare wannan Yodan ba.' 3 Yahweh Allahnku, zai sha gabanku; Zai hallaka waɗannan al'ummai a gaban ku, zaku ƙwace mallakarsu. Yoshuwa, zai jagorance ku, kamar yadda Yahweh ya faɗi. 4 Yahweh zai yi masu kamar yadda ya yi wa Sihon da kuma Og, sarakunan Amoriyawa, da kuma ƙasarsu, waɗanda ya hallakar. 5 Yahweh zai baku nasara a kansu sa'ad da zaku kara da su a yaƙi, zaku yi masu dukkan yadda na umarce ku. 6 Ku ƙarfafa kuyi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, kada kuma ku firgita domin su; gama Yahweh Allahnku, shi ne wanda ya ke tafiya tare daku; ba zai kunyatar daku ba ko ya yashe ku." 7 Musa ya kira Yoshuwa a gaban dukkan Isra'ila ya ce masa, "Ka ƙarfafa kayi karfin hali, gama zaka tafi da mutanen nan cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninsu zai basu; zaka sasu su gaje ta. 8 Yahweh, shi ne wanda ya sha gabanku; zai kasance tare daku; ba zai kunyatar daku ba ba zai yashe ku ba; kada ku ji tsoro, kada ku karaya." 9 Musa ya rubuta wannan doka yaba firistoci, 'ya'yan Lebi, waɗanda suke ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh; ya kuma ba dukkan dattawan Isra'ila. 10 Musa ya umarce su ya ce, "A ƙarshen kowacce shekara bakwai, lokacin da aka ƙayyade domin kashe basussuka, lokacin Idin Rumfuna, 11 lokacin da dukkan Isra'ila ke zuwa su bayyana a gaban Yahweh Allahnku a wurin da zai zaɓa domin haikalinsa, zaku karanta wannan doka a gaban dukkan Isra'ila a kunnuwansu. 12 A tara mutane, da maza, da mata, da 'yan ƙanana, da baƙon da ya ke a cikin ƙofar birninku, domin su ji su koya, domin kuma su girmama Yahweh Allahnku su kiyaye dukkan maganganun wannan dokoki. 13 Kuyi wannan domin 'ya'yansu da ba su sani ba, su ji su koya su girmama Yahweh Allahnku, dukkan kwanakin da zaku kasance a ƙasar nan da kuke ƙetare Yodan domin ku mallaketa." 14 Yahweh ya cewa Musa, "Duba rana tana zuwa, da dole ka mutu; ka kira Yoshuwa ku nuna kanku a rumfar taruwa, domin in ba shi umarni." Sai Musa da Yoshuwa suka tafi suka nuna kansu a rumfar taruwa. 15 Sai Yahweh ya bayyana a umudin girgije; umudin girgijen ya tsaya a bakin ƙofar rumfa. 16 Yahweh ya cewa Musa, "Duba, zaka yi barci tare da ubanninka; waɗannan mutane zasu tashi suyi kamar karuwai su bi waɗansu baƙin alloli waɗanda ke a tsakaninsu a cikin ƙasar da zasu. Zasu yasheni su karya alƙawarin da nayi da su. 17 Sa'annan, a ranar nan, fushina zai yi ƙuna a kansu zan kuwa yashe su. Zan ɓoye fuskata za a kuma hallaka su. Masifu da wahalai zasu auka masu zasu ce a ranan nan, 'Ba waɗannan masifu sun zo kanmu domin Allahnmu ba shi tare da mu ba?' 18 Hakika zan ɓoye fuskata daga gare su a ranar nan, saboda dukkan muguntar da zasu aikata, domin sun juya ga waɗansu alloli. 19 Saboda haka yanzu fa, ka rubuta wannan waƙa domin kanku ka koya wa mutanen Isra'ila. Ka sa a bakinsu, domin wannan waƙa ta zama shaida gãba da mutanen Isra'ila. 20 Gama bayan na kawo su cikin wannan ƙasar dana rantse zan ba kakaninsu ƙasa mai zuba da madara da zuma, bayan sun ci sun ƙoshi sun yi ƙiba, zasu juya ga wasu alloli su kuma bauta masu su rena ni su karya alƙawarina. 21 Sa'ad da mugayen abubuwa da wahalai suka zo kan mutanen nan wannan waƙa za ta faɗa a gabansu ita ce shaida (gama ba za a manta ta ba a bakunan tsararrakinsu). Gama na san shirye-shiryen da suke ƙuƙƙullawa yau, tun ma kafin in kawo su ƙasar dana alƙawarta masu." 22 Sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranan nan ya kuma koya wa mutanen isra'ila. 23 Yahweh ya ba Yoshuwa ɗan Nun umarni ya ce, "Ka ƙarfafa kayi ƙarfin hali; gama zaka kawo mutanen Isra'ila cikin ƙasar dana rantse masu, zan kuma kasance tare da kai." 24 Da Musa ya gama rubuta waɗannan maganganun shari'a a cikin littafi, 25 sai ya umarci Lebiyawa masu ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh, ya ce, 26 "Ku ɗauki wannan littafin sharia ku aje shi a gefen akwatin alƙawari na Yahweh Allahnku, domin ya kasance a can ya zama maku shaida gãba da ku. 27 Gama na san tayarwarku da taurin kanku; duba, da raina ma ina tare daku yau, kuna tawaye gãba da Yahweh; ballantana bayan na mutu? 28 Ku tattaro mani dattawan kabilunku, da shugabanninku, domin in faɗi maganganun nan a kunnuwansu in kira sama da ƙasa suyi shaida gãba da su. 29 Gama na sani bayan rasuwata zaku ƙazamtar da kanku zaku kauce ku bar tafarkin dana umarce ku; Masifa zata auka maku cikin kwanaki masu zuwa. Wannan zai faru domin zaku yi abin mugunta a idon Yahweh, har da zaku cakune shi ya yi fushi ta wurin aikin hannuwanku." 30 Musa ya maimaita maganganun wannan waƙa a kunnuwan dukkan taron Isra'ila har sai da suka ƙare.

Sura 32

1 Ku saurara, ku sammai, bari in yi magana. Bari duniya ta saurari maganganun bakina. 2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, bari maganata ta zubo kamar raɓa, kamar yayyafi a kan ɗanyar ciyawa, kamar ɗiɗɗigar ruwa akan shuke-shuke. 3 Domin zan yi shelar sunan Yahweh, kuma in faɗi girman Allanmu. 4 Dutse ne, aikinsa cikakke ne; gama duk hanyoyinsa na adalci ne. Shi Allah mai aminci ne, marar zunubi. Mai adalci ne nagari kuma. 5 Sun aikata mugunta gãba da shi. Ba 'ya'yansa ba ne. Abin ƙasƙancinsu ne. Su kam kangararru ne karkatacciyar tsara. 6 Haka zaku rama wa Yahweh, ku wawayen mutane marasa tunani? Shi ba mahaifinku bane, wanda ya hallice ku? Shi ya yi ku ya kuma kafa ku. 7 Ku tuna da kwanakai da lokatan dã, ku tuna da shekaru na zamanai da yawa da suka wuce. Ku tambayi mahaifinku zai nuna maku, dattawanku zasu kuma gaya maku. 8 Lokacin da Maɗaukaki yaba al'ummai gadonsu - sa'ad da ya raba 'yan adam, ya rabawa al'ummai wurin zamansu, kamar yadda ya san yawan allolinsu. 9 Gama rabon Yahweh mutanensa ne; Yakubu shi ne rabon gadonsa. 10 Ya same shi a cikin hamada, a cikin ƙasa marar amfani, wurin kuka a jeji; ya kare shi ya lura da shi, ya tsare shi kamar kwayar idonsa. 11 Kamar yadda gaggafa take tsare sheƙarta tana shawagi bisa 'ya'yanta, haka Yahweh ya buɗe fuka- fukansa ya ɗauke su, ya tafi da su a kan kafaɗarsa. 12 Yahweh kaɗai ya bishe su; babu baƙon allah tare da su. 13 Ya sa shi ya hau manyan tuddai na ƙasar, ya ciyar da shi da 'ya'yan itatuwan saura; ya yi kiwonsu da zuma daga dutse, da mai daga dutsen daya tsage.. 14 Ya sha man shanu daga garke kuma ya sha madara daga garken tumaki, daga ƙibar 'yan tumaki, ragunan Bashan da awakai, da lallausar garin alkama - kuka sha ruwan inabi mai kumfa da aka yi da ruwan 'ya'yan itacen inabi. 15 Amma Yeshurun ya yi ƙiba ya yi hauri - ka yi ƙiba, ka ma zarce da ƙiba, ka ci isasshe - sai ya yashe da Allahn da ya yi shi, yaƙi Dutsen cetonsa. 16 Suka sa Yahweh ya ji kyashi ta wurin baƙin allolinsu; da abubuwan ƙyamarsu suka sa shi fushi. 17 Suka yi wa al'jannu hadaya, waɗanda ba Allah ba - allolin da basu sani ba, sabobbin alloli, gumakun da ubanninku basu ji tsoro ba. 18 Kuka yashe da Dutsen, daya zama maku mahaifi, kuka manta da Allahn daya haife ku. 19 Yahweh ya ga haka ya kuma ƙi su, sabili da 'ya'yansa maza da 'ya'yansa mata sun tsokane shi. 20 "Zan ɓoye fuskata daga gare su," ya ce, "zan ga yadda ƙarshensu zai zama; gama kangararrun tsara ne, 'ya'ya marasa aminci. 21 Suka sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba suka sa ni fushi da abubuwan wofinsu. Zan sa suji kyashi da waɗanda ba mutane ba; tawurin wautar al'umma zan sasu yi fushi. 22 Gama fushina ya kunna wuta yana kuma ci zuwa zurfafan Lahira; yana hallaka duniya da girbinta; yana kunna wuta a harsashin duwatsu. 23 Zan tara masihu a kan su; zan harba dukkan kibiyoyina a kansu; 24 Yunwa za ta ƙarasa su zasu hallaka da ƙuna mai zafi da hallakarwa mai ɗaci; zan aika a bisansu haƙoran namun jeji, da dafin abubuwan da ke rarrafe cikin ƙura. 25 A waje takobi zai kawo rashi, a ɗakunan kwana razana zata yi haka. Zata hallaka matashi da budurwa, da jariri mai shan mama, da mutum mai furfura. 26 Na ce zan warwatsa su da nisa, in sa tunawa da su ya shuɗe daga 'yan adam. 27 Da ba domin ina tsoron tsokanar maƙiyi ba, cewa maƙiya zasu zaci kuskure, kuma zasu ce, 'Hannunmu ya sami ɗaukaka,' dana aikata dukkan waɗannan abubuwa. 28 Gama Isra'ila al'umma ce marar hikima, babu fahimta a cikinsu. 29 Ai ya, da suna da hikima, da sun fahimci wannan, da zasu yi la'akari da ƙaddararsu mai zuwa! 30 Ta ya ya ɗaya zai kori dubu, biyu su sa dubu goma su tsere, sai ko Dutsensu ya sayar da su, Yahweh kuma ya sadakar da su? 31 Gama dutsen maƙiyanmu ba kamar Dutsenmu ba, kamar dai yadda maƙiyanmu suke cewa. 32 Gama kuringar inabinsu ta zo ne daga kuringar Saduma, daga kuma jejin Gomarata; inabinsu inabin dafi ne; nonan masu ɗaci ne. 33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne, da mugun dafin kumurci. 34 Wannan shiri ban aje shi a ɓoye ba, a kunle cikin kayayyakina masu daraja ba? 35 Ni ke bada sakamako, da ramako, a lokacin da kafafunsu suka zarme; gama ranar masifa domin su tayi kusa, abubuwan da zasu zo ta kansu zasu hanzarta su faru." 36 Gama Yahweh zai yi wa mutanensa adalci, kuma zai ji tausayin bayinsa. Zai ga cewa ƙarfinsu ya ƙare, kuma ba wanda ya rage, ko bawa ko baratattun mutane. 37 Sa'annan zai ce, "Ina allolinsu suke, duwatsu waɗanda suka dogara a gare su? - 38 allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka sha ruwan inabin baye-bayensu na sha. Bari su tashi su taimaka maku; bari su zamar maku kariya. 39 Duba yanzu da Ni, har Ni, Allah nake, kuma babu wani allah banda ni; Nakan kashe, in kuma rayar; na kan sa rauni, in warkar, kuma ba wani da zai iya cetonku daga ƙarfina. 40 Gama na kan tada hannuna zuwa sama in ce, "kamar yadda na dawwama har abada, zan aikata. 41 Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya, kuma sa'ad da hannuna ya fara kawo adalci, zan yi sakayya akan maƙiyana, in kuma sãka wa duk waɗanda suka ƙi ni. 42 Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, takobina zai ci tsoka tare da jinin kasassu da kamammu, tun daga kan shugabannin maƙiyan.'" 43 Ku yi farinciki, ya ku al'ummai, da mutanen Allah, gama zai yi sakayyar jinin bayinsa; zai bada sakamako a kan maƙiyansa, kuma zai yi kafara domin ƙasarsa, kuma domin mutanensa. 44 Musa ya zo ya maimaita dukkan maganganun waƙar nan a kunnuwan mutane, shi, da Yoshuwa ɗan Nun. 45 Sai Musa ya gama maimaita dukkan waɗannan maganganun ga dukkan Isra'ila. 46 Ya ce masu, "Ku sa zuciyarku akan maganganun da nayi maku kashedi yau, domin ku umarci 'ya'yanku su kiyaye su, dukkan maganganun shari'ar nan. 47 Gama wannan ba wani abu ne kurum dominku ba, sabili da ranku ne, kuma tawurin wannan abu zaku tsawaita kwanakin ku a ƙasar da kuke tafiya ku haye Yodan ku mallaka." 48 A ranar nan Yahweh ya yi magana da Musa ya ce, 49 "Ka hau cikin waɗannan duwatsen Abarim, ƙolƙolin Dutsen Nebo, wanda ke ƙasar Mowab, hannun riga da Yariko. Zaka duba ƙasar Kan'ana, wanda nake ba mutanen Isra'ila abin mallakarsu. 50 Zaka mutu akan dutsen da zaka hau, za a tattara ka zuwa ga mutanenka, kamar yadda Haruna ɗan'uwanka Ba'isra'ile ya rasu akan Dutsen Hor aka tattara shi zuwa ga mutanensa. 51 Wannan zai faru domin ka yi rashin aminci a gare ni a tsakiyar mutanen Isra'ila a bakin ruwayen Meriba a Kadesh, a jejin Zin; domin baka ɗaukakani ba kuma baka girmama ni cikin mutanen Isra'ila ba. 52 Gama zaka hangi ƙasar a gabanka, amma ba zaka je can ba, cikin ƙasar da nake ba mutanen Isra'ila."

Sura 33

1 Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya albarkaci mutanen Isra'ila da ita kafin rasuwarsa. Ya ce: 2 Yahweh ya taho daga Sinai, kuma ya taso daga Seyir a bisansu. Ya haskaka daga Dutsen Faran, yazo da dubun dubbai goma na tsarkaka. A cikin hannun damarsa akwai tarwatsun walƙiya. 3 Hakika, yana ƙaunar mutane; dukkan tsarkakansa suna cikin hannunka, suna kuma russunawa a ƙafafunka; suna karɓar maganganunka. 4 Musa ya umarta mana ka'idodi, abin gãdo domin taro na Yakubu. 5 A sa'annan akwai sarki a Yeshurun, lokacin da shugabannin mutane suka taru, dukkan kabilar Isra'ila suka taru. 6 Bari Ruben ya rayu kada ya mutu, amma bari mutanensa su zama ƙalilan. 7 Wannan ce albarkar Yahuda, Musa ya ce: Ku saurara, Yahweh, ga muryar Yahuda, a sake dawo da shi ga mutanensa. Kuyi yaƙi dominsa; ku zama taimako gãba da maƙiyansa. 8 Game da Lebi, Musa ya ce: Da Tumim ka da Yurim ka na aminanka ne, waɗanda ka gwada su a Massa, waɗanda kayi jayayya da su a ruwayen Meriba. 9 Mutumin da ya ce game da mahaifinsa da mahaifiyarsa, "Ni ban gansu ba." Bai kuma shaidi 'yan'uwansa maza ba, hallau bai yi la'akari da 'ya'yansa na cikinsa ba. Gama ya tsare maganganunka ya kuma kiyaye alƙawarinka. 10 Yana koya wa Yakubu dokokinka da Isra'ila shari'arka. Zai sa turare a gabanka da dukkan baye- baye na ƙonawa akan bagadinka. 11 Kasa albarka, Yahweh, bisa mallakarsa, ka karɓi aikin hannunsa. Ka rushe kwankwasan waɗanda suka tashi gãba da shi, da mutanen da suka ƙi shi, domin kada su sake tashi kuma. 12 Game da Benyamin, Musa ya ce: Shi wanda Yahweh ya ke ƙauna yana zaune lafiya a gefensa; Yahweh ya kãre shi dukkan rana, yana zaune tsakiyar hannuwan Yahweh. 13 Game da Yosef, Musa ya ce: Bari Yahweh ya albarkaci ƙasarsa da abubuwa masu daraja na sama, tare da raɓa, kuma tare da zurfafa da ke kwance a ƙasa. 14 Bari ƙasarsa ta zama da albarkar abubuwa masu daraja na girbi dana rana, da abubuwa masu daraja na watanni, 15 tare da kyawawan abubuwa daga duwatsun dã, da kuma abubuwa masu daraja daga dawwamammun tuddai. 16 Bari a albarkaci ƙasarsa da abubuwa masu daraja na duniya duk da cikarta, tare kuma da fatan alheri ga wanda ya zauna cikin saura. Bari albarka ta sauka a kan Yosef, da a kan shi wanda ya zama sarki bisa 'yan'uwansa maza. 17 ‌Ɗan fari na bijimi, mai daraja ne shi, ƙahonninsa kamar ƙahonnin bijimin jeji ne. Da su zai tunkuɗe mutane, dukkansu, har ƙarshen duniya. Waɗannan su ne dubbai goma na Ifraimu; waɗannan su ne dubbai na Manasa. 18 Game da Zebaluna, Musa ya ce: Kayi farinciki, Zebaluna, cikin fitarka, kai kuma, Isakar, a cikin rumfunarka. 19 Zasu kira mutane zuwa duwatsu. A can zasu miƙa hadayu na adalci. Domin zasu sha wadatar tekuna, daga kuma yãshin da ke a bakin teku. 20 Game da Gad, Musa ya ce: Mai albarka ne wanda ya faɗaɗa Gad. Zai zauna a can kamar zakanya, zai kuma farke hannu ko ƙoƙon kai. 21 Ya samar wa kansa sashe mafi kyau, domin akwai rabon ƙasa da aka keɓe domin shugaba. Yazo da shugabannin mutane. Ya aiwata adalcin Yahweh da dokokinsa da Isra'ila. 22 Game da Dan, Musa ya ce: Dan ɗan zaki ne da ya yi tsalle waje daga Bashan. 23 Game da Naftali, Musa ya ce: Naftali, ya ƙoshi da tagomashi, cike ya ke da alheran Yahweh, ya mallaki ƙasar daga yamma da kudu. 24 Game da Ashiru, Musa ya ce: Mai albarka ne Ashiru fiye da sauran 'ya'ya maza; bari ya zama karɓaɓɓe ga 'ya'uwansa maza, bari ya tsoma ƙafarsa cikin man zaitun. 25 Bari ƙurfan birninka su zama na baƙin ƙarfe da tagulla; dukkan kwanakin ranka, haka ma tsaron lafiyarka. 26 Babu ko ɗaya kamar Allah, Yeshurun - mai gaskiyan nan, mai hawa cikin sammai ya kawo maka taimako, kuma cikin darajarsa bisa gajimarai. 27 Allah madawwami mafaka ne, a ƙarƙashi kuma dawwamammun hannuwa. Yakan kori maƙiya daga gaban ka, sai kuma ya ce, "Hallaka!" 28 Isra'ila ta zauna lafiya. Maɓulɓular Yakubu tana tsare cikin ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi; labudda, bari sammansa su zubo raɓa a kansa. 29 Albarkunka da yawa, Isra'ila! Wane ne kamarka, mutane da Yahweh ya ceta, garkuwar taimakonka, da takobin ɗaukakarka? Magabtanku zasu zo gare ku da rawar jiki, zaku tattake masujadarsu.

Sura 34

1 Musa ya haura daga filin Mowab zuwa Dutsen Nebo, zuwa ƙwolƙwolin Fizga, wacce take hannun riga da Yariko. A nan Yahweh ya nuna masa dukkan ƙasar Giliyad har ya zuwa Dan, 2 da dukkan Naftali, da ƙasar Ifraimu da ta Manasa, da dukkan ƙasar Yahuda, har ya zuwa tekun kudu, 3 da Nageb, da filin Kwarin Yariko, Birnin Itatuwan Dabino, har ya zuwa Zowar. 4 Yahweh ya ce masa, "Wannan ita ce ƙasar dana rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu, cewa, "Ni zan bada ita ga zuriyarku.' Na yardar maka ka ganta da idanunka, amma ba zaka je can ba." 5 Sai Musa bawan Yahweh, ya rasu a nan ƙasar Mowab, kamar yadda maganar Yahweh ta alƙawarta. 6 Yahweh ya bizne shi a cikin kwari cikin ƙasar Mowab mai hannun riga da Bet Feyor, amma ba wanda yasan inda kabarinsa ya ke har wa yau. 7 Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu, idanunsa basu dushe ba ƙarfinsa kuma bai ragu ba. 8 Mutanen Isra'ila suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana arba'in, sai kwanakin makoki domin Musa suka ƙare. 9 Yoshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Mutanen Isra'ila suka saurare shi kuma suka yi abin da Yahweh ya umarci Musa. 10 Ba wani annabi da ya taɓa tashi a Isra'ila kamar Musa, wanda Yahweh ya san shi fuska da fuska. 11 Ba a taɓa yin wani annabi kamarsa ba a cikin dukkan alamu da mu'ujizai waɗanda Yahweh ya aike shi ya yi a ƙasar Masar, wurin Fir'auna, da dukkan barorinsa, da dukkan ƙasarsa. 12 Ba a taɓa yin wani annabi kamarsa ba a dukkan manyan, ayyukan ban tsoro da Musa ya yi a idanun dukkan Isra'ila.

Littafin Yoshuwa
Littafin Yoshuwa
Sura 1

1 Ya zamana fa bayan mutuwar Musa bawan Yahweh, sai Yahweh ya yi magana da Yoshuwa ɗan Nun, babban mataimakin Musa, ya ce, 2 "Bawana Musa, ya rasu. Yanzu fa, ka tashi, ka haye wannan kogin Yodan, da kai da dukkan mutanen nan, zuwa cikin wannan ƙasa da zan ba su - ga mutanen Isra'ila. 3 Na rigaya na ba ku dukkan inda sawun ƙafafunku za su taka. Na baku ita, kamar yadda na yi wa Musa alƙawari. 4 Daga jejin Lebanon, har zuwa babban kogin Yufaratas, dukkan ƙasar Hatiyawa, da Babban Teku, inda rana take faɗuwa, za ta zama ƙasarku. 5 Ba wanda zai iya tsayayya da kai dukkan kwanakin ranka. Zan kasance tare da kai kamar yadda na kasance da Musa. Bazan yasheka ba ko in bar ka. 6 Ka dage ka yi ƙarfin hali. Za ka sa mutanen nan su gaji ƙasar da na alƙawarta wa kakanninsu zan ba su. 7 Ka dage ka yi ƙarfin hali sosai. Ka yi hankali ka yi biyayya da dukkan dokokin da bawana Musa ya umarce ka. Kada ka kauce masu zuwa dama ko hagu, domin ka yi nasara duk inda ka tafi. 8 Kullum za ka riƙa yin magana a kan wannan littafin shari'a. Za ka riƙa binbini a kansa dare da rana domin ka yi biyayya da dukkan abin da aka rubuta a ciki. Sa'annan za ka zama da albarka da nasara. 9 Ba ni ne na urmace ka ba? Ka ƙarfafa ka yi ƙarfin hali! Kada ka ji tsoro. Kada ka karaya. Yahweh Allahnka ya na nan tare da kai duk inda ka tafi." 10 Sai Yoshuwa ya umarci shugabannin jama'a, 11 "Ku tafi cikin sansanin ku dokaci mutanen, 'Ku shirya wa kanku guzuri. Cikin kwana uku za ku haye wannan Yodan ku mallaki wannan ƙasa da Yahweh Allahnku ya ke ba ku gãdo."' 12 Ga Rubainawa, da Gadawa da rabin kabilar Manasse, Yoshuwa ya ce, 13 "Ku tuna da maganar da Musa bawan Yahweh, ya umarce ku sa'ad da ya ce, 'Yahweh Allahnku ya na ba ku hutawa, ya na kuma ba ku wannan ƙasa.' 14 Matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobin ku za ku barsu a ƙasar da Musa ya ba ku, can ƙetaren Yodan. Amma jarumawanku za su tafi da 'yan 'uwanku su taimaka masu 15 har sai Yahweh ya ba 'yan 'uwanku hutawa kamar yadda ya baku. Haka su ma za su mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ke ba su. Sa'annan za ku dawo zuwa taku ƙasar ku gaje ta, ƙasar da Musa bawan Yahweh ya baku can ketaren Yodan inda rana take fitowa." 16 Sa'annan su ka amsa wa Yoshuwa, su ka ce, "Za mu yi dukkan abin da ka umarce mu, kuma duk in da ka aike mu za mu je. 17 Za mu yi maka biyayya kamar yadda muka yi wa Musa biyayya. Allahnka Yahweh dai ya kasance tare da kai, kamar yadda ya kasance da Musa. 18 Duk wanda ya yi tawaye gãba da umarninka ya kuma yi rashin biyayya da maganarka za a kashe shi. Ka dage ka yi ƙarfin hali."

Sura 2

1 Sai Yoshuwa ɗan Nun a asirce ya aiki mutum biyu daga Shittim magewaya. Ya ce; "Ku je, ku dubo ƙasar, musamman Yeriko." Su ka yi tafiyarsu su ka isa gidan wata karuwa mai suna Rahab, a nan ne su ka sauka. 2 Aka cewa sarkin Yeriko, "Duba, mutanen Isra'ila sun zo nan domin su leƙi ƙasar." 3 Sai sarkin Yeriko ya aika wa Rahab cewa, "Ki fito da mutanen da su ka zo wurinki waɗanda su ka shiga gidanki, gama sun zo ne domin leƙen dukkan ƙasar." 4 Amma matar ta rigaya ta ɗauki mutanen nan biyu ta ɓoye su. Sai ta amsa masu, "I, mutanen sun zo wurina amma ban san daga inda su ka fito ba. 5 Sun bar nan da sauran duhu, lokacin da ake kulle ƙofar birni. Ban san inda su ka tafi ba. Mai yiwuwa ku cim masu idan kun bi su da sauri." 6 Gama ta rigaya ta kai su bisa rufin ɗakinta ta rufe su da ƙeƙasheshen rama waɗanda ta shinfiɗa a bisa rufin. 7 Sai mutanen su ka bi su a kan hanya da ta kai su kwarin Yodan. Nan da nan aka rufe ƙofar bayan da masu bin su su ka fita. 8 Kafin mutanen su kwanta da dare, sai ta zo wurinsu a rufin kan ɗaki. 9 Ta ce, "Na sani Yahweh ya rigaya ya ba ku ƙasar kuma tsoronku ya faɗo kanmu. Dukkan waɗanda ke zaune a ƙasar za su narke a gabanku. 10 Mun ji yadda Yahweh ya sa ruwan Jan teku ya ƙafe dominku sa'ad da kuka fito daga Masar. Mun ji kuma abin da ku ka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa a hayin Yodan - Su Sihon da - Og waɗanda ku ka hallaka dukka. 11 Da dai mu ka ji haka, zukatanmu su ka narke har babu karfin hali da ya rage a cikin ko ɗayanmu. Domin Yahweh Allahnku, shi ne Allah na sama da na duniya a ƙasa. 12 Yanzu dai, ku rantse mani da Yahweh cewa, kamar yadda na yi maku alheri, kuma ku yi wa gidan ubana alheri. Ku bani tabbatacciyar alama 13 cewa za ku tsirar da ran mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan 'uwana maza, da mata da dukkan iyalansu, za ku kuma cece mu daga mutuwa." 14 Mutanen su ka ce ma ta, "Ran mu a bakin na ki, har ma ga mutuwa! Idan baki tona al'amarin nan ba, idan Yahweh ya ba mu ƙasar za mu nuna maki jinkai da aminci." 15 Sai ta zura su ƙasa ta taga da igiya. Gidan da take zaune an gina shi cikin ganuwar birnin. 16 Ta ce masu, "Ku hau cikin duwatsu ku ɓoye, ka da masu bin ku su same ku. ku ɓoye a can har kwana uku bayan masu bin ku sun dawo. Sa'annan ku yi tafiyarku." 17 Mutanen su ka ce ma ta, "Za mu zama kuɓutattu da ga rantsuwar da mu ka rantse ma ki, idan ba ki riƙe amanar ba. 18 Lokacin da za mu zo ƙasar, dole ki ɗaura wannan jar igiya a tagar da ki ka zura mu, za ki kawo cikin gidan ki mahaifinki da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki da dukkan gidan mahaifinki. 19 Duk wanda ya fita daga ƙofar gidanki zuwa titi, jininsu na bisa kansu, mu kuwa mun kuɓuta. Amma idan muka sa hannu a kan wanda ke cikin gida tare da ke, alhakin jininsa na kan mu. 20 Amma idan ki ka furta al'amarin nan, za mu kuɓuta daga rantsuwar da ki ka sa mu ka rantse maki," 21 Rahab ta amsa, "Bisa ga maganar da ku ka faɗa bari ya zama haka." Sai ta sallame su, su ka tafi. Sai ta ɗaura jar igiyar a tagar. 22 Su ka tafi su ka haye cikin tsaunuka su ka kuma zauna can kwana uku har sai da masu bin sawun su su ka koma. masu bin sawunsu su ka yi ta neman su a kan hanya ba su sami komai ba. 23 Mutanen biyu su ka ƙetare su ka komo wurin Yoshuwa, ɗan Nun, su ka labarta masa dukkan abubuwan da su ka faru da su. 24 Su ka ce ma Yoshuwa, "Gaskiya Yahweh ya ba mu wannan ƙasar. Dukkan mazaunan ƙasar su na ta narkewa sabili da mu."

Sura 3

1 Yoshuwa ya tashi da sassafe, sai su ka yi ƙaura daga Shittim. Su ka iso Yodan, shi da dukkan mutanen Isra'ila, su ka sauka a nan kafin su haye. 2 Bayan kwana uku, sai shugabanni su ka ratsa ta tsakiyar zangon; 3 su ka umarci mutane, "Lokacin da ku ka ga akwatin alƙawari na Yahweh Allahnku, da firistoci daga kabilar Lebiyawa ɗauke da shi, sai dole ku bar nan wajen ku bi shi. 4 Dole ku sa ratar ƙafa dubu biyu tsakanin ku da akwatin. Kada ku je kusa da shi, domin ku iya hango inda za ku bi, da shike ba ku taɓa bin wannan hanyar ba," 5 Yoshuwa ya cewa jama'a; "Ku tsarkake kanku gobe, domin Yahweh zai yi abin al'ajibi a tsakanin ku." 6 Sa'annan Yoshuwa ya cewa Firistoci, "Ku ɗauki akwatin alƙawari ku wuce gaban jama'a." Sai su ka ɗauki akwatin alƙawarin su ka wuce gaban jama'a da shi. 7 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "A ranar yau zan maishe ka babban mutum a idanun Isra'ilawa dukka. Za su sani, kamar yadda na kasance da Musa, zan kasance da kai. 8 Za ka umarci Firistoci su ɗauki akwatin alƙawari, 'Lokacin da ku ka isa bakin ruwayen Yodan, dole ku tsaya cik a cikin Kogin Yodan."' 9 Yoshuwa ya cewa mutanen Isra'ila, "Ku zo nan ku saurari maganar Yahweh Allahnku. 10 Ta wurin wannan za ku sani Allah mai rai na tare da ku zai kori Kan'aniyawa, Hatiyawa da Hibiyawa da Farizziyawa da Girgashiyawa da Amoriyawa da Yebusawa daga gaban ku. 11 Duba! Akwatin alƙawari na Ubangijin dukkan duniya ya shiga gaban ku zuwa cikin Yodan. 12 Yanzu ku zaɓi mutum goma sha biyu daga ƙabilar Isra'ila, mutum guda daga kowannen su. 13 Sa'ad da tafin sawun firistoci masu ɗauke da akawatin Yahweh, Ubangijin dukkan duniya, ya taɓa ruwayen Yodan, ruwayen za su datse, har ma ruwayen da suke kwararowa daga bisan kogin za su daina kwararowa su tsaya a tari guda." 14 A lokacin da jama'a su ka tashi domin su ƙetare Yodan, firistoci ɗauke da akwatin alƙawari su ka wuce gaban jama'a. 15 Da zarar mutane masu ɗauke da akwatin su ka iso Yodan, da ƙafafunsu su ka taɓa gacin ruwan (Yodan dai yakan yi ambaliya dukkan lokacin girbi), 16 sai ruwayen da suke gangarowa daga tudun rafin su ka taru wuri guda. Ruwan ya dena gangarowa daga nesa. Ya kuma dena gagarowa daga Adam, birnin da ke kusa da Zaretan, har ya zuwa tekun Negeb, Tekun Gishiri. Jama'a su ka ƙetare kurkusa da Yeriko. 17 Firistocin da ke ɗauke da akwatin alƙawari na Yahweh su ka tsaya a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Yodan har sai da jama'ar Isra'ila su ka ƙetare a kan busasshiyar ƙasa.

Sura 4

1 Sa'ad da dukkan mutane su ka ƙetare Yodan, Yahweh ya cewa Yoshuwa, 2 "Ku zaɓa wa kan ku mutum goma sha biyu, daga kowanne kabila mutum ɗaya. 3 Ka ba su wannan umarni: 'Ku ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Yodan inda firitoci ke tsaye a kan busasshiyar ƙasa, ku kawo su ku ajiye su inda za ku kwana daren yau."' 4 Sai Yoshuwa ya kira mutanen nan goma sha biyu waɗanda ya zaɓo daga kabilar Isra'ila, guda ɗaya daga kowacce kabila. 5 Yoshuwa ya ce masu, "Ku wuce gaban akwatin Yahweh Allahnku zuwa cikin tsakiyar Yodan. Kowannen ku zai ɗauki dutse a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilun mutanen Israila. 6 Wannan zai zamar ma ku alama a tsakanin ku sa'ad da 'ya'yanku za su tambaya a kwanaki masu zuwa, 'Menene ake nufi da waɗannan duwatsu?' 7 Sa'annan za ku ce, 'An yanke ruwayen Yodan a gaban akwatin alƙawari na Yahweh. Lokacin da ya ƙetare Yodan, ruwan Yodan ya yanke. Saboda haka waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga jama'ar Isra'ila har abada."' 8 Jama'ar Isra'ila su ka yi dai-dai abin da Yoshuwa ya umarce su, su ka ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Yodan, kamar yadda Yahweh ya cewa Yoshuwa. Suka shirya duwatsun yadda lambar kabilar Isra'ila ta ke. Su ka ɗebo duwatsu, su ka kawo masaukinsu su ka shirya su a nan. 9 Sa'annan Yoshuwa ya jera wasu duwatsu a tsakiyar Kogin Yodan, a inda sawun firistoci da su ka ɗauki akwatin alƙawari su ka tsaya. Wannan alamar tana nan har yau. 10 Firitoci da ke ɗauke da akwatin alƙawari su ka tsaya a tsakiyar Yodan cik har sai duk abubuwan da Yahweh ya umarci Yoshuwa ya faɗa wa mutane sun cika sarai, bisa ga duk abin da Musa ya umarci Yoshuwa. 11 Sa'ad da dukkan jama'a su ka gama ƙetarewa, akwatin Yahweh da firistoci su ka ƙetare a gaban jama'a. 12 Kabilar Ruben, da kabilar Gad, da rabin kabilar Manasse su ka wuce a gaban Isra'ilawa shirye 'yan yaƙi, kamar yadda Musa ya ce masu. 13 Kimanin maza dubu arba'in shiryayyu mayaƙa su ka wuce a gaban Yahweh, domin yaƙi wajen filayen Yeriko. 14 A ranan nan Yahweh ya ɗaukaka Yoshuwa a idanun dukkan Isra'ilawa. Su ka girmama shi - dai dai da yadda su ka ga ƙwarjinin Musa - dukkan kwanakinsa. 15 Sai Yahweh ya yi magana da Yoshuwa, 16 "Ka umarci firistoci masu ɗauke da akwatin alƙawari su hauro daga cikin Yodan." 17 Sai, Yoshuwa ya umarci firistoci, "Ku fito daga cikin Yodan." 18 Da firistoci da ke ɗauke da akwatin alƙawari na Yahweh su ka fito daga tsakiyar Yodan, su ka sa tafin ƙafarsu a busasshiyar ƙasa, sai ruwayen Yodan su ka koma magudanarsu su ka cike ta da ambaliya, kamar yadda ta ke kwanaki hudu da su ka wuce. 19 Jama'a su ka fito daga Yodan a rana ta goma ga watan ɗaya. Su ka zauna a Gilgal, gabashin Yeriko. 20 Duwatsu sha biyu da su ka ɗauko daga Yodan, Yoshuwa ya shiryasu a Gilgal. 21 Ya cewa jama'ar Isra'ila, "Sa'ad da zuriyarku za su tambayi ubanninku a zamanai masu zuwa, 'Waɗannan duwatsun fa?' 22 Ku gayawa 'ya'yanku, 'Nan ne Isra'ila ya ƙetare Yodan kan busasshiyar ƙasa.' 23 Yahweh Allahnku ya janye ruwan Yodan domin ku, har sai da su ka ƙetare, kamar yadda Yahweh Allahnku ya yi wa Jan Teku, wadda ya busar da ita domin mu sai da muka haye, 24 domin mutanen duniya dukka su sa ni hannun Yahweh mai karfi ne, ku kuma ku girmama Yahweh Allahnku har abada."

Sura 5

1 Nan da nan da dukkan sarakunan Amoriyawa na yamma da Yodan, da dukkan sarakunan Kan'aniyawa, waɗanda su ke gefen Babbar Teku, su ka ji yadda Yahweh ya sa ruwayen Yodan su ka ƙafe har sai da jama'ar Isra'ila suka haye zuwa ɗaya gacin, sai zukatansu suka narke, ba su da sauran wani ƙarfin hali kuma saboda mutanen Isra'ila. 2 A lokacin sai Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka yi wuƙar dutse ka sake yi wa dukkan mazajen isra'ila kaciya." 3 Sai Yoshuwa ya yi wuƙar dutse ya yi wa dukkan mazajen Isra'ila kaciya a Gibiyat Hãralot. 4 Wannan shi ne dalilin da Yoshuwa ya yi masu kaciya: dukkan mazajen da su ka fito daga Masar, tare da dukkan mayaƙa, sun mutu a cikin jeji a kan hanya, bayan sun baro Masar, 5 Ko da shike dukkan mazajen da su ka baro Masar suna da kaciya, amma, duk yara maza da aka haifa cikin jeji a kan hanyar fitowar su daga Masar ba su da kaciya. 6 Gama mutanen Isra'ila su ka yi tafiya shekara arba'in a jeji, har sai da dukkan mazajen da su ka fito Masar mayaƙa su ka mutu, domin ba su yi biyayya da muryar Yahweh ba. Yahweh ya rantse masu ba za su shiga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba mu, ƙasa wadda take zubo da madara da zuma. 7 'Ya'yansu ne waɗanda Yahweh ya tăda a madadinsu, su ne Yoshuwa ya yi wa kaciya, domin ba a yi masu kaciya a hanya ba. 8 Sa'ad da aka yi wa dukkan su kaciya, su ka zauna cikin sansani har sai da su ka warke. 9 Sai Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Wannan rana ta yau na cire ƙunyar Masar daga gare ku." Saboda haka, ake kiran sunan wurin Gilgal har wa yau. 10 Jama'ar Isra'ila su ka yi sansani a Gilgal. Su ka kiyaye Idin Ketarewa a rana ta goma sha hudu ga wata, da yammaci, a filayen Yeriko. 11 Su ka ci daga waɗansu amfanin ƙasar a rana ta fari bayan Idin Ketarewa: waina marar yisti da gasasshen hatsi. 12 Manna ta dena saukowa bayan ranar da su ka ci daga amfanin ƙasar. Babu manna kuma domin jama'ar Isra'ila, amma su ka ci daga cikin amfanin ƙasar Kan'ana a shekaran nan. 13 Sa'ad da Yoshuwa ya kusa da Yariko, sai ya tada idanunsa ya duba, sai, ga wani mutum tsaye a gabansa; da takobi a zare a hannunsa. Yoshuwa ya tafi wurin sa ya ce, "Kana wajenmu ne ko kana wajen abokan găbarmu?" 14 Sai ya ce, "Ko ɗaya. Ni ne sarkin yaƙin rundunar Yahweh. Yanzu na zo." Sai Yoshuwa ya russuna da fuskarsa ƙasa ya yi masa sujada ya ce, "Menene ubangijina zai faɗa wa bawansa?" 15 Sai sarkin yaƙin rundunar Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka cire takalmanka daga ƙafafunka, domin inda ka ke tsaye wuri mai tsarki ne." Haka kuwa Yoshuwa ya yi.

Sura 6

1 Aka rufe dukkan ƙofofin shiga Yeriko saboda mayaƙan Isra'ila. Ba wanda ya fita ko ya shigo. 2 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Duba, na bada Yeriko da sarkinta, da horarrun sojojinta a hannunka. 3 Dole ku zagaya birnin, dukkan mazaje mayaƙa za su zaga birnin sau ɗaya. Dole za ku yi haka har kwana shida. 4 Dole firistoci bakwai su ɗauki ƙahonni bakwai na raguna a gaban akwati. A rana ta bakwai, dole ku zagaya brinin sau bakwai, firistoci kuma dole su busa ƙahonni da babbar busa. 5 Daga nan dole su yi doguwar busa da ƙahon rago, kuma sa'ad da ku ka ji busar ƙahon dukkan mutane dole su yi ihu da babbar murya, garun birnin zai faɗi ya rushe. Dole sojojin su kai hari, kowannensu ya miƙe ya tafi gaba." 6 Sa'annan Yoshuwa ɗan Nun ya kira firistoci ya ce masu, "Ku ɗauki akwatin alƙawari, kuma firistoci bakwai su ɗauki ƙahonnin raguna bakwai a gaban akwatin Yahweh." 7 Ya cewa jama'a, "Ku tafi ku zagaya birnin, masu makamai kuma za su je gaban akwatin Yahweh." 8 Kamar yadda Yoshuwa ya cewa mutane, firistoci bakwai su ka ɗauki ƙahonni bakwai na raguna a gaban Yahweh. Da su ka cigaba da tafiya sai su ka busa ƙaho da babbar murya. Akwatin alƙawari na Yahweh na biye da su. 9 Masu makamai su ka tafi gaban firistoci, su ka yi babbar busa, wasu masu makamai kuma su ka bi bayan akwatin, firistoci kuma su ka yi ta busa ƙahonni. 10 Amma Yoshuwa ya dokaci mutane, cewa, "Kada ku yi ihu. Kada wata ƙara ta fito daga bakinku sai randa na ce ku yi ihu. Lokacin ne za ku yi ihu." 11 Sai ya sa aka zagaya birnin da akwatin Yahweh sau ɗaya a ranar. Sa'annan suka komo sansaninsu, su ka kwanta daren nan. 12 Sai Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma su ka ɗauki akwatin Yahweh. 13 Firistoci bakwai, masu ɗauke da ƙahonnin raguna bakwai a gaban akwatin Yahweh su ka yi ta busa ƙahonni su na tafiya gaba gaɗi. Sojoji masu makamai suna tafiya a gabansu. Amma sa'ad da 'yan tsaron baya su ka biyo akwatin Yahweh, sai aka dinga busa ƙahonni. 14 Su ka zaga birnin sau daya a rana ta biyu su ka komo sansaninsu. Haka suka dinga yi har kwana shida. 15 A rana ta bakwai su ka tashi da sassafe kafin gari ya waye, su ka zãga birnin kamar yadda su ka saba yi, wannan karon sau bakwai. 16 A wannan ranar ce su ka zagaya birnin sau bakwai, firistoci su ka busa ƙahonni, sai Yoshuwa ya umarci mutane, "Ku yi ihu! Gama Yahweh ya ba ku birnin. 17 Za a keɓe wa Yahweh birnin da dukkan abin da ke cikinta domin hallakarwa. Rahab karuwan nan ce kaɗai za ta rayu - ita da dukkan waɗanda ke tare da ita a gidanta - domin ta ɓoye waɗanda mu ka aika. 18 Amma ku kam, ku yi lura game da abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa, domin kada bayan kun waresu saboda hallakarwa, ku koma ku ɗauka. Idan ku ka yi haka, za ku maida sansanin Isra'ila abin da za a hallakar kuma za ku jawo ma ta masifa. 19 Dukkan azurfa, zinariya da abubuwan tagulla da ƙarfe a keɓe su ga Yahweh. Dole a kai su cikin ma'ajin Yahweh." 20 Da su ka yi babbar busa ƙahonni, sai mutane su ka yi gawurtaccen ihu ganuwar ta faɗi ƙasa, sa'annan kowanne mutum ya shiga ciki kai tsaye su ka ci birnin. 21 Su ka lalatar da dukkan abin da ke birnin da kaifin takobi - maza da mata, yaro da tsoho, shanu, tumaki, da jakai. 22 Sa'annan Yoshuwa ya cewa mutanen biyu da su ka leƙo asirin ƙasar, "Ku shiga gidan karuwar nan. Ku fitar da ita waje da dukkan waɗanda suke tare da ita, kamar yadda ku ka rantse ma ta." 23 Sai samarin nan biyu magewaya su ka shiga ciki su ka fitar da Rahab. Su ka fitar da mahaifinta, mahaifiyarta, 'yan'uwanta maza da dukkan 'yan'uwanta da su ke tare da ita. Su ka kai su wani wuri dabam da sansanin Isra'ila. 24 Su ka ƙona garin da dukkan abin da ke cikinsa. Sai dai azurfa, zinariya da kwanonin tagulla da na ƙarfe ne su ka ajiye a ma'ajin gidan Yahweh. 25 Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwa, gidan ubanta, da dukkan waɗanda ke tare da ita da rai. Tana zaune a Isra'ila har wayau domin ta ɓoye masu leƙen asirin ƙasa waɗanda Yoshuwa ya aika su leƙo Yeriko. 26 Sai Yoshuwa ya umarce su a lokacin da rantsuwa, ya kuma ce, "La'anannen mutum ne a idon Yahweh wanda ya sake gina wannan birni, Yeriko. A bakin ran ɗan farinsa, zai sa harsashen, a kuma bakin ran ɗan autansa, zai kafa ƙofofinta." 27 Haka Yahweh ya kasance tare da Yoshuwa, sunansa ya shahara ko'ina a faɗin ƙasar.

Sura 7

1 Amma jama'ar Isra'ila su ka yi rashin aminci game da abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa. Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi ɗan Zera, daga kabilar Yahuda ya ɗauka daga cikin abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa, sai fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan 'ya'yan Isra'ila. 2 Yoshuwa ya aiki mutane daga Yeriko zuwa Ai da take kusa da Bet Aben gabas da Betel. Ya ce masu, "Ku tafi ku leƙo ƙasar." Sai mutanen su ka tafi su ka leƙo Ai. 3 Da su ka dawo wurin Yoshuwa, su ka ce masa, "Kada ka aika mutane dukka zuwa Ai. Ka aika misalin dubu biyu ko uku kawai, su je su kai ma ta hari. Kada ka bari dukkan mutane su wahala a yaƙi, domin ba su da yawa." 4 Saboda haka mutum dubu uku ne kaɗai cikin mayaƙa su ka tafi. 5 Mutanen Ai su ka kashe misalin mutane talatin da shida su ka fafare su daga ƙofar birnin har zuwa mafasar duwatsu, su ka karkashe su sa'ad da su ke gangarowa daga kan tudu. Zukatan mutanen su ka tsorata ƙarfin halinsu kuma ya rabu da su. 6 Sai Yoshuwa ya yayyage tufafinsa. Da shi da shugabanin Isra'ila su ka zuba ƙura a kansu su ka faɗi rub da ciki a ƙasa a gaban akwatin Yahweh har yamma. 7 Sa'annan Yoshuwa ya ce, "Ya Ubangiji Yahweh, me ya sa ma ka haye da mutanennan daga Yodan? Don ka bashe mu a cikin hannun Amoriyawa su hallakar da mu? Ai da mun gwammace mu yi zamanmu a wancan hayin Yodan! 8 Ubangiji, me zan ce, bayan Isra'ila ta juya ta guje ma abokan gabanta? 9 Gama Kan'aniyawa da dukkan mazaunan ƙasar za su ji. Za su kewaye mu su sa mutanen duniya su manta da sunanmu. To me za ka yi domin sunanka mai girma?" 10 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Tashi! Me ya sa ka kwanta fuskarka ƙasa? 11 Isra'ila ta yi zunubi. Sun karya dokata da na umurce su. Sun sãci waɗansu abubuwan da aka keɓe. Sun sata sun kuma ɓoye zunubinsu ta wurin aje abubuwan da su ka ɗauka cikin kayansu. 12 Saboda haka ne, mutanen Isra'ila ba za su iya tsayawa a gaban maƙiyansu ba. Sun juya wa maƙiyansu baya domin su kan su an ƙebe su domin hallakarwa. Ba zan kasance tare da ku kuma ba sai ko kun hallaka waɗannan abubuwa da ya kamata an hallakar da su, amma suna nan tare da ku. 13 Tashi! Ka tsarkake jama'ar a gareni ka ce masu, 'Ku tsarkake kanku domin gobe. Domin Yahweh, Allah na Isra'ila ya ce, "Akwai abubuwan da aka keɓe saboda hallakarwa waɗanda su ke a tsakaninku, Isra'ila. Ba za ku iya tsayawa gaban maƙiyanku ba, sai kun fitar da dukkan abubuwan da aka keɓe domin hallakarwa daga tsakaninku." 14 Da safe, dole ku taru bisa ga kabilarku. Kabilar da Yahweh ya zaɓa za ta matso iyali - iyali. Iyalin da Yahweh ya zaɓa dole su matso gida - gida. Gidan da Yahweh ya ware dole a gabatar da su mutum - mutum. 15 Zai zamana duk wanda aka zaɓa, da yake da waɗannan keɓaɓɓun abubuwan hallakarwa, za a ƙone shi, da duk abin da yake da shi, domin ya karya dokar Yahweh, kuma ya yi abin ban kunya a Isra'ila."' 16 Saboda haka, Yoshuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa, kabila - kabila, sai aka zaɓi kabilar Yahuda. 17 Yoshuwa ya gabatar da kabilar Yahuda, sai aka zaɓi iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera mutum - mutum, sai aka zaɓi gidan Zabdi. 18 Ya gabatar da gidan Zabdi, mutum - mutum, sai aka zaɓi Akan, ɗan Karmi, ɗan Zera daga kabilar Yahuda, shi ne aka zaɓa. 19 Sai Yoshuwa ya cewa Akan, "‌Ɗana, ka faɗi gaskiya a gaban Yahweh Allah na Isra'ila, ka ba da shaidarka gareshi. Idan ka yarda, ka gaya ma ni abin da ka yi. Ka da ka ɓoye ma ni." 20 Akan ya amsa wa Yoshuwa, "Gaskiya na yi wa Yahweh zunubi, Allah na Isra'ila. Ga abin da na yi: 21 Sa'ad da na ga wata kyakkyawar alkyabba daga Babila, a cikin ganima, da shekel dari biyu na azurfa, da curin zinariya mai nawin shekel hamsin, sai na yi sha'awarsu na ɗauka. Sunanan a binne a ƙasa a tsakiyar rumfata, azurfar kuwa ta na ƙarƙashinsu. 22 Yoshuwa ya aiki manzanni, da su ka sheƙa da gudu zuwa rumfar, sai kuwa gasu. Da suka duba, su ka tarar da abubuwan bizne cikin rumfarsa, da azurfar a ƙarƙashi. 23 Sai su ka kwaso su daga tsakiyar rumfar su ka kawo wa Yoshuwa da dukkan mutanen Isra'ila. Su ka zuba su gaban Yahweh. 24 Sai Yoshuwa, tare da dukkan Isra'ila, su ka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da curin zinariyar, da 'ya'yansa maza da mata, da shanunsa, da jakunansa da tumakinsa, da rumfarsa da dukkan mallakarsa, su ka kawo su Kwarin Akor. 25 Sa'annan Yoshuwa ya ce, "Don me ka wahalshe mu? Yahweh zai wahalsheka yau." Dukkan Isra'ila su ka jejjefe shi da duwatsu. Su ka jejjefi sauran da duwatsu su ka ƙone su da wuta. 26 Su ka tula duwatsu a kansa mai tudu da su ke nan har yau. Yahweh ya juya daga fushinsa mai zafi. Saboda haka aka kira sunan wurin Kwarin Akor har zuwa yau.

Sura 8

1 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka da ka ji tsoro; ka da ka karaya. Ka ɗauki dukkan mayaƙa. Ku haura zuwa Ai. Duba, na rigaya na ba ka sarkin Ai, da mutanensa, birninsa da kuma ƙasarsa a hunnunka. 2 Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yeriko da sarkinta, amma za ku washe ganima da dabbobi domin kan ku. Ku yi kwanto a bayan birnin." 3 Saboda haka Yoshuwa ya tashi ya ɗauki dukkan mazaje mayaƙa zuwa Ai. Sa'annan Yoshuwa ya zaɓi mazaje dubu talatin - ƙarfafa, jarumawa -- ya aike su da dare. 4 Ya umarce su, "Ku duba, za ku yi wa birnin kwanto, a bayansa. ka da ku yi nisa da birnin sosai, amma dukkan ku ku kasance a shirye. 5 Ni da dukkan mutanen da ke tare da ni za mu kusanci birnin, sa'ad da da za su fito su yi karo da mu, za mu guje da ga garesu kamar dă. 6 Za su fito su fafare mu har sai mun rinjayesu daga birnin. Za su ce, 'Suna guje ma na karmar dă.' Haka za mu gudu da ga garesu.' 7 Sa'annan za ku fito da ga maɓuyarku, ku ci birnin. Yahweh Allahnku zai ba da shi a hannunku. 8 Sa'ad da ku ka ci birnin, za ku cinna masa wuta. Za ku yi wannan lokacin da ku ka yi biyayya da umarnin da aka bayar cikin maganar Yahweh. Duba, na umarce ku." 9 Yoshuwa ya aike su, su ka tafi wurin kwanto, su ka yi faƙo tsakanin Betal da Ai, wato yamma da Ai ke nan. Yoshuwa kuwa ya kwana cikin jama'a a daren nan. 10 Yoshuwa ya tashi da sassafe ya shirya sojojinsa, shi da shugabannin Isra'ila su ka kai wa mutanen Ai hari. 11 Dukkan mayaƙa maza da ke tare da shi su ka tafi tare da shi su ka kusanci birnin. Su ka matsa kusa arewa da Ai. Akwai kwari tsakaninsu da Ai. 12 Ya ɗauki mayaƙa kusan dubu biyar ya sa su ka yi kwanto yamma da birnin tsakanin Betel da Ai. 13 Ya sanya dukkan sojojin ko'ina, muhimman rundunar ya sa su arewa da birnin, 'yan tsaron baya kuwa a yammancin birnin. Yoshuwa ya kwana a kwari a darennan. 14 Ananan da sarkin Ai ya ga haka, sai shi da mayaƙansa suka tashi da sassafe su ka gaggauta su ka kai wa Isra'ila hari ta gefen da ya fuskanci kwarin kogin Yodan. Bai sani ba cewa 'yan kwanto suna jiran su auka wa birnin ta baya. 15 Yoshuwa da dukkan Isra'ila suka yi kamar an rinjayesu su ka gudu cikin jeji. 16 Aka kira dukkan mutane da ke cikin birnin su ka fafare su, su ka sheƙa da gudu su na bin Yoshuwa, aka kuwa rinjaye su nesa da birnin. 17 Ba a bar ko mutum ɗaya a cikin Ai da kuma Betel da bai fito ya fafari mutanen Isra'ila ba. Su ka bar birnin da ƙofofin sa a buɗe sa'ad da suke fafarar Israi'ila. 18 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka miƙa mashin da ke hannun ka wajen Ai, domin zan ba da Ai cikin hannunka."Yoshuwa ya miƙa mashin da ke hannunsa wajen birnin. 19 Sai sojojin da su ka yi kwanto a saura su ka fito da ga inda suke sa'ad da ya mika hannunsa. Su ka yi gudu su ka shiga birinin su ka cinye shi. Nan da nan su ka cinna wa birnin wuta. 20 Mutanen Ai su ka waiga baya. Su ka ga hayaƙi da ga birnin ya turmuƙe ya tashi sama, ba su iya kuɓucewa nan ko can ba. Gama sojojin Isra'ila da su ka gudu jeji su ka juyo su ka fuskanci masu fafarar su. 21 Sa'ad da Yoshuwa da dukkan Isra'ila su ka ga mutanen da su ka ɓoye sun kone birnin, da kuma hayaƙin da ke tashi, su ka juyo su ka karkashe mutanen Ai. 22 Sauran sojojin Isra'ila, waɗanda su ka shiga birnin, su ka fito su kai masu hari. Ta haka aka cafke mutanen Ai gaba da baya a tsakiyar rundunar Isra'ila, wasu a wannan gefe wasu a can. Isra'ila su ka buga mayaƙan Ai; ba wanda ya tsira ko ya kuɓuce. 23 Su ka tsare sarkin Ai, wanda suka kama da rai, su ka kawo shi wurin Yoshuwa. 24 Ana nan da Isra'ila ta gama karkashe mazaunan Ai a fili kusa da jejin da su ka fafare su, sa'ad da dukkansu, har ga na ƙarshe su ka mutu da kaifin takobi, dukkan Isra'ila su ka koma Ai. Su ka faɗa masu da kaifin takobi. 25 Dukkan waɗanda aka kashe maza da mata, dubu goma sha biyu ne, dukkan mutanen Ai. 26 Yoshuwa bai janye hannunsa ba da ya mika ta sa'ad da ya ke rike da mashi, har sai da ya gama hallakar da dukkan mutanen Ai. 27 Isra'ila su ka ɗauki dabbobi kawai da ganimar da ke cikin birnin don kan su, kamar yadda Yahweh ya umarci Yoshuwa. 28 Yoshuwa ya ƙone Ai ya maishe ta kango har abada. Yasasshen wurin ne har yau. 29 Ya rataye sarkin Ai akan bishiya har sai maraice. Da rana ta kusan faɗuwa, Yoshuwa ya umarta a saukar da gangar jikin sarki da ga itace a jeffa shi a kofar birnin. A nan ne su ka tula tarin duwatsu akansa. Tsibin ya na nan har yau. 30 Sai Yoshuwa ya ginawa Yahweh bagadi, Allah na Isra'ila, a kan Dutsen Ebal, 31 dai - dai yadda Musa bawan Yahweh ya umarci mutanen Isra'ila, kamar yadda aka rubuta a littafin shari'a ta Musa: "Bagadi da ga duwatsun da ba a sassaƙa ba, wanda ba mutumin da ya ɗibiya guduma a kai." Ya mika hadayun ƙonawa ga Yahweh akan bagadin, su ka kuma miƙa hadayun salama. 32 A nan a gaban mutanen Isra'ila ya rubuta shari'ar Musa bisa duwatsun. 33 Dukkan Isra'ila, da shugabanninsu, da hakimai, da mahukuntansu, su ka tsaya a gefe biyu na akwatin alƙawari a gaban firistoci da Lebiyawa da ke ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh - baƙi da haifaffun wurin - rabinsu su ka tsaya a gaban Dutsen Gerizin, rabin kuma su ka tsaya a gaban Dutsen Ebal. Su ka albarkaci mutanen Isra'ila, kamar yadda Musa bawan Yahweh ya umarce su tun da farko. 34 Bayan haka, Yoshuwa ya karanta dukkan zantattukan shari'a, da albarkun da la'anun, kamar yadda aka rubuta a littafin shari'a. 35 Babu kalma ko ɗaya da ga dukkan abin da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta a gaban taron Isra'ila ba, har ma da mata, da ƙananan yara. da baƙin da su ke zaune tare da su.

Sura 9

1 Sai dukkan sarakunan dake zaune a ƙetaren Yodan a ƙasar duwatsu, da kuma kwarin gaɓar Babbar Teku wajen Lebanon - Hitiyawa, Amoriyawa Kan'aniyawa, Feriziyawa Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa - 2 waɗannan su ka tattaru ƙarƙashin tuta guda, domin su yaƙi Yoshuwa da Isra'ila. 3 Da mazaunan Gibiyon su ka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai, 4 su ka yi masu hila. Suka tafi kamar jakadu. Su ka ɗauki koɗaɗɗun buhuna su ka ɗibiya su kan jakunansu. Su ka kuma ɗauki tsofaffin salkunan ruwan inabi da su ka ƙoɗe, yagaggu, sun kuma sha ɗinki. 5 Su ka sa tsoffofin takalman da suka sha gyara a ƙafafunsu, su ka sa ka tsofoffin riguna da su ka koɗe. Guzurin wainarsu kuma duk sun bushe sun yi fumfuna. 6 Su ka tafi wurin Yoshuwa a sansanin Gilgal, su ka ce masa da shi da mutanen Isra'ila, "Mun taho da ga ƙasa mai nisa, saboda haka sai ku yi alƙawari da mu." 7 mutanen Isra'ila su ka cewa Hiviyawa, "Watakila ku na zaune kusa da mu. ‌Ƙaƙa za mu yi alƙawari da ku?" 8 Su ka cewa Yoshuwa, "Mu bayinka ne," Yoshuwa ya ce masu, "Ku su wanene? Daga ina ku ka fito?" 9 Su ka ce masa, "Barorinka sun zo daga ƙasa mai nisa, sabili da sunan Yahweh Allahnka. Mun ji rahoto a kan sa da kuma dukkan abubuwan da ya yi a Masar - 10 da dukkan abubuwan nan da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa da ke hayin Yodan - Sihon sarkin Hesbon da kuma Og sarkin Bashan da ke Astarot. 11 Dattawanmu da dukkan mazaunan ƙasarmu su ka ce mana, 'Ku ɗauki guzuri a hannuwanku saboda tafiyarku. Ku je ku same su ku ce masu, "Mu bayinku ne. Ku yi yarjejeniya da mu." 12 Waɗannan gurasunmu ne, da ɗumi mu ka ɗauko su daga gida ranar da mu ka fito tafiya gunku. Amma yanzu, ku duba, sun bushe sun kuma yi funfuna. 13 Wannan salkunan ruwan inabi sabbi ne da muka cika su, amma ku duba, yanzu suna ɗiga. Rigunanmu da takalmanmu sun koɗe saboda nisan tafiya."' 14 Sai Isra'ilawa su ka karɓi waɗansu guzurinsu, amma ba su biɗi shawara ba da ga Yahweh domin ya bishe su. 15 Yoshuwa ya dai - daita da su ya kuma yi alƙawari da su, a barsu su rayu. Shugabannin mutanen kuma su ka yi masu alƙawari. 16 Bayan kwana uku da Isra'ilawa su ka yi alƙawari da su, sai su ka ji ai makwabtansu ne kuma su na zaune kurkusa. 17 Sai mutanen Israa'ila su ka tashi su ka isa biranensu a kan rana ta uku. Biranensu kenan Gibiya, Kefira, Birot, da Kiriyet - Yarim. 18 Mutanen Isra'ila ba su kai masu hari ba saboda shugabanninsu sun rantse masu a gaban Yahweh, Allah na Isra'ila. Isra'ilawa dukka su ka yi ta gunaguni găba da shugabanninsu. 19 Amma dukkan shugabanni su ka cewa mutane dukka, "Mun rigaya mun rantse masu da Yahweh Allah na Isra'ila, yanzu fa ba za mu cuce su ba. 20 Ga abin da za mu yi masu: Domin mu guji duk wani fushi da zai afko mana sabili da rantsuwa da mu ka yi masu, za mu bar su su rayu. 21 Shugabanni su ka cewa mutanensu, "Mu bar su su rayu." Sabili da haka, Gibiyaniyawa su ka zama masu sarar itace da masu jan ruwa domin dukkan Israa'ilawa, kamar yadda shugabanni su ka umarta game da su. 22 Yoshuwa ya kira su ya ce, "Me ya sa ku ka ruɗemu ku ka ce, 'Muna nesa da ku', alhali kuwa ku na nan cikinmu? 23 Yanzu fa, sabili da wannan, la'anannu ne ku waɗansunku za su zama bayi ko yaushe, masu saro itace da masu jan ruwa domin gidan Allahnmu." 24 Su ka amsa wa Yoshuwa su ka ce, "Sabili da an faɗa wa bayinka cewa, Yahweh Allahnku ya umarci bawansa Musa ya ba ku dukkan ƙasar, ya kuma karkashe dukkan mazaunan ƙasar a gabanku - shi ne mu ka ji tsoronku saboda ranmu. Shi ya sa mu ka yi wannan abu. 25 Yanzu dai, ku duba, muna ƙalƙashin ikonku. Duk iyakar abin da ku ka ga ya dace kuma dai -dai ne ku yi da mu, sai ku aiwatar." 26 Sai Yoshuwa ya yi masu haka: ya fitar da su da ga ƙarƙashin mallakar mutanen Isra'ila. Isra'ilawa kuwa ba su kashe su ba. 27 A ranar Yoshuwa ya maida Gibiyanawa masu sarar itace da masu jawo ruwa domin mutanen Isra'ila, da na bagadin Yahweh, har wa yau, duk inda Yahweh ya zaɓa.

Sura 10

1 Yanzu da Adonizedek, sarkin Yerusalem, ya ji yadda Yoshuwa ya kama Ai kuma har ya hallakar da ita baki ɗaya (kamar yadda ya yi da Yeriko da kuma sarkinta) ya kuma ji yadda mutanen Gibeyon suka ƙulla alkawarin zaman lafiya da Isra'ila har ma suna acikinsu. 2 Mutanen Yerusalem sun tsorata ƙwarai gama Gibeyon babban birnin ainin, kamar ɗaya daga cikin manyan sarakunan biranen. Har ma ta fi Ai ga shi kuma dukkan mayaƙan mazaje ne ƙarfafa. 3 Saboda haka Adonizedek, sarkin Yerusalem, ya aika da saƙo ga Hoham, sarkin Hebron, ga Piram, sarkinYarmut, da Yafiya sarkin Lakish, da kuma Debir sarkin Eglon: 4 "Ku zo nan wurina ku taimake ni. Bari mu je mu yaƙi Gibeyon gama sun ƙulla alkawarin salama tare da Joshuwa da kuma mutanen Isra'ila." 5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarkin Yerusalem da sarkin Hebron da sarkin Yarmut da sarkin Lakish, da sarkin Eglon sun zo, dukkansu kuma da abokan gãbarsu. Sun kafawa Gibeyon sansani domin su yaƙe ta. 6 Mutanen Gibeyon sun aika da saƙo ga Yoshuwa da kuma sojojin Gilgal. Sun ce, "Zo da sauri! Kada ka janye hanuwanka daga bayinka. Zo wurinmu da sauri ka ce-ce mu. Taimaka mana, domin dukkan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu." 7 Joshuwa ya tafi daga Gilgal, shi da dukkan mutanen yaƙinsa, tare da dukkan jarumawa. 8 Yahweh kuma ya ce da Yoshuwa, "Kada ka ji tsoronsu. Na riga na ba da su a hannunka. Babu wani daga cikinsu da zai hana ka yaƙe su." 9 Yoshuwa ya tafi nan da nan ya auka masu, bayan ya yi tattaki dukkan dare daga Gilgal. 10 Yahweh kuwa ya rikita abokan gãbar Isra'ila, Isra'ilawa kuwa su ka kashe su da yawa a Gibeyon su ka bi su ta hanyar haurawa zuwa Ber-horon, a nan masu ka yi ta karkashe su a hanyar Azeka da Makkeda. 11 A sa'ad da suke gudu daga Isra'ilawa, a gangarar hawan Bet-horon, Yahweh ya jefe su da manyan duwatsu daga sama a kansu dukka hanyar zuwa Azeka, sun kuma mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi yawan mutanen Isra'ila su ka kashe da takobi. 12 Sai Yoshuwa ya yi magana da Yahweh a ranar da Yahweh ya ba mutanen Israila nasara a kan Amoriyawa. Wannan shi ne abin da Yoshuwa ya ce da Yahweh a gaban Isra'ila, "Rana, ki tsaya a Gibeyon, wata kuma, a kwarin Ayalon." 13 Rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya ba ya motsi har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gãbarsu. Wannan ba shi ne ke rubuce a Littafin Yashar ba? Rana ta tsaya a tsakar sararin sama; ba ta faɗi ba dukkan yini. 14 Ba a taba yin yini kamar wannan ba ko kuma makamancinsa ba, da Yahweh ya saurari muryar mutum. Domin Yahweh ya yi yaƙi a madadin Isra'ila. 15 Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila sun koma zango a Gilgal. 16 Yanzu waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu suka ɓuya a cikin kogon Makkeda. 17 Sai aka faɗawa Yoshuwa, "An same su-sarakuna biyar suna ɓoye a kogon Makkeda." 18 Yoshuwa ya ce, "Murgina manyan duwatsu a kan bakin kógon a kuma sa sojoji a wurin don su tsaresu. 19 Amma kada ku tsaya. Sai ku runtumi abokan ǧabanku ku kuma faɗa masu daga baya. Kada ku bar su su shiga biranensu, gama Yahweh Allahnku ya rigaya ya ba da su a hannunku." 20 Yoshuwa da 'ya'yan Isra'ila sun gama karkashe su kisa mai yawa ƙwarai, har sai da aka kusan halaka su dukka; sai sauran kaɗan ne ba a kashe ba; sauran da su ka ragu suka shige birane masu garu. 21 Sa'annan dukkan sojojin sun koma da salama wurin Joshuwa a sansani a Makkeda. Ba kuma mutumin da ya faɗi wata kalmar ǧaba da ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila. 22 Sai Yoshuwa ya ce, "Ku buɗe bakin kógon kuma daga cikin kogon ku ba ni waɗannan sarakuna biyar." 23 Sun aikata kamar yadda ya ce. Sun kawo masa waɗannan sarakuna biyar daga kógon--sarkin Yerusalem, sarkin Hebron, sarkin Yarmut, sarkin Lakish, da kuma sarkin Eglon. 24 Da su ka kawo sarakunan a wurin Yoshuwa, ya ƙirawo kowanne mutum da ke Isra'ila. Ya cewa shugabanin mayaƙa waɗanda su ka tafi tare da shi, "Ku sa ƙafafunwanku a wuyansu."Su kuwa sun zo sun taka wuyansu da ƙafafuwansu. 25 Sai ya ce da su, "Kada ku ji tsoro ko kuwa ku razana. Ku yi ƙarfin hali. Wannan shi ne abin da Yahweh zai yi da dukkan abokan gãbarku waɗanda za ku yi yaƙi da su. 26 Sai Yoshuwa ya kai masu hari har ya kashe sarakunan. Ya kuma rataye su a kan itatuwa biyar. An rataye su a kan itatuwa har yamma. 27 Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Yoshuwa ya ba da umarni, sai aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan sai aka jefa su cikin kõgon da su ka ɓoye kansu. Sai su ka sa manyan duwatsu aka rufe baƙin kõgon. Waɗannan duwatsun suna nan har wannan rana. 28 Ta wannan hanya, Yoshuwa ya kama Makkeda a ranar, ya kuma kashe kome a wurin da takobi, har ma da sarkin. Ya hallakar da su da dukkan wani abu mai rai a wurin. Bai ƙyale kowa da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa sarkin Yeriko. 29 Yoshuwa tare da dukkan Isra'ilawa sun zarce daga Makkeda zuwa Libna. 30 Yahweh kuma ya ba su ita ta hannun Isra'ila -- tare da sarkinsu. Yoshuwa kuwa ya kashe kowanne abu da ke rayuwa a cikinta da takobi. Bai bar wani abu da zai rayu ba a cikinta. Ya yi wa sarkin kamar yadda ya yi wa sarkin Yeriko. 31 Sai Joshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka zarce daga Libna zuwa Lakish. Ya kewaye ta kuma ya auka mata da yaƙi. 32 Yahweh ya ba da Lakish a hannun Isra'ila. Yoshuwa ya cinye ta a rana ta biyu. Ya kashe kowanne abu mai rayuwa da takobi wanda ke cikinta, kamar yadda ya yi da Libna. 33 Sai Horam, sarkin Gezer, ya zo ya kawo wa Lakish taimako. Yoshuwa kuwa ya fãɗa masa shi da sojojinsa har babu wani abu mai rai da ya rage. 34 Sai Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka zarce zuwa Lakish ta Eglon. 35 Sun kewaye ta sun auka mata da yaƙi, a wannan rana su ka cinyeta da yaƙi. Sun buge ta da takobi sun kuma hallaka kowanne mutum da ke cikinta, kamar yadda Yoshuwa ya yi a Lakish. 36 Sai Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka haura daga Eglon zuwa Hebron. 37 Sun auka mata da yaƙi. Sun cinyeta suka kuma bugi kowanne mutum da ke cikinta da takobi, har ma da sarkin da kuma dukkan ƙauyukan da ke kewaye da ita, sun karkashe komai da ke rayuwa a cikinta, ba su ƙyale wani abu da zai rayu ba, kamar yadda Yoshuwa ya yi wa Eglon. Ya hallaka komai da kowanne abu mai raI a cikinta. 38 Sai Yoshuwa ya juya, tare da dukkan sojojin Isra'ila da ke tare da shi, sun kuma wuce zuwa Debir sun kuma auka mata da yaƙi. 39 Ya kame ta tare da sarkinta, da dukkan ƙauyukan da ke kewaye da ita. Sun buge su da takobi har sun kashe dukkan abun da ke rayuwa a cikinta. Yoshuwa bai bar masu rayuwa ba, kamar yadda ya yi a Hebron da sarkinta, da kuma kamar yadda ya yi a Libna da sarkinta. 40 Yoshuwa ya ci nasara da dukkan ƙasar, da tuddan ƙasar, da Negeb, da filayen kwarurruka, da kuma gangare. Da dukkan sarakunansu babu wanda ya tsira. Ya karkashe su babu wani abu mai rai, kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ummarta. 41 Yoshuwa kuwa ya kai masu hari da takobi tun daga Kadesh Barneya har zuwa Gaza, da dukkan ƙasar Goshen zuwa Gibeyon. 42 Yoshuwa kuma ya cinye dukkan waɗannan sarakuna da kuma ƙasashensu a lokaci ɗaya domin Yahweh Allah na Isra'ila, ya yi yaƙin don Isra'ila. 43 Sa'annan Yoshuwa, da dukkan Isra'ila tare da shi, sun koma zuwa zango a Gilgal.

Sura 11

1 Sa'ad da Yabin, sarkin Hazor, yaji wannan, ya aika da saƙo ga Yobab, sarkin Madon, zuwa ga sarkin Shimron, da sarkin Akshaf. 2 Ya kuma aika da saƙon ga sarakuna waɗanda suke arewacin ƙasar tuddai, da ke cikin kudancin Kinneret, da ke cikin filayen kwari da kuma tuddai da ke cikin Dor a yamma. 3 Ya kuma aika da saƙon zuwa ga Kanaaniya gabas da yamma da Amoriyawa da Hatiyawa da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa da suke cikin ƙasar tuddai, da kuma Hiwiyawa da ke Tsaunin Harmon a ƙasar Mizfa. 4 Dukkan mayaƙansu su ka fito wurinsu, babbar rundunar sojoji mai yawa kamar yashin teku. Su na da yawan dawakai da karusai ƙwarai da gaske. 5 Dukkan waɗannan sarakuna kuwa su ka shirya lokacin da za su haɗu, sun yi sansani a bakin ruwayen Merom don su yi yaƙi da Isra'ila. 6 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Kada ka ji tsoron kasancewarsu, domin gobe war haka zan ba da su ga dukkan Isra'ila kamar matattun mutane. Za ku daddatse agaran dawakansu, za ku kuma ƙone karusansu" 7 Yoshuwa da dukkan mayaƙansa za su ma-mayesu. Nan da nan suka zo ruwayen Meron, suka karkashe abokan ǧabarsu. 8 Yahweh kuma ya ba da abokan gãbar a hannun Isra'ila, sun kuma hallaka su da takobi su ka runtume su har zuwa Sidon, Misrefot Ma'im, har zuwa gabashin ƙwarin Mizfa. Sun karkashe su har babu wani mai tsira da ya rage a cikinsu. 9 Yoshuwa kuwa ya yi masu kamar yadda Yahweh ya faɗa masa. Ya daddatse agaran dawakansu ya kuma ƙone ƙarusansu. 10 A wannan lokaci Yoshuwa ya juya da baya ya ci Hazor. Ya kashe sarkinta da takobi. (Hazor ita ce cibiyar dukkan waɗannan mulkokin.) 11 Sun kashe dukkan abin da ke raye a wannan wurin da takobi, ya kuma hallakar da su kakaf, saboda haka babu wanda aka rage da rai a wurin. Ya kuma ƙone Hazor. 12 Yoshuwa kuwa ya ci dukkan biranen sarakunan. Ya kuma ci dukkan sarakunansu da takobi. Ya hallakar da su kakaf kamar yadda Musa bawan Yahweh ya ummarta. 13 Isra'ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da aka gina bisa tuddai ba, sai dai Hazor, ita kaɗai Yoshuwa ya ƙone. 14 Sojojin Isra'ila kuwa su ka kwashe dukkan ganima daga waɗannan birane tare da shanu domin kansu. Sun kashe kowanne mutum da takobi har sai da dukkansu su ka mutu. Ba su bar wata hallita da ke da rai ba. 15 Kamar yadda Yahweh ya ummarci bawansa Musa, ta hanyar da Musa ya ummarci Yoshuwa, haka nan Yoshuwa ya yi da ita. Bai bar kome ba da bai aikata ba cikin dukkan abin da Yahweh ya ummarci Musa ya yi. 16 Yoshuwa ya ɗauke dukkan ƙasar, da ƙasar tuddai, da dukkan Negeb, da dukkan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Yodan Kogin kwari, da ƙasar tuddai ta Isra'ila, da filayen gangare. 17 Daga Tsaunin Halak kusa da Idom, da wanda ya tafi zuwa arewa har zuwa wajen Ba'al Gad a kwari kusa da Lebanon a ƙarƙashin Tsaunin Hermon, ya kama dukkan sarakunansu ya kuma kashe su. 18 Yoshuwa ya ɗauki dogon lokaci yana yaƙi da dukkan sarakunan. 19 Ba bu wani birni da ya yi zaman salama da sojojin Isra'ila sai dai Hiwiyawa da su ke zaune a Gibiyon. Isra'ila kuwa ta ci dukkan sauran biranen da yaƙi. 20 Domin Yahweh ne ya taurare zukatansu har da za su tasar ma Isra'ila da yaƙi, don a hallaka su a kuma shafe su ba tare da tausayi ba, kamar yadda aka ummarci Musa. 21 A wannan lokaci kuwa Yoshuwa ya tafi ya kuma hallaka Anakawa. Ya kuma yi wannan a ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da kuma dukkan ƙasar tuddai ta Yahuda, da dukkan ƙasar tuddai ta Isra'ila. Yoshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu. 22 Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar Isra'ila sai ko Gaza, da Gat, da kuma Ashdod. 23 Ta haka Yoshuwa ya ci dukkan ƙasar, kamar yadda Yahweh ya faɗawa Musa. Yoshuwa kuwa ya ba da ita gãdo ga Israila bisa ga kabilar kowa, Sai ƙasar ta shaƙata daga yaƙe -yaƙe.

Sura 12

1 Yanzu waɗannan su ne sarakunan ƙasar, wadda mutanen Isra'ila su ka cinye da yaƙi. Isra'ilawa sun mallaki ƙasar a gabashin Yodan inda rana ta ke fitowa daga Kwarin Kogin Arnon zuwa Tsaunin Harmon, da dukkan Arabah wajen gabas. 2 Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower, wadda ta ke iyakar kwarin Arnon Gorge daga tsakiyar kwarin, har rabin Giliyad zuwa ga Kogin Yabbok iyakar Amoniyawa. 3 Sihon kuma ya yi mulki a kan Arabah zuwa Tekun Kinneret, da zuwa gabashin Tekun Arabah (Tekun Gishiri) a wajen gabas, da dukkan hanyar Ber Yeshimot da wajen kudu, zuwa gangaren gindin Tsaunin Fisga. 4 Og, sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayim, wanda ya zauna a Ashtarot da Edirai. 5 Ya yi mulki a Tsaunin Hermon, Salika, da dukkan Bashan, har zuwa iyakar mutanen Geshur da kuma Ma'akatiyawa, da rabin Giliyad, zuwa kan iyakar Sihon, sarkin Heshbon. 6 Musa bawan Yahweh, da mutanen Isra'ila sun yi nasara da su, kuma Musa bawan Yahweh ya ba su ƙasar gãdo ga Rubenawa, da Gadawa, da kuma rabin kabilar Manassa. 7 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar waɗanda Yoshuwa da mutanen Isra'ila suka ci a yammacin Yodan, daga Ba'al Gad a ƙwari kusa da Lebanon zuwa Tsaunin Halak kusa da Idom. Yoshuwa ya ba da ƙasar ga kabilun Isra'ila don su ǧada. 8 Ya ba da tuddan ƙasar, da kwaruruka, da Arabah, da gefan tuddai, da jejin da kuma Negeb - ƙasar Hitiyawa, Amoriyawa, Kan'aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa. 9 Sarakunan sun haɗa da sarkin Yeriko da sarkin Ai da ke kusa da Betel, 10 da sarkin Yerusalem da sarkin Enayim, 11 da sarkin Yarmut da sarkin Lakish, 12 da sarkin Eglon da sarkin Gezer, 13 da sarkin Debir da sarkin Geder, 14 da sarkin Horma da sarkin Arad, 15 da sarkin Libna da sarkin Adullam, 16 da sarkin Makkeda da sarkin Betel, 17 da sarkin Taffuwa da sarkin Hefer, 18 da sarkin Afek da sarkin Lasharon, 19 da sarkin Madon da sarkin Hazor, 20 da sarkin Shimron Meron da sarkin Akshaf, 21 da sarkin Ta'anak da sarkin Megiddo, 22 da sarkin Kedesh da sarkin Yokniyam a Karmel, 23 da sarkin Dor a Nafat Dor da sarkin Goyim a Gilgal, 24 da kuma sarkin Tirza. Yawan sarakunan kuwa talatin da ɗaya ne dukkansu.

Sura 13

1 Yanzu Yoshuwa ya tsufa ƙwarai sai Yahweh ya ce da shi, "Ka tsufa ƙwarai, amma har yanzu akwai sauran ƙasar da yawa da ba a mallaka ba. 2 Wannan ita ce ƙasar da ta rage: a dukkan sashin Filistiyawa, da dukkan waɗanda ke Geshuriyawa, 3 (daga Shihor, wanda ke gabas da Masar da wajen arewanci iyakar Ekron, wanda ake ɗauka ta Kan'aniyawa ce, da sarakuna biyar na Filistiyawa, da su ke Gaza, Ashdod, Ashkelon, Gat da Ekron - da ƙasar Aviyawa). 4 A kudu (da ƙasar Aviyawa); akwai sauran ƙasashen Kan'aniyawa, da Ara wanda ta ke ta Sidoniyawa, zuwa Afek har kuma iyakar Amoriyawa; 5 da ƙasar Gebaliyawa, dukkan Lebanon wajen fitowar rana, zuwa Ba'al Gad ƙasar Tsaunin Hermon zuwa Lebo Hamat. 6 Kuma da dukkan mazaunan ƙasar tuddai daga Lebanon har zuwa can Misrefot Mayim, da dukkan mutanen Sidon. Zan kore su a gaban sojojin Isra'ila. Ka tabbatar ka raba ƙasar ga Isra'ila a matsayin gãdonsu, kamar yadda na ummarce ka. 7 Raba wannan ƙasar a matsayin gãdo ga kabilu tara, da kuma ga rabin kabilar Manasse. 8 Tare da sauran rabin kabilar Manasse, da Rubenawa da kuma mutanen Gad sun karɓi nasu gãdon wanda Musa ya ba su a wajen gabas da Yodan, 9 daga Arowa wadda take a gefen kwarin Kogin Arnon (ya hada da birnin da ke tsakiyar kwarin), da dukkan ƙasar tudu ta Medeba har zuwa Dibon; 10 dukkan biranen Sihon da sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, zuwa ga iyakar Amoniyawa; 11 Giliyad, da kuma yankin Geshuriyawa da Makatiyawa da dukkan na Tsaunin Harmon da dukkan Bashan zuwa Saleka; 12 da dukkan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarauta a Ashtarot da Edirai - waɗannan su ne ragowar mutanen Refayim - Musa ya buge su ya kuma kore su. 13 Amma duk da haka mutanen Israila ba su kori Geshuriyawa ko Makatiyawa ba. Maimakon haka, Geshuriyawa da Makatiyawa sun zauna a cikin Isra'ila har wa yau. 14 Ga kabilar Lebi ne kaɗai Musa bai ba da ta gado ba. Hadayu na Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda aka yi da wuta, ǧadonsu, kamar yadda Allah ya faɗawa Musa. 15 Musa ya riga ya ba kabilar Ruben nasu ǧadon bisa ga iyali-iyali. 16 Nasu yankin ƙasar daga Arowa, a gefen ƙwarin Kogin Arnon, da kuma birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukkan tuddai kusa da Medeba. 17 Ruben kuma ya sami Heshbon da dukkan biranenta da suke kan tudu, Dibon, da Bamot Ba-al, da Bet Ba'al Miyon, 18 da Yahaz, da Kedemot, da Mefa'at, 19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret Shahar da ta ke bisa tudun da yake cikin kwarin. 20 Ruben kuma ya karɓi Bet Feyor, da gangaren Fisga, da Bet Yeshimot, 21 da dukkan biranen kan tudu, da dukkan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya sarauci Heshbon, wanda Musa ya ci shi da yaƙi tare da shugabanin Midiyawa, Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba, sarakunan Sihon, wanda ya zauna a ƙasar. 22 Mutanen Isra'ila kuma su ka kashe shi da takobi, Balaam ɗan Beyor, matsubbaci, daga cikin sauran waɗanda da su kashe. 23 A iyakar kabilar Ruben akwai Kogin Yodan, wannan shi ne iyakarsu. Wannan shi ne ǧadon kabilar Ruben, da aka ba kowanensu na iyalinsu, tare da biranensu da ƙauyukansu. 24 Wannan shi ne abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalinsu: 25 Yankin ƙasarsu shi ne Yaza, da dukkan biranen Giliyad da rabin ƙasar Ammoniyawa, zuwa Arowa, wadda ke gabas da Rabbah, 26 daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, daga Mahanayim zuwa iyakar Debir. 27 A kwarin, Musa ya ba su Bet Haram, Bet Nimrah, Sukkot da Zafon da sauran ragowar mulkin Sihon sarkin Heshbon, tare da Yodan ne iyaka, zuwa iyakar Tekun Kinneret a gabashin hayin Yodan. 28 Wannan shi ne gãdon kabilar Gad bisa ga iyalinsu, tare da biranensu da ƙauyukansu. 29 Musa ya ba da gãdo ga rabin kabilar Manasse. An ba da ita ga rabin kabilar mutanen Manasse, bisa ga iyalinsu. 30 Yankin ƙasarsu daga Mahanayim, da dukkan Bashan da dukkan sarautar Og sarkin Bashan da dukkan garuruwan Yayir da waɗanda su ke a Bashan, birane sittin ne; 31 rabin Giliyad, da Ashtarot da Edirai (biranen masarautar Og a Bashan). Waɗannan ne aka ba da su ga iyalin Makir ɗan Manasse - rabin mutanen Makir, an ba kowanne iyali. 32 Wannan shi ne gãdon da Musa ya ba su a kan filayen Mowab, a hayin gabashin Yodan na Yeriko. 33 Musa bai ba kabilar Lebi gãdo ba. Yahweh, Allah na Isra'ila, shi ne gãdonsu, kamar yadda ya faɗa masu.

Sura 14

1 Waɗannan su ne yankunan ƙasar da mutanen Isra'ila suka karɓa matsayin gãdo a ƙasar Kan'ana, wanda Eliyeza firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma iyalin shugabainin kabilun kakaninsu na mutanen Isra'ila. 2 Gãdonsu ya sa mu ne ta hanyar jefa kuri'a don kabilun nan tara da rabi, kamar yadda Yahweh ya ummarta ta hannun Musa. 3 Domin Musa ya riga ya ba da gãdon ga kabilu biyu da rabi can hayin Yodan, amma ga Lebiyawa bai ba su gãdo ba. 4 Kabila Yosef kuma kabilu biyu ne, Manasse da Ifaim. Lebiyawa kuwa ba a ba su wani yanki na ƙasar gãdo ba, sai dai an ba su birane da za su zauna, tare da filayen da za su yi kiwon garkensu da kuma kayan da su ke bukata. 5 Mutanen Isra'ila kuwa su ka yi kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa, sun rarraba ƙasar. 6 Sai kabilar Yahuda suka je wurin Yoshuwa a Gilgal. Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, "Ka san abin da Yahweh ya ce da Musa mutumin Allah a kanka da ni a Kadesh Barneya. 7 Ina da shekaru arba'in sa'ad da Musa bawan Yahweh ya aike ni daga Kadesh Barneya in leƙo asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda ya ke a zuciyata. 8 Amma 'yan'uwana da mu ka tafi tare sun karyar da zukatan mutanen da tsoro. Amma ni da na bi Yahweh Allahna. 9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana, cewa, 'Hakika a ƙasar nan wanda ƙafafunka su ka ta ka za ta zama gãdonka da kai da 'ya'yanka har abada, domin ka bi Yahweh Allahnka sosai.' 10 Yanzu, duba! Yahweh ya kiyaye ni da rai waɗannan shekaru arba'in da biyar, kamar yadda ya faɗa-daga lokacin da Yahweh ya faɗi wannan magana ga Musa, sa'ad da Isra'ila suke tafiya a jeji. Yanzu, duba! ina mai shekaru tamanin da biyar da haihuwa. 11 Har wannan rana ina nan kamar ranar da Musa ya aike ni waje. ƙarfina yanzu yana nan kamar ƙarfin dă domin yaƙi da kuma zuwa da kowowa. 12 Saboda haka yanzu ka ba ni ƙasar tuddai, wadda Yahweh ya yi mani alkawari a waccan rana. Gama ka ji a wannan rana yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu. Watakila Yahweh zai kasance tare da ni, ni kuma in kore su, kamar yadda Yahweh ya faɗa." 13 Sai Yoshuwa ya sa masa albarka ya kuma ba da Hebron a matsayin gãdo ga Kalibu ɗan Yefunne. 14 Saboda haka Hebron ta zama gãdon Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze har zuwa wannan rana, domin ya bi Yahweh, Allah na Israila sosai. 15 Yanzu sunan Hebron kamar da Kiriyat Arba ne. (Arba kuwa ya zama babbban mutum ne cikin gwarzayen.) ‌Ƙasar kuwa ta huta daga yaƙi.

Sura 15

1 Rabon ƙasar da aka yi wa kabilar mutanen Yahuda, an ba su ne bisa ga iyalansu, ya kai kudu iyaka da Idom, zuwa jejin Zin wanda ta ke can kudu nesa. 2 Iyakarsu wajen kudu ta mike tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga sashen gaɓar da ta fuskanci kudu. 3 Iyakarsu ta tafi har kudancin tuddan Akrabbim ta kuma zarce zuwa Zin, ta kuma tafi har zuwa kudancin Kadesh Barneya, ta wajen Hezron, har kuma zuwa Addar, ta kuwa karkata zuwa Karka. 4 Ta wuce zuwa Azmon, ta bi ta rafin Masar, kuma ta zo ƙarshe a teku. Wannan ita ce iyakarsu a kudu. 5 Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri, har zuwa bakin Yodan. Iyakar arewa kuma ta miƙe daga teku zuwa bakin Yodan. 6 Ta tafi zuwa Bet Hogla ta kuma wuce zuwa arewa da Bet Arabah. Sai ta haura zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben. 7 Iyakar da ta tafi Debir zuwa Kwarin Achor, da kuma arewacin, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal, wadda ta ke daura da tuddun Adummim, wanda ke kudu da gefen kwari. Sai ta zarce zuwa ruwan En Shemesh ta kuma tafi En Rogel. 8 Sai iyakar ta bi ta Kwarin Ben Hinnom a wajen kudancin birnin Yebusawa (wato Yerusalem). Sa'an nan ta bi ta sashen tuddun da ke shimfiɗe daura da kwarin Hinnom, wajen yamma, a arewacin ƙarshen Kwarin Refayim. 9 Sa'an nan iyakar ta faɗaɗa daga bisan tuddai zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, har zuwa can biranen Tsaunin Efron. Sai iyakar ta karkata zuwa Ba'ala (wato Kiriyat Yeyarim). 10 Sa'an nan iyakar ta kewaye yammacin Ba'ala zuwa Tsaunin Seyir, daga nan kuma ta zarce gefen Tsaunin Yeyarim a arewa (wato Kesalon), sai ta gangara zuwa Bet Shemesh, ta kuma ƙetare har can zuwa Timna. 11 Iyakar kuwa ta bi ta gefen arewacin tuddun Ekron, sa'an nan ta karkata kewayin Shikkeron ta kuma wuce zuwa Tsaunin Ba'ala, daga wurin ta tafi zuwa Yabneyel. Iyakar ta ƙare a teku. 12 Yammacin iyakar Babbar Tekun da kuma gaɓarta. Wannan iyakar na kewaye da kabilar Yahuda, bisa ga iyalin kowa. 13 Don kiyaye ummarnin Yahweh ga Yoshuwa, Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne rabonsa na ƙasar a tsakiyar kabilar Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron (Arba shi ne uban Anak). 14 Kaleb kuwa ya kori mazan 'ya'yansa uku daga wurin Anak: Sheshai, Ahiman da Talmai, zuriyar Anak. 15 Ya tafi daga wurin ta wurin rashin amincewar mazaunan Debir (Debir da dã ake Kiriyat Sefer). 16 Kaleb yace, "Duk mutumin da ya kai hari ga Kiriyat Sefer har kuma ya kama ta, zan ba shi 'yata Aksa a matsayin mata." 17 Da Otniyel ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kaleb, ya ci ta, Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa matsayin matarsa. 18 Bayan wannan, Aksa ta zo ga Otniyel ta kuma iza shi ya roƙi babanta fili. Da ta sauka daga kan jakinta, Kaleb ya ce mata, "Me kike bukata?" 19 Aksa ta amsa, "Ka yi mani alheri na musamman, da yake ka ba ni ƙasa a Negeb: ka kuma ba ni maɓuɓɓugar ruwa."Kaleb kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddu da kuma maɓuɓɓugar kwari. 20 Wannan shi ne gãdon kabilar Yahuda, da aka ba iyalinsu 21 Biranen na kabilar Yahuda da ke can kudu sosai, suna wajen iyakar Idom, su ne Kabzeyel, Eder, Yagur, 22 Kina, Dimona, Adada, 23 Kedesh, Hazor, Yitnan, 24 Zif, Telem, Beyalot. 25 Hazor Hadatta, Kiriyot Hezron (wato an san shi da Hazor), 26 Amam, Shema, Molada, 27 Hazar Gadda, Heshmon, Bet Felet, 28 Hazar Shuwal, Biyasheba, Biziyotiya. 29 Ba'ala, Iyim, Ezem, 30 Eltolad, Kesil, Horma, 31 Ziklag, Madmanna, Sansanna, 32 Labayot, Shilhim, Ayin, Rimmon. Wadannan su ne birane ashirin da tara dukkansu, har da ƙauyukansu. 33 A kwarin ƙasar tuddu ta yamma, akwai su Eshtawol, Zora, Ashna, 34 Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam, 35 Yamut, Adullam, Soko, Azeka 36 Shayarim, Aditayim, Gedera, (wato Gederotayim). Waɗannan su ne birane goma sha huɗu yawansu duk da ƙauyukansu. 37 Zenan, Hadasha, Migdalgad, 38 Diliyan, Mizfa, Yokteyel, 39 Lakish, Bozkat, Eglon. 40 Kabbon, Lahmas; Kitlish, 41 Gederot, Bet Dagon, Na'ama, Makkeda. Waɗannan su ne birane goma sha shida yawansu duk da ƙauyukansu. 42 Libna, Eter, Ashan, 43 Yifta, Ashna, Nezib, 44 Kaila, Akzib, Maresha. Waɗannan su ne birane tara, duk da ƙauyukansu. 45 Ekron, tare da kewayan garuruwa da ƙauyuka; 46 daga Ekron zuwa Babbar Teku, dukkan mazaune waɗanda su ke kusa da Ashdod, da dukkan ƙauyukanta. 47 Ashdod, da kewayan garuruwa da ƙauyukanta; Gaza, da kewayan garuruwa da ƙauyukanta; zuwa rafin Masar, da kuma zuwa Babbar Teku tare da gaɓarta. 48 A tuddun ƙasar, Shamir, Yattir, Soko, 49 Danna, Kiriyat Sanna (wato Debir), 50 Anab, Eshtimo, Anim, 51 Goshen, Holon, da Gilo. Waɗannan su ne birane goma sha daya, tare da ƙauyukansu. 52 Arab, Duma, Eshan, 53 Yanim, Bet Taffuwa, Afeka, 54 Humta, Kiriyat Arba (wato Hebron), da Ziyor. Waɗannan su ne birane tara, tare da ƙauyukansu. 55 Mawon, Karmel, Zif, Yutta, 56 Yezriyel, Yokdiyam, Zanowa, 57 Kayin, Gibiya, da kuma Timna, Waɗannan su ne birane goma, tare da ƙauyukansu. 58 Halhul, Bet Zur, Gedor, 59 Ma'arat, Bet Anot, da kuma Eltekon. Waɗannan su ne birane shida, tare da ƙauyukansu. 60 Kiriyat Ba'al (wato Kiriyat Yeyarim), da kuma Rabba. Waɗannan su ne birane biyu, tare da ƙauyukansu. 61 A cikin jeji kuwa, akwai su Bet Arabah, Middin, Sekaka, 62 Nibshan, da Birnin Gishiri, da En Gedi. Waɗannan su ne birane shida, tare da ƙauyukansu. 63 Amma domin Yebusiyawa, mazaunan Yerusalem, kabilar Yahuda ba su iya korar su ba, don haka Yebusiyawa su ka yi zamansu tare da kabilar Yahuda har zuwa wannan ranar.

Sura 16

1 Ƙasar da aka ba kabilar Yosef ta kama tun daga Yodan har zuwa Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, zuwa daji, ta haura daga Yeriko zuwa ƙasar tuddun Betel. 2 Sai ta tafi zuwa Betel ta Luz ta kuma zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa. 3 Sai ta gangara yammacin karkarar Yafletiyawa, har can ƙarƙashin karkarar Bet Horon, ta kuma tafi har Gezer; ta ƙare a teku. 4 Ta wannan hanyar ce kabilun Yosef, da Manasse da kuma Ifraim su ka sami na su gãdon. 5 Karkarar kabilar Ifraim wadda aka ba iyalinsu ta kama kamar haka: iyakar gãdonsu a wajen gabas ta tafi zuwa Atarot Addar har can kwarin Bet Horon, 6 daga can ta cigaba har teku. Daga Mikmetat a arewa ta juya zuwa gabashin Ta'anat Shilo, ta kuma wuce gaba wajen gabas da Yanowa. 7 Sai ta tafi can har Yanowa zuwa Atarot ta kuma tafi Na'ara, ta kuma kai Yeriko, ƙarshen Yodan. 8 Daga Taffuwa iyakarta ta tafi yammacin rafin Kana ta kuma ƙare a teku. Wannan shi ne gãdon kabilar Ifraim, wadda aka ba iyalinsu, 9 tare da biranen da aka zaɓa don kabilar Ifraim a cikin gãdon kabilar Manasse - dukkan biranen, tare da ƙauyukansu. 10 Su ba su ƙore Kan'aniyawa waɗanda su ke zama a Gezer ba, saboda haka Kan'aniyawan da ke zama cikin Ifraim su na nan har wannan rana, amma waɗannan mutanen an sa su yin aikin dole.

Sura 17

1 Wannan it ce ƙasar da aka ba kabilar Manasse (wanda ya ke shi ne ɗan farin Yosef) - wato, Makir wanda ya ke ɗan farin Manasse shi ma kuma uban Giliyad. Zuriyar Makir an ba su ƙasar Giliyad da Bashan, domin Makir mutum ne jarumi a gun yaƙi. 2 Ƙasar an ba da ita ga sauran kabilar Manassa, an ba da ita ga iyalinsu -- Abiyeza, Helek, Asriyel, Shekem, Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne zuriyar maza na Manasse ɗan Yosef, bisa ga iyalinsu. 3 Yanzu Zelofehad ɗan Hefer ɗan Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse ba shi da 'ya'ya maza, amma sai 'ya'ya mata kaɗai. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, Noah, Hogla, Milka, da Tirza. 4 Sun zo wurin Eliyeza firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabanin, sun kuma ce, "Yahweh ya umarci Musa da ya ba mu gãdo tare da 'yanuwanmu maza." Saboda, bin umarnin Yahweh, ya ba waɗannan matan gãdo a cikin 'yan'uwansu maza na mahaifinsu. 5 Yanki goma na ƙasar da aka ba Manasse a Giliyad da Bashan, wanda ya na ɗaya gefen Yodan, 6 domin 'ya'ya mata na Manasse sun karɓi gãdonsu tare da 'ya'yansa maza. Ƙasar Giliyed an ba sauran kabilar Manasse. 7 Yankin ƙasar Manasse ya kai daga Ashar zuwa Mikmetat, wadda ta ke gabas da Shekem. Sai kuma iyakarta ta tafi kudu zuwa waɗanda su ke zama kusa da ruwan Taffuwa. 8 (Ƙasar Taffuwa ta ƙarƙashin Manasse, amma garin Taffuwa ya na kan iyakar Manassa ƙarƙashin kabilar Ifraim.) 9 Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan biranen kudu da rafin da ke cikin garuruwan Manasse su na ƙarƙashin Ifraim. Iyakar Manasse kuwa tana arewacin rafin, ta kuma ƙarashe a teku. 10 Ƙasar da ke kudu ta na ƙarƙashin Ifraim, kuma ƙasar da ke arewa ta Manasse ce; kuma teku ce ƙarshen iyakarta. A arewacin gefenta kuwa Ashar za a tarar, a kuma gabashinta, Issaka. 11 A cikin Issaka kuma da Ashar, Manasse ya sa mi Bet Shan da ƙauyukanta, Ibleyam da ƙauyukanta, mazaunan Dor da ƙauyukanta, mazaunan Endor da ƙauyukanta, mazaunanTa'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta, (da kuma sulusin birin Nafet). 12 Duk da haka kabilar Manasse ba su iya mallakar waɗannan biranen ba, domin Kan'aniyawa sun ci gaba da zama a wannan ƙasar. 13 Lokacin da mutanen Isra'ila su ka yi ƙarfi, sai su ka tilasta wa Kan'aniyawa su yi aikin dole, amma ba su kore su gaba ki ɗaya ba. 14 Sai zuriyar Yosef su ka ce da Yoshuwa, "Me ya sa ka ba mu ƙasa ɗaya kaɗai da kuma kashin gãdo ɗaya, da ya ke mu mutane masu yawa ne, duk da albarkar da Yahweh ya yi mana?" 15 Yoshuwa yace da su, "Idan ku babbar jama'a masu yawa ce, ku tafi can da kanku a jeji ku gyarawa kanku ƙasa acikin ƙasar Ferizziyawa da kuma Refayawa. Ku yi haka, a tuddan ƙasar Ifraim da ya ke ta yi ma ku kaɗan ainun. 16 Sai zuriyar Yosef su ka ce, "Ƙasar tuddai ba za ta ishe mu ba. Amma dukkan Kan'aniyawa da su ke zaune a kwarin su na da karusai na ƙarafa, dukkan waɗanda zaune a Bet Shan da ƙauyukanta, da kuma waɗanda ke zaune a kwarin Yezriyel." 17 Yoshuwa kuwa ya cewa gidan Yosef - wato Ifraim da Manasse, "Ku mutane ne masu girma da yawa, kuma ku na da iko da ƙarfi. Kada ku tsaya a kashin ƙasa ɗaya kaɗai da aka ba ku. 18 Ƙasar tuddai ma za ta zama taku. Ko da yake daji ne, ku gyara ta ku kuma mallake ta har iyakokinta masu nisa. Sai ku kore Kan'aniyawa daga cikinta, ko da ya ke su na da karusai na ƙarfe, kuma su na da ƙarfi ainun."

Sura 18

1 Sai dukkan taron jama'ar Isra'ila su ka taru a Shilo. A wurin su ka kafa rumfar taruwa sun ci nasara akan ƙasar dake gabansu. 2 Har yanzu akwai kabilu bakwai cikin mutanen Isra'ila waɗanda ba a ba su na su gãdon ba tukuna. 3 Yoshuwa ya ce da mutanen Isra'ila, "Har yaushe za ku ƙi tafiya cikin ƙasa wadda Yahweh, Allah na kakanninku ya ba ku? 4 Ku sanya wa kanku mutum uku daga kowacce kabila, kuma zan aike su waje. Za su fita su duba ƙasar tudu da gangare. Za su rubuta bayanin ta bisa ga gădon kowannensu, sa'an nan za su komo wuri na. 5 Za su raba ta kashi bakwai. Yahuda za su kasance cikin na su yanki wajen kudu, sai gidan Yosef kuma za su ci gaba da zama a yankin arewa. 6 Za ku kasa ƙasar kashi bakwai sa'annan ku kawo taswirar ƙasar wurina. Zan jefa ma ku ƙuri'u a nan gaban Yahweh Allahn mu. 7 Gama Lebiyawa ba su da gădo a cikin ku, gama aikin Lebiyanci na Yahweh shi ne rabon su. Gad, da Ruben da rabin ƙabilar Manasse sun karɓi gadon su a ƙetaren Yodan. Wannan shi ne gãdon da Musa bawan Yahweh ya ba su." 8 Sai mutanen su ka tashi su ka tafi. Yoshuwa ya umarci waɗan da su ka tafi domin su rubuta tsarin taswirar ƙasar, ya ce, "Ku tafi ku kai ku komo cikin ƙasar ku rubuta adadinta sa'annan ku komo wurina. Zan jefa ƙuri'u a nan domin ku a gaban Yahweh a Shilo." 9 Mutanen kuwa su ka tashi suka tafi cikin ƙasar tudu da gangare su ka rubuta bayanin yadda ƙasar take kashi bakwai bisa ga biranenta, sun tsara biranen da sashin sa. Daga nan suka dawo wurin Yoshuwa cikin sansani a Shilo. 10 Sai Yoshuwa ya jefa masu ƙuri'u a Shilo gaban Yahweh. A can ne Yoshuwa ya rabawa mutanen Isra'ila ƙasar, kowannesu aka bashi nasa rabon ƙasar. 11 ‌Ƙasar da aka ba kabilar Benyamin kowanne an ba su bisa ga iyalinsu. Yankin ƙasarsu tana tsakanin zuriyar Yahuda da zuriyar Yosef. 12 Ta ɓangaren arewa, iyakarsu ta fara daga Yodan. Iyakar ta hau wajen sashin arewacin Yeriko, daga nan ta hau zuwa wajen tudun ƙasar yamma. Can ta kai jejin Bet Aben. 13 Daga can iyakar ta wuce zuwa kudu sashen Luz (wato Betel ke nan). Iyakar kuwa ta gangara zuwa Atarot Addar, tabi ta tsaunin da ke kwance a kudancin Bet Horon. 14 Sai iyakar tabi ta wani sashi dabam: ta ɓangaren yamma ya juya wajen kudu, ta nufi wajen hayin dutse daga Bet Horon. Wannan iyakar ta ƙarasa a Kiriyet Baal (wato Kiriyet Yeyarim), birni wanda mallakar kabilar Yahuda ne. Wannan ta haɗa iyakar yammaci. 15 Iyaka ta wajen kudu ta fara daga wajen Kiriyat Yeyarim. Iyakar ta tafi daga nan zuwa Efron, zuwa maɓulɓular ruwayen Neftowa. 16 Sai iyakar ta gangaro ƙasa zuwa iyakar dutsen dake akasi da Kwarin Ben Hinom, wanda ke arewacin ƙarshen Kwarin Refayim. Daga nan ya gangara zuwa Kwarin Hinnom, kudancin gangaren Yebusiyawa ya nausa ƙasa zuwa En Rogel. 17 Ta juya wajen arewa, ta nufi wajen En Shemesh, daga nan kuma ta fita zuwa Gelilot, wanda ke akasi da mahayin Adumim. Daga nan sai ya gangara zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben. 18 Ya wuce zuwa arewa inda suke kafaɗa da Bet Arabah ta gangara zuwa Arabah. 19 Iyakar ta wuce arewa kafaɗa da Bet Hogla. Iyakar ta ƙarasa arewa wajen gaɓar Tekun Gishiri, ta ɓangaren kudu ta ƙare a Yodan. Iyaka ta kudu kenan. 20 Yodan kuwa ta kafa iyakarta ta ɓangaren gabas. Wannan shi ne gadon Kabilar Benyamin, an kuma ba kowannensu bi sa ga zuriyar su, iyaka bayan iyaka, a ko'ina. 21 Biranen kabilar Benyamin bisa ga iyalansu su ne; Yeriko, Bet Hogla, da Emek Keziz, 22 Bet Arabah, Zemarayim, Betel, 23 Abbim, Fara, Ofra, 24 Kefar Ammoni, Ofni da Geba. Birane goma sha biyu ne haɗe da ƙauyukansu. 25 Akwai kuma biranen Gibiyon, Ramah, 26 Birot, Mizfa, Kefira, Mozah, 27 Rekem, Irfil, Tarala, 28 Zela, Hayelef, Yebus, (wato Yerusalem ke nan) Gibiya da Kiriyat. Akwai birane goma sha hudu, duk da ƙauyukan su. Wannan shi ne gãdon Benyamin domin zuriyarsu.

Sura 19

1 Kaɗa ƙuri'u na biyu ta faɗa kan Simiyon aka ba su bisa ga zuriyarsu. Gãdonsu ya na tsakiyar gãdon kabilar Yahuda. 2 Su ka samu domin gãdonsu Biyasheba, Sheba, Modala, 3 Hazar Shuwal, Balal, Ezem, 4 Eltolad, Betul, da Hormah. 5 Simiyon kuma ya na da Ziklag, Bet Markabot, Hazar Susa, 6 Bet Lebayot, da Sharuhen, Waɗannan birane goma sha uku sun haɗa da ƙauyukansu. 7 Har yanzu Simiyon ya na da Ayin, Rimmon, Etar da Ashan. Birane huɗu kenan duk da ƙauyukansu. 8 Waɗannan tare da ƙauyaukan dake tare da biranen har zuwa Ba'alat Biya (ɗaya suke da Ramah cikin Negeb). Wannan shi ne gãdon ƙabilar Simiyon, wanda aka ba iyalinsu. 9 Daga cikin gãdon ƙabilar Simiyon aka sami wani sashin rabon kabilar Yahuda. Saboda rabon ƙasar da aka ba Yahuda ya yi masu yawa, ƙabilar Simiyon sun karɓi gădonsu daga cikin tsakiyar nasu rabo. 10 Kaɗa ƙuri'u na uku ya faɗa akan kabilar Zebulun, aka kuma ba da ita ga zuriyarsu. Iyakar gãdonsu ta fara daga Sarid. 11 Iyakar su ta hau wajen yammaci ta nufi Marala, ta kai Dabbeshet; ta malala zuwa rafin dake akasi da Yokneyam. 12 Daga Sarid iyakar ta karkato zuwa gabashi ta tafi zuwa iyakar Kislot Tabor. Daga nan ta fita zuwa Daberat ta hau zuwa Yafiya. 13 Daga can ta ratsa zuwa gabas har Gat Hefa, zuwa Et Kazin; ta sake fita zuwa Rimmon ta juya zuwa wajen Neya. 14 Iyakar ta karkato zuwa wajen arewa zuwa Hannaton ta ƙarasa a Kwarin Ifta El. 15 Wannan yankin ya hada da biranen Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem. Akwai birane goma sha biyu duk da ƙauyukansu. 16 Wannan shi ne gãdon ƙabilar Zebulun, wanda aka ba zuriyarsu - da birane duk da ƙauyukansu. 17 Kaɗa kuri'u na hudu ya faɗa kan Issaka, an ba su bisa ga zuriyarsu. 18 Iyakarsu ta haɗa da Yezriyel, Kesulot, Shunem, 19 Hafarayim, Shiyon da Anaharat. 20 Ya haɗa da Rabbit, Kishon, Ebez, 21 Remet, En Gannim, En Hadda da Bet Fazzez. 22 Iyakarsu takai Tabor, Shahazuma, da Bet Shemesh, ta ƙarasa a Yodan. Birane goma sha shida, duk da ƙauyukansu. 23 Wannan shi ne gãdon kabilar Issaka, wanda aka ba su bisa ga zuriyarsu - birane da ƙauyukansu. 24 Kaɗa Kuri'u na biyar ya faɗa kan kabilar Asha, aka kuma ba zuriyarsu. 25 Iyakarsu ta hada da Helkat, Hali, Beten, Akshaf, 26 Allammelek, Amad da Mishall. Daga yamma iyakar ta kai zuwa Karmel da Shiho Libnat. 27 Daga nan ta karkata zuwa gabas zuwa Bet Dagon sa'an nan ta tafi har Zebulun, zuwa Kwarin Ifta El, arewaci zuwa Bet Emek da Neyiyel. Taci gaba zuwa Kabul wajen arewa. 28 Daga nan tayi wajen Abdon, Rehob, Hammon da Kana har zuwa Babban Sidon. 29 Iyakar tayi kwana zuwa Ramah, zuwa birnin Taya mai ganuwa. Sai iyakar ta karkata zuwa Hosa ta ƙarasa a teku a yankin Akzib, 30 Umma, Afek, da Rehob. Akwai birane ashirin da biyu duk da ƙauyukansu. 31 Wannan shi ne gãdon kabilar Asha, an basu bisa ga zuriyarsu - birane da ƙauyukansu. 32 Kaɗa Kuri'u na shida ya faɗa kan Naftali, aka kuma ba zuriyarsu. 33 Iyakar ta fara daga oak a Za'ananim, zuwa Adami Nekeb da Yabneyel, zuwa Lakkum; ta ƙarasa a Yodan. 34 Iyakar ta karkata zuwa yammaci har Aznot Tabor ta nausa zuwa Hukkok; ta taɓa Zebulun daga kudanci ta kai Asha daga yamma da Yahuda daga gabas har Kogin Yodan. 35 Birane masu ganuwa sune Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret, 36 Adama, Ramah, Hazor, 37 Kedesh, Edirai da En Hazor. 38 Har yanzu akwai Yiron, Migdal El, Horem, Bet Anat da Bet Shemesh. Akwai birane goma sha tara, duk da ƙauyukansu. 39 Wannan shi ne gãdon kabilar Naftali wanda aka ba zuriyarsu biranensu duk da ƙauyukansu. 40 Kãɗa kuri'u na bakwai suka faɗa kan kabilar Dan an basu bisa ga zuriyarsu. 41 Iyakar rabon su ya haɗa da Zora, Estawol, Ir Shemesh, 42 Sha'alabbin, Aijalon da Itla. 43 Ta haɗa da Elon, Timna, Ekron, 44 Elteke, Gibbeton, Ba'alat, 45 Yehud, Bene Berak, Gat Rimmon. 46 Me Yarkon da Rakkon tare da iyaka a ƙetare daga Yoppa. 47 Lokacin da iyakar kabilar Dan ta ɓace masu, sai su ka kaiwa Leshem hari su ka yi yaƙi da su, suka ci su, su ka kashe kowanensu da kaifin takobi, suka kwashe mallakar su, suka zauna cikin ta. Suka sake ma Leshem suna zuwa Dan sunan kakansu. 48 Wannan shi ne gãdon kabilar Dan, an ba zuriyarsu - biranensu, da ƙauyukansu. 49 Bayan da suka gama rarraba ƙasar a matsayin gãdonsu, mutanen Isra'ila suka ɗauka daga cikin gãdonsu suka ba Yoshuwa ɗan Nun. 50 Bisa ga umarnin Yahweh suka bashi birnin daya roƙa, an bashi Timnat Sera cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim. Ya gina birni ya zauna ciki. 51 Waɗannan sune gãdon da Eliyeza firist, Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin kabilu na mutanen Isra'ila suka raba bisa ga ƙuri'a a Shiloh, a gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa. Da haka suka gama rarraba ƙasar.

Sura 20

1 Sai Yahweh yace da Yoshuwa. 2 "Kayi magana da mutanen Isra'ila, kace, 'Ka keɓe biranen mafaka wanda nayi magana da kai ta hannun Musa. 3 Kayi haka domin duk wanda ya kashe wani bada gangan ba zai iya zuwa can. Waɗannan birane za su zama wurin mafaka domin duk wanda ya nemi ɗaukar fansar jinin mutumin da aka kashe. 4 Zai ruga zuwa ɗaya daga cikin waɗannan biranen zai tsaya a ƙofar shiga birnin, zai bayyyana damuwarsa ga dattawan garin. Daga nan za su ɗauke shi zuwa cikin birni su bashi wuri domin ya zauna a cikinsu. 5 Idan wani daga cikin su ya zo domin ya yi ƙoƙarin ɗaukar fansar jinin wanda aka kashe, mutanen garin ba za su bada wanda ya yi kisan ga hukuma ba. Ba za su yi haka ba domin ba da gan - gan ne ya kashe maƙwabcinsa ba, kuma bashi da wata ƙiyayya game dashi a baya. 6 Dole ya zauna cikin birnin har lokacin da zai tsaya gaban jama'a domin hukunci, har lokacin mutuwar babban Firist mai aiki a kwanakin nan, daga nan sai shi wanda ya yi kisan bisa ga kuskure ya koma garinsu gidansa kuma, daga in da ya gudu."' 7 Sai Isra'ilawa suka zaɓi Kedesh cikin Galili, cikin ƙasar duwatsu ta Naftali, Shekem cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim da Kiriyet Arba (wato Hebron ke nan) cikin ƙasar duwatsu ta Yahuda. 8 Ƙetaren Yodan gabashin Yeriko, suka zaɓi Beza, cikin jeji bisa tudu daga kabilar Ruben; Ramot Giliyad, daga kabilar Gad; da Golan cikin Bashan, daga kabilar Manasse. 9 Waɗannan sune biranen da aka zaɓa domin dukkan mutanen Isra'ila da kuma baƙin dake zaune cikinsu, domin duk wanda ya kashe wani bada gan - gan ba zai iya rugawa don tsirar da ransa. Wannan mutum ba zai mutu ta hanun wanda yake son ɗaukar fansar jinin da aka zubar ba, har sai shi wanda ake zargin ya tsaya gaban taron jama'a.

Sura 21

1 Daga nan sai shugabanni na zuriyar Lebiyawa suka zo wurin Eliyeza firist, da Yoshuwa ɗan Nun da shugabanni na iyalan kakanninsu a tsakanin mutanen Isra'ila. 2 Sai suka yi magana da su a Shilo cikin ƙasar Kan'ana suka ce, "Yahweh ya umarta ta hannun Musa a ba mu birane mu zauna ciki, tare da makiyayarsu domin dabbobinmu." 3 Bisa ga umarnin Yahweh, mutanen Isra'ila suka ɗiba daga cikin gãdonsu na birane da makiyayarsu suka ba Lebiyawa. 4 Kaɗa kuri'u domin zuriyar Kohatawa ya bada wannan sakamako: Firistoci - zuriyar Haruna waɗanda su ke daga Lebiyawa - sun karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuda, daga kabilar Simiyon da kuma daga kabilar Benyamin. 5 Sauran zuriyar Kohatawa bisa ga kuri'u sun karɓi birane goma daga zuriyar kabilar Ifraim, Dan da rabin kabilar Manasse. 6 Mutanen zuriyar Gashon an basu, ta wurin kaɗa kuri'u birane goma sha uku daga zuriyar Issaka, Asha, Naftali da rabin kabilar Manasse cikin Bashan. 7 Mutanen da su ke daga zuriyar Merari sun karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ruben, Gad da Zebulun. 8 Don haka mutanen Isra'ila sun bada waɗannan birane, ga Lebiyawa ta wurin jefa kuri'u (duk da makiyayarsu) kamar yadda Yahweh ya umarta ta hannun Musa. 9 Daga kabilun Yahuda da Simiyon aka bada waɗannan birane da aka lisafta sunayensu a nan. 10 Waɗannan birane an bayar da su ga zuriyar Haruna, waɗanda su ke daga zuriyar Kohatawa waɗanda daga kabilar Lebi su ke. Waɗanda kaɗa ƙuri'un farko kansu ya faɗa. 11 Isra'ilawa sun basu Kiriyat Arba (Arba shi ne uban Anak), wato Hebron ke nan, cikin ƙasar duwatsu ta Yahuda, tare da makiyayar da ke kewaye da ita. 12 Amma gonakin da ke birane da ƙauyukansu an riga an ba Kaleb ɗan Yefunne, a matsayin mallakarsa. 13 Ga zuriyar Haruna firist sun bashi Hebron da makiyayarta, wanda shi ne birnin mafaka ga wanda ya kashe wani cikin kuskure da Libna duk da makiyayarta. 14 Yattir da makiyayarta da Eshtemowa da makiyayarta. 15 Suka kuma ba da Holon da makiyayarta, Debir da makiyayaarta, 16 Ayin da makiyayarta, Jutta da makiyayarta da Bet Shemesh da makiyayarta. Akwai birane tara da aka bayar daga cikin kabilun nan biyu. 17 Daga kabilar Benyamin an bada Gibiyon duk da makiyayarta, Geba da makiyayarta, 18 Anatot duk da makiyayarta, da Almon da kewayenta birane huɗu ke nan. 19 Biranen da aka ba firistoci zuriyar Haruna, dukkan su birane goma sha uku ne, haɗe da makiyayarsu. 20 Sauran Kohatawa - su Lebiyawan nan waɗanda su ke daga iyalin Kohat - sun sami nasu biranen daga kabilar Ifraim, ta wurin jefa kuri'u. 21 An basu Shekem duk da makiyayarsu cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure - Geza da makiyayarsu. 22 Kibzayim da makiyayarsu, da Bet Horon da makiyayarsu - birane huɗu ne dukka. 23 Daga kabilar Dan, zuriyar Kohat an ba su Eltike da makiyayarsu, Gibbeton da makiyayarsu. 24 Aijalon da makiyayarsu da Gat Rimmon da makiyayarsu - duka birane huɗu ne. 25 Daga rabin kabilar Manasse, zuriyar Kohat an basu Ta'anak tare da makiyayarsu da Gar Rimmon tare da makiyayarsu - birane biyu. 26 Akwai birane goma dukka domin sauran zuriyar Kohatawa, duk da makiyayarsu. 27 Daga rabin kabilar Manasse, zuwa zuriyar Gashon waɗannan sauran zuriyar Lebi ne, an bada Golan cikin Bashan tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai bisa ga kuskure, tare da Be Eshtera da makiyayarsu - birane biyu ne duka. 28 Ga zuriyar Gashon an basu Kishon daga kabilar Issaka, tare da makiyayarsu, Daberat tare da makiyayarsu, 29 Yarmut tare da makiyayarsu, da En Gannim tare da makiyayarsu.- birane hudu. 30 Daga kabilar Asha, sun bada Mishal tare da makiyayarsu, Abdon tare da makiyayarsu, 31 Helkat tare da makiyayarsu da Rehob tare da makiyayarsu - birane huɗu ne dukka. 32 Daga kabilar Naftali, sun ba zuriyar Gashon Kedesh cikin Galili tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure; Hammot Dor tare da makiyayarsu, da Kartan tare da makiyayarsu - birane uku ne duka. 33 Akwai birane goma sha uku duka, daga zuriyar Gashon, tare da makiyayarsu. 34 Ga sauran Lebiyawa - na zuriyar Merari - an ba su daga cikin kabilar Zebulun: Yokniyam tare da makiyayarsu, Karta tare da makyyayarsu, 35 Dimna tare da makiyayarsu, da Nahalal tare da makiyayarsu - dukka birane huɗu ke nan. 36 Ga zuriyar Merari an ba su daga kabilar Ruben: Bezer tare da makiyayarsu, Yahaz tare da makiyayayarsu, 37 Kedemot tare da makiyayarsu, da Mefa'at tare da makiyayarsu - birane huɗu. 38 Daga cikin kabilar Gad an ba su Ramot cikin Giliyad tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure - da Mahanayim tare da makiyayarsu. 39 Zuriyar Merari an ba su Heshbon tare da makiyayarsu, da Yazer tare da makiyayarsu. Waɗannan birane huɗu ne dukka. 40 Dukkan waɗannan birane ne na zuriyar Merari, waɗanda su ke daga kabilar Lebi - dukka birane goma sha biyun an ba su ne bisa ga kaɗa ƙuri'u. 41 Biranen Lebiyawa da aka ɗauka daga cikin tsakiyar mallakar Isra'ila sun kai birane arba'in da takwas, ya haɗa da wuraren kiwonsu. 42 Waɗannan birane kowanne ya haɗa da makiyayarsu da ke kewaye da su. Haka ya ke ga dukkan waɗannan birane. 43 Haka nan Yahweh ya ba da wannan dukkan ƙasa da ya rantse wa kakanninsu, Isra'ilawa su ka mallaketa, su ka zauna cikinta. 44 Yahweh ya ba su hutawa ta kowanne gefe, kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin maƙiyansu da zai yi nasara da su. Yahweh ya ba da dukkan abokan gabarsu cikin hannunsu. 45 Babu wani cikin dukkan alƙawura masu kyau da Yahweh ya furta a kan gidan Isra'ila da ya kasa cika. Dukkan su sun tabbata.

Sura 22

1 A wan can lokaci Yoshuwa ya kira Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse. 2 ya ce masu, "Kun yi dukkan abin da Musa bawan Yahweh ya umarce ku. Kunyi biyayya da muryata a kan dukkan abinda na umarce ku. 3 Baku yãshe da 'yan uwanku a yawan kwanakin nan ba, har ya zuwa wannan rana, kun kuma kiyaye umarnan Yahweh Allahn ku. 4 Yanzu Yahweh Allahnku ya ba da hutu ga "yan'uwanku, kamar yadda ya alƙawarta masu. Don haka ku juya ku tafi rumfunanku cikin ƙasar mallakarku, wadda Musa bawan Yahweh ya baku a ƙetaren Yodan. 5 Don haka sai ku kula sosai ku kiyaye dokoki da umarnai waɗanda Musa bawan Yahweh ya umarce ku, ku ƙaunaci Yahweh Allahnku. Kuyi tafiya cikin hanyoyinsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa kuyi masa sujada da dukkan zuciyarku da ranku." 6 Sai Yoshuwa ya albarkace su ya sallame su sai su ka koma rumfunansu. 7 Yanzu ga rabin kabilar Manasse Musa ya rigaya ya ba su gãdonsu cikin Bashan, amma ga ɗaya rabin Yoshuwa ya bada gãdo daga cikin na 'yan'uwansu a yammacin Yodan. Yoshuwa ya sallamesu zuwa rumfunansu; ya sa masu albarka, ya ce da su, 8 "Ku koma rumfunanku da kuɗi masu yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa da zinariya, da tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawan gaske. Ku raba ganimar abokan gabanku tare da 'yan'uwanku." 9 Sai zuriyar Ruben da zuriyar Gad, da rabin kabilar Manasse su ka koma gida, suka bar mutanen Isra'ila a Shilo, wadda ke cikin ƙasar Kan'ana. Sun tafi zuwa yankin ƙasar Giliyad, zuwa ƙasar su, wadda su da kansu su ka mallaka, cikin biyayya ga umarnin Yahweh, ta hannun Musa. 10 Sa'ad da suka zo Yodan wadda ke cikin ƙasar Kan'ana, sai Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse su ka gina bagadi kusa da Yodan, babban bagadi shahararre kuma. 11 Da mutanen Isra'ila suka ji labarin nan cewa, "Duba! mutanen Ruben da Gad da rabin kabilar Manasse sun gina bagadi a gaban ƙasar Kan'ana a Gelilot, a yankin da ke kusa da Yodan, a yankin da ke mallakar mutanen Isra'ila." 12 Da mutanen suka ji haka, sai dukkan mutanen Isra'ila suka taru a Shilo domin su je su yi yaƙi gãba da su. 13 Sai mutanen Isra'ila suka aiki 'yan saƙo ga su Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse, cikin ƙasar Giliyad. Sun kuma aiki Finehas ɗan Eliyeza, Firist. 14 Tare da shi kuma akwai shugabanni goma, ɗaya daga cikin kowacce kabilar Isra'ila, kuma kowannensu shugabane daga cikin zuriyar mutanen Isra'ila. 15 Suka zo wurin mutanen Ruben da Gad da rabin kabilar Manasse, cikin ƙasar Giliyad, suka yi magana da su: 16 "Dukkan taron jama'ar Yahweh sun faɗi haka, "Wanne irin rashin aminci ne wannan ku ka aikata gãba da Allah na Isra'ila, a wannan rana kun juya daga bin Yahweh kun ginawa kanku bagadi don ku tayarwa Yahweh? 17 Zunubinmu a Feyor bai ishe mu ba? Har yanzu bamu tsarkake kanmu daga gare shi ba. Saboda wannan zunubi annobai su ka abko wa jama'ar Yahweh. 18 Ko ya zama dole ne ku juya ga bin Yahweh a wannnan rana? Idan kuma ku ka yi wa Yahweh tayarwa yau, gobe zai yi fushi da dukkan taron jama'ar Isra'ila. 19 Idan ƙasar da ku ka mallaka ta ƙazantu, sai ku ƙetaro ƙasa inda mazaunin Yahweh ya ke zaune domin ku samar wa kanku mallaka daga cikin mu. Ku dai kada ku tayarwa Yahweh, ko ku tayar mana ta wurin gina wa kanku bagadi banda bagadin Yahweh Allahnmu. 20 Ko Akan ɗan Zera, bai yi laifin karya imani akan zancen waɗannan abubuwa da su ke keɓaɓɓu domin Allah ba? ko hasala ba ta afko wa mutanen Isra'ila ba? Wannan mutum bai mutu shi kaɗai domin laifinsa ba." 21 Daga nan sai kabilar Ruben Gad da rabin kabilar Mannasse suka amsa wa shugabannin zuriyar Isra'ila: 22 "Maigirman nan, Allah, Yahweh! Maigirman nan, Allah, Yahweh! - Ya sani, bari Isra'ila kanta kuma ta sani! Idan cikin tayaswa ne ko cikin saɓawa imani gãba da Yahweh, kada ka yi mana ceto yau 23 domin mun gina bagadi muka juya ga bin Yahweh. Idan mun gina wannan bagadi domin mu miƙa hadayun ƙonawa, hadayun gari, ko hadayun salama a kansa to bari Yahweh yasa mu biya. 24 A'a! Munyi shi cikin tsoro da nufin cewa a lokaci mai zuwa 'ya'yanku za su iya cewa da 'ya'yanmu, 'Ina ruwanku da Yahweh, Allah na Isra'ila? 25 Gama Yahweh ya sa Yodan ta zama iyaka tsakanin mu da ku. Ku mutanen Ruben da mutanen Gad, baku da abinda zaku yi da Yahweh.'Da haka 'ya'yan ku zasu iya sa 'ya'yan mu su dena yin sujada ga Yahweh. 26 Don haka sai mu ka ce, 'Bari yanzu mu gina bagadi, ba don ƙonannun hadayu ba ba kuma domin wasu hadayu ba, 27 amma domin zama shaida tsakanin mu da ku, da kuma don zuriya masu tasowa bayan mu, da kuma zamu bauta wa Yahweh a gaban sa, da ƙonannun hadayu da kuma hadayun mu tare da hadayun mu na salama, domin kada 'ya'yanku su ce da 'ya'yanmu a lokaci mai zuwa, "Baku da rabo cikin Yahweh."' 28 Sai mu ka ce, 'Idan zasu faɗi mana haka ko su faɗi wa zuriyarmu a lokaci mai zuwa, za mu ce, "Duba! wannan shi ne kwatancin bagadin Yahweh, wanda kakanninmu suka yi, ba domin ƙonannun hadayu ba, ba kuma don hadayu ba, amma domin shaida tsakanin mu da ku". 29 Bari tayaswa ga Yahweh ta yi nesa da mu, har yau mu juya daga bin sa ta wurin gina bagadi domin ƙonanniyar hadaya, domin hadaya ta gari, ko domin hadayar yanka, banda bagadin Yahweh Allahn mu wanda ke gaban mazamninsa."' 30 Sa'ad da Fenihas firist da shugabannin jama'a, wato shugabannin zuriyar Isra'ila waɗanda suke tare dashi, su ka ji kalmomin mutanen Ruben, Gad, da Manasse suka ce, wannan ya zama abu mai kyau a garesu. 31 Sai Fenihas ɗan Eliyeza firist ya ce da mutanen Ruben, Gad, da Manasse, "Yau mun sani cewa Yahweh yana tsakiyar mu, saboda baku aikata wannan saɓo gãba da shi ba. Yanzu kun ceci mutanen Isra'ila daga hannun Yahweh." 32 Daga nan sai Fenihas ɗan Eliyeza firist da shugabannin su ka juya su ka bar Rubenawa da Gadawa, suka bar ƙasar Giliyad, su ka koma ƙasar Kan'ana, zuwa ga mutanen Isra'ila, su ka dawo masu da magana. 33 Rahoton su ya gamshi mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka albarkaci Allah ba su ƙara maganar yaƙi da Rubenawa da Gadawa ba kan zancen hallaka ƙasar da su ke zaune a ciki. 34 Sai mutanen Ruben da Gadawa suka ba bagadi suna, "Shaida" gama suka ce, "Shaida ce tsakanin mu cewa Yahweh shi ne Allah."

Sura 23

1 Bayan kwanaki masu yawa, bayan da Yahweh ya bada hutu ga Isra'ila daga abokan gãbansu da ke kewaye da su, Yoshuwa kuma ya tsufa ƙwarai. 2 Sai Yoshuwa ya kira dukkan Isra'ila, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da manyansu - ya ce masu, "Ni na tsufa sosai. 3 Kunga dukkan abin da Yahweh Allahn ku ya yi da dukkan ƙasashen nan domin ku, domin Yahweh Allahn ku shi ne ya yi yaƙi domin ku. 4 Duba! Na sanya sauran al'umman da su ka rage a cisu su zama abin gãdo ga kabilun ku tare da dukkan ƙasashen dana rigaya na hallakar daga Yodan zuwa Babban Teku daga yamma. 5 Yahweh Allahnku zai kore su. Zai tuttura su daga gaban ku. Zai ƙwace ƙasar su, za ku mallaki ƙasar su, kamar yadda Yahweh ya alƙawarta ma ku. 6 Sai ku yi ƙarfafa sosai, ku kuma kiyaye dukkan abin da aka rubuta cikin shari'ar Musa kada ku kauce daga gare ta dama ko hagu, 7 domin kada ku yi cuɗanya da waɗannan al'ummai da su ka rage a cikin ku kada ma ku ambaci sunayen allolin su, ko ku rantse da su, ko ku yi masu sujada, ko ku russuna masu. 8 Maimakon haka; dole ku manne wa Yahweh Allahn ku kamar yadda ku ka yi zuwa wannan rana. 9 Gama Yahweh ya kori al'ummai da manya, masu ƙarfi daga gaban ku. Amma ku, ba mutumin da ya iya tsayawa a gaban ku har wa yau. 10 Kowanne mutum ɗaya daga cikinku za ya runtumi dubu, domin Yahweh Allahnku, shi ne ya ke yaƙi domin ku, kamar yadda ya alƙawarta maku. 11 Ku kula da kyau, domin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku. 12 Amma idan ku ka juya ku ka manne wa waɗannan sauran al'ummai waɗanda su ka rage a tsakiyar ku, ko idan ku ka yi auratayya da su, ko in ku ka yi huɗɗa tare da su su kuma tare da ku, 13 ku sani tabbas cewa Yahweh Allahnku ba zai ƙara korar waɗannan al'ummai daga gaban ku ba, maimakon haka, za su zama azargiya da tarko gareku, bulala a bayanku, ƙayayuwa cikin idanunku, har sai kun hallaka daga ƙasan nan mai kyau wadda Yahweh Allahnku ya baku. 14 Gashi yanzu ina kan tafiya hanya ta dukkan duniya, kuma kun sani da dukkan zukatanku da rayukanku, babu wata kalma data kasa zama gaskiya cikin dukkan abubuwa masu kyau da Yahweh Allahnku ya alƙawarta game da ku, dukkan waɗannan abubuwa sun tabbata game da ku, babu wani abu daya ka sa cika. 15 Ya zama kuwa kamar yadda kowacce maganar Yahweh Allahnku ya alƙawarta ma ku ta cika, Yahweh zai kawo ma ku dukkan miyagun abubuwa har sai ya hallakar da ku daga ƙasa mai kyau wadda Yahweh Allahnku ya baku. 16 Zai yi haka idan har kuka karya alƙawarin Yahweh Allahnku, wadda ya umarce ku ku kiyaye. Idan ku ka je ku ka yi sujada ga waɗansu alloli ku ka russuna masu, sa'annan fushin Yahweh zai yi ƙuna a kan ku, da sauri zaku hallaka daga ƙasa mai kyau wadda ya baku."

Sura 24

1 Sai Yoshuwa ya tara dukkan kabilun Isra'ila a shekem, ya kira dattawan Isra'ila, da shugabanninsu, da alƙalansu, da magabatansu, suka bayyana kan su gaban Allah. 2 Sai Yoshuwa ya cewa dukkan jama'a, "Wannan shi ne abinda Yahweh Allah na Isra'ila, ya ce, 'Kakanninku da daɗewa su ka zauna a ƙetaren kogin Yuferatis - Tera, mahaifin Ibrahim da mahaifin Naho - sun kuma yi sujada ga waɗansu alloli. 3 Amma na ɗauki mahaifinku zuwa ƙetaren Yuferitis na bishe shi cikin ƙasar Kan'ana na bashi zuriya masu yawa ta wurin ɗan sa Ishaku. 4 Ga Ishaku na bashi Yakubu da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar tudu ta Seyir domin ya mallaketa, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar. 5 Na aika masu Musa da Haruna, Na azabtar da Masarawa da annobai. Bayan haka, sai na fito da ku daga ciki, 6 Na fito da kakanninku daga Masar. Ku ka zo teku. Masarawa su ka bi su da karusai da mahayan dawakai har zuwa jan teku. 7 Sa'ad da kakannin ku su ka yi kira ga Yahweh, ya sa duhu tsakanin ku da Masarawa. Ya jawo teku a kan su ta rufe su. Kun ga abin da na yi cikin Masar. Da ga nan ku ka zauna kwanaki da yawa cikin jeji. 8 Na kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, waɗanda su ke zaune a ƙetaren Yodan. Sun yi yaƙi da ku, na kuma bashe su cikin hannun ku. Ku ka mallaki ƙasar su, kuma na hallakar da su a gabanku. 9 Sai Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya ta shi ya kai hari a Isra'ila. Ya aika a kira Balaam ɗan Beyor, ya la'antaku. 10 Amma ban saurari Balaam ba. Babu shakka, sai ya albarkaceku. Da haka na cece ku daga hannunsa. 11 Kuka haye Yodan ku ka zo Yeriko. Shugabannin Yeriko su ka yi yaƙi da ku, tare da Amoriyawa da Ferizziyawa da Kan'aniyawa, da Hittiyawa da Girgashiyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa na ba ku nasara a kansu na sa su ƙarƙashin mulkinku. 12 Na ku ma aike da zirnaƙo gabanku, ya kore su daga gabanku da sarakuna biyu na Amoriyawa daga gabanku, wannan bai faru ta wurin takobinku ko bakanku ba. 13 Na ba ku ƙasa wadda ba ku yi aikin kome ba da biranen da ba ku gina ba, yanzu ku na zaune a cikinsu. Ku na cin 'ya'yan kuringar inabi da na zaitun wanda ba ku ne ku ka dasa su ba.' 14 Yanzu fa sai ku ji tsoron Yahweh ku bauta masa da dukkan sahihanci da gaskiya; sai ku ƙi allolin da kakannin ku suka yi wa sujada a ƙetaren Yodan da cikin Masar, ku yi wa Yahweh sujada. 15 Idan a gare ku ba daidai bane a yi wa Yahweh sujada, ku zaɓa da kan ku yau wanda zaku bautawa, ko dai alloli waɗanda kakanninku su ka yi wa sujada na ƙetaren Yufiretes ko kuwa allolin Amoriyawa, waɗanda ku ke zaune cikin ƙasarsu. Amma ni da gidana, Yahweh za mu yi wa sujada." 16 Daga nan mutanen suka amsa suka ce, "Ba zamu taɓa yashe da Yahweh sa'annan mu bautawa wa su alloli ba, 17 gama Yahweh Allahnmu wanda ya fitar da mu da kakanninmu da ga ƙasar Masar, da ga gidan bauta, wanda ya aikata manyan al'ajibai a idanun mu, ya ku ma tsare mu cikin dukkan hanyar da mu ka bi, da ku ma cikin dukkan al'umman da mu ka ratsa ta tsakiyarsu. 18 Yahweh kuma ya kori dukkan mutane daga gabanmu, har da Amoriyawa da su ke zaune cikin ƙasar. Don haka mu ma zamu yi wa Yahweh sujada, gama shi ne Allahnmu." 19 Amma Yoshuwa ya cewa mutane, "Ba zaku bautawa Yahweh ba, gama shi Allah ne mai kishi; ba zai gafarta laifofinku ko zunubanku ba. 20 Idan ku ka yashe da Yahweh ku ka yi sujada ga baƙin alloli, daga nan zai juya ya azabtar da ku. Daga nan zai hallaka ku, bayan da ya riga ya kyautata ma ku." 21 Amma mutanen suka cewa Yoshuwa, "Sam, za mu yi sujada ga Yahweh." 22 Daga nan sai Yoshuwa ya ce ma mutanen, "Ku shaidu ne bisa kanku kun zaɓi Yahweh, ku yi masa sujada." Su ka ce, "Mu shaidune" 23 Yanzu ku kawar da baƙin allolin da ke tare da ku, ku juyo da zuciyarku ga Yahweh, Allah na Isra'ila." 24 Sai mutanen suka cewa Yoshuwa, "Za mu yi sujada ga Yahweh Allahnmu. Za mu saurari muryarsa." 25 Yoshuwa ya yi wa'adi tare ta mutanen a wannan rana. Ya shimfiɗa masu dokoki da farillai a Shekem. 26 Yoshuwa ya rubuta waɗannan maganganu cikin littafin shari'ar Allah. Ya ɗauki babban dutse ya kafa shi ƙarƙashin itacen oak da ke kusa da wuri mai tsarki na Yahweh. 27 Yoshuwa ya cewa dukkan mutanen, "Duba, wannan dutse zai zama shaida a kanmu. Gama ya ji dukkan maganganun da Yahweh ya ce da mu. Don ha ka zai zama shaida a kanku, Idan har ku yi musun Allahnku." 28 Sai Yoshuwa ya sallami mutanen, kowanne ya tafi wurin gãdonsa. 29 Bayan waɗannan abubuwa Yoshuwa ɗan Nun, bawan Yahweh, ya rasu, yana da shekaru 110. 30 Aka bizne shi cikin iyakar, gãdonsa a Timnat Sera, wadda ke cikin ƙasar tuddai ta Ifraim, arewacin Tsaunin Gaash. 31 Isra'ila su ka yi sujada ga Yahweh dukkan kwanakin Yoshuwa, da dukkan kwanakin dattawan da su ka kasance bayan Yoshuwa, waɗanda su ka san dukkan abin da Yahweh ya yi domin Isra'ila. 32 Ƙasusuwan Yosef, da mutanen Isra'ila suka ɗauko daga Masar - aka bizne su a Shekem, ciki yankin ƙasar da Yakubu ya sayo daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem. Ya saye ta a bakin azurfa ɗari, ta zama gãdon zuriyar Yosef. 33 Eliyeza ɗan Haruna shi ma ya mutu. Su ka bizne shi a Gibiya, a birnin Fenihas ɗansa, wanda aka bashi. Tana cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim.

Littafin Alƙalai
Littafin Alƙalai
Sura 1

1 Bayan mutuwar Yoshuwa, mutanen Isra'ila suka tambayi Yahweh cewa, "Wane ne zai fara kai wa kan'aniyawa hari domin mu, don yin faɗa da su?" 2 Sai Yahweh yace "Yahuda zai kai hari, Duba, na ba su iko a kan ƙasar." 3 Mutanen Yahuda suka ce da mutanen Simiyon, 'yan'uwansu, "Ku zo tare da mu a yankin da aka ɗebo mana don mu je tare mu yi yaƙi da Ka'aniyawa. Mu ma za mu je tare da ku a yankin da aka ɗiba maku". Sai kabilar Simiyon ta tafi tare da su. 4 Mutanen Yahuda suka kai hari kuma Yahweh ya ba su nasara a kan Ka'aniyawa, da Feriziyawa. Suka kashe masu mutum dubu goma a Bezek. 5 Suka sami Adoni-Bezek a Bazek, sai suka yi yaƙi da shi suka kuma cinye Kan'aniyawa da Feriziyawa a yaƙi. 6 Amma Adoni-Bezek ya gudu, sai suka fafare shi suka kamo shi suka yanke yatsunsa da tafin ƙafafunsa. 7 Adoni-Bezek yace "Sarakuna saba'in da aka yanke masu yatsunsu da tafin ƙafafunsu suna neman abincinsu a ƙarƙashin teburina. "Kamar yadda na yi haka nima Allah ya yi mani." Sai suka kawo shi Yerusalem, ya kuma mutu a can. 8 Mutanen Yahuda sun yaƙi birnin Yerusalem suka kuma ɗauke ta. Sun kai hari da kaifin takobi kuma suka banka wa garin wuta. 9 Bayan haka mutanen Yahuda suka je suyi faɗa da Ka'aniyawa da ke zaune a bisan tsibirin ƙasar, a cikin Negeb, da cikin tsibirin duwatsun yammacin. 10 Yahuda ya haura gãba da Ka'aniyawa da ke zaune a Hebiron (sunan Hebiron a dã shi ne Kiriyat Arba), suka kuma buge Sheshai, da Ahiman, da Talmaye. 11 Daga can sai mutanen Yahuda suka nausa gãba da mazaunan Debir (sunan Debir a dã shi ne Kiriyat Sefa). 12 Kalibu ya ce, "Duk wanda ya kai wa Kiriyat Sefa hari ya kuma ɗauke ta, Zan ba shi Aksa, ɗiyata, ta zama matarsa." 13 Otniyel ɗan Kenaz (ƙanin Kaleb) ya yi nasara a kan Debir, sai Kaleb ya ba shi Aksa, ɗiyarsa, ta zama matarsa. 14 Da sauri Aksa ta zo wurin Otniyel, sai ta iza shi ya sa mahaifinta ya bata fili. Da ta ke saukowa a kan jaki, Kaleb ya tambaye ta, "Mene ne zan yi maki?" 15 Ta ce da shi, "Ba ni albarka. Tun da ka ba ni ƙasar Negeb, ka kuma ba ni maɓulɓullan ruwa." Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓullan tudu da na fadama. 16 Zuriyar surukin Musa Bakenine sun hauro daga Birnin Dabino tare da mutanen Yahuda, zuwa ga tsibirin Yahuda, wanda ke cikin Negeb, su zauna tare da mutanen Yahuda kusa da Arad. 17 Mutanen Yahuda suka tafi tare da mutanen Simiyon 'yan'uwansu sai suka tunkari Kan'aniyawan da ke zaune a Zefat suka hallakar da su kakaf. Sunan birnin Hormah. 18 Mutanen Yahuda suka kuma kame Gaza da ƙasashen da ke kewaye da ita, Ashkelon da ƙasar da ke maƙwabtaka da ita, da kuma Ekron tare da ƙasar da ke kewaye da ita. 19 Yahweh na tare da mutanen Yahuda suka kuma ɗauki mallakar ƙasar kan tudu, amma ba su iya korar mazaunan ƙasar kan tudun ba don su masu karusan ƙarfe ne. 20 Hebron kuwa Kaleb aka baiwa (kamar yarda Musa yace), ya kuma kori 'ya'yan Anak uku daga wurin. 21 Amma mutanen Benyamin ba su kori Yebusiyawan da ke zaune a Yerusalem ba. Sai Yebusiyawan suka zauna tare da mutanen Benyamin a Yerusalem har ranar nan. 22 Gidan Yosef suka yi shirin kai wa Betel hari, kuma Yahweh na tare da su. 23 Suka aiki maza su leƙo asirin Betel (Birnin da dã ake kira Luz). 24 Masu leken asirin suka ga wani mutum na fitowa daga birnin, sai suka ce da shi, "In ka yarda, nuna mana yadda za a shiga cikin birnin nan, kuma za mu yi maka alheri." 25 Ya nuna masu hanyar zuwa cikin birnin, sai suka kai wa birnin hari da kaifin takobi, amma suka bar mutumin da dukkan iyalinsa suka kuɓuta. 26 Sai mutumin ya je ƙasar Hitiyawa ya gina wani birnin da ya kira shi Luz, shi ne kuwa sunansa har wa yau. 27 Mutanen Manasse ba su kori mutanen da ke zama a biranen Bet Shan da ƙauyukansu ba, ko Ta'anak da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Dor da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Ibilim da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Megiddo da ƙauyukansu ba, domin Ka'aniyawan sun bugi ƙirjinsu don zama a cikin ƙasar. 28 Da Isra'ila ta yi ƙarfi, suka tilasta wa Ka'aniyawa su yi masu bauta ta aiki mai tsanani, amma ba su taɓa korar su kakaf ba. 29 Ifraim bai kori Ka'aniyawan da suka zauna a Gezer ba, don haka Ka'aniyawa suka ci gaba da zama a Gezer a cikin su. 30 Zebulun bai tumɓuke mutanen da ke zama a Kitiron, ko mutanen da ke zama a Nahalol ba, saboda haka Ka'aniyawan suka ci gaba da zama a cikinsu, amma Zebulun ya tilasta wa Ka'aniyawan su bauta masu tare da aiki mai tsanani. 31 Asha bai tumɓuke mutanen da ke zama a Akko, ko mutanen da ke zama a Sidon, ko waɗanda ke zama a Alab, Akzib, Helba, Afek, ko Rehob ba. 32 Don haka kabilar Asha ta zauna cikin Ka'aniyawan (waɗanda ke zaune a ƙasar), saboda ba su kore su ba. 33 Kabilar Naftali ba su kori waɗanda ke zaune a Bet Shemesha, ko waɗanda ke zaune a Bet Anat ba. Don haka kabilar Naftali ta zauna cikin Ka'aniyawa (mutanen da tun asali ke zaune a ƙasar). Duk da haka, aka nawaita wa mazaunan Bet Shemesha da Bet Anata aikin bauta ga Naftali 34 Amoriyawa suka tilasta wa kabilar Dan su zauna a ƙasar kan tudu, ba su kuma ba su damar saukowa kwari ba. 35 Don haka Amoriyawa suka zauna a Tsaunin Heres, a Aijalon, da Sha'albim, amma ƙarfin mayaƙan gidan Yosef ya mamaye su, ya kuma sa aka tilasta masu su bauta masu da aiki mai tsanani. 36 Iyakar Amoriyawa ta kama daga tudun Akrabbim a Sela zuwa cikin ƙasar kan tudu.

Sura 2

1 Mala'ikan Yahweh ya taso daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, "Na fitar da ku daga Masar, na kuma kawo ku ƙasar da na yi rantsuwa zan ba kakaninku. Na ce 'ba zan taɓa karya alƙawarina da ku ba. 2 Ba za ku yi yarjejeniya da mazaunan garin nan ba. Wajibi ne ku rurrushe bagadansu.' Amma ba ku saurari muryata ba. Me kenan ku ka yi? 3 Yanzu sai na ce, 'ba zan kori Kan'aniyawa daga gare ku ba, amma za su zama ƙaya a gare ku, kuma allolinsu za su zama tarko a gare ku."' 4 A lokacin da mala'ikan Yahweh ya furta waɗannan kalmomin ga mutanen Isra'ila, sai suka yi kuka mai ƙarfi. 5 Suka kira wurin Bokim. A wurin suka miƙa hadayu ga Yahweh. 6 Sa'ad da Yoshuwa ya aike mutanen a hanyarsu, kowanne ɗaya daga mutanen Isra'ila kuwa kowa ya nufi wurin da aka sa shi don mallakar ƙasar. 7 Mutanen kuwa sun bauta wa Yahweh a zamanin Yoshuwa da kuma ta dattawan da suka bi bayansa, waɗanda suka ga dukkan abubuwa masu girma da Yahweh ya yi wa Isra'ila. 8 Yoshuwa ɗan Nun, bawan Yahweh, ya rasu yana da shekaru 110. 9 Aka kuwa binne shi a tsibirin ƙasar da aka ba shi ya mallaka a Timnat Heres, a tudun ƙasar Ifiraim, arewa da Tsaunin Ga'ash. 10 Dukkan wannan tsarar kuwa sun kasance tare da kakaninsu. bayansu sai wata tsara da ba ta san Yahweh ko abin da ya yi wa Isra'ila ba ta taso biye da su. 11 Mutanen Isra'ila kuwa sun yi mugun abu a fuskar Yahweh suka kuma bautawa Ba'aloli. 12 Sun kauce daga Yahweh, Allahn kakaninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar. Sun bi waɗansu alloli, wato allolin mutanen da ke kewaye da su, kuma sun rusuna ƙasa gare su. Suka sa Yahweh ya fusata domin 13 sun kauce daga Yahweh sun kuma yi wa Ba'al da Ashtoret sujada. 14 Fushin Yahweh ya taso wa Isra'ila, sai ya sa 'yan fashi suka ƙwace mallakarsu daga gare su. Ya maishe su barorin da ke ƙarƙashin ƙarfin maƙiyansu da ke kewaye da su, saboda haka ba su iya kare kansu daga maƙiyansu ba. 15 Duk inda Isra'ila su ka je faɗa, hanuwan Yahweh na gãba da su don a yi nasara da su, kamar dai yadda ya rantse masu kuma sun shiga ƙunci mai tsanani. 16 Sa'an nan Yahweh ya taso da Alƙalai, waɗanda su ka ceto su daga hanuwan masu satar mallakarsu. 17 Duk da haka ba su saurari alƙalansu ba. Suka zama marasa aminci ga Yahweh, suka kuma maida kansu kamar karuwai ga waɗansu alloli suka kuma yi masu sujada. Suka juya baya daga hanyar da kakaninsu suka yi rayuwarsu - waɗanda suka yi biyayya da umurnin Yahweh - amma su da kansu ba su yi haka ba. 18 A lokacin da Yahweh ya naɗa masu alƙalai, Yahweh ya taimaki alƙalan ya kuma ƙuɓutar da su daga hanuwan maƙiyansu a dukkan kwanakin alƙalan. Yahweh ya yi masu tagomashi yayin da suke nishi saboda waɗanda ke zalunta da kuma ƙuntata masu. 19 Amma sa'ad da alƙalan su ka mutu, sai suka juya baya suna yin miyagun abubuwan da suka fi waɗanda ma ubaninsu suka yi. Suka biɗi waɗansu alloli don su bauta masu su kuma yi masu sujada. Suka ƙi barin miyagun ayukansu ko taurin kansu. 20 Fushin Yahweh kuwa ya taso ma Isra'ila; ya ce "Saboda wannan al'umma ta karya sharuɗan alkawarina wanda na kafa domin ubaninsu-saboda ba su saurari muryata ba - 21 Daga yanzu ba zan korar masu ko ɗaya daga cikin al'umman da Yoshuwa ya rage kafin mutuwarsa ba. 22 Zan yi haka domin in gwada Isra'ila, ko za su yi biyayya da hanyar Yahweh da tafiya cikinta ko ba za su yi ba. Kamar yadda ubaninsu suka yi biyayya." 23 Shi ya sa Yahweh ya bar al'ummomin nan bai kuma kore su da sauri ya ba da su ga hannun Yoshuwa ba.

Sura 3

1 Yanzu kuwa Yahweh ya bar waɗannan ƙasashen domin ya gwada Isra'ila ne, wato duk wanda bai taɓa sanin yaƙe-yaƙen da Isra'ila ta yi da Kan'ana ba 2 (Ya yi wannan ne domin ya koyar da al'amarin yaƙi ga sabon zamanin Isra'ilawan da ba su san shi ba.) 3 Waɗannan su ne alu'mman: sarakuna biyar wato Filistiyawa da dukkan Kan'aniyawa da Sidoniyawa, da Hibitiyawa da ke zaune a duwatsun Lebanon, daga Tsaunin Ba'al Hermon zuwa Hamat Fass. 4 Waɗannan al'umman aka rage da manufar kasancewar hanyar da Yaahweh zai gwada Isra'ila, ko tabbas za su yi biyayya da dokokin da ya ba kakaninsu ta wurin Musa. 5 Mutanen Isra'ila kuwa sun yi zama a cikin Kan'aniyawa da Hitiyawa da Amoriyawa da Feriziyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa. 6 Suka ɗauki 'yammatansu su zama matayensu, haka kuma nasu 'yammatan suka bayar ga samarinsu, suka kuma bauta wa allolinsu. 7 Mutanen Isra'ila sun yi mugun abu a fuskar Yahweh kuma sun mance da Yahweh Allahnsu. Suka bauta wa gumakan Ba'al da Ashira. 8 Ta haka, fushin Yahweh mai zafi ya sauko wa Isra'ila, sai ya sayar da su ga hannun Kushan Rishata'imi sarkin Aram Naharayim. Mutanen Isra'ila kuwa sun bautawa Kushan Rishatayim shekaru takwas. 9 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya tayar da wani wanda zai taimaka wa mutanen Isra'ila, wanda kuma zai kuɓutar da su: Otniyel ɗan Kenaz (ƙanin Kaleb). 10 Ruhun Yahweh ya ƙarfafa shi, ya yi alƙalancin Isra'ila, ya kuma je yaƙi. Yahweh ya ba shi nasara a kan Kushan Rishatayim sarkin Aram. Hanuwan Otniyel ya ragargaza Kushan Rishatayim. 11 Ƙasar ta kasance da salama shekaru arba'in. Sai Otniyel ɗan Kenaz ya mutu. 12 Bayan haka, Isra'ilawa kuma sun yi mugun abu a fuskar Yahweh, sai Yahweh ya ba Eglon sarkin Mowab ƙarfin da zai mallaki Isra'ilawa. 13 Eglon ya haɗu da Amoniyawa da Amelikawa sai suka yi nasara da Isra'ila, suka kuma ɗauki mallakar Birnin Dabino. 14 Mutanen Isra'ila sun bauta wa Eglon sarkin Mowab shekaru goma sha takwas. 15 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya tayar da wani mai taimako wanda zai taimake su, Ehud ɗan Gera, na kabilar Benyamin, bahago ne shi. Mutanen Isra'ila sun aike shi, da kyautukkansu, zuwa ga Eglon sarkin Mowab. 16 Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai ƙaifi biyu, kamu guda a tsawo; ya yi ɗammara da ta a ƙarƙashin tufafinsa ta wajen cinyarsa ta dama. 17 Ya ba da kyautar ga sarki Eglon na Mowab. (Eglon kuwa mai ƙiba ne.) 18 Bayan Ehud ya gama miƙa kyautar, sai ya bar wurin tare da waɗanda suka ɗauke ta suka kai ciki. 19 Ehud da kansa kuwa, ko da yake, lokacin da ya iso wurin da ake yin siffofi kusa da Gilgal, sai ya juyo ya koma baya, sai ya ce, "Ina da saƙo a asirce domin ka, sarkina." Eglon yace, "Shiru" Sai dukkan waɗanda ke yi masa hidima suka bar ɗakin. 20 Ehud ya je wurin sa. Sarkin yana zaune da kansa, shi kaɗai a inuwar bene. Ehud yace, "Ina da saƙo daga Allah domin ka." Sarkin ya miƙe tsaye daga kujerarsa. 21 Ehud ya shigar da hannun hagunsa ya ɗauki takobin daga cinyarsa ta dama, sai ya cake jikin sarkin. 22 Ƙotar takobin kuma ta shige cikin jikinsa biye da wuƙar. Tsinin takobin ya fita ta bayansa kuma rufe da ƙitse, domin Ehud bai zaro takobin daga tumbinsa ba. 23 Sai Ehud ya fita daga shirayin ya kukkulle ƙofofin babban benen a bayansa. 24 Bayan Ehud ya tafi, barorin sarki suka zo; suka ga ƙofofin ɓenen a kulle, sai suka yi zaton, "Tabbas ya na hutawa a inuwar benen ne." 25 Suka yi ta ƙaruwa da kulawa har sai da suka ji lallai suna sakaci da aikinsu ne yayin da sarki fa bai buɗe ƙofofin babban benen ba. Sai suka ɗauki makullin suka buɗe, sai ga ubangijinsu a kwance, a ƙasa, matacce. 26 Yayin da barorin ke jira, suka rasa mema za su yi, Ehud kuwa ya tsere har ya wuce wurin da ake sassaƙa sifofin gumaka, sai ya tsere zuwa Se'ira. 27 Sa'ad da ya iso, sai ya busa kakaki a ƙasar tudu ta Ifraim. Sa'an nan mutanen Isra'ila suka je ƙasa tare da shi daga tuddai, kuma yana yi masu jagora. 28 Ya ce masu, "Ku biyo ni, gama Yahweh na gab da yin nasara da maƙiyanku, Mowabawa. "Suka bi shi suka kuma kama mashigin Yodan ƙetare zuwa Mowabawa, ba su kuma bar wani ya ƙetare kogin ba. 29 A lokacin nan ne suka kashe kusan dubu goma na mazajen Mowab, kuma dukkan su masu ƙarfi ne gwarzaye. Babu ko ɗayan da ya tsere. 30 Wato, a ranar nan ne Isra'ila ta mamaye Mowab da ƙarfinta, kuma ƙasar ta sami hutawa shekaru tamanin 31 Bayan Ehud, alƙali na biye shi ne Shamgar ɗan Anat wanda ya kashe maza 600 na Filistiyawa da tsabgar dabbobi. Ya kuma kuɓutar da Isra'ila daga hatsari.

Sura 4

1 Bayan da Ehud ya mutu, mutanen Isra'ila suka sake yin mugun abu a fuskar Yahweh. 2 Yahweh ya sayar da su ga hanun Yabin sarkin Kan'ana wanda ya yi mulki a Hazor. Babban shugaban rundunar sojojinsa shi ne Sisera, yana zaune a Haroshet Haggoyim. 3 Mutanen Isra'ila sun yi kira ga Yahweh domin taimako, saboda Sisera na da karusan ƙarfe guda ɗari tara ya kuma ƙuntata wa mutanen Isra'ila shekaru ashirin. 4 Debora kuwa, annabiya (matar Laffidot), tana jagoranci a matsayin mai sharia a Isra'ila a lokacin. 5 Ta kan zauna a ƙarƙashin itacen dabino na Debora tsaƙanin Ramah da Betel a tuddun ƙasar Ifraim, kuma mutanen Isra'ila na zuwa wurinta domin sassanta jayayya a tsakaninsu 6 Ta aika saƙo ga Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali. Ta ce masa, "Yahweh, Allahn Isra'ila, ya umarce ka, 'Jeka Tsaunin Tabor, tare da kai ka ɗauki maza dubu goma daga Naftali da Zabulun. 7 Zan ciro Sisera, shugaban rundunar sojojin Yabin, ya haɗu da kai a Kogin Kishon, tare da karusansa da sojojinsa, kuma Zan ba ka nasara a kansa." 8 Barak yace ma ta, "Idan za ki tafi tare da ni zan je, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ba za ni ba." 9 Ta ce, "Zan tafi tare da kai tabbas. Ko da yake, hanyar da ka ke tafiya ba za ta kai ka ga martaba ba, domin Yahweh zai sayar da Sisera ga hannun mace." Sai Debora ta tashi tsaye ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh. 10 Barak ya yi kira ga mazan Zebulun da Naftali su zo tare a Kedesh. Maza dubu goma suka bi shi, kuma Debora ta tafi tare da shi. 11 Haber kuwa (Bakeniye) ya raba kansa daga Keniyawa - su zuriyar Hobab ne (surukin Musa) - ya kuma kafa rumfarsa a gefen itacen al'ul a Za'ananim kusa da Kedesh 12 Sa'ad da suka faɗa wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya hauro Tsaunin Tabor, 13 Sisera ya kira dukkan karussansa, karussan ƙarfe ɗari tara, da dukkan sojojin da ke tare da shi, daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon. 14 Debora ta ce da Barak, "Jeka! Domin wannan ranar ce Yahweh ya ba ka nasara a kan Sisera. Ashe ba Yahweh ne ke jagorantakar ka ba?" Sai Barak ya je gangare daga Tsaunin Tabor tare da maza dubu goma biye da shi. 15 Yahweh ya sa sojojin Sisera su ruɗe, dukkan karusansa, da dukkan sojojinsa. Mazajen Barak suka faɗa masu har Sisera ya sauko daga karusa ya gudu da ƙafa. 16 Amma Barak ya runtumi karusan da sojojin zuwa Haroshet Haggoyim, sai aka kashe dukkan sojojin Sisera da kaifin takobi, kuma babu mutumin da ya tsira. 17 Amma Sisera ya ruga a guje da kafa zuwa rumfar Ya'el, matar Heber Bakenine, gama akwai salama tsakanin Yabin sarkin Hazor, da gidan Heber Bakenine. 18 Ya'el ta fito ta sadu da Sisera sai ta ce masa, juyo, ubangijina; juyo gare ni kar ka ji tsoro." Sai ya juyo gare ta ya zo wurinta cikin rumfarta, sai ta rufe shi da bargo. 19 Ya ce mata, "In kin yarda ki ba ni ruwa kaɗan in sha, don ina jin ƙishi." Ta buɗe jakar fata ta madara ta ba shi ya sha, sai ta sake rufe shi. 20 Ya ce mata, "Tsaya a ƙofar rumfar. Idan wani ya zo ya tambaye ki, 'akwai wani a nan ne?', ki ce 'A a'." 21 Sai Ya'el (matar Heber) ta ɗauki turken rumfar da guduma a hannunta ta je gunsa a asirce, gama ya na cikin zurfin barci, sai ta kafa turken rumfar ta ɗora guduma har ta soke gefen kansa zuwa ƙasa, har ya mutu. 22 Yayin da Barak ke fakon Sisera, Ya'el ta je ta tarye shi ta ce masa, "Zo, Zan nuna maka mutumin da ka ke nema." Sai ya je tare da ita, sai ga Sisera kwance matacce, tare da turken rumfar a gefen kansa. 23 Don haka a ranar nan Allah ya yi nasara da Yabin, sarkin Kan'ana, a idon mutanen Isra'ila. 24 Ƙarfin mutanen Isra'ila ya ƙaru sosai gãba da Yabin sarkin Kan'ana, har suka hallakar da shi.

Sura 5

1 A ranar nan ne Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa: 2 "Sa'ad da shugabanin suka ɗauki jagorancin Isra'ila, sa'ad da mutane cikin murna suka miƙa kai domin yaƙi - mu yabi Yahweh! 3 Ku saurara, ku sarakuna! Mai da hankali, ku shugabanni! Ni, Zan raira waƙa ga Yahweh, Allahn Isra'ila. 4 Yahweh, sa'ad da ka fito daga Se'ir, a sa'ad da ka tako daga Idom, ƙasa ta girgiza, kuma sammai sun yi makyarkyata; har giza-gizai sun zubo ruwa ƙasa. 5 Duwatsu na rawa a gaban Yahweh; har Tsaunin Sinai na rawa a gaban Yahweh, Allahn Isra'ila. 6 A kwanakin Shamgar (ɗan Anat), a kwanakin Ya'el, an ƙyale manyan hanyoyi, kuma waɗanda ke tafiya na yin amfani da ƙananan hanyoyin ne kurum. 7 Akwai jarumawa ƙaɗan ne a Isra'ila, har sai lokacin da ni Debora, na ɗauki matsayin shugabanci a Isra'ila - uwa ta ɗauki shugabancin a Isra'ila! 8 Sa'ad da suka zaɓi sababbin alloli, an yi faɗa a ƙofofin biranen amma duk da haka babu garkuwoyin yaƙi ko mãsu da aka gani a cikin mutum dubu arba'in a Isra'ila. 9 Zuciyata ta tafi ga shugabanin rundunar sojojin Isra'ila, tare da mutanen da a cikin murna suka miƙa kansu - mu yabi Yahweh domin su! 10 Yi tunani a kan wannan - ku masu hawan fararen jakuna kuna zaune a shinfiɗun ɗaurawa, da ku masu tafiya a hanyar. 11 Ji muryoyin waɗanda ke waƙa a cikin lambu. A wurin suke sake faɗin adalcin ayyukan Yahweh, da aikin adalcin jarumansa a Isra'ila. Sai mutanen suka sauko ƙasa zuwa ƙofofin birnin 12 Tashi, tashi, Debora! Tashi, tashi, ki raira waƙa! Tashi tsaye, Barak, ka kama 'yan kurkukunka, kai ɗan Abinowam. 13 Sai waɗanda suka tsira suka zo gun masu martaba; mutanen Yahweh suka zo gare ni tare da jarumawa. 14 Suka iso daga Ifraim, waɗanda asalinsu na Amalek ne; mutanen Benyamin sun bi ka. Daga Makir shugabanin yaƙi suka iso, daga Zebulun kuma waɗanda ke ɗauke da sandar hafsan. 15 Sarakunan da ke Issaka na tare da Debora; kuma Issaka na tare da Barak yana biye da shi da sauri har cikin kwari a bisa ga umurninsa. Cikin zuriyar Ruben ana ta nazari a zuci. 16 Me ya sa kuka zauna a tsaƙanin wuraren jin ɗumi, kuna sauraron makiyaya na wasa da sandunansu domin garkensu? Zuriyar Ruben dai suna ta nazari a zuci. 17 Giliyad ya tsaya a ƙeteren Yodan; kuma Dan, me ya sa yake ta zirgazirga a jiragen ruwa? Asha ya kasance a bakin teku ya kuma zauna kusa da babbar matsayar jiragen teku, 18 Zebulun kabila ce waɗanda suka sadaukar da rayukansu har ga mutuwa, har da Naftali ma, a filin yaƙi. 19 Sarakunan suka iso, suka yi faɗa; sarakunan Kan'ana suka yi faɗa a Ta'anak cikin ruwayen Megiddo, Amma ba su ɗauki azurfa a matsayin ganima ba. 20 Daga sammai, taurari suka yi faɗa, daga hanyoyinsu a ƙeteren sammai suka yi faɗa gãba da Sisera. 21 Kogin Kishon ya share su daga nan, wannan tsohon kogin, Kogin Kishon. Taka ya raina, ka yi ƙarfin hali! 22 Sai ƙarar kofaton dawakan - sukuwa, sukuwar jarumawansa. 23 'La'anta Meroz!' inji mala'ikan Yahweh. 'Tabbas la'anta mazaunanta! - saboda ba su zo sun taimake Yahweh ba - su taimaki Yahweh a yaƙi gãba da manyan jarumawa.' 24 An albarkaci Ya'el fiye da dukkan mata, Ya'el (matar Heber Bakenine), ita mai albarka ce fiye da dukkan matan da ke zama a rumfuna. 25 Mutumin ya biɗi ruwa, sai ta ba shi madara; ta kawo masa nono a akushin da ya cancanci a ba 'ya'yan sarki. 26 Ta sa hannunta a turken rumfa, da guduma a hannun damarta; da gudumar ta buge Sisera, ta ragargaza kansa. ta farfasa masa ƙwaƙwalwa sa'ad da ta soke shi ta gefen kansa. 27 Ya kasa tashi tsakanin tafinta, ya kwanta warwas a wurin. Tsakanin tafin kafafunta ya faɖi laƙwas. A wurin da ya ɓungire ne aka kashe shi ƙarfi da yaji. 28 Ta taga ta duba - mahaifiyar Sisera ta duba ta taga ta yi kira cikin baƙinciki, 'Me ya sa aka ɗauki tsawon lokaci karusansa basu iso ba? Me ya sa karar kofaton dawakan da ke jan karusansa suka yi jinkiri?' 29 Gimbiyoyinta masu hikima suka ba ta amsa, ita kuma ta ba kanta amsa irin tasu. 30 Ko basu samo ganima sun raba ba ne? - Mace, mata biyu domin kowanne mutum; ganimar kyawawan tufafi domin Sisera, tufafi masu tsada, kashi biyu na tufafi masu tsada domin wuyan waɗanda suka kwaso ganima? 31 Don haka bari dukkan maƙiyanka su lalace, Yahweh! Amma abokanka su zama kamar rana sa'ad da ta tashi a cikin ƙarfinta." Sai ƙasar ta sami salama shekaru arba'in.

Sura 6

1 Mutanen Isra'ila sun kuma yin abin da ke mugu a fuskar Yahweh, sai ya bada su ga hannun Midiyan na tsawon shekaru bakwai. 2 Ikon Midiyan ya ƙuntata wa Isra'ila. Saboda Midiyan, mutanen Isra'ila sun yi wa kansu mafaka a ramummuka a tuddai da kogonni da wuraren ɓoyewa. 3 Sai ya zamana a duk lokacin da Isra'ila suka shuka amfanin gona, sai Midiyanawa da Amelikawa da mutanen gabas su kai wa Isra'ila hari 4 Sukan sa mayaƙansu a ƙasar su lalatar da hatsi, har zuwa Gaza. Ba za su bar ko abinci a Isra'ila ba, ko tumaki, ko shanu, ko jakuna ba. 5 Sa'ad da suka iso da dabbobbinsu da rumfuna, sukan shigo kamar cincirundon fãri, kuma ya kan zama da wuya a ƙidaya mutanen ko raƙumansu, Sun farmaƙe ƙasar ne don su hallaka ta. 6 Midiyan sun rage ƙarfin Isra'ilawa ƙwarai har ya kai ga mutanen Isra'ila yin kira ga Yahweh. 7 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh saboda Midiyan, 8 Yahweh ya aiko annabi ga mutanen Isra'ila. Anabin ya ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh, Allahn Isra'ila ya faɗi: 'Na kawo ku daga Masar; Na fitar da ku daga gidan bauta. 9 Na kuɓutar da ku daga hannun Masarawa, daga kuma hannun dukkan waɗanda ke muzguna maku. Na kore su daga gare ku, na kuma ba ku ƙasarsu. 10 Na ce da ku, "Ni ne Yahweh Ahllahnku; Na Umurce ku kada ku bauta wa allolin Amoriyawa, waɗanda a cikin ƙasarsu ku ke." Amma ba ku yi biyayya da muryata ba,"' 11 Yanzu kuwa Malai'kan Yahweh ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen rimi a Ofra, wanda yake na Yowash (Ba'abiyezare), sa'ad da Gidiyon, ɗan Yowash, ke bugun alkama a masussuka, a wurin matsar ruwan inabi - don ya ɓoye shi daga Midiyanawa. 12 Mala'ikan Yahweh ya bayyana gare shi ya ce masa, "Yahweh na tare da kai, kai jarumi mai ƙarfi!" 13 Gidiyon yace masa, "Kash, ubangijina, idan Yahweh na tare da mu, me yasa dukkan waɗannan abubuwan suke faruwa da mu? Ina dukkan ayyukan al'ajibansa da ubaninmu suka labarta mana, sa'ad da suka ce, 'Ba Yahweh ba ne ya kawo mu daga can Masar ba? Amma yanzu Yahweh ya yashe mu ya bayar da mu ga hannun Midiyanawa." 14 Yahweh ya dube shi ya ce, "Jeka cikin ƙarfin da ka ke da shi. Ka kuɓutar da Isra'ila daga hannun Midiyan. Ko ban aike ka ba ne?" 15 Gidiyon yace masa, "In ka yarda Ubangiji, ta yaya zan kuɓutar da Isra'ila? Duba, iyalina su ne mafi rashin ƙarfi a Manasse, kuma ni ne mafi ƙarancin muhimmanci a gidan mahaifina." 16 Yahweh yace masa, "Zan kasance tare da kai, kuma za ka yi nasara da dukkan sojojin Midiyanawa kai kaɗai kuwa." 17 Gidiyon yace masa, "Idan kana farinciki da ni, ka ba ni allamar cewa kai ne ka ke magana da ni. 18 In ka yarda, kar ka bar nan, sai na zo gare ka na kawo kyautata na ajiye a gabanka." Yahweh ya ce, "Zan jira sai ka dawo." 19 Gidiyon kuwa ya je ya shirya ɗan'akuya ya kuma auna gari misalin mudu guda, ya yi gurasa mara yisti. Ya sa nama a kwando, ya kuma sa romon a tukunya ya kawo su gare shi a ƙarƙashin itacen rimi, sai ya miƙa su. 20 Mala'ikan Allah ya ce masa, "Ɗauki naman da gurasa mara yisti ka sa su a wannan dutsen, ka kuma zuba romon a bisan su." Haka kuwa Gidiyon ya yi. 21 Sai mala'ikan Yahweh ya miƙo kan sandar da ke hannunsa. Da ita ya taɓa naman da gurasa mara yisti; Wuta kuwa ta fito daga dutsen ta cinye naman da gurasar mara yisti. Sai mala'ikan Yahweh ya tafi Gidiyon kuma bai kara ganin shi ba. 22 Gidiyon ya fahimci cewa wannan mala'ikan Yahweh ne. Gidiyon yace, Ah! Ubangiji Yahweh! Gama na ga mala'ikan Yahweh fuska da fuska!" 23 Yahweh yace ma sa, Salama a gareka! Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba." 24 Sai Gidiyon ya gina bagadi a wurin domin Yahweh. Ya kira shi, "Yahweh salama ne." Har yau yana nan a Ofra ta iyalin Abiyeza. 25 A daren nan Yahweh yace masa, "Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da bijimi na biyu mai shekara bakwai, kuma ka rurushe bagadin mahaifinka, ka sare Ashera da ke kusa da shi. 26 Ka gina wa Yahweh Allahnka bagadi a kan wannan wurin fakewa, ka gina shi da kyau. Ka miƙa bijimi na biyu a matsayin hadaya ta ƙonawa, kana amfani da itacen Ashera da ka sare." 27 Sai Gidiyon ya ɗauki goma daga cikin barorinsa ya yi dai dai yadda Yahweh ya faɗa masa. Amma saboda tsananin tsoron iyalin gidan mahaifinsa da mutanen gari bai yi shi da rana ba sai da dare. 28 Da sassafe lokacin da mutanen gari suka tashi, an kakkarya bagadin Ba'al, Ashera da ke kusa da shi kuma an datse shi, bajimi na biyu kuma an miƙa shi hadaya a kan bagadin da aka gina. 29 Mutanen gari suka ce da junansu, "wa ya yi wannan abu?" Da suka yi magana da waɗansu suka nemi amsoshi, suka ce, "Gidiyon ɗan Yowash ne ya yi wannan abu." 30 Daga nan sai mutanen gari suka ce da Yowash, Ka fiito da ɗanka domin a kashe shi, saboda ya rushe bagadin Ba'al, ya kuma datse Ashera da ke gefensa." 31 Yowash yace da dukkan mutanen da ke jayayya da shi, "Za ku yi hamayya domin Ba'al ne? Za ku cece shi ne? Duk wanda ya yi hamayya dominsa, bari a kashe shi da safe, Idan Ba'al allah ne, bari ya kare kansa sa'ad da wani ya rushe bagadinsa." 32 Saboda haka a ranan nan suka kira Gidiyon "Yerub Ba'al," domin ya ce, "Bari Ba'al ya kare kansa," domin Gidiyon ya rushe bagadin Ba'al. 33 Yanzu dukkan Midiyanawa da Amelikawa da mutanen gabas suka taru wuri ɗaya. Suka ƙetare kogin Yodan suka kuma kafa sansaninsu a kwarin Yezriyel 34 Amma Ruhun Yahweh ya sauko wa Gidiyon. Gidiyon ya busa ƙaho, yana kiran zuriyar Abiyeza, ko za su bi shi. 35 Ya aiki 'yan saƙo ga dukkan Manasse, kuma suma an kirawo su su bi shi. Ya kuma aiko da 'yan saƙo ga Asha da Zebulun da Naftali, suka kuma fito su tarbe shi. 36 Gidiyon yace da Allah, "Idan ka yi niyar ka more ni don ka ceci Isra'ila, kamar yadda ka faɗa - 37 Duba, Zan shimfiɗa ƙyallen ulu a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan kyallen ulu kaɗai, amma ƙasa ta kasance a bushe, to zan sani cewa zaka more ni ka ceci Isra'ila kamar yadda ka ce." 38 Ga abin da ya faru - washegari Gidiyon ya tashi da sassafe, ya matse kyallen ulun wuri ɗaya, har ruwan raɓar daga kyallen ulun ya cika ƙwarya. 39 Sai Gidiyon yace da Allah, "Kada ka yi fushi da ni, Zan yi magana sau ɗaya kuma. In ka yarda ka bari in ƙara gwaji ɗaya kuma da ƙyallen ulun. Wannan karon, ka sa ƙyallen ulun ya bushe amma bari dukkan ƙasa ta kasance da raɓa. 40 Allah ya yi abin da ya roƙa a cikin daren nan. ƙyallen ulun ya bushe amma ƙasa ta kasance da raɓa kewaye da shi.

Sura 7

1 Sai Yerub Ba'al (wato Gidiyon) ya tashi da sassafe, da dukkan mutanen da ke tare da shi, sai suka yi sansani a gefen rafin Harod. Zangon Midiyan kuwa na ɓangaren arewa da su a kwari kusa da tuddun Moreh. 2 Yahweh yace da Gidiyon, "Ana da sojoji fiye da yadda nake so domin in ba ka nasara kan Midiyanawa, don kar Isra'ila ta yi taƙama a kaina, cewa, 'Ikonmu ne ya cece mu.' Yanzu kuwa, ka shaida a cikin kunuwan mutanen ka ce, 3 'Duk wanda ya ke jin tsoro, duk wanda ke rawar jiki, bari ya koma ya tashi daga Tsaunin Giliyad."' Sai mutane dubu ashirin da biyu suka tafi, dubu goma kuma suka rage. 4 Sai Yahweh yace da Gidiyon, "Mutanen sun yi yawa har yanzu, Kai su wurin ruwa, Ni kuma zan rage yawansu domin ka a wurin. Idan nace maka, 'Wannan zai tafi da kai,' zai tafi da kai; amma idan na ce, 'Wannan ba zai tafi da kai ba,' ba zai tafi ba." 5 Sai Gidiyon ya kawo mutanen wurin ruwan, Yahweh kuma ya ce masa, "Ware duk wanda ya lashi ruwan, kamar yadda kare ke lasa, daga waɗanda suka durƙusa ƙasa suka sha." 6 Mutum ɗari uku suka lasa. 7 Yahweh yace da Gidiyon, "Da mutum ɗari ukun da suka lashi ruwa, zan 'yantar da kai in ba ka nasara a kan Midiyanawa. Sai kowanne mutum ya koma wurinsa." 8 Saboda haka waɗanda aka zaɓa suka ɗauki kayayyakin aiki da kakakinsu. Gidiyon ya komar da mazan Isra'ila, kowanne zuwa rumfarsa, amma ya keɓe mutum ɗari uku. Midiyanawan kuwa sun yi zango a ƙasa da shi a cikin kwari. 9 A wannan daren Yahweh ya ce masa, "Tashi! ka kai wa sansanin hari, domin zan ba ka nasara a kansa. 10 Amma idan kana tsoron gangarawa kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka, 11 sai ka ji abin da suke faɗi, ƙarfin halinka kuma ya ƙarfafa har ka kai hari a sansanin." Sai Gidiyon ya tafi da Fura baransa, zuwa ƙofar sansanin. 12 Midiyanawa, da Amelikawa da dukkan mutanen gabas suka yi shiri a kwarin, yawansu kamar cincirindon fãra. Raƙumansu sun fi ƙarfin a ƙirga; sun fi yashin teku yawa. 13 Sa'ad da Gidiyon ya iso wurin, wani mutum ya na gaya wa abokinsa mafarkin da ya yi. Mutumin yace, "Duba! Na yi mafarki, sai na ga dunƙulen gurasar bali mai fuskar waina ta na gangarawa zuwa sansanin Midiyanawa. Ta iso rumfar, ta kuma buge ta da ƙarfi har sai da ta faɗi ta juyad da rumfar, ta kuma kwantar da ita ƙasa. 14 Sai ɗaya mutumin ya ce, "Wannan ba komai ba ne ban da takobin Gidiyon (ɗan Yowash), Ba'isra'ile. Allah ya ba shi nasara a kan Midiyan da dukkan sojojinsu." 15 Sa'ad da Gidiyon ya ji yadda aka sake faɗin mafarkin da fasararsa, ya russuna ƙasa ya yi sujada. Ya koma sansanin Isra'ila ya ce, "Ku tashi tsaye! Yahweh ya ba ku nasara a kan sojojin Midiyan." 16 Ya raba mutun ɗari uku kashi uku, sai ya ba dukkansu kakaki da gorunan da ba kome a ciki, sai cocila. 17 Ya ce masu, "Dube ni ku yi abin da na yi. Duba! Sa'ad da na iso gab da iyakar sansanin, dole ku yi abin da na yi. 18 Sa'ad da na busa kakaki, Ni da duk waɗanda ke tare da ni, sai ku busa naku kakakin har a dukkan gefen sansanin gaba ɗaya kuma ku yi ihu, 'Domin Yahweh da kuma domin Gidiyon!'" 19 Sai Gidiyon da mazaje ɗari uku waɗanda ke tare da shi suka iso gabashin sansanin, misalin ƙarfe goma na dare. Dai-dai lokacin da Midiyanawan na canjin masu gadi, suka busa kakaki suka kuma farfasa gorunan da ke hanuwansu 20 Rundunoni ukun suka busa kakaki suka kuma farfasa gorunan. Suka riƙe tociloli a hannayen hagunsu da kuma kakaki a hannayen damarsu don su busa su. suka yi ihu, "Takobin Yahweh da na Gidiyon." 21 Kowanne mutum ya tsaya a wurinsa a kewaye da sansanin sai dukkan sojojin Midiyanawa suka tsere suka yi ihu suka ruga a guje. 22 Sa'ad da suka busa kakaki ɗari ukun, Yahweh ya sa kowanne sojan Midiyanawa ya ɗauki takobi gãba da ɗan'uwansa da kuma gãba da dukkan sojojin. Sojojin suka tsere ta Bet Shitta har zuwa Zerera, harma ga iyakar Abel Mehola, kusa da Tabbat. 23 Aka kira mazajen Isra'ila daga Naftali da Asha, da dukkan Manasa, suka kuma fafari Midiyan. 24 Gidiyon ya aiki masu ba da saƙo a ko'ina a duk tuddun ƙasar Ifraim, cewa, "A gangara gãba da Midiyan a mamaye Kogin Yodan, har faɗin Bet Bara, a tsayar da su." Saboda haka dukkan mutanen Ifraim suka taru suka kuma mamaye ruwayen, har zuwa Bet Bara da Kogin Yodan. 25 Suka cafko 'ya'yan sarakuna biyu na Midiyan wato Oreb da Ze'eb. Suka kashe Oreb a dutsen Oreb, suka kuma kashe Ze'eb a wurin matsar ruwan Inabi ta Ze'eb. Suka bi bayan Midiyanawa, suka kuma taho da kawunan Oreb da Ze'eb ga Gidiyon, wanda ke a keteren Yodan.

Sura 8

1 Mutanen Ifraim suka ce da Gidiyon, "Mene ne wannan da ka yi mana? Ba ka kira mu ba sa'ad da ka tafi wurin faɗa da Midiyan." Daga nan sai suka yi gardama mai zafi da shi. 2 Sai ya ce da su, "Me na yi idan a ka kwatanta da ku?" Kalar inabin Ifraim, ba ta fi cikakken girbin inabin Abiyeza ba? 3 Allah ya ba ku nasara a kan 'ya'yan sarakunan Midiyan -- Oreb da Ze'eb! Wacce riba na ci idan an kwatanta da ku?" Sai fushinsu ya huce sa'ad da ya faɗi masu haka. 4 Gidiyon ya zo ya haye Yodan, shi da mutane ɗari uku da ke tare da shi. Sun gaji, amma duk da haka ba su fasa bi ba. 5 Ya ce da mutanen Sukkot, "Idan kun yarda ku ba mutanen da suka biyo ni dunƙulen gurasa, gama sun gaji, domin ina bin sawunsu Zeba da Zalmunna sarakunan Midiyan." 6 Sai shugabannin suka ce, "Hannuwan Ziba da Zalmunna suna hannunka ne a yanzu? Me zai sa mu ba sojojin ka gurasa?" 7 Gidiyon yace, "Idan Yahweh ya ba mu nasara a kan Zeba da Zalmunna, zan yayyaga maku fata da ƙayayuwan sahara da tsabgogi." 8 Ya wuce zuwa Feniyel ya yi magana ga mutanen can ma, mutanen Feniyel masu ka ba shi amsa dai-dai da ta mutanen Sukkot. 9 Shi kuma ya yi magana da mutanen Feniyel ya ce, "Idan na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiyar." 10 Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da sojansu, wajan mutum dubu goma sha biyar, dukkan waɗanda suka rage a sojojin mutanen Gabas, gama mutane 120,000 waɗanda a ka koyar a yaƙi da takobi sun faɗi. 11 Gidiyon ya yi gaba kan hanyar da mazauna rumfa, ya wuce Nabo da Yogbeha. Ya ci nasara a kan sojojin abokan gãba, da yake ba su yi zaton za a kawo masu hari ba. 12 Zeba da Zalmunna suka gudu, Gidiyon kuma ya bi su, ya kamo sarakunan Midiyan su biyu - Zeba da Zalmunna - ya sa sojojinsu cikin ruɗami. 13 Gidiyon ɗan Yowash ya dawo daga yaƙi, ya bi ta Heres. 14 Ya gamu da wani saurayi daga mutanen Sukkot, ya nemi shawara daga wurinsa. Shi kuma ya baiyana masa game da shugabannin Sukkot da dattawansu mutum saba'in da bakwai. 15 Gidiyon ya zo ya sami mutanen Sukkot, ya ce "Da su ga Zeba da Zalmunna, da ku ka yi mani ba'a a kansu cewa, ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ne?" Ba mu sani wai sai mun ba sojojinka gurasa ba. 16 Gidiyon ya ɗauki dattawan ya hori mutanen Sukkot da ƙayayuwa. 17 Ya rushe hasumiyar Feniyel ya kashe mutanen wannan birnin. 18 Sa'an nan Gidiyon yace da Zeba da Zalmuna, "Wadanne irin mazaje ku ka kashe a Tabor"? Suka amsa, "Kamar yadda ka ke haka su ke, kowannensu kamar ɗan sarki ya ke." 19 Gidiyon yace, 'Yan'uwana ne, 'ya'yan mamata ne. Muddin Yahweh na raye, da ba ku kashe su ba, ni ma da ba zan kashe ku ba." 20 Ya ce da Yeter (ɗansa na fari), "Tashi ka karkashe su!" Amma matashin bai zaro takobinsa ba, yana jin tsoro, saboda shi yaro ne. 21 Sai Zeba da Zalmunna suka ce, "Tashi ka kashe mu kai da kan ka! gama yadda mutum yake, haka ƙarfinsa yake." Gidiyon ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna, kuma ya ɗauke kayan adon da ke a wuyan raƙumansu. 22 Mutanen Isra'ila suka ce da Gidiyon, "Ka yi mulkin mu da kai - da 'ya'yanka da jikokinka,- saboda ka cece mu daga hannun Midiyan." 23 Gidiyon yace da su, "Ni ba zan mulke ku ba, ɗana kuma ba zai mulke ku ba. Yahweh ne zai yi mulkinku. 24 Gidiyon yace da su, "Zan roƙe ku: abu ɗaya, kowannenku ya ba ni ɗankunne daga abin da ya samu ganima." (Midiyanawa su na da 'yankunne na zinariya saboda su "ya'yan Isma'ila ne.) 25 Suka amsa suka ce, "Da farinciki za mu baka su". Suka yi shimfiɗa, kowannen su ya buɗe ganimarsa suka yi ta jefa 'yan kunnen a kan ta daga cikin ganima. 26 'Yankunnen da ya buƙata, nauyinsu shekel 1,700 na zinariya ne. Wannan ganimar ƙari ee a kan kayan adon sarakunan Midiyan wato tufafinsu na shunaiya. Da kuma sarƙoƙin da ake sawa a wuyan raƙumansu. 27 Gidiyon ya yi falmara da 'yankunnen da yakarɓa yasa a cikin birnisa, a Ofra, dukkan Isra'ila suka yi karuwanci ta wurin yi masa sujada a can. Wannan ya zama tarko ga Gidiyon da waɗanda ke cikin gidansa. 28 Mutanen Isra'ila suka mallake Midiyanawa, kuma basu ƙara tada kansu ba. Ƙasar ta zauna cikin salama shakara arba'in a cikin kwanakin Gidiyon. 29 Yerub Ba'al ɗan Yowash ye je ya zauna a cikin gidansa. 30 Gidiyon yana da 'ya'ya saba'in a zuriyarsa, da yake yana da mata da yawa. 31 Ƙwarƙwararsa wadda ke a Shekem ma ta haifa masa ɗa, Gidiyon kuma ya ba shi suna Abimelek. 32 Gidiyon ɗan Yowash ya mutu cikin shekarun tsufa masu kyau, aka bizne shi cikin kabarin Yowash ubansa, na kabilar Abiyeza. 33 Bayan mutuwar Gidiyon mutanen Isra'ila suka koma karuwanci ta wurin bautawa Ba'aloli, sun maida Ba'al Berit allahnsu. 34 Mutanen Isra'ila ba su tuna su girmama Yahweh Allahnsu ba, wanda ya kuɓutar da su daga hannun abokan gãbarsu ta kowanne gefe. 35 Ba su kiyaye alƙawuransu ga gidan Yerub Ba'al ba (wato Gidiyon), sakamakon dukkan abin kirki da ya yi a Isra'ila.

Sura 9

1 Abimelek ɗan Yarub Ba'al, ya tafi wajan 'yan'uwan mamarsa a Shekem, ya ce da su da dukkan dangin mamarsa, 2 "Idan ka yarda ka fadi wannan domin dukkan shugabannin Shekem su ji, 'Wanne ya fi a gare ku, dukkan 'ya'ya saba'in na Yerub Ba'al su yi mulki a kanku ko kuwa guda ɗaya ya mulke ku?' Ku tuna ni ƙashinku ne da jikinku." 3 Dangin mamarsa suka yiwa shugabannin Shekem magana a kansa, suka amince, gama suka ce, "Shi ɗan'uwanmu ne" 4 Suka ba shi azurfa guda saba'in daga gidan Ba'al Berit, Abimelek kuma ya yi anfani da ita ya gaiyato mutane marasa ɗa'a da rashin hankali suka yi tafiya tare da shi. 5 Abimelek ya tafi gidan ubansa a Ofra ya yi makokin 'yan'uwansa su saba'in, 'ya'yan Yerub Ba'al a bisa wani dutse. Yotam ƙaraminsu kaɗai ya rage cikin 'ya'yan Yerub Ba'al, gama ya ɓoye kansa. 6 Dukkan shugabannin Shekem da Bet Millo suka zo suka taru suka maida Abimelek ya zama sarki daura da rimi, kusa da ginshiƙi wanda ke cikin Shekem. 7 Sa'ad da Yotam ya ji haka, ya tafi ya tsaya a kan Tsaunin Gerizim. Ya tada murya ya ce da su, "Ku saurare ni, ku shugabannin Shekem, ko Allah ya ji ku. 8 Itatuwa suka je domin su naɗa sarki. Gama sun ce da itacen zaitun ka zama sarkinmu,' 9 Amma itacen zaitun yace da su, 'In dena ba da maina da ake anfani da shi ana girmama alloli da mutane, in kuma dawo wurin sauran itatuwa?' 10 Itatuwan suka ce da itacen ɓaure, 'Kazo ka yi mulkin mu,' 11 Amma itacen ɓaure yace da su, 'Zan bar zaƙina da 'ya'yana masu kyau, domin in dawo in dogara ga sauran itatuwa?' 12 Itatuwa suka ce da inabi, 'Kazo ka yi mulkin mu,' 13 Inabi ya cewa, 'Zan bar ba da sabon ruwan anab ɗina mai ƙarfafa alloli da mutane, in dawo in dogara ga sauran itatuwa?' 14 Sai dukkan itatuwa suka ce da ƙaya, 'Ki zo ki yi mulkin mu.' 15 Sai ƙaya ta ce da itatuwa, 'Idan gaskiya ne kuna so ku naɗa ni sarauniya a bisanku, sai kowannenku ya zo ya sami wuri a ƙarƙashin inuwata. Idan ba haka ba, bari wuta ta fito daga cikin ƙaya ta ƙone rimi na Lebanon. 16 To yanzu, idan dai gaskiya ne kun yi aminci, da kuka sa Abimelek ya zama sarkinku, idan kun yi abin da ya wajaba ga Yerub Ba'al da gidansa, kuma kun yi masa horon da ya kamata - 17 - da tunanin ubana ya yi faɗa dominba, ya sa ransa cikin hatsari ya kuɓutar da ku daga hannun Midiyan - 18 amma yau kun tashi gãba da gidan ubana, kun kashe 'ya'yansa saba'in a bisa dutse ɗaya. Sa'an nan kun maida Abimelek ɗan baiwarsa ya zama sarkin shugabanin Shekem, da yake shi ɗan'uwanku ne. 19 Idan dai kun yi gaskiya da girmamawa ga gidan Yerub Ba'al, to ku yi farinciki da Abimelek shi ma ya yi farinciki da ku. 20 Amma idan ba haka ba ne, bari wuta ta fito daga cikin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet Millo. Bari wuta ta fito daga mutanen Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek. 21 Yotam ya gudu ya tafi ya gudu ya tafi Biya. Ya zauna a can da ya ke nesa ta ke da Abimelek, ɗan'uwansa. 22 Abimelek ya yi mulkin Isra'ila shekaru uku. 23 Sai Yahweh ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da shugabannin Shekem. Shugabannin Shekem suka juyawa Abimelek baya. 24 Yahweh ya yi haka ne domin a rama muguntar da aka yi a kan 'ya'yan Yerub Ba'al su saba'in, aka kuma lissafta muguntar a kan Abimelek ɗan'uwansu. Haka kuma aka lissafta muguntar kisan a kan shugabannin Shekem saboda sun taya Abimelek ya kashe 'yan'uwansa maza. 25 Shugabannin Shekem suka sa mazaje su yi masa kwanton ɓauna, suka yiwa dukkan masu wucewa fashi a kan hanyar. Aka kaiwa Abimelek rahoton wannan abu. 26 Ga'al ɗan Ebed yazo shi da 'yan'uwansa suka je Shekem. Shugabannin Shekem kuwa sun amince da shi. 27 Suka je cikin gona suka kakkaryo kuringar anab domin su bi ta kai. Suka yi buki a gidan allahnsu, suka ci suka sha, suka la'anci Abimelek. 28 Ga'al ɗan Ebed ya ce, "Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub Ba'al ba ne? Zebul ba jami'in sa ba ne? Ya bautawa mutanen Hamor, uban Shekem! Me zai sa mu bautawa Abimelek? 29 Dama mutanen nan ƙarƙashi na suke! In fitar da Abimelek. In ce da Abimelek, 'Ka kira dukkan sojanka dukka.'" 30 Sa'ad da Zebul, jami'in birni, ya ji maganar Ga'al da Ebed, ya ji haushi sosai. 31 Ya aika da 'yan saƙo zuwa ga Abimelek domin ya ruɗe shi, cewa, "Duba, ga Ga'al ɗan Ebed da 'yan'uwansa suna zuwa Shekem, suna kuma zuga birnin gãba da kai. 32 Ka tashi idan dare ya yi, kai da sojojin da ke tare da kai ku yi masu kwanton ɓauna a cikin daji. 33 Da safiya ta yi, sa'ad da rana ta fito, ka shiga ka kaiwa birnin hari. Idan shi da mutanensa suka taso maka, ka yi masu abin da ka ga dama." 34 Abimelek ya tashi daddare, suka kasu huɗu suka yiwa Shekem kwanton ɓauna. 35 Ga'al ɗan Ebed ya tashi ya tsaya a ƙofar birni. Abimelek da mazajen da ke tare da shi suka fito daga inda suke a ɓoye. 36 Da Ga'al ya ga mazajen, ya ce da Zebul, "Duba ga mutane na gangarowa daga kan duwatsu!" Zebul ya ce da shi, "Kana ganin inuwoyi a kan duwatsu ne kamar mutane." 37 Ga'al ya ƙara cewa, "Duba mutane suna gangarowa daga tsakiyar ƙasa, wani kashi kuma na zuwa ta hanyar rimi na masu duba." 38 Sai Zebul ya ce da shi, "Ina maganarka ta fankama yanzu, 'Kai da ka ce wane ne Abimelek da zamu bauta masa?' Waɗannan ba su ne mazajen da ka rena ba? Ka fita yanzu ka yi faɗa da su." 39 Ga'al ya jagoranci mazajen Shekem, suka yi faɗa da Abimelek. 40 Abimelek ya kore shi, Ga'al ya gudu daga gabansa. Da yawa suka faɗi da raunuka kafin mashgin ƙofar birni. 41 Abimelek ya tsaya a Aruma, Zebul ya kori Ga'al da 'yan'uwansa daga cikin Shekem. 42 Washegari mutanen Shekem suka fita cikin jeji, a ka kaiwa Abimelek rahoton haka. 43 Ya ɗauki mazajensa ya raba su uku, su ka yi kwanton ɓauna a jeji. Ya ga mazajen suna fitowa daga cikin birni, ya kai masu hari ya kashe su. 44 Abimelek da ƙungiyoyin da ke tare da shi suka kai hari suka toshe ƙofar birni. Sauran kungiyoyi biyu suka kaiwa waɗanda ke cikin jeji suka kashe su. 45 Abimelek ya yi faɗa da birnin dukkan yini, ya ci birnin ya kashe mutanen da ke cikinsa. Ya rushe ganuwar birnin ya barbaɗa mata gishiri. 46 Sa'ad da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji, suka shiga babbar maɓoya ta gidan El-Berit. 47 Aka kaiwa Abimelek labari cewa dukan shugabannin sun taru a hasumiyar Shekem. 48 Abimelek tare da mazajen da ke tare shi suka hau Tsaunin Zalmon. Abimelek ya ɗauki gatari ya datso rassa. Ya ɗora a kafaɗarsa ya ummurci mazajen da ke tare da shi. "Abin da ku ka ga na yi, ku yi sauri kowa ya yi." 49 Haka kowannen su ya saro rassa suka bi Abimelek. Suka tara su jikin hasumiyar birni, suka sa wuta, dukkan mutanen da ke hasumiyar Shekem suka mutu, kusan su dubu maza da mata. 50 Sai Abimelek ya tafi Tebez, ya ya kafa sansani a Tebez ya mallake ta. 51 Amma akwai wata hasumiya mai karfi a birnin, dukan mazaje da mata suka shiga cikin ta suka kulle kansu. Sa'an nan sai suka hau can kan hasumiyar. 52 Abimelek yazo wurin hasumiyar da faɗa, ya zo kusa kofar domin ya ƙone ta. 53 Amma wata mace ta sako nuƙunyar dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa masa kwanya. 54 Nan da nan ya kira saurayin da ke ɗaukar masa kayan yaƙi ya ce masa, "Ka zaro takobinka ka kashe ni, domin kada a ce, 'mace ce ta kashe shi.'" Sai saurayin ya soke shi, ya mutu. 55 Sa'ad da mazajen Isra'ila suka ga Abimelek ya mutu, sai suka koma gida. 56 Yahweh ya ɗauki fansa a kan Abimelek saboda muguntar da ya yi ta kashe 'yan'uwansa su saba'in. 57 Yahweh ya mai da muguntar mutanen Shekem ta koma kan su, da la'anar Yotam ɗan Yerub Ba'al.

Sura 10

1 Bayan Abimelek, Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo, mutumin Issaka wanda ya zauna a Shamir, a ƙasar duwatsu ta Ifraim, ya taso domin ya ceci Isra'ila. 2 Ya alƙalanci Isra'ila shekara ashirin da uku. Ya mutu aka binne shi a Shamir. 3 Ya'ir Bagiliyade ya bi bayansa, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara ashirin da biyu. 4 Yana da 'ya'ya talatin, masu hawan jakuna talatin, suna da birane talatin, waɗanda a ke kira Habbot Ya'ir har zuwa yau, suna cikin ƙasar Giliyad. 5 Ya'ir ya mutu a ka binne shi a cikin Kamon. 6 Mutanen Isra'ila suka ƙara a kan muguntar da suka yi a idanun Yahweh, suka bautawa Ba'al, da Ashtoret allolin Aram, da allolin Sidon, da allolin Mowab da allolin mutanen Amon da allolin Filistiyawa. Suka watsar da Yahweh suka dena bauta masa. 7 Yahweh ya yi fushi da mutanen Isra'ila, ya sayar da su a hannun Filistiyawa da Amoniyawa. 8 Suka ragargaza Isra'ila suka gallaza masu azaba a wannan shekara, shekara goma sha takwas suna gallazawa mutanen Isra'ila waɗanda suke a ƙetaren Yodan a ƙasar Amoriyawa wadda ke cikin ƙasar Giliyad. 9 Sai Amoniyawa suka ƙetare Yodan garin su yi faɗa da Yahuda, da Benyamin da gidan Ifraim, domin a wulaƙanta Isra'ila. 10 Sa'an nan mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, suka ce, "Mun yi maka zunubi da yake mun watsar da kai mun bautawa Ba'al." 11 Yahweh yace da mutanen Isra'ila, "Ban ceto ku daga Masarawa da Amoriyawa da Amoniyawa da Filistiyawa 12 da kuma Sidoniyawa ba?" Amelikawa da Ma'oniyawa waɗanda suke gallaza maku; kuka kira ni na, ceto ku daga ikonsu. 13 Duk da haka kuka watsar da ni kuka bautawa waɗansu alloli. Saboda haka ba zan ƙara wani lokaci na ceton ku ba. 14 Ku tafi wurin allolin da ku ke bautawa. Sai su kuɓutar da ku idan kuna da damuwa." 15 Mutanen Isra'ila suka ce da Yahweh, "Mun yi zunubi. Ka yi mana abin da ya yi maka kyau. Sai dai idan ka yarda ka cece mu yau." 16 Suka rabu da baƙin allolin da ke tare da su, suka yi sujada ga Yahweh. Daga nan ne Yahweh bai ƙara riƙe damuwarsu ba. 17 Sa'an nan Amoniyawa suka taru suka kafa sansani a Giliyad. Isra'ilawa kuma suka taru suka kafa sansaninsu a Mizfa. 18 Shugabannin Giliyad suka ce da junansu, "Wane ne zai fara yin faɗa da Amoniyawa? Shi ne zai zama shugaba a kan dukkan mazauna Giliyad."

Sura 11

1 Sai ga Yafta mutumi Giliyad babban mayaƙi ne, amma ɗan karuwane. Giliyad ne ubansa. 2 Matar Giliyad ta haifa masa waɗansu 'ya'ya, sa'ad da suka yi girma sai suka kori Yafta daga gidan, suka ce masa, "Ba zaka gaji kome a iyalinmu ba. Kai ɗan wata mata ne." 3 Sai Yafta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya tafi ya zauna a ƙasar Tob. Mutane marar sa ɗa'a suka haɗu da Yafta, suka tafi tare da shi. 4 Bayan waɗansu kwanaki, mutanen Amon suka yi yaƙi da Isra'ila. 5 Sa'ad da mutanen Amon suka yi yaƙi da Isra'ila, sai shugabannin Giliyad suka je suka dawo da Yafta daga ƙasar Tob. 6 Suka ce da Yafta, "Zo ka zama shugabanmu domin mu yi faɗa da mutanen Amon." 7 Yafta yace da shugabannin Giliyad, "Kun ƙi ni kun kore ni daga gidan ubana. Me ya sa kuka zo wurina yanzu da kuka sami damuwa?" 8 Shugabannin Giliyad, suka ce da Yafta, "Shi yasa muka zo wurin ka yanzu, ka zo muje ka yi faɗa da mutanen Amon, za ka zama shugaba a kan dukan mazauna a Giliyad." 9 Yafta yace da Shugannin Giliyad, "Idan ku ka kawo ni gida domin in yi faɗa da mutanen Amon, idan Yahweh ya ba mu nasara a kan su, zan zama shugabanku." 10 Shugabannin Giliyad suka ce da Yafta, "Yahweh ya zama shaida tsakanin mu da kai idan ba mu yi yadda muka ce ba." 11 Sai Yafta ya tafi tare da shugabannin Giliyad, mutanen suka sa ya zama jagora da shugaban sojojinsu. Sa'ad da yake a gaban Yahweh a Mizfa, Yafta ya maimaita dukkan alƙawuran da ya yi. 12 Daga nan Yafta ya aika jakadu wurin sarkin mutanen Amom, cewa, "Wacce matsala ce tsakaninmu da ku? Me ya sa kuka zo ku ƙwace kasarmu? 13 Sarkin mutanen Amon ya amsa wa jakadun Yafta, "Saboda lokacin da Isra'ila suka fito daga Masar, sun ƙwace ƙasarmu daga Arnon zuwa Yabbok har zuwa Yodan. Yanzu ku maido mana da ƙasarmu cikin salama." 14 Yafta ya sake aikawa da jakadu wurin sarkin mutanen Amon, 15 ya ce, "Ga abin da Yafta ke cewa: Isra'ila ba su ɗauki ƙasar Mowab da ƙasar mutanen Amon ba, 16 amma Isra'ila sun fito daga Masar suka bi ta jeji zuwa Tekun Iwa zuwa Kadesh." 17 Sa'ad da Isra'ila suka aika jakadu zuwa sarkin Idom, cewa, 'Idan ka yarda ka bari mu wuce ta ƙasarka', amma sarkin Idom bai saurare su ba. Suka kuma aika da jakadu wurin sarkin Mowab, amma ya ƙi, sai Isra'ila suka tsaya a Kadesh. 18 Sai suka bi ta jeji su kewaye ƙasar Idom da ƙasar Mowab, sai suka bi ta gabas da ƙasar Mowab, suka raɓi ƙasar Arnon suka sauka. Amma ba su je yankin Mowab ba, da ya ke Arnon iyakar Mowab ce. 19 Isra'ila suka aika da jakadu wurin Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon; Isra'ila suka ce masa, 'Idan ka yarda ka bari mu bi ta ƙasarka mu je wurin da ke namu.' 20 Amma Sihon bai amince da Isra'ila su bi ta yankinsa ba. Sai Sihon ya tattara sojojinsa ya zakuɗa zuwa Jahaz, can ya yi faɗa da Isra'ila. 21 Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ba da Sihon da mutanensa a hannun Isra'ila suka yi nasara a kan su. Isra'ila suka mallaki ƙasar Amoriyawa waɗanda ke zaune a wannan, ƙasar. 22 Suka mallake komi da komi na ƙasar Amoriyawa tun daga Arnon har zuwa Yabbok, daga jeji kuma har zuwa Yodan. 23 Haka kuma Yahweh, Allah na Isra'ila ya kori Amoriyawa a gaban mutanen Isra'ila, ko yanzu kuma za ku mallake ƙasarsu? 24 Ba zaku mallaki ƙasar da Kemosh, allahnku yake ba ku ba? Domin haka duk ƙasar da Yahweh Allahnmu ya ba mu za mu mamaye ta. 25 Yanzu ka fi Balak ɗan Ziffo, sarkin Mowab ne? Ya taɓa yin jayayya da Isra'ila ne? Ya taɓa yin yaƙi da su ne? 26 Sa'ad da Isra'ila suka zauna a Hesbon da ƙauyukanta shekara dari uku, da Arowa da ƙauyukanta, da kan iyakokin Arnon - meyasa ba ka mallake su a wancan lokaci ba? 27 Ni ban yi maka laifi ba, kai ne ka yi mani laifi da ka kawo mani hari. Yahweh mai shari'a, yau zaya hukunta tsakanin mutanen Isra'ila da mutanen Amon." 28 Amma sarkin mutanen Amon ya yi ƙi gargaɗin da Yafta ya aika masa. 29 Sai Ruhun Yahweh ya sauko kan Yafta, ya ratsa ta Giliyad da Manasse, ya kuma ratsa ta Giliyad ɗin Mizfa, daga Giliyad ɗin Mizfa ya bi ta mutanen Amon. 30 Yafta ya yi alƙawari da Yahweh ya ce, "Idan ka ba ni nasara a kan mutanen Amon, idan na dawo cikin salama, 31 duk abin da ya fito daga ƙofofin gidana ya tarbe ni zai zama na Yahweh, zan miƙa shi hadaya." 32 To sai Yafta ya bi ta wurin mutanen Amon ya yi faɗa da su, Yahweh kuma ya ba shi nasara. 33 Yakai masu hari ya yi babban kisa tun daga Arowa har zuwa Minnit - birane ashirin - da zuwa Abel Keramim. Ta haka mutanen Amon suka zauna a ƙarƙashin mutanen Isra'ila. 34 Yafta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga ɗiyarsa ta fito tarbarsa da kayan kiɗi da rawa. Ita kaɗai ce ɗiyarsa, banda ita ba shi da wani ɗa ko ɗiya. 35 Da dai ya gan ta ya yage tufafinsa ya ce, "Haba ɗiyata! Kin sa ni nukura, kin sa mani jin zafi a raina! Gama nayi alƙawari ga Yahweh, ba zan iya janye alƙawarina ba. 36 Ta ce masa "Babana, Ka yi wa Yahweh alƙawari, ka yi mani ko mene ne ka yi wa Yahweh alƙawari gama Yahweh ya ɗaukar maka fansa a kan abokan gabarka, Amoniyawa. 37 "Ta cewa babanta, "Bari wannan alƙawari ya zauna a kaina, ka bani wata biyu da zan je kan duwatsu in yi kukan budurcina ni da ƙawayena." 38 Ya ce da ita. "Jeki." Ya bata wata biyu. Ta tafi, ta bar shi ta tafi ita da Ƙawayenta suka yi kukan budurci a cikin tuddai. 39 Bayan watanni biyun ta dawo wurin babanta, wanda da ita bisa ga alƙawari na wa'adi. Ita kuwa ba ta san namiji ba, wannan ya zama al'ada a cikin Isra'ila 40 'yan'matan Isra'ila kowacce shekara sukan ɗauki kwanaki huɗu, suna maimaita labarin ɗiyar Yafta Bagiliyade.

Sura 12

1 Kira ya zo ga mazajen Ifraim, suka bi ta Zafon suka ce da Yafta, "Meyasa ka wuce ka yi faɗa da mutanen Amon baka ce mu zo mu tafi tare da kai ba? Za mu ƙone gidanka a kan ka." 2 Yafta ya ce da su, "Ni da mutanena muna da babbar matsala da mutanen Amon. Sa'ad da na kira ku baku cece ni daga wurinsu ba." 3 Sa'ad da naga ba ku cece ni ba, sai na sa raina da ƙarfina na wuce gãba da su, kuma Yahweh ya ba ni nasara. Meyasa kuka zo ku yi faɗa da ni yau? 4 Yafta ya tattaro dukan mazajen Giliyad ya yi faɗa da Ifraim. Mazajen Giliyad suka kai hari ga mazajen Ifraim saboda sun ce, "Ku Giliyadawa masu gudu ne na cikin Ifraim - da Ifraim da cikin Manasse." 5 Giliyadawa suka kama magangarun Yodan masu kaiwa Ifraim. Idan wani wanda ya tsira na Ifraim ya zo yace, "Bari in haye kogin", sai mazajen Giliyad su ce da shi, "Kai Ba'ifrane ne?" Idan ya ce, "A'a," 6 sai su ce da shi ka ce, "Shibbolet," idan ya ce, "Sibbolet" (gama ba zai iya fadin kalmar dai-dai ba), Giliyadawa sai su kama shi su kashe shi a magangarun Yodan. Mutanen Ifraim dubu arba'in da biyu aka kashe a wannan lokacin. 7 Yafta ya yi alƙalanci a Isra'ila shekara shida. Sa'an nan Yafta ya mutu aka bizne shi a cikin ɗaya daga biranen Giliyad. 8 Bayan shi Ibzan na Betlehem ya yi alƙalancin Isra'ila. 9 Yana da 'ya'ya talatin. Ya aurar da 'ya'ya mata talatin, kuma ya kawo wa 'ya'yansa 'yan'mata talatin, daga waje. Ya yi alƙalancin Isra'ila shekara bakwai. 10 Ibzan ya mutu aka bizne shi a Betlehem. 11 Bayan shi Ilon mutumin Zebulun ya yi alƙalanci a Isra'ila, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara goma. 12 Ilon mutumin Zebulun ya mutu aka bizne shi a Aijalon cikin ƙasar Zebulun. 13 Bayan shi, Abdon ɗan Hillel Ba-firatone ya yi alƙalancin Isra'ila. 14 Yana da 'ya'ya arba'in da jikoki talatin. Suna hawan jakai saba'in, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara takwas. 15 Abdon dan Hillel Ba-firatone ya mutu aka bizne shi a Firaton cikin ƙasar Ifraim a ƙasar duwatsu ta Amelikawa.

Sura 13

1 Mutanen Isra'ila suka sake yin aikin mugunta a fuskar Yahweh, kuma ya bayar da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in. 2 Akwai wani mutumin Zorah, na iyalin Danawa, sunansa Manowa. Matarsa ba ta iya ɗaukar juna biyu saboda haka bata haihu ba. 3 Mala'ikan Yahweh ya baiyana ga matar ya ce da ita, "Duba, baki iya kin ɗauki juna biyu ba, kuma baki haihu ba, amma za ki sami juna biyu, za ki haifi ɗa. 4 Duba, kada ki sha ruwan inabi, kada ki ci abu marar tsarki. 5 Duba za ki sami juna biyu, za ki haifi ɗa. Ba za a yi anfani da reza a kansa ba, gama yaron zai zama Naziri ga Yahweh tun daga cikin ciki. Shi zaya fara kuɓutar da Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa." 6 Matar ta je ta gaya wa mijinta, "Wani mutumin Yahweh, ya zo wurina, kamanninsa kamar na mala'ikan Yahweh, da ban razana ƙwarai. Ban tambaye shi daga inda ya fito ba, kuma bai faɗa mani sunansa ba. 7 Ya ce da ni, "Duba! Za ki yi juna biyu za ki haifi ɗa. Kada ki sha ruwan inabi ko wani abin sha mai ƙarfi, kada ki ci abin da shari'a ta ce ba shi da tsarki, gama yaron zai zama Naziri ga Yahweh tun daga cikin ciki har ranar mutuwarsa." 8 Sai Manowa ya yi addu'a ga Yahweh, ya ce, "Ya Yahweh, idan ka yarda ka sake aiko da wannan mutum domin ya koya mana yadda za mu yi da yaron da za a haifa ba da daɗewa ba." 9 Yahweh ya saurari muryar Manowa, kuma sai mala'ikan Yahweh ya zo wurin matar lokacin da ta ke zaune a fili. Amma mijinta Manowa ba ya tare da ita. 10 Sai matar ta yi gudu da sauri ta gaya wa mijinta, "Duba! Mutumin ya baiyana gare ni, wanda ya zo wuri na waccan ranar!" 11 Manowa ya tashi ya bi matarsa. Sa'ad da ya zo wurin mutumin, ya ce, "Kai ne mutumin da ya yi magana da matata?" Mutumin yace, "Ni ne." 12 Sai Manowa yace, bari maganganunka su zama gaskiya. Mene ne zai zama ka'idodi game da yaron, kuma mene ne zai zama aikinsa?" 13 Mala'ikan Yahweh ya ce da Manowa, "Dole ta yi hankali ta yi dukan abin da na faɗa mata. 14 Kada ta ci kowanne abu da ya fito daga kuringa, kada ta sha ruwan inabi ko abin sha mai ƙarfi; kada ka bari ta ci kowanne abinci da shari'a ta ce ba shi da tsarki. Ta yi biyaiya da dukan abin da na ummurce ta ta yi." 15 Manowa yace da mala'ikan Yahweh, "Idan ka yarda ka ɗan jira, ka ba mu lokaci mu shirya maka 'yar burguma." 16 Sai mala'ikan Yahweh yace da Manowa, "Ko na tsaya ba zan ci abincinku ba. Idan kun shirya hadaya ta ƙonawa, ku miƙa ta ga Yahweh." (Manowa bai san cewa shi mala'ikan Yahweh ne ba.) 17 Manowa yace da mala'ikan Yahweh, "Mene ne sunanka, domin mu darajanta ka, idan kalmominka suka zama gaskiya?" 18 Mala'ikan Yahweh ya ce masa, "Meyasa ka ke tambayar sunana? Shi ne abin mamaki!" 19 Sai Manowa ya ɗauki 'yar akuya da baiko na hatsi ya miƙa su a dutsen Yahweh. Ya yi wani abin mamaki Manowa da matasa suna kallo. 20 Sa'ad da harshen wuta ya tashi sama daga bagadin, mala'ikan Yahweh ya tafi sama cikin harshen wuta na bagadin. Da ganin haka Manowa da matarsa suka faɗi da fuskokinsu a ƙasa. 21 Mala'ikan Yahweh bai ƙara baiyana ga Manowa ba ko matarsa. Sa'an nan ne Manowa ya sani mala'ikan Yahweh ne. 22 Manowa yace da matarsa, "Ba shakka za mu mutu da ya ke mun ga Yahweh!" 23 Matarsa ta ce da shi, "Da Yahweh ya so ya kashe mu, da bai karɓi baiko na ƙonawa da hatsin da muka ba shi ba. "Da bai nuna mana dukkan waɗannan abubuwan ba, ko ya bari mu ji waɗannan abubuwa a wannan lokaci." 24 Daga baya, matar ta haifi ɗa, aka kira sunansa Samsin. Yaron ya yi girma, Yahweh ya albarkace shi. 25 Ruhun Yahweh ya fara ƙarfafa shi a cikin Mahane Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

Sura 14

1 Samsin ya je Timna, a can ya ga wata mata, ɗiyar Filistiyawa. 2 Sa'ad da ya dawo ya ce da babansa da mamarsa, "Na ga wata mata a Timna, ɗaya daga cikin 'ya'yan Filistiyawa. Sai ku ɗauko mani ita ta zama mata ta." 3 Babansa da mamarsa suka ce da shi, "Ba wata mata a cikin 'ya'yan danginka, ko cikin dukkan mutanen mu?" Za ka ɗauko mata daga Filistiyawa marasa kaciya?" Samsin yace da babansa, "A ɗauko ta domi na, idan na dube ta, ta gamshe ni." 4 Amma babansa da mamarsa ba su sani ba wannan daga wurin Yahweh ne, domin ya yi shirin ƙulla husuma da Filistiyawa (gama a wannan lokaci Filistiyawa ne ke mulki a Isra'ila). 5 Samsin ya gangara zuwa Timna tare da babansa da mamarsa, suka zo gonakin Timnah. Sai ga wani ɗan zaki ya taso masa ya na ruri. 6 Ruhun Yahweh ya zo kansa ya yayyaga ɗan zakin kamar ɗan akuya, kuma ba komi a hannunsa. Amma bai gaya wa babansa ko mamarsa abin da ya yi ba. 7 Ya je ya yi magana da matar, sa'ad da ya dube ta ta gamshi Samson. 8 Bayan 'yan kwanaki da ya dawo ya aure ta, ya juya ya dubi gawar zakin. Sai ga kututun zuma a cikin abin da ya rage na gawar zakin. 9 Ya yagi zuman ya tafi, yana tafiya ya na ci. Ya zo wurin babansa da mamarsa ya ba su su ma suka ci. Amma bai gaya masu ya samo zuman daga abin da ya rage na jikin gawar zakin ba ne. 10 Baban Samsin ya je wurin da matar ta ke, Samson ya yi buki a wurin gama wannan ita ce al'adar samarin. 11 Da dai danginta suka gan shi suka kawo masa abokai talatin su zauna tare da shi. 12 Samsin ya ce masu, "Bari in gaya maku wani karin magana. Idan wani a cikin ku ya gaya ma ni ma'anarsa cikin kwanakin nan bakwai na biki, zan ba da rigunan lilin guda talatin da suturu guda talatin. 13 Amma idan ba ku iya ba ni amsa ba, za ku ba ni rigunan lilin talatin da suturu guda talatin. Suka ce da shi, "Ka faɗa mana karin maganarka mu ji." 14 Ya ce da su, "A cikin maciyi, akwai abin da za a ci; a cikin mai ƙarfi akwai abu mai zaƙi." Amma baƙinsa ba su iya gano amsar cikin kwana uku ba. 15 A kan rana ta huɗu suka ce da matar Samsin, "Ki zolayi mijinki domin ya gaya mana amsar karin maganar, ko kuma mu ƙone gidan mahaifinki. Kin gaiyato mu nan ne domin ki mai da mu marasa anfani?" 16 Matar Samsin ta fara yin kuka a gabansa ta ce, "Dukkan abin da ka ke yi ƙi na! Ka ke yi ba ka ƙauna ta. Ka gaya wa waɗansu mutanena karin magana, amma ba ka gaya mani amsar ba." Samsin yace da ita, "Duba nan, abin da ban gaya wa babana ko mamata ba, sai in gaya maki?" 17 Dukkan kwanakin nan bakwai na buki ita tana ta kuka. Ta matsa masa ƙwarai, a rana ta bakwai ya gaya mata amsar. Ita kuma ta gayawa dangin mutanenta amsar. 18 A rana ta bakwai kafin rana ta faɗi, mazajen garin suka ce da shi, "Me ya fi zuma zaƙi? Me ya fi zaki ƙarfi? Samsin yace da su, "Da ba domin kun yi huɗa da karsanata ba, da ba ku gano amsar karin maganata ba." 19 Sai Ruhun Yahweh ya zo kan Samsin da iko. Samsin ya je Ashkelon ya kashe mazajen su guda talatin. Ya kwashe ganimarsu, ya bada tufafinsu ga waɗanda suka baiyana masa karin zaurancensa. Ya tafi gidan ubansa cikin fushi mai zafi. 20 Aka bada matar Samsin ga babban abokinsa.

Sura 15

1 Bayan waɗansu kwanaki, a lokacin girbin alkama, sai Samsin ya ɗauki 'yar akuya ya tafi domin ya ziyarci matarsa. Ya ce a ransa, "Zan shiga ɗakin matata." Amma mahaifinta bai bar shi ya shiga ba. 2 Sai mahaifinta yace, "Tabbas na zaci ka ƙi jininta, sai na bayar da ita ga abokinka. Ai ƙanwarta ta fi ta kyau, ko kuwa? Sai ka ɗauke ta a maimakonta." 3 Samsin yace masu, "Wannan karon ba ni da hakkin Filistiyawa duk zafin da zan sa masu game da wannan al'amari." 4 Samsin ya tafi ya kamo diloli ɗari uku ya ɗaura su biyu-biyu, bindi da bindi. Sai ya ɗauko gaushen wuta ya ɗaɗɗaura a tsakiyar kowanne ɗaurin bindi biyu. 5 Da ya kunnawa gaushen wuta, sai ya tura dilolin cikin hatsin Filistiyawa, suka cinnawa hatsin wuta duk da zangarniyar da ke cikin gonakin, duk da Inabinsu garka-garka da lambunan zaitun. 6 Filistiyawa kuwa suka yi tambaya, "Wane ne ya yi wannan?" Aka gaya masu, "Samsin ne, surukin Batimne ya yi haka, domin Batimnen ya ɗauki matar Samsin ya ba abokinsa." Sai Filistiyawan suka tafi suka ƙone ta tare da mahaifinta. 7 Samsin yace masu, "Idan haka ku ka yi, zan ɗauki ramuwata a kanku, bayan haka ya faru, zan dakata." 8 Sai ya datsa su gunduwa-gunduwa, kwankwaso da cinya, da babbar gunduwa. Sai ya gangara ya tafi ya zauna cikin kogon dutsen Itam. 9 Sai Filistiyawa suka fito da shirin yaƙi cikin Yahuda suka kuma jera sojojinsu a Lehi. 10 Mutanen Yahuda suka ce, "Mene ne ya sa ku ka fito ku kawo mana hari?" Suka ce, "Mun kawo hari ne domin mu kama Samsin, kuma mu yi masa yadda ya yi mana." 11 Sai mutanen Yahuda su dubu uku suka tafi suka gangara kogon dutsen Itam, suka kuma cewa Samsin, "Ba ka san cewa Filistiyawa ne ke mulkinmu ba? Mene ne ka yi mana haka?" Samsin yace masu, "Sun yi mani, saboda haka nima na yi masu." 12 Suka cewa Samsin, "Mun gangaro ne domin mu ɗaure ka kuma mu miƙa ka cikin hannun Filistiyawa." Samsin yace masu, "Ku rantse mani cewa ku da kanku ba za ku kashe ni ba." 13 Suka ce masa, "A a, zamu ɗaure ka ne kawai da igiyoyi kuma mu miƙa ka gare su. Mun yi alƙawari ba za mu kashe ka ba." Daga nan suka ɗaure shi da sabbin igiyoyi biyu suka fito da shi daga dutsen. 14 Da ya zo Lehi, Filistiyawa suka fito da Ihu yayin da suke zuwa su gamu da shi. Sai Ruhun Yahweh ya sauko kansa da iko. Sai igiyoyin da ke bisa hannuwansa suka zama kamar ƙonannar ciyawa, suka kuma zube daga hannuwansa. 15 Sai Samsin ya samo sabon ƙashin muƙamuƙin jaki, ya ɗauko ya kuma kashe mutane dubu da shi. 16 Samsin yace, "Da ƙashin muƙamuƙin jaki, tari bisa tari, da ƙashin muƙamuƙin jaki na kashe mutane dubu." 17 Da Samsin ya gama magana, sai ya jefar da ƙashin muƙamuƙin jakin, sai ya kira wurin da suna Ramat Lehi. 18 Samsin ya ji ƙishi sosai sai ya yi kira ga Yahweh ya ce, "Ka bayar da nasara mai girma ga bawanka. Amma yanzu zan mutu da ƙishi ne kuma in faɗa cikin hannuwan waɗancan marasa kaciyar?" 19 Sai Allah ya tsaga cikin sararin da ke Lehi sai ruwa ya ɓulɓulo. Da ya sha, sai karfinsa ya dawo kuma ya farfaɗo. Saboda haka ya kira sunan wannan wuri En Hakkori, kuma yana nan a Lehi har yau. 20 Samsin ya yi alƙalancin Isra'ilawa a zamanin Filistiyawa har shekaru ashirin.

Sura 16

1 Samsin ya tafi Gaza sai ya ga karuwa a can, sai kuwa ya kwana da ita. 2 Aka faɗa wa Gazawa, "Samsin ya shigo nan fa." Gazawa suka kewaye wurin a asirce, suka yi masa kwanto tsawon dare a ƙofar birnin. Suka yi tsit dukkan tsawon daren. Sun riga sun ce, "Mu jira har sai wayewar gari, sa'an nan kuma mu kashe shi." 3 Samsin ya yi kwance bisa gado har tsakiyar dare. Da dare ya yi tsaka sai Samsin ya tashi ya tafi ya kama ƙofar birnin da ginshiƙanta biyu. Ya tumɓuko su daga ƙasa, duk da ƙarafunan da komai, ya ɗorasu bisa kafaɗunsa, ya tafi da su bisa tudu, a gaban Hebron. 4 Bayan wannan, Samsin ya zo ya ƙaunaci wata mata da ke zaune a Kwarin Sorek. Sunanta Delila. 5 Masu mulkin Filistiyawa suka zo wurinta, suka ce da ita, "Ki yaudari Samsin domin ki gane inda babban ƙarfinsa yake, da kuma ta yaya zamu sha ƙarfinsa, domin mu ɗaure shi mu kuma yi masa wulaƙanci. Ki yi mana wannan, mu kuma kowanne zai ba ki azurfa 1,100 ." 6 Daga nan Delila ta ce da Samsin, "Ina roƙonka, ka gaya mani yadda aka yi ka ke da ƙarfi haka, kuma ta yaya za a iya ɗaure ka, domin a mulke ka?" 7 Samsin yace mata, "Idan aka ɗaure ni da ɗanyen ƙiri guda bakwai, daga nan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum." 8 Sai masu mulkin Filistiyawa suka kawo wa Delila igiyoyin ƙiri guda bakwai ɗanyu, ita kuwa ta ɗaure Samsin da su. 9 Ta riga ta ɓoye mutane a asirce, suna jira cikin ƙuryar ɗakinta. Sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Amma ya tsisttsinke igiyoyin kamar zare a mazari idan ya taɓa wuta. Ta haka ba a gane asirin ƙarfinsa ba. 10 Daga nan Delila ta ce da Samsin, "Yadda ka ruɗe ni kenan kuma ka yi mani ƙarya. Ina roƙon ka, ka faɗa mani yadda za a sha ƙarfinka." 11 Sai ya ce mata, "Idan aka ɗaure ni da sabbin igiyoyin da ba a taɓa aiki da su ba, daganan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum." 12 Sai Delila ta ɗauki sabbin igiyoyi ta ɗaure shi da su, sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Mutanen kuwa 'yankwanto suna cikin ƙuryar ɗakin. Samsin kuwa ya tsisttsinke igiyoyin kamar zare. 13 Delila ta ce da Samsin, "Har yanzu ruɗi na ka ke yi kuma kana faɗa mani ƙarairayi. Ka gaya mani yadda za a sha ƙarfinka." Samsin yace mata, "Idan ki ka saƙa tukkun kaina guda bakwai bisa masaƙa kamar yadda ake saƙa sutura, sa'an nan ki sa allura ki kafe gashin bisa gungumen masaƙar, zan zama kamar kowanne mutum." 14 Yayin da ya yi barci, sai Delila ta yi wa tukkun kansa bakwai saƙa kamar an saƙa sutura bisa masaƙa ta kuma sa allura ta kafe shi bisa masaƙa, sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Ya farka daga barci kuma ya yage gashin duk da allurar daga jikin masaƙar. 15 Sai ta ce masa, "Ta yaya za ka ce, 'Ina son ki,' amma baka iya faɗa mani asirinka ba? sau uku kenan kana yi mani ba a kuma ba ka gaya mani yadda aka yi ka ke da babban ƙarfi haka ba." 16 Kowacce rana ta dinga gasa masa tsanani ta wurin maganganu, ta tsananta masa ƙwarai da gaske har ya gwammace ya mutu. 17 Sai Samsin ya faɗa mata dukkan komai ya ce mata, "Ba a taɓa sa reza aka yanke gashin kaina ba, Gama ni Naziri ne domin Allah tun daga mahaifar uwata. Idan aka aske kaina, to ƙarfina zai rabu da ni, daganan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum." 18 Da Delila ta ga cewa ya faɗa mata gaskiya game da komai, sai ta aika aka kira masu mulkin Filistiyawa, ta na cewa, "Ku sake dawowa, gama ya faɗa mani komai." Sai masu mulkin Filistiyawa suka tafi wurinta, suna ɗauke da azurfa a hannuwansu. 19 Sai ta sa barci ya kwashe shi a bisa cinyarta. Ta kira wani mutum yazo ya aske tukkaye bakwai da ke a kansa, daga nan ta dinga jujjuya shi, domin ƙarfinsa ya riga ya rabu da shi. 20 Ta ce, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" ya farka daga barcinsa ya ce, "Zan tashi kamar lokutan baya in kuma girgije kaina kuɓutacce." Amma ba ya sani cewa Yahweh ya riga ya rabu da shi ba. 21 Filistiyawa suka kama shi suka ƙwaƙule masa idanu. Suka kawo shi har Gaza suka kuma ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Shi ne ke aikin juya dutsen niƙa a kurkuku. 22 Amma gashin kansa ya soma sake tuƙowa bayan askin da aka yi masa. 23 Masu mulkin Filistiyawa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga Dagon allahnsu, su kuma yi farinciki. Suka ce, "Allahnmu ya yi nasara da Samsin, maƙiyinmu, ya kuma sa shi cikin hannuwanmu." 24 Da mutanen suka gan shi, sai suka yi yabo ga allahnsu, domin suka ce, "Allahnmu ya yi nasara da maƙiyinmu kuma ya miƙa shi gare mu - mai lalatar da ƙasarmu, wanda ya kashe masu yawa daga cikinmu." 25 Yayin da suke cikin shagali, sai suka ce, "A kira mana Samsin, domin ya zo ya sa mu dariya." Aka kira Samsin daga cikin kurkuku ya zo ya yi ta ba su dariya. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙan ginin. 26 Samsin yace da saurayin da ya riƙe hannunsa, "Ka bar ni in taɓa ginshiƙan da ke riƙe da ginin, domin in jingina da su." 27 Yanzu fa gidan na cike da mutane maza da mata. Dukkan masu mulkin Filistiyawa suna wurin. A bisa rufin ginin akwai mutum dubu uku maza da mata, waɗanda ke kallo yayin da Samsin ke yi masu wasa. 28 Samsin ya yi kira ga Yahweh ya ce, "Ubangiji Yahweh, ka tuna da ni! Ina roƙon ka ka ƙarfafa ni sau ɗaya kacal, ya Allah, domin in ɗauki fansa bugu ɗaya tak akan Filistiyawa saboda idanuna biyu da suka ƙwaƙule." 29 Samsin ya riƙe ginshiƙan nan biyu da ke ɗauke da ginin, sai ya jingina kansa da su, hannunsa na dama na riƙe da ɗaya, kuma hannunsa na hagu na riƙe da ɗayan. 30 Samsin yace, "Bari in mutu tare da Filistiyawa!" Ya miƙe iya ƙarfinsa ginin kuwa ya rugurguje bisa masu mulkin da dukkan mutanen da ke ciki. Saboda haka matattun da ya kashe a mutuwarsa sun fi waɗanda ya kashe a lokacin rayuwarsa. 31 Daga nan 'yan'uwansa da dukkan gidan mahaifinsa suka gangaro. Suka ɗauko shi, suka dawo da shi suka kuma binne shi tsakanin Zora da Eshtawol a maƙabartar Manowa, mahaifinsa. Samsin ya yi alƙalacin Isra'ila shekaru ashirin.

Sura 17

1 Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraim, sunansa Mika. 2 Sai ya ce da mahaifiyarsa, "Azurfarki 1,100 da aka ɗauke maki, wanda kuma ki ka furta la'ana akai, wanda kuma na ji - duba nan! azurfar na wurina. Ni ne na sace." Mahaifiyarsa ta ce, "Yahweh ya albarkace ka, ɗana!" 3 Sai ya maido wa mahaifiyarsa azurfa 1,100 sai mahaifiyarsa ta ce, "Na keɓe wannan azurfa ga Yahweh, domin ɗana ya sassaƙa kuma ya sarrafa siffofi na ƙarfe. Saboda haka yanzu, na maido maka azurfar." 4 Da ya maido wa mahaifiyarsa kuɗin, sai mahaifiyarsa ta ɗauki azurfa ɗari biyu ta ba maƙeri wanda shi kuma ya sassaƙa ya kuma sarrafa siffofi na karfe da su, sai aka ajiye su a gidan Mika. 5 Mutumin nan Mika ya na da gidan gumaka sai ya yi falmarar haikali da kuma allolin gida, sai ya ɗauki hayar ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama firist. 6 A waɗannan kwanaki ba sarki a Isra'ila, kowa na yin abin da ya yi dai-dai a idanunsa. 7 Akwai wani saurayi daga Betlehem ta cikin Yahuda, daga iyalin Yahuda, shi kuwa Balebi ne. Ya na zaune anan domin ya aiwatar da ayyukansa. 8 Mutumin ya bar Betlehem ta Yahuda ne domin ya fita ya je ya sami wani wurin zama. Yayin da ya ke tafiya, sai ya zo gidan Mika da ke ƙasar tuddun Ifraim. 9 Sai Mika yace masa, "Daga ina ka fito?" Mutumin yace masa, "Ni Balebi ne na Betlehem ta cikin Yahuda, kuma na fito tafiya ne domin neman wurin zama." 10 Mika yace da shi, "Ka zauna da ni, sai ka zama uba da firist a gare ni. Zan ba ka azurfa goma a shekara, da kayan sawa, da abinci." Sai Balebin ya shiga cikin gidansa. 11 Balebin ya dangana da zama da mutumin, kuma saurayin ya zame wa Mika kamar ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza. 12 Mika ya keɓe Balebin saboda ayyukan ibada, sai saurayin ya zama firist ɗinsa, kuma yana cikin gidan Mika. 13 Sai Mika yace, "Yanzu na sani cewa Yahweh zai yi mani abin alheri, domin Balebin nan ya zama firist ɗina."

Sura 18

1 A waɗannan kwanaki babu sarki a Isra'ila. Kabilar zuriyar Dan suna neman wajen da za su yi wa kansu wurin zama, domin har zuwa wannan lokaci ba su karɓi wani gãdo daga cikin kabilun Isra'ila ba. 2 Mutanen Dan suka aika da mutum biyar daga dukkan cikin kabilarsu, mutanen da suka ƙware wajen yaƙi daga Zora zuwa Eshtawol, domin su kewaye ƙasar da ƙafa, kuma su duba ta. Suka ce masu, "Ku je ku duba ƙasar." Suka zo ƙasar tudu ta Ifraim, suka zo gidan Mika, suka kwana anan. 3 Da su na kusa da gidan Mika, sai suka gane karin harshen saurayin nan Balebiye. Sai suka tsaya suka tambaye shi, "Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan wurin? Meyasa ka ke nan?" 4 Ya ce masu, "Ga abin da Mika ya yi mani: Ya ɗauki hayata in zama firist ɗin sa." 5 Suka ce da shi, "Muna roƙon ka ka nemi shawara daga Allah, domin mu sani ko tafiyar nan da muke yi za ta yi nasara." 6 Sai firist ɗin ya ce masu, "Ku tafi cikin salama. Yahweh za ya bi da ku hanyar da zaku bi." 7 Sai mutanen nan biyar suka tafi har suka isa Layish, sai suka iske mutanen na zaune lafiya, hakanan kuma Sidoniyawa suke zaune, babu abin da ya dame su a tsare suke. Babu wanda ya taɓa yin nasara da su ko kuma ya taɓa tsananta masu a ƙasar ko kaɗan. Suna zaune nesa da Sidoniyawa kuma ba su da wata hurɗa da kowa. 8 Suka dawo wurin kabilarsu a Zora da Eshtawol. 'Yan'uwansu suka tambaye su, "Mene ne rahotonku?" 9 Suka ce, "Ku zo! Mu kai masu hari! Mun ga ƙasar kuma mai nagarta ce. Ba za kuyi wani abu ba? Kada ku yi jinkirin kai hari kuma ku ci ƙasar. 10 Idan ku ka je, za ku iske mutane waɗanda ke tunanin a tsare suke, kuma ƙasar na da fãɗi! Allah ya bayar da ita a gare ku - wurin da babu rashin komai a ƙasar." 11 Mutane ɗari shida daga kabilar Dan, shirye da kayan yaƙi, suka fito daga Zora da Eshtawol. 12 Suka tafi su ka yi sansani a Kiriyat Yerayim, cikin Yahuda. Wannan ya sa mutane ke kiran wurin Mahane Dan har wa yau; yana yamma da Kiriyat Yerayim. 13 Suka tafi daga wurin zuwa ƙasar tudu ta Ifraim sai suka zo gidan Mika. 14 Sai mutanen nan biyar da suka je gewayar ƙasar Layish suka ce da 'yan'uwansu, "Kun kuwa san cewa a cikin gidajen nan akwai falmarar haikali, da allolin gida, sassaƙaƙƙiyar siffa, da siffar ƙarfe da aka sarrafa? Yanzu ku yi shawarar abin da za ku yi." 15 Sai suka juya daga nan suka shiga gidan saurayin nan Balebi, a gidan Mika, sai suka gaishe shi. 16 Daga nan Danawan nan ɗari shida, shirye da kayan yaƙi, suka tsaitsaya a ƙofar gidan. 17 Mutanen nan biyar da suka je gewayar ƙasar suka shiga suka ɗauko sassaƙaƙƙiyar siffar, da falmarar haikalin, da allolin gida, da sarrafaffiyar siffar ƙarfen, lokacin da firist ɗin ke tsaye bakin ƙofar gidan tare da mutanen nan ɗari shidda da ke shirye da kayan yaƙi. 18 Da waɗannan suka shiga cikin gidan Mika suka ɗauko sassaƙaƙƙiyar siffar nan, da falmarar haikali, da allolin gida, da sarrafaffiyar siffar ƙarfen nan, sai firist ɗin ya ce masu, "Me ku ke yi?" 19 Suka ce da shi, "Yi shiru! Ka sa hannunka a bakinka ka taho tare da mu, sai ka zama Uba da firist a gare mu. Wanne ne ya fi maka ka zama firist na gidan mutum ɗaya, ko kuwa ka zama firist na kabila da kuma ɗaya daga cikin zuriyar Isra'ila?" 20 Firist ɗin ya yi murna a zuciyarsa. Ya ɗauki falmarar haikalin, da allolin gidan, da sassaƙaƙƙiyar siffar, sai ya tafi tare da mutanen. 21 Sai suka juya suka yi tafiyarsu. Suka sa ƙananan yaran a gabansu, da kuma shanun da dukkan mallakarsu. 22 Da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da ke maƙwaftaka da gidan Mika suka tattaru, suka tafi suka tarar da Danawan. 23 Suka yi kururuwa ga Danawan, suka juya suka ce wa Mika, "Me ya sa ku ka tattaro kanku?" 24 Ya ce, "Kun sãce allolin da na yi, kun ɗauke mani firist, kuma kun tafi. Me kuma ya rage mani? ya ya za ku yi mani tambaya, "Me ke damun ka?" 25 Mutanen Dan suka ce da shi, "Kada ka bari mu ji ka ce wani abu, ko kuwa wasu mutane masu fushi da ke nan wurin ransu ya ɓaci sosai su kai maka hari, kai da iyalinka kuma a kashe ku." 26 Sai mutanen Dan suka yi tafiyarsu. Da Mika ya ga cewa sun sha ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gidansa. 27 Mutanen Dan suka ɗauke abin da Mika ya sassaƙa, duk da firist ɗinsa, sai suka zo Layish, wurin mutanen da babu abin da ya dame su kuma cikin tsaro suka kashe su da takobi suka ƙone birnin. 28 Babu wanda yazo ya cece su domin sun yi nisa da Sidon, kuma ba su da wata hurɗa da wani. A kwari ne da ke kusa da Bet Rehob. Danawan suka sake gina birnin suka zauna a ciki. 29 Suka sa wa birnin suna Dan, bisa ga sunan Dan kakansu, wanda ya ke ɗaya daga cikin 'ya'yan Isra'ila. Amma dã sunan birnin Layish ne. 30 Mutanen Dan suka kafa wa kansu sassaƙaƙƙiyar siffar nan. Yonatan ɗan Gashom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza suka zama firistocin kabilar Danawa har zuwa ranar tafiya ƙasar bauta. 31 Haka nan suka yi sujada ga sassaƙaƙƙiyar siffar Mika wanda ya sarrafa dukkan tsawon kwanakin da gidan Allah ya ke a Shilo.

Sura 19

1 A waɗannan kwanaki, sa'ad da babu sarki a Isra'ila, akwai wani mutum, Balebi, ya yi zama na ɗan wani lokaci a wani ƙauye a ƙasar tudu ta Ifraim. Sai ya ɗauko wa kansa mace, kuyanga daga Betlehem cikin Yahuda. 2 Amma kuyangar tasa ta yi masa rashin aminci; sai ta bar shi ta koma gidan mahaifinta a Betlehem cikin Yahuda. Ta zauna a can watanni huɗu. 3 Sai mijinta ya tashi ya tafi wurinta domin ya lallashe ta ta dawo. Baransa kuwa na tare da shi, da jakai guda biyu. Sai ta kawo shi cikin gidan mahaifinta. Da mahaifin yarinyar ya gan shi, sai ya yi murna. 4 Sai surukinsa, mahaifin yarinyar, ya lallashe shi ya zauna kwana uku. Suka ci su ka sha suka kwana a can. 5 A rana ta huɗu suka tashi suka yi asubanci suka shirya domin su tafi, amma mahaifin yarinyar ya ce da surukinsa, "Ka ci ɗan abinci domin ka sami ƙarfi, daga nan sai ka tafi." 6 Sai su biyun suka zauna domin su ci su kuma sha tare. Daga nan mahaifin yariyar ya ce, "Ina roƙon ka ka yarda ka sãke kwana domin ka wartsake." 7 Da Balebin ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya roƙe shi da ya tsaya, sai ya canza shirinsa ya sake kwana. 8 A rana ta biyar ya tashi ya yi asubanci domin ya tafi, amma mahaifin yarinyar ya ce, "Ka ƙarfafa kanka, ka jira sai rana tayi." Sai suka zauna su ka ci abinci su biyu. 9 Da Balebin da kuyangarsa da baransa suka tashi za su tafi, sai surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce da shi, "Duba, yanzu yamma ta ƙarato. Ina roƙonka ka tsaya ka sãke kwana, ka kuma wartsake. Kana iya yin asubanci gobe ka tashi ka koma gida." 10 Amma Balebin ba ya so ya sake kwana. Sai ya tashi ya tafi. Ya yi tafiya ya fuskanci Yebus (wato Yerusalem). Yana da jakai biyu shiryayyu domin hawa - kuma kuyangarsa na tare da shi. 11 Da suka iso gaf da Yebus, rana ta kusa faɗuwa, sai baran ya ce wa maigidansa, "Ka zo, mu juya mu shiga birnin Yebusawa mu kwana a ciki." 12 Sai ubangidansa yace masa, "Ba za mu juya mu shiga birnin bãre waɗanda ba na mutanen Isra'ila ba ne. Mu ci gaba da tafiya mu kai Gibiya." 13 Balebin ya ce wa bãransa, "Zo, mu tafi ɗaya daga cikin wuraren nan, mu kwana a can ko dai Gibiya ko kuma Ramah." 14 Sai suka ci gaba da tafiya, rana kuwa ta faɗi da suka yi gaf da Gibiya, cikin yankin Benyamin. 15 Sai suka juya suka shiga domin su kwana a Gibiya. Sai suka je suka zauna a dandalin birnin, amma babu wanda ya kira su domin su kwana a gidansa. 16 Amma sai ga wani mutum tsoho yana dawowa daga aikin gonarsa a yammacin nan. Shi kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraim ne, amma ya na zama a Gibiya na ɗan wani lokaci. Amma mutanen da ke zama a wannan wuri Benyaminawa ne. 17 Ya ɗaga idanunsa sai ya ga matafiyin a dandalin birni. Tsohon ya ce, "Ina za ku? Daga ina ku ka fito?" 18 Balebinn yace masa, "Mun fito ne daga Betlehem cikin Yahuda za mu wani ƙauyen ƙasar tudu ta Ifraim, wato inda na fito. Na je Betlehem cikin Yahuda, kuma za ni gidan Yahweh, amma babu wanda zai karɓe ni cikin gidansa. 19 Muna da harawa da abinci domin jakkanmu, akwai gurasa da ruwan inabi domina da wannan mace baiwarka a nan, da kuma wannan saurayin tare da barorinka. Ba mu rasa komai ba." 20 Sai tsohon nan ya gaishe su, "Salama a gare ku! Zan biya dukkan buƙatunku. Kada dai ku kwana a dandali kawai." 21 Sai mutumin ya kawo Balebinn cikin gidansa ya kuma ba da abinci ga jakunansa. Suka wanke sawayensu suka ci suka sha. 22 Lokacin da suke cikin annashuwa, sai waɗansu mutanen birnin, 'yan'iskan gari, suka zo suka kewaye gidan, suna bubbuga ƙofar. Suka yi wa tsohon nan magana, wato mai gidan, suna cewa, "Ka fito da mutumin nan da ya shigo cikin gidanka, domin mu yi luɗu da shi." 23 Mutumin nan, mai gidan, ya fita ya same su ya ce masu, "A 'a, 'yan'uwana, ina roƙon ku kada ku yi wannan irin mugun abu! Tun da wannan mutum baƙon gidana ne, kada ku yi wannan irin mugun abu! 24 Duba, ɗiyata budurwa da kuma kuyangarsa ga su nan. Bari in fito da su yanzu. Ku yi masu fyaɗe ku kuma yi yadda kuka ga dama da su. Amma kada ku yi wannan irin mugun abu ga mutumin nan!" 25 Amma mutanen nan ba su saurare shi ba, sai mutumin nan ya fizgi kuyangarsa ya kuma fitar masu da ita. Suka fizge ta, suka yi mata fyaɗe, suka wulaƙanta ta dukkan tsawon dare, da asuba ta yi suka bar ta ta tafi. 26 Da asuba matar ta dawo sai ta faɗi a bakin ƙofar gidan mutumin inda maigidanta ya ke, sai ta yi kwance a nan har gari ya waye sarai. 27 Maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofofin gidan ya fita domin ya kama hanyar tafiyarsa. Sai ya lura da kuyangarsa a kwance a bakin ƙofa, da hannuwanta bisa dankarin ƙofar. 28 Balebin ya ce mata, "Tashi. Mu tafi." Amma ba ta amsa ba. Sai ya ɗora ta bisa jaki, mutumin kuwa ya kama hanya zuwa gidansa. 29 Sa'ad da Balebin nan ya iso gidansa, sai ya ɗauko wuƙa, ya kuma kama kunyangar tasa, ya daddatsa ta, ya yi mata gunduwa-gunduwa, ya kasa ta kashi goma sha biyu, sai ya aika da kashi-kashin nan ko'ina cikin dukkan ƙasar Isra'ila. 30 Dukkan waɗanda suka ga wannan abu suka ce, "Wannan irin abu bai taɓa faruwa ba ko aka taɓa ganinsa ba tun daga ranar da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar har ya zuwa wannan rana. Ku yi tunani akai! Ku bamu shawara! Ku gaya mana abin da za'a yi!"

Sura 20

1 Daga nan dukkan mutanen Isra'ila suka fito a matsayin mutum guda, daga Dan har zuwa Biyasheba, duk da ƙasar Giliyad ma, suka tattaru tare a gaban Yahweh a Mizfa. 2 Shugabannin dukkan mutanen, da kuma dukkan kabilun Isra'ila, suka ɗauki wurarensu a cikin taron mutanen Allah - Mutane 400,000 a ƙasa, waɗanda ke a shirye domin su tafi su yi yaƙi da takobi. 3 Mutanen Benyamin suka ji cewa mutanen Isra'ila sun haye zuwa Mizfa. Mutanen Isra'ila suka ce, "Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru." 4 Balebin mai gidan matar wadda aka kashe, ya amsa, "Na zo Gibiya ne wadda ke yankin Benyamin, ni da kuyangata, domin mu kwana. 5 A cikin dare, shugabannin Gibiya suka kawo mani hari, suka kewaye gidan suna nema su kashe ni. Suka fizge kuyangata su a yi mata fyaɗe, sai kuwa ta mutu. 6 Na ɗauki kuyangata na datsa ta kashi-kashi, na kuma aika cikin kowanne lardin gãdon Isra'ila, saboda sun aikata wannan irin mugunta da hasala a cikin Isra'ila. 7 Yanzu, dukkan ku Isra'ilawa, sai ku ba da shawara ku kuma ɗauki mataki a nan." 8 Dukkan mutanen suka tashi tsaye a matsayin mutum guda, suka ce, "Babu wani cikinmu da za ya koma rumfarsa, babu kuma wani cikinmu da zaya koma gidansa! 9 Amma dole yanzu ga abin da zamu yi wa Gibiya: Za mu kai mata hari bisa ga yadda ƙuri'a za ta bi da mu. 10 Za mu ɗauki mutane goma cikin ɗari daga cikin dukkan kabilun Isra'ila, da kuma mutane ɗari cikin dubu, mutane dubu cikin dubu goma, su samo kayan masarufi domin waɗannan mutanen, domin idan suka zo Gibiya ta Benyamin, su ba su horo domin muguntar da suka aikata a Isra'ila." 11 Sai dukkan sojojin Isra'ila suka taru a matsayin mutum guda, domin yin tsayayya da birnin. 12 Sai kabilun Isra'ila suka aika da mutane cikin dukkan kabilar Benyamin, suna cewa, "Wacce irin mugunta ce haka aka aikata a cikinku? 13 Saboda haka, ku ba mu waɗannan miyagun mutanen na Gibiya, domin mu kashe su, ta haka za mu cire wannan mugunta da ke cikin Isra'ila ɗungun." Amma Benyaminawa suka ƙi sauraron muryar 'yan'uwansu, mutanen Isra'ila. 14 Sai mutanen Benyamin suka fito daga cikin biranensu suka tattaru a Gibiya domin su yi shirin yin yaƙi da mutanen Isra'ila. 15 Mutanen Benyamin suka tattaro mutane daga cikin biranensu a wannan rana sojoji dubu ashirin da shida horarru wajen faɗa da takobi. Bugu da ƙari, akwai mutane ɗari bakwai zaɓaɓɓu daga cikin mazauna a Gibiya. 16 Daga cikin waɗannan sojoji dukka akwai mutane ɗari bakwai zaɓaɓɓu waɗanda su bahagwai ne. Kowannen su za ya iya wurga dutse ga gashin kai ba tare da yin kuskure ba. 17 Mutanen Isra'ila, ba tare da lissafin mutanen Benyamin ba, su mutum dubu ɗari huɗu ne, waɗanda kuma horarru ne wajen faɗa da takobi. Dukka waɗannan mutanen yaƙi ne. 18 Mutanen Isra'ila suka tashi, suka hau zuwa Betel, suka tambayi shawara daga wurin Allah. Suka yi tambaya,"Wane ne za ya fara kai wa mutanen Benyamin hari domin mu?" Yahweh yace, "Yahuda ne za ya fara kai hari." 19 Mutanen Isra'ila suka tashi da sassafe suka matsa da sansaninsu kusa da Gibiya. 20 Mutanen Isra'ila suka tafi yin yaƙi da Benyamin. Suka tashi suka yi jeren yaƙi da Gibiya. 21 Mutanen Benyamin suka fito daga cikin Gibiya, suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na sojojin Isra'ila a wannan rana. 22 Amma mutanen Isra'ila suka ƙarfafa kansu suka sãke kafa layin yaƙi dai-dai wurin da suka jera a rana ta farko. 23 Sai mutanen Isra'ila suka haye suka yi kuka a gaban Yahweh har zuwa yamma, suka kuma nemi bishewa daga wurin Yahweh. Suka ce, "Mu kuma sãke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Benyamin?" Yahweh yace, "Ku kai masu hari!" 24 Sai mutanen Isra'ila suka kai hari ga sojojin Benyamin a rana ta biyu. 25 A rana ta biyu, Benyamin ya fito daga Gibiya suka kuma kashe mutum dubu sha takwas daga cikin mutanen Isra'ila. Dukkan su horarru ne wajen faɗa da takobi. 26 Daga nan dukkan sojojin Isra'ila da dukkan mutanen Isra'ila suka tashi su ka haye zuwa Betel suka yi kuka, a nan suka zauna a gaban Yahweh suka yi azumi a wannan rana har zuwa yamma suka miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a gaban Yahweh. 27 Mutanen Isra'ila su ka tambayi Yahweh - domin akwatin alƙawari na Allah na nan a waɗannan kwanaki, 28 a sa'annan Fenihas, ɗan Eliyeza ɗan Haruna, yana hidima a gaban akwatin a waɗannan kwanaki - "Mu sake tafiya mu yaƙi mutanen Benyamin, 'yan'uwanmu, ko mu tsaya?" Yahweh yace, "Ku kai hari, gama gobe zan taimake ku ku yi nasara da su." 29 Sai Isra'ila suka sa mutane suka kewaye Gibiya gaba ɗaya a asirce. 30 Mutanen Isra'ila suka yi yaƙi da mutanen Benyamin a rana ta uku, suka kafa layin yaƙi da Gibiya kamar yadda suka yi a dã. 31 Mutanen Benyamin suka fita suka yi yaƙi da mutanen, har suka fita suka yi nisa da birnin. Suka fara kashe wasu daga cikin mutanen. Wajen mutane talatin na Isra'ila suka mutu cikin gonaki da bisa hanyoyi.‌ Ɗaya daga cikin hanyoyin ta hawa zuwa Betel ce, ɗayar kuma ta tafi zuwa Gibiya. 32 Sai mutanen Benyamin suka ce, "An kãshe su gashi nan suna guduwa daga gare mu, kamar yadda ya faru da farko." Amma sojojin Isra'ila suka ce, "Mu gudu baya domin mu janye su daga cikin birnin zuwa bisa hanyoyi." 33 Dukkan mutanen Isra'ila kuwa suka fito daga wurarensu suka jera kansu layi-layi domin yaƙi a Ba'al Tama. Sai sojojin Isra'ila waɗanda ke ɓoye a asirtattun wurare suka fito da gudu daga wurarensu daga Ma'are Gibiya. 34 Sai ga shi an fito wa Gibiya da yaƙi mutane dubu goma daga cikin dukkan Isra'ila, yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Benyamin ba su san bala'i na gaf da su ba. 35 Sai Yahweh ya kayar da Benyamin a gaban Isra'ila. A wannan rana, sojojin Isra'ila suka kashe mutum 25,100 na Benyamin. Dukkan waɗanda suka mutu horarru ne wajen faɗa da takobi. 36 Sai sojojin Benyamin suka ga cewa an kayar da su. Mutanen Isra'ila kuwa sun ba Benyamin sarari, sabo da suna la'akari da mutanen da ke ɓoye a kewaye da Gibiya. 37 Sai mutanen da ke a ɓoye suka tashi da sauri suka auka cikin Gibiya, da takubbansu kuwa suka kashe duk wanda ke zaune a cikin birnin. 38 Alamar da aka shirya tsakanin sojojin Isra'ila da mutanen da ke ɓoye a asirtattun wurare shi ne za su ga girgijen hayaƙi ya turniƙe yana fitowa daga birnin. 39 Idan aka aika da alamar sojojin Isra'ila za su juya daga yaƙin. To Benyamin ya fara kai hari har sun kashe mutane wajen talatin na Isra'ila, sai suka ce, "babu shakka an kayar da su a gabanmu, kamar a yaƙin farko." 40 Amma da tuƙuƙin hayaƙi ya fara tashi sama daga cikin birnin, mutanen Benyamin kuwa suka juya suka ga hayaƙi na tashi daga cikin dukkan birnin har zuwa sararin sama. 41 Sai kuwa mutanen Isra'ila suka juyo kansu. Mutanen Benyamin suka tsorata, domin sun ga bala'in da ya afko masu. 42 Sai suka gudu daga wurin mutanen Isra'ila, suna tserewa hanyar zuwa jeji. Amma yaƙin ya ci ƙarfinsu. Sojojin Isra'ila suka fito daga birane suka kuwa karkashe su a inda suke tsaye. 43 Suka kewaye mutanen Benyamin, su a kora su, suka tattake su a Noha, har ya zuwa gabashin Gibiya. 44 Daga kabilar Benyamin, mutane dubu goma sha takwas suka mutu, dukkan su mutane ne ƙwararru a yaƙi. 45 Suka juya suka sheƙa da gudu zuwa jeji zuwa dutsen Rimon. Isra'ilawa suka ƙara kashe mutane dubu biyar a kan hanyoyi. Suka ci gaba da bin su, suna binsu ƙut da ƙut har zuwa Gidom, suka kuma ƙara kashe dubu biyu a can. 46 Dukkan sojojin Benyamin da suka fãɗi a wannan rana mutane dubu ashirin da biyar ne - horarrun mutane wajen faɗa da takobi, dukkan su ƙwararru ne a wajen yaƙi. 47 Amma mutane ɗari shida suka juya suka gudu zuwa jeji, zuwa dutsen Rimon. Suka yi wata huɗu suna zama a dutsen Rimon. 48 Sojojin Isra'ila suka juya su ka fãɗa wa mutanen Benyamin suka hare su suka kashe birnin gaba ɗaya, da shanu dukka, da dukkan abin da suka iske. Suka kuma ƙone duk wani gari da suka iske a hanyarsu.

Sura 21

1 Daga nan mutanen Isra'ila suka ɗauki alƙawari a Mizfa, "Babu wani cikin mu da zai bada ɗiyarsa aure ga Benyamine." 2 Sai mutanen suka haye zuwa Betel suka zauna can a gaban Allah har yamma, da muryoyi masu ƙarfi suka yi kuka mai zafi. 3 Suka yi kira, "Meyasa, Yahweh, Allah na Isra'ila, wannan irin abu ya faru da Isra'ila, cewa a yau ɗaya daga cikin kabilunmu ya ɓace?" 4 Washegari mutanen suka tashi da sassafe suka gina bagadi suka miƙa baiko na ƙonawa da na salama. 5 Mutanen Isra'ila suka ce, "Daga cikin kabilun Isra'ila dukka wane ne bai fito taron Yahweh ba?" Gama sun riga sun ɗauki alƙawari mai muhimmanci game da duk wanda bai zo wurin Yahweh ba a Mizfa. Suka ce, "Babu shakka za a kashe shi." 6 Sai mutanen Isra'ila suka ji tausayin ɗan'uwansu Benyamin. Suka ce, "A yau an datse kabila ɗaya daga cikin Isra'ila. 7 Wane ne za ya bada matayen aure ga waɗanda suka rage, tun da mun riga mun yi alƙawari ga Yahweh cewa babu wanda za ya bar wani daga cikin su ya auri 'ya'yanmu mata?" 8 Suka ce, "Wace ce cikin kabilun Isra'ila ba ta zo wurin Yahweh ba a Mizfa?" Sai aka iske cewa babu wanda yazo taron daga Yabish Giliyad. 9 Domin da aka sa mutane suka tsaya jeri-jeri, duba, babu ko ɗaya daga cikin mazaunan Yabish Giliyad da ya kasance. 10 Sai taron suka aika da jarumawansu mutum dubu sha biyu da umarnin cewa su je Yabish Giliyad su kai masu hari, su kuma kashe su, har ma da mata da 'ya'ya. 11 "Haka za ku yi: dole ne ku kashe kowanne namiji da kowace mace da ta san namiji." 12 Mutanen suka samo daga cikin mazauna Yabish Giliyad 'yanmata ɗari huɗu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, suka kawo su sansani a Shilo, cikin Kan'ana. 13 Taron ga baki ɗaya suka aika da saƙo ga mutanen Benyamin da ke a dutsen Rimon su na cewa muna neman ku da salama. 14 Mutanen Benyamin suka dawo a wannan lokacin kuma suka basu matan Yabish Giliyad, amma kuma matan basu isa kowannen su ya samu ba. 15 Mutanen suka yi juyayin abin da ya faru da Benyamin, saboda Yahweh ya sa rarrabuwa a tsakanin kabilun Isra'ila. 16 Sai shugabannin taron suka ce, "Yaya za mu shirya wa mutanen Benyamin da suka rage matan aure, tun da an kashe matayen Benyamin?" 17 Sai suka ce, "Dole ne a sami gãdo domin waɗanda suka tsira a Benyamin, domin ka da kabila ɗaya ta lalace a Isra'ila. 18 Ba za mu iya ba su matan aure daga cikin 'ya'yanmu mata ba, gama mutanen Isra'ila sun yi alƙawari, 'La'ananne ne wanda ya ba da mace ga Benyamin.'" 19 Sai suka ce, "Kun san akwai bikin idin Yahweh kowacce shekara a Shilo (wadda ke arewa da Betel, gabas da hanyar da ke tafiya daga Betel zuwa Shekem, a kudacin Lebona)." 20 Sai suka yi wa mutanen Benyamin umarni, suka ce, "Ku je ku ɓoye a asirce ku yi kwanto cikin garkar inabi. 21 Ku lura da lokacin da 'yanmata daga Shilo za su fito rawa, sai ku hanzarto daga garkar inabin kowanen ku ya kama wa kansa mata daga cikin 'yanmatan Shilo, daga nan ku koma ƙasar Benyamin. 22 Idan ubanninsu ko 'yan'uwasu maza suka zo domin su yi mana tawaye, za mu ce masu, 'Ku yi mana tagomashi, ku bar su su zauna saboda ba mu samarwa dukkansu matan aure ba a lokacin yaƙin. Ba ku da laifi, tun da ba ku bayar da 'ya'yanku mata ba a gare su.'" 23 Mutanen Benyamin suka yi yadda aka ce. Suka ɗauki iya matan auren da suke bukata daga cikin 'yan'matan da ke rawa sai su da ke raka kwashe su suka tafi da su su zama matansu. Suka koma wurin gãdonsu. Suka sake gina garuruwansu suka zauna a ciki. 24 Daga nan mutanen Isra'ila suka bar wurin suka koma gida, kowanensu ya koma cikin kabilarsa da zuriyarsa, kowanensu kuma ga gãdonsa. 25 A cikin waɗannan kwanaki babu sarki a Isra'ila. Kowa yana yin abin da ya ga ya yi dai-dai a idanunsa.

Littafin Rut
Littafin Rut
Sura 1

1 Ya kasance a kwanakin da alƙalai ke mulki, sai a ka yi yunwa a cikin ƙasar, sai kuma wani mutumin Betlehem ta Yahuda ya tafi ƙasar Mowab tare da matarsa da 'ya'yansa maza guda biyu. 2 Sunan mutumin Elimelek, sunan matarsa kuma Na'omi. Sunayen 'ya'yansa biyu kuwa su ne Mahlon da Kiliyon, su Ifratawa ta Betlehem ta Yahuda ne, sai suka je ƙasar Mowab suka zauna a can. 3 Ana nan sai Elimelek mijin Na'omi ya mutu a ka bar ta da 'ya'yanta maza biyu. 4 Waɗannan 'ya'ya maza suka yi aure da 'yan matan Mowabawa guda biyu, sunayensu kuwa shi ne Orfa da Rut sun zauna a can har kusan shekaru goma. 5 A na nan sai Mahlon da Kiliyon suka mutu, aka bar Na'omi ba miji ba 'ya'yanta guda biyu. 6 Daga nan sai Na'omi ta yanke shawara ta bar Mowab tare da matan 'ya'yanta zuwa Yahuda saboda ta ji cewa Yahweh ya taimaki mutanensa da ke cikin buƙata ya kuma basu abinci. 7 Saboda haka sai ta bar wurin da take tare da surukanta biyu, suka kama hanya don su koma ƙasar Yahuda. 8 Sai Na'omi ta ce da surukanta biyu "Kowaccenku ta koma gidan iyayenta. Dama Yahweh ya yi mu ku jinkai, kamar yadda ku ka nuna jinkai gare ni da kuma mamatan. 9 Dama Ubangiji ya ba ku hutu a gidan mazanku da za ku aura. "Sai ta sunbace su sai suka tada murya suka yi kuka. 10 Sai suka ce da ita "A'a za mu koma wurin mutanenki tare da ke". 11 Amma Na'omi ta ce, "ku koma, 'ya'yana! Don me za ku tafi tare da ni? Har yanzu ina da sauran 'ya'ya maza a cikina dominku, da za su aure ku? 12 Haba 'ya'yana ku koma, don na tsufa sosai har da zan yi aure, Ko da ma ace ina begen yin aure yanzu, in haifi 'ya'ya maza, 13 Za ku jira har su yi girma? Za ku yi ta jira ba za ku yi aure yanzu ba? A'a 'ya'yana! Hakika ina cike da baƙin ciki sosai, fiye da na ku bakin cikin, Don Yahweh ya juya mani baya." 14 Sai surukanta su ka sake ɗaga murya su ka ɓarke da kuka. Sai Orfa ta sumbaci surukarta suka yi ban kwana, amma Rut ta manne mata. 15 Na'omi ta ce, kin ga 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da 'yar'uwarki." 16 Amma Rut ta ce, "Kar ki sa in rabu da ke, don inda za ki can za ni; inda kika zauna nan zan zauna, mutanenki za su zama mutanena, kuma Allahnki zai zama Allahna. 17 Inda ki ka mutu can zan mutu, a binne ni a can. Yahweh ya hukunta ni fiye da haka, idan har wani abu in ba mutuwa ba ya raba mu." 18 Sa'adda Na'omi ta ga Rut ta ƙudurta ta bi ta, sai ta dena gardama da ita. 19 Sai su biyun su ka yi tafiya har garin Betlehem. Bayan sun zo sai duk garin ya cika da murna saboda su, Sai mataye suka ce "Na'omi ce wannan?" 20 Amma ta ce da su "Kada ku kira ni Na'omi. Ku kira ni mai baƙinciki, don Mai Iko Dukka ya azabtar da ni. 21 Na fita a wadace, amma Yahweh ya sake dawo da ni gida hannu wofi. To don me ku ke kira na Na'omi, da ya ke Yahweh ya yashe ni, Mai iko dukka ya wahalshe ni?" 22 To Na'omi da surukarta Rut 'Yar Mowabawa su ka komo daga ƙasar Mowab. Suka zo Betlehem a farkon kakar bali.

Sura 2

1 Mijin Na'omi Elimelek ya na da ɗan'uwa mai suna Bo'aza, shi mawadaci ne, sananne. 2 Sai Rut 'yar Mowabawa ta ce da Na'omi, "Yanzu ki bar ni in je in yi kalar abin da ya ragu a gonakin hatsi. Zan bi duk wanda na sami tagomashi a wurinsa". Sai Na'omi ta ce da ita, '"Yata, ki je." 3 Sai Rut ta tafi ta yi kalar abin da ya ragu a gonaki bayan sun yi girbi, Sai ta je yankin gonar Bo'aza, wanda ɗan'uwa ne ga Elimelek. 4 Sai Bo'aza ya zo daga Betlehem ya ce da masu girbin, "Yahweh ya kasance tare da ku" Suka amsa masa, "Yahweh ya albarkace ka." 5 Sai Bo'aza ya ce wa barorinsa da ke kula da masu girbin, "Wannan yarinyar ɗiyar wanene?" 6 Baran da ke kula da masu girbin ya amsa, "Yar Mowabawa ce da ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab. 7 Ta ce da ni, "Ina roƙon ka bar ni in yi kalar abin da ya rage a gonar bayan masu girbin sun girbe hatsin. Sai ta zo nan tun da safe har yanzu, sai dai ɗan shaƙatawa da ta yi a gida" 8 Daga nan sai Bo'aza ya ce da Rut, 'Yata ki na ji na? Kada ki bar gonata ki je wata gona don ki yi kala, amma ki tsaya nan ki yi aiki tare da barorina mata da ke aiki. 9 Ki zuba idonki kawai a inda masu girbin ke girbi ki na bin bayan sauran matan. Ashe ban umarci mazan da kada su taɓa ki ba? Duk lokacin da ki ka ji ƙishi sai ki je wurin tulunan ruwa ki sha ruwan da mazan su ka ɗebo." 10 Daga nan sai ta sunkuyar da kanta har ƙasa a gaban Bo'aza. Ta ce, 'Ta yaya na sami tagomashi a gabanka, har da zaka kula da ni, ni da nake baƙuwa?" 11 Bo'aza ya amsa ya ce da ita, an labarta mini duk abin da ki ka yi tun lokacin da mijinki ya mutu, kin bar babanki, da kuma ƙasarki, ki ka biyo surukarki, ki ka zo wirin mutanen da ba ki sani ba. 12 Yahweh ya ba ki lada kan abin da ki ka yi, dama ki sami cikkaken lada daga Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda ki ka sami mafaka a gare shi." 13 Sai ta ce, "Bari in sami tagomashi a gareka, shugabana, don ka ta'azzantar da ni, ka yi mani maganar kirki, ko da ya ke ni ba ɗaya daga cikin barorinka mata ba ce." 14 A lokacin cin abinci sai Bo'aza ya ce da Rut "Zo nan ki ci wani abinci, ki kuma sa gutsuranki a cikin kunu." Sai ta zauna a gefen masu girbin, sai ya ba ta wani gasasshen hatsi. Ta ci har sai da ta ƙoshi ta bar sauransa. 15 Da ta tashi za ta yi kala sai Bo'aza ya ce da ma'aikatansa, "Ku barta ta yi kala har ma daga cikin dammunan, kada ku hana ta. 16 kuma ku dinga zarar ma ta zangarkun hatsin daga dammuna, ku bar ma ta ta tara ka da ku tsauta ma ta." 17 To sai ta yi ta kala a gonar har yamma. Daganan ta sussuke zangarkun hatsin ta sami kusan garwa biyu na bali. 18 Sai ta ɗauka ta tafi gari. Sai surukarta ta ga abin da ta samo. Rut kuma ta zo mata da soyayyen hatsin da ta ci ta rage sai ta bata. 19 Surukarta ta ce da ita, "Ina ki ka je kala yau? Ina ki ka je aiki yau? Dama mutumin da ya taimake ki ya sami albarka". Sai Rut ta faɗawa surukarta labarin mutumin da ya ke da gonar da kuma inda ta yi aiki. Ta ce "Sunan mutumin da na yi aiki a gonarsa Bo'aza" 20 Na'omi ta ce da surukarta Yahweh ya albarkace shi, wanda bai dena nuna amincinsa ga rayayyu da matattu ba." Na'omi ta ce wannan mutumin danginmune na kusa mai kuma fansarmu." 21 Rut mutumiyar Mowab ta ce, "Hakika, ya ce mani, "Ki dinga bin bayan ma'aikatana har sai sun gama girbin dukkan amfanin". 22 Sai Na'omi ta ce da Rut surukarta, '"Yata ya fi kyau da kike tafiya tare da ma'aikatansa 'yanmata, don ka da ki je wata gonar ki cutu." 23 To sai ta tsaya kusa da ma'aikatan Bo'aza 'yanmata don ta dinga kala har ya zuwa karshen kakar bali, don haka sai ta zauna tare da surukarta.

Sura 3

1 Surukarta, Naomi ta ce ma ta, '"Yata "Ba sai in samar miki wurin da za ki huta ba, don komai ya zamar miki dai-dai? 2 To yanzu shi Bo'aza da ki ke aiki tare da ma'aikantansa mata ba danginmu ba ne? Kin ga zai je shikar bali yau a masussuka. 3 Don haka, sai ki yi wanka ki yi kwalliya, ki sa tufafinki mafi kyau, ki tafi masussukar. Amma kada ki yarda ya gan ki har sai ya gama ci da sha. 4 Amma bayan ya kwanta, sai ki kula da inda ya kwanta don in an jima ki je wurinsa, ki yaye mayafinsa, ki kwanta a ƙafafunsa. Daga nan zai faɗa miki abin da za ki yi" 5 Rut ta ce wa Na'omi, "Zan yi duk abin da ki ka ce." 6 To sai ta tashi ta tafi masussukar, ta kuma bi umarnin surukarta. 7 Bayan Bo'aza ya ci ya sha zuciyarsa na annashuwa, sai ya je don ya kwanta a ƙarshen tarin hatsinsa. Daga nan sai ta lallaɓa ta yaye ƙafafunsa, ta kwanta. 8 Can wajen tsakar dare bayan mutumin ya farka, sai ya juya kawai sai ya ji mace kwance a ƙafafunsa! 9 Ya ce, "Ke wacece?". Ta ce, "Ni ce Rut baiwarka. Gama kai danginmune na kusa, sai ka bude mayafinka ka rufe ni." 10 Bo'aza ya ce '"Yata, Yahweh ya sa miki albarka. Yanzu a ƙarshe kin nuna kirki fiye da na farko, saboda ba ki je wurin matasa, ko matalauta, ko mawadata ba. 11 Yanzu, 'yata, ka da ki ji tsoro! Zan yi miki duk abin da ki ka ce, don duk mutanen garin nan sun san ke mace ce da ta can-canta. 12 Gaskiya ne ni dangi ne, amma akwai ɗan'uwan da ya fi kusa da ku fiye da ni. 13 Yanzu sai ki tsaya nan, da safe kuma in zai cika hakin ɗan'uwa a kanki to ya yi dai-dai, sai ya cika, Amma idan ba zai cika hakin ɗan'uwa ba to ni zan cika hakin ɗan'uwa a kanki, na rantse da Yahweh. Ki kwanta har sai da safe." 14 To sai ta kwanta a ƙafafunsa har sai da gari ya waye. Amma ta tashi tun kamin a fara gane mutane da sassafe. Don Bo'aza ya ce, "Don ka da a san cewa mace ta zo massusukar" 15 Bo'aza ya ce, "Kawo gyalenki ki shimfiɗa." Bayan ta yi haka, sai ya auna ma ta bali tiya shida a ciki ya dora ma ta. Daga nan sai ya tafi gari. 16 Bayan Rut ta dawo wurin surukarta sai ta ce, "Yaya ki ka yi ɗiyata?." Rut ta faɗa ma ta duk abin da mutumin ya yi ma ta. 17 Ta ce, "Wannan tiya shida ta bali shi ne ya ba ni, don ya ce, "Kada ki koma wurin surukarki ba tare da komai ba". 18 Sai Na'omi ta ce, "Yata ki zauna a nan, har sai kin san yadda al'amarin zai zama, don mutumin ba zai huta ba har sai ya gama wannan al'amarin yau."

Sura 4

1 To sai Bo'aza ya tashi ya tafi ƙofar gari ya zauna a can. Ba da jimawa ba, sai ga wani daga cikin dangin Na'omi na kusa wanda Bo'aza ya yi maganarsa ya zo zai wuce. Bo'aza yace da shi. "Abokina, zo nan ka zauna." Sai mutumin ya zo ya zauna. 2 Sai Bo'aza ya kira dattawan garin guda goma ya ce, "Ku zauna nan." Sai suka zauna. 3 Bo'aza yace da ɗan'uwan na kusa, "Na'omi, da ta dawo daga ƙasar Mowab, za ta sayar da wata gonar ɗa'uwanmu Elimelek. 4 Na yi tunanin in sanar da kai in kuma yi maka magana, 'ka saye ta a gaban waɗanda ke zaune tare da mu a nan, da a gaban dattawan mutanena, In har kana so ka fanshe ta. Amma in ba ka so ka fansa sai ka faɗa mani don in sani, don ba wanda ya dace ya fanshe ta daga kai sai ni a bayanka. "Sai mutumin ya ce zan fanshe ta." 5 Sai Bo'aza yace "A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, dole ne kuma ka haɗa da Rut 'yar Mowabawa, matar marigayin, don a tada sunan marigayin akan gãdonsa." 6 Sai wannan ɗan'uwan na kusa ya ce ba zan iya fansar ta don kaina ba, ba tare da ɓata nawa gãdon ba. Ka ɗauki tawa damar ta fansar don kanka, don ba zan iya fansar ta ba." 7 To wannan ita ce al'adar Isra'ila a waɗancan kwanakin akan al'amuran fansa da kuma canjin kayayyaki. Don a tabbatar da komai, sai mutum ya cire takalminsa ƙafa ɗaya ya ba maƙwabcinsa, haka ake yin yarjejeniyar da ta dace a Isra'ila. 8 To sai ɗan'uwan mafi kusa ya ce da Bo'aza, "Ka saye ta don kanka," sai ya tuɓe takalminsa. 9 Daga nan sai Bo'aza yace da dattawan da dukkan jama'ar, "Ku ne shaidu cewa yau na saye dukkan mallakar Elimelek, da duk abin da ke na Kiliyon da Mahlon daga hannun Na'omi. 10 Bugu da ƙari game da Rut ɗiyar Mowab, matar Mahlon; ita ma na mallake ta ta zama matata, don in tãda sunan marigayin a kan gãdonsa, don in kafa ma sa zuriya, don kada a yanke sunansa daga cikin 'yan'uwansa da kuma gidansa. Yau ku ne shaidu." 11 Dukkan mutanen da ke ƙofar da dattawan su ka ce, "Mu shaidune. Dãma Yahweh ya sa matar da ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu, su biyu da su ka kafa gidan Isra'ila; kuma dãma ka azurta a Ifarata ka kuma yi suna a Betlehem 12 Dãma gidanka ya zama kamar na Ferez wanda Tamar ta haifawa Yahuda, Ta wurin zuriyar da Yahweh zai ba ka tare da wannan matashiyar mata." 13 Sai Bo'aza ya ɗauki Rut, daga nan ta zama matarsa. Sai ya kwana da ita, sai Yahweh ya sa ta yi ciki, sai ta haifi ɗa namiji. 14 Sai mataye su ka ce da Na'omi, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda bai bar ki yau ba ɗan'uwa na kusa ba, wannan yaron. Dãma ya zama sanannen mutum a Isra'ila. 15 Dãma ya zama mai dawo maki da rayuwa ya kuma inganta kwanakinki na tsufa, saboda wannan surukar ta ki, wadda ta ƙaunace ki, wadda ta fi 'ya'ya bakwai maza a gare ki, ce ta haife shi." 16 Na'omi ta ɗauki ɗan, ta rungume shi a kafaɗarta, ta kuma kula da shi. 17 Mataye maƙwabta su ka ba shi suna cewa, "An haifawa Na'omi ɗa," Sai suka raɗa masa suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, wanda ya haifi Dauda. 18 To waɗanan su ne zuriyar Ferez: Ferez ya haifi Hezron, 19 Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab, 20 Aminadab ya haifi Nahshon, Nahshon ya haifi Salmon, 21 Salmon ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obed, 22 Obed ya haifi Yesse, Yesse ya haifi Dauda.

Littafin Sama'ila Na Farko
Littafin Sama'ila Na Farko
Sura 1

1 Akwai wani mutumin Ramatayim ta Zufiyawa, ta ƙasar tudu na Ifraim; Sunansa Elkana ɗan Yeroham ɗan Elihu ɗan Tohu ɗan Zuf, Ifraimiye. 2 Yana da mata biyu; Sunan ta farkon Hannatu, sunan ta biyun kuma Fenina. Fenina na da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta da ko ɗaya. 3 Wannan mutum yakan fita daga birninsa shekara bayan shekara domin ya yi sujada ya kuma yi hadaya ga Yahweh mai runduna a Shilo. 'Ya'yan Eli maza guda biyu, Hofni da Finehas, firistocin Yahweh, suna wurin. 4 Idan ranar ta zo wadda Elkana ke yin hadaya ko wace shekara, koyaushe yakan ba Fenina matarsa kason nama mai yawa, da dukkan 'ya'yan ta maza da mata. 5 Amma ga Hannatu a koyaushe yakan ba ta kaso ruɓi biyu, gama yana ƙaunarta, koda ya ke Yahweh ya rufe mahaifarta. 6 Kishiyarta kuma na tsokanar ta ƙwarai da gaske domin ta tunzura ta, saboda Yahweh ya rufe mahaifarta. 7 Domin haka shekara bayan shekara, idan ta tafi gidan Yahweh tare da iyalinta, kishiyarta a koyaushe tana tsokanar ta. Saboda haka takan yi kuka ta ƙi cin komai. 8 Elkana mijinta a koyaushe sai ya ce mata, "Hannatu, me yasa ki ke kuka? Me yasa ba za ki ci komai ba? Me yasa zuciyarki ta ɓaci? Ban fi 'ya'ya maza goma ba a gareki?" 9 A ɗaya daga cikin irin wannan tattaruwar, sai Hannatu ta tashi bayan da suka gama ci da sha a Shilo. Yanzu dai Eli firist yana zaune a bisa mazauninsa a ƙofar hanyar zuwa shiga Haikalin Yahweh. 10 Tana cikin ɓacin rai mai zurfi; ta yi addu'a ga Yahweh ta kuma yi kuka mai ɗaci. 11 Sai ta yi wa'adi ta ce, "Yahweh mai runduna, idan za ka dubi azabar baiwarka ka kuma tuna da ni, ba za ka kuma manta da baiwarka ba, amma za ka ba baiwarka ɗa namiji, daga nan zan ba da shi ga Yahweh dukkan kwanakin ransa, ba bu kuma wata aska da za ta taɓa kansa ko kaɗan." 12 Yayin da ta ci gaba da addu'a a gaban Yahweh, Sai Eli ya lura da bakinta. 13 Hannatu ta yi magana a zuciyarta. Leɓunanta na motsawa, amma ba a jin muryarta. Sai Eli ya yi tunanin ta bugu ne. 14 Eli ya ce mata, "Har yaushe za ki zama cikin buguwa? ki kawar da ruwan inabinki." 15 Hannatu ta amsa, "A a, shugabana, ni mace ce mai ruhu cike da baƙinciki. Ban sha ruwan inabi ba ko abin sha mai ƙarfi, amma ina kwarara rai na ne a gaban Yahweh. 16 Kada ka ɗauki baiwar ka a matsayin mace marar kunya; Ina magana ne daga cikin yalwar damuwata da tsokanata." 17 Daga nan Eli ya amsa ya ce, "Tafi cikin salama; bari Allah na Isra'ila ya ba ki abin nan da ki ka roƙe shi." 18 Ta ce, "Bari baiwarka ta sami tagomashi a gaban ka." Daga nan matar ta yi tafiyarta ta kuma ci abinci; fuskarta kuma ba ta sake nuna baƙinciki ba. 19 Suka tashi da sassafe suka kuma yi sujada a gaban Yahweh, daga nan kuma suka sake komawa gidansu a Rama. Elkana ya kwana da Hannatu matarsa, Yahweh kuma ya tuna da ita. 20 Da lokacin ya zo, Hannatu ta ɗauki ciki ta haifi ɗa namiji. Ta kira sunansa Sama'ila, tana cewa, "Saboda na roƙo shi daga Yahweh." 21 Sa'an nan kuma, Elkana da dukkan gidansa suka tafi domin su miƙa wa Yahweh hadaya ta shekara - shekara ya kuma biya wa'adinsa. 22 Amma Hannatu ba ta tafi ba; ta riga ta faɗa wa mijinta, "Ba zan tafi ba sai an yaye yaron; daga nan zan kawo shi, domin ya kasance gaban Yahweh ya kuma zauna wurin har abada." 23 Elkana mijinta ya ce da ita, "Ki yi abin da ya yi dai-dai a gare ki. Ki jira sai kin yaye shi; Yahweh ya tabbatar da maganarsa, kaɗai." Sai matar ta jira ta kuma yi renon ɗanta har sai da ta yaye shi. 24 Da ta yaye shi, sai ta ɗauke shi tare da ita, tare da sã ɗan shekara uku, da gari mudu ɗaya, da kwalbar ruwan inabi ɗaya, ta kawo shi kuma gidan Yahweh a Shilo. To har yanzu dai yaron ƙarami ne. 25 Suka yanka sãn, suka kuma kawo yaron wurin Eli. 26 Ta ce, "Ya, shugabana! muddin ka na raye, shugabana, ni ce matar nan da ta tsaya kusa da kai tana addu'a ga Yahweh. 27 Domin wannan yaron na yi addu'a kuma Yahweh ya ba ni abin da na roƙa daga gare shi. 28 Na bayar da shi ga Yahweh, dukkan tsawon ransa an ba da shi rance ga Yahweh." Daga nan ya yi sujada ga Yahweh a wurin.

Sura 2

1 Hannatu ta yi addu'a ta ce, "Zuciyata ta ɗaukaka Yahweh. ‌Ƙahona ya ɗaukaka cikin Yahweh. Bakina ya yi kuri mai yawa akan maƙiyana, saboda na yi farinciki cikin cetonka. 2 Babu wani mai tsarki kamar Yahweh, Gama babu wani baya gare ka; babu wani dutse kamar Allahnmu. 3 Kada a ƙara kuri cikin matuƙar girman kai; kada wata gadara ta fito daga bakinku. Gama Yahweh Allah ne masani; shi ne ke gwada ayyuka. 4 Bakan mutane masu ƙarfi ya karye, amma waɗanda suka yi tuntuɓe suka sanya ƙarfi kamar ɗamara. 5 Waɗanda suke a cike sun bayar da kansu haya domin gurasa; waɗanda suke jin yunwa sun daina jin yunwa. Bakarariya mata haifi bakwai, amma mace mai 'ya'ya da yawa ta yi yaushi. 6 Yahweh na kashewa kuma ya rayar. Yana korawa ƙasa zuwa lahira yana kuma ɗagawa sama. 7 Yahweh yana maida wasu mutane talakawa wasu kuma masu arziki. Yana ƙasƙantarwa yana kuma ɗaukakawa sama. 8 Yana ɗaga talaka daga turɓaya. Yana ɗaukaka mabuƙaci daga tarin toka ya sa ya zauna tare da sarakuna ya kuma sa ya gaji wurin zama mai daraja. Gama ginshiƙan duniya na Yahweh ne ya kuma ɗora duniyar a bisan su. 9 Yana bida sawayen amintattun mutanensa, amma za a rufe bakin mai mugunta cikin duhu, gama babu mai yin nasara ta ƙarfi. 10 Waɗanda ke tsayayya da Yahweh zasu karye gutsu-gutsu; zaya yi cida daga sama a kansu. Yahweh za ya hukunta ƙarshen duniya; zaya bada ƙarfi ga sarkinsa ya kuma ɗaukaka ƙahon shafaffensa." 11 Daga nan Elkana ya tafi Rama, zuwa gidansa. Yaron ya bauta wa Yahweh a gaban Eli firist. 12 Yanzu dai 'ya'yan Eli mutane ne marasa cancanta. Ba su san Yahweh ba. 13 Al'adar firistoci da mutanen shi ne idan kowanne mutum ya miƙa hadaya, bawan firist za ya zo da cokali mai yatsu uku a hannunsa, yayin da naman ke tafasa. 14 Za ya caka cokalin a cikin kaskon, ko garwar, ko tanderun, ko tukunyar. Duk abin da cokalin ya tsamo sama firist za ya ɗaukar wa kansa. Haka suka riƙa yi a Shilo ga dukkan Isra'ilawa da suka zo wurin. 15 Mafi ɓaci, kafin su ƙona kitsen, bawan firist za ya zo, ya kuma cewa mutumin da ke yin hadayar, "Bayar da naman gashi domin firist; domin ba za ya karɓi dafaffen nama ba daga gare ka, sai ɗanye kaɗai." 16 Idan mutumin ya ce masa, "Dole ne su ƙona kitsen da farko, daga nan sai ka ɗauki iya yadda kake so." Daga nan sai ya ce, "A a, yanzu zaka ba ni; idan ba haka ba, zan ɗauka da ƙarfi da yaji." 17 Zunubin waɗannan yara maza ya yi girma sosai a gaban Yahweh, gama sun wulaƙanta baikon Yahweh. 18 Amma Sama'ila ya bauta wa Yahweh a matsayin yaro yana sanye da falmarar linin. 19 Mahaifiyarsa takan yi masa ƙaramar riga ta kuma kai masa daga shekara zuwa shekara, idan ta zo tare da mijinta domin miƙa hadaya ta shekara-shekara. 20 Eli za ya albarkaci Elkana da matarsa ya ce, "Bari Yahweh ya ba ka ƙarin 'ya'ya ta wurin wannan matar saboda roƙon da ta yi ga Yahweh." Daga nan sai su koma nasu gidan. 21 Yahweh ya sake taimakon Hannatu, ta kuma sake ɗaukar ciki. Ta haifi 'ya'ya maza uku mata biyu. Yayin da ake haka, yaron kuwa Sama'ila ya yi girma gaban Yahweh. 22 Yanzu dai Eli ya tsufa; ya ji kuma dukkan abin da 'ya'yansa maza ke yi ga dukkan Isra'ila, da yadda suke kwana da dukkan matayen da ke bauta a ƙofar shiga rumfar taruwa. 23 ya ce masu, "Me yasa kuke yin irin abubuwan nan? gama na ji ayyukan muguntarku daga dukkan mutanen nan." 24 A'a, 'ya'ya na; Ba rahoto bane mai kyau da na ji. Ku na sa mutanen Yahweh rashin biyayya. 25 Idan mutum ɗaya ya yi zunubai gãba da wani, Allah za ya hukunta shi; amma idan mutum ya yi zunubai gãba da Yahweh, wane ne za ya yi magana a madadinsa?" Amma ba zasu saurari muryar mahaifinsu ba, saboda Yahweh ya shirya kashe su. 26 Yaron kuwa Sama'ila ya girma, ya ƙaru a tagomashi tare da Yahweh tare kuma da mutane. 27 Yanzu dai wani mutumin Allah ya zo wurin Eli ya ce ma shi, "Yahweh ya ce, 'Ban bayyana kai na ba ga gidan kakanka, sa'ad da suke a Masar cikin ƙangin gidan Fir'auna? 28 Na zaɓe shi daga cikin dukkan kabilun Isra'ila ya zama firist ɗi na, ya hau zuwa bagadi na, ya kuma ƙona turare, ya sanya falmara a gabana. Na bayar ga gidan kakanka dukkan baye-bayen mutanen Isra'ila da aka yi tare da wuta. 29 Me yasa, daga nan, ka yi ba'a ga hadayu na da baye-bayen da na buƙata a wurin da nake zama? Me yasa ka girmama 'ya'yanka fiye da ni ta wurin mai da kanka mai ƙiba tare da kowanne baikon mutane na Isra'ila?' 30 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ce, 'Na yi alƙawarin cewa gidanka, da gidan kakanka, zasu yi tafiya a gabana har abada.' Amma yanzu Yahweh ya ce, 'Ya yi nesa da ni in yi haka, gama zan girmama waɗanda ke girmama ni, amma waɗanda suka rena ni zasu sha ƙasƙanci. 31 Duba, kwanaki na zuwa da zan datse ƙarfinka da ƙarfin gidan mahaifinka, yadda ba za a sake samun tsohon mutum ba a cikin gidanka. 32 Za ka ga ƙunci a cikin wurin da nake zama. Koda ya ke abu mai kyau za a ba Isra'ila, ba za a sake samun tsohon mutum ba a gidanka. 33 Kowanne daga cikinku da ban datse ba daga bagadina, Zan kawo faɗawa ga idanunku, Zan kawo baƙinciki ga rayukanku. Dukkan mazajen da aka haifa a iyalinku zasu mutu. 34 Wannan zai zamar maka alama da zata zo bisa 'ya'yanka maza biyu, bisa Hofni da Finehas: Dukkan su zasu mutu a rana ɗaya. 35 Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai yi abin da ke cikin zuciyata da cikin raina. Zan gina masa tabbataccen gida; kuma za ya yi tafiya a gaban shafaffen sarkina har abada. 36 Duk wanda aka bari daga cikin gidanka zaya zo ya rusuna masa, yana roƙon ɓallin azurfa da gutsuren gurasa, kuma za ya ce, "Ina roƙon ka ka naɗa ni ɗaya daga cikin guraben firistoci domin in samu in ci gutsuren gurasa.""'

Sura 3

1 Yaron nan Sama'ila ya bauta wa Yahweh a gaban Eli. Maganar Yahweh ta yi ƙaranci a waɗannan kwanaki; babu yawan wahayin anabci. 2 A wannan lokaci, sa'ad da Eli, wanda idanunsa sun fara yin dishi-dishi yadda ba ya iya gani sosai, yana kwance a bisa nasa gadon. 3 Fitilar Allah bata riga ta mutu ba, kuma Sama'ila yana kwance domin ya yi barci a haikalin Yahweh, inda akwatin Yahweh ya ke. 4 Yahweh ya yi kira ga Sama'ila, wanda ya ce, "Ga ni nan." 5 Sama'ila ya ruga wurin Eli ya kuma ce, "Ga ni nan, gama ka kira ni." Eli ya ce, "Ban kira ka ba, ka sake kwantawa." Sai Sama'ila ya koma ya sake kwantawa. 6 Yahweh ya sake kira, "Samai'la." Sama'ila ya sake tashi ya tafi wurin Eli ya kuma ce, "Gani nan, gama ka kira ni." Eli ya amsa, "Ban kira ka ba, ɗana, ka sake kwantawa." 7 Yanzu dai Sama'ila bai taɓa samun wata gamuwa da Yahweh ba, ko wani saƙo daga Yahweh ya taɓa bayyana a gare shi ba. 8 Yahweh ya sake kiran Sama'ila karo na uku. Sama'ila ya sake ta shi ya tafi wurin Eli ya ce, "Ga ni nan, gama ka kira ni." Daga nan Eli ya fahimci cewa Yahweh ya kira yaron. 9 Daga nan Eli ya cewa Sama'ila, "Ka je ka sake kwantawa kuma, idan ya sake kiran ka, dole ka ce, 'Yi magana, Yahweh, gama bawanka yana saurare."' Daga nan Sama'ila ya tafi kuma ya sake kwantawa a na sa wurin kuma. 10 Yahweh ya zo ya tsaya; ya yi kira kamar sauran lokuttan, "Sama'ila, Sama'ila." Daga nan Sama'ila ya ce, "Yi magana, gama bawanka yana sauraro." 11 Yahweh ya cewa Sama'ila, duba, Ina gaf da yin wani abu a Isra'ila wanda kunnuwan dukkan wanda za ya ji za su karkaɗa. 12 A wannan rana zan aiwatar ga Eli dukkan abin da na ce game da gidansa, daga farko har ƙarshe. 13 Na gaya masa ina gaf da hukunta gidansa karo ɗaya tak domin zunubin da ya riga ya sani, saboda 'ya'yansa sun kawo la'ana a kansu bai kuma hana su ba. 14 Saboda wannan na yi rantsuwa game da gidan Eli cewa zunuban gidansa ba za a iya yi masu kaffara ba da hadaya ko baiko." 15 Sama'ila ya kwanta har gari ya waye; daga nan ya buɗe ƙofofin gidan Yahweh. Amma Sama'ila ya ji tsoron gaya wa Eli game da wahayin. 16 Daga nan Eli ya kira Sama'ila ya ce, "Sama'ila, ɗana." Sama'ila ya ce, "Ga ni nan." 17 ya ce, "Wacce magana ce ya faɗi maka? Ina roƙon ka kada ka ɓoye mani. Bari Allah ya yi maka haka, fiye da haka ma, idan ka ɓoye wani abu daga gare ni a dukkan maganganun da ya faɗi maka." 18 Sama'ila ya faɗi masa dukkan abu; bai ɓoye masa komai ba. Eli ya ce, "Yahweh ne. Bari ya yi abin da ya yi kyau a gare shi." 19 Sama'ila ya yi girma, kuma Yahweh na tare dashi kuma bai bar ko ɗaya daga cikin maganganun anabcinsa ba su kãsa zama gaskiya. 20 Dukkan Isra'ila daga Dan zuwa Biyasheba suka sani cewa an naɗa Sama'ila annabin Yahweh. 21 Yahweh ya sake bayyana a Shilo, gama ya bayyana kansa ga Sama'ila a Shilo ta wurin maganarsa.

Sura 4

1 Maganar Sama'ila ta zo ga dukkan Isra'ila. Yanzu dai Isra'ila sun fita yaƙi gãba da Filistiyawa. Suka kafa sansani a Ebeneza, Filistiyawa kuma sukakafa sansani a Afek. 2 Filistiyawa suka jera domin yaƙi gãba da Isra'ila. Da aka baza yaƙin, Filistiyawa sukakayar da Isra'ila, wanda sukakashe wajen mutum dubu huɗu a filin yaƙin. 3 Da mutanen suka zo cikin sansanin, dattawan Isra'ila suka ce, "Me yasa Yahweh yakayar damu yau a gaban Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alƙawarin Yahweh a nan daga Shilo, domin yakasance a nan tare da mu, domin ya ajiye mu a tsare daga hannun maƙiyanmu." 4 Sai mutanen suka aiki mazaje zuwa Shilo; daga nan suka ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh mai runduna, wanda ke zaune a bisa kerubim. 'Ya'yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas, suna nan tare da akwatin alƙawarin Allah. 5 Da akwatin alƙawarin Yahweh ya iso cikin sansani, dukkan mutanen Isra'ila suka yi babbar kururuwa, har ƙasa ta amsa. 6 Da Filistiyawa suka ji ƙarar kururuwar, suka ce, "Me wannan ƙarar kururuwar a cikin sansani Ibraniyawa ke nufi?" Sai suka tantance cewa akwatin Yahweh ya zo cikin sansanin. 7 Filistiyawa suka tsorata; suka ce, "Wani allah ya shigo cikin sansanin." Suka ce, "Kaitonmu! Babu wani abu kamar haka da ya faru a dã! 8 Kaitonmu! Wane ne zai cece mu daga ƙarfin waɗannan alloli masu iko? Waɗannan allolin ne sukakaiwa Masarawa hari da allobai iri-iri a cikin jeji. 9 Ku yi ƙarfin hali, ku kuma zama mazaje, ku Filistiyawa, ko kuwa ku zama bayi ga Ibraniyawa, kamar yadda suke bayi a gare ku. Ku zama mazaje, ku kuma yi faɗa." 10 Filistiyawa suka yi faɗa, aka kumakayar da Isra'ila. Kowanne mutum ya tsere zuwa gidansa, kisan da aka yi babba ne ƙwarai; gama sojojin ƙasa dubu talatin ne daga Isra'ila suka faɗi. 11 Aka ɗauke akwatin Allah, 'ya'yan Eli maza biyu kuma, Hofni da Finehas, suka mutu. 12 Wani mutumin Benyamin ya gudu daga fagen yaƙin ya kuma zo Shilo a ranar nan, ya iso da tufafinsa a yage da kuma ƙasa bisakansa. 13 Da ya iso, Eli na zaune bisa mazauninsa a bakin hanya yanakallo saboda zuciyarsa na fargaba tare da damuwa domin akwatin Allah. Da mutumin ya shiga cikin birnin ya faɗi labarin, dukkan birnin aka yi kuka. 14 Da Eli ya ji ƙarar kukan, ya ce, "Mene ne ma'anar wannan yamitsin?" Mutumin ya zo da sauri ya kuma faɗa wa Eli. 15 Yanzu dai Eli shekarunsa tasa'in da takwas; idanunsa ba su fuskanta dai-dai, kuma baya gani. 16 Mutumin ya cewa Eli, "Ni ne na zo daga fagen yaƙin. Na gudo daga yaƙin yau." Eli ya ce, "Ya abin ya tafi, ɗa na?" 17 Mutumin da yakawo labarin ya amsa kuma ya ce, "Isra'ila sun gudu daga Filistiyawa. Haka kuma, babbar kayarwa takasance a tsakanin mutanen. Haka kuma, 'ya'yan ka maza biyu, Hofni da Finehas, sun mutu, akwatin Allah kuma an ɗauke." 18 Da ya faɗi akwatin Allah, Eli ya fãɗi ta baya daga bisa kujerarsa ta gefen ƙofa. Wuyansa yakarye, ya kuma mutu, saboda ya tsufa kuma yana da nauyi. ya yi alƙalancin Isra'ila shekaru arba'in. 19 Yanzu dai surukarsa, matar Finehas, tana da ciki kuma ta yi gaf da haihuwa. Da ta ji labarin an cafke akwatin Allah da surukinta da mijinta kuma sun mutu, ta durƙusa kuma ta haihu, amma zafin naƙudarta ya mamaye ta. 20 Wajen lokacin mutuwarta matan da ke yi mata unguwar zoma suka ce mata, "Kada ki ji tsoro, gama kin haifi ɗa namiji." Amma ba ta amsa ba ko ta ɗauki abin da suka ce a zuciya. 21 Ta raɗa masa suna Ikabod, cewa, "‌Ɗaukaka ta tafi da ga Isra'ila!" domin an cafke akwatin Allah, saboda kuma surukinta da mijinta. 22 Ta ce, "‌Ɗaukaka ta tafi daga Isra'ila, saboda an cafke akwatin Allah."

Sura 5

1 Yanzu dai Filistiyawa sun cafke akwatin Allah, su ka kumakawo shi daga Ebeneza zuwa Asdod. 2 Filistiyawa suka ɗauki akwatin Allah, sukakawo shi cikin gidan Dagon, suka jera shi a gefen Dagon. 3 Da mutanen Asdod suka tashi da sassafe washegari, duba, Dagon ya faɗi ƙasa da fuskarsa ƙasa gaban Yahweh. Sai suka ɗauki Dagon suka kuma sake jera shi a wurinsa. 4 Amma da suka tashi da sassafe washegari, duba, Dagon ya faɗi ƙasa da fuskarsa ƙasa a gaban akwatin Yahweh. Kan Dagon da hannuwansa suna kwance datsastsu a hanyar ƙofa. Gangar jikin Dagon kawai ya rage. 5 Wannan ne yasa, har yau ma, firistocin Dagon da ko wane ne ya zo cikin gidan Dagon ba ya taka hanyar ƙofar Dagon a Asdod. 6 Hannun Yahweh kuwa ya yi nauyi a bisa mutanen Asdod. Ya lalatar da su ya azabce su da marurai. Asdod duk da kewayenta. 7 Da mutanen Asdod suka lura da abin da ke faruwa, suka ce, "Akwatin Allahn Isra'ila dole ba za ya zauna ta re da mu ba, saboda hannunsa ya yi tsanani gãba da mu da gãba da allahnmu Dagon." 8 Sai suka aika suka kuma tattaro tare dukkan shugabannin Filistiyawa; suka ce masu, "Me za mu yi da akwatin Allah na Isra'ila?" Suka amsa, "Bari akawo akwatin Allah na Isra'ila zuwa Gat." Sai suka ɗauki akwatin Allah na Isra'ila zuwa can. 9 Amma bayan da sukakawo shi wurin, hannun Yahweh ya yi gãba da birnin, ya sanya babbar ruɗewa. Ya azabtar da mutanen birnin, ƙarami da babba dukka; marurai kuma suka faso akansu. 10 Sai suka aika da akwatin Allah zuwa Ekron. Amma nan da nan da akwatin Allah ya zo cikin Ekron, Ekroniyawa suka koka, cewa, "Sun kawo mana akwatin Allah na Isra"ila domin yakashe mu da mutanenmu." 11 Sai suka aika aka tattaro tare dukkan shugabannin Filistiyawa; suka ce masu, "Ku aika da akwatin Allah na Isra'ila, bari kuma ya koma na sa wurin, domin kada yakashe mu da mutanenmu." Domin akwai razana mai mutuwa cikin dukkan birnin; hannun Allah yana da nauyi sosai a wurin. 12 Mutanen da ba su mutu ba an azabce su da marurai, kukan birnin kuma ya hau zuwa sammai.

Sura 6

1 Yanzu dai akwatin Yahweh na cikin ƙasar Filistiyawa har watanni bakwai. 2 Daga nan Mutanen Filistiyawa suka kira firistoci da masu sihiri; suka ce masu, "Me zamu yi da akwatin Yahweh? ku gaya mana yadda zamu aika da shi zuwa ƙasarsa." 3 Firistoci da masu sihiri suka ce, "Idan kuka aika da akwatin Allah na Isra'ila, kada ku aika da shi ba tare da kyauta ba; ta ko ƙaƙa ku aika masa da baiko na laifi. Daga nan zaku warke, daga nan kuma zaku ga ne dalilin da yasa hannunsa bai ɗauke ba daga bisanku har yanzu. 4 Daga nan suka ce, "Mene ne za ya zama baiko na laifin da zamu maida masa?" Suka maida amsa, "Marurai na zinariya biyar da ɓerayen zinariya biyar, biyar lissafin yawa ne wanda ya yi dai-dai da lissafin yawan shugabannin Filistiyawa. Domin annoba iri ɗaya ce ta azabce ku da shugabanninku. 5 Dole ku yi marurai na kwaikwayo, da ɓerayen kwaikwayo da suka addabi ƙasar, ku kuma bada ɗaukaka ga Allah na Isra'ila. Wataƙila zai ɗauke hannun sa daga gare ku, daga allolinku, daga kuma ƙasarku. 6 Me yasa zaku taurare zukatanku, kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Ta haka Allah na Isra'ila ya tsananta masu da zafi; Ashe Masarawan basu fitar da mutanen ba, suka kuma tafi? 7 To yanzu, ku shirya amalanke da shanu biyu masu shayarwa waɗanda ba a taɓa ɗaurawakarkiya ba. Ku ɗaura shanun ga amalanken, amma ku ɗauki 'yan maruƙansu daga gare su, ku kai gida. 8 Daga nan ku ɗauki akwatin Yahweh ku sa cikin amalanken. Ku sanya siffofin zinariyar da zaku maida masa a matsayin baiko na laifi cikin wani akwatin a gefensa. Daga nan ku aika da shi kuma bari ya tafi hanyarsa. 9 Daga nan ku kalla; Idan ya yi tafiyarsa bisa hanya zuwa cikin ƙasarsa zuwa Bet Shemesh, to Yahweh ne ya zartar da wannan babban bala'i. Amma idan ba haka ba, daga nan za mu sani cewa ba hannunsa ba ne ya azabtar damu ba; maimakon haka, zamu sani cewa ya faru da mu ne hakakawai." 10 Mutanen suka yi yadda aka gaya masu; suka ɗauki shanu biyu masu shayarwa; suka ɗaura su ga amalanken, suka tsare 'yan maruƙansu a gida. 11 Suka sanya akwatin Yahweh a cikin amalanken, tare da akwatin da ke ɗauke da ɓerayen zinariyar da sarrafaffun maruransu. 12 Shanun suka tafi a miƙe a hanyar Bet Shemesh. Suka tafi bisa babbar hanya, suna tafiya suna kuka, ba su kumakauce daga hanya ba ko zuwa dama ko zuwa hagu. Shugabannin Filistiyawa suka bi bayansu har zuwakan iyakar Bet Shemesh. 13 Yanzu dai mutanen Bet Shemesh suna girbin alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga idanunsu suka ga akwatin, suka yi farinciki. 14 Amalanken ya iso cikin gonar Yoshuwa daga Bet Shemesh ya kuma tsaya a wurin. Wani babban dutse na wurin, suka tsinke itacen amalanken, suka miƙa shanun a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh. 15 Lebiyawa suka sauke akwatin Yahweh da akwatin da ke tare da shi, inda siffofin zinariyar suke, suka ɗora su bisa babban dutsen. Mutanen Bet Shemesh suka miƙa baye-baye na ƙonawa suka kuma yi hadayu a wannan rana ga Yahweh. 16 Da shugabannin Filistiyawa biyar suka ga haka, suka koma Ekron a ranar. 17 Waɗannan ne maruran zinariya da Filistiyawa suka maido domin baiko na laifi ga Yahweh: ɗaya domin Asdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Askelon, ɗaya domin Gat, ɗaya domin Ekron.‌ 18 Ɓerayen zinariyar ma lissafinsu ya yi dai-dai da lissafin dukkan biranen Filistiyawa da sukakasance na shugabannin biyar, dukkansu tsararrun birane ne da ƙauyukansu. Babban dutsen, gefen da aka ajiye akwatin Yahweh, ya zama shaida har yau a cikin filin Yoshuwa Betshemiye. 19 Yahweh yakai hari ga wasu daga cikin mutanen Bet Shemesh saboda sun duba cikin akwatin Yahweh. Yakashe mutum 50,070. Mutanen suka yi makoki, saboda Yahweh ya ba mutanen babban naushi. 20 Mutanen Bet Shemesh suka ce, "Wane ne zaya iya tsayawa gaban Yahweh, wannan Allah mai tsarki? daga gare mu wurin wa akwatin zaya tafi?" 21 Suka aika manzanni zuwa ga mutanen Kiriyat Yerim, cewa, "Filistiyawa sun maido da akwatin Yahweh; ku zo ku ɗauka ku kuma koma da shi tare da ku."

Sura 7

1 Mutanen Kiriyat Yerim suka zo, suka ɗauki akwatin Yahweh, suka kumakawo shi cikin gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa Eliyeza ya ajiye akwatin Yahweh. 2 Daga ranar da akwatin ya zauna a Kiriyat Yerim, lokaci mai tsawo ya wuce, shekaru ashirin. Dukkan mutanen Isra'ila suka yi makoki kuma suka yi marmarin komawa ga Yahweh. 3 Sama'ila ya cewa gidan Isra'ila gaba ɗaya, "Idan kun dawo ga Yahweh da dukkan zuciyarku, ku cire bãƙin alloli da kuma Ashtoret daga cikinku, ku juyo da zukatanku ga Yahweh, ku kuma yi masa sujada shi kaɗai, daga nan zai kuɓutar daku daga hannun Filistiyawa." 4 Daga nan mutanen Isra'ila suka fitar da Ba'aloli da Ashtoret, suka kuma yi sujada ga Yahweh kaɗai. 5 Daga nan Sama'ila ya ce, "Ku kawo a tattare dukkan Isra'ila zuwa Mizfa, zan kuma yi addu'a ga Yahweh domin ku." 6 Suka tattaru a Mizfa, suka jawo ruwa suka zuba kuma a gaban Yahweh. Suka yi azumi a ranar suka ce, "Mun yi zunubi ga Yahweh." A can ne Sama'ila ya sasanta saɓanai domin mutanen Isra'ila ya kuma shugabanci mutanen. 7 Yanzu da Filistiyawa suka ji mutanen Isra'ila sun taru a Mizfa, sai shugabannin Filistiyawa sukakai hari ga Isra'ila. Da mutanen Isra'ila suka ji haka, suka ji tsoron Filistiyawa. 8 Daga nan mutanen Isra'ila suka cewa Sama'ila, "Kadaka daina kira ga Yahweh Allahnmu domin mu, domin ya cece mu daga hannun Filistiyawa." 9 Sama'ila ya ɗauki ɗan rago mai shan nono ya miƙa shi gaba ɗaya a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh. Daga nan Sama'ila ya yi kuka ga Yahweh domin Isra'ila, Yahweh kuma ya amsa masa. 10 Yayin da Sama'ila ke miƙa baikon ƙonawar, Filistiyawa suka matso domin su kawo hari ga Isra'ila. Amma Yahweh ya yi kwarankwatsi da babbar ƙara a wannan rana ga Filistiyawa ya kuma watsa su cikin ruɗewa, kuma suka shakaye a gaban Isra'ila. 11 Mutanen Isra'ila suka tafi daga Mizfa, suka kuma runtumi Filistiyawa suka kumakarkashe su har ya zuwa ƙarƙashin Bet Ka. 12 Daga nan Sama'ila ya ɗauki dutse yakafa tsakanin Mizfa da Shen. Ya raɗa masa suna Ebeneza, cewa, "Har ya zuwa haka Yahweh ya taimake mu." 13 Saboda haka Filistiyawa suka shakaye ba su kuma iya shigakan iyakar Isra'ila ba. Hannun Yahweh ya yi gãba da Filistiyawa dukkan kwanakin Sama'ila. 14 Garuruwan da Filistiyawa sukakarɓe daga Isra'ila aka maidawa Isra'ila, daga Ekron zuwa Gat; Isra'ila suka maido da lardinsu daga Filistiyawa. Daga nan aka sami salama tsakanin Isra'ila da Amoriyawa. 15 Sama'ila ya yi alƙalancin Isra'ila dukkan kwanakin ransa. 16 Kowacce shekara yakan tafi ya zagaye zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa. Yana ɗaukar mataki akan saɓanai domin Isra'ila a dukkan waɗannan wurare. 17 Daga nan sai ya koma Rama, saboda gidansa na wurin; haka kuma a anan yana ɗaukar mataki akan saɓanai domin Isra'ila. Ya kuma gina bagadi a wurin ga Yahweh.

Sura 8

1 Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa alƙalai bisa Isra'ila. 2 Sunan ɗan farinsa Yowel, sunan kuma ɗansa na biyu Abiya. 3 Su alƙalai ne a Biyasheba. 'Ya'yansa ba su yi tafiya bisa hanyoyinsa ba, amma suka bi bayan ƙazamar riba. Sukakarɓi cin hanci suka danne adalci. 4 Daga nan dukkan dattawan Isra'ila suka tattaru tare suka kuma zo wurin Sama'ila a Rama. 5 Suka ce masa, "Duba, ka tsufa, kuma 'ya'yanka ba su yi tafiya cikin hanyoyinka ba. Ka naɗa mana sarki ya yi hukunci akan mu kamar sauran al'ummai." 6 Amma Sama'ila bai ji daɗi ba da suka ce, "Ka bamu sarki ya yi hukuncinmu." Sai Sama'ila ya yi addu'a ga Yahweh. 7 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Ka yi biyayya da muryar mutanen a cikin dukkan abin da suka ce maka; gama bakai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarki a bisansu. 8 Suna aikatawa yanzu dai-dai yadda suka yi tun daga ranar dana fito da su daga Masar, suka yashe ni, da bautar wasu alloli, haka kumakaima suke yi maka. 9 Yanzu ka saurare su; ammaka gargaɗe su da aniya bari kuma su san yadda sarkin zai yi mulki akansu." 10 Sai Sama'ila ya faɗi dukkan maganganun Yahweh ga mutanen da ke tambaya domin sarki. 11 Ya ce, "Wannan zai zama al'adar sarkin da zai yi mulki a bisanku. Zai ɗauki 'ya'yanku maza ya naɗa su gakarusansa ya kuma sa su zama mutanen dawakansa, su kuma yi gudu a gaban karusansa. 12 Zai naɗa wakansa ofisoshin bataliyar sojoji dubbai, da ofisoshin bataliyar sojoji hamsin. Zai sa wasu su yi noman gonarsa, wasu suyi girbin amfaninsa, wasu kuma suyi masa makaman yaƙi dakayan karusansa. 13 Zai kuma ɗauki 'ya'yanku mata su zama masu yi masa turare, da girke-girke, da gashe-gashe. 14 Zai ɗauki gonakinku mafi kyau, da garkunan inabinku, da kuma fadamunku na itatuwan zaitun, ya bayar dasu ga bayinsa. 15 Zai ɗauki kashi goma daga cikin hatsinku da garkarku ya kuma ba ofisoshinsa da bayinsa. 16 Zai ɗauki bayinku maza da bayinku mata da mafi nagarta na matasanku maza da jakanku; zai sanya su duka su yi masa aiki. 17 Zai ɗauki kashi goma daga cikin garken dabbobinku, kuma za ku zama bayinsa. 18 Daga nan a wannan rana za ku koka game da sarkinku wanda kuka zaɓarwakanku; amma Yahweh ba zai amsa maku ba a ranar." 19 Amma mutanen suka ƙi sauraron Sama'ila; suka ce, "A a! dole sarki yakasance a bisanmu 20 saboda mu zamakamar dukkan sauran al'ummai, saboda kuma sarkinmu ya hukunta mu ya kuma fita a gabanmu ya kuma yi faɗan yaƙe-yaƙenmu." 21 Da Sama'ila ya ji dukkan maganganun mutanen sai ya maimaita su a kunnuwan Yahweh. 22 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Ka yi biyayya da muryarsu ka kuma sa wani ya zama sarki domin su." Sai Sama'ila ya cewa mutanen Isra'ila, "Kowanne mutum dole ya tafi nasa birnin."

Sura 9

1 Akwai wani mutum a Benyamin, sanannen mutum. Sunansa Kish ɗan Abiyel ɗan Zeror ɗan Bekorat ɗan Afiya, ɗan wani Benyamine. 2 Yana da wani ɗa mai suna Saul, kyakkyawan saurayi. Babu wani taliki a cikin mutanen Isra'ila wanda ya ke mai asali ne fiye da shi. Dagakafaɗarsa zuwa sama yafi kowanne mutanen tsayi. 3 Yanzu dai jakan Kish, mahaifin Saul, sun ɓace. Sai Kish ya cewa ɗansa Saul, "Ka ɗauki ɗaya daga cikin bayin tare dakai; ka ta shi ka tafi neman jakan." 4 Sai Saul ya ratsa ta cikin ƙasar tudu ta Ifraim ya kuma tafi ta cikin ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Daga nan suka ratsa ta cikin ƙasar Sha'alim, amma ba su a wurin. Sai ya ratsa ta cikin ƙasar Benyaminawa, amma ba su same su ba. 5 Da suka zo ƙasar Zuf, sai Saul ya cewa bawansa da ke tare da shi, "Zo, bari mu koma, ko mahaifina na iya daina damuwa domin jakan ya fara damuwa game da mu." 6 Amma bawan ya ce masa, "Saurara, akwai mutumin Allah a cikin wannan birnin. Mutum ne da aka riƙe da daraja; duk abin da ya ce yana zama gaskiya. Mu tafi can; watakila zai iya gaya mana wacce hanya zamu bi a tafiyarmu." 7 Daga nan Saul ya cewa bawansa, "Amma idan muka je, me za mu kawo wa mutumin? Domin gurasar da ke jakarmu ta ƙare, ba bu kuma wata kyauta da za mu kawo wa mutumin Allahn. Me muke da shi?" 8 Bawan ya amsa wa Saul ya kuma ce, "Nan, akwai tare da ni kwatar shekel na azurfa da zan ba mutumin Allahn, ya gaya mana hanyar da za mu je." 9 (A dã a Isra'ila, idan mutum ya tafi neman sanin nufin Allah, zai ce, "Zo, bari mu tafi wurin mai gani." Gama annabi a yau mai gani ake kiran sa a dã.) 10 Daga nan Saul ya cewa bawansa, "Faɗar ta yi dai-dai. Zo, bari mu tafi." Sai suka tafi birnin inda mutumin Allah ya ke. 11 Yayin da suka tafi zuwa tudun birnin, sai suka sami 'yan mata na fitowa jan ruwa; Saul da bawansa suka ce masu, "Mai ganin na nan?" 12 Suka amsa, suka kuma ce, "Yana nan; kalli, yana ɗan gaba da ku. Yi sauri, gama yana zuwa birnin yau, saboda mutanen suna hadaya a yau a wuri mai bisa. 13 Da zarar kun shiga birnin zaku same shi, kafin ya hau zuwa wuri mai bisa domin cin abinci. Mutanen ba zasu ci ba sai ya zo, saboda zai albarkaci hadayar; bayan haka waɗanda aka gayyata zasu ci. yanzu ku haura, gama zaku same shi nan da nan." 14 Sai suka tafi zuwa birnin. Yayin da suke shiga birnin, suka ga Sama'ila na zuwa ta wurinsu, domin ya tafi zuwa wuri mai bisa. 15 Yanzu dai ana gobe Saul zai zo, Yahweh ya bayyanawa Sama'ila: 16 "Gobe war haka zan aiko maka wani mutum daga ƙasar Benyamin, zaka kuma naɗa shi ya zama shugaba bisa mutane na Isra'ila. za ya ceci mutanena daga hannun Filistiyawa. Domin na dubi mutanena tare da tausayi saboda kiran su domin taimako ya zo gare ni." 17 Da Sama'ila ya ga Saul, Yahweh ya ce masa, "Shi ne mutumin da na gaya maka game da shi! shi ne wanda zai yi mulki bisa mutanena." 18 Daga nan Saul ya zo kusa da Sama'ila a ƙofa kuma ya ce, "Ka gaya mani ina ne gidan mai gani?" 19 Sama'ila ya amsa wa Saul ya ce, "Ni ne mai gani. Ka hau a gabana zuwa wuri mai bisa, domin yau zaka ci tare da ni. Da safe zan bar kaka tafi, kuma zan gaya maka kowanne abu da ke cikin ranka. 20 Game da jakanka da suka ɓace kwana uku da suka wuce, kadaka damu game da su, domin an same su. Daga nan akan wane ne dukkan marmarin Isra'ila yakasance? Ba akanka ba ne da kuma dukkan gidan mahaifinka?" 21 Saul ya amsa ya ce, "Ni ba Benyamine ba ne, daga mafi ƙanƙanta nakabilun Isra'ila? Ba zuriyarmu ce mafi ƙanƙanta ba a cikin dukkan zuriyar Benyamin? To me yasakake magana da ni irin haka. 22 Sai Sama'ila ya ɗauki Saul da baransa, yakawo su cikin harabar, ya zaunar da su a wuri mafi girma na waɗanda aka gayyata, waɗanda kimanin mutum talatin ne. 23 Sama'ila ya cewa mai girkin, "Kakawo kason da na baka, wanda na ce maka, 'Ka ajiye shi a gefe."' 24 Sai mai girkin ya ɗauko cinyar da abin da ke bisanta ya kuma sanya a gaban Saul. Daga nan Sama'ila ya ce, "Kalli abin da aka ajiye an sanya a gabanka. Ka ci, saboda an ajiye maka har zuwa zaɓaɓɓen lokaci, daga lokacin da na ce, 'Na gayyaci mutanen."' Sai Saul ya ci tare da Sama'ila a ranar. 25 Da suka sauko daga wuri mai bisa zuwa cikin birnin, Sama'ila ya yi magana da Saul a bisa saman rufi. 26 Daga nan da gari ya waye, Sama'ila ya yi kira ga Saul a bisa saman rufi ya kuma ce, "Ta shi, domin in aika dakai kan hanyarka." Sai Saul ya tashi, da shi da Sama'ila kuma dukka suka fita bisa titi. 27 Suna cikin tafiya zuwa waje da birnin, Sama'ila ya cewa Saul, "Ka cewa baran ya tafi gaba da mu" - sai ya tafi gaba - "amma dole ka tsaya a nan na ɗan lokaci, domin in shelar da saƙon Allah a gare ka."

Sura 10

1 Sai Sama'ila ya ɗauki kwalbar mai, ya zuba akan Saul, ya kuma sumbace shi. Ya ce, "Ba Yahweh ya shafe ka baka zama shugaba bisa gãdonsa? 2 Idan ka bar ni yau, zaka sami mutum biyu kusa dakabarin Rahila, cikin lardin Benyamin a Zelza. Zasu ce maka, 'Jakan dakake nema an same su. Yanzu mahaifinka ya daina kula wa da jakan yana damuwa game dakai, cewa, "Me zanyi game da ɗa na?"' 3 Daga nan zaka tafi daga wurin, zaka kuma zo rimin Tabor. Mutane uku masu tafiya wurin Allah a Betel zasu gamu dakai a wurin, ɗaya na ɗauke da 'yan awaki uku, wani kuma na ɗauke da dunƙulen gurasa uku, wani kuma na ɗauke da salkar inabi. 4 Zasu gaishe ka su baka dunƙulen gurasa biyu, wanda zakakarɓa daga hannuwansu. 5 Bayan wannan, zaka zo tudun Allah, inda sansanin Filistiyawa ya ke. Idan ka isa birnin, zaka iske ƙungiyar annabawa na saukowa daga wuri mai bisa tare da algaita, da tambari, dakakaki, da sarewa, a gabansu; za su riƙayin anabci. 6 Ruhun Yahweh zai abko maka, zaka kuma yi anabci tare da su, zaka kuma sauya zuwa wani mutum daban. 7 Yanzu, idan waɗannan alamu suka zo maka, ka aiwatar da duk abin da hannunka ya sami damar yi, gama Allah na tare dakai. 8 Ka gangara gaba da ni zuwa Gilgal. Daga nan zan gangaro zuwa gare ka in miƙa baye-baye na ƙonawa in kuma yi hadayar baye-baye na salama. Ka jira kwana bakwai har sai na zo gare ka in kuma nuna maka abin da dole ka yi." 9 Da Saul ya juya bayansa domin ya bar Sama'ila, Allah ya ba shi wata zuciyar. Daga nan dukkan waɗannan alamu suka faru a ranar. 10 Da suka iso tudun, wata ƙungiyar annabawa ta gamu da shi, Ruhun Allah kuma ya abko bisansa har ya yi anabci tare da su. 11 Da dukkan waɗanda suka san shi a dã suka ga yana anabci tare da annabawan, mutanen suka ce da junansu, "Mene ne ya faru da ɗan Kish? Saul shi ma ɗaya daga cikin annabawan ne yanzu?" 12 Wani mutum da ya fito daga wuri ɗaya da shi ya amsa, "To wane ne mahaifinsa?" Saboda wannan, ya zama abin faɗi, "Saul shi ma ɗaya ne daga cikin annabawan?" 13 Da ya gama anabcin, ya zo wuri mai bisan. 14 Daga nan kawun Saul ya ce masa da kuma bawansa, "Ina kuka je?" Ya mai da amsa, "Neman jakan. Da muka ga ba mu iya samo su ba, muka je wurin Sama'ila." 15 Kawun Saul ya ce, "Ina roƙon kaka gaya mani abin da Sama'ila ya ce maka." 16 Saul ya amsa wakawunsa, "Ya gaya mana a sarari cewa an samo jakan." Amma bai gaya masa game da al'amarin masarautar ba, wanda Sama'ila ya yi magana akai. 17 Yanzu Sama'ila ya kira mutanen tare a gaban Yahweh a Mizfa. 18 Ya cewa mutanen Isra'ila, "Wannan ne abin da Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗa: 'Nakawo Isra'ila daga ƙasar Masar kuma na ƙwato ku daga hannun Masarawa, daga kuma hannun dukkan masarautun da suka tsananta maku.' 19 Amma yau kun watsar da Allahnku, wanda ya cece ku daga dukkan bala'o'inku da ƙuncinku; kuma kun ce da shi, 'Naɗa sarki a bisanmu.' Yanzu ku gabatar dakanku a gaban Yahweh takabilunku da zuriyarku." 20 Sai Sama'ila yakawo dukkan kabilun Isra'ila kusa, kumakabilar Benyamin aka zaɓa. 21 Daga nan yakawo kabilar Benyamin kusa ta zuriyarsu; kuma zuriyar Matirawa aka zaɓa; kuma Saul ɗan Kish aka zaɓa. Amma da suka tafi neman sa, ba a iya samun sa ba. 22 Daga nan mutanen suka so su roƙi Allah ƙarin tambayoyi, "Akwai kuma wani mutumin da zai zo?" Yahweh ya amsa, "Ya ɓoye kansa cikin kayayyaki." 23 Daga nan suka ruga suka tsamo Saul daga wurin. Da ya tsaya cikin mutanen, yafi kowanne daga cikin mutanen tsayi, dagakafaɗarsa zuwa sama. 24 Daga nan Sama'ila ya cewa mutanen, "Kun ga mutumin da Yahweh ya zaɓa?" Babu wani kamar sa daga cikin dukkan mutanen!" Dukkan mutanen suka yi sowa, "Ran sarki ya daɗe!" 25 Daga nan Sama'ila ya gaya wa mutanen al'adu da dokokin sarautar, ya rubuta su cikin littafi, ya kuma ajiye su gaban Yahweh. Daga nan Sama'ila ya sallami dukkan mutanen, kowanne mutum zuwa nasa gidan. 26 Saul shi ma ya tafi gidansa a Gibiya, tare da shi kuma wasu ƙarfafan mutane, waɗanda Allah ya taɓa zukatansu. 27 Amma wasu mutane marasa amfani suka ce, "Ta yaya wannan mutum zai cece mu?" Waɗannan mutane suka rena Saul, ba su kumaka wo masa wata kyauta ba. Amma Saul ya yi shiru.

Sura 11

1 Daga nan Nahash Ba'ammoniye ya tafi yakafa sansani ga Yabesh Giliyad. Dukkan mutanen Yabesh suka cewa Nahash, "Ka yi alƙawari da mu, kuma za mu bauta maka." 2 Nahash Ba'ammoniye ya maida amsa, "Bisa wannan matsayin zan yi alƙawari da ku, cewa zan ƙwaƙule dukkan idanunku na dama, ta wannan hanya kuma in kawo kunya bisa dukkan Isra'ila." 3 Daga nan dattawan Yabesh Giliyad suka mai da masa amsa, "Ka rabu da mu na kwana bakwai, saboda mu aika da saƙonni ga dukkan lardin Isra'ila. Daga nan, idan ba bu wani da zai cece mu, za mu sadauƙar a gare ka." 4 Manzannin suka zo Gibiya, inda Saul ke zama, suka kuma gayawa mutanen abin da ya faru. Dukkan mutanen suka yi kuka da ƙarfi. 5 Yanzu dai Saul na biye da shanu daga saura. Saul ya ce, "Me ke damun mutanen da suke kuka?" Suka gaya wa Saul abin da mutanen Yabesh suka ce. 6 Da Saul ya ji haka, Ruhun Allah ya afko masa, ya kuma fusata sosai. 7 Ya ɗauki shanun huɗa biyu, ya datse su gunduwa-gunduwa, ya kuma aika da su cikin dukkan lardin Isra'ila tare da manzanni. ya ce, "Duk wanda bai fito bayan Saul da bayan Sama'ila ba, haka za a yi wa shanun huɗarsa." Daga nan razanar Yahweh ta faɗo bisa mutanen, suka kuma fito tare a matsayin mutum ɗaya. 8 Da ya tattara su a Berek, mutanen Isra'ila dubu ɗari uku ne, mutanen Yahuda kuma dubu talatin. 9 Suka ce wa manzannin da suka zo, "Za ku cewa mutanen Yabesh Giliyad, "Gobe, lokacin da rana takai tsaka, za a ceto ku." Sai manzannin suka tafi suka gaya wa mutanen Yabesh, suka kuma yi farinciki. 10 Daga nan mutanen Yabesh suka cewa Nahash, "Gobe za mu sadaukar a gare ka, sai kumaka yi da mu duk abin da ya yi kyau a gare ka." 11 washegari Saul yasa mutanen ƙungiya uku. Suka zo tsakiyar sansanin a lokacin wayewar gari, suka kumakai hari suka kumakayar da Ammoniyawa har zafin rana. Waɗanda suka tsira su ka watse, har babu mutum biyun su da aka bari tare. 12 Daga nan mutanen suka ce wa Sama'ila, "Wane ne wanda ya ce, 'Saul zai yi mulki a bisanmu?' akawo mutanen, domin mu kashe su." 13 Amma Saul ya ce, "Babu wanda za akashe dole a wannan ranar, saboda a wannan ranar Yahweh ya ceto Isra'ila." 14 Daga nan Sama'ila ya cewa mutanen, "Ku zo, bari mu tafi Gilgal mu sabunta sarautar a can." 15 Saboda haka dukkan mutanen suka tafi Gilgal suka kuma maida Saul sarki a gaban Yahweh a Gilgal. A can suka yi hadayar baye-baye don salama a gaban Yahweh, da Saul da dukkan mutanen Isra'ila suka yi farinciki babba.

Sura 12

1 Sama'ila ya cewa dukkan Isra'ila, "Na saurari dukkan abin da kuka faɗi mani, na kuma naɗa sarki a bisanku. 2 Yanzu, ga sarkin nan na tafiya a gabanku; kuma na tsufa da furfura; kuma, 'ya'yana maza na tare da ku. Nayi tafiya a gabanku daga ƙuruciyata har wa yau. 3 Ga ni nan; ku yi shaida gãba da ni a gaban Yahweh da gaban shafaffensa. Saniyar wa na ɗauka? Jakin wa na ɗauka? Wane ne na yi wa damfara? Wane ne na tsanantawa? Daga hannun wa nakarɓi cin hanci don ya makantar da idanuna da shi? Ku shaida gãba da ni, kuma zan maido maku da shi." 4 Suka ce, "Baka cuce mu ba, baka tsananta mana, ko ka saci wani abu daga hannun wani mutum ba." 5 ya ce masu, "Yahweh ne shaida gãba da ku, kuma shafaffensa shaida ne a yau, cewa ba ku sami komai ba a cikin hannuna." Suka mai da amsa, "Yahweh ne shaida." 6 Sama'ila ya ce da mutanen, "Yahweh ne ya naɗa Musa da Haruna, wanda kuma ya fito da ubanninku daga ƙasar Masar. 7 Yanzu daga nan, ku miƙakanku, domin in yi roƙo tare da ku a gaban Yahweh game da dukkan ayyukan adalci na Yahweh, wanda ya yi domin ku da ubanninku. 8 Da Yakubu ya zo Masar, kumakakanninku suka yi kuka ga Yahweh, daga nan Yahweh ya aika da Musa da Haruna, waɗanda suka bi dakakanninku fita daga Masar suka kuma zauna a wannan wuri. 9 Amma suka manta da Yahweh Allahnsu; ya sayar da su cikin hannun Sisera, shugaban sojojin Hãzo, cikin hannun Filistiyawa, kuma cikin hannun sarkin mutanen Mowab; dukkan waɗannan suka yi faɗa gãba dakakanninku. 10 Suka yi kuka ga Yahweh suka kuma ce, 'Mun yi zunubi, saboda mun yashe da Yahweh kuma mun bauta wa Ba'aloli da Ashtatori. Amma yanzu ka cece mu daga hannun maƙiyanmu, kuma za mu bauta maka.' 11 Sai Yahweh ya aika da Yerub Ba'al, Bedan, Yefta, da Sama'ila, ya kuma ba ku nasara akan maƙiyanku dukka a kewaye da ku, yadda kuka zauna cikin tsaro. 12 Da kuka ga Nahash sarkin mutanen Ammon yakawo maku hari, kuka ce mani, "A a! maimako, dole wani sarki ya yi mulki akanmu' - ko da ya ke Yahweh Allahnku, shi ne sarkinku. 13 Yanzu ga sarkin daku ka zaɓa, wanda kuka yi roƙo domin sa wanda kuma Yahweh ya naɗa sarki a bisanku. 14 Idan ku na tsoron Yahweh, ku bauta masa, ku yi biyayya da muryarsa, kuma ba wai ku kangare ga dokokin Yahweh ba, daga nan ku dukka da sarkin da ke mulki a bisanku za ku zama masu bin Yahweh Allahnku. 15 Idan ba ku yi biyayya da muryar Yahweh ba, amma kukakangare ga dokokin Yahweh, daga nan hannun Yahweh zai yi gãba da ku, kamar yadda ya yi gãba dakakanninku. 16 Ko yanzu ma ku miƙakanku kuma ku ga wannan babban abu wanda Yahweh zai yi a gaban idanunku. 17 Ba kamar alkama ba ce yau? Zan yi kira ga Yahweh, domin ya aiko da aradu da ruwan sama. Daga nan za ku sani ku kuma gani cewa muguntarku babba ce, wadda kuka aikata a idanun Yahweh, cikin roƙar wakanku sarki." 18 Sai Sama'ila ya yi kira ga Yahweh; a wannan rana kuma Yahweh ya aiko da aradu da ruwan sama. Daga nan dukkan mutanen suka ji tsoron Yahweh da Sama'ila ƙwarai. 19 Daga nan dukkan mutanen suka ce da Sama'ila, "Ka yi addu'a domin bayinka ga Yahweh Allahnka, domin kada mu mutu. Gama mun ƙara wakanmu dukkan zunubanmu wannan muguntar cikin roƙo domin sarki domin kanmu." 20 Sama'ila ya maida amsa, "Kada ku ji tsoro. Kun yi dukkan wannan mugunta, ammakada ku juya ga Yahweh, amma ku bauta wa Yahweh da dukkan zuciyarku. 21 Kada ku juya zuwa holoƙan abubuwa waɗanda ba za su iya bada riba ko cetonku ba, saboda ba su da amfani. 22 Domin albarkacin sunansa mai girma, Yahweh ba zai watsar da mutanensa ba, saboda ya gamshi Yahweh ya maida ku mutane domin kansa. 23 Game da ni, ya yi ne sa da ni in yi zunubi gãba da Yahweh ta wurin tsaida yin addu'a domin ku. Maimako, zan koyar da ku hanya da ke mai kyau kuma dai-dai. 24 Kawai dai ku ji tsoron Yahweh kuma ku bauta masa cikin gaskiya da dukkan zuciyarku. Kuyi la'akari da manyan abubuwan da ya yi domin ku. 25 Amma idan kuka nace ga aikata mugunta, ku dukka da sarkinku zaku lalace."

Sura 13

1 Saul na da shekaru talatin sa'ad da ya fara mulki; sa'ad da ya yi mulki shekaru arba'in a bisa Isra'ila, 2 ya zaɓi mutane dubu uku na Isra'ila. Dubu biyu suna tare da shi a Mikmash da kuma ƙasar tudu ta Betel, dubu ɗaya kuma suna tare da Yonatan a Gibiya ta Benyamin. Sauran sojojin ya aika da su gida, kowanne mutum zuwa rumfarsa. 3 Yonatan yakayar da sansanin Filistiyawa da ke Geba Filistiyawa kuma suka ji haka. Daga nan Saul ya busa ƙaho cikin dukkan ƙasar, cewa, "Bari Ibraniyawa su ji." 4 Dukkan Isra'ila kuwa suka ji cewa Saul yakayar da sansanin Filistiyawa, da cewa kuma Isra'ila ta zama ɗoyi mai ruɓa ga Filistiyawa. Daga nan aka yi wa sojojin sammace tare su haɗu da Saul a Gilgal. 5 Filistiyawa suka tattaru tare suyi faɗa gãba da Isra'ila: karusai dubu uku, mutane dubu shida suyi tuƙin karusan, rundunai kuma yawan su kamar rairayin da ke bakin teku. Suka zo sukakafa sansani a Mikmash, gabas da Bet Aben. 6 Da mutanen Isra'ila suka ga cewa suna cikin matsala - domin mutanen sun ƙuntata, mutanen suka ɓoɓɓoye a kogonni, da ƙarƙashin zangarniyoyi, da duwatsu, da rijiyoyi, da ramuka. 7 Wasu Ibraniyawan suka tafi ƙetaren Yodan zuwa ƙasar Gad da Giliyad. Amma Saul yana Gilgal tukuna, dukkan mutanen kuma suka bi shi suna rawar jiki. 8 Ya jira kwana bakwai, lokacin da Sama'ila ya tsaida. Amma Sama'ila bai zo Gilgal ba, mutanen kuma suna warwatsewa daga Saul. 9 Saul ya ce, "Kawo mani baikon ƙonawar da baye-bayen salamar." Daga nan ya miƙa baikon ƙonawar. 10 Nan da nan yana gama miƙa baikon ƙonawar Sama'ila ya iso. Saul ya fita domin ya same shi ya kuma gaishe shi. 11 Daga nan Sama'ila ya ce, "Mene ne ka yi?" Saul ya maida amsa, "Da naga cewa mutanen na bari na, kuma cewa baka zo ba cikin lokacin da aka tsaida, kuma cewa Filistiyawa sun riga sun taru a Mikmash, 12 Na ce, 'Yanzu Filistiyawa zasu gangaro gãba da ni a Gilgal, kuma ban biɗi tagomashin Yahweh ba.' Sai na tilasta wakaina in miƙa baikon ƙonawar." 13 Daga nan Sama'ila ya cewa Saul, "Ka yi wawanci. Baka kiyaye dokar Yahweh Allahnka ba wadda ya baka. Domin daga nan da Yahweh ya tabbatar da mulkin ka bisa Isra'ila har abada. 14 Amma yanzu mulkin ka ba zai ci gaba ba. Yahweh ya samo wani mutum bisa ga zuciyarsa, kuma Yahweh ya naɗa shi ya zama shugaba bisa mutanensa, saboda baka yi biyayya da abin da ya dokace ka ba." 15 Daga nan Sama'ila ya tashi ya tafi ya haye daga Gilgal zuwa Gibiya ta Benyamin. Daga nan Saul ya lissafa mutanen da ke tare da shi, kimanin mutane ɗari shida. 16 Saul, da ɗansa Yonatan, da mutanen da ke tare da su, suka tsaya a Geba ta Benyamin. Amma Filistiyawan suka yi sansani a Mikmash. 17 Mahaya suka zo daga sansanin Filistiyawa cikin ƙungiyoyi uku. ‌Ƙungiya ɗaya ta juya wajen Ofra, zuwa ƙasar Shuwal. 18 Wata ƙungiyar ta juya wajen Bet Horon, wata ƙungiyar kuma ta juya wajen kan iyakar da ke fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji. 19 Babu wani maƙeri da aka iya samu cikin dukkan ƙasar Isra'ila, saboda Filistiyawan sun ce, "Idan ba haka ba Ibraniyawa zasu yi takubba da mãsu domin kansu." 20 Amma dukkan mutanen Isra'ila sukan je wurin Filistiyawa, kowanne domin ya wãsakayan aikin gonarsa, da addarsa, da gatarinsa, da laujensa. 21 Farashin kuwakashi biyu cikin uku ne na shekel akan kowanne washin bakin kayan aiki, da adduna, dakashi ɗaya cikin uku na shekel domin washin gatura, domin kuma miƙar da silkuna. 22 Saboda haka a ranar yaƙi, babu takubba ko mãsu da aka samu a hannuwan ko ɗaya daga cikin sojojin da ke tare da Saul da Yonatan; Saul ne kaɗai da ɗansa Yonatan suke da su. 23 Sai sansanin Filistiyawa suka fita zuwa hanyar Mikmash.

Sura 14

1 Wata rana, Yonatan ɗan Saul ya cewa saurayin da ke ɗauke da makamansa, "Zo, mu tafi zuwa sansanin Filistiyawa da ke ɗaya ɓarayin." Amma bai gaya wa mahaifinsa ba. 2 Saul na zama a waje da Gibiya a ƙarƙashin itacen manta'uwa da ke cikin Migron. Wajen mutane ɗari shida na tare da shi, 3 har da Ahija ɗan Ahitub (ɗan'uwan Ikabod) ɗan Fenihas ɗan Eli, firist ɗin Yahweh a Shilo, wanda ya sanya falmara. Mutane ba su san cewa Yonatan ya tafi ba. 4 A kowanne gefen hanyar inda Yonatan ya so ya bi domin yakai ga sansanin Filistiyawan, akwai dutse mai tsini a gefe ɗaya da kuma wani dutsen mai tsini a ɗayan gefen. ‌Ɗaya dutse mai tsinin a na kiran sa Bozez ɗaya kuma dutsen mai tsini a na kiran sa Sene. 5 ‌Ɗ‌aya dutsen mai tsini yana tsaye a arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma a kudu a gaban Geba. 6 Yonatan ya ce da saurayin da ke ɗauke da makamansa, "Zo, mu ƙetara sansanin waɗannan marasakaciyar. Zai yiwu cewa, Yahweh ya yi aiki a madadin mu, domin babu abin da zai tsaida Yahweh daga yin ceto ta wurin masu yawa ko mutane kaɗan." 7 Mai ɗaukar makamansa ya maida amsa, "Ka yi duk abin da ke cikin zuciyarka. Ka yi gaba, duba, ina tare dakai, in yi biyayya ga dukkan dokokinka." 8 Daga nan Yonatan ya ce, "Za mu ƙetara zuwa ga mutanen, za mu kuma nunakanmu gare su. 9 Idan suka ce mana, 'Ku dakata nan har sai mun hauro gare ku'- daga nan za mu tsaya a wurinmu ba kuma za mu ƙetara zuwa gare su ba. 10 Amma idan suka maida amsa, 'Ku ƙetaro zuwa gare mu,' daga nan za mu ƙetara; saboda Yahweh ya bayar da su cikin hannunmu. Wannan ne zai zama alama a gare mu." 11 Sai dukkan su suka bayyanakansu ga sansanin Filistiyawa. Filistiyawan suka ce, "Duba, Ibraniyawa na fitowa daga ramukan da suka ɓoye kansu." 12 Daga nan mutanen sansanin suka yi kira ga Yonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce kuma, "Ku zo gare mu, za mu kuma nuna maku wani abu." Yonatan ya ce da mai ɗaukar makamansa, "Bi yo bayana, saboda Yahweh ya bayar da su cikin hannun Isra'ila." 13 Yonatan ya hau bisa hannuwansa da ƙafafunsa, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa. Filistiyawa suka sha kisa a gaban Yonatan, kuma mai ɗaukar makamansa yakarkashe wasu bayansa. 14 Wannan hari na farko da Yonatan da mai ɗaukar makamansa sukakai, yakashe mutane ashirin a cikin yankin fili kimanin rabin Eka. 15 akayi fargaba a sansanin, da cikin filayen, da kuma cikin mutane. Har sansanin da mahayansu suka yi fargaba. ‌Ƙ‌asa ta girgiza, aka kuma yi babbar fargaba. 16 Daga nan matsaran Saul a Gibiya ta Benyamin suka duba; taron sojojin Filistiyawa na bajewa, kuma suna tafiya nan da can. 17 Daga nan Saul ya ce da mutanen da ke tare da shi, "Ku lissafa ku gani wane ne ya ɓace a cikinmu." Da suka yi lissafi, Yonatan da mai ɗaukar makamansa sun ɓace. 18 Saul ya cewa Ahija, "Kawo akwatin Allah a nan," domin a lokacin yana tare da mutanen Isra'ila. 19 Yayin da Saul ke magana da firist, yamutsin a cikin sansanin Filistiyawa yana ci gaba kuma yana ƙaruwa. Daga nan Saul ya cewa firist, "Janye hannunka." 20 Saul da dukkan mutanen da ke tare da shi suka jera kuma suka shiga cikin yaƙin. Kowacce takobin Bafaliste tayi gãba da mutumin garinta, aka kuma yi babbar rikicewa. 21 Yanzu waɗannan Ibraniyawa waɗanda dã suke tare da Filistiyawa, waɗanda kuma suka tafi tare da su cikin sansani, su ma kuma suka haɗe tare da Isra'ilawan da ke tare da Saul da Yonatan. 22 Da mutanen Isra'ila waɗanda suka ɓoye kansu cikin tuddai kusa da Ifraim suka ji cewa Filistiyawa na tserewa, su ma suka bi bayansu cikin yaƙi. 23 Haka Yahweh ya ceto Isra'ila a wannan rana, Yaƙi kuma ya wuce har gaban Bet Aben. 24 A wannan rana mutanen Isra'ila sukakasance cikin ƙunci saboda Saul ya sanya mutanen ƙarƙashin rantsuwa ya kuma ce, "La'ananne ne mutumin da yaci wani abin ci har sai da yamma kuma nayi ramuwa akan maƙiyana." Don haka babu wani cikin mayaƙan da ya ɗanɗana abinci. 25 Daga nan dukkan mutanen suka shi ga cikin jeji kuma akwai zuma a bisa ƙasar. 26 Da mutanen suka shiga cikin jejin, zuman ya malalo, amma babu wanda ya sanya hannunsa ga bakinsa domin mutanen sun ji tsoron rantsuwar. 27 Amma Yonatan bai ji cewa mahaifinsa ya ɗaure mutanen tare da rantsuwa ba. Ya miƙa tsinin sandar da ke hannunsa ya luma cikin saƙar zuman. Ya ɗaga hannunsa zuwa bakinsa, idanunsa kuma suka wartsake. 28 Daga nan ɗaya daga cikin mutanen, ya amsa, "Mahaifinka ya yi wa mutane umarni mai tsanani tare da rantsuwa, ta wurin cewa, 'La'ananne ne mutumin da yaci abinci a wannan ranar,' ko da ya ke mutanen sun yi yaushi saboda yunwa. 29 Daga nan Yonatan ya ce, "Mahaifina ya aiwatar da matsala a ƙasar. Kalli yadda idanuna suka wartsake saboda na ɗanɗanakaɗan daga cikin zuman nan. 30 Yaya kuma in da mutanen yau sun ci a sake daga cikin ganima daga maƙiyansu da suka samo? Saboda yanzu kisan bai yi yawa ba a cikin Filistiyawa." 31 Sukakaiwa Filistiyawa hari a wannan rana daga Mikmash zuwa Aiyalon. Mutanen suka gaji sosai. 32 Mutanen suka afka da haɗama bisa ganimar suka kuma ɗauki tumaki, da shanu da maruƙa, suka kuma yanka su a ƙasa. Mutanen suka cinye su tare da jinin. 33 Daga nan suka gayawa Saul, "Duba, mutanen suna zunubi gãba da Yahweh ta wurin ci tare da jinin." Saul ya ce, "Kun aikata rashin aminci. Yanzu, a gangaro da wani babban dutse nan a gare ni." 34 Saul ya ce, "Fita cikin mutanen, ku kuma gaya masu, 'Bari kowanne mutum yakawo sansa da tunkiyarsa, ya yanka su a nan, ya kuma ci. Kada kuyi zunubi gãba da Yahweh ta wurin ci tare da jinin."' Sai kowanne mutum yakawo sansa tare da shi a wannan dare ya kuma yanka a wurin. 35 Saul ya gina bagadi ga Yahweh, shi ne kuma bagadi na farko da ya gina ga Yahweh. 36 Daga nan Saul ya ce, "Bari mu runtumi Filistiyawa da dare mu kuma warwatsa su har wayewar gari; kada mu bar ko ɗayan su da rai." Suka amsa, "Kayi duk abin da ya yi kyau a gare ka." Amma firist ɗin ya ce, "Bari mu kusanci Allah a nan." 37 Saul ya tambayi Allah, "In runtumi Filistiyawa? Zaka bayar da su cikin hannun Isra'ila?" Amma Allah bai amsa masa ba a wannan ranar. 38 Daga nan Saul ya ce, "Ku zo nan, dukkan ku shugabannin mutane; ku koya ku kuma duba yadda wannan zunubin ya faru a yau. 39 Domin, da wanzuwar Yahweh, wanda ke ceton Isra'ila, ko ma idan yana cikin Yonatan ne ɗana, tabbas zai mutu." Amma ba ko ɗaya daga cikin jama'ar daga cikin dukkan mutanen ya amsa masa. 40 Daga nan ya ce da dukkan Isra'ila, "Dole ku tsaya gefe ɗaya ni da Yonatan ɗana kuma mu tsaya gefe ɗaya." Mutanen suka ce da Saul, "Ka yi abin da ya yi kyau a gare ka." 41 Saul ya ce, Yahweh, Allah na Isra'ila! Idan ni ne na yi wannan zunubin ko kuma ɗana ne Yonatan ya yi shi, daga nan, Yahweh, Allah na Isra'ila, ka bada Urim. Amma idan wannan zunubi mutanenka Isra'ila ne suka aikata shi"Ka bada Tummim." Sai Yonatan da Saul aka ɗauka ta ƙuri'a, amma mayaƙan sukakaucewa Zaɓen. 42 Daga nan Saul ya ce, "akaɗa ƙuri'u tsakani na da Yonatan ɗa na." Daga nan aka ɗauki Yonatan ta ƙuri'a. 43 Daga nan Saul ya ce wa Yonatan, "Gaya mani abin daka yi." Yonatan ya gaya masa, "Na ɗanɗana zumakaɗan dakarshen sandar da ke hannuna. Ga ni nan; zan mutu." 44 Saul ya ce, "Allah ya yi haka kuma fiye ma a gare ni, idan baka mutu ba, Yonatan." 45 Daga nan mutanen suka cewa Saul, "Yonatan ya mutu kuwa, wanda ya aiwatar da wannan babbar nasara ga Isra'ila? Ya yi nesa da shi! da wanzuwar Yahweh, ba bu ko gashi ɗaya bisakansa da zai faɗi ƙasa, gama ya yi aiki tare da Allah a yau." Haka mutanen suka kuɓutar da Yonatan yadda bai mutu ba. 46 Daga nan Saul ya tsaida runtumar Filistiyawa, kuma Filistiyawan suka tafi na su wurin. 47 Da Saul ya fara mulki bisa Isra'ila, ya yi yaƙi gãba da maƙiyansa ta kowanne gefe. Ya yi yaƙi gãba da Mowab, Ammoniyawa, Idom, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya juya, yana azabta horo akansu. 48 Ya yi aiki da ƙarfin hali mai girma yakayar da Amalekawa. Ya kuɓutar da Isra'ila daga hannuwan waɗanda suka washe su. 49 'Ya'yan Saul maza su ne Yonatan, Ishbi, da Malkishuwa. Sunayen 'ya'yansa mata biyu kuwa su ne Merab, ta fari, da Mikal, ƙaramar. 50 Sunan matar Saul shi ne Ahinowam; ita ce ɗiyar Ahimãz. Sunan shugaban sojojinsa kuwa Abna ɗan Nã, kawun Saul. 51 Kish ne mahaifin Saul; Nã kuma, mahaifin Abna, shi ne ɗan Abiyel. 52 An yi yaƙi mai tsanani gãba da Filistiyawa dukkan kwanakin Saul. Idan Saul ya ga wani ƙaƙƙarfan mutum, ko mutum mai ƙwazo, sai ya jawo shi a gare shi.

Sura 15

1 Sama'ila ya cewa Saul, "Yahweh ya aiko ni in shafe ka sarki bisa mutanensa Isra'ila. Yanzu ka saurari maganganun Yahweh. 2 Wannan ne abin da Yahweh mai runduna ya ce, 'Na lura da abin da Amalek ya yiwa Isra'ila cikin tsayayya da su a bisa hanya, sa'ad da suka fito daga cikin Masar. 3 Yanzu ka je kakai hari ga Amalek ka kuma lalata duk abin da suke da shi ɗungum. Kadaka raga masu, ammaka kashe su maza da mata, yaro da jariri, saniya da tunkiya, raƙumi da jaki."' 4 Saul ya tattaro mutanen ya ƙidaya su a birnin Telem: mutane dubu ɗari bisa ƙafa, da mutanen Yahuda dubu goma. 5 Daga nan Saul ya zo cikin birnin Amalek ya kuma jira a cikin kwari. 6 Daga nan Saul ya cewa Keniyawa, "Ku je, ku tafi, ku fito daga cikin Amalekawa, domin kada in lalatar da ku tare da su. Domin kun nuna halin kirki ga dukkan mutanen Isra'ila, sa'ad da suka zo daga Masar." Sai Keniyawa suka wãre daga Amalekawa. 7 Sai Saul yakai hari ga Amalekawa, daga Habila har ya zuwa Shur, wadda ke gabas da Masar. 8 Daga nan ya ɗauki Agag sarkin Amalekawa da rai; gaba ɗaya ya lalatar da dukkan mutanen dakaifin takobi. 9 Amma Saul da mutanen suka bar Agag, duk da mafi kyau daga cikin tumaki, da shanu, da maraƙai masu ƙiba, da raguna. Kowanne abu da ke da kyau, ba su lalatar ba. Amma gaba ɗaya suka lalatar da duk wani abu wulaƙantacce marar amfani kuma. 10 Daga nan maganar Yahweh ta zo ga Sama'ila, cewa, 11 "Ya ba ni ɓacin rai cewa na naɗa Saul sarki, domin ya juya baya daga bi na bai kuma aiwatar da dokokina ba." Sama'ila ya fusata; ya yi kuka ga Yahweh dukkan dare. 12 Sama'ila ya farka da wurwuri domin ya sami Saul da safe. Aka cewa Sama'ila, "Saul ya tafi Kamel kuma yakafa wakansa wurin tunawa, daga nan ya juya kuma ya ci gaba zuwa Gilgal." 13 Daga nan Sama'ila ya zo wurin Saul, Saul kuma ya ce masa, "Mai albarka ne kai daga Yahweh! Na cika dokar Yahweh." 14 Sama'ila ya ce, "Daga nan mene ne wannan kukan tumakin a kunnuwa na, da kukan shanun da na ke ji?" 15 Saul ya maida amsa, "An kawo su ne daga Amalekawa. Domin mutanen sun keɓe mafi kyau daga cikin tumakin da shanun, domin hadaya ga Yahweh Allahnka. Sauran gaba ɗaya mun hallakar da su." 16 Daga nan Sama'ila ya cewa Saul, "Jira, kuma zan faɗi maka abin da Yahweh ya ce mani da daren nan." Saul ya ce masa, "Yi magana!" 17 Sama'ila ya ce, "Koda ya ke kai ƙarami ne a idanunka, ba an mai she ka shugaban kabilun Isra'ila ba? Daga nan Yahweh ya shafe ka sarki bisa Isra'ila, 18 Yahweh kuma ya aike ka bisa hanyarka ya kuma ce, 'Je kuma gaba ɗayaka hallakar da masu zunubi, Amalekawa, ka kuma yi faɗa gãba da su har sai sun hallaka.' 19 Me yasa baka yi biyayya da muryar Yahweh ba, amma a maimako ka ƙwato ganimaka kuma yi abin da ke mugunta a gaban Yahweh?" 20 Daga nan Saul ya cewa Sama'ila, "Lallai na yi biyayya da muryar Yahweh, kuma na tafi bisa hanyar da Yahweh ya aike ni. Nakamo Agag, sarkin Amalek, kuma gaba ɗaya na hallakar da Amalekawa. 21 Amma mutanen suka ɗauko wasu daga cikin ganimar - tumaki da shanu, abubuwa mafi kyau da aka keɓe ga hallakarwa, domin hadaya ga Yahweh Allahnka a Gilgal." 22 Sama'ila ya maida amsa, "Yahweh yana gamsuwa da baye-baye na ƙonawa da hadayu, fiye da biyayya da muryar Yahweh? Biyayya tafi hadaya, kuma saurare ya fi kitsen raguna. 23 Domin tawaye kamar zunubin tsafi ya ke, taurin kai kumakamar mugunta da ƙazanta. Sabodaka yi watsi da maganar Yahweh, shi ma ya ƙika da ga zama sarki." 24 Daga nan Saul ya cewa Sama'ila, "Na yi zunubi; domin nakarya dokar Yahweh da maganganunka, saboda ina jin tsoron mutanen na kuma yi biyayya da muryarsu. 25 Yanzu, ina roƙon kaka yafe zunubina, ka kuma juyo tare da ni domin in yi sujada ga Yahweh." 26 Sama'ila ya cewa Saul, "Ba zan koma tare dakai ba; domin ka yi watsi da maganar Yahweh, Yahweh kuma ya ƙika da zama sarki bisa Isra'ila." 27 Yayin da Sama'ila ya juya domin ya tafi, Saul ya riƙe haɓar rigarsa, ta kuma yage. 28 Sama'ila ya ce masa, "Yahweh ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka a yau ya kuma bayar da ita ga makwabcinka, wani wanda ya fi ka. 29 Haka kuma, ‌Ƙarfin Isra'ila ba zai yi ƙarya ba ko ya canza ra'ayinsa; domin shi ba mutum ba ne, da zai canza ra'ayinsa." 30 Daga nan Saul ya ce, "Na yi zunubi. Amma ina roƙon kaka darajanta ni yanzu a gaban dattawan mutanena da gaban Isra'ila. Ka sake juyowa tare da ni, domin in yi sujada ga Yahweh Allahnka." 31 Sai Sama'ila ya sake juyowa bayan Saul, Saul kuma ya yi sujada ga Yahweh. 32 Daga nan Sama'ila ya ce, "Kawo Agag sarkin Amalekawa nan wurina." Agag ya zo gare shi ɗaure cikin sarƙoƙi ya kuma ce, "Tabbas ɗacin mutuwa ya wuce." 33 Sama'ila ya maida amsa, "Kamar yadda takobin ka ta maida mata marasa 'ya'ya, haka mahaifiyarka za ta zama marar ɗa a cikin mata." Daga nan Sama'ila ya datse Agag gunduwa-gunduwa a gaban Yahweh a Gilgal. 34 Sama'ila ya tafi Rama, Saul kuma ya tafi gidansa a Gibiya ta Saul. 35 Sama'ila bai sake ganin Saul ba har sai ranar mutuwarsa, gama ya yi makoki domin Saul. Yahweh ya yi baƙinciki da cewa ya naɗa Saul sarki bisa Isra'ila.

Sura 16

1 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Har yaushe zaka yi makoki domin Saul, tunda nayi watsi da shi daga zama sarki bisa Isra'ila? Ka cika ƙahonka da mai ka kuma tafi. Zan aike ka ga Yesse na Betlehem, domin na zaɓar wakaina sarki cikin 'ya'yansa maza." 2 Sama'ila ya ce, "Yaya zan tafi? Idan Saul ya ji haka, zai kashe ni." Yahweh ya ce, "Ka ɗauki maraƙi tare dakai ka kuma ce, 'Na zo in yi hadaya ga Yahweh.' 3 Ka kira Yesse zuwa hadayar, zan kuma nuna maka abin da zaka yi. Zaka shafe mani wanda zan gaya maka." 4 Sama'ila ya yi yadda Yahweh ya faɗi ya kuma tafi Betlehem. Dattawan birnin suna rawar jiki yayin da su ka zo suka same shi suka kuma ce, "Kana zuwa cikin salama?" 5 Ya ce, "Cikin salama; Na zo in yi hadaya ga Yahweh. Ku shirya ku keɓe kanku ku kuma zo tare da ni wurin hadayar." Daga nan ya ware Yesse da kuma 'ya'yansa maza ya kuma gayyace su zuwa hadayar. 6 Da suka zo, yakalli Iliyab ya kuma faɗi wakansa cewa shafaffe na Yahweh ba bu shakka yana tsaye a gaba na. 7 Amma Yahweh ya cewa Sama'ila, "Kadaka dubi siffarsa ta zahiri, ko tsawon ƙirarsa; saboda na ƙi shi. Domin Yahweh ba ya duba yadda mutum ke duba wa; mutum yanakallon siffa a zahiri, amma Yahweh yanakallon zuciya." 8 Daga nan Yesse ya kira Abinadab ya kuma sa ya gitta a gaban Sama'ila. Daga nan Sama'ila ya ce, "Wannan ma Yahweh bai zaɓe shi ba." 9 Yesse daga nan yasa Shamma ya gitta, amma Sama'ila ya ce, "Wannan ma Yahweh bai zaɓe shi ba." 10 Yesse yasa 'ya'yansa maza bakwai suka gitta a gaban Sama'ila. Daga nan Sama'ila ya cewa Yesse, "Yahweh bai zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan ba." 11 Daga nan Sama'ila ya cewa Yesse, "Dukkan 'ya'yanka maza suna nan?" Ya maida amsa, "Akwai ƙaramin su da ya rage, amma yana lura da tumaki." Sama'ila ya cewa Yesse, "Ka aika akawo shi; domin ba za mu zauna ba har sai ya zo nan." 12 Yesse ya aika aka zo da shi ciki. Yanzu dai wannan ɗa jã ne da kyawawan idanu da kyakkyawar siffa. Yahweh ya ce, "Tãshi, shafe shi; domin shi ne." 13 Daga nan Sama'ila ya ɗauki ƙahon mai ya kuma shafe shi a tsakiyar 'yan uwansa. Ruhun Yahweh ya afko bisa Dauda daga wannan rana har zuwa gaba. Daga nan Sama'ila ya tashi ya kuma tafi Rama. 14 Yanzu Ruhun Yahweh ya bar Saul, ruhu mai illa kuma daga Yahweh yana azabtar da shi a maimako. 15 Bãyin Saul suka ce masa, "Duba, ruhu mai illa daga Allah na azabtar dakai. 16 Bari ubangijinmu yanzu ya umarci bãyinsa waɗanda ke tsaye a gabanka su nemo mutum wanda ya kware a kiɗin garaya. Daga nan idan ruhu mai illa daga Allah yana bisanka, zai kaɗa ta kuma zaka sami lafiya." 17 Saul ya cewa bãyinsa, "Ku samo mani mutum da ya iyakaɗa wa sosai ku kumakawo mani shi." 18 Daga nan ɗaya daga cikin samarin ya amsa, ya kuma ce, "Na ga wani ɗan Yesse Betlehemiye, wanda ya kware akaɗa wa, ƙaƙƙarfa, mutum mai ƙarfin hali, mutumin yãƙi, mai tattali a zance, mutum mai asali; kuma Yahweh yana tare da shi." 19 Sai Saul ya aika da manzanni wurin Yesse, ya kuma ce, "Ka aiko mani da ɗanka Dauda, wanda ke tare da tumaki." 20 Yesse ya ɗauki jaki danƙare da gurasa, da salkar inabi, da 'yar akuya, ya kuma aika da su tare da ɗansa Dauda wurin Saul. 21 Daga nan Dauda ya zo wurin Saul ya kuma shiga hidimarsa. Saul ya ƙaunace shi sosai, ya kuma zama mai ɗaukar makamansa. 22 Saul ya aika wa Yesse, cewa, "Bari Dauda ya tsaya a gabana, domin ya sami tagomashi a idanu na." 23 Duk sa'ad da ruhu mai illa daga Allah yana bisan Saul, Dauda zai ɗauki garaya ya kumakaɗa ta. Sai Saul ya wartsake ya kuma yi lafiya, kuma ruhu mai illar sai ya tafi daga gare shi.

Sura 17

1 Yanzu Filistiyawa suka tara rundunarsu domin yaƙi. Suka taru a Soko, wacce take ta Yahuda. Suka yi sansani tsakanin Soko da Azeka, cikin Ifes Dammim. 2 Saul tare da mutanen Isra'ila suka taru sukakafa sansani a kwarin Ila, suka jã layin dãga dominsu fuskanci Filistiyawa. 3 Filistiyawa suka tsaya a bisa dutse a sashen gefe, Isra'ila kuma na bisa dutse a wancan gefen a kwari da ke tsakaninsu. 4 Wani mutum mai ƙarfi ya fito daga cikin sansanin Filistiyawa, mutum mai suna Goliyat daga Gat, wanda tsayinsa kãmu shida ne da rabi. 5 Yana da hular tagulla a bisakansa, yana kuma sanye da tufafin yaƙi. Rigar nada nauyin Shekel dubu biyar na tagulla. 6 Yana sanye da makarin ƙafa na tagulla da kuma mãshi na tagulla a tsakiyar kafaɗunsa. 7 Sandar mashinsa na da girma, da tausasshen igiya domin harba takamar dirkar masaka. Kan mashinsa na da nauyin shekel na ƙarfe ɗari shida. Mai ɗaukar masa garkuwa na a gaba da shi. 8 Ya tsaya ya yi ihu ga sojojin Isra'ilawa, "Donme kuka fito waje kukakafa sansanin yaƙi? Ni ba Bafiliste ba ne, ku kuma ba bayi ne na Saul ba? Ku zaɓa wakanku mutum kuma bari ya sauko gare ni. 9 Idan ya iya faɗa da ni ya kumakashe ni, sa'an nan zamu zama bayinku. Amma idan na kãda shi na kumakashe shi, sai ku zama bayinmu ku kuma bauta mana." 10 Sai kuma Bafilisten ya ce, "Na ƙalubalanci rundunar Isra'ila yau. Ku ba ni wanda zamu yi faɗa tare." 11 Lokacin da Saul da dukkan Isra'ila suka ji abin da Bafilisten ya faɗi, sai sukakaraya da babban tsoro. 12 Yanzu dai Dauda ɗan Ifraimiye ne na Betlehem cikin Yahuda, mai suna Yesse. Yana da 'ya'ya maza takwas. Yesse tsohon mutum ne a cikin kwanakin Saul, tsoho ne tukub a tsakanin mutane. 13 Manyan 'ya'ya maza na Yesse suna tare da Saul a filin dãga. Sunayen 'ya'yansa maza uku da suka tafi bakin dãga su ne Iliyab wanda shi ne ɗan fari, na biyun Abinadab, sai na ukun Shammah. 14 Dauda shi ne ɗan ƙaraminsu. Yayyensa uku suka bi Saul. 15 Yanzu dai Dauda yana fita yana shigowa gaba da baya tsakanin rundunar Saul da kuma tumakin babansa a Betlehem, domin ya ciyar da su. 16 Kwana arba'in mai ƙarfin nan Bafilisten yana zuwa gaba safiya da yamma domin ya miƙakansa ga yaƙi. 17 Sai Yesse ya cewa ɗansa Dauda, "Ka ɗauko wa 'yan uwanka mudu 22 na wannan gasasshen hatsin da kuma wannan gurasar goma, ka kuma ɗauko su da sauri kakai su sansani zuwa ga 'yan'uwanka. 18 Ka kuma ɗauki curin man shanu goma ga shugabansu na dubu. Ka duba lafiyar 'yan'uwankaka kuma dawo da tabbacin suna lafiya. 19 'Yan'uwanka suna tare da Saul da dukkan mazajen Isra'ila a cikin kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa." 20 Dauda ya tashi da sassafe ya bar garken cikin hannun wani makiyayi domin ya kula da su. Ya ɗauki abincin ya tafi, kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya iso sansani lokacin da rundunar ke fitowa zuwa filin dãga suna sowa ta yaƙi. 21 Sa'an nan Isra'ila da Filistiyawa sukakafa layi domin dãga, runduna gãba da juna. 22 Dauda ya bar kayayyakinsa ajiya wurin maitsaron kayayyaki, ya ruga da gudu zuwa wurin rundunar, ya gaida 'yan'uwansa. 23 Yayin da ya ke cikin magana da su, mutumin mai ƙarfin, Bafilisten na Gat, mai suna Goliyat, ya kuma fito daga cikin rundunar Filistiyawa, ya kuma furta maganganun da ya ke furtawakamar da farko, Dauda kuwa ya ji su. 24 A lokacin da dukkan Isra'ila suka ga mutumin, suka yi gudu daga wurinsa kuma suka ji tsoro matuƙa. 25 Mazajen Isra'ila suka ce, "Ko kun ga wannan mutumin wanda ya fito? Ya fito domin ya cakuni Isra'ila. Sarki zai bai wa duk wadda yakashe shi dukiya mai yawa. kuma zai ba da ɗiyarsa gare shi ya aura, Kuma za ya raba gidan ubansa daga biyan haraji a Isra'ila." 26 Dauda ya cewa mutanen da ke tsaye kusa da shi, "Mene ne za a yiwa mutumin da yakashe wannan Bafilisten domin yakawar da kunya ga Isra'ila? Wane ne wannan Bafilite marar kaciya da har ya ke rena rundunar Allah mai rai?" 27 Sai mutanen suka furta abin da suka faɗa tun farko kuma suka ce masa, "Haka za a yiwa mutumin da yakashe shi." 28 Iliyab babban ɗan'uwansa ya ji sa'ad da ya yi magana da mutanen. Sai fushin Iliyab ya yi ƙuna a bisa Dauda, sai ya ce, "Mene ne dalilin da yasaka gangaro nan wurin? A hannun wane ne ka baro 'yan tumakan nan cikin jeji? Na san girman kanka, da kuma fahariyar zuciyarka; domin ka gangaro nan domin kayi kallon yaƙi ne." 29 Dauda ya ce, "Mene ne na yi yanzu? Ba tambayakawai na yi ba?" 30 Ya juya ya bar shi zuwa wurin wani, ya sake irin magana a yadda ya yi dã. Mutanen suka amsa masakamar dã. 31 Da aka ji maganganun da Dauda ya faɗa, sojoji suka maimaita su ga Saul, shi kuwa ya aika akakawo Dauda. 32 Sai Dauda ya cewa Saul. "Kada zuciyar kowanne mutum takaraya sabili da wancan Bafilisten; bawanka zai tafi ya yi faɗa da wannan Bafilisten." 33 Saul ya cewa Dauda, "Ba zaka iya fãɗawa Bafilisten nan ba domin ka yi faɗa da shi; gamakai matashi ne, amma shi mutum ne mayaƙi tun yana saurayi." 34 Amma Dauda ya cewa Saul, "Bawanka yana kula da tumakin mahaifinsa. Lokacin da zaki ko damisa ya taso ya ɗauki 'yar akuya daga cikin garken, 35 nakan bisu in kumakai masu farmaki, in kuma ƙubutar da shi daga bakinsa. Lokacin da zai tayar mani, nakama shi a gemunsa, na buga shi, na kumakashe shi. 36 Bawanka yakashe zaki da damisa. Wannan Bafilisten marar kaciya zai zamakamar ɗayansu, tunda ya ƙalubalanci rundunar Allah mai rai." 37 Dauda ya ce, "Yahweh ya ƙubutar da ni daga hannun zaki da kuma hannun damisa. Za ya ƙubutar da ni daga hannun wannan bafilisten." Sa'an nan Saul ya cewa Dauda, "Je ka, bari kuma Yahweh yakasance tare dakai." 38 Saul ya sanya wa Daudakayan yaƙinsa. Yasa masa hular tagulla akansa, ya kuma sanya masa mayafin wayoyi. 39 Dauda ya ɗaura takobinsa a rigar yaƙi. Amma yakasa tafiya ciki, domin baya yi koyi da su ba. Sai Dauda ya cewa Saul, "Ba zan iya fita in yi faɗa da wannan kaya ba, gama ban yi koyo da su ba." Saboda haka Dauda ya kwaɓe kayan. 40 Ya ɗauki sandar kiwonsa cikin hannunsa ya kuma zaɓi duwatsu biyar daga cikin rafi; ya zuba su cikin jakarsa ta kiwo. Majajjawarsa na cikin hannunsa sa'ad da ya fuskanci Bafilisten. 41 Bafilisten ya rugo zuwa wurin Dauda, da mai ɗaukar masa makamai a gabansa. 42 A lokacin da Bafilisten ya juya ya kuma ga Dauda, sai ya rena shi, gama ɗan yaro ne kawai, kuma jã, mai asalin siffa. 43 Sai Bafilisten ya cewa Dauda, "Ni kare ne, da zaka zo gare ni da sanduna?," sai kuma Bafilisten ya la'anci Dauda da allolinsa. 44 Bafilisten ya cewa Dauda, "Zo gare ni, zan kuma bada namanka ga tsunytsayen sammai ga kuma namomin jeji." 45 Dauda kuwa ya amsa wa Bafilisten, "Kai kana zuwa gare ni da takobi, da mashi, da kibiya. Amma na zo gare ka a cikin sunan Yahweh mai runduna, Allah na rundunar Isra'ila, wandaka rena. 46 Yau Yahweh zai ba ni nasara bisanka, zan kumakashe ka in kuma cire kanka daga jikinka. Yau zan miƙɑ gawawakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sammai ga kuma namomin jeji na ƙasa, saboda dukkan duniya ta san cewa akwai Allah a Isra'ila, 47 kuma dukkan wannan taro su san cewa Yahweh ba ya ba da nasara ta dalilin takobi ko mãshi. Gama yaƙin na Yahweh ne, kuma za ya miƙaka cikin hannunmu." 48 A lokacin da Bafilisten ya tashi ya kuma taso ga Dauda, sai Dauda ya rugo da sauri zuwa ga rundunar magabcin domin ya gamu da shi. 49 Dauda yasa hannunsa cikin jaka, ya ɗauko dutse daga ciki, sai ya jefi Bafilisten a tsakiyar goshi, sai ya faɗi a fuskarsa ƙasa. 50 Dauda ya ci nasara ga Bafilisten da majajjawa da dutse. Ya jefe Bafilisten ya kumakashe shi. Babu takobi cikin hannun Dauda. 51 Sai Dauda ya sheƙa a guje ya kuma tsaya a bisa Bafilisten ya kuma dauƙe takobinsa, ya zaro ta daga gidanta, yakashe shi, ya datse kansa da ita. A lokacin da Filistiyawa suka ga cewa mutuminsu mai ƙarfi ya mutu, suka gudu. 52 Sai mazajen Isra'ila da na Yahuda suka tashi da sowa, suka kuma runtumi Filistiyawa har zuwa kwari da ƙofofin Ekron. Matattun Filistiyawa suka kwanta akan hanya zuwa Sharem, hanyar zuwa Gat da Ekron. 53 Mutanen Isra'ila suka dawo daga runtumar Filistiyawa, suka kuma washe sansaninsu. 54 Dauda ya ɗauki kan Bafilisten yakawo shi Yerusalem, amma ya ajiye rigar yaƙinsa a tasa rumfar. 55 Da Saul ya ga Dauda ya fita gãba da Filistiyawa, ya cewa Abna, shugaban runduna, "Abna, yaron wane ne wannan matashin?" Abna ya ce, "Ranka ya daɗe, sarki, ban sani ba." 56 Sarkin ya ce, "Ka tambayi waɗanda suna iya sani, ɗan wane ne." 57 Da Dauda ya dawo daga kisan Filistiyawan, Abna ya ɗauke shi, yakawo shi wurin Saul tare dakan Bafilisten a cikin hannunsa. 58 Saul ya ce masa, "Kai ɗan wane ne, ɗan saurayi?" Dauda ya amsa, "Ni yaron bawanka ne Yesse mutumin Betlehem."

Sura 18

1 Bayan da ya gama magana da Saul, sai ran Yonatan ya manne wa ran Dauda, Yonatan kuwa ya ƙaunace shi kamar ransa. 2 Saul ya ɗauki Dauda zuwa cikin hidimarsa a wannan rana; baya barshi ya koma gidan mahaifinsa ba. 3 Sai Yonatan da Dauda suka yi alƙawari da juna na abokantaka domin Yonatan ya ƙaunace shi kamar ransa. 4 Yonatan ya tuɓe rigarsa wadda ya ke yãfe da ita ya kuma ba Dauda tare da rigar yaƙinsa, har da takobinsa, bakansa, da kuma maɗaurinsa. 5 Dauda ya tafi duk inda Saul ya aike shi, kuma ya ci nasara. Saul ya maida shi kai bisa mazajen yaƙi. Wannan ya ƙayatar a idanun dukkan mutanen da kuma idanun bayin Saul. 6 Da suka dawo daga hallaka Filistiyawan, matayen suka fito daga dukkan biranen Isra'ila, suna raira waƙa da rawa, su taryi Saul, dakacakaura, da farinciki, da kumakayan kiɗe-kiɗe. 7 Matayen suka riƙa yin waƙa da juna sa'ad da suke kaɗawa. Suka raira: "Saul yakashe dubbansa, Dauda kuma dubbansa goma." 8 Saul ya ji haushi ƙwarai, kuma wannan waƙa ta baƙanta masa rai. Ya ce, "Sun ba Dauda dubbai goma, amma ni sun ba ni dubbai kawai. To mene ne ya rage masa idan ba mulkin ba?" 9 Saul kuwa daga wannan rana ya fara yi wa Daudakallon rashin yarda. 10 washegari wani mugun ruhu daga wurin Allah ya saukar wa Saul ya kuma yi hauka cikin gidan. Sai Dauda yakaɗa garayarsa, kamar yadda ya saba kowacce rana. Saul yana ɗauke da mashi cikin hannunsa. 11 Saul ya jefa mashin, gama ya yi tunani, "Zan tsire Dauda ga bango." Amma Dauda ya tsira daga gaban Saul sau biyu kamar haka. 12 Saul ya ji tsoron Dauda, gama Yahweh na tare da shi, amma baya kuma tare da Saul. 13 Sai Saul ya fitar da shi daga gabansa ya kuma maishe shi shugaban dubu. Da haka Dauda ya dinga fita yana shigowa a fuskar mutanen. 14 Dauda ya yi nasara a dukkan hanyoyinsa, gama Yahweh na tare da shi. 15 Da Saul ya ga yana ci gaba, sai ya ji tsoronsa. 16 Amma dukkan Isra'ila da Yahuda suka ƙaunaci Dauda, gama yana fita yana shigowa a idanunsu. 17 Sai Saul ya cewa Dauda, "Ga babbar ɗiyata Merab. Zan baka ita ta zama matarka. Sai dai ka yi mazakutta dominaka kuma yi yaƙin Yahweh." Gama Saul ya yi tunani, "Kada hannuna ya tayar masa, amma bari hannun Filistiyawa ya sauka bisansa." 18 Dauda ya cewa Saul, "Ni wane ne, kuma su wane ne 'yan uwana, ko gidan mahaifina cikin Isra'ila, da zan zama suruki ga sarki?" 19 Amma a lokacin da Merab, ɗiyar Saul, yakamata a bada ita ga Dauda, sai aka bada ita ga Adriyel mutumin Meholat ta zama matarsa. 20 Amma Mikal, ɗiyar Saul, ta ƙaunaci Dauda. Suka gaya wa Saul, wannan kuma ya yiwa Saul daɗi. 21 Sai Saul ya ce a zuciyarsa, "Zan ba da ita gare shi, domin ta zama tarko a gare shi, kuma hannun Filistiyawa ya yi gãba da shi." Saboda haka Saul ya cewa Daudakaro na biyu, "Zaka zama surukina." 22 Saul ya umarce bayinsa, "Ku yi magana da Dauda a asirce, ku ce, 'Duba, sarki yana jin daɗinka, kuma dukkan bayinsa suna ƙaunar ka. To yanzu, ka zama surukin sarki."' 23 Saboda haka bayin Saul suka furta waɗannan maganganu ga Dauda. Sai Dauda ya ce, "Ko ƙaramin abu ne gare ku zaman surukin sarki, ganin cewar ni talaka ne, kuma ba sananne ba?" 24 Bayin Dauda suka mayar wa Saul da maganganun da Dauda ya faɗa. 25 Sai Saul ya ce, "Ku faɗi wannan ga Dauda, 'Sarki ba ya buƙatar wani sadãki, sai dai fatar loɓar Filistiyawa ɗari daya, da za a rama daga maƙiyan sarki."' Yanzu Saul ya yi tunani dai yasa Dauda ya mutu ta hannun Filistiyawa. 26 Da bayinsa suka gaya wa Dauda waɗannan maganganu, sai ya yiwa Dauda dai-dai ya zama surukin sarki. 27 Kafin waɗanan kwanaki su wuce, Dauda ya tafi tare da mazajensa ya kumakashe Filistiyawa ɗari biyu. Dauda ya dawo da fatar loɓarsu, sai aka miƙa su cikakku ga sarki, domin ya zama surukin sarki. Sai Saul ya ba Dauda Mikal ɗiyarsa ta zama matarsa. 28 Da Saul ya gani, ya kuma sasance da cewa Yahweh na tare da Dauda, kuma Mikal, ɗiyar Saul, ta ƙaunace shi, 29 Saul ya ƙara jin tsoron Dauda. Saul ya ci gaba da zama magabcin Dauda. 30 Sai sarakunan Filistiyawa suka fito domin yaƙi, kamar dai yadda suke fitowa, hakannan Dauda ya ke nasara fiye da dukkan bayin Saul, har sunansa ya zama abin girmamawa.

Sura 19

1 Saul ya cewa Yonatan ɗansa da kuma dukkan bayinsa cewa su kashe Dauda. Amma Yonatan, ɗan Saul, ya yi fahariya da Dauda. 2 Saboda haka Yonatan ya gaya wa Dauda, "Saul mahaifina na neman yakashe ka. Saboda hakaka yi zaman tsaro da safe ka kuma ɓoye kanka a boyayyen wuri. 3 Zan fita in tsaya kusa da mahaifina cikin fili a indakake, zan kuma yi magana da mahaifina game dakai. Idan na ji wani abu akanka, zan gaya maka." 4 Yonatan ya yi maganar alheri game da Dauda ga Saul mahaifinsa ya kuma ce masa, "Bari kada sarki ya yi laifi ga bawansa Dauda. Gama ba ya yi maka laifi ba, kuma ayyukansa masu kyau sun kawo maka alheri. 5 Gama ya ɗauki ransa cikin hannunsa ya kumakashe Bafilisten. Yahweh yakawo babbar nasara ga dukkan Isra'ila. Ka gani ka kuma yi murna. Donme zaka yi zunubi ga jinin marar laifi da zakakashe Dauda babu dalili?" 6 Saul ya saurari Yonatan. Saul ya rantse, "Har ga Allah, ba zai kashe shi ba." 7 Sai Yonatan ya kira Dauda, sai kuma Yonatan ya gaya masa dukkan waɗannan abubuwan. Yonatan kuma yakawo Dauda wurin Saul, yana kuma tsayawa a gabansakamar dã. 8 Sai aka sake yin yaƙi, Dauda kuma ya fita ya yi faɗa da Filistiyawa ya kuma ci nasara da su da babbar hallaka. Suka gudu daga fuskarsa. 9 Wani mugun ruhu daga wurin Yahweh ya saukar wa Saul da ya ke zaune a gidansa da mashinsa cikin hannunsa, kuma yayin da Dauda ke kaɗakayan kiɗinsa. 10 Saul ya yi koƙarin tsire Dauda har ga bango da mashinsa, amma ya tsere daga gaban Saul, har Saul yakafe mashin cikin bangon. Dauda ya gudu ya tsere a wannan dare. 11 Saul ya aika da manzanni zuwa gidan Dauda su kula da shi domin yakashe shi da safe. Mikal, matar Dauda, ta ce masa, "Idan baka ceci ranka a wannan daren ba, gobe za akashe ka." 12 Saboda haka Mikal ta zura Dauda ta tãga. Ya tafi ya gudu, ya tsere. 13 Mikal ta ɗauki gunkin gida ta ajiye bisa gado. Sai ta sanya matashin kai na gashin akuya akansa, ta kuma rufe shi dakayayyaki. 14 Da Saul ya aika 'yan saƙo su ɗauko Dauda, ta ce, "Yana barci." 15 Sai Saul ya aika 'yan saƙo su ga Dauda; ya ce, "Ku kawo mani shi akan gadon, domin in kashe shi." 16 A lokacin da 'yan saƙon suka shigo ciki, gashi, gunkin gida na bisakan gado bisa matashin kai mai gashi na ɗan rago a bisakansa. 17 Saul ya cewa Mikal, "Donme ki ka ruɗe ni har ki ka bar makiyina ya tafi, har ya tsira?" Mikal ta amsa wa Saul, "Ya ce mani, 'Bar ni in tafi. Donme zan kashe ka?" 18 Yanzu Dauda ya gudu ya kuma tsira, ya tafi wurin Sama'ila a Rama ya kuma gaya masa dukkan abin da Saul ya yi masa. Sa'annan shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot. 19 Aka gaya wa Saul, cewa, "Duba, Dauda na Nayot cikin Rama." 20 Sai Saul ya aika da 'yan saƙo su kamo Dauda. Da suka ga taron annabawa na annabci, Sama'ila kuma na tsaye a matsayin shugabansu, sai Ruhun Allah ya sauko bisa 'yan saƙon Saul, sai su ma suka yi annabci. 21 Da aka gaya wa Saul wannan, sai ya aika da wasu 'yan saƙon, sai suma suka yi anabci. Sai Saul ya sake aikawa da wasu 'yan saƙo kãro na uku, sai suma suka yi anabci. 22 Sai shi ma ya tafi Rama ya zo wurin rijiya mai zurfi da ke a Seku. Ya yi tambaya, "Ina Sama'ila da Dauda?" Wani ya ce, "Duba, suna a Natot cikin Rama." 23 Saul ya tafi Nayot a Rama. Sai Ruhun Allah ya sauko bisansa, yayin da ya ke tafiya ya yi ta anabci har ya iso Nayot a Rama. 24 Ya tuɓe rigunansa ya kuma yi anabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta tsirara dukkan rana da dukkan dare. Shi yasa suke tambaya, "Wai Saul na ɗaya daga cikin annabawa ne?"

Sura 20

1 Sai Dauda ya gudu daga Nayot a Rama ya kuma zo ya cewa Yonatan, "Me na yi? Mene ne laifina? Mene ne zunubina ga mahaifinka, da ya ke neman ɗaukan raina?" 2 Yonatan ya cewa Dauda, "Sam ba haka ba ne; ba zaka mutu ba. mahaifina ba ya yin wani abu mai girma ko ƙanƙani ba tare da ya gaya mani ba. Donme mahaifina zai ɓoye mani wannan abu daga gare ni? Ba haka ba ne." 3 Duk da haka Dauda ya sake rantsuwa kuma ce, "Mahaifinka ya san da cewar na sami tagomashi a idanunka. Dama ya ce, 'Kada a bari Yonatan ya san wannan, don kada ya damu.' Amma tabbas tun da Yahweh na raye, kumakamar yaddakaimaka ke rayuwa, rãtakaɗan ne tsakani na da mutuwa." 4 Sai Yonatan ya cewa Dauda, "Duk abin daka ce, zan yi maka." 5 Dauda ya cewa Yonatan, "Gobe ne sabon wata, kuma yakamata in zauna wurin cin abinci da sarki. Ammaka bar ni in tafi, domin in ɓoye kaina cikin saura har kwana na uku da yamma. 6 Idan mahaifinka ya damu game da ni sarai, sai kace, 'Dauda ya nemi izini daga wajena domin ya tafi Betlehem birninsa. Domin lokacin hadaya ta shekara ce ga dukkan dangin.' 7 Idan ya ce, 'lafiya lau,' bawanka zai sami salama. Amma idan ya husata ƙwarai, to ka sani ya ƙudurci aikata mugunta. 8 Saboda hakaka kyauta wa bawanka. Gamaka jawo bawanka cikin alƙawari na Yahweh tare dakai. Amma idan akwai zunubi cikina, kakashe ni dakanka; gama mene ne dalilin da zai saka kawo ni ga mahaifinka?" 9 Yonatan ya ce, "Sam haka ba zai yiwu ba! Idan na gane mahaifina yana da niyyar cutar dakai, ba zan gaya maka ba?" 10 Sai Dauda ya cewa Yonatan, "wane ne zai gaya mani idan ya zama cewa mahaifinka ya amsa maka da faɗa?" 11 Yonatan ya cewa Dauda, "Zo, mu tafi cikin saura." Sai suka tafi cikin saura tare su biyu. 12 Yonatan ya cewa Dauda, "Bari Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zama shaida. A lokacin da zan tambayi mahaifina gobe war haka, ko rana ta uku, duba, idan akwai shirin alheri game da Dauda, ba zan aika gare ka in kuma sanar dakai ba? 13 Idan ya gamshi mahaifina da ya cutar dakai, bari Yahweh ya yi wa Yonatan har fiye kuma idan ban sanar dakai in kuma sallame kaka tafi ba, domin ka tafi cikin salama. Bari Yahweh yakasance tare dakai, kamar yadda ya ke tare da mahaifina. 14 Idan ina nan da rai, ba zaka nuna mani amintaccen alƙawarin Yahweh ba, domin kada in mutu? 15 Kadaka datse amintaccen alƙawarinka daga gidana har abada- koda Yahweh ya datse kowanne magabcin Dauda daga fuskar ƙasa. 16 Saboda haka Yonatan ya yi alƙawari da gidan Dauda ya kuma ce, "Bari Yahweh ya nemi lissafi daga hannun magabtan Dauda." 17 Yonatan yasa Dauda ya yi rantsuwa kuma domin ƙaunar da ya ke kaunarsa, gama yanakaunarsakamar yadda ya ke kaunar ransa. 18 Sai Yonatan ya ce masa, "Gobe ne sabon wata. Za a yi kewarka domin mazauninka zai zama babu kowa. 19 Bayan ka zauna can har kwana uku, sai ka sake komawa can indaka ɓoye kanka a lokacin da al'amuran ke ci gaba, ka tsaya kusa da dutsen Ezel. 20 Zan harba kibiyoyi uku gefensa, kamar ina auna inda nakeso in harba. 21 Daga nan zan aika ɗan matashina in kuma ce masa, 'Tafi ka nemo kibiyoyin.' Idan na cewa ɗan yaron, 'Duba, kibiyoyin suna wannan gefenka; nemo su."; sai ka zo; gama akwai kariya dominka kuma ba cutarwa, na rantse da ran Yahweh. 22 Amma idan na ce wa matashin, 'Duba, kibiyoyin suna can gaba dakai,' sai ka yi tafiyarka, gama Yahweh ya sallame ka. 23 Amma batun alƙawarin da ni dakai mu ka furta, gama, Yahweh na tsakani na dakai har abada." 24 Sai Dauda ya ɓoye kansa cikin saura. Lokacin da sabon wata ya fito, sarkin ya zauna domin cin abinci. 25 Sarkin ya zauna a bisa kujerarsa, yadda ya saba, a bisa kujera ta jikin bango. Yonatan ya tashi, Abna kuma ya zauna ta gefen Saul. Amma kujerar Dauda babu kowa. 26 Duk da haka Saul baya ce komai ba wannan rana, domin ya yi tunani, "Wani abin ne ya faru da shi. Ba shi da tsarki; tabbas ba shi dai da tsarki." 27 Amma a rana ta biyu, ranar bayan sabon wata, wurin zaman Dauda babu kowa. Saul ya cewa Yonatan ɗansa, "Me yasa ɗan Yesse bai zo ya ci abinci jiya da yau ba?" 28 Yonatan ya amsa wa Saul, "Dauda ya nemi izini sosai daga wurina domin ya tafi Betlehem. 29 Ya ce, 'Na roƙe ka. Gama iyalina na da hadaya a birni, kuma ɗan'uwana ya umarce ni da in kasance. Yanzu, idan na sami tagomashi a idanunka, Na roƙe ka bari in je in ga 'yan'uwana. Saboda wannan dalili yasa bai zo kujerar sarki ba." 30 Sai haushin Saul ya yi ƙuna bisa Yonatan, ya kuma ce masa, "Kai ɗan lalatacciya, mace mai tayarwa! Ashe ban sani baka zaɓi ɗan gidan Yesse ga kunyarka, ga kuma kunyar tsiraicin mahaifiyarka? 31 Idan har ɗan Yesse na a raye a ƙasar, ko kai ko mulkinka ba zai kafu ba. To yanzu, ka aika akawo shi gare ni, gama dole ne ya mutu." 32 Yonatan ya amsa wa mahaifinsa, "Da wane dalili za akashe shi? Me ya yi?" 33 Sai Saul ya jefa mashinsa don yakashe shi. Sai Yonatan ya gane cewa mahaifinsa ya ƙudurta yakashe Dauda. 34 Yonatan ya tashi ya bar teburin cikin hasalar fushi baya kuma ci abinci ba a rana ta biyu ga watan, gama yana baƙinciki saboda Dauda, domin mahaifinsa ya wulaƙanta shi. 35 Da safe, Yonatan ya fita zuwa saura inda suka shirya su haɗu da Dauda, kuma ɗan saurayin na tare da shi. 36 Ya cewa ɗan saurayin, "Ka yi gudu ka nemi kibiyoyin da na harba." Yayin da ɗan saurayin ya ruga, ya harba wata kibiyar gaba da shi. 37 Lokacin da ɗan saurayin ya iso inda kibiyar da Yonatan ya harba ta sauka, Yonatan ya kira ɗan saurayin, ya ce, "Ba kibiyar na gabanka ba?" 38 Sai Yonatan ya kirawo ɗan saurayin, "Yi sauri, hanzarta, kadaka tsaya!" Sai ɗan saurayin Yonatan ya tattara kibiyoyin ya dawo wurin ubangidansa. 39 Amma ɗan saurayin bai san komai ba. Yonatan da Dauda ne kaɗai suka san zancen. 40 Yonatan ya ba ɗan saurayin makamansa ya ce masa, "Tafi, kakai su cikin birnin." 41 Ba da jimawa ba bayan tafiyar ɗan saurayin, Dauda ya fito daga bayan dutsen, ya kwanta fuskarsa ƙasa, ya durƙusa ƙasa har sau uku. Suka yi wa juna sumba da kuka tare, Dauda ya yi kuka sosai. 42 Yonatan ya cewa Dauda, "Ka tafi cikin salama, gama mu biyu mun rigaya mun rantse da sunan Yahweh muka kuma ce, 'Bari Yahweh yakasance tsakanin kai da ni, kuma tsakanin zuriyata da zuriyarka, har abada."' Sa'an nan Dauda ya tashi tsaye ya tafi, Yonatan kuma ya koma cikin birnin.

Sura 21

1 Sa'an nan Dauda ya zo Nob domin ya ga Ahimelek babban firist. Ahimelek yazo domin ya taryi Dauda jikinsa na rawa ya kuma ce masa, "Donme kake kai kaɗai kuma babu wani tare dakai?" 2 Dauda ya cewa Ahimelek babban firist, "Sarki ya aike ni wata hidima ya kuma ce da ni, 'Kada kowa yasan komai game da abin nan da na aike ka, da kuma abin da na umarce ka.' Na aike 'yan matasan wani wurin. 3 Yanzu dai me kake da shi a hannu? Ba ni 'yar gurasa guda biyar, ko duk abin da ke samuwa." 4 Firist ya amsa wa Dauda ya kuma ce, "Babu gurasa da ba a tsarkake ba, amma akwai gurasa mai tsarki- Idan 'yan samarin sun keɓe kansu daga mata." 5 Dauda ya amsa wa firist, "Tabbas mata sun yi nisa da mu tun kwana uku da suka wuce, kamar yadda ya ke idan na fita. Abin da ke na mazajen an keɓe su har ma game da ɗan ƙanƙanin hidimomi. Balle irin wannan na yau lalle duk abin da suke da shi za a keɓe!" 6 Saboda haka sai firist ya ba shi gurasa da aka keɓe. Gama babu wata gurasa a wurin sai dai gurasar bagadi, wadda aka cire daga wurin Yahweh, domin ya sanya gurasa mai zafi a wurinta a ranar da aka ɗauke ta. 7 Yanzu dai ɗaya daga cikin bayin Saul yana nan a wannan rana, tsararre a gaban Yahweh. Sunansa Doweg mutumin Idom, shugaban makiyayan Saul. 8 Dauda ya cewa Ahimelek, "Yanzu babu wani mashi ko takobi? Domin ban kawo takobi ko makamaina tare da ni ba, domin hidimar sarki na buƙatar hanzari." 9 Firist ya ce, "takobin Goliyat Bafiliste, wandaka kashe a cikin kwarin Ila, tana nan nannaɗe cikin kaya a bayan falmara. Idan kana so ka ɗauki wannan, ka ɗauke ta, gama babu wani makami a nan." Dauda ya ce, "Babu wata takobi irin wannan; ba ni ita." 10 Dauda ya tashi ya gudu daga wurin Saul a wannan rana ya kuma tafi wurin Akish, sarkin Gat. 11 Bayin Akish suka ce masa, "Ba wannan ba ne Dauda, sarkin ƙasar? Ba sun yi waƙa da rawa ga juna dominsa ba, 'Saul yakashe nasa dubbai, Dauda kuma yakashe nasa dubbai goma?" 12 Dauda ya ajiye waɗannan maganganu cikin zuciyarsa yana kuma jin tsoran Akish, sarkin Gat. 13 Sai ya canza yanayinsa ya yi kamar marar hankali cikin hannuwansu; sai ya yi alamomi a bisa ƙofofin kyamaren ya kuma bar yawu na zubowa ƙasa zuwa gemunsa. 14 Sai Akish ya cewa bayinsa, "Duba, ku ga mutumin na hauka. Donme kukakawo shi wurina? 15 Ko na rasa mahaukatan mutane ne, har da zaku kawo mani wannan talikin yana yin wannan hali a gabana? Anya wannan taliki zai shigo cikin gidana?"

Sura 22

1 Sai Dauda ya bar can ya kuma tsere zuwa ƙogon Adullam. A lokacin da 'yan'uwansa da dukkan gidan mahaifinsa suka ji haka, sai suka gangara zuwa wurinsa. 2 Duk wanda ke cikin ƙunci, da duk wanda ke cikin bãshi, da kuma marar jin daɗi-dukkansu suka taru wurinsa. Dauda ya zama shugabansu. An sami mazaje kamar ɗari huɗu tare da shi. 3 Sai Dauda ya bar wurin zuwa Mizfa cikin Mowab. Ya cewa sarkin Mowab, "Na roƙe kaka bar mahaifina da mahaifiyata su zauna dakai har sai na san abin da Allah zai yi mani." 4 Sai ya bar su tare da sarkin Mowab. Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka zauna tare da shi dukkan kwanakin da Dauda ke cikin sansaninsa. 5 Sai annabi Gad ya cewa Dauda, "Kadaka tsaya a sansaninka. Tashi ka kuma shiga cikin ƙasar Yahuda." Sai Dauda ya bar wurin ya kuma tafi cikin jejin Heret. 6 Saul ya ji cewa an ga Dauda, tare da mutanen da ke tare da shi. A yanzu dai Saul yana a Gibiya ƙarƙashin itaciyar tamarisk a Rama, da mashinsa a hannu, kuma dukkan bayinsa na tsaye zagaye da shi. 7 Saul ya cewa bayinsa da ke tsaye zagaye da shi, "Ku saurara yanzu, mutanen Benyamin! Ko ɗan Yesse zai ba kowannenku filayen zaitun ne? Zai maida ku dukka shugabannin dubbai da shugabannin ɗari, 8 domin misanyar dukkan ku don tayar mani? Babu wani daga cikin ku da ya gaya mani lokacin da ɗa na ya yi alƙawari da ɗan Yesse. Babu waninku da ya ji tausayi na. Babu waninku da ya gaya mani cewar ɗana ya zuga bawana Dauda gãba da ni. Yau ya ɓoye yana jirana domin su kai mani farmaki." 9 Sai Doweg mutumin Idom, wanda ya tsaya kusa da bayin Saul, ya amsa, "Na ga ɗan Yesse ya iso Nob, wurin Ahimelek ɗan Ahitub. 10 Ya yi addu'a ga Yahweh don ya taimake shi, kuma ya bashi guziri da kuma takobin Goliyat Bafiliste." 11 Sai sarki ya aiki wani domin yakawo Ahimelek Firist ɗan Ahitub da dukkan gidan mahaifinsa, su firistocin da ke a Nob. Dukkansu suka zo wurin sarkin. 12 Saul ya ce, "Saurara yanzu, ɗan Ahitub." Ya amsa, "Ga ni nan, ubangidana." 13 Saul ya ce masa, "Donme ka yi mani makirci, kai da ɗan gidan Yesse, har ka ba shi gurasa, da takobi, ka kuma yi addu'a ga Allah domin ya taimake shi, domin ya tayar mani, ya ɓoye a asirce, kamar yadda ya ke yi a yau?" 14 Sai Ahimelek ya amsa wa sarki ya kuma ce, "Wane ne cikin dukkan bayinka da ke amintacce kamar Dauda, wanda ya ke surukin sarki kuma shugaba bisa 'yan tsaro, kuma ana girmama shi cikin gidanka? 15 Yau ne na fara yi masa addu'a Allah ya taimake shi? Nesa da ni! Kada sarki ya sanya wa bawansa wani laifi ko ga dukkan gidan mahaifina. Gama bawanka bai san komai ba game da wannan batu." 16 Sarki ya amsa, "Dole ka mutu, Ahimelek, kai da gidan mahaifinka." 17 Sarki ya cewa mai tsaron da ke tsaye kusa da shi, "Ka juyaka kashe firistocin Yahweh. Domin hannunsu na tare da Dauda, kuma domin sun san ya gudu, amma ba su gaya mani ba." Amma bayin sarkin ba su iya ɗibiya hannunsu su kashe firistocin Yahweh ba. 18 Sa'an nan ya cewa Doweg, "Juyaka kashe firistocin." Sai Doweg Ba-Idome ya juya ya fãɗawa firistocin; yakashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke yafe da falmarar linin a wannan rana. 19 Dakaifin takobi, ya abkawa Nob, birnin firistocin, mazaje da mataye, yara da jarirai, kuma bijimai da jakai da tumakai yakashe su dukka dakaifin takobi. 20 Amma ɗaya daga cikin 'ya'yan Ahimelek ɗan Ahitub, mai suna Abiyata, ya tsere ya gudu zuwa wurin Dauda. 21 Abiyata ya gaya wa Dauda cewar Saul yakashe firistocin Yahweh. 22 Dauda ya cewa Abiyata, "Na sani a wannan ranar, da Doweg Ba-Idome ke wajen, zai faɗa wa Saul. Ni ke da laifi domin mutuwar kowanne a cikin iyalin mahaifinka! 23 Ka zauna tare da ni kumakadaka ji tsoro. Gama wanda ya ke neman ranka shi ke neman nawa kuma. Zaka zauna lafiya tare da ni."

Sura 23

1 Aka gaya wa Dauda, "Ga shi, Filistiyawa na yaƙar Keila kuma suna washe wurin shiƙar hatsi." 2 Sai Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako ya kuma tambaye shi, "Ko na tafi in kai wa waɗannan Filistiyawan farmaƙi? Yahweh ya cewa Dauda, "Tafi kakai wa Filistiyawa farmaƙi ka ƙubutar da Keila." 3 Mazajen Dauda suka ce masa, "Duba, muna jin fargaba a nan Yahuda. Balle wai har mu tafi Keila Gãba da rundunar Filistiyawa?" 4 Sai Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako kuma. Yahweh ya amsa, "Ka tashi, gangara zuwa Keila. Gama zan baka nasara a bisa Filistiyawan." 5 Dauda da mutanensa suka tafi Keila suka kuma yi yaƙi da Filistiyawa. Ya kora garkunansu ya kuma buga su da babban yanka. Da haka Dauda ya kuɓutar da mazaunan Keila. 6 Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek ya gudu zuwa wurin Dauda a Keila, ya zo da falmara a hannunsa. 7 Aka gaya wa Saul cewa Dauda ya tafi Keila. Saul ya ce, "Allah ya ba da shi cikin hannuna. Gama yana tsare domin ya shiga cikin birnin da ke da ƙofofi da ƙyamare." 8 Saul ya tattara dukkan rundunarsa domin yaƙi, don ya gangara zuwa Keila, don ya kewaye Dauda da mutanensa. 9 Dauda na sane da cewar Saul na ƙulla cuta gãba da shi. Ya cewa Abiyata firist, "Kawo falmara nan." 10 Sai Dauda ya ce, "Yahweh, Allah na Isra'ila, bawanka tabbas ya ji cewa Saul na shirin zuwa Keila, ya lallatar da birnin sabili da ni. 11 Mutanen Keila zasu bashe ni cikin hannunsa? Saul zai gangaro, kamar yadda bawanka ya ji? Yahweh, Allah na Isra'ila, na roƙe ka, ka gaya wa bawanka." Yahweh ya ce, "Zai gangaro ya zo." 12 Sai Dauda ya ce, "Mutanen Keila zasu miƙa ni da mazaje na cikin hannun Saul?" Yahweh ya ce, "Zasu miƙaka." 13 Sai Dauda tare da mazajensa, da suke kamar ɗari shida, suka tashi suka fita daga Keila, suka kuma tafi daga wancan wuri zuwa wancan wurin. Aka gaya wa Saul da cewar Dauda ya kubce daga cikin Keila, daga nan kuma ya fãsa bin sa. 14 Dauda ya zauna cikin ƙarfafan wuraren tsaro cikin jeji, a cikin ƙasar duwatsu cikin hamada ta Zif. Saul ya nace da nemansa kowacce rana, amma Allah bai miƙa shi cikin hannunsa ba. 15 Dauda yaga cewar Saul ya fito neman ransa; a yanzu dai Dauda na cikin Hamadar Zif a Horesh. 16 Sa'an nan Yonatan, ɗan Saul, ya tashi ya tafi wurin Dauda a Horesh, ya kuma ƙarfafa hannunsa cikin Allah. 17 Ya ce masa, "Ka daka ji tsoro. Gama hannun Saul mahaifina ba zai same ka ba. Zaka zama sarki bisa Isra'ila, ni kuma zan zama na kusa dakai. Saul mahaifina shi ma ya san da haka." 18 Suka yi alƙawari a gaban Yahweh. Dauda ya zauna a Horesh, Yonatan kuma ya tafi gida. 19 Sai Zifiyawa suka zo wurin Saul a Gibiya suka ce, "Ba a wurinmu Dauda ya ke ɓuya ba cikin ƙarfafan wuraren tsaro na Horesh, a bisa tudun Hakila, wanda ya ke kudu da Yeshimon? 20 Yanzu ka zo, sarki! Bisa ga buƙatarka, ka zo! Namu fannin shi ne mu miƙa shi a hannun sarki." 21 Saul ya ce, "Bari Yahweh ya albarkace ku. Gama kun ji tausayina. 22 Ku tafi, ku tabbatar da hakan. Ku lura ku gane inda ya ke ɓuya da kuma wane ne ya gan shi a wurin. An gaya mani cewa yana da wayau ƙwarai. 23 Sai ku lura, ku kuma fahimci dukkan wuraren da ya ke ɓoye kansa. Ku dawo gare ni da tabbataccen zance, sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana cikin ƙasar, zan binciko shi waje daga dukkan dubban Yahuda." 24 Sai suka tashi suka riga Saul zuwa Zif. Yanzu Dauda da mazajensa suna a cikin hamadar Mawon, a cikin Araba zuwa Kudu da Yeshimon. 25 Saul da mutanensa suka tafi neman shi. Amma aka gaya wa Dauda wannan, sai ya tafi zuwa tudun duwatsu ya kuma zauna a hamadar Mawon. Lokacin da Saul ya ji, ya runtumi Dauda zuwa hamadar Mawon. 26 Saul ya bi ta wancan sashen tudun, Dauda kuma da mazajensa na tafiya a wancan sashen tudun. Dauda ya hanzarta ya guje wa Saul. Da Saul da mutanensa na kewaye da Dauda da mazajensa don su kama su, 27 sai ɗan saƙo ya iso wurin Saul ya kuma ce, "Hanzartaka kuma zo, gama Filistiyawa sun kawo hari a ƙasar." 28 Saboda haka Saul ya komo daga bin Dauda ya kuma tafi gãba da Filistiyawa. Saboda haka ake kiran wurin Dutsen Tsira. 29 Dauda ya tafi daga nan ya kuma zauna cikin ƙarfafan wuraren tsaro na Engedi.

Sura 24

1 Lokacin da Saul ya komo daga bin Filistiyawa, aka gaya masa, "Dauda na cikin Hamadar Engedi." 2 Sai Saul ya ɗauki mazaje zaɓaɓɓu dubu uku daga dukkan Isra'ila ya tafi neman Dauda da mazajensa a bisa Duwatsu na Awakin jeji. 3 Ya zo wurin mazamnin awakai nakan hanya, a inda akwai kogo. Saul ya shiga ciki don ya rufe ƙafarsa. Yanzu Dauda da mazajensa na zama a can ƙarshen ƙurewar kogon. 4 Mazajen Dauda suka ce masa, "Wannan ita ce ranar da Yahweh ya yi magana da ya ce maka, 'Zan bã da maƙiyanka cikin hannunka, don ka yi masa duk abin daka ga dama."' Sai Dauda ya tashi a hankali yana tafiya gaba a rarrafe ya kuma yanko sashen rigar Saul. 5 Daga baya sai zuciyar Dauda ta dame shi domin ya yagi sashen rigar Saul. 6 Ya cewa mazajensa, "Yahweh ya sauwaƙe da yiwa ubangidana haka, shafaffen Yahweh, har da zan miƙa hannu gãba da shi, ganin cewar shafaffe ne na Yahweh." 7 Don haka sai Dauda ya tsauta wa mazajensa da waɗannan maganganu, kuma bai bar su su kai wa Saul farmaƙi ba. Saul ya tashi, ya fita daga cikin kogon, yakama hanyarsa. 8 Bayan haka, Dauda shi ma ya tashi, ya fita daga cikin kogon, ya yi kira ga Saul: "Ubangidana sarki." Lokacin da Saul ya waiga bayansa, sai Dauda ya rusuna da fuskarsa ƙasa ya nuna masa bangirma. 9 Dauda ya ce wa Saul, "Me yasakake sauraron mutanen da ke cewa, 'Duba, Dauda yana neman ya cutar dakai?' 10 Yau ka ga yadda Yahweh ya miƙaka cikin hannuna sa'ad da muke a cikin kogon. Wasu suka ce mani in kashe ka, amma na bar ka. Na ce, 'Ba zan miƙa hannuna gãba da ubangidana ba; gama shafaffe ne na Yahweh.' 11 Duba, mahaifina, dubi sashen rigarka a hannuna. Ai ko yadda na yanki sashen rigarka amma ban kashe ka ba, kana iya fahimta da ganin cewa babu wata mugunta ko makirci cikin hannuna, kuma ban yi maka zunubi ba, ko da ya ke kana neman rainaka ɗauke. 12 Bari Yahweh ya shar'anta tsakanina dakai, kuma bari Yahweh ya sãka mani gãba dakai, amma hannuna ba zai tayar maka ba. 13 Kamar yaddakarin maganar mutanen dã ke cewa, 'Daga cikin mugu mugunta ke fitowa.' Amma hannuna ba za ya tayar maka ba. 14 Wane ne sarki ke fita neman sa? Wane ne kake kora? Mataccen kare! Wofi! 15 Bari Yahweh ya zama mai shari'a ya kuma shar'anta tsakani na dakai, ya kuma tabbatar, ya kuma tsaya mani ya kuma sa in tsira daga hannunka." 16 Bayan da Dauda ya gama furta waɗannan maganganun ga Saul, Saul ya ce, "Muryarka ce wannan, ɗana Dauda?" Saul ya tãda muryarsa ya yi kuka. 17 Ya ce wa Dauda, "Kai mai adalci ne fiye da ni. Gamaka sake biya na da alheri, inda na maido maka mugunta. 18 Ka furta yau yaddaka yi mani alheri, gama baka kashe ni ba lokacin da Yahweh ya miƙa ni ga jinƙanka. 19 Domin idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Bari Yahweh ya sãka maka da alheri yaddaka yi mani a yau. 20 Yanzu, na sani tabbas zaka zama sarki kuma sarautar Isra'ila zatakafu a hannunka. 21 Ka rantse mani har ga Yahweh cewar ba zaka datse zuriyata bayana ba, kuma ba zaka lallatar da sunana daga gidan mahaifina ba. 22 Sai Dauda ya yi alƙawari ga Saul. Sa'an nan Saul ya tafi gida, amma Dauda da mazajensa suka haura zuwakagara mai ƙarfi.

Sura 25

1 Yanzu dai Sama'ila ya mutu. Dukkan Isra'ila suka taru tare suka kuma yi masa makoki, suka kuma binne shi a cikin gidansa a Rama. Sa'an nan Dauda ya tashi ya kuma tafi cikin hamadar Faran. 2 Akwai wani mutum a Mawon, wanda dukiyarsa na cikin Karmel. Mutumin mai arziki ne ainun. Yana da tumakai dubu uku da awakai dubu ɗaya. Yana sausayar gashin tumakinsa akamel. 3 Sunan mutumin Nabal, kuma sunan matarsa Abigel. Mata ce mai hikima da kyan gani. Amma mutumin mai zafin hali da mugun tafarki ne a al'amuransa. Shi daga zuriyar gidan Kaleb ne. 4 Dauda ya ji daga cikin hamada cewa Nabal yana sausayar gashin tumakinsa. 5 Don haka Dauda ya aika samari mutum goma. "Ku tafi zuwakamel, ku tafi wurin Nabal, ku gaishe shi da sunana. 6 Za ku ce masa, 'Ka zauna cikin wadata. Salama gare ka salama ga gidanka, kuma salama ga dukkan mallakarka. 7 Na ji cewakana da 'yan sausaya. Makiyayanka na tare da mu, kuma bamu cutar da su ba, basu kuma rasa komai ba cikin dukkan lokacin da suke akarmel. 8 Ka tambayi samarinka, zasu kuma gaya maka. Yanzu bari 'yan samarina su sami tagomashi a idanunka, gama mun kawo ga ranar buki. Na roƙe kaka bã da duk abin dakake da shi a hannunka ga bayinka ga kuma ɗan ka Dauda." 9 Lokacin da samarin Dauda suka iso, suka faɗi dukkan wannan ga Nabal a madadin Dauda suka kuma jira. 10 Nabal ya amsa wa bayin Dauda, "Wane ne Dauda, kuma wane ne ɗan Yesse? Akwai bayi da yawa da ke ƙaurace wa iyayen gidansu a wannan kwanaki. 11 To na ɗauki gurasata da ruwa na da namana da na yanka domin 'yan sausayata, in kuma bada su ga mutanen da ban san ko daga ina suke ba?" 12 Saboda haka 'yan samarin Dauda suka juya suka tafi suka kuma dawo, suka kuma gaya masa duk abin da aka ce. 13 Dauda ya cewa mazajensa, "Kowanne mutum ya ɗaura takobinsa." Sai kowanne mutum ya ɗaura takobinsa. Dauda shi ma ya ɗaura takobinsa. Mazajen wajen ɗari huɗu suka bi Dauda, ɗari biyu kuma suka tsaya wurin kayayyaki. 14 Amma ɗaya daga cikin 'yan samarin ya gaya wa Abigel, matar Nabal; ya ce, "Dauda ya aiko da manzanni daga cikin hamada domin su gaishe da ubangidanmu, amma ya zage su. 15 Kuma mazajen sun nuna mana alheri. Ba mu cutu ba kuma ba mu ɓatar da komai ba cikin dukkan tafiyar da muka yi da su lokacin da muke cikin filaye. 16 Sun zama ganuwa a garemu da rana da dare, dukkan lokutan da muke tare da su muna kula da garken. 17 Saboda haka ki san wannan ki kuma san abin da zaki yi, gama akwai shirin mugunta game da ubangidanmu, kuma gãba da dukkan gidansa. Shi mutum ne marar cancanta da ba mai iya shawartar sa." 18 Sai Abigel ta tashi da sauri ta ɗauki gurasa curi ɗari biyu, inabi kwalba biyu, tumakai guda biyar gyararru, awo biyar na busasshen hatsi, da curin kauɗar inabi guda ɗari, da wainar 'ya'yan ɓaure guda ɗari biyu, ta ɗora su bisa jakai. 19 Ta cewa matasanta, "Ku sha gabana, zan kuma bi ku a baya." Amma bata gaya wa mijinta Nabal ba. 20 Yayin da take zuwa bisa jakinta ta kuma sauka daga bakin ƙofar dutsen, Dauda da shi da mazajensa suna saukowa zuwa gare ta, ta kuma tarbe su. 21 Yanzu Dauda ya riga ya faɗa cewa, "Tabbas a banza na tsare dukkan mallakar wannan mutum cikin hamada, har babu abin da ya ɓace cikin dukkan abin da ke nasa, kuma sai ya sãka mani da mugunta. 22 Bari Allah ya yi mani haka, Dauda, fiye da haka kuma, idan war haka da safe na bar ko da namiji ɗaya wanda ke nasa." 23 Lokacin da Abigel ta ga Dauda, ta hanzarta ta sauko daga jakarta ta kuma kwanta a gaban Dauda da fuskarta ƙasa ta kuma rusunar dakanta zuwa ƙasa. 24 Ta kwanta dab da ƙafafunsa ta kuma ce, "akainakaɗai, ubangidana, laifin yakasance. Na roƙe ka bari baiwarka ta yi magana dakai, ka kuma saurari maganganun baiwarka. 25 Kada ubangidana ya kula da wannan talikin marar amfani, Nabal, gama yadda sunansa ya ke, haka ya ke. Nabal ne sunansa, kuma sakarci na tare da shi. Amma ni baiwarka ban ga 'yan samarin ubangidana ba, waɗandaka aiko. 26 Yanzu dai, ubangidana, a bisa ran Yahweh, da kuma ranka, har tun da Yahweh ya tsare ka daga zubda jini, kuma daga ramuwa domin kanka da hannunka, yanzu bari maƙiyanka, da waɗanda ke neman yin mugunta ga ubangidana, su zamakamar Nabal. 27 Yanzu bari wannan kyautar da baiwarka takawo ga ubangidana a ba 'yan samarin da ke biye da ubangidana. 28 Na roƙe ka daka gafarta wa bawanka, gama Yahweh za ya gina wa ubangidana tabbataccen gida, domin ubangidana yana yaƙin Yahweh ne; kuma ba za a sami mugunta a cikinka ba dukkan kwanakin ranka." 29 Koda shi ke mutane sun tashi neman ranka, duk da haka ran ubangidana za a kãre shi cikin taro na masu rai daga wurin Yahweh Allahnka; kuma za ya ɗauke rayukan maƙiyanka, kamar daga aljihu na majajjawa. 30 Yahweh zai aiwatar wa ubangidana komai da ya alƙawarta maka, ya kuma zaɓe ka shugaba bisa Isra'ila. 31 Wannan ba zai zama abin nauyi gare ka ba - cewaka zubar da jinin marar laifi, ko domin ubangidana na ƙoƙarin kuɓutar dakansa. Gama a lokacin da Yahweh zai yi wa ubangidana alheri, ka tuna da baiwarka." 32 Dauda ya cewa Abigel, "Mai albarka ne Yahweh, Allah na Isra'ila, shi wanda ya aiko ki da kika same ni yau. 33 Hikimarki mai albarka ce kuma ke mai albarka ce, domin kin tsare ni daga zubar da jini kuma daga rama wakaina da hannuna! 34 A gaskiya, yadda Yahweh, Allah na Isra'ila, ke raye, shi wanda ya kiyaye ni daga cutar da ke, da ba domin kin yi sauri kin zo gare ni ba, da ba za a sami wani ragowa domin Nabal ko da ɗan jariri ne zuwa wayewar gari ba." 35 Sai Dauda yakarɓi abin da takawo masa daga hannunta; ya ce ma ta, "Tafi cikin salama zuwa gidanki; duba, na saurari muryarki kuma na gamsu." 36 Sai Abigel ta koma ga Nabal; gashi kuwa, ya shirya shagali a gidansa, kamar shagali na sarki; kuma zuciyar Nabal ta shagalta cikinsa, gama ya bugu ainun. Sai ta ƙi gaya masa komai har hasken safiya. 37 Sai ya zamana da safe, lokacin da ƙarfin giya ya fita daga Nabal, sai matarsa ta gaya masa waɗannan abubuwan; zuciyarsa ta mutu cikinsa, sai ya zamakamar dutse. 38 Sai ya zama bayan kwana goma sai Yahweh yakai wa Nabal farmaƙi har yakashe shi. 39 Da Dauda ya ji cewa Nabal ya mutu, ya ce, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda ya ɗauki zargin zãgin da na sha daga hannun Nabal ya kuma kãre bawansa daga mugunta. Ya juyar da aikin muguntar Nabal bisakansa." Sai Dauda ya aika ya kuma yi magana da Abigel, domin ya ɗauke ta a matsayin matarsa. 40 Lokacin da bayin Dauda suka iso wurin Abigel akarmel, suka yi mata magana suka ce, "Dauda ya aike mu gare ki mu ɗauke ki zuwa wurinsa ki zama matarsa." 41 Ta tashi, ta sunkuyar dakanta zuwa ƙasa, ta kuma ce, "Duba, baiwarka baiwa ce da za ta wanke ƙafafun bayin ubangidana." 42 Sai Abigel ta yi sauri ta tashi, ta hawo bisa jaka tare da bayi 'yanmata biyar da ke nata waɗanda suka biyo ta; sai kuma ta biyo bayin Dauda ta kuma zama matarsa. 43 Yanzu dai Dauda ya ɗauko wakansa Ahinowam ta Jezril a matsayin matarsa; su biyu suka zama matansa. 44 Haka kuma, Saul ya rigaya ya bayar da 'yarsa, matar Dauda, ga Falti ɗan Layish, wanda mutumin Galim ne.

Sura 26

1 Sai Zifiyawa suka zo wurin Saul a Gibiya suka kuma ce, "Ba Dauda yana ɓoyewa a cikin tudun Hakila ba, wanda ya ke kamin Yeshimon?" 2 Sai Saul ya tashi ya kuma tafi zuwa hamada ta Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra'ila, domin neman Dauda a cikin hamadar Zif. 3 Saul yakafa sansani a bisa tudun Hakila, wanda ke kafin Yeshimon, a gefen hanya. Amma Dauda na zama cikin hamadar, kuma ya ga cewa Saul na zuwa gare shi a cikin hamadar. 4 Sai Dauda ya aiki 'yan leken asiri kuma ya fahimci cewa tabbas Saul ya zo. 5 Dauda ya tashi ya kuma tafi wurin da Saul yakafa sansani; ya ga inda Saul ya kwanta, tare da Abna ɗan Nã, shugaban rundunarsa; Saul ya kwanta cikin sansanin, kuma mutanen suka zagaye shi, dukkansu suna barci. 6 Sa'an nan Dauda ya cewa Ahimelek Bahittiye, kuma ga Abishai ɗan Zeruwa, ɗan'uwan Yowab, "Wane ne zai tafi da ni wurin Saul a cikin sansani?" Abishai ya ce, "Ni! Zan tafi tare dakai." 7 Sai Dauda tare da Abishai suka tafi wurin rundunar cikin dare. Saul na barci cikin tsakiyar sansani tare da mãshinsakafe da ƙasa kusa dakansa. Abna da kuma sojojinsa suka kwanta zagaye da shi. 8 Sai Abishai ya cewa Dauda, "Yau Allah ya miƙa maƙiyinka cikin hannunka. Yanzu na roƙe kaka bar ni in cake shi har ƙasa da mashi da bugu ɗaya tak. Ba zan cake shi sau biyu ba." 9 Dauda ya cewa Abishai, "Kadaka hallaka shi; gama wane ne za ya miƙa hannunsa gãba da shafaffen Yahweh ya kuma zama marar laifi?" 10 Dauda ya ce, "Na rantse da ran Yahweh, Yahweh zai kashe shi, ko kuma ranar mutuwarsa ta zo, ko kuma ya tafi yaƙi ya mutu. 11 Bari Yahweh ya sauwaƙe mani da in miƙa hannuna gãba da shafaffe; amma yanzu, na roƙe ka, ka ɗauki mashin da ke kusa dakansa da kuma gorar ruwa, sai mu tafi." 12 Sai Dauda ya ɗauke mashin da gorar ruwan da ke kusa dakan Saul, suka kuma tafi. Babu wanda ya gansu ko ya san komai game da haka, ko wani ya farka, gama duk sun yi barci, gama barci mai nauyi daga wurin Yahweh ya faɗo bisansu. 13 Sa'an nan Dauda ya tashi ya tafi wancan ɓangaren ya kuma tsaya akan tsauni can nesa; akwai babbar rãta tsakaninsu. 14 Dauda ya yi kira da ihu ga mutanen ga kuma Abna ɗan Nã; ya ce, "Baka amsa ba, Abna?" Sai Abna ya amsa ya ce, "Kai wane ne da ke yi wa sarki ihu?" 15 Dauda ya cewa Abna, "Kai ba mutum ba ne mai ƙarfin hali? Wane ne kamarka a Isra'ila? To donme baka yi tsaron ubangidanka sarki ba? Gama wani ya shigo domin yakashe sarki ubangidanka. 16 Wannan abin daka yi ba shi da kyau. Na rantse da ran Yahweh, ka cancanci ka mutu domin baka yi tsaron ran sarki ubangidanka ba, shafaffe na Yahweh. Yanzu ka duba inda mashi da gorar ruwa da ke kusa dakansa suke!" 17 Saul ya sasance muryar Dauda ya kuma ce, "Wannan muryarka ce, ɗana Dauda?" Dauda ya ce, "Muryata ce, ubangidana, sarki." 18 Ya ce, "Me yasa ubangidana ke neman bawansa? Me na yi? Wacce mugunta ce ke cikin hannuna? 19 Yanzu saboda haka, na roƙe ka, bari ubangidana sarki ya saurari maganganun bawansa. Idan Yahweh ne ya zugaka gãba da ni, bari yakarɓi baiko; amma idan mutum ne, bari ya la'anta a fuskar Yahweh, gama yau sun kore ni waje, domin kada in manne wa gãdon Yahweh; sun ce mani, "Je ka yi sujada ga wasu alloli.' 20 Saboda haka yanzu, kadaka bar jinina ya zuba nesa da fuskar Yahweh; gama sarkin Isra'ila ya fito neman ƙwaro ɗayakamar yadda wani ke fita farautar makwarwa a bisa duwatsu." 21 Sai Saul ya ce, "Na yi zunubi. Dawo, Dauda, ɗana; domin ba zan ƙara cutar dakai ba, domin yau raina ya zama abin daraja a idonka. Duba, na yi kamar wawa kuma na yi mugun kuskure." 22 Dauda ya amsa ya kuma ce, "Duba, mashin ka yana nan, sarki! Bari ɗaya daga cikin samarin ka ya zo yakarɓa yakai maka. 23 Bari Yahweh ya sãka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa; domin Yahweh ya miƙaka cikin hannuna yau, amma ba zan bugi shafaffensa ba. 24 Duba, kamar yadda ranka ke da daraja a idanuna yau, bari raina ya zama da daraja a fuskar Yahweh, kuma bari ya kuɓutar da ni daga dukkan wahala." 25 Sai Saul ya cewa Dauda, "Bari ka yi albarka, Dauda ɗana! Lallai zaka yi manyan abubuwa kuma zaka yi nasara cikin dukkansu." Sai Dauda yakama hanyarsa, Saul kuma ya koma fadarsa.

Sura 27

1 Dauda ya faɗi a cikin zuciyarsa, "Wata rana zan hallaka ta hannun Saul; ba abin da ya fiye mani sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa; da haka Saul zai dena nema na cikin dukkan iyakar Isra'ila; ta haka zan kubce daga hannunsa." 2 Dauda ya tashi ya tsallaka can, shi da mazajensa ɗari shida da ke tare da shi, wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat. 3 Dauda ya zauna tare da Akish a Gat, shi da mazajensa, kowanne mutum da iyalansa, Dauda tare da matayensa biyu, Ahinowam Yeziriya, da kuma Abigel Bakameliya, matar Nabal. 4 Da aka gaya wa Saul cewa Dauda ya tsere zuwa Gat, sai bai sãke neman sa ba. 5 Dauda ya cewa Akish, "Idan na sami tagomashi a idanunka, bari su bani wuri cikin ɗaya daga cikin biranen ƙasar, domin in zauna nan: donme bawanka za shi zauna cikin masarauta tare dakai?" 6 Sai Akish ya ba shi Ziklag a wannan rana; shi yasa Ziklag ta zama ta sarakunan Yahuda har wa yau. 7 Shekarun da Dauda ya zauna cikin ƙasar Filistiyawa shekara ɗaya ce cikakkiya da wata huɗu. 8 Dauda da mazajensa sukakaiwa wurare dabam dabam farmaƙi, suka hari Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa; gama waɗannan al'ummai su ne asalin mazaunan ƙasar, idan kana tafiya zuwa Shur, har zuwa ƙasar Masar. Suna zama a nan wurin tun zamanun dã. 9 Dauda yakai wa ƙasar farmaƙi kuma bai bar namiji ko mace da rai ba; ya kwashi tumaki, da awakai, da jakuna, da raƙuma, da kumakayayyaki; sai ya dawo kuma zuwa Akish. 10 Akish zai ce, "Gãba da su waye yau kakai hari?" Dauda zai amsa, "Gãba da kudancin Yahuda," ko "Gãba da kudancin Yeramiyawa," ko "Gãba da kudancin Keniyawa." 11 Dauda bai bar namiji ko mace da rai domin yakawo su zuwa Gat ba, ya ce, "Sabodakada su yi magana game da mu, su ce 'Dauda ya yi kaza dakaza.'" Haka ya yi dukkan lokutan da ya ke zama a ƙasar Filistiyawa. 12 Akish ya amince da Dauda, yana cewa, "Ya sa mutanensa Isra'ilawa suna ƙyamarsa; zai zama bawana har abada."

Sura 28

1 Sai ya zama a wannan kwanaki Filistiyawa suka tara rundunar yaƙinsu domin yaƙi da Isra'ila. Akish ya cewa Dauda, "Ka san da cewar zaka fita tare da ni cikin runduna, kai da mazajenka." 2 Dauda ya cewa Akish, "Da haka zaka san abin da bawanka zai iya aikatawa." Akish ya cewa Dauda, "Da haka zan maishe ka mai tsarona na din-din din." 3 Yanzu dai Sama'ila ya mutu, kuma dukkan Isra'ila sun yi masa makoki suka kuma binne shi a Rama, a cikin birninsa. Haka kuma, Saul ya fanfari masu hurɗa da matattu ko da ruhohi. 4 Sai Filistiyawa suka tarakansu wuri ɗaya suka zo sukakafa sansani a Shunem; Saul kuma ya tara dukkan Isra'ila tare, suka kumakafa sansani a Gilbowa. 5 Lokacin da Saul ya ga rundunar Filistiyawa, sai ya ji tsoro, zuciyarsa kuma ta yi rawa sosai. 6 Saul ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako, amma Yahweh bai amsa masa ba - ko ta mafarki, ko da Urim, kuma wurin annabawa ba. 7 Sai Saul ya cewa bayinsa, "Ku nemo mani mace wadda ta ke magana da matattu, domin in tafi wurinta in nemi shawararta." Bayinsa suka ce masa, "Duba, akwai wata mace a Endo wadda ta ke faɗin cewa tana magana da matattu." 8 Saul ya ɓaddakama, ya sanya wasu kaya, ya tafi, shi da mutum biyu tare da shi; suka tafi wurin matar da dare. Ya ce, "Ki duba mani, na roƙe ki, da ruhu, ki kuma kirawo mani duk wanda na faɗi maki." 9 Matar ta ce masa, "Duba, kasan dai abin da Saul ya yi, yadda ya kori waɗanda ke magana da matattu ko ga ruhohi. To me yasakake shirya wa raina tarko, ka sa ni in mutu?" 10 Saul ya rantse mata har ga Yahweh ya kuma ce, "Na rantse da ran Yahweh, babu hukuncin da zai same ki domin wannan." 11 Matar ta ce, "Wane ne kake so in kirawo maka?" Saul ya ce, "Kirawo mani Sama'ila." 12 Da matar ta ga Sama'ila, sai tayi ihu da babbar murya ta kuma yi magana da Saul, cewa, "Donme ka ruɗe ni? Gamakai Saul ne." 13 Sarkin ya ce ma ta, "Kada ki ji tsoro. Me kika gani?" Matar ta cewa Saul, "Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa." 14 Ya ce mata, "Yayakamaninsa ya ke?" Ta ce, "Tsohon mutum yana haurowa sama; yana sanye dakaya." Saul ya gane cewa Sama'ila ne, sai ya faɗi ƙasa fuskarsa ƙasa ya kuma nuna bangirmansa. 15 Sama'ila ya cewa Saul, "Donme ka dame ni har daka hauro da ni sama?" Saul ya amsa, "Na gaji sosai, Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni kuma ya ƙi ya amsa mani, ko ta wurin annabawa, ko ta mafarkai. Saboda haka na kirawo ka, domin ka sanar da ni abin da zan yi." 16 Sama'ila ya ce, "Mene ne kake tambaya ta, tun da Yahweh ya bar ka, kuma ya zama abokin gãbarka? 17 Yahweh ya aiwatar maka da abin da ya faɗa zai yi. Yahweh ya raba mulkin daga hannunka ya kuma bayar ga wani - ga Dauda. 18 Domin bakayi biyayya da muryar Yahweh ba kuma baka aiwatar da fushinsa mai ƙuna bisa Amalekawa ba, shi kuma ya yi maka haka a wannan rana. 19 Duk da haka, Yahweh zai miƙa Isra'ila dakai cikin hannuwan Filistiyawa. Gobe kai da 'ya'yanka maza zaku kasance tare da ni. Yahweh kuma za ya miƙa rundunar Isra'ila cikin hannuwan Filistiyawa." 20 Sa'an nan Saul nan da nan ya faɗi da ƙarfinsa zuwa ƙasa da kuma fargaba saboda maganganun Sama'ila. Babu wani sauran ƙarfi a cikinsa, gama bai ci abinci ba dukkan yini, ko a wannan dare. 21 Macen ta zo wurin Saul ta ga cewa yana cikin babbar damuwa, Ta ce masa, "Duba, baiwarka ta saurari muryarka; Na ɗibiya raina a cikin hannuwana na kuma saurari maganganun daka faɗi mani. 22 Don haka yanzu, na roƙe ka, kai maka saurari muryar baiwarka macen, na kuma shirya maka abinci ɗan kaɗan a gabanka. Ka ci sabodaka maido da ƙarfi domin sa'ad da zakakama hanyarka." 23 Amma Saul bai yarda ba ya kuma ce, "Ba zan ci ba." Amma bayinsa, tare da macen, suka nace masa, ya kuma saurari muryarsu. Saboda haka ya tashi daga ƙasa ya zaunakan gado. 24 Matar tana da ɗan maraƙi mai ƙiba a cikin gidan; ta yi sauri ta yanka shi; ta ɗauki gari, ta cuɗa shi, ta kuma shirya gurasa da shi. 25 Takawo ga Saul da bayinsa, suka kuma ci. Sa'an nan suka tashi suka kuma yi tafiyarsu a wannan daren.

Sura 29

1 Yanzu Filistiyawa sun taru tare dukkan rundunarsu a Afek; Isra'ilawa suka yi sansani kusa da magudanar ruwa da ke cikin Yezril. 2 Sarakunan Filistiyawa suka wuce a ɗari-ɗarinsu da kuma dubbai; Dauda da mazajensa suka wuce suna daga baya tare da Akish. 3 Sai sarakunan Filistiyawa suka ce, "Mene ne wannan Ibraniyawan ke yi a nan?" AKish ya cewa sauran sarakunan Filistiyawan, "Ba wannan ba ne Dauda, bawan Saul, sarkin Isra'ila, wanda ke tare da ni kwanakin nan, ko ace waɗannan shekaru, kuma ban same shi da wani laifi ba tun ranar da ya zo wurina har wa yau?" 4 Amma sarakunan Filistiyawa suka yi fushi da shi; suka ce masa, "Ka sa wannan mutum ya tafi, domin ya tafi wurin daka bashi, kadaka bar shi ya biyo mu zuwa filin dãga, domin kada ya juya ya zama maƙiyinmu cikin yaƙi. Don ta yaya wannan talikin zai yi sulhu da ubangidansa? Ba ta ɗaukar kawunan mutanen mu ba ne? 5 Ba wannan ba ne Dauda wanda aka yi wa waƙa a junansu cikin rawa, cewa, 'Saul yakashe dubbansa, Dauda kuma yakashe nasa dubbai goma'?" 6 Sai Akish ya kirawo Dauda ya kuma ce masa, "Na rantse da ran Yahweh, ka zama nagari, kuma fitarka da shigowarka tare da ni cikin runduna mai kyau ne a gani na; gama ban iske wani laifi gare ka ba tun randa ka zo wurina zuwa wannan rana. 7 Sai ka juya yanzu ka kuma tafi cikin salama, domin kada ka yi wa sarakunan Filistiyawa laifi." 8 Dauda ya cewa Akish, "Amma me na yi? Mene ne ka samu a cikin bawanka duk sa'ad da nake tare da kai zuwa wannan rana, da har ba zan je inyi yaƙi da maƙiyan ubangidana sarki ba?" 9 Akish ya amsa ya kuma cewa Dauda, "Na san da cewa kai marar laifi ne a idanuna kamar mala'ikan Allah; duk da haka sarakunan Filistiyawa suka ce, 'Ba zai haura tare da mu ba zuwa yaƙin.' 10 Saboda haka sai ka tashi da sassafe tare da bayin ubangidanka waɗanda suka zo tare da kai; da zarar ka tashi da asussuba ka kuma sami haske, ka tafi." 11 Sai Dauda ya tashi da sauri, shi da mazajensa, don su tafi da safe, su dawo ƙasar Filistiyawa. Amma Filistiyawan suka haura zuwa Yezril.

Sura 30

1 Ya zama kuma, da Dauda da mazajensa suka iso Ziklag a rana ta uku, da Amalekawa suka kawo farmaki bisa Negeb da kuma kan Ziklag. Suka kai wa Ziklag hari, suka ƙona ta, 2 suka kwashe matayen da kowa da ya ke ciki, da manya da ƙanana. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe suka yi tafiyarsu. 3 Lokacin da Dauda da mazajensa suka iso birnin, an ƙone, kuma matayensu, da 'ya'yansu maza, da 'ya'yansu mata an ɗauke su zuwa bauta. 4 Sa'an nan Dauda da mutanen da ke tare da shi suka tãda murya suka yi kuka har sai da babu wani sauran ƙarfi kuma da za su yi kuka. 5 Aka kwashe matan Dauda guda biyu, Ahinowam Yeziriya, da Abigel matar Nabal mutumiyar Karmel. 6 Dauda ya dãmu ƙwarai, gama mutanen suna magana game da su jefe shi da duwatsu, gama dukkan mutanen suna ɓacin rai, kowanne mutum domin 'ya'yansa maza da mata; amma Dauda ya ƙarfafa kansa cikin Yahweh, Allahnsa. 7 Dauda ya cewa Abiyata ɗan Ahimelek, firist, "Na roƙe ka, ka kawo mani falmara a nan wurina." Sai Abiyata ya kawo falmarar wurin Dauda. 8 Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin bishewa, cewa, "Idan na bi wannan mayaƙan, zan sha kansu?" Yahweh ya amsa, "Bi su, domin lallai za ka sha kansu, kuma tabbas za ka sake ƙwato dukkan abubuwan." 9 Sai Dauda ya tafi, shi da mazajensa ɗari shida waɗanda ke tare da shi; suka iso magudanar Beso, inda waɗanda aka bari suka zauna. 10 Amma Dauda ya ci gaba da runtumar su, shi da mazaje ɗari huɗu; gama ɗari biyu sun tsaya a baya, wato waɗanda ƙarfinsu ya gãza da baza su iya haurawa zuwa magudanar Beso ba. 11 Suka gamu da wani Bamasare cikin saura suka kawo shi ga Dauda; suka ba shi gurasa, ya kuma ci; suka ba shi ruwa ya sha; 12 sai kuma suka ba shi gutsuren wainar 'ya'yan ɓaure da curin kauɗar inabi guda biyu. Bayan da ya ci, ƙarfinsa ya dawo kuma, gama bai ci gurasa ba ko ya sha wani ruwa har kwana uku da yini uku. 13 Dauda ya ce masa, "Kai na wane ne? Daga ina ka fito?" Ya ce, "Ni ɗan matashin ƙasar Masar ne, bawan Ba-amaleke; ubangidana ya baro ni domin kwana uku da suka shige rashin lafiya ta same ni. 14 Mu ka kai farmaƙi a yankin Negeb na Keretiyawa, da abin da ya ke na Yahuda, da kuma Nageb na Kaleb, kuma muka ƙona Ziklag." 15 Dauda ya ce masa, "Za ka kawo ni zuwa wurin waɗannan maharan?" Bamasaren ya ce, "Ka rantse mani ga Allah da cewar ba zaka kashe ni ko ka bashe ni a cikin hannuwan ubangidana ba, ni kuma zan kawo ka wurin waɗannan maharan." 16 Da Bamasaren ya kawo Dauda wurin, maharan na nan barbaje a dukkan ƙasar, suna ci suna sha suna rawa saboda dukkan ganimar da suka kwaso daga cikin ƙasar Filistiyawa da kuma ƙasar Yahuda. 17 Sai Dauda ya kai masu hari tun daga wayewar gari har yammancin da gari ya waye. babu mutum wanda ya tsira sai dai 'yan matasa guda ɗari, waɗanda suka haura bisa raƙuma suka kuma gudu. 18 Sai Dauda ya maido da dukkan abin da Amalekawa suka ɗauke; kuma Dauda ya ƙubutar da matansa biyu. 19 Babu abin da ya ɓace, ko ƙarami ko babba, ko 'ya'ya maza ko 'ya'ya mata, ko kayan ganima, ko wani abu da maharan suka ɗauko wa kansu. 20 Dauda ya dawo da komai. Dauda ya ɗauko dukkan garken da kuma dabbobin, waɗanda mazajen suka koro gaba da sauran garkunan. Suka ce, "Wannan ganimar Dauda ce." 21 Sai Dauda ya komo wurin sauran ɗari biyun da ƙarfinsu ya gãza ba su bi shi ba, waɗanda sauran suka sa su jira a magudanar Beso. Waɗannan mazajen suka zo domin su tarbi Dauda da kuma mutanen da ke tare da shi. Da Dauda ya iso wurin mutanensu, ya gaishe su. 22 Sai dukkan mugayen mutanen da marasa amfani da ke cikin waɗanda suka tafi tare da Dauda suka ce, "Domin waɗannan mazajen ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su komai daga cikin ganimar da muka samu ba. Sai dai kowanne ɗaya daga cikinsu ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa, ya bishe su, su tafi." 23 Sa'an nan Dauda ya ce, "Ba za ku yi haka ba, 'yan'uwana, da abin da Yahweh ya ba mu. Ya kiyaye mu ya kuma bayar da maharan da suka tayar mana a hannuwanmu. 24 Waye zai saurari ku a kan wannan zance? Gama kamar yadda rabon kowanne da ya tafi yaƙin, haka zaya zama rabon duk wadda ya jira wurin kaya; za su sami rabo dai-dai da kowa." 25 Haka ya ci gaba da zama daga wannan rana har wa yau, gama Dauda ya maida haka doka da kuma ka'ida a Isra'ila. 26 Da Dauda ya kai Ziklag, ya aika daga cikin ganimar zuwa ga shugabannin Yahuda, zuwa ga abokansa, cewa, "Duba, ga kyauta domin ku daga ganimar maƙiyan Yahweh." 27 Ya kuma aika da waɗansu zuwa ga shugabannin da ke a Betel, da kuma waɗanda ke a Ramot na Kudu, kuma ga waɗanda suke daga Jattir, 28 kuma ga waɗanda ke cikin Arowa, kuma zuwa ga waɗanda ke a Sifmot, kuma ga waɗanda suke a Ishtemowa. 29 Ya kuma aika zuwa ga shugabannin da ke cikin Rakal, kuma zuwa ga waɗanda ke cikin biranen Yeramilawa, kuma ga waɗanda ke cikin biranen Kenawa, 30 kuma ga waɗanda ke cikin Homa, da kuma waɗanda ke zama a Borashan, ga kuma waɗanda ke cikin Atak, 31 ga kuma waɗanda ke cikin Hebron, ga kuma dukkan wuraren da Dauda da kansa da mazajensa ke zuwa kodayaushe.

Sura 31

1 Yanzu Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ila. Mazajen Isra'ila suka gudu daga fuskar Filistiyawa suka kuma faɗi matattu a Tsaunin Gilbowa. 2 Filistiyawa suka runtumi Saul da 'ya'yansa. Filistiyawa suka kashe Yonatan, Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yansa maza. 3 Yaƙin ya yi zafi gãba da Saul, kuma masu harbin bãka suka sha kansa. Yana cikin ƙunci da zafi sabili da su. 4 Sai Saul ya cewa mai ɗaukar masa makamai, "Zaro takobinka ka soke ni da ita. In ba haka ba, waɗannan marasa kaciyar zasu zo su wulaƙanta ni." Amma mai ɗaukar masa makamai ya ƙi, gama yana jin tsoro. Sai Saul ya ɗauki takobinsa ya faɗi bisanta. 5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya ɗauki ta sa takobin ya faɗa kanta ya mutu da shi. 6 Haka Saul ya mutu, 'ya'yansa uku, da kuma mai ɗaukar masa makamai - waɗannan mutanen dukka suka mutu tare rana ɗaya. 7 Lokacin da mutanen Isra'ila da ke a wancan ɓangaren kwarin, da kuma waɗanda ke gaba da Yodan, suka ga cewa mazajen Isra'ila sun gudu, kuma Saul da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka ƙaurace wa ƙauyukansu suka gudu, sai kuma Filistiyawa suka zo suka zauna cikinsu. 8 Sai ya zama kuma washegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka ga Saul tare da 'ya'yansa maza uku sun faɗi a Dutsen Gilbowa. 9 Suka yanke kansa suka kuma cire kayan yaƙinsa, suka kuma aika 'yan saƙo cikin ƙasar Filistiyawa ko'ina domin su kai labarai ga haikalin gumakansu kuma ga mutanensu. 10 Suka ajiye rigar yaƙinsa cikin haikalin Ashtoret, kuma suka rataye jikinsa ga ganuwar birnin Bet Shan. 11 Lokacin da mazaunan Yabesh Giliyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul, 12 dukkan mazaje 'yan yaƙi suka tashi suka yi tafiya dukkan dare suka ɗauki jikin Saul da kuma jikkunan 'ya'yansa daga ganuwar Bet Shan. Suka tafi Yabesh suka ƙona su a can. 13 Sai Suka ɗauki ƙasusuwansu suka binne su a ƙarƙashin itaciyar tamarisk a Yabesh, suka yi azumi na kwana bakwai.

Littafin Sama'ila Na Biyu
Littafin Sama'ila Na Biyu
Sura 1

1 Bayan mutuwar Saul, Dauda ya dawo daga harin Amelikawa ya kuma zauna a Ziglak kwana biyu. 2 A rana ta uku, wani mutum ya zo daga sansanin Saul da tufafinsa a yage da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dauda sai ya kwanta rub da ciki a ƙasa ya miƙe jikinsa ya yi ruku'u a gabansa. 3 Dauda ya ce masa, "Daga ina ka fito?" Ya amsa, "Na kubce daga sansanin Isra'ila ne." 4 Dauda ya ce masa, Idan ka yarda ka gaya mani yadda abubuwa suka kasance." Ya amsa, "Mutane sun gudu daga yaƙi. Da yawa sun faɗi kuma da yawa sun mutu. Saul da Yonatan ɗansa su ma sun mutu." 5 Dauda ya ce ma saurayin, "Yaya ka sani cewa Saul da Yonatan ɗansa sun mutu?" 6 Saurayin ya amsa, "Sa'a ce na ci. ya zamana ne ina kan Dutsen Gilbowa, sai ga Saul yana jingine akan mashinsa, karusai da mahaya suka kusa rutsasu. 7 Saul ya juya ya gan ni ya kuma kira ni da murya. Na amsa, 'Ga ni.' 8 Ya ce mani, "Waye kai?" Na amsa masa, 'Ni Ba-amelike ne.' 9 Ya ce mani, ' Idan ka yarda ka tsaya a kaina ka kasheni, gama zafin azaba ya sha kaina, amma duk da haka rai yana ciki na' 10 Saboda haka na tsaya a kansa na kasheshi, domin na sani ba zai rayu ba bayan ya faɗi. Sa'an nan na ɗauki kambin da ke kansa da ɗamarar da ke damtsensa kuma, na kawo su nan gunka, ubangidana." 11 Sai Dauda ya ƙeƙƙece tufafinsa dukkan mutanen da ke tare da shi suka yi haka su ma. 12 Suka yi makoki, da kuka, kuma suka yi azumi har yamma saboda Saul, domin ɗansa Yonatan, domin mutanen Yahweh, domin kuma gidan Isra'ila sabili da sun faɗi ta hannun takobi. 13 Dauda ya cewa saurayin, 'Daga ina ka ke?' Ya amsa, 'Ni yaron wani baƙo ne a ƙasar, Ba-amaleke." 14 Dauda ya ce masa, "Me ya sa ba ka ji tsoron kashe shafaffen sarki na Yahweh da hannunka ba?" 15 Dauda ya kira ɗaya daga cikin samarin ya ce, "Tafi ka kashe shi." Sai wannan mutumin ya tafi ya buga shi ƙasa. Sai Ba-ameliken ya mutu. 16 Sai Dauda ya cewa mataccen Ba'ameliken, '" Alhakin jininka na kanka domin bakinka da kansa yana shaida gãba da kai ya ce, 'Na kashe shafaffen sarki na Yahweh.'" 17 Sa'an nan Dauda ya yi wannan waƙar makoki game da Saul da Yonatan ɗansa. 18 Ya bada doka ga mutane su koyar da Waƙar Bãka ga 'ya'yan Yahuda, wanda aka rubuta a Littafin Yashar. 19 "‌Ɗ‌aukakarki, Isra'ila, ya mutu, an yi kisa a tuddanki! Aiya jarumawa sun faɗi! 20 Kada ku faɗa a Gat, kada ku yi shelarsa a titunan Askelon, domin kada 'yan'matan Filistiyawa su yi farinciki, domin kada 'yan'matan marasa kaciya su yi biki. 21 Duwatsun Gilbowa, kada raɓa ko ruwan sama su kasance a kanku, ko gonaki masu bada hatsi domin baiko, gama a nan aka lalata garkuwar ƙarfafa. Garkuwar Saul ba a ƙara shafe ta da mai ba. 22 Daga jinin waɗanda aka kashe, daga jikin ƙaƙƙarfa, bãkan Yonatan bai juya ba, kuma takobin Saul bata dawo wofi ba. 23 Saul da Yonathan ƙaunatattu ne masu alheri a rayuwa, a mutuwarsu ba a raba su ba. Sun fi gaggafai zafin gudu, sun fi zakoki ƙarfi. 24 Ku 'yan'matan Isra'ila, ku yi kuka domin Saul, wanda ya suturtar daku cikin shunayya da duwatsu masu daraja da kayan zinariya masu ƙayatarwa a tufafinku. 25 Aiya jarumawa sun faɗi tsakiyar yaƙi! An kashe Yonatan a tuddanki, 26 Ina da damuwa domin ka, ɗan'uwana Yonatan. Amintacce kake a gare ni. ‌Ƙaunarka a gare ni abin al'ajibi ne, ya zarce ƙaunar mata. 27 Aiya jarumawa sun faɗi, makaman yaƙi kuma sun lalace!"

Sura 2

1 Bayan wannan Dauda ya tambayi Yahweh ya ce, 'Ko in haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?" Yahweh ya amsa masa, "Ka haura." Dauda ya ce, "Wanne birnin zan je?" Yahweh ya amsa, "Zuwa Hebron." 2 Sai Dauda ya tafi Hebron da matayensa guda biyu, Ahinowam daga Yezril, da Abigel daga Karmel, gwauruwar Nabal. 3 Dauda ya kawo mutanen da ke tare da shi, waɗanda kowannen su ya kawo nasa iyalin, zuwa biranen Hebron inda suka fara zaunawa. 4 Sa'an nan mutane daga Yahuda suka zo suka naɗa Dauda sarki bisa gidan Yahuda. Aka cewa Dauda, '"Mutanen Yabes Giliyad ne suka bizne Saul." 5 Sai Dauda ya aiki manzanni ga mutanen Yabes Giliyad suka kuma ce masu, "Yahweh ya albarkace ku, tunda ku ka nuna wannan riƙon amana ga ubangidanku Saul har ku ka bizne shi. 6 Bari yanzu Yahweh ya nuna maku alƙawarin riƙon amana da aminci. Ni kuma zan yi maku wannan alheri domin kun yi wannan abu. 7 Yanzu dai, bari hannuwanku su ƙarfafa; ku yi ƙarfin hali domin Saul ubangidanku ya mutu kuma gidan Yahuda sun naɗa ni shafaffen sarki bisan su." 8 Amma Abna ɗan Nã, sarkin yaƙin rundunar Saul, ya ɗauki Ishboshet ɗan Saul ya kuma kawo shi Mahanam, 9 Ya naɗa Ishboshet sarki bisa Giliyad, Ashar, Yazril, Ifraim, Benyamin, da kuma bisa dukkan Isra'ila. 10 Ishboshet ɗan Saul, yana da shekaru arba'in da ya soma mulki bisa Isra'ila, ya kuma yi mulki shekara biyu. Amma gidan Yahuda suka bi Dauda. 11 Lokacin da Dauda ke sarki cikin Hebron bisa gidan Yahuda shekara bakwai ne da wata shida. 12 Abna ɗan Nã, da barorin Ishboshet ɗan Saul, su ka tafi daga Mahanayim zuwa Gibiyan. 13 Yowab ɗan Zeruya da barorin Dauda suka fita suka gamu da su a tafkin Gibiyan. A nan suka zauna, ɗaya ƙungiyar a ɗaya gefen tafkin ɗayan kuma a ɗaya wancan gefen. 14 Abna ya cewa Yowab, "Bari samarin su tashi su yi gãsa a gabanmu." Sai Yowab ya ce, "Bari su tashi." 15 Sai samarin suka tashi suka tattaru tare, sha biyu domin Benyami da Ishboshet ɗan Saul, kuma sha biyu daga barorin Dauda. 16 Kowanne ya danƙe abokin gasarsa a kai ya soke gefen cikin ɗan'uwansa da takobi, sai su ka faɗi ƙasa tare. Shi ya sa aka kira wurin nan da Ibraniyanci, "Helkat Hazzurim." ko "Filin Takkuba" wanda ya ke cikin Gibiyan. 17 Yaƙin ya yi zafi ainun a ranar nan kuma aka buga Abna da mutanen Isra'ila a gaban barorin Dauda. 18 'Ya'ya maza uku na Zeruya suna wurin: Yowab, Abishai, da Asahel. Asahel mai zafin gudu da ƙafa ne kamar barewar jeji. 19 Asahel ya sheƙa da gudu bayan Abna ya bishi kurkusa ba ratsewa wani gefen. 20 Abna ya waiga bayansa ya ce, "Kai ne kuwa Asahel?" Ya amsa, "I, ni ne." 21 Abna ya ce masa, "Ka juya zuwa gefenka na dama ko hagunka, ka cafke ɗaya daga cikin samarin ka karɓe makaminsa." Amma Asahel ya ƙi ratsewa wani gefen. 22 Sai Abna ya sãke cewa Asahel, "Ka dena bi na donme zan buga ka ƙasa? ‌Ƙaƙa kuma zan fuskanci, ɗan'uwanka Yowab?" 23 Amma Asahel ya ƙi ratsewa, saboda haka Abna ya soki jikinsa da kan mashinsa marar kaifi har ma mashin ya fito ta wancan gefen. Asahel ya faɗi ya mutu. Ya zamana fa duk wanda ya iso inda Asahel ya faɗi ya mutu, sai ya dakata ya tsaya shuru. 24 Amma Yowab da Abishai suka bi Abna. Sa'ad da rana take faɗuwa, suka iso tudun Amana, da ke kusa da Giya a hanyar da ta bi ta jejin Gibiyon. 25 Mutanen Benyaminu suka haɗa kansu gaba ɗaya suka goyi bayan Abna suka tsaya a kan tudu. 26 Sai Abna ya kira Yowab ya ce, "Dole ne takobi ya hallakar har abada? Ba ka sani zai zama da ɗaci a ƙarshe ba? Har yaushe zai zamana kafin ka gaya wa mutanenka su janye daga fafarar 'yan uwansu?" 27 Yowab ya amsa, "Na rantse da Yahweh, hakika da baka faɗi haka ba, da sojojina sun fafari 'yan 'uwansu har zuwa safiya!" 28 Sai Yowab ya busa ƙaho, mutanensa duk suka tsaya suka dena fafarar Isra'ila, kuma ba su sake yin faɗa ba. 29 Abna da mutanensa suka yi ta tafiya dare farai cikin Araba. Suka haye Yodan, suka yi ta tafiya dukkan safiyan nan, sa'annan ne suka kai Mahanayim. 30 Yowab ya juyo daga fafarar Abna. Ya tara dukkan mutanensa, cikinsu aka rasa Asahel da sojojin Dauda guda goma sha tara. 31 Amma mutanen Dauda sun riga sun kashe mutane 360 na Benyamin da ke tare da Abna. 32 Sai suka ɗauki Asahel suka binne shi cikin kabarin mahaifinsa, da ke a Baitalami. Yowab da mutanensa suka yi tafiya dare farai, gari kuma ya waye masu a Hebron.

Sura 3

1 Akwanakin nan dai aka yi dogon yaƙi tsakani gidan Saul da gidan Dauda. Gidan Dauda ya yi ta ƙara ƙarfi, amma gidan Saul ya yi ta raguwa. 2 Aka haifa wa Dauda 'ya'ya maza a Hebron.‌ Ɗan farinsa Amon, da Ahinowam daga Yazril ta haifa masa. 3 ‌Ɗansa na biyu, Kilyab, Abigel gwauruwar marigayi Nabal daga Karmel ta haifeshi, Ɗansa na ukun Absalom ne, ɗan Ma'aka, ɗiyar Talmai, sarki Geshu. 4 ‌Ɗan Dauda na huɗu, Adonija, ɗan Hagit ne. ‌Ɗansa na biyar Sefatiya ne ɗan Abtiyal, 5 na shidan, Itram ne, ɗan Egla matar Dauda. Waɗannan 'ya'ya maza aka haifa wa Dauda a Hebron. 6 Ya zamana fa a lokacin yaƙi tsakanin gidan Saul da gidan Dauda sai Abna ya ƙarfafa kansa a gidan Saul. 7 Saul na da kwarkwara wadda sunanta Risfa, ɗiyar Aya ce. Sai Ishboshet ya cewa Abna, "Me yasa ka kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?" 8 Sai Abna ya husata da maganganun Ishboshet ya ce, "Ni kan kare ne na Yahuda? Yau ina nuna aminci ga gidan Saul, mahaifinka, da 'yan'uwansa, da kuma abokanansa, ta wurin yadda ban basheku ba cikin hannun Dauda. Amma yanzu kana zargi na da laifi game da wannan matar. 9 Bari Allah ya yi mani, Abna, harma fiye da haka, idan ban yi wa Dauda yadda Yahweh ya rantse masa ba, 10 a tada masarautar daga gidan Saul, a kafa kursiyin Dauda bisa Isra'ila da bisa Yahuda daga Dan zuwa Bayasheba." 11 Ishboshet bai iya amsa wa Abna ba koda magana ɗaya, domin yana jin tsoronsa. 12 Sa'an nan Abna ya aika manzanni ga Dauda su yi masa magana dominsa cewa, "‌Ƙ‌asar wane ne wannan? Ka yi yarjejeniya da ni, gama hannuna na tare da kai, in kawo maka dukkan Isra'ila." 13 Dauda ya amsa, "Da kyau zan yi yarjejeniya da kai. Abu ɗaya na ke biɗa a gare ka shi ne cewa ba za ka ga fuskata ba sai dai da farko ka kawo Mikal, ɗiyar Saul, sa'ad da za ka zo ka gan ni." 14 Sai Dauda ya aika manzanni zuwa wurin Ishboshet, ɗan Saul, cewa, "Ka ba ni matata Ishboshet Mikal, wadda na biya sadakin loɓar kaciya ɗari na Filistiyawa domin ta. 15 Sai Ishboshet ya aika a kawo Mikal, ya kuma karɓe ta daga mijinta, Faltiyel ɗan Layis. 16 Mijinta ya tafi tare da ita, yana tafiya yana kuka, ya bi ta zuwa Bahurim. Sai Abna ya ce masa, "Ka koma gida yanzu." Sai ya koma. 17 Abna ya yi magana da dattawan Isra'ila cewa, "Da daɗewa kun yi ta ƙoƙarin ku naɗa Dauda ya zama sarki bisan ku. 18 Yanzu ku yi haka. Gama Yahweh ya yi magana game da Dauda cewa, 'Ta hannun bawana Dauda zan ceci mutanena Isra'ila daga hannun Filistiyawa daga kuma dukkan hannun maƙiyansu.'" 19 Abna kuma da kansa ya yi magana da mutanen Benyamin. Sai Abna kuma ya tafi ya yi magana da Dauda a Hebron domin ya bayyana masa dukkan abin da Isra'ila da dukkan gidan Benyamin gaba ɗaya suka yi niyar aikatawa. 20 Da Abna da mutanensa guda ashirin suka iso cikin Hebran domin su ga Dauda, Dauda ya shirya masu liyafa. 21 Abna ya bayyana wa Dauda, "Zan tashi in tattaro maka dukkan Isra'ila, ubangidana sarkina, domin su yi alƙawari da kai, domin ka yi mulki bisa dukkan abin da kake marmari." Sai Dauda ya sallami Abna, Abna kuma ya koma da salama. 22 Sai sojojin Dauda da Yowab suka dawo daga hari, tare da ganima mai tarin yawa. Amma Abna ba ya tare da Dauda a Hebran. Dauda ya rigaya ya sallame shi, Abna kuma ya tafi cikin salama. 23 Lokacin da Yowab da dukkan sojojin da ke tare da shi suka iso, aka gaya wa Yowab, "Abna ɗan Nã ya zo gun sarki, kuma sarki ya sallame shi, Abna kuma ya tafi cikin salama." 24 Sai Yowab ya zo wurin Sarki ya ce, "Mene ne ke nan ka yi? Duba, Abna ya zo wurin ka! Me yasa ka sallame shi, kuma ga shi ya tafi? 25 Baka sani ba Abna ɗan Nã ya zo domin ya yaudare ka ya kuma san shirye-shiryenka ya gane duk abubuwan da kake yi?" 26 Da Yowab ya bar Dauda, sai ya aika manzanni su bi Abna, suka kuma dawo da shi daga rijiyar Sira, amma Dauda bai san wannan ba. 27 Da Abna ya dawo Hebron, Yowab ya kai shi gefe a tsakiyar ƙofa domin ya yi magana da shi a kaɗaice. Nan Yowab ya soke shi a ciki ya kashe shi. Da haka Yowab ya ɗau fansar jinin ɗan'uwansa. Asahel. 28 Da Dauda ya ji wannan ya ce, "Da ni da mulkina baratattu ne a gaban Yahweh har abada game da jinin Abna ɗan Nã. 29 Bari alhakin mutuwar Abna ya faɗi kan Yowab da kuma dukkan gidan mahaifinsa. Bari kada a taɓa rasa a cikin iyalin Yowab wani wanda ke ɗigar miƙi ko ciwon fata ko kuma wanda ya ke gurgu kuma dole ya yi tafiya tokare da sanda ko kuma wanda takobi ya kashe shi ko wanda ya ke da rashin abinci." 30 Haka Yowab da ɗan uwansa Abishai suka kashe Abna, domin ya kashe ɗan uwansu Asahel a Gibiyan cikin yaƙi. 31 Dauda ya cewa Yowab da dukkan mutanen da ke tare da shi, "Ku kekketa tufafinku, ku sa tsumoki, ku yi makoki a gaban gawar Abna." 32 Sarki Dauda ya bi bayan gawar cikin tawagar makokin. Suka binne Abna a Hebron. Sarki ya yi kuka da kururuwa mai ƙara a kabarin Abna, dukkan mutane kuma su ka yi kuka. 33 Sarki ya yi makoki domin Abna ya yi waƙa, "Ya ƙyautu Abna ya mutu kamar yadda wawa ke mutuwa? 34 Ba wai an ɗaure hannuwanka ba. ‌Ƙafafunka ba a ɗaure su da sarƙa ba. Kamar yadda mutum yakan faɗi a gaban 'ya'yan rashin gaskiya, haka ka faɗi." Sai kuma dukkan mutane suka ƙara kuka a bisansa. 35 Dukkan mutane suka zo su sa Dauda ya ci abinci tun da sauran rana. Amma Dauda ya rantse, "Bari Allah ya hukunta ni, ya kuma ƙara yi, idan na ci abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi." 36 Dukkan mutane suka lura da ɓacin ran Dauda, suka ji daɗi, duk abin da sarki ya yi suka ji daɗin sa. 37 Sai dukkan mutane da kuma dukkan Isra'ila suka gane a ranar nan ba niyyar sarki ba ce a kashe Abna ɗan Nã. 38 Sarki ya cewa barorinsa, "Ba ku sani basarake da kuma babban mutum ne ya faɗi yau a cikin Isra'ila ba? 39 Yanzu na rarrauna yau, koda shi ke ni sarki ne zaɓaɓɓe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi kowa mugunta a gare ni. Bari Yahweh ya sãka wa mugu da hukuncin da ya cancanci muguntarsa."

Sura 4

1 Lokacin da Ishboshet, ɗan Saul, ya ji Abna ya mutu a Hebron, sai hannuwasa suka yi rauni, dukkan Isra'ila suka tsorata.‌ 2 Ɗan Saul yana da mutane biyu waɗanda shugabanni ne na ƙungiyoyin sojoji. Sunan ɗayan Bãna ɗayan kuma Rekab, 'ya'yan Rimon Babirote na mutanen Benyamin (gama ana ɗaukar Birot a yankin Benyamin ta ke), 3 Birotiyawa sun gudu ne zuwa Gittam kuma har yau suna zama a can. 4 Yanzu dai, Yonatan ɗan Saul, yana da ɗa wanda gurgu ne a ƙafa. Yana da shekara biyar sa'ad da labari ya zo akan Saul da Yonatan daga Yeziril. Sai mai renonsa ta ɗauke shi don ta gudu da shi. Amma da ta ke gudu, sai ɗan Yonatan ya faɗi ya gurgunce. Sunansa Mafiboshet. 5 Sai 'ya'yan Rimon Babirote, Rekab da Ba'ana, suka yi tafiya cikin zafin rana zuwa gidan 6 Mafiboshet lokacin da ya ke hutawa da tsakar rana. Matar da ke tsaron ƙofar barci ya kwashe ta sa'ad da ta ke tankaɗen alkama, sai Rekab da Bãna suka yi sanɗo shuru suka wuce ta. 7 To bayan da suka shiga ɗakin, sai suka faɗa masa suka kashe shi sa'ad da ya ke ƙwance kan gadonsa. Suka yanke kansa suka tafi da shi, suka yi tafiya dukkan dare zuwa Araba. 8 Suka kawo kan Mafiboshet gun Dauda a Hebron, suka kuma ce da sarki, "Duba, wannan kan Mafiboshet ɗan Saul ne, maƙiyinka, wanda ya nemi ranka. Yau Yahweh ya sãka wa maigidanmu sarki gãba da Saul da zuriyarsa." 9 Dauda ya amsa wa Rekab da Bãna ɗan'uwansa, 'ya'yan Riman Babirote; ya ce masu, "Na rantse da ran Yahweh, wanda ya ceci raina daga kowacce wahala, 10 dã wani ya gaya mani; 'Duba, Saul ya mutu,' yana tsammanin ya kawo labari mai daɗi, sai na danƙe shi na kashe shi a Ziglag. Wannan shi ne ladan dana bashi don labarinsa mai daɗi. 11 To ba zan yi fiye da haka ba, sa'ad da mugayen mutane suka kashe mutum marar laifi a cikin gidansa a kan gadonsa, yanzu ba zan nemi jininsa daga hannunku in kuma tumbuƙe ku daga duniya ba?" 12 Sa'an nan Dauda ya umarci samari, suka kashe su suka yanke hannuwansu da ƙafafunsu kuma suka rataye su a gaɓar tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Mefiboshet suka binne shi a kabarin Abna a Hebron.

Sura 5

1 Sa'an nan dukkan kabilun Isra'ila suka zo gun Dauda a Hebron suka ce, "Duba mu jikinka ne da ƙashinka. 2 A kwanakin baya, da Saul ya ke mulki bisanmu, kai ne ka bi da rundunar yaƙi ta Isra'ila. Yahweh ya ce maka, "Za ka yi kiwon jama'ata Isra'ila, za ka kuma zama sarki bisa Isra'ila.'" 3 Sai dukkan dattawan Isra'ila suka zo wurin sarki a Hebron, Sarki Dauda ya yi alƙawari da su a gaban Yahweh. Suka naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila. 4 Dauda yana da shekaru talatin sa'ad da ya fara sarauta, ya kuma yi mulki shekara arba'in. 5 A Hebron ya yi mulkin bisa Yahuda shekaru bakwai da wata shida, kuma a Yerusalem ya yi mulki shekaru talatin da uku bisa dukkan Isra'ila da Yahuda. 6 Sarki da mutanensa suka zo Yerusalem gãba da Yebusiyawa, mazamnan ƙasar. Suka cewa Dauda, "Ba za ka iya zuwa nan sai dai idan makafi da guragu ne za su kore ka. Dauda ba zai iya zuwa nan ba." 7 Duk da haka Dauda ya ci kagarar Sihiyona, wadda yanzu shi ne birnin Dauda. 8 A lokacin nan Dauda ya ce, "Waɗanda suka hari Yebusiyawa dole su bi ta wuriyar ruwa domin su kai ga "guragu da makafi' waɗanda su ne maƙiyan Dauda." Shi yasa mutane ke cewa, "Da 'makafi da kuma guragu' ba za su shiga fãda ba." 9 Sai Dauda ya zauna cikin kagara ya kira shi birnin Dauda. Ya tsare shi da gine- gine kewaye da shi tun daga waje zuwa ciki. 10 Dauda ya ƙasaita domin Yahweh, Allah mai runduna, yana tare da shi. 11 Sa'an nan Hiram sarkin Taya ya aika da manzanni gun Dauda, da itacen sida, da masassaƙa da masu fãsa duwatsu. Suka gina wa Dauda gida. 12 Dauda ya sani Yahweh ya naɗa shi sarki bisa Isra'ila kuma ya ɗaukaka masarautarsa sabili da mutanensa Isar'ila. 13 Bayan da Dauda ya bar Hebron ya zo Yerusalem, ya ƙara ɗaukar ƙwaraƙwarai da mataye a Yerusalem, aka ƙara haifa masa 'ya'ya maza da 'ya'ya mata. 14 Waɗannan su ne sunayen yaran da aka haifa masa a Yerusalem: Shammuwa, Sobab, Natan, Suleman, 15 Ibha, Elisuwa, Nefeg, Yafiya, 16 Elishama, Eliyada, da Elifelet 17 Da dai Filistiyawa suka ji cewa an naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila, sai suka fita dukka suna nemansa. Amma Dauda ya ji abin, sai ya gangara zuwa mafaƙa. 18 Yanzu Filistiyawa sun rigaya sun fito sun bazu a Kwarin Refayim. 19 Sai Dauda ya roƙi taimako daga Yahweh. Ya ce, "Ko in hari Filistiyawa? Za ka bani nasara akan su?" Yahweh ya cewa Dauda, "Ka hare su, domin hakika zan ba ka nasara bisa Filistiyawa." 20 Sai Dauda ya kai hari a Ba'al Ferazim, a nan ya kayar da su. Ya ce haka, "Yahweh ya fantsamo cikin maƙiyana a gabana kamar fantsamowar ruwan ambaliya." Saboda haka sunan wurin ya zama Ba'al Ferazim. 21 Filistiyawa suka bar gumakunsu a nan, Dauda kuma da mutanensa suka ɗauke su suka tafi da su. 22 Sai Filistiyawa suka sake tasowa kuma suka ƙara bazuwa cikin Kwarin Refayim. 23 Sai Dauda ya sake roƙon taimako daga Yahweh. Yahweh kuma ya ce masa, "Kada ka kai hari ta gabansu, maimakon haka ka zagaya ta bayansu ku afka masu ta cikin itatuwan tsamiya. 24 Sa'ad da kuka ji ƙarar takawar yaƙi cikin iska da ke bugawa a ƙwanƙolin itatuwan tsamiya, sai ku kai hari da karfi. Kuyi wannan domin Yahweh ya rigaya ya sha gabanku ya hari rundunar Filistiyawa." 25 Sai Dauda ya yi yadda Yahweh ya umarce shi. Ya kashe Filistiyawa daga Geba har zuwa Geza.

Sura 6

1 Dauda ya sake tattaro dukkan zaɓabbun mutanen Isra'ila, dubu talatin. 2 Dauda ya tashi ya tafi da dukkan mutanensa da ke tare da shi daga Bãla cikin Yahuda domin a ɗauko akwatin Yahweh daga can wanda ake kira da sunan Yahweh mai runduna, wanda ya ke zaune a kursiyi bisa kerubim. 3 Suka ɗora akwatin Yahweh bisa sabuwar karusa. Suka fito da shi daga gidan Abinadab, da ke kan wani tudu. Uza, da Ahiyo, 'ya'yansa, suke bi da sabuwar karusar. 4 Suka fito da karusar daga gidan Abinadab daga kan tudu tare da akwatin Yahweh a bisan sa. Ahiyo na tafiya a gaban akwatin. 5 Sai Dauda da dukkan gidan Isra'ila suka fara wasa a gaban Yahweh, suna biki tare da sassaƙaƙƙun kayayyakin waƙa, molaye, garayu, kacau-kacau, da kuge. 6 Da suka iso masussukar Nakon, sai sãn ya yi tuntuɓe, sai Uza ya miƙa hannunsa ya tallafi akwatin Allah, ya kuma kama shi. 7 Sai fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan Uza. Allahj ya kai masa hari nan take sabili da zunubinsa. Uza ya mutu nan take da akwatin Allah. 8 Dauda ya yi fushi domin Yahweh ya kai wa Uza hari, ya kira sunan wurin nan Ferez Uza. Wurin nan har yau ana kiransa Ferez Uza. 9 Dauda ya ji tsoron Yahweh a ranan nan. Ya ce, "Ƙaƙa akwatin Yahweh zai zo gare ni." 10 Saboda haka Dauda bai so ya ɗauki akwatin Yahweh tare da shi zuwa cikin birnin Dauda ba. Maimakon haka, sai ya ajiye shi a gefe cikin gidan Obed Idom Bagitte. 11 Akwatin Yahweh ya kasance a gidan Obed Idom Bagitte wata uku. Sai Yahweh yasa masa albarka da dukkan gidansa. 12 Sai aka gaya wa sarki Dauda, "Yahweh ya albarkaci gidan Obed Idom da dukkan abubuwan da ke nasa saboda akwatin Yahweh" Sai Dauda ta tafi ya ɗauko akwatin Yahweh daga gida Obed Idom zuwa birnin Dauda da murna. 13 Lokacin da waɗanda suke ɗauke da akwatin Yahweh suka yi tafiya taki shida, sai ya yi hadayarsa da kiwataccen ɗan maraƙi. 14 Dauda ya yi rawa a gaban Yahweh da dukkan ƙarfinsa; yana sanye da ɗan feton lilin kaɗai. 15 Sai Dauda da dukka gidan Isra'ila suka ɗauko akwatin Yahweh tare da sowa da kuma ƙarar ƙahonni. 16 Sa'ad da akwatin Yahweh ya shigo birnin Dauda, Mikal, ɗiyar Saul, ta leƙa waje ta taga. Ta ga Sarki Dauda yana tsalle yana rawa a gaban Yahweh. Sai ta rena shi a zuciyarta. 17 Suka kawo akwatin Yahweh ciki suka ajeye shi a mazauninsa, a tsakiyar rumfar da Dauda ya shirya dominsa. Sai Dauda ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a gaban Yahweh. 18 Lokacin da Dauda ya gama miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ya albarkaci mutane a cikin sunan Yahweh mai runduna. 19 Sai ya rarraba wa dukkan mutane, dukkan cin-cirindon Isra'ila gaba ɗaya, maza da mata, dunƙulen gurasa, ɗan gutsuren nama, da wainar kauɗar inabi. Sa'annan dukkan mutane suka tafi, kowanne ɗayan su ya koma zuwa nasa gida. 20 Sai Dauda ya koma ya albarkaci iyalinsa. Mikal, ɗiyar Saul, ta fito ta taryi Dauda ta ce, "Ina misalin girmamawar da sarkin Isra'ila ya samu yau, wanda ya tsirance kansa yau a idanun bayi 'yan mata cikin barorinsa, kamar ɗaya daga cikin ashararrun mutane wanda ba ko kunya yana tsiraratar da kansa!" 21 Dauda ya amsa wa Mikal, "Na yi wannan a gaban Yahweh, wanda ya zaɓe ni fiye da mahaifinki fiye kuma da dukkan iyalin gidansa, wanda ya aza ni shugaba bisa mutanen Yahweh, bisa Isra'ila, A gaban Yahweh zan yi murna! 22 Zan zama ma da tawali'u fiye da haka, in kuma kunyata a idanuna ma. Amma game da 'yan mata bayi da kika ambata, za a girmamani." 23 Saboda haka Mikal ɗiyar Saul, ba ta da 'ya'ya har ranar mutuwarta.

Sura 7

1 Ya zamana sa'ad da sarki yana zaune cikin gidansa, kuma Yahweh ya bashi hutu daga dukkan maƙiyansa kewaye, 2 sarki ya cewa annabi Natan, "Duba, ina zaune cikin gidan sida, amma akwatin Yahweh yana zaune a cikin tsakiyar rumfa." 3 Sai Natan ya cewa sarki, "Je ka, ka yi abin da ke zuciyarka, gama Yahweh yana tare da kai." 4 Amma a daren nan maganar Yahweh ta zo gun Natan cewa, 5 "Ka tafi ka gaya wa bawana Dauda, "Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi: Zaka gina mani gida inda zan zauna a ciki? 6 Gama ban taɓa zama a cikin gida ba daga ranar da na fitar da mutanen Isra'ila daga Masar har zuwa rana ta yau; maimakon haka ina ta yawo a cikin rumfa, a rumfar sujada. 7 A dukkan wuraren dana yi yawo a cikin mutanen Isra'ila, na taɓa gaya wa wani ɗaya daga cikin shugabannin Isra'ila wanda na naɗa ya yi makiyayancin mutanena Isra'ila, cewa, "Donme ba ka gina mani gidan itatuwan sida ba?'"' 8 Yanzu dai, ka gaya wa bawana Dauda, "Wannan shi ne abin da Yahweh mai runduna ya ce: "Na ɗauko ka daga makiyaya, daga bin tumaki, domin ka zama mai mulki bisa mutanena Isra'ila. 9 Na kasance tare da kai duk inda ka tafi. Na datse dukkan maƙiyan ka daga gaban ka. Yanzu zan sa sunanka ya shahara kamar sunayen shahararrun nan na duniya. 10 Zan sanya wa mutanena Isra'ila wuri, zan kuma kafa su a can, domin su zauna a mazaunin kansu kuma ba za a ƙara wahalshe su ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zambatar su ba, kamar yadda suka yi a dã, 11 kamar yadda suke ta yi daga ranar dana umarci alƙalai su kasance bisa mutane na Isra'ila. Yanzu zan ba su hutawa daga dukkan magabtansu. Bugu da ƙari, "Ni, Yahweh, na furta maka cewa zan yi maka gida. 12 Sa'ad da kwanakinka suka cika kuma ka kwanta tare da ubanninka, zan tada wani daga zuriyar ka a bayan ka, wanda zai fito daga cikin jikinka, kuma zan kafa mulkinsa. 13 Shi zai gina gida domin sunana, kuma ni zan kafa kursiyin mulkinsa har abada. 14 Zan zama uba a gare shi, shi kuma zai zama ɗana. Idan ya yi zunubi, zan hore shi da sandar mutane da kuma bulalar 'ya'yan mutane. 15 Amma alƙawarin amincina ba zai barshi ba, kamar yadda da na ɗauke shi daga Saul, wanda na kawar daga gabana. 16 Gidanka da mulkinka za a tabbatar har abada a gabanka. Kursiyinka zai tabbata har abada.'" 17 Natan ya yi magana da Dauda ya kuma gaya masa dukkan maganganun nan, ya kuma gaya masa game da wahayin dukka. 18 Sai sarki Dauda ya shiga ciki ya zauna a gaban Yahweh ya ce, "Wane ne ni, Yahweh Allah, kuma mene ne iyalina har daka kawo ni ga haka? 19 Yanzu dai wannan ƙaramin abu ne a idonka, Ubangiji Yahweh. Har ma ka yi magana game da iyalin bawanka a kan lokatai masu zuwa, ka kuma nuna mani tsararraki masu zuwa, Ubangiji Yahweh! 20 Me kuma ni, Dauda, zan ce maka? Ka girmama bawanka, Ubangiji Yahweh. 21 Sabili da maganarka, domin kuma ka cika nufinka, ka yi wannan babban abu kuma ka bayyana shi ga bawanka. 22 Saboda haka kai mai girma ne, Ubangiji Yahweh, domin babu wani kamar ka, kuma babu wani Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu. 23 Wacce al'umma ce kamar mutanenka Isra'ila, al'umman nan guda ɗaya a duniya wadda, kai Allah, ka je ka fanshe mu domin kanka? Ka yi wannan domin su zama mutanenka, domin ka yiwa kanka suna, ka kuma yi manyan al'amura dana ban tsoro domin ƙasarka. Ka kori al'ummai da gumakunsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar da su daga Masar. 24 Ka kafa Isra'ila a matsayin mutanenka har abada, kuma kai, Yahweh, ka zama Allahnsu. 25 Saboda haka yanzu, Yahweh Allah, bari alƙawarin da ka yi game da bawanka da iyalinsa ya tabbata har abada. Ka yi yadda ka faɗa. 26 Bari sunanka ya zama da girma har abada, domin mutane su ce, Yahweh mai runduna shi ne Allah na Isra'ila,' sa'an nan gidana ni, Dauda, bawanka ya tabbata a gaban ka. 27 Domin kai, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ka bayyana wa bawanka cewa za ka gina masa gida. Shi yasa, ni, bawanka, na sami ƙarfin hali in yi addu'a gare ka. 28 Yanzu dai, Ubangiji Yahweh, kai ne Allah, maganganunka abin dogara ne a gare su, kuma ka yi wannan alƙawari mai ƙyau ga bawanka. 29 Yanzu dai, bari ya gamsheka ka albarkaci gidan bawanka, domin ya dawwama a gabanka har abada. Domin kai, Ubangiji Yahweh, ka faɗi waɗannan abubuwa, da kuma albarkarka gidan bawanka zai zama da albarka har abada."

Sura 8

1 Bayan wannan ya zamana Dauda ya hari Filistiyawa ya kuma ci su, Sai Dauda ya karɓe Gat da ƙauyukanta daga karkashin linzamin Filistiyawa. 2 Sa'an nan ya buga Mowabawa, ya gwada mutanensu da igiya ta wurin sasu su kwanta a ƙasa. Ya gwada layi biyu da zai kashe, layi ɗaya mai tsawo sosai da zai bari da rai. Haka Mowabawa suka zama bayi ga Dauda suka biya shi haraji. 3 Dauda ya buga Hadadeza ɗan Rehob, sarkin Zoba, sa'ad da Hadadeza ya ke tafiya garin ya mai da mulkinsa na dã wajen Kogin Efratis. 4 Dauda ya ƙwace karusai daga gunsa guda 1,700 da matafiya a ƙasa dubu ashirin. Dauda ya yanke jijiyar ƙafafun dawakai masu jan karusai, amma ya bar wasu domin karusai ɗari. 5 Lokacin da Armeniyawa na Damaskus suka zo su taimaki Hadadeza sarkin Zoba, Dauda ya kashe Armeniyawa mutum dubu ashirin da biyu. 6 Sai Dauda ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Aram ta Damaskus, kuma Armeniyawa suka zama bayinsa suna biyan haraji. Yahweh ya ba Dauda nasara duk inda ya tafi. 7 Dauda ya ɗauko garkuwoyin zinariya da suke kan bayin Hadadeza ya kawo su Yerusalem. 8 Daga Beta da Berotai, biranen Hadadeza, Sarki Dauda ya kwaso tagulla masu ɗumbun yawa. 9 Da Tou, sarkin Hamat, ya ji Dauda ya kayar da dukkan rundunar Hadadeza, 10 Tou ya aika Hadoram ɗansa gun Sarki Dauda ya gaishe shi ya kuma sa masa albarka, domin Dauda ya yi yaƙi gãba da Hadadeza ya kuma ci shi, domin kuma a dã Hadadeza ya yi yaƙi gãba da Tou. Hadoram kansa ya zo tare da kayayyakin azurfa, zinariya, da tagulla. 11 Sarki Dauda ya ƙeɓe waɗannan kayayyaki domin Yahweh, su azurfa da zinariya daga dukkan al'umman da ya ci da yaƙi - 12 Aram, Mowab, da mutanen Ammon, da Filistiyawa, da Amelik, tare kuma da dukkan kayayyakin ganima na Hadadeza ɗan Rehob sarkin Zoba. 13 Sunan Dauda ya shahara sa'ad da ya komo daga bugun Armeniyawa cikin Kwarin Gishiri, da su da mutanensu dubu goma sha takwas. 14 Ya ajiye ƙungiyoyin sojoji cikin dukkan yankin Idom, dukkan Idomiyawa suka zama bayi gare shi. Yahweh ya ba Dauda nasara duk inda ya tafi. 15 Dauda ya yi mulki bisa dukkan Isra'ila, ya kuma aikata adalci da gaskiya ga dukkan mutanensa. 16 Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban rundunar yaƙi, Yehoshafat ɗan Alihud kuwa shi ne magatakarda. 17 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Seraya ne marubuci. 18 Binaya ɗan Yehoyaida shi ne mai lura da Keretiyawa da Feletiyawa, 'ya'yan Dauda su ne manyan hakimai masu ba sarki shawara.

Sura 9

1 Dauda yace, "Akwai ko ɗaya wanda ya rage cikin iyalin Saul wanda zan nuna masa alheri sabili da Yonatan?" 2 Akwai wani bawa cikin iyalin Saul mai suna Ziba, aka kuma kira shi ga Dauda. Sarki ya ce masa, "Kai ne Ziba," Ya amsa, "I. Ni ne bawanka." 3 Sai sarki yace, "Babu ko ɗaya da ya rage daga iyalin Saul wanda zan nuna masa alherin Allah." Ziba ya amsa wa sarki, "Yonatan har yanzu yana da ɗa, wanda yana da gurguntaka." 4 Sarki ya ce masa, "Ina ya ke." Ziba ya amsa wa sarki ya ce, "Duba, yana cikin gidan Maki ɗan Ammiyel a Lo Deba." 5 Sa'an nan Sarki Dauda ya aika a ka fito da shi daga gidan Maki ɗan Ammiyel a Lo Deba. 6 Sai Mefiboshet ɗan Yonatan ɗan Saul, ya zo gun Dauda ya russuna fuskarsa ƙasa ya girmama Dauda. Dauda ya ce, '"Mefiboshet," Ya amsa, "Duba, ni baranka ne!" 7 Dauda ya ce masa, "Kada ka ji tsoro, gama hakika zan nuna maka alheri sabili da Yonatan mahaifinka, kuma zan mayar maka dukkan ƙasar kakanka, za ka kuma ci kullum a teburina." 8 Mefiboshet ya russuna ya ce, "Wane ne ni baranka, da za ka dube ni da tagomashi mataccen kare kamar ni?" 9 Sai sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, "Duk mallakar Saul da iyalinsa na ba jikan ubangidanka. 10 Da kai, da 'ya'yanka maza, da kuma barorinka dole ku noma masa gonakansa dole kuma ku yi masa girbi domin jikan ubangidanka ya sami abinci. Gama dole Mefiboshet, jikan ubangidanka, ya riƙa ci kullum a teburina." Ziba yana da 'ya'ya maza goma sha biyar da barori ashirin. 11 Sai Ziba ya cewa sarki, bawanka zaiyi dukkan abin da ubangijinsa sarki ya dokaci bawansa." Sarki ya ƙara da cewa, "Game da Mefiboshet zai riƙa ci a teburina, kamar ɗaya daga cikin 'ya'yan sarki." 12 Mefiboshet yana da wani ɗa ƙarami mai suna Mika, Duk waɗanda suke zauna a gidan Ziba barori ne na Mefiboshet. 13 Sai Mefiboshet ya zauna a Yerusalem, kullum kuwa ya na ci a teburin sarki, koda shi ke gurgu ne a dukkan ƙafafunsa biyu.

Sura 10

1 Ananan da jimawa sai sarkin mutanen Ammon ya mutu, kuma ɗansa Hanun ya zama sarki a madadinsa. 2 Dauda ya ce, "Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahas, kamar yadda mahaifinsa ya nuna mani alheri." Sai Dauda ya aiki barorinsa su kai ta'aziya ga Hanun domin mahaifinsa. Barorinsa suka shiga ƙasar mutanen Ammon. 3 Amma shugabannin mutanen Ammon suka cewa Hanun ubangijinsu, Kana tsammani da gaske Dauda ya ke girmama mahaifinka saboda ya aiko mutane su yi maka ta'aziya? Ba Dauda ya aiko barorinsa domin su dubi birnin ba, su san shi, domin su hallaka shi?" 4 Sai Hanun ya ɗauki barorin Dauda, ya aske rabin gemunsu, ya yanke rigunansu har zuwa ɗuwawunsu, a sa'annan ya sallame su suka tafi. 5 Da suka labarta wa Dauda wannan, ya aika domin ya sadu da su, domin mutanen sun kunyata ainun. Sarki ya ce, "Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya toho, sa'annan ku dawo. 6 Lokaci da mutanen Ammon suka ga sun zama abin ƙyama ga Dauda, sai suka aika manzanni suka kuma yi hayar Aremiyawan Bet Rehob da Zoba, da sojoji 'yan tafiya a ƙasa dubu ashirin, da sarkin Mãka mai dubun mutane, da mutanen Tob masu mutane dubu goma sha biyu. 7 Da Dauda ya ji haka, sai ya aiki Yowab da dukkan rundunar sojoji. 8 Ammonawa suka fito suka ja dagar yaƙi a mashigar ƙofar garinsu, Aremiyawan Zoba kuwa da na Rehob, da kuma mutanen Tob da Mãka, suka tsaya su kaɗai a filaye. 9 Da Yowab ya ga dagar yaƙi biyu sun fuskance shi gaba da baya, sai ya zaɓi ƙwararrun mayaƙa na Isra'ila ya jera su gãba da Aremiyawa. 10 Sauran rundunar kuwa, ya bashe su ƙarƙashin jagorancin Abishai ɗan'uwansa ya sa kuma suka ja dagar yaƙi gaba da rundunar Ammon. 11 Yowab ya ce, Idan Aremiyawa suka sha ƙarfi na, sai kai Abishai ka ƙwace ni, amma idan rundunar Ammon suka sha ƙarfinka zan zo in ƙwace ka. 12 Ku ƙarfafa, mu kuma nuna kanmu masu ƙarfi ne domin mutanenmu da kuma biranen Allahnmu, gama Yahweh zai yi abin da ke da kyau domin nufinsa. 13 Sai Yowab da sojojin rundunarsa suka tashi zuwa yaƙi gãba da Aremiyawa waɗanda dole suka gudu daga gaban rundunar Isra'ila. 14 Da rundunar Ammoniyawa suka ga Aremiyawa sun gudu, sai suma suka gudu daga Abishai suka koma cikin birni. Sai Yowab ya dawo daga fafarar mutanen Ammon ya koma Yerusalem. 15 Da Aremiyawa suka ga Isra'ila na cinsu, suka sake tattara kansu. 16 Sai Hadareza ya aika sojojin Aremiya su zo daga ƙasar ƙetaren Kogin Yuferetis. Suka zo Helam da Shobak, sarkin yaƙi na rundunar Hadareza ya shugabance su. 17 Da aka gaya wa Dauda wannan, sai ya tara dukkan Isra'ila gaba ɗaya, suka haye Yodan, suka iso Helam. Aremiyawa suka ja dagar yaƙi gãba da Dauda suka yaƙe shi. 18 Aremiyawa suka gudu a gaban Isra'ila. Dauda ya kashe mahayan karusai ɗari bakwai na Aremiyawa, da dubu arba'in na mahaya dawakai. Shobak sarkin yaƙin rundunarsu aka ji masa rauni, ya mutu a nan. 19 Sa'ad da dukkan sarakunan da ke barorin Hadareza suka ga Isr'ila ta ci su, sai suka biɗi sulhu da Isra'ila suka zama bayinsu. Sai Aremiyawa suka ji tsoron su ƙara taimakon mutanen Ammon.

Sura 11

1 Ya zamana da bazara, lokacin da sarakuna ke tafiya yaƙi, sai sarki Dauda ya aiki Yowab, da barorinsa, da dukkan rundunar Isra'ila. Suka ragargaza rundunar Ammon, suka kafa wa Rabba sansani. Amma Dauda ya zauna a Yerusalem. 2 A na nan wata rana da yammaci, Dauda ya tashi daga gadonsa yana tafiya a kan soron fadarsa, Daga nan ya hango wata mata wadda take wanka, matar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai abar sha'awa. 3 Sai Dauda ya aika ya kuma tambayi mutane waɗanda suka san wani abu game da matar. Sai wani ya ce, "Ashe wannan ba Batsheba ce ba, ɗiyar Eliyam, kuma ashe ba matar Yuriya ba ce Bahitte?" 4 Dauda ya aika manzanni, aka ɗaukota, ta shiga ciki wurinsa sai ya kwana da ita (gama ba ta daɗe da tsarkake kanta daga hailarta ba). Sa'an nan ta koma gidanta. 5 Matar ta yi ciki sai ta aika aka gaya wa Dauda; ta ce, "Ina da ciki." 6 Sai Dauda ya aika wurin Yowab, "Ka aiko mani Yuriya Bahitte. Sai Yowab ya aika wa Dauda Yuriya. 7 Da Yuriya ya iso, Dauda ya tambaye shi yadda Yowab ya ke, yadda rundunar take, da kuma yadda yaƙin ke tafiya. 8 Dauda ya cewa Yuriya, "Ka gangara zuwa gidanka, ka wanke ƙafafuwanka." Sai Yuriya ya bar fadar sarki, sai sarki ya aika wa Yuriya kyauta bayan tafiyarsa. 9 Amma Yuriya ya yi barci a ƙofar fadar sarki tare da dukkan barorin maigidansa, bai kuwa gangara zuwa gidansa ba. 10 Da aka gaya wa Dauda, "Yuriya bai gangara zuwa gidansa ba." Dauda ya cewa Yuriya, "Ashe ba yanzu ka dawo daga tafiya ba, me yasa ba ka tafi gida ba?" 11 Yuriya ya amsa wa Dauda, "Akwatin alƙawari, da Isra'ila da Yahuda suna zaune cikin rumfa, maigidana kuma Yowab da barorin maigidana sun kafa sansani a fili.‌ Ƙaƙa fa zan tafi cikin gidana in ci in sha in kuma kwana da mata ta? Na rantse da ranka, ba zan yi wannan abu ba." 12 Sai Dauda ya cewa Yuriya, "Ka zauna a nan gobe zan barka ka tafi." Sai Yuriya ya zauna a Yerusalem ranar nan da kashegari kuma. Lokacin da Dauda ya kira shi, ya ci ya sha a gabansa, 13 Dauda ya bugar da shi. Da yamma Yuriya ya fita ya je ya kwanta a gadonsa tare da barorin maigidansa bai gangara zuwa gidansa ba. 14 Saboda haka da safe Dauda ya rubuta wa Yowab takarda, ya ba da ita ta hannun Yuriya. 15 Dauda ya rubuta cikin wasiƙar cewa, "A sa Yuriya a gaba in da yaƙi yafi zafi sosai, sa'an nan ku janye daga gare shi, domin a buge shi ya mutu." 16 Sa'ad da Yowab ya kafa wa birnin daga, ya sa Yuriya a inda ya sani ƙarfafan sojojin abokan gaba za su yi yaƙi. 17 Da mutanen garin suka fito suka gwabza yaƙi da rundunar Yowab, waɗansu sojojin Dauda suka faɗi, kuma Yuriya Bahitte shi ma aka kashe shi a wurin. 18 Da Yowab ya aika saƙo ga Dauda yadda dukkan abu ya gudana a yaƙin, 19 ya umarci manzon cewa, '"Sa'ad da ka gama faɗin komai game da yaƙin ga sarki, 20 mai yiwuwa sarki ya husata, ya kuma ce maka, "Me ya sa kuka matsa kusa da birnin kuka yi yaƙi? Ba ku sani za su yiwo harbi daga garun ba? 21 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubeset? Ba wata mace ce ta jeho dutsen niƙa daga kan garu a kansa ba, sai ya zo ya mutu a Tebez? Me ya sa kuka matsa kurkusa da garun?' Sa'an nan dole za ka amsa, "Bawanka Yuriya Bahitte shi ma ya mutu.'" 22 Sai manzon ya tashi ya tafi wurin Dauda ya faɗa masa dukkan abin da Yowab ya aike shi ya faɗa. 23 Sai manzon ya cewa Dauda, "Abokan gãba suka fi mu ƙarfi da fari; suka fafaremu har zuwa jeji, amma muka kora su baya har zuwa ƙofar gari. 24 Sai maharbansu suka harbi sojojinka daga kan garu, aka kashe waɗansu barorin sarki, shi ma baranka Yuriya Bahitte an kashe shi." 25 Sai Dauda ya cewa manzon, "Ka faɗa wa Yowab wannan, 'Kada ka da mu, 'Kada ka bar wannan ya ɓata maka rai, gama takobi ya kan hallakar da wannan da kuma wancan. Ka matsa wa birnin lamba da yaƙi, ku kãda shi,' ka kuma ƙarfafa shi." 26 Sa'ad da matar Yuriya ta ji cewa Yuriya mijinta ya mutu, ta yi makoki sosai domin mijnta. 27 Sa'ad da makokinta ya wuce, Dauda ya aika aka ɗaukota aka kawota gida a fãdarsa, ta zama matarsa ta kuma haifa masa yaro. Amma abin da Dauda ya yi ya baƙanta wa Yahweh rai.

Sura 12

1 Sa'an nan Yahweh ya aiki Natan wurin Dauda. Ya tafi wurinsa ya ce, "A kwai waɗansu mutum biyu cikin wani birni.‌ Ɗaya mutumin mai arziƙi ne ɗayan kuwa matalauci. 2 Mai arziƙin na da tumaki masu tarin yawa a garkunansa, 3 amma talakan nan ba shi da komai sai dai wata 'yar ƙaramar tunkiya, wacce ya saya ya yi kiwonta. Ta yi girma tare da shi da kuma yaransa. Har ma 'yar tunkiyar takan ci tare da shi ta kuma sha daga moɗarsa, takan yi barci cikin hannuwansa har ma kamar ɗiya take a gunsa. ' 4 Wata rana wani baƙo ya zo gun mutumin nan mai arziƙi, amma mai arziƙin nan bai so ya ɗauki dabba daga cikin nasa garken domin ya ciyar da shi ba. Mai makon haka ya ɗauki 'yar tunkiyar matalaucin nan ya yi wa baƙon abinci da ita. 5 Dauda ya husata ƙwarai gãba da mutumin nan mai arziƙi, sai ya tasar wa Natan da ihu, 6 "Na rantse da ran Yahweh, mutumin da ya yi wannan ya cancanci mutuwa. Dole ya biya ninki huɗu tamanin 'yar tunkiyan nan domin ya yi wannan domin kuma bai ji tausayin matalaucin nan ba. 7 Sai Natan ya cewa Dauda, "Kai ne mutumin! Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ce, 'Na naɗa ka sarki bisa Isra'ila, na kuma kuɓutar da kai daga hannun Saul. 8 Na baka gidan ubangidanka, da matan ubangidanka a hannnuwanka. Na kuma ba ka gidan Isra'ila da Yahuda. Idan dã waɗannan sun yi ƙanƙanta dana ba ka waɗansu abubuwa ƙari bisansu. 9 To me yasa ka raina dokokin Yahweh, har ka aikata abin da ke na mugunta a idonsa? Ka kashe Yuriya Bahitte da takobi ka ɗauki matarsa ta zama matarka. Ka kashe shi da takobin rundunar Ammon. 10 Saboda haka yanzu takobi ba zata taɓa rabuwa da gidanka ba, domin ka rena ni ka ɗauki matar Yuriya Bahitte ta zama matarka.' 11 Yahweh ya ce, "Duba, zan tayar maka da masifa gãba da kai daga cikin gidanka. A idanunka, zan ɗauki matanka in ba da su ga maƙwabcinka, zai kwana da matanka rana katã. 12 Gama ka yi naka zunubin a asirce, amma ni zan yi wannan a gaban duk Isra'ila, rana katã.'" 13 Sai Dauda ya cewa Natan, "Na yiwa Yahweh zunubi." Natan ya amsa wa Dauda, "Yahweh ma ya shafe zunubinka. Ba za a kashe ka ba. 14 Duk da haka, domin ta wurin yin wannan ka rena Yahweh, yaron da za a haifa maka hakika zai mutu." 15 Sa'an nan Natan ya bar shi ya tafi gida. Yahweh ya kai wa yaron da matar Yuriya ta haifa Dauda hari, da matsanancin ciwo. 16 Dauda ya roƙi Yahweh domin yaron. Dauda ya yi azumi ya shiga cikin ɗaki ya kwanta a ƙasa dukkan dare. 17 Dattawan gidansa suka tashi suka tsaya a gefensa, domin su tashe shi daga ƙasa, amma yaƙi ya tashi kuma ya ƙi ya ci tare da su. 18 Sai ya zamana a rana ta bakwai yaron ya mutu. Barorin Dauda suka ji tsoron su gaya masa cewa yaron ya rasu, domin sun ce, "Duba, sa'ad da yaron ke raye mun yi masa magana bai saurari muryar mu ba. Me zai yiwa kansa idan muka ce masa yaron ya mutu?!" 19 Amma da Dauda ya ga barorinsa suna raɗa da junansu, Dauda ya gane yaron ya mutu. Ya cewa barorinsa, "Yaron ya mutu?" Suka amsa, "Ya mutu." 20 Sai Dauda ya tashi daga ƙasa ya wanke kansa, ya shafa mai, ya canza rigunansa. Ya tafi zuwa rumfar sujada ta Yahweh, ya yi sujada a can, sa'an nan ya dawo fadarsa. Da ya buƙata, sai suka sa abinci a gabansa, ya kuma ci. 21 Sai barorinsa suka ce masa, "Me yasa ka yi haka? Ka yi azumi da kuka saboda yaron, sa'ad da ya ke da rai, amma da yaron ya mutu, ka tashi ka ci abinci." 22 Dauda ya amsa, "Sa'ad da yaron ke da rai na yi azumi da kuka. Na ce, 'Wa ya sani watakila Yahweh zai yi mani alheri, ya bar yaron da rai?' 23 Amma yanzu ya mutu, to donme zan yi azumi? Zan iya komo da shi da rai ne? Ni zan je gunsa, amma shi ba zai komo wuri na ba." 24 Dauda ya ta'azantar da Batsheba matarsa, ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Daga baya ta haifi yaro, aka sa wa yaron suna Suleman. Yahweh ya ƙaunace shi 25 ya kuma aika da saƙo ta hannun annabi Natan cewa a sa masa suna Yedidiya, domin Yahweh ya ƙauna ce shi. 26 Yanzu dai Yowab ya yi yaƙi gãba da Rabba, birnin masarautar mutanen Ammon, ya kama kagararta. 27 Sai Yowab ya aiki manzanni ga Dauda ya ce, "Na yaƙi Rabba, na kuma kama mashigar ruwan birnin. 28 Yanzu fa ka tattaro sauran rudunar ka kafa wa birnin sansani ka ci shi, domin in na ci birnin, za a kira shi da sunana." 29 Sai Dauda ya tattaro dukkan rundunar ga baki ɗaya suka tafi Rabba; suka yaƙi birnin, suka ci shi. 30 Dauda ya cire kambin zinariya da ke kan sarkin - nauyinsa talanti guda ne na zinariya, akwai wani dutse mai daraja a cikinsa. Aka ɗora wannan kambi a kan Dauda. Sa'an nan ya fito da ganimar birnin masu ɗumbun yawa. 31 Ya fitar da mutanen da ke cikin birnin, ya tislasta masu su yi aiki da zartuna, faretani, da gatura; ya kuma sa su su yi aiki a maginar tubali. Dauda ya tilasta wa dukkan biranen mutanen Ammon su yi wannan aiki tuƙuru. Sai Dauda da dukkan rundunarsa suka koma Yerusalem.

Sura 13

1 Ya zama fa bayan wannan sai Amnon ɗan Dauda, ya yi sha'awar 'yar'uwarsa Tama kyakkyawa wanda ubansu ɗaya ne, amma 'yar'uwar Absalom ce uwa ɗaya uba ɗaya, shi ma ɗaya ne daga cikin 'ya'yan Dauda maza. 2 Amnon ya jarabtu har ya kama ciwo saboda 'yar 'uwarsa Tama. Ita kuwa budurwa ce, a ganin Amnon ba zai taɓa yiwuwa ya yi ma ta wani abu ba. 3 Amma Amnon ya na da wani aboki mai suna Yonadab ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda. Yehonadab wani mutum ne mai hila. 4 Yehonadab ya cewa Amnon, "Me yasa ga ka ɗan sarki, kake damuwa kowacce safiya? Ba za ka gaya mani ba?" Amnon ya amsa masa, "Ina ƙaunar Tamar, 'yar 'uwar ɗan'uwana Absalom." 5 Sai Yonadab ya ce masa, "Ka kwanta a gadonka ka yi kamar baka da lafiya. Sa'ad da mahaifinka zai zo ganin ka, ka tambaye shi, "Idan ka yarda ka aiko Tama 'yar'uwata ta ba ni wani abu in ci, bari ta girka shi a gaba na, domin in gan shi in kuma ci shi daga hannunta?'" 6 Sai Amnon ya kwanta kamar ba shi da lafiya. Da sarki ya zo domin ya dube shi, Amnon ya cewa sarki, "Idan ka yarda ka aiko 'yar'uwata Tama ta yi mani ɗan abinci saboda rashin lafiyata domin in ci daga hannunta.'" 7 Sai Dauda ya aika saƙo ga Tama a fãdarsa, cewa, "Ki tafi yanzu gidan ɗan'uwanki Amnon ki shirya masa abinci." 8 Sai Tama ta tafi gidan ɗan'uwanta Amnon in da ya ke kwance. Sai ta ɗauki ƙullu ta cuɗa ta yi waina a idonsa, sa'an nan ta toya. 9 Ta ɗauki kaskon kuma ta ba shi wainar, amma ya ƙi ci. Sa'an nan Amnon ya cewa waɗanda ke wurinsa, '"Kowa ya fita waje, ku ba ni wuri." Sai kowanne ɗayan su ya fita daga gare shi. 10 Sai Amnon ya cewa Tama, "Kawo abincin nan ɗakina domin in ci daga hannunki." Sai Tama ta ɗauki wainar da ta yi, ta kawo ta cikin ɗakin Amnon ɗan'uwanta. 11 Da ta kawo masa abincin, sai ya cafke hannunta ya ce mata, "Ki zo, ki kwana da ni, 'yar uwata." 12 Ta amsa masa, "A'a, ɗan'uwana, kada ka matsa mani, domin ba makamancin abu haka da ya kamata ya faru a Isra'ila. Kada ka yi wannan abin kunya! 13 ‌Ƙaƙa zan rabu da kunyata? Kai kuma fa? Za ka zama kamar ɗaya daga cikin sakarkaru na Isra'ila! Yanzu fa in ka yarda ka yiwa sarki magana, ba zai hana ka ni ba." 14 Duk da haka Amnon ya ƙi ya saurare ta. Tun da ya fi Tama ƙarfi, sai ya kama ta ya kwana da ita. 15 Sa'an nan Amnon ya ƙi Tama da mummunar ƙiyayya. Ya ƙi ta fiye da yadda dã ya yi sha'awarta. Amnon ya ce mata, 16 "Tashi ki tafi." Amma ta amsa masa, "A, a! Wannan babbar muguntar sallamata in tafi ta fi muni da abin da ka yi mani!" Amma Amnon bai saurare ta ba. 17 Maimakon haka, sai ya kira baransa ya ce, "Ka fitar da wannan mata daga gabana, ka kulle ƙofar a bayanta." 18 Sai baransa ya fitar da ita ya kulle ƙofar a bayanta. Tama ta na saye da wata taguwa mai ado sosai domin 'ya'yan sarki mata waɗanda budurwai ne suna yin shiga irin haka. 19 Tama ta baɗa toka a kanta ta keta taguwarta. Ta ɗibiya hannayenta a kanta ta tafi, tana rusa kuka sa'ad da take tafiya. 20 Absalom ɗan'uwanta ya ce mata, "Ko ɗan'uwanki Amnon ya sadu da ke ne? Amma yanzu ki yi shuru, 'yar uwata. Shi ɗan'uwanki ne. Ka da ki riƙe wannan a zuciya." Haka Tama ta zauna ita kaɗai a gidan wanta Absalom. 21 Sa'ad da Sarki Dauda ya ji dukkan waɗannan abubuwa, sai ya husata ƙwarai. 22 Absalom bai cewa Amnon komai ba, gama Absalom ya ƙi shi sabili da abin da ya yi mata da yadda ya kunyatar da 'yar'uwarsa Tama. 23 Ya zama fa bayan shekara biyu cur, Absalom na da masu sausayar tumaki da ke aiki a Bãl Hazor, wadda ke kusa da Ifraim, Absalom kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki maza su ziyarci wurin. 24 Absalom ya tafi wurin sarki ya ce, "Duba yanzu, bawanka yana da masu sausayar tumaki. Idan ka yarda bari sarki da barorinsa su zo tare da ni, bawanka." 25 Sarki ya amsa wa Absalom, "A'a, ɗana kada dukkanmu mu tafi domin za mu wahalshe ka." Absalom ya ƙarfafa sarki, amma bai yarda ya tafi ba, sai dai ya albarkaci Absalom. 26 Sai Absalom ya ce, "In ba haka ba, idan ka yarda bari ɗan'uwana Amnon ya je tare da mu." Sai sarki ya ce masa, "Donme Amnon zai je tare da ku?" 27 Absalom ya matsa wa Dauda, sai ya bari Amnon da dukkan 'ya'yan sarki maza su tafi tare da shi. 28 Absalom ya dokaci barorinsa cewa, "Ku saurara sosai. Sa'ad da Amnon ya soma buguwa sosai da ruwan inabi, kuma sa'ad da zan ce maku, 'Ku hari Amnon,' sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ba nine na dokace ku ba? Ku yi ƙarfin hali ku yi mazakutta." 29 Sai barorin Absalom suka yiwa Amnon yadda aka dokace su. Sai dukkan 'ya'yan sarki maza suka tashi, kowanne mutum ya haye bisa alfadarinsa ya tsere. 30 Ya zamana fa, lokacin da suke kan hanya, sai labari ya kai wurin Dauda cewa, "Absalom ya kashe dukkan 'ya'yan sarki maza kuma babu ko ɗaya da ya rage a cikinsu." 31 Sai sarki ya miƙe ya kekketa tufafinsa, ya kwanta a ƙasa; dukkan barorinsa suka tsaya nan da tufafinsu a yayyage. 32 Yehonadab ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda, ya amsa ya ce, "Kada ubangidana ya gaskata cewa sun kashe dukkan samari waɗanda 'ya'yan sarki maza ne, gama Amnon ka ɗai ya mutu. Absalom ya ƙudura wanna abu tun daga randa Amnon ya ɓata 'yar'uwarsa Tama. 33 Saboda haka fa, kada maigidana sarki ya riƙe wannan rahoto a zuciyarsa har da zai gaskata cewa dukkan 'ya'yan sarki maza suka mutu, gama Amnon ne kaɗai ya mutu." 34 Absalom ya gudu. Wani bawa da ke tsaro ya tada idanunsa ya ga mutane da yawa suna zuwa a kan hanya a gefen dutse yamma da shi. 35 Sai Yonadab ya cewa sarki, "Duba, 'ya'yan sarki maza suna zuwa. Ya yi dai-dai da yadda bawanka ya faɗa." 36 Ya zama fa sa'ad da ya gama magana sai 'ya'yan sarki maza suka iso suka tada muryoyinsu suka yi kuka. Sarki da dukkan barorinsa ma suka yi kuka mai zafi. 37 Amma Absalom ya gudu ya tafi gunTalmai ɗan Ammihud, sarkin Geshu. Dauda ya yi ta makokin ɗansa da daɗewa. 38 Sai Absalom ya gudu ya tafi Geshu, inda ya kasance har shekara uku. 39 Ran Sarki Dauda ya yi marmarin ya tafi ya ga Absalom, gama ya ta'azantu game da Amnon da mutuwarsa.

Sura 14

1 Yanzu fa Yowab ɗan Zeruya ya fahimci cewar ran sarki na marmarin ganin Absalom. 2 Yowab ya aika da kalmar saƙo a Tekowa yasa a kawo masa mace mai hikima. Ya ce mata, "Ina roƙonki kiyi kamar kina makoki kisa tufafin makoki. Ina roƙon ki kada ki shafa mai a jikinki, amma kiyi kamar mace wadda ta daɗe tana makoki domin matacce. 3 Daga nan sai ki je wurin sarki kiyi magana da shi game da abin da zan kwatanta." Sai Yowab ya faɗa mata maganganun da za ta faɗi a wurin sarki. 4 Sa'ad da matar nan daga Tekowa ta yi magana da sarki, sai ta kwanta da fuskarta a ƙasa ta ce, "Ka taimake ni, ya sarki." 5 Sarki ya ce mata, "Me ya faru?" Sai ta amsa, "Gaskiyar ita ce ni gwauruwa ce, maigidana kuma ya mutu. 6 Ni baiwarka, ina da 'ya'ya biyu, sun yi faɗa tare a cikin saura, ba kuwa wani wanda zai raba su. ‌Ɗ‌aya ya bugi ‌ɗ‌ayan har ya kashe shi. 7 Yanzu duk zuriyar sun tashi gãba da baiwarka, su ka ce, 'Ki ba mu mutumin da ya kashe ɗan'uwansa cikin hannunmu, domin mu kashe shi, domin biyan ran ɗan'uwansa wanda ya kashe.' Da haka kuma za su hallaka magajin. Ta yin haka za su ɓice wutata da ta rage, kuma ba za su bar wa maigidana suna ko zuriya a doron ƙasa ba." 8 Sai sarki ya cewa matar, "Ki tafi gidanki, kuma zan umarta ayi wani abu domin ki." 9 Sai matar nan ta Tekowa ta amsa wa sarki, "Ya shugabana, sarki, bari alhakin laifin ya komo kaina da gidan iyalin mahaifina. Sarki da kursiyinsa basu da laifi." 10 Sai sarki ya amsa, duk wanda ya ce maki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara taɓa ki ba." 11 Daga nan sai ta ce, "Ina roƙon ka, bari sarki ya tuna da Yahweh Allahnka, domin kada mai ɗaukar fansar jini ya ƙara hallakar da wani, domin kada su hallaka ɗana." Sai sarki ya amsa, "Bisa ran Yahweh, babu gashin ɗanki ko ɗaya da zai faɗi ƙasa." 12 Daganan sai matar ta ce, "In ka yarda bari baiwarka ta sake yin magana ga shugabana sarki." Ya ce, "Ci gaba da magana" 13 Sai matar ta ce, "Donme ka kutta wannan maƙida gãba da mutanen Allah? Gama ta wurin faɗin wannan, sarki ya zama kamar wani mai laifi, saboda sarki bai sake dawo da korarren ɗansa gida ba. 14 Gama dukkan mu dole mu mutu, kuma muna kama da ruwan da aka zubar a ƙasa, wanda ba za a sake tattara shi ba. Amma Allah ba zai ɗauki rai ba; maimakon haka, ya kan nemi hanya domin waɗanda aka kora su dawo. 15 Yanzu fa, ganin yadda na zo in faɗi wannan abu ga shugabana sarki, saboda mutane sun sa na ji tsoro. Sai baiwarka ta ce a ranta, 'yanzu zan yi magana da sarki. Maiyiwuwa ne sarki ya aikata bisa ga roƙon baiwarsa. 16 Watakila sarki zai saurare ni kuma ya ceci baiwarsa daga hannun mutumin da zai hallaka ni da ɗana tare, daga cikin gãdon da Allah ya ba mu.' 17 Daga nan baiwarka ta yi addua, ta ce, Yahweh, in ka yarda bari maganar shugabana sarki ta ba ni sauƙi, gama kamar yadda mala'ikan Allah ya ke, haka shugabana sarki ya ke wajen faɗin abu mai kyau daga mugunta.' Bari Yahweh Allahnka ya kasance tare da kai." 18 Daga nan sarki ya amsa wa matar ya ce, 'Ina roƙon ki kada ki ɓoye mani komai da zan tambaye ki." Sai matar ta amsa ta ce, 'Yanzu bari shugabana sarki ya yi magana." 19 Sai sarki ya ce "Ko hannun Yowab bai tare da ke cikin dukkan al'amarin nan?" Sai matar ta amsa ta ce, "Bisa ga ranka, ya shugaba sarki, ba wani ko ɗaya da zai kuɓuta daga hannun dama ko hagu daga duk wani abin da shugabana sarki ya faɗi. Gama bawanka Yowab ne ya umarce ni ya kuma gaya mani dukkan abubuwan da baiwarka ta faɗi. 20 Bawanka Yowab ya yi wannan domin ya canza yanayin abin da ya ke faruwa. Shugabana kuma yana da hikima, hikima irinta mala'ikan Allah, kuma ya san dukkan abin da ya ke faruwa a cikin ƙasa." 21 Sai sarki ya cewa Yowab, Yanzu fa ka duba, zan yi wannan, jeka fa, ka komo da saurayin nan Absalom." 22 Sai Yowab ya kwanta da fuskarsa ƙasa cikin darajantawa da godiya ga sarki. Yowab ya ce, "Yau bawanka ya sani cewa Na sami tagomashi a idonka, ya shugabana, sarki, da shi ke sarki ya aikata bisa ga roƙon bawansa." 23 Sai Yowab ya ta shi, ya tafi Geshu, kuma ya zo da AbsalomYerusalem. 24 Sarki ya ce, "Zai iya komawa gidansa, amma ba lallai ya ga fuskata ba." Absalom ya dawo gidansa, amma bai ga fuskar sarki ba. 25 Yanzu kuwa a cikin dukkan Isra'ila babu wanda ake yabo domin kyansa fiye da Absalom. Daga tafin sawunsa zuwa bisa kansa babu wani aibi a cikinsa. 26 Sa'ad da ya aske gashin kansa a ƙarshen kowacce shekara, saboda ya kan yi masa nauyi, yakan auna gashin kansa, ya kan kai kimanin awo ɗari biyu, bisa ga mizanin ma'aunin sarki. 27 An haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace ɗaya, sunanta Tama. Ita kyakkyawar mace ce. 28 Absalom ya zauna cikakkun shekaru biyu a Yerusalem, ba tare da ganin fuskar sarki ba. 29 Daga nan Absalom ya aika a kira Yowab domin ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa wurinsa. Har yanzu Absalom ya sake aikawa karo na biyu, duk da haka Yowab ya ƙi zuwa. 30 Domin wannan Absalom ya ce da barorinsa, "Duba, gonar Yowab tana kusa da tawa, ga shi yana da bali a wurin. Ku je ku sa mata wuta." 31 Sai barorin Absalom suka sawa gonar wuta. Daga nan sai Yowab ya tashi ya zo wurin Absalom a gidansa, ya ce masa, "Donme barorinka suka sawa gonata wuta?" 32 Absalom ya amsa wa Yowab, "Duba na aika maka cewa, ka zo nan domin in aike ka wurin sarki ka ce, "Donme na dawo daga Geshu? ya fi mani sauƙi a ce har yanzu ina can. Yanzu bari in ga fuskar sarki, idan bani da gaskiya, bari ya kashe ni.'"' 33 Sai Yowab ya je wurin sarki ya faɗa masa. Sa'ad da sarki ya kira Absalom, sai ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki, sarki kuwa ya sumbaci Absalom.

Sura 15

1 Ana nan bayan wannan kuma Absalom ya shirya karusa da dawakai domin kansa, tare da mutane hamsin masu gudu a gabansa. 2 Absalom zai tashi da wuri ya tsaya a bakin hanya mai zuwa ƙofar birni, sa'ad da kowanne mutum ya ke da matsalar da za a kawo wa sarki domin shari'a, daga nan sai Absalom ya kira shi ya ce, "Daga wanne birni ka zo?" sai mutumin ya amsa, "Bawanka daga ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila ya ke." 3 Sai Absalom ya ce masa, Duba, maganarka tana da kyau da kuma gaskiya, amma sarki bai sanya kowa da zai ji maganarka ba." 4 Absalom ya ƙara da cewa, "Ina ma da ni aka sanya in zama alƙali cikin ƙasar, domin kowanne mutum da ke da kowacce irin matsala ko dalili ya zo wurina, kuma zan yi masa adalci!" 5 Ya zama kuwa idan kowanne mutum ya zo wurin Absalom domin ya girmama shi, Absalom ya kan miƙa hannunsa ya kama shi ya yi masa sumba. 6 Absalom ya aikata wannan ga dukkan Isra'ila musamman wanda ya zo wurin sarki domin shari'a. Da haka Absalom ya sace zukatan mutanen Isra'ila. 7 Ana nan bayan shekaru huɗu sai Absalom ya cewa sarki, "Ina roƙonka ka yardar mani in tafi in cika wa'adin da na yiwa Yahweh cikin Hebron. 8 Gama bawanka ya yi wa'adi lokacin da nake zama a Geshu cikin Aram, cewa, 'Idan ya tabbata Yahweh ya sake dawo da ni Yerusalem, daga nan zan yi wa Yahweh sujada.'" 9 Sai sarki ya ce masa, "Tafi lafiya" Sai Absalom ya tashi ya tafi Hebron. 10 Amma Absalom ya aika da masu leƙen asirin ƙasa cikin dukkan kabilun Isra'ila, ya na cewa, da zarar kun ji busar ƙaho, daga nan dole ku ce, 'Absalom ne sarki cikin Hebron.'" 11 Mazaje ɗari biyu suka ta fi tare da Absalom daga Yerusalem, waɗanda aka gayyata. Sun tafi cikin rashin sanin su, ba su da masaniyar abin da Absalom ya rigaya ya shirya. 12 Lokacin da Absalom ke cikin miƙa hadayu, ya aika a kirawo Ahitofel daga garinsa a Gilo. Shi ne mai ba Dauda shawara. Makircin Absalom kuwa ya yi ƙarfi, gama mutanen da ke bin Absalom kullum sai ƙaruwa suke yi. 13 Wani ɗan saƙo ya zo wurin Dauda ya ce, "Zukatan mutanen Isra'ila sun koma wajen Absalom." 14 Sai Dauda ya cewa dukkan bayinsa da e tare da shi a Yerusalem, "Tashi bari mu gudu, in ba haka ba a cikinmu babu wanda zai kuɓuta daga hannun Absalom. Mu hanzarta tashi, kada ya same mu da sauri, kuma ya kawo bala'i a kanmu ya bugi birnin da kaifin takobi. 15 Bayin sarki suka cewa sarki, "Duba, bayin sarki a shirye suke su yi duk iyakar abin da shugabanmu sarki ya ayyana." 16 Sarki ya fita dukkan iyalinsa kuma suka bi shi, amma sarki ya bar mata goma, waɗanda ƙwaraƙwarai ne domin su kula da fãda. 17 Bayan da sarki ya fita tare da dukkan mutanen da ke bayansa, suka tsaya a gida na ƙarshe. 18 Dukkan rundunarsa suka tafi tare da shi, a gaban sa kuma dukkan Keretawa, da dukkan Feletawa, da dukkan Gittiyawa - mutum ɗari shida waɗanda suka bi shi tun daga Gat. 19 Sa'an nan sarki ya cewa Ittai Bagitti, "Donme za ka zo, tare da mu? Ka koma ka zauna tare da sarki Absalom, gama kai baƙo ne ɗan bauta kuma, ka koma wurinka. 20 Da ya ke jiya kaɗai ka tafi, donme zan sa ka kai da komowa tare da mu? Gashi kuwa ban ma san inda zan tafi ba. Don haka sai ka juya ka koma ka ɗauki 'yan ƙasarka. Bari bangirmanka da aminci su tafi tare da kai." 21 Amma Ittai ya amsa wa sarki ya ce, "Na rantse da ran Yahweh, da ran shugabana sarki kuma, hakika duk wurinda shugabana sarki ya tafi, can ne kuma bawanka za shi, ko ya kai ga rayuwa ko ga mutuwa." 22 Sai Dauda ya cewa Ittai, "Jeka ka ci gaba tare da mu" Sai Ittai Bagitti ya haye tare da sarki, da dukkan mutane da dukkan iyalin da ke tare da shi. 23 Dukkan ƙasar kuwa ta yi kuka da babbar murya yayin da dukkan mutane suka ratsa ta hayin kwarin Kidron, sarki ma da kansa ya haye. Dukkan mutane suka yi tafiya a ƙasa zuwa wajen hanyar jeji. 24 Har su Zadok da dukkan Lebiyawa, masu ɗauke da akwatin alƙawarin Allah, suna wurin. Suka ajiye akwatin Allah a ƙasa, Abiyata ya bi su. Suka jira har saida dukkan mutane suka gama fitowa daga cikin birni. 25 Sai sarki ya cewa Zadok, "Ka ɗauki akwatin Allah ka mai da shi cikin birni. Idan na sami tagomashi a idon Yahweh, zai komo da ni nan, ya kuma sake nuna mani akwatin da wurin zamansa. 26 Amma idan ya ce, "Ba na jin daɗinka,' Duba Ina nan, bari ya yi mani abin da ya ga ya yi masa kyau." 27 Sai sarki ya cewa Zadok firist, kai ba mai gani ba ne? Ka koma cikin birni lafiya, da 'ya'yanka biyu tare da kai, Ahimãz ɗanka, da Yonatan ɗan Abiyata. 28 Duba, a wurin mashigai na jeji zan jira har sai magana ta zo daga gare ku ka sanar da ni." 29 Sai Zadok da Abiyata suka ɗauki akwatin alƙawari na Allah suka mai da shi cikin Yerusalem, suka kuma zauna can. 30 Amma Dauda ya haura ba takalmi yana kuka har zuwa Dutsen Zaituna, kuma ya rufe kansa. Kowanne mutum cikin mutanen da ke tare da shi ya rufe kansa, suka hau suna kuka yayin da suke tafiya. 31 Sai wani ya faɗawa Dauda ya ce, Ahitofel na cikin masu maƙida da Absalom." Dauda ya yi addu'a ya ce, "Ya Yahweh, ina roƙonka ka juyar da shawarar Ahitofel ta zama wawanci." 32 Ana nan sa'ad da Dauda ya kai kan hanya, inda a ke yiwa Allah sujada, Hushai Ba'arkite ya zo ya sadu da shi da yagaggar tufa da ƙura a kansa. 33 Dauda ya ce masa, "I dan za ka yi tafiya tare da ni, za ka zama nawaya a gare ni. 34 Amma idan ka juya cikin birni ka ce da Absalom, 'Zan zama bawanka, ya sarki, kamar yadda na zama bawan mahaifinka a kwanakin baya, haka kuma yanzu zan zama bawanka,' ta haka za ka ruɗar da shawarar Ahitofel domina. 35 Ba za ka tafi tare da Zadok da Abiyata firist tare da kai ba? Zai zama kuwa duk abin da ka ji a fadar sarki, dole ka faɗawa Zadok da Abiyata firist. 36 Duba can suna tare da 'yayansu biyu, Ahimãz ɗan Zadok da Yonatan ɗan Abiyata. Dole ta hannunsu za ku aiko mani da dukkan abin da kuka ji." 37 Sai Hushai, abokin Dauda, ya zo cikin birni yayin da Absalom ya kai kuma ya shiga cikin Yerusalem.

Sura 16

1 Sa'ad da Dauda ya hau har ya wuce kan tudu kaɗan, Ziba bawan Mefiboshet ya gamu da shi da jãkai guda biyu labtattu; a kansu kuwa dunƙulen gurasa guda ɗari biyu na curin kauɗar inabi ɗari, da curin 'ya'yan itacen ɓaure ɗari, da salkar ruwan inabi. 2 Sarki ya cewa Ziba, "Donme ka kawo waɗannan abubuwa?" Ziba ya amsa ya ce, "Jakai domin iyalin sarki ne su hau, gurasa da wainar itacen ɓaure domin mutanenka su ci, ruwan inabi kuma domin duk wanda ya sũma a cikin jeji ya sha." 3 Sarki ya ce, Ina jikan shugabanka?" Ziba ya amsa wa sarki ya ce, "Duba, ya tsaya baya cikin Yerusalem, gama ya ce, 'Yau gidan Isra'ila za su mayar mani da sarautar mahaifina.'" 4 Daga nan sai sarki ya cewa Ziba, "Duba, dukkan abin da ke mallakar Mefiboshet yanzu naka ne,'" Sai Ziba ya amsa, na sunkuya cikin bangirma gare ka, ya shugabana, sarki. Bari in sami tagomashi a idanunka." 5 Sa'ad da sarki Dauda ya gabato Bahurim, wani mutum daga gidan iyalin Saul ya zo, sunansa Shimei ɗan Gera. Ya fito yana tafiya yana la'antarwa. 6 Ya jefi Dauda da duwatsu har da shugabannin sarki, duk da sojoji da masu tsaro da ke hannun damansa da hannun hagu. 7 Shimei ya yi kira cikin la'antarwa, "Tafi daga nan, mutumin banza, mutumin jini! 8 Yahweh ya sãka wa dukkanku domin jinin iyalin gidan Saul, wanda kake mulki a matsayinsa. Yahweh ya bada mulkin a cikin hannun Absalom ɗanka. Gashi yanzu kuma ka hallaka saboda ka zama mutum mai zubda jini." 9 Daga nan sai Abishai ɗan Zeruya ya cewa sarki, "Donme wannan mataccen karen zai la'anta shugabana sarki? Ina roƙonka ka yardar mani in haye in fille masa kai." 10 Amma sarki ya ce, "Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Mai yiwuwa yana la'antani saboda Yahweh ne ya ce masa, "La'anta Dauda.' Wane ne zai ce masa, 'Donme kake la'antar sarki?'" 11 Sai Dauda ya cewa Abishai da dukkan bayinsa, "Duba, ɗana, wanda aka haifa daga cikin jikina, yana so ya ɗauki raina. Balle wannan mutumin Benyamin da ke marmarin ganin hallaka ta, Ku ƙyale shi kawai ku bar shi ya yi ta la'antarwa, gama Yahweh ne ya umarce shi. 12 Maiyiwuwa Yahweh ya duba irin gagarumin baƙincikin da ke kaina, ya sãka mani da alheri saboda la'antarwar da ya yi mani yau." 13 Hakanan Dauda da mazajensa suka yi tafiya kan hanya, Shimei kuma ya zaga gefen gangaren tudu, yana tafiya yana la'antarwa yana jifansa da duwatsu yana zuba masa turɓaya yayin da ya ke tafiya, 14 Daga nan sarki da dukkan mutanen da ke tare da shi suka zo da gajiya, can ya huta lokacin da suka tsaya da dare. 15 Absalom kuwa da dukkan matanen Isra'ila waɗanda ke tare da shi, suka zo Yerusalem, Ahitofel kuma na tare da shi. 16 Ya zama kuwa sa'ad da Hushai - Ba'arkite, abokin Dauda, ya zo wurin Absalom Hushai ya cewa Absalom, "Ran sarki ya daɗe! Ran sarki ya daɗe!" 17 Absalom ya cewa Hushai, "Wannan ita ce biyayyarka ga abokinka? Donme ba ka tafi tare da shi ba?" 18 Hushai ya cewa Absalom, "A'a! maimakon haka, shi wanda Yahweh da wannan jama'a da dukkan mutanen Isra'ila suka zaɓa, shi ne mutumin da ni zan zama nasa, kuma zan zauna tare da shi. 19 Kuma, wanne mutum zan bautawa? Ba gaban ɗansa ya kamata in yi bautar ba? kamar yadda na yi bautar gaban mahaifinka, hakanan zan yi bautar a gabanka." 20 Sa'an nan Absalom ya cewa Ahitofel sai ka ba mu shawara game da abin da za mu yi." 21 Ahitofel ya amsa wa Absalom, "Ka je ka kwana da bayin matan mahaifinka waɗanda ya bari domin su kula da fãda, daga nan dukkan Isra'ila za su ji ka zama abin ƙyama ga mahaifinka. Daga nan hannuwan dukkan waɗanda ke tare da kai za su yi ƙarfi." 22 Sai suka baza wa Absalom rumfa a bisa fãda, Absalom kuwa ya kwana da mata bayin mahaifinsa a idanun dukkan Isra'ila. 23 Ya zama kuwa shawarar da Ahitofel ya bayar a waɗannan kwanaki ta zama kamar wadda mutum ya ji daga bakin Allah da kansa. Haka dukkan shawarar Ahitofel ta zama a wurin Dauda da Absalom.

Sura 17

1 Daga nan sai Ahitofel ya cewa Absalom, "Yanzu bari in zaɓi maza dubu goma sha biyu, kuma zan tashi in fafari Dauda yau a daren nan. 2 Zan auka masa lokacin da ya yi raụni ya gaji in kuma ba shi mamaki da tsoro. Mutanen da ke tare da shi za su gudu, sarki kaɗai zan buge. 3 Zan dawo da dukkan mutane a gare ka. kamar amaryar da ke zuwa wurin mijinta, daga nan dukkan mutane za su zauna lafiya ƙarƙashinka." 4 Abin da Ahitofel ya faɗi ya faranta wa Absalom rai da dukkan dattawan Isra'ila. 5 Daga nan sai Absalom ya ce, yanzu ku kira Hushai Ba'akite shima, bari mu ji abin da ya ce." 6 Sa'ad da Hushai ya zo wurin Absalom, Absalom ya bayyana masa abin da Ahitofel ya faɗi sai ya tambayi Hushai, "Ko za mu iya yin abin da Ahitofel ya ce? In ba haka ba sai ka faɗi shawararka." 7 Sai Hushai ya cewa Absalom, "Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokacin ba ta da kyau." 8 Hushai ya ƙara da cewa, "Ka san mahaifinka da mazajensa jarumawa ne masu ƙarfi, kuma suna da zafin rai, kamar damisar da a ka ƙwace wa 'ya'yanta a cikin saura. Mahaifinka mayaƙine, ba zai kwana tare da mutane a daren nan ba. 9 Duba, yanzu haka mai yiwuwa yana wurin ɓuya cikin wasu ramummuka ko a wani wuri. Za ya zama kuwa idan aka kashe waɗansu mutanenka a farkon harin, iyakar wanda yaji zai ce, 'An yi yanka tsakanin sojojin da ke bin Absalom.' 10 Daga nan har su sojoji masu ƙarfin zuciya, waɗanda zukatansu suna kama da zuciyar zaki, za su ji tsoro domin dukkan Isra'ila sun sani cewa mahaifinka jarumi ne, kuma mutanen da ke tare da shi suna da ƙarfi ƙwarai. 11 Shawarata a gare ka ita ce a tattara dukkan Isra'ila a gare ka, daga Dan zuwa Biyasheba, kamar yashin da ke bakin teku yawa, kai kuwa da kanka ka tafi yaƙi. 12 Daga nan zamu abka masa a wurin da za a same shi, za mu rufe shi kamar yadda raɓa take faɗowa ƙasa. Ba za mu bar ko ɗaya daga cikin mazajensa, ko shi kansa, da rai ba. 13 Idan ya toge cikin birni, daga nan dukkan Isra'ila za su kawo igiyoyi zuwa ga birnin nan kuma za mu jãshi zuwa cikin rafi, har da ba za a tarar da ko ƙanƙanen dutse ɗaya a wurin ba." 14 Daga nan sai Absalom da dukkan mazajen Isra'ila suka ce, shawarar Hushai Ba-arkite tafi shawarar Ahitofel." Yahweh ya wajabta ƙin amincewa da shawara mai kyau ta Ahitofel domin a kawo hallakarwa a kan Absalom. 15 Daga nan sai Hushai ya cewa Zadok da Abiyata firistoci, "Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Israi'ila irin wannan shawarar, amma ni na bada wata shawarar dabam. 16 Yanzu kuwa, sai ku tafi da sauri ku sanar da Dauda; ku ce masa, 'Kada ku yi sansani a daren yau a mashigan Araba, amma ta ko ƙaƙa ka haye, in ba haka ba za a haɗiye sarki da dukkan mutanen da ke tare da shi." 17 Yanzu Yonatan da Ahimãz suna zama a maɓuɓɓugar En-Rogel. Wata mace baiwa takan je ta sanar da su abin da ya kamata su sani, domin bashi yiwuwa su ɗauki kasadar a yi ta ganinsu suna tafiya cikin birni. Idan saƙo ya zo sukan je su faɗa wa sarki Dauda. 18 Amma wani saurayi ya gan su a wannan lokacin sai ya faɗa wa Absalom. Sai Yonatan da Ahimãz suka fita a gaggauce suka zo gidan wani mutum a cikin Bahurim, wanda ya ke da rijiya a harabar gidansa, inda suka sauka ciki. 19 Matar mutumin kuma ta ɗauki murfin rijiyar ta rufe bakin rijiyar da shi, ta zuba hatsi a kai, ba wanda ya san cewa Yonatan da Ahimãz suna cikin rijiyar. 20 Mutanen Absalom suka zo wurin matar gidan suka ce, "Ina Ahimãz da Yonatan?" Sai matar tace masu, "Sun haye rafi." Bayan da suka dudduba ko'ina ba su same su ba, sai suka koma Yerusalem. 21 Ya zama kuwa bayan da suka tafi sai Yonatan da Ahimãz suka fito daga cikin rijiyar. Suka tafi su kai wa sarki Dauda rahoto; suka ce masa, "Ku tashi ku haye ruwa da sauri saboda Ahitofel ya bada irin wannan shawarar game da ku." 22 Daga nan sai Dauda ya tashi da dukkan mutanen da ke tare da shi, suka haye Yodan. Kafin wayewar hasken safiya babu ko ɗaya daga cikin su da ya kasa hayewa Yodan. 23 Sa'ad da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yiwa jãkinsa sirdi ya tafi. Ya koma gida cikin nasa birni, ya kimtsa al'amuransa, kuma ya rataye kansa. Ta haka ya mutu aka kuma bizne shi cikin kabarin mahaifinsa. 24 Daga nan sai Dauda ya zo Mahanayim. Absalom kuma, ya hayeYodan, shi da dukkan mazajen Isra'ila tare da shi. 25 Absalom kuma yasa Amasa shugaban rundunar yaƙi maimakon Yowab. Amasa ɗan Yeta Isma'ile, wanda ya kwana da Abigel wadda take ɗiyar Nahash 'yar'uwar Zeruya uwar Yowab. 26 Daga nan Isra'ila da Absalom suka kafa sansani cikin ƙasar Giliyad. 27 Ya zama kuwa sa'ad da Dauda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabbah na Ammonawa, da Maki ɗan Amiyel daga Lo Deba, da Barzillai Bagiliye daga Rogelim, 28 suka kawo tabarmin kwanciya da barguna, da masakai da tukwane, da alkama, garin bali, gasasshen hatsi, wake, da ganye, 29 zuma, da mai, tumaki da manshanu, domin Dauda da mutanen da ke tare da shi su ci. Mutanen nan suka ce, "Mutanen nan suna jin yunwa, da gajiya, da ƙishi a cikin jeji."

Sura 18

1 Dauda ya ƙidaya sojojin da ke tare da shi ya naɗa shugabanni na dubbai da na ɗarurruka a bisansu. 2 Daga nan Dauda ya aika da rundunar soja, ɗaya bisa uku ƙarƙashin, umarnin Yowab, waɗansu kashi uku kuma ƙarƙashin umarnin Abishai ɗan Zeruya, ɗan uwan Yowab, har yanzu wani kashi na uku kuma ƙarƙashin umarnin Ittai Ba-gitte. Sarki kuma ya cewa rundunar yaƙi, "Lallai zan fita tare daku da kaina, nima." 3 Amma mazajen suka ce, "Ba dole sai ka je yaƙi ba, gama idan mun gudu ba za su kula da mu ba, ko idan rabin mu sun mutu ba za su kula ba. Amma darajarka a bakin zambar goma tamu ce! Domin wannan ya fi kyau kai ka kasance da shirin yi mana taimako daga cikin birni." 4 Sai sarki ya amsa masu, "Zan yi duk abin da ku ka ga yafi maku kyau." Sarki ya tsaya a bakin ƙofar birni yayin da dukkan rundunar yaƙi suka fita ɗari-ɗari da dubu-dubu. 5 Sai sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai cewa, "kuyi a hankali da saurayin nan, da Absalom, sabili da ni." Dukkan mutane sun ji cewa sarki ya ba shugabanni wannan umarni game da Absalom. 6 Rundunar yaƙi suka fita zuwa cikin filin karkara garin suyi yaƙi da Isra'ila; yaƙin ya bazu zuwa cikin kurmin Ifraim. 7 Rundunar yaƙin Isra'ila sun sha kãshi a wurin a hannun sojojin Dauda; a rannar kuwa aka yi kisa mai yawa a wurin an kashe mazaje dubu ashirin. 8 Faɗan ya bazu ko'ina cikin ɓangaren ƙasar, mazajen da kurmi ya cinye suka fi waɗanda suka mutu ta kaifin takobi. 9 Ya kasance kuwa Absalom ya gamu da waɗansu sojojin Dauda. Absalom yana tafiya kan alfadarinsa, alfadarin kuwa ya shiga ƙarƙashin cikin rassa masu kauri na itacen rimi, itacen kuwa ya kama kansa cikin rassan. Yana reto tsakanin sama da ƙasa alfadarin da ya ke haye akai kuwa ya ci gaba da tafiya. 10 Wani mutum daya gani sai ya fada wa Yowab, "Duba, na ga Absalom rataye a itacen rimi!" 11 Yowab ya ce da mutumin daya faɗa masa game da Absalom, "Duba! ka ganshi! donme ba ka buge shi a ƙasa ba? Ai da na baka azurfa goma da ɗammara." 12 Sai mutumin ya amsa wa Yowab, "Koda na karɓi shekel ɗin azurfa dubu, duk da haka bazan miƙa hannuna gãba da ɗan sarki ba, domin mun ji umarnin da sarki ya ba ku, Abishai da Ittai cewa, 'kada kowa ya taɓa saurayin nan Abasalom.' 13 Da na yi kasada da raina ta wurin ƙarya (kuma babu abin da ke ɓoye a wurin sarki), da ka yashe ni," 14 Daga nan sai Yowab ya ce, "Ba zan jira ka ba." Sai Yowab ya ɗauki mãshi uku cikin hannunsa ya caka su cikin zuciyar Absalom, yayin da ya ke da rai ya ke kuma rataye a itacen rimi. 15 Daga nan majiya ƙarfi guda goma masu ɗauke da sulken Yowab suka kewaye Absalom, suka buge shi, suka kashe shi. 16 Yowab ya busa ƙaho, rundunar yaƙi suka dawo daga runtumar Isra'ilawa, gama Yowab ya rinjayi mutane. 17 Suka ɗauki Absalom suka jefa shi cikin babban rami a cikin kurmin; suka bizne jikinsa cikin ƙarƙashin babban tarin duwatsu, sa'an nan dukkan Isra'ila suka gudu, kowanne mutum zuwa nasa gida. 18 Yanzu kuwa, lokacin da Absalom ya ke da rai, ya gina wa kansa babban ginshiƙin dutse cikin kwarin sarki, gama ya ce, "Bani da ɗan da zai ɗauki suna na wanda za a tuna da ni." Ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kiran sunansa Surar Absalom har wa yau. 19 Sa'an nan Ahimãz, ɗan Zadok ya ce, "Bari in gudu yanzu in kai wa sarki labari mai daɗi, yadda Yahweh ya kuɓutar da shi daga hannun abokan gabarsa." 20 Yowab ya amsa masa, "Ba kai ne za ka zama mai ɗaukar labari yau ba; amma wata rana za ka kai. Yau ba za ka kai kowanne labari ba gama ɗan sarki ya mutu." 21 Sai Yowab ya cewa Ba-kushi, "Jeka ka faɗa wa sarki abin da ka gani. Sai Ba-kushi ya sunkuyar da kansa gaban Yowab, sai ya ruga. 22 Daga nan sai Ahimãz ɗan Zadok ya sake cewa Yowab, ba tare da la'akari da komai zai faru ba, ina roƙon ka ka bar ni in ruga in bi Ba-kushen."Yowab ya amsa, donme kake so ka ruga, ɗana? Ganin ba za ka sami wa ta ladar kai labarin ba?" 23 Kome ya faru, in ji Ahimãz, "Zan ruga" Yowab ya amsa ya ce masa, "Ruga." Sa'an nan Ahimãz ya ruga ta hanyar fili, ya tsere wa Ba-kushen. 24 Dauda kuwa yana zaune tsakanin ƙofofi biyu na ciki da na waje. Mai tsaro kuma ya hau benen ƙofa har zuwa cikin rufin garu ya tãda idanunsa. Da ya duba, sai ga wani ya sheƙo a guje shi kaɗai. 25 Sai mai tsaron ya tada murya ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, "Idan shi kaɗai ne, akwai labari a bakinsa." Mai gudun ya zo kurkusa kuma dab da birnin. 26 Sai mai tsaron ya lura da wani mutum kuma yana gudu, sai mai tsaron ya kira mai kula da ƙofa; ya ce, "Duba, ga wani mutum kuma yana gudu shi kaɗai," Sai sarki ya ce, "Shi ma yana kawo labari." 27 Sai mai tsaron ya ce, "A ganina irin gudun na gaban nan ya yi kama da gudun Ahimãz ɗan Zadok." Sarki ya ce, "Shi nagarin mutum ne, yana zuwa da labari mai daɗi." 28 Daga nan sai Ahimãz ya yi kira ya cewa sarki, "Komai lafiya lau ne" kuma ya sunkuyar da kansa da fuskarsa gaban sarki har ƙasa ya ce, "Mai albarka ne Yahweh Allahnka! Ya ba da mutanen da su miƙar da hannayensu gãba da shugabana sarki." 29 Sai Sarki ya amsa, "Ko saurayin nan Absalom yana lafiya?" Ahimãz ya amsa ya ce, lokacin da Yowab ya aike ni, bawan sarki, wurinka, ya sarki, na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba." 30 Sai sarki ya ce, "Juya gefe ka tsaya nan." Sai Ahimãz ya juya ya tsaya cik. 31 Nan da nan Ba-kushen ya zo ya ce, "Akwai albishir mai daɗi domin shugabana sarki, gama Yahweh ya ɗaukar maka fansa yau daga dukkan waɗanda suka tayar maka." 32 Daga nan sai sarki ya cewa Ba-kushen, ko lafiya dai da saurayin nan Absalom?" Ba-kushen ya amsa, maƙiyan shugabana sarki, da dukkan waɗanda suka tayar maka domin su cutar da kai, "Su zama kamar yadda saurayin nan ya ke." 33 Daga nan sarki ya yi juyayi mai zurfi, ya tafi ya hau kan ƙofar bene ya yi kuka. Yayin da ya ke baƙinciki yana tafe yana cewa "ɗana Absalom, ya ɗana, Absalom! Da ma ni ne na mutu a madadinka, Absalom, ɗana, ɗana!"

Sura 19

1 Aka faɗa wa Yowab cewa, "Duba, sarki yana kuka yana makoki domin Absalom." 2 Wato nasara ta ranar nan ta koma makoki ga dukkan jama'a, gama jama'a sun ji cewa a ran nan sarki yana makoki saboda ɗansa." 3 Ya zama lallai ga sojoji su saɗaɗa shiru cikin birni a wannan ranar, kamar mutane masu jin kunya su kan sace jiki sa'ad da suka gudu daga yaƙi. 4 Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da babbar murya, "Ya ɗana Absalom, Absalom, ya ɗana, ya ɗana!" 5 Yowab ya shigo cikin gida wurin sarki ya ce masa, "Yau ka kunyatar da fuskokin dukkan sojoji, waɗanda suka ceci ranka yau, da rayukan 'ya'yanka maza da mata, da rayukan matanka, da rayukan matanka bayi, 6 saboda kafi ƙaunar waɗanda suke ƙinka, kuma kana ƙin masoyanka. Gama yau ka nuna cewa Hafsoshi da sojoji ba komai bane a gare ka. Yau na gaskanta da Absalom ya rayu, dukkan mu kuma da mun mutu, wannan da ya faranta maka rai. 7 Yanzu fa sai ka tashi ka fita kayi magana mai daɗi ga sojojinka, gama na rantse da Yahweh, idan baka tafi ba, babu wanda zai zauna tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni cikin dukkan bala'o'in da suka faru da kai daga ƙuruciyarka zuwa yau." 8 Sa'an nan sarki ya tashi ya zauna a ƙofar birni, aka faɗa wa dukkan jama'a, cewa, "Duba fa, ga sarki can yana zaune a cikin ƙofa." Daga nan sai dukkan mutane suka zo gaban sarki. Isra'ila kuma suka gudu, kowanne mutum ya tafi gidansa. 9 Dukkan mutane kuma suna ta muhawara da juna cikin dukkan kabilun Isra'ila suna cewa, "Sarki ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya kuma cece mu daga hannun Filistiyawa yanzu kuma ya gudu daga ƙasar saboda Absalom. 10 Absalom kuma wanda muka sarautar da shi bisa kanmu, ya mutu cikin yaƙi, Yanzu fa donme bama cewa komai game da dawo da sarki?" 11 Sarki Dauda ya aika wurin Zadok da Abiyata firist cewa, 'Kuyi magana da dattawan Yahuda cewa, donme kune na ƙarshe wajen dawo da sarki fãdarsa, da shi ke sarki ya sami tagomashi daga dukkan Isra'ila, a dawo dashi fãdarsa? 12 Ku 'yan'uwana ne, ƙashina ne da namana. Donme ku ne na ƙarshen dawo da sarki?' 13 Ku cewa Amasa, 'Kai ba ƙashina bane da kuma namana? Allah ya yi mani haka, ya kuma ƙara mani, idan ba ka zama shugaban runduna ta ba daga yanzu zuwa nan gaba a madadin Yowab.'" 14 Kuma ya rinjayo da zukatan dukkan mutanen Yahuda kamar zuciyar mutum guda, sai suka aika wa sarki cewa, "Ka dawo, kai da dukkan mutanenka." 15 Sai sarki ya dawo, ya zo Yodan. Mutanen Yahuda kuma suka zo Gilgal don su tarbi sarki, daga nan suka kawo sarki ƙetaren Yodan. 16 Shimei ɗan Gera, Benyamine, wanda ya zo daga Bahurim, ya hanzarta ya sauko tare da mutanen Yahuda domin taryar sarki Dauda. 17 Akwai mutanen Benyamin dubu goma tare da shi, da Ziba bawan Saul, da kuma 'ya'yansa goma sha biyar da barorinsa ashirin tare da shi. 18 Suka haye taYodan a gaban sarki. Suka haye domin su kawo iyalin sarki domin ya yi abin da ya yi masa kyau. Shimei kuma ɗan Gera ya sunkuya a gaban sarki tun kafin ya fara haye Yodan. 19 Sai Shimei ya cewa sarki, "Kada, shugabana, ya same ni da laifi ko ya tuna da taurin kan da bawanka ya yi a ranar da shugabana sarki ya bar Yerusalem. In ka yarda, kada sarki ya ajiye wannan a zuciyarsa. 20 Gama bawanka ya sani na yi zunubi. Duba, shi yasa na zo yau a matsayin na fari daga cikin dukkan iyalin Yosef na zo domin in taryi shugabana sarki." 21 Amma Abishai ɗan Zeruya ya amsa ya ce, "Ba za a kashe Shimei ba saboda wannan, saboda ya la'anta shafaffe na Yahweh?" 22 Daga nan sai Dauda ya ce, "Me zanyi da ku, ku 'ya'yan Zeruya, da yau za ku zama maƙiyana? Za a kashe wani mutum yau a cikin Isra'ila? Gama bana sani cewa yau ni ne sarki bisa Isra'ila ba?" 23 Sarki kuwa ya cewa Shimei, "Ba za ka mutu ba" Sai sarki ya yi masa alƙawari tare da rantsuwa. 24 Daga nan sai Mefiboshet ɗan Saul ya zo domin ya tarbi sarki. Bai kuwa gyara ƙafafunsa ba, ko ya aske gemunsa, ko ya wanke tufafinsa tun daga lokacin da sarki ya tashi har ranar daya dawo cikin salama. 25 Ya zama kuwa sa'ad da ya zoYerusalem domin ya tarbi sarki, sarki ya ce masa, "Donme ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet? 26 Sai ya amsa, "Ya shugabana sarki, bawana ya ruɗe ni, gama Na ce, bari in yi ma jakina sirdi, domin in hau in tafi tare da sarki, gama bawanka gurgu ne.' 27 Bawana Ziba yaci zarafina, bawanka, a wurin shugabana sarki. Amma shugabana sarki kamar mala'ikan Allah ya ke. Don haka, sai ka yi duk abin da kaga ya gamshe ka. 28 Gama duk iyalin gidan mahaifina sun zama matattun mutane gaban shugabana sarki, amma ka sanya bawanka a cikin masu ci a teburinka. Wanne 'yanci nake dashi kuma da zan ƙara yiwa sarki kuka?" 29 Daga nan sarki ya ce masa, "Donme ka ƙara wani abu kuma? Na yanke shawarar cewa kai da Ziba za ku raba gonakin." 30 Sai Mefiboshet ya amsa wa sarki, "I, bari ya ɗauka duka, da shi ke shugabana sarki ya dawo gidansa lafiya." 31 Daga nan sai Barzillai Bagiliye ya zo daga Rogelim ya haye Yodan tare da sarki, domin ya raka shi hayin Yodan. 32 Yanzu dai Barzillai ya tsufa ƙwarai, shekarunsa tamanin. Ya tanadarwa sarki abin zaman gari lokacin da ya ke zaune a Mahanayim, gama shi mai arzaki ne. 33 Sarki ya ce da Barzillai, "Sai ka haye tare da ni, ni kuwa zan tanada maka ka zauna tare da ni a Yerusalem." 34 Barzillai ya amsa wa sarki, "Sauran kwanaki nawa suka rage cikin shekarun rayuwata, da zan haura tare da sarki zuwa Yerusalem? 35 Shekaruna tamanin. Zan iya banbance tsakanin abu mai kyau da mugu? Ko bawanka zai iya ɗanɗana abin da nake ci ko abin da nake sha? Yanzu zan iya jin kowacce muryar mawaƙa maza da waƙar mata? Donme bawanka za ya zama nawaya ga shugabana sarki? 36 Bawanka yana so ya haye Yodan kaɗai tare da sarki. Donme sarki zai saka mani da irin wannan ladar? 37 Ina roƙonka ka bar bawanka ya koma gida, domin in mutu cikin birnina a kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ka duba, ga bawanka Kimham. Bari ya haye tare da shugabana sarki, kayi masa abin da ya yi maka kyau." 38 Sarki ya amsa ya ce, "Kimham zai haye tare da ni, kuma zan yi masa abin da kake so, iyakar abin da kake nema kuma a gare ni, zan yi maka." 39 Daga nan sai dukkan mutane suka haye Yodan, sarki ma ya haye, sai sarki ya sumbaci Barzillai ya kuma albarkace shi. Daga nan sai Barzillai ya koma gidansa. 40 Sai sarki ya haye zuwa Gilgal, Kimham kuma ya haye tare da shi. Dukkan jama'ar Yahuda kuma suka ƙetarar da sarki, da rabin jama'ar Isra'ila kuma. 41 Nan da nan sai dukkan mutanen Isra'ila suka fara zuwa wurin sarki suka ce da sarki, "Donme 'yan'uwanmu, mutanen Yahuda, suka sace ka suka kawo sarki da iyalinsa hayin Yodan, da dukkan mazajen Dauda tare da shi?" 42 Sai mutanen Yahuda suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, domin sarki danginmu ne na kusa. donme kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abin da ya zama lallai sarki dole ya biya? Ko ya ba mu wasu kyaututtuka?" 43 Sai mutanen Isra'ila suka amsa wa mutanen Yahuda, "Mu na da kabilai goma da suke dangantaka da sarki, 'yancin da muke dashi wurin Dauda yafi naku. Donme ku ka rena mu? Ba shawarar mu aka fara ji ba ta dawo da sarkinmu?" Amma kalmomin mutanen Yahuda sun fi kalmomin mutanen Isra'ila zafi.

Sura 20

1 Ya kasance kuma a wannan wurin akwai wani mai tada hankali sunansa Sheba ɗan Bikri, Benyamine. Sai ya busa ƙaho ya ce, "Ba mu da rabo cikin Dauda ba mu kuwa da gãdo cikin ɗan Yesse, bari kowanne mutum ya koma gidansa, Isra'ila," 2 Sai dukkan mutanen Isra'ila suka yashe da Dauda suka bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka bi sarkinsu kurkusa, daga Yodan har zuwa Yerusalem. 3 Lokacin da Dauda yazo fãdarsa a Yerusalem, sai ya ɗauki matan nan goma bayi waɗanda ya bari su kula da fãda, ya sa su cikin gida yasa a kula da su, ya biya buƙatunsu, amma bai ƙara kwana da su ba. An kulle su har ranar mutuwarsu, suna zama kamar gwamraye. 4 Daga nan sai sarki ya ce da Amasa, ka kira mazajen Yahuda tare cikin kwana uku; dole kai ma ka kasance, a nan, 5 Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuda tare, amma ya jinkirta ya wuce lokacin da sarki ya sanya dominsa. 6 Sai Dauda ya ce da Abishai, "Yanzu Sheba ɗan Bikri za ya yi mana ɓarnar da ta fi wadda Absalom ya yi. Ka ɗauki bayin shugabanka, sojojina, ka bi bayansu, in ba haka ba zai iya samun birane masu ganuwa ya ɓace mana da gani." 7 Sai mutanen Yowab suka bi bayansa, da su da Keretawa da su da Feletawa, da dukkan jarumawa. Suka fita Yerusalem suka bi Sheba ɗan Bikri. 8 Yayin da suke a babban dutsen da ke a Gibeyon, Amasa ya zo ya tarbe su, Yowab kuwa yana saye da tufafinsa na yaƙi, wanda ya haɗa da ɗammara kewaye da ƙugunsa da takobin yaƙi ɗaure da shi. Ya yin da ya ci gaba da tafiya sai takobin ya faɗi. 9 Sai Yowab ya ce da Amasa, "Lafiya kake, ɗan'uwana?" Yowab ya kama Amasa wajen gemunsa da hannunsa na dama don ya yi masa sumba. 10 Amasa bai kula da takobin da ke cikin hannun Yowab na hagu ba. Yowab ya daɓa wa Amasa a ciki 'yan hanjinsa suka faɗi a ƙasa. Yowab bai sake bugunsa ba, Amasa kuwa ya mutu. Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi Sheba ɗan Bikri. 11 Sai ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya wajen Amasa, mutumin ya ce, "Wanda ya ke wajen Yowab da wanda ke wajen Dauda, bari ya bi Yowab." 12 Amasa ya kwanta yana ta birgima cikin jini a cikin tsakiyar hanya. Yayin da mutumin yaga dukkan jama'a sun tsaya cik, sai ya ɗauki Amasa ya kawar dashi daga kan hanya zuwa cikin saura. Ya jefa mayafi a kansa saboda ya ga duk wanda ya zo sai ya tsaya a kansa. 13 Bayan da aka kawar da Amasa a kan hanya, dukkan mutane suka bi bayan Yowab, wajen bin Sheba ɗan Bikri. 14 Sheba ya ratsa dukkan kabilun Isra'ila zuwa Abel ta Bet Maka, da zuwa dukkan kasar Beriyawa, waɗanda suka tattaru domin bin Sheba. 15 Suka kama shi suka kafa masa sansani cikin Abel ta Bet Maka. Suka tãra tulin tudun ƙasa gãba da birnin da ganuwar. Dukkan jama'ar da ke tare da Yowab suka bubbuge ganuwar suka rushe ta. 16 Sa'an nan wata mace mai hikima tayi kuka daga cikin birni ta ce, "Ku ji, ina roƙon ku kuji, Yowab, ka matso kusa da ni domin in yi magana da kai." 17 Sai Yowab ya je kusa da ita, sai matar ta ce, kai ne Yowab?" Sai ya amsa ya ce, "Ni ne," Sa'an nan ta ce masa, ka saurari kalmomin baiwarka," Ya amsa ya ce, Ina ji." 18 Sai ta ce, kwanakin dã an saba cewa, 'Lallai sai ka nemi shawara a Abel.' Wannan shawarar kuwa takan kawo ƙarshen al'amarin. 19 Mu ne ɗaya daga cikin birni da ke da salama da aminci a cikin Isra'ila. Ka na ƙoƙarin ka hallaka birni wanda ya ke uwa a cikin Isra'ila. Donme za ka haɗiye gãdon Yahweh?" 20 Sai Yowab ya amsa ya ce, "Hakika ba zai faru ba, bari ya zama nesa daga gare ni, da zan haɗiye ko in hallakar. 21 Wannan ba gaskiya ba ne. Amma wani mutum daga duwatsun ƙasar Ifraim sunan sa Sheba ɗan Bikri, ya ɗaga hannunsa sama gãba da sarki, gãba da Dauda. Shi kaɗai za a bayar ni kuwa zan janye daga birnin." Sai matar ta cewa Yowab, "Za a jefa maka kansa ta bisa ganuwa." 22 Daga nan sai matar taje wurin dukkan jama'a cikin hikimarta. Suka yanke kan Sheba ɗan Bikri, suka jefa shi waje wurin Yowab. Daga nan sai ya busa ƙaho mutanen Yowab suka bar birnin, kowa ya koma gidansa. Sai Yowab ya komaYerusalem wurin sarki. 23 Yanzu fa Yowab yana kan rundunar yaƙi ta Isra'ila, Benaiya kuma ɗan Yehoyida yana bisa kan Keretawa da Feletawa. 24 Adoram yana bisa mutane masu yin aikin dole, Yehoshafat kuma ɗan Ahilud shi ne magatakarda. 25 Sheba kuma marubuci da Zadok da Abiyata su ne Firistoci. 26 Ira Bajairi kuma babban mai yin hidima ga Dauda

Sura 21

1 A cikin zamanin Dauda aka yi yunwa shekara uku akai akai, Dauda kuwa ya nemi fuskar Yahweh. Sai Yahweh ya ce, "Wannan yunwar tana kan ka ne saboda Saul da iyalinsa masu kisa, saboda ya kashe Gibiyonawa." 2 Yanzu fa Gibiyonawa ba daga jama'ar Isra'ila bane, amma daga wajen sauran Amoriyawa ne. Mutanen Isra'ila sun rantse masu ba za su kashe su ba, amma saul ya yi ƙoƙari ya kashe su dukka a cikin himmarsa domin mutanen Isra'ila da Yahuda. 3 Sai Dauda ya kira mutanen Gibiyonawa ya ce masu, "Me zan yi domin ku? Ta yaya zan yi kaffara, domin ku albarkaci mutanen Yahweh, waɗanda suka gãji alherinsa da alƙawarai?" 4 Gibiyonawa suka ce masa, ba zancen azurfa ko zinariya tsakanin mu da Saul ko iyalinsa. Kuma ba domin mu za a kashe kowanne mutum a cikin Isra'ila ba." Dauda ya amsa, "Duk abin da za ku roƙa, shi ne abin da zan yi maku." 5 Sai suka amsa wa sarki suka ce, mutumin da ya yi ƙoƙarin ya kashe mu dukka, wanda ya ƙulla mana makirci, wanda da yanzu an hallaka mu, mu rasa wuri a tsakanin iyakar Isra'ila. 6 Bari a bamu mutum bakwai daga cikin zuriyarsa, mu kuwa za mu rataye su ga Yahweh cikin Gibiya ta Saul, zaɓaɓɓe na Yahweh." Sai sarki ya ce, "Zan ba ku su." 7 Amma sarki ya keɓe Mefiboshet ɗan Yonatan ɗan Saul, saboda rantsuwar Yahweh da ke tsakanin su, tsakanin Dauda da Yonatan ɗan Saul. 8 Amma sarki ya ɗauki 'ya'ya biyu na Rizfa ɗiyar Ayiya, 'ya'yan da ta haifawa Saul, sunayen 'ya'ya biyun data haifa su ne, Armoni da Mefiboshet; Dauda kuma ya ɗauki 'ya'ya biyar na Mirab ɗiyar Saul, waɗanda ta haifawa Adriyel ɗan Barzillai Meholatiye. 9 Ya miƙa su cikin hannun Gibiyonawa. Suka rataye su a kan dutse, gaban Yahweh. Dukkan su bakwai ɗin suka mutu tare. Sun mutu a lokacin girbi, kwanakin farko ne a farkon kakar bali. 10 Daga nan sai Rizfa ɗiyar Ayiya ta ɗauki tsummoki ta shimfiɗa wa kanta su a bisa dutsen, gefen gawarwakin, daga farkon kãka har lokacin da ruwan sama ya sauko a kansu. Bata bari tsuntsayen sararin sama su dame su da rana ba, ko namomin jeji da dare. 11 Aka faɗa wa Dauda abin da Rizfa ɗiyar Ayiya, baiwar matar Saul, ta yi. 12 Sai Dauda ya tafi ya ɗauki ƙasusuwan Saul da ƙasusuwan Yonatan ɗansa daga hannun mutanen Yabesh Giliyad, waɗanda suka sace a wurin filin Bet - Shan, inda Filistiyawa suka rataye su, bayan da Filistiyawa suka kashe Saul a Gilbowa. 13 Dauda ya kawar da ƙasusuwan Saul da ƙasusuwan Yonatan ɗansa, suka kuma tattara ƙasusuwan mutane bakwai waɗanda aka rataye su kuma. 14 Suka bizne ƙasusuwan Saul da Yonatan ɗansa cikin ƙasar Benyamin cikin Zela cikin kabarin Kish mahaifinsa. Suka aikata dukkan abin da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya amsa addu'o'insu domin ƙasar. 15 Daga nan sai Filistiyawa suka je su sake yin yaƙi da Isra'ilawa. Sai Dauda ya sauka da shi da mutanensa su yi yaƙi da Filistiyawa. Amma gajiyar yaƙi ta sa Dauda ya yi suwu. 16 Ishbi-Benob na zuriyar ƙattin nan wanda nauyin mashinsa ya yi nauyin shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma ɗauke da sabuwar takobi, ya yi nufin ya kashe Dauda. 17 Amma Abishai ɗan Zeruya ya ceci Dauda, ya bugi Bafilisten nan, ya kashe shi. Daga nan mazajen Dauda suka rantse masa, cewa, "Ba zaka ƙara tafiya yaƙi tare da mu ba, domin kada ka ɓice fitilar Isra'ila." 18 Bayan wannan kuwa aka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gob, lokacin da Sibbekai Bahushati ya kashe Saf, wanda ke ɗaya daga cikin zuriyar Refayim. 19 Ya zama kuma aka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Yayir mutumin Betlehem ya kashe Goliyat Bagittiye, wanda mãshin sa yana kama da dirkar masaƙa. 20 Ya zama kuma aka sake yin yaƙi a Gat inda akwai wani mutum mai tsayin gaske a kowanne hannunsa yana da yatsu shida a kowacce ƙafa kuma yana da yatsu shida, dukka ashirin da huɗu kenan. Shi ma har yanzu daga zuriyar Refayim ne. 21 Sa'ad da ya zazzagi Isra'ila, Yonatan ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda, ya kashe shi. 22 Waɗannan su ne zuriyar Refahayim na Gat an kashe su ta hannun Dauda da kuma ta hannun sojojinsa.

Sura 22

1 Dauda ya yi amfani da waɗannan kalmomi ya raira waƙa ga Yahweh a ranar da ya cece shi daga hannun dukkan abokan gabarsa, da kuma hannun Saul. 2 "Ya yi addu'a ya ce, Yahweh shi ne dutsena, da kagarata, shi wanda ya cece ni. 3 Allah shi ne dutse na. A cikinsa na sami mafaka, garkuwata da ƙahon cetona, hasumiyata mai tsawo, mafakata kuma, shi ne wanda ya cece ni daga tashin hankali. 4 Zan kira bisa Yahweh, wanda ya isa a yabe shi, kuma zan tsira daga hannun maƙiyana. 5 Gama ambaliyun mutuwa sun kewaye ni, haukan ruwayen hallakarwa sun tsoratadda ni. 6 Igiyoyin lahira sun kewaye ni; tarkunan mutuwa sun kama ni. 7 A cikin ƙuncina na kira Yahweh; Na kira Allahna; daga cikin haikalinsa ya ji muryata, kira na na neman taimako ya kai cikin kunnuwansa. 8 Sa'an nan ƙasa ta girgiza ta yi makyarkyata. Tussan sammai suka girgiza aka motsa su, saboda Allah ya yi fushi. 9 Hayaƙi ya fito daga hancinsa, wuta mai cinyewa ta fito daga bakinsa. Ta kunna gawayi ta wurinsa. 10 Ya buɗe sammai ya sauko ƙasa, duhu baƙiƙƙirin yana ƙarƙashin sawayensa. 11 Ya hau bisa Kerub, ya tashi. A bisa fukafukan iska aka ganshi. 12 Ya kuma maida duhu rumfa kewaye da shi, manyan hadura na tattaruwa cikin sararin sammai. 13 Daga sheƙin hasken gabansa gawayin wuta suka faɗo. 14 Yahweh ya yi tsawa daga sammai. Maɗaukaki ya tada muryarsa. 15 Ya harba kibawunsa, ya tarwatsa maƙiyansa - curirrikan walƙiya kuma sun tarwatsa su. 16 Sa'an nan hanyoyin ruwa suka bayyana; harsasun duniya suka tonu a kukan tsautawar Yahweh, da jin hucin numfashi daga hancinsa. 17 Daga bisa ya kai ƙasa; Ya riƙe ni! Daga cikin ruwaye masu yawa ya jawo ni. 18 Ya cece ni daga wurin maƙiyina mai ƙarfi, daga hannun waɗanda suka ƙi ni, gama sun fi karfina. 19 Suka afko mani a ranar masifata, amma Yahweh shi ne abin dogarata. 20 Ya kuma kawo ni waje a buɗaɗɗen wuri. Ya cece ni saboda yana murna da ni. 21 Yahweh ya sãka mani bisa ga ma'aunin adalcina; ya sãke gyara ni bisa ga tsabtar hannuwana. 22 Gama na kiyaye hanyoyin Yahweh ban kuma juya wa Allah baya ba ta wurin aikata mugunta. 23 Gama dukkan shari'unsa na adalci suna gabana; game da zancen farillansa kuma, ban rabu da su ba. 24 Marar laifi nake a gabansa, na kuma kiyaye kaina daga zunubi. 25 Domin wannan Yahweh ya sabunta ni ya sãka mani bisa ga adalcina, bisa ga matsayin tsabtata a idonsa. 26 Ga mai aminci, ka nuna kanka mai aminci ne; ga mutumin da ya ke marar laifi, zaka nuna kanka marar laifi. 27 Ga mai tsabta, ka zama da tsabta, amma ga fãsiki ka zama a murɗe. 28 Ka ceci rauna nan mutane, amma idanun ka na gãba da masu girmankai, kuma ka kawo su ƙasa. 29 Gama kai ne fitilata, Yahweh. Yahweh ya haskaka duhuna. 30 Gama ta wurinka zan iya zarce taron yaƙi; ta wurin Allahna nake tsallake ganuwa. 31 Domin Allah, hanyarsa cikakkiya ce. Shi garkuwa ne ga dukkan waɗanda suka nemi mafaka a cikin sa. 32 Gama wane ne Allah sai Yahweh? Wane ne dutse kuma sai Allahnmu? 33 Allah shi ne mafakata, yana kuma bida mutum marar laifi cikin hanyarsa. 34 Yana maida ƙafafuna suyi sauri kamar na naman jeji, ya kuma sanya ni a bisa dogayen tuddai. 35 Yana koyar da hannuwana domin yaƙi, damtsuna kuma su tausa baka na jan ƙarfe. 36 Ka kuma bani garkuwar cetonka, tagomashinka ya maishe ni mai girma. 37 Ka sanya wuri mai faɗi ƙarƙashin sawayena, santsi bai kwashe ƙafafuna ba. 38 Na fafari maƙiyana na kuma hallaka su. Ban juya ba har sai da suka hallaka. 39 Na cinye su na ragargaza su; ba za su tashi ba. Sun fãɗi ƙarƙashin sawayena. 40 Ka sanya ƙarfi a jikina kamar ɗammara domin yaƙi; waɗanda suka tayar mani ka sanya su ƙarƙashina. 41 Ka bani bayan maƙiyana' da wuyansu; Na datse wuyan waɗanda suka ƙi ni. 42 Sun yi kuka domin neman taimako, amma ba wanda ya cece su; sun yi kuka ga Yahweh, amma bai amsa masu ba. 43 Na buge su da kyau na niƙesu kamar turɓaya a ƙasa, na tattake su kamar laka na watsar da su cikin tituna. 44 Ka kuma ƙwatoni daga husumar mutanena. Ka kiyayeni a matsayin shugaban al'ummai. Mutanen da ban sani ba sun yi mani hidima. 45 Baƙi sun russuna mani dole. Da jin labarina, sun yi mani biyayya. 46 Baƙi sun fito daga wurin ɓuyarsu suna rawar jiki. 47 Yahweh mai rai ne! Bari a yabi dutsena. Bari Allah ya ɗaukaka, dutsen cetona. 48 Wannan shi ne Allah wanda ke tabbatar da sakayya domina, shi wanda ke ƙasƙantar da al'ummai ƙarƙashina. 49 Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiyana. Tabbas, ka ɗaukaka ni bisa kan waɗanda suka tayar mani. Ka kuɓutar da ni daga masu son cutar da ni. 50 Domin wannan Zan yi godiya gare ka, Yahweh, a tsakanin al'ummai; Zan raira waƙoƙin yabbai ga sunanka. 51 Allah ya bayar da babban ceto ga sarkinsa, yana nuna alƙawarin biyayya ga shafaffe na sa, ga Dauda da zuriyarsa har abada."

Sura 23

1 Yanzu fa waɗannan su ne ƙarshen zantattukan Dauda - Dauda ɗan Yesse, mutumin da aka girmama ƙwarai, shi wanda ya ke shafaffe daga Allahn Yakubu, mawaƙi mai daɗi na Isra'ila. 2 "Ruhun Yahweh ya yi magana da ni, maganarsa kuma tana kan harshena. 3 Allah na Isra'ila ya faɗi, Dutsen Isra'ila ya ce mani, 'Shi wanda ya ke mulkin mutane cikin adalci, mai yin mulki cikin tsoron Allah. 4 Zai zama kamar hasken safiya sa'ad da rana take fitowa, safiyar da babu giza-gizai, sa'ad da ɗanyar ciyawa take tsirowa daga ƙasa ta wurin hasken rana bayan saukowar ruwan sama. 5 Hakika ba haka iyalina suke a gaban Allah ba? Ko bai yi madawwamin alƙawari da ni, shimfiɗaɗɗe bisa ga ƙa'ida ya tabbatar ta kowacce hanya ba? Ko bai ƙara cetona ba kuma ya biya kowanne muradina ba? 6 Amma marasa amfani za su zama kamar ƙayayuwa da za a zubar, gama ba za su tattaru da hannu ɗaya ba. 7 Mutumin daya taɓa su dole ya yi amfani da makamin ƙarfe ko mashi mai tsini. Dole a ƙone su sarai a wurin da suka kwanta." 8 Waɗannan su ne sunayen shahararrun sojojin Dauda: Yeshbal mutumin Hakmoniya shugabane na sojoji masu ƙarfi. Ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci ɗaya. 9 Bayansa kuma sai Eliyazar ɗan Dodai Ba'ahotiye, ɗaya daga cikin jarumawa uku na Dauda. Yana nan lokacin da suka rena Filistiyawa da suka tattaru tare don suyi yaƙi, lokacin da mutanen Isra'ila sun rigaya sun bar wurin. 10 Eliyaza ya tashi tsaye ya bugi Filistiyawa har hannunsa ya gaji hannunsa kuma ya liƙe wa takobinsa. Yahweh ya kawo babbar nasara a wannan ranar. Jama'a suka koma bayan Eliyaza, domin kawai su tuɓe jikuna. 11 Bayansa kuma sai Shamma ɗan Agee, Harariye. Filistiyawa suka taru a filin dagar yaƙi, mutane kuwa suka gudu daga gabansu. 12 Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar yankin ƙasar ya kuma kareta. Ya kashe Filistiyawa, Yahweh ya kawo babbar nasara. 13 Uku daga cikin su talatin sojojin suka gangaro zuwa wurin Dauda a lokacin girbi, zuwa kogon Adullam. Rundunar Filistiyawa sunyi sansani cikin kwarin Refim. 14 A lokacin nan Dauda yana cikin kagararsa, a kogo, yayin da Filistiyawa kuma suka kafu a Betlehem. 15 Dauda ya ji ƙịṣḥi ya ce, "Ina ma wani zai bani ruwa daga rijiyar da ke a Betlehem, rijiyar da ke kusa da ƙofa!" 16 Sai jarumawannan uku suka fasa rundunar Filistiyawa suka ɗebo ruwa daga rijiyar da ke Betlehem, wadda ke kusa da ƙofa. Suka ɗauki ruwan suka kawowa Dauda, amma yaƙi sha, Maimakon haka sai ya zuba wa Yahweh. 17 Daga nan sai ya ce, "Bari wannan ya yi nesa da ni, Yahweh, har da zan sha wannan. Zan sha jinin mutanen da suka sadaukar da rayukansu?" Domin wannan bai yarda ya sha ba, Waɗannan su ne al'amuran da jarumawan nan uku suka yi. 18 Abishai ɗan'uwan Yowab, ɗan Zeruya, shi ne babba cikin su uku. Ya taɓa yin yaƙi da mashinsa ya kuwa kashe mutum ɗari uku. An sha ambatonsa tare da sojojin nan guda uku. 19 Ba shi ya fi ukun suna ba? An sanya shi shugabansu. Duk da haka, sunansa ba a kwatanta shi da darajar sauran sojoji ukun. 20 Benaiya daga Kabzeyel shi ɗa ne wurin Yahoiyada; shi mutum ne mai ƙarfi wanda ya yi manyan abubuwa na kasada. Ya kashe 'ya'ya biyu na Ariyel na Mowab. Ya kuma shiga cikin rami ya kashe zaki a lokacin dusar ƙanƙara. 21 Kuma ya kashe wani Bamasare mutum mai daraja. Bamasaren yana da mashi a hannunsa, amma Benaiya ya yi yaƙi dashi da sanda kawai, ya fizge mashin a hannun Bamasaren sa'an nan ya kashe shi da mashinsa. 22 Benaiya ɗan Yehoiyada ya yi waɗannan ayyukan kasada, an lissafa sunansa cikin sunayen jarumawannan uku. 23 An mutumta shi fiye da sauran sojojin nan talatin gaba ɗaya. Amma bai kai sauran sojojin nan uku masu ƙarfi ba. Duk da haka Dauda ya sa shi a bisa matsaransa. 24 Mutum talatin ɗin sun haɗa da: Asahel ɗan'uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem, 25 Shamma Baharodiye, Elika Baharodiye, 26 Helez Bafaltiye, Ira ɗan Ikkesh Batekoyi, 27 Abiyeza Ba'anatote, Mebunnai Bahushatiye, 28 Zalmon Ba'ahohite, Maharai Banetofatiye; 29 Heleb ɗan Bãna, Banetofatiye, Ittai ɗan Ribai daga Gibiya ta Benyamin, 30 Benaiya Bafiratoniye, Hiddai na wajen kwarin Gãsh. 31 Abi albon Ba'arbatiye, Azmabet Babarhumi, 32 Eliyaba Bashãlboniye 'ya'yan Yashen, Yonatan ɗan Shamma Baharariye; 33 Ahiyam ɗan Sharar Ba'arariye, 34 Elifelet ɗan Ahasbai Ma'akatiye, Eliyam ɗan Ahitofel Bagilone, 35 Hezro Bakarmile, Fãrai Ba'abite, 36 Igal ɗan Natan daga Zoba, Bani daga kabilar Gad. 37 Zelek Ammoniye, Naharai Baberote masu ɗaukarwa Yowab kayan yaƙi ɗan Zeruya, 38 Ira Ba'i tire, Gareb Ba'itire, 39 Yuriya Bahittiye dukkan su talatin da bakwai

Sura 24

1 Fushin Yahweh ya sake ƙuna akan Isra'ila, ya kuma iza Dauda akansu ya ce, "Jeka ka ƙidaya Isra'ila da Yahuda." 2 Sarki ya ce da Yowab shugaban runduna, wanda ya ke tare dashi, "Ka tafi cikin dukkan kabilun Isra'ila, daga Dan zuwa Biyasheba, ka ƙirga dukkan mutane, domin in san jimillar dukkan mutane da suka cancanta domin yaƙi." 3 Yowab ya cewa sarki, "Bari Yahweh Allahnka ya riɓanɓanya mutane sau ɗari, kuma bari idanun sarki shugabana ya ga faruwar haka. Amma donme shugabana sarki ya ke son wannan?" 4 Duk da haka maganar sarki ta zama ita ce ta ƙarshe akan ta Yowab da sauran shugabannin rundunar yaƙi. Sai Yowab da sarakunan rundunar yaƙi suka fita daga gaban sarki domin su ƙirga yawan mutanen Isra'ila. 5 Suka haye Yodan suka sauka kusa da Arowa, hannun dama ga birnin da ke cikin kwari. Daga nan suka yi tafiya zuwa Gad har zuwa Yazer. 6 Suka zo Giliyad da kuma ƙasar Tahtim Hodshi, daga nan sai Dan yăn da kewayen wajen Sidon. 7 Suka zo kagarar Taya da dukkan biranen Hibiyawa dana Kan'aniyawa. Daga nan suka fita zuwa Negeb cikin Yahuda a Biyasheba. 8 Ya yin da suka je dukkan ƙasar, sai suka dawo Yerusalem a ƙarshen watan tara da kwana ashirin. 9 Yowab ya bada rahoton jimillar yawan mayaƙa ga sarki. Akwai mutum 800,000 a cikin Isra'ila jarumawa masu zarar takobi, mazajen Yahuda kuma su 500,000 ne. 10 Daga nan sai zuciyar Dauda ta soke shi bayan ya lissafta mutanen. Sai ya ce da Yahweh, "Na yi babban zunubi ta wurin yin wannan. Yanzu fa, Yahweh, ka ɗauke laifin bawanka, gama na aikata wauta ƙwarai." 11 Sa'ad da Dauda ya tashi da safe, sai maganar Yahweh ta zo wurin annabi Gad, mai duba, na Dauda cewa, 12 "ka je kace da Dauda: 'Wanan shi ne abin da Yahweh ya ce: "'Ina miƙa maka abu uku, sai ka zaɓi ɗaya cikinsu."" 13 Sai Gad ya je wurin Dauda ya ce masa, "Ko shekaru uku na yunwa su zo maka cikin ƙasarka, ko kuwa zaka yi ta gudu wata uku daga abokan gabarka suna bin ka? ko kuwa za ayi annoba kwana uku a cikin ƙasarka? Yanzu sai kayi shawarar amsar da zan maida wa shi wanda ya aiko ni." 14 Sai Dauda ya cewa Gad, "I na cikin babbar damuwa." Bari mu faɗa cikin hannun Yahweh da mu faɗa cikin hannun mutum, gama ayyukan jinƙansa da girma suke." 15 Sai Yahweh ya aika da annoba kan Isra'ila daga safe zuwa lokacin da aka sanya, mutane dubu saba'in suka mutu daga Dan zuwa Biyasheba. 16 Lokacin da mala'ika ya miƙa hannunsa wajen Yerusalem domin ya hallakata, Yahweh ya canza tunaninsa game da ɓarnar, ya ce da mala'ikan da ke hallakar da mutanen, "Ya isa! Sai ka janye hannunka yanzu." A wancan lokacin mala'ikan Yahweh yana tsaye a masussukar Arauna Bayebushe. 17 Dauda ya yi magana da Yahweh da ya ga mala'ikan da ya bugi mutanen, ya ce, "Na yi zunubi, kuma na yi aikin shiririta. Amma tumakin nan me suka yi? Ina roƙon ka bari hannunka ya hukunta ni da iyalin mahaifina!" 18 Ran nan sai Gad ya zo wurin Dauda ya ce masa, "Ka hau ka gina bagade ga Yahweh a masussukar Arauna Bayebushe." 19 Dauda kuwa ya hau kamar yadda Gad ya faɗa masa ya yi, kamar yadda Yahweh ya umarta. 20 Arauna ya duba ya ga sarki da bayinsa suna isowa. Sai Arauna ya fito ya sunkuyar da kansa ga sarki da fuskarsa a ƙasa. 21 Daga nan sai Arauna ya ce, "Donme shugabana sarki ya zo wurina, bawansa?" Dauda ya amsa, "Domin in sa yi masussukarka, domin in gina bagadi ga Yahweh, domin a iya kawar da annoba cikin mutane." 22 Arauna ya cewa Dauda, "Ka ɗauke ta kamar ta ka, ya shugabana sarki. Ka yi dukka abin da ka ga dama. Duba, ga shanu domin hadaya ta ƙonawa da kayan masussuka da karkiyoyin shanu domin itace. 23 Dukkan waɗannan, sarkina, Ni, Arauna, zan ba ka." Sai ya ce da sarki, "Bari Yahweh Allahnka ya karɓe ka." 24 Sai sarki ya cewa Arauna, "A'a, lallai sai dai mu yi ciniki in saye ta. Ba zan miƙa hadayar ƙonawa ga Yahweh ta kowanne abin da ban biya ba." Dauda ya sayi masussukar da shanun akan awo hamsin na azurfa. 25 Dauda ya gina wa Yahweh bagadi a wurin ya miƙa ƙonannun hadayu, da hadayun zumunta. Da haka suka roƙi Yahweh a madadin ƙasar, ya kuma sa annobar ta tsaya a ko'ina cikin Isra'ila.

Littafin Sarakuna Na Ɗaya
Littafin Sarakuna Na Ɗaya
Sura 1

1 Sa'ad da Sarki Dauda ya tsufa sosai, suka lulluɓe shi da barguna amma bai ji ɗumi ba. 2 Sai bayinsa suka ce, "Bari mu samo wa shugabanmu sarki wata budurwa domin ta yi wa sarki hidima ta kula da shi. Ta kwanta a damatsen shugabanmu sarki domin ya ji ɗumi." 3 Suka bincika cikin dukkan lungunan Isra'ila, sai suka samo Abisha Bashunamiye su ka kawo ta wurin sarki. Budurwar kyakkyawa ce ƙwarai. 4 Ta yi wa sarki hidima ta lura da shi, amma sarkin bai kwana da ita ba. 5 A wannan lokacin Adonija ɗan Haggit ya ɗaukaka kansa, cewa, "Ni zan zama sarki." Ya shirya wa kansa karusai da mahaya, mazaje hamsin su wuce gabansa. 6 Babansa bai dame shi ba da cewa, "Meyasa ka yi wannan ko wancan?" Adonija ma kyakkyawan mutum ne ƙwarai, shi aka haifa bayan Absalom. 7 Ya haɗa kai da Yowab ɗan Zeruyiya da Abiyata firist. Suka bi Adonija suka taimaka masa. 8 Amma Zadok firist da Benayiya ɗan Yehoiada da Natan annabi da Shimai da Reyi da jarumawan da ke tare da Dauda ba su bi Adonija ba. 9 Adonija ya yi hadayar tumaki da bijjimai da kiwatattun shanu kusa da dutsen Zohelet, wanda ke daura da En Rogel. Ya gayyaci dukkan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki da dukkan mazajen Yahuda da bayin sarki. 10 Amma Natan annabi da Benayiya da mazajen Suleman ɗan'uwansa bai gaiyace su ba. 11 Sai Natan ya yi wa Batsheba uwar Suleman magana, cewa, "Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba, kuma ba da sannin Dauda shugabanmu ba? 12 Bari in ba ki shawara yanzu domin ki ceci ranki da na ɗanki Suleman. 13 Ki je wurin sarki Dauda, ki ce, shugabana, ba ka yi rantsuwa ga baiwarka ba, cewa, "Babu shakka Suleman ɗanki shi ne zai yi sarauta bayana, ya zauna kan kursiyina ba?" Me ya sa Adonija ke mulki?' 14 Sa'ad da ki ke magana da sarki, zan zo in tabbatar masa da maganganunki." 15 Sai Batsheba ta tafi ɗakin sarki. Sarki ya tsufa ƙwarai, Abisha Bashunamiya tana yi wa sarki hidima. 16 Batsheba ta sunkuya ta kwanta a gaban sarki. Sarki ya ce da ita, "Me ki ke so?" 17 Ta ce da shi, "Shugabana, ka rantsewa baiwarka da Yahweh Allahnka, cewa, 'Babu shakka Suleman ɗanki, shi zai yi mulki baya na, shi zai zauna a kursiyina?' 18 To yanzu ka ga, Adonija ne sarki, kai kuma shugabana sarki ba ka sani ba. 19 Ya yi hadaya da bijjimai da kiwatattun shanu da tumaki da yawa, kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki da Abiyata firist da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Suleman bawanka ba. 20 Game da kai shugabana sarki, dukkan idanun Isra'ila kai suke kallo, suna jira ka ce da su ga wanda zai yi mulki a bayana, shugabana. 21 Idan kuwa ba haka ba, zai zama bayan da shugana sarki ya yi barci tare da ubanninsa, ni da ɗana Suleman za a mai da mu kamar 'yan ta'adda." 22 Tana cikin magana da sarki, sai Natan annabi ya shigo. 23 Barori suka ce da sarki, "ga Natan annabi ya zo." Sa'ad da ya shigo gaban sarki, ya kwanta da fukarsa a ƙasa a gaban sarki. 24 Natan yace, "Shugabana sarki, ka ce Adonija zai yi mulki bayana, shi zai zauna kan kursiyina ne?' 25 Gama ya tafi yau ya yi hadaya da bijjimai da kiwattatun shanu da tumaki da yawa, kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki da shugaban sojoji da Abiyata firist. Suna ci suna sha a gabansa, suna cewa, 'ranka ya daɗe sarki Adonija!' 26 Amma ni, bawanka da Zadok firist da Benaiya ɗan Yehoiada da bawanka Suleman bai gayyace mu ba. 27 Shugabana ya yi haka ba tare da ya gaya mana bayinka ba, wanda zai zauna a kan kursiyinsa?" 28 Sai sarki ya amsa ya ce, "kira mani Batsheba ta dawo." Ta zo gaban sarki ta tsaya. 29 Sarki ya yi alƙawari ya ce, "Da ran Yahweh wanda ya cece ni daga dukkan wahalhalu, 30 kamar yadda na rantse maku da Yahweh, Allah na Isra'ila, cewa, 'Suleman ɗanki, shi zai yi mulki bayana, zai zauna kan kursiyna, zan yi haka yau." 31 Sa'an nan sai Batsheba ta sunkuya da fuskarta a ƙasa ta kwanta gaban sarki ta ce, "Ranka ya daɗe shugabana, sarki Dauda!" 32 Sarki Dauda yace, "A kira mani Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yahoiada." Sai su ka zo gaban sarki. 33 Sarki ya ce, "ku tafi da barorin shugabanku, ku sa Suleman ya hau alfadarina ku kai shi Gihon. 34 Bari Zadok firist da Natan annabi su shafe shi ya zama sarki akan Isra'ila su busa ƙaho su ce, 'Ranka ya daɗe sarki Suleman!' 35 Sai ku biyo shi, ya zo ya zauna kan kursiyina; domin shi ne zai gaje ni. Na naɗa shi ya zama sarki bisa Isra'ila da Yahuda." 36 Benayiya ɗan Yehoiada ya amsawa sarki ya ce, "Bari ya zama haka! Yahweh Allah na shugabana sarki, ya tabbatar da shi. 37 Kamar yadda Yahweh ya kasance da shugabana sarki, bari ya kasance da Suleman, kursiyinsa ya ɗaukaka fiye da kursiyin shugabana sarki Dauda." 38 Sai Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yehoiada da Keretawa da Feletiyawa suka je suka ɗora Suleman akan alfadarin Sarki Dauda; suka kawo shi Gihon. 39 Zadok firist ya ɗauko ƙahon mai daga cikin rumfa ya shafe Suleman. Sa'an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka ce, "Ranka ya daɗe sarki Suleman." 40 Sa'an nan dukkan mutane suka biyo shi suna busa sarewa suna farinciki da murna sosai, har ƙasa ta girgiza saboda ƙararsu. 41 Adonija da bãƙinsa da ke tare da shi suka ji sa'ad da suka gama ciye-ciye. Sa'ad da Yowab ya ji ƙarar ƙahon ya ce, "Me ya sa a ke hargowa a cikin birni?" 42 Yana cikin magana Yonatan ɗan Abiyata firist ya zo. Adonija yace, "Shiga, kai mai aminci ne ka kuma kawo labari mai daɗi." 43 Yonatan yace da Adonija, "Shugabanmu sarki Dauda ya sa Suleman ya zama sarki, 44 kuma sarki ya aiko shi tare da Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yehoiada da Keretawa da Feletiyawa. Sun sa Suleman ya hau alfadarin sarki. 45 Zadok firist da Natan annabi sun shafe shi ya zama sarki a Gihon, sun taho daga can su na murna, saboda haka birni ya cika da hargowa. Wannan ita ce hayaniyar da ka ke ji. 46 Kuma, Suleman yana zaune akan kursiyin mulki. 47 Bayan haka, barorin sarki sun zo suna sawa sarki Dauda albarka suna cewa, 'Bari Allahnka ya sa sunan Suleman ya fi naka.' Sai sarki ya sunkuya akan gado. 48 Sai sarki ya ce, 'Albarka ga Yahweh Allah na Isra'ila, da ya bada wanda zai zauna akan kursiyina yau, kuma idona yana gani.'" 49 Sai dukkan bãƙin Adonija suka firgita. Suka tashi tsaye kowa ya bi hanyarsa. 50 Adonija yana jin tsoron Suleman, ya je ya riƙe ƙahonin bagadi. 51 Sai aka gaya wa Suleman cewa, Duba, Adonija yana jin tsoron sarki Suleman, gama gashi can ya na riƙe da ƙahonin bagadi, yana cewa, 'Bari sarki Suleman ya rantse mani cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba."' 52 Suleman yace, "Idan zai nuna kansa mutumin kirki, ko gashin kansa ba zai faɗi a ƙasa ba, amma idan aka sami mugunta a wurinsa to zai mutu." 53 Sarki Suleman ya aika mutane suka saukar da Adonija daga bagadi. Ya zo ya russana a gaban Suleman, Suleman ya ce da shi, "Tafi gidanka."

Sura 2

1 Sa'ad da ranar mutuwar Dauda ta gabato, ya umurci ɗansa, Suleman cewa, 2 "ina bin hanyar dukkan duniya, ka ƙarfafa, ka nuna kanka namiji. 3 Ka kiyaye dokokin Ubangiji Allahnka, ka yi tafiya cikin hanyoyinsa, ka kiyaye farillansa da dokokinsa da shawarwarinsa da alƙawaransa, kana kiyaye abin da da aka rubuta cikin dokokin Musa domin ka wadata cikin dukkan abin da ka ke yi, a dukkan inda ka nufa, 4 domin Yahweh ya cika maganarsa wadda ya faɗi game da ni, cewa, 'Idan 'ya'yanka suka lura da tafarkinsu, suka yi tafiya a gabana da aminci da dukkan zuciyarsu da dukkan ransu, ba za ka rasa mutum akan kursiyin Isra'ila ba.' 5 Ka san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi ma ni da abin da ya yi wa jami'an sojojin Isra'ila su biyu, Abna ɗan Ner da Amasa ɗan Yatar waɗanda ya kashe. Ya zubar da jinin yaƙi cikin salama, ya sa jinin yaƙi akan ɗamarar da ke ƙugunsa da takalman da ke ƙafafunsa. 6 Ka yi da Yowab bisa ga hikimar da ka koya, amma kada ka bari furfurarsa ta tafi kabari cikin salama. 7 Duk da haka, ku yi mutunci ga 'ya'yan Barzilai Bagilide, ku bar su su zauna a cikinku su ci a teburinka, gama sun je wurina sa'ad da na gudu daga wurin ɗan'wanka Absolom. 8 Duba, Shimai ɗan Gera mutumin Benyamin ta Bahurim yana tare da ku, wanda ya zage ni, ya wulaƙanta ni, ya zazzage ni ranar da na je Mahanayim. Ya zo ya tarbe ni a Yodan, na rantse masa da sunan Yahweh cewa, 'Ba zan kashe ka da takobi ba.' 9 Kada ka bar shi ya tafi ba tare da ka hore shi ba. Kana da hikima ka san yadda za ka yi da shi. Ka sa furfurarsa ta faɗi cikin jini." 10 Sa'an nan Dauda ya yi barci tare da ubanninsa aka bizne shi a birnin Dauda. 11 Dauda ya yi mulki a Isra'ila shekaru arba'in, shekaru bakwai ya yi mulki a Hebron, a Yerusalem kuma ya yi mulki shekaru talatin da uku. 12 Suleman ya zauna akan kursiyin Dauda ubansa, mulkinsa kuwa ya kahu da ƙarfi ƙwarai. 13 Sai Adonija ɗan Haggit ya zo wurin Batsheba uwar Suleman. "Ta ce da shi cikin salama ka zo?" Ya ce, cikin salama ƙwarai." 14 Ya ce, ina da wani abu da zan faɗa maki." Sai ta ce, "To ka faɗi." 15 Adonija yace, "Kin san mulkin nawane, dukkan Isra'ila sun yi zaton ni zan zama sarki. Amma abubuwa sun canza, an ba ɗan'uwana sarauta, kuma wannan daga Yahweh ne. 16 Zan roƙi abu ɗaya a wurin ki, kada ki juya mani baya, Batsheba ta ce, "Ka faɗi." 17 Ya ce, "Ki yi magana da Suleman sarki, na san ba zai ƙi jin maganar ki ba, ki ce da shi ya ba ni Abishag Bashunamiye ta zama matata. 18 Batsheba ta ce, "Ya yi kyau, zan yi magana da sarki." 19 Sai Batsheba ta je wurin sarki ta faɗa masa maganar da Adonija ya yi. Sarki ya je ya tarbe ta, ya russana a gabanta. Sa'an nan ya zauna a kan kursiyinsa kuma ya sa aka kawo wa mamar sarki kujera. Ta zauna a hannun damarsa. 20 Ta ce da shi, "Zan roƙi wani ɗan abu daga wurinka, na sani ba za ka ƙi ba." Sai sarki ya ce, "Ki roƙa mama, ba zan ƙi ba." 21 Ta ce, "Ka bari a ba Adonija ɗan'uwanka Abishag Bashunamiye ta zama matarsa." 22 Sarki Suleman ya amsa ya ce da mamarsa, "Meyasa ki ka ce a ba Adonija Abishag Bashunamiye ta zama matarsa? Meyasa ba ki ce a ba shi mulkin ba kuma gama shi yayana ne - ne dai, domin Abiyata firist, ko domin Yowab ɗan Zeruya?" 23 Sarki Suleman ya rantse da sunan Yahweh, ya ce, "Bari Allah ya yi mani fiye da haka, idan Adonija ba a bakin ransa ya faɗi wannan magana ba. 24 Yanzu da ran Yahweh, wanda ya sa ni a kan kursiyin Dauda mahaifina, ya yi gida domina, babu shakka yau za a kashe Adonija." 25 Sarki Suleman ya aiki Benayiya ɗan Yehoiada, ya nemi Adonija ya kashe shi. 26 Sa'an nan sarki ya ce da Abiyata firist, ka tafi Anatot, ga gonakinka, kaima ka isa mutuwa, amma ba zan kashe ka a wannan lokaci ba, domin ka ɗauki akwatin Ubangiji Yahweh a gaban Dauda mahaifina, ka sha wahala kamar yadda mahaifina ya sha." 27 Ta haka Suleman ya kori Abiyatar daga zama firist na Yahweh, domin maganar da Yahweh ya faɗi a Shilo game da gidan Eli ta cika. 28 Sai maganar ta zo ga Yowab saboda ya goyi bayan Adonija, ko da ya ke bai goyi bayan Absolom ba. Sai Yowab ya gudu ya shiga rumfar Yahweh ya kama ƙahonin bagadi ya riƙe. 29 Sai aka gaya wa Suleman sarki, cewa ga Yowab can cikin rumfar Yahweh, sai ya ce da Benayiya ɗan Yehoiada, "Je ka same shi ka kashe shi." 30 To sai Benayiya ya zo rumfar Yahweh, ya ce masa, "Sarki ya ce, 'ka fito"' Yowab ya amsa ya ce, "A'a ni zan mutu a nan." Sai Benaiya ya koma ya gaya wa sarki, cewa, Yowab yace, Yana so ya mutu a kan bagadi." 31 Sai sarki ya ce da shi, yi yadda ya faɗi. Kashe shi ka ɗauke shi, ka bizne domin a kawar da jinin da Yowab ya zubar ba dalili daga gidan mahaifina. 32 Yahweh ya sa jininsa ya koma kansa, gama ya sami mutane biyu waɗanda sun fi shi, kuma sun fi shi sarki, ya kashe su da kaifin takobi. Wato Abna ɗan Na shugaban sojojin Isra'ila da Amasa ɗan Yeter shugaban sojojin Yahuda, ba tare da sanin mahaifina sarki Dauda ba. 33 Bari jininsu ya dawo kan Yowab da zuriyarsa har abada. Amma ga Dauda da zuriyarsa da gidansa da kursiyinsa, bari salama daga Yahweh ta kasance har abada." 34 Sai Benayiya ya je ya sami Yowab, ya far masa ya kashe shi. A ka bizne shi a gidansa cikin daji. 35 Sarki ya sa Binayiya ɗan Yehoiada ya zama shugaban sojoji maimakon sa, ya kuma sa Zadok firist a gurbin Abiyata. 36 Sai kuma sarki ya aika a ka kira Shimai, yace masa, "Ka gina gida domin kanka a cikin Yerusalem ka zauna nan, kada ka bar wurin ka je ko'ina. 37 Duk randa ka fita ka wuce kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu. Kuma jininka zai koma kanka." 38 Sai Shimai ya cewa sarki abin da ka faɗi ya yi kyau. Kamar yadda shugabana sarki ya faɗi, haka bawanka za ya yi." Daga nan Shimai ya zauna a Yerusalem kwanaki da yawa. 39 Amma bayan shekaru uku, bayin Shemai guda biyu suka guda suka je wurin Akish ɗan Ma'aka, sarkin Gat. A ka gaya wa Shimai, cewa, duba, bayinka "biyu fa sun koma Gat." 40 Sai Shimai ya tashi, ya sa sirdi a kan jakinsa, ya je wurin Akish a Gat neman bayinsa. Ya dawo da bayinsa daga Gat. 41 Sa'ad da a ka gaya wa Suleman, cewa Shimai ya fita daga Yerusalem ya je Gat ya dawo, 42 sarki ya aika a ka kira Shimai ya ce da shi, "Ba na sa ka yi rantsuwa da Yahweh ba na shaida maka, cewa, 'Ka sani duk randa ka bar nan ka je wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba.'? Ka ce mani, 'abin da ka faɗi ya yi kyau.' 43 To meyasa ba ka cika alƙawarinka ga Yahweh ba, da abin da na umurce ka?" 44 Sa'an nan sarki ya cewa Shimai, "Ka sani cikin zuciyarka dukkan muguntar da ka yi wa mahaifina Dauda. To Yahweh zai sa muguntarka ta koma kanka. 45 Amma sarki Suleman zai zama mai albarka, kursiyin Dauda kuma zai tabbata a gaban Yahweh har abada." 46 Sa'an nan sarki ya ummurci Benayiya ɗan Yehoiada. Ya fita waje ya kashe Shimai. Haka mulkin ya tabbata a hannun Suleman.

Sura 3

1 Suleman ya yi yarjejeniya da Fir'auna sarkin Masar ta dalilin aure. Ya ɗauko ɗiyar Fir'auna ya kawo ta cikin birnin Dauda har sai lokacin da ya gama ginin gidansa da gidan Yahweh da ganuwar da ta kewaye Yerusalem. 2 Mutane suna ta miƙa hadayu a wurare masu bisa, saboda ba a gina gida saboda sunan Yahweh ba tukuna. 3 Suleman ya nuna ƙauna ga Yahweh ta wurin tafiya cikin tafarkun mahaifinsa Dauda, sai dai shi ma ya miƙa hadaya kuma ya ƙona turare a wurare masu bisa. 4 Sarki ya je Gibiyon domin ya miƙa hadaya a can, domin can akwai wurare masu bisa sosai. Suleman ya miƙa hadayu dubu a kan bagadi. 5 Yahweh ya bayyana ga Suleman a cikin mafarki a Gibiyon, ya ce, "Ka roƙa! Mene ne zan ba ka?" 6 Sai Suleman yace, "Ka nuna girman alƙawarinka da jinƙai da aminci ga bawanka, mahaifina Dauda, saboda ya yi tafiya a gabanka cikin aminci da tsarki da gaskiya cikin zuciyarsa. Ka riƙe wannan alƙawarin da aminci da ka ba shi ɗa wanda zai zauna a kan kursiyinsa yau. 7 Yanzu fa, ya Yahweh Allahna, ka sa bawanka ya zama sarki a maimakon mahaifina Dauda, ko da ya ke ni ɗan yaro ne. Ban san yadda zan fita ko in shiga ba. 8 Bawanka yana cikin tsakiyar mutane waɗanda ka zaɓa, mutane masu yawa da sun fi gaban a lisafta ko a ƙidaya su. 9 Ka ba bawanka zuciya mai fahimta domin ya hukunta mutanenka, domin in gane bambanci tsakanin abu mai kyau da mummuna. Gama wane ne zai iya hukunta wannan jama'a taka mai yawa haka?" 10 Wannan roƙo na Suleman ya gamshi Ubangiji. 11 Sai Allah ya ce da shi, "Saboda ka roƙi wannan, ba ka roƙi tsawon rai ba, ko dukiya ko ran maƙiyanka ba, Amma ka roƙi fahimta domin ka gane gaskiya, 12 duba zan yi maka dukkan abin da ka roƙa a gare ni. Na ba ka zuciya mai hikima da ganewa, ba a yi wani mai hikima kamar ka a dã ba, ba kuma za a sami wani mai hikima kamar ka ba a nan gaba bayanka. 13 Kuma na ba ka har ma abin da ba ka roƙa ba, dukiya da martaba, yadda ba za a sami wani kamar ka ba a cikin sarakuna dukkan kwanakin ranka. 14 Idan ka yi tafiya cikin hanyoyina da farillaina da dokokina kamar yadda Dauda mahaifinka ya yi tafiya, zan haskaka kwanakinka." 15 Sai Suleman ya farka, ashe mafarki ya yi. Ya zo Yerusalem ya tsaya a gaban akwatin alƙawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa da na salama kuma ya yi liyafa domin dukkan bayinsa. 16 Sai ga waɗansu mata biyu karuwai suka zo gabansa suka tsaya. 17 Sai ɗaya matar ta ce, "Ya shugabana, ni da wannan matar muna zama a gida ɗaya, ni da ita muka haihu a gidan. 18 Bayan na haihu da kwana uku, wannan matar kuma sai ta haihu. muna tare. Ba kowa tare da mu sai mu biyu a gidan. 19 Sai ɗan wannan matar ya mutu cikin dare saboda ta kwanta a kansa. 20 Sai ta tashi cikin tsakiyar dare ta ɗauke ɗana daga kusa da ni, domin baiwarka ta yi barci, ta kwantar da shi a ƙirjinta, sai ta kwantar da nata mataccen ɗan a ƙirjina. 21 Sa'ad da na tashi da safe domin in shayar da ɗana sai na ga ya mutu. Amma da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ba ɗana ba ne wanda na haifa." 22 Sa'an nan sai ɗaya matar ta ce, "Ba haka ba ne, ɗan mai rai nawa ne ke kuma mataccen ne naki." Sai ɗaya matar ta ce, "A'a mataccen ne naki mai ran kuma shi ne ɗana." Haka suka yi ta magana a gaban sarki. 23 Daga nan sarki yace, "Ke kin ce, "Wannan ɗana ne mai ran, kuma naki ne mataccen,' ɗayar kuma ta ce, 'A'a, ɗanki shi ne mataccen, ɗana kuma shi ne mai ran."' 24 Sai sarki yace, "Ku kawo mani takobi." Sai aka kawo wa sarki takobi. 25 Daga nan sarki ya ce, "Ku raba ɗan mai rai kashi biyu, ku ba wannan mata rabi, rabi kuma ga ɗayar." 26 Sai ɗaya matar wadda ɗanta ne ya ke da rai, ta yi magana ta ce da sarki, gama zuciyarta ta cika da tausayi saboda ɗanta, ta ce, "Aiya, shugabana, a ba ta ɗan mai rai kada a kashe shi." Amma ɗaya matar ta ce, "Ba zai zama naki ko nawa ba. A raba shi." 27 Sai sarki ya yi magana ya ce, "Ku ba da ɗan mai rai ga matar ta farko, kada ku kashe shi, ita ce mahaifiyarsa." 28 Sa'ad da dukkan Isra'ila suka ji wannan hukunci, suka ji tsoron sarki, saboda sun ga hikimar Yahweh na tare da shi domin yanke hukunci.

Sura 4

1 Suleman shi ne sarki a bisa dukkan Isra'ila. 2 Waɗannan su ne jami'ansa: Azariya ɗan Zadok shi ne firist. 3 Elihoref da Ahija 'ya'yan Shisha su ne magatakarda, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci. 4 Benayiya ɗan Yehoiada shi ne shugaban sojoji. Zadok da Abiyata su ne firistoci. 5 Azariya ɗan Natan shi ne shugaban ma'aikata. Zabud ɗan Natan shi ma firist ne kuma abokin sarki. 6 Ahisha shi ne sarkin gida. Adoniram ɗan Abda shi ne shugaban masu aikin ƙarfi. 7 Suleman ya na da jami'ai goma sha biyu a dukkan Isra'ila waɗanda su ke tanada abinci domin sarki da mutanen gidansa. Kowanne mutum zai kawo abincin wata ɗaya a shekara. 8 Ga sunayensu: Ben Hur shi ne mai kula da tudun Ifraim; 9 Ben Deker shi ne a Makaz da Sha'albim da Bet Shemesh da Elon Bet Hanan; 10 Ben-Hesed a Arubbot (shi a ka damƙawa Sokoh da dukkan ƙasar Hefa); 11 Ben Abinadab shi ne cikin dukkan Nafot Dor (Tafat ɗiyar Suleman ita ce matarsa); 12 Ba'ana ɗan Ahilud ya na cikin Ta'anak da Megiddo da dukkan Bet Shan, wato kusa da Zaretan gangaren Yeziriyel, daga Bet Shan zuwa Abel Meholah har zuwa ɗaya gefen na Yokmiyam; 13 Ben Geber cikin Ramot Giliyad (shi aka danƙawa garuruwan Ja'ir ɗan Manasse waɗanda ke cikin Giliyad yankin Argob na wanda ke cikin Bashan ma nasa ne, manyan birane sittin masu ƙofofin jan ƙarfe); 14 Abinadab ɗan Iddo cikin Mahaniyam; 15 Ahima'az cikin Naftali (kuma ya auri Basemat ɗiyar Suleman ta zama matarsa); 16 Ba'ana ɗan Hushai cikin Asha da Bi'alot; 17 Yehoshafat ɗan Faruya cikin Issaka; 18 Shimei ɗan Ela, cikin Benyamin; 19 da Geber ɗan Uri cikin ƙasar Giliyad, da ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da Og sarki Bashan, kuma shi ne kaɗai jami'in da ke cikin ƙasar. 20 Yawan Yahuda da Isra'ila yana kama da yashin teku. Su na ci suna sha suna jin daɗi. 21 Suleman ya yi mulki kan dukkan mulkoki tun daga Kogi har zuwa ƙasar Filistiyawa da iyakar Masar. Suna bautawa Suleman suna kawo masa gaisuwa dukkan kwanakinsa. 22 Abincin gidan Suleman na rana ɗaya shi ne bahu talatin na niƙaƙƙen gari da kuma tsaba bahu sittin, 23 da bijimai masu ƙiba guda goma da shanu guda ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari, banda barewa da gadã da namijin barewai, da kaji masu mai. 24 Gama shi ne ya ke mulkin dukkan yankin da ke hayin Kogi, tun daga Tifsa har zuwa Gaza, a bisa dukkan sarakunan da ke hayin Kogi, kuma yana da salama a kowanne gefe. 25 Yahuda da Isra'ila sun sami tsaro har kowanne mutum yana zuwa gonarsa ta inabi da ta ɓaure, tun daga Dan zuwa Biyasheba a dukkan kwanakin Suleman. 26 Suleman yana da ɗakunan dawakai dubu arba'in domin karusansa, da masu hawan dawakai mutum dubu goma sha biyu. 27 Waɗannan jami'ai suna tanado abinci domin sarki Suleman da dukkan wanda ya zo ya ci a teburin sarki, kowanne mutum da watansa, ba su bari an rasa komai ba. 28 Kuma suna kawo hatsi da ciyawa saboda dawakan da suke jan karusai, kowanne mutum bisa ga iyawarsa. 29 Allah ya ba Suleman ƙasaitacciyar hikima da fahimta, faɗin ganewarsa yana kama da yashin da ke bakin teku. 30 Hikimar Suleman ta fi ta dukkan mutanen gabas da dukkan hikimar Masar. 31 Hikimarsa ta fi ta dukkan mutane - ya fi Etan Ba-ezrahi hikima harma da Heman da Kalkol da Darda 'ya'yan Mahol - ya zama sananne a dukkan al'umman da ke kewaye. 32 Ya faɗi misalai dubu uku, ya yi waƙoƙi dubu da biyar. 33 Ya yi bayani a kan tsire-tsire da itacen sidar da ke Lebanon har zuwa waɗanda suke fitowa a jikin bangon ɗaki. Ya yi bayani a kan namun daji da tsuntsaye da kifaye. 34 Mutane sukan zo daga wurare daban-daban domin su ji hikimar Suleman. Sukan zo daga wurin dukkan sarakunan da suka ji hikimar Suleman.

Sura 5

1 Hiram sarkin Taya ya aiki barorinsa wurin Suleman saboda ya ji an naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa; gama Hiram mai ƙaunar Dauda ne. 2 Suleman ya aika da magana zuwa ga Hiram, cewa, 3 "Ka sani mahaifina Dauda bai iya gina gida domin Yahweh Allansa ba, saboda yaƙe-yaƙen da suka kewaye shi, gama a lokacinsa Yahweh na ta sa abokan gabarsa a ƙarƙashin tafin sawunsa. 4 Amma yanzu, Yahweh ya ba ni hutawa a kowanne gefe. Ba abokin gãba kuma babu annoba. 5 To yanzu na yi niyya in gina haikali domin sunan Yahweh Allahna, kamar yadda Yahweh ya yi magana da mahaifina Dauda cewa, 'Ɗanka wanda zan sa a kan kursiyin mulki ya gaje ka, shi ne zai gina haikali domin sunana.' 6 To yanzu sai ka ba da umurni a saro mani itacen sida daga Lebanon. Bayina za su haɗu da bayinka, kuma zan biya bayinka dai-dai bisa ga abin da ka yarda da shi. Domin ka san a cikin mu ba wanda ya iya yankan katako kamar Sidoniyawa." 7 Lokacin da Hiram ya ji maganar Suleman, ya yi murna ƙwarai da gaske, ya ce, "Bari albarka ta kasance ga Yahweh yau, saboda ya ba Dauda ɗa mai hikima a kan jama'arsa mai girma." 8 Hiram ya aika da magana zuwa ga Suleman, cewa, "Na ji saƙon da ka aiko wurina. Zan ba ka dukkan katakon sida da na fir yadda ka ke bukata. 9 Bayina za su kawo itatuwan daga Lebanon zuwa teku, zan sa a ɗaɗɗaure su yadda za a iya sawo su a teku yadda ka ke so in yi, zan sa a yayyanka su domin ka ɗauko. Zan so ka bada abinci domin iyalin gidana. 10 Haka Hiram ya ba Suleman dukkan katakon sida da fir yadda ya bukata. 11 Suleman ya ba Hiram bahu dubu ashirin na alkama da mai wanda a ka tace garwa ashirin domin abincin gidansa, haka Suleman ya ba Hiram shekara biye da shekara. 12 Yahweh ya ba Suleman hikima, kamar yadda ya yi alƙawari. Salama ta kasance tsakanin Suleman da Hiram, suka ƙulla amana. 13 Sarki Suleman ya sa wa Isra'ilawa aikin dole. Mutanen da a ka sa aikin dolen sun kai dubu talatin. 14 Ya aika su Lebanon, mutum dubu goma an sa kowanne wata, wata ɗaya suna Lebanon, wata biyu kuma su na gida. Adoniram ya shugabanci waɗanda a ka sa su yi aikin dole ɗin. 15 Suleman yana da mutum dubu saba'in masu ɗaukar kaya, dubu takwas da kuma masu saro dutse cikin tsaunuka, 16 ban da haka Suleman yana da mutum 3,300 jami'ai ne na ma'aikata kuma masu duba ma'aikata. 17 Bisa ga ummurnin sarki, suka sassaƙo manyan duwatsu masu ƙwari domin a kafa tushen haikali. 18 Haka masu gini na wajan Suleman da na wajan Hiram da Gebalawa suka saro katakan suka shirya su tare da duwatsun domin ginin haikali.

Sura 6

1 Suleman ya fara gina haikalin Yahweh. Hakan ya faru a shekara ta 480 bayan dawowar 'ya'yan Isra'la daga Masar, a cikin shekara ta huɗu ta mulkin Suleman a bisa Isra'ila cikin watan Zif wato wata na biyu. 2 Haikalin da Sarki Suleman ya gina wa Yahweh, ratarsa kamu sittin ne, faɗinsa kamu ashirin ne, tsawonsa kuma kamu talatin ne. 3 Ratar shirayin da ke ƙofar haikalin kamu ashirin ne, dai-dai suke da faɗin haikalin, a gaban haikalin kuma ta kai kamu goma. 4 Ya yi wa gidan tagogi waɗanda faɗinsu daga ciki ya fi daga waje. 5 Ya gina ɗakuna kewaye da ɗakin taro, ɗakuna sun kewaye ɗakuna na ciki da na waje. Ya gina ɗakuna a kowanne gefe. 6 Bene na can ƙasa kamu biyar ne faɗinsa, na tsakiya kuma kamu shida ne a faɗi, na uku kuma kamu bakwai ne faɗinsa. Domin a kewaye da bangon gidan ya yi matokarai a bangon gidan a kowanne gefe domin kada a kafa wani abu a bangon gidan. 7 An gina gidan da sassaƙaƙƙun duwatsun da a ka shiryo a mahaƙar duwatsu. Sa'adda a ke ginin gidan ba a ji ƙarar gatari ko guduma ba. 8 A fuskar kudu ta haikalin an yi wurin shigowa daga ƙasa, a ka yi matakalu suka yi sama zuwa tsakiya, suka tafi har zuwa hawa na uku. 9 Haka Suleman ya gina haikalin ya gama shi; ya rufe gidan da matokarai da katakai na sida. 10 Ya yi ɗakuna a jikin ɗakunan taro na haikali, kowanne tsawonsa kamu biyar ne; a ka jingina su jikin gidan da katakai na sida. 11 Sai maganar Yahweh ta zo ga Suleman, cewa, 12 "Game da gidan da ka ke ginawa, idan ka kiyaye farillaina ka yi adalci, ka kiyaye dokokina ka yi tafiya a cikin su, sa'an nan zan tabbatar maka da alƙawarin da na yi wa Dauda mahaifinka. 13 Zan zauna cikin mutanen Isra'ila, ba zan yashe su ba." 14 Haka Suleman ya gina gidan ya gama shi. 15 Sa'an nan ya gina bangaye na ciki da falankai na sida. Ya rufe gidan da katakai tun daga ƙasa har sama, daɓen kuma ya rufe shi da falankai na fir. 16 Daga bayan gidan ya gina waɗansu ɗakuna masu kamu ashirin da katakai na sida tun daga ƙasa har sama. Ya gina wani ɗaki can ciki, shi ne wuri mafi tsarki. 17 Babban ɗakin, wato wuri mai tsarki wanda ke gaban wuri ma fi tsarki, tsawonsa kamu arba'in ne. 18 Akwai itacen sida a gidan, wanda a ka sassaƙa shi kamar ƙwarya a buɗe da furanni. Dukka sida ne a ciki. Ba bu aikin duwatsu da ake gani a ciki. 19 Suleman ya yi wani ɗaki can ciki domin a ajiye akwatin Yahweh a ciki. 20 Ratar ɗakin na can ciki kamu ashirin ne, faɗinsa kamu ashirin tsawonsa ma kamu ashirin ne. Suleman ya shafe bangayen da zinariya tsantsa bagadin kuma ya rufe shi da itacen sida. 21 Suleman ya shafe haikalin da zinariya tsantsa, ɗaki na can ciki kuma ya yi masa dajiya da zinariya, ya shafe gabansa da zinariya. 22 Ciki dukka ya shafe shi da zinariya har sai da a ka gama haikalin dukka. Bagadi na ɗaki na can ciki kuma ya shafe shi da zinariya. 23 Suleman ya yi sifofi biyu na kerubim da itacen zaitun, domin ɗaki na can ciki masu tsawon kamu goma. 24 Kowanne fiffike na kerub ɗin tsawonsa kamu biyar ne. Ya zama daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan ya zama kamu goma kenan. 25 Ɗayan kerub ɗin ma faɗin fiffikensa kamu goma ne. Dukkan kerubim ɗin dai-dai suke da juna ba wanda ya fi wani. 26 Tsayin kerub ɗaya kamu goma ne haka kuma na ɗayan kerub ɗin. 27 Suleman ya ajiye kerubim ɗin a ɗaki na can ciki. Suka buɗe fukafukansu na wannan ya taɓa wancan bango, na wancan kuma ya taɓa wancan bango. Fukafukansu suna taɓa juna a cikin wuri mafi tsarki. 28 Suleman ya shafe kerubin ɗin da zinariya. 29 Bangayen ɗakin an zane su da yatsun kerubim da ganyen dabino da buɗaɗɗun furanni tun daga ciki har waje. 30 Ƙasan gidan Suleman ya shafe shi da zinariya tun daga ɗakuna na ciki har zuwa na waje. 31 Ɗaki na ciki Suleman ya yi masa ƙofofin shiga da itacen zaitun. Dogaran ƙofar da ginshiƙansu suna da aiyanannun sassa guda biyar. 32 Haka ya yi ƙofofi biyu na itacen zaitun, ya sa a ka zana kerubim da ganyen dabino da furanni buɗaɗɗu. Ya shafe su da zinariya, kuma ya yayyafa zinariya a kan kerubim ɗin da kuma ganyen dabinan. 33 Ta haka Suleman ya yi wa haikalin ƙofofin shiga da itacen zaitun da aiyanannun sassa guda huɗu 34 da ƙofofi biyu na itacen fir. Ɓangare biyu na wannan ƙofa a kan naɗe su haka ma ɓangare biyu na waccan ƙofa a kan naɗe su. 35 Ya zana kerubim da ganyen dabino da furanni buɗaɗɗu a kansu, ya shafe zanen da zinariya dai-dai wa daida. 36 Ya gina farfajiya ta ciki da layika guda uku da sassaƙaƙƙen dutse da ginshiƙai na sida. 37 An kafa tushen gidan Yahweh a cikin shekara ta huɗu, a watan zif. 38 Cikin shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul wato wata na takwas a ka gama gidan, yadda a ke so tsarinsa ya kasance duka. Suleman ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.

Sura 7

1 Suleman ya ɗauki shekaru goma sha uku yana ginin fadarsa. 2 Ya gina fada ta jejin Lebanon. Tsawonta kamu ɗari ne, faɗinta hamsin ratarta kuma kamu talatin ne. Fadar an gina ta layi huɗu da ginshiƙai na sida da kalankuwa a kan ginshiƙan. 3 An rufe gidan da sida wanda ya kwanta a kan kalankuwoyin. Kalankuwoyin kuma ginshiƙai sun tallabe su. 4 Akwai kalankuwoyi arba'in da biyar, kowanne layi yana da goma sha biyar. Akwai kalankuwoyi a layuka uku. 5 Tagogin kuma suna duban junansu a layuka uku, dukkan ƙofofin tsawo da fãɗi bai ɗaya ne an yi masu kalankuwoyi kuma suna duban junansu layi uku. 6 Akwai baranda mai tsawon kamu hamsin faɗinta kuma kamu talatin, a gaba an yi kwararo mai ginshiƙai da rufi. 7 Suleman ya yi ɗakin kursiyinsa inda zai riƙa yin hukunci, wato ɗakin shari'ar adalci. An rufe dukkan daɓen shi da sida. 8 Gidan da Suleman zai zauna kuma yana wani ɓangare na fãdar, an gina shi kamar yadda a ka gina ɗakin shari'ar. Ya yi wani gida kamar haka saboda ɗiyar Fir'auna wadda ya ɗauko ta zama matarsa. 9 Gine-ginen an yi masu ado da duwatsu masu tsada waɗanda a ka sassaƙa su dai-dai a ka goge su a kowanne gefe. An yi amfani da duwatsun tun daga tushen ginin har zuwa sama, a waje kuma har zuwa babban ɗakin shari'a. 10 An kafa tushen gidan da manyan duwatsu masu tsada ratar su kamu takwas ne zuwa goma. 11 A sama an yi ado da duwatsu masu tsada waɗanda a ka sassaƙo su dai-dai wa daida, kuma da kalankuwa ta sida. 12 Katafaren ɗakin taron da ya kewaye fadar ya na da layuka uku na sassaƙaƙƙen dutse da kalankuwa ta sida kamar wanda ya ke cikin haikalin Yahweh da wurin shan iskarsa. 13 Sarki Suleman ya aika a ka kawo Huram daga Taya. 14 Huram ɗan wata gwauruwa ne ta kabilar Naftali, babansa kuma mutumin Taya ne, shi gwani ne a aikin tagulla. Huram yana cike da hikima da fasaha da basirar yin babban aiki da tagulla. Ya zo wurin sarki Suleman domin ya yi wa sarki aikin tagulla. 15 Huram ya tsara ginshiƙai biyu na tagulla kowanne tsawonsa kamu goma sha takwas ne kaurinsu kuma kamu goma sha biyu. 16 Ya kuma yi zankaye biyu da za a sa a kan kowanne ginshiƙi. Tsawon kowanne zanko kamu biyar ne. 17 Ya yi aikin raga da sarƙa ya yi wa zankayen ado don a sa su can saman ginshiƙan, guda bakwai ya yi domin kowanne zanko. 18 Haka Huram ya yi layika biyu na tagulla kewaye da ginshiƙan ya yi wa zankayensu ado. 19 Zankayen da ke kan ginshiƙan wurin shan iskar ya yi masu ado da furanni, kowanne fure, tsawonsa kamu huɗu. 20 Zankayen da ke kan ginshiƙan nan biyu, an yi masu 'yan kwararo-kwararo guda ɗari biyu kewaye da su a can ƙoli. 21 Ya ɗaga ginshiƙan wurin shan iska na haikali. Ginshiƙi na hannun dama ya ba shi suna Yakin, ginshiƙi na hannun hagu kuma ya ba shi suna Bo'aza. 22 A bisa ginshiƙan akwai ado mai kama da furanni. Haka aka tsara ginshiƙan. 23 Huram ya yi wani teku na zubi, kamu goma daga wannan gefe zuwa wancan. Tsawonsa kamu biyar ne, kewayensa kuma talatin. 24 A ƙarƙashin tekun na zubi ya yi butoci kamu goma, ya yi su lokacin da ya ke yin tekun na zubi ya yi su tare. 25 Ya ɗora tekun a bisa bijimai goma sha biyu, uku suna duban arewa, uku suna duban yamma, uku suna duban kudu, uku kuma suna duban gabas. aka ɗora "Tekun" a kansu, dukkan su cibiyoyinsu suna daga ciki. 26 Kaurin tekun kamar tafin hannu ya ke, an yi masa baki kamar na ƙoƙo, kamar fure ya na sheƙi. Tekun ya na ɗaukar ruwa garwa dubu biyu. 27 Huram ya yi diraku goma na tagulla. Ratar kowacce dirka kamu huɗu ne, faɗinta ma kamu huɗu, tsawonta kuma kamu uku. 28 Aikin dirakun shi ne, suna da mahaɗai a tsakaninsu, 29 kan dirakun da mahaɗarsu akwai zakuna da bijimai da kerubim. A saman zakunan da bijiman akwai zãnen furanni. 30 Kowacce dirka ta na da ƙafafu huɗu na tagulla, kusurwoyinta huɗu suna da matokarai saboda bangajin. Matokaran an yi su da zanen furanni a gefen kowacce ɗaya. 31 Bakinsu buɗe ya ke kamar kwano, faɗinsa kamu ɗaya da rabi ne, yana da kambi kamu ɗaya. A bakin su akwai zane-zane, kuma gefensu yana da tsawo da fãɗa bai ɗaya ba zagayayye ya ke ba. 32 Ƙafafunsu huɗu suna daga ƙarƙashinsu, abin da ya riƙe su kuma yana cikin dirkar. Tsayin gargaren kamu ɗaya da rabi ne. 33 Ƙafafunsu gargare kama da gargaren karusa. Abubuwan da suke riƙe da su da wayoyinsu ƙarfe ne na zubi. 34 An yi wurin kamawa huɗu ga kowacce dirka waɗanda suke liƙe a jikinsu. 35 a kan kowacce dirka an yi kambi rabin zurfinsa rabin kamu. Saman inda ta tsaya da gefenta haɗe su ke. 36 Jikin matokaran da gefensu, Huram ya zana zakuna da kerubim da ganyen dabino ya rufe inda ƙofofi suke ya zagaye su da furanni. 37 Yadda ya yi matokaran dukkan su zubinsu iri ɗaya ne girman su da tsarin su dukka ɗaya ne. 38 Huram ya yi bangazai goma, kowannen su zai ɗauki ruwa garwa goma. Kowanne bangaji kamu huɗu ne kuma ya sa bangaji ɗaya a bisa matokaran su goma. 39 Ya yi matokarai biyar daga kudu suna fuskantar haikalin, biyar kuma daga arewa su masu na fuskantar haikalin. Ya sa "Tekun" a kusurwar gabas, yana fuskantar kudu da haikalin. 40 Huram ya yi bangazai da moɗa da tasoshin yayyafawa. Daga nan ya gama dukkan aikin da zai yi wa Sarki Suleman cikin haikalin Yahweh. 41 Ginshiƙan biyu suna kama da zankayen da suke kan waɗancan ginshiƙan guda biyu. Ya yi zane guda biyu kamar tasoshi ya sa su domin su yi wa zankayen ado. 42 Ya yi zãne-zãne ɗari huɗu saboda sahu biyu na kayan adon da ya yi (layi biyu na zãne-zãne domin su rufe zankayen da suke a kan ginshiƙan guda biyu da); 43 matokaran su goma da bangajin nan guda goma na bisa matokaran. 44 Ya yi tekun da bajiman nan goma sha biyu da ke ƙarƙashinsa; 45 da tukwanen da moɗayen da bangazayen da dukkan sauran kayan aikin. Huram ya yi wa Sarki Suleman, su saboda haikalin Yahweh. 46 Sarki ya sa a zuba su filin Yodan a ƙasar yumɓu da ke tsakanin Sokot da Zaretan. 47 Suleman bai auna kayan aikin ba domin yawansu ya fi gaban aunawa, nauyin tagullar kuma ba za a iya auna su ba. 48 Dukkan kayan da ke cikin haikalin Yahweh Suleman ya yi su da zinariya: bagadi na zinariya da teburi wanda za a ajiye keɓaɓɓiyar gurasa. 49 Sandunan ajiye fitilu, biyar a hannun dama biyar kuma a hannun hagu, a gaba cikin ɗaki na can ciki an yi su da zinariya tsantsa da furannin da fitilun da yatsun dukka na zinariya ne. 50 ‌Kofinan da abubuwan kashe fitila da cokula da bangazaye da abubuwan ƙona turare dukka an yi su da zinariya tsantsa. Sakatu na ɗaki na can ciki wato wuri mafi tsarki da ƙofofin babban ɗakin taro na haikali dukka da zinariya aka yi su. 51 Da haka aka gama dukkan aikin da Sarki Suleman ya yi domin gidan Yahweh. Sai Suleman ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dauda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayan ɗaki ya sa su a cikin ɗakin ajiya a gidan Yahweh.

Sura 8

1 Sa'an nan Suleman ya tattara dukkan dattawan Isra'ila da shugabannin kabilu da shugabannin iyalai na mutanen Isra'ila a gabansa a Yerusalem, domin ya kawo akwatin alƙawarin Yahweh daga birnin Dauda wato Sihiyona. 2 Dukkan jama'ar Isra'ila suka taru a gaban Suleman a wurin liyafar, a cikin watan Itanim, wato wata na bakwai. 3 Dukkan dattawan Isra'ila da firistoci suka ɗauki akwatin. 4 Suka kawo akwatin Yahweh da rumfar taruwa da dukkan kaya masu tsarki da suke cikin rumfar. Firistoci da Lebiyawa ne suka kawo waɗannan kaya. 5 Sarki Suleman tare da dukkan taron Isra'ila suka zo gaban akwatin, suna miƙa hadayar tumaki da bijimai waɗanda ba su ƙidayuwa. 6 Firistoci suka kawo akwati na alƙawarin Yahweh suka sa shi a wurinsa, cikin ɗaki na can cikin gidan, wato wuri mafi tsarki a ƙarƙashin fukafukan kerubim. 7 Gama fukafukan kerubim ɗin sun kai wurin da akwatin ya ke, kuma sun rufe akwatin tare da sandunan da a ke ɗaukar sa. 8 Sandunan suna da tsawo sosai har ana iya ganin su daga wuri mafi tsarki a gaban ɗaki na can ciki, amma ba za a iya ganin su daga waje ba. Suna nan har zuwa yau. 9 Babu kome a cikin akwatin sai dai allunan nan na dutse da Musa ya sa ciki a Horeb, sa'ad da Yahweh ya yi alƙawari da mutanen Isra'ila lokacin da suka fito daga ƙasar Masar. 10 Ya zama lokacin da firistocin suka fito daga wuri mai tsarki sai girgije ya cika haikalin Yahweh. 11 Firistoci ba su iya tsayawa su yi hidima ba saboda girgijen. Gama darajar Yahweh ta cika gidansa. 12 Sa'an nan Suleman yace, "Yahweh ya ce zai zauna a cikin baƙin duhu, 13 Amma na gina maka wuri mai ƙawa, wurin da za ka zauna har abada." 14 Sa'an nan sarki ya juya ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka sa'ad da jama'ar Isra'ila suke a tsaye. 15 Ya ce, "Bari a yi yabo ga Yahweh Allah na Isra'ila wanda ya yi magana da mahaifina Dauda, kuma ya cika da hannunsa, cewa, 16 'Tun ranar da na kawo Isra'ila jama'ata daga Masar, ban zaɓi birni da zan gina gida domin in sa sunana a ciki ba. Na dai zaɓi Dauda ya yi mulkin jama'ata Isra'ila. 17 Yana dai cikin zuciyar Dauda mahaifina ya gina gida domin Yahweh Allah na Isra'ila. 18 Amma Yahweh ya ce da Dauda mahaifina, 'Ya yi kyau da ka ke da tunani a zucyarka domin ka gina ma ni gida. 19 Duk da haka ba za ka gina gidan ba, sai dai ɗanka wanda za a haifa ma ka shi ne zai gina gida domin sunana.' 20 Yahweh ya cika maganar da ya faɗi gama na taso a matsayin mahaifina Dauda, kuma ina zaune a kan kursiyi na mulkin Isra'ila kamar yadda Yahweh ya yi alƙawari. Na gina gida domin sunan Yahweh Allah na Isra'ila. 21 Na yi wa akwati wuri wanda a cikin sa alƙawarin Yahweh ya ke, wanda ya yi wa ubanninmu lokacin da ya fito da su daga ƙasar Masar." 22 Suleman ya tsaya a gaban akwatin Yahweh, gaban taron jama'ar Isra'ila ya buɗe hannuwansa zuwa sama. 23 Ya ce, "Yahweh, Allah na Isra'ila, babu wani Allah kamar ka a bisa cikin sama ko a nan ƙasa wanda ke riƙe alƙawarinsa da aminci zuwa ga bayinka waɗanda suke tafiya a gabanka da dukkan zuciyarsu; 24 kai wanda ya riƙe alƙawarin da ka yi wa bawanka Dauda mahaifina. I, ka faɗi da bakinka kuma ka cika da hannunka, kamar yadda ya ke a yau. 25 To yanzu dai, Yahweh, Allah na Isra'ila, ka cika alƙawarin da ka yi wa bawanka mahaifina Dauda, sa'ad da ka ce, 'Ba za ka rasa mutum wanda zai zauna a bisa kursiyin Isra'ila ba, idan dai zuriyarka za su yi hankali su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi tafiya a gabana.' 26 To yanzu dai Allah na Isra'ila, ina roƙon alƙawarin da ka yi wa bawanka Dauda mahaifina, ya zama gaske. 27 Amma gaskiya ne Allah zai zauna a ƙasa? Da ya ke dukkan duniya da sama ba za su iya riƙe ka ba, balle fa wannan haikalin da na gina! 28 Duk da haka, Yahweh, Allahna, ka yarda da wannan addu'a da roƙo na bawanka; ka saurari kuka da addu'ar da bawanka ya yi a gabanka yau. 29 Bari idanunka su zama a buɗe zuwa wannan haikali dare da rana, wanda ka yi magana a kansa cewa, 'Sunana da kasancewata za su zauna a can'- domin ka ji addu'o'in da bawanka zai yi a wurin nan. 30 Ka ji roƙon bawanka da na jama'ar Isra'ila sa'ad da muke yin addu'a a wannan wuri. I, ka ji daga wurin da ka ke, daga sama, kuma sa'ad da ka ji, ka yi gafara. 31 Idan wani mutum ya yi wa maƙwabcinsa zunubi, aka nemi da ya rantse da alƙawari, idan ya zo ya yi rantsuwa da alƙawari a gaban bagadinka a wannan gida, 32 ka ji daga sama ka yi wa bayinka hukunci, ka hukunta mai laifi ka sa abin da ya yi ya koma kansa, ka baratar da mai adalci ka yi masa sakamako saboda adalcinsa. 33 Idan abokin gãba ya yi nasara a kan bayinka jama'ar Isra'ila saboda suka yi maka zunubi, idan sun juyo sun kira sunanka a wnnan haikali, suka yi addu'a suka roƙi gafara - 34 idan ka yarda, ka ji daga sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila; ka dawo da su ƙasar da ka bayar ga kakanninsu. 35 Idan sama ta rufe babu ruwa, saboda mutanenka sun yi ma ka zunubi - idan su ka yi addu'a su na fuskantar wannan wuri, su ka kira sunanka kuma su ka juwo daga zunubinsu, bayan ka wahalshe su - 36 sai ka ji daga sama ka gafarta zunubin bayinka da na mutanen Isra'ila, sa'ad da ka koya masu hanyoyi masu kyau da ya kamata su bi. Ka aiko da ruwa a ƙasar da ka ba mutanenka gãdo. 37 A misali yunwa ta zo ƙasar ko cuta ko annobar gonaki ko cutar fatar jiki, ko fãri ko tsutsotsi, a misali kuma a ce abokin găba zai kawo hari a ƙasarsu, ko annoba ko wani ciwo - 38 A misali kuma wani ya yi addu'a ko roƙo ko dukkan jama'arka Isra'ila - kowanne ɗayansu yana sane da annobar a cikin zuciyarsa, idan suka tada hannuwansu zuwa wannan haikali. 39 Sai ka ji daga sama inda ka ke zaune, ka yi gafara kuma ka sãka wa kowanne mutum bisa ga dukkan abin da ya yi; ka san zucyarsa saboda kai kaɗai ne ka san dukkan zukatan mutane. 40 Yi haka domin su ji tsoron ka muddin suna zaune a ƙasar da ka bayar ga kakanninmu. 41 Har yanzu, game da baƙo wanda ba na cikin jama'arka Isra'ila ba ne: idan ya zo daga wuri mai nisa saboda sunanka - 42 gama za su ji labarin sunanka mai girma da hannunka mai iko da hannunka wanda ka tayar, idan ya yi addu'a yana fuskantar wannan haikali, 43 idan ka yarda, ka ji daga sama inda ka ke zaune, ka yi bisa ga abin da baƙon ya roƙe ka. Ka yi haka domin dukkan mutanen duniya su san ka su ji tsoron sunanka, kamar yadda jama'arka Isra'ila suke yi. Ka yi haka domin su san da sunanka a ke kiran wannan gida da na gina. 44 Idan jama'arka suka je yaƙi da abokan gaba, ta kowacce hanya ka aike su, Yahweh, idan suka yi addu'a suna fuskantar wannan birni wanda ka zaɓa da wannan gida da na gina domin sunanka. 45 Sai ka ji addu'arsu da roƙonsu daga sama ka yi taimako. 46 A misali idan suka yi maka zunubi, tun da ya ke ba wanda ba ya yin zunubi, a misali idan ka yi fushi da su, ka bashe su ga abokin găba, abokin găba ya kwashe su zuwa ƙasarsu, ko da nesa ko kusa. 47 A misali idan suka gane suna cikin ƙasar bauta, a misali idan suka tuba suka roƙi tagomashi a wurin ka daga ƙasar waɗanda suka bautar da su. A misali idan suka ce, 'Mun yi wauta mun yi zunubi. Mun yi aikin mugunta.' 48 Amisali idan suka juwo gare ka da dukkan zuciyarsu da dukkan ransu a cikin ƙasar abokan gãbarsu waɗanda suka kwashe su, idan suka yi addu'a suna fuskantar ƙasarsu, suna fuskantar birnin da ka zaɓa da wannan gida da na gina domin sunanka. 49 Sai ka ji addu'arsu da roƙonsu na neman taimako daga sama inda ka ke, ka dai-daita al'muransu. 50 Ka gafartawa mutanenka zunubin da suka yi maka da dukkan zunubansu da suka ƙetare dokokinka. Ka ji tausayin mutanenka a gaban abokan gãbarsu, domin abokan găbarsu su ji tausayin mutanenka. 51 Su mutanenka ne da ka zaɓa, waɗanda ka kuɓutar daga Masar kamar daga cikin tanderu inda a ke narkar da ƙarfe. 52 Ina roƙon idanunka su buɗe ga roƙon bawanka da roƙe-roƙen mutanenka Isra'ila, ka ji su daga ko'ina suka yi kuka gare ka. 53 Gama ka keɓe su daga dukkan mutanen duniya su zama na ka, su kuma karɓi alƙawuranka, Yahweh Ubangiji, kamar yadda ka bayyana ta wurin bawanka Musa sa'ad da ka kawo ubanninmu daga Masar, Ubangiji Yahweh." 54 Haka ya zama sa'ad da Suleman ya gama yin addu'a da dukkan roƙon da zai yi zuwa ga Yahweh, ya tashi daga gaban bagadin Yahweh, daga yin durƙusonsa a kan guiwoyinsa da ta da hannuwansa zuwa sama. 55 Ya miƙe ya sa wa dukkan taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, cewa, 56 yabo ga Yahweh wanda ya ba mutanensa Isra'ila hutawa, ya cika alƙawuransa. Ko kalma ɗaya ba a rasa ba cikin dukkan alƙawura masu kyau da Yahweh ya yi da bawansa Musa. 57 Yahweh ya kasance tare da mu, kamar yadda ya kasance tare da kakanninmu, kada ya bar mu ko ya yashe mu, 58 ya sa zuciyarmu ta manne masa, mu rayu cikin dokokinsa da ka'idodinsa da farillansa, waɗanda ya umurci ubanninmu. 59 Bari waɗannan maganganu da na faɗi, na yi roƙo ga Yahweh, su zauna a kusa da Yahweh Allahna, dare da rana, domin ya yi taimako cikin al'amuran bawansa da al'amuran jama'arsa Isra'ila a kowacce rana; 60 domin dukkan mutanen duniya su sani Yahweh shi ne Allah kuma ba bu wani Allah! 61 Saboda haka zuciyarku ta yi aminci ga Yahweh Allanmu, ku kiyaye farillansa da dokokinsa, kamar a yau." 62 Sai sarki tare da dukkan Isra'ila suka miƙa hadayu ga Yahweh. 63 Suleman ya miƙa baye-baye na zumunci waɗanda ya yi wa Yahweh: bijimai dubu ashirin da biyu da tumaki 120,000. Haka sarki da dukkan Isra'ila su ka keɓe gidan Yahweh. 64 A wannan ranar ne kuma sarki ya keɓe filin da ke tsakiya a gaban haikalin Yahweh. Gama a nan ne sarki ya miƙa baye-baye na ƙonawa, baye-baye na hatsi da kitsen baye-baye na zumunta, saboda bagadin da ya ke gaban Yahweh bai kai girman da zai ɗauki baikon ba, wato baye-baye na hatsi da kitsen baye-baye na zumunta. 65 Haka sarki ya yi liyafa a wannan lokaci da dukkan Isra'ila tare da shi, babban taro. Tun daga Lebo Hamat har zuwa iyakar Masar, suna gaban Ubangiji Allah kwana bakwai da waɗansu kwana bakwai kuma, wato kwana goma sha huɗu kenan dukka. 66 A kan rana ta takwas ya sallami mutanen, suka sa wa sarki albarka kowanne ya tafi gidansa da murna da farinciki saboda abubuwa masu kyau waɗanda Yahweh ya yi wa Dauda bawansa, da Isra'ila, mutanensa.

Sura 9

1 Bayan da Suleman ya gama ginin gidan Yahweh da fădar sarki, kuma bayan da ya gama dukkan abubuwan da ya ke so ya yi, 2 Sai Yahweh ya bayyana ga Suleman sau na biyu, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibiyon. 3 Daga nan Yahweh ya ce da shi, "Na ji addu'arka da roƙon da ka yi zuwa gare ni. Na keɓe wannan gida, wanda ka gina, domin kaina, in sa sunana a wurin. Idanuna da zuciyata za su kasance a wurin kowanne lokaci. 4 A gare ka kuma, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dauda mahaifinka ya yi cikin aminci da sahihancin zuciya, ka na yin biyayya ga dukkan abin da na ummurce ka ka na kiyaye farillaina da shari'una, 5 zan tabbatar da mulkinka a kan Isra'ila har abada, kamar yadda na yi wa Dauda mahaifinka alƙawari, cewa, 'Ba za a taɓa rasa zuriyarka a kan kursiyin Isra'ila ba.' 6 Amma idan ka fanɗare, ko kai, ko 'ya'yanka, ba ku kiyaye dokokina da farillaina waɗanda na shimfiɗa a gabanka ba, idan ku ka je ku ka bauta wa waɗansu alloli ku ka russana masu, 7 zan kawar da Isra'ila daga ƙasar da na ba su, wannan gida kuma wanda na keɓe domin sunana, zan kawar da fuskata daga gare shi, Isra'ila kuma za su zama misali da abin ba'a da abin raini ga dukkan mutane. 8 Wannan haikali kuma zai zama tarin juji, dukkan wanda ya wuce ta kusa da shi zai kaɗu ya yi ajiyar zuciya. Zai yi tambaya haka, 'Me ya sa Yahweh ya yi haka ga wannan ƙasa da wannan gida?' 9 Waɗansu za su amsa da cewa, 'Saboda sun watsar da Yahweh Allahnsu, wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, sun koma ga waɗansu alloli sun russana masu sun yi masu sujada. Shi ya sa Yahweh ya auko masu da wannan masifar.'" 10 Ya zama shekaru ashirin bayan da Suleman ya gama gine-ginen nan biyu, wato haikalin Yahweh da fãdar sarki. 11 Hiram sarkin Taya ya tanadawa Suleman sida da itatuwan fir da zinariya da dukkan abin da Suleman ya bukata-sai sarki Suleman ya ba shi birane ashirin cikin ƙasar Galili. 12 Sai Hiram ya zo daga Taya domin ya ga biranen da Suleman ya ba shi, amma ba su gamshe shi ba. 13 Hiram yace, "Waɗanne irin birane ne waɗannan da ka ba ni, ɗan'uwana?" Hiram ya ce da su ƙasar Kabul, haka a ke kiran su har yau. 14 Dã ma Hiram ya aika wa sarki zinariya awo 120. 15 Wannan shi ne dalilin aikin dole wanda sarki Suleman ya sa a yi: wato a gina haikalin Yahweh da fãdarsa, kuma a gina Millo da garun Yerusalem da kuma kariya ta Hazor da Maggido da Gezer. 16 Fir'auna sarkin Masar ya je ya kama Gezer. Ya ƙone ta ya karkashe Kan'aniyawan cikin birnin. Sai Fir'auna ya ba ɗiyarsa matar Suleman, biranen a matsayin kyautar aure. 17 Haka Suleman ya sake gina Gezer da Bet Horon ta gangare, 18 da Ba'alat da Tamar a ƙasar Yahuda cikin jeji, 19 da biranen da ya ke da su na ajiya da na karusansa da na mahaya dawakinsa da dukkan abin da ya yi sha'awar ginawa a Yerusalem domin jin daɗinsa a Lebanon da dukkan ƙasashen da su ke ƙarƙashin mulkinsa. 20 Game da mutanen da su ka rage na wajen Amoriyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Hiwiyawa da Yebusiyawa waɗanda ba sa cikin mutanen Isra'ila ba, 21 da zuriyarsu waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakawa duka ba, Suleman ya sa su ka zama masu aikin tilas haka kuwa su ke har yau. 22 Amma Suleman bai sa mutanen Isra'ila aikin tilas ba. Maimakon haka sai ya sa suka zama sojojinsa da bayinsa da jami'ansa da jami'an karusansa da mahaya dawakinsa. 23 Suleman ya na da jami'ai masu hidimar lura da masu duba aiki, yawan su shi ne 550, su ne suke lura da mutanen da suke yin aiki. 24 Ɗiyar Fir'auna ta tashi daga birnin Dauda ta koma gidan da Suleman da ya gina mata, sa'an nan Suleman ya gina Millo. 25 A shekara sau uku Suleman ya ke miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a kan bagadin da ya gina wa Yahweh, a gaban Yahweh ya ke ƙona su da turare. Ya gama haikalin yanzu yana amfani da shi. 26 Sarki Suleman kuma ya yi tashar jiragen ruwa a Eziyon Geber wadda ta ke kusa da Elat a bakin Jan Teku a ƙasar Idom. 27 Hiram ya aiko bayinsa zuwa tashar Suleman, masu tuƙin jirgi waɗanda suka saba da teku tare da bayin Suleman. 28 Suka je Ofir da bayin Suleman. Suka kawowa Suleman zinariya awo 420 daga can.

Sura 10

1 Sa'ad da sarauniyar Sheba ta ji labarin Suleman ya zama sananne game da sunan Yahweh, sai ta zo ta gwada shi da tambayoyi masu wuya. 2 Ta zo Yerusalem da raƙuma da yawa, da raƙuman da aka ɗorowa kayan yaji da zinariya mai yawa da duwatsu masu daraja da yawa. Sa'ad da ta zo sai ta gayawa Suleman dukkan abin da ke cikin zuciyarta. 3 Suleman ya amsa dukkan tambayoyinta. Ba wani abu da ta tambaya wanda Suleman bai ba da amsarsa ba. 4 Sa'ad da sarauniyar Sheba ta ga dukkan hikimar Suleman da fãdar da ya gina, 5 da abincin da ke kan teburinsa da wurin da bayinsa suke zama da ayyukan da bayinsa suke yi da tufafinsu, da masu yi ma sa hidima da yadda ya ke miƙa baye-baye na ƙonawa, sai ta zama ba ta da sauran ƙarfi. 6 Ta ce da sarki, "Rahoton da na ji a ƙasata game da maganarka da hikimarka gaskiya ne. 7 Ban gaskata da abin da na ji ba sai da na zo nan, yanzu idanuna sun gani. Ko rabin hikimarka da wadatarka ma ba a gaya mani ba! Sunanka ya wuce abin da na ji. 8 Matanka masu albarka ne, bayinka waɗanda suke tsayawa a gabanka kullum, masu albarka ne saboda suna jin hikimarka. 9 Yabo ga Yahweh Allahnka wanda ya yi farinciki da kai ya sa ka a bisa kursiyin Isra'ila. Saboda Yahweh ya ƙaunaci Isra'ila har abada ya sa ka zama sarki domin ka yi masu hukunci da adalci!" 10 Ta ba sarki awo 120 na zinariya da kayan yaji da yawa da duwatsu masu daraja. Ba a ƙara ba sarki Suleman kayan yaji masu yawa fiye da wanda sarauniyar Sheba ta ba shi ba. 11 Jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, daga Ofir ɗin kuma sun kawo itacen almug mai yawa da duwatsu masu daraja. 12 Sarkin ya yi ginshiƙai na itacen almug a haikalin Yahweh da fãdar sarki, kuma ya yi wa mawaƙa molaye da girayu. Ba a ƙara ganin itacen almug da yawa haka ba har zuwa yau. 13 Sarki Suleman ya ba sarauniyar Sheba dukkan abin da ta nuna sha'awa a kai da dukkan abin da ta roƙa, ƙari a kan kyautar da ya riga ya ba ta saboda karamci. Sai ta koma ƙasarta tare da bayinta. 14 Nauyin zinariyar da ta zo wa Suleman a cikin shekara ɗaya awo 666 ne, 15 ban da zinariyar da "yan kasuwa da fatake suka kawo. Dukkan sarakunan Arebiya da hakiman ƙasar masu ka kawo wa Suleman zinariya da azurfa. 16 Sarki Suleman ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na gogaggiyar zinariya. Kowaccen su an yi ta da awo ɗari shida na zinariya. 17 Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi ɗari uku na gogaggiyar zinariya, awon zinariya uku suka shiga kowacce garkuwa; sarki ya sa su can cikin fadar da ta ke a jejin Lebanon. 18 Kuma sarki ya yi wani babban dakalin mulki na hauren giwa ya shafe shi da zinariya mafi kyau. 19 Dakalin yana da matakalai shida, bayan shi kuma shan ƙwai ne a can sama. Kowannen su yana da wurin ajiye hannu a gefe, akwai zakuna biyu a tsaye gefen wurin ajiye hannun. 20 Zakuna goma sha biyu suna tsaye a kan matakalun, ɗaya a kan kowacce matakala. Babu wata masarautar da take da dakali kamar sa. 21 Dukkan kofinan sha na sarki Suleman na zinariya ne, dukkan kofinan sha da suke fãdar da ke cikin jejin Lebanon na zinariya ne tsantsa. Ba na azurfa ko ɗaya domin a zamanin Suleman azurfa ba ta da daraja. 22 Sarki ya na da jiragen ruwa masu yawo a kan teku, tare da jiragen Hiram. Sau ɗaya a cikin shekara uku jiragen ruwan sukan kawo zinariya da azurfa da hauren giwa da buka da ɗawisu masu daraja. 23 Sarki Suleman ya fi dukkan sarakunan duniya arziki da hikima. 24 Kowa da kowa a duniya suna so su zo wurin Suleman domin su ji hikimar da Yahweh ya sa cikin zuciyarsa. 25 Waɗanda ke zuwa su na kawo haraji, na santulan azurfa da zinariya, da kayan sawa da sulke da kayan yaji da dawakai da alfadarai, shekara biye da shekara. 26 Suleman ya tara karusai da mahaya dawaki. Ya na da karusai 1400 da mahaya dawaki dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye su a biranen da a ka ajiye karusai shi kansa kuwa ya na cikin Yerusalem. 27 Sarki ya na da azurfa a Yerusalem kamar yawan duwatsun da suke a doron ƙasa. Yana da itatuwan sida da yawa kamar yadda itatuwan ɓaure suke a cikin fadama. 28 Suleman ya na da dawakai da aka kawo daga Masar da Kilikiya. Abokan cinikin sarki sukan saye su garke-garke kowanne garke bisa ga farashinsa. 29 Akan sayo karusai daga Masar kowacce akan awo ɗari shida na azurfa, dawaki kuma akan 150 kowanne. Akan sayar da wasu da yawa daga cikin su ga sarakunan Hittiyawa da Siriya.

Sura 11

1 Yanzu sarki Suleman ya kaunaci baƙin mata: ɗiyar Fir'auna, da matan Mowabawa, da Ammonawa da Idomawa da Sidoniyawa da Hittiyawa. 2 Su na daga al'ummai waɗanda Yahweh ya ce da mutanen Isra'ila, "Ba za ku shiga cikinsu ba da aure, ko su zo cikinku, domin lallai za su juyar da zukatanku ga allolinsu." Amma duk da wannan Suleman kuwa ya ƙaunaci waɗannan mata. 3 Suleman ya na da gimbiyoyin mata ɗari bakwai da kuma ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matayensa su ka juyar da zuciyarsa. 4 Gama sa'ad da Suleman ya tsufa, sai matansa su ka juyar da zuciyarsa zuwa bin wasu alloli; bai miƙa dukkan zuciyarsa ga Yahweh Allahnsa ba, kamar zuciyar Dauda mahaifinsa. 5 Gama Suleman ya bi Ashtoret, gunkin Sidoniyawa, ya kuma bi Molek, wato gunkin Ammonawa. 6 Suleman ya yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh; bai bi Yahweh da zuciya ɗaya ba, ba kamar yadda mahaifinsa Dauda ya yi ba. 7 Sai Suleman ya gina masujadai domin Kemosh, kyamattacen gunkin Mowab, akan dutsen gabashin Yerusalem, da kuma domin Molek, da kyamataccen gunkin mutanen Amonawa. 8 Ya kuma gina masujadai domin dukkan baƙin mata, waɗanda su ke ƙona turare da hadayu ga allolinsu. 9 Yahweh kuwa ya yi fushi da Suleman, domin zuciyarsa ta rabu daga gare shi, Allah na Isra'ila, ko da ya ke ya bayyana a gare shi sau biyu, 10 ya kuma umarce shi akan wannan abu, da kada ya bi wasu allolin. Amma bai yi biyayya da wannan umarni na Yahweh ba. 11 Saboda haka Yahweh ya ce da Suleman, "Domin ka yi wannan ka kuma ƙi kiyaye alƙawari da ka'idodina waɗanda na umarceka, hakika zan tsaga mulkin daga gare ka in ba baranka. 12 Amma, saboda mahaifinka Dauda, ba zan yi ba a lokacin rayuwarka, amma zan tsaga ta daga hannun ɗanka. 13 Duk da haka ba zan ƙwace dukkan mulkin ba, zan ba kabila ɗaya ga ɗanka, saboda bawana Dauda, don kuma Yerusalem, wanda na zaɓa." 14 Sai Yahweh ya ta da abokin gãba ga Suleman, Hadad Ba'idome. Shi kuma daga iyalin sarautar Idom ne. 15 Gama sa'ad da Dauda yana cikin Idom, Yowab shugaban sojoji ya tafi don ya bizne matattu, kowanne mutum wanda aka kashe a Idom. 16 Yowab da dukkan Isra'ila su ka tsaya a Idom wata shida har sai da ya kashe mazajen Idom. 17 Amma an ɗauki Hadad tare da wasu Idomawa ta wurin bayin mahaifinsa zuwa Masar, tun lokacin da Hadad yana karamin yaro. 18 Su ka bar Madayana su ka zo Faran, daga nan su ka ɗauki mutane tare da su zuwa Masar, wurin Fir'auna sarkin Masar, wanda ya ba shi gida da kuma ƙasa da abinci. 19 Hadad kuwa ya sami tagomashi ƙwarai a fuskar Fir'auna, saboda haka Fir'auna ya bashi mata, ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes sarauniya. 20 'Yar'uwar Tafenes ta haifa wa Hadad ɗa. Suka sa masa suna Genubat. Tafenes ta yi renon sa a fadar. Genubat ya zauna a fadar Fir'auna a cikin yaran Fir'auna. 21 A lokacin da ya ke a Masar, Hadad ya ji labari Dauda ya rasu aka kuma rufe shi tare da kakanninsa, Yowab shugaban sojoji kuma ya mutu, sai Hadad ya cewa Fir'auna, "Ka yardar mani in tashi, in koma ƙasata." 22 Sai Fir'auna ya ce masa, "Amma me ka rasa a nan har da ka ke neman komawa ƙasarka?" Hadad ya amsa, "Ba bu kome, idan ka yarda bar ni in koma. 23 Allah kuma ya ta da wani abokin gãba ga Suleman, Rezon ɗan Eliyada, wanda ya zo daga wurin maigidansa Hadadezar sarkin Zobah. 24 Rezon ya tattaro wa kansa mutane har ya zama shugaba akan kananan mayaƙa, bayan da Dauda ya ci nasara akan mutanen Zobah. Rezo ya mulki Damaskus. 25 Ya zama abokin gãbar Isra'ila dukkan kwanakin Suleman, tare da wahalar da Hadad ya kawo. Rezon ya ƙi mutanen Isra'ila ƙwarai, ya yi mulkin Aram. 26 Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zeredan, ma'aikacin Suleman ne, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki. 27 Dalilin da ya sa ya tayar wa sarki shi ne domin Suleman ya gina masujada a Millo ya kuma gyara garun birnin Dauda mahaifinsa. 28 Yerobowam ƙaƙƙarfan mutum mai fasaha. Suleman ya ga saurayi ne mai himma, sai ya sa shi shugabanci akan dukkan aikin gidan Yosef. 29 A wanan lokacin, sai Yerobowam ya fita daga Yerusalem, annabi Ahijah mutumin Shilo ya same shi a hanya. 30 Yanzu kuwa Ahijah ya na saye da sabuwar riga tare da mutune biyu kaɗai a filin. Sai Ahijah ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa kashi goma sha biyu. 31 Ya cewa Yerobowam, "Ɗauki kyalle goma, gama haka Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗa, 'Duba, zan yaga mulkin daga hannun Suleman zan kuma ba da kabilu goma a gare ka 32 (amma Suleman zai sami kabila ɗaya, saboda bawana Dauda, ɗaya kuma saboda Yerusalem - birnin da na zaɓa daga cikin dukkan kabilan Isra'ila), 33 domin sun rabu da ni su na bauta wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, Kemosh allahn Mowab, da Milkon allahn mutanen Ammonawa. Ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ko su yi abin da ke dai-dai a idanuna da kiyaye dokokina da ka'idodina, kamar yadda Dauda mahaifinsa ya yi. 34 Duk da haka ba zan ɗauke dukkan mulkin daga hannun Suleman ba. A maimakon haka zan sa shi ya yi mulki dukkan kwanakin rayuwarsa, saboda bawana Dauda wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnina da dokokina. 35 Amma zan ɗauke mulkin daga hannun ɗansa, zan ba da shi gare ka, kabilu goma. 36 Zan ba da kabila ɗaya ga ɗan Suleman, saboda bawana Dauda wanda kullum yana riƙe fitila a gabana a Yerusalem, birnin da na zaɓa in sa sunana. 37 Zan ɗauke ka, za ka yi mulki ka cika dukkan buƙatarka, kuma za ka zama sarki akan Isra'ila, 38 Idan za ka saurari dukkan abin da zan umarce ka, idan kuma ka bi hanyata ka yi abin da ke dai-dai a idanuna, ka kiyaye dokokina da umarnina, kamar yadda Dauda bawana ya yi, sai in kasance tare da kai zan sa gidanka ya kahu, kamar yadda na sa gidan Dauda, zan ba da Isra'ila a gare ka. 39 Zan hori zuriyar Dauda, amma ba har abada ba." 40 Suleman kuwa ya yi ƙoƙarin kashe Yerobowam. Amma Yerobowam ya tashi ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak sarkin Masar, ya zauna a can har mutuwar Suleman. 41 Kamar sauran abubuwa game da Suleman, dukkan abin da ya yi da hikimarsa ba a rubuta su a littafin ayyukan Suleman ba? 42 Suleman ya yi mulki a Yerusalem akan dukkan Isra'ila har shekaru arba'in. 43 Ya mutu tare da kakaninsa kuma aka bizne shi a birnin Dauda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa.

Sura 12

1 Rehobowam ya tafi Shekem, domin dukkan Isra'ila sun tafi Shekem su maida shi sarki. 2 Ya zamana sa'ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (domin shi yana Masar, inda, ya gudu daga gaban sarki Suleman), don Yerobowam ya na zaune a Masar.

3 Sai su ka aika a kirawo shi, Yerobowam tare da dukkan taron mutanen Isra'ila suka zo suka ce da Rehobowam, 4 '"Mahaifinka ya nawaita mana. Yanzu sai ka rage mana wahalar aikin da tsohonka ya nawaita a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka." 5 Yerobowam ya ce da su, "Ku tafi har nan da kwana uku, sai bayan kwana uku ku dawo wuri na." Sai mutanen su ka tafi. 6 Sarki Rehobowam kuwa ya yi shawara tare da dattawa waɗanda suka tsaya tare da Suleman mahaifinsa a lokacin da ya ke da rai, sai ya ce masu, "Wacce shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?" 7 Su ka yi magana da shi, suka ce, "Idan za ka zama bara yau ga waɗannan mutane sai ka bauta masu, ka kuma amsa masu da magana mai kyau, su kuwa kullum za su zama barorinka." 8 Amma Rehobowam ya yi watsi da shawarar da dattawan mutanen su ka ba shi, sai ya yi shawara tare da matasan mutane waɗanda su ka yi girma tare da shi. 9 Ya ce masu, "Wacce shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka yi magana da ni cewa, 'Ka rage wahalar da tsohonka ya aza mana?'" 10 Matasan waɗanda su ka yi girma tare da Rehobowam su ka yi magana da shi, cewa, "Yi magana da mutanen nan waɗanda suka faɗa maka mahaifinka Suleman ya nawaita masu amma sai kai ka sauwaƙa masu. Sai ka ce da su, 'Karamin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri. 11 To yanzu, ko da mahaifina ya wahalar da ku da bauta, zan ƙara maku nawayar. Mahaifina ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.'" 12 Sai Yerobowom da dukkan mutane suka zo wurin Rehobowom a rana ta uku, kamar yadda sarki ya umarta a lokacin da ya ce, "Ku dawo wurina a rana ta uku." 13 Sarki ya amsa wa mutanen da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi. 14 Ya yi masu magana bisa ga shawarar matasa; ya ce, "Mahaifina ya nawaita maku, amma ni zan ƙara nawaita maku. mahaifina ya yi maku horo da bulala, amma ni zan yi maku da kunamai." 15 Haka nan kuwa sarki bai saurari mutanen ba, gama wannan al'amarin ya zama haka bisa ga shirin Yahweh, akan yadda zai cika maganar da ya faɗa ta wurin Ahijah Bashiloniye zuwa ga Yerobowom ɗan Nebat. 16 Sa'ad da dukkan mutane Isra'ila suka ga sarki bai saurare su ba, sai mutanen suka amsa masa suka ce, "Mene ne rabonmu da Dauda? Ba mu da gãdo a cikin ɗan Yesse! Ku tafi rumfunanku, Isra'ila. Yanzu ka duba gidanka, Dauda." Isra'ila suka koma rumfunansu. 17 Amma mutanen Isra'ila waɗanda suka zauna a biranen Yahuda, Rehobowom ya zama sarkinsu. 18 Sai sarki Rehobowom ya aiki Adoniram, wanda ya ke shi ne shugaban aikin tilas, amma dukkan Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowom da gaggawa ya hau karusarsa ya tsere zuwa Yerusalem. 19 Mutanen Isra'ila kuwa suka tayar wa gidan Dauda har zuwa wannan rana. 20 Ya zama haka dukkan Isra'ila suka ji Yerobowom ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron, suka naɗa shi sarki akan dukkan Isra'ila. Babu wanda ya bi iyalin Dauda, sai dai kabilar Yahuda. 21 Da Rehobowom ya komo Yerusalem, ya tara dukkan mutanen gidan Yahuda da kabilar Benyamin; suka kai mayaƙa 180,000 mutanen da aka zaɓa sojoji, da za su yi faɗa gãba da gidan Isra'ila, domin su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowom ɗan Suleman. 22 Amma maganar Allah ta zo ga Shemayya, mutumin Allah; ta ce, 23 "Faɗa wa Rehobowom ɗan Suleman, sarkin Yahuda, da Benyamin da sauran jama'a, ka ce, 24 "Yahweh ya ce wannan: Ba za ka yi yaƙi ko faɗa da 'yan'uwanku mutanen Isra'ila ba. Kowannenku ya koma gidansa, gama wannan al'amari ya faru ne daga gare ni.'" Sai suka saurari maganar Yahweh, suka juya suka koma hanyarsu, suka yi biyayya da maganarsa. 25 Sai Yerobowom ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraim, ya zauna a can. Ya fita daga can ya gina Feniyel. 26 Yerobowam kuwa ya yi tunani a cikin zuciyarsa, '"Yanzu mulki fa zai koma gidan Dauda. 27 Idan waɗannan mutanen suka ci gaba da miƙa hadiyu a haikalin Yahweh a Yerusalem, sai zuciyar waɗannan mutane su juya su yi gãba da maigidansu, Reroboam sarkin Yahuda. Za su kashe ni su koma wurin Rehobowom sarkin Yahuda." 28 Sai sarki Yerobowom ya nemi shawara ya siffanta 'yan maruka biyu da zinariya; ya cewa mutane, "Zai yi maku wuya don ku yi ta tafiya zuwa Yerusalem. Duba, ga waɗannan allolinku, ya Isra'ila, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar." 29 Ya sa siffar ɗaya a Betel ɗaya kuma a Dan. Wannan abu ya zama zunubi. 30 Mutane suka tafi wurin ɗaya ko ɗayan, dukka suka kama hanya zuwa Dan. 31 Yerobowom ya gina masujadai a tuddai, ya kuma sa firistoci a cikin dukkan mutanen, waɗanda ba 'ya'yan Lebi ba. 32 Yerobowom kuma ya sa a yi idi a watan takwas, ran goma sha biyar ga wata, kamar yadda ake yin idi a Yahuda, ya tafi bagadi. Ya yi kuma a Betel, hadayun siffofin maruƙan da ya yi a Betel ya sa firistoci a masujadan da ya gina. 33 Yerobowom ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, a watan ya shirya a tunaninsa; ya yi biki don mutanen Isra'ila ya kuma tafi bagade ya ƙona turare.

Sura 13

1 Mutumin Allah ya fito daga Yahuda ta wurin maganar Yahweh zuwa Betel. Yerobowom yana tsaye kusa da bagadin ƙona turare. 2 Ya yi kuka akan wannan mugunta ta bagadi ta wurin maganar Yahweh: "Bagadi, bagadi! Wannan shi ne abin da Yahweh ya fada, 'Duba, mai suna Yosiya za a haife shi a iyalin Dauda, da kai zan yi hadayun firistoci na masujadan tuddai waɗanda za su ƙona turare a kanka. A kanka kuma za su ƙona ƙasusuwan mutane.'" 3 Sai mutumin Allah ya ba da alamar ranar, cewa, "Wannan shi ne alamar da Yahweh ya yi magana: 'Duba, za a rushe bagadin, za a kuma watsar da tokar waje.'" 4 Da sarki ya ji abin da mutumin Allah ya ce, sai ya yi kuka akan bagadin da ya ke Betel, Yerobowam ya miƙa hannunsa daga bagadin, cewa, "Ku kama shi. "Sai hannun da ya miƙa akan mutumin ya bushe, domin bai iya komo da shi ba. 5 (Aka rushe bagadin aka kuma zubar da tokar bagadin, alamar da mutumin Allah ya ba da bisa ga maganar Yahweh.) 6 Sarki Yerobowom ya amsa ya ce da mutumin Allah, "Ka yi roƙo domin in sami tagomashi a wurin Yahweh Allahnka kuma ka yi addu'a domina, saboda ya warkar da hannuna." Mutumin Allah ya yi addu'a ga Yahweh, hannun sarki kuwa ya dawo gare shi kuma, dai-dai kamar yadda ya ke a dã. 7 Sarki ya ce da mutumin Allah, "Ka zo gida tare da ni ka shakata, zan ba ka lada." 8 Mutumin Allah kuwa ya ce da sarki, "Ko da za ka ba ni rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ko in ci abinci ko in sha ruwa a wannan wurin ba, 9 gama Yahweh ya umarce ni ta wurin maganarsa, 'Ba za ka ci gurasa ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo ba.'" 10 Haka kuwa mutumin Allah ya koma ta wata hanya dabam zuwa gidansa ba ta hanyar da ya zo Betel ba. 11 To akwai wani tsohon annabi wanda ke zaune a Betel, ɗaya daga cikin 'ya 'yansa maza ya tafi ya faɗa masa dukkan abubuwan da mutumin Allah ya yi a wannan rana a Betel. 'Ya'yansa kuwa suka faɗa wa mahaifinsu maganar da mutumin Allah ya faɗa wa sarki. 12 Mahaifinsu ya ce da su, "Wacce hanyar ya bi ya tafi?" 'Ya'yansa sun ga hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi ya tafi. 13 Ya ce da 'ya'yansa ku ɗaura wa jaki shimfiɗa domina." Sai suka ɗaura wa jaki shimfiɗa, shi kuwa ya hau ya tafi. 14 Tsohon annabin ya bi bayan mutumin Allah har ya same shi yana zama a ƙarƙashin itacen rimi; ya ce masa, "Kai ne mutumin Allahn nan da ya zo daga Yahuda?" Ya amsa, "I, ni ne." 15 Sai tsohon annabi ya ce da shi, "Zo gida tare da ni ka ci abinci." 16 Mutumin Allah ya amsa, ba zan koma tare da kai ba ko kuwa in shiga tare da kai, ko kuwa in ci abinci ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri, 17 gama umarni gare ni ta wurin maganar Yahweh, 'ba za ka ci wani abinci ko ka sha ruwa a wurin ba, ko ka koma ta hanyar da ka zo.'" 18 Sai tsohon annabin ya ce da shi, "Ai ni ma annabi ne kamar ka, mala'ika ya yi magana da ni ta wurin maganar Yahweh, cewa, 'Ka zo da shi tare da kai cikin gidanka, don ya ci abinci ya sha ruwa.'" Amma ƙarya ce tsohon annabin ya ke faɗa wa mutumin Allah. 19 Saboda haka sai mutumin Allah ya koma tare da tsohon annabi ya ci abinci ya kuma sha ruwa a gidansa. 20 Ya yin da suka zauna a tebur, sai maganar Yahweh ta zo ga annabi wanda ya komo da shi, 21 sai ya kira mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, cewa, "Yahweh ya ce, 'Domin ka yi rashin biyayya da maganar Yahweh, ba ka kuma kiyaye umarnin Yahweh Allahnka da ya ba ka ba, 22 amma ka komo ka ci abinci ka sha ruwa a wannan wurin wanda Yahweh ya faɗa ma ka kada ka ci abinci ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a bizne jikinka a kabarin ubanninka ba.'" 23 Bayan da ya ci abinci, ya kuma sha, sai annabin ya ɗaura wa jakin mutumin Allah sirdi, da kuma mutumin da ya komo tare da shi. 24 Sa'ad da mutumin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya ya kashe shi, ya bar gawar akan hanya. Sai jakin ya tsaya a gefenta, haka nan ma zaki ya tsaya kusa da gawar. 25 Sa'ad da mutane da ke wucewa ta wurin suka ga an yar da gawar akan hanya, zaki kuma ya tsaya a gefenta, suka zo suka faɗa a cikin birnin da tsohon annabi ya ke. 26 Sa'ad da annabi wanda ya komo da shi daga hanyar ya ji, sai ya ce, "Wannan mutumin Allah ne wanda bai yi biyayya da maganar Yahweh ba. Saboda haka Yahweh ya ba da shi ga zaki, wanda ya yayyage shi, ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Yahweh ta gargaɗe shi." 27 Sai tsohon annabi ya yi magana da 'ya 'yansa maza, cewa, "Ku ɗaura wa jakina sirdi," su kuma suka ɗaura wa jakin sirdi. 28 Ya tafi ya sami gawar an bar ta a hanya, jakin da zaki su na tsaye a gefen gawar. Zaki bai ci gawar ba, ko ma ya farma jakin. 29 Annabin ya ɗauki gawar mutumin Allah, ya ɗora ta akan jaki, ya komo da ita. Ya zo da ita birninsa ya yi makoki ya bizne shi. 30 Ya bizne gawar a cikin kabarinsa, suka yi makoki domin sa, cewa. "Kaito, ɗan'uwana!" 31 To bayan da ya bizne shi, tsohon annabin ya faɗa wa 'ya'yansa maza, cewa, "Sa'ad da na mutu, ku bizne ni a cikin kabari inda aka bizne mutumin Allah. Ku sa ƙasusuwana a kusa da nasa. 32 Gama an furta saƙon maganar Yahweh, a bagadin da ke Betel da kuma dukkan gidajen da ke kan tuddai a biranen Samariya, abin da lallai zai faru." 33 Bayan wannan Yerobowom bai juyo daga muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci don masujadai da ke kan tuddai a cikin dukkan mutane. Duk wanda ya ke so sai ya karɓe shi a matsayin firist. 34 Wannan abu ya zama zunubi ga iyalin Yerobowam ya yi dalilin da aka hallaka iyalinsa aka kuma shafe su kakaf daga fuskar duniya.

Sura 14

1 A lokacin nan Abija ɗan Yerobowom ba shi da lafiya sosai. 2 Yerobowom ya cewa matarsa, "Idan kin yarda ki tashi ki bad da kamarki, don ka da a gane ke matata ce, ki tafi Shilo, domin Ahija annabi yana can, shi ne wanda ya ce mani zan zama sarki akan waɗannan mutane. 3 Tare da ke ki ɗauki malmalar abinci goma, da waina da kurtun zuma, ki tafi wurin Ahija. Zai faɗa ma ki abin da zai faru da yaron." 4 Matar Yerobowom kuwa ta yi haka; ta tashi ta tafi Shilo har ta iso gidan Ahija. Yanzu Ahija ba ya gani; saboda ya rasa gani don tsufa. 5 Yahweh ya cewa Ahija, "Duba, ga matar Yerobowom ta na zuwa ta nemi shawara daga gare ka akan ɗanta, domin ba shi da lafiya. Ka ce haka, da haka da ita, gama sa'ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam." 6 Sa'ad da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin kofa, ya ce, "Ki shigo ciki, matar Yerobowam. Meyasa ki ke yi kamar ba ke ce ba? An aiko ni gare ki da labari mara daɗi. 7 Tafi, ki faɗa wa Yerobowam cewa Yahweh, Allah na Isra'ila ya ce, 'Na ɗaukaka daga cikin mutane na sa ka zama shugaba akan mutanena Isra'ila. 8 Na yage mulki daga iyalin Dauda na baka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dauda ba, wanda ya kiyaye umarnina ya bi ni da dukkan zuciyarsa, ya yi abin da ke dai-dai a idanuna. 9 Maimako haka, ka aikata mugunta, fiye da dukkan waɗanda suka riga ka. Ka yi waɗansu alloli, ka yi siffofi na zubi ka tsokane ni in yi fushi, ka jefar da ni a bayanka. 10 Saboda haka, duba, zan kawo masifa a iyalinka; zan datse daga gare ka kowanne ɗa namiji a Isra'ila, ko bawa ko 'yantacce, zan ƙori iyalinka gaba ɗaya, kamar mutum wanda ya ƙone juji kurmus. 11 Duk wanda ya ke na iyalinka wanda ya mutu a birni karnuka su cinye shi, wanda kuma ya mutu a fili tsuntsayen sammai su cinye shi, gama ni, Yahweh na faɗa. 12 Ki tashi, matar Yerobowom ki koma gidanki; ya yin da ƙafarki ta shiga birni, yaron Abija zai mutu. 13 Dukkan mutanen Isra'ila za su yi makoki dominsa za a bizne shi. Shi kaɗai ne daga iyalin Yerobowom wanda zai je kabari, gama shi kaɗai ne, daga cikin gidan Yerobowom, aka sa me shi da aikata abu mai kyau a fuskar Yahweh, Allah na Isra'ila. 14 Haka nan Yahweh zai ta da wani sarki a Isra'ila wanda zai yanke iyalin Yerobowom a wannan rana. Yau ita ce wannan rana, yanzun nan. 15 Gama Yahweh zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a ruwa, zai tuge Isra'ila daga wannan ƙasa mai kyau wadda ya ba kakanninsu. Zai watsar da su bayan Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu turaku na Ashera domin su tsokani Yahweh ya yi fushi. 16 Zai bayar da Isra'ila domin zunuban Yerobowom, zunuban da ya aikata, ta wurin sa Isra'ila su yi zunubi. 17 Sai matar Yerobowom ta tashi ta tafi, ta zo Tirza. Tana zuwa bakin ƙofar gidanta kenan, yaron ya mutu. 18 Dukkan Isra'ila su ka bizne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda aka faɗa masu ta wurin maganar Yahweh wanda ya yi magana ta wurin bawansa Ahija annabi. 19 Game da sauran abubuwa akan Yerobowom, yadda ya yi yaƙe-yaƙensa da sarautarsa, duba, an rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 20 Yerobowom ya yi mulki shekaru ashirin da biyu sa'an nan ya rasu tare da kakaninsa, ɗansa Nadab ya gaji sarauta a matsayin mahaifinsa. 21 Yanzu Rehobowom ɗan Suleman ya yi mulki a Yahuda. Rehobowom yana da shekare arba'in da ɗaya sa'ad da ya zama sarki, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai a Yerusalem, birnin da Yahweh ya zaɓa daga dukkan kabilun Isra'ila in da ya sa sunansa. Sunan mahaifiyarsa kuwa Na'ama Ammoniya. 22 Yahuda ta yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh; suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata, fiye da abin da kakanninsu suka yi. 23 Gama suma sun gina wa kansu wuraren tsafi, ginshiƙan dutse da turken Ashera a kan kowanne tudu mai tsawo da ƙarƙashin kowanne koren itace. 24 Akwai kuma karuwan tsafi a ƙasar. Suka yi abubuwan bankyama kamar al'ummai da Yahweh ya kawar daga wurin mutanen Isra'ila. 25 Wannan ya faru a shekara ta goma sha biyar ta mulkin Rehobowom da Shishak sarkin Masar ya gãba da Yerusalem. 26 Ya kwashe dukiyar gidan Yahweh, da dukiyar gidan sarki. Ya ɗauke kome da kome ya tafi da shi; ya kuma ɗauki garkuwoyin zinariya waɗanda Suleman ya yi. 27 Sarki Rehobowom ya yi garkuwoyin tagulla ya sa a hannun shugabannin masu tsaro, waɗanda ke tsaron ƙofar gidan sarki. 28 Ya zamana duk lokacin da sarki zai shiga gidan Yahweh, matsara za su ɗauke su; sai su kawo su a gidan tsaro. 29 Game da sauran abubuwa akan Rehobowom, dukkan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuda. 30 Kullum ana ta yin yaƙi tsakanin Rehobowom da Yerobowom. 31 Rehobowom kuwa ya yi barci tare da kakaninsa aka kuma bizne shi tare da su a birnin Dauda. Sunan mahaifiyarsa kuwa Na'ama daga Ammoniyawa. Abija ya gaji sarauta a matsayin mahaifinsa.

Sura 15

1 A shekara ta goma sha takwas ta sarki Yerobowom ɗan Nebat, Abija ya fara sarauta akan Yahuda. 2 Ya yi mulki shekaru uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Ma'aka. Ita ɗiyar Abishalom ce. 3 Shi ma ya yi tafiya a cikin dukkan irin zunubai da tsohonsa ya yi a lokacinsa; bai ba Yahweh Allahnsa dukkan zuciyarsa ba kamar yadda Dauda kakansa ya yi ba. 4 Duk da haka, saboda Dauda, Yahweh Allahnsa ya ba shi fitila a Yerusalem ta wurin ba ɗansa ya gaje shi saboda ya ƙarfafa Yerusalem. 5 Allah ya yi wannan domin Dauda ya yi abin da ke dai-dai a idanuwansa; a cikin dukkan kwanakin ransa, bai juya daga kowanne umarnin da aka ba shi ba, sai dai akan Yuriya Bahitte. 6 Yanzu akwai yaƙi a tsakanin Abija ɗan Yerobowom dukkan kwanakin rayuwar Abija. 7 Kamar sauran ayyukan Abija, duk da abubuwan da ya yi, ba suna rubuce a cikin littafin tarihi na sarakunan Yahuda ba? Akwai yaƙi tsakanin Abija ɗan Yerobowom. 8 Abija ya barci tare da kakaninsa, su ka bizne ne shi a birnin Dauda. Asa ɗansa ya zama sarki a maimakon mahaifinsa. 9 A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowom sarkin Isra'ila, Asa ya fara sarauta a Yahuda. 10 Ya yi shekaru arba'in da ɗaya yana sarauta a Yerusalem. Sunan kakarsa kuwa Ma'aka, yar Abishalom. 11 Asa ya yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh, kamar yadda Dauda, kakansa ya yi. 12 Ya kori karuwai matsafa daga ƙasar ya kuma cire dukkan gumakun da kakaninsa suka yi. 13 Ya kuma fitar Ma'aka da kakarsa, daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazamar siffa daga turken Ashera. Asa ya sassare ƙazamar siffar ya ƙone ta a Kwarin Kidron. 14 Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba. Duk da haka, Asa ya ba Yahweh dukkan zuciyarsa a dukkan kwanakinsa. 15 Ya kawo abubuwan da mahaifinsa ya keɓe da kuma azurfa da zinariya da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi a cikin gidan Yahweh. 16 Akwai yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha sarkin Isra'ila, dukkan kwanakinsu. 17 Ba'asha sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuda yaƙi ya gina Rama, don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga ƙasar Asa sarkin Yahuda. 18 Sai Asa ya kwashe dukkan azurfa da zinariya da suka rage a ɗakunan ajiya na gidan Yahweh, da na ɗakin ajiyar fãdar sarki. Ya sa su a cikin hannuwan barorinsa su kai su ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda ke zaune a Damaskus. Ya ce. 19 "Bari mu ƙulla alƙawari tsakani na da kai, kamar yadda ya ke tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Ka karya alƙawarinka da Ba'asha sarkin Isra'ila, domin ya bar ni." 20 Ben-Hadad kuwa ya saurari sarki Asa ya kuma aika shugabanin sojojinsa su ka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka yi faɗa da Iyon da Dan da Abe ta bet Ma'aka, da dukkan Kenneret tare da dukkan ƙasar Naftali. 21 Da Ba'asha ya ji wannan, sai ya daina ginin Rama ya koma Tirzah. 22 Sa'an nan sarki Asa ya yi jawabi ga dukkan mutanen Yahuda. Ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi su ka ɗauki duwatsu da katakai a Ramah waɗanda Ba'asha ke gina birnin. Sai sarki Asa ya yi amfani da kayan ginin ya gina Geba ta Benyamin da Mizfa. 23 Sauran dukkan abubuwa a game da Asa, dukkan ƙarfinsa, dukkan abubuwan da ya yi, da biranen da ya gina, ba su na nan ba a rubuce a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda? 24 Amma lokacin tsufansa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa. Asa ya rasu tare kakaninsa aka kuma bizne shi tare da su a cikin birnin Dauda mahaifinsa. Yehoshafat ɗansa ya zama sarki a matsayinsa. 25 Nadab ɗan Yerobowom ya fara sarauta a Isra'ila a shekara ta biyu ta sarki Asa na yin mulkin a Yahuda; ya yi sarautar Isra'ila shekaru biyu. 26 Ya yi mugunta a fuskar Yahweh ya yi tafiya a hanyar da mahaifinsa ya yi a cikin zunubinsa, ya jagoranci Isra'ila su yi zunubi. 27 Ba'asha ɗan Ahiji, na iyalin Issaka, ya yi wa Nadab maƙarƙashiya; Ba'asha kashe shi a Gibbeton wadda ke ta Filistiyawa, gama Nadab da dukkan Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi. 28 A cikin shekara ta uku da sarki Asa ke mulkin Yahuda, Ba'sha ya kashe Nadab ya kuma zama sarki a gurbinsa. 29 Nan da nan da ya zama sarki, Ba"asha ya kashe dukkan iyalin Yerobowom. Bai bar kowa ba a zuriyar Yerobowom wanda ke numfashi ba; a wannan hanya ya hallakar da gidan sarautarsa, kamar yadda Yahweh ya faɗa ta wurin bawansa Ahija mutumin Shilo, 30 domin zunuban Yerobowom wanda ya yi da kuma zunubin da ya sa mutanen Isra'ila suka yi, don ya tsokani Yahweh, Allah na Isra'ila ya yi fushi. 31 Kamar sauran abubuwa a kan Nadab, da dukkan abin da ya yi, ba suna a rubuci ba a cikin littafin tarihi na ayyukan sarakunan Isra'ila? 32 Akwai yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha sarkin Isra'ila a dukkan kwanakinsu. 33 A cikin shekara ta uku da Asa sarkin Yahuda, Ba'asha ɗan Ahija ya fara sarauta akan dukkan Isra'ila a Tirza ya kuma yi mulki sheraka ashirin da huɗu. 34 Ya yi abin da ke na mugunta a fuskar Yahweh ya kuma bi hanyar Yerobowom da kuma zunubin da ya sa Isra'ila suka yi.

Sura 16

1 Maganar Yahweh ta zo ga Yehu ɗan Hanani akan Ba'asha, cewa, 2 "Ko da ya ke na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaba akan mutanena Isra'ila, kai kuwa ka yi tafiya irin ta Yerobowom ka sa mutanena Isra'ila sun aikata zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu. 3 Duba, zan shafe Ba'asha da iyalinsa gaba ɗaya, zan maida iyalinka kamar iyalin Yerobowom ɗan Nebat. 4 Karnuka ne za su cinye kowanne mutum da ke na Ba'asha idan ya mutu a birni, tsuntsayen sama kuma ne za su cinye kowanne mutum da ya mutu a saura." 5 Sauran ayyuka akan Ba'asha, da abubuwan da ya yi, da ƙarfinsa, ba suna a rubuce a littafin tarihi na sarakunan Isra'ila ba? 6 Ba'asha ya yi barci aka kuma bizne shi tare da kakanninsa a Tirzah, Ela ɗansa kuma ya zama sarki a gurbinsa. 7 Sai maganar Yahweh ta zo wurin annabi Yehu ɗan Hanani akan Ba'asha da iyalinsa, duka kuma saboda dukkan mugutar da ya aikata a fuskar Yahweh, har ya yi fushi da ayyukan hannuwansa, kamar iyalin Yerobowom, kuma saboda ya hallaka dukkan iyalin Yerobowom. 8 A shekara ta ashirin da shida da Asa ke mulkin Yahuda, Ela ɗan Ba'asha ya fara sarauta akan Isra'ila a Tirzah; ya yi sarauta shekaru biyu. 9 Bawansa Zimri, shugaban rabin karusansa ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ela ya ke Tirzah, ya sha ya bugu a gidan Arza, wanda ya ke lura da fada a Tirzah. 10 Zimri ya tafi cikin gidan, ya buge shi har ya kashe shi, a shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Asa sarkin Yahuda, ya zama sarki a gurbinsa. 11 Da Zimri ya fara sarauta ya zauna akan kujerar mulki, yakashe dukkan iyalin Ba'asha. Bai bar namiji ko ɗaya a raye ba dangi ko abokai. 12 Haka Zimri ya hallaka dukkan iyalin Ba'asha, bisa ga maganar da Yahweh wanda ya faɗa akan Ba'asha ta bakin annabi Yehu, 13 saboda dukkan zunuban Ba'asha da zunuban Ela ɗansa su ka yi, da wanda su ka sa Isra'ila su ka yi, don sun tsokani Yahweh, Allah na Isra'ila, ya yi fushi da gumakunsu. 14 Game da sauran ayyukan Ela, da dukkan abin da ya yi, ba suna a rubuce a cikin littafin tarihi na sarakunan Isra'ila ba? 15 A shekara ta ashirin da bakwai da sarki Asa ke mulkin Yahuda, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirzah. A lokacin nan sojoji sun yi sansani a Gibbeton, wanda ta ke ta Filistiyawa. 16 Sojojin da suka yi sansani a wurin suka ji an ce, "Zimri ya shirya makirci ya kashe sarki." A wannan rana a sansanin, dukkan mutanen Isra'ila suka naɗa Omri, shugaban sojojin, sarkin Isra'ila. 17 Omri kuwa ya tafi daga Gibbeton da dukkan mutanen Israila tare da shi, su ka kewayeTirzah da yaƙi. 18 Da Zimri ya ga an ci birnin sai ya tafi ya shiga hasumiyar da ta ke a fãdar sarki, ya sawa fãdar ginin wuta ta cinye duk da shi, ta wannan hanyar ya mutu a zafin wuta. 19 Wannan ya faru saboda da zunuban da ya aikata ta wurin aikata mugunta a fuskar Yahweh, ya bi hanyar Yerobowam da zunuban da ya sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi. 20 Game da sauran ayyuka akan Zimri da makircin da ya aiwatar, ba a rubuce su ke ba a cikin littafin tarihi na sarakunan Isra'ila? 21 Sai mutanen Isra'ila suka rabu gida biyu. Rabin mutanen suka bi Tibni ɗan Ginat, don su naɗa shi sarki, rabi kuma suka bi Omri. 22 Amma mutane waɗanda suka bi Omri suna da ƙarfi fiye da mutanen da suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki. 23 Omri ya fara sarauta akan Isra'ila a shekara ta talatin da ɗaya ta Asa sarkin Yahuda, ya yi shekaru goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekaru shida yana mulki a Tirzah. 24 Ya sayi tudun Samariya daga Shemer akan talanti biyu na azurfa. Ya gina birni a tudu aka kira sunansa birnin Samariya, bayan sunan Shemer, mai tudun. 25 Omri kuwa ya aikata mugunta a fuskar Yahweh, ya yi mugunta fiye da dukkan waɗanda suka riga shi. 26 Gama ya yi tafiya a dukkan hanyoyin da Yerobowom ɗan Nebat da irin zunubansa wanda ya sa Isra'ila suka yi zunubi, suka sa Yahweh, Allah na Isra'ila, fushi don gumakunsu na wofi. 27 Game da sauran ayyuka wanda Omri ya yi, da ƙarfinsa da ya nuna, ba suna nan a cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 28 Omri kuwa ya yi barci, aka bizne shi tare da kakaninsa a Samariya, Ahab ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifnsa 29 A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya fara sarauta a Isra'ila. Ahab ɗan Omri ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shekaru ashirin da biyu. 30 Ahab ɗan Omri ya yi abubuwan da ke mugunta a fuskar Yahweh, fiye da dukkan waɗanda su ka riga shi. 31 Da ya ke Ahab abu ne mai sauki a gare shi ya bi zunuban Yerobowom ɗan Nebat, sai ya auro matarsa Yezebel 'yar Etba'al, sarkin Sidon; ya je yana bauta wa Ba'al, yana kuma yi masa sujada. 32 Ya gina bagadi domin Ba'al a gidan Ba'al, wanda ya gina a Samariya. 33 Ahab kuma ya yi turken gunkiyar nan Ashera. Ahab dai ya yi abin da zai tsokani Yahweh Allah na Isra'ila, zuwa fushi fiye da dukkan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi. 34 A lokacin sarautar Ahab, Hiyel na Betel ya gina Yariko. Hiyel ya sa tushen birni da farashin ran Abiram, ɗan farinsa; Segub, ɗan autansa, ya rasa ransa a lokacin da ya ke gina ƙofofin birnin, ta cikin ajiye maganar Yahweh wanda ya yi magana ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.

Sura 17

1 Iliya Batishbe, daga Tishbi a Giliyad, ya ce da Ahab, "Kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila ya ke raye wanda nake tsaye a gabansa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a waɗannan shekaru sai da faɗata." 2 Maganar Yahweh ta zo ga Iliya, cewa, 3 "Tashi daga nan ka tafi wajen gabas; ka ɓoye kanka a rafin Kerit, gabashin Yodan. 4 A can zai zamana inda za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can." 5 Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Yahweh ya umarta. Ya tafi ya zauna a rafin Kerit, gabas da Yodan. 6 Hankaki kuwa suka riƙa kawo masa abinci da nama da safe abinci da nama da maraice, yana shan ruwa daga rafin. 7 Amma bayan wani ɗan lokaci sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar. 8 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya, cewa. 9 "Tashi ka tafi Zarefat, wadda da ta ke ta Sidon, ka zauna a can. Duba, na umarci wata mace gwauruwa ta ciyar da kai." 10 Shi kuwa ya tashi ya tafi Zarefat, sa'ad da ya isa ƙofar birnin sai ga wata gwauruwa a wurin ta na tattara itace. Sai ya kira ta ya ce, "Idan kin yarda ki kawo mani ɗan ruwa in sha." 11 Tana juyawa za ta tafi ta kawo masa ruwan sha kenan, sai ya kira ta ya ce, "Idan kin yarda ki ba ni ɗan abinci a hannunki." 12 Sai ta amsa, "Kamar yadda Yahweh Allahnka ya ke da rai, ba ni da abinci, sai dai ɗan garin da ya ragu a tukunya da ɗan man da ke cikin kwalba. Ga ni, ina tattara yan itatuwa biyu don in je in girka shi domin ni da ɗana, mu ci, mu mutu." 13 Iliya ya ce mata, "Kada ki ji tsoro. Tafi ki yi yadda na ce, amma ki fara yi mani gurasa kaɗan tukuna ki kawo mani. Sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki. 14 Gama Yahweh Allah na Isra'ila, ya ce, 'Garin da ya ke a tukunyarki ba zai ƙare ba, ko da man ma ba zai dena zubuwa ba, sai dai ranar da Yahweh ya aiko da ruwan sama a duniya." 15 Ta tafi ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Ita da Iliya da sauran yan gidan, sun ci har kwanaki da yawa. 16 Garin bai ƙare ba, kwalbar man ma bata dena zubuwa ba, kamar yadda maganar Yahweh ta ce, kamar kuma yadda Iliya ya faɗa. 17 Bayan waɗannan abubuwa sai ɗan macen, matar wadda take da gidan, ya yi ciwo. Ciwonsa kuwa ya tsananta har ba sauran numfashi a cikinsa. 18 Sai mahaifiyar yaron ta ce da Iliya, "Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo gare ni ne don ka tuna ma ni da zunubina ka kuma kashe ɗa na?" 19 Sai Iliya ya amsa ma ta, "Ki ba ni ɗanki." Ya ɗauki yaron daga hannuwanta, ya kai shi a ɗaki inda ya ke zama, ya kwantar da yaron akan gadonsa. 20 Ya yi kuka ga Yahweh ya ce, "Yahweh Allahna, ka kuma kawo masifa akan gwauruwar nan wadda na ke zaune wurinta, ta wurin kashe mata ɗa? 21 Sa'an nan Iliya ya kwanta ya miƙe akan yaron sau uku, ya kuma yi kuka sosai ga Yahweh ya ce, "Yahweh Allahna, ina roƙonka, idan ka yarda bari ran yaron nan ya komo gare shi." 22 Yahweh kuwa ya saurari muryar Iliya; ran yaron ya komo gare shi sai ya farfaɗo. 23 Iliya ya ɗauki yaron daga ɗakinsa ya kawo shi ya kai shi cikin gida; ya bada yaron ga uwar ya ce, "Ki gani, ɗauki yaronki yana da rai." Matar kuwa ta cewa Iliya, 24 "Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, kuma maganar Yahweh kuwa da ke cikin bakinka gaskiya ce."

Sura 18

1 Bayan kwanaki masu yawa sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya, a shekara ta uku ta farin, cewa, 2 "Tafi, ka nuna kanka ga Ahab zan aiko da ruwan sama a ƙasar." Iliya kuwa ya tafi ya nuna kansa ga Ahab; yanzu kuwa yunwa ta tsananta a Samariya. 3 Ahab ya kira Obadiya, wanda ya ke shugaban fada. Obadiya kuwa yana girmama Yahweh sosai, 4 domin lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Yahweh, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin, hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su da gurasa ya kuma shayar da su. 5 Ahab ya cewa Obadiya, "Tafi cikin ƙasar nan duk inda maɓuɓɓugar ruwa da fadamu suke. Watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa dukkan dabbobin nan." 6 Saboda haka suka raba ƙasar a tsakaninsu suka shige ta su duba inda ruwa ya ke. Ahab ya bi ɗaya hanyar da kansa Obadiya kuma ya tafi wata hanyar. 7 Sa'ad da Obadiya ya ke tafiya a hanya, Iliya ya yi kaciɓus da shi. Obadiya ya gane da shi sai ya russana a ƙasa. Ya ce, "Kai ne shugabana Iliya?" 8 Iliya ya amsa masa. "Ni ne. Tafi ka faɗa wa shugabanka, 'Duba, Iliya na nan.'" 9 Obadiya ya amsa, "Wanne zunubi na yi, har da za ka bada bawanka a cikin hannun Ahab, domin ya kashe ni? 10 Kamar yadda Yahweh Allahnka ya ke raye, babu wata al'umma ko mulki da shugabana bai aika mutane a nemo ka ba. Duk wata al'umma ko mulki suka ce, 'Iliya ba ya nan,' Ahab ya sa su ɗauki rantsuwa ba su same ka ba. 11 Amma yanzu ka ce, "Tafi, faɗa wa shugabana cewa ga Iliya a nan.' 12 Ya yin da na tafi daga wurin ka, Ruhun Yahweh ya kai ka wurin da ban sani ba. Don haka idan na tafi na faɗa wa Ahab, idan kuma bai same ka ba, zai kashe ni. Ko da ya ke ni bawanka, ina bauta wa Yahweh tun daga kuruciyata. 13 Ashe ba a faɗa maka ba, shugabana, abin da na yi a lokacin da Yezebel ta kashe annabawan Yahweh, abin da na yi na ɓoye annanbawan Yahweh ɗari na raba su hamsin hamsin a kogo na kuma ciyar da su da gurasa da ruwa? 14 Yanzu kuwa ka ce da ni, "Tafi in faɗa wa shugabana ga Iliya a nan,' ai zai kashe ni." 15 Sai Iliya ya amsa, "Kamar yadda Yahweh mai runduna ya ke da rai, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina ga Ahab yau." 16 Saboda haka sai Obadiya ya tafi ya sadu da Ahab, ya faɗa masa abin da Iliya ya ce. Sai sarki ya tafi ya sadu da Iliya. 17 Lokacin da Ahab ya ga Iliya, ya ce masa, "Kai ne? wanda ke kawo wahala ga Isra'ila!" 18 Iliya ya amsa, "Ba ni ne na kawo wahala a Isra'ila ba, amma kai da iyalin mahaifinka su ne waɗanda suka jawo wahala ta wurin ƙin bin umarnan Yahweh kuna bin Ba'aloli. 19 Yanzu sai, ka aika da magana a tattara mani dukkan Isra'ila a Tsaunin Karmel, tare da annabawan Ba'al 450 da ɗari huɗu na annabawan Ashera waɗanda ke ci a teburin Yezebel." 20 Sai Ahab ya aika da magana ga dukkan mutanen Isra'ila da su tara annabawa gaba ɗaya a Dutsen Karmel. 21 Iliya ya zo kusa da dukkan mutane ya ce, "Har yaushe ne za ku ci gaba da canza tunaninku? Idan Yahweh ne Allah, ku bi shi. Amma idan Ba'al shi ne Allah, sai ku bi shi." Duk da haka mutane ba su amsa masa da magana ba. 22 Sai Iliya cewa mutane, "Ni, kaɗai ne na rage a matsayin annabin Yahweh, amma annabawan Ba'al su ɗari huɗu da hamsin. 23 Ku ba mu bijimai biyu. Bari su zaɓi ɗaya bijimin don kansu su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa su akan itacen, kada a sa masa wuta a ƙarƙashinsa. 24 Sai ku yi kira ga sunan allahnku, ni ma zan yi kira ga sunan Yahweh, duk Allahn da ya amsa da wuta bari ya kasance Allah. "Dukkan mutane suka amsa suka ce, "Wannan ya yi kyau." 25 Sai Iliya yace da annabawan Ba'al, "Ku zaɓi bijimi ɗaya domin kanku ku kuma shirya shi da farko, gama kuna da mutane da yawa. Sa'an nan ku yi kira ga sunan allahnku, amma kada kuma fa ku sa wuta a ƙarƙashi bijimin." 26 Suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi, suka yi kira da sunan Ba'al tun daga safe har rana ta yi tsaka, suna cewa, "Ba'al, ka ji mu mana." Amma babu wata murya, ko wani da ya amsa. Suka yi ta rawa a kewayan bagadin da suka gina. 27 Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi masu ba'a ya ce, "Ku yi ihu da ƙarfi! Shi allah ne! Watakila ya yi tafiya da nisa, ko watakila yana barci ne, sai ku tashe shi." 28 Suka yi ihu da ƙarfi sosai, suna kuma tsattsaga jikunansu, kamar yadda suke yi, tare da takubba da mãsu, har jini yana ta zuba daga jikunansu. 29 Da tsakar rana ta wuce, sai su kai ta yin sambatu har lokacin baikon hadayar yamma, amma ba bu wata murya ko wani wanda ya amsa; babu wani wanda ya kula da roƙe -roƙensu. 30 Sai Iliya yace da dukkan mutane, "Ku zo kusa da ni," dukkan mutane kuwa suka zo kusa da shi. Ya gyara bagadin Yahweh wanda aka lalatar. 31 Iliya ya ɗauko duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan 'ya 'yan Yakubu, ga Yakubu wanda maganar Yahweh ta zo, cewa, "Isra'ila ne zai zama sunanka." 32 Tare da duwatsun ya gina bagadi da sunan Yahweh, ya kuma haƙa rami babba sosai kewaye da bagadin isasshe da zai ci durom biyu na hatsi. 33 Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Ya ce, "Ku cika tuluna da ruwa a kwarara akan hadaya ta ƙonawar da kuma kan itacen." 34 Ya kuma ce, "Ku yi haka har sau lokaci na biyu," Suka yi haka a lokaci na biyu. Ya ce, "Su sake yi a lokaci na uku," suka yi haka a lokaci na uku. 35 Ruwa kuwa ya malale bagadin, ya kuma cika ramin. 36 Ya zama kuwa a lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai Iliya annabi ya matso kusa ya ce, "Yahweh, Allah na Ibrahim, na Ishaku da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa dukka bisa ga maganarka. 37 Ka ji ni, Yahweh, ka ji ni, saboda waɗannan mutane su san ka, kai ne Yahweh, Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu gare ka kuma." 38 Sai wutar Yahweh ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, duk da itacen, da duwatsun da kurar, ta kuma lashe ruwan da ya ke cikin ramin. 39 Sa'ad da dukkan mutanen suka ga wannan, suka russana suka sunkuyar da kai suka ce, "Yahweh, shi ne Allah! Yahweh, shi ne Allah!" 40 Iliya kuma ya ce masu, "Ku kama annabawan Ba'al. Ka da ku bar ko ɗaya daga cikinsu ya tsere." Sai suka kama su, Iliya ya kai annabawan Ba'al rafin Kishon, ya karkashe su a can. 41 Iliya ya cewa Ahab, "Tashi, ka ci ka sha, gama akwai motsin saukowar ruwan sama." 42 Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha. Iliya ya tafi can konkoli Karmel, ya zauna a ƙasa ya haɗa kai da gwiwa. 43 Ya ce da baransa, "Ka tafi ka duba wajen teku." Baran ya tafi ya duba, ya ce, "Ba bu kome." Sai Iliya ce, "Tafi kuma, har sau bakwai." 44 A zuwa na bakwai sai ya ce, "Na ga wani ɗan girgije yana zuwa daga teku, karami kamar tafin hannun mutum." Iliya ya amsa, "Tafi ka faɗa wa Ahab, 'Ya shirya karusarsa ya kuma gangara domin kada ruwan sama ya tsaida shi.'" 45 Ya zamana fa jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da giza-gizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab ya hau ya tafi wurin Yezriyel, 46 amma hannun Yahweh yana tare da Iliya. Ya sha ɗammara ya sheka a guje ya riga Ahab isa Yezriyel.

Sura 19

1 Ahab ya faɗa wa Yezebel dukkan abin da Iliya ya yi da yadda ya kashe dukkan annanbawa da takobi. 2 Sai Yezebel ta aika wurin Iliya, cewa, "Bari alloli su yi mani, harma fiye kuma, idan ban mai da ran ka kamar ran ɗaya daga waɗannan annanbawa gobe a dai-dai wannan lokacin ba." 3 Sa'ad da Iliya ya ji haka, ya ji tsoro, ya tsere domin ransa ya zo Biyasheba, wadda take ta Yahuda, ya bar baransa a can. 4 Amma shi da kansa ya yi tafiyar yini guda cikin jeji, ya zo ya zauna a gindin itacen aduwa. Ya yi roƙo domin kansa yadda zai mutu, ya kuma ce, "Ya isa haka, yanzu, Yahweh; ɗauke raina, gama ban fi kakannina ba." 5 Sai ya kwanta ya yi barci a gindin itace aduwa. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, "Tashi ka ci abinci." 6 Da Iliya ya duba, kusa da kansa sai ga gurasa ana gasawa akan garwashi da butar ruwa. Ya ci, ya sha, ya koma ya kwanta kuma. 7 Mala'ikan Yahweh kuma ya sake zuwa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, "Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za ta yi maka yawa. 8 Sai ya tashi ya ci ya sha, ya sami ƙarfin tafiya da wannan abincin har kwana arba'in dare da rana zuwa Horeb, wato tsaunin Allah. 9 Ya tafi wani kogo a can ya tsaya a cikinsa. Sai maganar Yahweh ta zo wurinsa ta ce da shi, "Me kake yi a nan, Iliya? 10 Iliya ya amsa, "Ni mai kishi domin Yahweh, Allah mai runduna ne, gama mutanen Isra'ila suka manta da alƙawarin ka, suka lalata bagadanka, suka kuma karkashe annanbawanka da takobi. Yanzu ni kaɗai na rage da ba su kashe ba, suna ma ƙoƙarin su ɗauke raina." 11 Yahweh ya amsa, "Tafi ka tsaya akan tsauni a gabana." Sai ga Yahweh yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsaga duwatsun, ta kuma farfasa shi rugu rugua gabanYahweh, amma Yahweh ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa ta zo, amma Yahweh ba ya cikin girgizar ƙasar. 12 Bayan girgizar kuma sai wuta, amma Yahweh ba ya cikin wutar. Daga nan bayan wutar, sai natsastsar ƙaramar murya. 13 Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai murya ta zo gare shi ta ce, "Me ka ke yi a nan, Iliya? 14 Iliya ya amsa, "Ni na zama mai kishi domin Yahweh, Allah mai runduna ne, amma mutanen Israel sun karya alƙawarinka, suka lalata bagadannka suka kuma karkashe annabawanka da takobi. Yanzu ni, kaɗai na rage suna ma ƙoƙarin su ɗauki raina. 15 Sai Yahweh yace da shi, "Tafi, ka juya akan hanyarka ta jeji kusa da Damaskus, idan ka isa can za ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya zama sarkin Aram, 16 za ka kuma keɓe Yehu ɗan Nimshi ya zama sarkin Isra'ila, za ka kuma zuba wa Elisha ɗan Shafat na Abel Mehola mai ya zama annabi a gurbinka. 17 Zai kasance Yehu zai kashe duk wanda ya tsere daga takobin Hazayel, Elisha zai kashe duk wanda ya tsere daga takobin Yehu. 18 Amma zan barwa kaina mutum dubu bakwai na Isra'ila don kaina, waɗanda ba su russuna wa Ba'al da gwiwonsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakunansu ba." 19 Iliya fa ya tashi daga wurin ya sami Elisha ɗan Shafat, wanda ke noma da shanun huɗa karkiya goma sha biyu, shi kansa kuma yana huɗa da karkiyar sha biyu. Iliya ya bi ta kusa da Elisha ya jefa masa alkyabbarsa. 20 Sai Elisha ya bar shanun noman, ya sheka da gudu gun Iliya ya ce, "Idan ka yarda bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka." Sai Iliya ya ce da shi, "Koma, amma ka yi tunanin abin da na yi maka." 21 Elisha ya komo daga wurin Iliya ya kama shanun noman, ya yanka dabbobin, ya dafa namansu da itace daga karkiyoyin. Sai ya ba mutane suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.

Sura 20

1 Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tara dukkan sojojinsa. Akwai sanannun sarakuna talatin da biyu da suke tare da shi, da dawakai da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya hari ya kuwa yi yaƙi da ita. 2 Ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin Ahab sarkin Isra'ila, ya ce da shi, "Ben Hadad ya ce wannan: 3 Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Matanka da 'ya'yanka, masu kyau, nawa ne.'" 4 Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Ya kasance kamar yadda ka ce, shugabana, sarki. Ni da dukkan abin da na ke da shi naka ne." 5 Jakadun suka dawo kuma suka ce, "Ben-Hadad ya ce wannan, 'Na aika maka da magana cewa dole ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka da 'ya'yanka. 6 Amma zan aiko barorina wurinka gobe a dai-dai wannan lokacin, za su bincike gidanka da gidajen barorinka. Za su kwashe duk abin da ka ke da shi daga hannuwanka su ɗauke abubuwan da suka gamshi idanuwansu.'" 7 Sai sarkin Isra'ila ya kirawo dukkan dattawan ƙasar ga baki ɗaya ya ce, "Idan kun yarda ku duba yadda wannan mutum ya ke neman rikici. Ya aiko wuri na domin in ba shi matana da 'ya'yana da azurfa da zinariyata, ni kuwa ban yardar masa ba." 8 Dukkan dattawa da dukkan mutane suka cewa Ahab, "Kada ka saurare shi ko ka da mu da abin da ya ke so." 9 Ahab ya ce da jakadun Ben-Hadad, "Ku faɗa wa shugabana sarki, 'Na yarda da dukkan abin da ka aiko barorinka su yi da farko, amma ba zan yarda da wannan buƙatar ta biyu ba.'" Jakadun kuwa suka koma da wannan amsa ga Ben-Hadad. 10 Sai Ben-Hadad ya sake aikawa da saƙonsa ga Ahab, ya ce, "Bari alloli su yi mani haka harma fiye idan tokar Samariya ba za ta isa domin dukkan mutane waɗanda suka biyo ni kowannensu ya sami ɗan kaɗan ba. 11 Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Ku faɗa wa Ben-Hadad, 'Ba wani wanda ya ke adali da zai sa sulke ya yi fahariya kamar ya ci yaƙin.'" 12 Ben-Hadad ya ji wannan saƙo sa'ad da ya ke sha, shi da sarakuna da ke ƙarƙashinsa waɗanda suke cikin rumfunoni. Ben-Hadad ya umarce mutanensa, "Kowa ya tsaya a wurinsa domin yaƙi. "Suka shirya kansu suka tsaya domin yaƙin ya fada wa birnin. 13 Sai ga wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra'ila ya ce, "Yahweh ya ce, "Ka ga wannan babban taron sojoji? Duba, zan ba da su a hannunka yau, za ka sani ni ne Yahweh.'" 14 Ahab ya amsa, "Wane ne zai yi jagorar babbar rundunar?" Yahweh ya amsa ya ce, "Ta wurin matasan ofisoshi waɗanda su ke yi wa gwamnonin larduna hidima." Sai Ahab ya ce, "Wane ne zai fara yaƙin?" Yahweh ya amsa, "Kai ne." 15 Sai Ahab ya tara matasan ofisoshi waɗanda suke yi wa gwamnonin larduna hidima. Su ɗari 232. Bayansu kuma ya tara dukkan sojoji da dukkan rundunar yaƙIn Isra'ila, jimilla dubu bakwai. 16 Suka tafi da tsakar rana. Ben-Hadad yana a buge da abin sha a rumfa, shi da sarakunan da ke ƙarƙashinsa su talatin da biyu waɗanda suke goyan bayansa. 17 Matasan ofisoshi waɗanda suke yi wa gwamnonin larduna hidima suka fara wucewa gaba. Sai Ben-Hadad ya ji labari ta wurin waɗanda ya aike su, "Mutane na zuwa daga Samariya." 18 Ben-Hadad yace, "Ko da sun zo don salama ko da yaƙi, ku kama su da rai." 19 Matasan ofisoshi waɗanda suke wa gwamnonin larduna hidima sun fita daga birnin sojoji kuma suna bin su. 20 Kowa ya kashe abokin gãbarsa, Aremiyawa suka gudu. Isra'ila kuwa suka rutume su. Ben-Hadad sarkin Aram ya tsere akan doki tare da mahayan dawakai. 21 Sarkin Isra'ila ya fita ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Aremiyawa masu yawa. 22 Sa'an nan annabi ya je wurin sarkin Isra'ila ya ce da shi, "Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka fahimci shirin abin da zaka yi, gama da juyuwar shekara sarkin Aram zai zo maka da harin yaƙi." 23 Barorin sarkin Aram suka ce da shi, "Na su allahn allah ne na tuddai. Don haka suka fi mu ƙarfi. Amma yanzu bari mu yi yaƙi da su a kwari, ba bu shakka za mu fi su ƙarfi. 24 Dole ka yi wannan: ka fitar da sarakuna daga matsayinsu na shugabanci ka maida hafsoshin sojoji a mamadinsu. 25 Ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa-dawakai domin dawakai da karusai domin karusai, mu kuma za mu yi yaƙi da su a kwari. Babu shakka za mu yi ƙarfi fiye da su." Ben-Hadad ya saurari shawararsu ya yi yadda suka ba da shawarar. 26 Bayan farkon sabuwar shekara, Ben-Hadad ya tara Suriyawa su ka haura zuwa Afek su yi yaƙi da Isra'ila. 27 Mutanen Isra'ila suka taru aka ba su guzuri da za su yi yaƙi da su. Mutanen Isra'ila suka kafa sasani a gabansu kamar kananan garkuna biyu na awaki, amma Aremiyawa suka cika ƙasar. 28 Sai mutumin Allah ya zo kusa ya yi magana da sarkin Isra'ila ya ce, "Yahweh ya ce: 'Gama da ya ke Aremiyawa sun ce Yahweh shi allah na tuddai ne, amma ba shi ne allah na kwari ba, zan ba da dukkan wannan babban taron sojojin nan a hannunka, za ka sani Ni ne Yahweh.'" 29 Sojojin suka kafa sansani daura da juna har kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin yaƙi ya fara. Mutanen Isra'ila suka kashe Aremiyawa nan ƙafa100,000 a rana ɗaya. 30 Sauran suka gudu zuwa Afek, cikin birni, garun kuma ya faɗo akan mutune dubu ashirin da bakwai waɗanda suka rage. Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga cikin birni, cikin ƙuryar ɗaki. 31 Barorin Ben-Hadad suka ce da shi, "Duba yanzu, mun ji cewa sarakunan gidan Isra'ila sarakuna ne masu jinƙai. Idan ka yarda bari mu sa tufafin makoki mu ɗaura igiyoyi a kawunanmu, mu tafi wurin sarkin Isra'ila. Watakila zai bar ka da rai." 32 Sai suka sa tufafin makoki suka ɗaura igiyoyi a kawunansu suka tafi wurin sarkin Isra'ila suka ce, "Baranka Ben-Hadad ya ce, 'Idan ka yarda ka bar ni da rai.'" Ahab yace, "Har yanzu yana da rai? Shi ɗan'uwana ne." 33 Yanzu mutanen suna sauraro kowace alama daga wurin Ahab, sai su yi saurin amsa masa, "I, ɗan'uwanka Ben-Hadad yana da rai." Sai Ahab ya ce, "Ku tafi ku kawo shi." Sai Ben-Hadad ya zo wurin sa, Ahab ya sa ya shiga da shi cikin karusarsa. 34 Ben-Hadad ya ce da Ahab, "Zan dawo maka da biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, kai kuma za ka yi kasuwanci a Damaskus, kamar yadda tsohona ya yi a Samariya." Ahab ya ba shi amsa, "Zan bar ka, ka tafi a kan alƙawari." Ahab ya yi alƙawari da shi, sa'an nan ya bar shi ya tafi. 35 Sai ga wani mutum, ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa, ya ce da ɗaya daga abokansa annabawa bisa ga maganar Yahweh, "Idan ka yarda ka buge ni." Amma mutumin ya ƙi ya buge shi. 36 Sai annabin ya ce da abokinsa annabi, "Da ya ke ba ka yi biyayya da muryar Yahweh ba, da zarar ka tashi daga wurina, zaki zai kashe ka." Da ya tashi daga wurinsa kuwa zaki ya zo ya gamu da shi, ya kashe shi. 37 Annabin kuma ya sami wani mutum ya ce, "Idan ka yarda ka buge ni." Mutumin kuwa ya buge shi har ya ji masa ciwo. 38 Sai annabin ya tafi ya jira sarki a hanya; ya bad da kama, ya rufe idanunsa da ƙyalle. 39 Sa'ad da sarki ya ke wucewa, sai annabi ya kira sarki ya ce, "Ni baranka na tafi wurin yaƙi mai zafi, sai soja ya tsaya ya kawo mani abokin gãba ya ce, 'Kula da wannan mutum. Idan wani abu ya sa ya tsere, za ka ba da ranka domin ransa, ko kuma ka biya talanti ɗaya na azurfa.' 40 Gama da ya ke baranka yana fama da kai da kawowa, abokin gãbar soja ya tsere." Sai sarkin Isra'ila ya ce da shi, "Wannan shi ne irin hukuncin da zan yi - kai da kanka ka shawarta haka." 41 Sai annabi ya yi sauri ya cire ƙyalle daga idanunsa, sarkin Isra'ila ya gane, ashe ɗaya daga cikin annabawa ne. 42 Annabin ya cewa sarki, "Yahweh ya ce, 'Da ya ke ka bar shi ya tafi daga hannunka mutum wanda na ƙaddara ga mutuwa, ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka kuma maimakon mutanensa.'" 43 Sarkin Isra'ila kuwa ya tafi gidansa da baƙinciki, a Samariya.

Sura 21

1 A wani lokaci kuma, Nabot Bayezrile yana da gonar inabi a Yezriyel, kusa da fãdar Ahab, sarkin Samariya. 2 Ahab ya yi magana da Nabot cewa, "Ka ba ni gonar inabinka, don in mai da ita lambu, domin gonar tana kusa da gidana. Ni kuwa zan ba ka wata gonar inabin mai kyau, ko kuma idan kana so, sai in biya ka tamanin kuɗinta." 3 Amma Nabot ya amsa wa Ahab, "Yahweh ya sawwake in ba ka gãdon kakannina." 4 Ahab ya koma fãdarsa da baƙinciki, saboda amsar da Nabot Bayezrile ya ba shi da ya ce, "Ni ba zan ba ka gãdon kakannina ba." Ya zauna akan gado, ya juya fuskarsa, ya ƙi cin kowanne abinci. 5 Yezebel matarsa ta zo wuinsa, ta ce da shi, "Me ya sa zuciyarka ta da mu, har ka ƙi cin kowanne abinci?" 6 Ya amsa mata, "Domin na yi magana da Nabot Bayezrile, na ce masa, 'Ya ba ni gonar inabinsa don in saya, idan ya yarda, zan ba ka wata gonar inabin ta zama ta ka.' Sai ya amsa mani, 'ba zan ba ka gonar inabina ba.'" 7 Yezebel matarsa ta amsa masa, "Ba kai ne ka ke mulkin Isra'ila ba? Tashi ka ci abinci; bari zuciyarka ta yi farinciki, zan samar maka gonar inabin Nabot Bayezrile." 8 Yezebel ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da su zuwa ga dattawa da mawadata masu kuɗi waɗanda suke zaune tare da shi a taruruka, da waɗanda suke zama kusa da Nabot. 9 Ta rubuta a wasiƙun, cewa, "A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban mutane. 10 A kuma sa 'yan iskan mutane biyu su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, 'Ka zagi Allah da sarki.'" Sa'an nan ku tafi da shi waje, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 11 Mutanen birnin da dattawa da masu arzaki da ke zaune a birnin Nabot, suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika masu. 12 Su kuwa suka yi shelar azumi, suka zaunar da Nabot a gaban mutane. 13 Sai mutune biyu suka zo, suka zauna a gaban Nabot suka yi ta shaidar zur akan Nabot a gaban mutane, cewa, "Nabot ya zagi Allah da sarki." Sai suka ɗauke shi wajen birni suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 14 Dattawa suka aika da magana ga Yezebel, cewa, "An jajjefe Nabot da duwatsu ya mutu." 15 Yayin da Yezebel ta ji labari an jajjefe Nabot da duwatsu har ya mutu, sai ta ce da Ahab, "Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot Bayezrile wadda ya ƙi ya ba ka, ka ba shi kuɗi, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu." 16 Da Ahab ya ji labarin Nabot Bayezrile ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezrile ya ɗauke ta ya mallake ta. 17 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya Batishbe, cewa, 18 "Tashi ka tafi ka sadu da Ahab sarkin Isra'ila, wanda ya ke zaune a Samariya. Yana cikin gonar inabin Nabot, inda ya tafi don ya mallake ta. 19 Dole ka yi magana da shi ka ce Yahweh ya ce, 'Ka yi kisa, ka kuma ɗauki abin da ya mallaka? Sai ka faɗa masa Yahweh ya ce, 'A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka, i, jininka.'" 20 Ahab ya ce da Iliya, "Ka same ni ko, maƙiyina?" Iliya ya amsa, na same ka, gama ka bada kanka ga aikata abin da ke mugunta a fuskar Yahweh. 21 Yahweh yace wannan da kai: 'Duba, zan kawo maka masifa, in shafe ka, in datse daga gare ka kowanne ɗa namiji bawa ko 'yantarcen mutum a Isra'ila. 22 Zan sa iyalinka kamar iyalin Yerobowam ɗan Nebat, su kuma zama kamar iyalin Ba'asha ɗan Ahija, saboda ka sani har na yi fushi, ka kuma sa mutanen Israila sun yi zunubi.' 23 Yahweh kuma ya sake yin magana akan Yezebel, cewa, 'Karnuka za su cinye Yezebel a gefen katangar Yezriyel.' 24 Duk wanda ya ke na Ahab da zai mutu a birni karnuka ne za su cinye shi, tsuntsayen sararin sama ne kuma za su cinye duk wanda ya mutu a saura." 25 Babu wani kamar Ahab, da ya ba da kansa ga aikata mugunta a fuskar Yahweh, wanda matarsa Yezebel ta zuga shi yin zunubi. 26 Ahab ya yi abin banƙyama ƙwarai saboda ya bi gumaka, kamar yadda Amoriyawa suka yi, waɗanda Yahweh ya kore su a gaban mutanen Isra'ila. 27 Da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, ya yage tufafinsa ya sa na makoki a jikinsa, ya yi azumi, ya kuma kwanta a tsummokaran makoki, ya zama da damuwa. 28 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya Batishbe, cewa, 29 "Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da ya ke ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba; sai dai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a cikin iyalinsa."

Sura 22

1 Shekaru uku da suka wuce ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra'ila ba. 2 Sai a cikin shekara ta uku ɗin, Yehoshafat sarkin Yahuda ya tafi wurin sarkin Isra'ila. 3 Sarkin Isra'ila ya ce da barorinsa, "Ko kun san Ramot Giliyad tamu ce, amma ba ma yin komai domin mu ƙwace ta daga hannun sarkin Aram?" 4 Ya ce da Yehoshafat, "Za ka tafi tare da ni zuwa yaƙi a Ramot Giliyad?" Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra'ila, "Ni kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina suna kamar naka ne." 5 Yehoshafat ya cewa sarkin Isra'ila, "Idan ka yarda ka nemi shawara daga Yahweh duk abin da za ka yi tukuna." 6 Sai sarkin Isra'ila ya tara annabawa wuri ɗaya, mutane ɗari huɗu ne, ya ce da su, "In tafi in yi yaƙi a Ramot Giliyad, ko kuwa kada in tafi?" Suka ce, "Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki." 7 Amma Yehoshafat ya ce, "Ba wani annabin Yahweh ne a nan wanda za mu nemi shawara daga wurinsa? 8 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu nemi shawara daga Yahweh da zai taimaka, Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, amma sai dai na masifa." Amma Yehoshafat ya ce, "Kada sarki ya ce haka." 9 Sa'an nan sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafade, ya bada umarni, "Kawo Mikaiya ɗan Imla, yanzu a nan." 10 Ahab sarkin Isra'ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune akan gãdon sarautarsu saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya, da dukkan annabawa suna ananbci a gabansu. 11 Zedekiya ɗan Kena'ana ya yi wa kansa ƙahonin ƙarfe, ya ce, "Yahweh ya faɗi wannan: 'Tare da waɗannan za ka tunkuyi Aremiyawa har su hallaka.'" 12 Dukkan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, cewa, "Ka haura zuwa Ramot Gileyad, zaka yi nasara, domin Yahweh zai ba da ita a hannun sarki." 13 Ɗan saƙo wanda ya tafi ya kira Mikaiya ya yi magana da shi, cewa, duba yanzu, maganar annabawa abubuwa ne mai kyau ga sarki da baki ɗaya. Idan ka yarda bari maganarka ta zama kamar tasu ka faɗi abu mai kyau." 14 Mikaiya ya amsa, "Kamar yadda Yahweh ke raye, ga abin da Yahweh ya ce da ni zan faɗa." 15 Da ya zo gaban sarki, sarki ya ce da shi, "Mikaiya, mu tafi Ramot Giliyad don yaƙi, ko a'a?" Mikaiya ya amsa masa, "Ka haura za ka yi nasara, Yahweh zai ba da ita a hannun sarki." 16 Sarki ya ce masa, "Sau nawa zan neme ka da ka rantse za ka faɗa mani kome idan ba gaskiya ba, da sunan Yahweh?" 17 Mikaiya ya ce, "Na ga dukkan Isra'ila a warwatse akan tuddai, kamar tumaki waɗanda ba su da makiyayi, Yahweh ya ce, "Waɗannan ba su da makiyayi. Bari kowanne mutum ya koma gidansa da salama." 18 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba, amma sai dai na masifa?" 19 Mikaiya yace, "Saboda haka ka ji maganar Yahweh: na ga Yahweh yana zaune a kursiyansa tare da dukkan mala'ikun sama suna tsaye wajen damarsa da hagunsa. 20 Yahweh yace, 'Wa zai yaudari Ahab, ya tafi ya faɗawa Ramot Giliyad?' Ɗaya daga cikin su ya faɗi wannan, wani kuma ya faɗi abu kaza. 21 Sai wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Yahweh, ya ce, 'Ni zan yaudare shi.' Yahweh ya ce da shi, 'Ta ya ya?' 22 Sai ruhun ya amsa, 'Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukkan annabawansa. 'Yahweh ya amsa, 'Kai za ka iya yaudarsa, za ka kuma yi nasara sosai. Tafi yanzu ka yi.' 23 Duba yanzu, Yahweh ya sa ruhun ƙarya a bakin dukkan waɗannan annabawansa, Yahweh kuma ya zartar maka da masifa." 24 Sai Zedekiya ɗan Kan'ana ya zo kusa ya mari Mikaiya a kumatu, ya ce, "Wacce hanya Ruhun Yahweh ya bar ni har ya zo wurinka ya yi magana da kai?" 25 Mikaiya yace, "Duba, za ka sani a ranar nan, lokacin da ka gudu ka shiga har ƙuryar ɗaki don ka ɓuya." 26 Sarkin Isra'ila ya ce da baransa, "Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, gwamnan birni, da Yowash, ɗana. 27 Ku ce da shi, 'Sarki ya ce, a jefa wannan mutum a kurkuku a riƙa ciyar da shi da waina kaɗan da ruwan sha kaɗan, har sai na komo lafiya.'" 28 Sai Mikaiya yace, "Idan har ka dawo lafiya, Yahweh bai yi magana da ni ba." Ya ƙara da cewa, "Ku saurari wannan, dukkan ku mutane." 29 Ahab sarkin Isra'ila, da Yehoshafat sarkin Yahuda, sun tafi Ramot Giliyad. 30 Sarkin Isra'ila ya ce da Yehoshafat, "Zan bad da kamata in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafin sarautarka." Sai sarkin Isra'ila ya bad da kamarsa ya tafi wurin yaƙi. 31 Yanzu sarkin Aram ya rigaya ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa su talatin da biyu, cewa, "Kada ku yi yaƙi da kowa komai matsayin sojojinsa. Sai dai sarkin Isra'ila kaɗai." 32 Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat sai suka ce, "Babu shakka wannan shi ne sarkin Isra'ila." Sun juya don su yi yaƙi da shi, Yehoshafat kuwa ya yi ihu. 33 Da shugabannin karusan yaƙi suka gane ba sarkin Isra'ila ba ne, sai su ka juya suka dena binsa. 34 Sai wani mutum ya shilla kibiya kawai, sai ta sami sarkin Isra'ila a tsakanin ƙafar sulkensa. Ahab ya ce da mai kora karusarsa, "Ka juya ka ɗauke ni daga yaƙin nan gama an yi mani rauni sosai." 35 A ran nan yaƙi ya yi tsanani ƙwarai, aka tallafi sarki a cikin karusarsa a gaban Aremiyawa. Ya mutu da yamma. Jinin yana fitowa daga raunin da aka yi masa yana zuba a cikin karusar. 36 A lokacin faɗuwar rana aka yi wa sojoji shelar cewa, "Kowanne mutum ya koma birninsa kuma kowanne mutum ya koma jiharsa. 37 Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, su ka bizne shi. 38 Su ka wanke karusarsa a tafkin Samariya, karnuka su ka lashe jininsa (wannan shi ne wurin da karuwai su ke yin wanka a tafkin) kamar yadda Yahweh ya furta. 39 Game da sauran al'amuran Ahab da dukkan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da biranen da ya gina, ba suna rubuce a littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 40 Ahab ya yi barci tare da kakaninsa, Ahaziya ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa. 41 Yehoshafat ɗan Asa ya fara sarauta a Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra'ila. 42 Yehoshafat yana da shekaru talatin da biyar sa'ad da ya fara sarauta, ya yi sarauta a Yerusalem yana da shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba 'yar Shilhi. 43 Ya yi tafiya cikin hanyoyi irin na Asa, mahaifinsa; bai karkace daga gare su ba; ya yi abin da dai-dai a fuskar Yahweh. Duk da haka ba a ɗauke wuraren tsafi na tuddai ba. Mutanen sun ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a tuddan. 44 Yehoshafat ya yi zaman salama da sarkin Isra'ila. 45 Sauran ayyuka game da Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, ba suna rubuce a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 46 Ya kori sauran karuwai daga ƙasar waɗanda suna nan tun zamanin mahaifinsa Asa. 47 Babu sarki a Idom, amma wakili ne ya yi mulki a wurin. 48 Yehoshafat ya yi jiragen ruwa, za su tafi Ofir domin zinariya, amma ba su iya tafiya ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon Geber. 49 Sai Ahaziya ɗan Ahab ya ce da Yehoshafat, "Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage." Amma Yehoshafat bai yarda ba. 50 Yehoshafat ya yi barci tare da kakaninsa aka bizne shi a wurin su a birnin Dauda, kakansa; Yahoram ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa. 51 Ahaziya ɗan Ahab ya fara sarauta a kan Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya yi sarauta shekara biyu a Isra'ila. 52 Ya yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh, ya yi tafiya ta hanyar mahaifinsa, a cikin hanyar mahaifiyarsa, da hanyar Yerobowom ɗan Nebot, wanda ya sa Isra'ila yin zunubi. 53 Ya bauta wa Ba'al ya yi masa sujada, ya kuma tsokani Yahweh na Isra'ila ya yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi.

Littafin Sarakuna Na Biyu
Littafin Sarakuna Na Biyu
Sura 1

1 Mowab ta tayar wa Isra'ila a bayan mutuwa Ahab. 2 To sai Ahaziya ya faɗo daga sakatar gidan samansa a Samariya, har ya yi rauni. Sai ya aika 'yan saƙo ya ce da su, "Ku je ku tambayi Ba'al Zebub, allahn Ekron, ko zan warke daga wannan raunin." 3 Amma mala'ikan Yahweh yace da Iliya Batishbe, "ka tashi ka je ka sadu da 'yan saƙon sarkin Samariya, ka tambaye su, ko domin ba Allah ne a Isra'ila shi ya sa kuka je kuka tuntuɓi Ba'al Zebub, allahn Ekron? 4 Domin haka Yahweh ya ce, ba za ka sauko daga wannan gadon da ka hau ba; a maimakon haka za ka mutu.'"' Daga nan sai Iliya ya tafi. 5 Bayan 'yan saƙon sun dawo wurin Ahaziya, sai ya ce da su, "Meyasa ku ka dawo?" 6 suka ce da shi wani mutum ne ya zo ya gamu da mu ya ce mana, ku koma wurin wanda ya aiko ku ku ce da shi, "Yahweh ya faɗi wannan; Ashe babu Allah ne a Isra'ila da ka aika 'yan saƙo Ekron su tambayi Ba'al Zebub? saboda haka ba za ka tashi daga gadon jinyarka ba, a maimakon haka hakika zaka mutu.""" 7 Ahaziya yace da 'yansaƙonsa "wanne irin mutum ne shi, mutumin da ya zo wurinku ya faɗa muku wannan magana"? 8 Suka ce da shi yana saye da rigar da a ka yi da gasusuwa da kuma ɗammara ta fata a kwankwasonsa," sai sarkin ya amsa ya ce Iliya ne Batishbe." 9 Sai sarki ya aika jami'ai da sojoji hamsin wurin Iliya. Jami'an suka je wurin Iliya a inda ya ke zaune a saman dutse. Jami'an suka yi magana da shi cewa, "Kai mutumin Allah, sarki ya ce ka sauko ƙasa." 10 Iliya ya amsa ya ce da jami'an, "In ni mutumin Allah ne, bari wuta tasauko daga sama ta ƙone mutanenku guda hamsin." Wuta ta sauko daga sama ta ƙone mutanensa hamsin tare da shi. 11 Sai sarki Ahaziya ya sake yin aike wurin Iliya da wata runduna ta mutum hamsin tare da hafsa. shi ma wannan hafsan ya sake cewa da Iliya, "Kai mutumin Allah, sarki ya ce ka sauko da sauri." 12 Iliya ya amsa ya ce da su, in ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta ƙone ku tare da mutanenka guda hamsin." Sai wuta ta sake saukowa daga sama ta ƙone shi tare da mutanensa guda hamsin. 13 Sarki kuma ya sake aikawa da ƙungiya ta uku tare da mazaje hamsin mayaƙa. wannan hafsan sai ya je ya durƙusa a gwiwarsa a gaban Iliya, ya roƙe shi ya ce da shi, "kai mutumin Allah ina roƙonka bari raina da na waɗannan sojoji hamsin ya sami daraja a gabanka. 14 Hakika wuta ta sauko daga sama ta ƙone rundunoni guda biyu na farko tare da hafsoshinsu, amma yanzu ina roƙo bari raina ya zama da daraja a gabanka." 15 Sai mala'ikan Yahweh yace da Iliya, "Ka sauka ƙasa tare da shi. kada ka ji tsoronsa." Sai Iliya ya tashi ya sauka ya tafi tare da shi zuwa wurin sarki. 16 Can sai Iliya ya ce da Ahaziya, "Wannan shi ne abin da Yahweh ya ce, 'Ka aika manzanni su tambayi Ba'al Zebub allan Ekron. Shin domin ba bu Allah ne a Isra'ila wanda zaka tambaya domin samun sadarwa? to yanzu hakika ba zaka sauko daga gadon da ka hau ba hakika za ka mutu." 17 Don haka sarki Ahaziya ya mutu bisa maganar Yahweh wadda Iliya ya furta. Sai Yorom ya gaji sarautarsa, a shekara ta biyu ta Yehoram ɗan Yehoshafat sarkin Yahuda, saboda Ahaziya ba shi da ɗa. 18 Game kuma da sauran abubuwa game da Ahaziya, ashe ba a rubuta su a littafin ayyukan sarakunan Isra'ila ba?

Sura 2

1 To sai ya zama a lokacin da Yahweh zai ɗauki Iliya zuwa sama ta guguwa, da Iliya ya rabu da Elisha zuwa Gilgal. 2 Iliya ya ce da Elisha "ka jira nan ina roƙonka domin Yahweh ya aike ni zuwa Betel, Elisha ya ce da shi "Muddin Yahweh na raye, kana kuma raye, ba zan bar ka ba." To sai suka tafi Betel tare. 3 "Ya'yan annabawa da ke a Betel suka zo wurin Elisha suka ce da shi, Ko ka san Yahweh zai ɗauke shugabanka daga gare ka yau?" Elisha ya amsa masu, i na sani, amma kada ku yi magana tukuna." 4 Iliya ya ce da shi, Elisha ka jira a nan, Domin Yahweh ya aike ni Yeriko." Sai Elisha ya amsa, "Muddin Yahweh na raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba." Domin haka suka tafi Yeriko. 5 Sai 'ya'yan annabawa da ke a Yariko suka zo wurin Elisha suka ce da shi, "Ko ka san cewa yau Yahweh zai ɗauke shugabanka da ga gare ka? "Elisha ya amsa, "I na sani, amma ka da ku yi maganar tukuna." 6 Sai Iliya ya ce da shi, "Ka tsaya nan, domin Yahweh ya aike ni Yodan.'" Elisha ya amsa, Muddin Yahweh na raye, kai kuma kana raye, Ba zan rabu da kai ba." domin haka su biyun suka tafi. 7 Can an jima sai 'ya'yan annabawa hamsin suka tsaya a gefensu da ɗan nisa su kuma biyun suka tsaya a gefen Yodan. 8 Iliya ya cire tufafinsa, ya naɗe shi sai ya bugi ruwa da shi. sai rafin ya rabu biyu ta kowanne gefe su biyu suka taka sandararriyar ƙasa suka ƙetare. 9 Bayan sun ƙetare, sai Iliya ya ce da Elisha, "ka roƙi abin da zan yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka." Elisha ya amsa, ina roƙo a ba ni riɓi biyu na ruhunka ya sauko a kaina." 10 Iliya ya amsa, "Ka roƙi abu mai wuya. amma duk haka, in ka gan ni a lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, wannan zai faru sabo domin ka, amma in ba haka ba, ba zai faru ba." 11 Da suka ƙara tafiya suna magana, sai ga karusai na wuta da dawakai na wuta suka baiyana, waɗanda suka raba tsakanin su, Iliya ya tafi sama ta guguwa. 12 Da Elisha ya gani ya yi kuka, ya ce "Babana, Babana, karusai na Isra'ila da mahaya dawakansu!" Bai ƙara ganin Iliya ba, sai ya ɗauki tufafinsa ya keta su biyu. 13 Sai ya ɗauki alkyabar Iliya da ta faɗo masa, ya koma ya tsaya a bakin Yodan. Ya bugi ruwan da tufafin Iliya wanda ya faɗo ya ce, "Ina Yahweh, Allah na Iliya?" 14 Bayan ya bugi ruwan sai ruwan ya rabu biyu ta kowanne gefe sai Elisha ya ƙetare. 15 Lokacin da 'ya'yan annabawa da ke Yeriko suka ga ya ƙetaro daga wurinsu, suka ce "Ruhun Iliya ya sauko akan Elisha!" Sai suka zo domin su tare shi, suka sunkuyar da kawunansu a ƙasa a gabansa. 16 Suka ce da shi, Duba yanzu a cikin barorinka akwai mazaje hamsin majiya ƙarfi. Ka bar su su je su nemo shugabanka, ƙila ko Ruhun Yahweh ya ɗauke shi ya kai shi bisa wasu duwatsu, ko kuma waɗansu kwarurruka." Elisha ya amsa ya ce kada ku aike su." 17 Amma bayan sun matsa masa sai ya ji nauyi, ya ce "ku aike su." Suka aiki mazaje hamsin suka yi ta nema har kwana uku amma basu same shi ba. 18 Suka dawo wurin Elisha, a lokacin da yake a Yeriko, sai ya ce da su, "Ashe ban ce da ku kada ku je ba'?" 19 Mutanen birnin suka ce da Elisha, "Duba muna roƙon ka, halin da muke ciki a garin nan yana da faranta rai sosai kamar yadda shugabana ya gani, amma ruwan ba shi da kyau ƙasar kuma ba ta bada hatsi." 20 Elisha ya amsa, "Ku samo mini sabon daro ku sa gishiri a cikinsa," domin haka suka kawo masa daro. 21 Sai Elisha ya fita ya tafi mafitar ruwan rafin ya sa gishirin a cikinsa; sai ya ce ga abin da Yahweh ya ce, na warkar da waɗannan ruwaye. daga yanzu ba za a sami mutuwa ko rashin 'ya'ya ba a cikin ƙasar.'" 22 Domin haka ruwan ya gyaru har ya zuwa yau, ta wurin maganar Elisha. 23 Sai ya tafi can zuwa Betel. Lokacin da yake tafiya akan hanya, sai samari suka fito daga birni suka yi masa ba'a; suka ce da shi, "Kai mai saiƙo ka tafi, kai mai saiƙo ka tafi!" 24 Sai Elisha ya duba gefensa ya gan su; Sai ya yi kira ga Yahweh ya la'antasu. Sai matan damisa guda biyu suka fito daga kogo suka raunata samari guda arba'in da biyu. 25 Daga nan sai Elisha ya bar wurin ya tafi Tsaunin Karmel, daga can kuma sai ya koma Samariya.

Sura 3

1 A shekara ta sha takwas ta Yohoshafat sarkin Yahuda, Yoram ɗan Ahab ya fara mulkin Isra'ila a Samariya; ya yi mulki na shekaru sha biyu. 2 Ya yi abin da ke mugu a gaban Yahweh, amma ba kamar mahaifinsa da mahaifiyarsa ba; domin ya kawar da masujadar Ba'al da mahaifinsa ya gina. 3 Duk da haka ya riƙe zunubin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi, bai kauce daga gare su ba. 4 Sai Mesha sarkin Mowab ya yi sausayar tumaki. Ya ba sarkin Isra'ila raguna 100,000 da kuma fatun raguna 100,000. 5 Amma bayan Ahab ya mutu, sai sarkin Mowab ya tayar wa sarkin Isra'ila. 6 Domin haka sarki Yoram ya gudu daga Samariya a wancan lokacin domin ya shirya sojojin Isra'ila domin yaƙi. 7 Sai ya aika da saƙo ga Yohoshafat sarkin Yahuda, cewa, Sarkin Mowab ya tayar mani. Ko za ka tafi tare da ni yaƙi gãba da Mowab?" Yehoshafat ya amsa, "Zan je. Ni ma kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina kamar dawakanka ne." 8 Sai ya ce, "Ta wacce hanya zamu kai masu hari?" Yehoshafat ya amsa, "Ta hanyar jejin Idom." 9 To sai sarakunan Isra'ila da Yahuda dana Idom suka yi ta kai da kawowa har tsawon kwanaki bakwai. Babu ruwan sha domin sojojinsu, babu kuma domin dawakansu ko kuma sauran dabbobi. 10 To sai sarkin Isra'ila ya ce, Me kenan? ko Yahweh ya tattaro sarakuna guda uku ya bashe su a hannun Mowab ne?" 11 Amma Yehoshafat ya ce, Ko babu wani annabin Yahweh ne, da zamu tambayi Yahweh ta wurinsa?" Sai ɗaya daga cikin barorin sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Eleisha ɗan Shafat yana nan, shi ne ya zuba ruwa a hannun Iliya." 12 Yehoshafat ya ce Maganar Yahweh na tare da shi." Domin haka Yehoshafat sarkin Isra'ila da sarkin Idom suka tafi wurinsa. 13 Elisha yace da sarkin Isra'ila, Me zan yi da kai? Ka tafi wurin annabawan mahaifinka da mahaifiyarka." Sai sarkin Isra'ila ya ce da shi, A'a domin Yahweh ya kira waɗannan sarakuna guda uku tare domin ya bashe su a hannun Mowab." 14 Elisha ya amsa, Muddin Yahweh na raye a gaban wanda nake tsaye, tabbas in da ba domin ina ganin darajar kasancewar Yehoshafat sarkin Yahuda ba, da ba zan ji ku ko in dube ku ba. 15 Amma yanzu ka kawo mani makaɗi."Sai mai kiɗa ya yi kiɗa, sai hannun Yahweh ya zo kan Elisha. 16 Ya ce Yahweh ya faɗi wannan, 'Ka sa tsirai su fito daga wannan kwarin.' 17 Domin Yahweh ya faɗi wannan, Ba zaka ga iska ba, ko kuma ka ga ruwan sama ba, amma wannan rafin zai cika da ruwa, zaku kuma sha, kai da bisashenka da dukkan dabbobinka.' 18 Wannan abu ne mai sauƙi a gaban Yahweh, Zai kuma ba ka nasara akan Mowabawa. 19 Za ka kai hari akan ƙayatatcen birni da kowanne birni ku sare kowacce bishiya mai kyau, ku kuma busar da kowanne wuri mai fid da ruwa, ku kuma mayar da kowanne wuri kufai da duwatsu." 20 Da safe a kusan lokacin miƙa hadaya, sai ga ruwa daga wajejen Idom; sai ƙasar ta cika da ruwa. 21 To bayan duk Mowabawa sun ji cewa sarakuna sun zo su yaƙe su, sai suka tattara kansu, duk waɗanda kan iya ɗaukar makami, sai suka tsaya akan iyaka. 22 Suka tashi da sassafe rana kuma ta haskaka. Da Mowabawa suka ga ruwa kusa da su, ya zama ja kamar jini. 23 Sai suka ce "Wannan jini ne! Hakika an hallaka sarakuna, sun kuma karkashe juna! To yanzu Mowab, ku mu je mu kwashe su ganima!" 24 Bayan sun zo sansanin Isra'ilawa, Isra'ilawa suka ba su mamaki suka hari Mowabawa, waɗanda suka tsere daga gabansu. Sojojin Isra'ila suka kori Mowabawa daga ƙasar, suka karkashe su. 25 Suka rushe biranen, da kuma duk wani yankin ƙasa kowannen su ya dinga tura dutse har sai da suka rufe birnin suka cike kowanne kwari na ruwa, suka cinye kowanne ɗan itaciya. Amma sojojin saye da kayan yaƙi suka sake kai hari a kansa. 26 Bayan sarki Mesha na Mowab ya ga ya yi rashin nasara, sai ya ɗauki mayaƙa masu sara domin su hari sarkin Idom, amma suka kasa. 27 Sai ya ɗauki babban ɗansa, wanda zai yi sarauta bayansa, ya miƙa shi a matsayin baiko na ƙonawa akan ganuwa. Domin haka aka sami babbar hasala gãba da Isra'ila, sojojin Isra'ila kuma suka rabu da sarki Mesha suka koma ƙasarsu.

Sura 4

1 Sai matar ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa ta zo tana kuka da Elisah, tana cewa, "Baranka mai gidana ya mutu, kuma ka sani baranka ya ji tsoron Yahweh. To wanda ke binsa bashi ya zo ya kwashe 'ya'yana maza guda biyu su zama bayinsa.' 2 'Sai Elesha ya ce da ita "Me ki ke so in yi maki? Ki faɗa mani abin da ki ke da shi a cikin gida? "Ta ce, baiwarka ba ta da komai a cikin gida, sai 'yar tukunya ɗaya ta mai." 3 Sai Elisha yace, "Ki je ki aro tuluna daga maƙwabtanki, tulunan da ba komai a ciki. Ki aro gwargwadon yadda za ki iya arowa. 4 Dole ne ki shiga ɗaki ki kulle ƙofa da ke da iyalanki sai ki zuzzuba mai a cikin dukkan tulunan; sai ki kawar da waɗanda suka cika." 5 Sai ta bar wurin Elesha ta kulle ƙofa ita da 'ya'yanta suka kawo mata tulunan, ta kuma cika su da mai. 6 Da tulunan suka cika, ta ce da ɗanta "Ka ƙaro mani wani tulun." Amma ya ce da ita, "Babu sauran tuluna." Sai man ya dena tsiyayowa. 7 Sai ta zo ta faɗawa damutumin Allah. Ya ce "Je ki sayar da man; ki biya bashinki, sauran sai ki gudanar da rayuwarki tare da 'ya'yanki da shi." 8 Wata rana Elisha ya je Shunem inda wata mata mai muhimmanci ke zama; Ta roƙe shi ya ci abinci tare da ita. Sau da dama Elisha yakan wuce ta wurin, ya kan bi ta wurin ya ci abinci. 9 Sai matar ta ce da mijinta, "Duba, yanzu na gane wannan mutum mai tsarki ne na Allah wanda yake wucewa kullun. 10 Sai mu yi masa ɗan ɗaki a saman rufi domin Elisha, sai mu sa gado a cikin ɗakin da teburi da kujeru da fitila. Domin in ya zo wurin mu, sai ya zauna a can." 11 To da ranar ta zo da Elisha ya tsaya a can, sai ya shiga can ya huta. 12 Elesha yace da Gehazi baransa, "Ka kira wannan Bashumaniye." Bayan ya kira ta, ta tsaya a gabansu. 13 Elisha yace da shi, "Ka ce da ita, kin sha duk wannan fama domin ki kula da mu. Me zamu yi maki? Ko ma yi magana da sarki ko kuma da Kwamandan soja?'" Ta amsa "Ina zama a cikin mutanena." 14 14 Domin haka Elisha yace,"To me za mu yi mata?" Gehazi ya amsa, "Hakika ba ta da ɗa Mai gidanta kuma ya tsufa." 15 Domin haka Elisha ya amsa, "Kira ta." Bayan ya kira ta, sai ta tsaya a ƙofa. 16 Elisha ya ce shekara mai zuwa war haka za ki riƙe ɗa." Ta ce, "A'a ya shugabana da kuma mutumin Allah, kada ka yi wa baiwarka ƙarya." 17 Amma matar ta yi ciki sai ta haifi ɗa a dai-dai lokacin da Elisha ya faɗa mata. 18 Bayan yaron ya yi girma, sai ya tafi wurin mahaifinsa wata rana, wanda ya ke tare da masu girbi. Sai ya ce da babansa, "Kaina, kaina." 19 Mahaifinsa ya ce da bayinsa, "Ku kai shi wurin mahaifiyarsa." 20 Lokacin da bayin suka ɗauki yaron suka kawo shi wurin mahaifiyarsa, yaron ya zauna a gwiwarta har tsakar rana daga nan sai ya mutu. 21 Sai matar ta tashi ta kwantar da yaron a gadon mutumin Allah, ta kulle ƙofa, ta fita. 22 Ta kira maigidanta, ta ce, "Ina roƙo ka aiko mani da ɗaya daga cikin bayi da kuma ɗaya daga cikin jakunan domin in yi sauri zuwa wurin mutumin Allah sa'an nan in dawo." 23 Maigidanta ya ce donme ki ke so ki je wurinsa yau? Ba sabon wata ba ne ko kuma Asabar ba. "Sai ta amsa, "Komai zai yi dai-dai. 24 " Sai ta ɗaura wa jaki sirdi ta ce da bayinta, "Ku kora shi da sauri; kada ku sausauta har sai na ce ku yi haka." 25 To sai ta tafi ta je wurin mutumin Allah a Tsaunin Karmel. Lokacin da mutumin Allah ya hange ta daga nesa, sai ya ce da Gehazi baransa, "Duba ga matar nan Bashunamiya tana tafe. 26 Ka ruga a guje ka tambaye ta, ko komai lafiya yake game da ita da maigidanta da kuma ɗanta?"' Ta amsa, "Ba damuwa." 27 Lokacin da ta zo wurin mutumin Allah akan dutsen sai ta kama ƙafafunsa, sai Gehazi ya zo zai ture ta amma mutumin Allah ya ce "Ka ƙyale ta, domin hankalinta a tashe yake Yahweh kuma ya ɓoye mani al'amarin, bai kuma faɗa mani komai ba." 28 Daga nan sai ta ce, "Na roƙe ka ɗa ne, ya shugaba na, Ashe ban ce kada ka yaudare ni ba?" 29 Sai Elisha ya ce da Gehazi, "Maza shirya ka riƙe sandana a hanunka. Ka je gidanta. "In ka gamu da wani in ya gaishe ka kada ka amsa, kada ka amsa masa. Ka ɗora sandana a fuskar yaron." 30 Amma mahaifiyar yaron ta ce, "Muddin Yahweh na raye, kana kuma raye, ba zan bar ka ba."Saboda haka Elisha ya tashi ya bi ta. 31 Gehazi ya ruga kafin su kai ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma yaron bai iya ji ko kuma ya yi magana ba. Saboda haka Gehazi ya dawo ya gamu da su, ya ce da Elisha "Yaron bai farfaɗo ba." 32 Lokacin da Elisha ya shiga gidan yaron a mace yake, yana kuma kwance akan gado. 33 Sai Elisha ya shiga ya kulle ƙofa da yaron ya yi addu'a ga Yahweh. 34 Sai ya hau ya kwanta akan yaron; ya sa bakinsa a bakinsa, idonnsa a idonsa, hannunsa a hannunsa. Sai ya miƙe akan yaron sai jikinsa ya yi ɗumi. 35 Sai Elisha ya tashi ya zagaya ɗakin ya sake kwantawa akan yaron ya miƙe, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, sai ya buɗe idonsa! 36 Sai Elisha ya kira Gehazi ya ce da shi "Ka kira Bashunamiye!" Sai ya kira ta, da ya kira ta, da ta shiga ɗakin sai Elisha ya ce da ita "Ɗauki ɗanki." 37 Sai ta kwanta a ƙafafunsa fuskarta a ƙasa, daga nan sai ta ɗauki ɗanta ta fita. 38 Sai Elisha ya sake zuwa Gilgal. Akwai yunwa kuma a ƙasar, 'ya'yan annabawa kuma na zaune a gabansa. Ya ce da baransa. "Ka ɗora babbar tukunya ka dafa miya domin 'ya'yan annabawa." 39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura domin ya samo ganyayen abinci sai ya samon ganyen inabi mai guba ya tara shi da yawa ya cika haɓar rigarsa, Suka yayyanka suka zuba a cikin abincin, amma ba su san irin su ba. 40 Sai suka zuba masu abinci su ci, can suna cikin cin abincin sai suka yi kuka suka ce "Da guba a cikin tukunyar!" Domin haka basu ƙara cin abincin ba. 41 Amma Elisha ya ce "Ku kawo mani gãri." Sai ya zuba a tukunyar ya ce, ku zuba wa mutane su ci, daga nan ba a sami wata guba a cikin tukunyar ba. 42 Sai wani mutum ya zo daga Ba'al Shalisha wurin mutumin Allah ya kawo masa curin gurasar sha'ir guda ashirin a cikin jakarsa daga cikin girbinsa, da kuma sababbin zargankun hatsi. Ya ce, "Ka ba mutane wannan domin su ci." 43 Bayinsa suka ce "Ƙaƙa zamu ba da wannan ga mutane ɗari?" Amma Elisha yace "Ku ba su wannan domin su ci, domin Yahweh ya ce, 'Za su ci su kuma bar saura.'" 44 Sai bayinsa suka ajiye shi a gabansu; suka ci suka bar saura, kamar yadda maganar Yahweh ta alkawarta.

Sura 5

1 Na'aman kwamadan sojan sarkin Aram, yana da girma da ƙima a gun shugabansa, saboda shi Yahweh yakan ba Aram nasara. Hakannan shi mutum ne mai ƙarfi da kuma ƙarfin halin, amma shi kuturu ne. 2 Aremiyawa suka kai hari runduna runduna suka ɗauki wata yarinya daga ƙasar Isra'ila, ta yiwa matar Na'aman hidima. 3 Sai yarinyar ta ce shugabarta, "Na so a ce shugabana tare yake da annabin da ke a Samariya! To zai warkar da shugabana daga kututtarsa." 4 Sai Na'aman ya je ya faɗa wa sarki abin da yarinyar da ta zo daga ƙasar Isra'ila ta faɗa. 5 Saboda haka sarkin Aram ya ce, "Yanzu ka tafi, zan kuma aika da wasiƙa zuwa ga sarkin Isra'ila." Sai Na'amam ya tafi ya ɗauki talanti goma na azurfa, da tsabar zinariya dubu shida, da kuma sauyin sutura guda goma. 6 Hakannan ya kai wa sarkin Isra'ila wasiƙar da ta ce, Lokacin da wannan wasiƙa ta zo wurinka, za ka ga cewa na aiko da barana Na'aman zuwa wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa." 7 Bayan sarkin Isra'ila ya karɓi wasiƙar ya karanta ta sai ya keta tufafinsa ya ce, "Ni Allah ne da zan iya rayarwa ko in kashe, da wannan mutum zai so in warkar da mutum daga kuturtarsa? Da alama yana neman jayayya da ni." 8 To bayan Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya ce "Me yasa ka keta tufafinka? Ka bar shi ya zo wurina yanzu zai kuma sani akwai annabi a Isra'iula." 9 Sai Na'aman ya je da karusarsa ya tsaya a ƙofar gidan Elisha. 10 Elisha ya aika masa da 'yan saƙo gare shi cewa. "Ka je ka yi nutso sau bakwai a kogin Yodan, jikinka zai dawo, zaka kuma tsaftata. 11 Amma Na'aman ya fusata ya tafi ya ce, "Duba na yi zaton tabbas zai zo wurina ya tsaya ya kira sunanYahweh Allahnsa, ya kuma ɗaga hannunsa a wurin ya warkar da kuturtar tawa, 12 Ashe kogunan Abana da na Farfar wato kogunan Damaskus, basu fi duk waɗannan ruwayen na Isra'ila tsafta ba?" Sai ya juya cikin matuƙar hasala. 13 Sai bayin Na'aman suka zo kusa suka yi magana da shi, "Babana, in da annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya ashe ba za ka yi ba? Amma me ya fi wannan da ya ce maka, "Ka yi nutso ka tsarkaka?'" 14 Daga nan sai ya gangara ya je ya yi nutson sau bakwai a kogin Yodan ya yi biyayya ga ummarnin mutumin Allah. Sai jikinsa ya dawo kamar na jariri sabuwar haihuwa, ya kuma warke. 15 Sai Na'aman ya koma wurin mutumin Allah shi da rundunarsa, ya ce "Duba yanzu na sani babu wani Allah a duk duniya sai a Isra'ila. To yanzu sai ka karɓi kyautai daga wurin baranka", 16 Amma Elisha ya ce "Muddin Yahweh wanda nake tsaye a gabansa na raye ba zan karɓi komai ba," Na'aman ya matsa wa Elisha ya karɓa amma Elisha ya ƙi karɓa. 17 To sai Na'aman yace, "In ba za ka karɓa ba sai a ba baranka kayan takarkari na kayan alatu, domin daga yanzu baranka ba zai miƙa hadaya ta ƙonawa ga wani allah ba sai ga Yahweh. 18 Ka gafarci baranka, wato a lokacin da sarkina ya je gidan Rimmon domin ya yi sujada a can, ya kuma lashe hannuna na kuma sunkuya a gidan Rimmon, ina roƙon Yahweh ya gafarci baranka akan wannan." 19 Elisha yace da shi, "Ka tafi da salama." Sai Na'aman ya tafi. 20 Ya ɗan yi nisa kenan, lokacin da Gehazi baran Elisha mutumin Allah ya ce a ransa, Duba, shugabana ya kyale Na'aman ɗin nan mutumin Aremiya bai karɓi kyautai da ya ya kawo daga hannunsa ba. Muddin Yahweh na raye zan bi shi in karɓi wani abu daga wurinsa." 21 Sai Gehazi ya bi Na'aman. Da Na'aman ya ga wani na biye da shi, sai ya dirgo daga karusa domin ya tare shi ya ce, "In ce ko lafiya?" 22 Gehazi yace, "Lafiya ƙalau. Ubangidana ne ya aiko ni, cewa, 'Duba, yanzunan ya yi baƙi daga ƙasa mai duwatsu ta Ifiraim samari biyu na 'ya'yan annabawa. Ina roƙo ka ba su jaka biyu na zinariya, da kayan alfarma guda biyu." 23 Na'aman ya amsa, "Ina murna sosai in ba ka talanti biyu." Na'aman ya bukaci Gehazi kuma ya ɗaure talanti biyu na azurfa a cikin jaka biyu, da riguna biyu, sai ya ɗora su akan bayinsa biyu, waɗanda ke ɗauke da jaka na azurfa a gaban Gehazi. 24 Bayan Gehazi ya zo wurin duwatsu, sai ya karɓe jaka na azurfa daga hannunsu ya ɓoye su a cikin gida; ya sallami mutanen, suka tafi. 25 Bayan Gehazi ya shiga ciki ya tsaya a gaban shugabansa, Elisha yace da shi, "Daga ina ka dawo, Gehazi?" Ya amsa, "Baranka bai je ko'ina ba." 26 Elisha yace da Gehazi, "Ashe ruhuna baya tare da kai ne a lokacin da mutumin ya juyo da karusarsa domin ya gamu da kai? Ko wannan ne lokacin karɓar kuɗi da sutura da man zaitun da garkar inabi, da tumaki da bijimai, da bayi maza da mata? 27 To kuturtar Na'aman za ta koma kanka da kuma zuriyarka har abada." Sai Gehazi ya fita daga gabansa a kuturce fari fat kamar auduga.

Sura 6

1 'Ya'yan annabawa suka ce da Elisha, "Wurin da muke zama tare da kai ya gaza mana dukkanmu. 2 Muna roƙo ka bar mu mu je Yodan, sai kowannen mu ya saro itace a can, sai mu gina wurin da zamu zauna." Elisha ya amsa, "To ku je" 3 Ɗaya daga cikinsu ya ce, "Ina roƙo ka tafi tare da barorinka." Elisha ya amsa "za ni." 4 To sai ya tafi tare da su, a lokacin da suka fara saran itatuwan. 5 Amma a lokacin da ɗayansu ke sara sai kan gatarin ya faɗa a cikin ruwa; sai ya yi waiyo ya ce "Ya shugabana, aro shi aka yi!" 6 Sai mutumin Allah yace, "A ina ya faɗa?" Mutumin ya nuna wa Elisha wurin. Sai ya saro 'yar tsafga, ya jefa ta cikin ruwa, sai ta sa ƙarfen ya ɗago sama. 7 Elisha yace, "Ka ɗauko shi." Sai mutumin ya ɗauko shi. 8 Sai sarkin Aram ya shirya kai hari kan Isra'ila. ya tuntuɓi barorinsa, cewa, "Sansanina ga yadda zai kasance da kuma inda zai kasance." 9 Sai mutumin Allah ya aika wurin sarkin Isra'ila, cewa, "Ka yi hankali kada ka wuce ta wurin nan, domin Aremiyawa suna gangarawa can." 10 Sai sarkin Isra'ila ya aika da saƙo can game da abin da mutumin Allah ya faɗa masa ya kuma gargaɗe shi. Ba sau ɗaya ko sau biyu ba duk lokacin da sarki zai wuce wurin yana cikin tsaro. 11 Sarkin Aram ya da mugame da wannan gargaɗi, sai ya kira bayinsa ya ce da su, "Ba za ku faɗa mani wane ne daga cikinmu ya ke goyon bayan sarkin Isra'ila ba" 12 Sai ɗaya daga cikin bayin ya ce, "Ba haka ba ne shugabana, sarki, domin Elisha annabi na Isra'ila ne ya faɗawa sarkin Isra'ila maganar da ka faɗa a ɗakin kwananka!" 13 Sarki ya amsa, "ku je ku duba inda Elisha yake domin in aika da mutane su kamo shi." An faɗa masa, "Duba yana a Dotan." 14 Domin haka sarki ya aika mahaya dawakai da karusai da sojoji masu yawa zuwa Dotan. Suka zo da dare suka kewaye birnin. 15 Da baran mutumin Allah ya tashi da asuba ya fita waje, sai ga rundunonin sojoji da karusai da mahaya dawakai sun kewaye birnin. Baransa ya ce da shi, "Ya shugabana! Me za mu yi?" 16 Elisha ya amsa, "Kada ka ji tsoro, domin waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su." 17 Elisha ya addu'a ya ce, "Yahweh, ina roƙonka ka buɗe idanunsa domin ya gani." Sai Yahweh ya buɗe idanun baran, Sai ya ga tsaunin na cike da dawakai da karusai na wuta kewaye da Elisha! 18 Lokacin da Aremiyawa suka zo gare shi, Elisha ya yi addu'a ga Yahweh ya ce, "Ka bugi mutanen nan da makanta, ina roƙonka." Sai Yahweh ya makantar da su, kamar yadda Elisha ya roƙa. 19 Sai Elisha ya ce da Aremiyawa, "Ba wannan ba ce hanyar, ba kuma wannan ba ne birnin. Ku biyo ni zan kai ku wurin mutumin da ku ke nema." Sai ya kai su Samariya. 20 Bayan sun zo Samariya, Elisha yace, "Yahweh, ka buɗe idanun mutanen nan domin su gani." Yahweh ya buɗe idanunsu, sai suka gan su a tsakiyar birnin Samariya. 21 Da sarkin Isra'ila ya gan su ya ce da Elisha "'Babana, in kashe su ne? In kashe sun ne?" 22 Elisha ya amsa, "Kada ka kashe su. Ko ka kashe bayin da ka kama da bãkanka da kuma takobinka? Ka ba su gurasa da ruwa domin su ci su sha, sai su tafi wurin shugabansu." 23 Sai sarki ya shirya abinci sosai domin su, bayan su ci sun sha, sai ya sallame su, suka je wurin shugabansu. Waɗannan ƙungiyoyin sojojin Aremiyawan ba su daɗe ba sosai a Isra'ila. 24 Bayan wannan Ben Hadad sarkin Aram ya tara dukkan sojojinsa ya kaiwa Samariya hari ya kwashe ta. 25 Domin haka aka yi babbar yunwa a Samariya. Duba sun washe ta har ana sayar da kan jaki tsaba tamanin na shekel, ana kuma sayar da kofin kashin kurciya a shekel biyar. 26 Da sarkin Isra'ila ya zo wucewa ta gefen katanga sai wata mata ta yi masa kuka, cewa, "Ka yi temako shugabana, sarki." 27 Ya ce, "Idan Yahweh bai taimake ki ba, ta yaya zan taimake ki? Ana samun wani abu ne daga masussuka ko kuma daga wurin matsar ruwan inabi?" 28 Sarki ya ci gaba, "Me ke damun ki?" Ta amsa, "Wanan matar ta ce da ni, 'Ki ba ni ɗanki domin mu dafa mu ci yau, gobe kuma sai mu ci ɗana."' 29 Domin haka muka dafa ɗana mu ka cinye shi, da gari ya waye na ce da ita, "Ki bada ɗanki domin mu cinye shi, amma ta ɓoye ɗanta." 30 To bayan sarki ya ji maganar wannan mata, sai ya keta tufafinsa (yana wucewa gefen katanga) sai mutane suka gan shi saye da tufafin makoki a jikinsa. 31 Sai ya ce "Dama Allah ya yi mini haka, in har kan Elisha ɗan Shafat ya tsaya a kansa yau." 32 Amma Elisha na zaune a gidansa, dattawa kuma na zaune tare da shi. Sai sarki ya aika manzo ya zo wurinsa, amma da manzon ya zo wurin Elisha, sai ya ce da dattawan, "Dubi yadda wannan ɗan mai kisan kai ya aika a sare mani kai? Duba lokacin da manzon ya zo, kulle ƙofa kulle ƙofar a hana masa shiga. Ashe ba ƙarar sawun mai gidansa na biye da shi ba?" 33 Yana cikin yi masu magana sai ɗan saƙo ya zo wurinsa. "Sarki ya ce, "Duba wannan matsala daga wurin Yahweh ta zo. Donme kuma zan ƙara jiran Yahweh?"

Sura 7

1 Elisha yace, ka ji maganar Yahweh, wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa: gobe kamar i yanzu a ƙofar shiga Samariya za a sayar da kofin garin alkama a shekel ɗaya, awo biyu na sha'ir a shekel,'" 2 Sai hafsan da aka aiko wurin Elisha ya ce da mutumin Allah, "Ko da ma ace Yahweh zai buɗe sakatun sama, wannan abin zai faru? "Elisha ya amsa, "Duba za ka ga abin na faruwa da idonka amma ba za ka ɗanɗana ko kaɗan daga cikinsa ba." 3 To akwai mutun huɗu da ke da ciwon kuturta a wajen ƙofar birni. Sai suka cewa juna, "Domin me za mu yi ta zama a nan har mu mutu? 4 In mun ce za mu cikin birni yunwar na can, za mu kuma mutu a can. Bari mu je sansanin Aremiyawa. In sun bar mu da rai mu rayu, in kuma zamu mutu mu mutu a can, amma ko da ma mun tsaya a nan zamu mutu. To yanzu sai mu je sansanin Aremiyawa. In sun bar mu da rai to, za mu rayau, in kuma sun kashe mu mutuwa kawai zamu yi." 5 To sai suka tashi da almuru suka nufi sansanin Aremiyawa; da suka isa tsakiyar wurin ba kowa a sansanin ba ko mutun ɗaya a wurin. 6 Domin Ubangiji yasa sojojin Aremiyawa su ji ƙarar karusai da ƙarar mahayan dawakai da kuma babbar ƙarar rundunar soja, suka ce da junansu. "Sarkin Isra'ila ya yi hayar sarakunan Hitiyawa da na Masar domin su kawo mana hari." 7 Domin haka sojoji suka ruga da almuru; suka bar rumfunansu, da dawakansu, da jakunansu da sansanin kamar yadda yake suka gudu domin su tsirar da ransu. 8 Lokacin da mutanen da ke da kuturta suka shiga tsakiyar sansanin suka shiga wata rumfa suka ci suka sha, suka kwashi shekel da zinariya da azurfa da da suturu suka tafi da su suka ɓoye su suka sake dawowa suka shiga wani sansanin suka kwashi ganima daga can suka tafi suka ɓoye ta. 9 Daga nan suka ce da juna, "Ba mu yin abin da ke dai dai ba yau. wannan ranar ta kai soƙo mai daɗi ce, amma munyi shiru game da batun. In mun jira har gari ya waye za mu fuskaci horo. To yanzu, ku zo mu je mu faɗa wa dukkan gidan sarki." 10 Sai suka tafi suka kira masu tsaron ƙofar birnin. Suka faɗa masu cewa, Mun je sansanin Aremiyawa, amma ba kowa a can, ba kuma motsin kowa, amma akwai dawakai a ɗaure, da jakai a ɗaure da kuma rumfunan kamar yadda suke." 11 Daga nan sai masu tsaron ƙofofin suka baza labarin, daga nan sai aka faɗa a cikin dukkan gidan sarki. 12 Sai sarki ya tashi da dare ya ce da bayinsa, "Yanzu zan faɗa maku abin da Aremiyawa suka yi mana. Sun sani muna jin yunwa, to sai suka bar sansanin suka je suka ɓuya a cikin sauruka. Suna cewa, "in sun fito wajen birnin, zamu kama su da rai, mu shiga cikin birnin."' 13 Ɗaya daga cikin bayin sarki ya ce, "'Ina roƙonka ka bar waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka rage a birnin. Su kamar sauran yawan Isra'ila ne da suka ragu - domin da yawansu sun mutu; sai mu aike su mu gani." 14 Sai suka kwashi karusan dawakai guda biyu, sai sarki ya aike su su bi Aremiyawa cewa, "Ku je ku gani." 15 Sai suka tafi har zuwa Yodan, hanyar kuma ta cika da suturu birjik da kuma kayayyakin da Aremiyawa suka warwatsar cikin saurinsu. Sai manzannin suka dawo suka faɗawa sarki. 16 Sai mutane suka fita suka kwashi ganimar sansanin Aremiyawa. Domin haka aka sayar da awon alkama a shekel ɗaya da kuma awon sha'ir biyu a shekel, kamar dai yadda maganar Yahweh ta faɗa. 17 Sai sarki ya sa wannan hafsan da ya aika ya zama mai kula da ƙofar, sai mutane suka tattake shi a ƙofar. Ya mutu kamar yadda mutumin Allah ya faɗa, a lokacin da sarki ya zo wurinsa. 18 Haka ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya faɗa wa sarki, cewa, war haka a ƙofar shiga Samariya, za, a sayar da awo biyu na sha'ir a shekel, awo ɗaya na alkama kuma a shekel." 19 Wannan hafsan ya ce da mutumin Allah, "Duba ko da Yahweh zai sa sakatun sama su buɗe, ko wannan zai faru?" Elisha ya ce, "Duba za ka gani yana faruwa a idanunka, amma ba za ka ci daga cikinsa ba." 20 Wannan shi ne hakikanin abin da ya faru da shi, domin mutane sun tattake shi a bakin ƙofa, ya kuma mutu.

Sura 8

1 To sai Elisha ya yi magana da matar da ya komar da ɗanta da rai. Ya ce da ita, "Ki tashi, da dukkan gidanki, zauna a duk inda za ki zauna a wata ƙasa, domin Yahweh ya saukar da yunwa a wannan ƙasa har tsawo shekaru bakwai." 2 Sai matar ta tashi ta yi biyayya da maganar mutumin Allah. Ta tafi da ita da mutanen gidanta zuwa ƙasar Filistiyawa har tsawon shekaru bakwai. 3 To a ƙarshen shekaru bakwai da wannan mata ta komo daga ƙasar filistiyawa, ta je wurin sarki ta roƙe shi domin gidanta da kuma ƙasarta. 4 To sarki na magana da Gehazi baran mutumin Allah, cewa "Ina roƙo ka faɗa mini dukkan manyan abubuwan da Elisha ya yi." 5 A lokacin da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya komar da ran yaron da ya mutu, sai wannan dai matar ta zo ta roƙi sarki saboda gidanta da kuma ƙasarta. Gehazi yace, "Shugabana, sarki, ga matar da kuma ɗan nata, da Elisha ya mayar wa da rai." 6 Lokacin da sarki ya tambayi matar game da ɗanta, ta yi masa bayani. Sai sarki ya sa wani hafsa dominta ya ce, "Ka ba ta duk abin da ke nata da kuma dukkan girbin gonarta tun daga ranar da ta bar ƙasar har ya zuwa yanzu." 7 Sai Elisha ya zo Damaskus. Inda Ben Hadad sarkin Aram ke ciwo. Sai aka faɗa wa sarki cewa, "Mutumin Allah ya zo nan." 8 Sai sarki yace da Hazayel, "Ɗauki kyauta a hannunka ka je wurin mutumin Allah, ka tuntuɓi Yahweh ta wurinsa, cewa 'Ko zan wartsake daga wannan rashin lafiyar?"' 9 To sai Hazayel ya tafi wurinsa da kyauta ta kowanne abu mai kyau na Damaskus, ya ɗora wa raƙuma arba'in. Sai Hazayel ya zo ya tsaya a gaban Elisha ya ce "Ɗanka Ben Hadad sarkin Aram ne ya aiko ni gare ka, cewa 'ko zan warke daga wannan rashin lafiyar?"' 10 Elisha ya ce da shi, "Ka je ka ce da Ben Hadad, 'Hakika za ka warke; amma Yahweh ya nuna mani cewa hakika zai mutu." 11 Sai Elisha ya ƙarfafa Hazayel har sai da ya ji kunya, mutumin Allah kuma ya yi kuka. 12 Hazayel ya tambaya, "Meyasa ka yi kuka, ya shugabana?" Ya amsa, "Saboda na san irin muguntar da zaka yi wa mutanen Isra'ila. Za ka ƙone hasumayoyinsu da wuta, za ka kuma kashe samarinsu da takobi, zaka kuma daddatsa 'yan ƙananansu, za ka kuma feɗe matayensu masu juna biyu." 13 Hazayel ya masa, "Wane ne baranka, da zai yi wannan babban abu? Ai shi kare ne kawai. Elisha ya amsa, Yahweh ya nuna mani cewa za ka yi sarautar Aram. 14 Daga nan Hazayel ya rabu da Elisha ya komo wurin mai gidansa, wanda ya ce da shi "Me Elisha ya faɗa maka?" ya amsa, ya faɗa mani hakika za ka warke." 15 To washegari Hazayel ya ɗauki bargo ya tsoma shi a ruwa, ya shimfiɗa shi a kan fuskar Ben Hadad da haka ya mutu. Sai Hazayel ya zama sarki a maimakon sa. 16 A shekara ta biyar ta sarautar Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, Yahoram ya fara sarauta. Shi ɗan Yehoshafat ne sarkin Yahuda. Ya fara sarauta a lokacin da Yehoshafat ke sarautar Yahuda. 17 Yahoram yana da shekaru talatin da biyu a lokacin da ya fara sarauta, ya yi sarauta ta shekaru takwas a Yerusalem. 18 Yahoram ya bi tafarkin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi; domin ya auri 'yar Ahab a matsayin matarsa, ya kuma yi abin da ke mugu a gaban Yahweh. 19 Duk da haka, saboda baransa Dauda bai so ya hallaka Yahuda ba, tun da ya yi masa alƙawari cewa har kullum ba za a rasa wanda zai yi sarauta daga zuriyarsa ba. 20 A kwanakin Yahoram, sai Idom ta tayar wa mulkin Yahuda, suka kuma naɗa wa kansu sarki. Sai 21 Yahoram ya tsallake shi da hafsoshinsa da dukkan karusansa. Sai ya tashi da duhu ya kai hari ya washe Idomawa, waɗanda suka kewaye shi da kuma hafsoshin karusai. Sai sojojin Yaharom suka tsere gidajensu. 22 To da haka Idom ta tayar wa mulkin Yahuda har ya zuwa yau. Libna ita ma ta tayar alokaci guda. 23 To game da sauran abubuwa game da Yahoram, da duk abin da ya yi, ashe ba a rubuce suke a littafin ayyukan sarakunan Yahuda ba? 24 Yahoram ya mutu ya huta tare da ubanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dauda. Daga nan ɗansa Ahaziya ya zama sarki a madadinsa. 25 A shekara ta sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, da Ahaziya ɗăn Yehoram, sarkin Yahuda, suka fara mulki. 26 Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu lokacin da ya fara sarauta; ya yi sarautar shekara ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Ataliya; Ita 'yar Omri ce, sarkin Isra'ila. 27 Ahaziya ya bi tafarkin gidan Ahab; ya yi abin da ke mugu a gaban Yahweh, kamar dai sauran abin da Ahab ya yi, domin Ahaziya suruki ne ga gidan Ahab. 28 Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab, domin su yi yaƙi gãba da Hazayel, sarkin Aram, a Ramot Giliyad. Aremiyawa suka yi wa Yoram rauni. 29 Sarki Yoram ya koma gida domin ya warke a Yazriyel daga raunin da aka yi masa a Rama, a lokacin da ya yi yaƙi da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yahoram sarkin Yahuda, ya tafi Yezriyel domin ya ga Yoram ɗan Ahab, saboda an yi wa Yoram rauni.

Sura 9

1 Sai annabi Elisha ya kira ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa ya ce da shi, "Ka shirya domin tafiya, ka riƙe wannan 'yar kwalbar man ka tafi Ramot Giliyad 2 lokacin da ka je sai ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat ɗan Nimshi, sai ka shiga ciki ka sa shi ya tashi daga abokan taraiyarsa ka bi da shi can cikin lalloki rumfa 3 Sai ka ɗauki kwalbar ka tsiyaya masa mai aka ce Yahweh ya faɗi wannan: "Na keɓe ka ka zama sarkin Isra'ila" daga nan sai ka buɗe ƙofa ka yi sauri ka gudu, kada ka yi jinkiri. 4 Sai saurayin, wato matashin annabin, ya tafi Ramot Giliyad. 5 Da ya isa sai ga hafsoshin sojoji na zaune. Sai matashin annabin ya ce, "Na zo wurin ɗaya daga cikinku, ne hafsoshi." Yehu ya amsa, Ga wa daga cikinmu?" Matashin annabin ya amsa "Gareka, hafsa" 6 Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida, sai annabin ya zuba masa mai a kã yace da Yehu, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: 'Na keɓe ka ka zama sarki akan mutanen Yahweh, Isra'ila. 7 Dole ne ka kashe iyalin Ahab shugabannka, domin in yi ramako akan bayina annabawa, da kuma jinin dukkan bayin Yahweh waɗanda Yezebel ta kashe. 8 Domin dukkan iyalan Ahab za su lalace zan kuma datse dukkan 'ya'ya maza na zuriyar Ahab ko shi bawa ne ko kuma mai 'yanci. 9 Zan mayar da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, kamar kuma gidan Ba'asha ɗan Ahija. 10 Karnuka kuma za su ci naman Yezebel a Yezriyel kuma ba za 'a sami wanda zai bizne ta ba.'" Daga nan sai annabin ya buɗe ƙofar, ya gudu. 11 Sai Yehu ya fito waje zuwa wurin bayin shugabansa, sai ɗaya daga cikinsu ya ce da shi, "Ko dai lafiya? Meyasa wannan mahaukacin ya zo wurinka?" Yehu ya amsa musu, "Kun san irin mutumin da irin abin da ya ke faɗi." 12 Suka ce, "Wannan ƙarya ne. Ka faɗa." Yehu ya amsa, "Ya faɗa mani abu kaza da kaza, hakan nan ya ce 'Ga abin da Yahweh yace: Na kebe ka ka zama sarkin Isra'ila."' 13 Sai dukkan su suka yi sauri suka tuɓe rigarsa ta waje suka sa ta ƙarƙashin Yehu akan matakan. Suka hura kakaki suka ce, "Yehu sarki ne." 14 Ta haka Yehu ɗan Yehoshafat ɗan Nimshi suka ƙulla maƙarƙashiya kan Yoram. A lokacin, Yoram yana kare Ramot Giliyad, shi da dukkan Isra'ila, saboda Hazayel sarkin Aram, 15 amma sarki Yoram ya koma Yezriyel domin ya warke daga raunin da Aremiyawa suka yi masa, lokacin da suka yi faɗa da Hazayel sarkin Aram. Yehu yace da bawan Yoram, "In wannan shi ne ra'ayinka, to kada kowa ya tsira ya fita daga birnin, saboda aje a faɗi labarin a Yezriyel." 16 Sai Yehu ya tuƙa karusa zuwa Yezriyel; Yoram yana shaƙatawa a can. Sai Ahaziya sarkin Yahuda ya zo domin ya ga Yoram. 17 Ɗan tsaro na tsaye akan hasumaya a Yezriyel, sai ya ga rundunar Yehu da ya matso kusa; sai yace, "Na ga kungiyar mazaje na zuwa." Yoram yace, "Ka kwashi mahayin dawakai, ka aike shi wurinsu; ka ce da shi ya tambaye su 'Kuna zuwa da salama ne?"' 18 Sai ya aika mutumin akan doki ya koma ya tare shi; sai ya ce, sarki ne ya faɗi wannan: 'Kuna zuwa da salama ne?"' Sai Yehu yace, "Me zaku yi da salama? Ka juya ka biyo ni."Sai ɗan tsaron ya faɗa wa sarki, "Ɗan saƙon ya same shi, amma ba zai dawo ba." 19 Sai ya sake aikar mutum na biyu ya sake komawa akan doki, wanda ya zo wurinsu ya ce, "Sarki ya faɗi wannan: 'Kuna zuwa da salama ne?'" Yehu ya amsa "Me za ku yi da salama? ka juyo ka biyo ni." 20 Sai wannan manzon ya sake mayar da amsa, "Ya same su, amma ba zai dawo ba. Domin hanyar da ya ke tuƙa dawakan ita ce Yehu ɗan Nimshi ya bi; kuma yana tuki a sukwane." 21 Sai Yoram yace, "Ka shirya karusata." Suka shiya karusarsa, sai Yoram sarkin Isra'ila da Ahaziya sarkin Yahuda suka fita akan dawakai, kowa da karusarsa domin su gamu da Yehu. Suka same shi a mallakar Nabot Bayezriyile. 22 Da Yoram ya ga Yehu, sai ya ce, "Yehu kana zuwa da salama ne?" Ya amsa, "Wacce salama kuma ke a can bayan akin zina da maitanci na mahaifiyarka Yezebel sun yi yawa?" 23 Sai Yoram ya juya karusarsa ya tsere ya ce da Ahaziya, "Akwai tashin hankali Ahaziya." 24 Daga nan Yehu ya ɗauko bakãnsa da cikkakken ƙarfinsa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa; kibiyar ta bi ta zuciyarsa, sai ya faɗi a cikin karusarsa. 25 Sai Yehu yace da Bidkar hafsansa, "Ciro shi ka jefar da shi a filin Nabot Bayezriyile. Tuna da yadda muka bi babansa Ahab, Yahweh ya ajeye hukuncinsa a kansa: 26 'Jiya na ga jinin Nabot da kuma jinin 'ya'yansa - inji Yahweh - kuma hakika zan sa ka biya shi a wannan fili - inji Yahweh. Yanzu, sai ka ciro shi ka jefar da shi a filin, bisa ga maganar Yahweh." 27 Da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga wannan, sai ya gudu daga hanya zuwa Bet Haggan. Amma Yehu ya bi shi, ya ce "Shi maku kashe shi a cikin karusarsa," sai suka harbe shi kusa da Gur, wadda ke wajen Ibliyam. Ahaziya ya gudu zuwa Megiddo ya mutu a can. 28 Bayin suka ɗauke gawarsa a cikin karusa zuwa Yerusalem suka bizne shi a maƙabarta tare da ubanninsa a birnin Dauda. 29 A shekara ta sha ɗaya ne ta Yoram ɗan Ahab Ahaziya ya fara mulkin Yahuda, 30 Da Yehu ya zo Yezriyel, Yezebel ta ji labari, sai ta yi kwalliya ta yi wa idonta zane ta gyara gashinta, ta duba ta taga. 31 A lokacin da Yehu ke shiga ƙofar ta ce da shi, "Kana zuwa da salama ne, kai Zimri, an kashe shugabanka ne?" 32 Yehu ya dubi tagar ya cewa, "Ke tare da ni? Ke?" Sai bãbãni biyu ko uku suka duba waje. 33 Sai Yehu yace, "Ku wurgo ta ƙasa." Sai su ka wurgo Yezebel ƙasa, har jininta ya fallatsa a bango da kuma jikin dawakai, Yehu kuma ya tattake ta da ƙafafu. 34 Da Yehu ya shiga fãdar sai ya ci ya sha. Ya ce, "Duba yanzu ku ɗauki wannan la'anarniyar matar ku bizne ta, domin ita 'yar sarki ce." 35 Sai suka tafi domin su bizne ta, amma ba su tarar da komai nata ba sai ƙoƙon kanta da ƙafa da tafin hannuwa. 36 Sai suka dawo suka faɗa wa Yehu. Ya ce, "Wannan maganar Yahweh ce wadda annabi Iliya Batishbe, ya faɗa, cewa 'A filin Yezriyel karnuka za su cinye gangar jikin Yezebel, 37 gangar jikin Yezebel kuma za ta zama kamar ɗan kututture a cikin filaye a ƙasar Yezriyel, domin kada wani ya iya cewa, "Wannan ce Yezebel.'"'

Sura 10

1 Ahab yana da zuriya saba'in a Samariya. Yehu ya rubuta wasiƙu ya aika da su Samariya, ga shugabannin Yezriyel, haɗe da dattawa da 'yan tsaro na zuriyar Ahab, cewa, 2 "Zuriyar shugabanku na tare da ku, kuma kuna da karusai da dawakai da ƙayatattun birane da makamai. 3 Domin haka da zarar wannan wasiƙa ta same ku, sai ku zaɓi wanda yafi cancanta daga cikin zuriyar shugabanku ku ɗora shi akan gadon sarautar mahaifinsa, ku kuma yi yaƙi domin gidan sarautar shugabanku." 4 Amma suka tsorata suka ce da junansu, "Duba sarukuna biyu ma ba su iya ja da Yehu ba. To yaya zamu iya ja da shi?" 5 Daga nan sai wanda ke shugabantar fãdar, da mai kula da birnin da kuma dattawan da kuma masu renon yara, suka sake mayar da magana ga Yehu, cewa, "Mu bayinka ne. Za mu yi duk abin da ka umarce mu. Baza mu naɗa kowa a matsayin sarki ba. Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau a idanunka." 6 Sai Yehu ya rubuta wasiƙa ta biyu zuwa gare su, cewa, "In kuna tare da ni, in kuma za ku ji muryata, dole ne ku ɗauko wanda yake shi ne shugaban zuriyarku ku zo da shi Yezriyel gobe war haka." To sai zuriyar sarkin, su saba'in, suka zama manyan mutane masu daraja a birnin waɗanda suke kula da su 7 To da wasiƙa ta zo gare su, sai suka kama 'ya'yan sarki suka karkashe su, mutane saba'in, suka ɗauki kawunansu suka aikawa da Yehu a Yezriyel. 8 Sai manzo ya zo wurin Yehu, ya ce, "Sun kawo kawunan 'ya'yan sarki maza." Sai ya ce ku ajiye su a mazubin a ƙofar shiga har sai gari ya waye." 9 Da safe sai Yehu ya fito ya tsaya ya ce da dukkan mutane, "Ba ku da laifi. Na shirya makirci kan shugabana na kuma kashe shi, amma wane ne ya kashe dukkan waɗannan? 10 To yanzu sai ku san cewa ba wani sashe na maganar Yahweh, da aka faɗa game da gidan Ahab, da zai faɗi ƙasa, domin Yahweh ya yi abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya." 11 Sai Yehu ya karkashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezriyel, ya kuma kashe mutanensa masu muhimmanci, da abokansa na ƙut da ƙut, da firistocinsa, har ta kai ga ba wanda ya ragu. 12 Sai Yehu ya tashi ya tafi; ya tafi zuwa Samariya. Da ya je Bet Eked ta makiyaya, 13 sai ya tarar da 'yan'uwan Ahaziya sarkin Yahuda. Yehu yace da su "Ku su wane ne?" Suka ce, "Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, kuma zamu mu gai da 'ya'yan sarki ne da kuma 'ya'yan Sarauniya Yezebel." 14 Yehu ya ce da mutanensa, "Ku kama su da ransu." Sai suka kama su da ransu suka karkashe su a ramin Bet Eked, dukkan mutanen arba'in da biyu ne. Bai bar ko ɗaya daga cikinsu da rai ba. 15 Da Yehu ya bar wurin, sai ya tarar da Yonadab ɗan Rekab yana zuwa domin ya same shi. Yehu ya gaishe shi ya ce da shi, "Ko zuciyarka na tare da ni, kamar yadda zuciyata ke tare da taka?" Yonadab ya amsa, "Tana nan." Yehu ya amsa, "In tana nan, ka ba ni hannunka." Sai Yonadab ya ba shi hannunsa, sai Yehu ya ɗauke shi a cikin karusarsa. 16 Yehu ya ce, "Ka zo tare da ni ka ga himmata domin Yahweh." Sai ya tafi da Yonadab yana tuƙi tare da shi a karusarsa. 17 Da ya zo Samariya, sai Yehu ya karkashe duk waɗanda suka ragu daga zuriyar Ahab a Samariya, har sai da ya kashe duk wani mai jinin sarauta na iyalin Ahab, kamar dai yadda maganar Yahweh ta faɗa ta wurin Iliya. 18 Sai Yehu ya tattara dukkan mutane wuri ɗaya ya ce da su, "Ahab ya bauta wa Ba'al ɗan kaɗan, amma Yehu ya fi bauta masa ya yawa. 19 To yanzu sai ku kirawo mani dukkan annabawan Ba'al, da duk masu bautarsa, da duk firistocinsa. Kar ku rage ko da guda ɗaya, domin ina da babbar hadaya da zan miƙa ga Ba'al. Duk wanda bai zo ba za, a kashe shi." Amma Yehu ya yi wannan yaudarar ne domin ya kashe duk masu bauta wa Ba'al. 20 Yehu yace, "Ku shirya lokaci da za mu yi taruwa domin Ba'al." Domin haka suka yi sanarwar ta. 21 Sai Yehu ya aika a ko'ina cikin dukkan Isra'ila sai duk masu bautar Ba'al suka zo, har ba waninsu da bai zo ba. Suka zo masujadar Ba'al, ta kuma cika maƙil. 22 Yehu yace da mutane masu, kula da ma'ajiyar kayan firistoci, "Ku fito da tufafi domin duk masu bautar Ba'al." Sai mutumin ya fito da tufafi dominsu. 23 Sai Yehu ya tafi tare da Yonadab ɗan Rekab zuwa gidan Ba'al, ya ce da masu bautar Ba'al, "Ku bincika ku tabbatar cewa ba wani daga cikin masu bautar Yahweh a cikinku, amma sai dai masu bautar Ba'al kaɗăi." 24 Sai suka shiga domin su miƙa hadayu da baiko na ƙonawa. Sa'an nan Yehu ya zaɓi mutane tamanin da ke tsaye a waje, ya ce da su, "In wani ya bar mutanen nan da na kawo ya kuɓuta to a bakin ransa, zan kashe wanda ya yi sakaci har wani ya gudu a madadin wancan da ya gudu." 25 To nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya da baiko na ƙona wa, ya ce da 'yan tsaro da hafsoshi, "Ku shiga ku kashe su. Kar ku bar wani ya fito waje." Domin haka suka karkashe su da kaifin takobi, da 'yan tsaro da hafsoshin suka jejjefar da su waje suka shiga can ƙuryar ɗakin gidan Ba'al. 26 Suka mummurgina duwatsun ginshiƙan gidan Ba'al suka ƙone su. 27 Suka kuma kakkarya ginshiƙan Ba'al, suka hallakar da gidan Ba'al suka mayar da shi makewayi wanda har yanzu haka wurin ya ke. 28 Da haka Yehu ya hallakar da bautar Ba'al daga Isra'ila. 29 Amma Yehu bai ƙyale zunubin Yerobowom ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi - wato bautar ɗan maraƙin zinariya a Betal da Dan. 30 Domin haka Yahweh yace da Yehu, "Saboda ka yi abin da ke dai dai a idona, ka kuma iy wa gidan Ahab gwargwadon abin da ke a zuciyata, zuriyarka zasu yi mulkin Isra'ila har ya zuwa tsara ta huɗju." 31 Amma Yehu bai da muya yi tafiya bisa tafarkin Yahweh, Allah na Isra'ila, da dukkan zuciyarsa ba. Bai kuma bar zunubinYarobowam ba, ta haka ya sa Isra'ila yin zunubi. 32 A waɗancan kwanakin Yahweh ya fara yanke sassa daga Isra'ila, sai Hazayel ya ci Isra'ila akan iyakokin Isra'ila, 33 daga gabashin Yodan, dukkan ƙasar Giliyad da ta Gadiyawa da ta Rubenawa da ta Manassawa, daga Arowa wadda ke a Kwarin Arno har ya zuwa Giliyad da kuma zuwa Bashan. 34 Game kuma da sauran abubuwa game da Yehu, da kuma duk abin da ya yi da dukkan ikonsa, ashe ba a rubuta su a cikin ayukan sarakunan Isra'ila ba? 35 Yehu ya yi barci tare da ubanninsa, suka kuma bizne shi a Samariya. Sai Yehoahaz ɗansa ya zama sarki a madadinsa. 36 Tsawon lokacin da Yehu ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shi ne shekaru ashirin da takwas.

Sura 11

1 To da Ataliya, mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta kashe duk 'ya'yan gidan sarauta. 2 Amma Yehosheba, 'yar sarki Yahoram da 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yo'ash ɗan Ahaziya ta ɓoye shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, tare da mai renonsa; ta sa su a ɗakin kwana. Suka ɓoye shi domin kada Ataliya ta gan shi ta kashe shi. 3 Yana tare da Yahosheba a ɓoye a gidan Yahweh har tsawon shekaru shida, a lokacin da Ataliya ke sarautar ƙasar. 4 A shekara ta bakwai, Yeho'iada ya aika da saƙonnin ya kuma fito da kwamandojin na ɗari-ɗari na Karitawa wato wata ƙungiyar mayaƙa ta gidan sarauta da 'yan tsaro ya kawo su wurinsa, cikin haikalin Yahweh. Ya yi yarjejeniya da su, ya kuma sa su su rantse a gidan Yahweh. Daga nan sai ya nuna musu ɗan sarki. 5 Ya umarce su, da cewa, "Wannan shi ne abin da tilas za ku yi. Kashi uku daga cikinku waɗanda ke zuwa da ranar Asabaci za su yi tsaron gidan sarki, 6 kashi uku su tsaya a Ƙofaf Sur, kuma kashe uku su tsaya a ƙofar bayan gidan 'yan tsaro." 7 Sauran ƙungiyoyin guda biyu da ba ku yin hidima da ranar asabar, dole ne ku yi tsaron gidan Yahweh domin sarki. 8 Dole ne ku kewaye sarki kowanne mutum da makaminsa a hannunsa, duk wanda ya shigo wurinku sai ku kashe shi. za ku kasance tare da sarki a lokacin da ya fita da lokacin da ya dawo ciki. 9 Sai kwamandojin ɗari-ɗari suka yi biyayya da duk abin da Yeho'iada ya firist ya ba da umarni. Kowannen su ya ya kwashi mutanensa, waɗanda ke zuwa hidima da Asabaci, da waɗanda ke zuwa daina hidima da Asabaci; suka zo wurin Yeho'iada firist. 10 Sai Yeho'iada firist ya ya ba kwamandojin ɗari-ɗari mãsu da garkuwoyi na sarki Dauda da kuma waɗanda ke gidan Yahweh. 11 Saboda haka 'yan tsaron suka tsaya, kowanne da makaminsa a hannunsa, daga gefen dama na haikalin zuwa gefen hagun na haikalin, kusa da bagadi da kuma haikalin, suna kewaye da sarki. 12 Sai Yeho'iada ya kawo ɗan sarki Yo'ash, ya sa masa kambi a kansa, ya kuma ba shi sharruɗan yarjejeniya. Sai suka naɗa shi sarki suka kuma shafe shi da mai. Suka tafa hannuwansu suka ce, "Ran sarki ya daɗe!" 13 Da Ataliya ta ji hayaniya ta 'yan tsaro da ta mutane, sai ta zo wurin mutane a gidan Yahweh. 14 Tana dubawa sai ga sarki a tsaye a jikin ginshiƙin, kamar yadda al'adar ta ke, da hafsoshi da masu hura ƙahonni na tare da sarki. Dukkan mutanen ƙasar na murna suna hura ƙahonni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta yi ihu tana cewa, "Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!" 15 Sai Yeho'iada firist ya bada umarni ga kwamandoji na ɗari ɗari masu shugabantar sojojin cewa, "Ku kawo ta a tsakanin rundunarku. Kuma duk wanda ya biyo ta, ku kashe shi da takobi. Domin firist ya ce, "Kada ku kashe ta a gidan Yahweh." 16 Domin haka suka ja ta da ta kai dai dai inda dawakai ke shiga wurin 'yan tsaron fãda a can aka kashe ta. 17 Sai Yeho'iada firist ya yi yarjejeniya da tsakanin Yahweh da sarki da kuma mutane, cewa za su zama mutanen Yahweh, hakannan kuma tsakanin mutane da sarki. 18 Domin haka dukkan mutanen ƙasar suka tafi gidan Ba'al suka rurrushe shi. Suka bubbuge bagadin Ba'al da gumakansa rugu rugu, suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagadojin. Sai Yeho'iada firist ya naɗa 'yan tsaro a haikalin Yahweh. 19 Sai Yeho'iada ya kwashi kwamandojin ɗari ɗari da Karitiyawa, mayaƙan fãda, da 'yan tsaro, da dukkan mutanen ƙasar tare suka ka kawo sarki daga gidan Yahweh suka tafi gidan sarki ta hanyar ƙofar 'yan tsaro. Sai Yo'ash ya hau gadon sarauta. 20 Domin haka duk mutanen ƙasar suka yi murna, sai birnin ya sami kwanciyar hankali bayan an kashe Ataliya da takobi a gidan sarki. 21 Yo'ash yana da shekaru bakwai a lokacin da ya fara sarauta.

Sura 12

1 A shekara ta bakwai ta Yehu, sarautar Yo'ash ta fara; ya yi sarauta tsawon shekaru arba'in a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ta Biyasheba. 2 Yoash ya yi abin da ke nagari a gaban Yahweh a dukkan lokaci, saboda Yeho'iada firist yana yi masa gargaɗi. 3 Amma ba a kawar da manya manya wurare ba. Har yanzu mutane na yin hadaya da ƙona turare a manyan wurare. 4 Sai Yo'ash yace da firistoci, "Dukkan ƙuɗaɗen da aka kawo a keɓaɓɓen wuri a cikin gidan Yahweh, wannan kuɗin da kuɗaɗen da aka tsara wa mutane - ko kuɗin da aka karɓa a wurin ƙidaya ne, ko kuma kuɗin da aka karɓa saboda wa'adi ne, ko kuma kuɗin da aka tara ta wurin yadda Yahweh ya zuga mutanensa - 5 sai firistoci su karbi kuɗin daga ɗaya daga cikin ma'ajiyarsu su gyara duk wata ɓarna da suka gani a cikin haikali." 6 Amma a shekara ta ashirin ta sarautar sarkin Yo'ash, firistoci ba su gyara komai ba a cikin haikalin. 7 Sai sarki Yo'ash ya kira Yeho'iada firist da kuma sauran firistoci, ya ce da su, "Meyasa baku gyara komai a cikin haikalin ba? To yanzu kada ku ƙara ɗaukan kuɗi daga masu biyan harajinku, amma ku ɗauki wanda aka karɓa ku ba waɗanda za su yi gyaran haikalin." 8 Sai firistoci suka yarda cewa ba za su ƙara karɓar kuɗi daga wurin mutane domin gyaran haikali da kansu ba. 9 A maimakon, Yeho'iada firist ya ɗauki mazubi ya yi masa huduwa a ƙasa, ya ajiye shi kusa da bagadin, daga gefen dama dai-dai inda mutane ke shiga gidan Yahweh. Sai firistoci da ke kula da ƙofar shiga haikalin suka zuba dukkan kuɗin da aka kawo gidan Yahweh. 10 Da zarar sun ga akwai kuɗi da yawa a cikin mazubin, sai marubuta na sarki da manyan firistoci su zo su zuba kuɗin a jakkuna sai su ƙirga kuɗin da aka samu a haikalin Yahweh. 11 Suka ba da kuɗin da aka tattaro daga hannun mutane masu kula da haikalin Yahweh. Suka biya masu aikin katako da magina waɗanda suka yi aiki a haikalin Yahweh, 12 haka kuma masu sayo katakai da yankawa, da masu sassaƙa duwatsu, domin gyaran haikalin Yahweh, da kuma duk abin da ake bukatar a biya shi. 13 Amma kuɗin da aka kawo cikin haikalin Yahweh ba a biya domin aikin yin kofin zinariya da fitilu da kwangiri da kakaki, ko kuma duk wani aiki na azurfa ba. 14 Sun bada kuɗin ga waɗanda suka yi aikin gyaran gidan Yahweh. 15 Haka kuma, basu bukaci kuɗi domin su biya masu biyan ma'aikata ba, domin waɗannan mutanen suna da aminci. 16 Amma kuɗin baiko na hadayar laifi da kuma na hadayar zunubi ba a kawo su zuwa cikin haikalin Yahweh ba, domin na firistoci ne. 17 Sai Hazayel sarkin Aram ya kai hari kan Gat ya kuma kame ta. Sai ya Hazayel ya juyo domin ya kawo hari Yerusalem. 18 Sai Yo'ash sarkin Yahuda ya ɗauke duk abubuwan da Yehoshafat da Yehoram da Ahaziya mahaifinsa da sarkunan Yahuda suka keɓe, da dukkan zinariya da aka samu a ɗakin ajiya na gidajen Yahweh da na gidan sarki ya aika da su wurin Hazayel sarkin Aram Sai Hazayel ya fita daga Yerusalem. 19 Game kuma da sauran abubuwa game da sarki Yo'ash da duk abin da ya yi, ashe ba a rubuta su a cikin littafin ayukan sarakunan Yahuda ba? 20 Sai barorinsa suka tashi suka haɗa kai suka shirya maƙarƙashiya; suka kai hari ga Yo'ash a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla. 21 Jozabad ɗan Shimeyet da Yehozabad ɗan Shomar, bayinsa suka kai masa hari, ya kuma mutu. Suka bizne Yo'ash tare da kakanninsa a birnin Dauda, Amaziya, ɗansa ya zama sarki a madadinsa.

Sura 13

1 A shekara ta ashirin da uku na Yo'ash ɗan Ahaziya sarkin Yahuda, Yehoahaz ɗan Yehu ya fara mulki akan Isra'ila da Samariya; ya yi mulkin har tsawon shekaru goma. sha bakwai. 2 Ya kuwa yi abin mugunta a fuskar Yahweh da bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi; kuma Yehoahaz bai juya baya daga hakan ba. 3 Fushin Yahweh ya yi ƙuna gãba da Isra'ila, sai ya ci gaba da bada su ga hannun Hazayel sarkin Aram da kuma ga hannun Ben Hadad ɗan Hazayel. 4 Saboda haka Yehoahaz ya yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya saurare shi domin ya ga danniyar da ake yi wa Isra'ila, yadda sarkin Aram ya ke zaluntarsu. 5 Don haka sai Yahweh ya ba Isra'ila maceci, sai suka kuɓuta daga ƙasar Aramiyawan, sai mutanen Isra'ila suka fara zama a gidajensu kamar yadda suke a dã. 6 Duk da haka, ba su kauce daga zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila suka yi zunubi, kuma suka ci gaba a cikin su; kuma gunkiyar Asherah tana nan a Samariya. 7 Aramiyawan suka bar Yehoahaz da mahayan dawakai hamsin ne kawai da karusai goma da dakarai dubu goma, gama sarkin Aram ya halakar da su kamar ƙaiƙai a lokacin casa. 8 Akan sauran zantuttukan game da Yehoahaz kuwa, da dukkan abin da ya yi da ikonsa, ba an rubuta su littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 9 Sai Yehoahaz ya kwanta tare da kakaninsa, aka kuwa bizine shi a Samariya. Yohoash ɗansa ya zama sarkin da ya gaje shi. 10 A shekara ta talatin da bakwai na Yo'ash sarkin Yahuda, mulkin Yohoash ɗan Yahoahaz ya fara kan Isra'ila a Samariya; ya yi mulki shekara goma sha shida. 11 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai bar ko wani abu daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, ta yadda ya sa Isra'ila ta yi zunubi, amma ya yi tafiya cikinsu. 12 A batun sauran zantuttukan da suka shafi Yohoash, da dukkan abin da ya yi, da ikonsa ta yadda ya yaƙi Amaziya sarkin Yahuda, ba an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 13 Yohoash ya kwanta tare da kakaninsa, sai Yerobowam ya zauna a kursiyinsa. An bizne Yohoash a Samariya tare da sarakunan Isra'ila. 14 Sai Elisha ya yi rashin lafiya da ciwon da yasa ya mutu daga baya, don haka sai Yohoash sarkin Isra'ila ya zo gare shi ya yi kuka a kansa. Ya ce, "Babana, babana, karusan Isra'ila da mahayan dawakanta suna ɗaukan ka!" 15 Elisha yace masa, "Ɗauki baka da kibbau," sai Yo'ash ya ɗauki baka da wassu kibbau. 16 Elisha ya cewa sarkin Isra'ila, "Ka sa hannuwanka a bakan," sai ya sa hannuwansa a nan. Sai Elisha ya dafa hannuwansa a hannuwan sarkin. 17 Elisha yace, "Buɗe tagar da ke wajen gabas," sai ya buɗe ta. Sa'annan Elisha yace, "Harba!", sai ya harba. Elisha yace, "Wannan kibiyar nasarar Yahweh ce, kibiyar nasara akan Aram, gama za ka kai wa Aramiyawan hari a Afek har sai ka yi kaca kaca da su." 18 Sai Elisha yace, "Ɗauki kibau," sai Yo'ash ya ɗauke su. Ya cewa sarkin Isra'ila, "Ka caki ƙasa da su," sai ya caki ƙasa sau uku, sa'annan ya tsaya. 19 Amma mutumin Allah ya yi fushi da shi ya ce, "Da ka bugi ƙasa sau biyar ko shida. Sa'annan da ka kai wa Aram hari har sai ka hallakar da ita, amma yanzu za ka kai wa Aram hari sau uku ne kawai." 20 Sai Elisha ya mutu, kuma aka bizne shi. Sai gungun Mowabawa suka mamaye ƙasar a farkon shekara. 21 Sa'ad da suke bizne wani mutun, suka ga gungũn Mowabawa, sai suka jefar da gangar jikin cikin kabarin Elisha. Da zarar mutumin ya taɓi ƙasussuwan Elisha, sai ya farfaɗo ya miƙe tsaye da kafafunsa. 22 Hazayel sarkin Aram ya muzguna wa Isra'ila dukkan kwanakin Yehoahaz. 23 Amma Yahweh ya yi alheri ga Isra'ila, ya kuma ji tausayin su ya kuma kula da su, saboda alƙawarinsa ga Ibrahim, Ishaku da Yakubu. Don haka Yahweh bai hallakar da su ba, haka kuma bai kore su daga gare shi ba. 24 Hazayel sarkin Aram ya mutu, sai Ben Hadad ‌ɗansa ya gaji sarautarsa. 25 Yehoash ‌ɗan Yehoahaz ya karɓi biranen daga Ben Hadah ‌ɗan Hazayel wan‌ɗanda Yehoahaz mahaifinsa ya ƙwato ta yaki. Yehoash ya kai masa hari sau uku, kuma ya karɓe biranen Isra'ila.

Sura 14

1 A shekara ta biyu ta Yehoash ɗan Yehoahaz, sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yo'ash, sarkin Yahuda, ya fara mulki. 2 Yana shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara sarauta; ya yi mulki na tsawon shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yehoaddan, ta Yerusalem. 3 Ya yi abin da ke da kyau a fuskar Yahweh, duk da haka ba kamar Dauda mahaifinsa ba. Ya yi dukkan abin da Yo'ash, mahaifinsa, ya yi. 4 Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane dai suka yi ta miƙa hadaya da ƙona turare a tuddan tsafi. 5 Sai ya zamana sa'ad da mulkinsa ya kafu sosai, sai ya kashe barorin da suka kashe mahaifinsa sarki. 6 Duk da haka bai kashe 'ya'yan masu kisan ba; maimakon haka, ya yi aiki bisa ga abin da ke rubuce a shari'a, a cikin Littafin Musa, kamar yadda Yahweh ya umurta, cewa, "Ubanni bai wajaba a kashe su saboda "ya'yansu ba, ko kuma a kashe 'ya'yan saboda iyayensu ba. Maimakon haka, duk mutumin da ya yi laifi lallai ne a kashe shi domin nasa zunuban." 7 Ya kashe sojoji dubu goma na Idom a Kwarin Gishiri; ya kuma cafko Sela a yaƙi ya kira ta Yoktil, kuma haka ake kiranta har wa yau. 8 Sa'an nan Amaziya ya aiko da manzanni ga Yehoash ɗan Yehoahaz ɗan Yehu sarkin Isra'ila, cewa, "Ka zo, mu sadu da juna ido da ido a yaƙi." 9 Amma Yehoash sarkin Isra'ila ya aike manzani su mayar da Amaziya sarkin Yahuda, cewa, "'Yar ƙaya da ke Lebanan ta aiko da saƙo ga itacen al'ul a Lebanan, cewa, 'Ki ba da ɗiyarki ga ɗa na don aure,' amma naman jeji a Lebanan ya wuce ta wurin ya tattaka ƙayar. 10 Hakika ka kai wa Idom hari, kuma zuciyarka ta ɗaga ka sama. Ka yi fahariya da nasararka, amma ka zauna a gida, gama donme zaka sawa kanka matsala ka faɗi, da kai da Yahuda tare da kai?" 11 Amma Amaziya bai saurara ba. Saboda haka Yehoash sarkin Isra'ila ya kai hari kuma shi da Amaziya sarkin Yahuda sun sadu da juna ido da ido a Beth Shemesh, wadda ke ta Yahuda. 12 Isra'ila ta kãda Yahuda, kuma kowanne mutun ya gudu gida 13 Yehoash sarkin Isra'ila, ya kamo Amaziya, sarkin Yahuda ɗan Yehoash ɗan Ahaziya, a Beth Shemesh. Ya zo Yerusalem ya rushe bangon Yerusalem daga Ƙofar Ifraim zuwa Ƙofar Kwana, mai nisan mita ɗari da tamanin. 14 Ya ɗauke dukkan zinariya da azurfa da dukkan abubuwan da aka samu a gidan Yahweh, da abubuwa masu daraja na fãdar sarki, tare da mutanen da aka ba da su jingina, sai ya koma Samariya. 15 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yehoash kuwa, dukkan abin da ya yi da ikonsa da yadda ya yi yaƙi da Amaziya sarkin Yahuda, ba an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 16 Sa'an nan Yehoash ya yi barci tare da kakaninsa kuma aka bizne shi a Samariya tare da sarakunan Isra'ila, kuma Yerobowam, ɗansa, ya zama sarki a madadin sa. 17 Amaziya ɗan Yo'ash, sarkin Yahuda, ya yi shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehoash ɗan Yehoahaz, sarkin Isra'ila. 18 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Amaziya, ba an rubota su a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 19 Suka yi maƙarƙashiya gãba da Amaziya a Yerusalem, sai ya gudu zuwa Lakish. Ya gudu zuwa ga Lakishna, amma an aiko da maza su bishi har Lakish su kashe shi a wurin. 20 Suka dawo da shi akan dawakai, sai aka bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda. 21 Dukkan mutanen Yahuda suka ɗauki Azariya, wanda ke shekara goma sha shida, suka maida shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya. 22 Azariya ne wanda ya gina Elat ya maida ita ta Yahuda, bayan Sarki Amaziya ya kwanta da kakaninsa. 23 A shekara ta goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yo'ash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehoash sarkin Isra'ila ya fara sarauta a Samariya; ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya. 24 Ya aikata mugunta a fuskar Yahweh. Bai kauce wa dukkan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi. 25 Ya maida iyakar Isra'ila daga Lebo Hamath zuwa Tekun Arabah, bisa ga bin umurnai na kalmar Yahweh, Allahn Isra'ila, wanda ya faɗa ta wurin bawansa Yona ɗan Amittai, annabin nan da ke daga Gat Hefa. 26 Gama Yahweh ya ga azabar da Isra'ila ke ciki, kowa yana cikin tsananin wahala, da bawa da sakakke, kuma babu maceci don Isra'ila. 27 Saboda haka Yahweh ya ce ba zai shafe sunan Isra'ila daga ƙarƙashin sammai ba; maimakon haka, Ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yehoash. 28 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yerobowam, da dukkan abin da ya yi da ikonsa, da yadda ya yi yaƙi ya ƙwato Damaskus da Hamath, waɗanda ke na Yahuda a dã, domin Isra'ila, Ba an rubuta su a littafin abubuwan da suka faru da sarakunan Isra'ila ba? 29 Yerobowam ya kwanta da kakaninsa, tare da sarakunan Isra'ila, sai Zekariya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.

Sura 15

1 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam, sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya sarkin Yahuda ya fara mulki. 2 Azariya yana shekara goma sha shida sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi sarauta ta shekara hamsin da biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya, kuma ita daga Yerusalem take. 3 Ya yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh, kamar yarda mahaifinsa Amaziya ya yi. 4 Sai dai, wuraren tsafin kan tuddai ba a rusa su ba. Mutanen dai na miƙa hadaya da ƙona turare a saman tuddai. 5 Yahweh ya addabi sarkin da kuturta har zuwa ranar mutuwarsa kuma ya yi ta zama a gidan da aka ware ne. Yotam, ɗan sarki, ya shugabanci gidan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar. 6 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Azariya da dukkan abin da ya yi, ba an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 7 Saboda haka Azariya ya yi barci tare da kakaninsa; su ka bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda. Yotam, ɗansa ya zama sarki a madadinsa. 8 A shekara ta talatin da takwas ta Azariya sarkin Isra'ila, Zekariya ɗan Yerobowam ya yi mulki a Isra'ila ta Samariya na wata shida. 9 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh, kamar yadda mahaifansa suka yi. Bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi. 10 Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zekariya maƙarƙashiya, ya kai masa hari a Ibleam, ya kashe shi. Sai ya zama sarki a madadinsa. 11 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Zekariya, An rubuta su a littafin abubuwan da suka faru da sarakunan Isra'ila. 12 Wannan ne batun da Yahweh ya faɗa wa Yehu, cewa, "Zuriyarka za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har zuwa tsara ta huɗu." Abin da ya faru kenan 13 Shullum ɗan Yabesh ya fara mulki a shekara ta talatin da tara na Azariya sarkin Yahuda, kuma ya yi mulki na wata ɗaya a Samariya. 14 Menahem ɗan Gadi ya tafi can daga Tirza zuwa Samariya. a wurin ya kai wa Shullum ɗan Yabesh hari, a Samariya. Ya kashe shi ya kuma zama sarki a madadinsa. 15 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Shallum da maƙarƙashiya da ya shirya, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. Sa'an nan 16 Menahem ya kai hari a Tifsa da dukkan waɗanda ke wurin da iyakar wuraren Tirzah, saboda ba su ba shi zarafin shiga birnin ba. Sai ya kai mata hari ya kuma feɗe dukkan mata masu junabiyu a ƙauyen nan. 17 A shekara ta talatin da tara ta Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya fara mulki a kan Isra'ila, Ya yi mulkin shekara goma a Samariya. 18 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Gama a dukkan rayuwarsa, bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi. 19 Sa'an nan Ful sarkin Asiriya ya zo gãba da ƙasar, sai Menaham ya bai wa Ful talanti dubu na azurfa, saboda Ful ya taimaka da gudumawa domin masarautar Isra'ila ta ƙarfafa a hannunsa. 20 Manehen ya ƙarbi wannan kuɗin daga Isra'ila ta wurin neman awo hamsin na azurfa daga dukkan atajiri domin ya bai wa sarkin Asiriya. Don haka Sarkin Asiriya ya juya baya kuma bai zauna cikin ƙasar ba. 21 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Manahem, da dukkan abin da ya yi, ba a rubuce suke a litaffin tarihin sarakunan Isra'ila ba? 22 Sai Manahem ya yi barci tare da kakaninsa, kuma Fekahiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa. 23 A shekara ta hamsin ta Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya fara mulki a Isra'ila cikin Samariya; ya yi mulki shekara biyu. 24 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai juya daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ta wurin hakan ya sa Isra'ila ta yi zunubi. 25 Fekahiya yana da hafsa mai suna Feka ɗan Remaliya, wanda ya ƙulla masa maƙarkashiya. Tare da mutane hamsin na Giliyad, Feka ya kashe Fekahiya da kuma Argob da Ariye a Samariya, a cikin sansanin hasumayar fadar sarki. Feka ya kashe Fekahiya ya kuma zama sarki a madadinsa. 26 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Fekahiya da dukkan abin da ya yi, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 27 A shekara ta hamsin da biyu na Azariya sarkin Yahuda, Fekah ɗan Remaliya ya fara mulki akan Isra'ila cikin Samariya; ya yi mulki shekara ashirin. 28 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi. 29 A kwanakin Feka sarkin Isra'ila, Tiglat Filesa sarkin Asiriya ya zo ya ɗauki Ijon da Abel Bet Ma'aka da Janoya da Kedesh da Hazor da Giliyad da Galili da dukkan ƙasar Naftali. Ya ɗauki mutanen zuwa Asiriya. 30 Don haka Hosheya ɗan Elah ya shirya maaƙarƙashiya găba da Feka ɗan Remaliya. Ya kai masa hari ya kuma kashe shi. Sa'an nan ya zama sarki a madadinsa, a shekara ta ashirn ta yotam ɗan Uzziya. 31 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Feka da dukkan abin da ya yi, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 32 A shekara ta biyu ta Peka ɗan Remaliya, sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya, sarkin Yahuda ya fara mulki. 33 Yana da shekara ashirin da biyar a sa'ad da ya fara mulki; Ya yi mulki shekara goma sha shida a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yerushah; Ita ɗiyar Zadok ce. 34 Yotam ya yi abin da ke da kyau a fuskar Yahweh. Ya bi misalin dukkan abubuwan da mahaifisa Azariya ya yi. 35 Duk da haka, ba a ƙwato wuraren tsafin kan tuddai ba. Mutanen na yin hadaya da ƙona turare a samman tuddai, Yotam ya gina ƙofarta bisa ta gidan Yaweh. 36 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yotam, da dukkan abin da ya yi, ba a rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 37 A kwanakin nan ne Yahweh ya fara aiko da Rezin sarkin Aram da Peka ‌ɗan Remaliya gaba da Yahuda. 38 Yotam ya kwanta da kakaninsa a birnin Dauda, kakansa. Sa'an nan Ahaz ‌ɗansa ya zama sarki a ma‌da‌dinsa.

Sura 16

1 A shekara ta goma sha bakwai ta Feka ɗan Remaliya, 2 Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda, ya fara mulki, kuma ya yi mulki shekara goma sha shida a Yerusalem. Bai yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh Allahnsa ba, kamar yadda Dauda kakansa ya yi ba. 3 Maimakon haka, ya yi tafiya a hanyar sarakunan Isra'ila; hakika, ya sa ɗansa a wuta domin hadaya ta ƙonawa, yana bin ayyukan ban ƙyama na al'ummai, waɗanda Yahwe ya fitar daga gaban mutanen Isra'ila. 4 Ya miƙa hadayu da kuma ƙona turare awurare bisa tuddai da ƙarƙashin kowanne koren Itace. 5 Sa'an nan Rezin, sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, sarkin Isra'ila, ya zo Yerusalem ya kawo hari. Suka tunkari Ahaz, amma ba su iya mamayar sa ba. 6 A lokacin nan, Rezin sarkin Aram ya maido Elath domin Aram ya kori mazajen Yahuda daga Elat. Sa'an nan Aramiyawa suka zo gun Elat inda suka zauna har yau. 7 Sai Ahaz ya aiki manzanni ga Tiglat Filesa sarkin Asiriya, cewa, "Ni baranka ne da ɗanka. Ka zo ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra'ila, waɗanda suka kawo mani hari." 8 Sai Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyan da aka tarar a gidan Yahweh da na cikin kayayyaki masu daraja na fãdar sarki ya aikar da su kyauta ga sarkin Asiriya. 9 Sa'an nan sarkin Asiriya ya saurare shi, kuma sarkin Asiriya ya farmaƙi Damaskus, ya mamaye ta, ya kuma ɗauke mutanenta ya kai su zaman bauta a Kir. Ya kuma kashe Rezin sarkin Aram. 10 Sarki Ahaz ya tafi Damaskus ya sadu da Tiglat Filesa sarkin Asiriya. A Damaskus ya ga wani bagadi. Ya aika wa Yuriya firist irin fasalin bagaden da yanayinsa da zane domin dukkan aikin da ake bukata. 11 Don haka Yuriya firist ya gina bagaden da zai zama kamar tsarin da sarki Ahaz ya aiko daga Damaskus. Ya gama shi kafin sarki Ahaz ya dawo daga Damaskus. 12 Sa'ad da sarki ya zo daga Damaskus ya ga bagaden; sarkin ya kusanci bagaden ya kuma yi bayarwa akan sa 13 Ya yi hadayarsa ta ƙonawar da hadayarsa ta hatsi, ya zubo hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta zumunci a bagaden. 14 Bagaden tagulla wanda ke gaban Yahweh - ya kawo shi daga gaban haikalin, daga tsakanin bagaden da haikalin Yahweh ya sa shi a gefen arewacin bagadensa 15 Sai sarki Ahaz ya umurci Yuriya firist, cewa, "A babban bagaden ka ƙona baikon ƙonawa na safe da baikon hatsi na yamma, da kuma baikon na ƙonawa na sarki da baikon hatsinsa, da baikon na ƙonawa na dukkan mutanen ƙasar, da baikon hatsinsu da baikon shansu. Ka yayyafa jinin akan dukkan baiko na ƙonawa, da dukka jinin hadayar. Amma bagadin tagulla zai zama nawa domin neman shawara don jagoranci." 16 Yuriya firist kuwa ya yi abin da sarki Ahaz ya umurta. 17 Sa'an nan sarki Ahaz ya ciro dakalan da darunan da suke bisansu; ya kuma ɗauke babban daron daga bijimin tagullar da ke ƙarƙashinsa ya sa shi a daɓen dutse. 18 Ya cire hanyar da aka killace ta Asabaci wanda aka gina a haikalin, tare da ƙofar dake waje ta shigar sarki zuwa haikalin Yahweh, saboda sarkin Asiriya. 19 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Ahaz da abin da ya yi, ba a rubuce suke cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 20 Ahaz ya kwanta da kakaninsa aka kuma bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda. Hezekiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.

Sura 17

1 A shekara ta goma sha biyu ta Ahaz sarkin Yahuda, mulkin Hosheya ɗan Elah ya fara, ya yi mulki a Samariya akan Isra'ila na shekara tara. 2 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh, duk da haka ba kamar sarakunan Isra'ila waɗanda suka gabace shi ba. 3 Shalmaneser sarkin Asiriya ya kai masa hari, kuma Hosheya ya zama baransa ya kawo masa haraji. 4 Sa'an nan sarkin Asiriya ya gano cewa Hosheya na ƙulla maƙarƙshiya gãba da shi, don Hoshiya ya aiko manzanni ga So sarkin Masar; haka kuma, babu kyautar da ya miƙo wa sarkin Asiriya, kamar yadda ya saba yi shekara da shekara. Saboda haka sarkin Assiriya ya kulle shi ya ɗaure shi a kurkuku. 5 Sa'an nan sarkin Asiriya ya kai hari a ko'ina a ƙasar, ya kuma kai wa Samariya hari ya mamaye ta shekara uku. 6 A shekara ta tara ta Hosheya, sarkin Asiriya ya ɗauki Samariya ya kuma ɗauki Isra'ila zuwa Asiriya. Ya sa su a Halah, a harabar Kogin Gozan, da kuma cikin biranen Medeyawa. 7 Mãmewar ta faru ne saboda mutanen Isra'ila sun yi zunubi ga Yahweh Allahnsu, wanda ya kawo su daga ƙasar Masar, daga ƙarƙashin hannun Fir'auna sarkin Masar. Mutanen suna bautawa waɗansu alloli ne 8 kuma suna tafiya cikin ayyukan al'umman da Yahweh ya kora daga mutanen Isra'ila, da kuma cikin ayyukan sarakunan Isra'ila da suka yi. 9 Mutanen Isra'ila sun yi wa Yahweh Allahnsu abubuwan da ba dai-dai ba a asirce. Sun gina wa kansu manyan wurare a dukkan biranensu, daga hasumiya zuwa birni mai garu. 10 Suka kuma kafa ginshiƙai da sandunan Ashera a ko'ina bisan tudu da ƙarƙashin dukkan koren itace. 11 A wurin suka ƙona turare cikin dukkan wurare masu bisa, kamar yarda al'ummai suka yi, waɗanda Yahweh ya fitar da su kafin su. Isra'ilawa sun aikata mugayen abubuwan da suka zuga Yahweh ga fushi, 12 sun bauta wa gumaka, irin waɗanda Yahweh ya ce masu, "Ba za ku yi wannan abin ba." 13 Duk da haka Yahweh ya yi shaida ga Isra'ila da kuma ga Yahuda ta wurin kowanne annabi da kowanne mai gani, cewa, "Ku juyo daga hanyoyin mugunta ku tsare dokokina da farillaina, kuma ku yi hankali da tsare dukkan dokokin da na ummurce ubanninku, da waɗanda na aiko maku ta hanun barorina annabawa." 14 Amma ba za su saurara ba; maiimakon haka suka taurare kamar ubanninsu waaɗnda ba su da aminci cikin Yahweh Allahnsu. 15 Suka ƙi dokokinsa da alƙawarin da ya yi da kakaninsu, da ummurnan alƙawarin da ya ba su. Suka bi ayyuka marasa amfani kuma su kansu suka zama marasa amfani. Suka bi al'umman arnan da ke kewaye da su, waɗanda Yahweh ya ummurce su kada su kwaikwaye su. 16 Suka ƙyale dukkan dokokin Yahweh Allahnsu. Suka ƙera sifofin zubi na ƙarfe na 'yan muruƙa biyu domin su bauta masu. Suka yi sandan Ashera, kuma suka bautawa dukkan taurari na sama da Ba'al. 17 Suka sa 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata cikin wutan, suka yi duba da tsubbace tsubbace, suka sayar da kansu don su yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh, kuma suka sa shi shi ya yi fushi. 18 Saboda haka Yahweh ya yi matuƙar fushi da Isra'ila ya cire su daga gabansa, Babu wanda aka bari ban da ƙabilar Yahuda ita ƙaɗai. 19 Ko Yahuda ma ba su tsare dokokin Yahweh Allahnsu ba, amma maimakon haka suka bi abin da Isra'ila ta yi. 20 Sai Yahweh ya ƙi dukkan zuriyar Isra'ila; ya wahalshe su ya bada su ga hannun waɗanda za su ɗauki mallakarsu a matakin ganima, har sai da ya watsar da su daga fuskarsa 21 Y a yago Isra'ila daga sarautar ta layin Dauda, suka kuma maida Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam ya kawar da Isra'ila daga bin Yahweh ya sa suka aikata gagarumin zunubi. 22 Mutanen Isra'ila kuwa suka bi dukkan zunuban Yerobowam kuma ba su kauce daga yin su ba, 23 saboda haka Yahweh ya cire Isra'ila daga fuskarsa, kamar yadda ya faɗa ta wurin barorinsa annabawa cewa zai yi. Saboda haka aka ɗauke Isra'ila daga tasu ƙasar zuwa Asiriya, kuma haka yake har wannan rana 24 Sarkin Asiriya ya kawo mutane daga Babila da Kutha da Avva da Hamat da Sefabayim, sai ya sa su a biranen Samariya a madadin mutanen Isra'ila. Suka mamaye Samariya suka zauna a biranenta. 25 Ya kasance a farkon zamansu a wurin ba su girmama Yahweh ba. Sai Yahweh ya aiko da Zakunan da suka kashe waɗansu daga cikinsu. 26 Sai suka yi magana da sarkin Asiriya, cewa, "Al'umman da ka ɗauke su ka sã a biranen Samariya ba su san ayyukan da allahn ƙasar ke buƙata ba. Saboda haka a aiko da zakuna a cikinsu, kuma, duba, zakunan na karkashe mutane a wurin saboda basu san ayyukan da allahn ƙasar ke buƙata ba 27 Sa'an nan sarkin Asiriya ya ummurta, cewa, "Ɗauki ɗaya daga cikin firistocin wurin waɗanda ka kawo su daga wurin, kuma sai ya je ya zauna a wurin, ya kuma bari a koyar da su ayyukan da allan ƙasar ya sa a yi." 28 Sai ɗaya daga cikin firistocin da aka ɗauko daga Samariya ya zo ya zauna a Betel; ya koya masu yadda za su girmama Yahweh. 29 Kowacce kabila sun yi alloli na kansu, kuma suka sa su a wuraren da Samariyawa suka yi - kowacce kabila a biranen da suke zama. 30 Mutanen Babila suka yi Succot Benot; mutanen Kuta suka yi Nergal; mutanen Hamat suka yi Ashima; 31 Avvitawa suka yi Nibhaz da Tartak. Sefavitawa suka ƙone 'ya'yansu a wuta ga Adrammelek da Anammelek, allolin Sefavitawa. 32 Suka girmama Yahweh, kuma suka naɗa firistocin manyan wuraren daga cikinsu, waɗanda ke yin masu hadaya a masujadai na tuddan wuraren. 33 Suka girmama Yahweh suka kuma bauta wa alloli na kansu, bisa ga al'adar al'umman da aka kawar. 34 Har wa yau suna ci gaba da al'adun dã. Basu girmama Yahweh, ko su bi farilla da umurni da doka, ko dokokin da Yahweh ya ba mutanen Yakubu - wanda ya kira Isra'ila ba - 35 kuma wanda Yahweh ya yi alƙawari ya kuma ummurce su, "Kada ku ji tsoron waɗansu alloli, ko ku russunar da kanku gare su, ko ku bauta masu ko ku yi masu hadaya. 36 Amma Yahweh, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar da iko mai girma da dantse a ɗage, shi ne wanda za ku girmama; gare shi ne za ku yi ruku'u, kuma gare shi za ku yi hadaya. 37 Da Farillan da ummurnan da attaura da dokokin da ya rubuta domin ku, za ku tsare su har abada. Saboda kada ku ji tsoron waɗansu alloli, 38 kuma alƙawarin da na yi da ku, ba zaku mance ba; kuma ba za ku girmama waɗansu alloli ba. 39 Amma Yahweh Allahnku shi ne wanda za ku girmama. Zai ƙuɓutar da ku daga ikon maƙiyanku." 40 Ba za su saurara ba, saboda sun ci gaba da yin abin da suke yi a baya. 41 Don haka al'umman sun ji tsoron Yahweh suka kuma bauta wa ƙerarrun sifofinsu, kuma 'ya'yansu suka yi hakan kuma - kamar yadda 'ya'yan 'ya'yansu suka yi. Suka ci gaba da yin abin da kakaninsu suka yi har wa yau.

Sura 18

1 Yanzu a shekara ta uku na Hosheya ɗan Ela, sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz, sarkin Yahuda ya fara mulki. 2 Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Abija; ita ɗiyar Zekariya ce. 3 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh, ya na bin misalin dukkan abubuwan da Dauda, kakansa ya yi. 4 Ya kawar da tuddan wurare, ya rusar da ginshiƙan dutse, ya farfashe sandan Ashera. Ya kakkarya tagullar macijin da Musa ya yi, saboda a kwanakin dã mutanen Isra'ila suna ƙona mata turare; a na kiran ta "Nehushtan." 5 Hezekiya ya dogara ga Yahweh, Allahn Isra'ila, saboda bayansa babu wani kamarsa a cikin sarakunan Yahuda, koma a cikin waɗanda suka gabace shi. 6 Gama ya manne wa Yahweh. Bai daina binsa ba gama ya kiyaye dokokinsa, waɗanda Yahweh ya ummurci Musa. 7 Saboda haka Yahweh yana tare da Hezekiya, kuma duk inda ya je ya wadata. Ya yi wa sarkin Asiriya tawaye kuma bai bai bauta masa ba. 8 Ya kai wa Filistiyawa hari har Gaza da iyakar da ke kewaya, daga hasumiyar zuwa birni mai garu. 9 A shekara ta huɗu na Hezekiya, wadda ke dai-dai da shekara ta bakwai ta Hosheya ɗan Elah sarkin Isra'ila, Shalmanesar sarkin Asiriya ya kawo wa Samariya hari ya mamaye su. 10 A ƙarshen shekaru uku suka ɗauke ta, a shekara ta shida na Hezekiya, wanda ke shekara ta tara ta Hosheya sarkin Isra'ila; a wannan hanyar kuwa aka kame Samariya. 11 Sai sarkin Asiriya ya ɗauki Isra'la zuwa Asiriya ya sa su a Halah da kuma a kogin Habor a Gozan da biranen Medeyawa. 12 Ya yi wannan ne saboda ba su yi biyayya da muryar Yahweh Allahnsu ba, amma sun wofintar da ƙudurorin alkawarinsa, dukkan abin da Musa bawan Yahweh ya ummurta. Suka ƙi su ji ko su aikata shi. 13 Sa'an nan a shekara ta goma sha huɗu ta Sarki Hezekiya, Senakerib sarkin Asiriya ya kai wa dukkan birane masu garu na Yahuda hari ya kuma danƙe su. 14 Saboda haka Hezekiya sarkin Yahuda ya aika wa sarkin Asiriya, wanda ke Lakish da kalma, cewa, "Na yi maka laifi. Ka janye daga gare ni. Duk abin da ka ɗora mani zan ɗauka." Sarkin Asiriya kuwa ya umarci Hezakiya sarkin Yahuda ya bada talanti ɗari uku na azurfa da talatin na zinariya masu yawa. 15 Sai Hezekiya ya ba shi dukkan azurfan da ke gidan Yahweh da na cikin ma'aji na fãdar sarki. 16 Sa'an nan Hezekiya ya ciro zinariyar da ke ƙofofin haikalin Yahweh da kuma daga madogaran da aka kafa; ya ba da zinarin ga sarkin Assiriya. 17 Amma sarkin Asiriya ya shiryo gagarumin sojojinsa, Ya aiki Tartan da Rabsaris da babbar rundunar sojojin daga Lakish zuwa ga Sarki Hezekiya a Yerusalem. Suka yi tafiya ta hanyoyin su ka kai wajen Yerusalem. Suka nufi kududdufi na sama wurin kwanciyar ruwa, wanda ke a kan kwaruwa zuwa wurin wanki, suka tsaya ta wurin. 18 Sa'ad da suka yi kira ga Sarki Hezekiya, Eliyakin ɗan Hilkiya, wanda ke wakilin gidan da Shebna magatakarda da Yowa ɗan Asaf, mai rubutun rohoto suka je su sadu da su. 19 Sai shugaban rundunar sojojin ya ce masu su faɗa wa Hezekiya abin da sarki mai girma, sarkin Asiriya, ya faɗa: "Mene ne masomin karfin halinka? 20 Kana faɗin kalmomi marasa amfani ne kawai, cewa akwai tarayya da ƙarfi domin yaƙi. Ga wa kake dogara? har da za ka tayar mani? 21 Duba, ka dogara ga sandan tafiya na raunannan ciyayin Masar, amma idan mutum ya manne mata, za ta haɗu da hannunsa ta soke shi. Wannan ne abin da Fir'auna sarkin Masar ya ke ga duk wanda ya dogara gare shi. 22 Amma idan ka ce mani, 'Muna dogara ga Yahweh Allahnmu ne,' ba shi ne wanda Hezekiya ya ɗauke masa wuraren sama da bagaden ba, ya kuma cewa Yahuda da Yerusalem, 'Lallai sai kun yi sujada a gaban bagaden nan a Yerusalem'? 23 Yanzu dai, ina so in yi maka gudunmawa daga ubangijina sarkin Asiriya. Zan baka dawakai dubu biyu, idan za ka samar masu mahaya. 24 Ta yaya zaka ma iya karawa da mafi ƙanƙantar shugaban sojojin ubangijina? Ka bada ƙarfinka ga Masar domin karusai da mahaya! 25 Na taɓa zuwa nan in yi yaƙi in hallka ta ba tare da Yahweh ba? Yahweh ya ce mani, 'Ka kai wa ƙasar nan hari ka hallaka ta."' 26 Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkaya da Shebna da Yowa suka cewa shugaban rundunar, "In ka yarda ka yi magana da harshen Aramayik, don shi muka gane. Kada ka yi magana da mu da harshen Yahuda a kunnen mutanen da ke a bangon." 27 Amma shugaban rundunar ya ce masu, Ba maganar da ubangijina ya aike ni ga ubangijinku in faɗa kenan ba? Ba shi ya aiko ni wurin mazan da ke zaune a bangon, waɗanda za su ci kaãshinsu su kuma sha fitsarinsu tare da ku ba?" 28 Sa'an nan shugaban rudunar sojojin ya tsaya ya yi kira da babbar murya a harshen Yahudawa, cewa, "Ku saurari maganar sarki mai girma, sarkin Asiriya. 29 Sarkin ya ce, 'Kar ka bar Hezekiya ya ruɗe ka, gama ba zai iya ya ƙubutar da kai daga ikona ba. 30 Kada ku yarda Hezekiya yasa ku dogara ga Allah, cewa, "Hakika Yahweh zai cece mu, kuma ba za a ba da wannan birnin ga hannun sarkin Asiriya ba."" 31 Kada ku saurari Hezekiya, gama ga abin da sarkin Asiriya ya ce: 'Ku yi amana da ni ku kuma zo gare ni. Sa'an nan kowannen ku zai ci daga tasa kuringar inabi da itacen ɓaurensa ya kuma sha daga cikin randarsa. 32 Zaku yi haka har lokacin da zan zo in ɗauke ku in kaiku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, ƙasar gurasa da lambuna, ƙasar itatuwan zaitun da zuma, saboda ku rayu kar ku mutu.' Kada ka saurari Hezekiya sa'ad da yake ƙoƙarin rinjayarku, cewa, 'Yahweh zai cece mu.' 33 Ko akwai wani daga cikin allolin mutanen da ya ceto su daga hanun sarkin Asiriya? 34 Ina allolin Hamat da Arfad? Ina allolin Sefabayim da Hena da Ivvah? Sun ceto Samariya daga hannuna ne? 35 A cikin allolin ƙasashe, akwai wani allahn da ya ceci ƙasarsa daga ikona? Ta yaya Yahweh zai ceci Yerusalem daga ikona?" 36 Amma mutane suka yi shiru basu ce uffan ba, domin sarki ya bada umarni, "Kada ku amsa masa." 37 Sai Eliyakim ɗan Hikiya, wanda ke shugabantar gidan; Shebna magatakarda; da Yowa ɗan Asaf, mai ɗaukan rohoto, suka zo wurin Hezikiya da tufafinsu a yage, suka bada rahoto gare shi kan maganganun babban hafsan.

Sura 19

1 Sai ya zamana sa'ad da sarki Hezekiya ya ji rohotonsu, ya yayyaga tufafinsa, ya rufe kansa da tsumma, ya je gidan Yahweh. 2 Ya aiki Eliyakim, wanda ke lura da gidan, da Shebna magatakarda, da dattawan firistoci, dukkan su saye da tufafin tsumma, ga annabi Ishaya ɗan Amoz. 3 Suka ce masa, "Hezekiya ya ce, 'wannan ranar ta ƙunci da tsutawa da bankunya, gama 'ya'ya sun kai lokacin haifuwa amma babu ƙarfi domin haifar su. 4 Yana yiwuwa Yahweh Allahnka zai ji dukkan kalmomin shugaban rundunar, wanda sarkin Asiriya ubangijinsa ya aiko don ya jã da Allah, ya kuma tsauta wa kalmomin da Yahweh Allahnka ya ji. To ka ɗaga murya cikin addu'arka domin ragowar da ke nan har yanzu."" 5 Saboda haka barorin sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, 6 sai Ishaya ya ce masu, "Ku faɗawa shugabanku: 'Yahweh ya ce, "Kada ku ji tsoron kalmomin da kuka ji, waɗanda barorin sarkin Asiriya suka yi mani rashin kunya. 7 Duba, zan sa wani ruhu a cikinsa, sai ya ji wani rohoto ya koma zuwa ƙasarsa. Zan sa ya fãɗi ta takobi a nasa ƙasan.""' 8 Sa'an nan shugaban rundunan ya komo ya tarar sarkin Asiriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji wai sarkin ya tashi daga Lakish. 9 Sa'an nan Senakirib ya ji cewa Tirhaka sarkin Kush da Masar sun yi shiri su yaƙe shi, sai ya aiki manzanni kuma ga Hezekiya da saƙo: 10 "Ku cewa Hezekiya sarkin Yahuda, 'Kada ka bar Allahnka wanda ka dogara gare shi ya ruɗe ka, cewa, "Ba zan ba da Yerusalem ga hannun sarkin Asiriya ba." 11 Duba, ka ji abin da sarkin Asiriya ya yi wa dukkan ƙasashe da ya hallakar da su sarai. To za ka kuɓuta? 12 Allolin al'ummai sun kuɓutar da su ne, al'umman da ubannina suka hallakar wato Gozan da Haran da Rezef da mutanen Eden a Tel Assar? 13 Ina sarakunan Hamat da na Arfad da na biranen Sefabayim da Ivvah?"' 14 Hezekiya ya karɓa wasiƙar daga manzannin ya karanta ta. Sai ya haura zuwa gidan Yahweh ya shinfiɗa ta a gabansa. 15 Sa'an nan Hezekiya ya yi addu'a a gaban Yahweh ya ce, '"Yahweh mai runduna, Allahn Isra'ila, Kai da ke zaune bisan kerubim, kai kaɗai ne Allah akan dukkan mulkokin duniya. Ka yi sammai da duniya. 16 Ka kasa kunnenka, Yahweh, ka saurara. Ka buɗe idanuwanka Yahweh, ka gani, ka kuma ji kalaman Senakerib, waɗanda ya aiko don ya yi wa Allah mai rai ba'a. 17 A gaskiya, Yahweh, sarakunan Asiriya sun hallakar da al'ummai da ƙasashensu. 18 Suka sa allolinsu cikin wuta, gama su ba alloli ba ne amma aikin hannuwan mutane ne, katako da dutse kawai. Don haka Asiriyawan suka hallaka su. 19 Yanzu, Yahweh Allahnmu, I na roƙe ka, ka cece mu, daga ikonsa, saboda dukkan mulkokin duniya su sani cewa kai, Yahweh, kai kaɗai ne Allah." 20 Sa'an nan Ishaya ɗan Amoz ya aiko da saƙo ga Hezekiya, cewa, "Yahweh, Allahn Isra'ila ya faɗi, 'Saboda ka yi addu'a gare ni game da Senakerib sarkin Asiriya, Na ji ka. 21 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗa game da shi: "Budurwan nan ɗiyar Sihiyona ta rena ka tana kuma yi maka dariyar reni. Ɗiyar Yerusalem na girgiza maka kanta. 22 Wane ne ka saɓa wa ka kuma yi wa reni? Wanda kuma ka ɗaukaka muryarka ka ɗaga idanuwanka cikin taƙama gãba da shi? Gãba da Mai Tsarkin Isra'ila! 23 Ta manzaninka ka saɓa wa Ubangiji, har ka ce, 'Tare da ɗumbin karusaina na kai duwatsu mafi tsawo, mafi tsawon tudddai ta Lebanan. Zan datse dogayen itatuwan sida da zaɓaɓɓun itatuwan Sifires a wurin. Zan shiga cikin manisancin kurminta, da dajinta da ya fi bada 'ya'ya. 24 Na gina rijiyoyi na kuma sha ruwan baƙuwar ƙasa. Na busar da dukkan kogunan Masar a ƙarƙashin tafin ƙafafuna.' 25 Ba ka taɓa jin yadda na ƙudura shi da daɗewa ba, na kuma yi shi tun zamanin zamanai ba? Yanzu zan aiwatar da shi. Kana nan domin rage birane masu wadata su zama kufai. 26 Mazaunansu, masu ƙarancin ƙarfi, suna a warwatse, kuma an kunyata su. Su ganyaye ne a fili, koriyar ciyawa, ciyawa a rufi ko a fili, da aka ƙone kafin ta yi girma. 27 Amma na san yadda kake zama a ƙasa da fitarka da shigarka, da tawayenka gãba da ni. 28 Saboda tayarwarka gãba da ni, kuma saboda taƙamarka ta kai kunuwana, zan sa ƙugiya a hancinka, da linzami a bakinka; zan komo da kai baya ta inda ka iso." 29 Wannan zai zama alama a gare ka: wannan shekarar za ku ci abin da ke girma a jeji, a shekara ta biyu kuma, abin da ya fita daga nan. amma a shekara ta uku kuma dole ka shuka ka girba, ka shuka gonakin inabi ka ci 'ya'yan itatuwansu 30 Ragowar gidan Yahuda da suka rayu za su sake yin saiwa su yi "ya'ya. 31 Gama daga Yerusalem za a fito da ragowa, daga Tsaunin Sihiyona waɗanda suka tsira za su zo. Himmar Yahweh mai runduna za ta yi haka. 32 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka game da sarkin Asiriya: "Ba zai zo cikin birnin ko ya harba kibiya a nan ba. Ko kuwa ya zo gabansa da garkuwa ko ya gina sansani gãba da shi ba. 33 Ta hanyar da ya zo, ta nan kuma zai tafi; ba zai shiga wannan birnin ba - wannan furcin Yahweh ne." 34 Gama zan kãre wannan birnin in kuɓutar da shi, domin kaina da kuma domin bawana Dauda."' 35 Sai ya zamana a daren nan da mala'ikan Yahweh ya je ya kai hari ga sansanin Asiriyawa, ya sa sojoji 185,000 suka mutu. Sa'ad da mazaje suka tashi da sassafe, sai ga gawawwaki kwance ko'ina. 36 Saboda haka Senakerib sarkin Asiriya ya bar Isra'ila ya tafi gida ya zauna a Nineba. 37 Bayan 'yan lokuta ƙaɗan, yayin da yake yin sujada a gidan allansa Nisrok, sai 'ya'yansa Adrammalek da Shareza suka kashe shi da takobi. Sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai Esarhadon ɗansa ya zama sarki a madadinsa

Sura 20

1 A kwanakin nan Hezekiya ya yi rashin lafiya har ya kusa da mutuwa. Saboda haka annabi Ishaya ɗan Amoz, ya zo gare shi, ya ce masa, "Yahweh ya ce, 'Ka shirya gidanka; gama zaka mutu, ba zaka rayu ba."' 2 Sa'an nan Hezekiya ya juya fuskarsa ga bango ya yi addu'a ga Yahweh yana cewa, 3 "In ka yarda Yahweh, ka tuna da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukkan zuciyata, da kuma abubuwan masu kyau da na yi a fuskarka." Sai Hezekiya ya yi kuka. 4 Kafin Ishaya ya fita cikin tsakiyar fãdar, maganar Yahweh ya zo gare shi, cewa, 5 "Ka juya baya, ka cewa Hezekiya, shugaban mutanena, 'Wannan shi ne abin da Yahweh, Allahn Dauda kakanka na asali, ya ce: "Na ji addu'arka, na ga hawayenka. Ina gab da warkar da kai a rana ta uku, kuma za ka haura zuwa gidan Yahweh. 6 Zan ƙara shekaru goma sha biyar ga rayuwarka, zan kuɓutar da wannan birnin daga hannun sarkin Asiriya, kuma zan kare birnin nan domin kaina domin kuma bawana Dauda""" 7 Sai Ishaya yace, "Ka ɗauki curin ɓaure."Su ka yi haka suka sa a marurunsa, sai ya samI lafiya. 8 Hezikiya ya cewa Ishaya, "Mene ne zai zama alamar cewa Yahweh zai warkar da ni, da kuma zai sa ni in je haikalin Yahweh a rana ta uku?" 9 Ishaya ya amsa, "Wannan ne zai zama alama dominka daga Yahweh, cewa Yahweh zai yi abin da ya faɗa. Inuwa ta yi gaba da taki goma, ko ta yi baya da taki goma?" 10 Hezekiya ya amsa, "Abu mai sauki ne ga inuwa ta yi gaba da taƙi goma. A'a, bari Inuwa ta yi baya da taƙi goma." 11 Sai annabi Ishaya ya yi kira ga Yahweh, sai ya komo da inuwar taƙi goma baya, daga inda ta motsa a matakalin Ahaz. 12 A lokacin nan Marduk-Baladan ɗan Baladan sarkin Babila ya aika da wasiƙu da kyautai ga Hezekiya, gama ya ji cewa Hezekiya ba shi da lafiya. 13 Hezekiya ya saurari wasiƙun nan, sai ya nuna wa manzaNnin dukkan fǎda da abubuwa masu daraja da azurfa da zinariya da kayan ƙanshi da mai, mai daraja da gidan ajiyar kayan yaƙi da dukkan abin da ke samuwa a gidajen ajiyarsa. Babu wani abu a gidansa, ko a mulkinsa, da Hezekiya bai nuãna masu ba. 14 Sa'annan annabi Ishaya ya zo wurin sarki Hezekiya ya tambaye shi, "Mene ne waɗannan mazajen suka ce maka? Daga ina suka fito?" Hezekiya ya ce, "Sun zo daga ƙasa mai nisa ta Babila." 15 Ishaya ya tambaye shi, "Mene ne suka gani a gidanka?" Hezekiya ya amsa, "Sun ga kome a gidana. Babu wani abu cikin abubuwa masu daraja da ban nuna masu ba." 16 Sai Ishaya ya cewa Hezekiya, "Ka saurari maganar Yahweh: 17 'Duba, ranakun na kusatowa da kowanne abu a fǎdarka, da abubuwan da kakaninka suka ajiye har zuwa yau, za a ɗauke su zuwa Babila. Babu abin da zai rage, inji Yahweh. 18 'Ya'yan da aka haifa maka waɗanda kai da kanka kake mahaifinsu - za a ɗauke su, zasu kuma zama bãbãni a fãdar sarkin Babila."' 19 Sa'annan Hezekiya ya cewa Ishaya, "Maganar Yahweh da ka faɗa tana da kyau." Saboda yana tunanin, "Ba za a sami salama da zaman lafiya a kwanakina ba?" 20 Game da waɗansu zantuttuka da suka shafi Hezekiya, da dukkan ikonsa da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa, da yadda ya kawo ruwa cikin birnin - ba a rubuce suke cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 21 Hezekiya ya yi barci tare da kakaninsa, sai Manasse ɗansa ya zama sarki a madadinsa.

Sura 21

1 Manasse na da shekaru goma sha biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru hamsin da biyar a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hefziba. 2 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh, kamar abubuwan banƙyama na al'umman da Yahweh ya kora a gaban mutanen Isra'ila. 3 Gama ya sake ginin wuraren bisa da Hezekiya mahaifinsa ya rurrushe, sai ya gina bagadi domin Ba'al, ya yi sandan Ashera, kamar yadda Ahab sarkin Isra'ila ya yi, ya kuma russuna wa dukkan tauraron sammai ya yi masu sujada. 4 Manasse ya gina bagadai a cikin gidan Yahweh, ko da yake Yahweh ya ummurta, "A Yerusalem ne sunana zai kasance har abada." 5 Ya gina bagadi domin dukkan taurarin sammai a filayen ciki biyu da ke gidan Yahweh. 6 Ya sa ɗansa ya wuce ta wuta, ya yi sihiri da dubã da ma'amula da waɗanda ke magana da matattu da waɗanda ke magana da ruhohi. Ya yi mugunta da yawa a gaban Yahweh, yana sa shi yin fushi. 7 Sarrafaffiyar siffa ta Ashera da ya yi, ya sata a gidan Yahweh. A game da wannan gidan ne Yahweh ya yi magana da Dauda da Suleimanu ɗansa; ya ce: "A wannan gidan da kuma Yerusalem ne, inda na zaɓa daga dukkan ƙabilun Isra'ila, da zan sa sunana har abada. 8 Ba zan sa ƙafafun Isra'ila su ƙara fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, Idan har zasu kula su yi biyayya da dukkan abin da na ummurce su, su kuma bi dukkan dokokin da bawana Musa ya Ummurce su." 9 Amma mutanen ba su ji ba, Manasse kuma ya jagorance su ga yin aikin mugunta fiye da al'umman da Yahweh ya hallakar a gaban mutanen Isra'ila. 10 Sai Yahweh ya yi magana ta wurin bayinsa annabawa, cewa, 11 "Saboda Manasse sarkin Yahuda ya yi waɗannan abubuwan banƙyama, ya kuma aikata mugunta fiye da dukkan abin da Amoriyawan da suke gabaninsa suka yi, ya kuma sa Yahuda ya yi zunubi da gumakansa, 12 don haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Duba, Ina gab da kawo bala'i a Yerusalem da Yahuda wanda duk wanda ya ji abin, dukkan kunuwansa za su ƙaɗu. 13 Zan miƙa a saman Yerusalem layin magwajin da zan gwada Samariya, da layin ma'aunin gwada gidan Ahab; Zan share Yerusalem fes-fes, kamar yadda mutum ke wanke kwano, yana share ta da kuma goge ta yana juya ta ko'ina. 14 Zan jefar da ragowar gãdona in ba da su ga hannun maƙiyansu. Za su zama waɗanda aka yi wa laifi da ganima ga dukkan makiyansu, 15 saboda sun yi abin mugunta a gabana, suka kuma zuga ni ga fushi, tun daga ranar da kakaninsu suka fito daga Masar, har yau." 16 Haka kuma, Manasse ya zub da jinin adalai da yawa, har sai da ya cika Yerusalem daga gefe ɗaya zuwa wani gefen da mutuwa. Banda zunubin da ya sa Yahuda suka yi, sa'ad da suka yi mugunta a gaban Yahweh. 17 A game da sauran zantuttukan da ya shafi Manasse da dukkan abin da ya yi, da zunuban da ya aikata, ba a rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 18 Manasse ya yi barci tare da kakaninsa aka bizne shi a lanbun gidansa, a lanbun Uzza. Amon ɗansa ya zama saki a madadinsa. 19 Amon na da shekaru ashirin da biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet; ita ɗiyar Haruz na Jotba ne. 20 Ya yi akin mugunta a gaban Yahweh, kamar yanda Manasse mahaifinsa ya yi.

21 Amon ya bi dukkan hanyar da mahaifinsa ya yi tafiya ya kuma bauta wa gumakan da mahaifisa ya bauta wa, ya yi masu ruku'u. 22 Ya ƙi Yahweh, Allah na ubanninsa, bai kuma yi tafiya a hanyar Yahweh ba. 23 Barorin Amon suka shirya maƙarƙashiya gãba da shi suka kashe shi a cikin gidansa. 24 Amma mutanen ƙasar suka kashe dukkan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiya, sai suka maida Yosiya, ɗansa sarki a madadinsa. 25 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Amon da abin da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 26 Mutanen suka bizne shi a kabarinsa cikin lambun Uzza, sai Yosiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.

Sura 22

1 Yosiya yana da shekaru takwas sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru talatin da uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yedida (Ita ɗiyar Adayiya na Bozkat ce). 2 Ya yi abin da ya dace a gaban Yahweh. Ya yi tafiya a hanyar Dauda kakansa, bai kuma kauce mata zuwa dama ko hagu ba. 3 Sai ya zamana a shekara ta goma sha takwas ta sarki Yosiya, ya aike Shafan ɗan Azaliya ɗan Mashullam, magatakarda, zuwa gidan Yahweh, cewa, 4 "Jeka wurin Hilkiya babban firist ka gaya masa ya ƙirga ƙuɗin da aka kawo cikin gidan Yahweh, wanda masu gadin haikali suka tara daga mutane. 5 A ba da shi ga hannun ma'aikatan da ke lura da gidan Yahweh, su ba ma'aikatan da ke gidan Yahweh domin su yi gyare-gyare a haikali. 6 Su bada ƙuɗi ga kafintoci da magina, a kuma sayi katakon timba a buga dutse domin gyaran haikali." 7 Amma babu bukatar rohoton kashe kuɗin da aka ba su, saboda sun yi aiki da shi cikin aminci. 8 Hilkiya babban firist ya cewa Shafan magatakarda, "Na sami littafin dokoki a gidan Yahweh." Sai Hilkiya ya ba da littafin ga Shafan, sai ya karanta shi. 9 Shafan ya je ya kai littafin gun sarki, ya kuma sanar da shi, cewa, "Barorinka sun kashe kuɗin da aka samu a haikali kuma sun ba da shi ga hannun ma'aikatan da ke shugabancin lura da gidan Yahweh." 10 Sa'annan Shafan magatakarda ya faɗa wa sarkin, "Hilkiya firist ya ba ni littafi." Sai Shafan ya karanta wa sarki. 11 Sai ya zamana sa'ad da sarki ya ji kalmomin dokokin, sai ya yayyaga tufafinsa. 12 Sarkin ya ummurci Hilkiya firist da Ahikam ɗan Shafan da Akbor ɗan Mikayiya da Shafan magatakarda da Asayiya bawansa cewa, 13 "Ku je ku ji daga wurin Yahweh domina da mutanen da dukkan Yahuda, saboda kalmomin wannan littafin da aka samo. Gama fushin Yahweh a gare mu na da girma saboda kakanninmu ba su saurari kalmomin wannan littafin don yin biyayya game da dukkan abin da aka rubuta game da mu ba." 14 Sa'an nan Hilkiya firist da Ahikam da Akbor da Shafan da Asayiya suka je wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikvah ɗan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiyan sutura (tana zaune a Yerusalem a yankin sabon birnin), sai suka yi magana tare da ita. 15 Ta ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗI: 'Gaya wa mutumin da ya aike ki gare ni, 16 Ga abin da Yahweh ya faɗi: 'Duba, zan auko da bala'i ga wannan wurin tare da mazaunansa, bisa ga dukkan abin da aka rubuta a littafin da sarkin Yahuda ya karanto. 17 Saboda kun yashe ni kuka kuma ƙona turare ga waɗansu alloli, don su tsokane ni ga yin fushi da dukkan ayyukan da suka yi - don haka na fito da wutar hasalata gãba da wannan wurin, kuma ba za ta mutu ba."' 18 Amma ga sarkin Yahuda, Wanda ya aike ku ku nemi nufin Yahweh, ga abin da zaku ce masa: "Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗi haka: 'game da kalmomin da ka ji, 19 saboda zuciyarka ta yi taushi, ka kuma yi tawali'u a gaban Yahweh, sa'ad da ka ji abin da na faɗa gãba da wannan wurin da mazaunansa, akan yadda zasu zama kango da la'ana, saboda kuma ka yayyaga tufafinka ka yi kuka a gabana, Ni kuma na saurare ka - wannan furcin Yahweh ne. 20 Duba, Zan tara ka ga kakanninka, kuma za a tara ka ga kabarinka cikin salama. Idanuwanka baza su ga dukkan masifun da zan auko da su akan wurin nan ba.""" Sai mazajen suka mayar da saƙon ga sarki.

Sura 23

1 Sa'an nan sarki ya aiko da manzanni waɗanda suka tara masa dukkan dattawan Yahuda da Yerusalem. 2 Sai sarki ya haura zuwa gidan Yahweh da dukkan mazaunan Yahuda da Yerusalem da ke tare shi, da firistoci da annabawa da dukkan mutane, daga ƙanƙani zuwa babba. Sai ya karanta dukkan kalmomin littafin Alƙawarin da aka samu a gidan Yahweh a kunnuwansu. 3 Sarkin ya tsaya a gefen ginshiƙi ya yi alƙawari ga Yahweh cewa zai bi Yahweh ya kiyaye dokokinsa, da ummurnansa da farillansa, da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa, ya kuma ka'idantar da kalmomin alƙawarin da aka rubuta a wannan littafin. Saboda haka mutanen suka yarda su tsaya akan alƙawarin. 4 Sa'an nan sarki ya ummurce Hilkiya babban firist da firistoci da ke ƙarƙashinsa da masu tsaron ƙofa su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al da Ashera daga haikalin Yahweh, da dukkan taurarin sama. Ya ƙone su a bayan Yerusalem a filayen Kwarin Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel. 5 Ya kuma kawar da firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuda suka naɗa don a ƙona turare a wuraren tuddai a biranen Yahuda da kewayen Yerusalem - waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana da wata da duniyoyi da dukkan taurarin sama. 6 Ya fitar da sandan Ashera daga haikalin Yahweh, wajen Yerusalem zuwa Kwarin Kidron ya ƙona shi a wurin. Ya buge ta har ga ƙura ya zubar da ƙurar cikin kaburburan talakawa. 7 Ya rusa ɗakunan karuwai matsafa waɗanda ke a haikalin Yahweh, inda matan ke saƙa tufafin Ashera. 8 Yosiya ya fitar da dukkan firistoci daga biranen Yahuda ya ƙazantar da tuddan wuraren da firistoci ke ƙona turare, daga Geba zuwa Biyasheba. Ya rurrushe tuddan wuraren a kofofin da ke mashigin ƙofofin Yoshuwa (gwamnan birnin), a gefen hagu na ƙofar birnin. 9 Ko da shike ba a bar firistocin waɗannan tuddan wuraren su yi aiki a bagadin Yahweh a Yerusalem ba, sun ci gurasa mara yisti cikin 'yan'uwansu maza. 10 Yosiya ya ƙazantar da Tofet, wanda ke cikin Kwarin Ben Hinom, saboda kar kowa ya sa ɗansa ko ɗiyarsa bi ta wuta a matsayin hadaya ga Molek. 11 Ya ɗauki dawakan da sarakunan Yahuda suka miƙa wa rana, Suna nan a wurin a ƙofar haikalin Yahweh kusa da ɗakin Natan-Melek shugaban shirayin da ke cikin farfajiya. Yosiya ya ƙona karusan rana. 12 Sarki Yosiya ya rurrusa bagadan da ke bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuda suka yi, da bagaden da Manasse ya yi a farfajiya biyu ta haikalin Yahweh. Yosiya ya rugurguza su ya jefar da su a Kwarin Kidron, 13 Sarkin ya rurrushe tuddan wuraren tsafi da ke gabashin Yerusalem kudu da dutsen hallaka wanda Suleman sarkin Isra'ila ya gina wa Ashtoret da ƙazantacciyar gunkiyar Sidoniyawa; don Kemosh, ƙazantaccen gunkin Mowab; kuma na Molek, da ƙazantaccen gunkin Amonawa. 14 Ya rurrushe ginshiƙai na dutse rugu-rugu ya kuma sassare sandunan Ashera sa'an nan ya rufe wuraren da ƙasussuwan mutane. 15 Yosiya ya rurrushe bagadan da ke a Betel kakaf da wuri mai tudu da Yerobowam ɗan Nebat (wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi) ya gina. Ya kuma ƙona bagadin da wuri mai tudu, ya buge shi har ga ƙura, ya ƙona sandan Ashera. 16 Yayin da Yosiya ya dubi dukkan kewayen, sai ya gano kaburburan da ke kan tuddu, ya aika maza su kwaso ƙasusuwan daga kaburburan; sai ya ƙona su a bagadin, wanda ya ƙazantar da shi. Wannan bisa ga maganar Yahweh ce wadda mutumin Allah ya faɗa, mutumin da ya faɗi waɗannan abubuwan tuntuni. 17 Sa'an nan ya ce, "Wanne kabari ne waccan da na gani?" Mutanen birnin suka gaya masa, "Waccan ne kabarin mutumin Allah da ya zo daga Yahuda, ya yi magana akan abubuwan nan da kayi gãba da bagaden Betel." 18 Sai Yosiya ya ce, ku bar shi kawai. Kada kowa ya motsa ƙasusuwansa, sai suka bar ƙasusuwansa tare da na annabin da yazo daga Samariya. 19 Sa'an nan Yosiya ya cire dukkan gidajen wuraren kan tudu da ke a Samariya, wanda sarakunan Isra'ila su ka yi, da ya sa Allah ya yi fushi. Ya yi masu dai-dai da abin da aka yi a Betel. 20 Ya yayyanka dukkan firistocin tuddan wuraren akan bagadan sai ya ƙona ƙasusuwan mutane akan su. Sa'an nan ya koma Yerusalem. 21 Sa'an nan Sarkin ya ummurci dukkan mutane cewa, "Ku kiyaye bikin Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku, kamar yadda aka rubuta a Littafin Alƙawari." 22 Irin hidimar bukin nan ba a taɓa yinsa ba tun daga kwanakin da alƙalai suka yi mulkin Isra'ila, ko dukkan kwanakin sarakunan Isra'ila ko Yahuda. 23 Amma a shakara ta goma sha takwas ta sarki Yosiya an yi bikin wannan Ƙetarewa na Yahweh a Yerusalem. 24 Yosiya kuwa ya kori dukkan mabiya waɗanda ke magana da matattu ko ruhohi. Ya kuma kori kawunan gidaje da gumaka da dukkan abubuwan banƙyama da ake gani a Yahuda da Yerusalem, saboda a ka'idantar da kalmomin dokokin da aka rubuta a littafin da Hilkiya firist ya samo a gidan Yahweh. 25 Kafin Yosiya, ba a yi wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Yahweh da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa da dukkan ƙarfinsa ba, wanda kuma ya bi dukkan dokokin Musa. Ba a kuwa yi wani sarki kamar Yosiya ba a bayansa. 26 Duk da haka, Yahweh bai juya baya daga zafin fushinsa ba, wanda ya yi gãba da Yahuda saboda dukkan abubuwan da Manasse ya yi na sashi shi ya yi fushi. 27 Saboda haka Yaweh ya ce, "Zan kuwa kawar da Yahuda daga fuskata, kamar yadda na tsige Isra'ila, zan kuma jefar da birnin da na zaɓa, Yerusalem, da kuma gidan da nace, 'Sunana zai kasance a wurin.'" 28 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yosiya da dukkan abubuwan da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 29 A kwanakinsa, Fir'auna Neko, sarkin Masar, ya je yaƙi da sarkin Asiriya a kogin Yuferatis. Sarki Yosiya ya je ya sami Neko a yaƙi, sai Neko ya kashe shi a Megiddo. 30 Sai baran Yosiya ya ɗauke shi a karusa daga Megiddo, ya taho da shi Yerusalem ya bizne shi a nasa kabarin. Sa'an nan Mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoahaz ɗan Yosiya, suka shafa masa mai, suka mai da shi sarki a madadin mahaifinsa. 31 Yehoahaz yana da shekaru ashirin da uku lokacinin da ya fara mulki, ya yi mulkin shekaru uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hamutal; ita ɗiyar Irmiya na Libna ne, 32 Yehoahaz ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh, kamar dukkan yadda kakaninsa suka yi. 33 Fir'auna Neko ya ɗaure shi a Ribla, a ƙasar Hamat, saboda kar ya yi mulkin Yerusalem. Sa'an nan Neko ya yi wa Isra'ila tarar talanti ɗari na azurfa da talanti ɗaya na zinariya. 34 Fir'auna Neko ya sa Eliyakim ɗan sarki Yosiya ya zama sarki a madadin mahaifinsa, sai ya canza masa suna zuwa Yehoiakim. Amma ya ɗauki Yehoahaz zuwa Masar har Yehoahaz ya mutu a can. 35 Yehoiakim ya biya azurfa da zinariya ga Fir'auna. Don ya iya yin yadda Fir'auna yake so, Yehoiakim ya sa ƙasar biyan haraji kuma ya tilasta kowanne mutum daga cikin mutanen ƙasar ya biya da azurfa da zinariya bisa ga yanayin tsarinsu. 36 Yehoiakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki na shekara goma sha ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Zebida ɗiyar Fediya na Ruma. 37 Yehoiakim ya yi akin mugunta a fuskar Yahweh, kamar yadda kakaninsa suka yi.

Sura 24

1 A kwanakin Yehoiakim, Nebukadnezza sarkin Babila ya kai wa Yahuda hari; Yehoiakim ya zama bawansa na shekaru uku. Sa'an nan Yehoiakim ya juya ya tayar wa Nebukadnezza. 2 Yahweh ya aiko da Yehoiakim, maharan Kaldiyawa da Aramiyawa da Mowabawa da Amoniyawa, ya aike su gãba da Yahuda su hallakar da shi. Wannan ya zo dai-dai ne da maganar Yahweh da aka faɗa ta barorinsa annabawa. 3 Hakika ta bakin Yahweh ne wannan ya zo ga Yahuda, ya cire su daga fuskarsa, saboda laifofin Manasse, dukkan abin da ya yi, 4 kuma saboda zub da jinin bayin Allah da ya yi, gama ya cika Yerusalem da jinin adalai, Yahweh bai yi niyar gafarta hakan ba. 5 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yehoiakim, da dukkan abubuwan da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 6 Yehoiakim ya yi barci tare da kakaninsa, sai Yehoiacin ɗansa ya zama sarki a madadinsa. 7 Sarkin Masar bai sake fita ƙasarsa ya kai wa wani hari ba, saboda sarkin Babila ya ƙwato dukkan ƙasashen da ke ƙarƙashin sarkin Masar, daga rafin Masar har zuwa kogin Yuferatis. 8 Yehoiacin ya na da shekaru goma sha takwas yayin da ya fara mulki a Yerusalem; ya yi mulkin wata uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Nehushta; ɗiyar Elnatan na Yerusalem. 9 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abubuwan da mahaifinsa ya yi. 10 A lokacin nan ne sojojin Nebukadnezza sarkin Babila suka kai wa Yerusalem hari, suka kewaye birnin da yaƙi, 11 Nebukadnezza ya zo birnin yayin da sojojinsa ke kewaye da shi, 12 sai Yehoiacin sarkin Yahuda ya je ya tari sarkin Babila, shi da mahaifiyarsa da barorinsa da 'ya'yansa da hafsoshinsa. Sarkin Babila ya kama shi a shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa. 13 Nebukadnezza ya ɗauki dukkan abubuwa masu daraja na gidan Yahweh, da waɗanda ke fãdar sarki. Ya farfashe dukkan tasoshin zinariyar da sarki Suleman ya yi a haikalin Yahweh, kamar yadda Yahweh ya ce zai faru. 14 Ya ɗauki 'yan zuwa zaman talala daga dukkan Yerusalem, da dukkan shugabanin da dukkan mayaƙa da kamammu dubu goma da dukkan 'yan fasaha da maƙera. Babu wanda aka bari sai fakirai na ƙasar. 15 Nebukadnezza ya ɗauki Yehoiacin zuwa zaman talala a Babila. da kuma mahaifiyar sarki da matansa da hafsoshi da manyan mazajen ƙasar. Ya ɗauke su zuwa zaman talala daga Yerusalem zuwa Babila. 16 Dukkan mayaƙa dubu bakwai da masu sana'a da maƙera dubu ɗaya dukkansu ƙarfafa ne da suka isa zuwa yaƙi - sarkin Babila ya kawo waɗannan mutanen ga zaman talala a Babila. 17 Sarkin Babila ya sa Mataniya, ɗan'uwan mahaifin Yehoiacin, ya zama sarki a madadinsa ya kuma canza masa suna zuwa Zedekiya. 18 Zedekiya yana da shekaru ashirin da ɗaya yayin da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru goma sha ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hamutal; ita ɗiyar Irmiya na Libna ne. 19 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abin da Yehoiakim ya yi. 20 Ta dalilin fushin Yahweh ne, dukkan waɗannan abubuwan suka faru a Yerusalem da Yahuda, har sai ya kore su daga gare shi. Sa'an nan Zedekiya ya yi tayar da gãba da sarkin Babila.

Sura 25

1 Sai ya zamana a shekara na tara a mulkin Zedekiya, a wata na goma, a rana ta goma ga watan, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo da dukkan sojojinsa gãba da Yerusalem. Ya yi sansani kusa da ita, ya gina kagarai kewaye da ita. 2 Saboda haka aka kewaye birnin da yaƙi har shekara goma sha ɗaya na mulkin Zedekiya. 3 A rana ta tara na watan huɗu na shekarar, yunwa ta yi tsanani a birnin har babu abinci domin mutanen ƙasar. 4 Sa'an nan aka shigo birnin, sai dukkan masu yaƙin suka gudu ta ƙofar dake tsakanin katangu biyu, ta lambun sarki, ko da shike Kaldiyawa suna kewaye da birnin. Sarki ya yi ta wajen Araba. 5 Amma sojojin Kaldiyawa suka yi fakon sarki Zedekiya har suka mamaye shi a filayen kwarin Kogin Yodan kusa da Yeriko. Dukkan sojinsa kuwa suka warwatsu daga gare shi. 6 Suka kamo sarkin suka kai shi gun sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci. 7 Game da 'ya'yan Zedekiya maza kuwa, an yayyanka su a gabansa. Sa'annan ya ƙwaƙule masa idanunsa, ya ɗaure shi da sarƙa ta tagulla, ya kai shi Babila. 8 Yanzu kuwa a wata na biyar, a rana ta bakwai ga watan, wanda ke a shekara ta goma sha tara ta mulkin Nebukadnezza sarkin Babila, Nebuzaradan, baran sarkin Babila da kuma shugaban masu gadin sarki, ya zo Yerusalem. 9 Ya ƙona gidan Yahweh da fãdar sarki da dukkan gidajen Yerusalem; ya kuma ƙone dukkan manyan gine-ginen birnin. 10 Game da garun kewaye da Yerusalem kuwa, dukkan sojojin Babilan da ke ƙarƙashin shugaban sun rurrushe su. 11 Game da sauran mutanen da aka bari a birnin da waɗanda suka tafi wurin sarkin Babila, da sauran ragowar mutanen - Nebuzaradan, shugaban masu gadin sarki, ya ɗauke su zuwa zaman talala. 12 Amma shugaban masu gadin sarki ya bar waɗansu matalautan ƙasar su ci gaba da aikin lambuna da filaye. 13 Game da ginshiƙan tagulla da ke gidan Yahweh, da dakalansu da takwanniyar ruwa da ke cikin gidan Yahweh, Kaldiyawa sun ragargaza su su ka kuma ɗauke tagullan su ka kai su Babila. 14 Kaldiyawan kuma su ka kwashe tukwane da manyan cokula da hantsuka da cokula da dukkan tasoshin tagulla waɗanda firistoci ke aiki da su a haikali - Kaldiyawa sun tafi da su dukka. 15 Tukwanen da ake amfani da su domin cire tokar bagaden darurruka da aka yi da zinariya da azurfa - shugaban masu gadin sarkin ya kwashe su dukka ya tafi da su. 16 Ginshiƙan biyu kuwa da takwanniyar ruwa da dakalan da Suleman ya yi domin gidan Yahweh suna ƙunshe da tagulla da yawa da ba a iya aunawa. 17 Tsawon ginshiƙi na farkon kamu goma sha takwas ne. dajiyar tagulla akan ginshiƙin kamu uku ne, wadda aka kewaye da raga da rumman, kuma dukka da tagulla aka yi su. Ɗaya ginshiƙin da ragarsa na dai-dai da ta farkon. 18 Shugaban masu gadin sarkin ya ɗauki Serayiya babban firist da Zefaniya da firist na biyun da mutun uku masu tsaron ƙofa. 19 Daga birnin kuwa ya ɗauki waɗansu manyan sojoji da mashawartan sarki guda biyar waɗanda ba a tafi da su ba duk ya kamo ya tsare su don kada su gudu. Ya kuma kamo babban sojan da ke shugabancin ɗaukan sojoji aiki, tare da mutum sitin kuma da ke cikin birnin. 20 Sa'an nan Nebuzaradan, shugaban masu gadin sarki, ya ɗauko su ya kai wa sarkin Babilan a Ribla. 21 Sarkin Babila ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Ta haka Yahuda ya bar ƙasarsa zuwa zaman bauta. 22 Game da mutanen da suka rage a ƙasar Yahuda, waɗanda Nebukadnezza sarkin Babilan ya bari, ya sa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, shugabancin su, 23 Yanzu kuwa da dukkan shugabanin sojojin, su da mazajensu, suka ji sarkin Babila ya maida Gedaliya gwamna, sai suka je wurin Gedaliya a Mizpa. Waɗannan mazajen su ne Isma'il ɗan Netaniya da Yohanan ɗan Kariya da Serayiya ɗan Tanhumet Banetofate da Ya'azaniya ɗan Ma'akatite - su da mazajensu. 24 Gedaliya ya yi amana da su da mazajensu, ya ce da su, "Kada ku ji tsoron shugabanin Kaldiyawa. Ku zauna a ƙasar ku yi wa sarkin Babilan hidima, kuma kome zai yi maku kyau." 25 Amma ya zamana dai a watan bakwai Isma'il ɗan Netaniya ɗan Elishama, daga iyali mai martaba, ya zo ya da mutum goma ya kai wa Gedaliya hari. Gedaliya ya mutu, tare da mutum goma na Yahuda da Babilonawan da ke tare da shi a Mizfa. 26 Sa'an nan dukkan mutanen, daga mafi ƙanƙanta zuwa masu muhiminci, da dukkan shugabani sojojin, suka tashi suka tafi Masar, saboda suna tsoron Babilonawan. 27 Ya zamana daga baya a shekara ta talatin da bakwai na zaman talalar Yahoiacin sarkin Yahuda, a wata na goma sha biyu, sai Awel Marduk sarkin Babilan ya saki Yahoiacin sarkin Yahuda daga kurkuku. Wannan ya faru ne a shekarar da Awel- Marduk ya fara mulki. 28 Ya yi maganar kirki da shi ya kuma ba shi wurin zaman da ya fi na waɗansu sarakunan da ke tare da shi a Babila. 29 Awel-Marduk ya cire wa Yahoiacin tufafin kurkuku, har Yahoiacin ya ci gaba da liyafa a teburin sarki dukkan rayuwarsa. 30 Ana kuwa biyansa albashin abinci dukkan kwanakin rayuwarsa.

Littafin Tarihi Na Ɗaya
Littafin Tarihi Na Ɗaya
Sura 1

1 Adamu, Set, Enosh, 2 Kenan, Mahalalel, Yared, 3 Enok, Metusela, Lamek. 4 'Ya'yan Nuhu su ne Shem, Ham da Yafet. 5 'Ya 'yan Yafet su ne Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek, Tiras. 6 'Ya'yan Gomer su ne Ashkenaz, Rifat da Togarma. 7 'Ya 'yan Yaban su ne Elisha, Tarshish, Kitiyawa, da Rodanawa. 8 'Ya'yan Ham su ne Kush, Masar, Fut da Kan'ana. 9 'Ya'yan Kush su ne Seba, Habila, Sabta, Ra'ama da Sabteka. 10 'Ya'yan Ra'ama su ne Sheba da Dedan. Kush ya zama mahaifin Nimrod, wanda shi ne ya fara zama jarumi a duniya. 11 Masar ya zama mahaifin mutanen Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa, da 12 Fatrusawa, da Kasluhawa (daga wannan tushen Filistiyawa suka fito), da Kaftorawa. 13 Kan'ana ya zama mahaifin Sidon, ɗan farinsa, da kuma Hitiyawa. 14 Shi ne ya zama kakan Yebusawa, Amoriyawa, Girgashawa, 15 Hibiyawa Arkiyawa, Siniyawa da 16 Arbiyawa, Zemarawa, da Hamatawa. 17 'Ya'yan Shem su ne Elam, Ashur, Arfazad, Lud, Aram, Uz, Hul, Geter, da Meshek, 18 Arfazad shi ne ya zama mahaifin Shela, Shela kuma ya zama mahaifin Eber. 19 Eber na da 'ya'ya biyu. Sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa ne duniya ta rabu. Sunan ɗan'uwansa Yoktan. 20 Yoktan ya zama mahaifin Almodad, Shelef, Hazamavet, Yera, 21 Hadoram, Uzal, Dikla, 22 Obal, Abimayel, Sheba, 23 Ofir, Habila, da Yobab, duk waɗannan daga zuriyar Yoktan ne. 24 Shem, Arfazad, Shelah, 25 Eber, Feleg, Rewu, 26 Serug, Nahor, Tera, 27 Abram shi ne Ibrahim. 28 'Ya'yan Ibrahim su ne Ishaku da Isma'il. 29 Waɗannan su ne 'ya'yansu:‌ Ɗan farin Isma'il Nebayot ne, sa'an nan Kedar, Adbeel, Mibsam, 30 Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema, 31 Yetur, Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'il. 32 'Ya'yan Ketura, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan su ne Sheba da Dedan. 33 'Ya'yan, Midiyan su ne Efa, Efer, Hanok, Abida, da Elda'ah. Dukkan waɗannan zuriyar Ketura ne. 34 Ibrahim ya zama mahaifin Ishaku. 'Ya'yan Ishaku su ne Isuwa da Isra'ila. 35 'Ya'yan Isuwa su ne Elifaz, Ruwel, Yewush, Yalam, da Kora. 36 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, Omar, Zefo, Gatam, Kenaz, Timna da Amalek. 37 'Ya'yan Ruwel su ne Nahat, Zera, Shamma, da Mizza. 38 'Ya'yan Seyir su ne Lotan, Shobal, Zibiyon, Ana, Dishon, Ezer, da Dishan. 39 'Ya'yan Lotan su ne Hori da Homam, Timna 'yar'uwar Lotan ce. 40 'Ya'yan Shobal su ne Alban, Manahat, Ebal, Shefo, da Onam. 'Ya'yan Zibiyon su ne Aiya da Ana. 41 ‌Ɗan Ana shi ne Dishon. 'Ya'yan Dishon su ne Hemran, Eshban, Itran, da Keran. 42 'Ya'yan Ezer su ne Bilhan Za'aban, Ya'akan da Akan. 'Ya'yan Dishan su ne Uz da Aran. 43 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a ƙasar Idom kafin wani sarki ya yi mulki bisa Isra'ilawa. Bela ɗan Beyor, sunan birninsa Dinhaba ne. 44 Da Bela ya mutu, Yobab ɗan Zera na Bozra ya yi mulki a gurbinsa. 45 Da Yobab ya mutu, Husham na ƙasar Temanawa ya yi mulki a gurbinsa. 46 Da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan a ƙasar Mowab, ya yi sarauta a gurbinsa. Sunan birninsa Avit. 47 Da Hadad ya mutu, Samla na Masreka ya yi sarauta a gurbinsa. 48 Da Samla ya mutu, Shawul na Rehobot wadda a kan kogin ya yi sarauta a gurbinsa. 49 Da Shawul ya mutu, Ba'al-Hanan ɗan Akbor ya yi mulki a gurbinsa. 50 Ba'al-Hanan ɗan Akbor ya mutu, Hadar ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Fawu. Sunan matarsa Mehetabel ce ɗiyar Matred ɗiyar Me Zahab. 51 Hadad ya mutu, shugaban iyalin Idom su ne Timna, Alba, Yetet, 52 Ohalibama, Elah, Finon, 53 Kenaz Teman, Mibza, 54 Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne shugabannin a Idom.

Sura 2

1 Waɗanan su ne 'ya'yan Isra'ila maza: Ruben, Simiyon, Lebi, Yahuda, Issaka, Zebulun, 2 Dan, Yosef, Benyamin, Naftali, Gad da Asha. 3 'Ya'yan Yahuda su ne Er, Onan, da Shela, waɗanda ɗiyar Shuwa ta haifa masa Bakan'aniye. Er ɗan farin Yahuda, mugu ne a gaban Yahweh, sai Yahweh ya kashe shi. 4 Tama, surukarsa, ta haifa masa Ferez da Zara. Yahuda yana da 'ya'ya biyar maza. 5 'Ya'yan Ferez su ne Hezron da Hamul. 6 'Ya'yan Zera su ne Zimri, Etan, Heman, Kalkol, da Darda su biyar cur‌. 7 ‌Ɗ‌an Karmi shi ne Akar, wanda ya kawo matsala ga Isra'ila lokacin da ya saci abubuwan da aka keɓe domin Yahweh.‌ 8 Ɗan Etan shi ne Azariya. 9 'Ya'yan Hezron su ne Yeramil, Ram, Kaleb. 10 Ram ya zama mahaifin Aminadab, Aminadab ya zama mahaifin Nashon, shugaba ne cikin zuriyar Yahuda. 11 Nashon ya zama mahaifin Salmon, Salmon ya zama mahaifi Bo'aza. 12 Bo'aza ya zama mahaifin Obed, Obed ya zama mahaifin Yesse. 13 Yesse ya zama mahaifin ɗan farinsa Eliab, Abinadab na biyu, Shimeya na uku, 14 Netanel na huɗu, Raddai na biyar, 15 Ozem na shida, sai Dauda na bakwai. 16 'Yan'uwansu mata su ne Zeruyiya da Abigel. 'Ya'yan Zeruyiya su ne Abishai, Yoab da Asahel, su uku. 17 Abigel ta haifi Amasa, mahaifinsa Yeter ne Ba'isma'ile. 18 Kaleb ɗan Hezron ya haifi 'ya'ya daga matarsa Azuba, da kuma Yeriyot. 'Ya'yansa maza su ne Yesher, Shobab, da Ardon. 19 Azuba ta mutu, sai Kaleb ya auro Efrat, wacce ta haifa masa Hur. 20 Hur ya zama mahaifin Uri, Uri kuma ya zama mahaifin Bezalel. 21 Daga baya Hezron (da ya cika shekaru sittin) ya auri ɗiyar Makir, mahaifin Giliyad. Ita ta haifa masa Segub. 22 Segub ya zama mahaifin Yayir, wanda ya mallaki birane ashirin da uku a ƙasar Giliyad. 23 Geshur da Aram suka ci garin Yayir da Kenat, har da garuruwa sittin na kewaye. Duk waɗannan mazauna zuriyar Makir ne, mahaifin Giliyad. 24 Bayan mutuwar Hezron, Kaleb ya kwana da Efrata, matar Hezron mahaifinsa. Ta haifa masa Ashhur, mahaifin Tekowa. 25 'Ya'yan Yeramil, ɗan farin Hezron, su ne Ram ɗan fari, Buna, Oren, Ozem, da Ahija. 26 Yeramil ya na da wa ta mata, wadda ta ke da suna Atara. Ita ce uwar Onam. 27 'Ya'yan Ram, ɗan farin Yeramel, su ne Ma'az, Yamin, da Eker. 28 'Ya'yan Onam su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai su ne Nadab da Abishur. 29 Sunan matar Abishur Abihel ne, ta kuma haifa masa Ahban da Molid. 30 'Ya'yan Nadab su ne Seled da Affayim, amma Seled ya mutu ba shi da 'ya'ya, 31 'Ɗan Affayim kuwa Ishi ne.‌ Ɗan Ishi shi ne Sheshan.‌ Ɗan Sheshan shi ne Ahlai. 32 'Ya'yan Yada, ɗan'uwan Shammai, su ne Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu ba shi da 'ya'ya. 33 'Ya'yan Yonatan su ne Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yeramil. 34 Sheshan ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sheshan ya na da bawa, Bamasare, mai suna Yarha. 35 Sai Sheshan ya ba baransa Yarha ɗiyarsa ta zama matarsa. Ita ce ta haifa masa Attai. 36 Attai ya zama mahaifin Natan, Natan ya zama mahaifin Zabad. 37 Zabad ya zama mahaifin Eflal, kuma Eflal ya zama mahaifin Obed. 38 Obed ya zama mahaifin Yehu, kuma Yehu ya zama mahaifin Azariya. 39 Azariya ya zama mahaifin Helez, Helez ya zama mahaifin Eleyasa. 40 Eleyasa ya zama mahaifin Sismai, Sismai kuma ya zama mahaifin Shallum. 41 Shallum ya zama mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma ya zama mahaifin Elishama. 42 'Ya'yan Kaleb, ɗan'uwan Yeramil, su ne Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif.‌ Ɗansa na biyu, Maresha, shi ne mahaifin Hebron. 43 'Ya'yan Hebron su ne Kora, Taffuwa, Rekem, da Shema. 44 Shema ya zama mahaifin Raham, mahaifin Yorkiyam. Rekem ya zama mahaifin Shammai. 45 ‌Ɗan Shammai kuwa shi ne Mawon, Mawon shi ne mahaifin Bet Zur. 46 Efah, ƙwarƙwarar Kaleb, ta haifi Haran, Moza, da Gazez. Haran ya zama mahaifin Gazez. 47 'Ya'yan Yahdai su ne Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efah da Sha'af. 48 Ma'aka, ƙwarƙwarar Kaleb, ta haifi Sheber da Tirhanah. 49 Ita ce kuma mahaifiyar Sha'af mahaifin Madmanna, Sheva mahaifin Makbena da mahaifin Gibeya.‌ Ɗiyar Kaleb ita ce Aksah. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. 50 Wàɗannan su ne 'ya'yan Hur, ɗan farinsa daga Efrata: Shobal mahaifin Kiriyat Yerim, 51 Salma mahaifin Betlehem da kuma Haref mahaifin Bet Gader. 52 Shobal mahaifin Kiriyat Yerayim yana da zuriya: Harowe, rabin jama'ar Manahatawa, 53 da kuma iyalin Kiriyat Yerayim: na Itirawa da na Futiyawa, da na Shumatawa da Mishrayawa. Daga waɗannan ne Zoratawa da Eshtawolawa suka fito. 54 Waɗannan su ne dangogin Salma: Betlehem, Netofatawa, Atrot Bet Yowab, da rabin Manahatawa - Zoritawa, 55 dangogin marubuta waɗanda suka zauna a Yabez: Tiratawa, Shimiatawa, da Sukatawa. Waɗannan su ne Kenitawa zuriyar da suka fito daga Hammat, kakan Rekabawa.

Sura 3

1 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda da aka haifa masa a Hebron: ɗan fari shi ne Amnon, ta wurin Ahinowam daga Yezriyel; na biyun shi ne Daniyel, ta wurin Abigel daga Karmel; 2 na ukun shi ne Absalom, wanda uwarsa ita ce Ma'aka, ɗiyar Talmai sarkin Geshur. Na huɗun shi ne Adonijah ɗan Haggit; 3 na biyar shi ne Shefatiya ta wurin Abital; na shida shi ne Itreyam ta wurin Egla matarsa. 4 Waɗannan shida aka haifa wa Dauda a Hebron, inda ya yi sarauta shekaru bakwai da wata shida. Sa'an nan ya yi sarauta a Yerusalem shekaru talatin da uku. 5 Waɗannan 'ya'ya maza huɗu ta wurin Batsheba ɗiyar Ammiyel aka haifa masa su a Yerusalem: Shamuwa, Shobab, Natan, da Suleman. 6 Wasu 'ya'ya maza na Dauda su ne: Ibhar, Elishuwa, Elifelet, 7 Nogah, Nefeg, Yafiya, 8 Elishama, Eliyada da Elifelet. 9 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda maza, banda 'ya'yan da ƙwaraƙwarai suka haifa masa. Tamar 'yar'uwarsu ce. 10 ‌Ɗan Suleman shi ne Rehobowam. Ɗ‌an Rehobowam shi ne Abiya.‌ Ɗan Abiya shi ne Asa. Ɗan Asa shi ne Yehoshafat. 11 Ɗan Yehoshafat shi ne Yehoram.‌ Ɗan Yehoram shi ne Ahaziya.‌ Ɗan Ahaziya shi ne Yo'ash.‌ 12 Ɗan Yo'ash shi ne Amaziya, ‌Ɗan Amaziya shi ne Azariya. ‌Ɗan Azariya shi ne Yotam. 13 ‌Ɗan Yotam shi ne Ahaz.‌ Ɗan Ahaz shi ne Hezekiya. ‌Ɗan Hezekiya shi ne Manasse. ‌Ɗ‌an 14 Manasse shi ne Amon. ‌Ɗan Amon shi ne Yosiya. 15 Ga 'ya'yan Yosiya na farkon shi ne Yohanan, ɗansa na biyu Yaho'iakim, ɗansa na uku Zedekiya, ɗansa na huɗu Shallum. 16 'Ya'yan Yeho'akim su ne Yeho'iacin da Zedekiya. 17 'Ya'yan Yaho'iacin, ɗan bautar talala, su ne Sheltiyal, 18 Malkiram, Fedayiya, Shenazza, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya. 19 'Ya'yan Fedayiya su ne Zerubabel da Shimei. ‌'Ya'yan Zerubabel su ne Meshullam da Hananiya; Shelomit 'yar'uwarsu ce. 20 Wasu 'ya'yansa maza biyar kuwa su ne Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya, Yushab-Hesed. 21 'Ya'yan Hananiya su ne Felatiya da Yeshayiya. ‌‌Ɗansa shi ne Refayiya, waɗansu sauran zuriyoyin su ne Arnan, Obadiya, da Shekaniya 22 ‌Ɗan Shekaniya shi ne Shemayiya. 'Ya'yan Shemayiya su ne Hattush, Igal, Bariya, Niyariya, da Shafat. 23 'Ya'yan Niyariya guda uku su ne Eliyonai, Hizkiya, da Azrikam. 24 'Ya'yan Eliyonai su bakwai ne su ne Hodabiya, Eliyashib, Felayiya, Akkub, Yohanan, Delayiya da Anani.

Sura 4

1 'Zuriyar Yahuda su ne Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal. 2 Shobal shi ne mahaifin Reyayiya. Reyayiya shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne dangogin Zoratawa. 3 Waɗannan su ne kakannin dangogin da ke cikin birnin Itam: Yezriyel, Ishma, da Idbash. Sunan 'yar'uwarsu Hazzelelfoni. 4 Feniyel shi ne kakan dangoginn da ke cikn birnin Gedor. Ezer shi ne na asalin dangogin da ke cikin Hushah. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata kuma shi ne asalin Betlehem. 5 Ashur mahaifin Tekowa ya na da mata biyu, Helah da Na'arah. 6 Na'arah ta haifa masa Ahuzzam, Hefa, Temeni, Hahashtari. Waɗannan su ne 'ya'yan Na'arah. 7 'Ya'yan Helah su ne Zeret, Zohar, Itnan, 8 da Koz wanda ya zama mahaifin Anub da Hazzobeba, da dangogin zuriyar da suka fito daga Ahahel ɗan Harum. 9 Yabez ya sami girmamawa fiye da 'yan'wansa. Mahaifiyarsa ta kira shi Yabez. Ta ce, "Domin na haife shi cikin azaba." 10 Yabez ya kira bisa sunan Yahweh na Isra'ila ya ce, "Idan da za ka albarkace ni da gaske, ka faɗaɗa mani iyakata, hannunka ya kasance tare da ni. Idan ka yi haka ka kare ni daga cuta, domin in 'yantu daga azaba!" Sai Yahweh ya amsa addu'arsa. 11 Kaleb ɗan'uwan Shuhah shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton. 12 Eshton shi ne mahaifin Bet Rafa, Faseya, da Tehinna, wanda shi ne mahaifin Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen da suka zauna a Reka. 13 'Ya'yan Kenaz su ne Otniyel da Serayiya. 'Ya'yan Otniyel su ne Hatat da Meyonotai. 14 Meyonotai ya zama mahaifin Ofra, Serayiya ya zama mahaifin Yowab wanda ya kafa Ge-Harashim, mutanen masassaƙa ne. 15 'Ya'yan Kaleb 'ɗan Yefune su ne Iru, Elah da Na'am.‌ Ɗ‌an Elah shi ne Kenaz. 16 'Ya'yan Yehallelel su ne Zif, Zifa, Tiriya da Asarel. 17 'Ya'yan Ezrah su ne Yeter, Mered, Efer, da Yalon. Matar Mered Bamasariye ta haifi Miriyam, Shammai, da Ishba, wanda shi ne mahaifin Estemowa. 18 Waɗannan su ne 'ya'yan Bitiya, ɗiyar Fir'auna, wadda Mered ya aura. Matar Mered Bayahude ta haifi Yarid, wanda shi ne mahaifin Gedor; Haba, wanda ya zama mahaifin Soko; da Yekutiyel, wanda shi ne ya zama mahaifin Zanowa. 19 Matar Hodiya 'yar'uwar Naham, tana da 'ya'ya maza biyu, ɗaya daga cikinsu ya zama mahaifin Keila Bagarme.‌ Ɗayan kuwa shi ne Eshtamowa Bamaakate. 20 'Ya'yan Shimon su ne Amon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. 'Ya'yan Ishi su ne Zohet da Ben-Zohet. 21 Zuriyar Shela ɗan Yahuda su ne Er mahaifin Leka, La'ada mahaifin Maresha da dangogin da ke sana'ar linin a Bet Ashbiya, 22 Yokim, mutanen Kozeba, da Yo'ash da Saraf, da ya yi mulki a Mowab da Yashubi Lehem. (Wannan labari daga daɗaɗen rubutu ne.) 23 Waɗannan su ne maginan tukwane da suka zauna a Netayim da Gedera, suka yi wa sarki aiki. 24 Zuriyar Simiyon su ne Nemuyel, Yamin, Yarib, Zera da Shawul. 25 Shallum ɗan Shawul ne, Mibsam ɗan Shallum ne, kuma Mishma ɗan Mibsam ne. 26 Zuriyar Mishma su ne ɗansa Hamuyel, Zakur jikansa da Shimei tattaɓa kunnensa. 27 Shimei yana da 'ya'ya goma sha shida da 'ya'ya mata shida. Ɗan'uwansa bai haifi 'ya'ya da yawa ba, saboda haka dangoginsu ba su yi yawa kamar mutanen Yahuda ba. 28 Su ka zauna a Biyasheba, Molada, da kuma Hazar Shuwal. 29 Sun kuma zauna a Bilha, Ezem, Tolad, 30 Betuwel, Horma, Ziklag, 31 Bet Markabot, Hazar Susim, Bet Biri, da Sha'arayim. Waɗannan su ne biranensu har ya zuwa mulkin Dauda. 32 ‌Ƙauyukansu biyar su ne Itam, Ain, Rimmon, Token, da Ashan, 33 da dukkan ƙauyukan da ke kewaye har zuwa Baalat. Waɗannan su ne mazauninsu, kuma suka adana tarihin zuriyarsu a rubuce. 34 Shugabannin dangi su ne Meshobab, Yamlek, Yosha ɗan Amaziya, 35 Yowel, Yehu ɗan Yoshibiya ɗan Serayiya ɗan Asiyel, 36 Eliyonai, Ya'akoba, Yeshohaiya, Asayiya, Adiyel, Yesimiyel, Binayiya 37 da Ziza ɗan Shifi ɗan Allon ɖan Yedayiya ɗan Shimri ɗan Shemayiya. 38 Waɗannan da aka ambata da sunaye shugabanni ne cikin dangoginsu, dangoginsu kuma su ka ƙaru ainun. 39 Su ka tafi kusa da Gebor, yamma da kwari, domin su nemi makiyaya saboda garkunansu. 40 Suka kuwa sami makiyaya mai dausayi. ‌Ƙasar mai girma ce, ba fitina ga kuma salama. Dã Hamawa suka zauna a wurin. 41 Waɗannan da aka lisafta da sunaye sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda, suka hari mazaunin Hamawa da na Mewunawa, waɗanda su ke a wurin. Suka hallakar da su gaba ɗaya suka gãje wurin sabili da sun sami makiyaya mai dausayi domin garkunansu. 42 Mutane ɗari biyar daga kabilar Simiyon su ka tafi Tsaunin Seyir, tare da shugabaninsu Felatiya, Niyeriya, Refayiya, da Uzziyel 'ya'yan Ishi. 43 Suka ci sauran Amelikawa 'yan gudun hijira, suka zauna a can har zuwa yau.

Sura 5

1 'Ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila - Ruben shi ne ɗan farin Isra'ila, amma aka ba da girman ɗan farinsa ga 'ya'yan Yosef ɗan Isra'ila domin Ruben ya ƙazantar da gadon mahaifinsa. Saboda haka ba a lisafta shi a matsayin ɗan fãri ba. 2 Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin 'ya'uwansa, shugaba kuma zai fito da ga cikinsa. Amma albarkar ɗan fari na Yosef ne - 3 'ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila su ne Hanok, Fallu, Hezron da Karmi. 4 Waɗannan su ne zuriyar Yowel: ‌Ɗan Yowel shi ne Shemayiya. ‌Ɗan Shemayiya shi ne Gog. ‌Ɗan Gog shi ne Shimei. 5 ‌Ɗan Shimei shi ne Mika. ‌Ɗan Mika shi ne Reyayiya. ‌Ɗan Reyayiya shi ne Ba'al. 6 ‌Ɗan Ba'al shi ne Bira, wanda Tilgat Filesa sarkin Asiriya ya kai su bautar talala. Bira shugaba ne cikin kabilar Ruben. 7 Waɗannan su ne 'yan'uwan Bira cikin dangoginsu ga yadda aka lisaftasu cikin rubutun tarihin asali: Yeyel shi ne babba, Zekariya, da 8 Bela ɗan Azaz ɗan Shema ɗan Yowel. Suka zauna a Arowa, har can nesa da Nebo da Ba'al Meyon, 9 daga gabas kuma har zuwa goshin jejin da ya miƙe zuwa Kogin Yuferatis. Wannan ya zama haka domin suna da garken dabbobi da yawa a ƙasar Giliyad. 10 A zamanin Saul, kabilar Ruben ta faɗa wa Hagarawa ta ci su. Suka zauna a rumfunan Hagarawa a dukkan ƙasar da ke gabashin Giliyad. 11 'Yan kabilar Gad suka zauna kusa da su, a cikin ƙasar Bashan har zuwa Saleka. 12 Shugabanninsu su ne Yowel, wanda shugaba ne, da Shafan shi ma wani shugaba ne, da Yanai da Shafat a Bashan. 13 'Yan'uwansu ta wurin iyalan mahaifisu su ne Mika'el, Meshulam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya, da Eber - su bakwai cur. 14 Waɗannan mutane da aka ambata a baya su ne zuriyar Abihal, Abihal ɗan Huri ne, Huri ɗan Yarowa ne. Yarowa ɗan Giliyad ne. Giliyad ɗan Mika'el ne. Mika'el ɗan Yeshishai ne. Yeshishai ɗan Yahdo ne. Yahdo ɗan Buz ne. 15 Ahi ɗan Abdiyel ɗan Guni, shugaba ne a iyalin mahaifinsa. 16 Sun zauna a Giliyad, da Bashan da cikin garuruwanta da kuma cikin dukkan makiyayan ƙasar Sharon har zuwa goshin iyakarta. 17 An rubuta waɗannan dukka bisa ga tarihin asali a kwanakin Yotam sarkin Yahuda da kuma Yerobowam sarkin Isra'ila. 18 Rubenawa da Gadawa, da rabin kabilar Manasse su na da jarumawa dubu arba'in da hudu gwanayen mayaƙa, ɗauke da garkuwa da takobi da masu harbi da baka. 19 Suka kai hari ga Hagarawa, Yetur, Nafish, da Nodab. 20 Suka sami taimakon yin yaƙi da abokan gabarsu daga Mai iko dukka. Da haka ne, su ka ci Hagarawa da dukkan waɗanda ke tare da su. Wannan ya faru domin Isra'ilawa sun yi kuka ga Allah cikin yaƙin, ya kuma sauraresu domin sun dogara gareshi. 21 Suka washe dabbobinsu, tare da raƙuma dubu hamsin, tumaki 250,000, jakai dubu biyu, da mazaje 100,000. 22 Sabili da Allah ya yi yaƙi domin su, suka kashe maƙiyansu da yawa. Suka zauna a ƙasarsu har lokacin zuwa bautar talala. 23 Rabin kabilar Manasse suka zauna a ƙasar Bashan har zuwa Ba'al Harmon da Senir (wato Tsaunin Harmon). 24 Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanninsu: Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodabiya, da Yadiyel. Waɗannan ƙarfafa ne kuma jarumawan mutane ne, shahararrun mutane, shugabannin gidajen ubanninsu. 25 Amma suka yi rashin aminci ga Allahn kakanninsu. A maimako, sai suka yi sujada ga allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallakar a gabansu. 26 Allah na Isra'ila ya zuga Ful sarkin Asiriya (ana kiransa Tilgat Filesa sarkin Asiriya). Ya kwashe waɗannan zuwa bautar talala Rubenawa, da Gadawa da rabin kabilar Manasse. Ya kawo su Halah, Habor, Hara, har kuma ya zuwa kogin Gozan, in da suke zaune har wa yau.

Sura 6

1 'Ya'yan Lebi su ne Geshon, Kohat, da Merari. 2 'Ya'yan Kohat su ne Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. 3 'Ya'yan Amram su ne Haruna, Musa da Miriyam. 'Ya'yan Haruna su ne Nadab, Abihu, Eliyeza da Itama. 4 Eliyeza ya zama mahaifin Finehas sai kuma Finehas ya zama mahaifin Abishuwa. 5 Abishuwa ya zama mahaifin Bukki. Sai Bukki ya zama mahaifni Uzzi. 6 Uzzi ya zama mahaifin Zerahiya, Zerahiya yazama mahaifni Merayot. 7 Merayot ya zama mahaifni Amariya, Amariya ya zama mahaifni Ahitub. 8 Ahitub ya zama mahaifin Zadok, Zadok ya zama mahaifin Ahima'az. 9 Ahima'az ya zama mahaifin Azariya, Azariya ya zama mahaifin Yohanan. 10 Yohanan ya zama mahaifin Azariya wanda ya yi hidima a haikalin da Suleman ya gina a Yerusalem. 11 Azariya ya zama mahaifin Amariya kuma Amariya ya zama mahaifin Ahitub. 12 Ahitub ya zama mahaifin Zadok, Zadok ya zama mahaifin Shallum. 13 Shallum ya zama mahaifin Hilkiya, Hilkiya ya zama mahaifin Azariya. 14 Azariya ya zama mahaifin Serayiya, sai kuma Serayiya ya zama mahaifin Yozadak. 15 Aka kama Yozadak aka tafi da shi a tsare lokacin da Yahweh ya aika Yahuda da Yerusalem bautar talala ta hannun Nebukadnezza. 16 'Ya'yan Lebi su ne Gashom, Kohat, da Merari. 17 'Ya'yan Gashom su ne Libni, da Shimei. 18 'Ya'yan Kohat su ne Amram, Izar, Hebron da Uzziyel. 19 'Ya'yan Merari su ne Mali da Mushi. Waɗannan ne suka zama kabilar Lebiyawa bisa ga gidajen ubanninsu. 20 Zuriyar Gershon ya soma da ɗansa Libni ɗan LIbni kuwa Yahat ne.‌ Ɗansa kuwa Zimma ne.‌ 21 Ɗansa Yohat ne.‌ Ɗansa Iddo ne.‌ Ɗansa Zera ne.‌ Ɗansa Yeyaterai ne. 22 Zuriyar Kohat: ‌Ɗansa shi ne Aminadab.‌ Ɗansa kuwa shi ne Kora.‌ Ɗansa shi ne Assir.‌ 23 Ɗansa shi ne Elkana. Ɗansa shi ne Abiyasaf. ‌Ɗansa shi ne Assir. 24 Ɗansa shi ne Tahat. Ɗansa shi ne Uriyel. Ɗansa shi ne Uzziya. ‌Ɗansa shi ne Shawul. 25 'Ya'yan Elkana su ne Amasai, Ahimot, da wani ɗa kuma da aka kira Elkana.; 26 Ɗansa shi ne Zofai.‌ Ɗansa shi ne Nahat.‌ 27 Ɗansa shi ne Eliyab.‌ Ɗansa shi ne Yeroham.‌ Ɗansa shi ne Elkana. 28 'Ya'yan Sama'ila su ne ɗan farinsa Yowel, da Abiya na biyu. 29 ‌Ɗan Merari shi ne Mahli.‌ Ɗansa shi ne Libni. ‌Ɗansa shi ne Shimei.‌ Ɗ‌ansa shi ne Uzza.‌ 30 Ɗansa shi neShimeya.‌ Ɗansa shi ne Haggiya.‌ Ɗansa shi ne Asayiya. 31 Waɗannan su ne sunayen mutanen da Dauda ya sa su bisa hidimar waƙa a haikalin Yahweh, bayan da akwatin alƙawari ya sami hutawa a wurin. 32 Suka yi hidima ta wurin waƙoƙi a gaban rumfar sujada, rumfar taruwa, har sai da Suleman ya gina haikalin Yahweh a Yerusalem. Suka aiwatar da hidimarsu bisa ga umarnin da aka ba su. 33 Waɗannan su ne suka yi hidima da 'ya'yansu. Daga dangogin Kohatawa aka sami Heman mawaƙi. Ga kakanninsa idan an koma lokacin baya: Heman ɗan Yowel ne. Yowel ɗan Sama'ila ne. 34 Sama'ila ɗan Elkana ne. Elkana ɗan Yeroham ne. Yeroham ɗan Eliyel ne. Eliyel ɗan Towa ne. 35 Towa ɗan Zuf ne. Zuf ɗan Elkana ne. Elkana ɗan Mahat ne. Mahat ɗan Amasai ne. Amasai ɗan Elkana ne. 36 Elkana ɗan Yowel ne. Yowel ɗan Azariya ne. Azariya ɗan Zefaniya ne. 37 Zefaniya ɗan Tahat ne. Tahat ɗan Assir ne. Assir ɗan Ebiyasaf ne. Ebiyasaf ɗan Kora ne. 38 Kora ɗan Izar ne. Izar Kohat ne. Kohat ɗan Lebi ne. Lebi ɗan Isra'ila ne. 39 Abokin Heman Asaf ne, shi ya tsaya a hannun damarsa. Asaf ɗan Berekiya ne. Berekiya ɗan Shimeya ne. 40 Shimeya ɗan Mika'el ne. Mika'el ɗan Ba'asiya ne. Ba'asiya ɗan Malkiya ne. 41 Malkiya ɗan Etni ne. Etni ɗan Zera ne. Zera ɗan Adaya ne. 42 Adaya ɗan Itam ne. Itam ɗan Zimma ne. Zimma ɗan Shimei ne. 43 Shimei ɗan Yahat ne. Yahat ɗan Geshon ne. Geshon ɗan Lebi ne. 44 A hannun hagun Herman akwai abokansa su ne "ya'ya Merari. Su ne waɗannan Etan ɗan Kishi. Kishi ɗan Abdi ne. Abdi ɗan Malluk ne. 45 Malluk ɗan Hashabiya ne. Hashabiya ɗan Amaziya ne. Amaziya ɗan Hilkiya ne. 46 Hilkiya ɗan Amzi ne. Amzi ɗan Bani ne. Bani ɗan Shemer ne. 47 Shemer ɗan Mahli ne. Mahli ɗan Mushi ne. Mushi ɗan Merari ne. Merari ɗan Lebi ne. 48 Aka ba abokan aikinsu Lebiyawa dukkan hidimar rumfar sujada, gidan Yahweh. 49 Haruna da 'ya'yansa suka yi hidimar miƙa baye-baye bisa bagadi domin baye-bayen ƙonawa; da kuma baiko bisa bagadin turare domin dukkan aiki a wuri mafi tsarki. Waɗannan baye-baye suka yi kaffara domin Isra'ila, bisa ga dukkan abin da bawan Allah Musa ya umurta. 50 Zuriyar Haruna kenan bi da bi: Ɗan Haruna shi ne Eliyeza.‌ Ɗan Eliyeza shi ne Fenihas.‌ Ɗan Fenihas shi ne Abishuwa.‌ 51 Ɗan Abishuwa shi ne Bukki.‌ Ɗan Bukki shi ne Uzzi.‌ Ɗan Uzzi shi ne Zerahiya.‌ 52 Ɗan Zerahiya shi ne Merayot‌. Ɗan Merayot shi ne Amariya.‌ Ɗan Amaraiya shi ne Ahitub.‌ 53 Ɗan Ahitub shi ne Zadok.‌ Ɗan Zadok shi ne Ahima'az. 54 Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna su zauna, wato, zuriyar Haruna waɗanda ke daga dangin Kohatawa (rabo na fari nasu ne). 55 Aka ba su Hebron a ƙasar Yahuda da kuma makiyayarta, 56 amma jejin birnin da ƙauyukansa aka ba Kaleb ɗan Yefunne. 57 Aka ba zuriyar Haruna: Hebron (birnin mafaƙa), da Libna da makiyayarta, Yattir, Estomawa da makiyayarta, 58 Hilen da makiyayarta, da Debir da makiyayarta. 59 Aka ba zuriyar Haruna: Ashan da makiyayarta, Yutta da Bet Shemesh da makiyayarta; 60 daga kabilar Benyamin aka ba su Geba da makiyayarta, Alemet da makiyayarta, da Anatot da makiyayarta. Dukkan biranen iyalen Kohat guda goma sha uku ne. 61 Ga sauran zuriyar Kohat ta wurin kuri'a aka ba su birane goma daga rabin kabilar Manasse. 62 Ga zuriyar Gershon a cikin dangoginsu da bam da bam aka ba su birane goma sha uku daga cikin kabilar Issaka, Asha, Naftali, da rabin kabilar Manasse a Bashan. 63 Aka ba zuriyar Merari birane goma sha biyu dangi bayan dangi, daga kabilar Ruben, Gad da Zebulun. 64 Sai mutanen Isra'ila suka bada waɗannan birane da makiyayarsu ga Lebiyawa. 65 Aka ba su ta wurin ƙuri'a garuruwan da aka zana a baya daga kabilun Yahuda, Simiyon da Benyamin. 66 Ga wasu dangogin Kohatawa aka bada birane daga gundumar Ifraim. 67 Aka basu: Shekem (birnin mafaƙa) da makiyayarta a ƙasar duwatsu ta Ifraim, Gezer da makiyayarta, 68 Yokmiyam da makiyayarta, Bet Horon da makiyayarta, 69 Aijalon da makiyayarta, da Gat Rimmon da makiyayarta. 70 Rabin kabilar Manasse suka ba Kohatawa: Aner da makiyayarta da Bileyam da makiyayarta. Waɗannan suka zama mallaƙar sauran dangogin Kohatawa. 71 Zuriyar Geshon daga dangogin rabin kabilar Manasse, aka ba Golan a Bashan da makiyayarta da Ashtarot da makiyayarta. 72 Kabilar Issaka ta ba zuriyar Geshon: Kedesh da makiyayarta, Daberat da makiyayarta, 73 Ramot da makiyayarta, da Anem da makiyayarta. 74 Daga kabilar Asha Issaka ta karɓi: Mashal da makiyayarta, Abdon da makiyayarta, 75 Hukok da makiyayarta, da Rehob da makiyayarta. 76 Suka karɓa daga kabilar Naftali: Kedesh a Galili da makiyayarta, Hammon da makiyayarta, Kiriyatayim da makiyayarta. 77 Ga sauran zuriyar Merari aka ba su daga kabilar Zebulun: Yokheyam, Kartah, Rimmono da makiyayarta da Tabor da makiyayarta; 78 daga na kabilar Ruben a hayin Yodan a Yeriko, a gabashin kogin: Beza a cikin jeji da makiyayarta, Yahza da makiyayarta, 79 Kedemot da makiyayarta, da Mefa'at da makiyayarta. 80 Daga kabilar Gad, Lebiyawa suka karɓi: Ramot a Giliyad da makiyayarta, Mahanayim da makiyayarta, 81 Heshbon da makiyayarta, da Yazer da makiyayarta.

Sura 7

1 'Ya'yan Issaka huɗu su ne: Tola, Fuwa, Yashub, da Shimron. 2 'Ya'yan Tola su ne; Uzzi, Refayiya, Yeriyel, Yahmai, Ibsam, da Sama'ila. Su ne shugabannin gidajen ubanninsu, daga zuriyar Tola an lissafa su cikin jarumawa a zamanin su. Sun kai mutum 22,600 a cikin zamanin Dauda. 3 Dan Uzzi shi ne Izrahiya. 'Ya'yansa su ne Mika'el, Obadiya, Yowel da Ishiya, dukkansu biyar ɗin shugabannin zuriya ne. 4 Tare da su kuma suna da taron rundunar yaƙi zambar talatin da shida, bisa ga tsarin dake na dangogin kakanninsu, gama suna da mata yawa da 'ya'ya. 5 'Yan'uwansu, mayaƙan mutane daga dukkan kabilar Issaka, suna da jarumawa dubu tamanin da bakwai, bisa ga lissafin tarihin asalinsu. 6 'Ya'yan Benyamin uku su ne Bela, Beker, da Yediyayel. 7 'Ya'yan Bela guda biyar su ne Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot, da Iri. Su sojoji ne kuma shugabannin gidajen ubanninsu. Mutanen su sun kai 22,034 mayaƙan mutane, bisa ga jerin lissafin dangogin kakanninsu. 8 'Ya'yan Beka su ne Zemirah, Yo'ash, Eliyeza, Eliyonai, Omri, Yeremot, Abijah, Anatot, da Alemet. Dukkan waɗannan 'ya'yansa ne. 9 Lissafin dangoginsu yakai 20,200 shugabannin gida idajen ubanninsu kuma jarumawa. 10 Ɗan Yediyel shi ne Bilhan. 'Ya'yan Bilhan su ne Yewush, Benyamin, Ehud, Kena'ana, Zetan, Tarshish, da Ahishaha. 11 Dukkan waɗannan 'ya'yan Yediyayel. Jerinsu cikin zuriyarsu sun kai 17,200 shugabannin gidajen ubanninsu kuma mayaƙa maza da su ka cancanci hidimar soja. 12 (Shuffitawa da Huffitawa 'ya'yan Ir, da Hushitawa ɗan Aher ne.) 13 'Ya'yan Naftali su ne Yahziyel, Guni, Yezer, da Shillem. Waɗannan su ne jikokin Bilha. 14 Manasse ya na da ɗa mai suna Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiye ta haifa. Ta kuma haifi Makir, mahaifin Giliyad. 15 Makir ya ɗauko mace daga wurin Huffitawa da Shuffitawa. Sunan 'yar'uwarta shi ne Ma'aka. Wata zuriyar Manasse kuma shi ne Zelofihad, wanda 'ya'yansa mata ne kaɗai. 16 Ma'aka matar Makir, ta haifa masa ɗa ta kira shi Feresh. Sunan ɗan'uwansa kuma shi ne Sheresh, 'ya'yansa kuma Ulam da Rakem. 17 '‌Ɗ‌an Ulam kuma shi ne Bedan. Waɗannan su ne zuriyar Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse. 18 'Yar'uwar Giliyad Hammoleket ta haifi Ishhod, Abiyeya, da Mahla. 19 'Ya'yan Shemida su ne Ahiyan, Shekem, Likhi, da Aniyam. 20 Zuriyar Ifraim su ne kamar haka: ɗan Ifraim shi ne Shutela. ‌Ɗ‌an Shutela shi ne Bered. Ɗan Bered shi ne Tahat. Ɗan Tahat shi ne Eleyada. Ɗan Eliyada shi ne Tahat. 21 Ɗan Tahad shi ne Zabad. Dan Zabad shi ne Shutela. (Ezer da Eleyad mutanen Gat ne suka kashe su, mutanen da aka haifa cikin ƙasar, lokacin da suka je su sace masu shanunsu. 22 Ifraim mahaifinsu ya yi makoki dominsu kwanaki da yawa, 'ya'uwansa kuma suka zo don su ta'azantar da shi. 23 Ya kwana da matarsa. Sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ifraim ya kira shi Beriya, saboda masifa ta zo wa iyalinsa.) 24 ‌Ɗ‌iyarsa ita ce Sheerah, wadda ta gina Runtse da Sama Bet Horon da Uzzen Sheerah. 25 ‌Ɗansa shi ne Refha. ‌Ɗan Refha shi ne Reshef. ‌Ɗ‌an Reshef shi ne Tela.‌ Ɗ‌an Tela shi ne Tahan. ‌Ɗan Tahan shi ne Ladan. 26 ‌Ɗ‌an Ladan shi ne Ammihud. ‌Ɗan Ammihud shi ne Elishama. 27 ‌Ɗ‌an Elishama shi ne Nun. ‌Ɗan Nun shi ne Yoshuwa. 28 Mallakarsu da mazaunansu Betel ne da ƙauyukansu na kewaye. Suka miƙa ta gabashi zuwa Na'aran da yammaci zuwa Gezar da ƙauyukansu, zuwa Shekem da ƙauyukansu zuwa Ayyah da ƙauyukansu. 29 Akan iyaka da Manasse su ne Bet Shan da ƙauyukansu, Ta'anak da ƙauyukansu Megiddo da ƙauyukansu, da Dor da ƙauyukansu. A cikin waɗannan garuruwa zuriyar Yosef ɗan Isra'ila suke zaune. 30 'Ya'yan Asha su ne Imna, Ishba, Ishbi, da Beriya. Serah 'yar'uwar su ce. 31 'Ya'yan Beriya su ne Heber da Malkiyel, shi ne mahaifin Birza'it. 32 'Ya'yan Heber su ne Yaflet, Shomer da Hotman. Shuwa 'yar'uwarsu ce. 33 'Ya'yan Yaflet su ne Fasak, Bimhal, da Ashbat. Waɗannan su ne 'ya'yan Yaflet. 34 Shomer, ɗan'uwan Yaflet, yana da 'ya'ya kamar haka: Roga, Hubba, da Aram. 35 ‌Ɗ‌an'uwan Shemer, wato Helem, yana da 'ya'ya kamar haka: Zofa, Imna, Shelesh, da Amal. 36 'Ya'yan Zofa su ne Suwa, Harnefa, Shuwal, Beri, Imrah, 37 Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran, da Beera. 38 'Ya'yan Yeter su ne Yefunne, Fisfa, da Ara. 39 'Ya'yan Ulla su ne Ara, Hanniyel, da Riziya. 40 Duk waɗannan zuriyar Ashar ne. Su ne kakannin dangogi, shugabannin gidajen ubanninsu, fitattun mutane, mayaƙan mutane, sarakuna a cikin shugabanni. Sun kai su dubu ashirin da shida mazaje da suka cancanta domin yin hidimar aikin soja, bisa ga jerin lissafinsu.

Sura 8

1 'Ya'yan Benyamin biyar su ne Bela ɗan farinsa, Ashbel, Aharan, 2 Nohah, da Rafa. 3 'Ya'yan Bela su ne Adda, Gera, Abihud, 4 Abishuwa, Na'aman, Ahowa, 5 Gera, Shefufan, da Huram. 6 Waɗannan su ne zuriyar Ehud shugabannin gidajen ubanninsu domin mazaunan Geba, waɗanda aka tilasta masu su tafi Manahat: 7 Na'aman, Ahiyah, da Gera. Na ƙarshen, Gera, ya jagorance su cikin tafiyarsu. Shi ne mahaifin Uzza da Ahihud. 8 Shaharayim ya zama mahaifni 'ya'ya cikin ƙasar Mowab, bayan ya saki matansa Hushim da Ba'ara. 9 Ta wurin matarsa Hodesh, Shaharayim ya zama mahaifin Yobab, Zibiya, Mesha, Malkam, 10 Yewuz, Shakiya, da Mirma. Waɗannan su ne 'ya'yansa, shugabanni cikin gidajen ubanninsu. 11 Ya rigaya ya zama mahaifin Abitub da Elfa'al ta wurin Hushim. 12 'Ya'yan Elfa'al su ne Eber, Misham, da Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan da ke kewaye da su). 13 Akwai kuma Beriya da Shema. Su ne shugabannin zuriyar da suke zama cikin Aijalon, waɗanda suka kori mazaunan Gat. 14 Beriya yana da waɗannan 'ya'ya: Ahio, Shashak, Yeremot, 15 Zebadiya, Arad, Eder, 16 Mika'el, Ishfa, da Yoha. 17 Elfa'al yana da waɗannan 'ya'yan: Zebadiya, Meshullam, Hizki, 18 Heber, Ishmerai, Izliya, da Yobab. 19 Shimei yana da waɗannan 'ya'yan: Yakim, Zikri, Zabdi, 20 Eliyenai, Zilletai, Eliyel, 21 Adayiya, Berayiya, da Shimrat. 22 Shashak yana da waɗannan 'ya'yan: Ishfan, Eber, Eliyel, 23 Abdon, Zikri, Hanan, 24 Hananiya, Elam, Antotijah, 25 Ifdeyiya, da Fenuwel. 26 Yeroham na da waɗannan 'ya'yan: Shamsherai, Shehariya, Ataliya, 27 Ya'areshiya, Iliya da Zikri. 28 Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanninsu da suka zauna cikin Yerusalem. 29 Yeyil, mahaifin Gibiyon, sunan matarsa ita ce Ma'aka, ya zamna cikin Gibiyon. 30 ‌'Ɗan farinsa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba'al, Nadab, 31 Gedor, Ahiyo, da Zeker. 32 Wani daga cikin 'ya'yan Yeyil shi ne Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Sun zauna kusa da 'yan'uwansu cikin Yerusalem. 33 Ner shi ne mahaifin Kish. Kish shi ne mahaifin Saul. Saul shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab, da Esh-Ba'al. 34 '‌Ɗan Yonatan shi ne Merib-Ba'al. Merib-Ba'al shi ne mahaifin Mika. 35 'Ya'yan Mika su ne, Fithon, Melek, Tareya, da Ahaz. 36 Ahaz ya zama mahaifin Yehoada. Yehoada shi ne mahaifin Alemet, Azmabet da Zimri, Zimri shi ne mahaifin Moza. 37 Moza shi ne mahaifin Bineya. Bineya shi ne mahaifin Rafa. Rafa shi ne mahaifin Eliyasa. Eliyasa shi ne mahaifin Azel. 38 Azel yana da 'ya'ya shida: Azrikam, Bokeru, Ishmail, Sheyariya, Obadiya, da Hanan. Dukkan waɗannan 'ya'yan Azel ne. 39 'Ya'yan Eshek, da ɗan'uwansa, su ne Ulam ɗan farinsa, Yewush na biyu, da Elifelet na uku. 40 'Ya'yan Ulam mayaƙa ne da maharba. Suna da 'ya'ya da jikoki da yawa, jimillarsu 150. Dukkan waɗannan daga zuriyar Benyamin suke.

Sura 9

1 Haka dukkan Isra'ila aka rubuta su bisa ga tarihin asalinsu. An rubuta su cikin littafin sarakunan Isra'ila. Amma game da Yahuda, an ɗauke su zuwa bauta cikin Babila saboda zunubinsu. 2 Na farko da suka zauna cikin biranensu su ne waɗansu Isra'ilawa, firistoci, Lebiyawa da bayin haikali. 3 Waɗansu zuriyar Yahuda, Benyamin, Ifraim, da Manasse sun zauna cikin Yerusalem. 4 Waɗanda suka zauna sun haɗa da Utai ɗan Ammihud ɗan Omri ɗan Imri ɗan Bani, ɗaya daga cikin zuriyar Ferez ɗan Yahuda. 5 A cikin Shelonawa su ne Asayiya ɗan fari da 'ya'yansa kuma. 6 A cikin zuriyar Zera akwai Yewuel. Yawan zuriyarsu ta kai 690. 7 Daga zuriyar Benyamin akwai Sallu ɗan Meshullam ɗan Hodabiya ɗan Hassenuya. 8 Akwai kuma Ibneyiya ɗan Yeroham; Elah ɗan Uzzi ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya ɗan Rewuel ɗan Ibnijah. 9 'Yan'uwansu da ke rubuce cikin tarihin asalinsu sun kai 956. Dukkan waɗannan mutanen shugabanni ne cikin zuriyar kakanninsu. 10 Firistoci su ne Yedayiya, Yeho'iarib, da Yakin. 11 Akwai kuma Azariya ɗan Hilkiya ɗan Meshullam ɗan Zadok ɗan Meraiyot ɗan Ahitub, shugaba a cikin gidan Allah. 12 Akwai Adayiya ɗan Yeroham ɗan Fashur ɗan Malkijah. Akwai kuma Ma'asai ɗan Adiyel ɗan Yahzera ɗan Meshullam ɗan Meshillemit ɗan Immer. 13 'Yan'uwansu, da suke shugabanni cikin gidajen kakanninsu, sun kai 1,760. Mutane ne da suka iya aiki cikin gidan Allah. 14 A wajen Lebiyawa, akwai Shemaiya ɗan Hasshub ɗan Azrikam ɗan Hashabiya, daga zuriyar Merari. 15 Akwai kuma Bakbakkar, Heresh, Galal, da Mattaniya ɗan Mika ɗan Zikri ɗan Asaf. 16 Akwai kuma Obadiya ɗan Shemaiya ɗan Galal ɗan Yedutun; and Berekiya ɗan Asa ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofatawa. 17 Matsaran ƙofa su ne Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman, da zuriyarsu. Shullam shi ne shugabansu. 18 Dã suna tsaro a ƙofar sarki ta wajen gabas domin sansanin zuriyar Lebi. 19 Shallum ɗan Kore ɗan Ebiyasaf, wanda a matsayinsa na ɗan Kora, da 'yan'uwansa daga gidan mahaifinsa, su Korawa, suna bisa aikin hidima, su na kula da ƙofar rumfa, kamar yadda kakanninsu suka kula da sansanin Yahweh, suna kuma tsaron wurin shiga. 20 Finehas ɗan Eliyeza shi ne shugabansu a dã, Yahweh kuma yana tare da shi. 21 Zekariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaron ƙofar shiga haikali, "rumfar taruwa." 22 Dukkan waɗanda aka zaɓe su matsaran ƙofofi sun kai 212. An rubata sunayensu cikin lissafin mutane cikin ƙauyukansu. Dauda da Sama'ila mai gani sun sanya su cikin muƙamansu na amana. 23 Da su da 'ya'yansu sun kula da ƙofofin gidan Yahweh, wato rumfar sujada. 24 An sanya matsran ƙofofi a dukkan kusurwoyi huɗu, wajen gabas, yamma, arewa, da kudu. 25 'Yan'uwansu, da ke zaune a ƙauyukansu, sun zo domin kewayawa na kwana bakwai, a juyi. 26 Amma shugabannin matsara huɗu, wato Lebiyawa, an sanya su kula da ɗakuna da ɗakunan ajiya cikin gidan Allah. 27 Sukan tsaya dukkan dare a wurarensu kewaye da gidan Allah. Domin suke da haƙƙin kula da shi. Za su buɗe shi kowacce safiya. 28 Waɗansun su suna kula da kayan haikali; suna ƙirga su yayin da aka kawo su ko aka fitar da su. 29 Waɗansu kuma an sanya su kula da abubuwa masu tsarki, kayayyaki, da kayan da aka tanada, waɗanda sun haɗa da gari mai laushi, ruwan inabi, mai, da turaren ƙonawa, da kayan yaji. 30 Waɗansu 'ya'yan firistoci sukan haɗa kayan yaji. 31 Mattitiya, ɗaya daga cikin Lebiyawa wanda ɗan fari ne a wurin Shallum Korahiye, shi ne ke ɗauke da nawayar shirya gurasa domin baye-baye. 32 Waɗansu 'yan'uwansu, zuriyar Kohatawa, su ne masu kula da yin gurasa, su shirya kowacce Asabaci. 33 Mawaƙa da shugabannin gidajen ubannin Lebiyawa sun zauna cikin ɗakuna a wuri mai tsarki lokacin da ba su da wani aiki, domin dole su aiwatar da nasu ayyuka dare da rana. 34 Waɗannan shugabannin gidajen ubannin cikin Lebiyawa ne, kamar yadda ya ke a jere cikin rubutaccen tarihin asalinsu. Suna zama cikin Yerusalem. 35 Mahaifin Gibiyon, Yeyiyel, sunan matarsa itace Ma'aka, ya zauna cikin Gibiyon. 36 'Dan farinsa shi ne Abdon, ɗansa shi ne Zur, Kish, Ba'al, Ner, Nadab, 37 Gedor Ahiyo, Zekariya da Miklot. 38 Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Sun zauna kusa da 'yan'uwansu cikin Yerusalem. 39 Ner shi ne mahaifin Kish. Kish mahaifin Saul. Saul mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab, da Esh-Ba'al. 40 ‌Ɗan Yonatan shi ne Merib-Ba'al. Merib-Ba'al shi ne mahaifin Mika. 41 'Ya'yan Mika su ne Fithon, Melek, Tareya, da Ahaz. 42 Ahaz shi ne mahaifin Yada. Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmabet, da Zimri. Zimri shi ne mahaifin Moza. 43 Moza shi ne mahaifin Bineya. Bineya shi ne mahaifin Refayiya. Refayiya shi ne mahaifin Eliyasa. Eliyasa shi ne mahaifin Azel. 44 'Ya'yan Azel shida su ne Azrikam, Bokeru, Ishma'el, Sheyariya, Obadiya, da Hanan. Waɗannan su ne 'Ya'yan Azel.

Sura 10

1 Yanzu fa Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ila. Kowanne mutumin Isra'ila ya gudu daga gaban Filistiyawa su ka faɗi matattu a kan Tsaunin Gilbowa. 2 Filistiyawa suka runtumi Saul da ɗansa kusa kusa. Filistiyawa suka kashe Yonatan, Abinadab, da Malki-Shuwa, 'ya'yansa. 3 Yaƙi ya tsananta gãba da Saul ƙwarai, maharba kuma sun cim masa, kuma suka yi masa rauni. 4 Daga nan sai Saul ya ceda mai ɗaukar masa makamai, "Ka zare takobinka ka kashe ni da ita. In ba haka ba, waɗannan marasa kaciyar za su zo su zage ni." Amma mai ɗaukar makamansa yaƙi, domin yana jin tsoro ƙwarai. Sai Saul ya ɗauki takobinsa ya faɗi a kanta. 5 Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, shi ma sai ya faɗi a kan takobinsa ya mutu. 6 Da haka Saul ya mutu, da 'ya'yansa uku. Dukkan iyalin gidansa suka mutu tare. 7 Sa 'ad da kowanne mutum a Isra'ila da ke cikin kwari yaga cewa sun gudu, kuma Saul da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar biranensu suka gudu. Daga nan sai Filistiyawa suka zo suka zauna cikinsu. 8 Ya zama kuwa washegari, sa'ad da Filistiyawa suka zo su ɗauki kayan matattu, sun tarar da Saul da 'ya'yansa matattu a Tsaunin Gilbowa. 9 Suka tuɓe shi suka ɗauki kansa da kayan yaƙinsa. Suka aikar da saƙo ko'ina cikin Filisitaya a kuma kai labarin ga gumakansu da mutane. 10 Suka sa kayan yaƙinsa cikin haikalin allolinsu, suka kafe kansa a gidan Dagon. 11 Sa'ad da dukkan mutanen Yabesh Giliyad suka ji dukkan abin da Filistiyawa suka yi wa Saul, 12 dukkan maza mayaƙa su ka je suka ɗauki jikin Saul da na 'ya'yansa, suka kawo su Yabesh. Suka bizne ƙasusuwansu ƙarƙashin itacen rimi cikin Yabesh suka yi azumi kwana bakwai. 13 Saul ya mutu saboda ya yi rashin amincin ga Yahweh. Bai yi biyayya ga umarnan Yahweh ba, amma ya nemi shawara a wurin wata mai yin magana da matattu. 14 Bai nemi shawara daga wurin Yahweh ba, shi yasa Yahweh ya kashe shi ya mayar da mulkin ga Dauda ɗan Yesse.

Sura 11

1 Daga nan si dukkan Isra'ila suka zo wurin Dauda a Hebron suka ce, "Duba, mu ƙashinka da namanka ne. 2 Cikin kwanakin dã, lokacin da Saul ya ke sarki a bisanmu, kai ne ka ke jagorancin mutanen Isra'ila. Yahweh Allahnka ya ce maka, 'Za ka yi kiwon mutanena Isra'ila, kuma zaka zama mai mulki bisan mutanena Isra'ila."" 3 Dukkan dattawan Isra'ila suka zo wurin sarki a Hebron, Dauda ya yi alƙawari da su gaban Yahweh. Suka ƙeɓe Dauda sarki a bisan Isra'ila. Ta haka maganar Yahweh wadda Sama'ila ya furta ta zama gaskiya. 4 Dauda da dukkan Isra'ila suka je Isra'ila (wato, Yebus). Yebusawa mazaunan ƙasar, su na can. 5 Mazaunan Yebus suka ce da Dauda, "Ba za ka zo nan ba." 6 Amma Dauda ya ci kagarar Sihiyona, wato, Birnin Dauda. Dauda ya ce, "Duk wanda ya fara bugun Yebusawa zai zama shugaban yaƙi." Yowab ɗan Zeruya ya fara kai hari, aka mai she shi ya zama shugaba. 7 Daga nan Dauda ya fara zama cikin kagara. Sai suka kira ta birnin Dauda. 8 Ya gina garu kewaye da birnin daga Millo da baya zuwa kewayan bangon. Yowab ya gina sauran birnin. 9 Dauda ya zama babba ya ƙasaita saboda Yahweh mai runduna yana tare da shi. 10 Wɗannan su ne shugabanni ƙarƙashin Dauda, waɗanda su ka taimaki mulkin Dauda ya zama da karfi, tare da dukkan Isra'ila, suka sa shi ya zama sarki, da biyayya da maganar Yahweh game da Isra'ila. 11 Waɗannan su ne jerin ƙwararrun sojojin Dauda: Yashobeyam, ɗan Bahakmonite, shi ne hafsan ofisoshi. Ya kashe mutum ɗari uku da mashin sa a lokaci ɗaya. 12 Bayan sa sai Eliyeza ɗan Dodo, Ba'ahohite, ɗaya daga cikin jarumawan nan uku. 13 Yana tare da Dauda a Fas Dammim, a wurin Filistiyawa suka taru domin yaƙi, inda akwai yankin ƙasa mutane kuma suka gudu daga gaban Filistiyawa. 14 Suka tsaya a tsakiyar filin. Suka kãre shi suka kuma kashe Filistiyawa da yawa Yahweh kuma ya cece su da babbar nasara. 15 Daga nan mutum uku cikin talatin suka tafi wurin Dauda cikin dutse, a kogon Adullam. Mutanen Filistiyawa suka yi sansani a cikin Kwarin Refayim. 16 A lokacin nan Dauda yana cikin kagara, a kogo, yayin da Filistiyawa suka kafa sansanin su a Betlehem. 17 Dauda ya ji ƙishin ruwa sai ya ce, "Da ma wani zaya bani ruwa in sha daga rijiyar da ke a Betlehem, rijiyar dake a bakin ƙofa!" 18 Sai jarumawan nan uku suka kụtsa cikin rundunar Filistiyawa suka ɗebo ruwa daga cikin rijiyar Betlehem, rijiyar da ke bakin ƙofa. Suka ɗauko ruwan suka kawo wa Dauda, amma yaƙi shan sa. Maimakon haka, ya tsiyaye shi ga Yahweh. 19 Sai ya ce, "Yahweh, ya nisantarda wannan daga gare ni, da zan sha wannan ruwan. Zan sha jinin mutane waɗanda su ka sadaukar da rayukansu?" Saboda sun sa ran su cikin haɗari, Dauda ya ƙi shan ruwan. Wannan shi ne abin da jarumawan nan uku suka yi. 20 Abishai ɗan'uwan Yowab, shugabane na jarumawan uku. Ya taɓa amfani da mãshin sa ya kashe mutum ɗari uku. An faɗe shi cikin su ukun nan. 21 A cikin ukun ɗin ya sami girmamawa riɓi biyu har ya zama shugabansu. Ko da shike baya ɗaya daga cikin su. 22 Benaiya ɗan Yeho'iada ya zama da ƙarfi daga Kabzeel wanda ya yi manyan abubuwa. Ya kashe 'ya'ya biyu na Ariyel mutumin Mowab. Ya kuma sauka cikin rami ya kashe zaki lokacin sanyin dusar ƙanƙara. 23 Har ya kashe Bamasare, tsawon mutumin ya kai kamu biyar. Bamasaren yana da babban mãshi misalin itacen sãƙa amma ya je wurin sa da sanda kawai. Ya fizge mãshin daga hanun Bamasaren ya kashe shi da mãshinsa. 24 Benaiya ɗan Yeho'iada ya yi waɗannan ayyuka, an sanya sunansa tare da jarumawan uku. 25 An mutunta shi fiye da sojojin nan talatin gaba ɗaya, amma ba kamar ƙwararrun sojojin nan uku ba. Duk da haka Dauda ya sanya shi shugaba akan matsaransa. 26 Jarumawan mutanen su ne: Asahel ɗan'uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo na Betlehem, 27 Shammot Baharore, Helek Bafelone, 28 Ira ɗan Ikkesh Batekoye, Abiyeza Ba'anatote, 29 Sibbekai Bahushate, Ilai Ba'ahohite. 30 Maharai Banetofate, Heled ɗan Baanah Banetofate, 31 Ittai ɗan Ribai na Gibiya na zuriyar Benyamin, Benaiya Bafiratone, 32 Hurai na kwarurrukan Ga'ash, Abiyel Ba'arbate, 33 Azmabet Baharume, Eliyaba Basha'albone, 34 'ya'yan Hashem Bagizoniye, Yonatan ɗan Shagi Baharare, 35 Ahiyam ɗan Sakar Baharare, Elifal ɗan Ur, 36 Hefar Bamekarate, Ahija Bafelone, 37 Hezro Bakarmele, Na'arai ɗan Ezbai, 38 Yowel ɗan'uwan Natan, Mibhar ɗan Hagri, 39 Zelek Ba'moniye, Naharai Baberote (mai ɗaukar wa Yowab makamai ɗan Zeruyiya) 40 Ira Ba'itriye, Gareb Ba'itriye, 41 Yuriya Bahitte, Zadab ɗan Ahlai, 42 Adina ɗan Shiza Barubeniye (shugaban Rubenawa) da mutum talatin tare dashi, 43 Hanan ɗan Ma'aka da Yoshafat Bamitiniye, 44 Uzziya Ba'ashterate, Shama da Yeyiyel 'ya'yan Hotam Ba'arowaye, 45 Yediyayel ɗan Shimri, Yoha (ɗan'uwansa Batize), 46 Eliyel Bamahabe, Yeribai da Yoshabiya 'ya'yan Elna'am, Itma Bamowabe, 47 Eliyel, Obed, da Ya'asiel Bamezobate.

Sura 12

1 Waɗannan su ne waɗanda suka zo wurin Dauda a Ziklag, tun lokacin da bai iya tsayawa gaban Saul ɗan Kish ba. Suna cikin sojoji, mataimakan sa a cikin yaƙi. 2 Maharban baka ne kuma sukan harba ta dama da hagu sukan jefa dutse da majaujawa wajen harbin kibiya da baka. Su mutanen Benyamin ne, mutanen kabilar Saul. 3 Sarki shi ne Ahiyaza, sai Yowash, dukkan su 'ya'yan Shema'ah Bagibeyate. Akwai Yeziyel da Felet, 'ya'yan Azmebet. Akwai kuma Berakah, Yehu Ba'anatote, 4 Ishmaiya Bagibiyone, sojane cikin talatin ɗin (Kuma shugaban talatin ɗin); Irmiya, Yahaziyel, Yonanan, Yozabad Bagaderate. 5 Eluzai, Yerimot, Beyaliye, Shemariya, Shefatiya Baharufiye, 6 Koratawa, Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezar, Yashobeyam, da 7 Yowela da Zebadiya, 'ya'yan Yeroham na Gedor. 8 Waɗansu Gadawa su ka haɗu da Dauda a kagara cikin jeji. Su jarumawa ne, Horarru domin yaƙi, waɗanda sun iya garkuwa da mashi; fuskokinsu kamar na zakuna. Sauri gare su kamar bareyi a kan duwatsu. 9 Akwai Ezer shugaba, Obadiya na biyu, Eliyab na uku, 10 Mishmanna na huɗu, Irmiya na biyar, 11 Attai na shida, Eliyel na bakwai, 12 Yonatan na takwas, Elzabad na tara, 13 Irmiya na goma, Makbannai na sha ɗaya. 14 Waɗannan 'ya'yan Gad shugabannin runduna ne. ƙaraminsu shi ke jagorancin ɗari, babbansu shi ke jagorancin dubbai. 15 Sun ƙetare Yodan cikin wata na fari, sa'ad da ya yi ambaliya ya kori dukkan waɗanda suke zama cikin kwarurruka, dukka da na wajen gabas da na wajen yamma. 16 Waɗansu mutanen Benyamin da na Yahuda suka zo kagara wurin Dauda. 17 Dauda ya fita domin ya tarye su ya yi masu jawabi yace: "Idan kun zo wurina da salama ku taimakeni, za ku iya haɗa hannu da ni. Amma idan kun zo ne domin ku bashe ni ga abokan gãba ta, bari Allah na kakanninku ya gani ya tsauta maku, gama ban yi wani abin da ba dai-dai ba." 18 Sa'an nan sai Ruhu ya sauko kan Amasai, wanda ya ke shugaban talatin ɗin. Amasai ya ce, "Mu na ka ne, ya Dauda. Wajen ka mu ke, ya ɗan Yesse. Salama, bari salama ta kasance ga duk wanda ya taimakeka. Bari salama ta kasance ga masu taimakonka, gama Allahnka ya na taimakonka." Daga nan Dauda ya karɓe su ya sa su zama shugabanni akan jama'arsa. 19 Waɗansu daga Manasse ku ma suka koma wajen Dauda sa'ad da ya zo tare da Filistiyawa domin ya yi yaƙi da Saul. Duk da haka ba su taimaki Filistiyawa ba, saboda shugabannin Filistiyawa sun tuntuɓi junansu sa'an nan suka sallame shi. Suka ce, "Zai koma wajen ubangidansa Saul zai jawo haɗari ga rayukanmu." 20 Da ya je Ziklag, mutanen Manasse da su ka haɗa hannu da su su ne Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika'el, Yozabad, Elihu, da Zilletai, shugabanni na dubbai na Manasse. 21 Sun taimaki Dauda yaƙi da taron mahara, gama su jarumawa ne. Daga baya su ka zama shugabanni cikin runduna. 22 Yau da gobe, mutane suka yi ta zuwa wurin Dauda domin su taimake shi, har aka sami babbar rundunar soja, kamar rundunar sojojin Allah. 23 Wannan shi ne lissafin sojoji masu makamai domin yaƙi, waɗanda suka zo wurin Dauda a Hebron, domin su juyar da mulkin Saul zuwa gare shi, domin tabbatar da maganar Yahweh. 24 Daga Yahuda waɗanda suke ɗauke da garkuwa da mãshi sun kai 6,800, a shirye domin yaƙi. 25 Daga zuriyar Simiyon sun kai jarumawa 7,100 26 Daga zuriyar Lebiyawa sun kai mayaƙa 4,600. 27 Yehoyada shi ne shugaban zuriyar 'ya'yan Haruna tare da shi akwai mutum 3,700. 28 Tare da Zadok saurayi, ƙaƙƙarfa, mutum mai ƙarfin hali, sun kai shugabanni ashirin da biyu daga iyalin mahaifinsa. 29 Daga Benyamin, kabilar Saul, sun kai dubu uku. Yawancinsu suka zama da biyayya ga Saul har zuwa lokacin nan. 30 Daga Ifraim sun kai mayaƙa 20,800, suna cikin gidajen mahaifansu. 31 Daga rabin kabilar Manasse akwai mutane dubu goma sha takwas waɗanda suka zo domin su naɗa Dauda sarki. 32 Daga Issaka, akwai shugabanni ɗari biyu masu gane zamanai sun san abin da ya kamata Isra'ila su yi. Dukkan 'yan'uwansu suna ƙarƙashin mulkinsu. 33 Daga Zebulun akwai mayaƙa dubu hamsin, shiryayyu domin yaƙi, da dukkan makaman yaƙi, a shirye suke suyi biyayya da zuciya ɗaya. 34 Daga Naftali akwai shugabanni dubu, tare da su kuma mutum dubu talatin da bakwai tare da garkuwa da mãsu. 35 Daga Danawa akwai mutane 28,600 shiryayyu domin yaƙi. 36 Daga Asha akwai mutane dubu arba'in shiryayyu domin yaƙi. 37 Daga ɗaya ƙetaren Yodan, daga Rubenawa, Gadawa, da rabin kabilar Manasse, akwai mutane 120,000 shirye domin kowanne irin yaƙi. 38 Dukkan waɗannan sojojin, shiryayyu ne domin yaƙi, sun zo Hebron da tsayayyar manufa wato su naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila. 39 Dukkan sauran Isra'ila kuma sun amince ya zama sarki. Suna can tare da Dauda kwana uku, suna ci da sha, gama 'yan'uwansu sun aike su da guzuri. 40 Har yanzu kuma, waɗanda ke kusa da su, kamar su Issaka da Zebulun da Naftali, sun kawo abinci akan jakuna da raƙuma, alfadarai, da shanu, guzurin gari, kauɗar 'ya'yan ɓaure, ruwan inabi, mai, shanu, da tumaki, gama Isra'ila tana murna.

Sura 13

1 Dauda ya tuntuɓi shugabanni na mutum dubbai da na ɗaruruwa, tare ta kowanne shugaba. 2 Dauda ya ce da dukkan taron Isra'ila, "Idan kun ga ya yi maku kyau, idan kuma wannan ya zo ne daga wurin Yahweh Allahnmu, bari mu aika da 'yan saƙo ko'ina ga 'yan'uwanmu, waɗanda suka rage cikin dukkan lardunan Isra'ila, ga Firistoci da Lebiyawa waɗanda suke cikin garuruwansu. Bari a sanar da su cewa su haɗa kai da mu. 3 Bari mu kawo akwatin Allahnmu gare mu, gama ba mu nemi nufinsa a cikin kwanakin mulkin Saul ba." 4 Dukkan taron jama'a suka yarda da waɗannan abubuwa, saboda ya yi dai-dai a idanun dukkan mutane. 5 Dauda fa ya tara dukkan Isra'ila tare, daga Shihor Kogi a cikin Masar zuwa Lebo Hamat, domin kawo akwatin Allah daga Kiriyat Yeyarim. 6 Dauda da dukkan Isra'ila suka hau zuwa Baalah, wato Kiriyat Yeyarim, wanda ke na Yahuda, domin daga can za a ɗauko akwatin Allah, wanda ake kira da sunan Yahweh, wanda ya ke zaune yana mulki akan Kerubim 7 Sai suka sanya akwatin Allah akan sabon keken shanu. Sun fito da shi daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suna kula da keken shanun. 8 Dauda da dukkan Isra'ila suna murna a gaban Allah da dukkan ƙarfinsu. Suna waƙa da garayu da molaye, kugenni, da kakaki 9 Sa'ad da suka zo masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa domin ya riƙe akwatin, saboda shanun sun yi tuntuɓe. 10 Daga nan fushin Yahweh ya yi ƙuna akan Uzza, Yahweh ya kashe shi domin Uzza ya miƙa hannunsa ya taɓa akwatin. Ya mutu a wurin a gaban Allah. 11 Dauda ya yi fushi saboda Yahweh ya abkawa Uzza. Ana kiran wannan wurin Ferez Uzza har wa yau. 12 Dauda ya ji tsoron Allah a wannan rana. Ya ce, "Ya ya zan kawo akwatin Allah in dawo da shi gidana?" 13 Dauda bai gusar da akwatin zuwa birnin Dauda ba, amma ya sa shi a gefe cikin gidan Obed Idom Bagittiye. 14 Akwatin Allah ya kasance cikin gidan Obed Idom har wata uku. Yahweh ya albarkaci gidansa da dukkan abin da ya mallaka.

Sura 14

1 Daga nan Hiram sarkin Taya ya aika da 'yan saƙo wurin Dauda, da itatuwan Sida, kafintoci da magina. Su ka gina masa gida. 2 Dauda kuwa ya sa ni Yahweh ya tabbatar da shi zama sarki akan Isra'ila, kuma mulkinsa zai ɗaukaka sama domin taimakon mutanensa Isra'ila. 3 A cikin Yerusalem, Dauda ya auri waɗansu mata, ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da 'ya'ya mata. 4 Waɗannan su ne 'ya'yan da aka haifa masa cikin Yerusalem: Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon, 5 Ibha, Elishuwa, Elfelet, 6 Noga, Nefeg, Yafiya, 7 Elishama, Biliyada, da Elifelet. 8 Sa'ad da Filistiyawa su ka ji cewa an keɓe Dauda ya zama sarki bisa Isra'ila, dukka suka fita suna neman sa. Amma Dauda ya ji labarin sai ya fita ya yi yaƙi da su. 9 Filistiyawa sun rigaya sun kawo hari cikin kwarin Refayim. 10 Daga nan Dauda ya nemi taimako a wurin Allah. Ya ce, "Ko zan iya kai wa Filistiyawa hari? Za ka bani nasara akan su?" Yahweh ya ce masa, "Kai masu hari, gama lallai zan ba she su gare ka." 11 Sai suka zo Ba'al Ferazim, a can ya yi nasara da su. Ya yaba ya ce, "Yahweh ya fasa abokan gãbata ta hannuna, kamar fasuwar ambaliyar ruwa." Sunan wannan wurin ya zama Ba'al Ferazim. 12 Filistiyawa suka bar allolinsu a wurin, Dauda kuma ya umarta a ƙone su. 13 Filistiyawa suka sake kai hari a cikin kwari. 14 Dauda ya sake neman taimako a wurin Allah. Allah ya ce masa, ba za ka kai hari ta gabansu ba, amma ka kewaye su ta itatuwan balsam sai ka kai masu hari ta baya." 15 Sa'ad da ka ji motsin tafiya cikin iska ta itatuwan balsam, daga nan sai ka kai hari da ƙarfi. Ka yi haka gama Allah ya rigaya ya tafi a gabanka domin ya bugi rundunar Filistiyawa." 16 Dauda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi. Ya ci nasara da rundunar Filistiyawa tun daga Gibiyon har zuwa Gezar. 17 Daga nan sunan Dauda ya bazu zuwa ko'ina cikin dukkan ƙasashe, Yahweh kuma ya sa dukkan ƙasashe su ji tsoron sa.

Sura 15

1 Dauda ya gina wa kansa gidaje a cikin birnin Dauda. Ya shirya rumfa saboda akwatinin Yahweh inda a ka ajiye shi. 2 Sa'an nan Dauda yace, "Lebiyawa ne kaɗai za su ɗauki akwatin Yahweh, domin su aka zaɓa su ɗauki akwatin Yahweh, su yi masa hidima har abada." 3 Sa'an nan Dauda ya tattara dukkan Isra'ila a Yerusalem domin a kawo akwatin Yahweh wurin da ya shirya masa. 4 Dauda ya tattara zuriyar Haruna da Lebiyawa. 5 Daga zuriyar Kohat akwai shugaba wato Yuriyel, da 'yan'uwansa mutum 120. 6 Daga zuriyar Merari akwai shugaba wato Asayiya, da 'yan'uwansa mutum 220. 7 Daga zuriyar Geshon akwai shugaba wato Yowel, da 'yan'uwansa mutum 130. 8 Daga zuriyar Elizafan, akwai shugaba wato Shemaiya, da 'yan'uwansa mutum 200. 9 Daga zuriyar Hebron akwai shugaba wato Eliyel, da 'yan'uwansa mutum tamanin. 10 Daga zuriyar Yuziyel akwai shugaba wato Amminadab da 'yan'uwansa mutum 112. 11 Dauda ya kira Zadok da Abiyata firistoci da Lebiyawa wato su, Yuriyel da Asayiya da Yowel da Shemaiya da Eliyel da Amminadab. 12 Ya ce da su, "Ku ne shugabannin Lebiyawa. Ku tsarkake kanku, ku da 'yan'uwanku domin ku kawo akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila a wurin da na shirya domin sa. 13 Ba ku ne ku ka ɗauke shi da farko ba. Shi ya sa Ubangiji Yahweh ya yi fushi da mu domin ba mu bi farillansa ba." 14 Sai firistoci da Lebiyawa suka tsarkake kansu domin su iya ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila. 15 Haka Lebiyawa suka ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila, a bisa kafaɗunsu da sandunan, kamar yadda Musa ya umurta - suna bin ka'idojin da aka shimfiɗa a maganar Yahweh. 16 Dauda ya yi magana da shugabannin Lebiyawa su sa 'yan'uwansa su zama mawaƙa, da kayan waƙoƙi, wato su garayu da molaye da kugenni, suna kaɗa su da ƙara sosai suna tada muryoyinsu suna murna. 17 Sai Lebiyawa suka naɗa Heman ɗan Yowel da wani cikin 'yan'uwansa, wato Asaf ɗan Berekiya. Daga cikin 'yan'uwansu, wato daga zuriyar Merari suka naɗa Itam ɗan Kushaiya. 18 Tare da su akwai 'yan'uwansu aji na biyu: wato su Zekariya da Ya'aziyel da Shemiramot da Yehiyel da Unni da Eliyab da Benaiya da Ma'aseiya da Mattitiya da Elifelehu da Miknaiya da Obed Idom da Yehiyel masu tsaron ƙofa. 19 Mawaƙan suka zaɓi Heman da Asaf da Itam su zama masu kaɗa kugenni masu ƙara na tagulla. 20 Zekariya da Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma'sseiya da Benaiya su ne masu kiɗan girayu, da aka shirya wa Alamot. 21 Mattitiya da Elifelehu da Mikneiya, Obed Idom, Yeyiyel da Azaziya suka bi da hanya tare da kiɗin girayu da aka shirya wa Sheminit. 22 Kenaniya, shugaban Lebiyawa shi ne kuma shugaban mawaƙa saboda shimai koyar da waƙa ne. 23 Berekiya da Elkana su ne masu tsaron akwati. 24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zekariya, Benaiya da Eliyeza, firistoci, su ne masu busa ƙaho a gaban akwatin Yahweh. Obed Idom da Yehiyel kuma su ne masu tsaron akwatin Yahweh. 25 Sai Dauda da dattawan Isra'ila da shugabannin dubbai suka tafi don su ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh daga gidan Obed Idom da murna. 26 Sa'an nan, Yahweh ya taimaki Lebiyawan da suka ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh, suka miƙa hadaya ta bijimai bakwai da raguna bakwai. 27 Dauda ya sa riga ta linin, haka kuma Lebiyawan da suka ɗauki akwatin da mawaƙa da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dauda kuma yana saye da falmara ta linin. 28 Haka dukkan Isra'ila suka kawo akwatin alƙawarin Yahweh da shewa ta farinciki, da ƙarar ƙahonni da kugenni da girayu da molaye. 29 Amma sa'ad da akwatin alƙawarin Yahweh ya shigo birnin Dauda, Mika'el ɗiyar Saul ta leƙa ta taga. Sai ta ga sarki Dauda yana rawa yana jin daɗi. Sai ta rena shi a cikin zuciyarta.

Sura 16

1 Su kawo akwatin Yahweh suka sa shi a tsakiyar rumfar da Dauda ya kafa domin sa. Sa'an nan suka yi baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta a gaban Yahweh. 2 Sa'ad da Dauda ya gama yin hadayu na ƙonawa da baye - baye na zumunta, ya sa wa mutanen albarka a cikin sunan Yahweh. 3 Ya ba kowanne mutum namiji da mace dunƙulen gurasa da yankan nama da curin kauɗar inabi. 4 Dauda ya sa waɗansu cikin Lebiyawa su yi hidima a gaban akwatin Yahweh, su yi farinciki da godiya su yi yabo ga Yahweh, Allah na Isra'ila. 5 Waɗannan Lebiyawa su ne Asaf, shi ne shugabansu da Zekariya, Yaaziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benaiya, Obed Idom da Yeyiyel. Waɗanna su ne za su kiɗa girayu da molaye. Asaf shi ne zai kiɗa kugenni da ƙara sosai. 6 Benaiya da Yahaziyel firistoci su ne za su yi ta busa ƙahonni, a gaban akwatin alƙawari na Allah. 7 A wannan rana Dauda ya fara sa Asaf da 'yan'uwansa su rera wannan waƙa ta godiya ga Yahweh. 8 Ku yi godiya ga Yahweh, ku kira bisa sunansa, ku sanar da ayyukansa a cikin al'ummai. 9 Ku rera gare shi, ku rera yabbai gare shi, ku faɗi dukkan ayyukansa na mamaki. 10 Ku yi fahariya cikin sunansa mai tsarki; bari zuciyar waɗanda suke neman Yahweh ta yi murna. 11 Ku nemi Yahweh da ƙarfinsa; ku nemi kasancewarsa a kullun. 12 Ku tuna aiyukan ban mamakin da ya yi, da al'ajibansa da dokokin bakinsa, 13 ku zuriyar Isra'ila bayinsa da ku mutanen Yakubu, zaɓaɓɓunsa. 14 Shi ne Yahweh, Allahnmu, dokokinsa suna cikin dukkan duniya. 15 Ku tsare alƙawarinsa a zukatanku har abada da maganar da ya umurta ga dubun tsararraki. 16 Yakan tuna alƙawarin da ya yi da Ibrahim da wa'adin da ya yi wa Ishaku. 17 Wannan shi ne ya tabbatar wa Yakubu ya zama ka'ida, ga Isra'ila kuma alƙawari na har abada. 18 Ya ce, "Zan ba ku ƙasar Kan'ana a matsayin rabonku na gădo." 19 Lokacin da ba su da yawa, 'yan ƙalilan, kuma baƙi a cikin ƙasar. 20 Suka yi yawo daga wannan al'umma zuwa waccan, daga wannan mulki zuwa wani. 21 Bai yarda wani ya tsanance su ba; ya ma hori sarakuna saboda su. 22 Ya ce, "Kada ku taɓa shafaffuna, kada ku cuci annabawana." 23 Ku rera ga Yahweh, ku duniya dukka, ku yi shelar cetonsa kowacce rana. 24 Ku shaida ɗaukakarsa a cikin al'ummai, ayyukansa na mamaki a cikin dukkan al'immai. 25 Gama Yahweh mai girma ne, a yabe shi ƙwarai, a ji tsoron sa fiye da dukkan alloli. 26 Gama dukkan alloli na al'ummai gumaka ne, Amma Yahweh, shi ne ya hallicci sammai. 27 Daraja da martaba na tare da shi. Iko da farinciki na wurinsa. 28 Ku bayar ga Yahweh, ku kabilun duniya, ku bayar da daraja da iko ga Yahweh! 29 Ku ba Yahweh darajar da ta dace da sunansa. Ku kawo masa baiko ku zo gabansa. Ku durƙusa ga Yahweh a cikin martabarsa mai tsarki. 30 Ku yi rawar jiki a gabansa ku duniya dukka. Duniya ta kahu, ba za ta iya girgiza ba. 31 Bari sammai su yi murna, bari duniya ta yi farinciki, a cikin al'ummai bari su ce, "Yahweh ne ya ke mulki." 32 Bari teku ya yi ruri, abin da ya ke cika shi kuma ya yi sowa ta farin ciki. Bari filaye su yi farinciki tare da dukkan abin da ke cikin su. 33 Bari itatuwan da ke cikin jeji su yi sowa ta farinciki a gaban Yahweh, gama yana zuwa domin ya hukunta duniya. 34 A yi godiya ga Yahweh, gama nagari ne shi, alƙawarinsa na jinƙai ya tabbata har abada. 35 Sai ku ce, "Ka cece mu, ya Allah na cetonmu. Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga sauran al'ummai, domin mu ba da godiya ga sunanka mai tsarki da ɗaukaka cikin yabonka." 36 A yi yabo ga Yahweh, Allah na Isra'ila har abada abadin. Dukkan mutane suka ce, "Amin" yabo ga Yahweh. 37 Sai Dauda ya bar Asaf da 'yan'uwansa a gaban akwatin alƙawari na Yahweh, su yi ta yin hidima a gaban akwatin, dai-dai da buƙatar kowacce rana. 38 Obed Idom haɗe da 'yan'uwan nan sittin da takwas. Obed Idom ɗan Yedutun tare da Hosah su ne masu tsaron ƙofa. 39 Zadok da abokan aikinsa firistoci kuma suka yi hidima a rumfar Yahweh a can tudun Gibiyon. 40 Su riƙa miƙa baye-baye na ƙonawa a kan bagadi babu fasawa safe da yamma, bisa ga abin da ke rubuce a cikin shari'ar Yahweh, wadda ya ba Isra'ila umarni. 41 Heman da Yedutun su na tare da su da kuma waɗanda a ka kira sunayensu a ka zaɓe su, su ba da godiya ga Yahweh saboda alƙawarinsa da amincinsa sun tabbata har abada. 42 Heman da Yedutun su ne za su lura da waɗanda za su busa ƙahonni da kugenni da sauran kayan kiɗin da a ke amfani da su lokacin da a ke rera waƙoƙi na saduda. 'ya'yan Yedutun su na tsaron ƙofa. 43 Daga nan dukkan jama'a su ka koma gidajensu, Dauda kuma ya koma gida domin ya sa wa mutanensa albarka.

Sura 17

1 Ya zama bayan da sarki ya kimtsa a gidansa, sai ya ce da annanbi Natan, "Duba ni ina zaune a cikin gidan sida, amma akwatin alƙawarin Yahweh yana zaune a rumfa." 2 Natan yace da Dauda, "Ka yi abin da ya ke a zuciyarka, gama Yahweh yana tara da kai." 3 Amma a wannan daren maganar Yahweh ta zo wurin Natan, cewa, 4 "Je ka, ka gaya wa Dauda bawana, 'ga abin da Yahweh ya ce: 'Kai ba za ka gina mani gidan da zan zauna ba. 5 Gama ba a gida ni ke zama ba tun daga ran da na kawo Isra'ila har zuwa yau. Sai dai a rumfa na ke zama da rumfar sujada a wurare dabam-daban. 6 A cikin dukkan wuraren da na zaga cikin Isra'ila, na taɓa yi wa wani cikin shugabannin da na sa, cewa, "Me ya sa ba ka gina mani gida na sida ba?""' 7 To yanzu, ka gaya wa bawana Dauda, 'Ga abin da Yahweh mai Runduna ya ce: Na ɗauko ka daga wurin kiwo, daga bin tumaki, domin ka yi mulkin jama'ata Isra'ila. 8 Ina tare da kai dukkan inda ka tafi, na kuma datse dukkan maƙiyanka daga gabanka, kuma zan sa ka yi suna, kamar sunan waɗanda suke manya a duniya. 9 Zan zaɓi wuri domin jama'ata Isra'ila, domin su zauna a wuri na kansu, don kada su ƙara samun tashin hankali. Mutane masu mugunta ba za su ƙara musguna masu yadda suka yi a dã ba, 10 kamar yadda su ka yi sa'ad da na umurci alƙalai su shugabanci jama'ata Isra'ila. Zan ladabtar da dukkan maƙiyanka. Har yanzu, ina gaya ma ka, Ni Yahweh, zan gina maka gida. 11 Za ya zama idan kwankinka suka cika da za ka tafi wurin ubanninka, zan tada zuriyarka a bayanka, wani daga cikin zuyarka, zan kafa masarautarsa. 12 Shi zai gina mani gida, kuma zan kafa kursiyinsa har abada. 13 Zan zama uba a gare shi, shi kuma zai zama ɗana. Ba zan ɗauke alƙawarin amincina daga gare shi ba kamar yadda na ɗauke daga wurin Saul, wanda ya yi mulki kafin ka. 14 Zan ɗora shi bisa gidana cikin masarautata har abada, kursiyinsa kuma zai tabbata har abada.'" 15 Natan ya yi magana da Dauda, ya baiyana masu dukkan waɗannan maganganu, ya kuma gaya masa game da wahayin gabaɗaya. 16 Sai Dauda ya shiga ciki ya zauna a gaban Yahweh; ya ce, "Wanene ni, Ubangiji Yahweh, menene kuma iyalina, da ka kawo ni a wannan matsayi? 17 Gama wannan ƙaramin abu ne a wurin ka Yahweh. Ka yi magana a kan iyalin bawanka game da babban lokaci mai zuwa, ka kuma nuna wa bawanka tsararraki na gaba, Allah Yahweh. 18 Ni Dauda, me kuma zan ce da kai? Ka ɗaukaka bawanka. Gama ka darajanta bawanka sosai. 19 Yahweh, saboda bawanka, kuma domin ka cika nufinka, ka yi wannan babban abu na baiyana ayyukanka masu girma. 20 Yahweh, ba wani kamar ka, kuma ba wani Allah ban da kai, kamar yadda mu ke ji koyaushe. 21 Gama ina wata al'umma kamar jama'arka Isra'ila, waɗanda ka kuɓutar daga Masar domin su zama mutanenka, su yi suna domin ka ta wurin aiyukanka masu girma da ban razana? Ka kori al'ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar. 22 Ka sa Isra'ila sun zama mutanenka har abada, kuma kai, Yahweh ka zama Allahnsu. 23 To yanzu, Yahweh, ka bari alƙawarin da ka yi game da bawanka da iyalinsa ya tabbata har abada. Ka yi kamar yadda ka ce. 24 Sunanka ya tabbata har abada ya yi girma domin mutane su ce, 'Yahweh mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila,' gidana kuma ni, Dauda ya tabbata a gabanka har abada. 25 Gama kai, Allahna, ka baiyanawa bawanka za ka gina gida domin sa. Shi ya sa ni bawanka, na sami ƙarfin in yi addu'a zuwa gare ka. 26 To yanzu, Yahweh, kai Allah ne, ka kuma yi wannan kyakkyawan alƙawari ga bawanka: 27 Gama ya gamshe ka, ka albarkaci gidan bawanka ya kasance a gabanka har abada. Kai Yahweh, kai ne ka albarkace shi, kuma zai zama mai albarka har abada."

Sura 18

1 Bayan wannan sai Dauda ya kai wa Filistiyawa hari kuma ya yi nasara a kan su. Ya ƙwace Gat da ƙauyukanta daga ƙarƙashin mulkin Filistiyawa. 2 Daga nan ya yi nasara da Mowab, Mowabawa suka zama bayin Dauda suka biya haraji gare shi. 3 Sa'an nan Dauda ya yi nasara da Hadadezer sarkin Zoba a Hamat, sa'ad da Hadadezer ya ke tafiya domin ya kafa mulkinsa a Kogin Yuferatis. 4 Dauda ya ƙwace masa karusai dubu da mahaya dawaki dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu ashirin. Dauda ya yaiyanke jijiyoyin gwuiwoyin dukkan dawakan da ke jan karusai, amma ya rage waɗanda za su ja karusai ɗari. 5 Sa'ad da Aramiyawan Damaskus suka zo domin su taimaki Hadadezar sarkin Zoba, Dauda ya kashe mutanen Aramiyawa dubu ashirin da biyu. 6 Sai Dauda ya kafa zangon sojoji a Aram ta Damaskus. Aramiyawa suka zama bayinsa suka kawo masa gaisuwa. Dukkan inda Dauda ya je, Yahweh yana ba shi nasara. 7 Dauda ya ɗauko garkuwowin zinari waɗanda bayin Hadadezar ke ɗauke da su ya kawo su Yerusalem. 8 Dauda ya ɗauko tagulla da yawa daga Tibhat da Kun biranen Hadadezar. Da wannan tagullar ne Suleman ya yi "Teku" na tagulla da ginshiƙai da sauran kayan aiki na tagulla. 9 Sa'ad da Tou sarkin Hamat ya ji labarin Dauda ya yi nasara da dukkan sojojin Hadadeza sarkin Zoba, 10 Sai Tou ya aika ɗansa Hadoram ya je ya gaida sarki Dauda ya sa masa albarka, saboda Dauda ya yi yaƙi da Hadadeza kuma ya yi nasara da shi, saboda Tou ya yi yaƙi da Hadadeza. Kuma Tou ya aika Dauda abubuwa daban-daban na zinariya da azurfa da tagulla. 11 Sarki Dauda ya keɓe waɗannan kaya ga Yahweh tare da dukkan azurfa da zinariyar da ya samo daga dukkan al'ummai: wato Idom, Mowab, da mutanen Ammon da Filistiyawa da Amelikawa. 12 Abishai ɗan Zeruyiya ya kashe Idomawa dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri. 13 Ya kafa zangon sojoji a Idom, dukkan Idomawa suka zama bayin Dauda. Yahweh ya ba Dauda nasara a dukkan inda ya je. 14 Dauda ya yi mulkin dukkan Isra'ila, kuma ya yi gaskiya da adalci ga dukkan mutane. 15 Yowab ɗan Zeruyiya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud kuma shi ne marubuci. 16 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Shabsha ne marubuci. 17 Benaiya ɗan Yehoiada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, 'ya'yan Dauda kuma su ne manyan masu ba da shawara.

Sura 19

1 Daga baya sai Nahash, sarkin mutanen Amon, ya mutu, ɗansa ya gaje shi. 2 Dauda yace, "Zan yi mutunci ga Hanum ɗan Nahash, saboda mahaifinsa ya nuna mutunci gare ni." Sai Dauda ya aika manzanni su yi masa gaisuwa game da mahaifinsa. Bayin Dauda suka shiga ƙasar Ammoniyawa suna je wurin Hanum domin su yi masa gaisuwa. 3 Amma sarakunan Ammoriyawa suka ce da Hanum, "Ka na tsammani Dauda girmama mahaifinka ya ke yi da ya aiko mutane su yi maka gaisuwa? Ba leƙen asiri ya kawo su domin su duba ƙasar nan da nufin su kaɓantar da ita ba?" 4 Sai Hanun ya kama bayin Dauda ya yi masu aski, ya yayyanke rigunansu har zuwa kwankwaso sa'an nan ya sallame su. 5 Sa'ad da suka yi wa Dauda bayani ya aika a ka tarbe su, saboda sun kunyata ƙwarai. Sarki yace da su, "Ku tsaya a Yeriko sai gemunanku sun fito, sa'an nan ku dawo." 6 Da Ammoniyawa suka ga sun maida kansu abin ƙyama ga Dauda, Hanun da Ammoniyawa suka aika da dubban awon azurfa domin su gaiyato karusan Arameyawa da mahaya dawaki daga Nahariyam da Ma'aka da Zoba. 7 Su ka gaiyato karusai dubu talatin da biyu tare da sarkin Ma'aka da mutanensa, waɗanda suka zo suka yi zango kusa da Medeba. Ammoniyawa suka tattaro daga biranensu, suka fito domin a yi yaƙi. 8 Da Dauda ya ji haka, sai ya aiki Yowab tare da dukkan sojojinsa su je su same su. 9 Mutanen Ammon su ka fito suka ja layi a ƙofar birni domin yaƙi, su kuma sarakunan da suka zo suka zauna cikin fili su kaɗai. 10 Lokacin da Yowab ya ga layin yaƙi na fuskantar sa gaba da baya, daga cikin mutanen Isra'ila ya zaɓi waɗansu gwanayen yaƙi ya shirya su, domin su kara da Arameyawa. 11 Sauran sojojin kuma ya ba da su ga Abishai ɗan'uwansa, domin ya sa su kara da sojojin Ammon. 12 Yowab yace, "Idan Arameyawa suka fi ƙarfi na, to kai Abishai, sai ka kuɓutar da ni. Amma idan sojojin Ammoniyawa suka fi ƙarfin ka to, ni zan zo in kuɓutar da kai. 13 Ka ƙarfafa, bari mu yi ƙarfin hali saboda mutanenmu kuma saboda biranen Allahnmu, gama Yahweh zai yi abin da ya gamshe shi." 14 Sai Yowab da sojojinsa suka nausa domin su yi yaƙi da sojojin Arameyawa, waɗanda aka tilasta wa su gudu a gaban sojojin Isra'ila. 15 Sa'ad da sojojin Ammon suka ga Arameyawa sun gudu, suma sai suka gudu daga wurin Abishai ɗan'uwan Yowab suka koma cikin birni. Daga nan Yowab ya koma daga wurin mutanen Ammon ya kuma koma Yerusalem. 16 Lokacin da Arameyawa suka ga Isra'ilawa sun yi nasara a kansu, sai suka nemi taimako daga ƙetaren Kogin Yuferatis, tare da Shofak shugaban sojojin Hadadeza. 17 Sa'ad da Dauda ya ji haka, sai ya tattara dukkan Isra'ila, suka haye Yodan, suka je wurin su. Ya shirya sojoji domin su yi yaƙi da Arameyawa, suka kuwa yi faɗa da shi. 18 Arameyawa suka gudu daga gaban Isra'ila, Dauda kuwa ya kashe sojojin karusan Arameyawa dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba'in. Ya kuma kashe Shofak shugaban sojojin. 19 Da dukkan sarakuna, wato bayin Hadadeza suka ga Isra'ila sun ci nasara a kan su, suka nemi salama da Dauda suka bauta masa. Sai ya zama mutanen Aram ba su ƙara marmarin su taimaka wa Amoniyawa ba.

Sura 20

1 Da lokaci ya yi sa'ad da sarakuna su kan tafi yaƙi, sai Yowab ya jagoranci sojoji suka je suka ragargaza ƙasar Amoniyawa. Ya ja daga a Rabba. Dauda kuma na Yerusalem. Yowab ya kai wa Rabba hari, ya yi nasara a kanta. 2 Dauda ya ɗauke rawanin sarkinsu daga kansa, sai ya tarar ya kai nauyin awo ɗaya na zinariya, kuma da duwatsu masu daraja a cikin sa. A ka ɗora rawanin a kan Dauda, kuma ya kawo ganima mai yawa daga birnin. 3 Ya fito da mutanen daga cikin birni ya tilasa su yi aiki da zartuna da ƙarafa masu tsini na aiki da gatura. Dauda ya sa dukkan mutanen da ke cikin biranen Ammon su yi wannan aikin. Daga nan Dauda da dukkan sojojin suka dawo Yerusalem. 4 Bayan wannan sai ya zama yaƙi ya ɓarke a Gezer da Filistiyawa. Sibbekai Bahushate ya kashe Siffai, wani daga cikin kabilar Refiyam, daga nan sai a ka ladabtar da Filistiyawa. 5 Sai ya zama a wani yaƙi kuma da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya'ir mutumin Betlehem ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliya mutumin Gat, wanda makamin mãshinsa ya yi kamar turken masaƙa. 6 A wani yaƙin kuma a Gat, a ka sami wani mutum mai tsawo ƙwarai, wanda ya ke da yatsu shida a kowanne hannunsa da kuma yatsu shida a kowacce ƙafarsa. shi ma daga Refiyam ya ke. 7 Da ya yi wa sojojin Isra'ila ba'a, Yehonadab ɗan Shemiya ɗan'uwan Dauda ya kashe shi. 8 Waɗannan zuriyar Refiyam na Gat ne, suka kashe su da hannuwan Dauda da sojojinsa.

Sura 21

1 Wani magafcin Isra'ila ya taso ya iza Dauda ya ƙidaya mutanen Isra'ila. 2 Sai Dauda yace da Yowab da manyan sojoji, "Ku je ku ƙidaya mutanen Isra'ila tun daga Biyasheba har zuwa Dan, ku kawo mani rahoto, domin in san yawansu." 3 Sai Yowab ya ce, "Dama Yahweh ya sa sojojinsa su fi haka yawa sau ɗari. Amma shugabana sarki, dukkan su ba bauta maka su ke yi ba? Me ya sa shugabana ya ke so a yi haka? Yaya za a kawo laifi a Isra'ila?" 4 Amma maganar sarki ta rinjayi Yowab. To, sai Yowab ya fita ya zagaya dukkan Isra'ila. Daga nan ya dawo Yerusalem. 5 Yowab ya kawo wa Dauda rahoton yawan sojoji. A Isra'ila masu zarar takobi su ne 1,100,000. A Yahuda kaɗai akwai sojoji 470,000. 6 Amma ba a ƙidaya Benyamin da Lebi tare da su ba, saboda Yowab bai ji daɗin maganar da sarki ya yi ba. 7 Yahweh bai ji daɗin wannan aikin ba, saboda haka sai ya buga Isra'ila. 8 Dauda ya ce da Yahweh, "Na yi zunubi mai girma da na yi haka. Yanzu, ka ɗauke zunubin bawanka gama na yi wauta ƙwarai." 9 Yahweh yace da Gad, annabin Dauda, 10 "Je ka ka ce da Dauda, 'Ga abin da Yahweh yace, ina ba ka zaɓi guda uku, sai ka zaɓi ɗaya daga cikin su." 11 Sai Gad ya je wurin Dauda ya ce da shi, "Ga abin da Yahweh ya ce, 'Ka zaɓi ɗaya cikin waɗannan: 12 yunwa ta shekaru uku ko wata uku na ƙanƙanci a hannun abokan gãbarka ko kuwa Yahweh ya bi ka da takobinsa har kwana uku, wato annoba ta afko cikin ƙasar, mala'ikan Yahweh ya bi ko'ina cikin ƙasar Isra'ila yana ta hallaka mutane.' To yanzu, sai ka yi tunani ka ba ni amsar da zan kai wa wanda ya aiko ni." 13 Sai Dauda yace da Gad, "Ina cikin babbar damuwa! Gara in faɗa cikin hannun Yahweh da in faɗa cikin hannun mutum, gama jinƙansa yana da yawa ƙwarai." 14 Sai Yahweh ya aiko da annoba a ƙasar Isra'ila, har mutum dubu saba'in suka mutu. 15 Sa'an nan Yahweh ya aiko mala'ika ya hallaka Yerusalem. Yana kusa da ya hallaka ta, sai Yahweh ya canza niyyarsa. Ya ce da mala'ikan mai hallakarwa, "Ya isa! Ka mayar da hannunka."A wannan lokacin, mala'ikan Yahweh yana tsaye masussukar Ornan Bayebushe. 16 Dauda ya tada ido, ya ga mala'kan Yahweh yana tsaye tsakanin sama da ƙasa, da takobi a zare cikin hannunsa ya ɗaga shi a kan Yerusalem. Sai Dauda ya ce da dattawa, ku sa tufafin makoki, ku kwanta da fuskokinku a ƙasa. 17 Dauda ya ce da Yahweh, "Ba ni ne na ba da umarnin a ƙidaya sojoji ba? Ni ne na yi wannan aikin mugunta, amma waɗannan tumaki, me suka yi? Yahweh Allahna! Ka sa hannunka ka buga ni, ni da iyalina, amma kada ka bari annobar ta zauna a kan mutanenka." 18 Sai mala'ikan Yahweh ya umurci Gad ya ce da Dauda, Dauda ya je ya ginawa Yahweh bagadi a masussukar Ornan Bayebushe. 19 Sai Dauda ya tafi ya yi kamar yadda Gad ya dokace shi a cikin sunan Yahweh. 20 Lokacin da Ornan ke sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala'ikan. Sai shi da 'ya'yansa su huɗu, suka ɓoye kansu. 21 Lokacin da Dauda ya zo wurin Ornan, sai Ornan ya duba ya ga Dauda. Sai ya bar wurin sussukar ya faɗi da fuskarsa a ƙasa a gaban Dauda. 22 Sa'an nan Dauda ya ce da Onan, "Ka sayar mani da wannan masussuka domin in gina wa Yahweh bagadi. Zan biya gaba ɗaya domin a cire annobar daga cikin jama'a." 23 Ornan ya ce da Dauda, "Ka ɗauke ta kamar taka ce, ya shugabana sarki. Ka yi abin da ka ga dama da ita. Duba, zan ba ka bijimaina domin hadaya ta ƙonawa, sandunan fyaɗi kuma ka yi makamashi da su, alkama kuma domin hadaya ta tsaba, zan ba ka su dukka." 24 Sarki Dauda yace da Ornan, "A'a gara dai in saya in biya. Ba zan ɗauki kayanka in yi hadaya ta ƙonawa ga Yahweh ba, ba tare da ya shafe ni da komi ba." 25 Sai Dauda ya sayi wurin a bakin zinariya awo ɗari shida. 26 Sai Dauda ya gina wa Yahweh bagadi a wurin, ya miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta. Ya yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa masa da wuta daga sama a kan baye-baye na ƙonawar. 27 Sa'an nan Yahweh ya umurci mala'ikan, mala'ikan kuma ya mayar da takobinsa cikin kubenta. 28 Da Dauda ya ga Yahweh ya amsa masa a masussukar Ornan Bayebushe, sai ya yi hadayar a wurin nan take. 29 A wannan lokaci wurin taruwa na Yahweh wanda Musa ya yi a cikin Jeji da bagadi domin baye-baye na ƙonawa suna can kan tudun Gibiyon. 30 Duk da haka, Dauda ba zai iya zuwa can domin ya nemi nufin Yahweh ba, saboda yana jin tsoron takobin mala'kan Yahweh.

Sura 22

1 Sai Dauda yace, "A nan gidan Yahweh Allah zai kasance, tare da bagadin ƙona baye-baye na Isra'ila." 2 Sai Dauda ya umurci bayinsa su tattaro baƙin da ke zaune a ƙasar Isra'ila. Ya sa su zama masu sassaƙo duwatsu, su sassaƙo tubulan duwatsu waɗanda za a gina gidan Yahweh da su. 3 Dauda kuma ya ba da ƙarafa masu tarin yawa domin a yi ƙusoshi saboda ƙofofi da ƙyamarensu da tagulla. Ya kuma ba da tagulla mai yawan da ba za a iya aunawa ba, 4 da itacen sida fiye da yadda za a iya ƙirgawa. (Sidoniyawa da mutanen Taya suka kawo wa Dauda gumaguman sida da yawa domin ya ƙidaya.) 5 Dauda ya ce ɗana Suleman yaro ne, bai ƙware ba tukuna, kuma gidan da za a gina wa Yahweh dole ne ya zama mai daraja sosai, domin ya zama da daraja ya yi suna a dukkan ƙasashe. Saboda haka zan yi shiri domin gininsa." Saboda haka, Dauda ya yi gagarimin shiri kafin mutuwarsa. 6 Sai ya kira Suleman ɗansa ya umurce shi ya gina gida saboda Yahweh, Allah na Isra'ila. 7 Dauda yace da Suleman, "Ɗana, na yi niyya ni da kaina in gina gida saboda sunan Yahweh, Allahna. 8 Amma Yahweh ya zo wuri na ya ce, 'Ka yi yaƙe-yaƙe da yawa ka zubar da jini. Ba za ka gina gida domin sunana ba, domin ka zubar da jini da yawa bisa ƙasa a idanuna. 9 Duk da haka, za ka sami ɗa wanda zai zama mutum mai salama. Zan ba shi hutawa daga dukkan maƙiyansa a kowanne sashi. Sunansa zai zama Suleman, kuma zan ba da salama da kwanciyar rai ga Isra'ila a kwanakinsa. 10 Shi ne zai gina mani gida, zai zama ɗa a gare ni, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan tabbatar da kursiyin mulkinsa bisa Isra'ila har abada.' 11 To yanzu, ɗana, Yahweh ya kasance tare da kai ya ba ka nasara. Za ka ginawa Yahweh Allahnka gida kamar yadda ya ce. 12 Bari Yahweh ya ba ka fahimi da hangen gaba, domin ka yi biyayya da dokar Yahweh Allahnka, sa'ad da ya ɗora ka bisa shugabancin Isra'ila. 13 Za ka yi nasara idan ka lura ka yi biyayya da farillai da dokokin da Yahweh ya ba Musa game da Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, kada ka karaya. 14 Yanzu ka duba, na yi baban ƙoƙari, na yi tanaji domin gidan Yahweh, zinariya awo 100,000, azurfa awo milyan ɗaya, da tagulla da ƙarafa masu tarin yawa. Na kuma tanaji katako da dutse. Na sani dole sai ka ƙara a kan su. 15 Kana da ma'aikata da yawa: masu sassaƙar dutse da magina da kafintoci da ƙwararru ga aikin hannu da yawa a kowanne fanni, 16 waɗanda za su iya yin aiki da zinariya da azurfa da tagulla da ƙarafa. Sai ka fara aiki, Yahweh ya kasance tare da kai." 17 Dauda kuma ya dokaci dukkan dattawan Isra'ila su taimaki ɗansa Suleman, da cewa, 18 "Yahweh Allahku yana tare da ku, kuma ya ba ku salama a kowanne sashi, ya ba da mazauna yankin cikin hannuna. An ladabtar da yankin a gaban Yahweh da mutanensa. 19 Sai ku nemi Yahweh Allah da dukkan zuciyarku da ranku. Sai ku tashi tsaye ku gina wuri mai tsarki na Yahweh Allah. Sa'an nan ne za ku iya kawo akwatin alƙawari na Yahweh tare da abubuwan da ke na Yahweh a cikin gidan da a ka gina domin sunan Yahweh."

Sura 23

1 Sa'ad da Dauda ya tsufa, yana kusa da ƙarshen rayuwarsa, sai ya naɗa ɗansa Suleman ya zama sarkin Isra'ila. 2 Ya tattara dukkan shugabannin Isra'ila, tare da firistoci da Lebiyawa. 3 Lebiyawa kuwa masu shekaru talatin da ma sama da haka, aka kidaya su, sun kai jimillar dubu talatin da takwas. 4 '"Dubu ashirin da huɗu daga cikin su za su yi hidimar gidan Yahweh, sai kuma dubu shida za su zama ma'aikata da alƙalai. 5 Dubu huɗu kuwa za su zama matsara ƙofofi da dubu huɗu kuma za su zama masu yabon Yahweh da kayayyakin bushe-bushe da kaɗe-kaɗe waɗanda za su yi yabo," Dauda ya ce. 6 Ya raba su kashi kashi bisa ga 'ya'yan Lebi: Geshon, da Kohat da Merari. 7 Daga zuriyar kabilar Geshon, akwai Ladan da Shimei. 8 Akwai 'ya'ya maza uku na Ladan: su ne Yehiyel shi ne shugaba da Zetam da Yowel. 9 Akwai 'ya'ya uku maza na Shimei, su ne Shelomit da Heziyel da Haran. Waɗannan su ne shugabannin kabilar Ladan. 10 Akwai 'ya'ya huɗu maza na Shimei, su ne Yahat, Ziza, Yewush da Beriya. 11 Yahat shi ne babba, Ziza shi ne na biyu, amma Yewush da Beriya ba su da 'ya'ya maza da yawa, saboda haka sai aka ɗauke su a matsayin kabila ɗaya tare da yin ayyuka iri ɗaya. 12 Akwai 'ya'ya maza huɗu na Kohat su ne Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. 13 Waɗannan 'ya'ya maza na Amram su ne Haruna da Musa. Haruna aka zaɓa aka kuma ƙeɓe shi domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, shi da kabilarsa su riƙa ƙona turare a gaban Yahweh, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada. 14 Amma Musa mutumin Allah, da 'ya'yansa maza aka ɗauke su a matsayin Lebiyawa. 15 'Ya'yan Musa maza kuwa su ne Geshon da Eliyeza. 16 A zuriyar Geshon Shebayel ne babban ɗansa. 17 Zuriyar Eliyeza Rehabiya ne ɗansa. Eliyeza ba shi da 'ya'ya maza, amma Rehabiya na da zuriya mai yawa. 18 Ɗan Izhar shi ne Shelomit na shugaba. 19 Zuriyar Hebron su ne Yeriya, babbansu, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da kuma Yekameyam na huɗu. 20 'Ya'yan Uzziyel maza kuwa su ne Mika ne babban da Ishija na biyu. 21 'Ya'yan Merari maza su ne Mali da Mushi. 'Ya'yan Mali maza su ne Eliyeza da Kish. 22 Eliyeza kuwa ya rasu ba shi da ko 'ya'ya maza. Yana da 'ya'ya mata ne kaɗai. 23 'Ya'ya maza na Kish ne suka aure su. 'Ya'yan Mushi uku maza su ne Mali, Eder da Yerimot. 24 Waɗannan su ne zuriyoyin Lebiyawa bisa ga dangoginsu. Su ne shugabannin, da aka lasafta aka jera su bisa ga sunaye, su ne dangogin da suka yi hidimar aiki a cikin gidan Yahweh, daga shekaru ashirin zuwa gaba. 25 Gama Dauda ya ce, '"Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ba da hutu ga sauran mutanensa. Ya mai da gidansa a Yerusalem har abada. 26 Lebiyawa ba sauran bukatar ɗauka rumfar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta." 27 Gama bisa ga maganar Dauda ta ƙarshe aka kiɗaya Lebiyawa, daga mai shekaru ashirin zuwa gaba. 28 Aikinsu kuwa shi ne su taimaki zuriyar Haruna gudanar da aiki cikin gidan Yahweh. Su kula da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan dukkan abubuwa da su ke na Yahweh, da sauran ayyuka a cikin gidan Allah. 29 Za su kuma ɗauki nauyin kula da wajen gurasar ajiyewa da lallausan gari na baiko na gari, da waina marar gami da soyayyun baye-baye, baye-bayen da ka gauraya da mai, da dukkan ma'aunan nauyi da girma abubuwa. 30 Suna kuma tsaye a kowacce safiya don su yi godiya da yabon Yahweh. Suna riƙa yin wannan da maraice 31 da duk lokacin baikon ƙonawa suna miƙa wa Yahweh, a ranakun Asabaci da lokacin tsayuwar sabon wata da bikin ƙayyadaddun idodi. Akwai adadin lambar da za a sa bisa ga ka'ida, kullum za su bayyana a gaban Yahweh. 32 Su ne za su riƙa lura da rumfar taruwa, da wuri mai tsarki, za su kuma taimaki abokansu, zuriyar Haruna hidima cikin gidan Yahweh.

Sura 24

1 Ga yadda aka raba aiki bisa ga zuriyar Haruna su ne: Nadab, Abihu, Eliyeza da kuma Itama. 2 Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa. Ba su da 'ya'ya, saboda haka Eliyeza da Itama suka shiga aikin firistoci. 3 Dauda, tare da Zadok, zuriyar Eliyeza da Ahimelek, da zuriyar Itama, sun karkasa su bisa ga ayyukansu na matsayin firistoci. 4 Akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Eliyeza fiye da zuriyar Itama, sai suka karkasa zuriyar Eliyeza zuwa kashi goma sha shida. Sun yi wannan bisa ga shugaban dangogi da kuma bisa ga zuriyar Itamar. Waɗannan rabe rabe guda takwas ne adadinsu, bisa ga dangoginsu. 5 Suka karkasa su ta hanyar ƙuri'a, domin akwai ma'aikatan wuri mai tsarki da kuma ma'aikata na Allah daga zuriyar Eliyeza da kuma zuriyar Itama. 6 Shemaiya ɗan Netanel marubuci, Balabe, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da ma'aikata, Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin firistoci da iyalan Lebiyawa. An sami dangi ɗaya ta wurin ƙuri'a daga zuriyar Eliyeza, an sake samun ɗaya daga zuriyar Itama. 7 ‌Ƙuri'a ta farko ta je ga Yehoyarib, ta biyu ga Yedayiya, 8 ta uku ga Harim, ta huɗu ga Seyorim, 9 ta biyar ga Malkija, ta shida ga Mijamin, 10 ta bakwai ga Hakkoz, ta takwas ga Abija, 11 Na tara Yeshuwa, ta goma ga Shekaniya, 12 ta goma sha ɗaya ga Eliyashib, ta goma sha biyu ga Yakim, 13 ta goma sha uku ga Huffa, ta goma sha huɗu ga Yeshebeyab, 14 Ta goma sha biyar ga Bilga, ta goma sha shida ga Immer, 15 Ta goma sha bakwai ga Hezir, ta goma sha takwas ga Haffizzez, 16 ta goma sha tara ga Fetahiya, ta ashirin ga Yehezkel, 17 ta ashirin da ɗaya ga Yakin, ta ashirin da biyu ga Gamul, 18 ta ashirin da uku ga Delaiya, da kuma ta ashirin da huɗu ga Ma'aziya. 19 Wannan shi ne tsarin aikinsu, idan sun zo hidima cikin gidan Yahweh, bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya ba su, kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila ya umarce shi. 20 Waɗannan su ne sauran Lebiyawa, 'ya'ya maza na wajen Amram, shi ne Shubawel; 'Ya'ya maza na Shubawel da Yedaiya. 21 'Ya'ya maza na Rehabiya shi ne Ishija shugaba. 22 Na wajen Izharawa: shi ne Shelomit; na wajen Shelomit: shi ne Yahat. 23 'Ya'ya maza na wajen Hebron Yeriya ne shugaba, Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da Yekameyam na huɗu. 24 'Ya'ya maza zuriyar Uzziyel ya haɗa da Mika. Zuriyar Mika ta haɗa da Shamir. 25 Ɗan'uwan Mika shi ne Ishija. 'Ya'ya maza ya haɗa da Zekariya. 26 'Ya'ya maza na Merari su ne Mali da Mushi. Ɗan Yaaziya shi ne Beno. 27 'Ya'ya maza na Merari su ne Yaaziya: Beno, Shoham, Zakkur da Ibri. 28 'Ya'ya maza na Mali su ne Eliyeza, wanda ba shi da 'ya'ya maza. 29 'Ya'ya maza na Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel. 30 'Ya'ya maza na Mushi su ne Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lebiyawa bisa ga iyalansu. 31 Waɗannan mutane su ne ke shugabatar kowanne gidan uba da kowane ɗan 'yan'uwansu, aka jefa ƙuri'a a gaban sarki Dauda da Zadok da kuma Ahimelek, tare da shugabanni na kowanne iyalan firistoci da Lebiyawa. Suka jefa ƙuri'a kamar yadda zuriyar Haruna suka yi.

Sura 25

1 Dauda da shugabannin Lebiyawa sun zaɓi waɗansu don aiki suna cikin 'ya'yan Asaf maza da na Heman da na Yedutun. Waɗannan mutane za su yi annabci da waɗannan kayayyakin bushe bushe irin su garayu da molaye da kuge. A nan ga adadin mutanen da suka yi wannan aikin: 2 Daga 'ya'yan Asaf maza, su ne Zakkur, Yosef, Netaniya da Asharela, Asaf mahaifinsu ne ya ke bi da su, shi ne kuma wanda ya ke waƙa a ƙarƙashin sarki. 3 Daga 'ya'yan Yedutun maza su ne Gedaliya, Zeri da Yeshayiya, Shimei, Hashabiya da Mattitiya, dukka su shida ne, mahaifinsu Yedutun ne ke kula da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya don godiya da yabon Yahweh. 4 Daga 'ya'yan Heman maza kuwa akwai Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot, Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da kuma Mahaziyot. 5 Dukkan waɗannan 'ya'ya maza ne na Heman annabin sarki. Allah ya ba Heman 'ya'ya maza goma sha huɗu da kuma 'ya'ya mata uku don ya girmama shi. 6 Dukkan waɗannan suna ƙarƙashin mahaifinsu. Su mawaƙan gidan Yahweh ne, tare da kaɗa kuge da molaye da garayu kamar yadda suke aiki cikin gidan Allah. Asaf da Yedutun da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki. 7 Su da 'yan'uwansu maza horarru ne sun kuma ƙware da mawaƙa ga Yahweh jimillarsu kuwa ita ce 288. 8 Suka jefa ƙuri'u don ayyukansu, dukka suna kama da juna, haka ma ya ke ga yaro da babba da malami da ɗalibi. 9 Yanzu game da 'ya'yan Asaf maza; ƙuri'a ta farko ta faɗa a kan iyalin Yosef; ta biyu ga iyalin Gedaliya, jimilla mutane goma sha biyu ne; 10 ta uku ta faɗa a kan Zakkur, da 'ya'yansa da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne, 11 ta hudu ta faɗa ga Izri, 'ya'yansa da danginsa jimilla mutane goma sha biyu ne; 12 ta biyar ta faɗa ga Netaniya, 'ya'yansa maza da danginsa jimilla mutane goma sha biyu ne; 13 ta shida ta faɗa ga Bukkiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 14 ta bakwai ta faɗa ga Yesarela, 'ya'yansa maza da danginsa jimilla mutane goma sha biyu na; 15 ta takwas ta faɗa ga Yeshayiya, 'ya'yansa dandinsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 16 ta tara ta faɗa ga Mattaniya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 17 ta goma ta fada ga Shimei, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 18 ta goma sha ɗaya ta faɗa ga Azarel, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 19 ta goma sha biyu ta faɗa ga Hashabiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 20 ta goma sha uku ta faɗa ga Shubayel, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 21 ta goma sha hudu ta faɗa ga Mattitiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 22 ta goma sha biyar ta faɗa ga Yerimot, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 23 ta goma sha shida ta faɗa ga Hananiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 24 ta goma sha bakwai ta faɗa ga Yoshbekasha, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 25 ta goma sha takwas ta faɗa ga Hanani, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 26 ta goma sha tara ta faɗa ga Malloti, 'ya'yansa da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 27 ta ashirin ta faɗa ga Eliyata, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 28 ta ashirin da ɗaya ta faɗa ga Hotir, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 29 ta ashirin da biyu ta faɗa ga Giddalti, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 30 ta ashirin da uku ta faɗa ga Mahaziyot, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne; 31 sai ta ashirin da huɗu ta faɗa ga Romamti-Ezer, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne.

Sura 26

1 A nan ga yadda aka raba masu tsaron ƙofofi: Daga Koratawa, Meshelemiah ɗan Kore ne, zuriyar Asaf. 2 Meshelemiya yana da 'ya'ya maza: Zekariya ne ɗan fari, Yediyayel ne na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu, 3 Elam na biyar, Yehohanan na shida, Eliyehoyenai ne ɗa na bakwai. 4 Obed Idom da 'ya'ya maza su ne, na fari shi ne Shemaiya, na biyu Yehozabad, na uku Yowa, na huɗu Sakar, na biyar Netanel, shida 5 Ammiyel, na bakwai Issaka, na takwas Fiyuletai, gama Allah ya sa wa Obed Idom albarka. 6 Shemaiya shi ne ɗan farin Obed Idom ya haifi 'ya'ya maza waɗanda suka yi shugabancin iyalansu; su jarumawan mutane ne. 7 'Ya'yan Shemaiya maza su ne Otni, Refayel, Obed, Elzabad. Danginsa Elihu da Shemakiya suma jaruman mutane ne. 8 Dukkan waɗannan kabilun Obed Idom. Su da 'ya'yansu maza da dangoginsu jarumai ne masu ƙarfi da gwaninta na yin hidima. Akwai mutane sittin da biyu da suke da dangantaka da Obed Idom. 9 Meshelemiya yana da 'ya'ya maza da 'yan'uwa, mutane ne masu ƙarfi da gwaninta, su dukka goma sha takwas ne. 10 Hosa, yana cikin zuriyar Merari, yana da 'ya'ya maza, Shimri shugaba (ko da ya ke ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka maihaifinsa ya maishe shugaba). 11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tabaliya na uku da Zekariya na huɗu. Dukkan 'ya'yan Hosa maza da 'yan'uwansa su goma sha uku ne. 12 Waɗannan su ne rabe rabe na masu tsaron ƙofa, bisa ga shugabanninsu, da ayyuka, kamar iyalansu, da za su yi hidima a gidan Yahweh. 13 Sai suka jefa kuri'a yaro da babba bisa ga iyalansu, don kowacce ƙofa. 14 Sai ƙuri'ar ƙofar gabas, ta faɗo a kan Shelemiya. Suka kuma jefa ƙuri'a don ɗansa Zekariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai ƙuri'arsa ta fito don ƙofar arewa. 15 An sa Obed Idom ƙofar kudu, an kuma sa 'ya'yansa maza lura da ɗakunan ajiya. 16 Shuffin da Hosa an sa su a ƙofa ta yamma tare da Shalleket, a kan hanyar da ta haura. Aka tabbatar da masu tsaron kowanne iyali. 17 A gefen gabas akwai Lebiyawa shida, a gefen arewa a rana ta huɗu, a gefen kudu a rana ta huɗu, an kuma sa biyu biyu a ɗakunan ajiya. 18 A ɗakin shari'a da ke yamma akwai masu tsaro huɗu, a hanya guda huɗu, biyu kuma a ɗakin shari'a. 19 Yadda aka raba masu tsaron ƙofofin kenan. Suna cike da zuriyoyin Kora da Merari. 20 A cikin Lebiyawa, Ahijah ne mai kula da ma'ajin gidan Allah, da ma'ajin abubuwa da ke na Yahweh. 21 Zuriyar Ladan, daga zuriyar Geshon ta wurinsa da waɗanda suke shugabannin iyalan Ladan Bageshone, su ne Yehiyeli, 22 da 'ya'yansa maza Zetam da Yowel ɗan'uwansa, su ne ke kula da ɗakunan ajiyar gidan Yahweh. 23 Akwai kuma masu tsaro da aka ɗauko daga kabilar Amram, da Izhar da Hebron da kuma Uzziyel. 24 Shubayel ɗan Geshom ɗan Musa, shi ne babban jami'in ɗakunan ajiya. 25 Danginsa daga kabilar Eliyeza su ne ɗansa Rehabiya, Yeshayiya ɗan Rehabiya, Yoram ɗan Yeshabiya, Zikri ɗan Yoram, da kuma Shelomit ɗan Zikri. 26 Shelomit da 'yan'uwansa ne ke lura da dukkan gidajen ajiya da abubuwan da ke na Yahweh, wanda Dauda sarki, da iyalin shugabanni, da shugabannin sojoji na dubu dubu na ɗari ɗari da kuma shugabannin sojojin da aka keɓe. 27 Su ne kuma aka keɓe don kula da ganimar yaƙe-yaƙe domin kuma gyaran gidan Yahweh. 28 Su ne kuma masu lura da kowane irin abubuwa da aka keɓe ga Yahweh ta wurin annabi Sama'ila, da Saul ɗan Kish da Abner ɗan Ner da Yowab ɗan Zeruyiya. Kowanne abu da aka keɓe ga Yahweh yana ƙarƙashin kulawar Shelomit da 'yan'uwansa. 29 Zuriyar Izhar da Kenaniya tare da 'ya'yansa maza su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ila. Su ne shugabanni da alƙalai. 30 Zuriyar Hebron da Hashabiya haɗe da 'yan'uwansa, 1700 gwanayen mutane ne, su ne masu lura da ayyukan Yahweh da na sarki. Suna wajen yammacin Yodan. 31 Daga zuriyar Hebron, Yeriya shi ne shugaban zuriyarsa, bisa ga asalin iyalansu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dauda sun bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a Yazer ta Giliyad. 32 Yeriya yana da 'yan'uwa har 2,700, waɗanda suke gwanaye shugabannin iyali. Dauda ya maida su masu lura da kabilar Ruben da ta Gad da kuma rabin kabilar Manasse, domin kowane abu da ke na Allah da kuma al'amuran sarki.

Sura 27

1 Wannan shi ne lissafin iyalin shugabannin Isra'ila, shugabannin sojoji na dubu dubu da ɗari ɗari, har da rudunar sojoji waɗanda suke yi wa sarki aiki ta hanyoyi dabam dabam. Kowace runduna za ta yi aiki wata wata har ƙarshen shekara. Kowanne kashi na da mutane dubu ashirin da huɗu. 2 A kowane kashi a wata na farko, shi ne na Yashobeyam ɗan Zabdiyel. A cikin kashinsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 3 Yana cikin zuriyar Pezer, shi ne kuma mai lura da dukkan shugabannin sojoji a watan farko. 4 Bisa ga kashi wata na biyu shi ne Dodai, daga kabilar zuriya daga Ahoya. Miklot shi ne na biyu a jerin. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 5 Shugaban ruduna a wata na uku shi ne Benaiya ɗan Yehoiada, firist ne kuma shugaba. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 6 Wannan shi ne Benaiya wanda shi ne shugaba a cikin talatin, da kuma bisa ga talatin. Ammizabad ɗansa mana cikin rabonsa. 7 Shugaban sojoji a wata na huɗu shi ne ɗan'uwan Asahel Yowab. Ɗansa Zebadiya ya zama shugaba a madadinsa. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 8 Shugaba na watan biyar shi ne Shamhut, a zuriyar Izra. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 9 Shugaba na watan shida shi ne Ira ɗansa Ikesh, daga Tekowa. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu. 10 Shugaba na watan bakwai shi ne Helez Bafelone, daga mutanen Ifraim. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 11 Shugaba na watan takwas shi ne Sibbekai Bahushate, daga kabilar zuriya daga Zera. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 12 Shugaba na watan tara shi ne Abiyeza Ba'anatot, daga kabilar Benyamin. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 13 Shugaba na watan goma shi ne Maharai daga birnin Netofa, daga dangin zuriya daga Zera. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 14 Shugaba na watan goma sha ɗaya shi ne Benaiya daga birnin Firaton, daga kabilar Ifraim. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 15 Shugaba na watan goma sha biyu shi ne Heldai daga birnin Netofa, daga dangin zuriya daga Otniyel. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne. 16 Waɗannan su ne shugabannin kabilun Isra'ila: Ga kabilar Ruben, Eliyeza ɗan Zikri shi ne shugaba. Ga kabilar Simiyonn, Shefatiya ɗan Ma'aka shi ne shugaba. 17 Ga kabilar Lebi, Hashabiya ɗan Kemuwel shi ne shugaba, Zadok shi ne jagora na zuriyar Haruna. 18 Ga kabilar Yahuda, Elihu, ɗaya daga cikin 'yan'uwan Dauda, shi ne shugaba. Ga kabilar Issaka, Omri ɗan Mika'el shi ne shugaba. 19 Ga kabilar Zebulun, Ishamaiya ɗan Obadiya shi ne shugaba. Ga kabilar Naftali, Yerimot ɗan Azriyel shi ne shugaba. 20 Ga kabilar Ifraim, Hosheya ɗan Azaziya shi ne shugaba. Ga rabin kabilar Manasse, Yowel ɗan Fedaiya shi ne shugaba. 21 Ga rabin kabilar Manasse a Gileyad, Iddo ɗan Zekariya shi ne shugaba. Ga kabilar Benyamin, Ya'asiyel ɗan Abner shi ne shugaba. 22 Ga kabilar Dan, Azarel ɗan Yeroham shi ne shugaba. Waɗannan su ne shugabannin kabìlun Isra'ila. 23 Dauda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu ba su kai ashirin ba ko kuma yara, gama Yahweh ya yi alƙawarin zai sa mutanen Isra'ila su yi yawa kamar taurarin sammai. 24 Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar mutanen nan, amma bai gama ba. Sai hukunci mai zafi ya sami Isra'ila saboda wannan. Wannan ƙidayar ba a rubuta ta ba cikin Tarihin Sarki Dauda ba. 25 Azmabet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ma'ajin sarki. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai kula da ɗakin ajiya a filaye da kuma cikin birane, har da ƙauyuka da kagaran hasumiyoyi. 26 Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da gonaki, da waɗanda suke huɗa a ƙasar. 27 Shimei Baramate shi ne mai kula da gonakin inabi da Zabdi Bashifime shi ne mai lura da itatuwan zaitun da inda ake ajiye kwalaben shaye-shaye. 28 Ga itatuwan zaitun da na ɓaure waɗanda suke a kwari shi ne Ba'al-Hanan daga Geder, kuma ɗakin ajiyar man shi ne Yowash. 29 Bisa ga garken shanu a Sharon shi ne Shitrai, daga Sharon kuma bisa ga garken shanu da ke cikin kwari shi ne Shafat ɗan Adlai. 30 Bisa ga rakuma shi ne Obil Ba'isma'ile, kuma bisa ga jakuna mata shi ne Yedaiya daga Meronot. Bisa ga tumaki shi ne Yaziz Bahagire. 31 Yazia Bahagire shi ne mai lura da garken. Dukkan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dauda. 32 Yonatan, kawun Dauda, shi ne mai ba da shawara, tun da shi mutum ne mai ganewa shi ne kuma magatakarda. Yehiyel ɗan Hakmoni shi ne mai kula da 'ya'yan sarki. 33 Ahitofel shi ne mai ba sarki shawara, Hushai daga mutanen Arkite su ne masu shawara na jikin sarki. 34 Ahitofel ɗan Benaiya an ba da makaminsa ga Yehoiada ɗan Benaiya ta wurin Abiyata. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.

Sura 28

1 Dauda ya tara dukkan shugabannin Isra'ila a Yerusalem: shugabannin kabilu da shugabannin kungiyoyi da ke yi wa sarki hidima a cikin shirin aikinsa, shugabannin dubu dubu da ɗari ɗari da manajoji bisa dukkan dukiya da mallakar sarki da 'ya'yansa da kuma fãdawa da mutane mayaƙa, tare da waɗanda suka zama mafiya fasaha. 2 Sai sarki Dauda ya mike tsaye ya ce, "Ku saurare ni, 'yan'uwana da jama'ata. Na yi niyya in gina haikalin akwatin alƙawari na Yahweh; wurin zaman zatin Allahnmu, na kuma riga na yi shirin ginin. 3 Amma Allah ya ce da ni, 'Ba za ka gina mani haikali da sunana ba, domin kai mutum ne mayaƙi, ka kuma zubar da jini.' 4 Duk da haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zaɓe ni daga dukkan iyalin mahaifina, in zama sarkin Isra'ila har abada. Shi ne ya zaɓi kabilar Yahuda da kuma gidan mahaifina, daga cikin dukkan 'ya'ya maza na mahaifina, shi ne ya zaɓe ni in zama sarkin Isra'ila. 5 Daga 'ya'ya maza da yawa Yahweh ya ba ni, ya zaɓe Suleman, ɗana, ya zauna a kan gãdon sarautar mulkin Yahweh, bisa Isra'ila. 6 Ya ce da ni, 'Suleman ɗanka ne zai gina mani gida da farfajiyoyina, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa zan zama uba a gare shi. 7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada, idan ya tsaya da gaske ya yi biyayya da dokokina da kuma ka'idodina.' 8 Saboda haka yanzu, a gaban dukkan Isra'ila, wannan taron Yahweh, da kuma gaban Allahnmu, dukkan ku dole ku kiyaye kuma yi ƙoƙari ku bi dukkan umarnan Yahweh Allahnku. Ku yi wannan don ku mallaki wannan ƙasar mai kyau, ku zauna a cikin ta a matsayin gãdo ga 'ya'yanku a bayanku har abada. 9 Amma kai, ɗana Suleman, ka yi biyayya da Allah na mahaifinka, ka bauta masa da dukkan zuciyarka da kuma yardar rai. Ka yi wannan gama Yahweh mai binciken dukkan zukata ne, ya kuma san kowanne irin nufi da tunanin kowanne mutum. Idan ka neme shi, zaka same shi, amma idan ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada. 10 Ka lura da cewa Yahweh ya zaɓe ka domin ka gina wannan rumfa mai tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama yi aiki." 11 Sa'an nan Dauda ya ba ɗansa Suleman tsarin ginshiƙan ƙofar haikalin, da gine-ginen haikali da ɗakunan ajiya da benaye da ɗakunan ciki da ɗakunan inda ake gafarta zunubi. 12 Ya ba shi tsarin da ya zãna domin farfajiyoyin gidan Yahweh, da dukkan kewayen ɗakunan, da ɗakunan ajiya na gidan Allah, da ma'ajiyai domin abubuwan da ke na Yahweh. 13 Ya kuma ba shi ƙa'idodin domin rarraba firistoci da Lebiyawa, da dukkan hidimar da za a yi a gidan Yahweh, domin kowanne aiki na cikin gidan Yahweh. 14 Ya fayyace nauyin santulan zinariya domin kowanne irin aiki, nauyin santulan azurfa domin kowanne irin aiki. 15 Nauyin zinariya domin dukkan kayayyakin zinariya, sun haɗa da kowanne alkuki da fitilunsa da fitilar zinariya, nauyin ma'aunin kowacce fitila da maɗori, nauyin ma'aunin kowacce azurfa domin kowanne maɗorin fitila, bisa ga yadda za'a yi amfani da kowanne maɗorin fitila a cikin sujada. 16 Ya ba da ma'aunin zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa don kowanne teburi, da kuma ma'aunin azurfa don teburorin azurfa. 17 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsu domin nama da daruna da kofuna da kwanoni da da ma'auni na yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita. 18 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita, da kuma zinariya da za a yi tsarin kerubobin da za su miƙa fikafikansu su rufe akwatin alƙawarin Yahweh. 19 Dauda ya ce, "Na sa dukkan wannan a rubuce ne kamar yadda Yahweh ya umarce ni, ya kuma ba ni don in fahimci fasalin aikin filla-filla." 20 Dauda ya ce da ɗansa Suleman, "Ka yi ƙarfi da jaruntaka. Ka yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka karai, gama Yahweh Allah, Allahna, na tare da kai. Ba zai bar ka ba ko ya ƙyale ka har sai ka gama dukkan aikin hidimar haikalin Yahweh. 21 Duba ga, karkasuwar firistoci da Lebiyawa na nan domin yin dukkan hidima a haikalin Allah. Za su kasance tare da kai, tare kuma da dukkan gwanayen mutanen da suka yarda su taimake ka a cikin aikin da yadda za a yi hidimar. Shugabanni da dukkan mutane na shirya su bi umarninka."

Sura 29

1 Sarki Dauda yace da dukkan taron, "Ɗana Suleman, wanda shi kaɗai Allah ya zaɓa, sai dai saurayi ne, kuma ba shi da ƙwarewa, kuma aikin babba ne. Gama haikalin ba na mutum ba ne, amma na Yahweh Allah ne. 2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda haikalin Allahna. Na ba da zinariya saboda abubuwa na zinariya, azurfa saboda abubuwa na azurfa, tagulla saboda abubuwa na tagulla, ƙarfe saboda abubuwa na ƙarfe, itace kuwa saboda na itace. Na kuma ba da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri-iri -da kowaɗanne irin duwatsu masu daraja - da duwatsu a yalwace. 3 Yanzu, saboda ƙaunar da na ke da ita ta gidan Allahna, shi ya sa na bada zinariyata da azurfata don wannan aiki. Ina ƙara yin wannan dukka don in shirya wannan haikali mai tsarki, 4 na bada zinariya tsantsa talanti dubu uku daga Ofir, azurfa tsantsa talanti dubu bakwai, domin yin ado a bangon ginin. 5 Na bada zinariya saboda abubuwa da abin da za ayi da zinariya, azurfa saboda abubuwan da za a yi na azurfa, da dukkan irin abubuwa da kafintoci za su yi. Wane ne kuma ya ke da niyyar bayarwa domin Yahweh yau, ya kuma ba da kansa gare shi? 6 Sai aka yi bayarwar yardar rai bisa ga shugabannin iyalan kakanni da shugabannin kabilun Isra'ila da shugabannin dubbai da ɗaruruwa da kuma shugabannin da suke yi wa sarki aiki. 7 Suka bada saboda hidimar gidan Allah talanti dubu biyar da darik dubu goma na zinariya, da talanti dubu goma na azurfa da dubu goma sha takwas na tagulla da kuma talanti 100,000 na ƙarfe. 8 Waɗanda suke da duwatsu masu daraja sun bada su cikin taskar gidan Yahweh, a ƙarƙashin kulawar Yehiyel, zuriyar Gashon. 9 Mutane suka yi murna domin waɗannan baye-baye na yardar rai, gama sun bayar da zuciya ɗaya ga Yahweh. Sarki Dauda kuma ya yi murna ƙwarai. 10 Dauda ya albarkaci Yahweh a gaban dukkan taron, ya ce, "Yabo naka ne, Yahweh, Allah na kakanmu Isra'ila, har abada abadin. 11 Naka ne, Yahweh, girma da iko da daraja da nasara da ɗaukaka. Gama dukkan abin da ke cikin sammai da duniya naka ne. Naka ne mulki, Yahweh, kai ne maɗaukaki mai mulki a bisa komai. 12 Dukkan wadata da ɗaukaka suna zuwa daga gare ka, kai ka ke mulki bisa dukkan mutane. A hannunka iko da ƙarfi su ke. Kai ne ka ke da ƙarfi da iko ka sa mutane su yi girma, ka kuma bada ƙarfi ga kowane mutum. 13 Yanzu, ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja. 14 Amma wãne ni, ko kuma mutanena da za mu iya kawo waɗannan abubuwa da yardar rai? Gama dukkan abubuwan nan sun zo daga gare ka ne, mu kuma muka ba ka abin da ke naka. 15 Gama mu bãƙi ne, matafiya kuma a gabanka, kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba mu da begen dauwama a duniya. 16 Yahweh Allahnmu, dukkan wannan dukiya da muka tattara domin mu gina haikali saboda ɗaukakar sunanka mai tsarki - sun zo daga gare ka ne kuma naka ne. Na kuma sani, ya Allahna, ka kan gwada zuciya, kana jin daɗin abin da ke nagari. 17 Amma ni, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukkan waɗannan abubuwa, yanzu ina dubawa da murna ganin mutanenka waɗanda suke nan da yardar su suka kawo maka kyautai. 18 Yahweh, Allah na Ibrahim da Ishaku da Isra'ila-kakanninmu - ka ajiye wannan har abada a cikin tunanin zukatan mutanenka. Ka bi da zukatansu zuwa gare ka. 19 Ka ba ɗana Suleman cikakkiyar zuciyar sha'awar kiyaye umarnanka da alƙawarin ka'idodi da dokokinka, domin ya aikata dukka waɗannan shirye-shirye na gina haikali wanda na riga na yi tanaji dominsa." 20 Dauda ya ce da dukkan taron, "Yanzu sai ku albarkaci Yahweh, Allahnku." Dukkan taron kuwa suka albarkaci Yahweh, Allah na kakaninsu, suka rusuna da kawunsu suka yi sujada ga Yahweh suka kuma sunkuyar da kansu a gaban sarki. 21 Washegari, sai suka miƙa wa Yahweh hadayu da hadayun ƙonawa gare shi. Sun miƙa bijimai dubu ɗaya, da raguna dubu ɗaya da kuma 'ya'yan tumakai dubu ɗaya, tare da hadayunsu na sha da hadayu masu yawan gaske domin dukkan Isra'ila. 22 A wannan rana, sun ci, sun sha a gaban Yahweh tare da bayyana murna da yabo. Sai suka sake naɗa Suleman ɗan Dauda, sarki a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa tare da ikon Yahweh ya zama mai mulki. Suka kuma keɓe Zadok don ya zama firist. 23 Sai Suleman ya zauna a kan gadon sarauta na Yahweh maimakon Dauda mahaifinsa. Ya yi wadata, kuma dukkan Isra'ila suka yi biyayya da shi. 24 Dukkan shugabanni da sojoji da 'ya'yan sarki suka yi alƙawari za su yi wa sarki Suleman biyayya. 25 Yahweh kuwa ya ɗaukaka Suleman ƙwarai da gaske a gaban dukkan Isra'ila, ya ba shi babban iko fiye da wani sarki kafin shi a Isra'ila. 26 Dauda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukkan Isra'ila. 27 Dauda ya yi mulki a Isra'ila har shekaru arba'in. Ya yi mulki a Hebron shekaru bakwai, sa'an nan ya yi mulki shekaru talatin da uku a Yerusalem. 28 Ya rasu da kyakkyawan tsufa, bayan ya ji daɗin rayuwa mai tsawo, da arziki da daraja. Suleman ɗansa ya gaje shi. 29 Abubuwan da sarki Dauda ya yi suna rubuce a cikin tarihin annabi Sama'ila, da annabi Natan da annabi Gad. 30 Abubuwan da ke rubuce su ne ayyukansa da mulkinsa, abubuwan da ya kammala da kuma waɗanda suka shafe shi da Isra'ila da dukkan mulkokin sauran ƙasashe.

Littafin Tarihi Na Biyu
Littafin Tarihi Na Biyu
Sura 1

1 Aka ƙarfafa Suleman ɗan Dauda a cikin mulkinsa, Yahweh Allahnsa na tare da shi ya kuma sa shi ya zama da iko sosai. 2 Suleman ya yi magana da dukkan Isra'ila, hafsoshi dubu-dubu dana ɗari-ɗari, da mahukunta da dukkan sarakuna a Isra'ila, da shugabannin gidajen ubanni. 3 Suleman da dukkan taro suka tafi babban tudu a Gibiyon, domin a can ne rumfar taruwa ta Allah take, wadda Musa bawan Yahweh ya yi a cikin jeji. 4 Amma Dauda ya kawo akwatin alƙawari na Allah daga Kiriyat Yerim zuwa wurin da ya keɓe dominsa. Domin ya kafa mata rumfa a Yerusalem, 5 Bugu da ƙari bagadin jan ƙarfen da Bezalel ɗan Uri ya yi yana wurin a gaban rumfar taruwa ta Yahweh; Suleman da dukkan taron suka tafi wurinta. 6 Suleman ya tafi can wurin bagadi na tagulla a gaban Yahweh, wadda take a rumfar taruwa, ya miƙa baye-bayen ƙonawa guda dubu a kansa. 7 Allah ya bayyana ga Suleman a wannan dare ya cemasa, "ka tambaya! Me zan baka?" 8 Suleman ya ceda Allah, '"Ka nuna babban amintaccen alƙawari ga Dauda mahaifina, kuma ka maida ni sarkin mutanensa a madadin sa. 9 Yanzu, Yahweh Allah, sai ka cika alƙawarin da kayi wa mahaifina Dauda, domin ka maida ni sarki kan mutane masu ɗumbin yawa kamar ƙasa. 10 Yanzu sai ka bani hikima da ilimi domin in iya jagorancin mutanen nan, domin wane ne zai iya yiwa mutanenka hukunci, su da keda yawa sosai?" 11 Allah ya ceda Suleman, "Saboda wannan ne yake zuciyarka, kuma domin baka roƙi wadata ba, ko kuɗi, ko girma, ko kuma ran waɗanda ke ƙinka, ko kuma tsawon ranka ba, amma ka roƙi hikima da ilimi domin kanka, domin ka iya mulkin mutanena, waɗanda na maishe ka sarki a kansu, to wannan shi ne abin da zan yi. 12 Yanzu zan baka hikima da ilimi. Hakannan zan baka arziki da wadata da girma, da ba a taɓa samun sarki kamarka a baya ba, ba kuma za a samu a bayan ka ba." 13 To sai Suleman ya komo Yerusalem wuri mai tudu da kea Gibiyon, daga wurin rumfar taruwa; ya yi sarauta akan Isra'ila. 14 Suleman ya tattara karusai da mahayan dawakai, yana da karusai 1,400 da mahayan dawakai dubu goma sha biyu waɗanda yasa a biranen karusai da kuma tare da shi sarki, a Yerusalem. 15 Sarki ya samar da zinariya da azurfa birjik kamar duwatsu a Yerusalem, ya kuma samar da itacen sida sosai kamar itacen ɓaure da ke cikin kwaruruka. 16 Game da sayo dawakai daga Masar da Kuye domin Suleman, fatakensa ne suka sayo su daga Kuye cikin rahusa. 17 Suka sayo karusa daga Masar a awo ɗari shida na zinariya, da kuma doki akan shekel 150. Suka kuma sayar da wasu ga sarakunan Hitiyawa da Aremiyawa.

Sura 2

1 Suleman kuma ya bada umarni domin ginin gida saboda sunan Yahweh da kuma gina fãda domin masarautarsa. 2 Suleman yasa mutune dubu saba'in su kwaso kayayyaki, mutane dubu tamanin masu saran duwatsu a cikin tsaunuka, da kuma mutane dubu 3,600 su dinga kula da su. 3 Suleman ya aika da saƙo zuwa sarki Hiram na Taya cewa "Kamar yadda ka yi ga mahaifina Dauda, kana aiko masa da itacen sida domin ya gina gidan da zai zauna, to sai kayi mani haka. 4 Duba ina gab da gina gida saboda sunan Yahweh Allahna, in keɓe shi dominsa, in ƙona turare mai ƙamshi a gabansa, in kuma kawo gurasa ta kasancewarsa da kuma hadaya ta ƙonawa safe da yamma, da ranakun asabarci da sabobbin watanni, da kuma ayyanannun bukukuwa domin Yahweh Allahnmu. Wannan na har abada ne, domin Isra'ila. 5 Gidan da zan gina zai zama da girma sosai, domin Allahnmu mai girma ne fiye da dukkan wasu alloli. 6 Amma wane ne zai iya gina gida domin Allah, da yake duniya da dukkan sammai da kansu basu ishe shi ba? Wane ni da zan gina masa gida, ba sai dai kawai in ƙona masa hadaya ba? 7 To sai ka aiko mani da mutum da ya ƙware a aikin zinariya, azurfa, tagulla, jan ƙarfe, da shunayya, da ja, da shuɗin u'lu, mutum wanda ya iya dukkan ingantattatu sassaƙa. Zai kasance tare da ƙwararrun mutane waɗanda ke tare da ni a Yahuda da Yerusalem, wanda Dauda mahaifina ya yi tanadi. 8 Ka aiko mani da itacen sida dana sifires da algun daga Lebanon. Duba barorina zasu tafi tare da barorinka, 9 domin a samar da katakai sosai, domin gidan da nake shirin ginawa zai zama babba da kuma ban mamaki. 10 Duba zan ba barorinka mutanen da zasu saro katakan, da kuma awo dubu ashirin na niƙaƙƙiyar alkama, da awo dubu ashirin na sha'ir, da salkunan ruwan inabi dubu ashirin, da kuma santulan mai guda dubu ashirin." 11 Sai Hiram, sarkin Taya ya amsa a rubuce ya aika wa Suleman: "Saboda Yahweh yana ƙaunar mutanensa, sai ya naɗa ka sarki a kansu." 12 Bugu da ƙari Hiram yace, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda ya hallici sama da duniya, wanda ya ba sarki Dauda ɗa mai hikima, da baiwa da kirki da fahimi, wanda zai gina gida domin Yahweh, da kuma fãda domin kansa. 13 Yanzu na aiko da mutum mai fasaha, da baiwa da fahimi, shi ne Huram-Abi. 14 Shi ɗan wata mata ne a cikin 'ya'yan Dan. Mahaifinsa ya zo ne daga Taya. Shi ƙwararre ne a aikin zinariya da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da duwatsu, da katakai, da shunayya, da shuɗi, da jan ulu, da lilin mai kyau. Hakannan kuma ƙwararre ne a fannin kowacce irin sassaƙa da zãne. Sai a samar masa wuri a cikin mutanenka ƙwararru da keyi maka aiki, da kuma na shugabana, Dauda, mahaifinka. 15 Yanzu kuma da alkama da riɗi, da maida ruwan inabi, wanda shugabana ya yi magana, sai ya aiko da waɗannan abubuwan ga bayinsa. 16 Zamu saro katako daga Lebanon, gwargwadon yawan katakon da kake bukata. Zamu kawo maka har zuwa tekun Yoffa, sai ka ɗauke su zuwa Yerusalem." 17 Suleman ya ƙirga dukkan baƙi da kea ƙasar Isra'ila, ya bi irin fasahar da Dauda mahaifinsa ya mora, ya ƙirga su aka sami mutum 153,600. 18 Yasa dubu saba'in daga cikinsu su suke ɗaukar kaya, dubu tamanin kuma masu saro katako a kan duwatsu, sai 3,600 su zama masu duba aikin da kuma sa mutanen suyi aikin

Sura 3

1 Sai Suleman ya fara gina gidan Yahweh a Yerusalem akan Tsaunin Moriya, inda Yahweh ya bayyana ga Dauda mahaifinsa. Ya shirya wurin da Dauda ya tsara dominsa, a masussukar Ornan na Yebusiya. 2 Ya fara ginin a rana ta biyu ta watan, a shekara ta huɗu ta mulkinsa. 3 Wannan shi ne fasalin ginshiƙin da Suleman ya kafa domin gidan Allah. ya yi amfani da tsohon salon awo, tsawonsa kamu sittin ne, sai faɗinsa kamu ashirin ne. 4 Awon harabar daga gaban gidan ya kai kamu ashirin, dai-dai da faɗin ginin. Tsayinsa kuma kamu ashirin ne, Suleman kuma ya dalaye cikin ginin da tsantsar zinariya. 5 ya yi wa rufin ainihin cikin harabar ado da sifires, waɗanda ya dalaye da zinariya mai kyau, waɗanda ya sassaƙa da itatuwan dabino da sarƙoƙi. 6 ya yi wa gidan ado da duwatsu masu daraja; zinariyar an samo ta ne daga Farbayim. 7 Hakannan ya yi daɓen ƙasa da bango, da ƙofofin da zinariya; da sassaƙaƙƙun kerubim a jikin bangayensa. 8 Ya gina wuri mafi tsarki. Tsawonsa ya kai awo ashirin dai-dai da faɗin ginin, haka kuma faɗin gidan shi ma kamu ashirin ne. Ya shafe shi da tsantsar zinariya dai-dai da yawan talanti dubu ɗari shida. 9 Nauyin awon ƙusa ya kai awo hamsin na zinariya. Ya shafe shi har sama da zinariya. 10 Ya yi siffofin kerubim guda biyu domin wuri mafi tsarki; masu aikin sassaƙa suka dalaye su da zinariya. 11 Faɗin fuka-fukan kerubobin kamu ashirin ne tsawonsu gaba ɗaya; Fuffuken kerub ɗin ya kai awo biyar a tsawo, wanda ya kai har bangon ɗakin; shi ma ɗaya fuffuken kamu biyar ne, yana taɓa fuffuken ɗaya kerub ɗin na farko. 12 Fuffuken ɗaya kerub ɗin ma kamu biyar ne, ya kai har bangon ɗakin; ɗayan fuffuken ma kamu biyar ne, yana taɓa fuffuken kerub na farko. 13 Fuka-fukan waɗannan kerubobin sun kai faɗin awo ashirin. Kerubobin suka tsaya kan ƙafafunsu, fuskokinsu na fuskantar babban ɗakin taron. 14 Ya mayar da labulen shuɗi, da shunayya, da jan ulu, ya sassaƙa zãnen kerubobi a kansa. 15 Hakannan Suleman ya kafa ginshiƙai guda biyu kowanne tsawonsa ya kai kamu talatin da biyar a tsawo, domin a gaban, abubuwan da kekansu sun kai kamu biyar na tsawo. 16 Ya yi sarƙoƙi domin ginshiƙan ya kuma dora su a kansu; hakannan yasa turaren ƙanshi ya haɗa su a jikin sarƙar. 17 Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya daga hannun hagu, ɗaya kuma daga hannun dama, yasa wa ginshiƙan hannun dama suna Yakin, na hannun hagun kuma Bo'aza.

Sura 4

1 Hakanan ya yi bagadi na tagulla; tsawonsa kamu hamsin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin ne, tsawonsa kuma goma ne. 2 Hakannan ya yi wani kewayayyen tafki na ƙarfe, kamu goma daga baki zuwa baki. Tsawonsa kamu biyar ne, tafkin kuma a kewaye kamu talatin ne. 3 A ƙarƙashin bakin tafkin akwai bijimai kewaye, kowanne awo goma, aka yi zuɓin ɗaya tare da tafkin sa'ad da aka yi zuɓin tafkin kansa. 4 Babban madatsar da ake kira "Tafkin" aka ɗora shi bisa bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku yamma, uku kudu, uku kuma gabas. Aka ɗora "Tafkin" a bisansu kuma gadon bayansu na fuskantar ciki. 5 "Bangajin" ya yi kaurin damtsen hannu, kuma aka goge bakinsa kamar bakin kofi, kamar buɗewar fure. "Tafkin" yana ɗaukar kimanin garwa dubu uku ta ruwa. 6 Hakannan ya yi tafkuna goma domin wankin abubuwa; yasa biyar daga ɓangaren kudu, biyar kuma daga arewa; za a dinga wanke kayayyakin miƙa baiko na ƙonawa a cikinsu. Babban madatsar da aka fi sani da "Tafki" firistoci ne suke amfani da ita domin wanke-wanke. 7 ya yi sandunan zinariya na ajiye fitilu guda goma kuma an tsara su ne kamar yadda aka umarta; ya ajiye su a cikin haikali, biyar a hannun dama biyar a hannun hagu. 8 ya yi tebura goma yasa su a cikin haikalin, biyar a bangon dama, biyar a bangon hagu. Ya yi kwanonin na zinariya guda ɗari. 9 Bugu da ƙari ya yi harabar firistoci, da babbar haraba da kuma ƙofofi domin harabar ya kuma dalaye ƙofofinsu da tagulla. 10 Ya ajiye madatsar da aka sani da "Tafki" a gefen gabas na haikalin, daga gabas kuma na haikalin, yana fuskantar kudu. 11 Huram ya yi tukwanen, cebura na ƙarfe da kwanoni na yayyafa ruwa. Da haka Huram ya kammala aikin da ya yi wa Suleman a cikin gidan Allah: 12 ginshiƙai guda biyu, gammunan biyu masu fasalin kwano da kebisa ginshiƙin biyu, tsare-tsaren aikin ado biyu da aka yi domin rufe gammunan biyu masu fasalin kwano waɗanda ke bisa ginshiƙan. 13 Ya kuma yi siffofin ruman guda ɗari huɗu domin suturta waɗannan kayayyakin: ya kawo dozin biyu na kayan kyalli domin a adana bangazan da kekan ginshiƙan. 14 Hakannan ya yi matokarai domin kawo tafkunan su zauna a matokaran; 15 tafki ɗaya bijimai sha biyu a ƙarƙashinsa, 16 Hakannan da tukwanen, da ceburan, cokulan nama masu yatsu, da dukkan sauran kayayyaki da Huram-Abi ya ƙera daga gogaggiyar tagulla domin Sarki Suleman, domin gidan Yahweh. 17 Sarki ya ajiye su a filin Yodon filin yumɓu tsakanin Sukkot da Zaretan. 18 Da haka Suleman ya yi dukkan waɗannan kayyayaki cikin babbar yalwa. Hakika ba a san nauyin tagullar da aka yi aiki da ita ba. 19 Suleman ya yi dukkan kayan ƙawa da kecikin haikalin Allah da kuma bagadi na zinariya, da kuma teburi inda ake ajiye gurasa; 20 Sandunan ajiye fitilu da fitilun da aka yi domin ƙona hadaya a gaban ɗakin ƙurya - waɗannan anyi su da tsantsar zinariya ne; 21 Hakannan furannin, da fitilun bangazan, da cokulan da abin ƙona turare duk da zinariya tsantsa, aka yi su. 22 Haka kuma abin gyara fitilu, da cokula, da bangazai da abin ƙona turare duk da tsantsar zinariya aka yi su. Game kuma da ƙofar gidan, da ƙofofinsu na ciki zuwa wuri mafi tsarki da kuma ƙofofin gidan, dake, na haikalin, duk da zinariya aka yi su.

Sura 5

1 Bayan Suleman ya kammala waɗannan ayyukan domin gidan Yahweh, Suleman ya kawo kayayyakin da Dauda mahaifinsa ya keɓe saboda wannan dalilin, haɗe da zinariya da azurfa, da dukkan kayayyakin ado - ya ajiye su a ma'ajin gidan Allah. 2 Daga nan Suleman ya tattaro dukkan dattawan Isra'ila, da dukkan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalai na mutanen Isra'ila, a Yerusalem domin su kawo akwatin alƙawari na Yahweh daga birnin Dauda, wato Sihiyona. 3 Dukkan mutanen Isra'ila suka tattaru a gaban sarki a wurin bikin, wanda aka yi a wata na bakwai. 4 Dukkan dattawan Isra'ila suka zo, Lebiyawa kuma suka ɗauko akwatin alƙawari. 5 Suka kawo akwatin, da rumfar taruwa, da dukkan kayayyakin da kecikin rumfar. Sai firistoci waɗanda ke daga kabilar Lebiyawa suka kawo waɗannan abubuwa 6 Sarki Suleman da dukkan taron mutanen Isra'ila suka taru a gaban akwatIn, suka yi hadaya da shanu har da ba za'a iya ƙirgawa ba. 7 Sai firistoci suka kawo akwatin alƙawari na Yahweh a wurinsa, a can ɗaki na ƙurya na gidan, zuwa wuri mafi tsarki, a ƙarƙashin fuka-fukan kerubim. 8 Domin kerubim sun buɗe fuka-fukansu a kan wurin akwatin sun kuma rufe akwatin da kuma sanduna da aka ɗauko shi da su. 9 Sandunan suna da tsawo sosai ana ganin ƙarshensu daga wuri mai tsarki a gaban ɗaki na can ciki, amma ba za a iya ganinsu daga waje ba. Suna nan a wurin har ya zuwa yau. 10 Ba komai a cikin akwatin sai allunan guda biyu da Musa ya saka a Tsaunin Horeb, a lokacin da Yahweh ya ƙulla alƙawari da Isra'ila, bayan sun fito daga Masar. 11 Sai ya zamana bayan firistoci sun fito daga wuri mai tsarki. Dukkan firistocin da kewurin suka tsarkake kansu ga Yahweh, basu bi tsarinsu na rabe-rabensu ba. 12 Hakannan Lebiyawa da kemawaƙa, dukkansu har da Asaf da Heman da Yedutun da 'ya'yansu da 'yan'uwansu suka yi ado da kaya masu kyau suna kaɗa molo da garayu, da goge, sarewa, suna tsaye a gabas da bagadin. Tare da su akwai firistoci 120 suna hura kakakai. 13 Sai ya zamana da masu hura kakakin da mawaƙan suna waƙa tare, suna fitar da murya ɗaya domin yabo da godiya ga Yahweh. Sun tada muryoyinsu da kakakinsu da molonsu da kayan kaɗe-kaɗensu, suka kuma yabi Yahweh. Suka rera waƙa cewa, "Domin shi managarci ne domin alƙawarinsa mai aminci ya tabbata har abada." Daga nan sai gidan, wato gidan Yahweh, ya cika da girgije. 14 Firistoci basu iya tsayawa suyi hidima ba saboda girgijen, domin daukakar Yahweh ta cika gidan.

Sura 6

1 Daga nan sai Suleman ya ce"Yahweh ya cezai zauna a cikin duhu baƙi ƙirin, 2 amma na gina maka wurin zama mai dacewa, wurin da zaka zauna har abada." 3 Bayan wannan sai sarki ya juya ya albarkaci dukkan taron mutanen Isra'ila a lokacin da taron Isra'ila ke tsaye. 4 ya ce dãma a yabi Yahweh na Isra'ila, wanda ya yi magana da mahaifina Dauda, ya kuma cika shi da hannunsa, cewa, 5 'Tun daga ranar dana fito da mutanena daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani wuri a cikin dukkan kabilun Isra'ila domin in gina gida saboda sunana a can ba. Ban kuma zaɓi wani mutum ya zama sarkin mutanena Isra'ila ba. 6 Duk da haka na zaɓi Yerusalem, domin sunana ya kasance a can, na kuma zaɓi Dauda ya zama sarkin mutanena Isra'ila,' 7 To a cikin zuciyar mahaifina Dauda ya ƙudurta ya gina gida domin Yahweh Allah na Isra'ila. 8 Amma Yahweh ya cewa Dauda mahaifina in har ka ƙudurta ka gina gida domina ka kyauta daka sa wannan a zuciyarka. 9 Duk da haka ba kaine zaka gina gidan ba; amma ɗanka ne, wanda zai fito daga tsatsonka, shi ne zai gina gida domin sunana.' 10 Yahweh ya cika maganar da ya faɗa, domin ina tsayawa a maimakon Dauda mahaifina, na kuma zauna a kan gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya alƙawarta. Na kuma gina gida domin sunan Yahweh, Allah na Isra'ila. 11 Na ajiye akwatin alƙawari a can, wanda shi ne alƙawarin Yahweh, wanda ya yi da mutanen Isra'ila." 12 Suleman ya tsaya a gaban bagadi na Yahweh a gaban dukkan taron Isra'ilawa ya buɗe hannuwansa. 13 Domin ya yi dakali na tagulla, tsawo kamu biyar, fãɗi kamu biyar, bisansa kamu biyar. Ya ajiye shi a tsakiyar harabar haikalin. Ya tsaya a kansa ya kuma durƙusa a gaban dukkan taron Isra'ila, daga nan sai ya buɗe hannuwansa zuwa sammai. 14 Yace, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a ƙasa, wanda ke cika alƙawari da madawwamiyar ƙauna ga bayinka da suka yi tafiya a gabanka da dukkan zuciyarsu; 15 kai wanda ka riƙe alƙawari da bawanka Dauda mahaifina, abin daka alƙawarta masa. I, kayi magana da bakinka ka kuma cikata da kanka kamar yadda ya ke a yau. 16 Yanzu Yahweh, Allah na Isra'ila, sai ka cika abin daka alƙawarta wa bawanka Dauda mahaifina, lokacin da kace 'Baza ka taɓa rasa wani mutun a gabana da zai zauna a kan gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka suka lura suyi tafiya bisa shari'ata, kamar yadda kayi tafiya a gabana.' 17 Yanzu, Yahweh, Allah na Isra'ila, ina roƙonka cewa ka tabbatar da alƙawarin da kayi wa bawanka Dauda. 18 Amma ko Allah zai yi rayuwa da mutum a duniya? duba, duniya ma kanta da sama basu isheka ba, balle kuma wannan haikalin dana gina! 19 Amma duk da haka ina roƙo ka girmama wannan addu'a ta bawanka, da kuma roƙonsa Yahweh Allahna; ka ji addu'a da kuma kukan da bawanka ke yi a gabanka. 20 Dama idanunka da kunnuwanka su kasance a buɗe rana da dare ga wannan haikalin. Wurin da kayi alƙawarin sa sunanka. Dama ka saurari addu'ar bayinka da zasu yi a wannan wurin. 21 To sai ka saurari roƙe-roƙen bawanka da mutanenka Isra'ila a lokacin da suka yi addu'a suna fuskantar wannan wuri. I, ka saurara daga wurin da kake zaune, daga sammai kuma bayan ka saurara, ka yi gafara. 22 In mutun ya yi laifi gãba da ɗan'uwansa in an bukace shi da ya rantse a gaban bagadinka a wannan gida, 23 to sai kaji daga sammai ka kuma hukunta bayinka, kayi wa mugu sakaiya, ka kuma ɗora masa hakinsa a kansa. Ka kuma shaida mai adalci mara laifi, ka bashi ladar aikinsa na adalci. 24 A lokacin da aka ci nasara kan mutanenka Isra'ila ta hannun maƙiya saboda sunyi maka zunubi, in sun juyo wurinka, suka kuma furta sunanka, suka yi addu'a, suka roƙi gafara a gabanka a wannan wuri- 25 to ina roƙo kaji daga sammai ka gafarta zunubin mutanenka Isra'ila; ka komo da su ƙasar daka basu, su da kakaninsu. 26 Idan sammai suka rufe kuma aka sami fãri saboda mutane sun yi maka zunubi - in sun yi addu'a suna fuskantar wannan wuri, suka furta sunanka, suka kuma juyo daga zunubinsu bayan ka hore su - 27 to sai kaji su a sama ka gafarta zunubin bayinka da mutanenka Isra'ila, lokacin daka bi da su ta hanya mai kyau da zasu bi. Ka aiko da ruwan sama a kan ƙasarka, wadda ka ba mutanenka gãdo. 28 Ko kuma ace ana yunwa a ƙasar, ko kuma akwai cuta, ko annoba, ko darɓa, ko funfuna; ko kuma ace a kwai magafta da suka kawo hari a ƙofofin birnin ƙasar, ko kuma wata masifa ta afko wa ƙasar ko rashin lafiya_ 29 ko kuma ace an yi adduo'i da roƙe-roƙe ta wurin mutum ɗaya ko kuma dukkan mutanenka Isra'ila-ko kuma na sane da annobar da kuma baƙincikin a zuciyarsa lokacin da ya buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali. 30 sai ka saurara daga sama, a wurin da kake zama; ka gafarta ka kuma sãka wa kowanne mutum gwargwadon aikinsa; ka san zuciyarsa, domin kai kaɗai ne kasan zukatan mutane. 31 Kayi wannan domin su ji tsoronka, domin suyi tafiya bisa tafarkunka a cikin dukkan kwanakin da suke a wannan ƙasa daka ba kakaninsu. 32 Game kuma da băƙi da ba mutanenka Isra'ila ba, amma saboda girman sunanka, da hannunka mai iko, da kuma damtsenka daka miƙa - suka zo suka yi addu'a suna fuskantar wannan wuri, 33 to ina roƙo ka saurara daga sama, wurin da kake zama, ka kuma yi duk abin da băƙin suka roƙe ka, domin dukkan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar mutanenka Isra'ila, domin kuma su san wannan gidan dana gina ana kiransa da sunanka. 34 Ko kuma in mutanenka suka tafi yaƙi gãba da maƙiyansu, ta kowacce hanya da zaka aike su, sai kuma suka yi addu'a gare ka suna fuskantar wannan birni daka zaɓa, suna kuma fuskantar wannan wuri dana gina domin sunanka. 35 To sai ka saurari addu'arsu da roƙonsu ka taimake su daga sammai. 36 Ko kuma in sunyi maka zunubi_ tunda ya ke ba wanda baya yin zunub i- ko kuma in kayi fushi da su ka kuma miƙa su ga maƙiya, domin maƙiya su kwashe su su kaisu bauta a ƙasarsu, ko kusa ko nesa. 37 Daga nan a misali in sun gane cewa suna ƙasar bauta, kuma a misali in sun tuba suka kuma nemi tagomashi daga wurinka a ƙasar da suke bauta. A misali kuma idan suka ce, 'Mun yi wauta mun yi zunubi. Mun yi halin mugunta.' 38 A misali idan suka juyo gare ka da dukkan zuciyarsu da ransu a ƙasar da suke bauta, inda suka ɗauke su a matsayin bautar talala, a misali kuma in sun yi addu'a suna fuskantar ƙasarsu, wadda ka ba kakaninsu, da kuma birni daka zaɓa, da kuma gidan da na gina domin sunanka. 39 Daga nan sai kaji addu'oinsu da roƙe-roƙensu ka kuma taimake su, daga sammai a wurin da kake zama ka taimaki al'amarinsu. Ka gafarta wa mutanenka, da suka yi maka zunubi. 40 Yanzu, Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kuma sa kunnuwanka suji addu'ar da za a yi a wannan wuri. 41 Yahweh Allah, sai ka tashi daga wurin hutawarka, kai da akwatin ƙarfinka. Yahweh kasa firistocinka su rufa da cetonka, ka kuma sa tsarkakanka suyi murna kan alheranka. 42 Yahweh Allah, kada ka juyar da fuskar keɓaɓɓunka daga wurinka. Ka tuna da abubuwan daka alƙawarta na yin aminci ga bawanka Dauda."

Sura 7

1 Da Suleman ya gama addu'a sai wuta ta sauko daga sama ta cinye baye-baye na ƙonawa da hadayu, sai ɗaukakar Yahweh ta cika gidan. 2 Firistoci basu iya samun damar shiga gidan Yahweh ba, saboda ɗaukakarsa ta cika gidansa. 3 Duk mutanen Isra'ila sun ga yadda wutar tazo daga sama ɗaukakar Yahweh kuma ta sauko a kan gidan, sai suka sunkuyar da kawunansu ƙasa a kan keɓaɓɓen dutse na sujada suka bada godiya ga Yahweh. Suka ce, "Domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada." 4 Sai sarki da dukkan mutanen suka miƙa hadaya ga Yahweh. 5 Sarki Suleman ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin, da tumaki da awaki 120,000. Sai sarki da dukkan mutanen suka keɓe gidan Allah. 6 Sai firistoci suka tsaya, kowanne ya tsaya a inda ya ke hidima, hakannan Lebiyawa suna ɗauke da kayan kiɗa na Yahweh, wanda sarki Dauda ya yi domin ya riƙa yin godiya ga Yahweh ta wurin waƙa, "Domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada." Sai dukkan firistoci suka hura kãkãki a gabansu, kuma sai dukkan Isra'ila suka miƙe tsaye. 7 Sai Suleman ya keɓe tsakiyar haikalin a gaban gidan Yahweh. A can ya miƙa baye-baye ta ƙonawa da kuma kitse na baye-baye na zumunci, domin wannan bagadi na tagulla da ya yi ya gaza ɗaukar baye-baye na ƙonawa, baye-baye ta hatsi, da kitsen. 8 Sai Suleman da ya yi bukin a wancan lokacin har na kwana bakwai tare kuma da dukkan Isra'ilawa, babban taro ne tun daga Lebo Hamat har zuwa iyakar Masar. 9 A rana ta takwas suka yi taron murna domin sun yi taron keɓe bagadi na kwana bakwai. 10 A rana ta ashirin da uku a wata na bakwai, Suleman ya sallami taron mutanen suka koma gidajensu da murna da farin ciki saboda alheran Yahweh daya nuna ga Dauda da Suleman da kuma Isra'ila, mutanensa. 11 Da haka Suleman ya kammala gidan Yahweh da kuma gidansa. Duk abin da yazo zuciyar Suleman game da gidan Yahweh da kuma gidansa ya yi su dukka. 12 Sai Yahweh ya bayyana ga Suleman da dare ya kuma ce da shi, "Na ji addu'arka na kuma zaɓi wannan wurin domin kaina domin ya zama gidan miƙa hadaya. 13 A misali da ace na rufe sammai domin kada ayi ruwa, ko kuma in umarci fări su cinye ƙasar, ko kuma idan na aiko da cuta cikin mutanena, 14 To indan mutanena da ake kira da sunana, zasu yi tawali'u su yi addu'a, su biɗi fuskata, su kuma juya daga mugayen hanyoyinsu, to zan ji daga sama, zan kuma gafarta zunubinsu, in kuma warkar da ƙasarsu. 15 Yanzu idanuna zasu zama a buɗe kunnuwana kuma zasu ji addu'o'in da za ayi a wannan wurin. 16 Domin yanzu na zaɓa na kuma keɓe wannan gida domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata zasu kasance a can kullum. 17 Kai kuma in zaka yi tafiya a gabana kamar yadda mahaifinka Dauda ya yi, ka kuma yi biyayya da duk abin da na umarce ka ka kuma kiyaye sharuɗana da farillaina, 18 To zan kafa gadon sarautarka, kamar yadda na faɗa a alƙawarina da Dauda mahaifinka, lokacin da nace, 'Ba za a taɓa rasa wani daga cikin zuriyarka ba wanda zai yi mulki a Isra'ila.' 19 Amma in ka juya, kayi watsi da farillaina da dokokina dana sa a gabanka, kuma idan ka juya ka bautawa gumaka ka russuna masu, 20 To zan tunɓuke su daga ƙasar dana basu. Wannan gidan kuma dana keɓe domin kaina zan kawar da shi daga gare ni, zan kuma maida shi abin habaici da ba'a ga dukkan al'ummai. 21 Koda ya ke wannan haikalin ya ƙayatu yanzu, duk wanda ya wuce ta gefensa zai razana ya yi tsaki. Zasu ce 'Me yasa Yahweh ya yi haka ga wannan gida da kuma wannan ƙasa?' 22 Sauran zasu amsa suce saboda sun yashe da Yahweh Allahnsu ne, wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, sai kuma suka kakkafa waɗansu gumaku suka russuna masu suka yi masu sujada. Shi yasa Yahweh ya aukar masu da duk wannan masifa."'

Sura 8

1 Sai ya kasance a karshen shekaru ashirin da Suleman ya gina gidan Yahweh da kuma gidansa, 2 sai Suleman ya sake gina garuruwan da Hiram ya bayar gare shi, ya kuma zaunar da mutanen Isra'ila a cikinsu. 3 Sai Suleman ya kai wa Hamatzoba hari ya kuma cinye ta. 4 Ya gina biranen ajiya a cikin hamada, da dukkan birane ƙayatattu da ya gina a Hamat. 5 Haka kuma sai ya gina Bet Horon na Sama da Bet Horon na Ƙasa, birane masu tsaro mai ƙarfi tare da katangai, ƙofofi, da ƙyamare. 6 Ya gina Balat da dukkan biranen ma'aji da ya mallaka, da dukkan biranem domin karusansa da kuma biranen domin mahayansa, kuma ko mene ne ya yi niyar ginawa domin jin daɗinsa a cikin Yerusalem, cikin Lebanon, da kuma cikin dukkan ƙasashen da keƙarƙashin mulkinsa. 7 Amma game da dukkan mutanen da aka rage na wajen su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa, waɗanda ba daga Isra'ila suke ba, 8 zuriyarsu da aka bari a bayansu cikin ƙasar, waɗanda mutanen Isra'ila basu hallakar ba - Suleman ya maishe su masu aikin tilas, haka suke har wa yau. 9 Duk da haka, Suleman bai ɗora wa jama'ar Isra'ila aikin tilas ba. A maimakon haka, suka zama sojojinsa, kwamandojinsa, da hafsoshinsa, da kuma kwamandojin karusan jarumawansa da kuma mahaya dawakansa. 10 Waɗannan kuma su ne manyan hafsoshin masu tafiyar da al'amuran masu kula waɗanda ke na Sarki Suleman, 250 ne suke, waɗanda suka kula da mutanen da suka yi aiki. 11 Sai Suleman ya fito da ɗiyar Fir'auna daga birnin Dauda zuwa gidan da ya gina mata, gama yace, "Matata bazata zauna a gidan Dauda sarkin Isra'ila ba, domin duk inda akwatin alƙawarin Yahweh ya shiga mai tsarki ne." 12 Sai Suleman ya miƙa baye-baye na ƙonawa ga Yahweh a bisa bagadin Yahweh daya gina a gaban Haikalin. 13 Ya miƙa hadayu kamar yadda ya wajaba cikin shirin kowacce rana; ya miƙa su, yana koyi da yadda aka shimfiɗa su a cikin umurnan Musa, a ranakun Asabaci, sabobbin watanni, da kuma kafaffun bikin sau uku kowacce shekara: Bikin Gurasa Mara Gami, Bikin Mako, da kuma Bikin Bukkoki. 14 Bisa ga dokokin mahaifinsa Dauda, Suleman ya naɗa ƙungiyoyin firistoci ga aikinsu, Lebiyawa kuma ga matsayinsu, domin suyi yabo ga Allah su kuma yi hidima a gaban firistoci, kamar yadda ya wajaba a kowacce rana. Ya kuma sa matsaran ƙofofi bisa ga tsarinsu a kowacce ƙofa, gama Dauda, mutumin Allah, ya umarta wannan. 15 Waɗannan mutane basu kauce daga dokokin sarki ga firistoci da Lebiyawa ba game da kowanne al'amari, ko game da ɗakunan ajiya. 16 Dukkan aikin da Suleman ya umartar aka gama, daga ranar da aka kafa harsashen gidan Yahweh har aka gama shi. Gidan Yahweh ya kammalu. 17 Sai Suleman ya tafi Eziyon Geba daga nan zuwa Elat a gaɓar teku, a ƙasar Idom. 18 Sai Hiram ya aika mashi da jirage da hafsoshinsa suka umarta, mazajen da suka ƙware a sha'anin teku, kuma tare da bayin Suleman suka tafi Ofir suka kuma ɗauka daga nan talanti 450 na zinariya suka kawo wurin Sarki Suleman.

Sura 9

1 Da sarauniyar Sheba taji game da girman Suleman, sai tazo Yeruslem domin ta gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da doguwar tawaga, tare da raƙuma ɗauke da kayayyakin ƙamshi, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja dayawa. Da ta iso wurin Suleman, sai ta gaya masa dukkan abin da kecikin zuciyarta. 2 Suleman ya bata amsar dukkan tambayoyinta; babu komai mai wuya ga Suleman; babu tambayar da bai bada amsar ta ba. 3 Da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Suleman da kuma fãdar da ya gina, 4 abincin teburinsa, da yanayin zaman bayinsa, aikin bayinsa da kuma tufafinsu, har da masu ba shi abin sha da irin tufafinsu, da kuma baye-baye na ƙonawa daya miƙa a gidan Yahweh, sai kuma babu sauran hanzari a cikinta. 5 Ta cewa sarkin, "Gaskiya ne, labarin da naji cikin ƙasata game da maganganunka da hikimarka. 6 Ban yarda da abin da naji ba har sai da nazo nan, kuma da idanuwana na gani. Ko rabi ba a gaya mani ba game hikima da wadatarka! Ka zarce girman da naji game da kai. 7 Mutanenka masu albarka ne, bayinka kuma waɗanda ke tsayawa gaban ka koyaushe masu albarka ne, domin suna sauraran hikimarka. 8 Mai albarka ne Yahweh Allahnka, wanda ya ke jin daɗinka, wanda ya ɗora ka a bisa kursiyinsa, ka zama sarki domin Yahweh Allahnka. Domin Allahnka na ƙaunar Isra'ila, domin ya kafa su har abada, ya maishe ka sarki bisansu, domin ka aikata gaskiya da adalci!" 9 Sai ta ba sarki talanti 120 na zinariya da kayan ƙamshi mai yawa da kuma duwatsu masu daraja. Babu kayan ƙamshi mai yawa haka kamar wannan da sarauniyar Sheba ta ba Sarki Suleman da aka ƙara kawo masa kuma. 10 Bayin Hiram da bayin Suleman, waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kawo kuma katakon algum da duwatsu masu daraja. 11 Da katakan algum ɗin, sarki ya yi matakalai na gidan Yahweh da kuma domin fadarsa, har kuma da garayu da molaye domin mawaƙa. Ba a taɓa ganin irin wannan katakon a ƙasar Yahuda ba. 12 Sarki Suleman ya ba sarauniyar Sheba dukkan abin da ta tambaya; ya bata fiye da abin da ta kawo wa sarki. Sai ta tafi ta koma ƙasarta, ita da bayinta. 13 Yanzu nauyin zinariyan da yazo wurin Suleman a cikin shekara ɗaya talanti 666 na zinariya ne, 14 ban da zinariyar da 'yan kasuwa da fatake suka kawo. Dukkan sarakunan Arabiya da gwamnoni a cikin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa ga Suleman. 15 Sarki Suleman ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na bugaggar zinariya. Awo ɗari shida na zinariya ne ya shiga kowacce ɗaya. 16 Ya kuma yi garkuwoyi na bugaggar zinariya guda ɗari uku. Minas uku na zinariya ne ya shiga kowacce garkuwa; sarki ya ajiye su a cikin Gida na Jejin Lebanon. 17 Sa'an nan sarki ya gina babban kursiyi na hauren giwa ya kuma dalaye ta da zinariya mafi kyau. 18 Da akwai matakalai guda shida na hawan kursiyin, kuma da kujeran ɗora ƙafa harɗe da mazamnin sarautar. A kowanne ɓangaren kursiyin akwai abin ɗora hannu da zakuna biyu tsaye kusa da kowannen su. 19 Zakuna goma sha biyu suna tsaye a matakalun, ɗaya a kowanne gefe na matakalai shidan. Babu wata masarautar da keda irin wannan kursiyin. 20 Dukkan abubuwan shan ruwan Sarki Suleman na zinare ne, kuma dukkan moɗayen shan ruwa da kea Gida na Jejin Lebanon duk na zallar zinare ne. Babu wadda suke daga azurfa domin azurfa ba abin daraja bane a kwanakin Suleman. 21 Sarkin yana da jiragen ruwa masu tafiya cikin teku, tare da jiragen na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku jiragen sukan tafi su kawo zinariya, azurfa, da kuma hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu. 22 Saboda haka sarki Suleman yafi dukkan sarakunan duniya arziki da kuma hikima. 23 Dukkan sarakunan duniya suka nemi su ga Suleman domin su saurari hikimarsa, wadda Allah yasa cikin zuciyarsa. 24 Waɗanda suka kawo ziyara suka zo masa da kyautai, kayayyaki na azurfa dana zinariya, riguna, kayan yaƙi, da kayan ƙanshi, da kuma dawakai da alfadarai, shekara bayan shekara. 25 Suleman yana da ɗakunan dawakai har dubu huɗu da karusai, da mahayan dawakai dubu sha biyu, waɗanda ya sanya su cikin birnin karusai tare da shi kuma a cikin Yerusalem. 26 ya yi mulki bisa dukkan sarakuna daga Kogin Yufiretis zuwa ƙasar Filistiyawa, zuwa iyakar Masar. 27 Sarkin yana da azurfa cikin Yerusalem, yawansu kamar duwatsun ƙasa. Ya maida itacen sida kamar itacen durumi mai yawa da suke ƙauyuka. 28 Aka kawo wa Suleman dawakai daga Masar da kuma daga dukkan ƙasashe. 29 Game da waɗansu batutuwa game da Suleman, farko da ƙarshe, ba an rubuta su cikin Tarihi na Nathan annabi ba, cikin Annabci Ahiya Ba-shiloni, kuma a cikin Wahayin Iddo Mai duba (wanda ya sami labari game da Yerobowam ɗan Nebat)? 30 Suleman ya yi mulki cikin Yerusalem bisa dukkan Isra'ila har shekara arba'in. 31 Ya yi barci tare da kakanninsa kuma mutanen suka binne shi a cikin birnin Dauda mahaifinsa. Rehobowam, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.

Sura 10

1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukkan Isra'ila na zuwa Shekem domin a naɗa shi sarki. 2 Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (domin yana cikin Masar, inda ya guje wa sarki Suleman), sai ya dawo daga Masar. 3 Sai suka aika aka kirawo shi, kuma Yerobowam da dukkan Isra'ila suka zo; suka yi magana da Rehobowam suka kuma ce, 4 "Mahaifinka yasa karkiyarmu da wuya. Yanzu kuwa, kasa aikin mahaifinka mai wuya ya zama da sauƙi, ka kuma sauƙaƙa karkiya mai nauyin da ya ɗora mana, mu kuma mu bauta maka." 5 Sai Rehobowam yace masu, "Ku komo gare ni bayan kwana uku." Sai mutanen suka tafi. 6 Sai sarki Rehobowam ya nemi shawara a wurin dattawa waɗanda suka tsaya a gaban Suleman mahaifinsa sa'ad da ya ke raye; yace, "Ta yaya zaku shawarce ni in bada amsa ga waɗannan mutanen?" 7 Suka yi magana da shi suka ce, "Idan kayi alheri ga waɗannan mutanen ka kuma kyauta masu, ka kuma faɗi masu maganganun alheri, sa'annan zasu zama bayin ka koyaushe." 8 Amma Rehobowam ya yi watsi da shawarar da dattawan suka bashi, amma ya nemi shawara daga matasa waɗanda suka girma tare dashi, waɗanda suka tsaya gabansa. 9 Yace masu, "Wacce shawara zaku bani, domin mu amsa ma mutanen da suka yi magana da ni suka ce, 'Ka rage mana nauyin karkiyar da mahaifinka ya ɗora mana'?" 10 Samarin da suka yi girma tare da Yerobowam suka yi magana dashi, cewa, "Ga yadda zaka yi magana da mutanen da suka ce maka mahaifinka Suleman yasa ƙarkiyarsu tayi nauyi, amma wai dole kasa ta zama da sauƙi. Ga abin da zaka ce masu, 'Ɗan ƙaramin yatsana yafi ƙugun mahaifina kauri. 11 Don haka yanzu, ko da ya ke mahaifina ya tsananta maku da karkiya mai nauyi, ni zan daɗa bisa karkiyarku. Mahaifina ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunnamai." 12 Sai Yerobowam da dukkan mutanen suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗi, "Ku dawo wurina a rana ta uku." 13 Sai Rehobowam ya yi masu magana da zafi, ya yi banza da shawarar dattawan. 14 ya yi masu magana bisa ga shawarar Samarin, cewa, "Mahaifina yasa ƙarkiyarku tayi nauyi, amma zan daɗa bisanta. Mahaifina ya yi maku horo da bulala, amma ni zanyi maku horo da kunamai." 15 Sarki kuwa bai saurari mutanen ba, gama al'amari ne wadda ke faruwa yadda Allah ya shirya, domin Yahweh ya aiwatar da maganarsa wadda Ahiya Bashilone ya faɗi ga Yerobowam ɗan Nebat. 16 Lokacin da dukkan Isra'ila suka ga cewa sarki bai saurare su ba, sai mutanen suka amsa masa suka ce, "Wanne rabo muke da shi a cikin Dauda? Bamu da gãdo a cikin ɗan Yesse! Kowannenku ya koma ga rumfarsa, Isra'ila. Yanzu ka kula da naka gidan, Dauda." Sai dukkan Isra'ila suka koma rumfunansu. 17 Amma game da mutanen Isra'ila waɗanda ke zaune cikin biranen Yahuda, Rehobowam ya yi mulki bisansu. 18 Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, wanda ke lura da aikin tilas, amma mutanen suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam ya tsere da sauri cikin karusansa zuwa Yerusalem. 19 Don haka Isra'ila ke tayarwa gãba da gidan Dauda har wa yau.

Sura 11

1 Da Rehobowam ya isa Yerusalem, ya tattaro gidan Yahuda da Benyamin, 180,000 zaɓaɓɓun mutane waɗanda suke sojoji, suyi yaƙi gãba da Isra'ila, su maido da masarautar ga Rehobowam. 2 Amma maganar Yahweh tazo wa Shamayya mutumin Allah, cewa, 3 "Ka cewa Rehobowan ɗan Suleman, sarkin Yahuda, da dukkan Isra'ila cikin Yahuda da Benyamin, 4 Yahweh ya faɗi wannan, "Kada ku kai hari ko kuyi yaƙi gãba da 'yan'uwanku. Kowanne dole ya koma ga nasa gidan, domin na sanya wannan ya faru."'" Sai suka yi biyayya da maganganun Yahweh suka kuma juya baya daga harin Yerobowam. 5 Rehobowam ya zauna cikin Yerusalem ya kuma gina birane domin tsaro. 6 Ya gina Betlehem, Itam, Tekoya, 7 Betzur, Soko, Adullam, 8 Gat, Maresa, Zif, 9 Adorayim, Lakish, Azeka, 10 Zora, Ayyalon, da kuma Hebron. Waɗannan tsararrun birane ne cikin Yahuda da Benyamin. 11 Ya ƙarfafa wuraren tsaronsu ya sanya ofisoshi a cikinsu, tare da tanadin abinci, da mai, da inabi. 12 Ya sanya garkuwoyi da mãsu a cikin dukkan biranen ya kuma maida su masu ƙarfi sosai. Haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa. 13 Firistoci da Lebiyawa daga cikin dukkan Isra'ila suka ƙetara zuwa gare shi daga cikin kan iyakokinsu. 14 Domin Lebiyawan suka bar gonakinsu na noma da kiwo da kaddarorinsu domin su zo Yahuda da Yerusalem, domin Yerobowam da 'ya'yansa maza sun kore su, don kada su sake aiwatar da ayyukan firistoci domin Yahweh. 15 Yerobowam ya naɗa wa kansa firistoci domin wuraren masujadai da kuma gumakan akuya da na maraƙi da ya yi. 16 Mutane daga dukkan kabilun Isra'ila suka biyo shi, waɗanda suka tsaida zukatansu su biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila; suka zo Yerusalem suyi hadaya ga Yahweh. Allahn Ubanninsu. 17 Sai suka ƙarfafa masarautar Yahuda suka kuma sa Rehobowam ɗan Suleman ya yi ƙarfi lokacin shekaru uku, suka kuma yi tafiya shekaru uku cikin hanyar Dauda da Suleman. 18 Rehobowam ya ɗaukar wa kansa mata: Mahalat, ɗiyar Yerimot, ɗan Dauda, da Abihayil, ɗiyar Eliyab, ɗan Yesse. 19 Ta haifa masa 'ya'ya maza: Yewush, Shemariya, da Zaham. 20 Bayan Mahalat, Rehobowam ya ɗauki Ma'aka, ɗiyar Absalom; ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza, da Shelomit. 21 Rehobowam yana ƙaunar Ma'aka, ɗiyar Absalom, fiye da dukkan matansa da ƙwaraƙwaransa (ya ɗauki mata sha takwas da ƙwaraƙwarai sittin, ya kuma zama mahaifin 'ya'ya maza ashirin da takwas da 'ya'ya mata sittin). 22 Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma'aka ya zama basarake, shugaba a tsakanin 'yan'uwansa; yana tunanin maida shi sarki. 23 Rehobowam ya yi mulki da hikima; ya baza dukkan 'ya'yansa maza cikin dukkan ƙasar Yahuda da Benyamin zuwa kowanne tsararren birni. Ya kuma basu abinci a yalwace ya kuma nemo mataye da yawa domin su.

Sura 12

1 Sai ya kasance, da mulkin Rehobowam ya kafu ya kuma yi ƙarfi, sai ya watsar da shari'ar Yahweh - da dukkan Isra'ila tare da shi. 2 Ya faru a shekara ta biyar na sarki Rehobowam, Shishak, sarkin Masar, yazo gãba da Yerusalem, saboda mutanen sun yi rashin aminci ga Yahweh. 3 Yazo da karusai ɗari sha biyu da mahaya dawakai dubu sittin. Sojoji babu iyaka suka zo tare da shi daga Masar: Libiyawa, Sukkiyawa, da Kushiyawa. 4 Ya ƙwaci tsararrun birane da kena Yahuda ya kuma zo Yerusalem. 5 Yanzu Shemayya annabi yazo wurin Rehobowam da shugabannin Yahuda da suka tattaru tare a Yerusalem saboda Shishak. Shemayya yace masu, "Wannan ne abin da Yahweh ya faɗa: Kun yashe ni, don haka nima na bayar daku cikin hannun Shishak." 6 Daga nan shugabannin Isra'ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka kuma ce, "Yahweh mai adalci ne." 7 Da Yahweh yaga cewa sun ƙasƙantar da kansu, maganar Yahweh tazo ga Shemayya, cewa, "Sun ƙasƙantar da kansu. Ba zan rusa su ba; zan ƙubutar da su na wani matsayi, fushina kuma ba zai zubo bisa Yerusalem ta hannun Shishak ba. 8 Duk da haka, zasu zama bayinsa, domin su fahimci bambanci tsakanin yi mani bauta da kuma bauta wa shugabannin sauran ƙasashen." 9 Sai Shishak sarkin Masar yazo gãba da Yerusalem ya kuma ɗauke taskokin cikin gidan Yahweh, da taskokin cikin gidan sarki. Ya ɗauke komai da komai; ya ɗauke garkuwoyi ta zinariya da Suleman ya yi. 10 Sarki Rehobowam ya yi garkuwoyi na tagulla a mamadinsu ya miƙa su kuma cikin hannuwan ofisoshin tsaro, waɗanda ke tsaron ƙofofin zuwa gidan sarki. 11 Sai ya kasance duk sa'ad da sarki ya shiga gidan Yahweh, matsaran zasu ɗauke su; daga nan zasu maido da su cikin gidan tsaro. 12 Da Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, fushin Yahweh ya juya daga gare shi, domin kada a lalatar da shi ɗungun; baya da haka, akwai sauran wasu abubuwan nagarta da ake samu cikin Yahuda. 13 Sai sarki Rehobowam yasa sarautarsa tayi ƙarfi a Yerusalem, haka kuma ya yi mulki. Rehobowam na da shekaru arba'in da ɗaya sa'ad da ya fara mulki, ya kuma yi mulki shekaru sha bakwai a Yerusalem, birnin da Yahweh ya zaɓa daga dukkan kabilun Isra'ila saboda yasa sunansa a wurin. Sunan mahaifiyarsa Na'ama, Ba'ammoniya. 14 Ya aikata abin da ke mugunta, saboda bai kafa zuciyarsa ba domin ya biɗi Yahweh. 15 Sauran al'amura kuwa game da Rehobowam, farko da ƙarshe, ba a rubuce suke ba a cikin rubuce-rubucen Shemayya annabi da Iddo mai dubawa, waɗanda kuma suke da lissafe - lissafen asaloli da ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam? 16 Rehobowam ya yi barci da kakanninsa aka kuma binne shi cikin birnin Dauda; Abiya ɗansa ya zama sarki a gurbinsa.

Sura 13

1 A cikin shekara ta sha takwas ta sarki Yerobowam, Abiya ya fara mulki bisa Yahuda. 2 ya yi mulki shekaru uku a Yerusalem; sunan mahaifiyarsa Ma'aka, ɗiyar Yuriyel na Gibiya. Aka yi yaƙi tsakanin Abiya da Yerobowam. 3 Abiya ya tafi cikin yaƙin da mayaƙa ƙarfafa, sojoji masu ƙarfin hali, zaɓaɓɓun mutane 400,000. Yerobowam yaja dagar yaƙi gãba da shi tare da zaɓaɓɓun mutane 800,000, ƙarfafa, sojoji masu ƙarfin hali. 4 Abiya ya tsaya a tsaunin Zemarayim, wanda ke ƙasar tudu ta Ifraim, ya kuma ce, "Ku saurare ni, Yerobowam da dukkan Isra'ila! 5 Baku san cewa Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bayar da mulki bisa Isra'ila ga Dauda ba har abada, gare shi da 'ya'yansa bisa tsararren alƙawari? 6 Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, bawan Suleman ɗan Dauda, ya tashi da tawaye gãba da ubangijinsa. 7 Mutane marasa amfani, ƙasƙantattun jama'a, suka tattaru gare shi. Sun zo gãba da Rehobowam ɗan Suleman, duk da cewa Rehobowam yaro ne kuma bai da ƙwarewa kuma ba zai iya tsayayya da su ba. 8 Yanzu kunce wai zaku iya ƙin ikon mulkin Yahweh cikin hannun zuriyar Dauda. Ku mayaƙa ne masu yawa, tare daku kuma akwai maruƙan zinariya da Yerobowam ya yi a matsayin alloli dominku. 9 Ba ku kuka kori firistocin Yahweh, zuriyar Haruna, da Lebiyawa ba? Ba kun naɗa wa kanku firistoci bisa ga ɗabi'ar mutanen sauran ƙasashe ba? Duk wanda yazo ya keɓe kansa da ɗan maraƙi da raguna bakwai zai zama firist na abubuwan da ba alloli ba. 10 Amma mu kam, Yahweh ne Allahnmu, kuma bamu yashe shi ba. Muna da firistoci, zuriyar Haruna, suna bautar Yahweh, da Lebiyawa, waɗanda ke kan aikinsu. 11 Kowacce safiya da maraice suna ƙona wa Yahweh baye-baye na ƙonawa da turaren ƙamshi. Suna kuma shirya gurasar miƙawa a bisa tsastsarkan teburi; suna kuma lura da mazaunin fitila na zinariya tare da fitilunsu, domin su riƙa ci kowacce safiya. Muna kiyaye dokokin Yahweh, Allahnmu, amma kun yashe shi. 12 Duba, Allah yana tare da mu a bisa kanmu, kuma firistocinsa suna nan tare da kãkãki domin su busa ƙara gãba daku. Mutanen Isra'ila, kada kuyi faɗa gãba da Yahweh, Allah na kakanninku, domin baza kuyi nasara ba." 13 Amma Yerobowam ya shirya kwanto a bayansu; mayaƙansa suna gaban Yahuda, masu kwanton kuma a bayansu. 14 Da Yahuda suka waiga baya, duba, yaƙin yana gabansu kuma yana bayansu. Suka yi kuka ga Yahweh, firistocin kuma suka busa kãkãki. 15 Dagana mutanen Yahuda suka yi kuwwa; yayin da suka yi kuwwar, sai Allah ya mazge Yerobowam da dukkan Isra'ila a gaban Abiya da Yahuda. 16 Mutanen Isra'ila suka guje daga gaban Yahuda, Allah kuma ya bayar da su cikin hannun Yahuda. 17 Abiya da mayaƙansa suka kashe su da babban yanka; zaɓaɓɓun mutane 500,000 na Isra'ila suka fãɗi matattu. 18 Ta wannan hanya, mutanen Isra'ila aka kayar da su a wannan lokaci; mutanen Yahuda suka yi nasara saboda sun dogara ga Yahweh, Allah na kakanninsu. 19 Ya runtumi Yerobowam; Ya ɗauke birane daga gare shi: Betel da kauyukanta, Yeshana da ƙauyukanta, da Efron da ƙauyukanta. 20 Yerobowam bai taɓa sake samun iko ba a lokacin kwanakin Abiya; Yahweh ya buge shi, kuma ya mutu. 21 Amma Abiya ya zama cike da iko; ya ɗaukar wa kansa mata sha huɗu ya kuma zama mahaifin 'ya'ya maza ashirin da biyu da 'ya'ya mata sha shida. 22 Sauran ayyukan da Abiya ya aiwatar, ɗabi'arsa da maganganunsa an rubuta a cikin taƙaitaccen labarin Annabi Iddo.

Sura 14

1 Abiya ya yi barci tare da kakanninsa, aka kuma bizne shi a cikin birnin Dauda. Asa, ɗansa, ya zama sarki a gurbin sa. A kwanakin sa ƙasar ta kasance shiru na shekaru goma. 2 Asa ya yi abin da kemai kyau da dai-dai a idanun Yahweh Allahnsa, 3 domin ya ɗauke bãƙin bagadai da wuraren tuddai. Ya farfasa ginshiƙan dutse ya kuma datse kafe-kafen Astarot. 4 Ya dokaci Yahuda su biɗi Yahweh, Allah na kakanninsu, su kuma aiwatar da shari'ar da dokokin. 5 Haka kuma ya ɗauke wuraren tuddai da bagadan turare daga dukkan biranen Yahuda. Masarautar ta sami hutawa a ƙarƙashin sa. 6 Ya gina tsararrun birane a Yahuda, domin ƙasar ta kasance shiru, kuma ba shi da yaƙi a waɗannan shekaru, saboda Yahweh ya ba shi salama. 7 Domin Asa ya cewa Yahuda, "Bari mu gina waɗannan birane muyi katangai kewaye da su, da hasumiyoyi, da ƙofofi, da ƙarafuna; ƙasar har wayau tamu ce, saboda mun biɗo Yahweh Allahnmu. Mun biɗo shi, kuma ya bamu salama ta kowanne gefe." Sai suka yi gini kuma suka yi nasara. 8 Asa na da mayaƙa da ke ɗaukar garkuwoyi da mãsu; daga Yahuda yana da mutane 300,000, daga kuma Benyamin, mutane 280,000 waɗanda ke ɗauke da garkuwoyi suna kuma jan bakkuna. Dukkan waɗannan ƙarfafa ne, mutane masu ƙarfin hali. 9 Zera Bakushe yazo gãba da su tare da mayaƙa sojoji miliyan ɗaya da karusai ɗari uku; yazo Maresha. 10 Daga nan Asa ya fita domin ya gamu da shi, suka kuma kafa dãgar yaƙi a kwarin Zefata a Maresha. 11 Asa ya yi kuka ga Yahweh, Allahnsa, ya kuma ce, "Yahweh, babu wani sai kai da zai taimaki wanda ba shi da ƙarfi yayin da ya ke fuskantar masu yawa. Ka taimake mu, Yahweh Allahnmu, domin mun dogara gare ka, kuma a cikin sunanka munzo gãba da wannan babban taro. Yahweh, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum ya yi nasara da kai." 12 Yahweh ya buge Kushiyawa a gaban Asa da Yahuda; Kushiyawa suka tsere. 13 Asa da sojojin da ketare da shi suka runtume su zuwa Gera. Kushiyawa da yawa suka fãɗi yadda basu iya murmurowa ba, domin an lalatar da su gaba ɗaya a gaban Yahweh da mayaƙansa. Mayaƙan suka kwashe ganima mai yawa. 14 Mayaƙan suka hallakar da dukkan ƙauyukan da ke kewaye da Gera, domin fargaban Yahweh ya sauko bisa dukkan mazaunansu. Mayaƙan suka washe dukkan ƙauyukan, kuma akwai ganima da yawa a cikin su. 15 Mayaƙan kuma suka hallakar da rumfar zaman makiyaya mayawata; suka kwashe ganimar tumaki masu yawa, tare da raƙuma, sa'an nan suka koma Yerusalem.

Sura 15

1 Ruhun Allah yazo bisa Azariya ɗan Oded. 2 Ya fita ya sami Asa ya kuma ce masa, "Ka saurare ni, Asa, da dukkan Yahuda da Benyamin: Yahweh yana tare da kai, yayin da kake tare da shi. Idan ka biɗe shi, zaya samu gare ka; amma idan ka yashe shi, zai yashe ka. 3 Yanzu lokaci mai tsawo, Isra'ila basu tare da Allah na gaskiya, babu firist mai koyarwa, babu kuma shari'a. 4 Amma idan a cikin ƙuncinsu suka juya ga Yahweh, Allahnsu, suka kuma biɗe shi, sai ya samu a gare su. 5 A waɗannan lokuta babu salama ga wanda ya yi tafiyarsa zuwa wani wuri, ko wanda ya yi tafiya zuwa nan; maimako, manyan matsaloli na bisa dukkan mazauna ƙasashen. 6 Aka karya su gutsu-gutsu, al'umma gãba da al'umma, birni kuma gãba da birni, domin Allah ya azabtar da su da dukkan wahalu iri - iri. 7 Amma ka ƙarfafa, kada kuma ka bar hannunka ya zama kasasshe, domin aikin ka zai sami sakamako." 8 Sa'ad da Asa yaji waɗannan maganganu, anabcin Oded annabi, sai ya yi ƙarfin hali ya kori ƙazantattun abubuwa daga dukkan ƙasar Yahuda da Benyamin, daga kuma biranen da ya kame daga ƙasar tudu ta Ifraimu, ya kuma sake gina bagadin Yahweh, wanda ke gaban rumfar gidan Yahweh. 9 Ya tattaro dukkan Yahuda da Benyamin, da waɗanda ke zama tare da su - mutane daga na Ifraim da Manasse, daga kuma Simiyon. Domin sunzo daga Isra'ila zuwa gare shi babban taro, da suka ga cewa Yahweh Allahnsa na tare da shi. 10 Sai suka tattaru tare a Yerusalem a cikin wata na uku, a cikin shekara ta sha biyar na mulkin Asa. 11 Suka yi hadaya ga Yahweh a wannan rana daga cikin ganimar da suka kawo: shanu ɗari bakwai da tumaki da awaki dubu bakwai. 12 Suka shiga cikin alƙawari su biɗi Yahweh, Allah na kakanninsu, da dukkan zuciyarsu kuma da dukkan ransu. 13 Suka yarda da cewa duk wanda ya ƙi ya biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila, za a kashe shi, ko da ƙarami ne ko babba, ko namiji ko mace. 14 Suka yi rantsuwa ga Yahweh da babbar murya, tare da sowa, kuma da kãkãki da ƙahonni. 15 Dukkan Yahuda suka yi farinciki da alƙawarin, domin sun yi rantsuwa da dukkan zuciyarsu, suka kuma biɗi Allah da dukkan buƙatunsu, kuma ya samu a gare su. Yahweh ya basu salama a dukkan kewayensu. 16 Ya kuma cire Ma'aka, kakarsa, daga zama sarauniya, domin tayi ƙazantaccen siffa daga wani ƙarfen Ashera. Asa ya datse ƙazantaccen siffar, ya niƙe shi zuwa turɓaya ya kuma ƙone shi a magudanar Kidron. 17 Amma bisan wurare ba a ɗauke su ba daga Isra'ila. Duk da haka Asa ya sadaukar da zuciyarsa gaba ɗaya dukkan kwanakinsa. 18 Ya kawo cikin gidan Allah abubuwan mahaifinsa da abubuwansa wanda ke na Yahweh: Kayayyakin azurfa da zinariya. 19 Babu sauran yaƙi kuma har shekara talatin da biyar na mulkin Asa.

Sura 16

1 Cikin shekara ta talatin da shida na mulkin Asa, Ba'asha, sarkin Isra'ila, ya nuna tsageranci gãba da Yahuda ya kuma gina Rama, domin kada ya bar wani ya tashi ko ya tafi ƙasar Asa, sarkin Yahuda. 2 Daga nan Asa ya fito da azurfa da zinariya daga ɗakunan ajiya na cikin gidan Yahweh da gidan sarki, ya kuma aika su ga Ben Hadad sarkin Aram, wanda ke zama a Damaskus. Yace, 3 "Bari alƙawari ya kasance tsakani na da kai, kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifi na da mahaifin ka. Duba, na aiko maka da azurfa da zinariya. Ka karya alƙawarinka da Ba'asha, sarkin Isra'ila, saboda ya rabu da ni." 4 Ben Hadad ya saurari sarki Asa ya kuma aika da shugabannin mayaƙansa gãba da biranen Isra'ila. Suka kai hari ga Iyon, Dan, Abelmayim, da dukkan biranen ajiya na Naftali. 5 Sai ya kasance da Ba'asha yaji wannan, sai ya dena ginin Rama, ya kuma bar aikinsa ya tsaya. 6 Daga nan Asa sarki ya ɗauki dukkan Yahuda tare da shi. Suka ɗauke duwatsu da katakai daga Rama wanda Ba'asha ke ginin birnin da su. Daga nan nan sarki Asa ya ɗauki waɗannan kayan gini ya yi amfani da su ya gina Geba da Mizfa. 7 A wannan lokaci Hanani mai gani ya tafi wurin Asa, sarkin Yahuda, ya kuma ce ma shi, "Saboda ka dogara ga sarkin Aram baka kuma dogara ga Yahweh Allahnka ba, mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka. 8 Kushiyawa da Libiyawa ba manyan mayaƙa ba ne, tare da karusai masu yawa da mahaya dawakai? Duk da haka, saboda ka dogara ga Yahweh, ya baka nasara a bisansu. 9 Gama idanun Yahweh na dubawa ko'ina cikin dukkan duniya, domin ya nuna kansa mai karfi a madadin waɗanda zukatansu ke shiryayyu zuwa gare shi. Amma ka aikata wawanci a cikin wannan al'amari. Daga yanzu zuwa nan gaba, zaka sami yaƙi." 10 Daga nan Asa ya fusata da mai ganin; ya sanya shi cikin kurkuku, domin ya yi fushi da shi game da wannan al'amari. A dai-dai wannan lokacin kuma, Asa ya tsananta wa wasu daga cikin mutanen. 11 Duba, ayyukan Asa, daga farko zuwa karshe, duba, an rubuta su cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila. 12 A cikin shekara ta talatin da tara na mulkinsa, Asa ya kamu da cuta a ƙafafunsa; cutarsa kuwa ta yi tsanani sosai. Duk da haka, bai nemi taimako ba daga Yahweh, amma daga masu magani kaɗai. 13 Asa ya yi barci tare da kakanninsa; ya mutu a shekara ta arba'in da ɗaya na mulkinsa. 14 Suka bizne shi a nasa kabarin, wanda ya haƙa domin kansa a cikin birnin Dauda. Aka kwantar da shi cikin maɗauki da ke cike da ƙanshi mai daɗi da kayan ƙanshi daban-daban da ƙwararrun masu haɗa turare suka haɗa. Daga nan suka haɗa babbar wuta domin girmama shi.

Sura 17

1 Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarki a gurbinsa. Yehoshafat ya ƙarfafa kansa gãba da Isra'ila. 2 Ya sanya 'yan doka a cikin dukkan ƙarfafan biranen Yahuda, ya kuma kafa sansanai a cikin ƙasar Yahuda da cikin biranen Ifraim, waɗanda Asa mahaifinsa ya kame. 3 Yahweh yana tare da Yehoshafat saboda ya yi tafiya cikin hanyoyin farko na mahaifinsa Dauda, bai kuma biɗi ba'aloli ba. 4 Maimako, ya dogara ga Allah na mahaifinsa, ya kuma yi tafiya cikin dokokinsa, ba bisa ga ɗabi'ar Isra'ila ba. 5 Sai Yahweh ya tabbatar da mulkin a hannunsa; dukkan Isra'ila suka kawo haraji ga Yehoshafat. Yana da dukiya da daraja a yalwace. 6 Zuciyarsa ya sadaukar ga hanyoyin Yahweh. Ya cire wuraren tuddai da kafe-kafen Ashera daga Yahuda. 7 A cikin shekara uku na mulkinsa ya aika da ofisoshinsa Benhayin, Obadiya, Zakariya, Netanel, da Mikaya, su koyar a cikin biranen Yahuda. 8 Tare da su kuma akwai Lebiyawa: Shemayya, Nataniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya, da Tobadoniya; tare da su kuma akwai firistoci Elishama da Yehoram. 9 Suka koyar a Yahuda, suna da littafin shari'ar Yahweh tare da su. Suka yi yawo cikin dukkan biranen Yahuda suka kuma yi koyarwa a cikin mutanen. 10 Fargabar Yahweh ya sauko bisa dukkan masarautun ƙasashen da kekewaye da Yahuda, har da ba su iya yaƙar Yehoshafat ba. 11 Wasu daga cikin Filistiyawa suka kawo kyautai ga Yehoshafat, da azurfa a matsayin haraji. Larabawa kuma suka kawo masa garkuna, raguna 7,700, da awaki 7,700. 12 Yehoshafat ya zama cike da iko sosai. Ya gina tsararrun birane da wuraren ajiya a Yahuda. 13 Yana da kayan biyan buƙatu masu yawa a cikin biranen Yahuda, da sojoji - ƙarfafa, mutane masu ƙarfin hali - a Yerusalem. 14 Ga lissafinsu an tsãra bisa ga sunayen gidajen ubanninsu: Daga Yahuda, shugabannin dubbai; Adna shugaba, tare da shi kuma mutanen yaƙi 300,000; 15 gaba da shi kuma Yehohanan shugaba, tare da shi kuma mutane 280,000; 16 gaba da shi kuma Amasiya ɗan Zikri, wanda ya miƙa kansa ya bautawa Yahweh da yardan ransa; tare da shi kuma mutanen yaƙi 200,000. 17 Daga Benyamin: Eliyada cike da iko mutum mai ƙwazo, tare da shi kuma 200,000 shiryayyu da bakkuna da garkuwoyi; 18 gaba da shi kuma Yehozabad, tare da shi kuma 180,000 a shirye shiryayyu domin yaƙi. 19 Waɗannan ne waɗanda suka bauta wa sarki, baya ga waɗanda sarki ya sanya a tsararrun birane a cikin dukkan Yahuda.

Sura 18

1 Yanzu Yehoshafat yana da dukiya da yawa da kuma girma; sai ya haɗa kai da Ahab ta wurin miƙa ɗaya daga cikin iyalinsa ya auri 'yarsa. 2 Bayan 'yan shekaru sai ya tafi wurin Ahab a Samariya. Ahab ya yanyanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanensa da ketare da shi. Ahab yasa shi ya kai wa Ramot Giliyad hari tare da shi. 3 Ahab sarkin Isra'ila yace da Yehoshafat, sarkin Yahuda, "Ko za ka bini zuwa Ramot Giliyad?" Yehoshafat ya amsa masa, ni kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne; zamu kasance tare da kai a cikin yaƙin." 4 Sai Yehoshafat yace da sarkin Isra'ila, "Na roƙe ka ka fara neman maganar Yahweh domin amsarka." 5 Daga nan sai sarki ya tattara dukkan annabawa tare har su ɗari huɗu sai yace da su, "Ko ma iya zuwa Ramot Gileyad yaƙi, ko kuwa kada mu je?" Suka ce, "Ka kai hari, domin Allah zai bada ita a hannun sarki." 6 Amma Yehoshafat yace, "Babu wani annabin Yahweh da ba shi nan da zamu nemi shawara?" 7 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Har yanzu akwai wani da zamu nemi shawarar Yahweh, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa domin bai taɓa yi mini wani anabci mai kyau ba, amma kullum na mugunta ne." Amma Yehoshafat yace, "Bai kamata sarki ya faɗi haka ba." 8 Sai sarkin Israila ya kira hafsa yace, "Ka yi hanzari ka kawo Mikaiya ɗan Imla." 9 To Ahab sarkin Isra'ila da Yehoshafat sarkin Yahuda na zaune a kujerar mulki kowannensu ya yi adonsa na sarauta a filin Allah a ƙofar shiga Yerusalem, kuma dukkan annabawa na zaune a gabansu. 10 Sai Zedekiya ɗan Kena'ana ya yi wa kansa ƙaho na ƙarfe ya ce"Yahweh ya faɗi wannan. Da wannan zaka rarraki Aremiyawa har sai an haɗiye su. 11 Duk annabawan suka yi annabci iri ɗaya suna cewa ka kai hari kan Ramot Gileyad kayi nasara, gama Yahweh ya bayar da ita a hannun sarki." 12 Manzon da aka aika wurin Mikaiya ya yi magana da shi yace, "Duba, dukkan annabawa sun faɗi maganganu masu kyau game da sarki. Ina roƙonka kaima maganarka ta zama kamar tasu, ka faɗi abubuwa masu kyau." 13 Mikaiya ya amsa, "Na rantse da Yahweh abin da Allah ya faɗi shi zan faɗa." 14 Sa'ad da yazo wurin sarki, sarki ya ceda shi, "Mikaiya, ma iya zuwa Ramot Gileyad yaƙi, ko a'a?" Mikaiya ya amsa masa, "Ka kai hari ka kuma yi nasara! Domin zata zama babbar nasara." 15 Sai sarki ya ceda shi, "Har sau nawa zan buƙace ka da ka rantse ka faɗa mini gaskiya da sunan Yahweh?" 16 To sai Mikaiya yace, "Na ga dukkan Isra'ila a warwatse a kan tuddai, kamar tumakin da basu da makiyayi, Yahweh kuma yace, 'Waɗannan basu da makiyayi. Bari kowanne mutum ya koma gidansa cikin salama.'" 17 To sai sarkin Isra'ila ya ceda Yehoshafat, "Ashe ban faɗa maka cewa ba zai yi annabci mai kyau game da ni ba, amma sai na masifa?" 18 Sai Mikaiya ya ce yanzu dukkan ku sai ku ji maganar Yahweh: Na ga Yahweh zaune kan kursiyinsa, kuma dukkan rundunar sama na tsaye a gefen damansa da hagunsa. 19 Yahweh yace, Wane ne zai yaudari Ahab, sarkin Isra'ila, domin ya haura ya faɗi a Ramot Gileyad?' Wannan ya ce haka wani kuma ya ce wancan. 20 Daga nan sai wani ruhu ya sauko daga wurin Yahweh yace, 'zan ruɗe shi. 'Yahweh ya ceda shi ta yaya?' 21 Sai ruhun ya amsa, 'Zan je in zama ruhun ƙarya a bakin annabawansa dukka. Yahweh ya amsa, 'Zaka ruɗe shi, kuma zaka yi nasara. To yanzu sai ka tafi ka yi haka.' 22 Yanzu duba, Yahweh yasa ruhun ƙarya a bakin annabawan nan naka, Yahweh kuma ya umarta masifa dominka." 23 Sai Zedekiya ɗan Kena'aya, yazo gaba, ya mari Mikaiya a kunci, yace, "Ta wacce hanya Ruhun Yahweh ya barni har ya yi magana da kai?" 24 Mikaiya yace, "Duba za ka san haka a waccan ranar, lokacin da ka shiga lungun ɗaki domin ka ɓuya." 25 Sarkin Isra'ila ya ceda wanɗansu bayi, "Ku je ku kama Mikaiya ku kai shi wurin Amon gwamnan birnin, da kuma Yowash, ɗana. 26 kuce da shi, 'Sarki ya ceka sa wannan mutum a kurkuku ka kuma ciyar da shi da 'yar gurasa da ɗan ruwa, har sai na dawo lafiya.'" 27 Sai Mikaiya ya cein har ka dawo lafiya to ba Yahweh ne ya yi magana ta wurina ba." Ya ƙara da cewa, dukkan ku mutane ku ji wannan." 28 To sai Ahab, sarkin Isra'ila, da Yehoshafat, sarkin Yahuda, suka tafi yaƙi a Ramot Gileyad. 29 Sarkin Isra'ila ya ceda Yehoshafat, "Zan yi ɓadda kama in tafi yaƙin, amma kai sai ka sa rigunanka na sarauta." Sai sarkin Isra'ila ya yi ɓadda kama suka tafi yaƙin. 30 Shi kuma sarkin Aram ya bada umarni ga shugaban mayaƙan karusai cewa "Kada ya hari ƙananan mayaƙa sai dai sarkin Isra'ila kaɗai." 31 Sai ya kasance bayan shugaban mayaƙan ya ga Yehoshafat sai yace, "Wancan sarkin Isra'ila ne." Sai suka juya domin su kai masa hari, amma Yehoshafat ya ƙwala ihu, Yahweh kuma ya taimake shi. Allah ya juyar da su daga binsa. 32 Bayan da shugabannin yaƙin suka gane ba sarkin Isra'ila bane sai suka juya suka dena fafararsa. 33 Amma wani mutum ya ciro bakansa ya yi harbi a iska sai ya bugi sarkin Isra'ila a mahaɗar makamansa. Sai Ahab ya ceda mai tuƙa karusarsa, ka juya ka fitar da ni daga filin dãga, domin na sami mummunan rauni sosai." 34 Yaƙi ya yi zafi sosai a wannan rana, ana kuma riƙe da sarkin Isra'ila a cikin karusarsa da kefuskantar Aremiyawa har yamma. Can kusan faɗuwar rana, sai ya mutu.

Sura 19

1 Yehoshafat sarkin Yahuda ya koma gidansa a Yerusalem lafiya. 2 Sai Yehu ɗan Hanani, mai duba yaje ya tare shi ya cewa sarki Yehoshafat, "Ko zaka dinga taimakon mugaye? Ko zaka ƙaunaci maƙiyan Yahweh? Domin wannan, fushi daga Yahweh na kanka. 3 Duk da haka akwai 'yan waɗansu halaye nagari a cikinka, domin kã kawar da sandunan Ashera daga ƙasar, ka kuma sa zuciyarka ga neman Allah." 4 Yehoshafat ya zauna a Yerusalem; ya kuma sake yin tafiya cikin mutanen Biyarsheba zuwa ƙasar duwatsu ta Ifiraimu ya kuma komo da su ga Yahweh, Allah na ubanninsu. 5 Ya sa mahukunta a cikin ƙasar a cikin dukkan tsararrun biranen Yahuda, daga birni zuwa birni. 6 ya ceda mahukuntan, "Ku yi la'akari da abin da zaku yi, domin ba saboda mutum kuke yin hukuncin ba, amma saboda Yahweh; yana tare daku a cikin zartar da hukunci. 7 Yanzu dai, sai ku bar tsoron Yahweh ya zauna a bisanku. Ku yi hankali a lokacin da kuke yin hukunci, domin babu laifofi ga Yahweh Allahnmu, kuma babu wata tara ko karɓar rashawa." 8 Bugu da ƙari, a Yerusalem Yehoshafat ya naɗa waɗansu daga cikin Lebiyawa da firistoci da waɗansu shugabannin kakanni na gidajen Isra'ila, da su gudanar da hukunci domin Yahweh, da kuma sasanta saɓani. Suka zauna a Yerusalem. 9 Ya umarce su, da cewa, "Dole ku yi hidima cikin girmamawa ga Yahweh, da kuma aminci, da kuma dukkan zuciyarku. 10 Duk inda akwai wani saɓani da ya zo gare ku daga ɗan'uwa da kezaune a birninsu, ko dai game da zubar da jini, ko game da dokokin da aka umarta, da sharuɗa da farillai, dole ku gargaɗe su kada su zama da laifi a gaban Yahweh, ko kuma fushi ya sauko maku daku da "yan'uwanku. Wannan zaku yi kuma ba zaku zama da laifi ba. 11 Duba, Amariya babban firist shi ne shugabanku a kan dukkan al'amuran Yahweh. Zebadiya ɗan Isma'ila, shugaban gidan Yahuda, shi ne ke da ragamar duk abin da ya shafi sarki. Hakannan Lebiyawa zasu zama hafsoshi suna yi maku hidima. Ku yi ƙarfin hali ku kiyaye dokokin ku, Bari Yahweh kuma ya kasance da masu aikata nagarta."

Sura 20

1 Sai ya kasance bayan wannan, sai mutanen Mowab da Ammon, da waɗansu Meyunawa suka kawo wa Yehoshafat yaƙi. 2 Sai waɗansu suka faɗa wa Yehoshafat cewa, "Babbar runduna na zuwa găba da kai daga hayin Mataccen Teku, daga Idom. Duba suna nan a Hazezon Tamar," wato Engedi. 3 Sai Yehoshafat ya tsorata ya kuma ƙudurta ya nemi Yahweh. ya yi shelar azumi a cikin dukkan Yahuda. 4 Yahuda ta taru domin neman Yahweh; Suka zo su nemi Yahweh daga dukkan biranen Yahuda. 5 Yehoshafat ya miƙe a cikin taron mutanen Yahuda da Yerusalem, a gidan Yahweh, a gaban sabon harabar. 6 ya ce"Yahweh Allah na ubanninmu, ba kai bane Allah a sama? Ba kai bane mai mulkin dukkan mulkokin al'ummai? Ƙarfi da iko naka ne, domin haka ba wanda zai iya yin tsayayya da kai. 7 Allahnmu ashe ba kai ka kori mazaunan wannan ƙasa ba daga gaban mutanen ka Isra'ila, ka kuma bada ita har abada ga zuriyar Ibrahim? 8 Sun zauna a cikinta suka gina maka wuri mai tsarki a cikinsa da sunanka cewa, 9 'In wata masifa ta taso a kanmu - ko takobin hukunci, ko cuta, ko yunwa - zamu tsaya a gaban wannan gida, da kuma gabanka (domin sunanka na a cikin wannan gida), kuma zamu yi kuka zuwa gare ka a cikin ƙuncinmu, zaka kuma jimu ka kuma cece mu.' 10 Duba yanzu, ga mutanen Ammon, da Mowab, da Tsaunin Seyir waɗanda baka bari mu hallakar da su ba a lokacin da suka fito daga ƙasar Masar; a maimakon haka, Isra'ila suka juya daga wurinsu basu kuma hallaka su ba. 11 Dubi yadda suke sãka mana; suna tafe domin su kore mu daga ƙasar da ka bamu gãdo. 12 Allahnmu, ba zaka hukunta su ba? Domin bamu da ikon yin yaƙi da wannan babbar rundunar da kezuwa domin su yaƙe mu. Ba mu san abin da zamu yi ba, amma mun zuba ido gare ka." 13 Dukkan Yahuda suka tsaya a gaban Yahweh, duk da ƙananansu da matayensu, da yaransu. 14 To a cikin tsakiyar tattaruwar, sai Ruhun Yahweh ya zo kan Yahaziyel, ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yeyel, ɗan Mataniya, Balebi, ɗaya daga cikin 'ya'yan Asaf. 15 Yahaziyel yace, "Ku saurara, ku dukkan Yahuda da mazaunar Yerusalem, da sarki Yehoshafat. Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa maku, ' Kada kuji tsoro; kada ku karaya saboda girman wannan babbar rundunar, domin yaƙin ba naku bane na Allah ne. 16 Dole ne kuje ku yaƙe su gobe. Duba suna zuwa ta mashigin Ziz. Zaku same su a ƙarshen kwari kafin hamadar Yeruwel. 17 Ba zaku bukaci ku yi faɗa ba a wannan yaƙin. Ku tsaya a wurarenku, ku tsaya ku jira, ku ga ceton Yahweh tare daku, Yahuda da Yerusalem. Kada ku tsorata ko ku karaya. Kuje ku hare su gobe, domin Yahweh yana tare daku.'" 18 Yehoshafat ya sunkuyar da kansa ƙasa. Dukkan Yahuda da mazauna Yerusalem suka faɗi a gaban Yahweh, suna yi masa sujada. 19 Da Lebiyawa, na zuriyar Kohatiyawa, suka miƙe suka yabi Yahweh, Allah na Isra'ila, da babbar murya. 20 Da sassafe suka tashi suka tafi hamadar Tekowa. A lokacin da suka fita, Yehoshafat ya tashi tsaye yace, "Ku saurare ni Yahuda da ku mazauna Yerusalem! Ku dogara ga Yahweh Allahnku, zaku sami kafuwa. Ku dogara ga annabawansa, zaku yi nasara." 21 Bayan da ya tuntuɓi mutane, sai ya naɗa waɗanda zasu raira yabo ga Yahweh su ba shi waƙar yabo domin ɗaukakarsa mai tsarki, a lokacin da suka tafi suna tunkarar sojoji, suka ce, "Ku yi godiya ga Yahweh, domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada." 22 Sa'ad da suka fara waƙar yabo, sai Yahweh yasa masu kwanto gãba da mutanen Ammon, da Mowab, da Tsaunin Seyir waɗanda ke zuwa domin su kawo hari ga Yahuda, aka yi nasara da su. 23 Domin mutanen Ammon da Mowab suka fita suka yaƙi mazaunan Tsaunin Seyir, suka karkashe su suka hallakar da su. Bayan sun hallaka mazaunan Tsaunin Seyir. Sai duk suka taimaka wajen hallaka junansu. 24 Sa'ad da Yahuda suka zo su dudduba hamada sai suka dubi sojojin. Duba, sun fãɗi ƙasa matattu; ba wanda ya tsira. 25 Yehoshafat da dukkan mutanensa suka zo domin su kwashi ganima daga gare su, sai suka sami kayayyakin da aka yi watsi da su, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka ɗebar wa kansu, fiye da yadda zasu iya ɗauka. Ya ɗauke su kwana uku kafin su iya kwashe ganimar, domin akwai ta birjik. 26 A rana ta huɗu sai suka taru a kwarin Beraka. A can suka yabi Yahweh, domin haka ake kiran sunan wurin "Kwarin Beraka" har ya zuwa yau. 27 Daga nan sai suka juya, dukkan mutanen Yahuda da na Yerusalem, Yehoshafat kuma yana yi masu jagora, suka sake koma Yerusalem da farinciki, domin Yahweh ya sake sa su suyi murna a kan maƙiyansu. 28 Suka zo Yerusalem zuwa gidan Yahweh da garayu, da molo, da kãkãki. 29 Razanar Allah ta kama dukkan mulkokin al'ummai sa'ad da suka ji Yahweh ya yaƙi maƙiyan Isra'ila. 30 Ta haka mulkin Yehoshafat ya zama da kwanciyar hankali, domin Allahnsa ya ba shi salama a dukkan yankunansa. 31 Yehoshafat ya yi mulkin Yahuda: Yana da shekaru talatin da biyar a lokacin da ya fara sarauta, ya kuma yi mulkin Yerusalem na tsawon shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba, 'yar Shilhi. 32 ya yi tafiya bisa tafarkin Asa, mahaifinsa, bai kuma juya ya barsu ba; ya yi abin da keda kyau a gaban Yahweh. 33 Duk da haka, ba a ɗauke wuraren tuddai ba. Mutanen basu juyar da zukatansu ga Allah na kakanninsu ba. 34 A kan kuma sauran abubuwa game da Yehoshafat, farko da ƙarshe, duba an rubuta su a cikin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a cikin littafin sarakunan Isra'ila. 35 Bayan wannan Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya haɗa kai da Ahaziya, sarkin Isra'ila, wanda ya yi aikin ƙeta sosai. 36 Ya haɗa kai da shi domin ya yi jiragen ruwa domin zuwa Tarshish. Sun kafa jiragen a Eziyon Geba. 37 Daga nan sai Eliyeza ɗan Dodabahu na Maresha, ya yi annabci gãba da Yehoshafat; ya ce"Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Yahweh ya rushe ayyukanka." Sai aka ragargaje jiragen domin kada a iya tafiya.

Sura 21

1 Yehoshafat ya yi barci tare da kakanninsa aka binne shi tare da su a birnin Dauda; Yehoram, ɗansa, ya zama sarki a madadin sa. 2 Yehoram na da 'yan'uwa, ga 'ya'yan Yehoshafat: Azariya, Yehiyel, Zekariya, Azariyahu, Mika'ilu da Shefatiya. Dukkan waɗannan 'ya'yan Yehoshafat ne sarkin Isra'ila. 3 Mahaifinsu ya basu kyautar zinariya da azurfa masu ɗumbin yawa da sauran kayayyaki masu daraja, da ƙayatattun birane a Yahuda, amma sai ya bada gadon sarauta ga Yehoram, saboda shi ne ɗan fari. 4 To lokacin da Yehoram ya gãji mahaifinsa a sarauta ya kuma kafa kansa sosai a matsayin sarki, sai ya karkashe dukkan 'yan'uwansa da takobi, haka kuma da shugabannin Isra'ila da ban da ban. 5 Yehoram na da shekaru talatin da biyu lokacin da ya fara mulkin, ya kuma yi mulki a Yerusalem na tsawon shekaru takwas. 6 ya yi tafiya bisa tafarkin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, domin ya auri ɗiyar Ahab ta zama matarsa sai ya yi mugun abu a gaban Yahweh. 7 Duk da haka Yahweh bai so ya hallakar da gidan Dauda ba saboda alƙawarin da ya yi da Dauda; ya yi alƙawarin cewa kullum zai ba da rai a gare shi da kuma zuriyarsa. 8 A kwanakin Yehoram, Idom ta ɓalle daga mulkin Yahuda, suka kuma naɗawa kansu sarki. 9 Daga nan sai Yehoram da jarumawansa suka ƙetara da karusansa. Da duhu ya tashi ya yaƙi Idomawan da suka kewaye shi da dukkan jarumawan karusansa. 10 Ta haka Idom ta ci gaba da tayar wa Yahuda har wa yau. Libna ita ma sai ta tayar a lokaci guda, domin Yehoram ya rabu da Yahweh, Allah na kakanninsa. 11 Haka kuma, Yehoram ya gina manyan wurare a duwatsun Yahuda yasa mazaunan Yerusalem su yi rayuwa kamar karuwai, ya kuma karkatar da Yahuda. 12 Wasiƙa daga annabi Iliya ta zo ga Yehoram. Cewa, "Wannan shi ne abin da Yahweh, Allah na Dauda mahaifinka, ya ce: Saboda baka yi tafiya bisa tafarkin Yehoshafat mahaifinka ba, baka kuma bi tafarkin Asa sarkin Yahuda ba, 13 amma ka bi tafarkin sarakunan Isra'ila, ka kuma sa Yahuda da mazauna Yerusalem su zama kamar karuwai, kamar yadda gidan Ahab suka yi-saboda kuma ka kashe 'yan'uwanka a cikin iyalin mahaifinka ko mariƙa takobi da suka fi ka shahara- 14 Duba, Yahweh zaya kawo wa mutanenka da matanka da 'ya'yanka da mallakarka babbar annoba. 15 Kai kuma da kanka ka zama da matsananciyar cuta saboda cutar da kecikin hanjinka, har sai hanjinka ya fito waje saboda cutar, kwana bayan kwana." 16 Yahweh ya tayar da ruhun Filistiyawa da na Larabawa gãba da Yehoram waɗanda ke kusa da Kush. 17 Suka kawo wa Yahuda hari, suka washe ta, suka kwashe dukkan wadatarta da suka samu a gidan sarki. Suka kuma kwashe 'ya'yansa da matansa. Basu bar masa ko ɗa ɗaya ba sai dai Yehowahaz, ƙaramin ɗansa. 18 Bayan duk waɗannan, Yahweh ya buge shi a hanjinsa da cuta mara warkewa. 19 Sai ya kasance a lokacin a ƙarshen shekaru biyu, sai hanjinsa ya fito saboda rashin lafiyarsa, sai ya mutu ta wurin matsananciyar cuta. Mutanensa basu yi wata wata domin girmama shi ba kamar yadda suke yi wa kakanninsa. 20 Ya fara sarauta a lokacin da yake da shekaru talatin da biyu; ya yi mulkin Yerusalem na tsawon shekaru takwas, sai ya mutu ba tare da makoki ba. Suka binne shi a birnin Dauda, amma ba a maƙabartar sarakuna ba.

Sura 22

1 Mazauna Yerusalem suka naɗa Ahaziya sarki, wato ƙaramin ɗan Yehoram sarki, a madadinsa, domin rundunonin Larabawa sun kashe dukkan manyan 'ya'yansa. Domin haka Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya zama sarki. 2 Ahaziya na da shekaru ashirin da biyu a lokacin da ya fara sarauta; ya yi mulkin Yerusalem shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya; ita 'yar Omri ce. 3 Shi ma ya bi tafarkin Ahab domin mahaifiyarsa ce ke ba shi shawara a cikin yin ayyukan mugunta. 4 Ahaziya ya yi abin mugunta a gaban Yahweh, kamar yadda gidan Ahab suka yi, domin su ne mashawartansa bayan mutuwar mahaifinsa zuwa hallakarsa. 5 Hakanan ya bi shawararsu; ya yi tafiya tare da Yerom ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, domin su kai hari ga Hazzaiyel, sarkin Aram, a Ramot Gileyad. Aremiyawa suka yi wa Yoram rauni. ` 6 Yoram ya komo domin ya warke daga raunukan da suka ji masa a Rama, lokacin da ya fita ya yi yaƙi da Hazeyel, sarkin Aram. Domin haka Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya tafi can Yezril domin ya ga Yoram ɗan Ahab, domin an raunata Yoram. 7 To an kawo hallakar Ahaziya daga Allah a ziyarar da Ahaziya ya kai wa Yoram. A lokacin da ya isa, sai ya tafi tare da Yehoram domin su kai hari ga Yehu ɗan Nimshi, wanda Yahweh ya zaɓa ya hallakar da gidan Ahab. 8 A lokacin da Yehu ke aiwatar da hukuncin Allah a kan gidan Ahab, sai ya tarar da shugabannin Yahuda da kuma 'ya'yan ɗau'uwan Ahaziya suna yi wa Ahaziya hidima. Sai Yehu ya kashe su. 9 Yehu ya nemi Ahaziya, suka kama shi yana ɓoye a Samariya, sai suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi. Sai suka binne shi, domin sun ce, "Shi ɗan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Yahweh da dukkan zuciyarsa." Domin haka gidan Ahaziya ba shi da sauran iko yin sarautar mulkin. 10 Yanzu bayan Ataliya, ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta kashe dukkan 'ya'yan sarauta a cikin gidan Yahuda. 11 Amma Yehosheba, ɗiyar sarki, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya a asirce ta ware shi da ban da sauran 'ya'ya maza na sarki waɗanda ake shirin kashewa. Ta sa shi da kuma mai renon shi a ɗakin kwana. Da haka Yehosheba 'yar sarki Yehoram, matar Yehoida firist (domin ita 'yar'uwar Ahaziya ce) sai ta ɓoye shi daga Ataliya domin kada Ataliya ta kashe shi. 12 Yana tare da su a gidan Allah har tsawon shekaru shida, bayan Ataliya ta yi mulkin ƙasar.

Sura 23

1 A shekara ta bakwai, Yehoyida ya nuna ƙarfinsa ya shiga alƙawari da shugabannin ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ila ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, Ma'asiya ɗan Adayiya, da Elishafat ɗan Zikri. 2 Suka zazzaga Yahuda suka tattara Lebiyawa daga dukkan biranen Yahuda, da kuma shugabannin kabilu na gida-gidan Isra'ila sai suka zo Yerusalem. 3 Dukkan taron mutanen suka yi alƙawari da sarki a gidan Allah. Yehoyida ya ce da su, Duba ɗan sarki ne zai yi mulki, kamar yadda Yahweh ya faɗi game da zuriyar Dauda. 4 Wannan ne abin da dole zaku yi: kashi uku na firistoci da Lebiyawa da suka zo yin hidima a ranar Asabar, zasu zama masu tsaro a ƙofofi. 5 Kashi uku kuma su tsaya a fadar sarki, kashi uku kuma a wurin da aka kafa harsashin ƙofa. Dukkan mutane zasu kasance a harabar gidan Yahweh. 6 Kada ku bar kowa ya shiga haikalin Yahweh sai dai firistoci da Lebiyawan da keyin hidima kai ɗai. Zasu shiga domin an keɓe su, amma sauran dole ne su yi biyayya da umarnin Yahweh. 7 Dole ne Lebiyawa su kewaye sarki, kowanne na riƙe da makami a hannunsa. Duk wanda ya shigo gidan kuma sai a kashe shi. "Ku tsaya wurin sarki a lokacin da ya shigo da kuma lokacin da ya fita." 8 To sai Lebiyawa da dukkan Yahuda suka yi kamar yadda Yehoyida firist ya umarta. Kowannen su ya ɗauki mutanensa, masu zuwa domin su yi hidima a ranar Asabar, da kuma waɗanda ba zasu yi hidima a ranar Asabar ba, domin Yehoyida firist bai sallami kowacce runduna ba tukuna. 9 Sai Yehoyida firist ya kawo masu da manya da ƙananan garkuwoyi da sarki Dauda ya ajiye a gidan Allah ya ba kwamandojin. 10 Yehoyida ya sanya dukkan sojojin, kowanne mutum da makaminsa a hannusa, daga sashen dama na haikalin zuwa sashen hagu na haikalin, kusa da bagadin da kuma haikalin, zagaye da sarkin. 11 Sai suka fito da ɗan sarki suka sa masa rawani suka kuma bashi kundin dokoki na alƙawari, suka naɗa shi sarki daga nan sai Yehoyida firist da 'ya'yansa suka keɓe shi ya zama sarki suka ce, "Ranka ya daɗe sarki." 12 Lokacin da Ataliya ta ji hayaniyar mutanen suna yabon sarki sai ta zo cikin mutane ta shiga haikalin, 13 ta na dubawa sai ga sarki tsaye kan dakalin sarauta riƙe da sandar sarauta a ƙofar shiga, ga kuma kwamandoji da masu hura kakaki kewaye da sarki. Dukkan mutanen ƙasar na murna suna busa kakaki, mawaƙa suna kaɗa kayan kaɗe-kaɗe suna kuma bida waƙoƙin yabo. Sai Ataliya ta keta tufafinta tana cewa, "Cin amana! Cin amana!" 14 Daga nan sai Yehoyida ya ce da kwamandojin ɗari-ɗari su zo su fito da ita a kashe ta da takobi tare da duk waɗanda suka biyo ta. domin firist ya ce, "Kada ku kashe ta a cikin gidan Yahweh". 15 To sai suka buɗa mata hanya ta bi ta Ƙofar Doki zuwa gidan sarki a can suka kashe ta. 16 To sai Yehoaida da sarki da dukkan mutanen suka yi alƙawari cewa za su zama mutanen Yahweh. 17 Sai dukkan mutanen suka tafi gidan Ba'al suka rushe shi, suka ɓaɓɓalle bagadin Ba'al da kuma gunkinsa. Suka kashe matan firist na Ba'al a gaban waɗanan bagadan. 18 Yehoyida ya zaɓi shugabannin haikalin Yahweh ta wurin jagorancin firistoci, da ke Lebiyawa waɗanda Dauda ya sa domin su yi hidima a gidan Yahweh, domin su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh tare da farinciki kamar yadda Dauda ya yi umarni, kamar yadda ya ke a rubuce a shari'ar musa. 19 Yehoyida ya sa 'yan tsaro a ƙofar haikalin Yahweh, domin kada duk wani marar tsarki ta kowanne fanni ya shiga. 20 Yehoyida ya kwashi kwamandoji da mutane ma su daraja da gwamnoni tare da shi da dukkan mutanen ƙasar. Ya kawo sarki daga gidan Yahweh, mutane suka shiga ta babbar ƙofa zuwa gidan sarki daga gidan suka zaunar da sarki akan gadon sarauta. 21 domin haka dukkan mutanen ƙasar suka yi murna birnin kuma ya sami kwanciyar hankali. Ataliya kuma aka kashe ta da takobi.

Sura 24

1 Yowash yana da shekaru bakwai lokacin da ya fara mulki, ya yi mulki na tsawon shekaru arba'in a Yerusalem, sunan mahaifiyarsa Zibiya, daga Biyasheba. 2 Yoash ya yi abin da kenagari a gaban Yahweh a dukkan kwankin Yehoyida, firist. 3 Yehoyida ya aura masa mata biyu, sai ya zama uba na 'ya'ya maza da mata. 4 Bayan wannan Yowash ya yanke shawarar gyara gidan Yahweh. 5 Sai ya tara firistoci da Lebiyawa ya ce da su, "Kowacce shekara sai ku je cikin dukkan biranen Yahuda ku tattaro kuɗin da za a gyara gidan Allahnku daga dukkan mutanen Isra'ila. Ku tabbata kun fara yanzu." Lebiyawa basu yi komai ba da farko. 6 Sai sarki ya kirawo Yehoyida babban firist ya ce da shi, "Meyasa baka bukaci Lebiyawa su kawo haraji daga Yahuda da kuma Yerusalem ba kamar yadda Musa bawan Yahweh da kuma taron Isra'ila suka yi ba domin rumfar alƙawarin dokoki ba?" 7 Domin 'ya'ya maza na Ataliya wannan muguwar mata, sun rushe gidan Allah suka kuma kwashe dukkan kayayyaki masu tsarki na gidan Yahweh suka kai suka bayar ga Ba'al. 8 To sai sarki ya umarta, suka yi taska suka sa ta daga wajen ƙɔfar shiga gidan Yahweh. 9 Sai suka yi shela a cikin dukkan Yahuda da Yerusalem domin mutane su biya haraji domin gidan Yahweh harajin da Musa bawan Allah ya sa wa Isra'ila a jeji. 10 Dukkan shugabanni da dukkan mutane suka yi murna suka kawo kuɗi suka sa a taska har sai da suka cika ta. 11 To bayan an kawo taskar wurin fadawan sarki ta hannun Lebiyawa duk lokacin da suka ga taskar ta cika da kuɗi sosai a cikinta, marubutan sarki da manyan firistoci su kan zo, su ɗauke ta su kwashe sai su mayar da ita wurin da ta ke. Haka suka dinga yi kowacce rana, suka dinga tara kuɗaɗe masu yawa. 12 Sai sarki da Yehoyida suka ba da kuɗaɗen ga masu yin aikin hidima a gidan Yahweh. Waɗannan mutanen suka yi hayar masu aikin dutse da masu aikin katako domin su komo da gidan Yahweh, haɗe da masu aikin ƙarfe da tagulla. 13 To sai ma'aikatan, suka gudanar da aikin ta hannuwansu; suka tayar da gidan Yahweh suka komar da shi kamar yadda ya ke da farko, suka kuma ƙarfafa shi. 14 Bayan sun gama sai suka mayar da sauran kuɗin ga sarki da kuma Yehoyida. Wannan kuɗin da shi aka yi aikin kujerun gidan Yahweh, da kayayyaki wanda aka mora domin karɓar baiko- cokula da kayayyaki na zinariya da azurfa. Suka yi ta miƙa baye-baye na ƙonawa a gidan Yahweh a dukkan kwanakin Yehoyida. 15 Yehoyida ya tsufa yana da cikkakun kwanaki, ya mutu yana da shekaru 130. 16 Suka binne shi a birnin Dauda a cikin sarakuna, saboda ya yi abu mai kyau a Isra'ila, a gaban Allah da kuma gidan Allah. 17 To yanzu kuma bayan mutuwar Yehoyida, mutanen Yahuda suka zo domin su nuna karramawa ga sarki. Sai sarki ya saurare su. 18 Suka yi watsi da gidan Yahweh, Allah na kakanninsu suka bautawa gumakan Ashera da siffofinta. Fushin Allah ya auko kan Yahuda da Yerusalem saboda wannan aikin na su mara dacewa. 19 Duk da haka ya aiko annabawa gare su domin su sake komo da su gare shi, annabawan suka ce Yahweh na gãba da mutanen, amma suka ƙi saurara. 20 Sai Ruhun Allah ya zo kan Zakariya ɗan Yehoyida, firist; Zakariya ya miƙe a sama da mutanen ya ce da su, "Allah ya faɗi wannan: Me yasa ku ke aikata laifofi ga dokokin Yahweh, domin kada ku azurta? Da yake kun yi watsi da Yahweh, shima ya yi watsi da ku. 21 "Amma suka yi masa maƙarƙarshiya; sarki ya umarta a jejjefe shi da duwatsu a dandalin gidan Yahweh. 22 Ta irin wannan hali Yowash, sarki, ya jahilci kirkin da Yehoyida mahaifin Zakariya ya yi masa. A memakon haka ya kashe ɗan Yehoyida. Lokacin da Zakariya ke mutuwa ya faɗi cewa, "Dãma Yahweh ya ga wannan ya kuma sa ka bada lissafi." 23 To bayan kusan ƙarshen shekara, sai sojojin Aram suka tasarwa Yowash. Suka zo Yahuda da Yerusalem; suka kashe dukkan shugabannin mutane suka kuma kwashe dukkan ganimarsu zuwa ga sarkin Damaskus. 24 Sojojin Armeniyawa kuma suka zo da ƙaramar rundunar soja, amma Yahweh ya ba su nasara kan babbar rundunar soja, domin Yahuda ta yi watsi da Yahweh na kakanninsu. Allah na kakanninsu. Da haka Armeniyawa suka kawo hukunci a kan Yowash. 25 A lokacin da Armeniyawa suka fice, an yi wa Yowash mummunan rauni. Bayinsa suka yi masa maƙarƙashiya saboda ya kashe Zakariya ɗan Yehoyida, firist. Suka kashe shi a kan gadonsa; suka binne shi a birnin Dauda, amma ba a maƙabartar sarakuna ba. 26 Waɗannan su ne mutanen da suka yi masa maƙarƙashiya: Zabad ɗan Shimeyat mace Ba'ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit, mace Bamowabiya. 27 To lissafin 'ya'yansa, da kuma annabci mai muhimmanci da aka yi a kansa, da kuma sake gina haikalin Allah, duba an rubuta su a cikin Littafin shashi akan sarakuna. Sai Amaziya ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.

Sura 25

1 Amaziya yana da shekaru ashirin da biyar a lokacin da ya fara sarauta; ya yi sarauta ta shekaru ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddan ta Yerusalem. 2 ya yi abin da kemai kyau a gaban Yahweh, amma ba da cikakkiyar miƙa zuciya ba. 3 Sai ya zamana nan da nan bayan mulkinsa ya kafu sai ya kashe bayin da suka kashe mahaifinsa, sarki. 4 Amma bai kashe 'ya'yan waɗanda suka yi kisan kan ba. Amma ya yi kamar yadda aka rubuta cikin shari'ar Musa, kamar yadda Yahweh ya umarta, "Dole ne iyaye ba zasu taɓa mutuwa ba saboda 'ya'ya, ko 'ya'ya su mutu saboda iyayensu ba, a maimakon haka, kowa zai ɗauki alhakin zunubinsa." 5 Bugu da ƙari, Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya yi masu ƙidaya bisa ga kabilar kakanninsu, a ƙarƙashin jagorancin shugabannin dubu-dubu da na ɗari-ɗari da dukkan Yahuda da Benyamin. Ya ƙirga su daga 'yan shekaru ashirin zuwa sama, ya sami mutane kusan 300,000 zaɓaɓɓu domin yaƙi waɗanda zasu iya riƙe mashi da garkuwa. 6 Hakannan ya yi hayar mayaƙa 100,000 daga Isra'ila akan kuɗi azurfa ɗari ɗaya. 7 Amma sai mutumin Allah ya zo gunsa ya ce masa "Sarki kada ka bari mutanen Israi'la domin Yahweh ba ya tare da Isra'ila - ba ko ɗaya daga cikin mutanen Ifiraimu, 8 Amma ko dama a ce kana da ƙarfi na yi yin yaƙin Ubangiji zai rikirtar da kai a gaban maƙiya, domin Yahweh ya na da ikon taimako yana kuma da ikon rushewa." 9 Amaziya ya ce da mutumin Allah, "Amma me za muyi da talanti ɗari dana ba sojojin Isra'ila?" Mutumin Allah ya amsa da cewa "Yahweh zai iya baka fiye da wannan." 10 To sai Amaziya ya rarraba sojojin da suka zo daga Ifiraimu; ya sake aika su gida. Fushinsu ya yi zafi sosai a kan Yahuda, suka koma gida da matsanancin fushi. 11 Amaziya ya yi ƙarfin hali har ya tafi da mutanensa zuwa Kwarin Gishiri; a can ya karkashe sojojin Seyir guda dubu goma. 12 Sojojin Yahuda kuma suka kama sojoji duba goma da ransu. Suka kai su can ƙonƙolin tsauni suka tutturo su ƙasa duk suka kakkarye. 13 Amma sojojin da Amaziya ya komar da su domin kada su je yaƙi tare da shi, suka je suka kai hari a Yahuda daga Samariya har zuwa Betahoron. Suka kashe mutane dubu uku suka kuma kwashi ganima mai yawa. 14 Sai ya zamana, bayan Amaziya ya dawo daga kisan Idomawa, sai ya kwaso allolin Seyir ya maida su allolinsa. Ya russuna masu ya kuma ƙona masu turare. 15 Domin haka fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan Amaziya. Ya aika masa da saƙo ta hannun annabi cewa, "Meyasa ka je ka tuntuɓi allololin da basu iya ceton mutanensu daga hannunka ba?" 16 To lokacin da annabin keyi masa magana, sarki ya ce da shi, "Ko mun maida kai mashawarcin sarki ne? Ka bari! donme za a kashe ka?" Daga nan sai annabin ya bari ya ce na sani Allah ya yi ƙudiri na hallakar da kai saboda ka yi waɗannan abubuwa ba ka kuma ji shawarata ba." 17 To sai Amaziya sarkin Yahuda ya tuntuɓi mashawartansa ya aika da 'yan saƙo zuwa ga Yehowash ɗan Yehoyahaz ɗan Yehu, sarkin Isra'ila, cewa, "Ka zo mu sadu da juna fuska da fuska a cikin yaƙi." 18 Amma Yehowash sarkin Isra'ila ya aika da 'yan saƙo ga Amaziya sarkin Yahuda, cewa, "Ɗan ƙaramin sassabe da kea Lebanon ya aika da saƙo ga itacen sida a Lebanon, cewa, "Ka bada 'yarka ga ɗana a matsayin mata; amma sai dabbar daji a Lebanon ta zo ta tattake ɗan sassaben. 19 Ka kuma ce, duba na rugurguje Idom; amma zuciyarka ta kumburaka. Ka yi taƙama da ɗaukakarka, amma ka tsaya a gida, gama donme zaka jawo wa kanka masifa da faɗuwa, kai da Yahuda tare da kai?" 20 Amma Amaziya ba zai saurara ba, domin wannan al'amarin daga Allah ne, domin ya miƙa Yahuda ga hannun maƙiyanta, domin sun nemi shawara daga allolin Idom. 21 To sai Yowash sarkin Isra'ila ya kai hari; shi da Amaziya, sarkin Yahuda, suka gamu fuska da fuska a Betshemesh, wadda take mallakar Yahuda. 22 A ka ragargaza Yahuda a idon Isra'ila kowa kuma ya tsere gida. 23 Yehowash, sarkin Isra'ila, ya kame Amaziya ɗan Yehowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, a Betshemesh. Ya kawo shi Yerusalem daga Ifiraimu ya kuma rushe ganuwar Yerusalem daga ƙofar Ifiraimu zuwa kusurwar ƙofar, tsawon kamu ɗari huɗu ne. 24 Ya kwashe dukkan zinariya da duk abubuwan da ya iske a gidan Allah da Obida da Idom, da kuma abubuwa masu daraja na gidan sarki, tare da kamammun yaƙi, sai ya koma Samariya. 25 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuda ya yi mulki na tsawon shekaru sha biyar yana mulkin Yahuda bayan mutuwar Yehoyash, ɗan Yehoyahaz, sarkin Isra'ila. 26 Game da sauran ayyukan Amaziya na farko da na ƙarshe duba an rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda da Isra'ila. 27 Yanzu tun daga lokacin da Amaziya ya juya wa Yahweh baya, sai suka fara shirya masa maƙarƙashiya a Yeruslem. Sai ya gudu zuwa Lakish suka kashe shi a can. 28 Suka komo da shi a kan dawakai suka binne shi a maƙabartar kakanninsa a birnin Yahuda.

Sura 26

1 Dukkan mutanen Yahuda suka ɗauki Uziya lokacin ya na ɗan shekara sha shida suka naɗă shi sarki a madadin babansa Amaziya. 2 Shi ne wanda ya sake gina Ilat ya sake komo da ita Yahuda. Bayan wannan sai ya mutu tare da kakanninsa. 3 Uziya yana da shekara sha shida lokacin da ya fara sarauta. ya yi mulki na tsawon shekaru hamsin da biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya; ita daga Yerusalem ce. 4 ya yi abin da kemai kyau a gaban Yahweh, ya bi misalin mahaifinsa, Amaziya, ta kowanne abu. 5 Yasa kansa ga tafarkin neman Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya bashi dokoki na yin biyayya ga Allah. Da yake ya nemi Yahweh sai Yahweh ya wadata shi. 6 Sai Uziya ya fita ya je ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe ganuwar birnin Gat da Yamna da ta Ashdod; ya gina birane a ƙasar Ashdod da` kuma cikin Filistiyawa. 7 Allah ya taimake shi gãba da Filistiyawa da Larabawan da suka zauna a Gurba'al da kuma Maunayawa. 8 Ammoniyawa kuma su ka biya haraji ga Uziya ƙarfinsa kuma ya kai har Masar, domin yana ƙara samun iko sosai. 9 Bugu da ƙari kuma Uziya ya gina hasumiya a Yerusalem akan Ƙofar Kwana, a Ƙofar Kwari, ya kuma ƙayata su. 10 Ya kuma gina hasumiyar tsaro a jeji ya kuma haƙa rijiyoyi da yawa domin yana da dabbobi masu yawa a kwarurruka da kuma a saura. Yana da manoma da masu kula da itatuwan inabi a ƙasa mai duwatsu da kuma a filaye masu 'ya'yan itatuwa, domin ya ƙaunaci aikin gona sosai. 11 Kuma Uziya yana da mayaƙan sojoji da kezuwa yaƙi a ƙungiyance bisa yadda aka rarraba su bisa ga yawansu yadda Yeyil marubuci da Ma'asiya, hafsa, ƙarƙashin ikon Hananiya ɗaya daga ciki kwamandojin sarki. 12 Dukkan yawan shugabannin mayaƙa na kabilu shi ne 2600. 13 A karƙashin ikonsu kuma akwai soja guda 307,500 da keyin yaƙi da iko mai ƙarfi domin su taimaki sarki yaƙi da maƙiya. 14 Uziya ya shirya su - domin su zama da dukkan garkuwoyi suturun yaƙi da kwari da kibaw da duwatsun majajjawa. 15 A Yerusalem ya yi masu aikin ƙira da mutane masu fasaha suka samar su kasance a kan hasumiyoyin da kuma filayen dãga, domin su dinga harba kibiyoyi da kuma manyan duwatsu. Ikonsa ya kai har ƙasashe masu nisa, domin ya sami taimako sosai har sai da ya zama da iko sosai. 16 Amma bayan Uziya ya sami iko sosai sai zuciyarsa ta kumbura domin haka ya yi abin da ba shi da kyau; ya yi wa Yahweh Allahnsa zunubi, domin ya tafi gidan Yahweh domin ya ƙona turare akan bagadin ƙona turare. 17 Sai Azariya firist ya bi shi tare da shi kuma akwai firistocin Yahweh guda tamanin, waɗanda mutane ne masu ƙarfin hali. 18 Suka yi tsayayya da sarki Uziya, suka ce da shi, "Uziya ba aikinka bane ka ƙona turare, amma aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna waɗanda aka keɓe su ƙona turare. Ka fita daga wuri mai tsarki, domin kana da rashin aminci kuma Yahweh Allah ba zai girmamaka ba" 19 Sai Uziya ya yi fushi. yana riƙe da sandan tasar ƙona turare a hannunsa. Lokacin da yake fushi da firistoci, sai kuturta ta kama shi a goshi a gaban firistocin a gidan Yahweh, a gefen bagadin ƙona turare. 20 Sai Azariya da dukkan firistoci suka duba, sai, suka ga ya zama kuturu a goshinsa. Sai suka yi sauri suka fitar da shi daga can. Hakika, shima ya gaugauta fita, domin Yahweh ya buge shi. 21 Sarki Uziya ya zama kuturu har ya zuwa randa ya mutu, ya kuma zauna a keɓaɓɓen gida saboda ya zama kuturu, domin an fitar da shi daga gidan Yahweh. Ɗansa, Yotam, ya zama mai kula da gidan sarki, ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar. 22 Game kuma da sauran abubuwa akan Uziya farko da ƙarshe, an rubuta su a cikin abin da annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta. 23 Sai Uziya ya yi barci tare da kakanninsa aka binne shi a maƙabartar sarakuna, domin sun ce, "Shi kuturu ne." Yotam, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.

Sura 27

1 Yotam yana da shekaru ashirin da biyar lokacin da ya fara mulki; ya yi mulki na shekaru sha shida a Yerusalem, sunan mahaifiyarsa Yerusha; ita ɗiyar Zadok ce. 2 Ya yi abin da kemai kyau a idon Yahweh, ya bi gurbin mahaifinsa Uziya ta kowanne abu. Ya kuma ƙi shiga wuri mai tsarki na Yahweh, amma duk da haka mutane basu daina aikin mugunta ba. 3 Ya gina ƙofar sama ta gidan Yahweh, akan tsaunin Ofel kuma ya yi gine-gine masu yawa. 4 Ya kuma yi gine-gine a ƙasa mai duwatsu ta Yahuda, a cikin daji kuma ya gina tsararrun wurare da hasumiyoyi. 5 Ya kuma yi yaƙi da mutanen Amon ya kuma cinye su. A wannan shekarar, dai mutanen Amon suka bashi talanti ɗari na zinariya, da awo goma na alkama, da awo goma na riɗi, haka mutanen Amon suka riƙa ba shi a shekara ta biyu da ta uku. 6 Sai Yotam ya zama da iko sosai saboda ya yi tafiya da ƙarfi tare da Yahweh Allahnsa. 7 Game kuma da sauran abubuwa game da Yotam, da dukkan yaƙe-yaƙensa, duba, an rubuta su a cikin littafin sarakunan Isra'ila da Yahuda. 8 Yana da shekaru ashirin da biyar a lokacin da ya fara mulki, ya yi mulki a Yerusalem na tsawon shekaru sha shida. 9 Yotam ya yi barci tare da kakanninsa, aka binne shi a birnin Dauda. Ahaz, ɗansa, ya gaje shi a sarauta.

Sura 28

1 Ahaz na da shekaru ashirin ne sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki na shekara goma sha shida a Yerusalem. Bai yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh ba, kamar yadda Dauda kakansa ya yi, 2 Maimakon haka, ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra'ila; ya kuma ƙera zubin ƙarfe domin Ba'al. 3 Bugu da ƙari, ya ƙona turare a ƙwarin Ben Hinnom kuma yasa 'ya'yansa cikin wuta, bisa ga ayyukan ɓautar gumaka na mutanen da Yahweh ya kora daga ƙasarsu kafin mutanen Isra'ila. 4 ya yi hadaya da ƙona turare a wuraren bisa da kan tuddai da ƙarƙashin kowanne koren itace. 5 Saboda haka Yahweh Allahn Ahaz, ya bada shi ga hannun sarkin Aram. Aramiyawan suka buge shi kuma suka ɗauke daga gare shi gagarumin taron ɗaurarru, aka tafi da su Damaskus. Ahaz ma aka bada shi ga hannun sarkin Isra'ila wanda ya buge shi da mummunar kisa. 6 Gama Pekah ɗan Remaliya a rana ɗaya, ya kashe sojoji Yahuda 120,000, dukkansu maza masu ƙarfin hali ne, saboda sun yashe da Yahweh, Allahn kakanninsu. 7 Zikiri, mutum mai ƙarfi daga Ifraimu, ya kashe Ma'asiyya ɗan sarki, Azirikam, shugaban făda da Elkana, wanda ke bin sarki a muƙami. 8 Mayaƙan Isra'ila sun ɗauki kãmammu daga danginsu mata 200,000 da 'ya'ya maza da mata. Suka kuma kwaso ganima da yawa, wadda suka komo da su Samariya. 9 Amma akwai wani annabin Yahweh a wurin, sunansa Oded. Ya je ya sadu da mayaƙan da kezuwa Samariya. Ya ce masu, "Saboda Yahweh, Allahn kakanninku, na fushi daYahuda, ya bada su ga hannun ku. Amma kuka yanka su cikin harzuƙan da ta kai samma. 10 Yanzu kun yi niyar ku ajiye maza da matan Yahuda da Yerusalem kamar bayinku. Amma ba ku da laifin zunubanku ga Yahweh Allahnku? 11 To yanzu, ku saurare ni: Ku mayar da kamammun, waɗanda kuka ɗauko cikin naku 'yan'uwan, gama zafin fushin Yahweh na kanku." 12 Sa'annan waɗansu shugabannin mutanen Ifraimu- Azariya ɗan Yohanan da Berakiya ɗan Meshilemot da Yehizkiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka taso gãba da waɗanda suka dawo daga yaƙin. 13 Suka ce da su, "Kada ku kawo kamammun nan, gama kunyi niyar wani abu da zai kawo wa kanmu zunubi ga Yahweh, ya kuma ƙara a kan zunubanmu da laifofinmu, gama laifofinmu na da yawa, kuma akwai fushi mai zafi a kan Isra'ila." 14 Sai mayaƙan suka bar kamammun da ganimar a gaban shugabannin da dukkan taron. 15 Mutanen da aka kira sunansu suka tashi suka ɗauki kãmammun, suka suturad da dukkan waɗanda ke a tsirance cikinsu tare da ganimar. Suka suturad da su suka basu takalma. Suka basu abinci su ci su sha. Suka yi jinyar masu raunuka kuma suka sa masu rauni a kan jakuna. Suka komo da su ga iyalansu a Yeriko, (wadda ake kira Birnin Dabino). Sa'annan suka koma Samariya. 16 A wancan lokacin sarki Ahaz ya aiki manzanni zuwa sarakunan Assiriya domin neman su taimake shi. 17 Gama Idomawa sun sake kawo wa Yahuda hari, suna ɗaukar kamammu suna tafiya da su. 18 Filistiyawa kuma sun mamaye biranen da keƙwararru da na Negev ta Yahuda. Suka ɗauki Beth Shemesh, da Aijalon, da Gederot, da Soko tare da ƙauyukanta, da Timna tare da ƙauyukanta, da kuma Gimzo tare da ƙauyukanta. Suka tafi su zauna a wuraren. 19 Gama Yahweh ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz, sarkin Isra'ila; domin ya yi mugunta a Yahuda kuma ya yi wa Yahweh zunubi mai nauyi. 20 Tiglat Filesar, sarkin Assiriya, ya zo wurinsa ya dame shi maimakon ya ƙarfafa shi. 21 Domin Ahaz ya ɗebo kaya daga gidan Yahweh da gidajen sarki da shugabanni, ya bada abubuwa masu daraja ga sarakunan Assiriya. Amma yin hakan bai sa yaci riba ba. 22 Wannan sarki Ahaz kuma ya yi zunubi ƙwarai ga Yahweh a lokacin wahalarsa. 23 Gama ya yi wa allolin Damaskus hadaya, allolin da suka kada shi. Ya ce, "Saboda allolin sarakunan Aram sun taimaka masu, zan yi masu hadaya, don su taimake ni." Amma su suka zama masa dalilin lalacewa da dukkan Isra'ila. 24 Ahaz ya tattara kayan ɗaki na gidan Allah ya datse su gunduwa-gunduwa. Ya ƙulle kofofin gidan Yahweh sai ya yi wa kansa bagadai a dukkan lungunan Yerusalem. 25 A kowanne birni a Yahuda ya yi wuraren tuddai na ƙone hadaya ga waɗansu alloli. Ya harzuƙa Yahweh, Allahn kakaninsa, ga fushi. 26 Yanzu sauran aikinsa, da dukkan hanyoyinsa, na farko dana karshe, Duba, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila. 27 Ahaz ya kwanta da kakanninsa, kuma suka binne shi a birnin, a Yerusalem, amma ba su kawo shi cikin hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.

Sura 29

1 Hezekiya ya fara mulki a sa'ad da yake da shekaru ashirin da biyar da haifuwa; ya yi mulki shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Abijah; ita ɗiyar Zakariya ce. 2 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh kamar yadda mahaifinsa Dauda ya yi. 3 A shekara ta farko na mulkinsa, A wata na farko, Hezekiya ya ɓuɗe ƙofofin Gidan Yahweh ya gyaggyara su. 4 Ya kawo firistoci da Lebiyawa, ya tattaro su a farfajiyar gefen gabas. 5 ya ce da su, "Ku saurare ni, ku Lebiyawa! Ku keɓe kanku, ku kuma keɓe gidan Yahweh, Allahn kakanninku, ku cire ƙazamci daga wuri mai tsarki. 6 Gama kakanninmu sun kauce daga hanya suka yi mugun abu a fuskar Yahweh Allahnmu; suka yashe shi, suka juye fuskarsu daga wurin da Yahweh ke zamne, kuma suka juya ma wurin baya. 7 Haka kuma suka kukkulle ƙofofin rumfuna suka kakkashe wutan fitilun; basu ƙona turare ko miƙa baye-baye na ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra'ila ba. 8 Saboda haka fushinYahweh ya faɗo wa Yahuda da Yerusalem, kuma yasa suka zama abin razana da tsoro da ba'a, kamar yadda ku ke gani da idanunku. 9 Wannan shi yasa ubaninmu suka faɗi ta kaifin takobi, kuma 'ya'ya mazanmu da 'ya'ya matanmu da matayenmu suke cikin bautar talala. 10 Yanzu kuwa yana zuciyata in yi alƙawari da Yahweh, Allah na Isra'ila, saboda zafin fushinsa ya juya daga auko mana. 11 'Ya'yana maza kada ku zama da ragwanci yanzu, gama Yahweh ya zaɓe ku ku tsaya a gabansa, kuyi masa sujada, ku kuma zama barorinsa ku ƙona turare." 12 Sa'annan Lebiyawa suka tashi: Mahat ɗan Amasai da Yowel ɗan Azariya, na mutanen Kohatawa; da mutanen Merari, wato Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yahalelel; da Gershonawa, wato Yowa ɗan Zimma, da Iden ɗan Yowa; 13 na 'ya'yan Elizafan, Shimri da Yewuyel; dana 'ya'yan Asaf wato Zekariya da Mataniya; 14 na 'ya'yan Heman, Yehuwel da Shimei; da na 'ya'yan Yedutun wato Shemayya da Uziyel. 15 Suka tattara 'yan'uwansu maza suka tsarkake kawunansu, sai suka shiga ciki, kamar yadda sarki ya umarta, biye da maganar Yahweh, a tsabtace gidan Yahweh. 16 Firistocin suka je cikin gidan Yahweh domin su tsabtace shi suka fitar da dukkan kazamtar da suka samo a haikalin Yahweh, suka zuba a harabar gidan. Sai Lebiyawa suka kwashe ta suka kai waje zuwa rafin Kidron. 17 Sai suka fara aikin tsarkakewa a rana ta fari a watan ɗaya. A rana ta takwas ga wata suka kai shirayin Yahweh da aikin, Sa'annan bayan kwana takwas kuma suka tsarkake gidan Yahweh. A ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama. 18 Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya, a cikin fada, suka ce, "Mun tsabtace haikalin Yahweh dukka da bagadin baye-bayen ƙonawa tare da dukkan tasoshi, da kayayyaki, da teburan gurasar kasancewa, da dukkan kayayyakin da suke ciki. 19 Saboda haka muka shirya muka kuma tsarkake dukkan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar sa'ad da ya yi aikin rashin aminci a lokacin da yake mulki. Duba, su na nan a gaban bagadin Yahweh." 20 Sa'annan sarki Hezekiya ya tashi da sassafe ya tattara shugabanin birnin; ya haura can zuwa gidan Yahweh. 21 Suka kawo bijimai bakwai da raguna bakwai da 'yan raguna bakwai da bunsura bakwai a matsayin baikon zunubi masarauta da wuri mai tsarki, domin kuma Yahuda. Sai ya umarci firistioci, wato 'ya'yan Haruna maza, su miƙa su a kan bagadin Yahweh. 22 Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a bagadin. Suka yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagadin; hakanan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagadin. 23 Suka kawo bunsuran yin hadaya domin zunubi a gaban sarki da taron jama'a; suka ɗora hannuwansu a kansu. 24 Sai firistoci suka yankasu suka yi hadaya domin zunubi da jinin a bagadin domin ayi kafara saboda dukkan Isra'ila, gama sarki ya umarta ayi baiko na ƙonawa da baiko domin zunubi saboda dukkan Isra'ila. 25 Sai Hezekiya ya sanya Lebiyawa a gidan Yahweh tare da kuge da molaye da garayu. Suka jerasu bisa ga umarnin Dauda, da na Gad, mai gani na sarki, da annabi Nathan, gama umarnin daga wurin Yahweh ya zo ta wurin annabawansa. 26 Lebiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dauda, firistoci kuwa suna rike da ƙahonni. 27 Sai Hezekiya ya bada umarni a miƙa baiko na ƙonawa a bisa bagadin. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa sai waƙa ga Yahweh ma ta fara tasowa tare da busa ƙaho da sauran kayan kiɗe-kiɗe dana bushe- bushe na Dauda sarkin Isra'ila. 28 Dukkan taron suka yi sujada. mawaƙa suka raira waƙa, masu ƙahonni su ka yi ta busawa; Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa. 29 Bayan da aka gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukkan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada. 30 Bugu da ƙari, sarki Hezekiya, tare da shugabanin suka umarci Lebiyawa su raira waƙar yabo ga Yahweh da kalmomin Dauda da na Asaf mai gani. Suka raira wakokin yabo tare da murna, suka sunkuya suka yi sujada. 31 Sai Hezekiya ya ce, "yanzu dai kun tsarkake kanku ga Yahweh. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a cikin gidan Yahweh. Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, kuma dukkan waɗanda suka yi niya sun kawo hadayan ƙonawa. 32 Jimilar hadayu na waɗanda taron suka kawo su ne bijimai saba'in da raguna ɗari da 'yan raguna ɗari biyu. waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Yahweh. 33 Tsarkakakkun baye-bayen kuwa bijimai ɗari shida da tumaki dubu uku ne. 34 Amma firistocin kima ne don haka suka kasa feɗe dukkan dabbobin da za a miƙa su baye-baye na ƙonawa, sai 'yan'uwansu, Lebiyawa, suka taimake su har aka gama aikin kamin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. gama Lebiyawan su na la'akari da tsarkake kansu fiye da firistocin. 35 Bugu da ƙari, akwai hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi; suka aikatu da kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowacce hadaya ta ƙonawa. Da haka aka maido da hidimar gidan Yahweh. 36 Hezekiya ya ji daɗi, haka ma dukkan jama'a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama'a, gama farat ɗaya aka yi aikin.

Sura 30

1 Hezikiya ya aiko da saƙo ga dukkan Isra'ila da Yahuda, ya kuma rubutawa Manasa da Ifraimu wasiƙu, da cewa su zo gidan Yahweh a Yerusalem, su yi Idin ‌Ƙetarewa ga Yahweh, Allah na Isra'ila, 2 Gama sarkin, da shugabaninsa da dukkan taron jama'a sun gana tare, cewa sun shirya su yi Idin ‌Ƙ‌etarewa a wata na biyu. 3 Ba su iya yinsa a lokacin da aka saba yi ba, saboda babu firistocin da suka tsarkake kansu, kuma mutane ba su tattaro kansu gaba ɗaya zuwa Yerusalem ba. 4 Wannan shirin kuwa ya yi dai-dai a idanuwan sarki da dukkan taron jama'a. 5 Saboda haka suka yarda su yi shelar umarnin a ko'ina a Isra'ila daga Biyarsheba zuwa Dan, cewa mutanen su zo su yi bikin Idin ‌Ƙ‌etarewa ga Yahweh, Allahn Isra'ila, a Yerusalem. Domin sun lura ba su taɓa yin sa da mutane da yawa ba, bisa ga abin da kea rubuce. 6 Sai masu kai saƙo suka tafi da wasiƙu daga sarki da shugabaninsa zuwa ga dukkan Isra'ila da Yahuda, da umarnin sarkin, Suka ce ku mutanen Isra'ila, ku juyo ga Yahweh, Allahn Ibrahim da Ishaku da Iara'ila. Saboda shi ma ya sake juyowa ga ragowarku da kuka kuɓuta daga hannun sarkin Assiriya. 7 Kada ku zama kamar kakaninku ko 'yan'uwanku maza, waɗanda suka kauce daga Yahweh, Allahn kakaninsu, har yasa ya bar su ga hallaka, kamar yadda kuka gani. 8 Yanzu kuwa kada kuyi taurin kai, kamar yadda kakaninku suka yi, ku miƙa kanku ga Yahweh, ku kuma zo wurinsa mai tsarki, wadda ya tsarkake har abada, kuyi sujada ga Yahweh Allahnku, saboda zafin fushinsa zai kauce daga aukowa maku. 9 Gama idan kuka juya baya ga Yahweh, 'yanuwanku maza da yaranku zasu sami tagomashi a gaban waɗanda suka tafi da su a matsayin kamammu, kuma zasu dawo wannan ƙasar. Gama Yahweh Allahnku mai alheri da jinkai ne kuma ba zai juya fuskarsa daga gare ku ba idan kun juyo zuwa gare shi." 10 Sai manzanin suka wuce daga birni zuwa birni a dukkan lardin Ifraimu da Manasa, har zuwa Zabulun, amma mutanen suka yi masu dariya da ba'a. 11 Ko da yake, waɗansu mutanen Asha da Manasa da Zabulun suka yi tawali'u suka zo Yerusalem. 12 Hannun Allah kuma ya zo ga Yahuda, ya basu zuciya daya, su yi abin da sarki da shugabanin suka umarta ta wurin maganar Yahweh. 13 Mutane da yawa, taron jama'a mai girma, suka taru a Yerusalem domin su yi Bikin Idin Abinci Marar Gami a wata na biyu. 14 Suka tashi suka cire bagadan da kecikin Yerusalem, da dukkan bagadan ƙona turare; suka zubar da su a kwarin Kidron. 15 Sa'an nan suka kashe ragunan Idin ‌Ƙetarewa a rana ta huɗu ga watan biyu, Firistoci da Lebiyawa kuwa suka ji kunya, saboda haka suka tsarkake kansu suka kawo hadayu na ƙonawa a gidan Ubangiji. 16 Suka ɗauki gwalgwadon matsayinsu, bisa ga yadda dokar Musa, mutumin tsauni ta faɗa, Firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lebiyawa. 17 Gama akwai waɗansu da yawa a taron da ba su tsarkake kansu ba. Saboda haka Lebiyawan suka yanka ragunan Idin ‌Ƙ‌etarewa domin duk wanda ba shi da tsarki kuma ba zai iya tsarkake hadayunsa ga Yahweh ba 18 Gama babban taron mutane, yawancinsu daga Ifraimu da Manasa da Issaka da Zabulun, ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci abincin Idin, găba da rubutaccen umarnan. Gama Hezekiya ya yi masu addu'a cewa, 19 "Ubangiji Yahweh ya gafarci duk wanda ya sa zuciyarsa ga neman tsauni, Yahweh, tsaunin kakaninsa, ko bai da tsarki ta ka'idar tsarkakewa na wuri mai tsarki." 20 Saboda haka Yahweh ya saurari Hezekiya ya kuma warkar da mutanen. 21 Mutanen Isra'ila waɗanda suke a Yerusalem sun yi Idin Abinci Mara Gami da murna mai yawa har kwana bakwai. Lebiyawa da firistoci suka yabi Yahweh rana bayan rana, suna waƙa da kayayyakin kiɗe-kiɗe masu ƙara ga Yahweh. 22 Hezekiya ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukkan Lebiyawan da suka gane hidimar Yahweh. Sai suka ci abinci a duk lokacin idin na kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta furta zunubai ga Yahweh, tsauni na kakaninsu. 23 Dukkan taron jama'an kuwa suka shirya su ƙara yi bikin na kwana bakwai kuma, suka kuma yi haka da murna. 24 Gama Hezekiya sarkin Yahuda ya ba jama'an bijimai dubu ɗaya da tumaki dubu bakwai a matsayin baiko; shugabanin kuma suka baiwa jama'ar bijimai dubu ɗaya da tumakai da awakai dubu ɗaya. Firistoci da yawa kuma suka tsarkake kansu. 25 Dukkan jama'ar Yahuda, tare da firistoci da Lebiyawa, da dukkan mutanen da suka zo tare daga Isra'ila, da kuma baƙin da suka zo daga ƙasar Isra'ila da waɗanda ke zaune a Yahuda - Dukkansu sun yi farin ciki. 26 Saboda haka aka yi babban murna a Yerusalem, gama tun daga lokacin Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila, babu wani abu kamar haka a Yerusalem. 27 Sa'an nan firistoci da Lebiyawa suka tashi suka sa wa mutane albarka. Aka kuwa ji muryarsu, addu'arsu kuma ta kai sama, wuri mai tsarki da tsauni yake.

Sura 31

1 Yanzu sa'ad da aka gama dukkan waɗannan, sai mutanen Isra'ila da kewurin suka fiita daga biranen Yahuda suka rurrushe ginshiƙan duwatsu suka kakkarye sandunan Ashera, suka kuma karya masujadar bisa da bagadun a dukkan Yahuda da Benyamin da Ifraim da Manasse, har sai da suka rurrusa su dukka. Sai dukkan mutanen Isra'ila suka dawo, kowanne ga nasa mallaka da nasa birnin. 2 Hezekiya ya rarraba ɓangarorin firistoci Lebiyawa kumaya shirya su bisa ga ɓangarorinsu, kowanne mutum da aikinsa, da firistoci da Lebiyawa. Yasa su su yi hadayun ƙonawa dana zumunci, su yi hidima, su yi godiya, su yi yabo a ƙofar haikalin Yahweh. 3 Ya kuma shirya sashin hadayar ƙonawa ta sarki daga mallakarsa, wato domin hadayun ƙonawa na safe dana yamma da hadayun ƙonawa domin ranakun Asabar, saɓobbin watanni, da sanyayyun bukukuwa, kamar yadda yake a rubuce a shari'ar Yahweh. 4 Bugu da ƙari, ya umarci mutanen da kezama a Yerusalem su bada ɓangaren da ya shafi firistoci da Lebiyawa, saboda su ci gaba da sa ƙarfi ga biyayya da doka na Yahweh. 5 Ba tare da ɓata lokaci ba bayan an aiko da umarnin, mutanen Isra'ila suka bayar hannu sake wato nunan fari na hatsi da sabon ruwan inabi da maida zuma da dukkan girbin gona. Suka kawo zakka na dukkan kome; waɗannan abu kuwa masu tarin yawa ne. 6 Mutanen Isra'ila da Yahuda waɗanda ke zama a biranen Yahuda suka kawo zakkar shanu da tumaki, da kuma zakkar abubuwa masu tsarkin da aka keɓe ga Yahweh tsauninsu, kuma suka tattaro su dami-dami. 7 A watan uku ne sa'ad da suka fara harhaɗa gudunmawarsu dami-dami, suka kuma gama a wata na bakwai. 8 Sa'an da Hezekiya da shugabanin suka zo suka ga dammunan, suka albarkaci sunan Yahweh da mutanensa Isra'ila. 9 Sa'annan Hezekiya ya tambayi firistocin da Lebiyawa game da dammunan. 10 Azariya, babban firist, na gidan Zadok, ya amsa masa ya ce, "Tun da mutanen suka fara kawo baye-baye cikin gidan Yahweh, Mun ci kuma mun sami isasshe, kuma muna da ragowa da yawa, gama Yahweh ya albarkaci mutanensa. Abin da ya rage shi ne wannan da yawa a nan." 11 Sa'an nan Hezekiya ya umarta ayi wuraren ajiya a gidan Yahweh, sai suka kuwa shirya wuraren. 12 Sa'an nan suka yi aminci suka kawo baye-bayen, zakka da abubuwan da kena Yahweh. Kononiya, Balebiye, shi ne shugaba mai lura da su, kuma Shimei, dan'uwansa ne na biye da shi. 13 Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaya na karkashin Konaniya da Shime'i dan'uwamsa, bisa ga zaɓen Hezekiya, sarki, da Azariya, mai lura da gidan Yahweh. 14 Kore ɗan Imna Balebiye da shugaba na ƙofar gabas, su ne masu lura da bayarwar yardar rai ga tsauni da shugabanci a kan rarrabawar baye-baye ga Yahweh da abubuwa mafi tsarki cikin baye-bayen. 15 A ƙarƙashinsa akwai Iden da Mini'amin da Yeshuwa da Shemaya da Amariya da Shekaniya a biranen firistocin. Suka cika ayyukan amanar shugabanci, Domin a bayar da waɗannan baye-baye ga 'yan'uwansu maza ɓangare ɓangare ga kowa da kowa. 16 Suka kuma ba wa mazajen da keshekara uku zuwa sama, waɗanda aka lisafta a rohotonin kakaninsu da suka shiga gidan Yahweh, kamar yadda ake bukata a kowacce rana, ayi aiki bisa ga muƙamansu da ɓangarorinsu. 17 Suka rarraba wa firistocin bisa ga rahotonin kakaninsu, haka kuma ga Lebiyawan da kesama da shekara ashirin ko fiye, bisa ga muƙamansu da ɓangarorinsu. 18 Suka haɗa da 'yan ƙananansu da matayensu da 'ya'ya mazansu da 'ya'ya matansu, a dukkan unguwan, gama su masu aminci ne ga kiyaye zaman tsarkinsu. 19 Gama firistocin wato zuriyar Haruna waɗanda ke filayen ƙauyukan da keta biranensu ne, ko kuwa a kowacce birni dai, akwai mazajen da aka sa da sunayesu, su bada rabo ga duk mazaje cikin firistoci, da kuma ga waɗanda aka lisafta a rahotonin kakaninsu cewa suna cikin Lebiyawa. 20 Hezekiya ya yi wannan a dukan Yahuda. Ya aiwatar da abin da kenagari, dai-dai, da kuma aminci a gaban Yahweh, tsauninsa, 21 A duk aikin da ya fara cikin hidimar gidan tsauni da dokoki da farilai, don kusantuwa da tsauninsa, ya aikata su da dukkan zuciyarsa, kuma ya yi nasara.

Sura 32

1 Bayan waɗannan abubuwan da amintattun ayyuka, Senakirib sarkin Asuriya, ya zo ya shiga Yahuda. Ya kafa sansani ya kai ma birane masu garu hari, da niyar ya yi kamu domin kansa. 2 Sa'ad da Hezekiya ya ga Senakirib ya iso kuma ya yi niyar yaƙi da Yerusalem, 3 sai ya yi shawara da shugabanninsa da mazajensa masu iko su tsayar da ruwayen da kefitowa daga maɓuɓɓugar da suke bayan birnin; suka taimake shi ya yi hakan. 4 Saboda haka mutane da yawa suka taru suka tsayar da dukkan maɓuɓɓugai da rafuffuka da kegudu ta cikin ƙasar. Su na cewa, "Me zai sa sarakunan Asuriya su zo su sami ruwa mai yawa?" 5 Hezekiya ya yi karfin hali ya sake gina dukkan ganuwar da aka rushe, ya gina hasumiyar da inganci, haka kuma ɗaya garun da kewaje. Ya kuwa ƙara ƙarfin Milo a birnin Dauda, ya kuma yi makamai na yaƙi da yawa da garkuwoyi. 6 Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci mutane. Ya tattaro su gareshi a dandalin ƙofar birnin ya yi magana ta ƙarfafawa da su. Ya ce, 7 "Ku ƙarfafa da nagartaccen ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Asuriya da dukkan sojojin da ketare da shi, gama wani yana tare da mu wanda ya fi waɗanda ke tare da shi. 8 Hannun mutum ne kawai ke tare da shi, amma mu Yahweh tsauninmu yake tare da mu domin ya taimake mu ya yi mana yaƙi." Mutane kuwa suka ta'azantu da maganar Hezekiya, sarkin Yahuda. 9 Bayan wannan, sai Senakirib sarkin Asuriya ya aika da barorinsa zuwa Yerusalem (Yanzu dai yana a gaban Lakish, kuma dukkan mayaƙansa na tare da shi), ga Hezekiya, sarkin Yahuda da dukkan Yahuda waɗanda ke a Yerusalem. Ya ce, 10 Ga abin da Senakirib, sarkin Asuriya, ya ce: "Ga me kake dogara a kai don ka dage wa yaƙi kewaye da kai a cikin Yerusalem? 11 Ba ruɗin ku Hezekiya yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi, sa'ad da yake gayă maku, 'Yahweh tsauninmu zai cece mu daga hannun sarkin Asuriya'? 12 Ba wannan Hezekiyan ba ne yake ɗauke wuraren bisansa da bagadensa ya kuma umarci Yahuda da Yerusalem, 'A kan bagadi guda ne ya wajaba ku yi sujada, a kansa ne kuma zaku ƙona hadayunku? 13 Ba kun san abin da ni da kakannina muka yi wa dukkan manyan mutane na waɗansu ƙasashen ba? Allolin manyan mutane na ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna? 14 Daga cikin dukkan manyan waɗancan al'ummai waɗanda kakannina suka hallakar kakaf, da wanda ya iya ceton mutanensa daga hannuna? Donme tsauninku zai iya cetonku daga hannuna? 15 Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku ko ya ɓadda ku haka. Kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani tsauni na wata al'umma ko mulki wanda ya taɓa ceton mutanensa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane ne tsaunin ku har da zai iya cetonku daga hannuna?" 16 Barorin Senakirib sun yi maganganu fiye da haka găba da Yahweh tsauni da bawansa Hezekiya. 17 Senakirib ya kuma rubuta wasiƙu don ya yi ba'a ga Yahweh, tsauni na Isra'ila, ya kuma yi maganar găba da shi. Ya ce, "Kamar yadda allolin al'ummai na sauran ƙasashe basu ceci mutanensu daga hannuna ba, hakanan kuma tsaunin Hezekiya ba zai iya ceton mutanensa daga hannuna ba." 18 Suka yi kuka da babban murya, da harshen Yahudanci, suka yi ta magana da mutanen Yerusalem waɗanda suke kan garu, don su tsoratar da su, su kuma firgita su, domin su danƙe birnin. 19 Suka yi magana a kan tsauni na Yerusalem kamar yadda suka yi ta magana a kan allolin waɗansu mutanen duniya, waɗanda aikin hannuwan mutane ne kurum. 20 Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari kuma suka yi kuka zuwa sama 21 Yahweh kuwa ya aiki mala'ika, wanda ya karkashe mazajen yaƙi da manyan jarumawa da shugabanni na sarkin a sansanin. Saboda haka Senakirib ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan tsauninsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi. 22 Ta haka Yahweh ya ceci Hezikiya da mazaunan Yerusalem daga hannun Senakirib, sarkin Asuriya, daga kuma hannun dukkan sauran, ya kuma hutar da su ta kowace ɓangare. 23 Mutane da yawa suka kawo wa Yahweh sadakoki a Yerusalem, da kuma abubuwa masu daraja ga Hezekiya sarkin Yahuda, saboda haka ya sami ɗaukaka a idanun dukkan sauran al'ummai tun daga lokaci nan har zuwa gaba. 24 A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa. Sai ya yi addu'a ga Yahweh, wanda kuwa ya yi magana da shi ya ba shi alamar cewa zai warke. 25 Amma Hezekiya bai mayar da godiya a kan taimakon da ya ba shi ba, domin a zuciyarsa akwai girman kai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuda da Yerusalem. 26 Duk da haka dai, daga baya Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda fahariyar zuciya da ya yi, da shi da mazaunan Yerusalem, don haka hasalar Yahweh ba ta faɗo masu ba a kwanakin Hezekiya. 27 Hezekiya yana da dukiya ƙwarai yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiye azurfa da zinariya da duwatsu masu daraja da kayan yaji da garkuwoyi da dukkan tasoshi, da kwanoni masu daraja. 28 Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi dana mai, da wuraren turke dabbobi na kowanne iri, yana kuma da garkuna a cikin rufar dabbobinsa. 29 Bugu da ƙari, ya kuma tanada wa kansa birane da mallakar garkunnan tumaki da na shanu a yalwace. Gama tsauni yaba shi wadata mai yawa. 30 Hezekiyan nan ne kuwa ya datse ruwan da yake gangarowa daga kogin Gihon, ya kuma kawo su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dauda. Hezekiya ya yi nasara da dukkan ayyukansa. 31 Ko da shi ke, game da jakadun hakiman Babila, waɗanda aka aika su tambaye shi game da waɗanda suka san irin abin al'ajibin da aka yi a ƙasar, sai tsauni ya ƙyale shi kurum, don ya jaraba shi ya san dukkan abin da kea zuciyarsa. 32 Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, gashi an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz a littafin Sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 33 Sai Hezekiya ya rasu, suka bizne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dauda, maza da dukkan Yahuda da mazaunan Yerusalem suka girmama shi sa'ad da ya rasu, sai Manasa ɗansa ya gaji gădon sarautarsa.

Sura 33

1 Manasse yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru hamsin da biyar a Yerusalem. 2 Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh, kamar ƙazantattun abubuwan da al'umman da Yahweh ya kore su a gaban mutanen Isra'ila. 3 Gama ya gina wuraren kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe, kuma ya gina bagadai domin Ba'aloli. Ya ƙera sandunan Ashera, kuma ya russuna wa dukkan taurarin sammai ya yi masu sujada. 4 Manasse ya gina bagadin a gidan Yahweh, koda shi ke dai Yahweh bai umarta ba, "A Yerusalem ne sunana zai kafu har abada." 5 Ya gina bagadai ga dukkan taurarin sama a cikin shirayu biyun da kegidan Yahweh. 6 A Kwarin Ben Hinnom ya sa 'ya'yansa maza a wuta. Ya aikata tsafe-tsafen tsubbu; ya yi karatun baƙaƙen zabura; kuma ya tuntuɓi masu magana da matattu da ruhohi. Manasse aikata miyagun ayyuka da dama a fuskar Yahweh, ya kuma tsokani Yahweh ga fushi. 7 Sarafaffen siffar da ya yi, ya sa shi a gidan tsauni. A kan wannan gidan ne tsauni ya yi magana da Dauda da Suleman ɗansa. Ya ce, "A wannan gidan da Yerusalem ne, waɗanda na zaɓa daga dukan ƙabilun Isra'ila, cewa zan kafa sunana har abada. 8 Ba zan ƙara fitar da mutanen Isra'ila daga ƙasar dana ba wa kakaninsu ba, idan za su yi biyayya su kiyaye dukkan abin dana umarce su, su bi dukkan dokoki da farillai dana umarta ta hannun Musa." 9 Manasse ya jagoranci Yahuda da mazaunan Yerusalem ga yin mugunta fiye da al'umman da tsauni ya hallakar a gaban mutanen Isra'ila. 10 Yahweh ya yi magana da Manasse da jama'arsa amma babu wanda ya kula. 11 Saboda haka Yahweh yasa sarakunan yaƙi na sarkin Asiriya su kama Manasase su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla su kai shi Babila. 12 Sa'ad da Manasse ke shan wahala, sai ya roƙi Yahweh, tsauninsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban tsauni na kakaninsa. 13 ya yi addu'a zuwa gare shi; sai ya roƙi tsauni, sai tsauni ya ji rokonsa ya komo da shi Yerusalem, ga mulkinsa. Sa'an nan ne Manasse ya sani Yahweh shi ne tsauni. 14 Bayan haka sai Manasse ya gina garu a bayan birnin Dauda a gefen yammacin Gihon, a kwari, zuwa ‌Ƙofar Kifi. Ya kewaye tudun Ofel, bayan wannan kuma ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan yasa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuda. 15 Ya kwashe baƙin alloli, wato gumaku daga cikin gidan Yahweh, da dukkan bagadin da ya giggina a bisa dutse na gidan Yahweh da Yerusalem. Ya zubar da su a bayan birnin. 16 Ya kuma komar da bagadin Ubangiji ya miƙa hadayu na salama dana godiya a kansu; ya kuma umarci Yahuda da ta bauta wa Yahweh, tsauni na Isra'ila. 17 Duk da haka, jama'a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadar bisa, amma ga Yahweh, tsauninsu kaɗai. 18 Game da sauran ayyukan Manasse da addu'o'insa ga tsauninsa, da abubuwan da masu gani suka faɗa masa cikin sunan Yahweh, tsauni na Isra'ila, gasu, suna a rubuce cikin ayyukan sarakunan Isra'ila. 19 A cikin rahoton akwai tarihin addu'arsa, da yadda tsauni ya ƙarɓi rokonsa, akwai kuma rahoton dukkan zunubinsa da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujada a bisa, ya kafa sandar Ashera da sarafaffun siffofi, kamin ya ƙasƙantar da kansa - suna nan a rubuce a Tarihin Masu Duba. 20 Haka dai Manasse ya kwanta tare da kakaninsa, suka binne shi a gidansa. Sai Amon, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa. 21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya fara sarauta, ya yi shekara biyu yana mulki a Yerusalem. 22 Ya aikata mugunta a gaban Yahweh, kamar yadda Manasse, mahaifisa ya yi. Amon ya miƙa hadayu ga dukkan siffofin da mahaifinsa Manasse ya yi, ya bauta masu. 23 Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Yahweh, kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi ba. Maimakon haka, shi wannan Amon fa ya ƙara yin zunubi gaba-gaba. 24 Sai fadawansa suka yi masa maƙarkashiya suka kashe shi a gidansa. 25 Amma jama'ar ƙasar suka ƙarkashe dukkan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiya, sai suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gaji gadon sarautarsa.

Sura 34

1 Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya fara sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Yerusalem. 2 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh, ya kuma yi tafiya a hanyoyin Dauda mahaifinsa, kuma bai juya dama ko hagu ba. 3 Gama a shekara ta takwas na mulkinsa, tun yana yaro ya fara biɗan tsauni na Dauda, kakansa, a shekara ta goma sha biyu ne ya fara tsarkake Yahuda da Yerusalem daga tsafin wuraren bisa da sandar Ashera da sarafaffun siffofi da zuben siffofin ƙarfe. 4 Mutanen suka rurrusa bagadan Ba'alolin a gabansa; ya rurrusa bagadan turaren da kebisansu. Ya karya sandar Ashera da saraffaffun sifoffi da siffofin ƙarafuna har suka ragargaje zuwa ƙura. Ya yayyafa ƙurar a kan kaburburan waɗanda suka yi masu hadaya. 5 Ya ƙona kasusuwan firistocinsu a bagadansu. Ta haka ya tsarkake Yahuda da Yerusalem. 6 Ya yi haka kuma a biranen Manasa da Ifraimu da Saminu har zuwa Naftali da lalatattun wurare da kekewaye da su. 7 Ya rusar da bagadan; ya ragargaza sandar Ashira da sarafaffun siffofi zuwa gǎri, ya kuma rurrusa bagadan turare a dukkan ƙasar Isra'ila; sa'an nan ya koma Yerusalem. 8 Yanzu a shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan Yosiya ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Ma'aseya da gwamnan birnin da Yowa ɗan Yowahaz magatakarda, da su gyaggyara gidan Yahweh tsauninsa. 9 Suka je wurin Hilkaya, babban firist, suka danƙa masa kuɗin da aka kawo gidan Yahweh wanda Lebiyawa da masu gadin ƙofofi suka tara daga Manasse da Ifraimu, daga dukkan ragowar Isra'ila, daga dukkan Yahuda da Benyamin da kuma daga mazaunan Yerusalem. 10 Suka danƙa kuɗin ga mazan da kelura da gidan Yahweh. Waɗannan mazan ne ke biyan ma'aikatan da ke gyaggyarawa da adana haikalin. 11 Suka biya kafintoci da magina kuɗin da zasu sayi sassaƙaƙƙen duwatsu da katakai domin yin tsaiko kuma da tankaru don gine- ginen da waɗansu sarakuna na Yahuda suka bar su suka lalace. 12 Mazajen sun yi aikin da aminci. Masu shugabancinsu su ne Yahat da Obadiya wato Lebiyawa, 'ya'yan Merari; da Zekariya da Meshullam, daga 'ya'ya mazan Kohatawa. Sauran Lebiyawan waɗanda dukkansu ƙwararrun mawaƙa ne, sun yi shugabancin ma'aikatan. 13 Waɗannan Lebiyawan ne ke shugabancin masu ɗaukan kayan gini da duk sauran ma'aikata daban-daban. Akwai kuma Lebiyawan da kemasu rubuce=rubuce da masu gudanar da shugabanci da masu gadin ƙofofi. 14 Sa'ad da suka kawo kuɗin da aka kawo gidan Yahweh, Hikaya firist ya samo littafin shari'a ta Yahweh wanda aka bayar ta wurin Musa. 15 Hikaya ya cewa Shafan magatakarda, "Na sami littafin shari'a a gidan Yahweh." Hikaya ya kawo littafin ga Shafan. 16 Shafan ya kai ma sarki littafin, ya kuwa ba shi rahoto, cewa, "Barorinka na yin dukkan abubuwan da aka basu amanan yi. 17 Suka tattaro kuɗin da aka samu agidan Yahweh, sai suka bayar da shi ga hannun shugabannin lura da mazan aikin." 18 Shafan magatakarda ya faɗa wa sarki, "Hilkaya firist ya ba ni littafi." Sa'an nan Shafan ya karanta wa sarkin. 19 Ya zamana kuwa a sa'an da sarki ya ji kalmomin shari'a, sai ya yayyage tufafinsa. 20 Sarkin ya umarce Hilkaya da Ahikam ɗan Shafan da Abdon ɗan Micah da Shafan magatakarada da Ashaya, baransa, cewa, 21 "Ku je ku bincika nufin Yahweh domina, da kuma domin waɗanda aka bar su a Isra'ila da Yahuda, saboda kalmomin littafi da aka samo. Gama yana da girma, hasalar Yahweh da aka zubo mana. yana da yawa, saboda kakaninmu basu saurari kalmomin wannan littafi ba don su yi biyayya da dukkan abin da aka rubuto cikinta." 22 Saboda haka Hilkaya, da waɗanda sarki ya umarta, suka je wurin annabiya Huldah, matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai lura da tufafin firistoci (tayi zama a Yerusalem a Gunduma ta Biyu), sai suka yi magana da ita haka. 23 Sai ta ce masu, "Ga abin da Yahweh, tsaunin Isra'ila, ya ce: "Gaya wa mutumin da ya aiko ku wuri na, 24 Ga abin da Yahweh ya faɗi: Duba. 'Ina gab da kawo bala'i a nan wurin da kan mazaunanta, dukkan la'anonin da aka rubuta a littafi da suka karanta a gaban sarkin Yahuda. 25 Saboda sun ƙi ni kuma sun ƙona turare ga waɗansu alloli, saboda su zuga ni ga fushi da dukkan ayyukan da suka aikata- Don haka fushi na zai zubo a wannan wurin, kuma ba za a datse shi ba.' 26 Amma ga sarkin Yahuda, wanda ya aiko ku ku tambayi Yahweh abin da zai yi, ga abin da zaku gaya ma sa, 'Yahweh, tsauni na Isra'ila ya faɗi haka: Game da maganganun da ka ji, 27 saboda baka taurare zuciyarka ba, kuma ka ƙasƙantar da kanka a gaban tsauni sa'ad da ka saurari maganganu game da wannan wurin da mazaunanta, kuma domin ka ƙasƙantar da kanka a gaba na, ka yayyaga taufafinka ka yi kuka a gabana, Ni kuma na saurare ka - wannan furcin Yahweh ne - 28 duba, Zan tattara ka da kakaninka. Za a tattara ka zuwa kabarinka cikin salama, kuma idanuwanka ba za su ga bala'in da zan kawo a wurin nan da mazaunanta ba." Mazajen nan suka kai wa sarki wannan saƙon. 29 Sa'an nan sarkin ya aiko manzanni su tattaro dukkan dattawan Yahuda da Yerusalem tare. 30 Sa'an nan sarkin ya haura zuwa gidan Yahweh, da dukkan mazajen Yahuda da mazaunan Yerusalem, da firistoci da Lebiyawa da dukkan mutane, daga manya zuwa ƙanana. Sa'an nan ya karanto ga saurarawarsu dukkan kalamomin littafin Alƙawari da aka samo a gidan Yahweh. 31 Sarkin ya tsaya a wurinsa ya yi alƙawari a gaban Yahweh, ya yi tafiya bisa ga jagorancin Yahweh, ya kuma kiyaye dokokinsa da farillansa da umarnansa, da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa, ya yi biyayya da maganganun alƙawari da kea rubuce a wannan littafi. 32 Ya sa dukkan waɗanda aka same su a Yerusalem da Benyamin su tsaya a kan alƙawarin. Mazaunan Yerusalem sun yi aiki cikin biyayya ga alƙawarin tsauni, tsauni na kakanninsu. 33 Yosiya ya ɗauke dukkan ƙazamtattun abubuwa daga ƙasashen da suke na mutanen Isra'ila. Ya sa kowa a Isra'ila ya bauta wa Yahweh, tsauninsa. Gama a dukkan kwanakinsa, ba su juya daga bin Yahweh, tsaunin kakaninsu ba.

Sura 35

1 Yosiya ya kiyaye Idin ‌Ƙetarewa ga Yahweh a Yerusalem, kuma suka kashe 'yan ragunan Idin a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari. 2 Ya sa firistocin a matsayinsu ya ƙarfafa su a cikin hidimar gidan Yahweh. 3 Ya cewa Lebiyawan da suka koyar da dukkan Isra'ila waɗanda aka keɓe ga Yahweh, "Ku sa akwati mai tsarki a gidan da Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila ya gina. Kada ku dinga ɗaukar sa a bisa kafaɗunku kuma. Yanzu ku bauta wa Yahweh tsauninku, ku yi wa mutanensa Isra'ila hidima. 4 Ku shirya kanku ta sunayen gidajen kakaninku da ɓangarorinku, bisa ga rubutaccen umarnin Dauda, sarkin Isra'ila, da ta Suleman, ɗansa. 5 Ku tsaya a wuri mai tsarki, kuna ɗaukan matsayinku tare da ɓangarorin 'yan'uwanninku maza ta cikin gidajen kakaninku da zuriyoyin mutane, kuna kuma ɗaukan matsayinku tare da ɓangarorinku ta cikin gidajen kakaninku na Lebiyawa. 6 Ku kashe 'yan ragunan Idin ‌Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya ragunan domin 'yan'uwanku maza, kuyi bisa ga maganar Yahweh da aka bayar ta hannun Musa." 7 Yosiya ya baiwa dukkan mutane 'yan raguna dubu talatin da 'yan awakai daga turkuna domin baikon Idin ‌Ƙ‌etarewa ga dukkan waɗanda suka kasance. Ya kuma bada bijimai dubu talatin; waɗannan daga mallakar sarki ne. 8 Shugabaninsa sun bayar da baikon yardar rai ga mutane da firistoci da Lebiyawa. Hilkaya da Zekariya da Yehiyel da manyan ma'aikatan da kelura da gidan tsauni, sun ba firistoci baikon ƙananan shanu 2,600 da bijimai ɗari uku domin Idin ‌Ƙetarewa. 9 Konaniya kuwa da Shemaya da Netanel, 'yan'uwansa maza, da Hashabiya da Ye'iyel, da Yozabad, waɗanda ke shugabancin Lebiyawa, sun ba Lebiyawan baiko domin Idin ‌Ƙ‌etarewa ƙananan shanu dubu da bijimai ɗari biyar. 10 Don haka aka shirya hidimar, sai firistocin suka tsaya bisa ga matsayinsu, da Lebiyawan ta ɓangarorinsu, cikin yin biyayya da umarnin sarki. 11 Suka kashe 'yan ragunan Idin ‌Ƙ‌etarewa, sai firistoci suka zuba jinin da suka karɓo daga hannun Lebiyawan, sai Lebiyawan suka feɗe 'yan ragunan. 12 Suka cire hadayun ƙonawa, don su rarraba su ga ɓangarorin gidajen kakanin mutanen, suƙa miƙa su ga Yahweh, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Musa. Suka yi haka kuma da bijiman. 13 Suka gaggasa 'yan ragunan Idin ‌Ƙetarewan da wuta bisa ga umarni. Game da tsarkakkun baye-bayen, suka dafa su cikin ruwa a tukwane daban-daban, suka kuma ɗauka da sauri suka kai wa dukkan mutane. 14 Suka shirya baye-baye daga baya domin kansu da firistocin, saboda firistocin, wato zuriyar Haruna, suna fama da miƙa hadaya ta ƙonawa da kitsen har sai dare ya yi, saboda haka Lebiyawan sun shirya baye-bayen domin kansu da firistoci, zuriyar Haruna. 15 Mawaƙan, zuriyar Asaf, suna wurin, bisa ga bishewar Dauda da Asaf da Heman da Yedutun mai duba na sarki, kuma masu tsaro suna a kowacce ƙofa. Ba za su taɓa barin wurin tsayawarsu ba, saboda 'yan'uwansu Lebiyawa sun shirya abu dominsu. 16 Don haka, a lokacin nan dukkan hidimar Yahweh ana yi domin bikin Idin ‌Ƙ‌etarewa ne da miƙa baye-bayen ƙonawa a bagaden Yahweh, kamar yadda sarki Yosiya ya umarta. 17 Mutanen Isra'ilan da suka kasance sun kiyaye Idin ‌Ƙ‌etarewa a lokacin, sa'an nan kuma da Shagulgulan Gurasa Marar Gami na kwana bakwai. 18 Irin wannan bikin Idin ‌Ƙetarewan ba a taɓa yin sa a Isra'ila ba tun daga kwanakin su annabi Sama'ila, ba kuwa wani daga cikin sauran sarakunan Isra'ila da ya yi hidimar bikin Idin ‌Ƙ‌etarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci da Lebiyawa da dukkan mutanen Isra'ilan da suka kasance, kuma da mazaunan Yerusalem. 19 Wannan Idin ‌Ƙ‌etarewa an kiyaye shi ne a shekara ta goma sha takwas na mulkin Yosiya. 20 Bayan dukkan wannan, bayan Yosiya ya shirya haikalin bisa ga tsari, Neko, sarkin Masar, ya hauro ya yi faɗa da Karkemish a Kogin Yuferetis, sai Yosiya ya je ya yi faɗa da shi. 21 Amma Neko ya aiko wakilai gun sa, cewa, "Mene ne zan yi da kai, sarkin Yahuda? Ba na zuwa găba da kai yau, amma găba da gidan da nake yaƙi da su. tsauni ya umarce ni da in yi sauri, saboda haka ka janye daga shisshigi da Allah, wanda ke tare da ni, don zai iya hallaka ka." 22 Koda shi ke, Yosiya ya ƙi ya juyo daga gare shi. Ya ɓoye kamaninsa don ya yi yaƙi da shi. Bai saurari maganar Neko da ta zo daga bakin Allah ba; sai ya je ya yi faɗa a Kwarin Megiddo. 23 Jarumawa suka harbi Yosiya, sai sarki ya cewa barorinsa, "Ku tafi dani, gama na sami mumunar rauni," 24 Sai barorinsa suka ɗauke shi daga karusar, suka sa shi a karusa ta biyu. Suka kai shi Yerusalem, inda ya mutu. Aka binne shi a wurin binne kakaninsa. Dukkan Yahuda da Yerusalem suka yi makoki domin Yosiya. 25 Irimiya ya yi makoki domin Yosiya; dukkan mazaje da mata mawaƙa suna maƙoƙi game da Yosiya har yau. Waɗannan waƙoƙin suka zama al'ada a Isra'ila; Suna a rubuce a waƙoƙin maƙoƙi. 26 Game da sauran abubuwan da suka shafi Yosiya, da nagargarun ayyukansa da ya yi cikin biyayya da abin da kea rubuce a shari'ar Yahweh - 27 kuma dukkan ayyukansa, daga farko zuwa karshe, na a rubuce cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila.

Sura 36

1 Sa'an nan mutanen ƙasar suka ɗauki Yehowahas ɗan Yosiya, suka maida shi sarki a madadin mahaifinsa a Yerusalem. 2 Yehowahas yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya fara mulki, ya kuma yi mulki watanni uku a Yerusalem. 3 Sarkin Masar ya cire shi a Yerusalem, ya sa wa ƙasar tara na talenti ɗari na azurfa da talenti ɗaya na zinariya. 4 Sarkin Masar ya maida Iliyakim, ɗan'uwansa, sarki a kan Yahuda da Yerusalem, (ya sauya wa Iliyakim suna zuwa Yehoyakim). Sa'an nan Neko ya ɗauki ɗan'uwan Iliyakim Yehowahas ya kawo shi Masar. 5 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Yerusalem. Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh Allahnsa. 6 Sa'an nan Nebukadnezar, sarkin Babila, ya kai masa hari ya ɗaure shi da sarƙoƙi ya kai shi Babila. 7 Nebukadnezar kuma ya ɗauki waɗansu kayayyakin gidan Yahweh zuwa Babila, ya sa su a fadarsa a Babila. 8 Game da sauran zantattukan da suka shafi Yehoyakim, abubuwan ƙazamtar da ya yi, da abin da aka samo găba da shi, gashi, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila. Sa'an nan Yehoyakin, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa. 9 Yehoyakin yana da shekara takwas sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki wata uku da kwana goma a Yerusalem. Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh. 10 Da bazara, Sarki Nebudkanezar ya aiki mazaje aka kawo shi Babila, tare da abubuwa masu daraja daga gidan Yahweh, sai ya maida Zedekiya, danginsa, sarki a kan Yahuda da Yerusalem. 11 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Yerusalem. 12 Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh Allahnsa. Bai ƙasƙantar da kansa a gaban annabi Irimiya ba, wanda ya yi magana daga bakin Yahweh. 13 Zedekiya kuwa ya yi tayarwa gãba da Sarki Nebudkanezar, wanda ya sa shi rantsuwar yin biyayya gare shi da sunan Allah. Amma Zedekiya ya taurare zuciyarsa da wuyansa gãba da juyowa ga Yahweh, Allahn Isra'ila. 14 Bugu da ƙari, dukkan shugabannin firistocin da mutanen sun yi mummunan rashin aminci, kuma suka bi kazamtattun aikin al'ummai. Suka lalatar da gidan Yahweh wanda ya tsarkake a Yerusalem. 15 Yahweh, Allahn kakaninsu, ya aiko da kalma garesu ta manzaninsa a kai a kai, saboda yana da tausayi a kan mutanensa da wurin da yake zamne. 16 Amma sun yi ma manzanin Allah ba'a, suka yi banza da maganarsa, suka kuma wulaƙantar da annabawansa, har sai da fushin Allah ya taso gãba da mutanensa, har babu taimako game da haka. 17 Don haka Allah ya kawo masu sarkin Kaldiyawa, wanda ya kashe 'yan mazansu da takobi a masujada, kuma ba su ji tausayin 'yan maza ko budurwai ko tsofoffin maza ko masu farin gashi ba. Allah ya bayar da su dukka ga hannunsa. 18 Dukkan kayan ɗaki na gidan Allah, masu manya da ƙanana da dukiyoyin gidan Yahweh da dukiyoyin sarki da ma'aikatansa- dukkan waɗannan ya kwashe zuwa Babila. 19 Suka ƙona gidan Allah, suka rurrushe garun Yerusalem, suka ƙona dukkan fadodinta, kuma suka hallakar da dukkan abubuwa masu kyau a ciki. 20 Sarki ya ɗauke zuwa Babila waɗanda suka kuɓce wa takobi. Suka zama barori dominsa da 'ya'yansa maza har zuwa mulkin Fasha. 21 Wannan ya faru ne domin a cika maganar Yahweh ta bakin Irimiya, har sai ƙasar ta ji daɗin hutun Asabatunta. Ta jira Asabbatu na tsawon lokacin da take zama a yashe, don a wuce shekaru saba'in ta haka. 22 Yanzu kuwa a shekara ta farko ta Sairus, sarkin Fasha, domin maganar Yahweh ta bakin Irimiya ta cika, Yahweh ya zuga ruhun Sairus, sarkin Fasha, don haka ya sanar da umarni ga dukkan mulkinsa, ya kuma sa ta a rubuce. Ya ce, 23 Ga abin da Sairus, sarkin Fasha, ya ce: "Yahweh, Allahn sammai, ya bani dukkan mulkokin duniya. Ya umarce ni in gina gida dominsa a Yerusalem, wanda yake a Yahuda. Duk wanda ke cikinku daga dukkan mutanesa, Yahweh Allahnku, ya kasance tare da ku. Bari ya haura can zuwa ƙasar."

Littafin Ezra
Littafin Ezra
Sura 1

1 A shekarar farko ta sarautar Sairus, sarkin Fasiya, Yahweh ya cika maganarsa wadda ta zo ta bakin Irmiya, wadda ta motsa ruhun Sairus. Muryar Sairus ta kai dukkan masarautarsa. Wannan shi ne abin da aka faɗa aka kuma rubuta: 2 "Sairus sarkin Fasiya ya ce; Yahweh, Allah na Sama, ya bani dukkan mulkokin duniya, ya kuma zaɓe ni in gina masa gida a Yerusalem a Yahudiya. 3 Duk wanda ya ke daga cikin mutanensa (Ubangijinsa ya kasance tare da shi) zai tafi Yerusalem ya gina gida domin Yahweh, Allah na Isra'ila, Allah da ke a Yerusalem. 4 Mutanen da ke kowanne sashi na mulkin inda waɗanda suka ragu ke zama sai su basu guzirin azurfa da zinariya, da mallakoki da dabbobi, da kuma kyauta ta yardar rai domin gidan Allah a Yerusalem." 5 Sai shugabannin zuriyar Yahuda da ta Benyamin, da firistoci da Lebiyawa, da duk waɗanda Allah ya iza ruhunsu su je su gina gidansa ya kafu. 6 Waɗanda ke kewaye da su suka taimaki aikinsu da azurfa da zinariya da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai. 7 Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin da ke gidan Yahweh waɗanda Nebukadnezza ya kwaso daga Yerusalem ya kuma ajiye a gidajen allolinsa. 8 Sai Sairus ya danƙa su a hannun Miteredat ma'aji, wanda ya ƙirga su ta hannun Sheshbazza shugaban Yahudiya. 9 Wannan shi ne yawansu: daro talatin na azurfa, daro dubu ɗaya na zinariya, da kuma wasu daro ashirin na sauran kayayyaki, 10 Tasoshi talatin na azurfa, ƙananan tasoshi na zinariya guda 410, da kuma sauran kayayyaki guda dubu. 11 Akwai a ƙalla kayayyakin zinariya da azurfa guda 5,400 da aka haɗa jimla dukka. Sheshbazza ya kawo dukkan waɗannan a lokacin da masu zaman talala suka fita daga Babila zuwa Yerusalem.

Sura 2

1 Waɗannan su ne mutanen lardin da suka fita daga bautar talalar sarki Nebukadnezza, wanda ya bautar da su a Babila, mutanen da suka koma biranensu na Yerusalem da kuma Yahudiya. 2 Sun dawo tare da Zerubbabel, Yoshuwa, Nehemiya, Serayya, da Re'elaya, Modekai, Bilshan, Misfar, Bigbai, Rehum, da Bãna. Wannan shi ne lissafin mutanen Isra'ila. 3 Zuriyar Farosh: 2,172. 4 Zuriyar Shefatiya: 372. 5 Zuriyar Arak: 775. 6 Zuriyar Fahat Mowab, ta wurin Yeshuwa da Yowab: 2,812. 7 Zuriyar Elam: 1254. 8 Zuriyar Zattu: 945. 9 Zuriyar Zakkai: 760. 10 Zuriyar Bani: 642. 11 Zuriyar Bebai: 623. 12 Zuriyar Azgad: 1,222. 13 Zuriyar Adonikam: 666. 14 Zuriyar Bigbai: 2,056. 15 Zuriyar Adin: 454. 16 Mutanen Ater, ta wurin Hezekiya: su tasa'in da takwas. 17 Zuriyar Bezai: 323. 18 Zuriyar Yorah: 112. 19 Mutanen Hashum: 223. 20 Mutanen Gibba: tasa'in da biyar. 21 Mutanen Betlehem: 123. 22 Mutanen Netofa: hamsin da shida. 23 Mutanen Anatot:128. 24 Mutanen Azmabet: arba'in da biyu. 25 Mutanen Kiriyat Arim, Kefira, da Birot: 743. 26 Mutanen Rama da Geba: 621. 27 Mutanen Mikmas:122. 28 Mutanen Betel da Ai: 223. 29 Mutanen Nebo: hamsin da biyu. 30 Mutanen Magbish: 156. 31 Mutanen ɗayar Elam: 1,254. 32 Mutanen Harim: 320. 33 Mutanen Lod, Hadid, da Ono: 725. 34 Mutanen Yeriko: 345. 35 Mutanen Senã: 3,630. 36 Sai firistoci zuriyar Yedayya na gidan Yeshuwa: 973. 37 Zuriyar Immer: 1,052. 38 Zuriyar Fashur: 1,247. 39 Zuriyar Harim: 1,017. 40 Lebiyawa zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel zuriyar Hodabiya: saba'in da huɗu. 41 Mawaƙan haikali, zuriyar Asaf: 128. 42 Zuriyar masu kula da ƙofa: na Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai: 139. 43 Waɗanda aka sa su yi hidima a haikali: zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, 44 Keros, Siyaha, Fadon, 45 Lebana, Hagaba, Akkub, 46 Hagab, Shalmai, da Hanan. 47 Zuriyar Giddel: Gahar, Re'ayya, 48 Rezin, Nekoda, Gazzam, 49 Uzza, Faseya, Besai, 50 Asnah, Meyunim, da Nefusim. 51 Zuriyar Bakbuk: Hakufa, Harhur, 52 Bazlut, Mehida, Harsha, 53 Barkos, Sisera, Tema, 54 Neziya, da Hatifa. 55 Zuriyar bayin Suleman: zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda, 56 Jãla, Dakon, Giddel, 57 Shefatiya, Hattil, Fokeret Hazzebem, da Ami. 58 Akwai 392 jimlar zuriyar waɗanda aka sasu yi aiki a haikali da kuma zuriyar bayin Suleman. 59 Waɗanda suka fita Tel Melah, Kerub, Addon, da Imma - amma basu iya gane asalinsu a Isra'ila ba - 60 sun kai 652 in an haɗa da zuriyar Delayya, Tobiya, da Nekoda. 61 Hakanan, daga zuriyar firistoci: da zuriyar Habayya, Hakkoz, da Barzillai (wanda ya auro matarsa daga 'ya'yan Barzillai ta Gileyed waɗanda kuma ake kiran su da sunansu). 62 Sun yi ta bincika asalinsu amma basu samo su ba don haka aka cire su daga aikin firist saboda rashin tsarki. 63 Don haka gwamnan ya ce da su kada su ci duk wani abu mai tsarki na hadaya har sai firist da Urim da Tummin sun amince. 64 Aka haɗa jimlarsu dukka ta kai mutum 42,360, 65 ba a haɗa da bayinsu ba (waɗannan sun kai 7,337) da mazansu da matansu mawaƙan haikali sun kai (ɗari biyu). 66 Dawakansu: 736. 67 Takarkaransu: 245. Raƙumansu: 435. Jakunansu: 6,720. 68 Da suka je gidan Yahweh a Yerusalem, manyan ubanni suka yi bayarwa ta yardar rai don a gina gida. 69 Sun bayar gwargwadon iyawarsu don asusun raya aikin: suka bada awon zinariya sittin da ɗaya, da azurfa jaka dubu biyar da kuma kayan sha na firistoci guda ɗari. 70 To sai firistoci da Lebiyawa, da jama'a, da mawaƙan haikalin da masu tsaron ƙofofi, da waɗanda aka sa suyi hidima a haikali suka mallaki biranensu. Dukkan mutane a Isra'ila suka zauna a biranensu

Sura 3

1 A wata na bakwai ne bayan da mutanen Isra'ila suka dawo biranensu, inda suka tattaru a matsayin al'umma ɗaya a Yerusalem. 2 Yeshuwa ɗan Yozadak da 'yan'uwansa firistoci, Zerubbabel ɗan Sheltiyyel da 'yan uwansa suka tashi don su gina bagadin haikalin Allah na Isra'ila don su miƙa hadaya ta ƙonawa kamar yadda aka umarta a shari'ar Musa mutumin Allah. 3 Sai suka kafa bagadin a wurin tsayuwarsa, don sun firgita saboda mutanen ƙasar. Suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh da yammaci. 4 Hakanan suka yi idin bukkoki kamar yadda ya ke a rubuce suka riƙa miƙa hadaya kowacce rana kamar yadda aka aiyana, ana yin kowanne aiki bisa ga ranarsa. 5 Bisa ka'ida, akwai baye-baye na ƙonawa ta kowacce rana da kowanne wata da kuma baye-baye na kowanne idi na Yahweh da aka aiyana tare da dukkan kyautai na yardar rai. 6 Suka fara miƙa baye-baye na ƙonawa ga Yahweh a rana ta farko a wata na bakwai, koda ya ke ba a kafa haikali ba tukuna. 7 Don haka suka bada zinariya ga masu aikin dutse da maƙera, suka bada abinci, da abin sha, da mai ga mutanen Sidon da Taya don su kawo itacen sida ta kan teku daga Lebanon zuwa Yoffa kamar yadda sarki Sairus ya bada umarni ga sarkin Fasiya. 8 Sa'an nan a wata na biyu na shekara ta biyu bayan sun zo gidan Allah a Yerusalem, sai Zerubbabel ɗan Sheltiyyel, Yeshuwa ɗan Yozadak, da sauran firistoci da Lebiyawa da waɗanda suka dawo daga bauta zuwa Yerusalem suka fara aiki. Suka sa Lebiyawa 'yan shekaru ashirin su kula da aikin gidan Yahweh. 9 Yeshuwa yasa 'ya'yansa da 'yan'uwansa, Kadmiyel yasa 'ya'yansa, (da zuriyar Hodabiya), kuma 'ya'yan Henadad da 'ya'yansu da 'yan'uwansa - dukkansu Lebiyawa ne - da suka haɗu tare wajen lura da masu yin aikin gidan Allah. 10 Masu ginin suka kafa harsashen ginin haikalin Yahweh. Wannan yaba firistoci da masu sa tufafinsu da kayan hurawarsu, su kuma Lebiyawa 'ya'yan Asaf suka yabi Yahweh da garaya, kamar yadda Dauda ya yi umarni. 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Yahweh, Cewa "Shi nagari ne! Amintaccen alƙawarinsa mai aminci ga Isra'ila ya tabbata har abada."Dukkan mutane suka tada babbar murya da ƙarfi suna yabon Yahweh saboda kafa harsashin ginin haikalin da aka yi. 12 Amma da yawa daga cikin firistoci da Lebiyawa, da manyan ubannin shugabanni, da tsofaffin mutanen da suka ga lokacin da aka kafa harsashen ginin haikali na farko suka yi kuka da ƙarfi. Amma da yawa suka rera waƙar farinciki da murna da muryoyi masu daɗi. 13 A sakamakon haka mutane ba su iya tantance muryar farinciki da ta baƙinciki ba, Don mutane suna ta kuka da matuƙar farinciki, kuma an jiwo ƙararsu daga nesa.

Sura 4

1 Yanzu kuwa waɗansu abokan gãba na Yahuda da Benyamin suka ji cewa mutanen da ke ƙasar bauta sun fara gina haikali domin Yahweh, Allahn Isra'ila. 2 Sai suka tuntuɓi Zarubbabel da sarakunan zuriyoyin kakaninsu. Suka ce da su, "Bari mu yi gini tare da ku, gama kamar ku, muna neman Allahnku kuma mun yi hadaya gare shi tun kwanakin da Esarhadon, sarkin Asiriya, ya kawo mu nan wurin." 3 Amma Zarubbabel da Yeshuwa da shugabanin dangogin kakannin suka ce, "Ba ku ba ne, amma mune waɗanda tilas ne mu gina gidan Allahnmu, gama mune waɗanda zasu yi gini domin Yahweh, Allah na Isra'ila, kamar yadda sarki Sairus na Fasiya ya umarta." 4 Sai mutanen ƙasar suka sa hannuwan mutanen Yahuda suka raunana; 5 Suka sa mutanen Yahuda suka tsorata da ci gaba da yin ginin. Suka kuma ba mashawartan cin hanci don su lalatar da shirin. A wannan lokacin sun yi haka a dukkan kwanakin sarki Sairus har zuwa mulkin Dariyos sarkin Fasiya. 6 To sai a farkon mulkin Ahasuras suka rubuto takardar tuhuma game da mazaunan Yahuda da Yerusalem. 7 A kwanakin Atazazas ne Bishilam, da Mitiredat, Tabiyel da aminansu suka rubuto wa Atazazas. An rubuta wasiƙar a harshen Aramaik aka kuma fassara. 8 Rehum babban rundunan sojoji da Shimshaya marubuci sun rubuta haka ga Atazazas game da Yerusalem. 9 Sai Rehum da Shimshaya da aminansu waɗanda ke Alƙalai da waɗansu hafsoshi a gwamnati, da Fasiyawa, daga mazajen Irek da Babila da mazajen Susa (wato Ilemawa) - suka rubuta wasiƙa - 10 suka haɗa kai da mutane masu daraja da Ashurbanifal ya tilasta su zama a Samariya suka bi su tare da sauran waɗanda ke a Lardin Gaba da Kogin. 11 Wannan ne kwafin wasiƙar da suka aika wa Atazazas: "Barorinka, mazajen Lardin Gaba da Kogin, sun rubuta wannan: 12 Bari sarki ya sani cewa Yahudawan da suka tafi daga gareka sun taso mana a Yerusalem don su gina birnin tayarwa. Sun kammala garun da gyare-gyaren harsasun. 13 Yanzu kuwa bari sarki ya sani cewa idan birnin nan ya ginu kuma an kammala garun, ba zasu bayar da kuɗin fito da haraji ba, amma zasu azabtar da sarakunan. 14 Tabbas saboda mun ɗanɗana gishirin fãda, bai cancanci mu ga wani raini na faruwa da sarki ba. Saboda haka ne muke sanar da sarki 15 ka duba daga cikin rubutun kididdiga na mahaifinka don ka tabbatar da cewa wannan birnin tayarwa ne da zai azabtar da sarakuna da lardunan. Ya sha tayar da matsaloli ga sarki da kuma larduna. Ya kuma zama cibiyar tawaye tun da daɗewa. Dalilin haka ne ma aka hallakar da birnin. 16 Muna sanar da sarki cewa idan aka gina wannan birnin da garun, to babu wani abin da zai rage dominka a Lardin Gaba da Kogin." 17 Sai sarkin ya aika da amsa ga Rehum da Shimshaya da aminansu a Samariya da sauran waɗanda ke a Lardin Gaba da Kogin: "Salama gareku. 18 Wasiƙar da kuka aika mani an karanta an kuma fassara mani. 19 Don haka nasa aka yi bincike kuma na gano cewa a kwanakin baya sun yi tayarwa da rashin hankali ga sarakuna. 20 Sarakuna masu iko sun yi mulki a kan Yerusalem kuma sun kasance da iko a kan kowanne abu a Lardin Gaba da Kogin. Ana kuma biyansu haraji. 21 Yanzu kuwa a yi umarni ga waɗannan mutanen su tsaya kuma kada su gina wannan birnin sai na umarta. 22 Ku yi hankali kar ku yi banza da wannan. Me zai sa a bar wannan jayayyar ta yi girma ta sa mu hasara a wannan masarauta? 23 Sa'ad da aka karanta umarnin sarki Atazazas a gaban Rehum, da Shimshaya da aminansu, sai suka fita da sauri zuwa Yerusalem suka sa Yahudawan su tsayar da ginin. 24 Don haka aiki a gidan Allah a Yerusalem ya tsaya har zuwa shekara ta biyu ta mulkin Dariyos sarkin Fasiya.

Sura 5

1 Sai annabi Haggai da Zakariya ɗan annabi Iddo suka yi annabci da sunan Allah na Isra'ila ga Yahudawa a Yahuda da Yerusalem. 2 Zarubbabel ɗan Sheltiyyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka tashi tsaye suka fara gina gidan Allah a Yerusalem tare da annabawan da suka ƙarfafa su. 3 Daga nan Tattenai gwamnan Lardin Gaba da Kogin, Shetar Bozenai, da abokan aikinsa suka zo suka ce masu, "Wane ne ya baku umarni ku gina wannan gidan ku kuma ƙarasa waɗannan katangun?" 4 Sai suka kuma ce, Mene ne sunayen mutanen da ke yin wannan ginin?" 5 Amma idanun Allah na kan dattawan Yahudawa kuma maƙiyansu basu tsayar da su ba. Suna jiran wasiƙar da za a aika wa sarki da kuma umarnin da za a komar masu game da wannan. 6 Wannan shi ne kwafin wasiƙar Tattenai wato gwamnan Lardin Gaba da Kogi, da Shetar Bozinai da tawagarsa a cikin Lardin Gaba da Kogi, wanda suka aikawa sarki Dariyos. 7 Sun aika da rahoto, suka rubuta wa sarki Dariyos haka, "Bari dukkan salama ta zama taka. 8 Bari sarki ya sani cewa mun je Yahuda gidan Allah mai Girma. Ana gininta da manyan duwatsu da katakan da aka shirya a ganuwar. Wannan aikin kuwa ana yin sa sosai da sosai, kuma yana tafiya dai-dai a hannuwansu. 9 Muka tambayi dattawan, 'Wa ya baku umarni ku gina wannan gida da wannan ganuwar?' 10 Mun kuma tambayi sunayensu domin ka iya sanin sunan kowanne mutum da ya jagorance su. 11 Suka amsa suka ce, 'Mu barorin wanda shi ne Allah na sama da ƙasa, kuma muna ginin wannan gida wanda aka gina a shekarun baya masu yawa a sa'ad da sarki mai girma na Isra'ila ya gina, ya kuma ƙarasa shi. 12 Koda ya ke, Sa'ad da kakaninmu suka sa Allah na sama ya yi fushi, sai ya bada su ga hannuwan Nebukadnezza, sarkin Babila, wanda ya rushe wannan gidan ya kuma ɗauke mutanen zuwa ɓauta a Babila. 13 Duk da haka, a shekara ta fari sa'ad da Sairus ya ke sarkin Babila, Sairus ya bada umarni a gina gidan Allah. 14 Sarki Sairus ya kuma mayar da kayayyakin zinariya da azurfa na gidan Allah da Nebukadnezza ya kawo daga haikali a Yerusalem zuwa ga haikali na Babila. Ya mayar da su ga Sheshbazza, wanda yasa ya zama gwamna. 15 Ya ce da shi, "‌Ɗauki waɗannan kayayyakin. Tafi ka aje su a haikali a Yerusalem. Bari a sake gina gidan Allah a wurin." 16 Sai Sheshbazza yazo ya ƙafa harsashe domin gidan Allah a Yerusalem; kuma ana kan yi, amma ba a ƙarasa shi ba.' 17 Yanzu kuwa, idan sarki ya yarda, sai a bincika a gidan ajiyar rahotonin dã a Babila koda akwai huƙunci daga Sarki Sairus game da gina gidan Allah a Yerusalem. To sai sarki ya aiko da ra'ayinsa gare mu.

Sura 6

1 Sai sarki Dariyos ya bada umarni a yi bincike a gidan ajiyar rahotanin dã a Babila. 2 A ƙasaitaccen birnin Ikbatana a Midiya aka sami takarda; wannan ne abin da aka rubuta a cikinta: 3 A shekara ta farko ta Sarki Sairus, Sairus ya bada umarni game da gidan Allah a Yerusalem: 'Bari gidan ya sake ginuwa domin ya zama wurin hadaya, bari a kafa harsasunsa, bari tsawonsa ya zama kamu 27, faɗinsa kamu 27, 4 da layin manyan duwatsu guda uku da layi ɗaya na sababbin katakai, kuma bari gidan sarki ya biya duk kuɗin da aka kashe. 5 Yanzu a dawo da kayayyakin zinariya da azurfa na gidan Allah wanda Nebukadnezza ya kawo Babila daga haikali a Yerusalem sai a aika da su kuma ga haikali a Yerusalem. Zaku kuwa aje su a gidan Allah.' 6 Yanzu Tattenai, gwamnan Lardin Gaba da Kogi da Shetar Bozinai da tawagar da ke Lardin Gaba da Kogi, ku rabu da su! 7 Ku bar aikin gidan nan na Allah yadda ya ke. Gwamna da dattawan Yahudawa zasu gina wannan gidan Allah a wancan wurin. 8 Ina umarta cewa tilas ne kuyi wannan domin waɗannan dattawan Yahudawan da suka gina wannan gida na Allah: Kuɗi daga asusun sarkin gaba da Kogi za a yi amfani da su a biya waɗannan mutanen don kada su tsayar da aikinsu. 9 Ko mene ne ake bukata - bijimai, ko raguna, ko 'yan raguna domin hadaya ga Allah na Sama, ko hatsi, ko gishiri, ko ruwan inabi, ko mai bisa ga umarnin firistocin Yerusalem - ku ba su waɗannan abubuwa kowacce rana babu fasawa. 10 Ku yi wannan domin su kawo bayarwarsu ga Allah na Sama kuma ku yi mani addu'a, sarki, da 'ya'yansa. 11 Ina umarta cewa duk wanda ya taka wannan doka, za a ciro ginshiƙi daga gidansa a soke shi da shi. Gidansa kuwa tilas ne a mayar da shi juji saboda wannan. 12 Bari Allah wanda yasa sunansa ya zauna a wurin ya cisge kowanne sarkin ko mutanen da suka ɗaga hannu su canza wannan doka, ko su lalata wannan gidan na Allah a Yerusalem. Ni, Dariyos, nake umarta wannan. Bari a yi tare da kula!" 13 To saboda umarnin da sarki Dariyos ya aika, Tattenai, gwamnan Lardin Gaba da Kogi da Shetar-Bozinai da abokan aikinsa, suka yi dukkan abin da Sarki Dariyos ya umarta. 14 Saboda haka dattawan Isra'ila suka yi ginin kamar yadda Haggai da Zakariya suka umarta ta wurin annabci. Suka gina shi bisa ga dokar Allah na Isra'ila da Sairus da Dariyos da Atazazas, sarakuna Fasiya 15 An kammala gidan a rana ta uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta mulkin sarki Dariyos. 16 Mutanen Isra'ila da firistoci da Lebiyawa da sauran masu zaman bauta suka yi bukin keɓe gidan Allah tare da jin daɗi. 17 Suka ba da bijimai ɗari da raguna ɗari da 'yan raguna ɗari huɗu domin keɓe gidan Allah. Awaki goma sha biyu aka bayar a matsayin bayarwa ta wanke zunubi domin dukkan Isra'ila, ɗaya domin kowacce kabilar Isra'ila. 18 Suka kuma sa firistoci da Lebiyawa su rarraba wa mutanen aiki domin sujada ga Allah a Yerusalem, kamar yadda aka rubuta a Littafin Musa. 19 Saboda haka waɗanda suke cikin bauta suka yi bukin idin Ƙetarewa a watan huɗu. 20 Firistocin da Lebiyawa dukka suka tsarkake kansu suka kuma yanyanka hadayun idin ‌Ƙetarewa domin dukkan waɗanda suka yi bauta, har da su kansu. 21 Mutanen Isra'ila da suka ci kaɗan daga cikin naman idin ‌Ƙetarewa su ne waɗanda suka dawo daga bauta suka kuma raba kansu daga rashin tsarkin mutanen ƙasar suka kuma biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila. 22 Cikin jin daɗi kuwa suka sha shagulgulan bukin gurasa marar gami har kwanaki bakwai, gama Yahweh ya kawo masu jin daɗi ya kuma juya zuciyar sarkin Asiriya ta ƙarfafa hannunsu a cikin aikin gidansa, gidan Allah na Isra'ila.

Sura 7

1 Yanzu bayan wannan, a zamanin mulkin Atazazas sarkin Fasiya, Ezra ya dawo daga Babila. Kakannin Ezra su ne kamar haka, Seraiya, Azariya, Hilkiya, 2 Shallum, Zadok, Ahitub, 3 Amariya, Azariya, Merayot, 4 Zerahiya, Uzzi, Bukki, 5 Abishuwa, Fenihas, Eliyeza, wanda shi ne ɗan Haruna babban firist. 6 Ezra ya dawo daga ƙasar Babila kuma ƙwararren marubuci ne cikin shari'ar Musa wanda Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bayar. Sarki ya ba shi dukkan abin da ya ke buƙata domin hannun Yahweh na tare da shi. 7 Wasu daga cikin zuriyar Isra'ila da kuma firistoci, da Lebiyawa, da mawaƙan haikali, da masu tsaron ƙofa da kuma waɗanda aka shirya domin hidima a haikali suma suka tafi Yerusalem a cikin wata na bakwai na mulkin Atazazas. 8 Ya isa Yerusalem a wata na biyar na wannan shekara. 9 Ya baro Babila a rana ta ɗaya na watan farko. A rana ta ɗaya ne na watan biyar ya isa Yerusalem, tun da hannun Allah mai kyau na tare da shi. 10 Ezra ya kafa zuciyarsa domin ya yi bincike, ya aikata, ya kuma koyar da farillai da hukumtai da dokokin Yahweh. 11 Wannan shi ne umarnin da sarki Atazazas ya ba Ezra firist da kuma marubucin dokoki da farillun Yahweh domin Isra'ila. 12 "Sarkin sarakuna Atazazas, zuwa ga firist Ezra, marubuci na dokokin Allah na sama: 13 Ina bada umarni cewa kowannene daga Isra'ila cikin harabar mulkina tare da firistocinsu da Lebiyawa da ya ke da niyar tafiya zuwa Yerusalem, zaya iya tafiya da kai. 14 Ni, sarki, tare da mashawartana guda bakwai, muna aiken ku dukka ku bincika game da Yahuda da kuma Yerusalem bisa ga dokokin Allah, wanda ke cikin hannuwanku. 15 Ku dawo da azurfa da zinariyar da suka bayar da yardar rai zuwa ga Allah na Isra'ila, wanda mazauninsa ke a Yerusalem. 16 Ku bayar hannu sake dukkan azurfa da zinariya da dukkan Babila ta bayar kuma da dukkan abin da mutane da firistoci suka bayar hannu sake domin gidan Allah a Yerusalem. 17 Saboda haka ku saya da farashi cikakke shanun, da ragunan, da 'yan tumakin, da hatsi da baye-baye na sha. Ku miƙa su a bisa bagadin da ke cikin gidan Allahnku a Yerusalem. 18 Ku yi haka da sauran azurfar da zinariyar dukkan abin da kuka ga ya dace maku da 'yan'uwanku, domin ku gamshi Allahnku. 19 Ku ɗibiya kayayyakin da aka yi maku kyautarsu a gabansa domin hidima cikin gidan Allahnku a Yerusalem. 20 Duk wani abin da ake buƙata domin gidan Allahnku da za kuyi bukatarsa, sai a biya daga cikin ma'ajina. 21 Ni, sarki Atazazas, na yi umarni ga dukkan masu ajiya cikin Lardin Gaba da Kogi, da cewa dukkan abin da Ezra zai yi buƙata daga gareku bari a ba shi a cike, 22 har sama da talantai na azurfa ɗari, tuli buhu ɗari na hatsi, da ruwan inabi gallan ɗari, da gallan ɗari na mai, da kuma gishiri babu iyaka. 23 Dukkan abin da suka fito daga umarnin Allah na Sama, ka aikata da kuzari, domin gidansa. Donme ne ne hasalarsa za ta yi ƙuna a bisa masarauta ta da 'ya'yana? 24 Muna sanar da su game da ku da kada su ɗora maku wata tãra ko haraji ga kowanne firistoci, ko Lebiyawa, ko mawaƙa, ko masu tsaron ƙofa, ko ga mutanen da aka ba hidimar haikalin da kuma bayin gidan wannan Allah. 25 Ezra, ta wurin hikimar da Allah ya baka, dole ka naɗa alƙalai da masanan hikima su yiwa mutane hidima a cikin dukkan Lardin Gaba da Kogi, su kuma yi hidima ga kowannene da ya san shari'ar Allahnka. Dole kuma ka koyar da shari'ar ga dukkan waɗanda basu san dokar ba. 26 Ku hori duk wanda ba ya yi cikakkiyar biyayya ga shari'ar Allah ba ko shari'ar sarki ba, ko ta mutuwa, ko kora daga ƙasa, ko a ƙwace mallakarsu, ko jefawa cikin kurkuku. 27 Yi yabo ga Yahweh, Allahn kakanninmu, wanda ya sanya dukkan wannan cikin zuciyar sarki ya ɗaukaka gidan Yahweh cikin Yerusalem, 28 kuma wanda ya nuna amincin alƙawarinsa gareni a gaban sarki, da mashawartansa, da kuma dukkan majalisarsa masu iko. Na sami ƙarfafawa daga hannun Yahweh Allahna, sai na tara shugabanni daga Isra'ila su tafi tare da ni.

Sura 8

1 Waɗannan su ne shugabanni na kakannin iyalansu waɗanda suka baro Babila tare da ni a zamanin mulkin sarki Atazazas. 2 Na zuriyar Fenihas, Geshom. Na zuriyar Itamar, Daniyel. Na zuriyar Dauda, Hattush, 3 wanda ya zama na zuriyar Shekaniya, wanda ya zama daga zuriyar Farosh; da kuma Zakariya, kuma tare da shi akwai mazaje 150 da aka lisafta su cikin rubutattun tarihin zuriyarsu. 4 Na zuriyar Fahat Mowab, Elihonai ɗan Zerahiya kuma tare da shi akwai mazaje ɗari biyu. 5 Na zuriyar Zatti, Ben Yahaziyel kuma tare da shi akwai mazaje ɗari uku. 6 Na zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan kuma tare da shi an lisafta mazaje hamsin. 7 Na zuriyar Ilam, Yeshayya ɗan Ataliya kuma tare da shi an lisafta mazaje saba'in. 8 Na zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mikayel kuma tare da shi an lisafta mazaje tamanin. 9 Na zuriyar Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel kuma tare da shi aka lisafta mazaje 218. 10 Na zuriyar Bani, Shelomit ɗan Yesofiya kuma tare da shi aka lisafta mazaje 160. 11 Na zuriyar Bebai, Zakariya ɗan Bebai kuma tare da shi aka lisafta mazaje ashirin da takwas. 12 Na zuriyar Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan kuma tare da shi aka lisafta mazaje 110. 13 Waɗanda suke daga zuriyar Adonikam suka zo daga baya. Waɗannan su ne sunayensu: Elifelet, Yewuyel, tare da Shemayya kuma mazaje sittin ne suka zo tare da su. 14 Na zuriyar Bigbai, Uttai da Zakku kuma tare da shi aka lisafta mazaje saba'in. 15 Na tara matafiyan a mashigin daya tafi har zuwa Ahaba, kuma muka yi sansani a nan kwana uku. Na bincike mutanen da kuma firistoci, amma babu wani daga zuriyar Lebi a nan. 16 Sai na aika a kirawo mani Eliyeza, da Ariyel, da Shemayya, da Elnatan, da Yarib, da kuma Elnatan da Natan, da Zakariya da kuma Meshullam - waɗanda su ne shugabanni - da kuma Yoyarib tare da Elnatan waɗanda su ne masu koyarwa. 17 Daga nan sai na aike su wurin Iddo, shugaban da ke a Kasifiya. Na faɗa masu abin da zasu faɗawa Iddo da kuma danginsa, su bayi na haikali da ke zaune a Kasifiya, wato, su aika mana da bayi domin gidan Allah. 18 Sai suka aika mana ta hannun Allahnmu mai nagari mutum mai suna Sherebiya, mutum mai tattali. Shi daga zuriyar Mahali ne ɗan Lebi ɗan Isra'ila. Ya zo da 'ya'ya sha takwas da 'yan'uwa. 19 Hashabiya ya zo tare da shi. Haka kuma akwai Yeshayya, ɗaya daga cikin 'ya'yan Merari, da ɗan'uwansa tare da 'ya'yansu, dukkan su mazaje ashirin. 20 Cikin waɗanda aka ɗaurawa hidimar haikali, waɗanda Dauda da bayinsa suka ɗora wa haƙin yiwa Lebiyawa hidima: 220, kowanne ɗayansu aikinsa bisa ga sunansa. 21 Sai nayi shelar azumi a mashigin Ahaba domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu biɗi hanya madaidaiciya dominmu, domin ƙanananmu, da dukkan mallakarmu. 22 Na ji kunyar tambayar sarki sojoji ko dawakai da zasu yi tsaronmu daga maƙiya a hanya, gama mun gaya wa sarki, 'hannun Allah na bisa dukkan waɗanda suka neme shi da gaskiya, amma ƙarfinsa da fushinsa na bisa dukkan waɗanda suka manta da shi.' 23 Sai muka yi azumi muka nemi Allah game da wannan, muka yi roko gare shi. 24 Daga wannan sai na zaɓi mazaje guda sha-biyu daga cikin shugabannin firistoci: Sherebiya, Hashabiya, da kuma yan'uwansu guda goma. 25 Na auna masu azurfa goma, da zinariya, da kayayyaki da baye-baye na gidan Allah da sarki, da mashawartansa da kuma shugabanninsu, da dukkan Isra'ila suka bayar hannu sake. 26 Sai na auna cikin hannunsu azurfa talanti 650, talanti ɗari na kayayyakin azurfa, talanti ɗari na zinariya, 27 kwanonin zinariya guda ashirin waɗanda aka haɗa su dukka aka ƙimanta farashinsu akan sulallan zinari dubu ɗaya, da kuma a kan gogaggun tagulla biyu masu daraja kamar zinariya. 28 Sa'an nan na ce masu, "An keɓe ku ga Yahweh, da waɗannan kayayyakin, kuma azurfar da zinariyar dukka baiko ne na yardar rai ga Yahweh, Allah na kakaninku. 29 Ku kula da su ku kuma adanasu, har sai kun auna su a gaban shugabannin firistoci, da Lebiyawa, da kuma shugabannin kakannin zuriyar Isra'ila a Yerusalem cikin ɗakunan gidan Allah." 30 Su firistoci da kuma Lebiyawa suka yi na'am da azurfa, da zinariya da kuma kayayyakin da aka auna domin su tafi da su Yerusalem, zuwa gidan Allahnmu. 31 Muka fito daga mashigin Ahaba a rana ta sha biyu na watan farko domin mu tafi Yerusalem. Hannun Allahnmu na a bisanmu; ya kare mu daga hannun maƙiyanmu da kuma waɗanda suka yi niyyar yi mana kwanto a kan hanya. 32 Sai muka shiga Yerusalem muka kwana uku a cikinta. 33 Daga nan a rana ta huɗu aka auna azurfa, da zinariya, da kuma kayayyakin cikin gidan Allahnmu ta hannun Meremot ɗan Yuriya firist, kuma tare da shi akwai su Eliyeza ɗan Fenihas, Yozabad ɗan Yeshuwa, da kuma Nodiya ɗan Binnui Balebi. 34 Aka tabbatar da jimilla da nauyin komai. Dukkan nauyin komai aka rubuta a wannan lokacin. 35 Waɗanda suka komo daga bautar talala, su mutanen 'yan gudun hijira, suka miƙa ƙonannun baye-baye zuwa ga Allah na Isra'ila: raguna goma sha biyu, awakai tasa'in da shida, tumaki guda saba'in da bakwai, da kuma tunkiyoyi goma sha biyu domin hadayar zunubi. Dukkansu hadayu ne na ƙonawa na Yahweh. 36 Sa'an nan suka ba da umarnai na sarki ta hannun manyan shugabannin sarki da kuma gwamnonin Lardin Gaba da Kogi. Sai kuma suka taimaki jama'ar da kuma gidan Allah.

Sura 9

1 Bayan waɗannan abubuwa sun faru, shugabanni suka same ni suka ce, "Mutanen Isra'ila, da firistoci da Lebiyawa basu keɓe kansu daga mutanen sauran ƙasashe ba da kuma abin ƙyamarsu: Kan'aniyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Yebusiyawa da Ammoniyawa da Mowabiyawa da Masarawa da kuma Amoriyawa. 2 Domin sun ɗauki wasu daga cikin 'yan matansu da samarinsu, kuma sun hada mutane masu tsarki da sauran mutanen ƙasashen, shugabanni da magabata su ne na farko ga wannan rashin bangaskiya." 3 Lokacin da na ji wannan, na yayyage rigata da alkyabbata na kuma tsittsige gashin kaina da gemuna, sai na zauna a ruɗe. 4 Sai dukkan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra'ila saboda wannan rashin aminci da suka same ni lokacin da nake zaune ina jin kunya har baikon yamma. 5 Amma a lokacin baikon yamma sai na tashi daga matsayin ƙasƙanci a cikin rigata da alkyabbata a yayyage, na russuna da gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Yahweh Allahna. 6 Na ce, "Ya Allahna, ina jin kunya da takaici in ɗaga fuskata gare ka, muguntarmu ta ƙaru a kanmu, kuma zunubanmu sun yi girma har sun kai sammai. 7 Tun daga lokacin kakanninmu har yanzu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu sun bada mu a hannun sarakunan wannan duniya, ga takobi, ga bauta, da ganima da kuma kunyatar da mu, kamar yadda muke a yau. 8 Amma yanzu a ƙaramin lokaci, alheri daga Yahweh Allahnmu ya zo ya bar mana ringi ya kuma bamu wuri a wurinsa mai tsarki. Wannan yasa Allahnmu ya buɗe mana idanu, ya kuma bamu 'yar wartsakewa daga bautarmu. 9 Domin mu bayi ne, amma duk da haka Allahnmu bai manta da mu ba amma ya cika alƙawarinsa da amincinsa a gare mu. Ya yi wannan ta wurin sarkin Fasiya domin ya bamu ƙarfi, don mu sake gina gidan Allahnmu mu kuma sake gyaransa. Ya yi wannan saboda ya bamu tsaron gina garu a Yahuda da Yerusalem. 10 Amma yanzu, Allahnmu, me zamu ce bayan wannan? Mun manta da umarnanka, 11 umarnan daka ba bayinka annabawa, daka ce, "Wannan ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta ƙazamtaciyar ƙasa ce. Ta ƙazamtu ta wurin mutanen ƙasar da abubuwan ƙyamarsu. Sun cikata daga ƙarshe zuwa ƙarshe da abubuwansu na ban ƙyama. 12 Saboda haka, kada ku bada 'ya'yanku 'yan mata su auri 'ya'yansu maza; kada ku ɗauki 'ya'yansu mata don 'ya'yanku maza, kuma kada ku nemi salamarsu da jin daɗi, don zaku yi ƙarfi ku ci abu mai kyau a ƙasar, domin zaku sa 'ya'yanku su gaje ta a dukkan lokaci." 13 Bayan da dukkan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa - tun da kai, Allanmu, ka ɗauke dukkan laifoffinmu ka kuma bar mana ringi - 14 ko zamu sake karya umarninka mu kuma yi auratayya tare da waɗannan mutane da ke ƙazamtattu? Ba zaka yi fushi da mu ka shafe mu don kada a sami wani da ya rage, har babu wani da zai tsira ba? 15 Yahweh, Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama mun zama 'yan ringi da suka tsira a wannan rana. Duba! Ga mu nan gabanka da zunubanmu, don ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.

Sura 10

1 Sa'ad da Ezra ya ke yin addu'a da roƙon gafara, ya yi kuka har yasa kansa ƙasa a gaban gidan Allah. Sai babban taron jama'a maza da mata da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa, don mutane na kuka mai zafi sosai. 2 Shekaniya ɗan Yehiyel na zuriyar Elam ya ce da Ezra, "Mun yiwa Allahnmu rashin aminci har mun auri mata bãƙi daga mutanen ƙasar waje. Amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila. 3 Saboda haka yanzu bari muyi alƙawari da Allahnmu mu kori dukkan matan da 'ya'yansu bisa ga umarnin shugabanni da waɗanda suke rawar jiki don umarnin Allahnmu, bari a yi haka bisa ga doka. 4 Tashi, domin wannan hakinka ne ka aiwatar, mu kuma muna tare da kai. Ka yi ƙarfin hali, ka yi wannan." 5 Ezra kuwa ya tashi, yasa shugabannin firistoci, Lebiyawa, da dukkan Isra'ila su yi alƙawarin aiki ta wannan hanyar. Saboda haka dukkansu suka ɗauki alƙawarin rantsuwa. 6 Sai Ezra ya tashi daga gidan Allah, ya tafi ɗakunan Yehohanan ɗan Eliyashib. Bai ci ko da gurasa ba bai kuma sha ruwa ba, tun da ya ke yana baƙinciki a kan rashin amincin waɗanda suka yi a zaman talala. 7 Saboda haka suka aika da magana a Yahuda da Yerusalem ga dukkan mutane da suka komo daga zaman talala su kasance a Yerusalem. 8 Duk wanda bai zo ba a cikin kwana uku bisa ga umarni daga shugabanni da dattawa zai rasa dukkan abin da ya mallaka za a kuma ware shi daga cikin babban taron mutanen da suka dawo daga zaman talala. 9 Sai dukkan mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Yerusalem a cikin kwana uku. A ranar ashirin ga watan tara. Dukkan mutanen suka tsaya a dandalin gidan Allah, suna kuma rawar jiki saboda maganar da kuma ruwan sama. 10 Ezra firist kuma ya miƙe tsaye ya ce, "Ku kunyi rashin aminci. Kun zauna da mata bãƙi ta haka kuka ƙarawa Isra'ila laifi. 11 Amma yanzu sai ku bada yabo ga Yahweh, Allah na kakanninku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware daga mutanen ƙasar da mata bãƙi. 12 Dukkan taron suka amsa da babbar murya, '"Za muyi kamar yadda ka ce. 13 Amma, akwai mutane da yawa, kuma lokacin marka ne. Ba mu da ƙarfin tsayawa a waje, kuma wannan ba aikin da za ayi shi a kwana ɗaya ko biyu bane, tun da mun yi babban laifi a wannan al'amari. 14 Saboda haka bari shugabanninmu su wakilci dukkan taron. Bari dukkan waɗanda suka bar baƙin mata su zauna a biranenmu su zo su sa lokaci tare da dattawan birni da kuma alƙalan birnin har sai fushin Allah ya huce daga kanmu. 15 Yonatan ɗan Asahel da Yazeyya ɗan Tikba ne basu yarda da wannan ba, da Meshullam da Shabbetai Balebi suka goyi bayansu. 16 Saboda haka mutane waɗanda suka komo daga zaman talala suka yi wannan. Ezra firist ya zaɓi maza, da dattawa kakanin zuriyarmu da gidaje - dukkansu kuwa ta wurin sunaye, sai suka duba al'amarin a kan rana ta farko ga wata na goma. 17 Sun gama binciken a rana ta farko a wata na farko ga mazajen da suke zama tare da baƙin mata. 18 A cikin zuriyar firistoci ma akwai waɗanda suke zama da bãƙin mata. A cikin zuriyar Yeshuwa ɗan Yehodak da ɗan'uwansa su ne Mãseyya, Eliyeza, Yarib da Gedaliya. 19 Suka yi niyyar sakin matansu. Tun da su masu laifi ne, suka bada baikon rago daga cikin garkensu don laifinsu. 20 A cikin zuriyar Imma akwai Hanani da Zebadiya. 21 A cikin zuriyar Harim akwai Mãseyya da Iliya da Shemayya da Yehiyel da Uzziya. 22 A cikin zuriyar Fashu akwai Elihonai da Mãseyya, Isma'il da Netanel da Yozabad da Elasa. 23 A cikin Lebiyawa akwai Yozabad da Shimei da Kelayya - wato Kelita, Fetahiya, Yahuda da Eliyeza. 24 a cikin mawaƙa akwai Eliyashib. 25 A cikin masu tsaron ƙofa akwai Shallum, Telem da Uri. A cikin sauran Isra'ilawa - a cikin zuriyar Farosh akwai Ramiya, Izziya, Malkiya, Miyamin, Eliyeza, Malkiya da Benayya. 26 A cikin zuriyar Elam akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot da Iliya. 27 A cikin zuriyar Zattu akwai Elihonai, Eliyashib, Mattaniya, Yeremot, Zabad da Aziza. 28 A cikin zuriyar Bebai akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai da Atlai. 29 A cikin zuriyar Bani akwai Meshullam, Malluk, Adayya, Yashub da Shil Yeremot. 30 A cikin zuriyar Fahat Mowab akwai Adana, Kelal, Benayya, Mãseyya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi da Manasse. 31 A cikin zuriyar Harim akwai Eliyeza, Ishiya, Malkiya, Shemayya, Shimiyon, 32 Benyamin, Malluk da Shemariya. 33 A cikin zuriyar Hashum akwai Mattenai, Matatta, Zabad, Elifelet, Yeremai, Manasse, Shimei. 34 A cikin zuriyar Bani akwai Mãdai, Amram, Uwel, 35 Benayya, Bedeya, Keluhi, 36 Waniya, Meremot, Eliyashib, 37 Mattaniya, Mattenai, da Yãsu. 38 A cikin zuriyar Binnuyi akwai Shimei, 39 Shelemiya, Natan, Adayya, 40 Maknadebai, Shashai, Sharai, 41 Azarel, Shelemiya, Shemariya, 42 Shallum, Amariya da Yosef. 43 A cikin zuriyar Nebo: Yehiyel, Matitiya, Zabad, Zebina, Yaddai da Yowel da Benayya. 44 Dukkan waɗannan sun auro mata bãƙi kuma suna da 'ya'ya tare da wasun su.

Littafin Nehemiya
Littafin Nehemiya
Sura 1

1 Maganar Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan: A wata na Kislif, a shekara ta ashirin, a lokacin da nake a fãdar Shusha, 2 Sai wani daga cikin 'yan'uwana mai suna Hanani ya zo tare da waɗansu mutane daga Yahuda, sai na tambaye su labarin Yahudawan da suka tsira, da kuma sauran Yahudawan da ke a can, waɗanda ke a Yerusalem. 3 Suka ce da ni "waɗanda suka kuɓuta daga zaman bauta suna cikin babbar damuwa da wulaƙanci, saboda ganuwar Yerusalem ta karye ta faɗi, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta" 4 Nan da nan bayan na ji waɗannan maganganu sai na zauna na yi kuka, har tsawon kwanaki ina damuwa da azumi a gaban Yahweh na sama. 5 Sai na ce Yahweh "kai ne Ubangiji Allah na sama, Allah wanda ya ke da girma da nagarta, mai cika alƙawari, mai kuma madawammiyar ƙauna ga masu ƙaunarsa da kuma kiyaye dokokinsa. 6 Ka ji addu'ata ka kuma buɗe idanunka, don ka ji addu'o'in bayinka da nake yi a gare ka dare da rana, don mutaten Isra'ila bayinka. Ina furta zunuban mutanen Isra'ila, waɗanda suka yi maka. Duk da ni da gidan ubana mun yi zunubi. 7 Mun yi aikin mugunta sosai a gabanka kuma bamu kiyaye dokokinka da farillanka waɗanda ka ba mu ba, da kuma ƙa'idojin da ka umarci bawanka Musa. 8 Ka tuna da abin da ka umarci bawanka Musa, cewa "In kun yi rashin biyayya, zan warwatsa ku cikin al'ummai, 9 amma in kun komo gare ni kuka kuma bi umarnina kuka aikata su, to ko da ya ke an warwatsa mutanenku a faɗin duniya, zan tattaro su daga can zan kuma kawo su wurin nan da na zaɓa domin sunana ya zauna." 10 Yanzu su bayinka ne da kuma mutanenka, waɗanda ka kuɓutar da ƙarfin ikonka da kuma ƙarfin dantsenka. 11 Yahweh ina roƙon ka, ka saurari addu'ar bayinka yanzu, kuma addu'ar bayinka waɗanda ke son yi maka biyayya, yanzu ka ba bawanka nasara, ka kuma ba shi tagomashi a gaban wannan mutum." Ni mai aikin shayar da sarki ne.

Sura 2

1 A watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar Atazazas sarki, ya zaɓi ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin na ba sarki. Sai ya zamana fuskata ta ɓaci a gaban sarki kuma ban taba ɓata fuska a gabansa ba. 2 Amma sarki ya ce mani " me ya sa fuskarka ta ɓaci haka? Kuma gashi ba ciwo kake yi ba. Hakika wannan damuwar zuciya ce "Daga nan sai na tsorata sosai. 3 Na ce da sarki "Ran sarki ya daɗe! me zai hana ni baƙinciki? Da ya ke birni da maƙabartar iyayena sun zama kufai, kuma an ƙone ƙofofinta da wuta." 4 Sai sarki ya ce mani "Me kake so in yi?" Sai na yi addu'a ga Allah na sama. 5 Sai na amsa wa sarki" Idan ya gamshi sarki, in kuma na sami tagomashi a idon sarki, sai ka aike ni Yahudiya, garin maƙabartar iyayena, don in sake gina shi." 6 Sai sarki ya amsa mani (sarauniya kuma tana zaune a gefen sarki), "Har zuwa yaushe za ka ɗauka, kuma yaushe za ka dawo?" Bayan na faɗawa sarki lokacin da zan dawo sai ya yi farincikin aike na. 7 Sai na ce da sarki "Idan ya gamshi sarki, ina roƙo a ba ni wasiƙu domin gwamnonin lardin da ke gefen rafi don su bani damar wucewa ta yankunansu a kan hanyata ta zuwa Yahuda. 8 Kuma ina roƙo a bani wasiƙa domin in ba Asaf mai kula da mashigin dajin sarki don ya ba ni katakan da zan yi madogarai na mashigin kusa da haikalin, da kuma ganuwar birnin, da kuma ɗakin da zan zauna." To da ya ke hannun Allah na tare da ni, sai sarki ya yarda da buƙatuna. 9 Sai na zo wurin gwamnoni a cikin Lardi Gaba da Kogin na basu wasiƙun sarki. Sarki kuma ya haɗa ni tare da waɗansu jarumawa na sojojin dawakai. 10 Lokacin da Samballat Bahorine da kuma Tobiya Ba'amone bayi suka ji wannan, sai suka da mu sosai cewa wani ya zo don ya taimaki mutanen Isra'ila. 11 Sai na zo Yerusalem na zauna a can har kwana uku. 12 Sai na tashi da dare ni da mutane kima da ke tare da ni. Ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi domin Yerusalem ba. Ba dabba tare da ni, in ban da wacce na ke hawa ba. 13 Da duhu sai na bi ta Ƙofar Kwari, kusa da Rijiyar Dila zuwa Ƙofar Kashin Shanu, na dudduba ganuwar Yerusalem, an rushe ta kuma a buɗe take, aka kuma ƙone ƙofofinta na katakai da wuta. 14 Daga nan sai na je ƙofar ƙorama da kuma Madatsin ruwan Sarki. Wurin yana da matsi sosai ga dabbar da nake a kai har da za ta iya wucewa ta ciki. 15 To sai na tafi da duhu ta kwari na dudduba ganuwar, sai na dawo na shiga Ƙofar Kwari, ta haka na dawo. 16 Shugabanni basu san inda na je da kuma abin da na yi ba, kuma ban sanar da Yahudawa ba tukuna, ban kuma faɗa wa firistoci ba, hakanan ma manyan mutanen garin, da kuma sauran mutanen da suka yi aikin. 17 Sai na ce da su, "Kun ga masifar da muke ciki, yadda Yerusalem ta zama kufai kuma an ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sake gina ganuwar Yerusalem, don kada mu ƙara zama abin wulaƙanci." 18 Na faɗa masu cewa hannun Allah na tare da mu da kuma maganar da sarki ya faɗa mani. Sai suka ce "Mu tashi mu kama ginin." Sai suka ƙarfafa hannuwansu don wannan aiki nagari. 19 Amma lakacin da Samballat Bahorine, da Tobiya bawan nan Ba'amone, da Geshem Balarabe suka ji labarin aikin, sai suka yi mani ba'a da reni, suka ce, "Me ku ke yi? Kuna yiwa sarki tayarwa ne?" 20 Sai na amsa masu na ce, "Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa ne kuma za mu tashi muyi ginin. Amma ku baku da gãdo, ko iko, kuma baku da tarihin da zaku ce naku ne a Yerusalem".

Sura 3

1 Eliyashib ya tashi tare da 'yan'uwansa firistoci, sai suka gina Ƙofar Tumaki. Suka ke‌ɓe ta suka sa ƙofofinta a inda suke. Suka keɓe ta har zuwa Hasumiyar Ɗari da kuma Hasumiyar Hananel. 2 A gaba da shi sai mutanen Yeriko suka yi aiki, a gaba da su kuma Zakkur ɗan Imri ne ya yi aiki. 3 'Ya'yan Hassina'a ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka sa mata madogarai, da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. 4 Meremot ne ya gyara sashi na gaba. Shi ɗan Yuriya ne ɗan Hakkoz. Gaba da su sai Meshullam ya gyara. Shi ɗan Berekiya ne ɗan Meshezabel. Gaba da su sai Zadok ya gyara. Shi ɗan Ba'ana ne. 5 Gaba da su sai Tikoyitawa suka gyara, amma shugabanninsu suka ƙi yin aikin da masu duba aikinsu suka umarce su. 6 Yohaida ɗan Fasiya da Meshullam ɗan Besodeiya ne suka gyara Tsohuwar Ƙofa. Suka sa mata madogarai, da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. 7 Gaba da su sai Melatiya mutumin Gibiyon da Yadon mutumin Meronot, su mutanen Gibiyon da Mizfa ne, suka yi gyare-gyaren inda gwamnan Lardin Gaba da Kogi ke zama. 8 Gaba da shi sai Uziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin maƙeran zinariya, ya yi gyara, Gaba da shi kuma sai Hananiya mai yin turare. Su ne suka sake gina Yerusalem da Babban Garun. 9 Gaba da su kuma sai Refayiya ɗan Hur ya gyara. Shi ke mulkin rabin gundumar Yerusalem. 10 Gaba da su sai Yedayiya ɗan Harumaf ya gyara kusa da gidansa. Gaba da shi sai Huttush ɗan Hashabniya ya gyara. 11 Malkiya ɗan Harim da Hasshub ɗan Fahat- Mowab suka gyara ɗaya sashin tare da Hasumiyar Matoya. 12 Gaba da su sai Shallum ɗan Hallohesh, shugaban sashin gundumar Yerusalem, ya yi gyara tare da 'ya'yansa mata. 13 Hannun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sake gina ta suka sa ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. Suka yi gyara har zuwa kamu dubu tun daga Ƙofar Kashin Shanu. 14 Malkiya ɗan Rekab, shugaban gundumar Bet Hakkerem, ya gyara Ƙofar Kashin Shanu. Ya gina ta ya sa ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. 15 Shallun ɗan Kol-Hozeh, shugaban gundumar Mizfa, ya sake gina Ƙofar Ruwa. Ya gina ta ya sa murfi akan ta da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. Hakanan ya sake gina Shirayin Siloyam a lambun sarki, tun daga ƙasa har ya zuwa birnin Dauda. 16 Nehemiya ɗan Azbuk, shugaban rabin gundumar Bet Zur, ya yi gyara har zuwa wurin kabarin Dauda, zuwa madatsar ruwan da mutum ya yi, har ya kai gidan manyan mutane. 17 Bayansa sai Lebiyawa suka yi gyara, tare da Rehum ɗan Bani, gaba da shi kuma sai Hashabiya, shugaban rabin gundumar Keilah don gundumarsa. 18 Bayansa sai jama'ar ƙasarsu suka yi gyara, suka haɗa da Binuyi ɗan Henadad, shugaban rabin gundumar Keilah. 19 Gaba da shi sai, Ezar ɗan Yeshuwa, shugaban Mizfa, ya gyara ɗaya sashin da ke fuskantar ƙurya har kwanar garun. 20 Bayansa sai Baruk ɗan Zabbai ya ba da kansa domin gyaran ɗaya gefen, tun daga kwanar garun har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist. 21 Bayansa sai Meremot ɗan Yuriya ɗan Hakkoz ya gyara ɗaya gefen ƙofar gidan Eliyashib har zuwa ƙarshen gidan Eliyashib. 22 Gaba da shi sai firistoci, da sauran mutane daga yankin Yerusalem suka yi gyara. 23 Gaba da su Benyamin da Hasshub suka gyara gefen gidajensu. Gaba da su Azariya ɗan Ma'asiya ɗan Hananiya ya gyara kusa da gidansa. 24 Gaba da shi Binuyi ɗan Henadad ya gyara ɗaya gefen daga gidan Azariya zuwa kwanar garun. 25 Falal ɗan Uzai ya yi gyaran wajen kwanar bango, da kuma hasumayar da ta kai har dogon gidan sarki a fãdar tsaro. Gaba da shi sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyara. 26 Barorin da ke zama a Ofel suka yi gyara har kusa da Ƙofar Ruwa a wajen gabas da kuma bangon da ya haɗe garin. 27 Daga shi sai Tekoyawa suka yi gyaran ɗaya gefen da ke kusa da babbar hasumaya har zuwa garun Ofel. 28 Sai firistoci suka gyara sama da Ƙofar Doki, kowanne kusa da gidansa. 29 Bayansu sai Zadok ɗan Immar ya gyara wajen sashen gidansa. Daga bayansa sai Shemaiya ɗan Shekaniya mai tsaron ƙofar gabas ya yi gyara. 30 Bayansa Hananiya ɗan Shelemiya da Hanun ɗan Zalaf na shida, ya gyara ɗaya ɓangaren. Bayansa sai Meshullam ɗan Berekiya ya gyara kusa da ɗakin da ya ke zama. 31 Bayansa sai Malkiya, ɗaya daga cikin maƙeran azurfa, ya yi gyara har zuwa gidan masu hidima a haikali da kuma na fataken dake haɗe da ƙofa da kuma ɗakin fira na kan kwana 32 Maƙeran zinariya da kuma fatake suka gyara sama da ɗakin fira da ke kwanar Ƙofar Tumaki.

Sura 4

1 Da Sanballat ya ji muna yin ginin ganuwar, sai abin ya dame shi, ya fusata sosai, ya yi wa Yahudawa ba'a. 2 A gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya, sai ya ce, mene ne waɗannan kumaman Yahudawan ke yi? Ko zasu iya dawo da birni don kansu? Ko zasu miƙa hadayu? Ko zasu iya gama aikin a rana ɗaya? Ko zasu iya samun duwatsu daga tarin matattun duwatsu da aka ƙone? 3 Tobiya Ba'amone na tare da shi, sai ya ce, "Ai ganuwar da suke ginawa dila ma kawai in ya bi ta kan abin da suke ginawa zai rushe ganuwarsu ta dutse!" 4 Ya Allahnmu, ka ji yadda aka rena mu. Ka mayar masu da reninsu a kansu, ka sa a kwashe su suzama ganimar yaƙi zuwa ƙasar da zasu yi zaman jarun. 5 Kada ka rufe laifofinsu, kada ka shafe zunubansu daga fuskarka, don sun sa maginan sun yi fushi, 6 To sai muka gina katangar kuma katangar ta haɗu har ta kai rabin tsawonta, don jama'ar na da marmarin aiki. 7 Amma bayan Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Amoniyawa, da kuma Ashdodiyawa suka ji yadda ake yin gyaran katangar Yerusalem da kuma yadda aka gyaggyara wuraren da suka lalace, sai matsanancin fushi ya kama su. 8 Sai duk suka haɗa baki, suka fito don su yaƙi Yerusalem, da kuma kawo rikici a cikinta. 9 Amma muka yi addu'a ga Allahnmu kuma muka sa masu tsaronsu dare da rana, saboda wannan maƙarƙashiyar tasu. 10 Daga nan sai mutanen Yahuda suka ce, "Ƙarfin ma'aikatan yana kasawa. Akwai kayayyaki da yawa da za a kwashe, kuma ba zamu iya ci gaba da ginin ganuwar ba". 11 Maƙiyanmu suka ce, "Ba za su gan mu ko su san lokacin da zamu auko masu mu kashe su ba, mu tsayar da aikin." 12 A lokacin, Yahudawan da ke zama kusa da su ne suka zo ta ko'ina suka yi magana da mu sau goma, suka gargaɗe mu akan maƙarƙashiyar da suke shirya mana. 13 Sai na sa mutane a gangaren ganuwar a wuraren da ke da hatsari nasa kowanne iyali da takobinsu, mãshi, da kibiya. 14 Daga nan sai na miƙe na duba, sai na ce da manyan mutane da shugabanni, da sauran mutanen, "Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda ya ke da girma da kuma ban razana. Ku yi yaƙi domin iyalinku da 'ya'yanku maza da mata da matayenku da kuma gidajenku." 15 Sai ya kasance bayan maƙiyanmu sun ji mun san shirye-shiryensu, Allah kuma ya rikirkita shirye-shiryensu, sai kowa ya koma ya kama aikin garun, kowa ga nasa aikin 16 Tun daga rabin barorina suka koma aikin katanngar, rabinsu kuma suka riƙe mãsu da kwalkwali da kwari, suka kuma sa sauran kayan yaƙi, shugabanni kuma na bayan mutanen Yahuda. 17 Mutanen dai dake aikin ginin katangar da kuma ɗauko kaya, suke kuma tsaron in da suke. Sai kowannen su ya kama aiki da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma yana riƙe da makami. 18 Kowanne mai gini kuma yana rataye da takobinsa a kwiɓi, yadda suka yi aikin kenan, mai busa ƙaho kuma yana gefena. 19 Sai na ce da manyan mutane da shugabannin, "Aikin babba ne kuma yanzu ya yi fãɗi, kuma mun rabu a kan garun, mun kuma yi wa juna nisa 20 To dole ne ku ruga inda kuka ji ƙarar ƙaho sai ku tattaru a can. Allahnmu zai yi yaƙi a madadinmu." 21 Da haka muka yi aiki. Rabinsu na riƙe da mãshi tun daga safe har fitowar taurari. 22 Hakannan sai na ce da mutanen a wancan lokacin, "Sai kowanne mutum da baransa su kwana a tsakiyar Yerusalem, don su zama masu gadi, da dare da kuma ma'aikata da rana." 23 To ko ni ko 'yan'uwana, ko bayina, ko masu gadi dake tare da mu ba wanda ya canza tufafin da yasa, kuma kowannen mu ya ɗauki makaminsa, ko dama ya tafi ɗebo ruwa ne.

Sura 5

1 Daga nan sai mazaje da matansu suka yi babban kuka kan 'yan'uwansu Yahuduwa. 2 akwai waɗanda suka ce "Mu da 'ya'yanmu maza da mata muna da yawa. To sai mu sami hatsin da za mu ci mu rayu." 3 Akwai waɗanda suka ce, muna jinginar da filayenmu da kuringar inabinmu, da gidajenmu don mu sami abinci a lokacin yunwa." 4 Hakannan waɗansu suka ce. '"Mun ranci kuɗi don mu biya harajin sarki saboda gonakin inabinmu. 5 Yanzu kuma jikkunanmu da jininmu dai-dai ya ke da na 'yan'uwanmu, 'ya'yanmu kuma dai-dai da nasu 'ya'yan. An tilasta mana mu sayar da 'ya'yanmu su zama bayi. Tuni ma aka bautar da 'ya'yanmu mata. Amma mu ba mu da iko mu yi komai sabada gonakinmu na inabi suna hannun waɗansu mutane" 6 Bayan na ji wannan kuka nasu da waɗannan maganganu sai na fusata sosai 7 Sai na yi tunani na kuma ba manyan mutane da shugabanni laifi. Na ce da su, "Kowa na neman riba a kan ɗan'uwansa." Sai na jagoranci babban taron gãba da su, 8 sai na faɗa masu cewa, "Mun sha fama kafin mu fito daga ƙangin bauta musamman 'yan'uwanmu Yahudawa da aka sayar a cikin al'ummai, amma sai ga shi kuna sake sayar da 'yan'uwanmu don a sake sayar da su a gare mu kuma!" Sai suka yi shiru ba wanda ya ce uffan. 9 Hakanan na ce da su abin da kuke yi ba shi da kyau. A she ba za ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu ba, don kada mu zama abin ba'a ga al'umman da ke gãba da mu ba? 10 Ni da 'yan'uwana da bayina ne ke basu rancen kuɗi da hatsi. Amma dole ne mu dena sa ruwa a kan wannan bashin. 11 Sai ku mayar masu da filayensu, da gonakin inabinsu. Da na zaitun ɗinsu, da gidajensu da kuma ƙiyasin kuɗi da na hatsi, da sabon ruwan inabi, da kuma man da kuka karɓa daga gare su." 12 Daga nan sai suka ce. "Za mu mayar da abin da muka karɓa daga wurinsu, kuma ba za mu karɓi komai daga wurinsu ba. Za mu yi kamar yadda ka faɗi. 'Daga nan sai na kira firistoci, na sa su rantse cewa zasu yi kamar yadda suka alƙawarta. 13 Sai na kakkaɓe tufafina na ce, "Ubangiji ya kakkaɓe dukiya da gidan duk wanda bai cika alƙawaransa ba. Da ma a kakkaɓe shi ya zama fanko sai taron suka amsa, "Amin," sai suka yabi Yahweh jama'ar kuma suka aikatata kamar yadda suka yi alƙawari. 14 To, tun daga lokacin da aka naɗa ni na zama gwamnan a ƙasar Yahuda, daga shekara ta ashirin har ya zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Atazazas, ko kuma in ce shekaru sha biyu ba mu taɓa cin abincin da ake ba gwamna ba. 15 Amma su tsofaffin gwamnoni da suka gabace ni suka ɗora wa jama'ar ɗawainiya mai nauyi, suka kuma karɓi awo, da zinariya da kuma abincin yau da kullum, da ruwan inabi. Har ma bayinsu suka dinga ƙuntatawa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda tsoron Allah. 16 Na kuma ci gaba da aikin ganuwar, ba mu kuma sayi ƙasa ba, duk barorina suka taru a can don wannan aiki. 17 A kan teburi kuma inda Yahudawa da shugabaninsu, su 150 suke, in ban da sauran waɗanda suka zo tare da mu daga al'umman dake kewaye da mu. 18 Kuma kowacce rana akwai sã da aka shirya, zaɓaɓɓun tumaki guda shida, da tsuntsaye, kuma bayan kwana goma a kan kawo kowanne irin ruwan inabi, kuma duk da haka ban taɓa karɓar kuɗin abincin gwamna ba, don buƙatu sun yi wa mutane yawa. 19 Ka tuna da ni ya Allahna, saboda duk abin da na yi domin mutanen nan.

Sura 6

1 To, bayan Sanballat da Tobiya da Geshem Balarabe da sauran maƙiyanmu suka ji labarin na sake gina ganuwar, ba kuma inda ya ragu a buɗe, duk da ya ke ban sa ƙyamare a ƙofofin ba, 2 sai Sanballat da Geshem suka aiko mani da saƙo cewa, "Ka zo mu haɗu a wani wuri a filin Ono." Amma so suke su cutar da ni. 3 Na aika masu da 'yan'saƙo, cewa, "Ina yin babban aiki, kuma ba zan sauko ƙasa ba. Donme aiki zai tsaya a lokacin da na bar shi na gangaro wurinku?" 4 Sai suka sake aiko mani da dai irin wannan saƙon har sau huɗu kuma na dinga ba su amsa da irin amsar da na saba basu a kullum. 5 Sanballat ya aiko bawansa gare ni da dai irin wannan saƙon a karo na biyar, da rubutu a buɗe a hannunsa. 6 A cikin sa aka rubuta cewa, "An ba da rahoto cikin al'ummai hakannan Geshem shi ma ya faɗa cewa, kai da Yahudawa kuna so kuyi tayarwa, don wannan ya sa kuke sake gina ganuwar. Daga cikin abin da rahoton ya ce har ma ka kusa zama sarkinsu. 7 Kuma ka zaɓi annabawa su yi wannan shela game da kai a Yerusalem, cewa, 'Akwai sarki a Yahuda!' Kuma ka tabbata sarki zai ji waɗannan saƙonnin. Don haka ka zo muyi magana da juna." 8 Sai na aika da saƙo gare shi cewa, "Ba wani abu kamar irin abin da ka ce ya faru, amma ka ƙago su ne daga cikin zuciyarka." 9 Don dukkansu sun so su tsoratar da mu, suna tunanin, "Za su sa hannunsu su tsai da aikin, don kada a kammala shi." Amma ya Allah ka ƙarfafa hannuwana. 10 Na je gidan Shemaiya ɗan Delaiya ɗan Mehetabel, wanda a gidansa aka ƙulla maƙarƙashiyar. Ya ce, "Sai mu je gidan Allah tare a cikin haikali, sai mu kulle ƙofofin haikalin don suna zuwa don su kashe ka. Da dare suna son su kashe ka." 11 Na ba su amsa cewa, "Ko namiji kamar ni zai iya guduwa? Ko namiji kamar ni zai iya zuwa haikali don ya tsirar da ransa? Ba za ni ciki ba." 12 Na gane cewa ba Allah ne ya aiko shi ba, amma ya yi anabci ne gãba da ni. Tobiya da Sanballat ne suka yi hayar sa. 13 Sun yi hayar sa don ya tsoratar da ni, don in yi abin da ya ce in yi zunubi, don su bani laifi har su wulaƙanta ni. 14 Ya Allahna ka tuna da Tobiya da Sanballat, da duk abin da suka yi. Hakannan ka tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawan da suka so su sa in tsorata. 15 Da haka aka kammala ginin garun a ranar ashirin da biyar ga watan Elul, bayan kwana hamsin da biyu. 16 Bayan duk maƙiyanmu sun ji labarinsa, sai dukkan al'umman da ke kewaye da mu suka ji tsoro sosai duk fuskarsu ta yanƙwane. Don sun san an kammala aikin ne ta wurin taimakon Allahnmu. 17 A wannan lokaci sai masu daraja na Yahuda suka aika da wasiƙu masu yawa ga Tobiya, wasiƙun Tobiya kuma suka zo masu. 18 Don akwai waɗanda ke yi masa alƙawari, don shi surukin Shekaniya ne, ɗan Ara. Ɗansa Yehohanan ya auri 'yar Meshullam ɗan Berekiya ta zama matarsa. 19 Sun faɗa mani labarin ayyukansa masu kyau nima kuma na bashi nawa rahoton. Tobiya ya aika mani da wasiƙu don ya firgita ni.

Sura 7

1 Bayan an gama ganuwar na kuma sa ƙofofin a wurarensu, na kuma zaɓi masu tsaron ƙofofin da mawaƙa da Lebiyawa, 2 na ba ɗan'uwana Hanani iko kan Yerusalem, tare da Hananiya muka kula da masarautar, don shi amintacce ne, kuma mai tsoron Allah fiye da masu yawa daga cikinsu. 3 Na ce da su, "Ka da ku buɗe ƙofofin Yerusalem har sai rana ta yi zafi. Lokacin da masu tsaron ƙofofin ke tsaro, zaku kulle ƙofofin kusa mãkaransu. Ku zaɓi masu gadi daga cikin mazaunan Yerusalem, waɗansu a bayan gidajensu, waɗansu kuma su tsaya inda aka sa su gadin." 4 Yanzu birnin yana da faɗi da kuma girma, amma kuma waɗanda ke ciki basu da yawa, kuma ba'a gama sake gina gidaje ba tukuna. 5 Ya Allahna ka ba ni iko in tattara mutane masu girma da shugabanni da dukkan jama'a in sa su bisa ga iyalansu. Sai na samo littafin asalin waɗanda suka dawo daga farko sai na samo wannan rubutun a cikinsa. 6 Waɗannan sune mutanen lardin da suka fito daga bautar talala waɗanda sarki Nebukadnezza sarkin Babila ya kwasa zuwa bauta. Sun dawo zuwa Yerusalem da Yahuda, zuwa birninsa. 7 Sun zo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra'amiya, da Nahamani, da Modakai, da Bilshan, da Misferet, da Bigbai, da Nehum, da Ba'ana. Yawan mazajen mutanen Isra'ila ya haɗa da waɗannan. 8 Zuriyar Farosh, 2,172. 9 Zuriyar Shefatiya, 372. 10 Zuriyar Ara, 652. 11 Zuriyar Fahat-Mowab, zuwa zuriyar Yeshuwa da Yowab, 2,818. 12 Zuriyar Elam, 1,254. 13 Zuriyar Zattu, 845. 14 Zuriyar Zakkai, 760. 15 Zuriyar Binuyi, 648. 16 Zuriyar Bebai, 628. 17 Zuriyar Azgad, 2,322. 18 Zuriyar Adonikam, 667. 19 Zuriyar Bigbai, 2,067. 20 Zuriyar Adin, 655. 21 Zuriyar Ater na Hezekiya, 98. 22 Zuriyar Hashum, 328. 23 Zuriyar Bezai, 324. 24 Zuriyar Harif, 112. 25 Zuriyar Gibiyon, 95. 26 Mutane daga Betlehem da Netofa, 188. 27 Mazaje daga Anatot, 128. 28 Mutane daga Bet Azmabet, 42. 29 Mutanen daga Kiriyat Yeriyim, da Kefira, da Birot, 743. 30 Mutanen daga Rama da Geba, 621. 31 Mutanen Mikmas,122. 32 Mutanen Betal da Ai, 123. 33 Mutanen Nebo, 52. 34 Mutanen wancan Elam, 1,254. 35 Mutanen Harim, 320. 36 Mutanen Yeriko, 345. 37 Mutanen Lod, Hadid, da Ono, 721. 38 Mutanen Sena'a, 3,930. 39 Sai firistoci: Zuriyar Yedayya (na gidan Yeshuwa), 973. 40 Zuriyar Immer, 1,052. 41 Zuriyar Fashur, 1,247. 42 Zuriyar Harim, 1,017. 43 Sai Lebiyawa: Zuriyar Yeshuwa, na Kadmiyel, na Binuyi, da Hodiba, 74. 44 Mawaƙa: Zuriyar Asaf, 148. 45 Masu tsaron ƙofa na zuriyar Shallum, da zuriyar Ater, da zuriyar Talmon, da zuriyar Akkub, da zuriyar Hatita, da kuma zuriyar Shobai, 138. 46 Masu hidimar haikali: Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot, 47 da zuriyar Keros, da zuriyar Siya, da zuriyar Fadon, 48 da zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Shalmai, 49 da zuriyar Hanan, da zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar. 50 Da zuriyar Riyayya, da zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda, 51 da zuriyar Gazzam, da zuriyar Uzza, da zuriyar Faseya, 52 da zuriyar Besai, da zuriyar Mewunim, da zuriyar Nefushesim. 53 Da zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa, da zuriyar Harhur, 54 da zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha, 55 da zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Timah, 56 da zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa. 57 Da zuriyar bayin Suleman: da zuriyar Sotai, da zuriyar Soferet, da zuriyar Ferida, 58 da zuriyar Ya'ala, da zuriyar Darkon, da zuriyar Giddel, 59 da zuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret Hazzebayim, da zuriyar Amon. 60 Dukkan masu hidimar haikali, da zuriyar bayin Suleman, 392. 61 Waɗannan su ne mutanen da suka tafi daga Tel Mela, Telkasha, Kerub, Addon, da Imma. Amma ba zasu iya ba da shaida cewa iyayensu zuriyar Isra'ila ba ne: 62 da zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda, 642. 63 Waɗanda ke daga firistoci: zuriyar Habaiya, da Hakkoz, da Barzilai (wanda ya auro matarsa daga mutanen Barzillai na Giliyad ake kuma kiran su da sunansu). 64 Waɗannan sun binciko rubutaccen tarihinsu a cikin waɗanda aka karɓo tarihinsu bisa ga asalinsu, amma ba'a samu ba, don haka aka cire su daga aikin firist don ba su da tsarki. 65 Daga nan sai gwamna ya ce da su ba za a barsu su ci rabon firistoci ba na abinci daga cikin abincin hadaya har sai an sami firist tare da Urim da Tummim. 66 Dukkan taron baki ɗaya shi ne 42,360, 67 ban da barorinsu maza da mata, waɗanda daga cikinsu aka sami 7,337. Suna da mawaƙa maza da mata da suka kai 245. 68 Dawakansu guda 736, bijimansu 245, 69 raƙumansu, 435, da jakunansu, 6,720. 70 Waɗansu daga cikin shugabannin iyaye suka bada kyautai domin aikin. Gwamna ya bada awo dubu na zinariya, da bangaji 50, da suturar firistoci guda 530. 71 Waɗansu daga cikin shugabannin iyalai suka bayar da awo dubu ashirin na zinariya da awon azurfa 2,200. 72 Sauran jama'a suka bayar da awo dubu ashirin na zinariya, da kuma awo dubu biyu na azurfa, da suturar firistoci guda sittin da bakwai, 73 To sai firistoci da Lebiyawa, da masu tsaron ƙofa da mawaƙa, da waɗansu mutane da masu hidima a haikali da dukkan Isra'ila dake cikin birane. A wata na bakwai sai mutanen Isra'ila suka zauna a biranensu."

Sura 8

1 Sai dukkan mutane suka taru a matsayin mutum ɗaya a fili a gaban Ƙofar Ruwa. Sai suka tambayi Ezra marubuci ya kawo Littafin Shari'a na Musa, wanda Yahweh ya umarci Isra'ila. 2 A rana ta fari a wata na bakwai, Ezra firist ya kawo shari'a a gaban taron mutanen maza da mata, da duk waɗanda zasu iya ji su kuma fahimta. 3 Sai ya fuskanci filin Ƙofar Ɍuwa, sai ya yi karatu daga cikinsa tun daga asubahi har zuwa tsakar rana, a gaban dukkan maza da mata waɗanda zasu ji su kuma fahimta, kuma dukkan mutanen suka saurari karatun littafin shari'a a hankali. 4 Sai Ezra marubuci ya tsaya a kan dogon dakali na katako wanda mutane suka shirya saboda wannan dalilin. Waɗanda ke tsaye a gefansa su ne Mattitiya, Shema, Ananiya, Yuriya, Hilkiya, da Ma'aseiya, a gefen damarsa; da Fedaiya, Mishyel, Malkiya, Hashun, Hashbaddana, Zakariya, da Meshullum suna gefensa na hagu. 5 Sai Ezra ya buɗe littafin a gaban dukkan mutane, don yana tsaye ne a saman mutanen, sa'ad da ya buɗe littafin sai dukkan mutane suka miƙe tsaye. 6 Sai Ezra ya yi godiya ga Yahweh, Allah mai girma, sai dukkan mutane suka ɗaga hannuwansu sama suka amsa, "Amin! Amin!" Sai suka sunkuyar da kansu suka yi sujada ga Yahweh da fuskokinsu a ƙasa. 7 Hakannan Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma'aseiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan, da Felaiya - Lebiyawa - suka taimaki mutane su fahimci shari'ar, a sa'ad da mutane suke a wurarensu. 8 Sun karanta daga cikin littafin, Shari'ar Allah, suka faiyace ta a fili suka kuma fassarata suka bada ma'anarta ga mutane don mutane su fahimci karatun. 9 Nehemiya gwamna, da Ezra firist da marubuci, da kuma Lebiyawa da ke yiwa mutane fassara suka ce da dukkan mutanen, "Wannan rana ce mai tsarki ga Yahweh Allanku. Kada ku yi baƙinciki ko kuka." Don dukkan mutanen sun yi kuka bayan da suka ji manganganun shari'a. 10 Sai Nehemiya ya ce da su, "Kuje ku ci kitse ku kuma sami abu mai zaƙi ku sha, ku kuma aikawa waɗanda basu da abin yin bikin, don wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi alhini, don farincikin Yahweh shi ne ƙarfinku." 11 Sai Lebiyawa suka sa mutane su yi shiru, suna cewa, "Ku natsu! Don wannan rana mai tsarki ce. Kada ku yi baƙincikin." 12 Daga nan sai mutane suka tafi don su ci, su sha, su kuma yi zumunci, suyi biki cikin murna sosai saboda sun fahimci maganar da aka koyar da su. 13 A rana ta uku sai shugabannin iyalai da iyaye daga dukkan mutane, da firistoci, da Lebiyawa, suka taru a wurin Ezra marubuci don su sami fahimta daga manganganun shari'a. 14 Sai suka ga wani wuri inda Yahweh ya umarta ta wurin Musa cewa 'ya'yan Israi'la su taru a cikin bukkoki a lokacin bikin watan bakwai. 15 Sai suyi shela a cikin dukkan biranensu, da Yerusalem, cewa, "Kuje can ƙasa mai duwatsu, ku kawo rassan zaitun da zaitun na daji, da tuwon-biri, da na dabino, da durumi da sauran itatuwa masu rassa don ku yi bukkoki, kamar yadda ya ke a rubuce." 16 To sai mutanen suka fita suka samo rassan suka yi wa kansu bukkoki, dukkansu kowa da nasa rufe-rufen, da harabunsu, da kuma harabar gidan Allah, a fili a gaban Ƙofar Ruwa da kuma dandalin dake ƙofar Efiraim. 17 Dukkan mutanen da suka dawo daga bautar talala suka kakkafa bukkoki suka zauna a cikinsu. Don tun daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har ya zuwa wannan rana mutanen Isra'ila ba su yi wannan biki ba, don haka suka yi murna sosai. 18 Hakanan rana bayan rana, daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra ya karanta littafin shari'ar Allah. Su kan yi bikin a kwanaki bakwai a rana ta takwas sai ayi babban taro, don nuna biyayya ga wannan umarni.

Sura 9

1 A rana ta ashirin da huɗu a wannan watan dai sai mutanen Israi'la suka taru suna kuma yin azumi, suna sanye da tufafin makoki, suka kuma baɗa toka a kawunansu. 2 Zuriyar Israi'la suka keɓe kansu daga dukkan bãƙi. Suka tsaya, suka furta zunubansu, da kuma ayyukan mugunta na kakaninsu. 3 Suka tsaya a wurarensu, har kusan faɗuwar rana suna karanta littafin shari'ar Yahweh Allahnsu. Har kusan rabin ɗaya ranar suna ta furta zunubansu suna sunkuyawa a gaban Yahweh Allahnsu. 4 Sai Lebiyawa, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani, da Kenani, suka tsaya a filin suka yi kuka ga Yahweh Allahnsu. 5 Sai Lebiyawa, Yeshuwa, da Kadmiyel, Bani, Hashabneyya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya, da Fetahiya, suka ce, "Ku miƙe tsaye ku yabi Yahweh Allahnku har abada abadin." Dama su yabi sunanka maɗaukaki, kuma ya ɗaukaka fiye da dukkan albarku da yabo. 6 Kai ne Yahweh. Kai kaɗai. Ka yi samaniya da sammai mafiya nisa, da dukkan rundunoninsu, da duniya da duk abin da ke cikinta, da tekuna da duk abin da ke cikinsu. Ka ba dukkan su rai, kuma dukkan rundunar sama na yi maka sujada. 7 Kai ne Yahweh, Allahn da ya zaɓi Abram, ya kawo shi daga Ur ta Kaldiyawa ya bashi suna Ibrahim. 8 Ka gane cewa yana da aminci a gare ka, ka kuma yi masa alƙawari zaka bada ƙasar Kan'aniyawa, da Hitiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Yebusiyawa, da Girgashiyawa, ga zuriyarsa. Ka kiyaye alƙawarinka saboda kai adali ne. 9 Ka ga ƙuncin kakanninmu a Masar ka kuma ji kukansu a bakin Tekun Iwa. 10 Ka bada alamu da al'ajibai gãba da Fir'auna da dukkan bayinsa da dukkan mazaunan ƙasarsa don ka san Masarawa sun yi masu mugun hali sosai. Amma ka samarwa kanka suna wanda ya ke nan har ya zuwa yau. 11 Kai ne kuma ka raba teku biyu a gabansu, don su bi ta cikin tsakiyar teku a kan sandararriyar ƙasa; ka kuma kora masu runtumarsu cikin zurfafa kamar dutse a cikin ruwaye zurfafa. 12 Ka bida su ta wurin ginshiƙin girgije da rana, da kuma ginshiƙin wuta da dare don ta nuna masu hanyar da za su bi. 13 A kan Dutsen Sinai ka sauko ƙasa ka yi magana da su daga sama ka kuma ba su ka'idojinka na adalci da kuma shari'arka ta gaskiya, da farillanka da dokokinka masu kyau. 14 Ka koyar da su game da Asabar ɗinka mai tsarki, ka basu dokoki da farillai da shari'u ta wurin Musa bawanka. 15 Ka basu gurasa daga sama saboda yunwarsu, da kuma ruwa daga dutse saboda ƙishinsu, ka kuma ce da su ku shiga ku mallaki ƙasar da ka rantse za ka basu. 16 Amma su da kakaninmu suka nuna rashin girmamawa, suka yi taurin kai, basu saurari dokokinka ba, 17 Suka ƙi su saurara, kuma suka ƙi tunani a kan al'ajibanka da kayi a cikinsu, amma suka yi tayarwa, saboda tayarwarsu suka zaɓi shugaba don su koma zaman bautarsu. Amma kai Allah ne wanda ya ke cike da gafara, da alheri da tausayi, mai jinkirin fushi, mai madawwamiyar ƙauna. Baka yashe su ba. 18 Ko ma a lokacin da suka kafa ɗan maraƙin daga narkakken ƙarfe suka ce, 'Wannan Allahnku wanda ya fitar da ku daga ƙasar Masar,' suka kuma yi babban saɓo, 19 kai, cikin tausayinka, baka yashe su ba a cikin jeji. Ginshiƙin girgijen ya bi da su akan hanya bai kuma rabu da su ba da rana, hakama ginshiƙin wutar bai rabu da su ba da dare don ya haskaka masu hanyar da zasu bi. 20 Ruhunka manargaci ka basu don ya gargaɗe su, Baka janye mannarka daga bakunansu ba, ka kuma basu ruwa saboda ƙishinsu. 21 Har shekaru arba'in ka yi masu tanadi a cikin jeji, kuma basu rasa komai ba. Suturunsu basu koɗe ba ƙafafunsu kuma ba su kumbura ba. 22 Ka basu mulkoki da al'ummai ka ba kowannesu lungu-lungu na ƙasar. Sa'an nan suka mallaki ƙasar Sihon da sarkin Heshbon da kuma ƙasar Og sarkin Bashan. 23 Ka sa 'ya'yansu su yawaita kamar taurarin sama, ka kuma kawo su ƙasar da ka faɗawa ubanninsu su je su mallake ta. 24 Sai mutanen suka je suka mallaki ƙasar ka kuma kori mazauna ƙasar a idonsu, wato Kan'aniyawa. Ka ba da su a hannuwansu, tare da sarakunansu da mutanensu na ƙasar, don Isra'ila su yi yadda suka so da su. 25 Suka kame ƙayatattun birane da kuma ƙasa mai bada abinci, sun kuma mamaye gidaje cike da abubuwa kyawawa da rijiyoyin da tuni aka haƙa, da garkar inabi da ta zaitun, da itatuwa masu bada 'ya'ya sosai. Da suka ci suka ƙoshi suka yi ƙiba suka ji daɗin kansu a cikin babbar nagartarka. 26 Daga nan suka yi rashin biyayya a gare ka. Suka yi watsi da dokokinka. Suka karkashe annabawanka da suka gargaɗe su su komo gare ka, sun kuma yi babban aikin saɓo. 27 Don haka sai ka ba da su a hannun maƙiyansu, waɗanda suka wahalashe su. A cikin wahalarsu, suka yi kuka gare ka, ka kuwa ji su daga sama, Kuma saboda babban jinƙanka ka aika masu da masu kuɓutarwa waɗanda suka kuɓutar da su daga ƙasar maƙiyansu. 28 Amma bayan sun huta, sai suka ƙara yin aikin mugunta a gabanka, sai ka yashe su a hannun maƙiyansu suka mulke su. Duk da haka sa'ad da suka juyo suka yi kuka gare ka, ka ji su daga sama, da kuma a lokuta da yawa saboda yawan jinƙanka ka 'yanto su. 29 Ka gargaɗe su da su juyo ga dokokinka. Duk da haka suka yi husuma kuma ba su saurari umarnanka ba. Suka yi zunubi kan sharuɗan da ke bada rai ga wanda ya kiyaye su. Sun miƙa kafaɗunsu na taurin kai suka ƙi sauraro. 30 Ka yi ta watsi da su da kuma yi masu gargaɗi ta wurin Ruhunka ta hannun annabawanka. Duk da haka ba su saurara ba. Don haka sai ka miƙa su ga magabtan ƙasashensu 31 Amma a cikin jinƙanka mai girma baka hallakar da su dukka ba, ko kuma ka yashe su, Don kai Allah ne mai yawan jinƙai da alheri. 32 Yanzu saboda haka ya Allahnmu - kai mai girma ne, maɗaukaki, managarci wanda ka riƙe alƙawarinka da kuma ƙaunarka madauwamiya - kar ka bari duk wannan wahalar da ta same mu ta zama kamar 'yar ƙarama a gare ka, ga sarakunanmu, ga masu mulkinmu, da kuma firistocinmu, da annabawanmu, da iyayenmu, da dukkan mutanenka tun daga kwanakin sarakunan Asiriya har ya zuwa yau. 33 Kai mai adalci ne a cikin duk abin da ya same mu, don da amincinka ka bi da mu, amma muka yi aikin mugunta. 34 Sarakunanmu da masu mulkinmu, da firistocinmu da iyayenmu, ba mu kiyaye shari'arka ba, ko mu saurari dokokinka ko sharuɗɗan da ka gindaya mana waɗanda kuma ka gargaɗe su ba. 35 Koma da a cikin mulkinsu, sa'ad da suka ji daɗin babban alherinka a gare su, a wannan babbar ƙasa mai yalwa da ka basu, ba su bauta maka ba ko kuma su juyo daga mugayen hanyoyinsu ba. 36 Yanzu mu bayi ne a ƙasar da ka ba iyayenmu su ji daɗin yalwarta da dukkan abubauwa masu kyau da ke cikinta, yanzu mun zama bayi a cikinta! 37 Dukkan wadatar da ka ba mu tana hannun sarakunan da ka ɗora a kanmu saboda zunubanmu. Suna mulkin jikkunanmu da dabbobinmu yadda suka so. Muna cikin babban ƙunci. 38 Saboda dukkan wannan, muka yi dauwamammen alƙawari a rubuce. A kan littafin da aka hatimce akwai sunayen shugabanninmu, da Lebiyawa da firistoci."

Sura 10

1 A bisa takardu masu tambari akwai Nehemiya, wanda ya ke gwamna, ɗan Hakaliya da Zedekiya, 2 Sera'iya, Azariya, Irmiya, 3 Fashhur, Amariya, Malkiya, 4 Hattush, Shebaniya, Malluk, 5 Harim, Meremot, Obadiya, 6 Daniyel, Ginneton, Baruk, 7 Meshullam, Abiya, Miyamin, 8 Ma'aziya, Bilgai, da kuma Shemaiya. Waɗannan su ne firistocin. 9 Lebiyawan su ne: Yeshuwa ɗan Azaniya, Binuyi na iyalin Henadad, Kadmiyel, 10 da kuma sauran yan'uwansu Lebiyawa, Shebaniya, Hodiya, Kelita, Felaiya, Hanan, 11 Mika, Rehob, Hashabiya, 12 Zakkur, Sherebiya, Shebaniya, 13 Hodiya, Bani, da kuma Beninu. 14 Shugabannin mutanen su ne: Farosh, Fahat-Mowab, Ilam, Zattu, da Bani, 15 Bunni, Azgad, Bebai, 16 Adoniya, Bigbai, Adin, 17 Atar, Hezekiya, Azzur, 18 Hodiya, Hashum, Bezai, 19 Harif, Anatot, Nebai, 20 Magfiyash, Meshullam, Hezir, 21 Meshezabel, Zadok, da Yadduwa, 22 Felatiya, Hanan, Anaya, 23 Hoshiya, Hananiya, Hasshub, 24 Hallohesh, Filha, Shobek, 25 Rehum, Hashabna, Ma'aseiya 26 Ahiya, Hanan, Anan, 27 Malluk, Harim, da kuma Ba'ana. 28 Game da sauran mutanen kuwa, waɗanda suke firistoci, Lebiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, da masu hidimar haikali, da kuma dukkan waɗanda suka keɓe kansu daga mutanen ƙasashen maƙwabta suka kuma miƙa kansu ga shari'ar Allah, har da matayensu, da 'ya'yansu maza da mata, dukkan waɗanda suke da ilimi da kuma fahimta, 29 suka haɗu tare da 'yan'uwansu, da sarakunansu, kuma suka ɗaure kansu da la'ana da kuma alƙawarin yin tafiya bisa shari'un Allah, wadda Musa bawan Allah ya bayar, su kuma kula su kuma yi biyayya da dukkan dokokin Yahweh Ubangijinmu da kuma umarnai da kuma farillunsa. 30 Mun yi alƙawari ba zamu ba da 'ya'yanmu mata aure ga mazaunan ƙasar ba ko mu auro 'yan matansu ga 'ya'yanmu maza. 31 Mun kuma yi alƙawari idan mazaunan ƙasar suka kawo kayayyaki ko wani hatsi domin sayarwa a ranar Asabarci, ba zamu saya daga gare su ba a ranar Asabaci ko wata rana mai tsarki. Kowacce shekara ta bakwai zamu bar filayenmu su huta, kuma zamu ṣoke dukkan basusuwan da aka yi. 32 Mun yi na'am da dokokin bayar da ɗaya cikin uku na awo a shekara domin hidimar gidan Allahnmu, 33 domin tanadin gurasar wuri-mai tsarki, da kuma hatsin baiko na kullum, baye-baye na ƙonawa a ranakun Asabaci, bukukuwan sabon wata da kuma shiryayyar liyafa, da kuma baye-baye masu tsarki, da kuma baye-baye na zunubi domin yi wa Isra'ila kaffara, haka kuma domin dukkan ayyukan gidan Allahnmu. 34 Da firistoci da Lebiyawa da mutane suka jefa ƙuri'u domin itacen yin baiko. Ƙuri'un zasu zaɓi wane ne daga cikin iyalanmu zai kawo itace zuwa gidan Allahnmu a sanyayyun lokatai kowacce shekara, domin ƙonawa a bisa bagadin Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya ke a rubuce cikin shari'a. 35 Mun yi alƙawari mu kawo nunar fari da aka shuka a ƙasarmu cikin gidan Yahweh, da kuma nunar fari na kowanne itace duk shekara. 36 Kamar yadda aka rubuta a shari'a, mun yi alƙawari mu kawo cikin gidan Allah da kuma ga firistoci masu hidima a can, ɗan fari cikin 'ya'yanmu da kuma na garkunan shanunmu da garkunan tumakinmu. 37 Zamu kawo cụrinmu na fari da kuma baye-bayenmu na hatsi, da kuma 'ya'yan kowacce itaciya, da kuma sabon inabi da kuma mai zamu kawo su ga firistoci, ga rumbunan gidan Allahnmu. Zamu kawo wa Lebiyawa zakka daga ƙasarmu domin su Lebiyawa na karɓar ɗaya daga goma daga dukkan garuruwan da muke aiki. 38 Firist, zuriyar Haruna, dole yana tare da Lebiyawa sa'ad da suke karɓar ɗaya daga goma. Su Lebiyawa dole su kawo ɗaya daga goma ga gidan Allahnmu zuwa cikin runbunan ma'aji. 39 Gama mutanen Isra'ila da kuma zuriyar Lebi zasu kawo gudumuwoyin na hatsi, da sabon inabi, da kuma mai zuwa ga runbuna inda ake ajiyar santalolin wuri mai tsarki inda firistoci masu hidima suke, da kuma matsaran ƙofa, da kuma inda mawaƙa ke zama. Ba za mu yi watsi da gidan Allahnmu ba.

Sura 11

1 Shugabannin mutanen suka zauna cikin Yerusalem, sai kuma sauran mutanen suka jefa ƙuri'u domin kawo ɗaya daga cikin goma ya zauna a Yerusalem, birni mai tsarki, sai kuma sauran kashi taran a bar su a wasu garuruwan. 2 Sai mutanen suka albarkaci dukkan waɗanda suka yarda su zauna a Yerusalem. 3 Waɗannan su ne shuagabannin lardin dake zama Yerusalem. Duk da haka, a cikin garuruwan Yahuda kowanne na zama a ƙasarsa, harma da waɗansu Isra'ilawa, firistoci, Lebiyawa, masu hidimar haikali, da zuriyar bayin Suleman. 4 A Yerusalem akwai mazauna waɗanda suke na zuriyar Yahuda da kuma zuriyar Benyamin. Mutanen Yahuda su ne: Atayya ɗan Uzziya ɗan Zakariya ɗan Amariya ɗan Shefatiya ɗan Mahalalel, na zuriyar Ferez. 5 Akwai Ma'aseiya ɗan Baruk ɗan Kol-Hoze ɗan Hazayya ɗan Adayya ɗan Yoyarib ɗan Zakariya, ɗan Bashiloni. 6 Dukkan 'ya'yan Ferez da suka zauna cikin Yerusalem 468 ne. Su zama shahararrun mutane. 7 Waɗannan su ne zuriyar Benyamin: Sallu ɗan Meshullam ɗan Yoyed ɗan Fedayya ɗan Kolayya ɗan Ma'aseyya ɗan Itiyel ɗan Yeshayya, 8 da waɗanda suke binsa, da Gabbai da Sallai, mutane 928. 9 Yowel ɗan Zikri shi ne mai kula da su, da kuma Yahuda ɗan Hassenuwa shi ya zama na biyu a shugabanci bisa birnin. 10 Daga firistocin: Yedayya ɗan Yoyarib, Yakin, 11 Serayya ɗan Hilkiya ɗan Meshullam ɗan Zadok ɗan Merayot ɗan Ahitub, babban mai kula da gidan Allah, 12 da kuma abokan aikinsu waɗanda suka yi aikin gidan Allah, mutane 822, tare da Adayya ɗan Yeroham ɗan Felaliya ɗan Amzi ɗan Zakariya ɗan Fashhur ɗan Malkiya. 13 Yan'uwansa ne shugabannin zuriya, mutane 242; da kuma Amashsai ɗan Azarel ɗan Ahzai ɗan Meshillemot ɗan Immer, 14 da kuma yan'uwansu, mutane 128 masu ƙarfin halin yaƙi; mai kula da su shi ne Zabdiyel ɗan Hagedolim. 15 Daga Lebiyawa: Shemayya ɗan Hashub ɗan Azrikam ɗan Hashabiya ɗan Bunni, 16 da kuma Shabbetai da Yozabad, su da ke daga wajen shugabannin Lebiyawa kuma su ne ke da haƙin aikin waje da gidan Allah. 17 Akwai Mattaniya ɗan Mika ɗan Zabdi, na zuriyar Asaf, shi ne jagora da ya fara bada godiya cikin addu'a, da kuma Bakbukiya, shi ne na biyu cikin yan'uwansa, da kuma Abda ɗan Shammuwa ɗan Galal ɗan Yedutun. 18 Dukkan Lebiyawa da ke cikin birni mai tsarki lissafinsu 284 ne. 19 Masu kula da ƙofa: Akkub, Talmon, kuma sauran abokan hurɗarsu, da suke kula da ƙofofi, mutane 172. 20 Sauran Isra'ila da kuma sauran firistoci da Lebiyawa suna cikin dukkan garuruwan Yahuda. Kowannen su na zaune a wurinsa na gãdo. 21 Ma'aikatan haikali suna zaune cikin Ofel, da Ziha da Gishfa su ne masu kula da su. 22 Babban shugaba a bisa Lebiyawan da ke a Yerusalem shi ne Uzzi ɗan Bani ɗan Hashabiya ɗan Mattaniya ɗan Mika, daga zuriyar Asaf, mawaƙa a bisa aikin cikin gidan Allah. 23 Suna a ƙarƙashin umarnai masu girma daga wurin sarki, kuma an bada umarnai masu tsanani ga mawaƙa yadda kowacce rana ke bukata. 24 Sai Fetaniya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera ɗan Yahuda, ya zauna a ɓarayin sarki a game da kowanne al'amari da ya shafi mutane. 25 A game da ƙauyuka da kuma filayensu, wasu mutanen Yahuda sun zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da kuma cikin Dibon da ƙauyukanta, da kuma cikin Yekabzil da ƙauyukanta, 26 da cikin Yeshuwa, Molada, Bet Felet, 27 Hazar Shuwal, da kuma Biyasheba da ƙauyukanta. 28 Wasu daga mutanen Yahuda sun zauna cikin Ziklag, Mekona da kuma ƙauyukanta, 29 Enrimmon, Zora, Yamut, 30 Zanowa, Adullam, da kuma ƙauyukanta, da cikin Lakish da filayenta, da Azeka da ƙauyukanta. Sai suka zauna daga Biyasheba zuwa Kwarin Hinnom. 31 Benyamin suka zauna daga Geba, a Mikmash da Aiya, a kuma Betel da ƙauyukanta, 32 Anatot, Nob, Ananiya, 33 Ramah, Gittayim, 34 Hadid, Zeboyin, Neballat, 35 da kuma Ono kwarin maƙera. 36 daga cikin Lebiyawa dake zama cikin Yahuda aka sanya su kan mutanen Benyamin.

Sura 12

1 Waɗannan su ne firistoci da Lebiyawa da suka fito tare da Zerubbabel ɗan Sheltiyel da kuma tare da Yeshuwa: Serayya, da Irmiya, Ezra, 2 Amariya, Malluk, Hattush, 3 Shekaniya, Rehum, da kuma Meremot. 4 Akwai su Iddo, Ginneton, Abiya, 5 Miyamin, Mowadiya, Bilga, 6 Shemayya, da Yoyarib, Yedayya, 7 Sallu, Amok, Hilkiya, da Yedayya. Waɗannan ne shugabannin firistoci da mataimakansu a kwanakin Yeshuwa. 8 Lebiyawan su ne Yeshuwa, Binuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da Mattaniya, wanda shi ne shugaban waƙoƙin godiya, tare da abokan aikinsa. 9 Bakbukiya da Unni, su ne abokan aikinsu, suka tsaya daura da su lokacin yin sujada. 10 Yeshuwa shi ne mahaifin Yowakim, Yowakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib ne Mahaifin Yowada, 11 Yowada ne mahaifin Yonatan, kuma Yonatan shi ne mahaifin Yadduwa. 12 A zamanin Yowakim waɗannan su ne firistoci, su ne shugabannin iyalai: Merayya ne shugaban Serayya, Hananiya ne shugaban Irmiya, 13 Meshullam shi ne shugaban Ezra, Yehohanan shi ne shugaban Amariya, 14 Yonatan ne shugaban Malluk, kuma Yosef shi ne shugaban Shebaniya. 15 Adna ne shugaban Harim, Helkai shugaban Merayot, 16 Zakariya shi ne shugaban Iddo, Meshullam shi ne shugaban Ginneton 17 Zikri shi ne shugaban Abiya. ... na Miniamim. Filtai shi ne shugaban Mowadiya. 18 Shammuwa shi ne shugaban Bilga, Yehonatan shi ne shugaban Shemayya, 19 Mattenai shi ne shugaban Yoyarib, Uzzi shi ne shugaban Yedayya, 20 Kallai shi ne shugaban Sallai, Eba shi ne shugaban Amok, 21 Hashabiya shi ne shugaban Hilkiya, da Netanel shi ne shugaban Yedayya. 22 A kwanakin Eliyashib, Lebiyawa Eliyashib, Yowada, Yohanan, da Yadduwa aka lisafta su a matsayin shugabannin iyalai, kuma aka lisafta firistocin a zamanin mulkin Dariyos na Fasiya. 23 Su zuriyar Lebi, shugabannin iyalansu aka lisafta su a cikin littafi na tarihi har zuwa kwanakin Yohanan ɗan Eliyashib. 24 Su shugabannin Lebiyawan su ne Hashabiya, Sherebiya, da Yeshuwa ɗan Kadmiyel, tare da abokan tarayyarsu, suna zaune daura da su domin raira waƙoƙin yabo da kuma bada godiya, suna aikinsu cikin ka'ida, suna biyayya da umarnin Dauda, mutumin Allah. 25 Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon, da Akkub su ne matsaran ƙofofi masu tsaro a tsaye a ɗakunan ajiya dake gefen ƙofofin. 26 Sun yi hidima a cikin kwanakin Yoyakim ɗan Yeshuwa ɗan Yozadak, da kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma Ezra firist da marubuci. 27 A lokacin keɓewar ganuwar Yerusalem, mutane suka nemi firistoci dukkan inda suke zama, suka kawo su Yerusalem su yi bikin keɓewar tare da farinciki, da godiya da kuma waƙoki tare da kuge, da molo, da giraya, da tsarkiyoyi. 28 Zumuntar mawaƙa suka tattaru tare daga garuruwa kewaye da Yerusalem daga kuma ƙauyuka na Netofatiyawa. 29 Sun kuma fito daga Bet Gilgal daga kuma filin Geba da Azmabet, domin mawaƙa sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Yerusalem. 30 Su firistoci da Lebiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake mutanen, da ƙofofin, da kuma ganuwar. 31 Sai na sa shugabannin Yahuda suka hau kan ganuwar, na kuma shirya manyan ƙungiyoyin mawaƙa guda biyu domin su yi waƙoƙin godiya. Sashi ɗaya suka yi dama bisa ganuwar ta sashen ‌Ƙofar Kashin Shanu. 32 Hoshayya da rabin shugabannin Yahuda suka tafi tare da su, 33 bayan su Azariya, Ezra, Meshullam, 34 Yahuda, Benyamin, Shemayya, da Irmiya, 35 da wasu 'ya'yan firistoci ɗauke da algaitu, da kuma Zekariya ɗan Yonatan ɗan Shemayya ɗan Mattaniya ɗan Mikayya ɗan Zakkur ɗan Asaf. 36 Da akwai waɗansu cikin 'yan'uwan Zakariya, Shemayya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma'ai, Netanel, Yahuda, Hanani, suna ɗauke da kayayyakin kiɗe-kiɗen Dauda mutumin Allah. Ezra marubuci na tsaye gabansu. 37 Daga ‌Ƙofar Maɓulɓula suka haura kai tsaye zuwa matakalar birnin Dauda, daga matakala zuwa ganuwa a bisa fãdar Dauda, zuwa wajen Kofar Ruwa daga gabas. 38 ‌Ɗaya ƙungiyar mawaƙan masu bada godiya suka tafi zuwa wancan sashen. Na bi su a bisa ganuwar tare da rabin mutanen, sama da Hasumiyar Murahu, zuwa kan Ganuwa Mai Faɗi, 39 da bisa Kofar Ifraim, da kuma daga Tsohuwar ‌Ƙofa, da kuma daga ‌Ƙofar Kifi da kuma Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiyar Ɗari, zuwa ga ‌Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a ‌Ƙofar Matsara. 40 Da haka dukkan mawaƙa suka bada godiya suka ɗauki wurinsu a cikin gidan Allah, nima na ɗauki wurina tare da rabin ma'aikatan da ke tare da ni. 41 Sai su firistoci suka ɗauki wurin zamansu: Eliyakim, Ma'aseyya, Miniyamin, Mikayya, Elihonai, Zakariya, da kuma Hananiya, tare da ƙahonni, 42 da kuma Ma'aseyya, Shemayya, Eliyaza, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam, da kuma Eza, sai kuma mawaƙan suka sa aka ji su Jezrahiya kuma shi ne shugabansu. 43 Suka bada manyan hadayu a wannan rana, da farinciki kuma, gama Allah ya sa suka yi farinciki da murna mai girma. Haka mataye da kuma yara suka yi murna. Da haka aka ji farincikin Yerusalem daga nesa. 44 A wannan rana aka naɗa mutane su shugabanci ɗakunan ajiya domin gudumuwa, nunar fari, da zakka, domin su tara adadin da aka shirya bisa ga shari'a a cikinsu domin firistoci da kuma Lebiyawa. Kowannen su aka ba shi aikin noma filayen da ke kusa da garuruwan. Domin Yahuda sun yi farinciki da firistoci da kuma Lebiyawa waɗanda ke tsaye a gabansu. 45 Suka yi hidimar Allahnsu, da kuma hidimar tsarkakewa, haka kuma mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, domin kiyaye umarnan Dauda da na Suleman ɗansa. 46 A tun zamanin dã, cikin kwanakin Dauda da Asaf, akwai shugabannin mawaƙa, aka yi waƙokin yabo da godiya ga Allah. 47 A zamanin Zerubbabel da kuma zamanin Nehemiya, dukkan Isra'ilawa suka kawo rabonsu na kowacce rana ga mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi. Suka keɓe wa Lebiyawa rabonsu na kowacce rana, su kuma Lebiyawa suka keɓe wa 'ya'yan Haruna nasu rabon.

Sura 13

1 A wannan rana suka karanta Littafin Musa mutane na saurare. Aka iske a rubucce a cikinsa cewa kada wani Ba'ammone ko mutumin Mowab ya shigo cikin taron jama'ar Allah, har abada. 2 Dalili kuwa shi ne domin basu taryi mutanen Isra'ila da gurasa da ruwan sha ba, amma suka yiwo hayar Bala'am domin ya la'anci Isra'ila. Duk da haka, Allahnmu ya juyar da la'anar zuwa albarka. 3 Da dai suka ji shari'ar, sai suka ware kowanne baƙo daga Isra'ila. 4 Yanzu dai kafin wannan aka sa Eliyashib firist ya zama shugaban ɗakunan ajiya na gidan Allahnmu. Yana da dangantaka da Tobiya. 5 Eliyashib ya shirya wa Tobiya babban ɗaki na ajiya, inda dã aka ajiye hadayar gari, da ta turare, da tasoshi, da kuma zakkar hatsi, da sabon inabi, da mai, wanda aka keɓe domin Lebiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofofi, da kuma gudumuwa domin firistocin. 6 Amma cikin dukkan wannan lokacin ba na cikin Yerusalem. Gama a cikin shekara ta talatin da biyu ta sarautar Atazazas sarkin Babila na tafi wurin sarki. Bayan lokaci kaɗan sai na nemi izinin tafiya daga wurin sarki 7 sai kuma na komo Yerusalem. Na fahimci muguntar da Eliyashib ya aikata da ya ba Tobiya ɗakin ajiya a cikin haikali na gidan Allah. 8 Na fusata ƙwarai sai na watsar da kayan ɗakin Tobiya zuwa waje daga ɗakin ajiya. 9 Na umarta a tsabtace ɗakunan ajiyar, na sake zuba kayayyakin gidan Allah a cikinsu, wato baye-bayen hatsi, da kuma turare. 10 Sai na fahimci cewa ba a ba wa Lebiyawa rabonsu ba, kuma duk sun gudu, kowannen su zuwa ga gonarsa, su Lebiyawa da mawaƙa waɗanda suka yi aikin. 11 Sai na yiwa shugabannin faɗa na ce, "Me ya sa aka yi watsi da gidan Allah?" Na tara su tare kowannen su a wurin aikinsa. 12 Sa'annan dukkan Yahuda suka kawo zakkar hatsi, sabon inabi, da kuma mai cikin ɗakunan ajiya. 13 Sai naɗa ma'aji bisa gidajen ajiya su Shelemiya firist da Zadok marubuci, kuma daga wurin Lebiyawa, Fedayya. Na kusa da su shi ne Hanan ɗan Zakkur ɗan Mattaniya, gama an iske su amintattu ne. Aikinsu shi ne su rarraba ragowar kayayyakin ga abokan aikinsu. 14 Ka tuna da ni, Allahna, game da wannan, kuma kada ka shafe sarai ayyukan alherin da na aikata sabili da gidan Allahna da kuma hidimarsa. 15 A waɗannan kwanakin na gani a Yahuda mutane na matsar inabi a ranar Asabaci suna kuma kawo tulin hatsi da ɗauro su bisa jakkai, da kuma inabi, da zaitun, da ɓaure, da kuma kowanne kayan nauyi, wanda suka kawo cikin Yerusalem a ranar Asabaci. Na yi tsayayya da su ganin cewar suna sayar da abinci a wannan rana. 16 Mutanen Tiya masu zama cikin Yerusalem suka kawo kifi da dukkan kowanne kayayyaki, suka sayar a ranar Asabaci ga mutanen Yahuda da kuma cikin birnin! 17 Sai na fuskanci shugabannin Yahuda kai tsaye, "Wacce irin mugunta ce haka kuke yi, ku na mai da ranar Asabaci wofi? 18 Ba abin da iyayenku suka yi ba kenan? Ba Allahnmu ya aiko da dukkan wannan masifar a bisanmu da kuma wannan birni ba? Yanzu kuna ƙara kawo wata hasala kan Isra'ila ta wofintar da Asabaci." 19 Daga nan da zarar dare ya yi a bakin ƙofofin Yerusalem kafin Asabaci, na ba da umarni a kulle ƙofofin kada kuma a buɗe su har sai bayan Asabaci. Na sanya wasu bayina a bakin ƙofofin don kada a iya shigo da kaya ciki ranar Asabaci. 20 'Yan kasuwa da masu sayar da kowanne irin tufafi suka taru a wajen Yerusalem sau ɗaya ko biyu. 21 Amma na yi masu kashedi, "Donme ku ke taruwa a wajen ganuwa? Idan kuka ƙara yin haka, zan kore ku da hannuna!" Daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabaci ba. 22 Sai na dokaci Lebiyawa su tsabtace kansu, su kuma zo su tsare ƙofofin, a tsarkake ranar Asabacin. Ka tuna da ni game da wannan kuma, Allahna, ka kuma yi mani jinƙai sabili da amintaccen alƙawarinka zuwa gare ni. 23 A waɗannan kwanaki na kuma ga Yahudawan da suka auro matan Ashdod, da Ammon, da kuma Mowab. 24 Rabin 'ya'yansu na magana da yaren Ashdod. Babu waninsu da zai iya magana da harshen Yahuda, amma sai ɗaya daga cikin harshen sauran mutanen kawai. 25 Na fuskance su kai tsaye, na kuma la'anta su, na kuma bugi wasu daga cikinsu har na tsige sumar kansu. Na sa suka yi rantsuwa ga Allah, cewa, "Ba za ku bada 'ya'yanku mata ga samarinsu ba, ko ku ɗauko wa 'ya'yanku maza 'yanmatansu, ko don kanku. 26 Ba haka Suleman sarkin Isra'ila ya yi zunubi ta dalilin waɗannan matayen ba? A cikin al'ummai masu yawa babu sarki kamarsa, kuma Allahnsa ya ƙaunace shi, kuma Allah ya maishe shi sarki bisa dukkan Isra'ila. Duk da haka, matayensa bãƙi suka sa yayi zunubi. 27 ‌Ƙaƙa zamu saurare ku mu aikata dukkan wannan babbar mugunta, mu kuma yi rashin aminci ga Allahnmu ta wurin auro mataye bãƙi?" 28 ‌Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yowada ɗan Eliyashib babban firist surukin Sanballat Bahorone ne. Saboda haka na sa shi ya gudu daga fuskata. 29 Ka tuna da su, Allahna, domin sun ƙazantar da firistanci, da kuma alƙawarin firistanci da kuma Lebiyawa. 30 Da haka na tsabtace su daga duk abin da da ke na bãƙunci, na kuma kafa ayyukan firistoci da na Lebiyawa, kowanne ga aikinsa. 31 Na yi tanadi domin baikon itace a lokatansu da na nunar fari. Ka tuna da ni, Allahna, domin alheri.

Littafin Esta
Littafin Esta
Sura 1

1 A kwanakin Ahasuros (wannan shi ne Ahasuros wanda yayi mulki daga Indiya har zuwa Kush, bisa larduna 127), 2 a kwanakin nan Sarki Ahasuros ya zauna bisa kursiyin sarautarsa a fadar Susa. 3 A shekara ta uku ta sarautarsa, yayi wa dukkan sarakunansa da barorinsa biki. Mayaƙan Fasiya da Midiya da manyan sarakuna da hakimai da gamnonin larduna duk suna gabansa. 4 Ya nuna darajar arziƙin mulkinsa da bangirman ɗaukakar ƙasaitarsa kwanaki da yawa, har kwanaki 180. 5 Da kwanakin nan suka cika, sarki yayi biki kuma na kwana bakwai. Yayi bikin ne saboda dukkan mutanen da suke a fadar Susa, manya da ƙanana. Anyi wannan a farfajiyar lambu da ke a fãdar sarki. 6 Anyi wa farfajiyar lambun ado da labulai farare da shunayya, aka ratayesu bisa kirtani na lallausar lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa aka ɗaure ajikin ginshiƙan duwatsu masu daraja. Akwai kujeru na zinariya, dana azurfa da suke a shirayin da aka daɓe da duwatsun ado masu daraja kamar su fofari mabil, fiyel da duwatsun dakali masu launi. 7 Aka bada abin sha a moɗayen zinariya, kowacce moɗa daban take, kuma ga ruwan inabin sarakai a yalwace saboda tsabar alfarmar sarki. 8 An shayar ne bisa ga umarni, "Kada a tilasa wa kowa." Sarki ya ba fadawan fadarsa umarni suyi wa kowa yadda yake so. 9 Har wayau, Sarauniya Bashti ta yawa mata biki a fadar Sarki Ahasuros. 10 A rana ta bakwai da sarki ke jin daɗi a zuciyarsa saboda ruwan inabi, ya cewa Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar, da Karkas (shugabanni bakwai da ke masa hidima), 11 su kawo Sarauniya Bashti a gabansa da kambin sarauta a kanta. Yana so ya nuna wa mutane da fadawansa ƙyanta, gama tana da ƙyaƙƙyawan fasali. 12 Amma Sarauniya Bashti taƙi zuwa bisa ga faɗar sarki sa'ad da fadawa suka je suka faɗa mata. Sai sarki ya husata ƙwarai; fushinsa yayi ƙuna a ransa. 13 Sai sarki yayi shawara da waɗanda aka san su masu hikima ne, sun fahimci lokatai (domin haka sarki ya saba yi ga waɗanda suka ƙware a shari'a da hukunci). 14 Na kusa da shi su ne Karshina, Shetar, Admata, Tashish, Meres, Marsina, da Memukan, sarakuna bakwai na Fasiya da Midiya. Suna da 'yancin shiga gun sarki, suke da mafifitan muƙamai a mulkin. 15 "Bisa ga shari'a me za a yiwa Sarauniya Bashti saboda taƙi yin biyayya da umarnin Sarki Ahasuros wanda ya aika mata ta hannun shugabanni?' 16 Sai Memukan yace a gaban sarki da fadawansa, "Ba ga sarki ne kaɗai Sarauniya Basti tayi laifi ba, amma ga dukkan fadawa da dukkan mutanen da ke a lardunan Sarki Ahasuros. 17 Gama wannan al'amari da sarauniya ta aikata zai zama sananne ga dukkan mata. Zai sasu rena mazajensu. Zasu ce, 'Sarki Ahasuros ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa amma taƙi. 18 Kafin faɗuwar ranar yau manyan matan Fasiya da Midiya da suka ji al'amarin sarauniya zasu maimaita wa dukkan hakiman sarki haka. Wannan zai kawo reni da fushi mai yawa. 19 Idan ya gamshi sarki bari a aika dokar sarauta daga gareshi, a kuma rubuta a shari'ar Fasiyawa da Midiyawa da bata canzawa, cewa Bashti ba zata ƙara zuwa gaban sarki ba. Bari sarki ya bada matsayin ta ga wacce ta fita. 20 Sa'ad da dokar sarki ta kai ko'ina a faɗin masarautarsa, dukkan mata zasu girmama mazansu, daga manyansu har zuwa ƙananansu." 21 Sarki da hakimansa sun gamsu ƙwarai da wannan shawara. Sarki kuwa yayi yadda Memukan ya shawarta. 22 Ya aika wasiƙu zuwa dukkan lardunansa, kowanne lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane da harshensu. Ya umarta kowanne namiji ya zama shugaban gidansa. Wannan doka an bada ita a cikin harshen kowaɗanne mutane da ke cikin masarautarsa.

Sura 2

1 Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da fushin Sarki Ahasuros ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da tayi. Ya kuma tuna da dokar da ya zartar akanta. 2 Sai samari waɗanda ke wa sarki hidima suka ce, "Bari a madadin sarki a binciko kyawawan budurwai masu tãshe." 3 Bari sarki yasa shugabanni a dukkan lardunan mulkinsa, su tara dukkan kyawawan budurwai ma su tãshe a gidan mata a cikin masarauta a Susa. A sasu a ƙarƙashin shugabancin Hegai, hakimin sarki, wanda shi ne mai lura da mata, ya kuma basu kayan kwalliyarsu. 4 Bari yarinyar data gamshi sarki ta zama sarauniya a madadin Bashti." Wannan shawarar ta gamshi sarki, sai yayi haka. 5 Akwai wani Bayahude a fadar Susa mai suna Modakai ɗan Yair ɗan Shimeya ɗan Kish ɗan Benyamin. 6 An ɗauko shi ne daga Yerusalem tare da 'yan bautar talala waɗanda aka kwasosu tare da Yehoiachin, sarkin Yahuda, su ne Nebukadnezza sarkin Babila ya kwashe. 7 Yayi ta lura da Hadassa, wato Esta ɗiyar kawunsa, domin bata da uba ko uwa. Yarinyar tana da kyan fasali tana kuma da kyan fuska. Modakai ya ɗauketa a matsayin 'yarsa. 8 Sa'ad da aka yi shelar umarni da dokar sarki, aka kawo 'yan mata da yawa a masarautar Susa. Sai aka sasu a hannun Hegai ya kula dasu. Esta ma aka kaita fadar sarki aka sata a ƙarƙashin Hegai mai lura da mata. 9 'Yar yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashi a wurinsa. Sai nan da nan ya tanada mata kayan kwalliyarta da kuma abincinta. Ya tanada mata kuyangi bakwai daga fadar sarki, ya kuma kaita da ita da kuyanginta wuri mafi kyau a gidan mata. 10 Esta bata gayawa kowa su wane ne mutanenta da danginta ba, gama Modakai ya umarce ta kada ta faɗa. 11 Kowacce rana Modakai yana kai da kawowa a shirayin gidan da aka sa mata, domin ya san lafiyar Esta, da kuma ko me za ayi da ita. 12 Da lokaci yayi da kowacce yarinya zata shiga wurin Sarki Ahasuros - bisa ga ƙa'idar da ke na mata, kowacce yarinya sai ta cika watanni goma sha biyu na kwalliyar mata, wata shida tana shafe jikinta da man mur, wata shida tana shafa turare da mai - 13 sa'ad da yarinya mace ta shiga wurin sarki, duk abin da ranta yaso sai a bata daga cikin gidan matayen domin ta kai fãda. 14 Da yamma zata shiga ciki, da safe zata koma gidan matayen na biyu, a hannun Sha'ashigaz, shugaba na sarki wanda shi ke lura da ƙwaraƙwarai. Ba zata ƙara komawa wurin sarki ba sai in ko yaji daɗinta a ransa kamin ya sake kiranta. 15 Sa'ad da lokacin Esta ('yar Abihel kawun Modakai wanda ya ɗauke ta a matsayin 'yarsa) yazo da zata shiga wurin sarki, bata roƙi komai ba sai abin Hegai bafaden sarki, wanda shi ke kula da matayen, ya bata. A yanzu Esta ta sami farin jini wurin dukkan waɗanda suka dube ta. 16 Aka kai Esta wurin Sarki Ahasuros a masarautar fãda a wata na goma, wanda shi ne watan Tebet a shekararsa ta bakwai da mulki. 17 Sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukkan sauran matayen ta kuma sami karɓuwa da tagomashi daga gare shi, fiye da dukkan sauran budurwan. Sai ya ɗibiya mata kambin sarauta a kanta ya maisheta sarauniya a madadin Bashti. 18 Sai sarki ya yi ƙasaitaccen biki domin dukkan hakimansa da kuma barorinsa, wato, "Bikin Esta'," kuma ya tsaida biyan haraji a duk lardunansa. Ya kuma bada kyautai bisa ga falalar yalwar mulkinsa. 19 Ananan sa'ad da aka tara budurwai karo na biyu, Modakai ya zauna a ƙofar sarki. 20 Esta ba ta rigaya ta faɗa wa kowa game da 'yan uwanta ko mutanenta ba, domin Modakai ya umarceta. Ta ci gaba da bin shawarar Modakai, kamar yadda tayi lokacin daya reneta. 21 A kwanakin da Modakai ke zama a ƙofar sarki, hakiman sarki guda biyu, Bigtan da Teres, masu tsaron ƙofa, suka fusata suka nema su cuci Sarki Ahasuros. 22 Da aka bayyana wa Modakai al'amarin sai ya gaya wa Sarauniya Esta, Esta ta faɗa wa sarki a sunan Modakai. 23 Aka bincika rahoton aka tabbatar haka yake, sai aka rataye dukkansu biyun a bisa gungume. Aka rubuta wannan al'amari a Littafin Tarihi a gaban sarki.

Sura 3

1 Bayan waɗannan abubuwa, Sarki Ahasuros ya ɗaukaka Haman ɗan Hamedata Ba'agage, ya fifita matsayin ikonsa bisa kan dukkan shugabanni da ke tare da shi. 2 Dukkan barorin sarki da ke ƙofar sarki kulluyomi sukan durƙusa su rusuna wa Haman, gama sarki ya umarta suyi haka. Amma Modakai bai durƙusa masa ba ko kuma ya rusuna masa ba. 3 Sai barorin sarki da ke a kofar sarki suka cewa Modakai, "Me yasa kake rashin biyayya da dokar sarki?" 4 Suka yita masa magana kowacce rana, amma yaƙi ya cika burinsu. Saboda haka suka gaya wa Haman domin suga ko za a bar al'amarin game da Modakai ya zama haka, gama ya gaya musu shi Bayahude ne. 5 Da Haman yaga Modakai baya durƙusa ko ya rusuna masa ba, sai Haman ya cika da hasala. 6 Sai ya ƙudurta ba Modakai kaɗai zai kashe ba, gama barorin sarki sun gaya masa irin mutanen Modakai. Haman yana so ya hallakar da dukkan Yahudawa, mutanen Modakai, waɗanda suke cikin dukkan masarautar Ahasuros. 7 A cikin wata na fari (wanda shi ne watan Nisan), a shekara ta goma sha biyu ta mulkin Sarki Ahasuros, aka jefa Fur - wato ƙuri'a - a gaban Haman, domin a zaɓi rana da wata. Suka yita jefa ƙuri'a akai akai har sai data faɗa akan watan goma sha biyu (wato watan Ada). 8 Sa'an nan Haman ya cewa Sarki Ahasuros, "Akwai waɗansu mutane a warwatse an kuma baza su a dukkan lardunan masarautarka. Shari'arsu daban take data sauran mutane, basa kuma kiyaye dokokin sarki, sabili da haka bai kyautu ba sarki ya bar su da rai. 9 Idan sarki ya amince, ya bada umarni a kashe su, ni kuma zan bada talanti dubu goma na azurfa a hannun waɗanda ke tafiyar da cinikaiyar sarki, domin susa a cikin baitulmalin sarki." 10 Sai sarki ya tuɓe zobensa daga yatsansa ya ba Haman ɗan Hamedata Ba'agagite, maƙiyin Yahudawa. 11 Sarki ya cewa Haman, "Zan tabbatar an mayar maka da kuɗin da kuma mutanenka. Za ka yi abin daka gadama da su." 12 Sai aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari, aka rubuta doka game da dukkan umarnin da Haman ya bayar zuwa ga masu mulkin lardunan sarki, waɗanda suke bisa dukkan larduna, zuwa ga gwamnonin dukkan al'umma, da shugabannin dukkan mutane, ga kowanne lardi bisa ga irin rubutunsa, da kowacce al'umma kuma bisa ga harshenta. Da sunan Sarki Ahasuros aka rubuta, aka kuma hatimce shi da zobensa. 13 Aka aika da takardun hannu da hannu ta wurin manzanin zuwa ga dukkan lardunan sarki, domin a shafe su, a kashe, a kuma hallaka dukkan Yahudawa, samari da tsofaffi, yara da mata, rana ɗaya - a rana ta goma sha uku a watan goma sha biyu (wato watan Ada) - a kuma washe mallaƙarsu. 14 Sai aka sanar kowanne lardi takardar data zama shari'a. Aka sanar da dukkan mutane a kowanne lardi cewa su shirya domin wannan rana. 15 Manzanin suka tafi da hanzari domin su baza umarin sarki. Aka baza umarnin kuma a fadar Susa. Da sarki da Haman suka zauna domin su sha, amma birnin Susa ya ruɗe.

Sura 4

1 Da Modakai ya ji dukkan abin da aka riga aka yi, sai ya kyekketa tufafinsa yasa rigar makoki da toka. Ya fita waje ya je tsakiyar birni, ya yita rusa kuka da bacin rai mai tsanani. 2 Iyakarsa bakin ƙofar sarki kaɗai, domin ba a yardar wa kowa ya wuce wurin sanye da tsummoki ba. 3 A kowanne lardi, duk inda umarnin da dokar sarki ya kai, Yahudawa suka yi ta makoki ƙwarai, tare da azumi, kuka da makoki. Da yawa kuma suka zauna cikin tsummoki da toka. 4 Da kuyangun Esta da barorinta suka zo suka faɗa mata, sarauniya ta damu ƙwarai. Ta aika wa Modakai tufafin sawa (domin ya tuɓe tsummokaransa), amma ya ƙi karɓarsu. 5 Sai Esta ta kira Hatak, ɗaya daga cikin wakilan sarki wanda aka sasu yi mata hidima. Ta umarce shi ya je wajen Modakai ya binciko abin daya faru da kuma ma'anar al'amarin. 6 Sai Hatak ya tafi wurin Modakai a dandalin birnin da ke gaban ƙofar sarki. 7 Modakai ya gaya masa dukkan abin daya faru da shi, da kuma jimillar azurfar da Haman ya alƙawarta zai auna ya sa a baitulmalin sarki domin a kashe Yahudawa. 8 Ya kuma ba shi takardar umarnin bugu na biyu a Susa domin hallaka Yahudawa. Yayi haka ne domin Hatak ya nuna wa Esta, ya kuma ba ta nawaiyar tafiya wurin sarki don ta roƙi tagomashi ta kuma nemi alfarma daga gare shi game da mutanenta. 9 Sai Hatak ya tafi ya faɗa wa Esta abin da Modakai yace. 10 Sai Esta ta yi magana da Hatak cewa ya koma wurin Modakai. 11 Ta ce, "Dukkan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani cewa duk wani namiji ko mace wanda ya shiga cikin farfajiyar sarki ba tare da an kira shi ba, doka ɗaya ce tak: wato dole a kashe shi - sai ko wanda sarki ya miƙa wa sandar zinariya kaɗai domin ya rayu. Ba a kira ni in je wurin sarki ba kwanakin nan talatin." 12 Sai Hatak ya tafi ya faɗa wa Modakai abin da Esta ta ce. 13 Modakai ya mayar da wannan saƙo: "Kada ki yi tsammanin saboda kina gidan sarki zaki kuɓuta fiye da sauran Yahudawa. 14 Idan kika yi shiru a wannan lokaci, to gudunmawa da tsira zasu zo wa Yahudawa daga wani wuri, amma ke da gidan mahaifinki zaku hallaka. Wa ya sani ko kin sami wannan matsayin mulkin saboda makamancin lokaci irin wannan?" 15 Sa'an nan Esta ta aika wa Modakai wannan saƙo, 16 "Kaje ka tattara dukkan Yahudawan da ke zaune a Susa, kuyi azumi domina. Kada ku ci ko ku sha har kwana uku, rana ko dare. Ni da 'yan matana ma zamu yi haka. Sa'an nan zan je wajen sarki, koda yake yin hakan ya saɓa wa shari'a, idan na hallaka, na hallaka." 17 Modakai ya tafi yayi duk abin da Esta ta faɗa masa yayi.

Sura 5

1 Bayan kwana uku, sai Esta ta saka rigunan sarauta ta tafi ta tsaya a shirayin ciki na fadar sarki, a gaban gidan sarki. Sarki yana zaune a kan kursiyinsa a masarautar gidansa, yana fuskantar kofar shiga gidan. 2 Lokacin da sarki ya ga sarauniya Esta tana tsaye a shirayi, sai ta sami amincewa a idanunsa. Sai ya miƙa mata sandar zinariya da ke hannunsa. Sa'an nan Esta ta matso ta taɓa kan sandar. 3 Sa'an nan sarki yace mata, "Mene ne kike so Sarauniya Esta? Mene ne roƙon ki? Har ma rabin masarautata, za a ba ki." 4 Esta tace, "Idan sarki ya yarda, bari sarki da Haman su zo yau wurin liyafar dana shirya domin sa." 5 Sa'an nan sarki yace, "Ku kawo Haman nan da nan, yayi abin da Esta ta ce." Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Sarauniya Esta ta shirya. 6 Lokacin da ana raba ruwan inabi a liyafar, sai sarki ya cewa Esta, "Me kike so? Za a baki. Mene ne kike roƙo? Har ma rabin masarautar, za a baki ita." 7 Esta ta amsa, "Abin da nike so da kuma roƙona shi ne, 8 idan na sami tagomashi a idanun sarki kuma idan ya gamshi sarki ya amsa roƙona kuma ya girmama roƙona, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan shirya maka gobe, sa'an nan zan amsa tambayar sarki." 9 A wannan rana Haman ya tafi gida da murna da farinciki, a zuciyarsa. Amma da Haman ya ga Modakai a bakin ƙofar sarki, kuma Modakai bai tashi tsaye ba balle yayi rawar jiki a gabansa da ko wani tsoro, sai ya cika da hasala găba da Modakai. 10 Duk da haka Haman ya kame kansa ya tafi gidansa. Ya aika aka kira abokansa, ya kuma tattarosu da matarsa Zeresh. 11 Haman ya rattaba masu darajar wadatarsa, yawan "ya'yansa maza, da dukkan yawan matsayi da sarki ya girmama shi da su, da yadda yake da fifikon daya zarce na dukkan shugabanni da barorin sarki. 12 Haman yace, "Sarauniya Esta bata gayyaci kowa ba sai ni zan je da sarki liyafar data shirya. Har ma gobe ta sake gayyata ta in zo tare da sarki. 13 Amma ban ɗauki duk wannan a bakin komai ba a gareni muddin in na ganin Modakai zaune a bakin ƙofar sarki." 14 Sai Zeresh matarsa ta cewa Haman da dukkan abokansa. Bari a kafa wani gungume mai tsawon ƙafa hamsin. Da safe sai ka yi magana da sarki domin su rataye Modakai a kai. Sa'an nan ka tafi da murna tare da sarki wurin liyafar." Wannan ya gamshi Haman sai yasa aka kafa gungumen.

Sura 6

1 A daren nan sarki ya kasa barci. Sai ya umarci barori su kawo tarihin ayyukan mulkinsa, aka kuma riƙa karanta wa sarki da murya. 2 Sai aka tarar a rubuce a wurin cewa Modakai ya faɗi game da Bigtana da Teresh, fadawan sarki biyu da ke tsaron ƙofa, da suka yi ƙoƙarin su cuci Sarki Ahasuros. 3 Sarki ya tambaya, "Me aka yi don a bashi girma ko a maida Modakai sananne saboda yayi wannan abu?" Sai samari matasa na sarki da ke masa hidima suka ce, "Ba a yi masa komai ba." 4 Sarki yace, "Wa ke a shirayi?" Yanzu fa Haman ya rigaya ya shigo shirayin gidan sarki na waje domin yayi masa magana game da rataye Modakai a kan gungumen daya kafa masa. 5 "Barorin sarki suka ce masa, Haman yana tsaye a shirayi." Sarki yace bari ya shigo ciki." 6 Da Haman ya shigo, sarki yace masa, "Me za a yiwa mutumin da sarki yake jin daɗin ya girmama shi?" Sai Haman yace a zuciyarsa, "Wane ne kuwa sarki zai ji daɗin girmama shi fiye da ni?" 7 Haman ya cewa sarki, "Saboda mutumin da sarki ke jin daɗin girmama shi, 8 bari a kawo rigunan sarauta, waɗanda sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, kuma a sa masa kambin sarauta. 9 Sa'an nan da rigunan da dokin a ba da su ga ɗaya daga cikin manyan shugabanni. Bari su sa wa mutumin da sarki ke so ya girmama rigunan, bari kuma su bishe shi a kan dokin, a titunan birni. Bari kuma su yi shela a gabansa, "Wannan shi ne abin da ake yi wa wanda sarki ke jin daɗin girmama shi!'" 10 Sai sarki ya cewa Haman, "Yi hanzari ka ɗauki rigunan da dokin, kamar yadda ka faɗi kayi wa Modakai Bayahude wanda ya kan zauna a ƙofar sarki. Kada ka kasa yin ko abu ɗaya daga abin da ka faɗa." 11 Sai Haman ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sanya wa Modakai rigunan ya bishe shi bisa dokin a dukkan titunan birnin. Yayi ta shela a gabansa, '"Haka ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗin girmama shi." 12 Modakai ya dawo ƙofar sarki. Amma Haman ya gaggauta zuwa gidansa, yana makoki, da kansa a lulluɓe. 13 Haman ya gaya wa matarsa Zeresh da dukkan abokanansa duk abubuwan da suka faru da shi. Sai mutanensa sanannu domin hikimarsu, da Zeresh matarsa suka ce masa, "Idan dai Modakai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa Bayahude ne, ba zaka ci nasara a kansa ba, amma hakika zaka faɗi a gabansa." 14 Suna cikin magana da shi haka, sai ga hakiman sarki sun iso. Suka gaggauta suka tafi da Haman wurin liyafar da Esta ta shirya.

Sura 7

1 Sai sarki da Haman suka tafi su yi liyafa da Sarauniya Esta. 2 A kan rana ta biyu, da ake bada ruwan inabi, sarki ya cewa Esta, "Mene ne roƙonki, Sarauniya Esta? Za a biya maki. Me kike tambaya? Har ma rabin masarautar ma, za a kuma baki." 3 Sai Sarauniya Esta ta amsa, "Idan na sami tagomashi a idanun ka, idan kuma ka yarda, bari a barni da raina - wannan shi ne roƙona, ina kuma roƙon wannan domin mutanena. 4 Gama an sayar damu - ni da mutanena, domin a hallaka mu, a kashe, a kuma shafe mu gaba ɗaya. Dama a ce an sayar damu ga bauta, maza da mata bayi, dana yi shuru, gama ba wani ƙunci makamancin haka da zai bada dalilin damun sarki." 5 Sai Sarki Ahasuros ya cewa Sarauniya Esta, "Wa ye shi? Ina za a sami wannan mutum daya ƙudurta a zuciyarsa yayi makamancin abu haka?" 6 Esta tace, "Mafaɗacin mutumin, wannan maƙiyi shi ne mugun nan Haman!" Sai Haman ya firgita a gaban sarki da sarauniya. 7 Sarki ya miƙe tsaye cikin hasala wurin shan ruwan inabin liyafar ya tafi cikin lambun fãda, amma Haman ya jira ya roƙi ransa daga Sarauniya Esta. Ya lura sarki yana niyyar zartar da hallakarwa gãba da shi. 8 Sarki ya komo daga lambun fãda zuwa cikin ɗakin da aka shayar da su ruwan inabi. Haman ya faɗi a kan kujerar da Esta take. Sai sarki yace, "Zai ci mutuncin sarauniya a gabana a cikin gidana?" Da zarar fitar wannan magana daga bakin sarki, sai barorin suka lulluɓe fuskar Haman. 9 Sai Harbona, ɗaya daga cikin hakimai da ke wa sarki hidima, ya ce, "Akwai wani gugume mai tsawon kamu hamsin kusa da gidan Haman. Ya kafa shi ne saboda Modakai, wanda yayi magana domin a kare sarki." Sarki yace, "A rataye shi a kai." 10 Sai suka rataye Haman bisa gungumen da ya shirya saboda Modakai. Sai hasalar sarki ya huce.

Sura 8

1 A wannan ranar Sarki Ahasuros ya bai wa Sarauniya Esta mallakar Haman, maƙiyin Yahudawa, sai kuma Modakai ya fara hidima a gaban sarki, gama Esta ta gaya wa sarki dangartakarta da Modakai. 2 Sai sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓe daga wurin Haman, sai ya ba da shi ga Modakai. Esta ta sa Modakai ya zama mai lura da gidagen Haman. 3 Sai Esta ta sake yin magana da sarki. Ta kwantar da fuskartar a ƙasa tana kuka yayinda take roƙo gareshi ya kawo ƙarshen mugun shirin Haman Ba'agage, da maƙarkashiyar daya ƙulla wa Yahudawa. 4 Sai sarki ya miƙo sandar zinariya na sarauta ga Esta, ta tashi ta tsaya a gaban sarki. 5 Sai ta ce, "Idan ya gamshi sarki, kuma idan na sami tagomashi a wurinka, idan abin yayi dai-dai a ganin sarki, kuma idan na sami tagomashi a idanunka, bari a bada rubutaccen umarni da zai soke wasi‌ƙ‌un da Haman ɗan Hamedata Ba'agage, ya rubuta domin ya hallakar da Yahudawa waɗanda suke warwatse cikin lardunan sarki. 6 Gama yaya zan jimre da ganin masifar da za ta faɗo wa mutanena? Ta yaya zan iya daure wa ganin hallakarwar dangina?" 7 Sarki Ahasuros ya cewa Sarauniya Esta da kuma Modakai Bayahude, "Duba, na miƙa wa Esta gidan Haman, kuma sun rataye shi a bisa gungume, domin yayi shirin kaiwa Yahudawa farmaki. 8 Rubuta wani umarni domin Yahudawa a cikin sunan sarki a kuma hatimce shi da zoben sarki. Gama umarnin da aka riga aka rubuta da sunan sarki aka kuma hatimce shi da zoben sarki ba za a iya soke shi ba." 9 Sai aka kirawo magatakardan sarki a wannan lokaci, a cikin wata na uku, wanda shi ne watan Siban, a ranar ashirin da uku ga wata. Aka rubuta umarni ɗauke da dukkan abin da Modakai ya umarta game da Yahudawa. Aka rubuta zuwa ga gwamnonin larduna, su gwamnoni da shugabannin lardunar da ke zaune daga Indiya zuwa Kush, larduna 127, ga kowanne lardi aka rubuta da irin rubutunsu, da kuma ga kowaɗanne mutane cikin yarensu, da kuma ga Yahudawa da rubutunsu da yarensu. 10 Modakai yayi rubutu da sunan sarki Ahasuros ya kuma hatimce shi da zoben hatimin sarki. Ya aika takardun ta hannun 'yan kada ta kwana mahaya doki masu gudu sosai da ake yin anfani da su a hidimar sarki, wanda aka yi renon su daga masarauta. 11 Sarki ya baiwa Yahudawa na kowanne birni izinin taruwa tare a kuma yi tsayayya don kariyar rayukarsu: su shafe su gaba ɗaya, su kashe, su kuma hallakar da kowacce taruwar masu makamai daga kowaɗanne mutane, ko lardin da ke niyyar kawo masu farmaki, da yaransu da kuma matayensu, ko su kwashi dukiyoyinsu ganima. 12 Wannan za a aiwatar cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, a ranar sha uku na watan sha biyu, wanda shi ne watar Ada. 13 Takardar dokar za a miƙa ta a matsayin shari'a kuma za a bayyana ta a fili ga dukkan mutane. Yahudawa sai su zauna da shiri a wannan rana don ɗaukar fansa kan maƙiyansu. 14 Sai 'yan kada ta kwana suka hau dawakan masarauta da ake amfani dasu a hidimar sarki. Suka tafi babu ɓata lokaci. Dokar sarki kuwa aka miƙa ta daga fada a Susa. 15 Sai Modakai ya tashi daga gaban sarki sanye da rigunan sarauta na shuɗi da fari, tare da gagarumin kambi na zinariya da kuma alkyabba ta lillin mai ruwan shunayya, sai birnin Susa tayi sowa da kuma farinciki. 16 Yahudawa suka sami sauƙi da kuma farinciki, da kuma murna da kuma daraja. 17 A kowanne lardi da cikin kowanne birni, dukkan inda umarnin sarki ya kai, aka yi farinciki da kuma murna a tsakanin Yahudawa, aka yi biki da kuma hutu. Dayawa daga cikin mutane daban-daban a ƙasar suka zama Yahudawa, domin tsoron Yahudawa ya faɗo masu.

Sura 9

1 Yanzu a cikin watan sha biyu, wanda shi ne watan Ada, a ranar sha uku, lokacin da za a aiwatar da shari'a da kuma dokar sarki, a ranar da makiyan Yahudawa ke sa ran zasu sha karfinsu, aka juyad da yanayin. Yahudawa suka sha karfin waɗanda suka tsane su. 2 Yahudawa suka tattaru a biranensu cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, su tayar wa waɗanda suka so su kawo masu bala'i. Babu wanda ya iya tsayayya dasu, gama tsoronsu ya abko wa dukkan mutanen. 3 Dukkan shugannin lardunar, da gwamnonin lardunar, su gwamnoni, da ma'aikatan sarki, suka taimaka wa Yahudawa domin tsoron Modakai ya abko masu. 4 Gama Modakai ya zama mutum mai girma a gidan sarki, kuma labarinsa ya bazu a dukkan larduna, domin mutumin Modakai ya zama mai girma. 5 Yahudawa suka kai hari ga makiyansu da takobi, suna kisansu da hallakar da su, kuma suka yi masu yadda suka ga dama ga waɗanda suka ƙisu. 6 A cikin fãdar Susa da kanta Yahudawa suka kashe da kuma hallakar da mutum ɗari biyar. 7 Suka kashe Farshandata, Dalfon, Asfata, 8 Forata, Adaliya, Aridata, 9 Farmashta, Arisai, Aridai, da Baizata, 10 da kuma 'ya'ya maza na Haman ɗan Hamedata su goma, maƙiyin Yahudawa. Amma basu kwashi ganima ba. 11 A wannan rana jimillar waɗanda aka kashe cikin fãdar Susa, aka faɗa wa sarki. 12 Sai sarki ya cewa Sarauniya Esta, "Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar cikin fãdar Susa, har da 'ya'ya maza na Haman su goma. Mene ne kuma suka aiwatar cikin sauran lardunar sarki? Yanzu mene ne roƙonki? Za a baki. Mene ne bukatarki? Za a biya maki." 13 Esta tace, "Idan ya dace a ganin sarki, bari a baiwa Yahudawan da ke cikin Susa izinin aiwatar da dokar yau a gobe kuma, bari kuma a rataye gawawakin 'ya'ya maza na Haman su goma a bisa gumagumai." 14 Sai sarki ya umarta da a yi haka. Aka zartar da dokar a cikin Susa, aka kuma rataye 'ya'ya maza goma na Haman. 15 Yahudawa da ke a Susa suka taru tare a rana ta sha huɗu a watan Ada, suka kashe mutum ɗari uku cikin Susa, amma ba su kwashi ganima ba. 16 Sauran Yahudawa da ke a lardunan sarki suka taru tare don su kare rayukansu, sun kuma ƙuɓuta daga makiyansu suka kuma kashe mutum dubu saba'in da biyar daga waɗanda suka tsanesu, amma basu ɗibiya hannunsu bisa dukiyan waɗanda suka kashe ba. 17 Wannan ya faru ne a ranar sha uku na watan Ada. A rana ta sha huɗu sai suka huta suka maishe ta ranar shagali da kuma murna. 18 Amma Yahudawan da ke a Susa suka taru tare a ranakun sha uku da sha huɗu. A rana ta sha biyar suka ka huta suka maishe ta ranar shagali da kuma murna. 19 Shi yasa Yahudawan da ke ƙauyuka, waɗanda suka yi gidajensu a ƙauyukan karkara, suka maida rana ta sha huɗu na watan Ada ranar murna da kuma shagali, da kuma ranar da zasu aika wa juna kyaututtukan abinci. 20 Modakai ya rubuta waɗannan abubuwan ya kuma aika wasiƙu zuwa ga dukkan Yahudawan da ke cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, na kusa dana nesa, 21 yana umurtansu dasu kula su kuma kiyaye ranakun sha huɗu da kuma sha biyar na Ada a kowacce shekara. 22 A wannan kwanaki ne Yahudawa suka kuɓuta daga maƙiyansu, da kuma watan da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, kuma ranar makoki ta zama ranar shagali. Zasu maishe su ranakun shagali da kuma murna, da kuma aikar da kyaututtukan abinci ga juna, da kuma kyaututtuka ga talakawa. 23 Sai Yahudawa suka cigaba da shagali kamar yadda suka fara, suna aiwatar da abin da Modakai ya rubuta garesu. 24 A wannan lokacin da Haman ɗan Hamedata Ba'agage, maƙiyin dukkan Yahudawa, ya shirya wa Yahudawa makirci don ya hallakar dasu, ya kuma jefa Fur (wato, ya jefa ƙuri'u), don ya hargitsa su ya hallakar da su. 25 Amma da zancen ya kai ga sarki, sai ya bada umarnai ta wasiƙu domin makircin da Haman ya ƙulla gãba da Yahudawa shi koma kansa, da kuma a rataye shi da 'ya'yansa maza a bisa gumagumai. 26 Saboda haka aka kira waɗannan ranakun sunan Furim, bisa ga sunan Fur. Saboda dukkan abubuwan da aka rubuta cikin wannan wasiƙa, da dukkan abin da suka gani da idanunsu ta kuma same su, 27 Yahudawa suka yi na'am da sababbin ranaku da al'ada. Wannan ranaku zasu zama dominsu, da kuma zuriyarsu, da kuma dukkan wanda zai haɗa kai da su. Ya kuma zama cewa za su tuna da waɗannan ranakun biyu sau biyu a kowacce shekara. Zasu kula da waɗannan ranakun a hanyoyi na musamman da kuma a lokaci ɗaya kowacce shekara. 28 Waɗannan ranaku za a yi bukukuwa a kuma kula dasu a kowacce tsara, da kowanne iyali, da kowanne lardi, da kowanne birni. Waɗannan Yahudawan da kuma zuriyarsu ba zasu dena tunawa da waɗannan ranakun Furim cikin aminci ba, domin kada su manta da su. 29 Sarauniya Esta ɗiyar Abihel da Modakai Bayahude suka yi rubutu da cikakken iko suka kuma tabbatar da wannan wasika ta biyu game da Furim. 30 Aka aika wasiƙu zuwa ga dukkan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Ahasuros, ana yi wa Yahudawa barka na salama da gaskiya. 31 Waɗannan wasiƙu suka tabbatar da ranakun Furim cikin lokacinsu, kamar yadda Modakai Bayahude da Sarauniya Esta suka dokaci Yahudawa. Yahudawa suka yi na'am da wannan doka domin kansu da kuma zuriyarsu, kuma kamar yadda suka yi na'am da lokacin azumi da makoki. 32 Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan sharuɗɗai game da Furim, an kuma rubuta su cikin littafi.

Sura 10

1 Sa'an nan Sarki Ahasuros yasa dokar haraji a ƙasar da kuma kasashen tuddai na bakin teku. 2 Dukkan aikin ci gaba na iko dana karfi, tare da cikakken tarihin girman Modakai ta yadda sarki ya darajartar da shi, aka rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Midiya da kuma Fasiya. 3 Modakai Bayahude ya zama na biyu bayan sarki Ahasuros ta fannin mulki. Mai girma ne cikin Yahudawa da kuma sananne cikin 'yan'uwansa Yahudawa masu yawa, gama yana kula da lafiyar mutanensa yana yin maganar salama domin dukkan mutanensa.

Littafin Ayuba
Littafin Ayuba
Sura 1

1 Akwai wani mutum a ƙasar Uz mai suna Ayuba; Ayuba kuwa marar laifi ne mai gaskiya, wanda ke tsoron Yahweh ya kuma juya wa mugunta baya. 2 A ka haifa masa 'ya'ya bakwai maza da 'yammata uku. 3 Ya mallaki tumaki dubu bakwai da raƙuma dubu uku da bijimai ɗari biyar da jakai ɗari biyar da kuma bayi masu yawan gaske. Shi ne ya fi girma a cikin dukkan mutanen Gabas. 4 An keɓe rana domin kowanne ɗă, ya yi liyafa a cikin gidansa. Sukan aika a kira 'yan'uwansu mata su uku su ci su sha tare da su. 5 Sa'ad da kwanakin liyafar suka ƙare, sai Ayuba ya aika su zo ya tsarkake su. Ya kan tashi da sassafe ya miƙa baye--baye na ƙonawa domin kowanne ɗaya a cikin 'ya'yansa, gama ya kan ce, "Ya yiwu yarana sun yi zunubi sun yi saɓon Yahweh a cikin zukatansu." Haka Ayuba yakan yi kullun. 6 A ranar da 'ya'yan Allah maza suka zo domin su bayyana kansu a gaban Yahweh. Sai Shaiɗan ma ya biyo su. Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Daga ina ka zo?" 7 Sai Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Daga garari cikin duniya da zirga--zirga a cikinta." 8 Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Ka kuwa lura da Ayuba bawana? Gama babu kamar sa a duniya, marar laifi ne kuma mutum ne mai gaskiya yana tsoron Yahweh ya juya wa mugunta baya. 9 Sa'annan Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Haka nan Ayuba ya ke tsoron Allah ba dalili? 10 Ba ka kare shi ta kowanne gefe ba, shi da gidansa da dukkan abin da ya ke da shi? K a sawa ayyukan hannuwansa albarka da shanunsa sun yaɗu da yawa a cikin ƙasa. 11 Amma yanzu ka miƙa hannunka ka taɓa abin da ya ke da shi dukka, ka gani idan bai la'ance ka kana gani ba." 12 Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Duba, dukkan abin da ya ke da shi na hannunka." Sai dai a kansa ne kaɗai ba zaka sa hannunka ba." Sa'annan Shaiɗan ya fita daga wurin Yahweh. 13 Sai ya zama a wata rana, 'ya'yansa maza da mata suna ci suna shan ruwan inabi a gidan babban wansu. 14 Wani ɗan aike ya zo wurin Ayuba yace, "Bijimai suna huɗa jakai kuma suna kiwo a gefensu. 15 Sai Sabiyawa suka auko ba zato suka kwashe su. Bayin kuma sun kashe su da kaifin takobi. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka." 16 Yana cikin yin magana, sai wani kuma ya zo ya ce, "Wutar Allah ta sauko daga sama ta cinye tumaki duk da bayin. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka." 17 Yana cikin yin magana, sai wani kuma ya zo ya ce, "Kaldiyawa sun zo a ƙungiyoyi uku, sun kawo hari a kan raƙuman sun kwashe su. Sun kuma kashe bayin da kaifin takobi. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka." 18 Yana cikin yin magana, wani kuma ya zo ya ce, "Ya'yanka maza da matan suna ci suna sha a gidan babban wansu. 19 Sai wata iska mai ƙarfi ta taso daga cikin jeji ta buge kusurwoyin gidan guda huɗu. Gidan ya faɗa a kan matasan, kuma sun mutu. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka." 20 Sai Ayuba ya tashi, ya keta tufafinsa, ya aske kansa, ya faɗi da fuskarsa a ƙasa, ya yi wa Yahweh sujada. 21 Ya ce, "Sa'ad da na fito daga cikin mahaifiyata tsirara nake, kuma tsirara zan koma can. Yahweh ne ya bayar, Yahweh ne kuma ya ɗauke. Bari sunan Yahweh ya zama mai albarka." 22 A cikin wannan lamari dukka, Ayuba bai yi zunubi ba, bai kuma yi zargi ga Allah kan ya yi kuskure ba.

Sura 2

1 Wata rana kuma da 'ya'yan Allah maza suka zo su baiyana kansu a gaban Yahweh. Shaiɗan ma ya biyo su don ya baiyana kansa a gaban Yahweh. 2 Yahweh yace da Shaiɗan, "Daga ina ka zo?" Sai Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Daga garari cikin duniya da kai da kawowa a kanta." 3 Yahweh yace da Shaiɗan, "Ka lura da bawana Ayuba? Gama babu kamar sa a duniya, marar laifi ne, mutum ne mai gaskiya, yana juya wa mugunta baya. Har yanzu yana nan riƙe da nagartarsa, duk da yake ka sa in yi gãba da shi, don in hallaka shi babu wani dalili." 4 Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Jiki magayi, tabbas mutum zai iya rabuwa da dukkan abin da yake da shi domin ya ceci ransa. 5 Amma ka miƙa hannunka yanzu ka taɓa ƙasusuwansa da jikinsa, ka gani idan bai la'ance ka kana gani ba." 6 Yahweh yace da Shaiɗan, "Ga shi, yana hannunka; ransa ne kaɗai ba zaka taɓa ba." 7 Daga nan sai Shaiɗan ya tafi daga gaban Yahweh. Ya bugi Ayuba da marurai tun daga tafin ƙafarsa har zuwa kansa. 8 Ayuba ya ɗauki ɓallin kasko yana susa da shi, kuma ya zauna a cikin tsakiyar toka. 9 Sai matarsa tace da shi, "Har yanzu kana nan riƙe da nagartarka? Ka la'anci Allah ka mutu." 10 Amma ya ce da ita, "Kina yin magana kamar yadda gaɓuwar mace ke yi. Za mu karɓi abu mai kyau daga wurin Allah mu ƙi karɓar marar kyau"? A cikin wannan lamari dukka, Ayuba bai yi zunubi da leɓunansa ba. 11 A na nan, sa'ad da abokan Ayuba uku suka ji dukkan wannan bala'in da ya same shi, kowannen su ya tawo daga garinsa: Elifaz Batemane da Bildad Bashune da Zofar Banamate. Suka sa lokaci domin suzo su makoki tare da shi su kuma ta'azantar da shi. 12 Sa'ad da suka hango daga nesa, basu iya gane shi ba. Suka tada muryoyinsu suka yi kuka; kowannen su ya keta tufafinsa ya watsa ƙura a sama dakuma bisa kansa. 13 Sa'an nan suka zauna a ƙasa tare da shi a ƙasa har yini uku da dare uku. Ba wanda ya yi masa magana, gama sun ga yana da baƙin ciki mai yawa.

Sura 3

1 Bayan wannan, Ayuba ya buɗe bakinsa ya la'anci ranar da aka haife shi. 2 Ya ce: 3 "Bari ranar da a ka haife ni ta lalace, kuma da daren aka ce, 'an ɗauki cikin yaro.' 4 Bari ranar ta zama baƙa; Dãma kada Yahweh ya tuna da ita daga sama, kada ma rana ta yi haske a kanta. 5 Dãma duhu da inuwar kwarin mutuwa su maishe ta tasu. Dãma girgije ya tsaya a kan ta, dãma kowanne abu mai sa rana ta yi baƙi ya ba ta tsoro da gaske. 6 Wannan daren kuma, dãma baƙin duhu ya rufe shi. Dãma kada ta yi farinciki a ranakun shekara; dãma kada a lissafa ta cikin kwanakin watanni. 7 Duba, dãma wannan dare ya zama wofi; kada muryar farinciki ta zo cikinsa. 8 Dãma su la'anci wannan rana, waɗanda suka san yadda a ke tashin Lebiyatan. 9 Dãma taurarin wayewar giri na wannan rana su yi duhu. Dãma wannan rana ta nemi haske, amma ta rasa; dãma kada ta ga ƙyallin wayewar gari, 10 saboda bata rufe ƙofofin cikin uwata ba, kuma domin bata ɓoye masifa daga idanuna ba. 11 Me yasa ban mutu sa'ad da na fito daga ciki ba? Me yasa ban saki ruhuna sa'ad da uwata ta haife ni ba? 12 Me yasa gwiwoyinta suka marabce ni? Me yasa nonanta suka yarda na shã su? 13 Gama da yanzu ina kwance shiru. Da ina barci ina hutawa 14 tare da sarakuna da mashawartan duniya, waɗanda suka gina wa kansu kaburbura kuma yanzu sun ruɓe. 15 Ko kuwa da yanzu ina kwance tare da sarakuna waɗanda dã suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa. 16 Ko kuwa ƙila da an yi ɓari na, kamar jariran da basu taɓa ganin haske ba. 17 A can masu mugunta sun huta da masifa; a can masu gajjiya suna cikin hutu. 18 A can 'yan kurkuku sun sami saki tare; bãsu jin muryar masu kora bayi. 19 Manya da ƙananan mutane suna can; bawa yana da 'yanci daga wurin ubangijinsa a can. 20 Me yasa ake ba wanda ke cikin ƙunci haske? Me yasa a ke ba wanda ke da baƙin ciki rai, 21 wanda ya ƙagara yaga mutuwa bata zo ba, ga wanda yake neman mutuwa kamar ɓoyayyiyar dukiya? 22 Me yasa a ke bada haske ga wanda yake farinciki ƙwarai da murna idan ya sami kabari? 23 Me yasa a ke ba mutum wanda hanyarsa take a ɓoye haske, mutum wanda Allah ya kulle shi? 24 Gama ajjiyar zuciya nake yi maimakon cin abinci; an zubar da gurnanina kamar ruwa. 25 Gama abin da na ji tsoro ya zo kaina; abin dana tsorata yazo mani. 26 Ba sauƙi a gare ni, ban yi shuru ba, kuma ban huta ba; maimakon haka masifa ce take zuwa."

Sura 4

1 Sai Elifaz Batemane ya amsa ya ce, 2 Idan wani yayi ƙoƙari ya yi magana da kai, baza ka yi haƙuri ba? Amma wa zai iya hana kansa yin magana? 3 Ka ga, ka koyawa mutane da yawa; ka ƙarfafa raunanan hannuwa. 4 Kalmominka sun tallafi wanda yake faɗuwa; ka sa raunanan gwiwoyi sun yi ƙarfi. 5 Amma yanzu masifa ta zo kanka, kuma ka gaji; ta taɓa ka, kuma ka kaɗu. 6 Tsoronka bai zama ƙarfi a gare ka ba, ammincinka bai ishe ka bege ba? 7 In ka yarda yi tunanin game da wannan: Wanda ba shi da laifi ya taɓa lalacewa? Ko a ina aka taɓa datse masu adalci? 8 Bisa ga abin da na gani, waɗanda suka huɗa mugunta suka shuka masifa su ke girbin ta. 9 Sukan lalace ta wurin numfashi Yahweh; zafin fushinsa ya kan cinye su. 10 Rurin zaki, muryar zaki mai ban tsoro, haƙoran 'yan zakuna --sukan karye. 11 Tsohon zaki yakan lalace idan ba abin da zai kama; 'ya'yan zakanya sukan warwatsu ko'ina. 12 An kawo mani wata matsala a asirce, kunnena ya karɓi raɗa game da ita. 13 Sa'annan tunanin ruya ya zo mani cikin dare, sa'adda barci mai nauyi ya zo kan mutane. 14 A cikin dare tsoro da fargaba suka zo mani, dukkan ƙasusuwana suka motsa. 15 Sai wani ruhu ya wuce a gaban fuskata, gashin jikina ya tashi tsaye. 16 Ruhun ya tsaya cik, amma ban iya gane baiyanuwarsa ba. Wani abu ya rufe idanuna; an yi shiru, sai na ji wata murya tace, 17 "Mutum mai mutuwa ya iya fin Allah adalci? Mutum zai iya fin mahallicinsa tsarki? 18 Ka gani, idan Yahweh bai amince da bayinsa ba; idan ya zargi mala'ikunsa da wawanci, 19 yaya ga waɗanda ke zama a cikin gidaje na yumɓu, waɗanda tushensu yana cikin ƙasa, waɗanda a kan mutsuke su nan da nan fiye da ƙwaro. 20 Tsakanin safiya zuwa yamma an hallaka su; sun lalace har abada ba abin da zai sa a tuna da su. 21 Ba a kan tsinke iggiyar ransu a jikinsu ba? Su mutu; su mutu ba tare da hikima ba.

Sura 5

1 Ka yi kira yanzu; akwai wani mai ansa maka? Ga wanne cikin masu tsarkin zaka juya? 2 Gama fushi ya kan kashe wawan mutum; kishi yakan kashe dolo. 3 Na ga wawan mutum yana kahuwa, amma nan take na la'anci gidansa. 4 Zaman lafiya yana nesa da 'ya'yansa; an murƙushe su a ƙofar birni. Ba wanda zai kuɓutar da su. 5 Mayunwaci ya kan cinye anfaninsa dukka; sukan ma ɗauko shi daga cikin ƙayayuwa. Masu jin ƙishi suna hãki domin dukiyarsu. 6 Gama wahala bata fitowa daga cikin turɓaya; masifa kuma bata fitowa daga cikin ƙasa. 7 Maimakon haka an haifi mutum saboda masifa, kamar yadda tartsatsi yakan tashi sama. 8 Amma a gare ni, zan juya wajen Allah shi da kansa; a gare shi zan danƙa al'amurana-- 9 shi wanda ke yin manyan al'amuran da ba a iya ganewa, abubuwan mamakin da basu lissaftuwa. 10 Yakan bada ruwa a kan ƙasa, yakan aika da ruwa bisa filaye. 11 Yakan yi haka ne domin ya tada ƙasƙantattu; yasa masu baƙin ciki su zauna lafiya. 12 Yakan lalata shirye--shiryen masu yaudara, domin kada su kai ga cika manufarsu. 13 Yakan kama mutane masu wayo cikin aikin yaudararsu; da sauri shirye--shiryen masu murɗiya sukan zo ƙarshe. 14 Dare kan same su da rana, sukan yi lalube da rana sai kace dare ne. 15 Amma ya kan ceci mutum matalauci da takobi cikin bakinsu mabukata kuma daga hannun ƙarfafan mutane. 16 Domin mutum matalauci ya sami bege, rashin adalci kuma ya rufe bakinsa. 17 Duba, mai albarka ne mutumin da Allah yakan hore shi; saboda haka kada ka rena horon Mai Iko Dukka. 18 Gama yakan sa a ji ciwo yayi magani, ya kan sa a ji rauni hannunsa kuma ya warkar. 19 Zai kuɓutar da kai daga masifu shida; hakika, a cikin masifu bakwai, babu muguntar da zata taɓa ka. 20 A cikin yunwa zai fanshe ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma daga hannun takobi. 21 Za a ɓoye ka daga la'anar harshe; ba zaka ji tsoron hallaka ba ko ta zo. 22 Zaka yi dariya a kan hallakar yunwa, ba zaka ji tsoron namun jeji na duniya ba. 23 Gama zaka yi alƙawari da duwatsu a gonarka, namun jeji na gona zasu yi zaman lafiya da kai. 24 Zaka sani rumfarka tana lafiya; zaka ziyarci garken tumakinka ba kuwa zaka rasa kome ba. 25 Zaka kuma sani irinka zai yi girma, tsatsonka zasu zama kamar ciyawa a kan ƙasa. 26 Zaka je kabari da tsufanka, kamar zangarkun damin hatsi da suke tafiya a lokacinsa. 27 Ka gani, mun yi binciken wannan lamari; ga kamanninsa, ka saurare shi, ka san shi kai da kanka."

Sura 6

1 Sa'an nan Ayuba ya amsa ya ce, 2 "Oh, da dai an auna nauyinbaƙin cikina; da dai an sa wahalata a ma'auni! 3 Gama yanzu za tafi yashin tekuna nauyi. Shi yasa nake magana barkatai. 4 Gama kibawun Mai Iko Dukka suna cikina, ruhuna yana shan dafin; razana daga Yahweh ta shiryo kanta gãba da ni. 5 Jakin jeji yakan yi hargowa inda yana da ciyawa? Sã yakan yi kuka ga abinci a gabansa? 6 Za a iya cin abin da ba shi da ɗanɗano ba tare da an sa masa gishiri ba? Ko akwai ɗanɗano ga farin ƙwai? 7 Na ƙi taɓa su; suna kama da abinci mai gundura a gare ni. 8 Oh, dãmã za a amsa mani roƙona; oh, dãma Yahweh zai yarda in sami abin da nake ta nema in samu: 9 dãma Yahweh zai yarda ya ruƙurƙushe ni kawai, dã zai saki hannunsa ya datse ni daga wannan rayuwa! 10 Bari wannan ya zama abin ƙarfafa ni--ko da ciwona ya ƙaru bai ragu ba: ban yi musun maganar mai tsarki ba. 11 Menene ƙarfina, da zan yi ƙoƙarin jira? mene ne ƙarshena, da zan ci gaba da rayuwa? 12 Ƙarfina kamar ƙarfin dutse yake? Ko an yi jikina da tagulla ne? 13 Ba gaskiya ba ne cewa ba ni da taimako a cikin kaina ba, kuma an kori hikima daga cikina? 14 Mutumin da ya kusa suma, ya kamata abokansa su ji tausayinsa; ko da ya watsar da jin tsoron Mai Iko Dukka. 15 Amma 'yan'uwana sun zama da aminci kamar hamadar da kan ƙafe, kamar magudanar ruwa marar anfani da ke wucewa a magudanai, 16 waɗanda sukan yi duhu saboda ƙanƙara ta rufe su, kuma saboda dusar ƙanƙara da ta ke a cikin su. 17 Idan su ka ji ɗumi sai su, sai su ɓace; idan zafi ya zo, sai su narke a inda suke. 18 Fataken da ke bi ta wurinsu sukan ruƙa neman ruwa; sukan yi garari a busasshiyar ƙasa su lalace. 19 Fatake daga Tema sun duba can, fatake daga Sheba sun sa bege a cikin su. 20 Sun kunyata saboda sun gaskata zasu sami ruwa. Sun je wurin, amma an ruɗe su. 21 Gama yanzu ku abokai baku da anfani a gare ni; kun ga takaicin da nake ciki kun ji tsoro. 22 Nace da ku, 'ku bani wani abu ne?' Ko ku bani wani abu daga dukiyarku?' 23 Ko ku cece ni daga hannun maƙiyina?' Ko ku fanshe ni daga hannun mai tsananta mani?' 24 Ku koya mani, ni kuwa zan yi shiru; ku ganar da ni inda ban yi dai-dai ba. 25 Gaskiya dai ɗaci gare ta! A ina gardandaminku suka ga laifina? 26 Kun yi shirin ku watsar da maganata, ku ɗauki maganar mutumin da yake cikin wahala kamar iska? 27 Tabbas, kun jefa ƙuri'a a kan ɗan da bashi da uba, kun mai da aboki abin samun riba. 28 To, yanzu, idan kun yarda ku dube ni, gama tabbas ba zan yi ƙarya a gaban kuba ba. 29 Ku dena magana haka, na roƙe ku; kada kuyi rashin gaskiya; hakika ne, ku dena yin haka, hakika ina da gaskiya a al'amarina. 30 Akwai mugunta a kan harshena ne? Bakina ba zai iya ganewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?

Sura 7

1 Ba wani mutum da ya taɓa yin aiki mai wuya ne a duniya? 2 Ashe kwanakinsa ba kamar na ɗan ƙwadago suke ba? Kamar bawan da ya ƙosa yamma ta yi, kamar ɗan ƙwadago mai neman haƙƙoƙinsa - 3 don haka an sa ni in jure da watannin wahala; An ba ni kwanaki cike da wahala. 4 Sa'ad da na kwanta, sai in ce da kaina, 'Yaushe zan tashi kuma yaushe gari zai waye? Ina ta juye-juye har sai gari ya waye. 5 Jikina yana cike da tsutsotsi da sanyin ƙasa; gyambunan jikina sukan bushe sai kuma su fashe su zama sababbi. 6 Kwanakina sun fi kibiya sauri; sukan wuce ba bege. 7 Allah ya tuna raina numfashi ne kawai; idona ba zai ƙara ganin alheri ba. 8 Idon Yahweh, da ke gani na, ba zai ƙara gani na ba; idanun Yahweh za su dube ni, amma ba zan kasance ba. 9 Kamar yadda girgije yakan ɓace, haka wanda ya je Lahira ba zai ƙara fitowa ba. 10 Ba zai ƙara dawowa gidansa ba.; wurinsa ba zai ƙara sanin sa ba. 11 Saboda haka ba zan kama bakina ba; zan yi magana cikin zafin rai a ruhuna; zan yi gunaguni cikin ɗacin raina. 12 Ni teku ce ko ni dorina ce da kuke tsaro na? 13 Idan nace, 'gadona zai yi mani ta'aziya, shimfiɗata zata sa in ji sauƙi,' 14 sai ka firgita ni da mafarkai ka sa in ji tsoro da wahayoyi, 15 har na kan so a maƙare ni in mutu da a raya ƙasusuwana. 16 Na rena rayuwata; bana marmarin in rayu koyaushe; ku ƙyale ni gama kwanakina basu da anfani. 17 Mene ne mutum har da zaka lura da shi, da zaka sa hankalinka a kan sa, 18 da zaka lura da shi kowacce safiya ka gwada shi kowanne lokaci? 19 Sai yaushe zaka dena dube na, kafin ka bar ni ni kaɗai in samu in haɗiyi yawuna? 20 Ko dana yi zunubi, me zaka yi da ni, kai da kake tsaron mutane? Me yasa ka sã mani ido, har da zan zama matsala a gare ka? 21 Me yasa ba zaka yafe laifofina ka ɗauke muguntata ba? Gama yanzu zan kwanta a cikin turɓaya; zaka neme ni a hankali, amma ba zan kasance ba."

Sura 8

1 Sa'an nan Bildad Bashune ya amsa ya ce, 2 "Har yaushe zaka yi ta faɗin waɗannan abubuwa? Har yaushe maganar bakinka zata zama iska mai ƙarfi? 3 Ko Allah yana ɓata shari'a ne? Ko Mai Iko Dukka yana ɓata adalci ne? 4 'Ya'yanka sun yi masa zunubi; mun san wannan, gama ya bashe su a hannun zunubansu. 5 Dama ace ka jure da neman Allah da miƙa roƙonka ga Mai iko dukka. 6 Idan da kana da tsarki da aminci, to da babu shakka da ya tashi da kansa a madadin ka ya dawo da kai inda ya kamace ka. 7 Ko da yake ka farkonka kaɗan ne, har yanzu matsayin ƙarshenka ya fishi girma ƙwarai. 8 Idan ka yarda ka tambayi mutanen dã, ka mai da hankali a kan abin da ubanninmu suka koya. 9 (Jiya a ka haife mu kuma bamu san kome ba saboda kwanankinmu a duniya inuwa ne). 10 Baza su gaya maka ko su koya maka ba? Baza su yi magana daga zuciyarsu ba? 11 Tsire-tsire kan iya yin girma inda ba laima? Iwa ta iya yin girma ba tare da ruwa ba? 12 Tun suna da korensu ba tare da an sare su ba, zasu riga kowacce shuka bushewa. 13 Haka kuma hanyoyin dukkan wanda ya mance da Allah; begen wanda bashi da halin kirki zai lalace. 14 Gabagaɗinsa zai lalace, bangaskiyarsa bata da ƙarfi kamar yanar gizo take. 15 Ya dogara ga gidansa, amma ba zai tallafe shi ba; ya riƙe shi, amma bai tsaya ba. 16 A ƙarƙashin rana kore ne shi, rassansa sukan rufe lambunsa dukka. 17 Tarin duwatsu sun rufe sauyoyinsa, sukan nemi wurare masu kyau cikin duwatsu. 18 Amma idan aka hallaka wannan mutum daga wurinsa, sa'an nan wannan wurin zai yi musun sa yace, 'Ban taɓa ganin ka ba.' 19 Duba, wannan ne "farinciki" na mutum mai irin wannan hali; waɗansu shuke--shuken zasu fito a wannan ƙasar a wurinsa. 20 Duba, Allah ba ya jefar da mutum marar laifi; kuma ba ya kama hannuwan masu aikin mugunta. 21 Zaya sake cika bakinka da dariya, leɓunanka kuma da sowa. 22 Kunya zata rufe maƙiyanka; rumfar masu mugunta zata lalace har abada."

Sura 9

1 Sa'an nan Ayuba ya amsa yace, 2 "Gaskiya ne haka yake na sani. Amma yaya mutum zai iya zama dai-dai wurin Allah? 3 Idan yana so yayi gardama da Allah, a cikin dubu ba zai iya amsawa ko sau ɗaya ba. 4 Allah mai hikima ne kuma mai ƙarfi ne; wane ne ya taɓa yin jayayya da shi yaci nasara 5 shi wanda yake cire duwatsu ba tare da gargaɗi ba yakan birkice kowannen su a cikin fushinsa-- 6 shi wanda yake girgiza duniya daga wurinta yasa ginshiƙanta su raurawa. 7 Shi ne Allahn nan wanda yakan ce da rana kada ta fito, kuma ba ta fito ba, shi wanda ya kan lulluɓe taurari, 8 shi wanda yakan miƙar da sammai da kansa ya tattaka raƙuman ruwan teku, 9 shi wanda ƙungiyoyin taurari da zara da gamzaki da mafarauci da kare da zomo da kuma kaza da 'yayanta, gungun taurarin kudu. 10 Shi wanda ke yin manyan abubuwan da ba za a iya bincika su ba, da abubuwan mamaki da basu lissaftuwa. 11 Duba, yana tare da ni kuma bana ganin sa, kuma yakan wuce, amma bana ganin sa. 12 Idan ya ɗauke wani abu, wa zai iya hana shi? Wane ne zai iya cewa da shi, 'Me kake yi?' 13 Allah ba zai janye fushinsa ba; masu taimakon Rahab suna sunkuya wa a ƙarƙashinsa. 14 Yaya zan iya amsa masa, zan iya zaɓar kalmomin da zan iya yin nazari tare da shi? 15 Ko da ace ni mai adalci ne, ba zan iya amsa masa ba; sai dai in roƙi jinƙai kaɗai daga mai yi mani hukunci. 16 Ko dana yi kira ya amsa mani, ba zan gaskata cewa yana sauraren muryata ba. 17 Gama ya karairaya ni da iska mai ƙarfi ya ruɓanɓanya ciwukana ba dalili. 18 Ya hana ni in ja numfashi kuma; ya cika ni da baƙinciki. 19 Idan maganar ƙarfi ce, duba, shi mai iko ne! Idan maganar shari'a ce, wa zai iya sashi ya zo? 20 Ko da ina da gaskiya, bakina zai kãshe ni; koda ba ni da abin zargi, maganata zata nuna ni mai laifi ne. 21 Bani da abin zargi, amma ban damu da kaina ba ko kaɗan; na rena raina. 22 Bai bambanta da komai ba da nace yakan hallaka marar abin zargi tare da mai mugunta. 23 Idan bulala tayi kisa nan da nan, sai ya yi wa al'amuran marar laifi ba'a. 24 An bayar da duniya a hannun masu mugunta; Yahweh ya rufe fuskokin alƙalanta. Idan bashi ba ne, to, wane ne? 25 Kwanakina sun fi ɗan aike mai gudu sauri; kwanakina suna wucewa; basu ganin alheri a ko'ina. 26 Suna da sauri kamar jiragen ruwan iwa, yana sauri kamar gaggafar da ta kawo bãra a kan nama. 27 Idan nace zan mance da koke--kokena, zan dena baƙinciki in yi murna, 28 sai in ji tsoron dukkan wahalhaluna saboda na sani kai ba zaka dube ni a matsayin marar laifi ba. 29 Tun da za a kashe ni, me kenan, zan yi ƙoƙari a wofi? 30 Idan na yi wanka da ruwan ƙanƙara nasa hannuwana suka yi tsafta sosai, 31 Allah zai tura ni a kwari mai taɓo, tufafina zasu zama abin ƙyama tare da ni. 32 Gama Allah ba mutum ba ne, kamar yadda nake, balle in ba shi amsa, har da zamu zo kotu tare da shi. 33 Ba wani alƙali a tsakanin mu wanda zai sa mana hannu mu dukka biyu. 34 Ba wani alƙalin da zai iya ɗauke sandan Allah daga kaina, wanda ya hana tsoronsa ya firgitar da ni. 35 Sa'an nan ba zan yi magana in ji tsoronsa ba. Amma ga yadda abubuwa suke yanzu, ba zan iya yin haka ba.

Sura 10

1 Na gaji da raina; zan yi maganar matsalata a fili; zan yi magana cikin ɗacin raina. 2 Zan ce da Allah, 'Kada ka kashe ni haka kawai; ka nuna mani abin da kake zargi na a kai. 3 Ya yi maka kyau ka wahalshe ni, ka rena aikin hannuwanka sa'ad da kake yin murmushi da shirye--shiryen masu mugunta. 4 Ko kana da idanu na jiki ne? Kokana gani kamar mutum ne? 5 Ko kwanakinka kamar na ɗan'adam ne ko shekarunka kamar na mutane ne, 6 da kake yin bincike a kan muguntata kana neman zunubina, 7 duk da ka san bani da laifi kuma ba wanda zai iya kuɓutar da ni daga hannunka? 8 Hannuwanka ne suka sifanta ni suka tsara kome nawa, amma kana hallaka ni. 9 Ina roƙon ka, ka tuna kai ne ka siffanta ni kamar yumɓu; zaka maishe ni cikin turɓaya ne kuma? 10 Baka zubar da ni kamar madara ka cakuɗe ni kamar abin taunawa ba? 11 Ka lulluɓe ni da fata da nama ka ɗinke ni da ƙasusuwa da guringuntsi. 12 Ka bani rai da jiyejiyenƙai; taimakonka ya tsare ruhuna. 13 Duk da haka ka ɓoye waɗannan abubuwaa zuciyarka--na san waɗannan abubuwan ne da kake tunaninsu: 14 idan na yi zunubi zaka kula da shi; ba zaka baratar da ni daga muguntata ba. 15 Idan na yi aikin mugunta, kaito na; ko da nayi aikin adalci, ba zan yi fahariya ba, da yake ina cike da kunya ka dubi wahalata! 16 Idan na ɗaukaka kaina zaka bi ni kamar zaki; kuma zaka nuna kanka da ayyukan na ban mamaki na iko a kaina. 17 Ka kawo mani sababbin shaidu ka ƙara fushinka a kaina; ka kawo mani hari da sababbin sojoji. 18 To, me yasa ka fito da ni daga cikin ciki? Dama na saki ruhuna ba idon da ya gan ni. 19 Dãma na zama kamar ban taɓa kasancewa ba; dama an ɗauke ni daga cikin ciki zuwa kabari. 20 Kwanakina ba 'yan kaɗan ba ne? Tsaya haka, ka rabu da ni, domin in ɗan sami hutu 21 kamin in kai inda ba zan iya dawowa ba, zuwa ƙasar duhu da inuwar mutuwa, 22 ƙasa mai duhu kamar tsakiyar dare, ƙasa ta inuwar mutuwa, babu wata ka'ida, inda haske kamar tsakar dare yake.'"

Sura 11

1 Sa'an nan Zofar Banamate ya amsa ya ce, 2 "Ba za a bada amsa a kan waɗanan maganganun masu yawa ba? A gaskata da wannan mutumin, mai yawan magana? 3 Fankamarka zata sa sauran mutane suyi shuru ne? Sa'ad da kayi ba'a, ba wanda zai sa ka ji kunya ne? 4 Gama kace da Allah, 'Bangaskiyata sahihiya ce, bani da laifi a idanunka.' 5 Amma, da Allah zai yi magana ya buɗe bakinsa gãba da kai; 6 da zai nuna maka asirin hikima! Gama shi yana da fahimta mai girma. Ka sani ba kamar yadda muguntarka take Allah yake nema ba. 7 Zaka iya ganewa da Allah ta wurin binciken sa? Zaka iya fahimtar Yahweh sarai? 8 Matsalar tayi tsawo kamar samaniya ne; me zaka iya yi? Ta fi Lahira zurfi; me zaka iya sani? 9 Ta fi duniya tsawo, kuma ta fi teku faɗi. 10 Idan ya wuce ya kulle wani, ko idan ya hukunta wani, wane ne zai iya hana shi? 11 Gama ya san maƙaryata; idan ya ga mugunta, baya lura da ita ne? 12 Amma wawayen mutane basu ganewa; zasu same ta sa'ad da jakin jeji ya haifi ɗan mutum. 13 Amma da ka tsayar da zuciyarka sosai ka miƙa hannuwanka zuwa ga Yahweh; 14 da akwai mugunta a hannunka, amma daka kasa ta nesa da kai, da baka bari rashin adalci ya zauna a rumfarka ba. 15 Da ka tada fuskarka ba tare da kunya ba; lallai da ka tsaya da ƙarfi ba tare da tsoro ba. 16 Da ka manta da damuwarka; sai dai ka tuna da ita kamar wucewar ruwa. 17 Da ranka yayi haske fiye da rana; ko da akwai duhu da ya zama kamar safiya. 18 Da zaka natsu saboda akwai bege; lallai da ka sami tsaro kewaye da kai da ka huta a tsanake. Kuma da ka kwanta ka huta, 19 Kuma ba wanda zai tsoratar da kai; lallai da mutane da yawa sun nemi tagomashi a wurin ka. 20 Amma idanun masu mugunta zasu kasa; ba zasu sami wurin ɓuya ba; begensu numfashin ƙarshe ne kaɗai"

Sura 12

1 Sa'an nan Ayuba ya amsa ya ce, 2 "Ba shakka ku ne mutanen; hikima za ta mutu tare da ku. 3 Amma ni ma ina da fahimta kamar yadda kuma kuke da shi; ni ban gaza ku ba. Hakika, waye bai san irin abubuwa kamar waɗannan ba? 4 Ni wani abu ne da makwabcina zai yiwa dariya - Ni, da nake kira bisa sunan Allah wanda ya kuma amsa mani! Ni, mutum mai adalci marar aibu kuma - yanzu na zama wani abin dariya. 5 A tunanin wani wanda yake zaune lafiya, akwai reni game da masifa; yakan yi tunani irin na ƙara kawo masifa kan waɗanda ƙafafunsu ke zarmewa. 6 Rumfunan mafasa na azurta, waɗanda kuma ke cakunar Allah suna nan lafiya; hannunwansu ne allolinsu. 7 Amma yanzu ka tambayi dabbobi, kuma zasu koya maka; ka tambayi tsuntsayen sammai, zasu kuma gaya maka. 8 Ko kuma kayi wa ƙasa magana, zata kuma koya maka; kifayen teku zasu shaida maka. 9 Wace dabba ce cikin dukkan waɗannan da bata sani cewa hannun Yahweh ne yayi wannan ba? 10 A cikin hannunsa ran kowanne rayayyen abu yake da kuma numfashin dukkan 'yan adam. 11 Ashe kunne ba yakan gwada dukkan maganganu kamar yadda baki ke ɗanɗana abinci ba? 12 Hikima tana ga tsoffin mutane; a tsawon kwanaki kuma akwai fahimta. 13 Hikima da iko suna ga Allah; shi ke da shawara da fahimta. 14 Duba, yakan rushe, ba za a kuma iya ginawa ba, idan ya kulle mutum, ba sauran kuɓutarwa. 15 Duba, idan ya janye ruwaye, sai su bushe ƙurmus; kuma idan ya aika da su, sai su malale ƙasa. 16 A gunsa ƙarfi da hikima suke; mutanen da aka ruɗe su da mai ruɗin dukkansu biyu suna cikin ikonsa. 17 Yakan ɓad da mashawarta zuwa baƙinciki, ya mai da alƙalai wawaye. 18 Yakan tuɓe rawanin iko daga sarakuna; ya ɗaura ɗan ƙyalle a kwankwasonsu. 19 Yakan ɓad da firistoci su tafi ƙafa ba takalmi cikin baƙinciki ya kuma kaɓantar da manyan mutane. 20 Yakan ɗauke iya maganar mutanen da aka dogara gare su ya kuma ɗauke fahimtar dattawa. 21 Yakan zuba reni a kan hakimai ya kuma kwaɓe ɗamarar mutane masu ƙarfi. 22 Yakan bayyana zurfafan abubuwan duhu ya kuma kawo baƙin duhu cikin haske. 23 Yakan sa al'ummai suyi ƙarfi, yakan kuma hallakasu; yakan faɗaɗa al'ummai, ya kuma bi da su kamar 'yan kurkuku. 24 Yakan ɗauke fahimta daga shugabanin mutanen duniya; yasa su suyi ta yawo a jeji inda ba tafarki. 25 Suyi lalube cikin duhu babu haske; yakan sa suyi tangaɗi kamar bugaggen mutum.

Sura 13

1 Duba, idona ya ga duk wannan; kunnena yaji ya kuma fahimce shi. 2 Abin da kuka sani, ni ma ina sane da shi; ni ban gaza ku ba. 3 Duk da haka, na gwammace in yi magana da Mai Iko Dukka; ina so in tattauna da Allah. 4 Amma ku kuna lulluɓe gaskiya da ƙarereyi; ku dukka likitoci ne marasa amfani. 5 Kash, dama zaku yi shuru! Wannan zai zama maku hikima. 6 Ku saurari nawa hujjojin; ku kasa kunne ga ƙarar tawa leɓunan. 7 Za ku yi magana marar adalci domin Allah, zaku kuma yi maganar munafunci dominsa? 8 Zaku nuna masa bambanci? Zaku yi jayayya domin Allah? 9 Zai zama da kyau domin ku sa'ad da ya bincike ku? Zaku iya ruɗinsa kamar yadda zaku ruɗi mutane? 10 Hakika zai kwaɓe ku idan a ɓoye kuka nuna bambanci. 11 Darajarsa ba zata firgita ku ba, tsoronsa kuma ya faɗo a kanku? 12 Batutuwanku masu daɗin ji misalai ne da aka yi su da toka; hanzarinku hanzari ne da aka yi su da yumɓu. 13 Ku riƙe salamarku, ku kyale ni kawai, domin in yi magana, bari abin da zai auko kaina ya auko. 14 Zan sa namana a bakina; in ɗauki raina a hannuwana. 15 Bari mu gani, ko zai kashe ni, zan zama ba sauran bege; duk da haka, zan kare hanyoyina a gabansa. 16 Wannan zai zama dalilin cetona, gama ba wani mugun mutum da zai zo gabansa. 17 Allah, ka kasa kunne ga furcina; bari furcina ya zo kunnuwanka. 18 Duba yanzu, na shirya hanzarina sosai; na sani ba ni da aibu. 19 Wane ne wannan da zai yi jayayya gãba da ni a gaban sharia? Idan kun zo ne don ku yi, idan kun tabbatar da laifina, sai in yi shuru in saki raina. 20 Allah, kayi mani abu biyu kawai, sa'an nan bazan boye kaina daga fuskarka ba: 21 ka janye hannunka mai azaba daga gare ni, kuma kada ka bari razanarka ta tsorata ni. 22 Sa'an nan ka kira ni, zan kuma amsa; ko kuma ka bari in yi magana da kai, kai ka amsa mani. 23 Laifofina da zunubaina nawa ne? Bari in san kuskurena da zunubina. 24 Don me kake boye fuskarka daga gare ni ka maishe ni kamar maƙiyinka? 25 Zaka tsanantawa ganyen da iska ke kora? Zaka far wa tattaka? 26 Domin ka rubuta abubuwa masu ɗaci gãba da ni; kasa in gãji laifofin ƙuruciyata. 27 Ka kuma sa ƙafafuna a turu; kana duba dukkan tafarkuna kurkusa; kana bincike inda sawayen ƙafafuna suka taka, 28 ko da yake ni kamar ruɓaɓɓen abu ne da yake lalacewa, kamar rigar da asu suka cinye.

Sura 14

1 Mutum, da mace ta haifa, ya kan rayu 'yan kwanaki kaɗan yana kuma cike da damuwa. 2 Ya kan tsiro daga ƙasa kamar fure sai kuma a datse shi; ya tsere kamar inuwa baya daɗewa. 3 Kana duba kowanne su? Kana gabatar da ni a gaban shari'a tare da kai? 4 Wane ne zai iya fitar da abu mai tsabta daga cikin marar tsabta? Babu ko ɗaya. 5 Kwanakin mutum a ƙayyade suke. Yawan watanninsa na tare da kai; ka ƙayyade masa iyaka da ba zai iya wucewa ba. 6 Ka ɗauke idonka daga gare shi domin ya huta, domin ya ji daɗin kwanansa kamar ɗan ƙwadago in ya iya. 7 Mai yiwuwa ne itace na da bege; idan an sare shi, zai iya toho kuma, 'yan sabbin rassansa ba sa ɓata. 8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa a ƙasa, kututturensa kuma ya mutu a ƙasa, 9 amma da zarar ya ji ƙanshin ruwa, sai yayi toho ya kuma fid da rassa kamar tsiro. 10 Amma mutum yakan mutu; ya zama da rauni; hakika, mutum yakan bar yin numfashi, sa'an nan fa ina yake? 11 Kamar yadda ruwa ke ɓacewa a tafki, da yadda rafi ke rasa ruwa ya ƙone, 12 haka mutane ke kwantawa basa sake tashi. Sai ko in sammai sun ɓace, ba zasu farka ba ko kuma a tashe su daga barcinsu. 13 Kash, dama zaka ɓoye ni can Lahira nesa da wahalhalu, ka kuma a ajiye ni a ɓoye har sai fushinka ya wuce, sai kasa mani lokaci da zan kasance a can sa'an nan ka tuna da ni! 14 Idan mutum ya mutu, zai sake rayyuwa kuma? Idan haka ne, zan so in jira dukkan lokacin gajiyata a can har sai 'yantarwata ta zo. 15 Zaka kira, zan kuwa amsa maka. Zaka zama da marmarin aikin hannuwanka. 16 Zaka ƙididdige ka kuma lura da takawata; baza ka bi diddigin zunubina ba. 17 Za a ɗaure kurakuraina a jaka; zaka rufe laifofina. 18 Amma har tsaunuka ma sukan faɗi su zama ba komai ba, harma duwatsu akan kawar da su daga wurinsu; 19 ruwaye sukan zaizaye duwatsu; ambaliyarsu na kwashe ƙurar ƙasa. Haka nan ne, kake hallakar da begen mutum. 20 Kullum kana cin nasara a kansa, sai ya rasu; ka kan sauya fuskarsa ka aike shi ya mutu. 21 Idan an girmama 'ya'yansa maza, ba zai sani ba; ko kuma an wulaƙanta su, ba zai gani ba. 22 Yakan ji ciwon jikinsa ne kawai, yana kuma makokin domin kansa.

Sura 15

1 Sa'an nan Elifaz Batemane ya amsa ya ce, 2 "Ya kamata mutum mai hikima ya amsa da ilimin banza kuma cika kansa da iskar gabas? 3 Koya kamata ya kawo hujja da magana marar amfani ko kuma furce furce waɗanda baza su amfana ba? 4 Hakika, kana rushe bangirma ga Allah; kana hana sujada gare shi, 5 gama ƙuraƙuranka suna koya wa bakinka; ka zaɓa ka zama da harshen mutum mai wayo. 6 Bakinka da kansa ya kashe ka, ba nawa ba; hakika, leɓunanka suna shaida gãba da kai. 7 Kai ne mutum na fari da aka haifa? An kawo ka cikin rayyuwa kafin tuddai ne? 8 Ko ka taɓa jin asirin ilimin Allah? Ka ɗauka kai kaɗai ke da hikima? 9 Me ka sani da bamu sani ba? Me ka fahimta da baya cikinmu muma? 10 Tare da mu akwai masu furfura da tsoffi maza waɗanda suka girmi mahaifinka ainun. 11 Ta'aziyun Allah sun yi maka kaɗan ne, maganganu masu taushi zuwa gare ka? 12 Don me zuciyarka take yaudarar ka? Me yasa ka ke ruwan idanu, 13 har ka mai da ruhunka gãba da Allah kana fitar da maganganu irin waɗannan daga bakinka? 14 Wane ne mutum da zai zama da tsarki? Waye shi wanda mace ce ta haife shi da zai zama da tsarki? 15 Duba, Allah ba ya amincewa da tsarkakansa; hakika, sammai basu da tsarki a idanunsa; 16 ballantana wanda ya gaza a tsarki ƙazantacce lalatacce kuma, mutum wanda yake shan laifi kamar ruwa! 17 Zan nuna maka; ka kasa kunne gare ni; zan yi maka shelar abubuwan da na gani, 18 abubuwan da masu hikima suka gãda daga ubanninsu, abubuwan da kakannisu basu ̀ɓoye ba. 19 Waɗannan su ne kakanninsu, waɗanda su kaɗai aka ba ƙasar, wanda ba wani baƙo da ya taɓa ratsawa. 20 Mugun mutum yana murmurɗewa don zafin ciwo dukkan kwanakinsa, shekarun da aka aza wa a‌zalumi yasha azaba.‌ 21 Ƙarar firgitarwa na cikin kunnuwansa; sa'ad da yake cikin wadata, mai hallakarwa zai auka masa. 22 Baya tunani cewa zai komo daga cikin duhu; takobi na jiransa. 23 Sai ya tafi wurare da bam da ban domin abinci, yana cewa, 'Ina yake?' Ya sani ranar duhu ta gabato. 24 ‌Ƙunci da raɗaɗi sukan tsoratar da shi; su ci nasara a kansa, kamar sarkin da ya shirya domin yaƙi. 25 Domin ya miƙa hannunsa gãba da Allah, ya kuma nuna girman kai gãba da Mai Iko Dukka, 26 wannan mugun mutum yana gudu zuwa ga Allah da taurararriyar zuciya, da garkuwa kakkaura. 27 Wannan gaskiya ne, ko da yake ya rufe fuskarsa da kitsensa ya kuma tara kitse a kwiɓinsa, 28 ya kuma zauna a rusassun birane; a gidajen da ba mazauna yanzu kuma suna shirye su zama tsibi. 29 Ba zai yi arzaki ba; arzaƙinsa ba zai daɗe ba kuma mallakarsa baza ta yaɗu a ƙasar ba. 30 Ba zai fita daga duhu ba; harshen wuta zai ƙona karmaminsa; numfashi daga bakin Allah zai kora shi ya tafi.. 31 Kada ya dogara ga abubuwa marasa amfani, yana ruɗin kansa; gama abubuwa marasa amfani zasu zama ladansa. 32 Zai faru kafin lokacin mutuwarsa yazo; reshensa ba zai zama kore ba. 33 Zai kakkaɓe ɗanyun inabinsa kamar kuringar inabi; zai zubar da furanninta kamar itacen zaitun. 34 Gama tawagar marasa tsoron Allah ba zasu zama da zuriya ba; wuta zata cinye rumfar masu cin hanci. 35 Sukan ɗauki cikin ƙeta su haifi zunubi; mahaifarsu na ɗaukar cikin rikirkicewa.

Sura 16

1 Sa'an nan Ayuba ya amsa yace, 2 "Na sha jin abubuwa da yawa kamar haka; ku dukka masu ta'aziyar ma abin ban tausai ne. 3 Maganganu marasa amfani basu da ƙarshe ne? Me ya dame ku da kuke amsawa haka? 4 Nima zan iya magana kamar yadda kuke yi, in da kuna gurbina; zan iya tattara maganganu in haɗa su tare gãba da ku kuma in girgiza kaina a gabanku don reni. 5 Zan ƙarfafa ku da bakina, ƙaɗawar leɓunana zasu kawo maku sauƙi. 6 Idan na yi magana wannan ba zai sauƙaƙe baƙincikina ba; idan na yi shiru, ƙaƙa wannan zai taimake ni? 7 Amma yanzu, Allah, ka sani na gaji; ka mai da dukkan iyali na wofi. 8 Ka sa na ƙeƙashe, wannan ma shaida ce gãba da ni; ƙeƙashewar jikina ya tashi gãba da ni, yana kuma shaida gãba da ni a fuskata. 9 Allah ya kekketa ni cikin hasalarsa ya kuma tsananta mani; Yana tauna haƙoransa cikin zafin fushi; magabcina ya kafa idanunsa a kaina sa'ad da ya kekketa ni. 10 Mutane sun buɗe bakinsu suna mani gwalo; sun buge ni ba dalili a kunci; sun taru gaba ɗaya gãba da ni. 11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefar da ni cikin hannun mugayen mutane. 12 Ina zaune lau, sai ya kakkarya ni. Hakika, ya kama ni a wuya ya jefar ya jefar da ni gutsu-gutsu; ya kuma tsai da ni daf a gabansa. 13 Maharbansa dukka sun kewaye ni; Allah ya sossoke ka'idojina bai yi mani rangwame ba; ya zubar da matsarmamata a ƙasa. 14 Yana bubbuga bangona akai akai; yana gudu a kaina kamar mayaƙi. 15 Na ɗaura tsumma a fatata; na soka ƙaho na cikin ƙasa. 16 Fuskata tayi jawur da kuka; a kan girata akwai inuwar mutuwa 17 ko da yake ba ta'addanci a hannuwana, addu'ata mai tsarki ce. 18 ‌Ƙasa, kada ki rufe jinina; kada kukana ya sami wurin hutawa. 19 Ko yanzu ma, duba, shaidata tana cikin sama; wanda yake lamuni domina yana sama. 20 Abokaina suna yi mani ba'a, amma idona yana zubar da hawaye ga Allah. 21 Ina roƙo domin wannan mashaidi a cikin sama yayi muhauwara da Allah kamar yadda mutum zai yi da makwabcinsa! 22 Domin bayan 'yan shekaru sun wuce, zan tafi wurin da bazan komowa daga can ba.

Sura 17

1 An cinye ruhuna, kwanakina sun ƙare; kabari na shirye domina. 2 Lallai da akwai masu ba' a tare da ni; idona dole kullum ya ga cakunar su. 3 Ka bani shaida, kayi mani lamuni da kanka; wane ne kuma ke nan da zai taimake ni? 4 Domin kai, Allah, ka hana wa zuciyarsu fahimta; saboda haka, ba zaka ɗaukaka su a bisa na ba. 5 Wanda yaci amanar abokansa domin ya sami lada, idanun 'ya'yansa zasu dushe. 6 Amma ya maishe ni abin karin magana ga mutane; suna tofa mani miyau a fuska. 7 Idona ya sace saboda baƙin ciki; dukkan gaɓaɓuwan jikina sun ƙanjame kamar inuwa. 8 Mutane masu adalci zasu yi mamaki da wannan; mutum marar aibu zai husata kansa gãba da mugayen mutane. 9 Mutum mai adalci zai kiyaye hanyarsa; wanda ya ke da hannuwa mararsa laifi zai yi ta ƙaruwa da ƙarfi. 10 Amma game da dukkanku, kuzo yanzu; ba zan sami wani mai hikima a cikinku ba. 11 Shekaruna sun wuce; shirye shiryena sun watse, haka kuma marmarin zuciyata. 12 Waɗannan mutane, waɗannan masu reni, suna sauya dare zuwa rana; haske ya fi kusa da duhu. 13 Idan gidan da nake bege Lahira ne kaɗai; idan na baza shimfiɗata cikin duhu; 14 idan kuma na cewa rami, 'Kai ne mahaifina,' da kuma tsutsa, 'Ke ce mahaifiyata ko kuma 'yar'uwata,' 15 to ina begena ya ke? A game da begena, wa ya iya ganin ko da ɗan kaɗan? 16 Bege zai tafi tare da ni zuwa ƙofar Lahira ne sa'ad da zamu gangara cikin turɓaya?

Sura 18

1 Sai Bildad Bashune ya amsa ya ce, 2 "Shin yaushe zaka dena maganarka? Kayi tunani, daga bayan haka zamu yi magana. 3 Don me za a ɗauke mu dabbobi, marasa wayo a ganinka? 4 Kai da ka ke yayyage kanka a cikin fushinka, ya kamata a kawar da duniya domin ka ko kuma ya kamata a tumbuƙe duwatsu daga wurarensu? 5 Hakika, za a ɓice hasken mugun mutum; tarwatsun wutarsa ba za ta haskaka ba. 6 Haske zai zama duhu a rumfarsa; fitilar da ke bisansa za a ɓice ta. 7 Takawar ƙarfinsa zata ragu; shirye shiryen kansa zasu kada shi. 8 Gama za a jefa shi cikin raga da ƙafarsa; zai yi tafiya zuwa cikin tarko. 9 Tarko zai kama diddigensa; ashibta zata riƙe shi. 10 An binne masa igiyar zarmewa a ƙasa a ɓoye; tarko ne dominsa akan hanya. 11 Banrazana zai sa shi tsoro a kowanne gefe; zasu fafari digadigansa. 12 Arzikinsa zai juya ya zama yunwa, kuma masifa na shirye a gefensa. 13 Gaɓaɓuwan jikinsa zasu mutu; hakika, ɗan farin mutuwa zai ci gaɓaɓuwansa. 14 Za a fizge shi daga rumfarsa da yake zaune lafiya a kora shi zuwa ga sarkin razanai. 15 Mutanen da ba nasa ba zasu zauna a rumfarsa bayan da suka ga wutar ƙibiritu ta bazu cikin gidansa. 16 Saiwowinsa zasu bushe daga ƙasa; a sama za a daddatse rassansa. 17 Ba sauran tunawa da shi a duniya; ba zai sami suna a titi ba. 18 Za a kora shi daga haske zuwa cikin duhu kuma za a kore shi daga wannan duniya. 19 Ba zai zama da ɗa namiji ko jikoki maza a cikin mutanensa ba, ko ragowar dangi inda dã ya zauna. 20 Waɗanda ke zaune a kudu zasu tsorata da abin da ya faru da shi wata rana; waɗanda ke zaune a gabas zasu firgita da wannan. 21 Tabbas haka gidan marasa adalci yake, wuraren waɗanda basu san Allah ba."

Sura 19

1 Sai Ayuba ya amsa ya ce, 2 "Har yaushe zaku sa ni cikin wahala kuma ku daddatse ni gutsu gutsu da maganganu? 3 Sau goma ɗin nan kun zarge ni; baku ji kunya ba cewa kun wulaƙanta ni ainun. 4 Idan lallai gaskiya ne nayi kuskure, to kuskurena ya zama abin da ni kaina zan yi tunani sa. 5 Idan hakika zaku ɗaukaka kanku fiye da ni ku kuma yi amfani da ƙasƙancina gãba da ni, 6 sai ku sani Allah bai yi mani dai-dai ba ya kuma kama ni cikin ragarsa. 7 Duba, na ƙwala ihu, "Ta'adanci!" amma ban sami amsa ba. Na yi kira domin neman taimako, amma babu adalci. 8 Yasa katanga a hanyata domin kada in iya wucewa, ya kuma sa duhu a tafarkina. 9 Ya tuɓe mani darajata, ya kuma ɗauke kambi daga kaina. 10 Ya kakkarya ni ta kowanne gefe, na kuma ƙare; ya janye begena kamar itace. 11 Ya kuma kunna wutar hasalarsa gãba da ni; ya maishe ni ɗaya daga cikin abokan gabarsa. 12 Rundunarsa sun tashi gaba ɗaya; sun tula tsibin shara gãba da ni kuma sun kewaye rumfata. 13 Ya nisantar da 'yan'uwana maza daga gare ni; sanin idona an ware su gaba ɗaya daga gare ni. 14 Dangina sun yashe ni; aminaina na kurkusa sun manta da ni. 15 Waɗanda dã na saukar baƙi a gidana da barorina mata sun maishe ni kamar baƙo; ni bare ne a idanunnunsu. 16 Na kira barana, amma bai ba ni amsa ba ko da yake na roƙe shi da bakina. 17 Numfashina ya dunguri matata; har ta maishe ni abin watsi ga waɗanda mahaifiyarmu ɗaya. 18 Har ma 'yan yara ƙanana sun rena ni; idan na tashi zan yi magana, sai suyi magana gãba da ni. 19 Dukkan idon sani abokanaina sun kyamace ni; Waɗanda nake ƙauna suna gãba da ni. 20 ‌Ƙasusuwana sun manne wa fatata da kuma naman jikina; ina raye da ƙyar. 21 Ku ji tausayina, ku ji tausayi na, abokaina, gama hannun Allah ya taɓa ni. 22 Me yasa kuke farautata kamar yadda Allah ke yi? Zaku taɓa ƙoshi da naman jikina? 23 Kash, da ma za a rubuta maganganuna! Aiya, dama za a rubuta su a cikin littafi! 24 Kash, dama da alƙalamin ƙarfe da tamã aka sassaƙa rubutun akan dutse har abada! 25 Amma a gare ni, na sani mai fansata yana raye, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya; 26 bayan fatata, watau, wannan jiki, an hallaka shi, sa'an nan a cikin jiki zan ga Allah. 27 Zan gan shi da idanuna-ni, ba kuma wani da bam ba. Zuciyata ta karai a cikina. 28 Idan kun ce, 'Yaya zamu tsananta masa! Tushen matsalarsa tana cikinsa,' 29 sai ku ji tsoron takobi, domin hasala na kawo hukuncin takobi, domin ku sani a kwai shari'a."

Sura 20

1 Sa'an nan Zofar Banamate ya amsa ya ce, 2 "Tunane tunanena suna sa ni in amsa da garaje saboda damuwar da ke cikina. 3 Ina jin zargi da ke kunyatar da ni, amma wani ruhu daga fahimtata yana amsa mani. 4 Baka san wannan abu tun daga zamanan dã ba, da Allah ya ajiye mutum a duniya: 5 cin nasarar mugun mutum na gajeren lokaci ne, kuma murnar marar tsoron Allah daɗewarta kamar ƙiftawar ido ne? 6 Ko da tsayinsa ya kai sammai, kuma kansa ya taɓa gizagizai, 7 duk da haka irin mutumin nan zai lalace tuttur kamar najasarsa; waɗanda suka gan shi zasu ce, 'Ina yake?' 8 Zai yi firiya ya ɓace kamar mafarki ba za a kuma same shi ba; hakika, za a fafare shi kamar wahayin dare. 9 Idon da ya ganshi ba zai ƙara ganin sa ba; mazauninsa ba zai ƙara ganinsa ba. 10 'Ya'yansa zasu roƙi gafarar matatalauta; hannuwansa zasu mayar da dukiyarsa. 11 ‌Ƙasusuwansa suna cike da ƙarfin ƙuruciya, amma zai kwanta tare da shi cikin turɓaya. 12 Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa, ko da yake ya ɓoye shi ƙarƙashin harshensa, 13 ko da yake ya riƙe shi a can bai bari ya fita ba amma ya riƙe ya gama cikin bakinsa - 14 abincin da ke cikin hanjinsa zai juya ya zama da ɗaci; ya zama dafin maciji a cikinsa. 15 Yakan haɗiye arziki, amma sai ya haras da su kuma; Allah zai tutturo su waje daga cikinsa. 16 Zai sha dafin maciji; harshen kububuwa zai kashe shi. 17 Ba zai ji daɗin rafuffuka ba, yalwar zuma da madara. 18 Zai mayar da rabon wahalar aikinsa kuma ba zai iya ya cin sa ba; ba zai ji daɗin dukiyar da ya samu ta wurin cinikaiyarsa ba. 19 Gama ya wulaƙanta matalauta ya kuma yashe su; ya ƙwace gidajen da bai gina ba ƙarfi da yaji. 20 Domin bai san ƙoshi ba, ba zai iya tanada wani abin da yake marmari ba. 21 Ba wani abin da ya rage da bai cinye shi ba; saboda haka arzikinsa ba zai daɗe ba. 22 A cikin yalwar wadatarsa zai faɗa cikin wahala; hannun kowanne matalauci zai yi tsayayya da shi. 23 Sa'ad da yake gaf da cika cikinsa, Allah zai jeho masa fushinsa mai ƙuna a kansa; Allah zai kwararo masa shi sa'ad da yake cin abinci. 24 Ko da yake mutumin nan ya guje wa makamin ƙarfe, bakan tagulla zai harbe shi. 25 Idan ya cire shi a bayansa sai bakin mai tsini ya shiga hantarsa. Razana zata faɗo masa. 26 Duhu ne baƙi ƙirin ke ajiye domin kayansa masu daraja; wutar da ba a izawa zata cinye shi; zata cinye ragowar abin da ke rumfarsa. 27 Sammai zasu bayyana zunubansa, ƙasa kuma zata miƙe gãba da shi ta zama shaida. 28 Dukiyar gidansa zata ɓace; kayayyakinsa zasu gudu a ranar hasalar Allah. 29 Wannan shi ne rabon mugu daga Allah, gadon da Allah ya ajiye masa kenan."

Sura 21

1 Sai Ayuba ya amsa ya ce, 2 "Ku kasa kunne da kyau ga maganganuna, kuma bari wannan ya zama ta'aziyar da kuke yi mani. 3 Ku daure da ni, ni kuma zan yi magana; bayan nayi magana, sai ku cigaba da ba'a. 4 Ni dai kam, ƙarata ga mutum ne? Don mene ne bazan yi rashin haƙuri ba? 5 Ku duba ni kuyi mamaki, ku ɗibiya hannuku a kan bakinku. 6 Sa'ad da nayi tunani akan wahaluna, nakan tsorata, makyarkyata sai ta kama jikina. 7 Me yasa mugayen mutane suke a rayuwa, su tsufa, su girma su ƙasaita a iko? 8 Zuriyarsu ta kafu tare da su a kan idanunsu, kuma jikokinsu su da su a idanunsu. 9 Gidajensu lafiya ba tsoro; kuma babu hukuncin Allah a kansu. 10 Bijiminsu na barbara; baya fasa yi; shanunsu suna haifuwa basa yin ɓarin 'yan maruƙansu' 11 Sukan aika da 'yan maruƙansu kamar garke, 'ya'yansu suna rawa. 12 Suna waƙa da kuge da molo kuma suna farinciki da waƙar sarewa. 13 Suna zaman kwanakinsu cikin wadata, su gangara shuru zuwa Lahira. 14 Sai su cewa Allah, 'Ka rabu da mu domin ba ma son wani fahimta game da hanyoyinka. 15 Wanene Mai Iko Dukka, da zamu yi masa sujada? Wace riba ce zamu samu idan muka yi addu'a gare shi?' 16 Duba, arzikinsu ba a hannunsu yake ba? Ba ruwana da shawarar mugayen mutane. 17 Sau nawa fitilar mugayen mutane ana hure ta, ko kuma masifarsu ta auka masu? Sau nawa yakan faru sai Allah ya rarraba ma su baƙin ciki cikin fushinsa? 18 Sau nawa su ke zama kamar tattaka cikn iska ko kamar ƙaiƙai da iskar hadari ke kwashewa. 19 Kun ce, 'Allah yana tara alhakin mutum domin 'ya'yansa su biya.' Bari shi da kansa ya biya, domin ya san laifinsa. 20 Bari idanunsa su ga hallakarsa, kuma bari ya sha hasalar Mai Iko Dukka. 21 Gama me ya dame shi da iyalinsa da ya bari bayan an datse kwanakinsa? 22 Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da shima yana shari'anta har waɗanda suke sama? 23 Wani mutum yakan mutu cikin goshin ƙarfinsa, ya yi shuru a natse. 24 Jikinsa na cike da madara, kuma ɓargon ƙashinsa da danshi. 25 Wani mutum kuma ya mutu cikin ɓacin zuciya, wanda bai taɓa ɗanɗana wani abin kirki ba. 26 Dukkan su sukan kwanta a cikin turɓaya; tsutsotsi su mamayesu. 27 Duba, na san tunaninku, kuma da hanyoyin da ku ke so ku aibata ni. 28 Domin kun ce, 'Ina yanzu gidan ɗan sarki? Ina rumfar da mugun mutumin nan ya zauna a ciki?' 29 Baku taɓa tambayar mutane matafiya ba? Ko ba ku san shaidar da zasu iya faɗi ba, 30 cewa mugun mutum an keɓe shi daga ranar masifa, an kuma janye shi daga ranar hasala? 31 Wane ne zai zargi hanyoyin mugun mutum a fuskarsa? Wane ne zai sãka masa domin abin da ya yi? 32 Duk da haka za a kai shi kabari; mutane zasu yi ta kiyaye kushewarsa. 33 ‌Ƙurar kabarinsa da aka tula a kansa zata zama masa da daɗi; dukkan mutane za su bi bayansa, kamar yadda mutanen ba su ƙidayuwa sun sha gabansa. 34 To ƙaƙa zaku ta'azantar da ni da rashin hankali, tun da cikin amsoshinku babu komai sai ƙarairayi?"

Sura 22

1 Sai Elifaz Batemane ya amsa, yace, 2 "Mutum zai zama da amfani ga Allah? Mutum mai wayau zai zama da amfani ga gare shi? 3 Zai zama da jin daɗi ga Mai Iko idan ka zama mai adalci? Zai zama da wata riba gare shi idan hanyoyinsa marasa laifi ne? 4 Ai ba domin kana tsoronsa ba ne ya kwaɓe ka, ko kuma ka ɗauki shari'a? 5 Ba babbar muguntarka ba ce? Ashe babu ƙarshen muguntarka? 6 Domin ka bukaci a ba ka bashin da ke daga wurin ɗan'uwanka ba tare da wani dalili ba, ka kuma ƙwace tufafi daga wurin wanda ba shi da komai. 7 Ka hana ruwa ga mutane masu ƙishinruwa su sha; ka hana abinci ga mutane masu jin yunwa 8 ko da ya ke kai mutum ne mai iko, kana da kayan duniya, ko da ya ke kai, mutum ne mai girma, kana rayuw a cikinta. 9 Ka kori mata da mazajensu suka mutu ba tare da komai ba; hannuwan marayu sun karye. 10 Saboda haka, ramummuka a ko'ina kewaye da kai, sun kuma kawo maka tsoron damuwa. 11 Akwai duhu, saboda har baza ka iya gani ba; ruwaye masu yawa sun sha kanka. 12 Ashe Allah ba a saman sammai yake ba? Dubi taurare a sama, yaya nesan su a can! 13 Kace, 'Me Allah ya sani? Zai iya shari'a a cikin baƙin duhu? 14 Gizagizai masu duhu sune ke rufe shi, saboda haka ba ya ganin mu; yana tafiya a kan iyakar sararin sama.' 15 Kana bin tsohowar hanyar da mugayen mutane suke tafiya a kai-- 16 waɗanda aka ƙwace kafin lokacinsu, waɗanda tuwasunsu suka shafe kamar rafi, 17 sune waɗanda suka ce da Allah, 'Tafi daga wurin mu,' su ne suka ce, 'Mene ne Mai Iko zai yi da mu?' 18 Duk da haka ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, shirye-shiryen mugayen mutane suna nesa daga gare ni. 19 Adalan mutane su na ganin kaddararsu suna murna; mutane marasa laifi kuma suna dariyarsu. 20 Sun ce, 'Babu shakka waɗanda suka taso gãba da mu an yanke su, wuta kuwa ta lashe mallakarsu.' 21 Yanzu ka yarda da Allah salama ta kasance tare da kai; ta wannan hanya, abu mai kyau zai zo gare ka. 22 Karɓi, ina rokon ka, ka koya daga bakinsa; ka riƙe kalmominsa a zuciyarka. 23 Idan zaka juyo ga Mai Iko, za a sake gina ka, idan za ka ajiye rashin adalci nesa daga gidanka. 24 Ka ajiye dukiyarka can cikin ƙura, zinariya daga ofir a cikin duwatsun rafuffuka, 25 Mai Iko zai zama dukiyarka, da azurfa mai daraja ga gare ka. 26 Sa'an nan zaka sami farin ciki a wurin Mai Iko, za ka tada fuskarka ga Allah. 27 Za ka yi addu'a gare shi, shi kuma zai ji ka; zaka kiyaye alkawaran da ka yi masa. 28 Za ka kuma hurta komai, za a kuma tabbatar maka, haske zai haskaka a hanyoyinka. 29 Allah yakan ƙasƙantar da mutum mai girmankai, yakan ceci mai tawali'u. 30 Zai ceci kowane mutum wanda ke da laifi; wanda za a ceta ta wurin abin da hannuwansa ke yi dai-dai."

Sura 23

1 Sai Ayuba amsa ya ce, 2 "Har yau ƙarata nada zafi, hannuna yayi nauyi saboda gunagunina. 3 Oh, dama na san inda zan same shi! Oh, da sai in tafi wurinsa! 4 Da zan kai ƙarata a gabansa, da na cika bakina da muhawara. 5 Zan koyi kalmomi waɗanda zaya amsa mani, yadda zan san abin da zai ce da ni. 6 Zaya yi gardamar gãba da ni duk da ƙarfin ikonsa? A'a, zai saurare ni. 7 Akwai amintaccen mutum da zai yi gardama da shi. Ta wannan hanyar zan tabbatar da aminci har abada ta wurin shari'a ta. 8 Duba, na tafi gabashi, amma baya can, yammaci, amma ban same shi ba. 9 A arewa, a wurin yake aiki, duk da haka ban gan shi ba, a kudu, a wurin ya ɓoye kansa domin kada in gan shi. 10 Gama ya san hanyar da na ɗauka; ya jarraba ni, zan fito kamar zinariya. 11 Ƙafata tana bin sawun ƙafarsa; ina bin hanyarsa ban kuma kauce wani gefen ba. 12 Ban kuma koma da baya ba daga umarnin leɓunansa; na ajiye kalmomin baƙinsa sun zama abinci na. 13 Gama yana ɗaya daga cikin masu kirki, wa zai iya juyar da shi? Abin da yake so ya aikata. 14 Gama ya ɗauki ka'ida gãba da ni; akwai da yawa kamar su. 15 Saboda haka, ina rawar jiki a gabansa; duk lokacin da nake tunani a kansa. 16 Domin Allah ya sa zuciyata tayi sanyi; Mai Iko ya tsorata ni. 17 Amma duhu bai kawo ni ƙarshe ba, ko da yake baƙin duhu ya rufe mani fuskata.

Sura 24

1 Meyasa Mai Iko bai tsaida lokatan shari'ar mugayen mutane ba? Meyasa bai tsayar wa waɗanda suke adalai ga Allah suga kwanakinsa na shari'a ya zo? 2 Akwai mugayen mutane da yawa da suke kawar da iyaka; akwai mugayen mutane waɗanda suke ɗaukan garke da tsiya su zuba cikin makiyayarsu. 3 Sukan saci jakin marayu; su kama takarkarin gwauruwa a matsayin jingina. 4 Sukan tilastawa mutane masu bukata su bar masu hanya; mutane matalauta na ƙasa dukka su ɓoye kansu daga gare su. 5 Duba, waɗannan mutane matalauta su fita daga wurin ayyukansu kamar jakunan daji a jeji, suna bi hankali su na neman abinci; me yiwuwa Arabah zai ba su abinci domin 'ya'yansu. 6 Matalautan mutane na girbi da dare a gonakin wasu mutanen, su na tattara 'ya'yan inabi daga gonakin waɗannan mugayen mutanen. 7 Su na kwance tsirara dukkan dare ba tare da tufa ba, basu da abin da zai hana su jin sanyi. 8 Suna jike sharkaf da ruwa da ke kwararowa daga kan duwatsu; suna kwance kusa da manyan duwatsu domin basu da mafaka. 9 Akwai mugayen mutane waɗanda suke figar marayu daga nonon iyayansu mata, mugayen mutane waɗanda suke ɗaukan yara a matsayin jingina daga matalautan mutane. 10 Amma matalautan mutane suna tafiya babu kaya a jikinsu; suna tafiya da yunwa, suna ɗauke da damunan hatsi na waɗansu mutane. 11 Matalautan mutane na matse mai a katangar mugayen mutane; suna kuma matsar ruwan inabin mugayen mutane, amma su da kansu suna fama da ƙishi. 12 Daga cikin birni ana jin nishin masu mutuwa, makogwaron masu rauni na kukan neman taimako. Amma Allah bai kula da masu laifin ba. 13 Wasu daga cikin waɗannan mugayen mutanen suna ƙin haske; basu san hanyarsa ba, ko su tsaya a hanyarsa. 14 Kafin hasken rana mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci da mutane masu bukata; da dare kuma ya kan zama kamar ɓarawo. 15 Har yau, idon mazinaci yakan jira sai da magariba; ya faɗa, 'Babu idon da zai gan ni.' Yana ɓoye fuskarsa. 16 A cikin duhu mugayen mutane sukan kutsa kai cikin gidaje; amma suna ɓoye kansu da rana; basu damu da haske ba. 17 Gama dukkan su, mattsanancin duhu ne kamar duhun safiya; domin su abokan "yan ta'addar baƙin duhu ne. 18 Suna wucewa da sauri, duk da haka, kamar kumfa a kan fuskar ruwaye; ƙasar da suka mallaka an la'anta ta; babu wanda zai tafi yayi aiki a cikin gonar inabi. 19 Kamar dusar ƙanƙara take narkewa, iska mai laima cikin ruwaye, haka Lahira ke ɗaukan waɗanda suka yi zunubi. 20 Cikin da ya haife shi ba zai tuna da shi ba; macijin ciki zai ji daɗin ƙoshi a kansa; ba za a ƙara tunawa da shi ba; ta wannan hanya, miyagu zasu lalace kamar itace. 21 Mugun da ya lanƙwame matan da basu haifi yara ba; bai kuma nuna alheri ga matar da ke gwauruwa ba. 22 Duk da haka Allah yakan ja mutane masu iko ta wurin ikonsa; yakan ɗaga ya kuma hana su ƙarfi a rayuwarsu. 23 Allah ya kan bar su da tunanin sun tsira, suna murna a kan haka, amma idanuwansa na kan hanyoyinsu. 24 An ɗaukaka waɗannan mutane; a ɗan lokaci kaɗan, zasu ɓace; za a ƙasƙantar da su; za a tattara su wuri ɗaya kamar sauran; za a hallaka su kamar karan dawa da aka yanke. 25 Idan ba haka ba, wane ne ya tabbatar ni maƙaryaci ne; wa zai ce kalmomina ba gaskiya ba ne?"

Sura 25

1 Sai Bildad Bashune ya amsa ya ce, 2 "Mulki da tsoro suna tare da shi, yayi samaniya wurarensa. 3 Akwai ƙarshen jimilar yawan sojojinsa? A kan wane ne haskensa yaƙi haskakawa? 4 Yaya mutum zai zama adali tare da Allah? Yaya shi wanda mace ta haifa zai zama da tsabta, ƙarɓaɓɓe gare shi? 5 Duba, ko da wata bashi da haske gare shi, taurari ma basu da tsarki a gabansa. 6 Yaya kuma mutum, wanda aka haifa--ɗan mutum, wanda aka haife shi!"

Sura 26

1 Sai Ayuba ya amsa ya ce, 2 "Yaya ka taimakawa wanda bashi da ƙarfi! Ka cece hannun da bashi da ƙarfi! 3 Yaya kake ba wanda bashi da hikima shawara, kana sanar da amon ilimi! 4 Ta wurin wa ka sami taimako ka ke yin maganar waɗannan kalmomi? Wanne ruhu ne ya fito daga gare ka? 5 Matattu suna rawar jiki, su waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukkan waɗanda su ke zama da su. 6 Lahira ta na tsirara gaban Allah; hallakarwa da ke kanta ba rufe take ba a gare shi. 7 Ya shimfiɗa arewa a sarari a kan abin da ke fili, ya rataya duniya ba bisa kan kome ba. 8 Ya ɗaure ruwaye a gizagizai, amma gizagizan ba a ƙarƙashinsu suke ba. 9 Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa girgije a kanta. 10 Ya zana kewayanta a kan iyakar fuskar ruwaye kamar layi tsakanin haske da duhu. 11 Ginshiƙan samaniya sun girgiza, sun firgice sakamakon tsautawarsa. 12 Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku; ta wurin saninsa ya hallakar da Rahab. 13 Ta wurin numfashinsa yasa sararin sama yayi garau; da hannunsa ya sha zarar macijin nan mai gudu. 14 Duba, amma waɗannan su ne yatsun hanyoyinsa; yaya ƙanƙantar raɗa da muke ji a gare shi! Wane ne ya gane tsawar ikonsa?"

Sura 27

1 Ayuba ya fara magana, ya ce, 2 "Yadda Allah na raye, wanda ya ɗauke mani adalci, Mai Iko, wanda yasa rayuwata ɗaci, 3 har yanzu raina baya tare da ni, numfashi daga Allah ya cika hancina, wannan shi ne abin da zan yi. 4 Leɓena ba zai faɗi mugunta ba, ko harshena ya hurta maganganun yaudara; 5 ba zan taɓa yarda cewa ku ukun kun yi dai-dai ba; har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba. 6 Ina rike da adalcina ba kuwa zan sake shi ba ya tafi; tunanina ba zai zarge ni ba idan dai ina raye. 7 Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum; bari wanda ya ke gãba da ni ya zama kamar mutum marar adalci. 8 Gama wacce sa zuciya ke ga mutum marar tsoron Allah sa'ad da Allah ya datse shi, sa'ad da Allah ya ɗauke ransa? 9 Allah kuwa zai ji kukansa a lokacin da wahala ta same shi? 10 Zai yi farinciki da kansa a wurin Mai Iko, zai yi kira ga Allah a dukkan lokatai? 11 Zan koya maka game da hannun Allah; ba zan ɓoye tunanin Mai Iko ba. 12 Duba, dukkan ku kun ga wannan da kanku; me yasa kuke yin wannan magana ta wawanci? 13 Wannan shi ne rabon mugun mutum a wurin Allah, gãdo ne kuma wanda azzalumi zai karɓa daga wurin Mai Iko: 14 Idan 'ya'yansa sun riɓamɓanya, zasu zama rabon takobi; zuriyarsa kuwa ba zata sami isasshen abinci ba. 15 Duk wanda ya tsira za a bizne shi da annoba, gwaurayensu ba zasu yi makoki domin su ba. 16 Ko da yake mugun mutum ya tsibe azurfa kamar turɓaya, tarin tufafi kamar laka, 17 zai iya tara tufafi, amma adalan mutane zasu zuba a kai, mutanen kirki zasu raba azurfar a tsakaninsu. 18 Ya gina gidansa kamar saƙar gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro. 19 Ya kwanta a gadon mai arzaki, amma ba zai ci gaba da yin haka ba, zai buɗe idanunsa, yaga komai ya tafi. 20 Razana zata auko masa kamar ruwaye; iska zata tafi da shi da dare. 21 Iskar gabas zata fyauce shi, zai tashi; zata share shi daga wurinsa. 22 Zata jefar da kanta a kansa, babu tsayawa; zai yi ƙoƙari ya tsere daga hannunsa. 23 Zata tafa hannuwanta a kansa domin ba'a; zata yi masa ƙara daga wurinsa.

Sura 28

1 Babu shakka akwai ma'adani na azurfa, a wurin da ake tace zinarya. 2 Ana samun ƙarfe daga cikin ƙasa; a kuma narkar da tagulla daga dutse. 3 Mutum ya kan kawar da duhu, ya kuma bincike zuzzurfar iyaka, ya haƙo duwatsun a lunguna masu sulɓi da ke cikin duhu baƙi ƙirin. 4 Ya kan buɗe ƙyaure daga wurin da mutane ke zama, wuraren da ƙafar wani ba zata manta ba. Yakan kafa abin lilo nesa da mutane; yayi ta lilo zuwa da komawa. 5 Daga cikin ƙasa ake samun abinci, takan juyo ƙarƙashinta kamar ta wurin wuta. 6 Duwatsu ne wurin da ke samun shudin yakutu, zinariya ɗauke da ƙurarta. 7 Tsuntsu mai cin nama bai san hanyarta ba, shaho ma da idanuwansa bai ganta ba. 8 Namomi masu fahariya basu taɓa bin irin hanyar ba, ko zaki mai zafi ma bai taɓa wucewa can ba. 9 Mutum yasa hannunsa a kan ƙanƙarar dutse, yana kuma iya tunɓuke tushen duwatsun daga saiwoyinsu. 10 Yana kuma iya sarar magudanar ruwa cikin duwatsu; idannunsa kan ga kowanne abu mai daraja a can. 11 Yana iya datse rafuffuka ya hana su gudu; ya binciko abin da ke ɓoye a can ya kawo shi a sarari. 12 Daga ina za a samo hikima? Ina ne wurin haziƙanci? 13 Mutum bai san darajarta ba; ko a samo ta a ƙasar masu rai. 14 Zurfafan ruwaye a ƙarƙashin ƙasa sun ce, 'Bata cikina,' teku ta faɗa, 'Bata tare da ni.' 15 Ba zata iya samuwa daga zinariya ba; ko azurfa bata yi nauyi kamar tamaninta ba. 16 Ba zata yi kimanin zinariyar Ofir, tare da darajar baƙin dutse mai daraja ba ko saffir. 17 Zinariya da madubi ba zasu yi dai-dai da tamaninta ba; ko kuma a musanyata da murjanin da aka yi da zinariya mai kyau. 18 Kada ma a ambaci darajar murjani ko dutse mai walkiya; lallai tamanin hikima yafi shi. 19 Duwatsu masu darajar Kush ba za a dai-dai su da tamaninta ba; ko kuma darajar tamaninta yafi na zinariya tsantsa. 20 Daga ina hikima take fitowa? A wanne wuri kuma hazaƙa take? 21 Hikima a ɓoye take daga idon dukkan abubuwa masu rayuwa, haka nan yake a ɓoye ga tsuntsaye da ke tashi a sammai. 22 Hallaka da mutuwa sun ce, 'Mun ji ƙishin-ƙishin a kanta a kunnuwanmu.' 23 Allah ya fahimci hanyar zuwa gare ta; ya san wurinta. 24 Saboda yana ganin ƙarshen duniya, yana duban ƙarƙashin dukkan sammai. 25 Yasa iska mai ƙarfi da ƙunshi daga ciki ta wurin auna ruwaye. 26 Yayi ka'ida domin ruwan sama da hanya domin tsawa. 27 Sai ya ga hikima, ya sanar da ita; ya tabbatar da ita; ya gwada ta. 28 Ga mutane yace, 'Duba, tsoron Ubangiji -- shi ne hikima; rabuwa daga mugunta kuma ita ce hazaƙa.'"

Sura 29

1 Ayuba yaci gaba da magana yace, 2 "Oh, dama ina ma yadda nake a watanin da suka wuce ne? lokacin da Allah yake lura da ni, 3 sa'ad da fitilarsa take haska mani kai, da kuma lokacin da nake tafiya cikin duhu ta wurin haskensa. 4 Kash, dãma na tsaya yadda nake cikakke a kwanakina, sa'ad da abokantaka da Allah ke kan gidana, 5 lokacin da Mai Iko ke tare da ni, 'ya'yana ke kewaye ni, 6 sa'ad da aka rufe hanyata da madara, duwatsu kuma na fito mani da rafuffukan mai! 7 A lokacin da nakan fito ƙofar birni, sa'ad da na zauna a wurin zamana a dandali, 8 da samari sukan gan ni, sai su kawar da kansu daga gare ni don girmamawa, tsofaffi mutane kuma su miƙe tsaye domi na. 9 Sarakuna na yin shiru da magana sa'ad da nazo; sai su ɗora hannuwansu a kan bakinsu. 10 Muryoyin manyan mutane sun yi tsit, harshensu ya liƙe a dasashin bakunansu. 11 Gama bayan da kunnuwansu suka ji ni, sai su albarkace ni; bayan da idanuwansu suka gan ni, sai su ba da shaida a kaina su kuma amince da ni 12 domin nakan ceci duk matalauci sa'ad da yayi kuka, da kuma wanda bashi da uba kuma bashi da wanda zai taimake shi. 13 Albarka ga wanda yake bakin mutuwa idan yazo gare ni; nakan sa zuciyar gwauraye ta yi waƙar murna. 14 Na sa sutura ta adalci, ta rufe ni; gaskiyata ita ce kamar suturata da rawanina. 15 Ni ne idon makafin mutane; ni ne ƙafaffun guragun mutane. 16 Ni mahaifi ne ga mutane masu bukata; nakan yi bincike don in warware al'amari harma wanda ban san shi ba. 17 Nakan karya muƙamuƙan mutum marar adalci; in fisge wanda aka zalunta daga cikin tsakanin haƙoransa. 18 Sa'an nan nace, 'Zan mutu cikin gidana; zan riɓaɓɓanya kwanakina kamar tsabar yashi. 19 Saiwoyina suna shimfiɗe cikin ruwaye, raɓa na sauka a dukkan dare a rassana. 20 Daraja a gare ni kullum garau take, baka shi ne ƙarfina kullum sabo yake a hannuna. 21 A gare ni mutane ke saurare; suna jira na, sun tsaya shiru su ji shawarata. 22 Bayan na gama magana ba wanda ya sake wata magana kuma; maganata tana sauka kamar ruwa a kansu. 23 Suna jira na kullum kamar yadda ake jiran ruwan sama; sun buɗe bakinsu sosai don su sha daga kalmomina, kamar yadda suke jiranruwan bazara. 24 Na yi masu murmushi sa'ad da basu sa tsammaninsaba; ba su yi watsi da fara'ar fuskata ba. 25 Nakan zaɓar masu hanya, in zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin sojojinsa, kamar wanda yake ta'azantar da masu makoki.

Sura 30

1 Yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a kaɗai suke yi mani -- waɗannan matasa maza waɗanda iyayensu ban ma yarda in bar su suyi aiki tare da karnukan da suke kiwon garke tumakina ba. 2 Lallai, ƙarfin hannuwan iyayensu maza, ba zasu iya taimako na ba--mutanen waɗanda ƙarfin balagarsu yake lalacewa? 3 Sun rame daga talauci da yunwa; sai gaigayar ƙasa suke yi da duhu, cikin jeji da kufai. 4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, doyar jeji ita ce abincinsu. 5 Aka kore su daga cikin mutane ana bin su da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo ihu. 6 Sai a kwazazzaban rafi suke zama, ramummukan ƙasa da kogwannin duwatsu. 7 A cikin jeji suke ta kuka kamar jakai, sukan taru tare a ƙarƙashin sarƙaƙiya. 8 Su 'ya'yan wawaye ne, lallai, 'ya'ya maza marasa suna a mutane! Aka kore su daga ƙasar tare da tsumagu. 9 Amma yanzu na zama abin yiwa zambo, na zama abin magana a gare su. 10 Suna ƙyamata ta, sun tsaya da nisa daga gare ni; basu daina tofa mani yawu a fuskata ba. 11 Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙantar da ni, waɗanda suka yi mani ba'a sun hana ni sakewa in yi wani abu. 12 A hannun damana 'yan iska sun taso mani; sun kore ni suna gãba da ni sun tura ni hanyarsu ta hallaka. 13 Sun lalata hanyata, sun jawo bala'i domi na, ba wanda ya hana su. 14 Sun zo suna gãba da ni kamar soja wanda yabi ta babbar kafar bangon birni; a tsakiyar hallaka sun naɗa kansu a kaina. 15 Babban tsoro ya faɗo mani; an kore darajata kamar iska; wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije. 16 Yanzu raina yana kwararowa daga gare ni; kwanakin wahala sun same ni. 17 A cikin dare ƙasusuwana na karkaɗawa; azaba tana gaigaya ta ba hutawa. 18 Ƙarfin girman Allah yaci wuyan rigata; ya kuma kewaye ni kamar ƙarfin taguwata. 19 Ya jefar da ni cikin laka; na zama kamar ƙura da toka. 20 Na yi kuka a gare ka, Allah, amma ba ka amsa mani ba; na tashi tsaye, ka dai kalle ni kawai. 21 Ka canja sai ka zama mara tausayi a gare ni; da ƙarfin hannunka ka tsananta mani. 22 Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ta kora ni; ka jefa ni baya da gaba a cikin hadari. 23 Gama na sani zaka kai ni ga mutuwa, a gidan da aka ƙaddara wa kowanne mai rai. 24 Duk da haka, ba wanda ya isa ya miƙa hannunsa ya roƙi taimako idan ya faɗi? Babu wani da zai nemi taimako idan ya shiga cikin wahala? 25 Ashe ban yi kuka saboda shi wanda yake cikin wahala ba? Ashe ban yi ɓacin rai saboda mutum mai bukata ba? 26 Sa'ad da nasa bege don abin kirki, sai ga mugunta ta zo; sa'ad da nake jiran haske, sai duhu ya zo. 27 Zuciyata tana cikin damuwa, bata huta ba; kwanakin wahala ya zo a kaina. 28 Na tafi kamar wanda ke rayuwa cikin duhu, amma ba domin rana ba, na tsaya a gaban taron jama'a ina kukan neman taimako. 29 Na zama ɗan'uwan dila, aminin jiminai. 30 Fatata baƙa ce, ta faɗi daga gare ni; ƙasusuwana suna ƙuna da zafi. 31 Saboda haka garayata ta juya ga waƙar makoki, sarewata kuma ta zama waƙoƙi ga waɗanda ke kuka.

Sura 31

1 Na yi alƙawari da idanuna; me zai sa in dubi budurwa har in yi sha'awa? 2 Gama wanne irin rabo zan samu daga wurin Alla a sama, gãdon me kuma zan samu daga wurin Mai Iko a samaniya? 3 Na kan yi tunanin masifa daga wurin mutane mara sa adalci, bala'i na masu aikata mugunta ne. 4 Ko Allah ba ya ganin hanyoyina da dukkan matakallaina? 5 Idan ina tafiya da rashin gaskiya, idan kafata tana hanzarin aikata yaudara, 6 bari a auna ni da ma'aunin yadda Allah zai san halayena na kwarai. 7 Idan ƙafata ta kauce daga hanya, idan kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna, idan akwai wani aibi ya wuce ta hanuwana, 8 to bari na shuka, bari wani yaci, bari kuma amfanina ya tumɓuke. 9 Idan zuciyata tayi sha'awar wata mace, idan har naje na laɓe a ƙofar maƙwabcina, 10 to bari matata tayi niƙan hatsi domin wani, bari waɗansu su kwanta a kanta. 11 Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai; lallai, alƙalai ne zasu hukunta. 12 Domin wuta mai ci zata hallaka, zata cinye har zuwa Abaddon, zata kone dukkan girbina har saiwa. 13 Idan naƙi kulawa da roƙo domin adalci daga barorina maza da mata sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina, 14 to me zan yi lokacin da Allah ya tashi don ya hukuntar da ni? Sa'ad da yazo yi mani shari'a, ya ya zan amsa masa? 15 Ai shi wanda yayi ni a mahaifa shi ne ya yi su kuma? Ba shi ne dai ya siffata mu dukka a cikin mahaifa ba? 16 Idan na taɓa hana matalautan mutane daga sha'awarsu, ko idan nasa gwauruwar da mijinta ya mutu idanunta su dushe da kuka, 17 ko kuwa naci ɗan abincina ni kaɗai ban bar waɗanda basu da iyaye maza suma su ci abincina ba-- 18 gama tun daga yarintaka marayu suka yi girma tare da ni kamar mahaifi, na lura da mahaifiyarsa, gwauruwa, daga cikin mahaifiyata. 19 Idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura; ko idan naga wani mutum da bukata na rashin sutura; 20 idan zuciyarsa bata albarkace ni ba domin bai ji dumi da ulun tumakina ba, 21 idan na daga hannuna gãba da marayun mutane, don naga taimakona a ƙofar birni, sai a kawo ƙara a kaina! 22 Idan na yi waɗannan abubuwa, bari kafaɗata ta ɓaɓɓalle daga in da su ke, bari hannuna ya karye daga mahadarsa. 23 Gama firgici da bala'i daga wurin Allah; saboda ɗaukakarsa, ba zan iya yin kome a kan waɗannan abubuwa ba. 24 Idan nasa zinariya abin fatana, idan nace ina da zinariya mai kyau, 'Kana nan yadda na ke da aminci; 25 idan ina murna saboda dukiyata ta na da girma, ko saboda abin da na mallaka ne, sai su kawo s̀̀̀u a kaina! 26 Idan na ga rana tana haske, ko wata yana tafiya da haskensa, 27 idan zuciyata jarabtu a asirce, yadda bakina zai sumbace hannun a sujadarsu-- 28 wannan ma zai zama laifi wanda shari'a zata hukunta, gama na musanta Allah wanda ke sama. 29 Idan ina murna saboda hallaka ta sami wanda ya ke maƙiyina, ko zan yiwa kaina barka ne, idan wahala ta same shi, zai kawo ƙarata! 30 Lallai, ban ma yarda in bar bakina ya yi zunubi ta wurin tambaya don ransa tare da la'ana. 31 Idan a rumfata akwai mutanen da suka ce, 'Wane ne zai sami wanda bai ƙoshi da abincin Ayuba ba?" 32 (ko da baƙon da baya zama a dandalin birni, domin kullum ina buɗe ƙofufina ga mai tafiya), idan ba haka ba ne, sai a kawo ƙarata! 33 Idan, kamar 'yan adam, na ɓoye zunubai na ta wurin ɓoye laifi a cikina 34 (saboda ina jin tsoron babban taron jama'a, domin tsoron rainin iyalai gare ni, na yi shuru, ban ma iya fita waje ba), sai a kawo ƙarata! 35 Oh, idan za a sami wani shi kaɗai ya ji ni! Duba a nan ga sa hannuna; bari Mai Iko ya amsa mani! Idan ni kaɗai na yi ƙarar maƙiyana a rubuce! 36 Babu shakka zan ɗauke ta a buɗe a kan kafaɗata; zan sa ta kamar rawani. 37 Zan furta a kansa lissafin takawa ta; a matsayin asirin sarki zan tafi wurinsa. 38 Idan ƙasata tana kuka da ni, tare da ƙungiyoyinta, 39 idan na ci amfaninta ba tare da biya ba, ko na yi sanaɗin mutuwar masu ita, 40 bari ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama, tsire tsire marasa amfani kuma maimakon bali." Maganganun Ayuba sun kare.

Sura 32

1 Sai mutanen uku suka daina ba Ayuba amsa saboda yana ganin kansa shi adali ne. 2 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz daga iyalin Arama, ya husata da fushi a kan Ayuba saboda ya baratar da kansa maimakon Allah ya baratar da shi. 3 Elihu ya fusata da fushi a kan abokansa uku saboda sun rasa amsawa Ayuba, duk da haka sun gani Ayuba ne ke da laifi. 4 Yanzu Elihu ya jira ya yi magana da Ayuba, don sauran mutanen uku sun girme shi da shekaru. 5 Sa'ad da Elihu ya ga babu wata amsa a bakunan waɗannan mutanen uku, har fushinsa ya yi ƙuna. 6 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya yi magana ya ce, "Ni yaro ne, ku manya ne sosai. Wannan ya sa na yi shuru, ban iya faɗa maku ra'ayina ba. 7 Na ce, "Yawan kwana su yi magana; yawan shekaru kuma su koyar da hikima. 8 Amma akwai ruhu a cikin mutum; numfashin Mai Iko ya ke ba da sani da basira. 9 Ba manyan mutane ne kaɗai waɗanda suke da wayo da hankali ba, ko tsofaffin mutane kaɗai suke da sanin adalci da gaskiya. 10 Don haka nace da ku, 'Ku saurare ni; zan kuma faɗa maku ta wa fahintar.' 11 Duba, na jira domin inji maganarku; na kasa kunne da jin muhawararku, tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa. 12 Lallai, na saurare ku, amma duba, babu wanda ya kada Ayuba ko wanda ya bashi amsar maganganunsa. 13 Ku yi hankali kada wani ya ce, "Mun sami hikima! Allah ne zai ci nasara a kan Ayuba; mutum mai mutuntaka ba zai iya ba. 14 Gama Ayuba ba da ni ya ke magana ba, saboda haka ba zan amsa da irin amsarku ba. 15 Waɗannan mutane uku abin ya cika masu ciki, ba su ƙara amsawa Ayuba ba; ba su da sauran abin da za su ce kuma. 16 Ni kuma zan tsaya don su basu ce kome ba, don sun tsaya a wurin shiru, basu da wata amsa kuma? 17 A'a, ni kuma zan ba da ta wa amsa; zan kuma faɗa masu na wa sanin. 18 Gama ina cike da magana, ruhu da ke ciki na ya iza ni. 19 Duba, kirjina ya na kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska. kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda ya ke shirin ya fashe. 20 Zan yi magana saboda in huce, zan buɗe lebuna na in ba da amsa. 21 Ba zan nuna san zuciya ba, ko kuma in yi wa wani mutum fadanci. 22 Gama ni ban san yadda zan iya yi fadanci ba; idan nayi haka kuwa Mahaliccina zai ɗauke ni nan da nan.

Sura 33

1 Amma yanzu, kai Ayuba, ina roƙon ka, ka saurari abin da zan ce, ka saurari dukkan maganganuna. 2 Duba yanzu, na buɗe bakina; harshena ya yi magana da bakina. 3 Kalmomina sun zo da gaskiyar zuciyata; leɓuna suna faɗar ilimi tsantsa. 4 Ruhun Allah ne yayi ni; numfashin Mai Iko ne ya bani rai. 5 Idan za ka iya ka amsa mani; ka shirya kalmominka dai-dai a gabana, kayi tsaye a kansu. 6 Duba, ni kamar ka mu ke a wajen Allah; ni kuma daga yumɓu aka siffanta ni. 7 Duba, razanata ba zata sa ka ji tsoro ba, ko matsawata ta zama da nauyi a kanka. 8 Babu shakka maganar da ka yi na ji ta; na kuwa ji amon maganganunka, 9 ni tsabtattace ne, ba wani laifi, bani da laifi, kuma ba wani zunubi a gare ni. 10 Duba, Allah ya sami damar zargi na, ya ɗauke ni tankar maƙiyinsa. 11 Ya sa ƙafaffuna a turu, ya na lura da dukkan hanyoyina.' 12 Duba, a wannan kayi kuskure--zan baka amsa, gama Allah ya fi kowane mutum girma. 13 Me yasa kake yi masa gunaguni? Baya lissafin kowanne abu da yayi. 14 Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne--i, har sau biyu, duk da haka mutum baya kula da ita. 15 Cikin mafarki, ko cikin wahayi da dare, a sa'ad da dogon barci ya faɗo wa mutane, ana barci a kan gado-- 16 sai Allah ya buɗe kunnuwan mutane, ya tsorata su da faɗakarwarsa, 17 don ya kawar da mutum daga zunubinsa da yayi nufi, ya kuma kawar da girmankai daga gare shi. 18 Allah yakan hana ran mutum daga faɗawa rami, rayuwarsa daga haurawa zuwa mutuwa. 19 A kan hori mutum kuma da cuta mai zafi a gadonsa, yayi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa, 20 saboda da ransa ya kyamaci abinci, kurwarsa ta ƙyamaci daɗinsa. 21 Tsokar jikinsa ta rame ƙangayau yadda ba za a iya ganinta ba, ƙasusuwansa baza a iya gani ba, yanzu sun zama waje. 22 Lallai, ranna yasa gab da shiga rami, ransa yana wurin waɗanda suke so su hallaka shi. 23 Amma idan a ce akwai wani mala'ika wanda zai yi sulhu dominsa, mai sulhu, ɗaya daga cikin duban mala'iku, zai nuna masa abin da ke dai-dai da zai yi, 24 idan mala'ikan da zai yi masa alheri ya faɗa wa Allah, 'Cece wannan mutum daga gangarawa zuwa cikin ramin; dana sami abin da zai fansa domin sa,' 25 Naman jikinsa zai koma fiye da na yaro, zai komo irin kwanakin ƙarfin ƙuruciyarsa. 26 Zai yi addu'a ga Allah, Allah kuma zai yi masa alheri, saboda ya ga fuskar Allah da murna. Allah zai ba mutumin nasararsa. 27 Sai wannan mutum ya raira waƙa a gaban sauran mutane yace, 'Na yi zunubi, ban yi dai-dai ba, amma zunubi bai sa a hore ni ba. 28 Allah ya fanshi raina daga tafiya can cikin rami, raina zai cigaba da ganin haske. 29 Duba, Allah yayi dukkan waɗannan abubuwa ga mutum harma sau biyu, i, harma lokatai uku, 30 ya komo da ransa daga rami, don a haskaka shi da hasken rai. 31 Ka yi lura Ayuba, ka saurare ni, kayi shiru, zan yi magana. 32 Idan kana da wani abu da zaka ce, ka amsa mani, yi magana, don in tabbatar maka kana dai-dai. 33 Idan ba haka ba, sai kayi shiru ka ji ni, ka zauna shiru, zan kuwa koya maka hikima."

Sura 34

1 Hakanan, Elihu ya ci gaba da magana: 2 "Ku saurari kalmomina, ku masu hikima; ku ji ni, ku masu ilimi. 3 Domin kunnuwa na gwada kalmomi kamar yadda faranti ke ɗanɗana abinci. 4 Bari mu zaɓar wa kanmu abin da ke na adalci, mu kuma yiwa kanmu abin da ke mai kyau. 5 Domin Ayuba yace ni adali ne, amma Allah ya ɗauke abin da ke dai-dai. 6 Ba a ma la'akari da adalcina, sai aka ɗauke ni maƙaryaci, raunukana kuma basu warkuwa duk da yake bani da zunubi. 7 Wanne irin mutum ne Ayuba wanda ke shan ba'a kamar ruwa, 8 wanda ke tafiya da ma su yin mugunta, wanda kuma ke rayuwa tare da miyagu. 9 Domin ya ce ba amfani mutum yayi abin da ke mai kyau a gaban Allah 10 Ku saurare ni ku mutane masu fahimta Allah ya sauƙaƙe ace Allah yayi aikin mugunta, kuma Allah ya sha ƙarfin ace yayi zunubi, 11 Domin yana sakawa kowanne mutum gwargwadon aikinsa, kowanne mutum kuma gwargwadon abin da ya aikata. 12 Hakika Allah ba ya aikata mugunta, kuma mai iko dukka bai taɓa watsi da adalci ba 13 Wane ne ya ɗora shi bisa duniya? Wane ne kuma ya ɗora duniya a ƙarƙashinsa? 14 Shi kaɗai ne yasan abin da yake so ya aikata, in har ya taɓa tattaro ruhunsa da numfashinsa, 15 daga nan sai dukkan talikai su lalace mutum kuma ya koma ƙura. 16 I kuna da fahimta yanzu sai ku saurari wannan ku saurari ƙarar kalmomina. 17 Ko wanda yaƙi adalci zai iya yin shugabanci? Ko zaku iya shari'anta Allah? Wanda ke da adalci da kuma girma? 18 Allah wanda ke cewa da sarki kai ɗan tawaye ne? ko kuma ya ce da masu daraja ku miyagu ne'? 19 Allah wanda baya nuna tara ga shugabanni kuma baya la'akari da mawadata fiye da matalauta, domin dukkansu aikin hannunsa ne. 20 A cikin ɗan lokaci sukan mutu; da tsakar dare za a girgiza mutane zasu kuwa shuɗe; za a kwashe ƙarfafan mutane, amma ba ta hannuwan mutum ba. 21 Domin idanun Allah suna bisa hanyoyin mutum; yana ganin dukkan sawayensa. 22 Babu duhu, ko dishi-dishi inda ƙofofin laifofi zasu ɓoye kansu, 23 Domin Allah baya bukatar ya sake yiwa mutum ƙwanƙwanto; babu bukatar kowanne mutum yaje gabansa domin alƙalanci. 24 Ya kakkarya mutane masu girma gunduwa-gunduwa domin tafarkinsu da ke bukatar ƙarin bincike; ya ɗora waɗansu a madadinsu. 25 Ta wannan fannin yasan abin da suke yi; ya kaɓantar da waɗannan mutane da dare an kuma hallakar da su. 26 A idon sauran, ya karkashe su saboda miyagun ayyukansu kamar masu aikata miyagun laifofi, 27 saboda sun juya masa baya sun kuma ƙi yin la'akari da dukkan tafarkunsa. 28 Ta wannan hanya, suka sa kukan mutane matalauta yazo gare shi; yaji kukan waɗanda ake zalunta. 29 In ya yi shiru wane ne zai bashi laifi? in ya ɓoye fuskarsa, wane ne zai ji shi? Yana mulkin al'uma haka kuma kowa, 30 domin kada mutum marar tsoron Allah ya yi mulki, domin kada a sami wanda zai jefa mutane cikin tarko. 31 A misali in a ce wani zai ce da Allah, ' Hakika nayi laifi, amma bazan ƙara yin laifi ba, 32 koya mani abin da bazan gani ba; Nayi zunubi, amma bazan ƙara yinsa ba.' 33 Kana tunanin cewa Allah zai hori zunubin na wancan mutum, tun da yake kun ƙi abin da Allah ke yi? Dole ne kuyi zaɓi, ba ni ba. To sai ku faɗi abin nan da kuka sani. 34 Mutane masu fahimta zasu ce da ni-hakika, duk mutum mai fahimta da ya ji ni zai ce, 35 Ayuba na yin magana ba tare da sani ba; kalmominsa kuma basu da hikima.' 36 In da za a sa Ayuba a ma'auni na ɗan lokaci saboda maganarsa kamar ta miyagun mutane. 37 Domin ya ƙara tawaye a kan zunubinsa; ya tafa hannuwansa cikin zagi a tsakiyarmu; ya jera kalmomi gãba da Allah."

Sura 35

1 Bugu da ƙari Elihu ya ƙara cewa, 2 "Kana tunanin hakan dai-dai ne a lokacin da kayi magana, 'Hakina a gaban Allah'? 3 Domin kayi tambaya, cewa wanne amfani yake da shi a gare ni?' kuma 'Ashe bai fi ba in da a ce nayi zunubi?' 4 Zan amsa maka kai da abokanka. 5 Ka dubi rana a sama, ka gan ta; ka dubi sararin sama wanda ya fi ka tsayi. 6 In ka yi zunubi a ina ka sa Allah ya ji zafi? In laifofinka su jeru zuwa sama, me zaka yi masa? 7 In kana da adalci me zaka iya bashi? Me zai karɓa daga hanunka? 8 Aikin muguntarka na iya cutar da mutum, kamar yadda kake mutum, aikin adalcinka kuma na iya amfanar wani ɗan mutum. 9 Sabo da ayyukana na tsanantawa, mutane suka yi kuka; suka nemi taimako daga damatsan ƙarfafan mutane. 10 Amma ba wanda yace ina Allah mahallicina, wanda ke bada waƙoƙi da dare, 11 wanda ke koyar damu fiye da yadda yake koyar da dabbobin duniya, wanda kuma yasa muka fi tsuntsayen sararin sama hikima?' 12 Suka yi kuka a can amma Allah bai amsa ba saboda girman kan miyagun mutane. 13 Hakika Allah ba zai ji kuka na wawanci ba, maɗaukaki ba zai saurare shi ba. 14 Yaya kuma zai ƙi amsa maka in ka ce baka ganinsa, cewa kuma ƙararka na gabansa, da kuma cewa kana jiransa! 15 Yanzu kuma kuka ce fushinsa baya yin hukunci, kuma baya ko ɗan kula da laifofi. 16 To Ayuba ya buɗe bakinsa domin kawai ya faɗi maganar; ya jera kalmomi ba tare kuma da sani ba."

Sura 36

1 Elihu yaci gaba ya ce, 2 Bani dama in yi magana 'yar kaɗan, zan kuma nuna maka wani abu domin ina da ɗan sauran abin faɗi domin in kare Allah. 3 Zan sami fahimtata daga can nesa; Zan yi la'akari da adalcin da ke na Mahallicina. 4 Domin hakika kalmomina baza su zama ƙarya ba; wani wanda yayi girma cikin sanina tare da kai. 5 Duba Allah mai iko ne, kuma baya rena kowa; yana da ƙarfi cikin ikon fahimta. 6 Baya kiyaye rayukan miyagun mutane, amma a memakon haka ya kan yi abin da ke dai-dai ga waɗanda ke shan wahala. 7 Baya kawar da idanunsa daga adalan mutane amma yakan ɗora su a kursayi kamar sarakuna har abada, kuma sun ɗaukaka sosai. 8 In an ɗaure su da sarƙoƙi da karkiya ta wahala, 9 to sai ya baiyana musu abin da suka yi, da laifofinsu da girman kansu. 10 Hakannan ya buɗe kunnuwansu ga umarnansa, da dokokinsa ya kuma gargaɗe su da su juyo daga aikata laifofi. 11 In sun saurare shi sun kuma yi masa sujada, zasu yi kwanakinsu cikin wadata, shekarunsu kuma cikin wadar zuci. 12 Duk da haka, in basu saurare shi ba, zasu hallaka ta wurin takobi; zasu mutu saboda basu da sani. 13 Marasa tsoron Allah a zuciya na ajiye wa kansu fushi; basu yi kukan neman temako ba koma da a lokacin da Allah ya ɗaure su. 14 Sun mutu cikin ƙuruciyarsu; rayukansu sun kai ga ƙarshe a cikin ɗabi'ar karuwanci. 15 Allah na kuɓutar da waɗanda ake tsananta wa, ya buɗe kunnuwansu ta wurin tsananinsu. 16 Hakika zai so ya jawo ka daga cikin tsanani zuwa wuri inda ba ƙunci, kuma inda za a shirya teburinka da abinci mai cike da kitse. 17 Amma ka cika da hukunci ga miyagun mutane; hukuncisu ne ke riƙe ka. 18 Kar ka yarda fushinka ya ruɗe ka ga yin zagi, ko kuwa girman fansa yasa ka ka kauce. 19 Ko wadatarka zata amfane ka, domin kada ka shiga damuwa, ko kuwa ƙarfinka zai taimake ka? 20 Kada kayi marmarin da zaka yi zunubi ga waɗansu, lokacin da a ka kama mutane a cikin wurarensu. 21 Ka lura domin kada ka koma ga yin zunubi saboda an gwada ka da tsanani domin kada kayi zunubi. 22 Duba Allah ya sami ɗaukaka cikin ikonsa, wane ne mai koyarwa kamarsa? 23 Wa ya taɓa bashi umarni game da tafarkinsa? Wane ne zai iya cewa da shi, ka aikata rashin adalci? 24 Tuna ka yabi ayyukansa, wanda mutane suka rera waƙarsu. 25 Dukkan mutane sun duba waɗannan ayyukan, amma daga nesa ne kawai suke ganin su. 26 Duba Allah nada girma, amma bamu fahimce shi sosai ba; yawan shekarunsa basu ƙidayuwa. 27 Domin ya jawo ɗigon ruwa wanda yasa ya zama ruwan sama daga taskarsa, 28 wanda giza-gizai ke sheƙowa daga sama cikin wadatuwar mutum. 29 Hakika ko akwai wanda zai iya fahimtar yawan faɗin yadda giza-gizai suke da kuma yadda tsawa take daga gare shi? 30 Duba ya shimfiɗa walƙiyarsa a kewaye da shi ya rufe sauyoyin teku. 31 A wannan hanya ya hukunta mutane kuma yana bada abinci a yalwace. 32 Ya cika hannuwansa da walƙiya har sai da ya umarce ta takai iyakarta. 33 Tsawarta takan gargaɗi hadari, dabbobima kan ji tana zuwa.

Sura 37

1 Hakika zuciyata ta firgita a kan wanan; an cire shi daga wurinsa. 2 Ku saurara, i ku saurari ƙarar muryarsa, ƙarar da ke fita daga bakinsa. 3 Ya fitar da ita waje a ƙarƙashin dukkan sararin sama, ya kuma aika da walƙiyarsa zuwa iyakokin duniya. 4 Sai wata murya tayi ruri a bayansa, yayi tsawa da muryar darajarsa; bai hana mariƙin walƙiya ba a lokacin da aka ji muryarsa. 5 Allah yayi tsawa mai ban mamaki da muryarsa; yayi manyan abubuwa da ba zamu iya bada da bayaninsu ba. 6 Domin yace da ƙanƙara, 'faɗo a duniya', haka nan ruwan sama shima ya sheƙo, 'Ya zama babbar mafitar ruwa.' 7 Ya dakatar da hanun kowa daga aiki, domin dukkan mutanen daya hallitta suga ayyukansa. 8 Sai dabbobi su gudu zuwa maɓoya su kuma zauna a kogonninsu. 9 Hadari yakan zo daga mazauninsa a kudu kuma sanyi ya tattaru daga iskar da ta warwatsu a arewa. 10 Ta wurin numfashin Allah a ka bayar da ƙanƙara; sai ruwa ya daskare kamar ƙarfe. 11 Hakika ya kan tarwatsa baƙin girgije da ikonsa; ya warwatsa walƙiyarsa a cikin giza-gizai. 12 Yakan sarrafa giza-gizai ta wurin bishewarsa, domin su yi duk abin da ya umarce su a sararin duniya. 13 Yasa duk wannan ya faru; waɗansu lokutan yana faruwa domin gyara, waɗansu lokutan domin ƙasarsa, waɗansu lokutan su zama ayyukan amintaccen alkawari. 14 Ayuba ka saurari wannan; ka dena kayi tunani kan al'amuran Allah masu girma. 15 Ko ka san yadda Allah ya shimfiɗa giza-gizai ya kuma sa walƙiya ta haskaka a cikin su 16 Ko ka fahimci tashin giza-gizai, da ayyukan ban mamaki na Allah, wanda ke da cikakken sani? 17 Ko ka fahimci yadda tufafinka suka zama da zafi lokacin da ƙasar ta tsaya saboda iska ta taso daga kudu? 18 Zaka iya shimfiɗa rana kamar yadda zai yi, wadda keda ƙarfi kamar madubi an kuma zuba shi kamar ƙarfe? 19 Koya mana abin da za mu ce da shi, domin ba zamu iya shimfiɗa gardamarmu bisa tsari ba saboda duhun tunaninmu. 20 Ko za a faɗa masa abin da naso yi masa magana? Ko mutum zai so a haɗiye shi? 21 Yanzu kuma mutane baza su iya duban rana ba lokacin da tayi zafi a sararin sama ba bayan iska ta wuce ta share giza-gizanta. 22 Daga cikin arewa ake samun wadatar zinariya-a sama Allah ya isa aji tsoronsa cikin daraja. 23 Ga mai iko dukka, ba zamu iya samunsa ba! Yana da girma cikin iko; baya ƙuntatawa adalci da cikakakken adalci. 24 Saboda haka mutane ke tsoronsa. Baya sauraron waɗanda ke da hikima a cikin tunaninsu."

Sura 38

1 Sai Yahweh ya kira Ayuba ta cikin gawurtacciyar guguwa yace, 2 "Wane ne wannan da ke kawo duhu domin shirye shirye ta wurin kalmomin da ba ilimi? 3 Yanzu sai ka yi ɗammara kamar namiji domin zan tambaye ka, kuma dole ne ka ba ni amsa. 4 Ina ka ke sa'ad da na shimfiɗa ginshiƙan duniya? Faɗa mini, in kana da isarshiyar ganewa. 5 Wane ne ke aiyana inda iyakokinta? Faɗa mini, in ka sani. Wane ne ya miƙa fitaccen layi a kan ta? 6 A kan me a ka kafa ginshiƙanta? wane ne ya ɗora dutsen kan kusurwarta? 7 lokacin da taurarin asubahi suka rera waƙa tare kuma dukkan 'ya'yan Allah suka yi sowa domin farinciki? 8 Wane ne ya kulle tekuna da ƙofofi lokacin da suka tumbatsa, inda ta zama kamar tazo daga mahaifa- 9 lokacin da nayi giza-gizai su zama suturarta, kuma baƙin duhu ya zama babbar iyakokinta? 10 Cewa lokacin da nasa alamomi a kan tekuna da kuma iyakokina, 11 da kuma lokacin dana sa kuryoyin ƙofofinta, lokacin kuma da nace da ita, 'Zaki iya zuwa daga wannan nisan, amma ba ci gaba; nan ne zan sa iyakoki ga wannan fahariyar ta raƙuman ruwanki.' 12 Ka taɓa ba da umarni ga safiya, ko ka sa faɗuwar rana ta san wurinta, 13 domin ta jira iyakokin duniya ta kuma kakkaɓe miyagu daga cikin ta? 14 An canja fasalin duniya kamar yadda yunɓu ke canjawa a ƙarƙashin hatimi; dukkan abubuwa sukan tsaya a kanta a sarari kamar gezar sutura. 15 Daga miyagu sai aka ɗauke haskensu; dantsensu da ya ɗaukaka sai aka kakkarya shi. 16 Ka taɓa zuwa maɓɓuɓɓugan ruwan tekuna? ka taɓa yin tafiya a wuri mafi zurfi? 17 Ko an taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa, ka taɓa ganin ƙofofin inuwar mutuwa? 18 Ko ka fahimci duniya da duk cikarta? faɗa mini in ka san ta dukka. 19 Ina hanyar da haske ke bi domin hutawa-game da dare kuma ina nasa wurin? 20 Zaka iya yi wa haske da dare jagora zuwa wuraren aikinsu? Zaka iya samun hanya domin su bi su koma gidajensu! 21 Babu shakka ka sani, domin an haife ka a lokacin; shekarunka kuma suna da yawa! 22 Ka taɓa zuwa ma'ajiyar sino, ko ka taɓa ganin ma'ajiyar ƙanƙara, 23 waɗannan abubuwan da na adana na tsawon lokaci saboda masifa, domin ranar hargitsi da yaƙe-yaƙe? 24 Ina ne sashen da walƙiya ke warwatsuwa ko kuma inda ake warwatsa iska daga gabas akan duniya? 25 Wane ne ya yi kwazazzaban da ruwan damina ke bi, ko kuma wane ne ya yi wa aradu hanya, 26 yasa tayi ruwa a bisa ƙasa inda ba wani mutum da ke wurin, da kuma jeji, inda ba kowa, 27 don ƙosar da yasassun wurare ya kuma sa ciyayi su firfito? 28 Ko ruwan sama yana da uba, ko kuma wane ne ya zama uba ga raɓa? 29 Daga mahaifar wa ƙanƙara ke zuwa? Wane ne ya kafa daɓen hasken sararin sama? 30 Ruwaye kan ɓoye kansu su zama kamar dutse; cikin zurfafa kuma ya zama daskararru 31 Zaka iya kafa sarƙoƙi kan taurari na musamman ko ka datse sarƙar Oriyon? 32 Za ka iya yiwa dandazon taurari jagora su baiyana a lokutan da suka dace? Zaka iya yi wa damisa da 'ya'yanta jagora? 33 Ko ka san sharruɗan sararin sama? Zaka iya saita wurin da sararin sama ke mulki a kan duniya? 34 Zaka iya tada murya har zuwa cikin giza-gizai, domin ruwa mai yawa ya rufe ka? 35 Zaka iya aika cincirindon walƙiya domin su fita, domin suce da kai, ga mu nan'? 36 Wane ne ya bayar da hikima a cikin giza-gizai ko kuma ya bada fahimta ga masu tatsuniya? 37 Wane ne zai iya ƙirga giza-gizai ta wurin fasaharsa? Wane ne zai iya kwararo ruwan sararin sama, 38 lokacin da ƙura ta murtuke ƙasa kuma ta murtuke tare? 39 Zaka iya kamo abin da zakanya zata ci? ko kuma ka iya ƙosar da marmarin 'ya'yan zaki, 40 lokacin da suke kuyakuyai a cikin kogonninsu suke kuma cikin inuwa a ɓoye suna fako? 41 Wake bada kamammu ga hankaki lokacin da ƙananansu suka yi kuka ga Allah suka kuma yi yako saboda ƙarancin abinci?

Sura 39

1 Ko ka san lokacin da awakin jeji ke renon ƙananansu a cikin duwatsu? Zaka iya jira lokacin da kishimai ke maza? 2 Zaka iya ƙirga watannin da suke kammala ɗaukan ciki? Ka san lokacin da suke renon 'ya'yansu? 3 Sukan durƙusa su haifi 'ya'yansu, daga nan su gama zafin naƙudarsu. 4 'Ya'yansu kan yi ƙarfi su yi girma a cikin saura, sai su tafi ba su kuma ƙara dawowa. 5 Wane ne ke 'yantar da jakin jeji? wane ne ke kwance dabaibayin jaki, 6 gidan wa na yi a Arabah, gidansa a ƙasa mai gishiri. 7 Sai ya yi dariyar reni ga hayaniyar cikin birni; ba ya jin tsawar mai tuƙi. 8 Ya yi ta gararanba a kan duwatsu a matsayin makiyayarsa; a can ya yi ta neman koren tsiron da zai ci. 9 Ko takarkarin jeji zai yi murna ya bauta maka? Ko zai so ya tsaya a wurin kwaminka? 10 Za ka iya riƙe jakin jeji da igiya lokacin da ya fusata? Za ka iya baje kwarurruka a lokacin da ya rarake ka? 11 Ka iya amincewa da shi domin yana da ƙarfi sosai? Zaka iya bar masa aikinka yayi maka? 12 Zaka iya dogara gare shi domin ya kawo maka hatsinka gida, ya tattara hatsi domin masussukarka? 13 Fukafukan jimina na da faɗi sosai, to amma ko dogayen gashin fuka-fukan da kuma ƙananan gasusuwan zasu iya kare ta? 14 Domin ta kan bar ƙwaiƙwayenta a ƙasa, ta kan barsu su sha ɗumi a cikin ƙura, 15 takan manta cewa sawaye zasu iya farfasa su ko kuma dabbobin jeji su tattake su. 16 Takan azabtar da 'ya'yanta kamar ba ita ta haife su ba; bata jin tsoro kada naƙudarta ta zama a banza, 17 domin Allah bai bata hikima ba kuma bai bata wani fahimta ba. 18 Lokacin da take gudu takan yi dariyar wulaƙanci ga doki da kuma mahayin dokin. 19 Ka ba doki ƙarfinsa ne? kai ne ka yiwa wuyansa ado da dogon gashi mai sheƙi? 20 Ka taɓa sa shi ya yi tsalle kamar bãbe? Girman haniniyarsa abin tsoro ne. 21 Yana haniniya da ƙarfi, yana kuma murna da ƙarfinsa; yakan fita domin ya tunkari makamai. 22 Ya kan rena tsoro kuma baya alhini; baya kafcewa takobi. 23 Kwari da bãka na hararsa, tare da sheƙin mãshi da dogon ƙarfe mai tsini. 24 Yana haɗiye ƙasa cikin ƙarfi ya murtuke ta a lokacin da ya ji ƙarar ƙaho, baya tsayuwa wuri ɗaya. 25 Duk lokacin da ya ji ƙarar ƙaho, yakan ce, Aha! Ya kan sunsini yaƙi daga nesa-ƙara mai ƙarfi da ihun kwamandoji da hayaniyarsu. 26 Ta wurin hikimarka ne shaho ke miƙar da fuka-fukansa ya fuskanci kudu da su? 27 Ko ta wurin umarninka ne gaggafa ke yin sheƙarta a can ƙonƙoli? 28 Yakan zauna a can ƙonƙolin itace yakan yi sheƙarsa a reɗimar rassa, ya zama mafakarsa. 29 Daga can yake duban abincinsa idanunsa na hangen su daga can nesa, hakanan 30 'Ya'yanta kan sha jini a inda aka karkashe mutane, a can yake.

Sura 40

1 Yahweh yaci gaba da yiwa Ayuba magana cewa, 2 "Ko duk wani da ke ƙoƙarin ganin laifi zai iya ƙoƙarin yi wa Mafi iko dukka gyara? Shi wanda ke gardama da Allah sai ya amsa." 3 Sai Ayuba ya amsawa Yahweh cewa, 4 "'Duba ni da ban can-canta ba; yaya zan amsa maka? Na sa hanunna a kan bakina. 5 Sau ɗaya na yi magana, kuma ba zan amsa ba; hakika sau biyu ne, amma ba zan ci gaba da yi ba." 6 Sai Yahweh ya amsawa Ayuba daga cikin hadari yace, 7 "Yanzu sai ka yi wa kanka ɗammara kamar jarumi, domin zan tambaye ka tambayoyi, kuma dole ne ka amsa mini. 8 Ko hakika za ka ce ba ni da adalci, ko za ka hukunta ni domin ka nuna mini cewa ka yi dai-dai? 9 Ko kana da damatsa kamar na Allah? Ko za ka iya yin tsawa da murya kamar sa? 10 To ka yi wa kanka sutura cikin ɗaukaka da ƙima, ka yi wa kanka kwalliya da daraja. 11 Ka baje kewaye da fushinka, ka dubi kowanne mai fahariya ka ƙasƙantar da shi. 12 Ka duba duk mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake miyagu a inda suke tsayiwa. 13 Ka bisne su tare a ƙasa, ka kulle su a ɓoyayyen wuri, 14 Daga nan zan yi la'akari da kai da kuma sanin cewa hannunka na dama zai cece ka. 15 Yanzu ka duba dodon ruwa, lokacin da nayi a lokacin da na halice ka, yana cin ciyawa kamar takarkari, 16 Yanzu duba, ka ga yadda ƙarfinsa ke ƙirjinsa, ikonsa kuma yana cikin tumbinsa. 17 Ya mayar da bindinsa kamar sidar, haƙoransa a haɗe suke. 18 Ƙasusuwansa kamar cikin ƙarfe suke, ƙafafunsa kuma kamar makaran ƙarfe suke. 19 Shi ne sarki a cikin hallitar Allah. Allahn da ya yi shi ne kawai ke iya kayar da shi, 20 Domin tuddai ne ke ba shi abinci, sauran dabbobi kuma na kusa da wurin suna wasa a kusa. 21 Yana kwance can cikin lollokin ganyaye. 22 Ganyaye masu toho sun rufe shi da inuwarsu duhuwar itatuwa ta shinge shi. Duba 23 Idan rafi yayi ambaliya ba ya fIrgita, yana da ƙarfin hali ko da ruwan Yodan zai kawo masa iya bakinsa. 24 Ko wani zai iya kama shi da ashifta, ko ya iya huda hancinsa ta wurin yaudara?

Sura 41

1 Ko za ka iya jawo Lebiyatan da ƙugiyar kamun kifi? za ka iya ɗaure wuyanta da sarƙa? 2 Za ka iya sa igiya a hancinta? ko ka iya huda cikin bakinta da ƙugiya? lokacin da ta ke yi maka gurnani 3 Ko za ta ji daɗinka? Ko za ta yi maka magana mai lumana? 4 Kuna da yarjejeniya da ita kan cewa ba za ka mai da ita baiwarka ba har abada? 5 ko za ka iya wasa da ita kamar yadda zaka yi da tsuntsu? Za ka iya ɗaure ta kamar bayinka mata? 6 Ko masunta zasu iya ƙulla wata yarjejeniya dominta? Ko zasu iya yin fataucinta a cikin fatake? 7 Za ka cika maɓoyarsa da ƙayayuwa, Ko kansa da mãsun kamun kifi? 8 Ka ɗora hanunka bisansa sau ɗaya tak daga nan za ka san yaƙi ba kuma za ka ƙara yinsa ba. 9 Duba duk mai begen yin hakan ƙarya yake yi; ba wanda za a jefa masa a gabansa da ba zai tattake ba. 10 Ba wanda zai iya tarar dorinar ruwa ba tare da ya furgita ba? 11 Wane ne ya fara ba ni wani abu domin in biya shi? Duk abin da ke ƙarƙashin sararin sama nawa ne. 12 Ba zan yi shiru ba game da ƙafafun dorinar ruwa, da kuma game da al'amarin ƙarfinta ba, ba kuma game da tagomashin hallitar da take da ita ba. 13 Wane ne zai iya yaye masa wannan lulluɓin na samansa? Wane ne zai iya ratsa garkuwoyinsa masu ninki biyu? 14 Wane ne zai iya buɗe ƙofofin fuskarsa-zagaye da haƙoransa masu banrazana? 15 bayansa an yi shi ne da garkuwoyi aka harhaɗa su wuri ɗaya, kamar da wata rufarfiyar alama. 16 Suna marmatse da juna domin kada iska ta iya ratsa su, suna harhaɗe da juna. 17 Suna manne da juna, domin kada a ɓamɓare su. 18 Haske na walƙatawa daga gurnaninsa; haskensa kamar na hasken fitowar rana. 19 Daga cikin bakinsa tartsatsin wuta na fita. 20 Daga cikin hancinsa kuma hayaƙi na fita kamar na matoyar tukunya da ta toyu ta yi zafi sosai. 21 Numfashinsa ne ke samar da gawayin wutar; wuta na fita daga bakinsa. 22 Wuyansa na da ƙarfi, masifa na rawa a gabansa. 23 Maɗaukan jikinsa a harhaɗe suke tare, suna kafe a jikinsa; baza su iya ciruwa ba. 24 Zuciyarsa na da ƙarfi kamar dutse, hakika tana da tauri kamar dutsen niƙa. 25 Sa'ad da ya miƙar da kansa tsaye alloli ma kan firgita saboda tsoro, sukan ja baya. 26 In takobi ya sare shi, ba ya yi masa komai- hakama mãsu da sauran makamai duk ba su yi masa komai. 27 Ya na ganin kibiya kamar rauga ce kawai, namijin ƙarfe kuma kamar abin da tsatsa ta riga ta cinye. 28 Kibiya ba ta sa shi gudu; a gare shi duwatsu masu sulɓi kamar ƙaiƙai suke. 29 Rundunoni kuma kamar tattakar ciyawa; ya kan yiwa walƙiyar kibiya dariya. 30 Ƙananan sassansa kamar rusarshiyar masana'antar tukwane ce, yakan bar wuri a damalmale kamar wurin da a ka yi kwaɓar fitar da zinariya da azurfa. 31 Ya kan haƙa wuri ya yi zurfi ya zama kamar tukunyar dafa ruwa; ya kan mayar da teku ta zama kamar tukunyar mai. 32 Ya kan sa haske ya haskaka bayansa; wani zai yi tunanin yadda zurfin suma mai furfura take. 33 A cikin duniya babu wanda ke dai-dai da shi, wanda aka yi shi ya zama da rashin tsoro. 34 Yana ganin duk wani abu da ke taƙama; shi sarki ne a kan dukan 'ya'yan masu taƙama.

Sura 42

1 Daga nan sai Ayuba ya amsawa Yahweh ya ce, 2 "Na sani zaka iya yin komai, kuma ba wani nufi naka da ba zai cika ba. 3 Wane ne wannan da ke ɓata shiri ba tare da ilimi ba? Hakika, na faɗi abubuwan da ban fahimta ba, abubuwan da ke da wahalar fahimta a gare ni, waɗanda ban sani ba. 4 Ka ce da ni, 'Yanzu ka saurara, zan yi magana; zan tambaye ka abubuwan da za ka faɗa mini'. 5 Na ji labarinka da jin kunnuwana, amma yanzu na ganka. 6 Domin haka na rena kaina ina hurwa cikin toka da ƙura. 7 Sai ya zamana bayan ya faɗi waɗannan maganganu ga Ayuba, sai Yahweh yace da Elifhas Batishmine, fushina yayi ƙuna a kanka da kai da abokanka guda biyu, domin ba ku yi mani maganar da ta dace ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi ba. 8 To yanzu sai ku tanada wa kanku shanu bakwai da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa baiko na ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi muku addu'a, zan kuma amsa addu'arsa, domin kada in yi fushi da ku saboda wawancinku, domin ba ku faɗi abin da ya dace game da ni kamar yadda Ayuba bawana ya yi ba." 9 Sai Elifas da Bildad Bashune, da Zofar Bana'ame suka je suka yi kamar yadda Yahweh ya umarce su, Yahweh kuma ya karɓi Ayuba. 10 Bayan Ayuba ya yi addu'a domin abokansa, Yahweh ya komo masa da wadatarsa. Yahweh ya ninka wa Ayuba wadatarsa fiye da ta dã. 11 Daga nan 'yan'uwan Ayuba mata, da duk waɗanda suka san shi a dã suka zo suka ci abinci tare da shi a gidansa. Suka nuna tausayinsu da kuma ta'aziya a gare shi kan duk asarar da Yahweh ya aukar masa, kowanen su kuma ya ba shi zoben zinariya da kuma azurfa. 12 Yahweh ya albarkaci ƙarshen rayuwar Ayuba fiye da lokacin farko, yana da tumaki dubu goma sha huɗu, raƙuma dubu shida, bijimai dubu ɗaya, da matan jakuna ɗari. 13 Haka nan ya sake samun 'ya'ya bakwai maza da 'ya'ya mata uku. 14 Ya raɗa wa ta fari suna Yemima ta biyun kuma Keziya, ta ukun kuma Keren-Haffuk. 15 A cikin dukkan ƙasar babu matan da aka samu kyawawa da suka kai su kyau, mahaifinsu ya ba su gãdo tare da 'yan'uwansu maza. 16 Bayan wannan Ayuba ya rayu shekaru 140; ya ga 'ya'yansa da kuma jikokinsa. Har zuwa tsara ta huɗu. 17 Bayan nan Ayuba ya mutu cikin tsufa da kuma cikakkun kwanaki.

Littafin Zabura
Littafin Zabura
Zabura 1

1 Albarka ga mutum wanda ba ya tafiya a cikin shawarar miyagu ko ya tsaya a hanyar masu zunubi ko ya zauna tare da masu ba'a. 2 Amma yana jin daɗin shari'ar Yahweh, yana nazarinta dare da rana. 3 Zai zama kamar itacen da aka dasa a gefen ƙorama wanda ya ke bada 'ya'yansa a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, ya kan yi nasara a dukkan abin da ya ke yi. 4 Mugaye ba haka suke ba, amma suna kamar yayi wanda iska ke kwashewa. 5 Saboda haka mugaye ba zasu tsaya a shari'a ba, ko masu zunubi su taru a wurin adalai ba. 6 Gama Yahweh yana lura da hanyar adalai, Amma hanyar mugaye za ta lalace.

Zabura 2

1 Meyasa al'ummai suke shirin tayarwa, kuma don me mutane ke ƙulla shawarwarin banza? 2 Sarakunan duniya ke ɗaukar matsayi tare, masu mulki kuma suna shirya maƙarƙshiya tare su yi gãba da Yahweh da kuma zaɓaɓɓensa Almasihu, cewa, 3 "Bari mu tsaga karkiyar da suka ɗora a kanmu, kuma mu jefar da sarƙoƙinsu." 4 Shi wanda ke zaune a sammai zai yi masu dariya; Ubangiji yana yi masu ba'a. 5 Ya yi masu magana cikin fushinsa da razanar dasu da kuma hasalarsa, cewa, 6 "Ni da kaina na naɗa sarkina a Sihiyona, tsattsarkan dutsena." 7 Zan yi shelar abin da Yahweh ya furta. Ya ce da ni, "Kai ɗana ne! Wannan rana na zama mahaifinka. 8 Ka roƙe ni, zan kuma ba ka al'ummai don gãdonka da yankunan duniya domin su zama mallakarka. 9 Za ka mallake su da sandar ƙarfe; za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu, za ka ragargaza su su farfashe." 10 To yanzu, ku sarakuna, ku ji gargaɗi; ku mai da hankali, ku sarakunan duniya. 11 Ku bauta wa Yahweh da tsoro da kuma murna tare da rawar jiki. 12 Sumbaci ɗan ko ya yi fushi da ku, zaku mutu ta hanyar fushinsa na ɗan lokaci. Albarka ta tabbata ga dukkan waɗanda ke zuwa gare shi neman mafaka.

Zabura 3

Zabura ta Dauda, lokacin da ya guda daga ɗansa Absalom.

1 Yahweh, nawa ne maƙiyana! Nawa ne suka tashi suna gãba da ni. 2 Da yawa suna magana a kaina, "Babu taimako dominsa daga Allah." Selah 3 Amma kai, Yahweh, kai ne garkuwa a gare ni, darajata, kuma wanda ke tallafar kaina. 4 Na yi kira da muryata ga Yahweh, ya kuma amsa mani daga tsattsarkan dutsensa. Selah 5 Na kwanta na kuma yi barci; na farka, gama Yahweh ya tsare ni. 6 Ba zan ji tsoron taron mutane waɗanda suka kewaye ni ta kowanne gefe. 7 Tashi, Yahweh! Ka cece ni, Allahna! Gama zaka buga dukkan abokan gãba har ƙasa; zaka kakkarye haƙuran mugaye. 8 Ceto zai zo daga wurin Yahweh. Bari ya sa wa jama'arsa albarka. Selah

Zabura 4

Domin shugaban mawaƙa; a kayayyakin kiɗa masu tsarkiya. Zabura ta Dauda.

1 Ka amsa mani sa'ad da cikin matsuwa nayi kira, Allahna mai adalci; ba ni hutu a lokacin da nake cikin matsuwa. Ka ji tausayina ka kuma saurari addu'ata. 2 Ku mutanen nan, sai yaushe zaku daina juya ɗaukakata zuwa kunya? Har yaushe zaku yi ta ƙaunar abubuwan banza kuna kuma cigaba da neman abin da ya ke na ƙarairayi? Selah 3 Amma kun sani Yahweh ne ya keɓe mai tsoronsa don kansa. Yahweh zai ji idan na yi kira a gare shi. 4 Ku ji tsoro, domin ku daina zunubi! Ku yi nazari a cikin zukatanku a kan gadajenku, kuma ku yi shuru. Selah 5 Ku miƙa hadayun adalci kuna kuma dogara ga Yahweh. 6 Da yawa sun ce, "Wane ne zai nuna mana wani abu mai kyau? Yahweh, ka ɗaga hasken fuskarka a kanmu. 7 Ka ba zuciyata farinciki fiye da na waɗanda ke da wadatar hatsi da sabon ruwa inabi. 8 A cikin salama zan kwanta har barci ya kwashe ni, domin kai kaɗai ne, Yahweh, ka kiyaye ni cikin lafiya sosai.

Zabura 5

Domin shugaban mawaƙa da kayayyakin kiɗa na bushe-bushe. Zabura ta Dauda.

1 Ka saurari kira na zuwa gare ka, Yahweh; kayi tunani a kan nishe-nishena. 2 Ka saurari muryar kirana, sarkina da Allahna, gama a gare ka nake yin wannan addu'ar. 3 Yahweh, da safe kaji kukana; da safe zan kawo rokona gare ka in kuma jira ka. 4 Gaskiya ne kai ba Allahn dake yarda da mugunta ba ne; ko mugayen mutane su zama bãƙinka. 5 Masu fahariya ba zasu tsaya a gabanka ba; kana ƙin dukkan mugaye. 6 Ka kan hallakar da maƙaryata; Yahweh yakan rena masu ta da hankali da mayaudaran mutane. 7 Amma ni, saboda babban alƙawarin ƙaunarka, zan zo cikin gidanka; in kuma rusuna maka da bangirma a tsattsarkan haikalinka. 8 Ya Ubangiji, ka bida ni in aikata adalcinka domin abokan gãbana; ka kuma fayyace mani hanyarka a gabana. 9 Gama babu gaskiya a cikin bakinsu; abubuwansu mugunta ne; harshensu kamar buɗaɗɗen kabari ya ke; suna yaudara da harshensu. 10 Ka furta su masu laifi ne, Allah; bari shirye-shiryensu su zama dalilin faɗuwarsu! Ka kore su sabili da yawan zunubansu, da kuma tayarwar da suke yi maka. 11 Amma bari dukkan waɗanda suka fake gare ka su yi farinciki; bari kullum su yi ta murna don kana kiyaye waɗanda ke ƙaunar sunanka. 12 Gama ka sawa masu adalci albarka, Yahweh; zaka kewaye su da alheri kamar garkuwa.

Zabura 6

Domin shugaban mawaƙa akan kayan kiɗa masu tsarkiya da aka shirya wa Sheminit. Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, kada ka tsauta mani a lokacin fushinka ko ka hukunta ni da fushinka. 2 Ka yi mani jinƙai, Yahweh, gama na tafke sarai, ka warkar da ni, Yahweh, domin ƙasusuwana na makyarkyata. 3 Raina yana damuwa ƙwarai. Amma kai, Yahweh - har sai yaushe wannan zai ci gaba? 4 Ka zo, Yahweh! ka kuɓutar da ni. Ka cece ni domin alƙawarin amincinka! 5 Gama a cikin mutuwa ba a tunawa da kai. Don wane ne zai yi maka godiya a lahira? 6 Na gaji tilis saboda baƙinciki. Dukkan dare gadona ya kan jiƙe da hawayena; Na jiƙa matashin kaina da hawayena. 7 Idanuna sun yi kumburi saboda kuka; sun zama marasa ƙarfi saboda dukkan abokan gãbana. 8 Ku tafi daga wuri na, dukkan ku masu aikin mugunta; Gama Yahweh ya ji kukana. Yahweh ya ji rokona don jinƙai; 9 Yahweh ya amsa mani addu'ata. 10 Dukkan abokan gãbana zasu sha kunya da babbar damuwa. Zasu juya baya tare da babban ƙasƙanci.

Zabura 7

Haɗe-haɗen waƙoƙin Dauda wanda ya yi wa Yahweh game da maganganun Kush Benyamine.

1 Yahweh Allahna, na sami mafaka a wurinka! Ka cece ni daga dukkan masu nema na, ka ƙwace ni. 2 Idan ba haka ba kuwa zasu ɗauke ni kamar zaki, su yayyaga ni har babu wani da zai kawo mani ceto. 3 Yahweh Allahna, ban aikata abin da maƙiya suka ce nayi ba; babu rashin adalci a cikin hannuwana. 4 Ban yi wani abu da ba dai-dai ga kowa ba wanda muke zaman salama dani, ko da ga wani mai gãba da ni. 5 Idan ba gaskiya nake faɗa ba bari maƙiya su nemi raina har su kama shi; bari ya taka rayayyen jikina a ƙasa ya bar ni da kunyata a ƙura. Selah 6 Ka tashi, Yahweh, cikin fushinka; tashi kayi gãba da hasalar abokan gãbana; ka tashi domina ka aiwatar da alƙawarin amincinka da aka sanka da shi. 7 Dukkan kabilu sun taru a gabanka; ka sake ɗaukar wurinka a bisan su. 8 Yahweh, kai ne alƙalin dukkan alummai; ka 'yantar da ni, Yahweh, gama ni adali ne bani da laifi, Maɗaukaki. 9 Bari mugun abu na masu aikata mugunta ya zo ƙarshe, amma ka tabbatar da adalan mutane, Allah mai adalci, kai kake gwada zukata da tunane-tunane. 10 Kariyata tana zuwa daga Allah, wanda ya ke ceton masu yin adalci a zuciya. 11 Allah ne alƙali mai adalci, Allah wanda ya ke jin haushi a kowacce rana. 12 Idan mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa ya kuma shirya bakansa don yaƙi. 13 Zai shirya kayayyakin faɗa gãba da shi; zai auna kibansa masu wuta. 14 Ka yi tunani akan wanda ya ɗauki ciki da mugunta, wanda ya shirya aiwatar da mugunta, wanda ya haifi cutar ƙarairayi. 15 Yana haƙa rami mai zurfi har kuma ya faɗa ramin da ya gina. 16 Mugun shirin da yayi ya koma a kansa kenan, don rikicin ya sauka a kansa kenan. 17 Zan gode wa Yahweh saboda adalcinsa; zan raira yabo ga Yahweh Maɗaukaki.

Zabura 8

Domin shugaban mawaƙa; tsari na salon waƙar bagitte. Zabura ta Dauda.

1 Yahweh Ubangijinmu, yaya girman sunanka ya ke a dukkan duniya, ka bayyana ɗaukakarka a cikin sammai. 2 Daga cikin bakin yara da jarirai ka shirya yabo domin maƙiyanka, domin ka tsai da abokan gãbarka da ramako. 3 Sa'ad da na duba sararin sammai, wanda yatsunka suka yi, wata da taurari, waɗanda kasa a wuraren zamansu. 4 Mene ne mahimmancin 'yan adam har da kake tunawa da su, ko mutune har da kake lura da su? 5 Duk da haka ka maida su ƙasa kaɗan da halittun dake sama ka kuma naɗa su da ɗaukaka da daraja. 6 Ka sa shi yayi mulkin dukkan abin da kayi da hannuwanka; ka ɗora dukkan abubuwa a ƙarƙashin ƙafafuwansa: 7 dukkan tumaki da shanu har ma da namomin jeji, 8 tsuntsayen sammai da kifayen teku da dukkan halittun dake cikin tekuna. 9 Yahweh Ubangijinmu yaya girman sunanka ya ke a cikin dukkan duniya!

Zabura 9

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsara bisa salon Mut Labben. Zabura ta Dauda.

1 Zan yi maka goɗiya Yahweh da dukkan zuciyata; zan furta dukkan abubuwa masu ban mamaki da ka yi. 2 Zan yi murna da farinciki da kai; zan raira waƙar yabo ga sunanka Maɗaukaki! 3 Lokacin da magabtana suka ja da baya, sun faɗi sun mutu a gabanka. 4 Gama kai ka tsare ni; ka zauna a kan kursiyinka, mai shari'ar adalci! 5 Ka kwaɓi al'ummai, ka kuma hallakar da mugaye; ka kawar da sunayensu har abada abadin. 6 An rugurguje abokan gãba kamar kangaye a lokacin da aka lalata biranensu. Dukkan tunawa dasu ya ƙare. 7 Amma Yahweh ka kasance har abada; ka kafa kursiyinka domin yin shari'a. 8 Zan yi mulkin dukkan duniya da adalci, kuma zai yi wa mutane shari'a da gaskiya. 9 Yahweh kuma zai zama mafaka ga waɗanda ake zalunta, wurin ɓuya a lokatan wahala. 10 Waɗanda suka san sunanka zasu dogara gare ka, domin kai ne, Yahweh, ba za ka yi watsi da duk wanda ya neme ka ba. 11 Ku yi waƙar yabo ga Yahweh, wanda ke mulki a Sihiyona; ku faɗa wa al'ummai abin da ya yi. 12 Gama Allah wanda ke ramakon jinin da aka zubar na tunawa; baya mantawa da kukan waɗanda ake cutar su. 13 Ka yi mani jinƙai, Yahweh; dubi yadda waɗanda ke gãba da ni suka wulaƙanta ni, kaine wanda zai kuɓutar da ni daga ƙofofin mutuwa. 14 Dãma inyi shelar dukkan yabonka. A ƙofofin budurwar Sihiyona zan yi farincikin cetonka! 15 Al'ummai sun faɗa cikin ramin da suka haƙa; tarkon da suka kafa don su buya ya kama ƙafafuwansu. 16 Yahweh ya bayyana kansa; ya gudanar da shari'a; mugu ya kama kansa da abubuwan da ya aikata. Selah 17 An maida miyagu makomarsu a Lahira, rabon dukkan waɗanda suka manta da Allah. 18 Gama ba kullum ne ake mantawa da masu buƙata ba ko masu bege waɗanda ake zalunta zasu ɓace har abada. 19 Ka tashi, Yahweh; kada ka bar mutum yayi nasara da kai; bari a yiwa al'ummai hukunci a gabanka. 20 Tsoratar da su, Yahweh; bari al'ummai su sani su mutane ne kawai.

Zabura 10

1 Yahweh don me kake tsaye, a can nesa? Me ya sa ka ɓoye kanka a lokatan wahala? 2 Domin fahariyarsu, mugayen mutane na tsananta wa matalauta; amma bari tarkon da mugaye suka ɗana ya kama su. 3 Gama mugun mutum yana fahariya da manufofinsa; yana albarkatar haɗamarsa har yakan zagi Yahweh. 4 Mugun mutum yana ɗaga fuska; ba ya neman Allah. Ba ya tunani a kan Allah domin bai damu ya kula da dukkan al'amura a kansa ba. 5 Ya kan yi nasara a dukkan lokatai, domin adalcin dokokinka sun yi masa tsada; yana furci a kan abokan gãbansa. 6 Ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zan taba faɗuwa ba; a cikin dukkan tsararraki ba zan sadu da wahala ba." 7 Maganganunsa suna cike da zage-zage da yaudara, da mugayen kalmomi; harshensa kuma mai hatsari ne da hallakar wa. 8 Yana kwanto kusa da ƙauyuka; a ɓoyayyun wurare har ya kashe marasa laifi; idanuwansa kuma suna duban waɗanda baza su iya yin komai ba. 9 Yana jira a inda ya ɓuya kamar zaki a cikin kurmi; ya kan kwanta yana fakon wanda zai kama lokacin da yasa tarkonsa. 10 Kamammunsa kuma an buga su har ƙasa; suka faɗa cikin ƙaƙƙarfan ragarsa. 11 Ya ce a cikin zuciyarsa, "Allah ya manta; ya rufe fuskarsa; ba zai damu ya duba ba." 12 Tashi, Yahweh! Ɗaga hannunka, Allah! Kada ka manta da waɗanda ake tsanantawa. 13 Me yasa mugun mutum zai ƙi Allah har ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zai kama ni da wani alhaki ba"? 14 Kana kula da komai, don kullum kana ganin wanda ake sa masa damuwa da baƙinciki. Kana sa mai bukata yasa dogararsa a gare ka; kana kuɓutar da marasa iyaye. 15 Ka karya hannun mugu da mai aikata mugunta. Kasa ya ɗauki laifin mugun aikinsa, kada ya yi tunanin ba za a taba ganewa ba. 16 Yahweh Sarki na har abada abadin; al'ummai kuma za a kore su daga ƙasarsa. 17 Yahweh, ka ji buƙatun wanda ake tsanantawa; ka karfafa zukatansu, ka saurari addu'arsu. 18 Zaka kãre marasa iyaye da waɗanda ake ƙuntata masu saboda babu wani mutum a wannan duniya da zai sake jawo razana.

Zabura 11

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Na sami mafaka a wurin Yahweh; yaya zaka ce da ni, "Ka tashi kamar tsuntsu akan tsauni"? 2 Amma duba! miyagu sun shirya ƙibansu a kan tsarkiya don su harba cikin duhu a zuciyar adali. 3 Gama idan ginshiƙai suka lalace, mene ne adali zai iya yi? 4 Yahweh yana cikin tsatsarkan haikalinsa; idanuwansa suna kallo, idanuwansa suna gwada 'ya'yan 'yan adam. 5 Yahweh yana gwada masu kirki da miyagu dukka, amma yana ƙin waɗanda ke ƙaunar tashin hankali. 6 Yana ruwan garwashin wuta da ƙibiritu a kan mugaye; iska zata kone rabonsu daga finjilinsa! 7 Gama Yahweh mai adalci ne, yana kuma ƙaunar masu gaskiya; adalai kuma zasu ga fuskarsa.

Zabura 12

Domin shugaban mawaƙa; da aka shirya wa Sheminit. Zabura ta Dauda.

1 Ka yi taimako, Yahweh, saboda mutanen kirki sun ɓace; aminitattu ma sun ɓace. 2 Kowanne mutum yana maganar banza ga maƙwabcinsa; kowanne yana maganar yaudara da leɓuna da zuciya biyu. 3 Yahweh, ka datsa dukkan leɓunan yaudara, kowanne harshe ya riƙa faɗin manyan abubuwa. 4 Waɗannan sune waɗanda suka ce, "Ta wurin harshenmu zamu rinjaya. Sa'ad da leɓunanmu suka yi magana, wane ne zai zama gwani a bisanmu?" 5 "Saboda tashin hankali akan matalauta, domin nishin masu buƙata, zan tashi," inji Yahweh. "Zan basu tsaron da suka yi marmari." 6 Kalmomin Yahweh kalmomi ne zalla, kamar azurfar da aka narkar a tanderun wuta, aka tace har sau bakwai. 7 Kai ne Yahweh! Ka kiyaye su. Ka tsare mutanen kirki daga muguwar tsara har abada. 8 Mugaye suna tafiya ko'ina a lokacin da mugunta ke ɗaukaka a cikin 'yan adam.

Zabura 13

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, har sai yaushe, za ka ci gaba da mantawa da ni? Har yaushe ne zaka ɓoye mani fuskarka daga gare ni? 2 Har yaushe ne zan daina damuwa da baƙinciki a zuciyata dukkan yini? Har yaushe ne maƙiyana zasu rika cin nasara a kaina? 3 Ka dube ni ka kuma amsa mani, Yahweh Allahna! Ka bani haske ga idanuwana, ko in yi barcin mutuwa. 4 Kada ka bar maƙiyina ya ce, "Na ce nasara a kansa," don kada maƙiyina ya sami abin cewa, "Na yi rinjaye akan abokin gãbana;" idan ba haka ba, maƙiyina zai yi murna saboda faɗuwata. 5 Amma na dogara ga amintaccen alƙawarinka; zuciyata zata yi murna da cetonka. 6 Zan yi waƙa ga Yahweh domin ya yi mani abin kirki ƙwarai.

Zabura 14

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Wawa yace a cikin zuciyarsa, "Ba Allah." Sun lalace sun kuma aikata laifin ban ƙyama; babu wani wanda ya aikata nagarta. 2 Yahweh ya duba ƙasa daga sama a kan 'yan adam ya gani idan ko akwai wani mai fahimta, wanda ke neman sa. 3 Dukkansu sun koma baya. Ga baki ɗayansu sun zama marasa kirki. Ba wanda ya ke aikata abin da ya ke dai-dai, babu ko ɗaya. 4 Sun san wani abu, waɗanda suka aikata laifi, waɗanda suke cin mutanena kamar yadda suke cin gurasa, amma wane ne ba ya kiran Yahweh? 5 Sun razana tare da fargaba, gama Allah yana tare da taruwar adalai! 6 Kuna so ku ci mutuncin matalaucin mutum koda ya ke Yahweh ne mafakarsa. 7 Oh, dama ceton Isra'ila zai zo daga Sihiyona! Sa'ad da Yahweh ya dawo da mutanensa daga bauta, Yakubu zai yi murna, Isra'ila ma zata yi farinciki!

Zabura 15

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, wane ne zai iya tsaya wa a rumfar sujadarka? Wa zai iya zama a tudun ka mai tsarki? 2 Duk wanda ba shi da laifi, wanda ke aikata abin dake dai-dai wanda kuma ya ke faɗar gaskiya daga zuciyarsa. 3 Wanda baya ɓatanci da harshensa, baya cin mutuncin wasu, baya ɓatanci ga maƙwabcinsa. 4 Mutumin wofi abin reni ne a idanunsa, amma yana girmama waɗanda ke tsoron Yahweh. Yana rantsuwa ba don kansa ba, kuma yana cika alƙawaran da yayi. 5 Baya karɓar ruwa a kuɗin da ya bayar bashi. Baya karɓar cin hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Duk wanda ya ke yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa girgiza ba.

Zabura 16

Salon waƙar Dauda.

1 Ka tsare ni, Allah, gama na zo neman mafaka a gare ka. 2 Na ce da Yahweh, "Kai ne Ubangijina; nagarta ta a banza take idan bana tare da kai. 3 Kamar yadda tsarkakakkun mutane waɗanda ke a duniya, su mutane masu kirki; dukkan murnata a gare su take. 4 Wahalolinsu zasu ƙaru, waɗanda ke neman waɗansu gumaka. Ba zan zubo masu da baye-baye na shan jinin allolinsu ba ko in furta sunayensu da leɓuna na ba. 5 Yahweh, kaine kaɗai na zaɓa da ƙoƙona. Kai ne kake riƙe da rabona. 6 An ajiye ma'aunan layi domina a wuraren jin daɗi; babu shakka gãdon dake kawo jin daɗi nawa ne. 7 Zan albarkaci Yahweh, wanda ke bani shawara; ko da dare ma ina tunanin umarninsa. 8 Na sa kaina a wurin Yahweh a dukkan lokuta, saboda kada in girgiza daga hannun damarsa! 9 Don haka cike nake da murna; ɗaukakata na farinciki. Babu shakka zan zauna a cikin tsaro. 10 Saboda baza ka bar raina a Lahira ba. Ba zaka bar amintaccenka ya ga rami ba. 11 Ka koya mani hanyar rai; yalwataccen farinciki na kasancewarka; murna zata zauna a hannun damarka har abada!"

Zabura 17

Addu'ar Dauda.

1 Ka kasa kunne ga roƙona don adalci, Yahweh; ka saurari kirana na neman taimako! Ka kasa kunne ga addu'ata daga leɓuna marasa yaudara. 2 Bari baratarwata ta zo daga wurinka; bari idanuwanka su ga abin dake dai-dai! 3 Idan zaka gwada zuciyata, idan zaka zo gare ni da dare, zaka tsarkakeni ba kuma za a sami wata mugunta a shirye-shiryena ba; bakina ba zai yi saɓo ba. 4 Game kuma da ayyukan mutane; sune a cikin maganar leɓunanka waɗanda na tsare kaina daga hanyoyi na marasa bin doka. 5 Na yi tafiya a kan tafarkinka sosai; sawayena basu kauce ba. 6 Na yi kira a gare ka, domin ka amsa mani, ya Allah; ka juyo da kunnenka gare ni ka kuma saurara a lokacin da na yi magana. 7 Ka nuna mani amintaccen alƙawarinka ta hanya mai banmamaki, kai da ke yin ceto ta hannun damarka ga waɗanda ke neman mafaka a gare ka daga maƙiyansu! 8 Ka tsare ni kamar ƙwayar idanunka; ka ɓoye ni a ƙarƙashin inuwar fukafukanka 9 daga fuskar miyagu waɗanda ke zargi na, maƙiyana da suka kewaye ni. 10 Basa jin tausayin kowa; bakunansu na magana da fahariya. 11 Sun kewaye sawayena. Sun sa idanuwansu don su fyaɗa ni ƙasa. 12 Su kamar zakoki ne sun ƙosa su ga abin da zasu hallaka, kamar 'ya'yan zakoki suna laɓe a ɓoyayyun wurare. 13 Ka tashi, Yahweh! Ka hare su! Ka jefar da su a ƙasa a kan fuskokinsu! Ka cece raina daga takobin mugaye! 14 Yahweh, ka cece ni daga gare su da hannun ka, daga mutanen wannan duniya waɗanda arziƙinsu a cikin wannan rayuwa ne kaɗai! Za ka cike wuraren ajiyar mutanenka da arziki; zasu zama da 'ya'ya dayawa kuma zasu bar wadatarsu ga 'ya'yansu. 15 Amma ni, zan ga fuskarka a cikin adalci; zan gamsu, sa'ad da na farka, da ganin ka.

Zabura 18

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda, baran Yahweh, sa'ad da ya rera wa Yahweh maganganun wannan waƙa a ranar da Yahweh ya kuɓutar da shi daga hannun dukkan maƙiyansa da kuma hannun Saul. Ya raira waƙa cewa:

1 Ina ƙaunarka, Yahweh, ƙarfina. 2 Yahweh ne dutsena, hasumiya ta, wanda ke kawo mani tsaro; shi ne Allahna, dutsena; zan ɓoye a cikinsa. Shi ne garkuwata, ƙahon cetona, shi ne kuma ƙarfina. 3 Zan yi kira ga Yahweh wanda ya cancanci a yabe shi, za a kuma cece ni daga maƙiyana. 4 Sarƙoƙin mutuwa sun kewaye ni, hargowar ruwaye marasa daraja sun sha kaina. 5 Sarƙoƙin Lahira sun kewaye ni; tarkon mutuwa kuwa ya kama ni. 6 A cikin ƙuncina na yi kira ga Yahweh; na yi kiran neman taimako ga Allahna. Ya ji muryata daga haikalinsa; kirana na neman taimako ya kai gare shi; ya shiga har cikin kunnuwansa. 7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza; ginshiƙan duwatsu kuwa suka jijjigu suka kuma yi rawar jiki saboda Allah ya husata. 8 Hayaƙi kuwa ya yi ta tuƙaƙowa daga kafofin hancinsa, harshen wuta ya fito daga bakinsa. Gawayin garwashi suka fita ta wurinsa. 9 Ya buɗe sammai ya sauko ƙasa, duhu kuma baƙiƙƙirin na ƙarƙashin ƙafafunsa. 10 Ya hau kan kerub ya tashi; ya yi tafiya a kan fikafikan iska. 11 Ya maida duhu rumfa a kewaye da shi, gizagizan ruwan sama masu nauyi a sararin sama. 12 Ƙanƙara da garwashin wuta sun faɗo daga walƙiya dake gabansa. 13 Yahweh ya yi tsawa a cikin sammai! Muryar Maɗaukaki ta yi tsawa. 14 Ya harba kibansa, ya warwatsar da magabtansa; walƙatawar walƙiyoyi ta warwatsar da su. 15 Daga nan hanyoyin ruwa suka bayyana; ginshiƙan duniya dukka aka bayyana su a cikin kukan yaƙinka, Yahweh- a cikin hurawa mai ƙarfi ta numfashin kafofin hancinka. 16 Ya miƙo hannunsa ƙasa daga samaniya; ya riƙe ni! Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi. 17 Ya kuɓutar da ni daga ƙaƙƙarfan abokin gãbata, daga waɗanda ke ƙi na, domin sun fi ni ƙarfi sosai. 18 Sun tasar mani a ranar shan ƙuncina amma Yahweh ne mai taimako na! 19 Ya fitar da ni daga hatsari a buɗaɗɗen wuri; ya cece ni domin yana farinciki dani. 20 Yahweh ya sãka mani saboda adalcina; ya dawo da ni saboda hannuwana na da tsarki. 21 Domin na kiyaye tafarkun Yahweh ban kuma juya ga mugunta daga Allahna ba. 22 Gama dukkan ka'idodinsa na adalci suna gaba na; game kuma da fariilansa, ban kauce daga gare su ba. 23 Na kuma zama marar laifi a gabansa, na kiyaye kaina daga zunubi. 24 Domin haka Yahweh ya dawo dani saboda adalcina, domin hannuwana masu tsafta ne a idanunsa. 25 Ga kowanne mai aminci, kana nuna kanka mai aminci; ga mutum marar laifi, ka nuna kanka marar laifi. 26 Ga duk wani mai tsarki, ka nuna kanka mai tsarki; amma kana da dabara ga duk mai aikin mugunta. 27 Gama kana ceton mutane daga wahala, amma ka kan ƙasƙantar da masu girmankai da suka ɗaga idanunsu! 28 Domin ka bada haske ga fitilata; Yahweh Allahna ka haskaka duhuna. 29 Gama ta wurinka zan iya tserewa maƙiyana; ta wurin Allahna zan iya tsallake saman katanga. 30 Kamar yadda Allah ya ke, hanyarsa dai-dai take. Maganar Yahweh tsartsarka ce! Shi garkuwane ga duk wanda yake neman mafaka a wurinsa. 31 Gama wane ne Allah sai Yahweh? Wane ne dutse in ba Allahnmu ba? 32 Shi ne Allahn dake ƙarfafa ni kamar ɗammara, wanda ya ke sa mutanen da basu da aibu a kan hanyarsa. 33 Yana tabbatar da lafiyar ƙafafuna kamar barewa ya kuma sa ni a bisa! 34 Yakan koyar da hannuwana don yaƙi makamaina kuma za su tankware bakan tagulla. 35 Kai ka bani garguwar cetona. Hannunka na dama yana ƙarfafa ni, tagomashinka kuma ya maida ni babba. 36 Kayi mani buɗaɗɗen wuri don ƙafafuwana suna ƙarƙashina saboda kada santsi ya ɗauke ƙafafuwana. 37 Na kori maƙiyana har na kama su; ban juya ba har sai da na lalata su dukka. 38 Na buga su har ba wanda zai iya tashi; sun faɗi a ƙarƙashin ƙafafuna. 39 Gama ka sa ƙarfi a kaina kamar ɗamara don yaƙi; ka sa waɗanda ke gãba da ni a ƙarƙashina. 40 Ka bani nasara akan maƙiyana; zan hallaka waɗanda ke gãba da ni. 41 Suna kira don taimako, amma babu wani da ya cece su; sun yi kira ga Yahweh, amma bai amsa masu ba. 42 Na buge su har sun zama gutsu-gutsu kamar ƙura a fuskar iska; na jefar da su waje kamar laka a tituna. 43 Ka cece ni daga mutane masu husuma. Ka maida ni shugaba a kan al'ummai. Mutanen da ban san su ba, ban ma yi masu aiki ba. 44 Yayin da suka ji ni, zasu yi mani biyayya; bãƙi zasu rusuna mani dole. 45 Bãƙin zasu zo da rawar jiki daga kagarunsu. 46 Yahweh mai rai ne; dutsena abin yabo. Allah mai cetona a gimama shi. 47 Shi ne Allah wanda ya ke ɗaukar fansa domina, yana sawa a rinjaye al'ummai a ƙarƙashina. 48 Ni 'yantacce ne daga maƙiyana! Lalle, ka ɗaukaka ni sama da waɗanda suka taso suna gãba da ni! Ka cece ni daga mutane masu tawaye. 49 Saboda haka zan yi yabo a gare ka, Yahweh, a cikin al'ummai; zan raira maka waƙar yabon sunanka! 50 Allah yana bada babbar nasara ga sarkinsa, ya kan nuna amintaccen alƙawarinsa ga wanda ya zaɓa, ga Dauda da zuriyarsa har abada.

Zabura 19

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Sammai na bayyana ɗaukakar Allah, sararin sama kuma na bayyana ayyukan hannunsa! 2 A kowacce rana ana fitar da magana; dare bisa dare na bayyana ilimi. 3 Babu magana ko kalma da aka furta; ba a ji amonsu ba. 4 Duk da haka maganarsu ta tafi dukkan duniya, jawabinsu kuma har ƙarshen duniya. Ya kafa rumfa domin rana a cikinsu. 5 Rana kamar ango na taƙama daga kagararsa, kuma kamar ƙaƙƙarfan mutum wanda ke farinciki idan ya ƙosa ya yi tsere. 6 Rana tana fitowa daga ɗaya gefen zuwa ɗaya tsallaken; ba abin da zai tsere daga zafinta. 7 Dokar Yahweh cikakkiya ce, tana wartsakar da rai; shaidar Yahweh kuwa abar dogara ce, tana ba da hikima ga masu buƙata. 8 Ka'idodin Yahweh dai-dai suke, tana sa zuciya ta ji daɗi; umarnin Yahweh na da kyau, yana kawo haske ga idanuwa. 9 Tsoron Yahweh tsabbatacce ne, tabbatacce ne har abada; dokokin Yahweh gaskiya ne dukkansu dai-dai suke! 10 Suna da girma da daraja fiye da zinariya, fiye ma da zinariyar da aka tace; sun fi zuma zaƙi, zuman dake ɗigowa daga saƙarsa. 11 I, ta wurinsu bawanka ya sami gargaɗi; akwai lada mai girma idan an yi biyayya dasu. 12 Wane ne zai iya rarrrabe kuskuren kansa? Ka tsabtacce ni daga ɓoyayyun laifuffuka. 13 Ka tsare bawanka kuma daga zunubai marasa kangado; kada ka bari su yi mulki a kaina. Sa'an nan ne zan zama kamili, zan kuma zama mara laifi daga laifuffukana masu yawa. 14 Ka sa maganar baƙina da tunanin zuciyata su zama abin karɓa a wurinka, Yahweh, dutsena da fansata.

Zabura 20

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Bari Yahweh ya taimake ka a ranar wahala; bari sunan Allah na Yakubu ya tsare ka, 2 ya kuma aika taimako daga wuri mai tsarki ya kawo maka tallafi daga Sihiyona. 3 Bari ya tuna da dukkanbaye-bayenka ya kuma karɓi hadayun ƙonawarka. Selah 4 Ya biya maka buƙatar zuciyarka, ya kuma cika maka dukkan shirye-shiryenka. 5 Sai mu yi sowa ta farinciki saboda ka ci nasara, a cikin sunan Allahnmu, zamu ɗaga tutoci. Yahweh zai biya dukkan roƙe-roƙenmu. 6 Yanzu dai na sani Yahweh zai ceci zaɓaɓɓensa; zai amsa masa daga wurinsa mai tsarki a sama da iko a hannun damarsa wanda ya cece shi. 7 Waɗansu sun dogara ga karusansu wasu kuma ga dawakansu, amma mu muna kira ga Yahweh Allahnmu. 8 Su zasu yi tuntuɓe har su faɗi ƙasa, amma mu zamu tashi mu tsaya daram! 9 Yahweh, ka ceci sarki; ka taimake mu sa'ad da muka yi kira.

Zabura 21

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Sarki na yi farinciki cikin ƙarfinka, Yahweh! Babu iyaka ga farincikinsa daga cikin ceton da ka tanada! 2 Ka biya masa buƙatar zuciyarsa baka kuma hana masa roƙon leɓunansa ba. Selah. 3 Gama ka kawo masa albarku masu wadata; ka sanya bisa kansa kambi na tsabar zinariya. 4 Ya nemi rai daga gare ka; ka bashi; ka bashi tsawon kwanaki har abada abadin. 5 Darajarsa na da girma sabili da nasarar ka; ka ɗibiya masa daraja da ɗaukaka. 6 Gama ka bashi madawwaman albarku; ka sashi jin daɗi da farinciki da ke a gabanka. 7 Gama sarki yana dogara ga Yahweh; ta wurin alƙawarin amincin Maɗaukaki ba zaya jijjigu ba. 8 Hannunka zaya kama dukkan maƙiyanka; Hannunka na dama zaya kama waɗanda suka ƙi ka. 9 A lokacin hasalarka; zaka ƙona su sarai kamar daga cikin tanderu mai ƙuna. Yahweh zai haɗiye su cikin hasalarsa, kuma wutar za ta cinye su. 10 Zaka hallakar da zuriyarsu daga ƙasar kuma zuriyarsu daga cikin 'yan adam. 11 Gama sun shirya yi maka mugunta; sun tsiro da shiri wanda ba za su iya yin nasara ba! 12 Gama za ka sa su koma da baya; zaka jã kwarinka a fuskarsu. 13 Ka ɗaukaka, Yahweh, cikin ƙarfin ka; zamu raira waƙa mu kuma yaɓi ikonka.

Zabura 22

Domin shugaban mawaƙa; an tsara bisa ga tsallen barewa. Zabura ta Dauda.

1 Allahna, Allahna, me yasa ka yashe ni? Me yasa ka yi nisa daga ƙubutar da ni kuma kayi nisa daga muryata ta azaba? 2 Allahna, na yi kuka da tsakar rana, amma baka amsa mani ba, da dare kuma ban yi shuru ba! 3 Amma kai mai tsarki ne; kana zaman sarki tare da yabon Isra'ila. 4 Iyayenmu sun dogara gare ka; sun dogara gare ka, ka kuma ƙubutar da su. Sun yi kira gare ka an kuma ƙuɓutar da su. 5 Sun dogara gare ka basu kuma kunyata ba. 6 Amma ni tsutsa ne ba mutum ba, abin kunya ga "yan adam da kuma abin raini ga mutane. 7 Dukkan waɗanda suka ganni suka cakune ni; suka yi mani haibaici; suka kaɗa mani kai. 8 Suka ce, "Ya dogara ga Yahweh; bari Yahweh ya kuɓutar da shi. Bari ya kuɓutar da shi, gama yana fahariya da shi." 9 Gama ka fito dani daga mahaifa; ka sa in dogara gare ka a sa'ad da nake shan nono wurin mahaifiyata. 10 Tun daga mahaifa aka jefo ni gare ka; kai Allahna ne tun daga mahaifar mahaifiyata! 11 Kada ka yi nisa dani, gama damuwa na kusa; babu wani mai taimako. 12 Bajimai masu yawa sun kewaye ni; Bajimai masu ƙarfi na Bashan suna zagaye dani. 13 Sun buɗe bakinsu da girma gãba dani kamar zaki mai ruri yana yagar abin da ya kama. 14 An kwararo ni kamar ruwa, kuma dukkan ƙasusuwana sun goce. Zuciyata kamar kitse; ta narke daga cikin cikina. 15 Ƙarfina ya bushe kaf kamar fasasshiyar tukunya; harshena ya manne sama a bakina. Ka kwantar da ni a cikin ƙurar mutuwa. 16 Gama karnuka suka zagaye ni; taron masu aikata mugunta suka kewaye ni; suka huda hannuwana da ƙafafuna. 17 Zan iya ƙirga ƙasusuwana. Suka duba suka kuma zura mani ido. 18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, suka jefa ƙuri'a a bisa kayana. 19 Kada ka yi nisa, Yahweh; ina roƙon ka kayi sauri domin ka taimake ni, ƙarfina! 20 Ka kuɓutar da raina daga takobi, raina ɗaya daga hannuwan karnukan daji. 21 Ka cece ni daga bakin zaki; ka kuɓutar dani daga ƙahonni na shanun daji. 22 Zan furta sunanka ga 'yan'uwana; a tsakiyar taruwar jama'a zan yabe ka. 23 Ku da kuke tsoron Yahweh, yabe shi! Dukkan ku zuriyar Yakubu, girmama shi! Ku tsaya cik cikin tsoronsa, dukkan ku zuriyar Isra'ila! 24 Gama baya rena ko yayi banza da wahalar ƙuntattu ba; Yahweh baya ɓoye fuskarsa daga gare shi ba; a lokacin da ƙuntacce yayi kira gare shi, ya ji. 25 Yabona zai zama sabili da kai a cikin babban taron jama'a; Zan cika wa'adina a gaban waɗanda ke tsoron sa. 26 Tsanantattu za su ci su ƙoshi; Waɗanda suka nemi Yahweh zasu yabe shi. Bari zukatanku su rayu har abada. 27 Dukkan mazamnan duniya zasu tuna su kuma juyo ga Yahweh; dukkan iyalan al'ummai zasu durƙusa a gabanka. 28 Gama mulki na Yahweh ne; shi yake mulki bisa al'ummai. 29 Dukkan mawadatan mutanen duniya za su yi buki su kuma yi sujada; dukkan su masu gangarawa zuwa turɓaya zasu durƙusa a gabansa, su waɗanda baza su iya adana rayyukansu ba. 30 Tsara mai zuwa zata yi masa hidima; zasu gaya wa tsara ta gaba game da Ubangiji. 31 Zasu zo su kuma yi magana game da adalcinsa; zasu faɗi abin da yayi ga mutanen da ba a haife su ba.

Zabura 23

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh makiyayina ne; ba zan rasa komai ba. 2 Yana sa ni in kwanta a cikin korayen makiyayu; yana bi da ni kurkusa da kwantaccen ruwa. 3 Ya maido da raina; yana bishe ni ta tafarku madaidaita domin sunansa. 4 Ko da ina tafiya ta cikin kwari na inuwa mafi duhu, ba zan ji tsoron cutarwa ba tun da kana tare da ni; sandarka da kerenka na ta'azantar da ni. 5 Ka shirya teburi a gabana a fuskar maƙiyana; ka shafe kaina da mai; ƙoƙona ya cika har yana zuba. 6 Tabbas nagarta da amintaccen alƙawari zasu bi ni dukkan kwanakin raina; zan kuma zauna a cikin gidan Yahweh na lokaci mai tsawo sosai!

Zabura 24

Zabura ta Dauda.

1 Ƙasa ta Yahweh ce, da dukkan cikarta, duniyar, da dukkan mazauna cikinta. 2 Gama ya gina ta a bisa tekuna ya kuma ƙafa ta a bisa koguna. 3 Wane ne zai haura tudun Yahweh? Wane ne zai tsaya a cikin wurinsa mai tsarki? 4 Shi wanda ke da hannuwa masu tsarki da kuma zuciya mai tsabta; wanda baya faɗar ƙarya, ba ya kuma yin rantsuwa domin yayi yaudara. 5 Zai karɓi albarka daga wurin Yahweh da kuma adalci daga Allah na cetonsa. 6 Haka ya ke ga tsarar masu neman sa, masu neman fuskar Allah na Yakubu. Selah 7 Tãda kanku, ku ƙyamare; ku tashi, madawwaman ƙofofi, domin Sarkin daraja ya shigo ciki! 8 Wane ne wannan Sarkin daraja? Yahweh, mai ƙarfi da girma; Yahweh, mai girma cikin yaƙi. 9 Tãda kanku, ku ƙyamare; ku tashi, madawaman ƙofofi, domin Sarki na daraja ya shigo ciki! 10 Wane ne wannan Sarkin daraja? Yahweh mai runduna, shi ne Sarkin daraja. Selah

Zabura 25

Zabura ta Dauda.

1 A gare ka, Yahweh, na miƙa raina! 2 Allahna, Na dogara gare ka. Kar ka bari a wulaƙanta ni; kar ka bari maƙiyana suyi farincikin nasara a kaina. 3 Duk wanda yasa begensa a kan kada shi kunyata bari waɗanda suke aikata makirci babu dalili su ji kunya! 4 Ka bayyana mani hanyarka, Yahweh; koya mani tafarkinka. 5 Bishe ni cikin gaskiyarka ka kuma koyar dani, gama kai ne Allah na cetona; na sa begena bisan ka a koda yaushe. 6 Ka tuna, Yahweh, ayyukanka na tausayi da kuma amintaccen alƙawari; gama sun kasance tun tuni. 7 Kada kayi tunanin zunubaina na ƙuruciyata ko tayarwata; ka tuna da ni game da amintaccen alƙawarinka sabili da alherinka, Yahweh! 8 Yahweh yana da nagarta kuma yana da alheri saboda haka yana koyawa masu zunubi tafarki. 9 Yana bi da kamili ga abin da ke dai-dai kuma yana koya masu hanyarsa. 10 Dukkan tafarkun Yahweh na dawwamammiyar ƙauna ne da kuma aminci ga waɗanda ke kiyaye alƙawarinsa da kuma umarnansa tabbatattu. 11 Sabili da sunanka, Yahweh, ka gafarta zunubina, gama yana da girma sosai. 12 Wane ne mutumin dake tsoron Yahweh? Ubangiji zaya umarce shi a hanyar da zaya zaɓa. 13 Rayuwarsa zata bi ta hanya mai kyau; kuma zuriyarsa zasu gaji ƙasar. 14 Abokantakar Yahweh na ga waɗanda ke girmama shi, kuma yana sanar da alƙawarinsa gare su. 15 Idanuna suna bisa Yahweh koda yaushe, gama zaya ƙuɓutar da sawayena daga tarko. 16 Ka juyo gare ni kayi mani jinƙai; gama ni kaɗai ne kuma cikin ƙunci. 17 Damuwoyin zuciyata sun yawaita; ka tsamo ni daga nawayata! 18 Ka dubi wahalata da kuma matsalolina; ka gafarta zunubaina. 19 Ka dubi maƙiyana, gama suna da yawa; suna ƙina da ƙiyayya mai zafi. 20 Ka kare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari a wulaƙanta ni, gama ina samun mafaka a wurinka! 21 Bari nagarta da aminci su kiyaye ni, gama begena a cikinka ya ke. 22 Ka kuɓutar da Isra'ila, Allah, daga dukkan wahalolinsa!

Zabura 26

Zabura ta Dauda.

1 Yi mani shari'a, Yahweh, gama nayi tafiya da aminci; na dogara ga Yahweh babu ja da baya. 2 Ka gwada ni, Yahweh, ka kuma jaraba ni; jaraba tsabtar cikin raina da zuciyata! 3 Gama amintaccen alƙawarinka na gaban idanuna, kuma ina tafiya cikin amincinka. 4 Ban yi hurɗa da mutane marasa gaskiya ba, ko in yi cuɗanya da mutane macuta ba. 5 Na ƙi jinin taruwar masu aikata mugunta, ban kuma zauna da mugaye ba. 6 Na wanke hannuna cikin rashin laifi, ina kuma zagaya bagadinka, Yahweh, 7 domin in raira waƙar yabo da ƙarfi in kuma shaida dukkan ayyukanka masu ban girma. 8 Yahweh, ina ƙaunar gidan da kake zama, inda ɗaukakarka take! 9 Kada ka kawar dani tare da masu zunubi, ko raina tare da mutane masu marmarin shan jini, 10 waɗanda a cikin hannuwansu akwai mugun shiri, kuma hanunsa na dama ke cike da rashawa. 11 Amma ni, zan yi tafiya cikin aminci; ka fanshe ni ka kuma yi mani jinƙai. 12 Sawayena suna tsaye a shimfiɗarɗiyar ƙasa; a cikin taruwa zan albarkaci Yahweh!

Zabura 27

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh ne haske na da cetona; wane ne zan ji tsoro? Yahweh ne mafakar raina; wane ne zai razana ni? 2 Lokacin da masu aikata mugunta suka taso mani domin su cinye namana, magabtana da maƙiyana suka yi tuntuɓe suka kuma faɗi. 3 Koda runduna zasu zagaye ni da gãba, zuciyata baza ta ji tsoro ba; koda yaƙi zai taso gãba dani, duk da haka zan kasance da ƙarfin hali. 4 Abu guda ɗaya nayi roƙo ga Yahweh, zan kuma biɗi wannan; shi ne in zauna a cikin gidan Yahweh dukkan kwanakin raina, in dubi kyawun Yahweh in kuma yi bimbini a cikin haikalinsa. 5 Gama a ranar wahala zaya ɓoye ni a cikin fukafukansa; a ƙarƙashin inuwar rumfarsa zaya suturce ni. Zaya ɗaukaka ni a bisa dutse mai tsawo! 6 Sa'an nan za a ɗaukaka kaina fiye da maƙiyana dake kewaye dani, zan kuma miƙa hadayu na farinciki a cikin rumfarsa! Zan raira waƙa in kuma yi waƙoƙi ga Yahweh! 7 Yahweh ka ji, muryata a lokacin da nayi kuka! Kayi mani jinƙai, ka kuma amsa mani! 8 Zuciyata na ce da kai, "Nemi fuskarsa!" Na nemi fuskarka, Yahweh! 9 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni; kada ka juyar da bawanka daga gare ka cikin fushi! Tun dama kaine mai taimakona; kada ka yashe ni ko kayi banza dani, Allah na cetona! 10 Koda mahaifina ko mahaifiyata sun yashe ni, Yahweh zaya karɓeni. 11 Ka koya mani tafarkinka, Yahweh! Ka bishe ni a daidaitacciyar hanya saboda maƙiyana. 12 Kada ka bayar da ni ga nufin maƙiyana, gama shaidun ƙarya sun tashi gãba dani, suna kuma huro da ta'addanci! 13 Da mene ne zai faru dani da ba domin na yarda cewa zan ga alherin Yahweh a cikin ƙasar masu rai ba? 14 Ka jira ga Yahweh; yi ƙarfi, bari zuciyarka ta ƙarfafa! Saurari Yahweh!

Zabura 28

Zabura ta Dauda.

1 A gare ka, Yahweh, nayi kuka; dutsena, kada kayi banza da ni. Idan baka amsa mani ba, zan harɗe da waɗanda ke gangarawa zuwa kabari. 2 Kaji ƙarar roƙona a lokacin da nayi kira domin taimako daga gare ka, a lokacin da na tãda hannuwa na zuwa wurinka mai tsarki! 3 Kada ka kawar dani tare da masu aikata mugunta, su masu aikata laifuffuka, su dake faɗin alheri da maƙwabtansu da baki amma zuciyarsu cike take da mugunta. 4 Ka basu dai-dai abin da ayyukansu ya dace dasu da kuma abin da muguntarsu ta wajaba, ka biya su bisa ga aikin hannuwansu ka kuma mayar masu bisa ga ladarsu. 5 Domin basu gane da ayyukan Yahweh ba ko ayyukan hannuwansa, zaya buga su ƙasa baza a ƙara gina su ba. 6 Albarka ga Yahweh domin ya ji muryar kukana! 7 Yahweh ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta dogara gare shi, na kuma sami taimako. Saboda haka zuciyata tayi farinciki ƙwarai, zan kuma yabe shi da raira waƙoƙi. 8 Yahweh ne karfin mutanensa, kuma shi ne maɓoyar ceto na shafaffensa. 9 Ka ceci mutanenka ka kuma albarkaci gãdonka. Ka zama makiyayinsu ka kuma ɗauke su har abada.

Zabura 29

Zabura ta Dauda.

1 Bada yabo ga Yahweh, ku 'ya'yan Allah! Bada yabo ga Yahweh domin ɗaukakarsa da ƙarfinsa. 2 Ba Yahweh ɗaukakar da ta cancanci sunansa. Durƙusa ƙasa ga Yahweh cikin jamalin tsarkinsa. 3 An ji muryar Yahweh har bisa ruwaye; Allah maɗaukaki ya yi tsawa, Yahweh na tsawa bisa ruwaye masu yawa. 4 Muryar Yahweh na da cikakken iko; Muryar Yahweh mai daraja ne. 5 Muryar Yahweh na fasa itatuwan sida; Yahweh na fasa gutsu-gutsu itatuwan sida na Lebanon. 6 Yana sa Lebanon tayi tsalle kamar ɗan maraki da kuma Dutsen Hamon kamar ɗan shanu. 7 Muryar Yahweh na aikar da harshen wuta. 8 Muryar Yahweh na girgiza hamada; Yahweh na girgiza hamadar Kadesh. 9 Muryar Yahweh nasa rimaye su tanƙware tana kuma kware daji a fili. Kowanne a cikin haikali na cewa, "Daukaka!" 10 Yahweh na zaman sarki a bisa ruwa mai ambaliya; Yahweh na zaman sarki har abada. 11 Yahweh yana bada karfi ga mutanensa; Yahweh yana albarkatar mutanensa da salama.

Zabura 30

Zabura; waƙar da aka yi a keɓewar haikali. Zabura ta Dauda.

1 Zan girmama ka, Yahweh, gama ka tã dani sama kuma baka bari maƙiyana sun yi farinciki bisa na ba. 2 Yahweh Allahna, nayi kuka gare ka domin taimako, ka kuma warkar dani. 3 Yahweh, ka tsamo raina daga Lahira; ka adana ni da rai kada in gangara ƙasa zuwa kabari. 4 Raira yabbai ga Yahweh, ku amintattunsa! Ku bada godiya a lokacin da kuka tuna da tsarkinsa. 5 Gama fushin sa na lokaci kaɗan ne; amma tagomashinsa na har abada ne. Kuka na zuwa da dare ne, amma farinciki na zuwa da safe. 6 Da ƙarfin hali nace. "Ba zan jijjigu ba." 7 Yahweh, da tagomashinka ka kafa ni kamar ƙaƙƙarfan tsauni; amma daka ɓoye fuskarka, na shiga damuwa. 8 Nayi kira gare ka, na kuma nemi tagomashi daga wurin Ubangijina! 9 Wacce riba ce ke cikin mutuwata, idan na gangara cikin kabari? Ko turɓaya zata yabe ka? Zata furta tabbatattun amincinka? 10 Ka saurara, Yahweh, kayi mani jinƙai! Yahweh, ka zama mai taimakona. 11 Ka juyar da makokina zuwa rawa; ka cire mani tsumma ka kuma sanya mani rigar farinciki. 12 Yanzu ɗaukakata zata yi maka waƙar yabo kuma ba zata yi shuru ba; Yahweh Allahna, zan yi maka godiya har abada!

Zabura 31

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 A cikin ka, Yahweh, na sami mafaka; kada ka barni in wulaƙanta. Ka kuɓutar dani cikin adalcinka. 2 Ka saurare ni; Ka kuɓutar dani da sauri; ka zama dutsen mafakata, ƙaƙƙarfar maɓoya domin cetona. 3 Gama kai ne dutsena da kuma mafakata; Saboda haka sabili da sunanka, ka shugabance ni ka kuma bishe ni. 4 Ka ƙwato ni daga cikin tãrun da suka ɓoye domi na, gama kai ne maɓuyata. 5 A cikin hannuwanka nake bada ruhuna; zaka fanshe ni, Yahweh, Allah madogarata. 6 Na ƙi jinin waɗandɑ s‌uke bautawa gumakan banza, amma na dogara ga Yahweh. 7 Zan yi murna da kuma farinciki cikin amintaccen alƙawarinka, gama ka ga ƙuncina; ka san matsalar raina. 8 Baka miƙa ni a cikin hannuwan maƙiyana ba. Ka kafa ƙafafuwana a buɗaɗɗen wuri mai faɗi. 9 Kayi mani jinƙai, Yahweh, gama ina cikin ƙunci; idanuna sun yi nauyi da azaba tare da raina da jikina. 10 Gama raina yayi nauyi da makoki kuma shekaruna na cike da nishe-nishe. Ƙarfina ya gaza sabili da zunubina, ƙasusuwana suna lalacewa sarai. 11 Sabili da maƙiyana, mutane sun yi banza dani; maƙwabtana suka gaji da yanayina, kuma waɗanda suka san ni suka tsorata. Waɗanda suka gamu dani a hanya suka gudu daga gare ni. 12 An manta da ni kamar mataccen mutum wanda babu wanda ke tunaninsa. Ina kama da fasasshiyar tukunya. 13 Gama na ji raɗe-raɗe masu yawa, labarai masu ban tsoro daga kowanne sashe sa'ad da suke shiri gãba da ni. Sun yi shiri domin su ɗauke raina. 14 Amma na dogara gare ka, Yahweh; Na ce, "Kai ne Allahna." 15 Ƙaddarata na cikin hannuwanka. Ka ‌kuɓutar dani daga hannuwan magabtana daga kuma waɗanda suke fafarata. 16 Bari fuskarka ta haskaka bisa bawanka; ka cece ni cikin amintaccen alƙawarinka. 17 Kada ka bar ni in wulaƙantu, Yahweh; gama na yi kira gare ka! Bari mugu ya wulaƙanta! Bari suyi shuru a cikin Lahira. 18 Bari harsuna masu ƙarya suyi shuru su dake magana gãba da mai adalci da renin girma da kuma tozartarwa. 19 girman alherinka da ka shirya wa masu girmama ka, abin da kake aiwatar wa domin waɗanda suka yi mafaka a cikinka a gaban dukkan 'ya'yan talikai! 20 A cikin mahallin bayyanuwarka, ka ɓoye su daga makircin mutane. Ka ɓoye su a cikin mahalli daga ta'addancin harsuna. 21 Mai albarka ne Yahweh, gama ya nuna mani amintaccen alƙawarinsa mai ban mamaki a lokacin da nake a cikin birnin kwanto. 22 Ko da ya ke na faɗa cikin gaggawata, "An datse ni daga fuskarka," duk da haka ka ji roƙona domin taimako lokacin da nayi kuka gare ka. 23 Oh, ƙaunaci Yahweh, dukkan ku amintattun mabiya. Yahweh yana tsare amintattu, amma yana sãka wa masu girman kai. 24 Ku ƙarfafa kuyi ƙarfi, dukkan ku dake dogara cikin Yahweh domin taimako.

Zabura 32

Zabura ta Dauda. Waƙar hikima.

1 Mai albarka ne taliki wanda an gafarta masa kurakuransa, wanda aka rufe zunubinsa. 2 Mai albarka ne mutum wanda Yahweh ba ya lisafta laifi bisansa kuma wanda babu algus cikin ruhunsa. 3 Da na yi shuru, ƙasusuwana suna lalacewa sa'ad da nake nishe-nishe dukkan yini. 4 Gama rana da dare hannunka na da nauyi bisana. ƙarfina ya gaza kamar lokacin fãrin kaka. 5 Sa'an nan na furta zunubi na gare ka, ban kuma ƙara ɓoye laifi na ba. Na ce, "Zan furta kurakuraina ga Yahweh," ka kuma gafarta mani ladar zunubina. 6 Saboda wannan, dukkan waɗanda ke na allahntaka suna adu'a a gare ka a lokacin gwagwarmaya mai girma. Sa'an nan lokacin da ruwaye masu hauka suka taso, baza su cimma waɗannan mutane ba. 7 Kai ne maɓuyata; zaka tsare ni daga wahala. Zaka zagaye ni da waƙoƙin nasara. 8 Zan umarce ka in koya maka hanyar da zaka bi. Zan umarce ka da idanuna a bisanka. 9 Kada ka zama kamar doki ko kamar alfadari, wanda ba shi da fahimta; sai tare da linzami da ragama domin a bi da su inda ake so su tafi. 10 Mugu yana da baƙinciki mai yawa, amma amintaccen alƙawarin Yahweh zai zagaye wanda ya dogara gare shi. 11 Yi murna cikin Yahweh, da farinciki, ku adalai; yi sowa ta farinciki, dukkan ku masu tsabta cikin zuciya.

Zabura 33

1 Yi farinciki cikin Yahweh, ku adalai; Yin yabo ya dace ga adalai. 2 Kuyi godiya ga Yahweh da molo; yi waƙoƙin yabo gare shi da molo mai tsarkiya goma. 3 Raira sabuwar waƙa gare shi; ku yi kiɗa da ƙwarewarku kuna raira waƙa tare da farinciki. 4 Gama maganar Yahweh mai adalci ce, kuma dukkan abin da ya aikata dai-dai ne. 5 Yana ƙaunar adalci da shari'a. Duniya na cike da amintaccen alƙawarinsa. 6 Da maganar Yahweh aka hallici sammai, kuma dukkan taurari sun kasance ne ta numfashin bakinsa. 7 Yana tara ruwayen teku wuri ɗaya kamar tudu; ya ajiye tekuna cikin ɗakunan ajiya. 8 Bari dukkan ƙasar taji tsoron Yahweh; Bari dukkan mazaunan duniya su tsaya cik a gabansa. 9 Gama ya yi magana, aka kuma aikata; ya umarta, ya kuma tabbata. 10 Yahweh yana lalatar da ƙawancen al'ummai; yana mulki akan shirye-shiryen mutane. 11 Shirin Yahweh ya tsaya har abada, shirye-shiryen zuciyarsa ga dukkan tsararraki. 12 Mai albarka ce al'ummar da Yahweh ne Allahnta, mutanen da ya zaɓa abin gãdonsa. 13 Yahweh yana gani daga sama; yana ganin dukkan mutane. 14 Daga wurin da ya ke zama, yana duban dukkan masu zama cikin ƙasar. 15 Shi wanda ya ke shirya zuciyarsu dukka yana la'akari da ayyukansu. 16 Babu sarkin da zai tsira sabili da yawan runduna; jarumi baya tsira ta dalilin ƙarfinsa. 17 Doki tsaro ne na banza domin nasara; duk da ƙarfinsa, ba zai iya ƙubutarwa ba. 18 Duba, idanun Yahweh na bisan waɗanda ke tsoronsa, a bisa waɗanda suka dangana bisa amintaccen alƙawarinsa 19 domin ya kuɓutar da rayukansu daga mutuwa ya kuma kiyaye su da rai a lokacin yunwa. 20 Muna jiran Yahweh; shi ne taimakonmu da kuma garkuwarmu. 21 Zuciyarmu tayi farinciki cikinsa, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki. 22 Bari amintaccen alƙawarinka, Yahweh, ya kasance da mu a lokacin da muka kafa begenmu cikinka.

Zabura 34

Zabura ta Dauda; lokacin da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, wanda ya kore shi waje.

1 Zan yabi Yahweh a dukkan lokaci, Yabonsa zai kasance a bakina koda yaushe. 2 Zan yabi Yahweh! Bari ƙuntattu su ji su kuma yi farinciki. 3 Ku yabi Yahweh tare da ni, bari mu ɗaukaka sunansa tare. 4 Na nemi Yahweh kuma ya amsa mani, ya kuma ba ni nasara bisa dukkan tsorona. 5 Waɗanda ke duban sa suna haskakawa, kuma fuskarsu ba ta ji kunya ba. 6 Wannan matsattsen mutum yayi kuka Yahweh kuma ya ji ya kuma cece shi daga dukkan matsalolinsa. 7 Mala'ikan Yahweh na zagaye waɗanda ke tsoronsa ya kuma ƙubutar da su. 8 Ku ɗanɗana ku kuma gani cewa Yahweh na da kyau. Mai albarka ne mutum wanda ke ɓuya cikinsa. 9 Ku ji tsoron Yahweh, ku mutanensa masu tsarki. Babu rashi ga waɗanda ke tsoronsa. 10 'Ya'yan zakuna wasu lokuttan suna rasa abinci su kuma ji yunwa, amma waɗanda suka nemi Yahweh baza su rasa kowanne abu mai kyau ba. 11 Ku zo, 'ya'ya maza, ku saurare ni. Zan koya maku jin tsoron Yahweh. 12 Wanne mutum ne mai biɗar rai ya ke kuma ƙaunar ranaku masu yawa, domin ya ga alheri? 13 To, sai ka tsare harshenka daga faɗin mugunta leɓunanka kuma daga faɗin ƙarya. 14 Ka juyo daga barin mugunta ka kuma aikata nagarta. Nemi salama ka kuma bi ta. 15 Idanun Yahweh suna bisa masu adalci kuma kunnuwansa suna karkatawa zuwa ga kukansu. 16 Fuskar Yahweh na gãba da waɗanda ke aikata mugunta, domin a datse tunawa da su daga duniya. 17 Masu adalci sun yi kira Yahweh kuma yana kuɓutar da su daga dukkan matsalolinsu. 18 Yahweh yana kurkusa da masu karyayyar zuciya, kuma yana ceton waɗanda aka ƙuntatawa a cikin ruhu. 19 Da yawa suke matsalolin masu adalci, amma Yahweh yana ƙubutar da su daga dukkan su. 20 Ya kare dukkan ƙasusuwansa, babu ko ɗaya daga cikinsu da za a karya. 21 Mugunta zata kashe mai mugunta. Waɗanda suka ƙi masu adalci za a hallakar da su. 22 Yahweh yana ƙubutar da rayukan bayinsa. Babu ɗaya daga cikin waɗanda ke neman mafaka wurinsa da za a kayar.

Zabura 35

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, ka yi gãba da waɗanda ke aiki gãba da ni; ka yaƙi waɗanda ke yaƙi da ni. 2 Ka ɗauki garkuwarka ƙarama da babba; tashi ka taimake ni. 3 Yi amfani da mashi da gatarin yaƙin ka gãba da waɗanda ke runtuma ta; ka ce da raina, "Ni ne cetonka." 4 Bari su waɗanda ke neman raina su ji kunya su kuma faɗi. Bari waɗanda ke shirin cuta na a juyar da su a kuma hargitsa su. 5 Bari su zama kamar ƙaiƙayi a fuskar isaka, a sa'ad da mala'ikan Yahweh ke korar su. 6 Bari hanyar su ta duhunta tana kuma zamewa, a sa'ad da mala'ikan Yahweh ke runtumar su. 7 Babu dalili suka shirya mani tarkonsu; Babu dalili suka haƙa rami domin raina. 8 Bari halakarwa ta auko masu ba zato. Bari tarkon da suka ɗana ya kama su. Bari su faɗa ciki, ga hallakarsu. 9 Amma zan yi farinciki cikin Yahweh in kuma yi murna cikin cetonsa. 10 Dukkan ƙasusuwana za su ce, "Yahweh, wane ne kamar ka, wanda ke ƙuɓutar da ƙuntattu daga waɗanda suka fi ƙarfinsu da kuma matalauta da kuma mabuƙata daga waɗanda ke ƙoƙarin yi masu fashi?" 11 Shaidu marasa adalci sun tashi; sun yi mani zargin ƙarya. 12 Sun sãka mani nagarta da mugunta. Ina cike da ɓacin rai. 13 Amma a lokacin da suke ciwo, na sanya tsummokara; na yi azumi a madadinsu da kaina sunkuye ga ƙirjina. 14 Na yi tafiya cikin ƙunci domin ɗan'uwana; Na durƙusa cikin makoki domin mahaifiyata. 15 Amma da nayi tuntuɓe, suka yi murna suka taru wuri ɗaya; suka taru wuri ɗaya gãba da ni, kuma suka bani mamaki. Suka kawo mani farmaƙi babu fasawa. 16 Da rashin girmamawa samsam suka yi mani ba'a; suka tauna mani haƙoransu. 17 Ubangiji, har yaushe zaka duba? Ka ƙuɓutar da raina daga farmaƙinsu mai hallakarwa, raina daga zakuna. 18 Sa'an nan zan gode maka a babban taro mai girma; Zan yabe ka a cikin mutane masu yawa. 19 Kada ka bar maƙiyana masu ƙarya su yi murna a kaina; kada ka barsu su aiwatar da mugun shirinsu. 20 Gama basu maganar salama, amma suka shirya maganganun ƙarya gãba da waɗanda ke zaman salama cikin ƙasar. 21 Sun buɗe bakunansu da girma gãba da ni; suka ce, "Aha, Aha, idanunmu sun gan shi." 22 Ka gan shi, Yahweh, kada ka yi shuru; Ubangiji, kada kayi nisa dani. 23 Ka tãda kanka ka kuma farka domin ka kare ni; Allahna da Ubangijina, ka kare bukatata. 24 Ka kãre ni, Yahweh Allahna, sabili da adalcinka; kada ka bar su suyi murna a kaina. 25 Kada ka bari su faɗa a cikin zuciyarsu, Aha, mun sami abin da muke nema." Kada ka bar su su ce, "Mun haɗiye shi." 26 Ka basu kunya ka kuma ruɗar da waɗanda ke niyyar cutar da ni. Bari waɗanda ke cakuna ta a rufe su da kunya da ƙasƙanci. 27 Bari su dake marmarin kuɓutata suyi sowa ta murna su kuma ji daɗi; bari koyaushe su ce, "Bari Yahweh ya ɗaukaka, shi da ya ke jin daɗi cikin wadatar bawansa." 28 Sa'an nan zan faɗi game da shari'arka in kuma yabe ka dukkan yini.

Zabura 36

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda bawan Yahweh.

1 Mugun mutum yana zancen kurakuransa daga cikin zuciyarsa, babu tsoron Allah a idanunsa. 2 Gama yana yiwa kansa ta'aziya, da tunanin cewar zunubansa ba zasu tonu ba ko kuma a ƙi su. 3 Maganganunsa na zunubi ne da yaudara; ba ya son ya zama mai hikima ya kuma aikata nagarta. 4 A lokacin da ya ke kwance a gado, yana shirya yadda zai yi zunubi; ba ya ƙin mugunta. 5 Amintaccen alƙawarinka, Yahweh, na kaiwa har zuwa sammai; amincinka na kaiwa zuwa cikin giza-gizai. 6 Adalcinka na kama da duwatsun Allah; shari'unka na kama da manyan zurfafa. Yahweh, ka kare talikai da dabbobi. 7 Yaya darajar amintaccen alƙawarinka ya ke, Allah! Bil'adama na fakewa a ƙarƙashin inuwar fukafukanka. 8 Zasu ƙoshi daga yalwar abincin gidanka; zaka sa su sha daga cikin koginka mai manyan albarku. 9 Domin a gare ka akwai maɓulɓular rai; cikin haskenka zamu ga haske. 10 Ka kawo gare ni amintaccen alƙawarinka cikakke ga waɗanda suka san ka, kariyarka zuwa ga kamilai a zuci. 11 Ka da ka bar ƙafafun mai girman kai shi zo kusa dani. Ka da ka bar hannun mugaye su kore ni da nisa. 12 A can mugaye suka faɗi; aka buga su ƙasa basu kuma iya tashi ba.

Zabura 37

Zabura ta Dauda.

1 Kada ka damu da masu mugunta; kada ka ji ƙyashin waɗanda ke ayyukan rashin adalci. 2 Gama zasu bushe da wuri kamar ciyawa, su kuma yanƙwane kamar korayen tsire-tsire. 3 Ka dogara ga Yahweh kuma ka yi abin da ke nagari; ka zauna a ƙasar ka yi kiwo cikin aminci. 4 Sa'an nan ka yi murna da al'amuran Yahweh, kuma zai biya maka buƙatun zuciyarka. 5 Ka miƙa hanyoyinka ga Yahweh; ka dagara gare shi, kuma zai yi abu a madadinka. 6 Zai nuna aɗalcinka kamar hasken rana da rashin laifinka kamar rana tsaka. 7 Ka natsu a gaban Yahweh kuma kayi jira da haƙuri domin sa. Kada ka ji haushi idan wani ya yi nasara da abin da ya ke yi, ko sa'ad da ya ke ƙulla mugunta. 8 Kada ka ji haushi da takaici. Kada ka damu. Wannan na bada damuwa ne kawai. 9 Za a datse miyagu, amma waɗanda ke jiran Yahweh zasu gãji ƙasar. 10 A ɗan lokaci ƙaɗan mugun mutum zai ɓace; zaka dubi wurinsa, amma ba zai kasance ba. 11 Amma masu tawali'u zasu gãji ƙasar kuma zasu yi murna da gagarumar wadata. 12 Mugun mutum yana shirya maƙarƙashiya gãba da adali yana kuma cizon haƙora gãba da shi. 13 Ubangiji yana yi masa dariya, gama yana ganin zuwan ranarsa. 14 Mugaye sun zare takubbansu suka kuma tanƙware bakkunansu don su kãda waɗanda ake masu danniya da masu buƙata, su kashe waɗanda ke da nagarta. 15 Takkubansu zasu soke zukatansu, kuma bakkunansu zasu kakkarye. 16 Gara ƙanƙanen abin da mutumin kirki ya ke da shi da yawan abubuwan mugayen mutane. 17 Gama za a ƙarɓe ƙarfin mugayen mutane, amma Yahweh zai taimaki adalai 18 Yahweh yana lura da marasa abin zargi a kowacce rana, kuma gãdonsu zai kasance har abada. 19 Ba za su ji kunya a lokacin masifa ba. Sa'ad da Yunwa tazo, zasu samu isasshen abinci. 20 Amma mugaye zasu lalace. Maƙiyan Yahweh za su zama kamar darajar ciyawa; za a cinye su su ɓace kamar hayaƙi. 21 Mugu yakan ci bashi amma ba ya biya, amma adali yana bayarwa hannu sake. 22 Waɗanda Allah ya sawa albarka zasu gãji ƙasar; waɗanda ya la'anta zasu zama korarru. 23 Ta wurin Yahweh ne hanyoyin mutum ke kafuwa, mutumin da hanyarsa amintacciya ce a fuskar Allah. 24 Ko da ya ke yana tuntuɓe, ba zai faɗi ba, gama Yahweh na riƙe shi da hannunsa. 25 Dã ni yaro ne kuma yanzu na tsufa; ban taɓa ganin an yashe da adali ba ko kuma 'ya'yansa na roƙon abinci. 26 Dukkan yini yana yin alheri yana ba da rance, kuma 'ya'yansa sun zama albarka. 27 Ka bar mugunta kayi abin da ke dai-dai; zaka cetu har abada. 28 Gama Yahweh yana ƙaunar adalci kuma baya rabuwa da amintattun masu binsa. Yana kiyaye su har abada, amma zuriyar mugaye zasu zama korarru. 29 Adalai zasu gãji ƙasar su zauna ciki har abada. 30 Bakin adali yana maganar hikima da kuma ƙara adalci. 31 Shari'ar Allahnsa na zuciyarsa; ƙafafunsa ba za su yi santsi ba. 32 Mugu yakan yi fakon adali ya nemi hanyar kashe shi. 33 Yahweh ba zai bar shi a hannun mugun ba ko kuwa ya yanke masa hukunci sa'ad da ya ke masa shari'a. 34 Ka jira Yahweh ka kuma kiyaye hanyoyinsa, zaya kuma ɗaga ka sama ka mallaki ƙasar. Za ka gani sa'ad da ake korar mugaye. 35 Na ga mugu da azzalumin taliki ya baje kamar koren itace a ƙasarsa ta asali. 36 Amma sa'ad da na sãke wucewa kuma, bai kasance a wurin ba. Na neme shi, amma ba ya samuwa. 37 Dubi mutumin kirki, ka kuma lura da adali; gaba zai zama da kyau ga mutumin salama, 38 Masu zunubi kuwa za a hallaka su ƙaƙaf; za a kuma share zuriyar mugun mutum. 39 Ceton adalai yakan zo daga Yahweh ne; yakan kiyaye su a lokatan damuwa. 40 Yahwe ya taimake su ya kuɓutar da su, Ya kuɓutar dasu daga mugaye ya cece su saboda sun sami garkuwa a cikinsa.

Zabura 38

Zabura ta Dauda, domin ya kawo tunawa.

1 Yahweh, kada ka tsauta mani a cikin fushinka; kada ka hukunta ni a cikin hasalarka. 2 Gama kibiyoyinka suna sukana, kuma hannunka na matse ni har ƙasa. 3 Dukkan jikina na ciwo saboda hasalarka; babu lafiya a ƙasusuwana saboda laifina. 4 Gama zunubaina sun fi ƙarfina; sun zamar mani kaya mai nauyi da yawa. 5 Raunukana sun harbu suna wari saboda wawancin zunubaina. 6 Ana dakatar dani ana wulaƙanta ni kowacce rana; Ina ta makoki dukkan tsawon rana. 7 Gama daga ciki, ina cike da zafin ciwo; babu lafiya a jikina. 8 An sandare ni an ragargaza ni; ina gunaguni saboda fushin zuciyata. 9 Ubangiji kana sane da buƙatar zuciyata, kuma gunagunina basa ɓoyu ba daga gare ka. 10 Zuciyata na bugawa, ƙarfina na ƙarewa, bana kuma gani sosai. 11 Abokaina da aminai sun ƙaurace mani saboda yanayina; maƙwabtana na tsaye daga nesa. 12 Waɗanda ke so su kashe ni sun ƙafa mani tarko. Su waɗanda ke neman yi mani rauni suna maganar hallakarwa da faɗin kalmomin ruɗu dukkan tsawon rana. 13 Amma ni, ina kamar kurman mutum kuma bana jin komai; ina kamar beben da ba ya iya faɗin komai. 14 Ina kamar mutumin da ba ya ji kuma ba shi da amsa. 15 Tabbas ina jiranka, Yahweh; zaka amsa, Ubangiji, Allahna. 16 Na faɗi haka saboda maƙiyana ba zasu yi murna a kan damuwata ba. Idan tafin ƙafata ya zame, zasu yi mani mugayen abubuwa. 17 Gama ina gab da mutuwa, kuma ina cikin wahala kowacce sa'a. 18 Na furta laifofina; na kuma damu da zunubina. 19 Amma maƙiyana na da yawa; waɗanda suka ƙi ni cikin kuskure na da yawa. 20 Suna rama mani nagarta da mugunta; suna ta tuhuma ta koda ya ke ina neman abin da ke nagari. 21 Kada ka yashe ni, Yahweh; Allahna, kada ka tsaya nesa dani. 22 Ka zo da sauri ka taimakeni, Ubangiji, cetona.

Zabura 39

Domin shugaban mawaƙa, domin Yedutan. Zabura ta Dauda.

1 Na yi shiri, "Zan lura da furcin da zan yi saboda kada in yi zunubi da harshe na. Zan sa wa bakina takunkumi a lokacin da nake wurin da mugu ya kasance." 2 Na yi shiru; Na riƙe maganganuna daga faɗin wani abu koda nagari ne, shanwuta kuma ta ƙaru. 3 Zuciyata ta yi zafi; sa'ad da nayi tunani a kan abubuwan nan, yana ci kamar wuta. Sa'an nan a ƙarshe nayi magana. 4 "Yahweh, kasa in san yaushe ne ƙarshen rayuwata da tsawon kwanakina. Ka nuna mani ina kurkusa da matuwa. 5 Duba, kã maida kwanakina kamar tsawon hannuna, kuma rayuwata kamar ba komai take ba a wurinka. Hakika kowanne mutum lumfashi ɗaya ne. Selah 6 Hakika kowanne mutum yana tafiya kamar inuwa. Hakika dukkan kowa yana hanzari ya tattara arziki ko da yake basu san wanda zai karbe su ba. 7 Yanzu, Ubangiji, domin me nake jira? Kai ƙaɗai ne begena. 8 Ka cece ni daga zunubaina; kada ka bari in zama abin ba'a ga wawaye. 9 Na yi shiru kuma bazan iya buɗe bakina ba, saboda kai ne kayi haka. 10 Ka daina yi mani rauni; na karaya ta wurin bugun hannunka. 11 Sa'ad da kake horar da mutane don zunubi, kakan cinye abubuwan da suke marmari kamar asu; hakika dukkan mutane ba komai bane banda tururi kawai. Seleh 12 Ka ji addu'ata, Yahweh, ka saurare ni; ka saurari kukana! Kada ka zama kurma a gare ni, gama ni kamar baƙo ne tare da kai, ɗan gudun hijira kamar yadda dukkan kakannina suke. 13 Ka juyar da harararka daga gare ni domin in sake yin murmushi kafin in mutu,"

Zabura 40

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Na jira Yahweh da haƙuri; ya saurare ni ya ji kukana. 2 Ya fitar dani daga rami mai furgitarwa, daga taɓo, ya sa ƙafafuna a kan dutse ya tsare takawata. 3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina, yabo ga Allahnmu. Da yawa zasu gani su kuma girmama shi su dogara ga Yahweh. 4 Mai albarka ne mutumin da ya maida Yahweh madogararsa kuma baya girmama masu fahariya ko waɗanda suka juya daga gare shi zuwa ƙarairayi. 5 Da yawa suke, Yahweh Allahna, ayyukan al'ajiban da ka yi, kuma babu wanda zai iya ƙirga abubuwan da kake tunani gme da mu; Idan na yanke shawara in yi magana a kan su, za su fi abin da za a iya ƙirgawa. 6 Ba ka buƙatar hadaya ko baiko, amma ka buɗe kunnuwana; ba ka buƙatar baye-baye na ƙonawa ko baye-baye na zunubi. 7 Sa'an nan na ce, "Duba, Na zo; a rubuce ya ke a game dani cikin littafin Yahweh. 8 Ina jin daɗin yin nufinka, Allahna, shari'unka na cikin zuciyata." 9 Na yi shelar nagartattun labaran ayyukanka na adalci a babban taron jama'a; Yahweh, ka san leɓunana basu dena yin wannan ba. 10 Ban ɓoye ayyukan adalcinka a zuciyata kaɗai ba; Na furta amincinka da cetonka; Ban ɓoye amintaccen alƙawarinka ko madawwamiyar ƙaunarka daga babban taron jama'a ba. 11 Kada ka yi jinkirin yi mani ayyukan jinƙai; ka bar amintaccen alƙawarinka da madawwamiyar ƙaunarka su kiyaye ni. 12 Damuwoyin da basu ƙidayuwa sun kewaye ni; alhakin zunubaina ya tarar da ni har yasa bana iya ganin wani abu; Sun fi gashin kaina yawa, kuma zuciyata ta karaya. 13 In ka yarda, Yahweh, ka cece ni; ka yi hanzari ka taimake ni, Yahweh. 14 Ka sa waɗanda suke son kashe ni su sha kunya da yawa. Kasa su koma baya a ci nasara a kansu, ka kawo waɗanda ke murna saboda wahalar da nake sha, cikin ƙasƙanci. 15 Kasa su razana saboda kunya, su waɗanda ke yi mani ba'a, " 16 Amma bari dukkan waɗanda ke neman ka su yi farinciki da murna a cikinka; ka sa duk mai ƙaunar cetonka ya ci gaba da cewa, "A yabi Yahweh." 17 Na talauce na zama mabuƙaci; duk da haka Ubangiji yana tunani a kai na. Kai ne mai taimako na kuma ka zo domin ka cece ni; kada ka yi jinkiri, Allahna.

Zabura 41

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Mai albarka ne wanda ke kulawa da marasa ƙarfi; a ranar masifa, Yahweh zai 'yantar da shi. 2 Yahweh zai kiyaye shi ya kare shi, kuma zai zama da albarka a duniya; Yahweh ba zai bar shi ga nufin maƙiyansa ba. 3 Yahweh zai yi masa gudummawa a gadon wahalarsa; zaka maida gadonsa na ciwo zuwa gadonsa na warkarwa. 4 Na ce, "Yahweh, ka yi mani jinƙai! Ka warkar dani, gama na yi maka laifi." 5 Maƙiyana suna muguwar magana gãba da ni, cewa, 'Yaushe ne zai mutu kuma sunansa ya lalace?' 6 Idan maƙiyina ya zo gani na, ya furta maganganun banza; zuciyarsa na ƙoƙarin sanin dukkan matsalolina; sa'ad da ya tafi daga gare ni, sai ya gaya wa kowa game da su. 7 Dukkan waɗanda ke ƙi na na raɗa da juna gãba da ni; gãba da ni suna fatan shan wahalata. 8 Suna cewa, "Mugun ciwo ya make shi; yanzu da ya ke kwance ƙasa, ba zai ƙara tashi ba." 9 Lallai, ko abokina na ƙut da ƙut, da na yarda da shi, wanda ya ci gurasata, ya juya mani baya. 10 Amma kai, Yahweh, ka yi mani jinƙai ka ɗaga ni sama saboda in mai da martani. 11 Ta wannan na san kana farinciki dani, gama maƙiyina bai yi murna a kaina ba. 12 Amma ni, ka tallefe ni cikin aminncina kuma zaka kiyaye ni a fuskarka har abada. 13 Bari Yahweh, Allah na Isra'ila a yabe shi daga dawwama zuwa dawwama. Amin da Amin. Littafi Biyu

Zabura 42

Domin shugaban mawaƙa. 'Salon waƙa ta 'ya'yan Kora.

1 Kamar yadda mariri ke marmarin rafukan ruwa, haka nake ƙishinka, Allah. 2 Ina ƙishin Allah, Allah mai rai, yaushe zan zo in bayyana a gaban Allah? 3 Hawayena sun zama abincina dare da rana, lokacin da maƙiyana kullum suna cewa dani, "Ina Allahnka?" 4 Waɗannan abubuwan nake tunawa da su yayin da nake zubo raina: yadda na tafi tare da taron mutane na jagorance su zuwa gidan Allah tare da muryar jin daɗi da yabo, babban taro na shagalin buki. 5 Me yasa ka rusuna ƙasa, raina? Me yasa kake damuwa daga can ciki? Yi bege ga Allah, gama zan ƙara yabonsa wanda shi ne cetona. 6 Allahna, raina ya rusuna ƙasa a can ciki, don haka na tuna da kai daga ƙasar Yordan, daga ƙololuwar Dutsen Hamon, kuma daga tudun Miza. 7 Zurfi na kira ga zurfi da jin ƙarar kwararowar ruwanka; dukkan raƙuman ruwanka da matsirgan ruwanka sun mamaye ni. 8 Duk da haka Yahweh zai umarci amintaccen alƙawarinsa da rana; da dare waƙarsa zata kasance tare da ni, addu'a ce ga Allah na rayuwata. 9 Zan yi magana ga Allah, dutsena, "Me yasa ka mance da ni" Me yasa nake makoki saboda danniyar maƙiyina?" 10 Kamar da takobi a ƙasusuwana, maƙiyana ke yi mani zargi, yayin da kullum suke cewa dani, "Ina Allahnka?" 11 Me yasa kake rusuna a ƙasa, raina? Me yasa kake damuwa can ciki? Yi bege cikin Allah, gama kuma zan yabe shi wanda shi ne cetona da Allahna.

Zabura 43

1 Kawo mani adalci, Allah, kayi mani taimakon kãriya a kan al'umma marasa tsoron ka. 2 Gama kai ne Allah na ƙarfina. Meyasa ka yashe ni? Me yasa nake tafiya cikin makoki saboda muzgunawar maƙiya? 3 Oh, ka aiko da haskenka da gaskiyarka, su jagorance ni. su kawo ni ga tudunka mai tsarki da wurin zamanka. 4 Sa'an nan zan yi tafya zuwa ga bagadin Allah, ga Allah matuƙar jin daɗina. Zan yabeka da garaya, Allah, Allahna. 5 Me yasa ka rusuna ƙasa, raina? Me ya sa kake damuwa can ciki? Yi bege cikin Allah, gama zan ƙara yabonsa wanda shi ne cetona da Allahna.

Zabura 44

Domin shugaban mawaƙa. Salon waƙa ta 'ya'yan Kora.

1 Mun ji da kunnuwanmu, Allah, Kakanninmu suka faɗa mana irin aikin da ka yi a kwanakinsu, a kwanakin dã. 2 Ka kore al'ummai da hannunka, amma ka dasa mutanenmu; ka azabci mutane, amma ka baza mutanenmu cikin ƙasar. 3 Gama basu samu mallakar ƙasar ta takobin kansu ba, ba kuma ƙarfin kansu ba ne ya cece su; amma hannun damanka da ƙarfinka da hasken fuskarka ne, saboda yi tagomashi gare su. 4 Allah, kai ne sarkina; ka umarta nasara domin Yakubu. 5 Da taimakonka zamu tura maƙiyanmu; da sunanka za mu tattakesu, waɗanda suka tashi gãba da mu. 6 Gama ba zan dogara ga bakana ba, takobina kuma ba zai cece ni ba. 7 Amma ka cece mu daga maƙiyanmu, ka ba masu ƙinmu kunya. 8 A cikin Allah muke fahariya a kullum, kuma za mu yi godiya ga sunanka har abada. Selah 9 Amma yanzu ka ƙi mu ka kawo mu ga kunya, kuma baka yi tafiya tare da mayaƙanmu ba. 10 Ka sa muka juya baya daga maƙiyin; kuma waɗanda suka ƙi mu suna ɗibi ganima domin kansu. 11 Ka maida mu kamar tumakin da aka ƙaddara don abinci ka warwatsar da mu cikin al'ummai. 12 Ba a bakin komai ka sayar da mutanenka ba; ba ka ƙara wadatarka ta yin haka ba. 13 Ka maida mu abin zargi ga maƙwabtanmu, waɗanda ke kewaye da mu suna yi mana reni da ba'a. 14 Ka sa mun zama abin zãgi cikin al'ummai, abin girgiza kai cikin tarrukan mutane. 15 A dukkan tsawon rana ƙasƙancina na gabana, kuma kunyar fuskata ta rufe ni 16 saboda muryar wanda ke tsautarwa da zage-zage, saboda maƙiyi da mai ɗaukar fansa. 17 Dukkan waɗannan sun zo a kanmu; duk da haka ba mu mance da kai ba ko kuwa mu yi aiki cikin rahin gaskiya da alƙawaranka. 18 Zuciyarmu bata juya ba; ƙafafunmu ba su yi nisa daga hanyarka ba. 19 Duk da haka ka kakkarya mu a wurin diloli ka rufe mu da inuwar mutuwa. 20 Idan mun mance da sunan Allahnmu ko kuwa muka buɗe hannuwanmu ga wani bãƙon allah, 21 Allah ba zai bincika haka ba? Gama ya san asiran zuciya. 22 Hakika, ta dalilinka ake karkashe mu dukkan rana; ana yi mana kallon tumaki domin yanka. 23 Farka, me yasa kake barci, Ubangiji? Tashi, kada ka jefar da mu da daɗewa. 24 Me yasa ka ɓoye fuskarka ka mance da matsananciyar azabarmu da wahalarmu? 25 Gama mun narke mun zama ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa. 26 Tashi tsaye domin taimakonmu ka 'yantar da mu ta dalilin amintaccen alƙawarinka.

Zabura 45

Domin shugaban mawaƙa; an shirya domin shoshanayim. Zabura ta 'ya'yan Kora. Salon waƙa. Waƙar ƙauna.

1 Zuciyata na jin daɗi da nagartaccen zance; Zan karanta kalmomin da na harhaɗo a kan sarki da ƙarfi; harshena shi ne al'ƙalamin shiryayyen marubuci. 2 Ka fi 'ya'yan ɗan Adam kyau; an zuba alheri a leɓunanka; saboda haka mun san Allah ya albarkaceka har abada. 3 Kasa takobinka a gefenka, mai girma, cikin ɗaukakarka da martabarka. 4 Cikin darajarka ka hau dokinka cikin murna saboda yarda da tawali'u da ayyukan adalci; hannun damanka zai koya maka abubuwan bantsoro. 5 Kibawunka na da ƙaifi; mutane sun faɗa ƙarƙashinka; kibawunka na cikin zukatan maƙiyan sarki. 6 Kursiyinka, Allah, yana nan har abada, sandar adalci shi ne sandar mulkinka. 7 Kana ƙaunar ayyukan adalci kuma kana ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya shafe ka da mai na murna fiye da abokan taraiyarka. 8 Dukkan tufafinka na ƙamshin turaren mur da aloyes da ƙahonnin da aka samo; daga kowacce fadar hauren giwa kayyakin busa da kiɗe-kiɗe sun saka murna. 9 'Ya'ya mata na sarakuna na cikin matayenka masu martaba; sarauniya na tsaye da tufafin zinariya da Ofir a hannun damanka, 10 Saurara, ɗiya, ki maida hankali ki buɗe kunne, ki mance da mutanenki da gidan mahaifinki. 11 Ta haka sarkin zai yi marmarin kyanki; shi shugabanki ne; ki girmama shi. 12 Ɗiyar Taya zata kasance a wurin da kyauta; masu arziki cikin mutanen za su nemi alfarmarku. 13 Ɗiya gimbiya a fãda tana cikin dukkan ɗaukaka; an yi aikin tufafinta da zinariya. 14 Za a kaita wurin sarki cikin kyawawan tufafi masu ado kala-kala; budurwai, ƙawayenta dake binta, za a kawo maka. 15 Za a jagorance su da murna da farinciki; za su shiga cikin fadar sarki. 16 A fãdar ubanninka 'ya'yanka zasu kasance, waɗanda zaka maida su yarimai a dukkan duniya. 17 Zan sa sunanka ya dawwama a dukkan tsararraki; saboda haka mutanen zasu yi maka godiya har abada abadin.

Zabura 46

Domin shugaban mawaka. Zabura ta 'ya'yan Kora; shirin Alamot. Waƙa.

1 Allah shi ne mafakarmu da ƙarfinmu, Mai matuƙar taimako a lokacin wahala. 2 Domin haka ba za mu ji tsoro ba, ko duniya zata canza, ko an girgiza duwatsu har cikin tekuna, 3 ko ruwayenta sun yi ruri da tangaɗi, duwatsu kuma suna motsi saboda kumburinsu. Selah 4 Akwai kogi, da ƙoramu waɗanda ke sa birnin Allah farinciki, wuri mai tsarki na shirayi na Maɗaukaki. 5 Allah yana cikin tsakiyarta; ba zata kawu ba; Allah zai taimake ta, kuma zai yi haka da sassafen safiya. 6 Al'ummai suka fusata kuma mulkoki suka girgiza; ya tayar da muryarsa, kuma duniya ta narke. 7 Yahweh mai runduna na tare da mu; Allah na Yakubu shi ne mafakarmu. Selah 8 Zo, dubi ayyukan Yahweh, hallakar da ya kawo wa duniya. 9 Ya sa yaƙe-yaƙe su ƙare har zuwa iyakar duniya; ya kakkarya baka ya daddatsa mãsu gutsu--gutsu; ya ƙone garkuwoyi. 10 Ku yi shiru ku sani Ni ne Allah; Zan sami ɗaukaka a cikin al'ummai; Za a ɗaukaka ni a duniya. 11 Yahweh mai runduna na tare da mu; Allah na Yakubu ne mafakarmu. Saleh

Zabura 47

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.

1 Ku tafa hannuwanku, ku dukkan mutane; ku yi sowa ga Allah da muryar nasara. 2 Gama Yahweh Maɗaukaki abin tsoro ne; shi Sarki ne mai girma bisa dukkan duniya. 3 Ya mayar da mutane ƙarƙashinmu, ya sa al'ummai a ƙarƙƙashin ƙafafunmu. 4 Ya zaɓi gãdonmu dominmu, ɗaukakar Yakubu wanda ya ke ƙauna. Selah 5 Allah ya tafi sama da sowa, Yahweh da ƙarar kakaki. 6 Raira waƙoƙin yabo ga Allah. raira waƙoƙin yabo; raira waƙoƙin yabo ga Sarkinmu, raira waƙoƙin yabo. 7 Gama Allah Sarki ne a kan dukkan duniya; raira woƙoƙin yabo da ganewa. 8 Allah yana mulki a kan al'ummai; Allah na zaune a tsattsarkan kursiyinsa. 9 'Ya'yan sarakuna sun tattaru wurin mutanen Allah na Ibrahim; gama garkuwoyin duniya na Allah ne; yana da ɗaukaka mai girma.

Zabura 48

Waƙa; zabura ta 'ya'yan Kora.

1 Yahweh mai girma ne kuma a yabe shi da girma, cikin birnin Allahnmu a tsauni mai tsarki. 2 Mai kyakkyawan tsawo, farincikin duk duniya, shi ne Tsaunin Sihiyona, a kusurwoyin arewa, birnin sarki mai girma. 3 Allah ya maida kansa sananne a cikin fadodinta a matsayin mafaka. 4 Gama, duba, sarakuna sun tattaro kansu; suna wucewa tare. 5 Suka gan ta, sa'an nan suka yi mamaki; suka damu ƙwarai, sai suka wuce da sauri. 6 Firgici ya mamaye su a wurin, da azaba kamar ta mace mai naƙuda. 7 Da iskar gabas ka karya jiragen ruwan Tarshish. 8 Kamar yadda muka ji haka muka gani a birnin Yahweh mai runduna, a birnin Allahnmu; Allah zai kafa shi har abada. Selah 9 Mun yi tunanin amintaccen alƙawarinka, Allah. a tsakiyar haikalinka. 10 Kamar yadda sunanka ya ke, Allah, haka yabonka har ga iyakar duniya; hannun damanka na cike da ayyukan adalci. 11 Tsaunin Sihiyona yi murna, bari 'ya'ya mata na Yahuda su yi farinciki saboda shari'unka masu adalci. 12 Yi tafiya a kewayen Dutsen Sihiyona, je ka kewaya ta, harabarta da hasumiyarta, 13 lura da bangayenta sosai kuma ka duba fãdodinta da kyau, don ka faɗa wa tsara mai zuwa. 14 Gama wannan Allahn shi ne Allahnmu har abada abadin; shi zai bi damu har mutuwa.

Zabura 49

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.

1 Ku ji wannan, dukkanku mutane; ku kasa kunne, dukkanku mazaunan duniya, ƙanana da manya, 2 masu arziki da matalauta dukka. 3 Bakina zai yi maganar hikima kuma nazarin zuciyata zai zama na ganewa. 4 Zan sa kunnena ga misali; zan fara misalina da molo. 5 Me zai sa in ji tsoron kwanakin mugunta, sa'ad da zunuban maƙiyana suka kewaye ni. 6 Me zai sa in ji tsoron waɗanda suka dogara ga wadatarsu suke kuma yin fahariya game da arzikinsu? 7 Tabbas babu wanda zai iya fansar ɗan'uwansa ko ya ba Allah fansa dominsa, 8 Gama 'yantar da ran wani na da tsada, kuma ba wanda zai iya biyan bashinmu. 9 Babu wanda zai dawwama da har jikinsa ba zai ruɓe ba. 10 Gama zai ga ruɓa. Masu hikima na mutuwa; wawaye da sakarkaru ma na lalacewa su kuma bar wadatarsu ga waɗansu. 11 Tunaninsu na can ciki shi ne iyalansu zasu cigaba har abada, wuraren da suke zama kuma, su cigaba har dukkan tsararraki; suna kiran gonakinsu da sunayensu. 12 Amma mutum, mai arziki ba shi rayuwa har abada; yana kamar dabbobi dake mutuwa. 13 Wannan, hanyarsu, ita ce wautarsu; duk da haka bayansu, mutane suna amincewa da maganganunsu. 14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga Lahira, kuma mutuwa zata zama mai kiwon su. Adalai zasu yi mulki a kansu da safe, kuma jikunansu zasu hallaka a Lahira, tare da rashin wurin zama dominsu. 15 Amma Allah zai 'yantar da rai na daga ikon lahira; zai karɓe ni. Selah 16 Kada ka ji tsoro sa'ad da wani ya yi arziki, kuma darajar gidansa ta ƙaru. 17 Gama sa'ad da ya mutu ba zai tafi da komai ba; darajarsa ba zata tafi tare da shi ba sa'ad da ya mutu. 18 Ko da mutum yana farinciki da nasararsa saboda arzikinsa yayin da ya ke raye- kuma mutane na yabonka sa'ad da kake rayuwa don kanka- 19 zai tafi zuwa tsarar ubanninsa kuma ba za su ƙara ganin haske kuma ba. 20 Mai wadata amma ba shi da ganewa yana kamar dabbobi, dake lalacewa.

Zabura 50

Zabura ta Asaf.

1 Maɗaukaki, Allah, Yahweh, ya yi magana yana kiran duniya daga fitar rana zuwa faɗuwarta. 2 Daga Sihiyona, wuri mafi kyau, Allah yana haskakawa. 3 Allahnmu ya zo kuma ba ya tsaye shiru; wuta na ci a gabansa, kuma babban hadari na kewaye da shi. 4 Ya kira sammai da duniya domin ya shar'anta mutanensa. 5 Tattaro mani amintattuna dukka gare ni, waɗanda suka yi alƙawari dani ta miƙa hadaya." 6 Sammai zasu yi shelar ayyukan adalcinsa, gama Allah da kansa alƙali ne. Selah 7 Ku ji, mutanena, kuma zan yi magana; Ni ne Allah, Allahnku. 8 Ba zan kwaɓe ku domin hadayunku ba; hadayunku na ƙonawa na gabana kullum. 9 Ba zan ƙarɓi bijimi daga gidanku ba, ko kuwa bunsurai daga garkenku ba. 10 Gama kowanne naman jeji nawa ne da shanun kan tuddai dubu. 11 Na san dukkan tsuntsayen duwatsu, kuma namomin jeji na fili nawa ne. 12 Idan ina jin yunwa, ba zan faɗa maku ba; gama duniya tawa ce, da dukkan abin da ke cikinta. 13 Ko zan ci naman bijimai ko in sha jinin awakai? 14 Ku miƙa wa Allah hadayar godiya, kuma ku bada alƙawaranku ta rantsuwa ga Mai iko dukka. 15 Ku yi kira gare ni a ranar damuwa; Zan cece ku, kuma zaku girmama ni." 16 Amma ga mugaye Allah yace, "Me zaku yi da furtawar farillaina, har da zaku ɗauki alƙawarina a bakinku, 17 tunda kun ƙi umarnina kuma kun jefar da maganganuna? 18 Sa'ad da kuka ga barawo, kuka yarda da shi; kuna ayyuka tare da waɗanda ke yin zina. 19 Kun bada bakinku ga mugunta, kuma harshenku na fitar da ruɗu. 20 Ka zauna kana magana gãba da ɗan'uwanka; ka na saran ɗan mahaifiyarka. 21 Kun aikata waɗannan abubuwan, amma na yi shiru, sai kuka zata cewa Ni kamarku nake. Amma zan kwaɓe ku in kawo a gaban idanuwanku, dukkan abubuwan da kuka yi. 22 Ku lura da wannan da kulawa, ku da kuka mance da Allah, ko kuma zan yayyaga ku gutsu-gutsu, kuma babu wanda zai zo ya taimake ku! 23 Wanda ya ke miƙa hadayar godiya yana yabona ne, kuma ga duk wanda ya ke rayuwarsa a hanyar da ta dace zan nuna masa ceton Allah."

Zabura 51

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda; Sa'ad da annabi Natan ya je gunsa bayan da ya kwanta da Batsheba.

1 Ka yi mani jinƙai, Allah, saboda amintaccen alƙawarinka; saboda kana yin ayyukan jinƙai masu yawa, ka tsige kurakuraina. 2 Ka wanke ni sosai daga zunubina ka share mani laifina. 3 Gama na san kurakuraina, kuma laifina yana gabana kullum. 4 Gãba da kai, kai kaɗai, na yiwa laifi kuma na yi abin mugunta a fuskarka; ka yi dai-dai sa'ad da kayi magana; baka yi kuskure ba sa'ad da ka shar'anta. 5 Duba, An haife ni a cikin zunubi; tun daga cikin mahaifiyata, ina cikin zunubi. 6 Duba, kana so in yi marmarin aminci cikin zuciyata; a cikin zuciyata zaka sa in san hikima. 7 Ka tsarkake ni da abin tsarkakewa, zan kuwa tsarkaka; ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari. 8 Ka sa in ji daɗin rai da murna saboda ƙasusuwan da ka karya suyi farinciki. 9 Ka ɓoye fuskarka daga laifofina ka hure dukkan zunubaina. 10 Ka sa in so yi maka biyayya kullum, Allah, ka sa kullum in so yin abin da ke dai-dai. 11 Kada ka kore ni daga gare ka, kar kuma ka ɗauke mani Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni. 12 Ka maido mani da farincikin cetonka, ka riƙe ni da ruhun yin biyayya. 13 Sa'an nan zan koya wa masu zunubi hanyoyinka, masu laifi kuma zasu komo gare ka 14 Ka gafarce ni domin zub da jini, Allahn cetona, sai in yi sowa domin farincikin ayyukan adalcinka. 15 Ubangiji, ka buɗe leɓunana, sai bakina ya furta yabonka. 16 Gama baka murna da sadaka, da zan bada ita; Baka jin daɗin baye-bayen ƙonawa. 17 Hadayu na Allah sune karyayyen ruhu. Kai, Allah, baza ka ƙi zuciya mai tuba da kuma tawali'u ba. 18 Kayi nagarta cikin managarcin jin daɗinka ga Sihiyona; ka sake gina garun Yerusalem. 19 Sa'an nan zaka yi murna da sadakokin ayyukan aɗalci da baye-bayen ƙonawa da ainihin baye-yen ƙonawa; sa'an nan mutanenmu zasu miƙa bijimai a bagadinka.

Zabura 52

Domin shugaban mawaƙa. Salon waƙar Dauda; lokacin da Dowaj Ba'idome yazo ya faɗawa Saul, ya ce da shi, "Dauda ya zo gidan Ahimelek."

1 Meyasa kuke taƙama da tada fitina, ku manyan mutane? Alƙawarin Allah mai aminci yana zuwa kullum. 2 Harshenku yana shirya hallakarwa kamar reza mai kaifi, kuna aikata yaudara. 3 Kuna ƙaunar mugunta fiye da nagarta ƙarya kuma fiye da maganar adalci. Selah 4 Ka na ƙaunar maganar da zata hallaka waɗansu, kai harshe mai yaudara. 5 Haka Allah zai hallaka ka har abada, zai ɗauke ka daga rumfarka ya tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Selah. 6 Masu adalci zasu gani su ji tsoro; su yi masa dariya su ce, 7 "Ku dubi mutumin da bai mayar da Allah wurin fakewarsa ba, amma ya dogara ga dukiya da yawa, kuma yana da ƙarfi sa'ad da ya hallaka waɗansu." 8 Amma ni, ina kama da itacen inabi mai sheƙi a cikin gidan Allah; zan dogara ga alƙawarin Allah mai aminci har abada. 9 Zan yi godiya gare ka har abada saboda abin da kayi. Zan jira ga sunanka, saboda yana da kyau a cikin taron jama'arka masu tsoron ka.

Zabura 53

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Mahalat. Salon waƙar Dauda.

1 Wawa a zuciyarsa yace, "Babu wani Allah." Dukkan su sun gurɓace sun yi aikin mugunta; babu ko ɗaya dake aikata abin kirki. 2 Allah ya dubo 'yan Adam daga sama, ya gani ko akwai wani mai fahimta, wanda ke neman sa. 3 Dukkan su sun fanɗare. Gabaɗayan su sun gurɓace. Ba wani mai aikata abin kirki, babu ko guda ɗaya. 4 Waɗanda ke aikata mugunta basu da fahimta ne--waɗanda ke cin naman mutanena kamar suna cin gurasa kuma ba su kira ga Allah ba? 5 Suna cikin tsoro mai yawa ko da ya ke ba wani abin tsoratarwa; gama Allah zai tarwatsa duk wanda ya yi maku kwanto; irin waɗannan mutane zasu sha kunya gama Allah ya ƙi su. 6 Oh, dama ceton Isra'ila ya zo daga Sihiyona! Sa'ad da Allah ya dawo da mutanensa daga bauta, Yakubu zai yi farinciki, Isra'ila kuma zai yi murna!

Zabura 54

Domin shugaban mawaƙa; Akan kayan kaɗe-kaɗe. Salon Dauda; lokacin da Zifaniyawa suka zo suka ce da Saul, "Ashe ba Dauda na ɓoye a cikinmu ba?"

1 Ka cece ni ya Allah, ta wurin sunanka, ka yi mani shari'a cikin ƙarfin ikonka. 2 Allah, ka ji addu'ata, ka saurari kalmomin bakina. 3 Gama bãƙi sun afko mani, lalatattun mutane na neman raina, basu sa Allah a gabansu ba. Selah. 4 Duba, Allah shi ne mai taimako na, Ubangiji shi ne mai tallafa ta. 5 Zai saka wa maƙiyana da mugunta; cikin amincinka, ka hallaka su! 6 Zan baka hadaya ta yardar rai, zan yi godiya ga sunanka, Yahweh gama haka na da kyau. 7 Gama ya kuɓutar dani daga kowacce damuwa; idona na duban nasara a kan maƙiyana.

Zabura 55

Domin shugaban mawaƙa akan kayan kiɗa na tsarkiya. Salon Dauda.

1 Allah, ka ji addu'ata, kada ka ɓoye kanka daga roƙona. 2 Ka saurare ni ka amsa mani, gama bani da hutu cikin wahaluna, 3 saboda muryar maƙiyana, saboda matsin masu mugunta, gama suna tsananta mani cikin fushi. 4 Zuciyata tana kiɗima a cikina, tsoron mutuwa ya faɗo kaina. 5 Firgita da razana sun zo kaina, kuma fargaba ya sha kaina. 6 Na ce, "Oh, dãma ina da fukafukai kamar kurciya! Da na tashi in je in huta. 7 Da zan tafi can nesa in zauna a cikin jeji. Selah 8 Da zan yi hanzari in sami mafaka daga hadari mai iska da guguwa. 9 Ka haɗiye su, Ubangiji, kasa ruɗami cikin harsunansu! Gama na ga ta'addanci da hargitsi a cikin birnin. 10 Suna ta yawo a kan ganuwarsa dare da rana. Mugunta da lalata suna cikin tsakiyarsa. 11 Aikin mugunta na cikin tsakiyarsu; Tsanani da zamba ba su bar hanyoyinsu ba. 12 Gama da maƙiyi ne ke tsauta mani, da na iya jurewa; ba kuma wanda ya ke gaba dani ne ya tada kansa gaba dani ba, da na ɓoye kaina daga wurin sa. 13 Amma kai ne mutum kamar ni, abokina, da aminina kuma. 14 Mun yi zumunci mai kyau tare, mun je gidan Yahweh tare da ƙarfafa. 15 Bari mutuwa ta afko masu, bara su gangara lahira, gama mugunta ce kaɗai rayuwarsu, haka suke. 16 Ni kuwa zan kira ga Allah, Yahweh zai cece ni. 17 Ko da yamma ko da rana ko da safe, idan na yi ƙara da nishi zai ji muryata. 18 Zai kuɓutar da raina daga masu kawo mani hari, gama waɗanda ke faɗa dani suna da yawa. 19 Yahweh, wanda ya ke mulki tun daga farko, zai ji su ya ƙasƙantar dasu. Ba zasu taɓa canzawa ba, kuma ba sa tsoron Yahweh. 20 Abokina ya tada hannuwansa gaba da waɗanda ke zaman salama dani. Bai cika alƙawarin da ya yi ba. 21 Bakinsa yana da taushi kamar mai, amma zuciyarsa tana da hasala; kalmominsa suna da taushi kamar mai, amma a gaskiya takubba ne zararru. 22 Ka ɗora wa Yahweh matsalolinka, shi zai riƙe ka, ba zai bari adalai su lalace ba. 23 Amma kai Allah, za ka kawo miyagu cikin ramin hallakarwa. Masu shan jini da mayaudaran mutane ba za su rayu koda kamar na rabin sauran mutane ba, amma zan dogara gare ka.

Zabura 56

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Yanat elem rehokim. Zabura ta Dauda. Kewa; lokacin da Filistiyawa suka ɗauke shi zuwa Gat.

1 Ka ji ƙaina ya Allah, gama mutane na kawo mani hari! Dukkan yini suna tsananta ɓatancin da suke yi mani. 2 Maƙiyana na musguna mani dukkan yini, gama waɗanda ke yin faɗa dani cikin wauta suna da yawa. 3 Sa'anda na ji tsoro, zan dogara gare ka. 4 Ina jin daɗin maganar Allah, ga Allah zan dogara; ba zan ji tsoro ba; me mutum kawai zai iya yi ma ni? 5 Juya maganata suke yi dukkan yini, dukkan tunaninsu a kaina na mugunta ne. 6 Sun tattara kansu, sun yi kwanto, suna bin sawuna, suna neman raina. 7 Kada ka bari su dena yin mugunta. Ya Allah, ka kayar da su a cikin fushinka. 8 Ka lissafa yawace-yawacena ka kuma sa hawayena cikin kwalba; ko ba a cikin littafinka suke ba? 9 Sa'ad da na kira ka, maƙiyana zasu koma da baya, abin da na sani kenan, Allah yana tare da ni. 10 A cikin Allah --wanda maganarsa nake yabo, a cikin Yahweh-- 11 a cikin Allah na dogara, bazan ji tsoro ba. Me wani zai iya yi mani? 12 Aikina shi ne in cika wa'adina gare ka, Yahweh. Zan miƙa baye-baye na godiya a gare ka. 13 Gama ka kuɓutar da raina daga mutuwa, ka tsare ƙafafuna daga faɗuwa, domin in yi tafiya a gaban Allah a cikin masu rai.

Zabura 57

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa; lokacin da ya gudu daga wurin Saul a cikin kogo.

1 Ka yi mani jinƙai, Yahweh, ka yi mani jinƙai, gama na fake wurin ka har sai waɗannan wahalu sun wuce. Na tsaya a ƙarƙashin inuwar fukafukanka har sai wannan hallaka ta ƙare. 2 Zan yi kuka ga Allah Maɗaukaki, ga Allah, wanda ya ke yi mani komai. 3 Zai aiko da taimako daga sama ya cece ni, yana jin haushin waɗanda ke ƙuje ni. Allah zai aiko mani da jinƙansa da amincinsa. 4 Raina yana cikin zakuna, ina cikin waɗanda suke a shirye su cinye ni. Ina cikin mutanen da haƙoransu mãsu ne da kibau, haƙoransu kuma kamar takubba masu kaifi. 5 Ya Yahweh, ka ɗaukaka a bisa sammai, bari ɗaukakarka ta zama a bisa duniya. 6 Sun baza taru saboda ƙafafuna; Na shiga cikin ƙunci. Sun gina rami a gabana. Amma su da kansu ne suka faɗa a cikin tsakiyarsa! Selah 7 Zuciyata ta kafu, Allah, zuciyata a kafe take; Zan raira, I, zan raira yabbai. 8 Tashi, ke zuciyata mai daraja, tashi, ke sarewa da molo, nima tun da asuba zan tashi. 9 A cikin jama'a zan yi maka godiya, ya Ubangiji; zan raira yabo gare ka a cikin al'ummai. 10 Gama ƙaunarka tana da girma ƙwarai, ta kai har sama, amincika kuma ya kai gizagizai. 11 Ka ɗaukaka ya Allah, sama da sammai, darajarka ta ɗaukaka bisa dukkan duniya.

Zabura 58

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsara ga salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa.

1 Ku shugabanni kuna faɗin gaskiya? Ku jama'a kuna yin shari'ar gaskiya? 2 Babu, kun yi aikin mugunta cikin zuciyarku; kun baza tashin hankali da hannuwanku a cikin ƙasar dukka. 3 Tun daga cikin ciki, masu mugunta ke fanɗarewa, tun daga haihuwarsu suke ratsewa, suna faɗin ƙarya. 4 Dafinsu kamar dafin maciji ya ke, suna kama da kurmar ƙasa wadda take toshe kunnuwanta, 5 wadda bata jin muryar masu layu, komai gwanintarsu. 6 Ka karairaya haƙoransu a cikin bakunansu, ya Allah; ka ciccire manyan haƙoran 'yan zakuna, ya Yahweh. 7 Bari su narke kamar ruwan dake gangarewa; idan suka harba kibansu, bari su zama kamar basu yi saiti ba. 8 Bari su zama kamar dodon koɗi wanda ke narkewa ya lalace, kamar jaririn da mace ta haifa kafin lokacinsa yayi wanda bai taɓa ganin hasken rana ba. 9 Kafin tukunyarka ta ji zafin wuta, zai kwashe su da guguwa, da ɗanye da wanda a ke ƙonawa dukka. 10 Mai adalci zai yi farinciki sa'ad da ya ga ramako daga Allah, zai wanke ƙafafunsa da jinin masu mugunta, 11 domin mutane su ce, "Gaskiya ne akwai lada ga mutum mai adalci, gaskiya ne akwai Allah wanda ke shar'anta duniya.

Zabura 59

Domin shugaban mawaƙa; wadda aka tsarawa salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa lokacin da Saul ya aika, suka kuma yi fakon gidan domin su kashe shi.

1 Ka kuɓutar dani daga maƙiyana, ya Allahna; ka ɗora ni can sama nesa daga waɗanda suke taso mani. 2 Ka tsare ni daga waɗanda suke aikata mugunta, ka cece ni daga mutane waɗanda suke zubar da jini. 3 Gama, duba, sun yi kwanto domin su ɗauki raina. Manya manyan masu aika mugunta sun tattara kansu gãba dani, amma ba saboda nayi kuskure ko zunubi ba, Yahweh. 4 Sun shirya domin su tattake ni ba tare da laifina ba, duba, tashi ka taimake ni. 5 Kai Yahweh, Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, tashi ka hori dukkan al'ummai. Kada ka ji tausan wani mai laifin aika mugunta ko ɗaya. 6 Sukan dawo da yamma, su zagaya birnin suna haushi kamar karnuka. 7 Duba suna yin gyatsa da bakunansu, takubba suna kan leɓunansu, suna cewa, "Wane ne ya ke sauraren mu?" 8 Amma kai, Yahweh, kana yi masu dariya, dukkan al'ummai ba a bakin komai suke a gare ka ba. 9 Allah, ƙarfina, zan kasa kunne gare ka, kaine hasumiyata mai tsawo. 10 Allahna zai same ni da alƙawarin amincinsa, Yahweh, zai biya muradina a kan maƙiyana. 11 Kada ka kashe su domin kada jama'ata su mance. Yahweh, garkuwarmu, ka warwatsa su, ka sa su faɗi. 12 Saboda kalmomin bakinsa, da maganar leɓunansu, ka bari a kwashe su cikin girman kansu, kuma saboda la'ana da ƙarairayin da suka bayyana. 13 Ka hallaka su cikin hasalarka, ka hallaka su domin kada su ƙara kasancewa. Bari su sani, Allah ne ke mulki cikin Yakubu kuma har iyakar duniya. Selah 14 Sukan dawo da yamma, su zagaya birnin suna haushi kamar karnuka. 15 Sukan yi yawo suna neman abinci, sukan yi gurnani idan ba su ƙoshi ba. 16 Amma zan yi rairawa game da ƙarfinka, da safe kuma zan yi rairawa saboda ƙaunarka madawwamiya! Gama ka zama hasumiyata mai tsawo, mafaka a lokacin dani ke cikin matsala. 17 A gare ka ƙarfina zan raira yabo, gama Yahweh ne hasumiyata mai tsawo, Allah mai amincin alƙawari.

Zabura 60

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Shushan Idut. Salon waƙar Dauda, domin koyarwa. Lokacin da ya yi faɗa da Aram Naharayim da kuma Aram Zoba da Yowab ya dawo daga kisan Idomawa dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.

1 Yahweh, ka yashe mu, ka kutsa cikin matsararmu, ka yi fushi, ka dawo da mu. 2 Kasa ƙasar ta girgiza, ka ɓarke ta; tana girgiza, ka warkar da ɓarakarta. 3 Kasa mutanenka su ga abubuwa masu wuya, kasa mun sha ruwan inabin tangaɗi. 4 Saboda waɗanda ke darjantaka, kasa an tada tuta gãba da masu ɗaukar baka. 5 Saboda waɗanda kake ƙauna su kuɓuta, ka amsa mani ka kuɓutar da mu da hannun damanka. 6 Allah ya yi magana cikin tsarkinsa, "Zan yi farinciki, zan raba Shekem, zan karkasa Kwarin Sukot. 7 Giliyad tawa ce Manasse ma tawa ce, Ifraim kuma hular kwanona ce, Yahuda kuma sandar girmana ce. 8 Mowab bangajin wankina ne, zan ajiye takalmina a kan Idom, zan yi sowa ta murna saboda Filistiya." 9 Wa zai kawo ni birni mai ƙarfi? Wa zai kai ni Idom? 10 Amma kai Yahweh, ba ka yashe mu ba? Gama ba ka tafi yaƙi tare da sojojinmu ba. 11 Ka taimake mu gãba da maƙiyanmu gama taimakon mutum banza ne. 12 Da taimakon Allah za mu yi nasara; shi zai tattake maƙiyanmu.

Zabura 61

Domin shugaban mawaƙa; akan kayan kiɗa na tsarkiya. Zabura ta Dauda.

1 Ka ji kukana Yahweh, ka amsa addu'ata. 2 Daga iyakar duniya zan kira gare ka lokacin da zuciyata ta ruɗe, ka kai ni wurin dutsen da ya fi ni tsawo. 3 Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi daga maƙiyana. 4 Ka bar ni in zauna a shirayinka har abada! Ka bar ni in ɓoye cikin inuwar fukafukanka. Selah 5 Gama kai Allah, ka ji wa'adina, ka bani gãdon waɗanda suke darjanta sunanka. 6 Za ka sa ran sarki ya yi tsawo, shekarunsa kuma kamar tsararraki da yawa. 7 Zai kasance a gaban Yahweh har abada. 8 Zan raira yabo ga sunanka har abada, domin in cika wa'dina gare ka kowacce rana.

Zabura 62

Domin shugaban mawaƙa; bisa ɗabi'ar Yedutun. Zabura ta Dauda.

1 Na yi shiru a gaban Yahweh kaɗai, daga wurin sa cetona ya ke zuwa. 2 Shi kaɗai ne cetona, shi ne hasumiyata mai tsawo, ba zan girgiza ba sosai. 3 Har yaushe ku dukka, zaku kai hari ga mutum ɗaya? Domin ku rufe shi kamar bangon da a ke jigina da shi, shinge mai rawa? 4 Suna shawara da shi ne domin su ture shi daga matsayinsa mai daraja kaɗai; su na ƙaunar faɗin ƙarya, suna sa masa albarka da bakinsu, amma cikin zuciyarsu suna la'antar sa. Selah 5 Ga Allah kaɗai nake saurare, gama shi ne begena. 6 Shi kaɗai ne dutsena da cetona, shi ne hasumiyata mai tsawo ba zan jijjigu ba. 7 Allah ne cetona da ɗaukakata, dutsen ƙarfina da mafakata a cikin Allah suke. 8 Ku dogara gare shi kowanne lokaci, ku mutane, ku kafa zuciyarku a gaban sa, Allah shi ne mafakarmu. Selah 9 Ba shakka mutanen da basu da matsayi ba komai bane, waɗanda ke da matsayin kuma ƙarya ne. Idan a ka auna su a ma'auni ba su da nauyi, inda za a haɗa su a auna ba su da nauyin komai. 10 Kada ku dogara ga aikin zalunci ko ƙwace, kada ku sa begenku ga dukiyar wofi, gama ba su da amfanin komai, kada ku sa zuciya gare su. 11 Allah ya yi magana sau ɗaya, sau biyu kuwa na ji wannan: iko na Allah ne. 12 Kuma Ubangiji, a gare ka alƙawarin gaskiya yake. Gama kana ramawa kowanne mutum bisa ga abin da ya yi.

Zabura 63

Zabura ta Dauda, lokacin da ya ke a cikin dajin Yahuda.

1 Allah, kai ne Allahna, da gaske raina ya ke neman ka, raina yana ƙishin ka, jikina ya ƙagara ya gan ka, a cikin ƙasa da turɓaya in da babu ruwa. 2 Na dubo zuwa gare ka a cikin mutane masu tsarki domin in ga ikonka da ɗaukakarka. 3 Saboda alƙawarin ka mai aminci yafi rai, leɓunana zasu yabe ka. 4 Zan albarkace ka sa'ad da nake da rai, a cikin sunanka zan tada hannuwana. 5 Zai zama kamar na ci abinci mai ɓargo da kitse, zan yabe ka da leɓuna masu farinciki, 6 sa'ad da ni ke tunaninka a kan gadona, sa'ad da nake nazarin ka a cikin dare. 7 Gama kai ne taimakona, a ƙarƙashin inuwar fukafukanka nake yin farinciki. 8 Na manne maka hannun damanka yana tallafa ta. 9 Amma waɗanda ke nema su hallaka raina, zasu faɗa cikin wuri mai zurfi na duniya; 10 za a bashe su ga hannun masu aiki da takobi, zasu zama abicin diloli. 11 Amma sarki zai yi farinciki cikin Allah, dukkan wanda ya rantse da shi, zai yi fahariya da shi kuma, amma bakin masu faɗin ƙarya za a kwaɓe shi.

Zabura 64

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Ka ji muryata, Allah, ka saurari ƙarata; ka tsare raina daga tsoron maƙiyana. 2 Ka ɓoye ni daga shirin miyagu, daga hargowar masu aika mugunta. 3 Sun wasa harsunansu kamar takubba, sun haro kibansu, wato maganganu masu ɗaci, 4 domin su harbi wanda ba shi da laifi daga wurin da suke ɓoye, nan da nan suka harbe shi ba tare da sun ji tsoro ba. 5 Suna ƙarfafa kansu cikin shirya mugunta, suna shawara a asirce domin su ɗana tarkuna, suna cewa, "Wa zai gan mu?" 6 Suna ƙulla mugunta; "Mun gama" suka ce, "Natsastsen shiri" Tunanin ciki da zuciyar mutum suna da zurfi. 7 Amma Yahweh, zai harbe su, nan da nan kibau zasu ji masu ciwo. 8 Zasu yi tuntuɓe tun da ya ke harshensu yana gãba da su; dukkan waɗanda suka gan su zasu kaɗa kansu. 9 Dukkan mutane zasu ji tsoro su bayyana ayyukan Allah. Cikin hikima zasu yi tunani a kan abin da ya yi. 10 Masu adalci zasu yi murna da Yahweh, zasu sami mafaka a wurinsa. Dukkan waɗanda ke tafiya dai-dai zasu yi fahariya a cikin sa.

Zabura 65

Domin shugaban mawaƙa. Zabura. Waƙar Dauda.

1 Domin kai Allah a Sihiyona ne, yabonmu; da wa'adodinmu, za a kawo maka su a cikin Sihiyona. 2 Kai da kake jin addu'a, a gare ka dukkan mutane za su zo. 3 Laifofi sun yi mana tsayayya, amma za ka gafarta zunubanmu, za ka kuma gafarta su. 4 Mai albarka ne mutumin daka zaɓa ya zo ya zauna a kusa da kai a cikin harabarka. Za mu gamsu da kyawawan abubuwan dake a gidanka, haikalinka mai tsarki. 5 Cikin adalci za ka amsa mana ka yi abubuwan mamaki, kai Allah na cetonmu, Kai wanda dukkan mutane ke dagara gake ka har da waɗanda ke a can hayin teku. 6 Gama kai ne ka kafa duwatsu suka yi ƙarfi, kai wanda ka yi ɗamara da iko. 7 Kai ne ka kwantar da rurin tekuna da balalloƙansu da hargowar mutane 8 Su waɗanda ke zama a can ƙarshen duniya suna jin tsoron alamun ayyukanka, kasa gabas da yamma suna farinciki. 9 Ka zo domin ka taimaki duniya; ka yi mata banruwa, kasa ta yi arziki, kogin Allah na cike da ruwa; tun da ka hallicci duniya ka tanadawa ɗan Adam hatsi. 10 Ka jiƙe kwarin kunyai a wadace, ka dai-daita kwarin kunyai sosai, kakan sa su yi taushi, kasa albarka a kan yabanyarsu. 11 Ka yi wa shekara dajiyar alherai, sawayen karusanka suka zubo da kitse a kan duniya. 12 Wuraren kiwo a jeji sun jiƙe da raɓa, ka sa tsire--tsire suyi farinciki. 13 Wuraren kiwo sun cika da garkuna, kwarurruka sun cika da hatsi, suna shewa ta farinciki, suna rairawa.

Zabura 66

Domin shugaban mawaƙa. Waƙa ta Zabura.

1 Ku yi sowa ta farinciki ga Yahweh, ku duniya dukka. 2 Ku raira ɗaukakar sunansa, ku sa yabonsa ya zama ɗaukakakke. 3 Ku ce da Allah, "Ayyukanka suna da ban tsoro! Da girman ikonka kasa maƙiyanka su yi ladabi a gabanka. 4 Dukkan duniya zasu bauta maka su raira yabo gare ka, zasu yi rairawa ga sunanka." Selah 5 Ku zo ku ga ayyukan Yahweh, ayyukansa na da ban mamaki ga 'yan Adam. 6 Ya mayar da teku busasshiyar ƙasa; sun bi ta cikin teku da ƙafa; can muka yi farinciki a cikin sa. 7 Da ikonsa ya ke mulki har abada, idanunsa suna lura da al'ummai; kada masu tawaye su ɗaukaka kansu. Selah 8 Ku albarkaci Allah, ku mutane, bari a ji amon yabonsa. 9 Ya bar mu cikin masu rai, bai bari ƙafafunmu suka yi tuntuɓe ba. 10 Gama kai Yahweh ka gwada mu, ka gwada mu kamar yadda a ke gwada azurfa. 11 Ka kawo mu cikin taru, ka ɗora mana kaya mai nauyi a kanmu. 12 Ka bari mutane su tattaka mu, mun shiga cikin wuta da ruwa, amma ka kawo mu cikin wuri mai faɗi. 13 Zan zo cikin gidanka da baiko na ƙonawa, zan cika wa'adodina gare ka, 14 waɗanda leɓunana suka yi alƙawarin su, bakina kuma ya furta, sa'ad da nake cikin wahala. 15 Zan kawo maka baiko na ƙonawa da dabbobi masu ƙiba da ƙamshin raguna; zan miƙa bijjimai da awaki. 16 Ku zo ku saurara, dukkan ku dake tsoron Allah, zan bayyana abin da ya yi domin raina. 17 Na yi kuka gare shi da bakina, harshena kuma ya yabe shi. 18 Idan dana dubi zunubi a cikin zuciyata, da Ubangiji bai saurare ni ba. 19 Amma da gaske Allah ya ji; ya kula da muryar addu'ata. 20 Albarka ta tabbata ga Allah, wanda bai yi watsi da addu'ata ba ko ya ɗauke alƙawarinsa mai aminci daga gare ni ba.

Zabura 67

Domin shugaban mawaƙa; a kan kayan kiɗa na tsarkiya. Zabura, waƙa.

1 Bari Allah ya yi mana jinƙai, yasa fuskarsa ta haskaka wajenmu. Selah 2 domin a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma cikin al'ummai dukka. 3 Bari mutane su yabi Allah, dukkan mutane su yabe ka. 4 Oh, bari al'ummai suyi murna su raira domin farinciki, gama za ka hukunta mutane cikin adalci, ka shugabanci mutanen duniya. Selah 5 Bari mutane su yabe ka Allah, bari dukkan mutane su yabe ka. 6 Ƙasa ta ba da amfaninta kuma Allah, Allahnmu ya albarkace mu. 7 Allah ya albarkace mu kuma dukkan ƙarshen duniya na darjanta shi.

Zabura 68

Domin shugaban mawaƙa; Zabura ta Dauda, waƙa.

1 Bari Allah ya tashi, bari maƙiyansa su warwatse, bari kuma waɗanda ke ƙin sa su gudu daga gabansa. 2 Ka kore su kamar yadda hayaƙi ke watsewa, kamar yadda saƙar zuma kan narke a gaban wuta, haka masu mugunta zasu lalace a gaban Allah. 3 Amma bari masu adalci suyi murna, su ɗaukaka a gaban Allah; bari su yi farinciki su kuma ji daɗi. 4 Ku raira ga Allah! Ku raira yabbai ga sunansa! Ku yabe shi wanda ke ratsawa ta filin kwarin Kogin Yodan! Yahweh ne sunansa! Ku yi farinciki a gabansa! 5 Uban marar uba, alƙali saboda gwauraye, shi ne Allah daga wurin zamansa mai tsarki. 6 Allah yakan sa masu kaɗaici cikin iyali, ya kan fito da 'yan kurkuku cikin waƙa, amma 'yan tawaye suna zama a faƙo. 7 Allah idan da kayi tafiya a gaban mutanenka, idan ka bi ta cikin jeji, Selah 8 Ƙasa takan girgiza, sama kan zubo da ruwa a gaban Allah, a gaban Allah sa'ad da ya zo Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra'ila. 9 Kai, Allah, ka aiko da ruwa isasshe, ka ƙarfafa abin gãdonka sa'ad da suka gaji. 10 Mutanenka suka zauna a ciki; kai, Allah, daga cikin alherinka ka bayar ga matalauta. 11 Ubangiji ya bada umarnai, waɗanda suka sanar da su kuwa manyan sojoji ne. 12 Sarakunan sojoji sun gudu, suka gudu, matayen dake zama a gida kuwa suka raba ganima. 13 Kurciyoyi rufe da azurfa, da fukafukan zinariya rawaya. Sa'ad da waɗansu ku mutane kuka tsaya a garkunan tumaki, me ya sa kuka yi haka? 14 Mai iko dukka ya tarwatsa sarakuna a wurin, sai ya zama kamar dusar ƙanƙara a Dutsen Zalmon. 15 Babban dutse shi ne tudun ƙasar Bashan, dutse mai tsawo shi ne tudun ƙasar Bashan. 16 Me yasa ki ke ƙyashi ke ƙasar kan tudu, a kan dutsen da Allah ya zaɓi ya zauna a wurin? Tabbas, Yahweh zai zauna a cikinta har abada. 17 Karusan Allah dubu ashirin ne, dubbai bisa dubbai; Ubangiji na cikinsu a wuri mai tsarki, kamar a Sinai. 18 Ka haye sama, ka kwashi 'yan bauta, ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga waɗanda suka yi faɗa da kai, domin kai Yahweh Allah, ka zauna a can. 19 Albarka ga Ubangiji, wanda kullum ya ke kula da mu, Allah wanda shi ne cetonmu. 20 Allahnmu, Allah ne wanda ke yin ceto. Yahweh, Ubangiji, shi ne kaɗai wanda zai iya kuɓutar da mu daga mutuwa. 21 Amma Allah zai rotsa kan maƙiyansa, ta wurin fatar kai mai gashi ta waɗanda ke tafiya cikin yi masa laifi. 22 Ubangiji yace, "Zan dawo da maƙiyana daga Bashan, zan dawo da su daga cikin zurfin teku 23 domin ka ragargaza maƙiyanka, kana tsoma ƙafarka cikin jini, domin harsunan karnukanka su sami rabo daga cikin maƙiyanka." 24 Sun ga shigowar ka, Allah, shigowar Allahna, Sarkina cikin wuri mai tsarki. 25 Mawaƙa suka fara yin gaba, masu busa na bin baya, a tsakiya kuwa 'yammata na kaɗa molo. 26 Ku albarkaci Allah a cikin taro, ku yabi Yahweh, ku zuriyar Isra'ila na gaskiya. 27 Da fari akwai Benyamin, kabila mafi ƙanƙanta, sai kuma shugabannin Yahuda da jama'arsu, shugabannin Zebulun da shugannin Naftali. 28 Allahnka, ya Isra'ila ya umarta ƙarfinka, ka nuna ikonka, Allah, kamar yadda ka nuna shi a lokacin dã. 29 Ka nuna mana ikonka daga Yerusalem inda sarakuna ke kawo maka kyautai. 30 Yi ruri cikin yaƙi gãba da namomin jejin dake zama cikin iwa, a kan mutane, da bijimai masu yawa da 'yan maruƙa. Kunyatar dasu kasa su kawo maka kyautai, ka tarwatsa mutanen dake ƙaunar yin yaƙi. 31 Sarakuna zasu fito daga Masar; Itofiya zata yi sauri ta kawo hannuwanta ga Allah. 32 Ku raira yabbai ga Allah ku mulkokin duniya; Selah ku raira yabbai ga Yahweh. 33 Gare shi wanda ke sukuwa kan saman sammai, shi wanda ya kasance tun zamanin dã; duba, ya tada muryarsa da iko. 34 Ku furta ƙarfi ga Allah, darajarsa tana kan Isra'ila, ikonsa na cikin sararin sama. 35 Allah, kai abin tsoro ne a cikin wurinka mai tsarki, Allah na Isra'la yana ba da ƙarfi da iko ga mutanensa. Albarka ga Allah.

Zabura 69

Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Shoshanayim. Zabura ta Dauda.

1 Ka cece ni Allah, gama ruwaye sun sa raina cikin hatsari. 2 Na nutse cikin laka, mai zurfi inda ba wurin tsayawa; na zo cikin ruwa mai zurfi, rigyawa ta sha kaina. 3 Na gaji da kuka, maƙogwarona ya bushe, idanuna sun dishe sa'ad da nake jiran Allahna. 4 Waɗanda ke ƙi jinina ba dalili sun fi gashin kaina yawa, su waɗanda zasu datse ni saboda dalilan da ba dai-dai ba, suna da ƙarfi, abin da ban sata ba, sai na mayar. 5 Allah, ka san wawancina, zunubaina kuma ba ɓoye suke a gare ka ba. 6 Kada waɗanda ke jiran ka su ji kunya saboda ni, Ubangiji Yahweh Mai Runduna, kada masu neman ka su ƙasƙanta saboda ni, Allah na Isra'ila. 7 Saboda kai na jure da tsautawa; kunya ta rufe fuskata. 8 Na zama bãƙo ga 'ya'uwana, bare kuma ga 'ya'yan mahaifiyata. 9 Gama niyyar zuwa gidanka ta ɗauke hankalina, tsautawar waɗanda ke tsauta maka ta faɗo kaina. 10 Idan na yi kuka na ƙi cin abinci, sai su zage ni. 11 Idan kayan makoki suka zama kayan sawata, sai in zama abin misali gare su. 12 Waɗanda ke zama a ƙofar birni magana suke yi a kaina, mashaya waƙa su ke yi a kaina. 13 Amma ni addu'ata gare ka take, Yahweh, sa'ad da ka ga yayi dai-dai, ka amsa mani cikin aminci cetonka. 14 Ka tsamo ni daga cikin laka, kada ka bari ni nutse; bari a ɗauke ni daga waɗanda ke ƙina, a kuma tsamo ni daga cikin ruwaye masu zurfi. 15 Kada ka bari rigyawa ta sha kai na, kada ka bari zurfi ya haɗiye ni. Kada ka bari rami ya rufe bakinsa a kaina. 16 Ka amsa mani Yahweh, gama alƙawarin amincinka yana da kyau; domin jiye-jiyen ƙanka suna da yawa zuwa gare ni, ka juyo wajena. 17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka, gama ina cikin wahala, ka amsa mani da sauri. 18 Ka zo wuri na ka cece ni, saboda maƙiyana ka fanshe ni. 19 Ka san tsautawar da a ke yi mani, ka san kunyata, ka san ƙasƙancin da nake sha; dukkan magabtana a gabana suke. 20 Tsautawa ta karya zuciyata; cike nake da nauyi; na duba ko wani zai ji tausayi na, amma ban samu ba. 21 Sun ba ni dafi shi ne abincina, cikin ƙishina kuma sai suka ba ni ruwan tsami domin in sha. 22 Bari teburin gabansu ya zama tarko, sa'ad da suke tsammanin suna lafiya bari ya zama tarko a gare su. 23 Bari idanunsu su dishe yadda ba zasu iya gani ba; bari kwankwasonsu su riƙa yin rawa. 24 Ka zuba masu hasalarka, bari zafin fushinka ya yi ƙuna a kan su. 25 Bari wurin zamansu ya zama kufai; kada kowa ya zauna a rumfunansu. 26 Gama sun tsanantawa wanda ka fyaɗe ƙasa. Sun ƙarawa waɗanda suka ji rauni zafin ciwo. 27 Ka zarge su a kan aikata mugunta a kan mugunta; kada ka bari su zo cikin nasararka mai adalci. 28 Bari a shafe su daga cikin lattafin rai, kada a rubutasu tare da tsarkaka. 29 Amma ni matalauci ne mai baƙinciki, bari cetonka; Allah, ya sanya ni can sama. 30 Zan yabi sunan Allah da waƙa, zan ɗaukaka shi da shaidar godiya. 31 Wannan zai gamshi Yahweh fiye da sã da bijimi mai ƙahonni da kofatai. 32 Masu taushin zuciya za su gani suyi murna, ku da kuke neman Yahweh, zukatanku zasu rayu. 33 Gama Yahweh na sauraron mabuƙata, ba ya kuma raina 'yan sarƙarsa. 34 Bari sama da ƙasa su yabe shi da tekuna da dukkan abubuwan dake iyo a cikinsu. 35 Gama Allah zai ceci Sihiyona, zai sake gina biranen Yahuda; mutane zasu zauna a can ya zama nasu. 36 Zuriyar bayinsa zasu gaje shi, waɗanda ke ƙaunar sunansa zasu zauna a can.

Zabura 70

Domin shugaban mawaƙa Zabura ta Dauda; ta kawo tunawa.

1 Ka cece ni ya Allah, Yahweh, ka zo da sauri ka taimake ni. 2 Bari waɗanda ke so su ɗauki raina su ji kunya su ƙasƙanta; bari su koma baya a wulaƙance, su waɗanda ke murna da raɗaɗina. 3 Bari su koma baya cikin kunya, su waɗanda ke cewa, "Aha, aha." 4 Bari dukkan waɗanda ke neman ka suyi farinciki, suyi murna a cikin ka, bari waɗanda ke ƙaunar cetonka koyaushe su ce, "A yabi Allah." 5 Amma ni matalauci ne mai bukata, ka yiwo sauri wurina Allah, kai ne taimakona ka kuɓutar dani, Yahweh, kada ka yi jinkiri.

Zabura 71

1 Yahweh, a gare ka nake samun mafaka, kada ka taɓa bari in ji kunya. 2 Ka kuɓutar da ni ka sa in zauna lafiya cikin adalcinka. 3 Ka zama dutsen fakewa a gare ni inda zan zo ko yaushe, ka bada umarni a cece ni, gama kai ne dutsena da kagarata. 4 Ka cece ni, Allahna daga hannun miyagu, daga masu shirya mugunta. 5 Gama kai ne begena, Ubangiji Yahweh. Na dogara gare ka tun ina yaro. 6 Kai ne kake ta taimako na tun daga cikin ciki; kai ne ka fito dani daga cikin mahaifiyata; yabona a gare ka ya ke koyaushe. 7 Na zama misali ga mutane da yawa, kai ne mafakata mai ƙarfi. 8 Bakina zai cika da yabonka, da ɗaukakarka dukkan yini. 9 Kada ka yashe ni a lokacin dana tsufa, kada ka manta dani lokacin da ƙarfina ya ƙare. 10 Gama maƙiyana maganata, waɗanda ke neman raina suna shiri tare. 11 Sun ce, "Allah ya yashe shi, ku bi ku ɗauko shi, gama ba wanda zai cece shi." 12 Allah, kada ka yi nisa dani, Allahna, ka yi sauri ka taimake ni. 13 Bari su sha kunya su hallaka su waɗanda suka hasalar da raina; su ji kunya su hallaka. bari zarga da raini su rufe su, su waɗanda ke so su lahanta ni. 14 Amma zan sa begena a gare ka, zan yabe ka gaba-gaba. 15 Bakina zai yi maganar adalcinka da cetonka dukkan yini, koda yake ba zan iya gane shi ba. 16 Zan zo da manyan ayyukan Ubangiji Yahweh, zan faɗi adalcinka, naka kaɗai. 17 Allah, ka koya mani tun ina saurayi, har yanzu ina shelar ayyukanka na ban mamaki. 18 I, ko lokacin da kaina ya yi furfura, Allah, kada ka yashe ni, ina ta shelar ƙarfinka ga tsara mai zuwa, ikonka kuma ga kowanne mai zuwa. 19 Adalcinka kuma, ya Allah yana da tsawo ƙwarai, kai da ka yi manyan abubuwa, Allah, wane ne kamar ka? 20 Kai da ka nuna mana wahalhalu da yawa masu tsanani, za ka farfaɗo damu, ka fito damu daga ƙarƙashin ƙasa. 21 Ka ƙara mani martaba, ka juyo ka ƙarfafa ni. 22 Zan kuma yi maka godiya da molo saboda amincinka, Allahna; gare ka zan yi yabo da molo, mai tsarki na Isra'ila. 23 Leɓunana zasu yi sowa ta farinciki, sa'ad da nake raira yabo a gare ka-har da raina, wanda ka fanso. 24 Harshena kuma zai yi maganar adalcinka dukkan yini; gama sun ji kunya sun rikice, su waɗanda ke nema su lahanta ni.

Zabura 72

Zabura ta Suleman.

1 Ka ba sarki dokokinka masu adalci, Allah, adalcinka kuma ga ɗan sarkin. 2 Dãma ya hukunta jama'arka da adalci, matalautanka kuma da adalci. 3 Dãma duwatsu su fito da salama saboda mutanenka; dãma tuddai kuma su fito da adalci. 4 Dãma ya hukunta mutane matalauta; dãma ya ceci 'ya'yan mabuƙata, ya ragargaza azzalumi. 5 Dãma su ba ka daraja muddin rana tana haskakawa, wata kuma yana nan har zuwa tsararraki dukka. 6 Dãma ya sauko kamar ruwan sama a kan ciyawar da a ka tattake, kamar zubowar ruwan sama a kan ƙasa. 7 Dãma masu adalci su yalwata a kwanakinsa, dãma kuma a sami salama a yalwace har sai wata ya shuɗe. 8 Dãma ya yi mulki daga teku zuwa teku, daga kogi har zuwa ƙarshen duniya. 9 Dãma waɗanda ke zama a jeji su rusuna a gabansa; dãma maƙiyansa kuma su lashi turɓaya. 10 Dãma sarkunan Tarshish da na tsibirai su kawo gaisuwa a gare shi, dãma sarakunan Sheba da Seba su ba shi kyautai. 11 I, dãma dukkan sarakuna su rusuna a gabansa, dãma kuma dukkan al'ummai su bauta masa. 12 Gama ya kan taimaki mabuƙacin da yayi kuka da matalaucin da ba shi da mai taimako. 13 Ya ji tausayin mabuƙata da matalauta, ya kuma ceci ran mabuƙata. 14 Ya fanshi rayukansu daga wahala da kuma wulaƙanci, jininsu kuma yana da daraja a idanunsa. 15 Dãma ya rayu! Dãma a ba da zinariyar Sheba a gare shi. Bari mutane su yi masa addu'a koyaushe; dãma Yahweh ya albarkace shi dukkan yini. 16 Dãma a sami hatsi a yalwace a cikin ƙasa, na kan tudu kuma amfaninsu ya yi yabanya. Dãma kawunan hatsinsu ya zama kamar Lebanon, dãma jama'a su sami albarka kamar ciyawa ta saura. 17 Dãma sunansa ya kasance har abada, dãma sunansa ya ci gaba muddin rana ta nan; dãma jama'a su sami albarka ta wurinsa; dãma dukkan al'ummai su kira shi mai albarka. 18 Dãma Allah Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zama mai albarka; wanda shi kaɗai ne ke yin abubuwan ban mamaki. 19 Dãma sunansa mai daraja ya zama mai albarka har abada, dãma kuma dukkan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin -- Amin. 20 Dauda ɗan Yesse ya gama yin addu'o'insa. Littafi na Uku.

Zabura 73

Zabura ta Asaf.

1 Hakika Allah mai alheri ne ga Isra'ila, gare su da suke da tsabtar zuciya. 2 Amma a gare ni kafafuna sun kusa su zame; kafafuna sun kusa su zame waje daga karkashina. 3 saboda na ji kishin masu girmankai sa'ad da na ga wadatar masu mugunta. 4 Gama basu da raɗaɗi har ranar mutuwarsu, amma suna da ƙarfi kuma suna ci da kyau. Basu da nawayar sauran mutane; 5 Basu da masifu kamar na sauran mutane. 6 Girmankai na rataye a wuyansu kamar sarƙa; tashin hankali ya rufe su kamar riga. 7 Daga irin wannan makantar zunubi ke zuwa; mugayen tunani sun ratsa zukatansu 8 Suna ba'a kuma suna magana cikin mugunta; cikin fankamarsu suna yin kurarin zalunci. 9 Suna magana gãba da sammai, harsunan su kuma na tattaki a ƙasa. 10 Domin haka mutanensa sun juya gare su isassun ruwaye sun cika kwararo. 11 Suka ce, "Ta yaya Allah ya sani? Akwai wani sani a wurin maɗaukaki?" 12 Kula: waɗannan mutane mugayene; a koyaushe a huce suke, sai ƙara zama mawadata suke yi. 13 Lallai a banza na kiyaye zuciyata kuma na wanke hannuwana cikin rashin laifi. 14 Kowacce rana ina shan azaba da horo kowacce safiya. 15 Idan nace, "Zan faɗi waɗannan abubuwa," da naci amanar wannan tsarar ta 'ya'yanka. 16 Ko da shike na yi ƙoƙarin fahimtar waɗannan abubuwa, ya zama da wahala a gare ni. 17 Daga nan sai na tafi cikin wuri mai tsarki na Allah daga nan na fahimci makomarsu. 18 Hakika ka sanya su a wurare masu santsi; ka kawo su ƙasa ga hallaka. 19 Yadda suka zama jeji farat ɗaya! ƙarshensu yazo sun ƙarasa cikin babban tsoro. 20 Sun zama kamar mafarki bayan da mutum ya farka; Ya Ubangiji, sa'ad da ka tashi, ba zaka yi tunanin komai game da waɗannan mafarkan ba. 21 Gama zuciyata ta damu, a cikina nayi rauni. Na zama jahili na kuma rasa basira; 22 Na zama kamar dabba marar tunani a gabanka. 23 Duk da haka kullum ina tare da kai; Ka riƙe hannuna na dama. 24 Zaka bishe ni da shawarar ka bayan wannan ka karɓe ni zuwa ɗaukaka. 25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba wani a duniya da nake marmari in ba kai ba. 26 Jikina da zuciyata sun yi sanyi, amma Allah shi ne ƙarfin zuciyata har abada. 27 Waɗanda suke nesa da kai zasu lalace; zaka hallaka dukkan marasa aminci gare ka. 28 Amma ni, abin da nake bukata shi ne in kusanci Allah. Na mai da Ubangiji Yahweh mafakata. Zan bayyana dukkan ayyukanka.

Zabura 74

Salon waƙar Asaf.

1 Ya Allah, don me ka yashe mu har abada? Don me fushin ka yayi ƙuna a kan tumakin makiyayarka? 2 Ka da tuna mutanenka, waɗanda ka saya a zamanin dã, kabila wadda ka fãnsa su zama abin gãdonka, da Tsaunin Sihiyona, inda kake zama. 3 Kazo ka dubi dukkan hallakarwa, dukkan ɓarnar da maƙiyi yayi a cikin wuri mai tsarki. 4 Abokan gãbar ka sun yi ruri a tsakiyar zaɓaɓɓen wurinka; sun kafa tutocin yaƙinsu. 5 Sun sassare ruƙuƙin kurmi da gatura. 6 Sun ragargaza sun kuma sassake su dukka; sun karya su da gatura da gudumai. 7 Sun kunna wa wurinka mai tsarki wuta; sun tozarta wurin zaman ka, sun buga shi har ƙasa. 8 A cikin zuciyarsu suka ce, "Zamu hallakar dasu dukka," Sun ƙone dukkan wuraren taruwarka cikin ƙasar. 9 Bamu ga wasu alamu ba; ba sauran wani annabi, ba wani a cikin mu da yasan har yaushe wannan zai ƙare. 10 Ya Allah, har yaushe maƙiyi zai yi ta cin mutuncin ka? Maƙiyi zai yi ta saɓon sunanka har abada? 11 Donme ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fito da hannunka na dama daga cikin rigarka ka hallaka su. 12 Duk da haka Allah sarkina ne tun zamanun dã, mai kawo ceto a duniya. 13 Ka raba teku da ƙarfinka; ka farfasa kawunan dodannin teku cikin ruwaye. 14 Ka murƙushe kan Lebiyatan; ka ciyar da waɗanda suke zama cikin jeji da shi. 15 Ka karya buɗaɗɗun maɓuɓɓulai da ƙoramai; kasa koguna masu gudu su ƙafe. 16 Yini naka ne, dare kuma naka ne; kaine ka sanya rana da wata. 17 Kaine ka sanya dukkan iyakokin duniya; kayi damina da rani. 18 Yahweh, Ka tuna yadda maƙiyi yayi ta jefa maganganun banza a kanka, wawayen mutanen nan sun yi saɓon sunanka. 19 Kada ka miƙa ran kurciyarka ga naman jeji. Kada ka manta da ran mutanenka da ake zalunta har abada. 20 Katuna da alƙawarinka, gama wurare masu duhu na ƙasa suna cike da tashin hankali. 21 Kada ka bari waɗanda ake zalunta su dawo cikin kunya; bari talakawa da waɗanda ake zalunta su yabi sunanka. 22 Ka tashi, ya Allah; ka kãre mutuncinka; ka tuna yadda wawaye suke zaginka dukkan yini. 23 Kada ka manta da muryar magabtanka ko hargowar waɗannan da suke ci gaba da adawa da kai.

Zabura 75

Domin shugaban mawaƙa; ga Salon murya. Zabura ta Asaf, waƙa.

1 Muna yi maka godiya, ya Allah; muna godiya, domin ka bayyana kasancewarka; mutane suna faɗin ayyukanka na al'ajabi. 2 A ƙayyadajjen lokaci zanyi hukunci da dai-daita. 3 Koda ya ke duniya da mazauna cikinta sun girgiza cikin tsoro, na kafa wa duniya ginshiƙai. Selah 4 Nace wa masu girmankai, "Kada kuyi girmankai," ga masu mugunta kuma, "Kada ku ɗaga ƙaho; 5 kada ku ɗaga ƙahonku ga sammai; kada kuyi magana da ɗaga wuya na rashin mutuntawa." 6 Ba daga gabas bane ko daga yamma, kuma ba daga jeji bane ɗaukaka take fitowa ba. 7 Amma Allah ne mai shari'a; yakan ƙasƙantar yakan kuma ɗaukaka sama. 8 Gama Yahweh ya riƙe ƙoƙon inabi cikin hannunsa mai sa buguwa, wanda yake gauraye da kayan yaji, yana tsiyayar da shi. Hakika dukkan miyagun duniya zasu shanye shi dukka. 9 Amma zan ci gaba da faɗin abin da kayi; Zan raira yabbai ga Allah na Yakubu. 10 Yace, zan datse dukkan ƙahonnin miyagu, amma‌‌ ƙahonnin masu adalci zasu ɗaukaka."

Zabura 76

Domin shugaban mawaƙa, a bisa kan girayu. Zabura ta Asaf, waƙa.

1 Allah ya sanar da kansa cikin Yahuda; sunansa mai girma ne cikin Isra'ila. 2 Rumfarsa cikin Salem take; wurin zaman sa cikin Sihiyona ya ke. 3 A can ya kakkarya kibawu na baka, garkuwa da takobi da sauran kayan yaƙi. Selah 4 Ka haskaka da sheƙi kuma ka bayyana ɗaukakarka, daka sauka daga duwatsu, wurin daka kashe masu azabtar da kai. 5 Masu ƙarfin zuciya an washe su; an kashe su. Dukkan jarumawa sun rasa mai taimako. 6 Bisa ga tsautawarka, Allah na Yakubu, doki da mahayinsa sun faɗi sun mutu. 7 Kai, I kaine za a ji tsoro; wa zai tsaya gabanka lokacin da kayi fushi? 8 Daga sama kasa aji hukuncinka; duniya ta ji tsoro tayi shiru 9 lokacin da kai, Allah, ka tashi don tabbatar da hukunci kuma ka ceci dukkan waɗanda ake zalunta na duniya. Selah 10 Hakika fushin hukuncin ka akan ɗan adam zai kawo maka yabo; ka yiwa kanka ɗamara da sauran abin da ya ragu na fushinka. 11 Kayi alƙawura ga Yahweh Allahnka ka kumaa cika su. Bari duk waɗanda suke kewaye da shi su kawo kyautai gare shi wanda ya isa a ji tsoronsa. 12 Ya datse ruhun 'ya'yan sarakai; sarakunan duniya sun ji tsoron sa.

Zabura 77

Domin shugaban mawaƙa; kamar na Yedutun. Zabura ta Asaf.

1 Da muryata zan yi kira ga Allah; Zan yi kira da muryata ga Allah, Allah zai ji ni. 2 A cikin ranar masifata na biɗi Ubangiji; da dare na miƙar da hannuwana waje, ba kuwa zasu gaji ba. Raina yaƙi ta'azantuwa. 3 Na tuna da Allah yayin da nayi nishi; Nayi tunaninsa yayin dana sụma. Selah 4 Ka riƙe idanuna a buɗe; na damu ƙwarai na kasa magana. 5 Na tuna da kwanakin dã, game da lokuttan da suka wuce tun-tuni. 6 A cikin dare na tuna da waƙar dana taɓa rairawa. Nayi tunani a hankali kuma nayi ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru. 7 Ko Ubangiji zai ƙini har abada? Ba zai ƙara nuna cewa ya ji ɗaɗi na ba? 8 Amintaccen alƙawarinsa ya tafi har abada? Ko alƙawarinsa ya tsinke har abada? 9 Ko Allah ya manta zama mai alheri? Ko fushinsa ya kulle jinƙansa ne? Selah 10 Nace, "Wannan baƙinciki na ne: Canjin hannun dama na Maɗaukaki a kanmu." 11 Amma zan tuna da ayyukanka; Zan yi tunani game da ayyukanka na al'ajabi na dã. 12 Zan yi bin-binin dukkan ayyukanka kuma in yi tunani a kansu. 13 Hanyarka, ya Allah, mai tsarki ce, ba wani allah da za a kwatanta shi da Allahnmu babba? 14 Kaine Allah wanda kake aikata al'ajibai; ka bayyana ƙarfinka tsakanin dangogi. 15 Ka ba mutanenka nasara ta wurin girman ikonka - zuriyar Yakubu da Yosef. Selah 16 Ruwaye sun ganka, ya Allah; ruwaye sun ganka, kuma sunji tsoro; zurfafa sun raurawa. 17 Giza-gizai sun zubo da ruwa ƙasa; hadarin sammai sun yi tsawa; hasken walƙiyarka sun tashi kamar kibau. 18 Muryar tsawarka an ji ta cikin guguwa; hasken ya ɗaga duniya; duniya ta raurawa ta girgiza kuma. 19 Hanyarka tabi ta teku tafarkin ka kuma ta manyan ruwaye, amma ba a ga sawayenka ba. 20 Ka bi da mutanenka kamar garken tumaki ta hannun Musa da Haruna.

Zabura 78

Salon waƙar Asaf.

1 Ku ji koyarwata, ya mutanena, ku saurari maganar bakina. 2 Zan buɗe bakina cikin misalai; Zan raira game da ɓoyayyun abubuwa na dã. 3 Waɗannan sune abubuwan da muka ji muka kuma koya, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana. Ba zamu ɓoye su daga zuriyarsu ba. 4 Zamu sanar da tsara mai zuwa game da yabban ayyukan Yahweh, ƙarfinsa, da al'ajiban da ya aikata. 5 Gama ya tabbatadda shaidar alƙawari cikin Yakubu ya sanya shari'a cikin Isra'ila. Ya umarci kakanninmu cewa su koyar dasu ga 'ya'yansu. 6 Ya umarta wannan domin tsara mai zuwa ta iya sanin umarnansa, 'ya'yan da ba a haifa ba, su kuma su faɗi wa 'ya'yansu. 7 Daga nan sai su sa zuciyarsu ga Allah kada su manta da ayyukansa amma su kiyaye dokokinsa. 8 Daga nan ba zasu zama kamar kakanninsu ba, da suka zama da taurin kai da tsara mai tayarwa, tsarar da zukatansu ba dai-dai suke ba, waɗanda ruhohinsu basu tsaya sun yi aminci ga Allah ba. 9 'Ya'yan Ifraim sun riƙe makamai tare da bakukkuna, amma suka juya baya a ranar yaƙi. 10 Basu kiyaye alƙawari da Allah ba, suka ƙi yin biyayya da dokarsa. 11 Suka manta da ayyukansa, ayyukan al'ajiban daya nuna masu. 12 Sun manta da ayyukan mamaki da yayi a idanun kakanninsu a cikin ƙasar masar, cikin ƙasar Zowan. 13 Ya raba teku ya ƙetaradda su; ya sa ruwa ya tsaya kamar bangaye. 14 Da rana ya bishe su da girgije dukkan dare kuma da hasken wuta. 15 Ya tsaga duwatsu cikin jeji, ya basu ruwa a yalwace, isasshe dake iya cika zurfafan teku. 16 Yasa rafuffuka su malala daga cikin dutse ya kuma sa ruwan ya gudana kamar koguna. 17 Duk da haka suka ci gaba da yi masa zunubi, suna tayar wa Maɗaukaki cikin ƙasa busasshiya. 18 Suka ƙalubalanci Allah cikin zukatansu ta wurin tambayar abinci domin ƙosar da marmarinsu. 19 Sun yi wa Allah baƙar magana; suka ce, "Zai yiwu Allah ya shirya teburi a cikin jeji? 20 Duba, lokacin da ya bugi dutsen, ruwaye suka ɓullo rafuffuka suka yi ambaliya. Amma zai yiwu ya bada gurasa kuma? Zai iya tanada nama domin mutanensa?" 21 Lokacin da Yahweh ya ji wannan, yayi fushi; wutarsa tayi ƙuna akan Yakubu, fushinsa kuma ya hari Isra'ila, 22 saboda basu gaskata Allah ba basu kuma dogara ga cetonsa ba. 23 Duk da haka ya umarci sammai a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sararin sama. 24 Ya zuba masu manna su ci, ya kuma basu hatsi daga sama. 25 Mutane suka ci abincin mala'iku. Ya aika masu da abinci isasshe. 26 Yasa iskar gabas ta hura cikin sama, ta wurin ikonsa kuma ya jagoranci iskar kudu. 27 Ya zuba masu nama kamar ƙura, tsuntsaye da yawa kamar yashin teku. 28 Suka faɗo a tsakiyar sansaninsu, ko'ina kewaye da rumfunansu. 29 Suka ci suka ƙoshi sosai. Ya basu abin da suke marmari. 30 Amma duk da haka basu cika ba; tun abincinsu na cikin bakinsu. 31 Daga nan fushin Allah ya buge su ya kashe mafi ƙarfin su. Majiya ƙarfin Isra'ila ya buga su ƙasa. 32 Duk da wannan, sun ci gaba da yin zunubi kuma basu gaskata ayyukan al'ajabansa ba. 33 Domin haka Allah ya taƙaita kwanakin su; shekarunsu suna cike da razana. 34 Duk sa'ad da Allah ya buge su, sai su fara neman sa, za su juyo su neme shi da gaske. 35 Zasu tuna cewa Allah ne dutsensu Allah maɗaukaki kuma shi ne mai fansarsu. 36 Amma suka yi masa daɗin baki suka kuma yi masa ƙarya da maganganunsu. 37 Gama zukatansu basu dogara gare shi ba, basu yi aminci ga alƙawarinsa ba. 38 Amma shi, mai tausayi ne, ya gafarta laifofinsu bai hallaka su ba. I, lokuta da yawa yakan janye fushinsa bai tayar da dukkan hasalarsa ba. 39 Ya tuna cikin jiki aka yi su, iska mai wucewa da bata dawowa. 40 Sau nawa suka yi ta tayar masa cikin jeji suka ɓata masa rai cikin hamada! 41 Akai akai suka tuhunci Allah suka cakuni Mai tsarki na Isra'ila. 42 Ba su tuna da ikonsa ba, yadda ya fanso su daga abokin gaba. 43 Lokacin da ya aikata alamominsa masu tsoratarwa cikin Masar da al'ajabansa cikin yankin Zowan. 44 Ya juyarda kogunan Masarawa su zama jini don kada su sha daga rafuffukansu. 45 Ya aika da cincirindon ƙudaje da suka cinye su da kwaɗi da suka mamaye ƙasar. 46 Ya bada amfaninsu ga fãra aikin hannun su kuma ga babe. 47 Ya lalata inabinsu da ƙanƙara itatuwansu masu bada 'ya'ya ga jaura. 48 Ya saukar da ƙanƙara ga garkunansu aradu kuma ta fãɗa akan dabbobinsu. 49 Ya zuba masu zafin fushinsa. Ya aika da fushi, hasala, da wahala kamar wakili mai kawo masifa. 50 Ya baje wa fushinsa hanya; bai barsu su rayu ba amma ya ba she su ga annoba. 51 Ya kashe dukkan 'ya'yan fari cikin Masar, ɗan farin ƙarfinsu cikin rumfunan Ham. 52 Ya fitar da mutanensa waje kamar tumaki ya bishe su cikin jeji kamar garke. 53 Ya kare su kuma ba su ji tsoro ba, amma teku ya dulmiyadda abokan gabarsu. 54 Daga nan ya kawo su kan iyakar ƙasarsa mai tsarki, zuwa tsaunin nan da hannun damansa ya saya. 55 Ya kori al'ummai daga gaban su ya raba masu gadonsu. Ya sa kabilun Isra'ila suka zauna cikin rumfunansu. 56 Duk da haka suka ƙalubalanci da tozartar da Allah Maɗaukaki kuma ba su kiyaye umarnansa ba. 57 Sun yi rashin aminci suka yi yaudara kamar ubanninsu; suka zama marasa abin dogaro kamar tanƙwararren baka. 58 Gama sun sa shi fushi da masujadansu kuma suka harzuƙa shi ga yin kishi da gumakansu. 59 Sa'ad da Allah ya ji wannan, ya hasala ya ƙi Isra'ila gaba ɗaya. 60 Ya yashe da wuri mai tsarki na Shilo, rumfar in da ya zauna a tsakiyar mutane. 61 Ya bari a ƙwace ƙarfinsa ya bada ɗaukakarsa a cikin hannun abokan gãba. 62 Ya miƙa mutanensa ga takobi, yayi fushi da abin gãdonsa. 63 Wuta ta cinye majiya ƙarfinsu, "yanmatansu kuma ba su sami waƙar aure ba. 64 Firistocinsu sun faɗi ta kaifin takobi, gwaurayensu kuma suka kasa yin kuka. 65 Sa'an nan sai Ubangiji ya farka sai ka ce mai tashi daga barci, kamar jarumi wanda ya fasa kuwwa saboda buguwa da ruwan inabi. 66 Ya kori magabtansa baya; ya sa su cikin kunya ta har abada. 67 Ya ƙi rumfar Yosef, bai kuma zaɓi kabilar Ifraim ba. 68 Ya zaɓi kabilar Yahuda da Tsaunin Sihiyona wanda yake ƙauna. 69 Ya gina tsatsarkan wurinsa kamar sammai, kamar duniya wadda ya kafa ta har abada. 70 Ya zaɓi Dauda, bawansa, ya ɗauke shi daga wurin tsaron tumaki. 71 Ya ɗauke shi daga bin tumaki da ƙananan su, ya kawo shi ya zama makiyayin Yakubu, mutanensa, da Isra'ila, abin gãdonsa. 72 Dauda yayi kiwonsu da mutuncin zuciyarsa, ya bishe su da gwanintar hannuwansa.

Zabura 79

Zabura ta Asaf.

1 Ya Allah bãƙin alummai sun zo cikin gãdonka; sun kazantar da haikalinka maitsarki; sun maida Yerusalem ta zama tsibin kangaye. 2 Sun bada gawawwakin bayinka a matsayin abinci ga tsuntsayen sararin sama, jikkunan amintattun mutanenka ga dabbobin duniya. 3 Sun zubar da jininsu kamar ruwa kewaye da Yerusalem, ba wanda zai yi jana'izar su. 4 Mun zama abin ba'a ga makwabtanmu, ba'a da reni ga waɗanda ke kewaye damu. Har yaushe, Yahweh? Zaka yi ta fushi har abada? 5 Har yaushe kishin fushinka zai yi ta ci har abada? 6 Ka zubo da fushinka kan al'umman da basu san ka ba da bisa mulkokin da basu kira bisa sunanka ba. 7 Gama sun cinye Yakubu sun hallaka ƙauyukansa. 8 Kada kayi ta tunawa da zunubin kakanninmu har su shafe mu; bari ayyukan jinƙanka su zo kanmu, gama mun yi sanyi ƙwarai. 9 Ka taimake mu, ya Allah na cetonmu, domin ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka yafe zunubanmu sabili da sunanka. 10 Don me al'ummai zasu ce, "Ina Allahn su?" Bari jinin bayinka da aka zubar yayi ramako akan al'ummai a idanunmu. 11 Bari nishin ɗaurarru ya zo gabanka; da girman ikonka ka tsare 'ya'yan waɗanda aka yanke wa mutuwa da rai. 12 Ya Ubangiji. Ka maida zagin da ƙasashe maƙwabtanmu suka zazzageka ka sau bakwai bisa cinyoyinsu. 13 Don haka mu mutanenka da tumakin makiyayarka zamu yi maka godiya har abada. Za mu faɗi yabbanka ga dukkan tsararraki.

Zabura 80

Domin shugaban mawaƙa shiryayyen salo domin Shoshanayim. Zabura ta Asaf.

1 Ka kasa kunne, Ya Makiyayi na Isra'ila, kai mai bida Yosef kamar tumaki; kai mai zama bisan Kerubim, ka haskaka a bisanmu! 2 A idon Ifraim da Benyamin da Manasse, ka motsa ikon ka; zo ka cece mu. 3 Ya Allah, ka maishe mu; ka sa fuskarka ta haskaka a bisanmu, mu kuwa zamu tsira. 4 Ya Yahweh Allah mai runduna, har yaushe zaka yi fushi da addu'ar mutanenka? 5 Ka ciyar dasu da gurasar hawaye ka basu hawaye mai yawa su sha. 6 Kasa mana wani abin da zamuyi jayayya da maƙ‌wabtanmu a kansa, maƙiyanmu kuma suna yi mana dariya tsakaninsu. 7 Ya Allah mai runduna; ka dawo damu; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu tsira. 8 Ka fito da kuringa daga Masar; Ka kori al'ummai ka dasa ta. 9 Ka gyara kasa domin ta; ta kafa saiwa ta cika ƙasa. 10 Duwatsu sun rufe ta da inuwarta, Rassanta suna kama da itacen sida na Allah. 11 Ta miƙa rassanta har bakin teku tohonta kuma har bakin Kogin Yuferitis. 12 Don me ka rushe garunta har dukkan masu wucewa ta hanyar zasu tsinki 'ya'yanta. 13 Aladun kurmi sun batata, namomin jeji kuma suna kiwo cikin ta. 14 Ya Allah mai runduna; ka juyo, ka duba daga sama kayi la'akari ka kula da wannan kuringar. 15 Wannan itace sauyar daka dasa da hannunka na dama, reshen da kasa ya girma. 16 An ƙone shi da wuta an sare shi ƙasa; sun hallaka saboda tsautawarka. 17 Bari hannunka ya kasance bisa mutumin hannunka na dama, bisa ɗan mutum wanda kasa ya zama da karfi domin kanka. 18 Daga nan ba zamu juya daga gare ka ba; ka farkar da mu, mu kuwa zamu kira bisa sunanka. 19 Ya Yahweh, Allah mai runduna, ka dawo damu; kasa fuskarka ta haskaka a kanmu, ta haka zamu tsira.

Zabura 81

Domin shugaban mawaƙa bisa ga salon Gitit. Zabura ta Asaf.

1 Ku raira da ƙarfi ga Allah karfinmu; ku tada muryar farinciki ga Allah na Yakubu. 2 Ku raira waƙa ku kaɗa ganga, garaya mai daɗi da molo. 3 Ku busa ƙahon rago a ranar tsayawar sabon wata, a ranar cikar wata, ranar da bukukuwanmu ke farawa. 4 Gama farilla ce ga Isra'ila, sharia da Allah na Yakubu ya bayar. 5 Ya bada ita a matsayin doka cikin Yosef lokacin da ya tafi gãba da kasar Masar, in da naji muryar da ban fahimta ba. 6 Na kawar da nauyin daga kafaɗarsa; an raba hannunsa daga ɗaukar kwando. 7 A cikin masifa ka yi kira, na taimake ka; Na amsa maka daga duhun tsawar girgije. Na gwada ka a bakin ruwayen Meriba. Selah 8 Ku saurara, mutanena, gama zan gargaɗe ku, zan so da kun saurare ni! 9 Kada wani bãƙon allah ya kasance a cikinku; baza kuyi sujada ga wani bãƙon allah ba. 10 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga kasar Masar. Ku wage bakinku, ni ma in cika shi. 11 Amma mutanena basu saurara ga maganata ba; Isra'ila bata yi mani biyayya ba. 12 Domin haka na bar su da taurinkansu domin suyi abin da suka ga dama. 13 Ina ma, mutanena zasu saurare ni; ina ma, mutanena zasu yi tafiya cikin tafarkuna. 14 Dana hanzarta mamaye abokan gabarsu in kuma juya hannuna akan masu zaluntar su. 15 Dama waɗanda suka ƙi Yahweh su faɗi cikin tsoro gabansa! Dama su ƙasƙanta har abada. Zan ciyar da Isra'ila da alkama mai kyau; 16 Zan ƙosarda ku da zuma daga cikin dutse."

Zabura 82

Zabura ta Asaf.

1 Allah yana tsaye cikin taron jama'ar Allah; cikin tsakiyar alloli yana zartar da hukunci. 2 Har yaushe zaka yi hukuncin rashin gaskiya ka nuna kana goyon bayan masu mugunta? Selah 3 Ka kare talakawa da marasa mahaifa; ka kare hakkin masu shan azaba da marasa galihu. 4 Ka ceci fakirai da mabukata; ka fisshe su daga hannun mugu. 5 Basu da sani basu kuwa da fahimta; suna kai da komowa cikin duhu; dukkan harsasun duniya sun rugurguje. 6 Na ce, ku alloline, dukkan ku kuma 'ya'yan Maɗaukaki ne. 7 Duk da haka za ku mutu kamar mutane kuma ku faɗi kamar ɗaya daga cikin sarakuna." 8 Ya Allah, ka tashi, ka shar'anta duniya, gama kana da gãdo cikin dukkan al'ummai.

Zabura 83

Waƙa. Zabura ta Asaf.

1 Ya Allah, kada kayi shiru! Kada ka manta damu kada kuma kaƙi taimakon mu, ya Allah. 2 Duba, abokan gabarka suna tada hankali, su da suka ƙi ka sun tada kansu. 3 Sun shirya wa mutanenka makirci suna ƙulli gaba da waɗanda ka kãre. 4 Suka ce, "Ku zo mu hallaka su a matsayin al'umma. Daga nan ba za'a ƙara tunawa da sunan Yahweh ba. 5 "Sun ƙulla Makirci tare dabararsu ɗaya ce; don suyi gãba dakai suka yi ƙawance. 6 Wannan ya haɗa da rumfunan Idom da na Ishma'ilawa, da mutanen Mowab da Hagarawa, waɗanda suka ƙulla tare da 7 Gebal, Ammon, Amalek; ya kuma haɗa da Filistiya da mazaunan Taya. 8 Assuriya kuma ta hada kai dasu; suna taimakon zuriyar Lot. Selah 9 Kayi masu kamar yadda kayi wa Midiyan kamar yadda kayi da Sisera da Yabin a Kogin Kishon. 10 Suka hallaka a Endo suka zama kamar taki domin ƙasa. 11 Ka sa shugabanninsu sun zama kamar Oreb da Zib, da dukkan sarakunansu kamar Ziba da Zalmunna. 12 Suka ce, "Bari mu ɗaukar wa kanmu makiyayar Allah." 13 Ya Allahna, ka maishe su kamar ƙurar guguwa, kamar ƙaiƙai gaban iska, 14 kamar wuta mai cin kurmi, kamar harshen wuta mai kama duwatsu. 15 Ka koresu da iskarka mai ƙarfi, ka razanar dasu da guguwar hadari. 16 Ka cika fuskokinsu da kunya domin su nemi sunanka, Ya Yahweh, 17 bari su sha kunya su firgita har abada; dama su lalace cikin kunya. 18 Daga nan zasu sani kai kaɗai ne, Yahweh, kai ne Maɗaukaki bisa dukkan duniya.

Zabura 84

Domin shugaban mawaƙa; Bisa ga salon Gitit. Zabura ta 'ya'yan Kora.

1 Ina misalin ƙaunar wurin da kake zaune, Yahweh mai runduna! 2 Ina marmarin harabun Yahweh, marmarin da nake da shi dominsa yasa na suƙe. Zuciyata da dukkan kome nawa ya kira ga Allah mai rai. 3 Har tsaddu ta samar wa kanta gida mashillira ta yi wa kanta sheka inda zata ajiye 'ya'yanta kusa da bagadanka, Yahweh mai runduna, sarkina, Allahna kuma. 4 Masu albarkane waɗanda suka zauna cikin gidanka, zasu yita ci gaba da yabonka. Selah 5 Mai albarkane mutumin da ƙarfinsa yana cikinka, wanda zuciyarsa ke marmarin zuwa Sihiyona. 6 Cikin ratsawa zuwa kwarin Hawaye, sun iske maɓulɓulan ruwa domin sha. Ruwan farko ya rufe shi da albarku. 7 Suna tafiya daga karfi zuwa karfi; kowanne ɗayan su ya bayyana gaban Allah cikin Sihiyona. 8 Yahweh Allah mai runduna, kaji addu'ata; Allahn Yakubu, ka saurari abin da nake cewa! Selah 9 Ya Allah, ka duba garkuwarmu; ka nuna damuwarka ga shafaffenka. 10 Gama yini ɗaya cikin harabunka ya fi dubu a wani wuri. Na gwammace in zama mai tsaron ƙofa cikin gidan Allahna, da in zauna tsakanin rumfuna na masu mugunta. 11 Gama Yahweh Allah shi ne ranar mu da garkuwa; 12 Yahweh zai bada alheri da ɗaukaka; ba ya hana wani abu mai kyau ga waɗanda suke tafiya cikin gaskiya. Yahweh mai runduna, mai albarkane mutumin da ya ke dogara gare ka.

Zabura 85

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.

1 Yahweh ka nuna wa ƙasarka tagomashi; ka dawo da lafiya da arzikin Yakubu. 2 Ka yafe zunubin mutanenka; ka rufe dukkan zunubinsu. 3 Ka janye dukkan fushinka; ka juya baya daga zafin fushinka. 4 Ka dawo damu, Allahn cetonmu, kasa rashin jindaɗinka tare da mu ya wuce. 5 Zaka yi ta fushi da mu har abada? Zaka yi ta yin fushi har ga tsararraki masu zuwa? 6 Ba zaka sake falkar damu ba? Daga nan mutanenka za suyi murna a cikin ka. 7 Ka nuna ma na amincin alƙawarinka ya Yahweh, ka bamu cetonka. 8 Zan saurari abin da Yahweh Allah zai ce, gama zai kawo salama ga mutanensa, amintattun mabiyansa. duk da haka ba zasu koma ga bin hanyoyinsu na wauta ba. 9 Hakika cetonsa yana kusa da masu tsoronsa; daga nan ɗaukaka zata zauna cikin ƙasarmu. 10 Alƙawarin aminci da gaskiya sun haɗu tare; adalci da salama sun yi wa juna sumba. 11 Gaskiya tana tsirowa daga ƙasa, adalci yana kallo daga sama. 12 I, Yahweh zai ba da albarku masu kyau, ƙasarmu zata bada amfaninta. 13 Adalci zai tafi gabansa kuma zai yi hanya domin sawayensa.

Zabura 86

Addu'ar Dauda.

1 Ka saurara, Yahweh, ka kuma amsa mani, domin ni matalauci ne, wanda aka tsanantawa. 2 Ka kare ni domin ina biyayya, ya Allahna, ka ceci bawanka wanda ya ke dogara a gare ka. 3 Ka yi mani jinƙai, ya Ubangiji, don a gare ka nake kuka dukkan yini. 4 Kasa bawanka yayi murna domin a gare ka nayi addu'a ya Ubangiji. 5 Ubangiji, kai nagari ne, kuma kana shirye kayi gafara. Kana kuma nuna jinƙai ga duk waɗanda suka yi kuka gare ka. 6 Yahweh, ka ji addu'ata, ka kuma ji muryar roƙona. 7 A ranar masifata nayi kira gare ka, domin zaka amsa mani. 8 Ya Ubangiji ba wanda za a kwatanta shi da kai a cikin alloli, ba ayyukan da za a kwatanta su da naka. 9 Dukkan al, umman da kayi zasu zo su rusuna maka. Za su girmama sunanka. 10 Domin kana da girma kana kuma yin abubuwan al'ajabi, kai kaɗai ne Allah. 11 Ka koya mani tafarkinka Yahweh. Sa'an nan zan yi tafiya cikin gaskiyarka. Ka haɗa zuciyata ta girmamaka. 12 Ubangiji Allahna zan yabe ka da dukkan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada. 13 Domin alƙawarinka mai aminci yana da girma a gare ni, domin ka ceto raina daga zurfafan Lahira. 14 Ya Allah marasa hankali sun tasar mani. Ƙungiyar masu husuma sun tasar mani suna neman raina, ba su kula da kai ba. 15 Amma kai, Ubangiji, Allah ne mai jinƙai da alheri, mai jinkirin fushi, mai mayalwacin alƙawari mai aminci da kuma madogara. 16 Ka juyo wurina kayi mani jinƙai; ka bada ƙarfinka ga bawanka; ka ceci ɗan baiwarka. 17 Ka nuna mani alamar jinƙanka. Sa'an nan waɗanda ke ƙi na zasu gani su kunyata saboda kai, Yahweh, ka taimake ni ka kuma ta'azantar dani.

Zabura 87

Zabura ta 'ya'yan Kora; waƙa.

1 Akan dutse mai tsarki birninsa da ya samo ya tsaya; 2 Yahweh yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da rumfuna na Yakubu. 3 An faɗi maɗaukakan abubuwa game da kai birnin Allah. Selah. 4 Na ambaci Rahab da Babila ga masu bi na. Duba, akwai Filistiya, da Taya, tare da Itofiya- kuma zasu ce, 'Wannan an haife shi a can.'" 5 Ga Sihiyona za'a ce, "Dukkan wɗannan an haife su a cikinta, kuma Mafi Girma dukka da kansa zai kafa ta." 6 Yahweh ya rubuta a cikin littafin ƙidaya na al'ummai, "Wannan an haife shi a can." Selah 7 Haka kuma mawaƙa da masu rawa suka faɗa tare, "Dukkan maɓulɓulaina suna cikinka."

Zabura 88

Waƙar zabura ta 'ya'yan Kora; domin shugaban mawaƙa; da aka shirya bisa ga salon Mahalat Leyanot. Salon Heman Ezrahiye.

1 Yahweh, Allah na cetona, Na yi kuka a gabanka dare da rana. 2 Ka ji addu'ata, ka saurari kukana. 3 Domin na cika da damuwoyi, raina kuma ya kai Lahira. 4 Mutane sun ɗauke ni kamar waɗanda suka faɗa rami; Mutumin da ba shi da ƙarfi. 5 An yi watsi da ni a cikin matattu; Ina kama da matacce dake kwance a kabari, game da wanda ka daina kula da shi saboda an datse su daga ikonka. 6 Ka ajiye ni a wuri mafi ƙasƙanci na cikin rami, a wuri mai zurfi da kuma duhu. 7 Fushinka yayi nauyi a kaina, kuma dukkan rigyawarka tabi ta kaina. Selah 8 Saboda kai, abokan tarayyata suka yashe ni. Ka maishe ni abin rawar jiki a gare su. An shinge ni a ciki ba kuma zan tsira ba. 9 Idanuna sun gaji da damuwa; Dukkan yini ina kira gare ka, Yahweh; na buɗe hannuwana gare ka. 10 Ko zaka yi mu'ujuzai ga matattu? Ko waɗanda suka mutu zasu tashi su yabe ka? Selah 11 Ko za'a yi shelar alƙawarin amincinka a kabari, amincinka kuma a wurin matattu? 12 Ko za'a san ayyukanka na al'ajibai a cikin duhu, ko kuma adalcinka a wurare na mantuwa? 13 Amma nayi kuka gare ka, Yahweh; da safe addu'ata tana zuwa gare ka. 14 Yahweh me yasa ka ƙi ni? Me yasa ka ɓoye fuskarka daga gare ni? 15 Har kullum an tsananta mani kamar a hallaka ni tun daga ƙuruciyata. Na sha hukuncin horonka ina cikin fargaba. 16 Ayyukanka na fushi sun bi ta kaina, kuma ayyukanka masu ban razana sun kawar da ni. 17 Sun kewaye ni kamar ruwa a dukkan yini; dukkan su sun kewaye ni. 18 Ka kawar da abokaina da duk waɗanda suka shaƙu dani daga gare ni. Wanda ya shaƙu dani duhu ne kaɗai.

Zabura 89

Salon Etan Ezrahiye.

1 Zan raira yabon ayyukan alƙawarin amincin Yahweh na har abada, Zan yi shelar gaskiyarka ga tsararraki masu zuwa. 2 Domin na ce "Anyi amintaccen alƙawari na har abada; ka kuma kafa gaskiyarka a cikin sammai." 3 Na yi alƙawari da zaɓaɓɓena, nayi alƙawari ga Dauda bawana. 4 Zan kafa zuriyarka har abada, kuma zan kafa kursiyinka a dukkan tsararraki." Selah 5 Sammai na yabon al'ajibanka, Yahweh; a na yabon gaskiyarka a taron tsarkaka. 6 Domin da wane ne za a kwatanta shi da Yahweh a sammai? Wane ne za a kwatanta shi da Yahweh? 7 Shi Allah ne dake da girmamawa a taron tsarkaka yana kuma da kwarjini ga dukkan waɗanda suka kewaye shi. 8 Yahweh Allah mai runduna, wa keda ƙarfi kamar ka? amincinka ya kewaye ka. 9 Kana mulkin haukan teku; lokacin da ambaliyoyi su ka tashi ka kwantar da su. 10 Ka buge Rahab kamar wadda aka kashe. Ka warwatsa maƙiyanka da ƙarfin damtsenka. 11 Sammai naka ne, haka kuma duniya. Ka hallici duniya da dukkan abin da ke cikin ta. 12 Ka hallici arewa da kudu. Tabor da Harmon na murna a cikin sunanka. 13 Kana da damtse mai iko da kuma hannu mai ƙarfi, hannunka na dama kuma yana da tsayi. 14 Aikin adalci da adalci su ne ginshiƙan mulkinka. Alƙawari mai aminci da kuma dogara daga gare ka suke zuwa. 15 Masu albarka ne waɗanda ke yi maka sujada! Yahweh, suna tafiya a cikin hasken fuskarka, 16 Suna murna da sunanka dukkan yini. Ayyukan adalcinka kuma sun ɗaukaka ka. 17 Kai ne ƙarfin ikonsu, ta wurin jinƙanka kuma mun yi nasara. 18 Domin garkuwoyinmu na Yahweh ne; sarkinmu kuma na Mai tsarki na Isra'ila ne. 19 Tun da daɗewa kayi magana da tsarkakanka ta wurin wahayi; kace "Na sa kambi bisa mai iko; Na tayar da wani da aka zaɓa daga cikin mutane. 20 Na zaɓi Dauda bawana, da maina na keɓe shi. 21 Hannuna zai taimake shi. Damtsena kuma zai ƙarfafa shi. 22 Ba maƙiyin da zai yaudare shi; ba kuma ɗan magabcin da zai ƙuntata masa. 23 Zan buge maƙiyansa a gabansa, masu ƙin sa kuma zan hallaka su. 24 Gaskiyata da alƙawarin amincina zai kasance tare da shi, ta wurin sunana zai yi nasara. 25 Zan ɗora hannunsa a kan teku, hannunsa na dama kuma bisa koguna. 26 Zai yi kira gare ni yace kai ne ubana, 'Kai ne Ubana kuma Allahna, da kuma dutsen cetona.' 27 Zan ɗora shi a matsayin ɗan farina, mafi ɗaukaka a cikin sarakunan duniya. 28 Zan tsawaita alƙawarin amincina a gare shi har abada; zan kuma riƙe alƙawarina da shi. 29 Zan kafa zuriyarsa har abada, mulkinsa kuma zai kai har sammai. 30 Idan 'ya'yansa suka yi watsi da shari'una suka kuma yi rashin biyayya ga sharuɗɗana, 31 idan kuma sun karya dokokina basu kuma kiyaye umarnaina ba, 32 to sai in hori rashin biyayyarsu da sandar ƙarfe laifofinsu kuma da nushe-nushe. 33 Amma ba zan janye madawammiyar ƙaunata ba daga gare shi ko kuma in yi rashin aminci a kan alƙawarina ba, 34 Ba zan karya alƙawarina ba ko kuma in canza maganganun leɓuna na ba. 35 Sau ɗaya tak na rantse da tsarkina-Ba zan yiwa Dauda ƙarya ba: 36 zuriyarsa zata ɗore har abada mulkinsa kuma zai zama kamar rana a gabana. 37 Za a kafa shi har abada kamar wata, amintaccen mashaidi a sararin sama." Selah 38 Amma ka ƙi ka kuma yi watsi; kana kuma fushi da shafaffen sarki. 39 Ka kuma musunta alƙawarin bawanka. Ka ƙazamtar da rawaninsa a ƙasa. 40 Ka kuma rushe katangunsa dukka. Ka kuma mayar da ƙarfafan kagarunsa kufai. 41 Duk masu wucewa suka yi masa ƙwace. Ya zama abin ƙyama a cikin maƙwabta. 42 Ka tayar da hannun damar maƙiyansa; ka kuma sa dukkan maƙiyansa suyi farinciki. 43 Ka juya takobinsa ka kuma hana shi ya tsaya a lokacin yaƙi. 44 Ka kawo ƙarshen martabarsa; ka kuma karya mulkinsa 45 Ka gajarta kwanakin ƙuruciyarsa. Ka kuma rufe shi da kunya. Selah 46 Yahweh har yaushe? Ko zaka ɓoye kanka, har abada? Har yaushe zaka bar fushinka yayi ta ƙuna kamar wuta? 47 Oh, ka yi tunanin yadda gajartar lokacina ya ke, da kuma rashin amfanin yadda ka hallici dukkan mutane! 48 Wane ne zai rayu ba zai mutu ba, ko kuma ya iya kuɓutar da ransa daga Lahira? Selah 49 Ya Ubangiji, ina ayyukanka na dã a kan alƙawarin amincinka da ka rantsewa Dauda a cikin gaskiyarka? 50 Ka tuna ya Ubangiji da rainin da aka yi wa bayinka da kuma yadda na ji a zuciyata ire-iren cin mutunci daga al'ummai. 51 Maƙiyanka suna nuna wulaƙanci, Yahweh; suna wulaƙanta sawayen keɓaɓɓenka. 52 Albarka ta tabbata ga Yahweh har abada. Amin da Amin. Littafi na Huɗu

Zabura 90

Addu'ar Musa mutumin Allah.

1 Ubangiji kai ne mafakarmu a dukkan tsararraki. 2 Kafin a kafa duwatsu, ko kuma ka hallici duniya da abin dake cikinta, har abada abadin, kai Allah ne. 3 Ka kan komar da mutum ƙura, ka ce "ku koma ku zuriyar ɗan adam." 4 Domin shekaru dubu a gare ka kamar jiya ne data wuce, kamar kuma sa'ar tsaro ce ta dare. 5 Ka share su kamar da rigyawa sun kuma yi barci; da safe suna kama da ciyayi da suka yi girma. 6 Da safe sukan yi yabanya suyi girma; da yamma kuma su kan yanƙwane su bushe. 7 Hakika, an cinye mu a cikin fushinka, a cikin fushinka kuma mun gigice. 8 Ka jejjera zunubanmu a gabanka, laifofinmu na ɓoye kuma kasa su a hasken gabanka. 9 Ran mu yana shuɗewa a ƙarƙashin fushinka; 10 shekarunmu kuma sun wuce da sauri kamar ajiyar zuciya. Shekarunmu saba'in ne, ko kuma tamanin in muna da lafiya; amma koma da shekarunmu mafiya kyau suna cike da damuwa da baƙinciki. Hakika, sukan wuce da sauri sai kuma mu ɓace. 11 Wa ya san ƙarfin fushinka, da kuma fushinka da ke dai-dai da tsoronka? 12 ka koya mana yadda zamu yi la'akari da rayuwarmu domin mu yi rayuwa cikin hikima. 13 Juya, Yahweh! Har yaushe zai zama? Ka ji tausayin bayinka. 14 Ka ƙosar da mu da alƙawarin amincinka da safe domin muyi farinciki a cikin dukkan kwanakinmu. 15 Ka samu muyi murna gwargwadon kwanakin daka azabtar damu da kuma shekarun da muka fuskanci matsala. 16 Ka bar bayinka suga aikinka, kuma ka bar 'ya'yanmu suga darajarka. 17 Da ma jinƙan Ubangiji Allahnmu ya zama namu; ka wadata aikin hannuwanmu; hakika, ka wadata aikin hannuwanmu.

Zabura 91

1 Wanda ya ke rayuwa a bukkar Mafi Ɗaukaka zai zauna a inuwar Mai Iko Dukka. 2 Zan ce da Yahweh, "Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda na dogara a gare shi." 3 Domin zai kuɓutar da kai daga wayon tarkon maharbi kuma daga annoba mai hallakarwa. 4 Zai rufe ka da fukafukansa, kuma a ƙarƙashin fukafukansa zaka sami mafaka. Madogararsa garkuwa ce da kuma kariya. 5 Ba za ka ji tsoron masifa ba da dare, ko kuma kibiyoyin dake shawagi da rana. 6 Ko kuma annobar dake aukowa da dare ba. 7 Ko cutar dake samuwa da tsakar rana ba. Dubu zasu faɗi a gefenka dubu goma kuma a hannunka na dama, amma ba zasu iso wurinka ba. 8 Zaka duba ne kawai kaga hukuncin da za'a yiwa miyagu, 9 Domin Yahweh ne mafakata! Kuma ka maida Maɗaukaki mafakarka. 10 Ba mugun abin da zai same ka; ba wani abu mai cutarwa da zai kusanci gidanka. 11 Domin zai umarci mala'ikunsa su kare ka, su kuma yi tsaronka a cikin dukkan hanyoyinka. 12 Zasu tayar da kai tsaye da hannunsu domin kada kayi tuntuɓe a kan dutse. 13 Zaka hamɓare zãkuna da damisoshi a ƙarƙashin ƙafafunka; zaka tattake 'yan zãkoki da kuma macizai. 14 Saboda ya sadaukar da kansa gare ni, zan cece shi. Zan kare shi saboda yana yi mani biyayya. 15 Sa'ad da yayi kira gare ni zan amsa masa. Zan kasance tare da shi a cikin masifa; Zan ba shi nasara zan kuma girmama shi. 16 Zan ƙosar da shi da tsawon rai in kuma nuna masa cetona.

Zabura 92

Zabura. Waƙar ranar Asabaci.

1 Abu mai kyau ne a yi godiya ga Yahweh, a kuma yi waƙar yabo ga sunanka, Maɗaukaki, 2 a kuma yi shelar alƙawarin amincinka da safe gaskiyarka kuma kowanne dare, 3 da garaya mai tsarkiya goma da kuma kayan kaɗe-kaɗe masu daɗi. 4 Domin kai, Yahweh, kasa ni murna ta wurin ayyukanka. Zanyi waƙar farinciki saboda ayyukan hannuwanka. 5 Ina misalin girman ayyukanka, Yahweh! Tunane-tunanenka suna da zurfi. 6 Daƙiƙin mutun bai sani ba, haka ma wawa bai fahimci wannan ba: 7 Lokacin da miyagu suka firfito kamar ciyawa, ko ma a lokacin da miyagu suka taru, duk da haka an miƙa su ga hallaka ta har abada. 8 Amma kai Yahweh zaka yi mulki har abada. 9 Hakika ka duba maƙiyanka, Yahweh! Hakika ka duba maƙiyanka. Hakika zasu hallaka! Duk masu aikin mugunta za'a warwatsa su. 10 Ka tada ƙahona kamar na bijimin sã; An keɓe ni da sabon mai. 11 Idanuna sun ga faɗuwar maƙiyana; kunnuwana kuma sun ji hallakar miyagun maƙiyana. 12 Masu adalci zasu yi yaɗo kamar gazarin dabino; zasu yi girma kamar itacen sida na Lebonon. 13 An dasa sune a gidan Yahweh; Suna sheƙi a harabar Allahnmu. 14 Suna ba da 'ya'ya har ma a kwanakin tsufansu; suna nan kore shar, 15 Don ayi shela cewa Yahweh mai adalci ne. Shi ne dutsena, ba kuma rashin adalci a cikinsa.

Zabura 93

1 Yahweh yana mulki; Yana saye da daraja; Yahweh yasa sutura ya kuma yiwa kansa ɗammara da ƙarfi. An kafa duniya daram; kuma ba zata gusa ba. 2 Kursiyinka ya kafu tun zamanin dã can; kana nan tun fil azal. 3 Tekuna suka tashe, Yahweh; sun ta da muryarsu; raƙuman tekuna sunyi tumbotso sunyi ruri. 4 Sun fi dukkan sauran ambaliyoyi masu ikon karya teku, Yahweh na sama maigirma ne. 5 Manyan umarnanka abin dogara ne na hakika; Yahweh, tsarki ya ƙayata gidanka, har abada.

Zabura 94

1 Yahweh, Allah mai sakayya, Allah mai sakayya ka haskaka a bisan mu. 2 Ka tashi tsaye mai shari'ar duniya ka ba masu girman kai abin da ya kamance su. 3 Har yaushe miyagu, Yahweh har yaushe miyagu za suyi farinciki 4 Dukkan masu aikin mugunta suna ta yin maganganunsu na wauta; Duk masu mugunta suna fahariya. 5 Yahweh; sun buge mutanenka, Sun ƙuntata wa al'ummarka. 6 Sun kashe gwauruwa da bãƙon dake zaune a ƙasarsu, sun kuma kashe marayu. 7 Suka ce, "Allah ba zai gani ba, Yahweh na Yakubu bai kula da abin ba." 8 Ku lura mutane marasa hankali! Ku wawaye, har sai yaushe zaku koyi darasi? 9 Shi wanda yayi kunne ashe ba zai ji ba? Shi wanda yayi ido ba ya gani ne? 10 Shi dake horon al'ummai, ashe ba zai tsautar ba? Shi ne mai ba da ilimi ga mutum. 11 Yahweh ya san tunanin mutane, cewa turiri ne kawai. 12 Mai albarka ne wanda ka yiwa gargaɗi, Yahweh wanda ka koyar daga cikin shari'arka 13 Ka bashi hutu a lokutan damuwa har sai da aka gina rami domin miyagu. 14 Domin Yahweh ba zai yashe da mutanensa ba ko kuma yayi watsi da abin gãdonsa ba. 15 Domin hukunci zai sake zama da adalci; kuma dukkan masu tsarkin rai zasu bi shi. 16 Wa zai tashi ya kuɓutar dani daga masu mugunta? 17 In da ba domin Yahweh ya taimake ni ba da yanzu ina can kwance a lahira. 18 Lokacin dana ce ƙafafuna na barci," Yahweh alƙawarin amincinka ya ɗaga ni sama. 19 Lokacin da fargaba ya cika ni ta'aziyarka ta kan sani in cika da murna. 20 Ko akwai hurɗa tsakaninka da mulkin hallakarwa da ya kafa rashin adalci? 21 Sun shirya maƙarƙashiya tare domin su kashe mai adalci sun kuma hukuntawa marar laifi mutuwa. 22 Amma Yahweh ne babbar hasumiyata, Allahna kuma shi ne dutsen fakewa ta. 23 Zai saukar masu da laifofinsu zai kuma daddatsa su a cikin aikin muguntarsu. Yahweh Allahnmu zai daddatse su.

Zabura 95

1 Ku zo mu raira yabo ga Yahweh, Sai mu raira waƙar farinciki ga dutsen cetonmu. 2 Sai mu zo gabansa da godiya, sai mu raira masa yabo da waƙoƙin zabura. 3 Domin Yahweh Allah ne mai girma, sarki ne mai girma da yafi dukkan alloli. 4 Zurfafan duniya dukka a hannunsa suke; Duwatsu masu tsawo kuma nasa ne. 5 Teku tasa ce, shi ne yayi ta. Hannuwansa kuma suka yi busasshiyar ƙasa. 6 Ku zo muyi sujada mu durƙusa ƙasa, sai mu durƙusa a gaban Yahweh mahallicinmu; 7 Domin shi ne Allahnmu, mu mutanen makiyayarsa ne, tumakin hannunsa kuma. Yau ace dai za ku ji muryarsa! 8 Kada ku taurare zuciyarku, kamar a Meriba, ko kuma kamar ranar Massa a cikin jeji, 9 inda ubanninku suka gwada ni suka kuma jaraba ni, koda ya ke sun ga aikina. 10 Shekaru arba'in ina fushi da waccan tsarar na ce, "Waɗannan mutane ne da zuciyarsu ta karkace; basu san hanyoyina ba. 11 'Domin haka cikn fushina na rantse cewa ba zasu taɓa shiga wurin hutu na ba

Zabura 96

1 Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh; ku raira waƙa ga Yahweh, dukkan duniya. 2 Ku raira waƙa ga Yahweh, ku albarkaci sunansa; kuyi shelar cetonsa a kowacce rana. 3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al'ummai, ayyukansa na ban mamaki a cikin al'ummai. 4 Domin Yahweh yana da girma ya kuma isa yabo sosai. A ji tsoron sa fiye da dukkan sauran alloli. 5 Saboda allolin al'ummai gumaka ne, amma Yahweh ne ya hallici sammai, martaba da wadata suna gabansa. 6 Jamali da ƙarfi suna cikin wurinsa mai tsarki. 7 Kuyi yabo ga yahweh ku dukkan kabilu na mutane, ku yabi Yahweh sabili da ɗaukakarsa da ƙarfinsa. 8 Ku ba yahweh ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo baiko a haikalinsa. 9 Ku durƙusa a gaban Yahweh saye da tufafin dake girmama tsarkinsa. Yi rawar jiki a gabansa, dukkan duniya. 10 Ku faɗa a cikin al'ummai cewa,"Yahweh ne ke mulki." Hakannan kuma aka kafa duniya; ba kuma zata jijjigu ba. Yana yiwa mutane shari'ar dake dai-dai. 11 Sai sammai suyi murna, sai duniya kuma ta yi farinciki; sai teku yayi ruri abin da ke cikinsa kuma su cika da murna. 12 Filaye suyi murna da duk abin da ke cikin su. Sa'an nan kuma dukkan bishiyoyin duniya su ɓarke da yabo 13 a gaban Yahweh, domin yana tafe. Yana zuwa domin ya shar'anta duniya. Zai shar'anta duniya da adalci da mutane kuma cikin amincinsa.

Zabura 97

1 Yahweh na mulki sai duniya ta yi murna, sai dukkan ƙasashe masu nisa suyi murna. 2 Gizagizai da duhu na kewaye da shi. Adalci da gaskiya ne harsashen kursiyinsa. 3 Wuta na tafe a gabansa tana cinye magafta ko ina 4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta furgita. 5 Duwatsu kuma sun narke kamar tufa a gaban Yahweh Ubangijin dukkan duniya. 6 Sararin sama na shaida adalcinsa, dukkan al'ummai kuma sun ga ɗaukakarsa. 7 Duk waɗanda ke bauta wa abin da hannu ya sassaƙa zasu kunyata, masu taƙama da gumaka marasa amfani- ku rusuna masa da dukkan allolinku! 8 Sihiyona taji sai tayi farinciki, biranen Yahuda kuma suka yi murna saboda dokokinka na adalci, Yahweh. 9 Domin kai, Yahweh, kafi kowa ɗaukaka a cikin dukkan duniya. An ɗaukaka ka fiye da dukkan alloli. 10 Ku dake ƙaunar Yahweh ku ƙi mugunta! Yana kare ran tsarkakansa, ya karɓo su daga hannun mugun. 11 An shuka haske domin adalai farinciki kuma domin masu zukata masu aminci. 12 Kuyi murna cikin Yahweh ku adalai; ku kuma yi masa godiya lokacin da kuka tuna da tsarkinsa.

Zabura 98

Zabura.

1 Oh, ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh domin yayi ayyuka masu ban mamaki; hannunsa na dama da damtsensa sun ba shi nasara. 2 Yahweh ya sa cetonsa ya sanu; ya nuna adalcinsa a fili ga dukkan al'ummai. 3 Ya tuna da alƙawarinsa mai aminci da gaskiya ga gidan Isra'ila; dukkan iyakokin duniya zasu ga nasarar Allahnmu. 4 Ku raira waƙar farinciki ga Yahweh, dukkan duniya ku ɓarke da waƙa, kuyi waƙa domin murna, kuyi waƙoƙin yabo. 5 Ku raira yabo ga Yahweh da garaya, tare da garaya haɗe da waƙoƙi masu daɗi. 6 Tare da kakaki da ƙarar ƙaho, ku tada muryoyi masu daɗi a gaban Sarki, Yahweh. 7 Sai teku yayi ihu da dukkan abin dake cikinsa! 8 Sai rafuffuka su tafa hannuwansu, sai duwatsu kuma su raira waƙar yabo. 9 Yahweh yana zuwa domin ya yi wa duniya shari'a da adalci da kuma al'ummai tare da gaskiya.

Zabura 99

1 Yahweh na mulki; bari al'ummai suyi rawar jiki, yana zaune kan kursiyi sama da Kerubim, duniya ta girgiza, 2 Yahweh yana da girma a Sihiyona yana da ɗaukaka fiye da dukkan al'ummai. 3 Sai a yabi sunanka mai jamali da girma; yana da tsarki. 4 Sarki yana da ƙarfi, yana kuma ƙaunar adalci. ka kafa gaskiya; ka aikata adalci akwai adalci kuma a cikin Yakubu. 5 A yabi Yahweh Allahnmu a kuma yi sujada a digadigansa. Ya na da tsarki. 6 Musa da Haruna na cikin firistocinsa, Sama'ila kuma na cikin waɗanda suka yi addu'a gare shi. Sun yi addu'a ga Yahweh, ya kuma amsa masu. 7 Ya yi masu magana daga ginshinƙin girgije. Sun kiyaye tsattsarkan umarninsa da farillan da ya basu. 8 Ka amsa masu, Yahweh Allahnmu. Kai Allah ne mai gafara a gare su, amma kuma kana horon ayyukansu na zunubi. 9 Ku yabi Yahweh Allahnmu, ku kuma yi sujada akan tudunsa mai tsarki, gama Yahweh Allahnmu yana da tsarki.

Zabura 100

Zabura ta Dauda.

1 Kuyi ihu da farinciki ga Yahweh ku dukkan duniya, 2 Ku bautawa yahweh da farar zuciya, kuzo gabansa da waƙoƙin farinciki. 3 Ku sani Yahweh Allah ne; yayi mu, mu kuma nasa ne. Tumakin makiyayarsa kuma. 4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya cikin gidansa da yabo. Kuyi masa godiya ku albarkaci sunansa. 5 Domin Yahweh nagari ne; alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada gaskiyarsa kuma har dukkan tsararraki ne.

Zabura 101

Zabura ta Dauda.

1 Zan raira alƙawarin aminci da gaskiya; a gare ka, Yahweh, zan raira yabbai. 2 Zan yi tafiya cikin aminci. Oh, yaushe zaka zo wurina ne? Ni da gidana za muyi tafiya cikin nagarta. 3 Ba zan ƙyale mugunta a idanuna ba; Na ƙi mugun aiki marar cancanta; ba zai manne mani ba. 4 Ɓatattun mutane zasu rabu dani; bana yin biyayya ga mugunta. 5 Zan hallaka duk wanda ya yiwa maƙwabcinsa yanke a asirce. Ba zan ƙyale duk wani mai fankama da rashin hankali ba. 6 Zan nemi masu aminci na ƙasar su zauna a gefena. Masu tafiya cikin gaskiya da riƙon amana ne zasu bauta mani. 7 Mayaudara ba zasu kasance a gidana ba; maƙaryata bazan marabce su a idona ba. 8 Duk safiya zan hallakar da miyagu dukka daga ƙasar; Zan kawar da dukkan miyagu daga birnin Yahweh.

Zabura 102

Addu'ar wanda ya ke cikin ƙunci sa'ad da yake cikin damuwa ya kuma zuba makokinsa gaban Yahweh.

1 Yahweh ka ji addu'ata, Yahweh ka ji kukana dana keyi gare ka. 2 Kada ka ɓoye mani fuskarka a lokacin da nake damuwa. Ka ji ni. A lokacin da nayi kira gare ka, ka amsa mani da sauri. 3 Gama kwanakina sun wuce kamar hayaƙi, ƙasusuwana kuma na ƙuna kamar wuta. 4 An buge zuciyata na zama kamar ciyawar data bushe. Na manta in ci wani abinci. 5 Da nishe-nishena na kullum, na rame. 6 Na zama kamar zalɓe a hamada; na zama kamar mujiya a kufai. 7 Na kwanta ba tare da yin barci ba, kamar tsuntsun dake kaɗaici, shi kaɗai a bisa kan gida. 8 Maƙiyana nayi mani ba'a; masu yi mani habaici na la'anta sunana. 9 Toka ce abincina kuma gurasa abin shana ya gauraye da hawaye na. 10 Saboda fargaban fushinka ka ɗaga ni sama domin ka fyaɗa ni ƙasa. 11 Kwanakina sun zama kamar inuwar data gushe, na kuma yanƙwane kamar ciyawa. 12 Amma kai Yahweh, kana raye har abada, kuma shahararka ta dukkan tsararraki ce. 13 Zaka tashi kayi jinƙai ga Sihiyona. Yanzu ne lokacin nuna mata jinƙai; lokacinta da kasa yayi. 14 Domin bayinka sun riƙe duwatsunta ƙaunatacce ka ji tausayi saboda ƙurar kufanta. 15 Al'ummai zasu girmama sunanka, Yahweh, kuma dukkan sarakunan duniya zasu girmama ɗaukakarka. 16 Yahweh zai sake gina Sihiyona ya kuma bayyana a cikin ɗaukakarsa. 17 A wancan lokacin, zai amsa addu'ar wulaƙantattu; ba zai ƙi addu'arsu ba. 18 Za a rubuta wannan saboda tsararraki masu zuwa, da mutanen da ba'a haifa ba tukuna zasu yabi Yahweh. 19 Domin ya dubo ƙasa daga can sammai; Daga samaniya Yahweh ya dubi duniya, 20 domin ya ji nishe-nishen 'yan sarƙa, ya kuɓutar da waɗanda aka hukuntawa mutuwa. 21 Mutane zasu yi shelar sunan Yahweh a Sihiyona da kuma yabonsa a Yerusalem 22 lokacin da mutane da mulkoki suka tattaru tare su bauta wa yahweh. 23 Ya ɗauke ƙarfina a tsakiyar rayuwata. Ya gajarta kwanakina. 24 Na ce Allahna kada ka kawar dani a tsakiyar rayuwa; kana nan a dukkan tsararraki. 25 A can lokacin dã ka kafa duniya a wurinta; sammai kuma aikin hannuwanka ne. 26 Zasu lalace amma kai zaka dawwama; duk zasu tsufa kamar sutura; kamar tufafi, zaka cire su, zasu kuma ɓace. 27 Amma kai kana nan yadda kake, shekarunka kuma basu da iyaka. 28 'Ya'yan bayinka zasu rayu, zuriyarsu kuma zasu rayu a gabanka."

Zabura 103

Zabura ta Dauda.

1 Ina godiya ga Yahweh da dukkan raina, da dukkan abin da ke cikina, Ina yabon sunansa mai tsarki. 2 Ina godiya ga Yahweh da dukkan raina, na kuma tuna da dukkan ayyukansa nagari. 3 Ya gafarta dukkan zunubanka, ya kuma warkar da dukkan cututtukanka. 4 Ya ceci ranka daga hallaka yayi maka rawani da alƙawarin aminci da ayyukan jinƙai. 5 Ya ƙosar da ranka da abubuwa masu kyau domin haka ƙuruciyarka ta sabunta kamar gaggafa. 6 Yahweh yakan yi abin dake dai-dai da adalci ga duk waɗanda aka tsanantawa. 7 ya sanar da hanyoyinsa ga Musa, ayyukansa kuma ga zuriyar Isra'ila. 8 Yahweh mai jinƙai ne da alheri; yana da haƙuri; yana da matuƙar amincin alƙawari. 9 Ba kullum ya kanyi horo ba; ba kullum kuma ya kanyi fushi ba. 10 Baya yi mana bisa ga gwargwadon zunubanmu ko ya saka mana kan hukuncin zunubanmu ba. 11 Domin kamar yadda sammai ke nesa da duniya, to haka girman alƙawarinsa ya ke ga masu girmama shi. 12 Kamar yadda gabas tayi nisa da yamma hakannan ya kawar da laifofin zunubanmu daga gare mu. 13 Kamar yadda mahaifi ke tausayin 'ya'yansa, haka Yahweh ke tausayin masu girmama shi. 14 Domin yasan yadda aka yi mu; ya sani cewa mu ƙura ne. 15 mutum kwanakinsa kamar ciyawa ce yakan yi yabanya kamar furen saura. 16 Iska ta kan hura ta kansa, sai kuma ya ɓace kuma ba wanda zai san yadda yayi girma. 17 Amma alƙawarin Yahweh mai aminci har abada abadin ne ga masu girmama shi. Adalcinsa ya kai har ga zuriyar su. 18 Sun kiyaye alƙawarinsa sun kuma tuna su yi biyayya da dokokinsa. 19 Yahweh ya kafa kursiyinsa a sammai, masarautarsa kuma na mulkin kowa. 20 A yi yabo ga Yahweh, ku mala'ikunsa, ku masu iko dukka dake yin biyayya da maganarsa. 21 Ku yabi Yahweh, dukkan rundunoninsa, ku bayinsa ne dake yin nufinsa. 22 A yabi Yahweh, dukkan halittunsa, a dukkan wuraren da ya ke mulki. Zan yabi Yahweh da dukkan raina.

Zabura 104

1 Na bada yabo ga Yahweh da dukkan raina, Yahweh Allahna, kai mai girma ne da ƙawa; Kayi sutura da martaba da daraja. 2 Ka rufe kanka da haske kamar da sutura; ka shimfiɗa sammai kamar yadda ake simfiɗa labulen rumfa. 3 Ka shimfiɗa katakan fadodinka a kan gajimarai; ka mai da gajimarai karusanka; kana tafiya akan fika-fikan iska. 4 Ya mai da iskoki manzanninsa, harsunan wuta kuma bayinsa. 5 Ya kafa tushen duniya ba kuma zata jijjigu ba. 6 Ka rufe duniya da ruwa kamar sutura; ruwa ya rufe duwatsu. 7 Tsautawarka nasa ruwaye su janye; da jin ƙarar tsawarka sai suka gudu. 8 Duwatsu sun tashi, kwarurruka kuma suka bazu zuwa wuraren da ka shirya masu. 9 Ka yi masu iyakar da ba zasu tsallake ba; ba zasu ƙara rufe duniya ba. 10 Yasa maɓuɓɓugan ruwa su gudana zuwa kwarurruka; maɓulɓulan sun kwarara tsakanin duwatsu. 11 Suna bayar da ruwa ga dukkan dabbobin saura; jakunan jeji a wurin ne suke kashe ƙishinsu. 12 A bakin kogunan ruwa tsuntsaye suka yi sheƙunansu; suna raira waƙa a cikin rassa. 13 Ya shayar da duwatsu daga ruwansa ya kafa kursiyinsa a sammai. Duniya ta cika da 'ya'yan aikinsa. 14 Yasa ciyawa ta fito domin dabbobi da kuma tsire-tsire domin mutum ya nome ya sami abinci daga ƙasa. 15 Yayi inabi domin mutum yayi murna, mai kuma domin fuskarsa tayi haske, abinci kuma domin rayuwarsa. 16 Itatuwan Yahweh suna samun ruwa; Sidar Lebanon da ya dasa 17 Acan tsuntsaye ke yin sheƙunansu. Shamuwa ta mai da itacen sifurus gidanta. 18 Awakin jeji kuma suna zama a kan duwatsu; rimaye kuma sun mayar da ƙonƙolin duwatsu mafakarsu. 19 Yasa wata ya nuna lokuta; rana kuma ta san lokacin faɗuwarta. 20 Ka yi duhun dare lokacin da duk daji ke fitowa waje. 21 Sagarun zakuna kan yi gurnani domin neman abincinsu daga wurin Allah. 22 Lokacin da rana ta fito sai su koma suyi barci a kogunansu. 23 Hakanan mutane kan je waje wurin aikinsu suyi ta aiki har yamma. 24 Yahweh ayyukanka iri-iri guda nawa ne! Da hikima kayi su dukka; duniya ta cika maƙil da ayyukanka. 25 A can kuma sai teku, mai zurfi da faɗi cike da manya da ƙananan hallitu marasa ƙidayuwa, 26 Jiragen ruwa sukan je can, Lebiyatan kuma a can ya ke, wanda ka yi domin yayi wasa a cikin teku. 27 Duk waɗannan gare ka suke zuba ido domin samun abinci a kan lokaci 28 Lokacin da ka basu, su kan tara; lokacin daka buɗe hannunka, sukan ƙoshi. 29 Lokacin da ka ɓoye fuskarka, sukan shiga damuwa; in ka ɗauke numfashinsu sukan mutu su koma ƙura. 30 Lokacin da ka aiko Ruhunka, aka hallice su, ka kuma sabunta gefen ƙasarsu. 31 Dãma ɗaukakar Yahweh ta dawwama har abada; dãma Yahweh ya ji daɗin hallitarsa. 32 Ya dubi duniya, sai ta girgiza; yakan taɓa duwatsu suyi hayaƙi. 33 Zan raira yabo ga Yahweh a dukkan kwanakin raina; zan raira waƙar yabo ga Allah muddin ina raye. 34 Dãma tunane-tunanena su zama da zaƙi a gare shi; Zan yi murna cikin Yahweh. 35 Dãma masu zunubi su hallaka daga duniya, dãma miyagu su ɓace daga duniya. Ina yabon Yahweh dukkan kwanakin raina. A yabi Yahweh.

Zabura 105

1 Ku bada godiya ga Yahweh, ku kira bisa sunansa; ku sanar da ayyukansa cikin al'ummai. 2 Ku raira gare shi, ku raira yabbai gare shi; kuyi maganar dukkan ayyukansa na ban mamaki. 3 Kuyi taƙama cikin sunan sa mai tsarki; bari zuciyar waɗanda ke biɗar Yahweh ta yi farinciki. 4 Ku biɗi Yahweh da ƙarfinsa kuma; ku biɗi bayyanuwarsa ba fasawa. 5 Ku tuna da abubuwan ban mamaki da yayi, al'ajibansa da kuma dokoki daga bakinsa, 6 ku zuriyar Ibrahim bawansa, ku mutanen Yakubu, zaɓaɓɓunsa. 7 Shi ne Yahweh, Allahnmu. Dokokin sa suna bisan dukkan duniya. 8 Cikin ransa yana ajiye alƙawarinsa har abada, maganarsa da ya umarta domin dubun tsararraki. 9 Yana tunawa a cikin ransa alƙawarin da yayi da Ibrahim da kuma rantsuwarsa ga Ishaku. 10 Wannan ne abin da ya tabbatar wa Yakubu a matsayin farilla da Isra'ila a matsayin madawwamin alƙawari. 11 Ya ce, "Zan baku ƙasar kan'ana a matsayin kasonku na gãdonku." 12 Ya faɗi wannan sa'ad da suke kaɗan a lissafi, 'yan kima sosai, kuma suna baƙi a ƙasar. 13 Suka tafi daga al'umma zuwa al'umma kuma daga masarauta zuwa wata. 14 Bai bar wani ya tsananta masu ba; ya tsautawa sarakuna sabili da su. 15 Ya ce, "Kada ku taɓa shafaffuna, kada kuma ku yi lahani ga annabawana." 16 Yayi kira domin yunwa bisa ƙasar; ya yanke dukkan biyan buƙatar gurasa. 17 Ya aika da mutum gaba da su; Yosef a ka sayar da shi a matsayin bawa. 18 Aka ɗaure ƙafafunsa da sarƙoƙi; a bisa wuyansa aka sa maɗaurin ƙarfe, 19 har sai lokacin da maganganun sa suka zama gaskiya, kuma maganar Yahweh ta gwada shi. 20 Sarki ya aika da bayi su sake shi; shugaban mutanen ya 'yantar da shi. 21 Ya sanya shi lura da gidansa a matsayin shugaban dukkan mallakarsa 22 ya bayar da umarni ga shugabanninsa yadda ya so ya kuma koyar da dattawansa hikima. 23 Daga nan Isra'ila ya zo cikin Masar, Yakubu kuma ya zauna na wani lokaci a cikin ƙasar Ham. 24 Yahweh yasa mutanen sa suka yi 'ya'ya, ya kuma sa suka yi ƙarfi fiye da maƙiyansu. 25 Ya kuma sa maƙiyansa suka ƙi Jinin mutanensa, suka muzguna wa bayinsa. 26 Ya aika da Musa, bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa. 27 Suka aikata alamunsa a tsakiyar masarawa, al'ajibansa a ƙasar Ham. 28 Ya aika da duhu ya maida ƙasar duhu, amma mutanen ta basu yi biyayya da umarninsa ba. 29 Ya maida ruwansu ya zama jini ya kuma kashe kifinsu. 30 ‌Ƙasar ta cika da gungun kwaɗi, har ma cikin ɗakunan shugabanninsu. 31 Yayi magana, kuma gungun ƙudaje da ƙwari suka zo cikin dukkan ƙasar. 32 Ya maida ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da wuta mai ci balbal bisa ƙasarsu. 33 Ya lalata kuringun inabinsu da itatuwan ɓaurensu; ya karya itatuwan ƙasarsu. 34 Yayi magana, fãri suka zo, fãri masu yawan gaske. 35 Fãrin suka cinye dukkan ganyayyaki a ƙasar; suka cinye dukkan amfanin gona. 36 Ya kashe kowanne ɗan fãri a cikin ƙasar, 'ya'yan fãrin dukkan ƙarfinsu. 37 Ya fito da Isra'ilawa tare da azurfa da zinariya; babu wani cikin kabilunsa da yayi tuntuɓe a hanya. 38 Masar ta yi farinciki da suka tafi, domin masarawa sunji tsoronsu. 39 Ya shimfiɗa girgije a matsayin abin rufa ya kuma yi wuta ta haskaka dare. 40 Isra'ilawa suka yi roƙon abinci, ya kuma kawo makwarwa ya kuma ƙosar da su da gurasa daga sama. 41 Ya fasa dutse ruwa kuma ya ɓulɓulo daga gare shi; ya malala cikin jeji kamar kogi. 42 Domin ya tuna a ransa da alƙawarin sa mai tsarki wanda yayi wa Ibrahim bawansa. 43 Ya bida mutanen sa suka fita da farinciki, zaɓaɓɓunsa da sowace-sowace fiye da gaban masu nasara. 44 Ya basu ƙasashen al'ummai; suka ɗauki mallakar dukiyar mutanen 45 domin su kiyaye farillansa su kuma yi biyayya da shari'unsa. A yabi Yahweh.

Zabura 106

1 A yabi Yahweh. A bada girma ga Yahweh, domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 2 Wa zai lissafa manyan ayyukan Yahweh ko yayi cikakken shelar dukkan ayyukansa da suka cancanci yabo? 3 Masu albarka ne waɗanda suke yin abin dake dai-dai, waɗanda kuma a koyaushe ayyukansu baratattu ne. 4 Ka tuna dani a rai, Yahweh, sa'ad da ka nuna tagomashi ga mutanenka; ka taimake ni sa'ad da ka cece su. 5 Daga nan zan ga wadatar zaɓaɓɓun ka, in yi farinciki cikin murnar ƙasarka, da ɗaukaka tare da gãdonka. 6 Mun yi zunubi kamar Kakanninmu; mun yi laifi, mun kuma aikata mugunta. 7 Ubanninmu basu yaba wa ayyukanka masu ban mamaki ba a Masar; suka yi banza da ayyukanka masu yawa na alƙawarin aminci; suka yi tawaye a bakin teku, Tekun Iwa. 8 Duk da haka, ya cece su domin sunansa saboda ya bayyana ikonsa. 9 Ya tsautawa Tekun Iwa, ya kuwa bushe. Daga nan ya bida su ta cikin zurfafan, kamar ta cikin jeji. 10 Ya cece su daga hannun waɗanda suka ƙi su, ya kuma ƙwato su daga hannun maƙiyansu. 11 Amma ruwayen suka rufe magaftansu; babu wanin su da ya tsira. 12 Daga nan suka gaskata maganganunsa, kuma suka raira yabonsa. 13 Amma nan da nan suka manta da abin da yayi; ba su jira umarninsa ba. 14 Suka yi kwaɗayi marar ƙosarwa a jeji, kuma suka ƙalubalanci Allah a cikin hamada. 15 Ya basu abin da suka roƙa, amma ya aika da cuta wadda ta cinye jikkunansu. 16 A sansanin suka zama masu kishin Musa da Haruna, firist mai tsarki na Yahweh. 17 ‌Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta kuma rufe mabiyan Abiram. 18 Wuta ta ɓarke a tsakaninsu; wutar ta cinye mãsu mugunta. 19 Suka yi maraƙi a Horeb suka kuma yi sujada ga sarrafaffar siffar ƙarfe. 20 Suka musanya ɗaukakar Allah domin siffar maraƙi mai cin ciyawa. 21 Suka manta da Allah Maicetonsu, wanda yayi manyan ayyuka a Masar. 22 Yayi abubuwan ban mamaki a ƙasar Ham ya kuma yi ayyuka masu iko a Tekun Iwa. 23 Da ya zartar da dokar hallakar dasu, inda ba domin Musa, zaɓaɓɓensa, ya shiga tsakaninsu da shi ba ya juya fushinsa daga hallakar dasu. 24 Daga nan suka raina ƙasa mai bayar da amfani; ba su gaskata da alƙawarinsa ba, 25 amma suka yi gunaguni a rumfunansu, ba su kuma yi biyayya da Yahweh ba. 26 Saboda haka ya ɗaga hannunsa kuma ya rantse masu cewa zai barsu su mutu a hamada, 27 ya warwatsa zuriyarsu cikin al'ummai, ya kuma warwatsa su cikin bãƙin ƙasashe. 28 Suka yi sujada ga Ba'al na fowa suka kuma ci hadayun da a ke miƙawa ga matattu. 29 Suka cakune shi ya yi fushi da ayyukansu, annoba kuwa ta faso a tsakaninsu. 30 Daga nan Fenihas ya tashi ya kai ɗauki, annobar kuwa ta tsagaita. 31 Aka lissafa masa shi a matsayin aikin adalci ga dukkan tsara har abada. 32 Suka kuma ba Yahweh haushi a ruwayen Meriba, Musa kuma ya sha wahala saboda su. 33 Suka sa Musa ya ji haushi, ya kuma yi magana da fushi. 34 Basu hallakar da al'ummai ba kamar yadda Yahweh ya dokace su, 35 amma suka gauraye da al'ummai suka kuma koyi hanyoyinsu 36 kuma suka yi sujada ga gumakansu, waɗanda suka zamar masu tarko. 37 Suka yi hadayar 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata ga aljanu. 38 Suka zubar da jini marar laifi, jinin 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata, waɗanda suka yi hadaya dasu ga gumakan Kan'ana, suka ƙazantar da ƙasar da jini. 39 Suka ɓãci da ayyukansu; cikin ayyukansu suka zama kamar karuwai. 40 Saboda haka Yahweh ya yi fushi da mutanensa, ya kuma rena nasa mutanen. 41 Ya bayar dasu cikin hannun al'ummai, waɗanda kuma suka ƙi su suka yi mulki a kansu. 42 Maƙiyan su suka tsananta masu, aka kuma kawo su ƙarƙashin hukuncinsu. 43 Lokutta da yawa yazo ya taimake su, amma suka ci gaba da yin tawaye aka kuma kawo su ƙasa ta wurin zunubinsu. 44 Duk da haka, ya lura da ƙuncin su sa'ad da ya ji kukansu domin taimako. 45 Ya tuna a ransa da alƙawarin sa tare dasu ya kuma yi jinkiri saboda matuƙar ƙaunarsa. 46 Ya sa dukkan waɗanda suka yi nasara dasu suka ji tausayin su. 47 Ka cece mu, Yahweh, Allahnmu. Ka tattaro mu daga cikin al'ummai domin mu ba da godiya ga sunan ka mai tsarki mu kuma yi ɗaukaka cikin yabban ka. 48 Bari Yahweh, Allah na Isra'ila, ya sami yabo daga matuƙa zuwa matuƙa. Dukkan mutane sukace, "Amin." A yabi Yahweh. Littafi na Biyar

Zabura 107

1 Ku ba da godiya ga Yahweh, domin shi nagari ne, kuma alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 2 Bari fansassun Yahweh suyi magana, waɗanda ya cafko daga hannun maƙiyi. 3 Ya tattaro su daga bãƙin ƙasashe, daga gabas daga kuma yamma, daga arewa daga kuma kudu. 4 Suka yi yawo a jeji bisa hanyar hamada ba su kuma sami birnin da zasu zauna ba. 5 Saboda sunji yunwa da ƙishi, suka some cikin gajiya. 6 Daga nan suka yi kira ga Yahweh cikin damuwarsu, ya kuma ceto su daga ƙuncinsu. 7 Ya bida su ta miƙaƙƙen tafarki saboda su tafi cikin birnin da zasu zauna. 8 Da ma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da yayi domin 'yan adam! 9 Domin ya biya buƙatun begen masu jin ƙishi, da marmarin masu jin yunwa ya cika da abubuwa masu kyau. 10 Waɗansu suka zauna cikin duhu da ɓoyewa, 'yan kurkuku cikin ƙunci da sarƙoƙi. 11 Wannan kuwa saboda sun yi tawaye gãba da maganar Yahweh suka kuma yi watsi da umarnin Maɗaukaki. 12 Ya ƙasƙantar da zukatansu ta wurin shan wuya; suka yi tuntuɓe kuma babu wanda zai taimake su ya ɗaga su. 13 Daga nan suka yi kira ga Yahweh a cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncinsu. 14 Ya fito dasu daga cikin duhu da ɓoyewa ya kuma karya karkiyarsu. 15 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da ya yi domin 'yan adam! 16 Domin ya karya ƙofofin tagulla ya kuma datse ginshiƙan ƙarfe. 17 Sun yi wawanci a cikin hanyoyinsu na tawaye suka kuma ƙuntata saboda zunubansu. 18 Marmarinsu na cin abinci ya ɓace, suka kuma zo kusa da ƙofofin mutuwa. 19 Daga nan suka yi kira ga Yahweh a cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncin su. 20 Ya aika da maganarsa ya warkar da su, ya kuma ceto su daga hallakarsu. 21 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da yayi domin 'yan adam! 22 Bari su miƙa hadayun godiya su kuma yi shelar ayyukansa cikin waƙa. 23 Waɗansu suka yi tafiya bisa teku cikin jiragen ruwa suka kuma yi sana'o'i bisa tekuna. 24 Waɗannan sun ga ayyukan Yahweh da al'ajibansa bisa tekuna. 25 Domin ya bada umarni ya kuma zuga iskar guguwa dake motsa tekuna. 26 Suna kaiwa ga sararin sama; su tafi ƙasa cikin zurfafa. Rayuwar suna narkewa cikin ƙunci. 27 Suna gushewa suyi tangaɗi kamar bugaggu waɗanda kuma suka kawo ga ƙarshen iyawarsu. 28 Daga nan suka yi kira ga Yahweh cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncinsu. 29 Ya tausar da guguwar, kuma raƙuman suka yi tsit. 30 Daga nan suka yi farinciki saboda tekun ya tausu, ya kuma kawo su in da suke so su sauka. 31 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da ya yi domin 'yan adam! 32 Bari su ɗaukaka shi a cikin taron mutane su kuma yabe shi a majalisar dattawa. 33 Ya maida koguna suka koma jeji, maɓulɓulan ruwa suka koma busasshiyar ƙasa, 34 da ƙasa mai bada 'ya'ya zuwa bakararen wuri saboda muguntar mutanenta. 35 Ya maida jeji kuma ya zama tafkin ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulan ruwa. 36 Ya wadatar da masu jin yunwa a wurin, suka kuma gina birni su zauna a ciki. 37 Suka gina birni su dasa gonaki a ciki, su dasa garkunan inabi, su kuma kawo yalwar kaka. 38 Ya albarkace su suka zama fiye da lissafi sosai. Bai bar garken dabbobinsu ba su ragu a lissafi. 39 Suka ragu aka kuma ƙasƙantar dasu ta wurin ƙunci mai zafi da wahala. 40 Ya zubo raini bisa shugabanninsu yasa kuma suka yi yawo cikin jeji, in da babu hanyoyi. 41 Amma ya kiyaye mabuƙata daga ƙunci ya kuma lura da iyalinsa kamar garken tumaki. 42 Masu adalci zasu dubi wannan suyi farinciki, dukkan mugunta kuma ta rufe bakinta. 43 Duk mai hikima ya yi la'akari da waɗannan abubuwa ya kuma yi tunani bisa ayyukan Yahweh na alƙawarin aminci.

Zabura 108

Zabura ta Dauda.

1 Zuciyata ta kafu, Allah; zan raira, I, zan raira yabbai kuma tare da zuciyata ta girmamawa. 2 Ku tashi, sarewa da garaya; zan tashi da asuba. 3 Zan bada godiya gare ka, Yahweh, a tsakanin mutane; zan raira yabbai gareka a tsakanin al'ummai. 4 Domin alƙawarin amincinka mai girma ne sama da sammai; amincin ka kuma ya kai sararin sama. 5 Ka ɗaukaka, Allah, sama da sammai, bari kuma darajarka ta ɗaukaka sama da dukkan duniya. 6 Domin waɗanda kake ƙauna su sami ceto, ka ceto mu da hannunka na dama ka kuma amsa mani. 7 Allah yayi magana cikin tsarkinsa; "Zan yi farinciki; zan raba Shekem in kuma yi kason kwarin Sukkot. 8 Giliyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Ifraim ma ƙwalƙwali nane; Yahuda kuma sandar sarautana ne. 9 Mowab kwanon wankina ne; bisa Idom zan jefa takalmina; Zanyi sowa cikin nasara saboda Filitiya. 10 Wa zai kawo ni ckin birni mai karfi? Wa zai bida ni zuwa Idom?" 11 Allah, baka watsar damu ba? Baka tafi cikin yaƙi tare da mayaƙanmu ba. 12 Ka ba mu taimako gãba da maƙiyinmu, domin taimakon mutum wofi ne. 13 Zamu yi nasara da taimakon Allah; zaya tattake maƙiyanmu.

Zabura 109

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Allah wanda nake yabo, kada ka yi shiru, 2 Domin miyagu da macuta sun kawo mani hari; sun faɗi ƙarairayi game dani. 3 Sun kewaye ni kuma sun faɗi abubuwan ƙiyayya, kuma sun kawo mani hari babu dalili. 4 A ramuwar ƙaunata sun kawo mani sãra, amma nayi addu'a domin su. 5 Sun biya nagarta ta da mugunta, kuma sun ƙi ƙauna ta. 6 Ka naɗa mugun mutum bisa irin waɗannan maƙiya kamar waɗannan mutanen; ka naɗa mai sãra ya tsaya a hannun damansa. 7 Idan aka shar'anta shi, bari a same shi mai laifi; bari addu'arsa a ɗauke ta zunubi. 8 Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani ya ɗauki gurbinsa. 9 Bari 'ya'yansa su zama marasa mahaifi, matar sa kuma gwauruwa. 10 Bari 'ya'yan sa su tafi gantali da bara. Suna roƙon abin da aka rage yayin da suka bar rusassun gidajensu. 11 Bari mai bin bashi ya ɗauke dukkan abin da ya mallaka; bari bãƙi su washe abin da ya ke samu. 12 Kada wani ya miƙa wani halin kirki gare shi; kada wani ya ji tausayin 'ya'yansa marasa mahaifi. 13 Bari a datse 'ya'yan sa; bari a share sunansu daga tsara ta gaba. 14 Bari a faɗi zunuban kakanninsa ga Yahweh; bari kuma kada a manta da zunubin mahaifiyarsa. 15 Bari laifinsu a koyaushe ya kasance a gaban Yahweh; Bari Yahweh ya datse tunawa dasu daga duniya. 16 Bari Yahweh yayi haka saboda mutumin nan bai kula daya nuna wani alƙawarin aminci ba, amma a maimako ya firgitar da masu shan tsanani, masu buƙata, da masu ɓacin zuciya har ga mutuwa. 17 Yana ƙaunar la'ana; bari ta dawo kansa. Yaƙi albarka; bari kada albarka ta zo gareshi. 18 Ya lulluɓe kansa da la'ana kamar tufafi, kuma la'anarsa ta shiga cikin sa kamar ruwa, kamar mai cikin ƙasusuwansa. 19 Bari la'anoninsa su zame masa kamar suturar da ya ke sanyawa ya rufe kansa, kamar ɗamarar da ya ke sanyawa koyaushe. 20 Bari wannan ya zama rabon masu zargina daga Yahweh, ga waɗanda ke faɗin miyagun abubuwa game dani. 21 Yahweh Ubangijina, ka yi mani alheri sabili da sunanka. Saboda alƙawarin amincinka nagari ne, ka cece ni. 22 Domin ni mai shan tsanani ne mai buƙata kuma, zuciya ta kuma taji ciwo a cikina. 23 Ina ƙarewa kamar inuwar maraice; Ina kakkaɓewa kamar fãra. 24 Gwiwowina sun rasa ƙarfi daga azumi; Ina komawa fata da ƙasusuwa. 25 Na zama wulaƙantacce wurin masu zargina; idan suka ganni, suna girgiza kawunansu. 26 Ka taimake ni, Yahweh Allahna; ka cece ni ta wurin alƙawarin amincin ka. 27 Bari su san cewa wannan yinka ne, cewa kai, Yahweh, ka yi wannan. 28 Koda ya ke sun la'ance ni, ina roƙon ka ka albarkace ni; Idan suka kawo hari, bari su sha kunya, amma bari bawanka yayi farinciki. 29 Bari magafta na suyi sutura da kunya; bari su sanya kunyar su kamar alkyabba. 30 Da bakina na bada babbar godiya ga Yahweh; Zan yabe shi a tsakiyar taro. 31 Domin zai tsaya a hannun daman wanda keda buƙata; ya cece shi daga waɗanda ke shar'ianta shi.

Zabura 110

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh ya cewa ubangijina, "Ka zauna hannun damana har sai na maida maƙiyanka abin takawar ka." 2 Yahweh zai riƙe sandar mulkin ƙarfin ka daga Sihiyona; kayi mulki a tsakiyar maƙiyanka. 3 Mutanenka zasu bi ka cikin tsarkakan tufafi da nufin kansu ranar ikonka; daga mahaifar asubahi ƙuruciyar ka zata zame maka a kamar raɓa. 4 Yahweh yayi rantsuwa, kuma ba zai canza ba: "Kai firist ne na har abada, bisa ga ɗabi'ar Melkizadek." 5 Ubangiji yana hannun damanka. Zai kashe sarakuna a ranar fushinsa. 6 Zai shar'anta al'ummai; zai cika filin yaƙi da gawarwaki; zai kashe shugabanni a ƙasashe masu yawa. 7 Zai sha daga rafin bakin hanya, daga nan kuma zai ɗaga kansa sama bayan nasara.

Zabura 111

1 Ku yabi Yahweh. Zan bada godiya ga Yahweh da dukkan zuciyata a cikin taron masu adalci, a cikin tattaruwarsu. 2 Ayyukan Yahweh masu girma ne, ana jira da ɗoki ga dukkan waɗanda ke marmarin su. 3 Aikin sa mai daraja ne cike da ɗaukaka, adalcinsa kuma ya dawwama har abada. 4 Yana yin abubuwan ban mamaki daza a tuna; Yahweh cike da alheri ya ke cike kuma da jinƙai. 5 Yana bayar da abinci ga amintattun mabiyansa. Za ya tuna a ransa koyaushe da alƙawarinsa. 6 Ya nuna ayyukansa a cike da iko ga mutanensa inda ya basu gãdon al'ummai. 7 Ayyukan hannuwansa sun isa amincewa da hukunci; dukkan umarninsa abin dogara ne. 8 An kafa su har abada, domin a kiyaye su da aminci a dai-dai kuma. 9 Ya bada nasara ga mutanensa; ya naɗa alƙawarinsa har abada; tsarki da ban mamaki ne sunansa. 10 Girmama Yahweh shi ne farkon hikima; waɗanda suke aikata umarninsa suna da fahimta mai kyau. Yabonsa ya dawwama har abada.

Zabura 112

1 A yabi Yahweh. Mai albarka ne mutumin dake biyayya da Yahweh, wanda ya ke jin daɗin dokokinsa sosai. 2 Zuriyarsa zasu zama cike da iko a duniya; zuriyar mutum mai tsoron Allah masu albarka ne. 3 Dukiya da arziki suna cikin gidansa; adalcinsa zai dawwama har abada. 4 Haske yana haskaka wa cikin duhu domin taliki mai tsoron Allah; yana cike da alheri, cike da jinƙai, da hukunci. 5 Yana tafiya lafiya ga mutumin dake aikata alheri da bayar da rancen kuɗi, wanda ke tafiyar da al'amuransa tare da gaskiya. 6 Domin ba zai taɓa gusawa ba; mai adalci za a tuna da shi har abada. 7 Baya jin tsoron mugun labari; yana da ƙarfin hali, dogara ga Yahweh. 8 Zuciyar sa lif, ba tare da tsoro ba, har sai ya duba cikin nasara bisa magabtansa. 9 A yalwace ya ke bayar wa ga talakawa; adalcinsa ya dawwama har abada; za a ɗaukaka shi da girmamawa. 10 Wanda ke mugu zai duba wannan kuma ya ji haushi; zai ciza haƙoransa ya kuma narke; marmarin miyagun mutane zaya lalace.

Zabura 113

1 Ku yabi Yahweh. Ku yabe shi ku bayin Yahweh; ku yabi sunan Yahweh. 2 Albarka ta tabbata ga sunan Yahweh, duk da yanzu da har abada abadin. 3 Daga tasowar rana har zuwa faɗuwarta, sunan Yahweh ya sami yabo. 4 Yahweh ya ɗaukaka sama da dukkan al'ummai, darajarsa kuma ta wuce gaban sararin sammai. 5 Wane ne kamar Yahweh Allahnmu, wanda keda mazauninsa a sama, 6 wanda ke duba sararin sama da duniya? 7 Yana taso da talaka daga datti kuma ya ɗaga mabuƙaci daga tarin toka, 8 domin ya zaunar da shi tare da shugabanni, tare da shugabannin mutanensa. 9 Yana bayar da gida ga bakarariyar macen gidan, yana mayar da ita uwar 'ya'ya cike da farinciki. A yabi Yahweh!

Zabura 114

1 Da Isra'ila suka bar Masar, gidan Yakubu daga waɗannan bãƙin mutane, 2 Yahuda ya zama wurinsa mai tsarki, Isar'ila masarautarsa. 3 Teku ya duba kuma ya gudu; Yodan ya juya baya. 4 Duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai suka yi tsalle kamar 'yan raguna. 5 Me yasa ka gudu, teku? Yodan, me yasa ka juya baya? 6 Duwatsu, me yasa kuka yi tsalle kamar raguna? Ku ƙananan tuddai, me yasa kuka yi tsalle kamar 'yan raguna? 7 Yi rawar jiki, duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allahn Yakubu. 8 Ya juya dutse ya zama tafkin ruwa, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓular ruwa.

Zabura 115

1 Ba gare mu ba, Yahweh, ba gare mu ba, amma ga sunanka ka kawo daraja, domin alƙawarin amincinka domin kuma isar amincewarka. 2 Me yasa al'ummai zasu ce, "Ina Allahnsu?" 3 Allahnmu yana sama; yana yin abin daya so. 4 Gumakan al'ummai azurfa ne da zinariya, aikin hannuwan mutane. 5 Waɗannan gumakai suna da baki, amma ba su magana; suna da idanu, amma basu gani; 6 suna da kunnuwa, amma basu ji; suna da hanci, amma basu sunsuna wa. 7 Waɗannan gumakai suna da hannuwa, amma basu taɓa wa; suna da tafin ƙafafu, amma basu tafiya; ko kuwa suyi magana daga bakunansu. 8 Waɗanda suka yi su kamar su suke, haka ma duk wanda ya dogara gare su. 9 Isra'ila, ku dogara ga Yahweh; shi ne taimakonku da garkuwarku. 10 Gidan Haruna, ku dogara ga Yahweh; shi ne taimakonku da garkuwarku. 11 Ku waɗanda ke girmama Yahweh, ku dogara gare shi; shi ne taimakonku da garkuwarku. 12 Yahweh yana la'akari damu kuma zai albarkace mu; zai albarkaci iyalin Isra'ila; zai albarkaci iyalin Haruna. 13 Zai albarkaci waɗanda ke girmama shi, yara da tsofaffi. 14 Bari Yahweh ya ƙara lissafin ku ƙari da ƙari, naku dana zuriyarku. 15 Bari ku yi albarka ta wurin Yahweh, wanda yayi sama da duniya. 16 Sammai na Yahweh ne; amma duniya ya bayar ga 'yan adam. 17 Matattu basu yabon Yahweh, ko kuwa wani wanda ya gangara cikin shiru; 18 Amma zamu albarkaci Yahweh yanzu da har abada abadin. A Yabi Yahweh.

Zabura 116

1 Ina ƙaunar Yahweh saboda yana jin murya ta da kuma roƙe-roƙe na domin jinƙai. 2 Saboda yana saurare na, zan yi kira a gare shi muddan ina da rai. 3 Sarƙoƙin mutuwa sun kewaye ni, tarkon Lahira kuma ya fuskance ni; naji ƙunci da baƙinciki. 4 Daga nan nayi kira ga sunan Yahweh: "Ina roƙon ka Yahweh, ka ceto rai na." 5 Yahweh yana cike da jinƙai da adalci; Allahnmu mai tausayi ne. 6 Yahweh yana kiyaye marasa sani; an kawo ni ƙasa, kuma ya cece ni. 7 Raina zai koma wurin hutawarsa, domin Yahweh yana yi mani da kyau. 8 Domin ka ceto raina daga mutuwa, idanu na daga hawaye, tafin ƙafafuna kuma daga tuntuɓe. 9 Zan bauta wa Yahweh a ƙasar masu rai. 10 Na bada gaskiya a gare shi, ko sa'ad da nace, "Ina cikin babban ƙunci." 11 Nayi garejen cewa, "Dukkan mutane maƙaryata ne." 12 Yaya zan biya Yahweh domin dukkan jiyejiyenƙansa zuwa gare ni? 13 Zan ɗaga ƙoƙon ceto, in kuma yi kira ga sunan Yahweh. 14 Zan cika alƙawaraina ga Yahweh a gaban dukkan mutanensa. 15 Abu mai daraja a gaban Yahweh shi ne mutuwar tsarkakansa. 16 Yahweh, tabbas, ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ɗauke tsarƙoƙina. 17 Zan miƙa maka hadayar godiya in kuma yi kira ga sunan Yahweh. 18 Zan cika alƙawaraina ga Yahweh a gaban dukkan mutanensa, 19 cikin harabun gidan Yahweh, a tsakiyarki, Yerusalem. A yabi Yahweh.

Zabura 117

1 Ku yabi Yahweh, dukkan ku al'ummai; ku ɗaukaka shi, dukkan ku mutane. 2 Domin alƙawarin amincinsa mai girma ne zuwa gare mu, isar amincin Yahweh kuma ya dawwama har abada. A yabi Yahweh.

Zabura 118

1 Ku bada godiya ga Yahweh, domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 2 Bari Isra'ila su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada." 3 Bari gidan Haruna su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada." 4 Bari amintattun masu bin Yahweh su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada." 5 A cikin ƙuncina nayi kira ga Yahweh; Yahweh ya amsa mani ya kuma 'yantar dani. 6 Yahweh yana tare dani; ba zan ji tsoro ba; me mutum zai yi mani? 7 Yahweh yana gefe na a matsayin mai taimako na; zan duba cikin nasara bisa waɗanda suka ƙi ni. 8 Ya fi kyau a ɗauki mahalli cikin Yahweh da a sa dogara cikin mutum. 9 Gwamma a ɗauki mafaka cikin Yahweh da wani yasa dogararsa cikin sarakuna. 10 Dukkan al'ummai sun kewaye ni; a cikin sunan Yahweh na datse su. 11 Sun kewaye ni; I, sun kewaye ni; a cikin sunan Yahweh na datse su. 12 Sun kewaye ni kamar zuma; sun ɓace da sauri kamar wuta a tsakiyar sarƙaƙiya; a cikin sunan Yahweh na datse su. 13 Sun kawo mani hari saboda su mãke ni ƙasa, amma Yahweh ya taimake ni. 14 Yahweh ne ƙarfina da farincikina, shi ne kuma ya ceto ni. 15 Sowar farinciki ta nasara aka ji a cikin rumfunan adalai; hannun dama na Yahweh ya ci nasara. 16 Hannun dama na Yahweh ya ɗaukaka; hannun dama na Yahweh yaci nasara. 17 Ba zan mutu ba, amma zan rayu kuma inyi shelar ayyukan Yahweh. 18 Yahweh ya horar da ni da zafi; amma bai miƙa ni ga mutuwa ba. 19 Ka buɗe mani ƙofofin adalci; zan shige su kuma zan bada godiya ga Yahweh. 20 Wannan ce ƙofar Yahweh; adali yana bi ta ciki. 21 Zan bada godiya a gare ka, domin ka amsa mani, kuma ka zama cetona. 22 Dutsen da magina suka watsar ya zama dutsen kusurwa. 23 Wannan yin Yahweh ne; mai ban mamaki ne a idanunmu. 24 Wannan ce ranar da Yahweh ya yi aiki; za muyi farinciki da murna a cikin ta. 25 Ina roƙon ka, Yahweh, ka bamu nasara! Ina roƙon ka, Yahweh, ka bamu ci gaba! 26 Mai albarka ne wanda ya zo cikin sunan Yahweh; mun albarkace ka daga gidan Yahweh. 27 Yahweh Allahn ne, ya kuma bamu haske; ku ɗaure hadaya da igiyoyi a ƙahonnin bagadi. 28 Kai Allahna ne, kuma zan bada godiya a gare ka; kai Allahna ne; zan ɗaukaka ka. 29 Oh, ku bada gadiya ga Yahweh; domin shi nagari ne; domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.

Zabura 119

ALEPH

1 Masu albarka ne waɗanda hanyoyinsu basu da laifi, waɗanda ke tafiya cikin shari'ar Yahweh. 2 Masu albarka ne waɗanda suka kiyaye umarnansa masu tsarki masu neman sa da dukkan zuciyarsu. 3 Sun yi abin da ke dai-dai; suna tafiya cikin hanyoyinsa. 4 Ka umarce mu mu kiyaye dokokinka, domin muyi lura mu kiyaye su, 5 Kash, ina ma zan ɗore a cikin lura da farillanka! 6 To da ba za a kunyata ni ba a lokacin da nayi tunanin dukkan dokokinka. 7 Zan yi maka godiya da zuciya mai tsarki a lokacin dana koyi sharuɗɗanka. 8 Zan kiyaye farillanka; kar ka barni ni kaɗai.

BETH

9 Yaya matashi zai tsare tafarkinsa da tsabta? Ta wurin kiyaye maganarka. 10 Da dukkan zuciyata na neme ka; Kar ka barni in kauce wa umarnanka. 11 Na adana maganarka a cikin zuciyata domin kada in yi maka zunubi. 12 Yahweh kai mai albarka ne, ka koya mani farillanka. 13 Da bakina na furta dukkan ayyukanka na jinƙai da ka bayyana mani. 14 Ina murna da umarnanka fiye da dukkan wadata. 15 Zan yi ta nazarin dokokinka in kuma saurari sharuɗɗanka. 16 Ina jin daɗin farillanka; ba kuma zan manta da maganarka ba.

GIMEL

17 Yiwa bawanka kirki domin in rayu in kiyaye maganarka. 18 Buɗe idanuna domin in ga ayyukan al'ajibi a cikin shari'arka. 19 Ni bãƙo ne a cikin ƙasar; kada ka ɓoye umarnanka daga gare ni. 20 An rushe marmarina ta wurin jimirin sanin umarnanka masu adalci a kowanne lokaci. 21 Ka tsauta wa masu fahariya, waɗanda aka la'anta, Waɗanda suka bauɗe wa dokokinka. 22 Kãre ni daga wulaƙanci da cin mutunci, domin na kiyaye sharuɗɗan alƙawarinka. 23 Koda ya ke shugabanni sun ƙudurta suka yi mani maƙarƙashiya, ni bawanka ina binbinin farillanka. 24 Alƙawaran farillanka sune nake jin daɗi, sune kuma ke yi mini jagora.

DALETH

25 Raina yana birgima a ƙura! Ka bani rai ta wurin maganarka. 26 Na faɗa maka hanyoyina, ka kuma amsa mani; ka koya mani farillanka. 27 Ka sani in fahimci tafarkin umarninka, domin in yi ta nazarin koyarwarka mai al'ajibi. 28 Baƙinciki ya cika ni! Ka ƙarfafa ni ta wurin maganarka. 29 Ka jutar daga gare ni hanyar yaudara; ta wurin alheri ka koya mani shari'arka. 30 Na zaɓi hanyar aminci; Har kullum na kiyaye farillanka masu adalci daka sa a gabana. 31 Na manne wa umarnin alƙawarinka; Yahweh kada ka bar ni in ji kunya. 32 Zan bi hanyoyin dokokinka da gudu, gama ka faɗaɗa zuciyata tayi haka.

HE

33 Ka koya mani, Yahweh, hanyar umarnanka, kuma zan kiyaye su har ga ƙarshe. 34 Ka bani ganewa, kuma zan kiyaye shari'arka; Zan lura da ita da dukkan zuciyata. 35 Ka bishe ni ta tafarkin dokokinka, gama ina fahariya in yi tafiya cikinta. 36 Ka jagoranci zuciyata ga alƙawarin umarnanka da kaucewa daga ƙazamar riba. 37 Ka juya idanuwana daga duban wofintattun abubuwa; ka rayar da ni cikin hanyoyinka. 38 Ka cika wa bawanka alƙawarin da kayi ga waɗanda ke girmama ka. 39 Ka ɗauke zage-zagen da nake tsoro, gama hukuncin adalcinka na da kyau. 40 Duba, na jira umarnanka; ka farkar dani cikin sanin gaskiyarka.

VAV

41 Yahweh, ka ba ni madawwamiyar ƙaunarka- cetonka bisa ga alƙawarinka; 42 sa'an nan zan sami amsa domin duk mai yi mani ba'a, gama na amince da maganarka. 43 Kada ka ɗauke maganar gaskiya daga bakina, gama Na yi jira domin umarnan sanin gaskiyarka. 44 Zan kiyaye dokarka babu fasawa, har abada abadin. 45 Zan yi tafiya cikin kwanciyar hankali, gama ina neman ka'idodinka. 46 Zan yi magana a kan hakikanin umarninka a gaban sarakuna kuma ba zan ji kunya ba. 47 Ina murna da dokokinka, waɗanda nake ƙauna sosai. 48 Zan ɗaga hannuwana ga dokokinka, waɗanda nake ƙauna; Zan yi nazari a kan farillanka.

ZAYIN

49 Ka tuna da alƙawarinka zuwa ga bawanka domin ka ba ni bege. 50 Wannan itace ta'aziyata a cikin ƙuncina: cewa alƙawarinka ya kiyaye ni da rai. 51 Mai girman kai ya yi mani gwalo, duk da haka ban juya daga dokarka ba. 52 Nayi tunanin umarnanka masu adalci dake tun zamanun dã, Yahweh, kuma sai na yi wa kaina ta'aziya. 53 Fushi mai ƙuna ya riƙe ni sabili da mugu da ya ƙi dokarka. 54 Farillannka sun zama waƙoƙina a cikin gidan da nake zama na ɗan lokaci. 55 Na yi tunanin sunanka a cikin dare, Yahweh, na kuma riƙe dokarka. 56 Wannan ya zama abin da na ke yi domin na kula da umarnanka.

HETH

57 Yahweh ne rabona; nayi ƙudirin kula da maganganunka. 58 Nayi matuƙar neman tagomashinka da dukkan zuciyata; ka yi mani jinƙai, kamar yadda maganarka tayi alƙawari. 59 Nayi la'akari da tafarkina na kuma juyar da ƙafafuna zuwa ga umarnan alƙawarinka. 60 Nayi sauri ban kuma ɓata lokaci ba domin in kiyaye dokokin ka. 61 Igiyoyin mai mugunta suka nannaɗe ni; Ban manta da shari'arka ba. 62 Cikin dare na tashi domin inyi maka godiya sabili da dokokinka masu adalci. 63 Ni abokin dukkan waɗanda ke girmamaka ne, da dukkan waɗanda ke kula da umarnanka. 64 ƙasar, Yahweh, tana cike da amintaccen alƙawarinka; ka koya mani farillanka.

TETH

65 Kayi abin alheri ga bawanka, Yahweh, ta wurin maganarka. 66 Ka koya mani sasancewa da fahimta, gama na gaskata da dokokinka.' 67 Kamin a wahalshe ni sai da na bijire, amma yanzu ina kula da maganarka. 68 Kana da kyau, kuma kai ne mai aikata abu mai kyau; ka koya mani farillanka. 69 Mai girman kai ya rufe ni da ƙarairayi, amma na adana umarninka da dukkan zuciyata. 70 Zuciyarsu ta taurare, amma ina fahariya da shari'arka. 71 Ya dace dani dana sha wahala domin in koyi farillanka. 72 Umarni daga bakinka ya fiye mani daraja fiye da dubban zinariya da azurfa.

YOD

73 Hannayenka sunyi ni ka ƙera ni; ka ba ni fahimta domin in koyi dokokinka. 74 Waɗanda suke yi maka biyayya za suyi murna idan suka ganni saboda na sami bege cikin maganarka. 75 Yahweh, Na sani, dokokinka masu adalci ne, cikin amincinka kuma ka hukunta ni. 76 Bari alƙawarin amincinka ya ta'azantar dani, kamar yadda ka alƙawarta wa bawanka. 77 Ka nuna mani jinƙai domin in rayu, gama shari'arka ita ce jin daɗina. 78 Bari masu girmankai su sha kunya, gama sun ɓata sunana; amma zan yi nazarin umarnanka. 79 Bari masu darjanta ka su juyo gare ni, su da suka san alƙawaran dokokinka. 80 Bari zuciyata ta zama da rashin laifi da darjanta farillanka domin kada in sha kunya.

KAPH

81 Na suma domin sauraron cetonka! Na sa zuciya cikin maganarka. 82 Idanuna na jiran ganin alƙawarinka; yaushe za ka ta'azantar dani? 83 Gama na zama kamar salka cikin hayaƙi; Ban manta da farillanka ba. 84 Har yaushe bawanka zai jiure da wannan; yaushe zaka hukunta waɗanda suke tsananta mani? 85 Masu girmankai sun haƙa ramuka domina, suna rena shari'arka. 86 Dukkan dokokinka abin dogaro ne; waɗannan mutanen suna tsananta mani cikin kuskure; ka taimake ni. 87 Saura kaɗan su kawo ƙarshena a duniya, amma ban ƙi umarnanka ba. 88 Ta wurin tsayayyar ƙaunarka, ka kiyaye ni a raye, domin inyi biyayya da umarnanka.

LAMEDH

89 Yahweh, maganarka ta tsaya har abada; maganarka ta kahu da ƙarfi a cikin sama. 90 Amincinka ya dawwama ga dukkan tsararraki; ka kafa duniya, ta kuwa tsaya. 91 Dukkan abubuwa sun ci gaba har yau, kamar yadda ka faɗi cikin amintattun umarnanka, gama dukkan abubuwa bayinka ne. 92 Da shari'arka ba jin daɗina ba ce, da na hallaka a cikin ƙuncina. 93 Ba zan taɓa mantawa da umarnanka ba, gama ta wurinsu ka kiyaye ni da rai. 94 Ni naka ne; ka cece ni, gama na nemi umarnanka. 95 Masu mugunta sunyi shirin hallakar dani, amma zan nemi in san alƙawarin umarnanka. 96 Naga cewa dukkan abu yana da iyakarsa, amma dokokinka suna da fãɗi, basu da iyaka.

MEM

97 Oh ina ƙaunar shari'arka! ita ce abin bin-binina dukkan yini. 98 Dokokinka sun sani na zama da hikima fiye da maƙiyana, gama dokokinka kullum suna tare dani. 99 Ina da sani fiye da dukkan malamaina, gama ina tunani akan alƙawaran umarnanka. 100 Ina da sani fiye da waɗanda suka girmeni; wannan ya faru domin na kiyaye umarnanka. 101 Na kiyaye sawayena daga hanyar mugaye saboda in lura da maganarka. 102 Ban juya daga dokokin adalcinka ba, saboda kai ne ka bani umarni. 103 Ya ya zaƙin maganarka ga ɗanɗanona, I, tafi zuma zaƙi a bakina! 104 Ta wurin umarninka na ƙaru da basira; saboda haka ina ƙin kowacce hanyar ƙarya.

NUN

105 Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma ga hanyata. 106 Na rantse na kuma tabbatar da ita, saboda haka zan kula da adalcin dokokinka. 107 Ina shan azaba; ka bar ni a raye, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta a cikin maganarka. 108 Yahweh, idan ka yarda karɓi shaidar godiyar bakina, ka koya mani adalcin dokokinka. 109 Raina kullum yana hannuna, duk da haka ban manta da shari'arka ba. 110 Mugaye sun ɗana tarko domina, amma ban ratse daga umarninka ba. 111 Na nemi alƙawaran dokokinka a matsayin gãdona har abada, gama su ne murnar zuciyata. 112 Zuciyata a shirye take don biyayya da farillanka har abada, har kuma zuwa ƙarshe.

SAMEKH

113 Ina ƙin waɗanda ba sa son yi maka biyayya, amma ina ƙaunar shari'arka. 114 Kai ne kake tsare ni da garkuwarka; ina jiran maganarka. 115 Ku tafi daga gare ni, ku masu aikata mugunta, domin in kiyaye dokokin Allahna. 116 Ka ƙarfafa ni ta wurin maganarka saboda in rayu ba domin inji kunyar sa begena ba. 117 Ka ƙarfafa ni, zan kuma tsira. Zan yi ta nazari a kan umarninka. 118 Ka ƙi dukkan waɗanda suka ratse daga umarninka, domin waɗancan mutanen masu yaudara ne kuma ba abin dogara ba ne. 119 Ka cire dukkan mugayen duniya kamar dattin maƙera; saboda haka ina ƙaunar mahimman umarninka. 120 Na cika da tsoronka, kuma ina jin tsoron adalcin ka'idodinka.

AYIN

121 Na yi abin da ke na gaskiya da adalci, kada ka bashe ni a wurin masu yi mani tsanani. 122 Ka tsare lafiyar bawanka, kada ka bari masu girman kai su wahallar da shi. 123 Idanuna sun gaji sa'ad da nake jiran cetonka da maganarka mai adalci. 124 Ka nuna wa bawanka amincin alƙawarinka, ka koya mani farillanka. 125 Ni bawanka ne, ka bani fahimta domin in sa alƙawarin farillanka. 126 Lokaci ya yi da Yahweh zai yi aiki, domin mutane sun karya shari'arka. 127 Gaskiya ne ina ƙaunar dokokinka fiye da zinariya, fiye da zinariya mai kyau. 128 Saboda haka na bi umarninka a hankali, na tsani kowacce hanya ta ƙarya.

PE

129 Ka'idojinka suna da ban mamaki, shi yasa nake yin biyayya dasu. 130 Buɗewar maganarka tana bada haske, tana bada ganewa ga wanda ba koyayye ba. 131 Na buɗe bakina ina haki, saboda na ƙagara domin maganarka. 132 Ka juyo wajena ka yi mani jinƙai kamar yadda ka ke yiwa waɗanda ke ƙaunar sunanka. 133 Ka bida ƙafafuna da maganarka, kada ka bari wani zunubi yayi mulki a kaina. 134 Ka fanshe ni daga hannun masu zalunci domin in lura da umarninka. 135 Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka, ka koya mani farillanka. 136 Ƙoramun ruwaye suna gudu daga idanuna saboda mutane ba sa lura da shari'arka ba.

TSADHE

137 Mai adalci ne kai, Yahweh, dokokinka kuma dai-dai suke. 138 Ka bada dokokinka na alƙawari masu adalci kuma amintattu. 139 Fushi ya hallaka ni saboda maƙiyana sun manta da maganganunka. 140 An jaraba maganarka sau da yawa, bawanka kuma yana ƙaunar su. 141 Ni ba komai bane an kuma rena ni, duk da haka ban manta da umarninka ba. 142 Adalcinka dai-dai ya ke har abada, shari'arka madogara ce. 143 Koda ya ke wahala da azaba sun afko mani, duk da haka dokokinka suna faranta mani rai. 144 ‌dokokinka na alƙawari masu adalci ne har abada.; ka bani fahimta domin in rayu.

QOPH

145 Nayi kuka da dukkan zuciyata, "Ka amsa mani, Yahweh, zan yi biyayya da farillanka. 146 Na kira ka; ka cece ni, zan kuwa aikata dokokinka na alƙawari. 147 Da asussuba nake tashi in yi kukan neman taimako. Na sa begena a cikin maganarka. 148 Na kan farka kafin masu gadin dare suyi sauyi domin in yi bin-binin maganarka. 149 Ka saurari muryata a cikin alƙawarin amincinka; ka barni da rai, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta a cikin dokokinka na adalci. 150 Su waɗanda suke tsananta mani suna matsowa kusa dani, amma suna nesa da shari'arka. 151 Kana kusa, Yahweh, kuma duk umarnanka amintattu ne. 152 Tun dã can na koya daga dokokin alƙawaranka cewa ka tsaida su har abada.

RESH

153 Ka dubi ƙunci na kayi mani taimako, gama ban manta da shari'arka ba. 154 Ka tsaya mani ka kuma fanshe ni; ka riƙe ni, kamar yadda ka alƙawarta a maganarka. 155 Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa ƙaunar farillanka. 156 Ayyukanka na jinƙai masu girma ne, Yahweh; ka kiyaye ni da rai, kamar yadda ka saba yi. 157 Masu zaluntata da maƙiyana suna da yawa, duk da haka ban bar bin dokokinka na alƙawari ba. 158 Ina duban maciya amana a ƙyamace domin ba sa biyayya da maganarka. 159 Dubi yadda nake ƙaunar umarninka; ka kiyaye ni da rai, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta ta wurin alƙawarinka mai aminci. 160 Cibiyar maganarka ita ce gaskiya; kowanne ɗaya daga cikin dokokinka na adalci ne sun tabbata har abada.

SHIN

161 Sarakuna suna tsananta mani ba dalili; zuciya ta ta karai, gama ina jin tsoron karya maganarka. 162 Ina farinciki da maganarka kamar wanda ya sami ɗumbin ganima. 163 Ina ƙin ƙarairayi ina kuma wofintar dasu, amma ina ƙaunar shari'arka. 164 Ina yabon ka sau bakwai a rana sabili da dokokinka na adalci. 165 Masu ƙaunar shari'arka, suna da babbar salama; ba abin da zai sasu suyi tuntuɓe. 166 Ina jiran cetonka, Yahweh, ina kuma biyayya da dokokinka. 167 Ina aikata dokokinka tabbatattu, ina kuma ƙaunarsu ƙwarai. 168 Ina biyayya da umarninka da kuma dokokinka tabbatattu, gama kana sane da duk abin da nake yi.

TAV

169 Ka saurari kukana na neman taimako, Yahweh; ka bani fahimtar maganarka. 170 Bari roƙona ya zo gaba gare ka; ka taimake ni, kamar yadda ka alƙawarta a maganarka. 171 Bari leɓunana su cika da yabo, gama kana koya mani farillanka. 172 Bari harshena yayi waƙa akan maganarka, gama dukkan dokokinka dai-dai suke. 173 Bari hannunka ya taimake ni, gama na zaɓi umarnanka. 174 Ina marmarin cetonka, Yahweh, shari'arka ce farincikina. 175 Ka rayar dani don in yabe ka, bari dokokinka na adalci su taimake ni. 176 Nayi makuwa kamar ɓatacciyar tunkiya; ka nemi bawanka, gama ban manta da dokokinka ba.

Zabura 120

Waƙar takawa sama.

1 A cikin ƙuncina nayi kira ga Yahweh, ya kuma amsa mani. 2 Ka ƙwato raina, Yahweh, daga waɗanda ke ƙarya da leɓunansu da ruɗi da harsunansu. 3 Ta yaya zai hore ka, mene ne kuma zai ƙara yi maka, kai wanda ke da harshe na ƙarya? 4 Zai hore ka da kibiyoyin mayaƙi da aka wãsa bisa garwashin wutar ƙiraren itace. 5 Kaito na saboda ina zaune jim kaɗan cikin Meshek; Dã na zauna a rumfunan Keda. 6 Har dogon lokaci na zauna tare da waɗanda suka ƙi salama. 7 Ni domin salama nake, amma idan na yi magana, domin yaƙi suke.

Zabura 121

Waƙar takawa sama.

1 Zan ɗaga idanu na ga duwatsu. Daga ina taimakona zai zo? 2 Taimakona na zuwa daga Yahweh, wanda yayi sama da duniya. 3 Ba zai bar sawunka ya zãme ba; shi wanda ya ke kiyaye ka ba zai yi gyangyaɗi ba. 4 Duba, mai lura da Isra'ila ba zai taɓa gyangyaɗi ba ko barci. 5 Yahweh shi ne mai lura da kai; Yahweh shi ne inuwa a hannun damanka. 6 Rana ba zata cutar da kai ba da rana, ko kuma wata da daddare. 7 Yahweh zai kiyaye ka daga dukkan cutarwa, kuma zai kiyaye ranka. 8 Yahweh zai kiyaye ka cikin dukkan abin da kake yi yanzu da har abada abadin.

Zabura 122

Waƙar takawa sama, ta Dauda.

1 Nayi farinciki da suka ce mani, "Bari mu tafi gidan Yahweh." 2 Yerusalem, sawayenmu na tsaye cikin ƙofofinki! 3 Yerusalem, an gina ki birnin da aka yiwa shiri a hankali! 4 Kabilun suna tafiya Yerusalem - kabilun Yahweh - a matsayin shaida ga Isra'ila, su bada godiya ga sunan Yahweh. 5 An kafa kursiyoyin hukuncinsu, kursiyoyin gidan Dauda. 6 Kuyi addu'a domin salamar Yerusalem! "Bari masu ƙaunar ki su sami salama. 7 Bari salama ta kasance cikin katangogin dake kãre ki, bari kuma su sami salama cikin ƙarfafan wurin tsaronki." 8 Domin albarkacin 'yan'uwana da abokaina zan ce, "Bari salama ta kasance a cikin ki." 9 Domin albarkacin gidan Yahweh Allahnmu, zan biɗi alheri game dake.

Zabura 123

Waƙar takawa sama.

1 A gare ka na ɗaga idanuna, kai wanda kake bisa kursiyi a sammai. 2 Duba, kamar yadda idanun bãyi ke duban hannun ubangijinsu, kamar yadda idanun baiwa ke duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu ke duban Yahweh Allahnmu har sai ya nuna mana jinƙai. 3 Kayi mana jinƙai, Yahweh, kayi mana jinƙai, domin cike muke da wulaƙanci. 4 Mun ma fi cike da ba'ar masu ba'a da kuma renin masu fahariya.

Zabura 124

Waƙar takawa sama, ta Dauda.

1 "Idan da ba don Yahweh yana gefenmu ba," bari Isra'ila suce yanzu, 2 "Idan da ba don Yahweh yana gefenmu ba sa'ad da mutane suka taso gãba da mu, 3 daga nan da sun haɗiye mu ɗungum da rai sa'ad da fushin su ya wo hauka gãba da mu. 4 Da ruwa ya share mu; igiyoyin da sun sha ƙarfinmu. 5 Daga nan haukan ruwayen da ya shanye mu." 6 Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda bai bari haƙoran sa suka yayyage mu ba. 7 Mun kucce kamar tsuntsu daga tarkon mafarauta; tarkon ya karye, mun kuma kucce. 8 Taimakonmu yana cikin Yahweh, wanda ya yi sama da ƙasa.

Zabura 125

Waƙar takawa sama.

1 Waɗanda suka sa dogararsu ga Yahweh suna kama da Tsaunin Sihiyona, marar jijjiguwa, mai dawwama har abada. 2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Yerusalem, haka Yahweh ya kewaye mutanensa yanzu da har abada. 3 Sandar mulkin mugunta ba za tayi mulki ba a ƙasar mai adalci. Idan ba haka ba mai adalci zai iya yin abin da ba dai-dai ba. 4 Kayi da kyau, Yahweh, ga waɗanda suke yi da kyau waɗanda kuma suke masu adalci a zukatansu. 5 Amma ga waɗanda suka kauce gefe ga karkatattun hanyoyinsu, Yahweh zai kawar dasu tare da masu aikata mugunta. Bari salama ta kasance a Isra'ila.

Zabura 126

Waƙar takawa sama.

1 Sa'ad da Yahweh ya maido da kadarorin Sihiyona, mun zama kamar masu mafarki. 2 Daga nan bakunanmu suka cika da dariya harsunanmu kuma da waƙa. Daga nan suka ce a tsakanin al'ummai, "Yahweh ya yi masu manyan abubuwa." 3 Yahweh ya yi mana manyan abubuwa; mun kuwa yi murna! 4 Ka maido da kadarorinmu, Yahweh, kamar rafuffukan Negeb. 5 Su waɗanda suka yi shuka cikin hawaye zasu yi girbi tare da sowace-sowacen farinciki. 6 Shi wanda ya fita da kuka, yana ɗauke da irin shuka, zai sake dawowa da sowace-sowacen farinciki, yana kawo dammunansa tare da shi.

Zabura 127

Waƙar takawa sama, ta Suleman.

1 Sai idan Yahweh ne ya gina gida, sun yi aikin banza, su waɗanda ke ginin. Sai idan Yahweh ne yayi tsaron birni, masu tsaron suna tsayawa tsaro a banza. 2 Aikin banza ne a gare ka ka tashi da wuri, ka dawo gida da latti, ko ka ci gurasar aiki tuƙuru, domin Yahweh yana biyan buƙatun masu ƙaunarsa yayin da suke barci. 3 Duba, 'ya'ya gãdo ne daga Yahweh, kuma ɗiyan mahaifa lada ne daga gare shi. 4 Kamar kibiyoyi a hannun mayaƙi, haka nan 'ya'yan ƙuruciyar mutum. 5 Yaya albarkar mutumin da yake da kwarinsa cike da su. Ba zai sha kunya ba sa'ad da ya fuskanci maƙiyansa a ƙofa.

Zabura 128

Waƙar takawa sama.

1 Mai albarka ne duk wanda ya girmama Yahweh, wanda ya ke tafiya cikin hanyoyinsa. 2 Abin da hannuwanka suka wadatar, zaka ji daɗin sa; zaka yi albarka da wadata. 3 Matarka zata zama kamar inabi mai bada 'ya'ya a cikin gidanka; 'ya'yanka zasu zama kamar itatuwan zaitun yayin da suka zauna kewaye da teburinka. 4 I, tabbas, mutumin zai zama mai albarka wanda ya ke girmama Yahweh. 5 Bari Yahweh ya albarkace ka daga Sihiyona; bari kaga wadatar Yerusalem dukkan kwanakin rayuwarka. 6 Bari ka rayu ka ga 'ya'yan 'ya'yanka. Bari salama ta kasance bisa Isra'ila.

Zabura 129

Waƙar takawa sama.

1 "Sau da yawa tun ƙuruciya ta suke kawo mani hari," bari Isra'ila yace. 2 "Sau da yawa tun ƙuruciya ta suke kawo mani hari, duk da haka ba su kayar dani ba. 3 Masu huɗa suna huɗa bisa bayana; sunyi kuyyoyinsu da tsawo. 4 Yahweh mai adalci ne; ya datse igiyoyin mai mugunta." 5 Bari dukkan su su sha kunya su kuma koma baya, su waɗanda suka ƙi jinin Sihiyona. 6 Bari su zama kamar ciyawar dake bisa rufin gida wadda ke yaushi kafin ta girma, 7 wadda ba zata cika hannun mai girbi ba ko ƙirjin mai ɗaure dammuna. 8 Bari waɗanda ke ratsawa su wuce kada su ce, "Bari albarkar Yahweh ta kasance a kan ka; mun albarkace ka a cikin sunan Yahweh."

Zabura 130

Waƙar takawa sama.

1 Daga zurfafa nayi kuka gare ka, Yahweh. 2 Ubangiji, ka ji murya ta; bari kunnuwanka su saurari roƙe-roƙe na domin jinƙai. 3 Idan kai, Yahweh, zaka kula da kurakurai, Ubangiji, wane ne zai iya tsayawa? 4 Amma akwai gafartawa tare da kai, saboda a girmama ka. 5 Nayi jira domin ka Yahweh, raina yana jira, kuma a cikin maganarsa nake da bege. 6 Raina yana jira domin Ubangiji fiye da yadda masu tsaro ke jira domin safiya. 7 Isra'ila, kuyi bege cikin Yahweh. Yahweh yana cike da jinƙai, kuma yana da nufin gafartawa sosai. 8 Shi ne wanda zai fanshi Isra'ila daga dukkan zunubansa.

Zabura 131

Waƙar takawa sama; ta Dauda.

1 Yahweh, zuciyata ba tayi fahariya ba ko idanuna suyi tsauri. Bani da manyan bege domin kaina ko in dami kaina da abubuwan da suka sha kaina. 2 Tabbas na tsaida kuma na tausar da raina; kamar ɗan da aka yaye tare da mahaifiyarsa, raina a ciki na kamar ɗan yaye ya ke. 3 Isra'ila, kasa bege cikin Yahweh yanzu da har abada.

Zabura 132

Waƙar takawa sama.

1 Yahweh, albarkacin Dauda ka tuna da dukkan ƙuncinsa. 2 Ka tuna da yadda ya rantse wa Yahweh, yadda yayi wa'adi ga Mai Iko Dukka na Yakubu. 3 Yace, "Ba zan shiga gidana ba ko in kwanta a kan gadona ba, 4 ba zan ba idanuna barci ba ko kuma in rintsa 5 sai na samawa Yahweh wuri, rumfar sujada domin Maɗaukaki na Yakubu." 6 Duba, munji haka a Ifrata; mun same shi a jejin Yayir. 7 Zamu shiga rumfar sujada ta Allah; zamu yi sujada a ƙafafunsa. 8 Tashi, Yahweh, zuwa wurin hutawarka, kai da akwatin alƙawarinka mai nuna ƙarfinka! 9 Bari firistocinka su suturta da adalci; bari amintattunka suyi ihu don murna. 10 Saboda bawanka Dauda, kada ka juya wa zaɓaɓɓen sarkinka baya. 11 Yahweh ya rantse da tabbatacciyen wa'adi ga Dauda, tabbataccen wa'adi da ba zai janye ba: "Zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyarka in sa shi bisa gadon sarautarka. 12 Idan 'ya'yanka sun yi biyayya da umarnina da kuma dokokin da zan koya masu, 'ya'yansu zasu zauna a gadon sarautarka har abada." 13 Hakika Yahweh ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa. 14 "Nan ne wurin hutawana har abada. Zan zauna a nan, gama ina marmarinta. 15 Zan albarkaceta da yalwar abin da take buƙata, zan ƙosar da matalautanta da abinci. 16 Zan suturta firistocinta da ceto, amintattunta zasu yi sowa da ƙarfi don murna. 17 Can zan sa ƙaho ya toho domin Dauda zan kuma kafa fitila domin zaɓaɓɓena. 18 Zan suturta maƙiyansa da kunya, amma a kansa kambinsa zai yi walƙiya."

Zabura 133

Waƙar takawa sama, ta Dauda.

1 Duba, yadda ya ke da kyau da kuma daɗi idan 'yan'uwa suka zauna tare! 2 Wannan yana kama da mai mai kyau a kai dake gangarowa zuwa gemu - gemun Haruna, yana kuma gangarowa har kan wuyar rigarsa. 3 Kamar raɓar Hermon da take fadowa bisa duwatsun Sihiyona. Gama a nan ne Yahweh ya umarta albarka - rai na har abada.

Zabura 134

Waƙar takawa sama.

1 Ku zo, ku albarkaci Yahweh, dukkanku bayin Yahweh, ku da kuke wa Yahweh hidima da dare a haikalinsa. 2 Ku ɗaga hannunwanku zuwa wuri mai tsarki ku albarkaci Yahweh. 3 Bari Yahweh ya albarkace ku daga Sihiyona, Shi da yayi sama da ƙasa.

Zabura 135

1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi sunan Yahweh. Ku yabe shi, ku barorin Yahweh, 2 ku da kuke tsayawa a cikin haikalinsa, cikin harabun gidan Allahnmu. 3 Ku yabi Yahweh, gama shi nagari ne; ku raira waƙoƙin yabo ga sunansa, gama yana da ƙyau a yi haka. 4 Gama Yahweh ya zaɓi Yakubu domin kansa, Isra'ila abin mallakarsa. 5 Na sani Yahweh mai girma ne, kuma Ubangijinmu yafi dukkan alloli. 6 Ko mene ne Yahweh ya ke marmari, yakan yi shi a cikin sama, da ƙasa, a cikin ruwaye da dukkan zurfafan tekuna. 7 Yakan kawo gizagizai daga nesa, yakan sa walƙiya da ruwan sama su taho tare, ya kuma fito da iska daga rumbunsa. 8 Ya kashe ɗan farin Masar, na mutum dana dabbobi. 9 Ya aika da alamu da al'ajibai a tsakiyarsu, Masar, gãba da Fir'auna da dukkan barorinsa. 10 Ya hari al'ummai da yawa ya kuma kashe manyan sarkuna, 11 Sihon sarkin Amoriyawa da Og sakin Bashan da dukkan mulkokin Kan'ana. 12 Ya ba mu ƙasarsu abin gãdo, gãdo ga Isra'ila mutanensa. 13 Sunanka, Yahweh, ya dawwama har abada; ka shahara, Yahweh, dawwamamme har tsararraki dukka. 14 Gama Yahweh zai kare mutanensa, yana juyayin barorinsa. 15 Allolin al'ummai azurfa ne da zinariya, aikin hannuwan mutane. 16 Waɗannan allolin suna da bakuna, amma ba su yin magana; suna da idanu, amma ba sa gani; 17 suna da kunnuwa, amma ba sa ji, babu kuma numfashi a bakunansu. 18 Waɗanda suka siffanta su kamar su suke, haka kuma wanda ya dogara gare su. 19 Zuriyar Isra'ila, ku albarkaci Yahweh; ku zuriyar Haruna, ku albarkaci Yahweh. 20 Ku zuriyar Lebi, ku albarkaci Yahweh; ku da kuke girmama Yahweh, ku albarci Yahweh. 21 Mai albarka ne Yahweh a cikin Sihiyona, shi wanda da ya ke zaune cikin Yerusalem. Ku yabi Yahweh.

Zabura 136

1 Oh, kuyi godiya ga Yahweh; gama nagari ne, gama alƙawarin amincisa ya dawwama har abada. 2 Oh, kuyi godiya ga Allahn alloli, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 3 Oh, ku yi godiya ga Ubangiji iyayengiji, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 4 Kuyi godiya ga wanda shi ƙaɗai ya ke manyan mu'ujizai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 5 ga shi wanda ta wurin hikima yayi sammai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 6 Ku yi godiya ga shi wanda ya shinfiɗa ƙasa da sama da ruwaye, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 7 ga shi wanda yayi manyan haske, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 8 Kuyi godiya ga wanda ya bada rana yayi mulkin yini, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 9 wata da taurari suyi mulki da dare, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 10 Kuyi godiya ga wanda ya karkashe 'ya'yan fari na Masar, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 11 ya fitar da Isra'ila daga tsakiyarsu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 12 da ƙarfin hannunsa ba janyewa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 13 Ku yi godiya ga wanda ya tsaga Tekun Iwa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 14 yasa Isra'ila suka wuce ta tsakiyarsa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 15 amma ya dulmayar da Fir'auna da rundunarsa cikin Tekun Iwa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 16 Kuyi godiya ga wanda ya bida mutanensa cikin jeji, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 17 ga shi wanda ya kashe manyan sarakuna, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 18 Kuyi godiya ga wanda ya kashe shahararrun sarakuna, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 19 Sihon sarkin Amoriyawa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 20 da Og sarkin Bashan, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 21 Kuyi godiya ga shi wanda ya bada ƙasarsu abin gado, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 22 abin gado ga Isra'ila bawansa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 23 ga wanda ya tuna damu ya kuma taimake mu cikin ƙasƙancinmu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 24 Kuyi godiya ga shi wanda ya bamu nasara bisa maƙiyanmu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada - 25 ga wanda ke bada abinci ga dukkan masu rai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada. 26 Oh, sai ku yi godiya ga Allah na sama, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.

Zabura 137

1 Muka zauna a bakin kogunan Babila muka yi ta kuka da muka tuna da Sihiyona. 2 Muka rataye garayunmu akan itatuwa. 3 A can waɗanda suka bautar damu suka roƙa muyi masu waƙoƙi, kuma waɗanda suka yi mana ba'a suka matsa mana muyi farinciki, suna cewa, "Ku raira mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona." 4 Ƙaƙa zamu raira waƙa kan Yahweh a baƙuwar ƙasa? 5 Idan na ƙyale tunawa dake, Yerusalem, bari hannun damana ya manta da iya kaɗa garaya. 6 Bari harshena ya manne a rufin bakina, idan na dena tunaninki, idan ban fi son Yerusalem da abin da nafi jin daɗi ba. 7 Ka tuna, Yahweh, abin da Idomawa suka yi a ranar da Yerusalem ta faɗi. Suka ce, "A ragargazata, a ragargazata har harsashenta." 8 ‌Ɗiyar Babila, an kusa hallaka ki - bari mutumin nan ya zama da albarka, ko ma wane ne wanda ya sãka maki domin abin da kika yi mana. 9 Bari mutumin nan ya sami albarka, duk wanda ya kwashe 'ya'yanki ƙanana ya fyaɗa su kan duwatsu.

Zabura 138

Zabura ta Dauda.

1 Zan yi maka godiya da dukkan zuciyata; a gaban alloli zan raira yabbai gare ka. 2 Zan rusuna ina fuskantar haikalinka mai tsarki in kuma bada godiya ga sunanka sabili da amincinka na alƙawarinka domin kuma amincewarka. Ka fifita maganarka da sunanka da muhimmanci fiye da komai. 3 A ranar dana kira ka, ka amsa mani; ka ƙarfafa ni ka bani karfin zuciya. 4 Dukkan sarakunan duniya zasu yi maka godiya, Yahweh, gama zasu ji maganganun bakinka. 5 Hakika, zasu raira waƙoƙi akan abubuwan da Yahweh yayi, gama ɗaukakar Yahweh mai girma ce. 6 Gama ko da ya ke Yahweh mafifici ne, duk da haka yana kula da masu kaɗaici, amma ya san masu girman kai tun daga nesa. 7 Koda ya ke ina tafiya a tsakiyar hatsari, zaka tsare raina; zaka miƙa hannunka gãba da hushin maƙiyana, hannun damanka zai cece ni. 8 Yahweh yana tare da ni har ƙarshe; alƙawarin amincinka, Yahweh, dawwamamme ne har abada. Kada ka yasar da waɗanda hannuwanka suka yi.

Zabura 139

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, ka jaraba ni, ka kuma sanni. 2 Ka san lokacin da zan zauna da lokacin da zan tashi; ka san tunanina tun daga nesa. 3 Kana lura da tafarkina da kwanciyata; hanyoyina sanannu ne dukka a gareka. 4 Gama kafin magana ta kasance a kan harshena, ka sani sarai. 5 Ka kewaye ni gaba da baya kuma ka ɗibiya hannunka a kaina. 6 Wannan sani ya fi ƙarfina ƙwarai; yayi mani zurfi, ba zan iya fahimtar sa ba. 7 Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan guje wa fuskarka? 8 Idan na hau cikin sammai, kana can; Idan na tafi na zauna cikin Lahira, to duba, kana can. 9 Idan nayi asubanci na tashi sama akan fukafukai na tafi na zauna can nesa a ƙurewar teku, 10 ko can ma hannunka zai bishe ni, hannun damanka zai riƙe ni. 11 Idan nace, "Hakika duhu zai rufe ni, haske kuma ya zama dare kewaye dani," 12 ko duhunma ba zai zama duhu a gare ka ba. Daren zai haskaka kamar rana, gama da duhu da haske duk ɗaya suke a gare ka. 13 Kai ka yi gaɓaɓuwan cikin cikina; kai ka siffanta ni a cikin mahaifiyata. 14 Zan yabe ka, gama an yini da ƙyan gaske. Raina ya tabbatar da wannan sosai. 15 ‌Ƙasusuwana ba a ɓoye suke ba gare ka sa'ad da aka siffanta ni a ɓoye, sa'ad da aka hallita ni a can cikin zurfin ƙasa. 16 Ka ganni a cikin mahaifa; dukkan kwanakin da an ƙaddara mani suna rubuce cikin littafinka tun kafin na farkon ya faru. 17 Tunaninka yana da daraja a guna, Allah! Tarinsu da yawa basu lisaftuwa. 18 Idan na yi ƙoƙarin ƙididdiga su, zasu fi yashi yawa. Sa'ad da na farka, ina tare da kai. 19 Dãma zaka kashe mugaye, ya Allah; ku rabu dani, ku 'yan ta'adda. 20 Suna yi maka tawaye suna aikata munafunci, maƙiyanka suna faɗar ƙarairayi. 21 Ba na ƙi waɗanda suka ƙi ka ba, Yahweh? Ba ina rena waɗanda suka tashi gãba da kai ba? 22 Na ƙi su fau-fau; sun zama maƙiyana. 23 Ka jaraba ni, ya Allah, ka san zuciyata; ka gwada ni ka san tunanina. 24 Ka duba ko akwai muguwar hanya a cikina, ka kuma bishe ni a madawwamiyar hanya.

Zabura 140

Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, ka cece ni daga mugaye; ka kiyaye ni daga mutane masu zafin rai. 2 Sukan shirya mugunta a zuciyarsu; sukan sa yaƙi kowacce rana. 3 Harsunansu suna sara kamar maciji; dafin kububuwa na leɓunansu. Selah 4 Ka tsare ni daga hannuwan mugaye, Yahweh; ka tsare ni daga mutane masu zafin rai waɗanda suka shirya su kada ni ƙasa. 5 Masu fariya sun ɗana mani tarko; sun baza taru; sun shirya mani tarko. Selah 6 Na cewa Yahweh, "Kai ne Allahna; ka kasa kunne ga koke-kokena na neman jinƙai. 7 Yahweh, Ubangijina, kai mai iko ne ka iya ceto na; kana kare kaina a lokacin yaƙi. 8 Yahweh, kada ka biya buƙatun mugaye; kada ka bari shirye-shiryensu yayi nasara. Selah 9 Waɗanda suka ɗaga kansu sun kewaye ni; bari makircin leɓunansu ya rufe su. 10 Bari garwashin wuta su afko masu; ka jefa su cikin wuta, cikin rami marar matuƙa, kada su ƙara tashi. 11 Kada mutane masu mugun harshe su sami kwanciyar rai a duniya; bari bala'i ya farauci ɗan ta'adda ya buge shi ya mutu. 12 Na sani Yahweh zai kyautata wa mai shan ƙunci a shari'a kuma zai yi adalci ga matalauci. 13 Hakika mutane masu adalci zasu bada godiya ga sunanka; mutanen dake yin gaskiya zasu kasance a gabanka.

Zabura 141

Zabura ta Dauda.

1 Yahweh, ina kuka gare ka; ka zo wurina da sauri. Ka saurare ni sa'ad da na kira ka. 2 Bari addu'ata ta zama kamar turare a gaban ka; bari tãda hannuwana sama ya zama kamar hadayar maraice. 3 Yahweh, kasa mai tsaro a bakina; ka kiyaye ƙofar leɓunana, 4 Kada ka bari zuciyata ta yi marmarin wani mugun abu ko in haɗa kai cikin ayyukan zunubi tare da mutanen dake aikata mugunta. Kada ma in ci wani kayan lashe-lashensu. 5 Bari adilin mutum ya buge ni; zai zamar mani alheri. Bari ya tsauta mani; zai zama kamar mai a kaina; bari kada in ƙi karɓar wannan. Amma addu'ata kullum gãba take da ayyukan muguntarsu. 6 Za a jefar da shugabanninsu daga kan duwatsu; zasu ji cewa maganganuna masu daɗi ne. 7 Tilas zasu ce, "Kamar yadda mutum yakan yi huɗa ya rugurguza ƙasa, haka suka warwatsar da ƙasusuwanmu a ƙofar Lahira." 8 Hakika idanuna suna kanka, Yahweh, Ubangiji; a cikinka zan fake; kar ka bar raina ba tsaro. 9 Ka tsare ni daga tarkunan da suka ɗana mani, daga tarkunan masu mugun aiki. 10 Bari mugaye su faɗa cikin tarkonsu ni kuwa in kubce.

Zabura 142

Salon waƙa ta Dauda, lokacin da ya ke cikin kogo; addu'a.

1 Da muryata nayi kuka domin neman taimako daga Yahweh; da muryata na roƙi Yahweh tagomashi. 2 Na zuba masa koke-kokena a gabansa; na gaya masa wahaluna. 3 Sa'ad da ruhuna ya raunana a cikina, ka san tafarkina. Sun ɗana ɓoyayyen tarko domina a hanyar da nake bi. 4 Na duba hannun damana sai na ga babu wanda ya kula dani. Ba mafita domina, ba wanda ya kula da rayuwata. 5 Na kira gare ka, Yahweh; nace, "Kai ne mafakata, rabona kuma a ƙasar rayayyu. 6 Ka kasa kunne ga kirana, gama an ƙasƙantar dani; ka cece ni daga masu tsananta mani, gama sun fi ƙarfi na, 7 Ka fitar da raina daga kurkuku domin in yi godiya ga sunanka. Masu adalci zasu tattaru kewaye dani domin ka yi mani alheri."

Zabura 143

Zabura ta Dauda.

1 Ka ji addu'ata, Yahweh; ka ji roƙona. Saboda amincinka da adalcinka, ka amsa mani! 2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari'a gama a gabanka babu mai adalci ko ɗaya. 3 Maƙiyina ya hari raina; ya ture ni ƙasa; ya sãni in zauna cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun-tuni. 4 Ruhuna ya karaya a cikina; babu sauran bege a raina. 5 Idan na tuna kwanakin dã; na kan yi bin-bini akan ayyukanka; ina tunani akan nasararka. 6 Na tada hannuwana zuwa gare ka cikin addu'a; raina yana da ƙishinka cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa. Selah 7 Ka amsa mani da wuri, Yahweh, saboda ruhuna ya some. Kada ka ɓoye mani fuskarka, domin kada in zama kamar masu gangarawa cikin rami. 8 Bari inji alƙawarinka na aminci da safe, gama na dogara gare ka. Ka nuna mani tafarkin da zan bi, gama nasa zuciyata a gare ka. 9 Ka cece ni daga maƙiyana, Yahweh; ina gudu gare ka domin in ɓoye. 10 Ka koya mani in aikata nufinka, gama kai ne Allahna. Bari Ruhunka mai kyau ya bishe ni cikin ƙasar da ake adalci. 11 Yahweh, sabili da sunanka, ka barni da rai; cikin adalcinka ka fitar da raina daga wahala. 12 Cikin alƙawarin amincinka ka datse maƙiyana kuma ka hallaka dukkan maƙiyan rayuwata, gama ni baranka ne.

Zabura 144

Zabura ta Dauda.

1 Mai albarka ne Yahweh, dutsena, wanda ya ke horar da hannuwana domin yaƙi da yatsuna domin faɗa. 2 Kai nawane mai amintaccen alƙawari da mafakata, kaine hasumiyata mai tsawo wanda ya ke ceto na, garkuwata wanda a cikinsa nake fakewa, shi ya ke sarayar da al'ummai ƙarƙashina. 3 Yahweh, wane ne mutum har da kake kula shi ko ɗan mutum da kake tunani a kansa? 4 Mutum kamar huci ya ke; kwanakinsa kamar inuwa mai wucewa ne. 5 Ka sa sararin sama ya tsage ka sabko ƙasa, Yahweh; ka taɓa duwatsu ka sa suyi hayaƙi. 6 Ka aika walƙiyar tsawa ka warwatsar da maƙiyana; ka harba kibanka ka kore su su sheƙa a ruɗe. 7 Ka miƙo hannunka daga sama; ka cece ni daga ɗumbin ruwaye; daga hannun baƙi. 8 Bakunansu suna faɗar ƙarairayi, komai kuma dake hannunsu sun samu ne daga rashin gaskiya. 9 Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah; akan garaya mai igiya goma zan raira maka yabo, 10 kai wanda ke bada ceto ga sarakai, wanda ya tsirar da Dauda bawanka daga mugun takobi. 11 Ka cece ni ka 'yantar dani daga hannun baƙi. Bakunansu suna faɗar ƙarairayi, a hannun damansu kuma akwai rashin gaskiya. 12 Bari 'ya'yanmu maza su zama kamar dashe-dashen da suka yi girma suka ƙosa a samartakarsu 'ya'yanmu mata kuma kamar sassaƙaƙƙun ginshiƙan fãda masu kyan fasali. 13 Bari rumbunanmu su cika da kowanne irin amfani, bari kuma tumakinmu su hayayyafa dubbai kan dubbai har sau goma a saura. 14 Sa'an nan shanunmu zasu haifi 'yan maruƙa da yawa. Ba wanda zai hudo ta katangunmu; baza a tafi bautar talala ba ko a ji koke-koke a tituna. 15 Masu albarka ne mutanen dake da waɗannan albarku; masu farinciki ne mutanen da Allahnsu shi ne Yahweh.

Zabura 145

Zabura ta yabo. Ta Dauda.

1 Zan ɗaukaka ka, ya Allah, Sarki; zan albarkaci sunanka har abada abadin. 2 Kowace rana zan albarkace ka; zan albarkaci sunanka har abada abadin. 3 Yahweh Mai Girma ne, ƙasaitarsa ta cancanci yabo; Girmansa ba ya bincikuwa. 4 Daga wata tsara zuwa wata tsara za a yabi ayyukanka kuma za a labarta manyan ayyukanka. 5 Zan yi bin-bini akan martabar ɗaukakarka da kuma ayyukanka masu ban mamaki. 6 Zasu yi magana akan ikon manya-manyan ayyukanka, ni kuwa zan yi shelar girmanka. 7 Zasu yi shelar ayyukanka nagari masu yawa, kuma zasu raira yabo akan adalcinka. 8 Yahweh mai alheri ne kuma mai jinƙai ne, mai jinkirin fushi amincinsa kuma cikin alƙawari ba iyaka. 9 Yahweh yana yi wa kowa kirki; jinƙansa na bisa dukkan aikin hannunsa. 10 Dukkan abubuwan da kayi zasu yi maka godiya, Yahweh; amintattunka zasu sa maka albarka. 11 Amintattunka zasu yi magana akan darajar mulkinka, zasu faɗi ikonka. 12 Zasu sanar da 'yan adam ayyukan Allah masu girma da kuma ɗaukakar darajar mulkinka. 13 Mulkinka, dawwamammen mulki ne, masarautarka ta dawwama har tsararraki dukka. 14 Yahweh yakan tallafa wa dukkan waɗanda suke faɗuwa ya kuma tãda dukkan waɗanda ke a wulaƙance. 15 Idanun kowa na jiranka; ka kan basu abincinsu a madai-daicin lokaci. 16 Ka kan buɗe hannuwanka ka biya buƙatun kowanne abu mai rai. 17 Yahweh mai adalci ne a dukkan tafarkunsa mai alheri ne a dukkan abin da ya ke yi. 18 Yahweh na kusa da dukkan waɗanda suke kira gareshi, ga dukkan waɗanda suke kiransa da amincewa. 19 Yana biyan buƙatun waɗanda suke girmama shi; yana jin kukansu sai kuma ya cece su. 20 Yahweh yana lura da dukkan waɗanda ke ƙaunarsa, amma zai hallaka duk mugaye. 21 Bakina zai furta yabon Yahweh; bari duk 'yan adam su albarkaci sunansa mai tsarki har abada abadin.

Zabura 146

1 Ka yabi Yahweh, Yabi Yahweh, ya raina. 2 Ina ba da yabo ga Yahweh a dukkan rayuwata; Zan raira yabo ga Allahna muddin ina raye. 3 Kada ka dogara ga sarakuna ko ga ɗan adam, waɗanda babu ceto gare su. 4 Sa'ad da ran mutum ya dena numfashi, sai ya koma turɓaya; a ranan nan shawarwarinsa zasu watse. 5 Mai albarka ne wanda mataimakinsa Allahn Yakubu ne, wanda begensa na cikin Yahweh Allahnsa. 6 Yahweh ne yayi sama da ƙasa, da teku, da dukkan abubuwan dake cikinsu; yana kiyaye gaskiya har abada. 7 Yana zartar da hukunci domin dukkan waɗanda ake zalumta kuma yana bada abinci ga mayunwata. Yahweh yakan 'yantar da ɗaurarru; 8 Yahweh yana ba makafi ganin gari; Yahweh yana tãda waɗanda an tanƙwaresu; Yahweh yana ƙaunar mutane masu aikata adalci. 9 Yahweh yana kãre bãƙin dake cikin ƙasa; yana agajin marayu da gwauraye, amma yana tsayayya da mugaye. 10 Yahweh zai yi mulki har abada, Allahnki, Sihiyona, domin dukkan tsararraki. Mu yabi Yahweh.

Zabura 147

1 Ku yabi Yahweh gama yana da kyau a raira yabo ga Allahnmu, yana da daɗi, ya dace a yi yabo. 2 Yahweh zai sake gina Yerusalem, zai sake tattaro warwatsatsun mutanen Isra'ila. 3 Yana warkar da masu karyayyar zuciya ya ɗaure raunukansu. 4 Yana ƙididdiga taurari, ya ba dukkansu sunaye. 5 Mai girma ne Ubangijinmu mai daraja a iko, saninsa ya zarce gaban aunawa. 6 Yahweh yana tãda waɗanda aka wulaƙantasu, yakan jawo miyagu ƙasa. 7 Ku raira waƙa ga Yahweh tare da godiya, mu raira yabbai ga Allahnmu da garaya. 8 Yakan rufe sammai da gizagizai ya shirya ruwan sama domin ƙasa, ya sa ciyayi su tsiro bisa duwatsu. 9 Yana ba dabbobi abincinsu da kuma 'ya'yan hankaki lokacinda suka yi kuka. 10 Ba ya jin daɗin ƙarfin doki, ba ya dogara ga ƙarfin mutum. 11 Yahweh yana jin daɗin waɗanda suke girmama shi, waɗanda suka kafa begensu akan amintaccen alƙawarinsa. 12 Ku yabi Yahweh, Yerusalem, ki yabi Allahnki, Sihiyona. 13 Gama yana ƙarfafa ƙarafun ƙofofinki, yana albarkatar 'ya'yanki a cikinku. 14 Yana kawo wadata cikin iyakar ƙasarki, yana ƙosar dake da kyakkyawar alkama. 15 Yana aika dokokinsa cikin duniya, dokokinsa yakan sheƙa da gudu. 16 Yakan yin ƙanƙara kamar ulu, ya baza dusarta kamar toka. 17 Yakan aiko da ƙanƙara kamar 'yan gutsittsire, wa zai iya jure sanyin da ya ke aikowa? 18 Ya aika dokokinsa ya narkar dasu, yakan sa iska ta buga su sai ruwan ya kwarara. 19 Ya yi shelar maganarsa ga Yakubu, farillansa da dokokinsa masu adalci ga Isra'ila. 20 Bai taɓa yin haka ba da wata al'umma, game da dokokinsa ma, basu san su ba. Mu yabi Yahweh.

Zabura 148

1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi Yahweh, ku dake cikin sammai; ku yabe shi, ku dake can tuddan sama. 2 Ku yabe shi, dukkanku mala'ikunsa; ku yabe shi, dukkan rundunarsa. 3 Ku yabe shi, rana da wata; ku yabe shi, dukkanku taurari masu ƙyalli. 4 Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi daku ruwayen dake sama da sarari. 5 Bari su yabi sunan Yahweh, gama ya bada umarnj, sai aka hallicesu. 6 Ya kuma kafasu har abada abadin; ya zartar da doka da bazata taɓa canzawa ba. 7 Ku yabe shi daga duniya, ku dodannin ruwa, da dukkan zurfafan teku, 8 wuta da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da giza-gizai, iskar hadari masu biyayya da maganarsa. 9 Ku yabe shi, duwatsu, da dukkan tuddai, itatuwa masu bada 'ya'ya, da duk itatuwan sida, 10 namun jeji da na gida, hallitu masu rarrafe da tsuntsaye. 11 Ku yabi Yahweh, sarakunan duniya da dukkan al'ummai, hakimai da dukkan masu mulki a duniya, 12 samari da 'yan mata, dattawa da yara. 13 Bari dukkansu su yabi sunan Yahweh, gama sunansa kaɗai aka fiffita, ɗaukakarsa kuma ta mamaye duniya da sammai. 14 Ya ɗaga ƙahon mutanensa domin yabo daga dukkan amintattunsa Isra'ilawa. Mutanen dake kurkusa da shi. Ku yabi Yahweh.

Zabura 149

1 Ku yabi Yahweh. Ku raira wa Yahweh sabuwar waƙa; ku raira yabonsa cikin taron amintattunsa. 2 Bari Isra'ila su yi murna cikin wannan daya yi su; bari mutanen Sihiyona su yi murna da sarkin sarkinsu. 3 Bari su yabi sunansa suna rawa; bari su raira masa yabo da bandiri da molo. 4 Gama Yahweh yana jin daɗin mutanensa; yana ɗaukaka masu tawali'u da cetonsa. 5 Bari masu tsoronsa su yi murna cikin nasara; bari su yi waƙa don murna bisa gadajensu. 6 Bari yabon Allah ya kasance a bakinsu da takkuba masu kaifi biyu a hannunsu 7 domin su maida martani kan al'ummai da ayyukan hukunci akan mutane. 8 Zasu ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi shugabanninsu kuma da baƙin ƙarfe. 9 Zasu aiwata hukunci da aka rubuta. Wannan ne zai zama ɗaukaka domin dukkan amintattunsa. Ku yabi Yahweh.

Zabura 150

1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi Allah cikin wurinsa mai tsarki; ku yabi ƙarfinsa cikin sammai. 2 Ku yabe shi saboda manyan ayyukansa; ku yabe shi saboda fiffikon girmansa. 3 Ku yabe shi da ƙarar ƙaho; ku yabe shi da garayu da molaye. 4 Ku yabe shi da bandiri da rawa; ku yabe shi da garayu da sarewa. 5 Ku yabe shi da kuge masu ƙara; ku yabe shi da kuge masu amo. 6 Bari dukkan abin dake da numfashi su yabi Yahweh. Ku yabi Yahweh.

Littafin Misalai
Littafin Misalai
Sura 1

1 Misalai na Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila. 2 Waɗannan misalai zasu koyar da hikima da koyarwa, zasu koyar da maganganun fasaha, 3 domin ka sami koyarwa domin ka rayu ta wurin yin abin da ke dai-dai, gaskiya da adalci. 4 Waɗannan misalai kuma zasu bada hikima ga marar sani, su kuma bada ilimi da fahimta ga matasa. 5 Bari mutane masu hikima su saurara su ƙaru a koyonsu, bari mutane masu ganewa su sami bishewa, 6 su kuma fahimci misalai, karin magana, da maganganun mutane masu hikima da kacici-kacicinsu. 7 Tsoron Yahweh shi ne mafarin ilimi - wawaye sukan rena hikima da koyarwa.‌ 8 Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, kada kuma ka watsar da dokokin mahaifiyarka; 9 zasu zamar maka rawani cike da alheri a kanka da abubuwan ratayawa masu kyau a wuyanka. 10 ‌Ɗana, idan masu zunubi suka jarabce ka zuwa cikin zunubinsu, kada ka bi su. 11 Idan suka ce, "Ka zo tare da mu, bari mu yi fakon jinin, bari mu yi kwanto mu kai farmaƙi ga mutane marasa laifi ba tare da dalili ba. 12 Bari mu haɗiye su da rai, kamar yadda Lahira take ɗauke waɗanda ke lafiyayyu, ta maishe su kamar waɗanda suka faɗa cikin rami. 13 Zamu sami abubuwa iri iri masu daraja; zamu cika gidajenmu da ganimar da muka sato gun waɗansu. 14 Ka haɗa kai da mu; zamu kasance dukka da ma'aji guda tare." 15 ‌Ɗana, kada ka bi wannan hanyar tare da su; kada ka yarda ƙafarka ta bi wajen da suke tafiya; 16 ƙafafunsu suna gudu garin yin mugunta suna hanzari su zubda jini. 17 Gama ba amfani a kafa wa tsuntsu tarko a idanunsa. 18 Waɗannan mutane jininsu ne suke kafa wa tarko - suna kwanto ne su kama rayukansu. 19 Haka kuma duk hanyoyin wanda ya sami arziƙi ta rashin adalci; ƙazamar riba takan ɗauke rayukan waɗanda suka riƙe ta kam-kam. 20 Hikima tana kuka da ƙarfi a tituna, tana ɗaga murya a dandali; 21 a karafku da ake hayaniya tana kururuwa, a ƙofofin birane tana magana, 22 "Har yaushe, ku mutane marasa ganewa, zaku ƙaunaci rashin ganewa? Har yaushe, ku masu ba'a, zaku ci gaba da jin daɗin ba'a, kuma har yaushe, ku wawaye zaku ƙi ilimi? 23 Ku kasa kunne ga tsautawa ta; zan faɗa maku tunanina; Zan sanar maku da maganganuna. 24 Na yi kira, amma kuka ƙi ku saurara; na miƙa maku hannuna, amma ba wanda ya kula. 25 Amma duk kun yi watsi da koyarwata ba ku saurara da gyaran da na yi maku ba. 26 Zan yi dariya sa'ad da masifa ta zo maku, zan yi maku ba'a sa'ad da razana ta zo - 27 lokacin da abin da kuke jin tsoro ya zo kamar hadari kuma bala'i ya auko kanku kamar guguwa, lokacin da azaba da damuwa suka sauko bisa kanku. 28 Sa'an nan zasu kira ni, ba zan kuma amsa ba; zasu kira ni da himma, amma ba zasu same ni ba. 29 Domin sun ƙi ilimi, kuma ba su zaɓi tsoron Yahweh ba, 30 ba zasu bi koyarwata ba, kuma suka rena dukkan gyaran kuskurensu da na yi masu. 31 Zasu ci 'ya'yan hanyoyinsu, da kuma 'ya'yan shirye shiryensu zasu ƙoshi. 32 Domin a kan kashe dolaye lokacin da suka bar tafarki, wautar wawaye ta rashin kulawa zata hallaka su. 33 Amma dukkan wanda ya kasa kunne gare ni zai zauna lafiya, zai huta a tsare babu tsoron masifa."

Sura 2

1 ‌Ɗana, idan ka karɓi zantattukana kuma ka ajiye dokokina tare da kai kamar abu mai tamani, 2 ka sa kunnenka ya maida hankali ga hikima kuma ka bada zuciyarka ga fahimta. 3 Idan ka ƙwala kira domin fahimta ka ɗaga murya dominta, 4 idan ka nemeta kamar yadda zaka nemi azurfa ka kuma biɗi fahimta kamar yadda zaka biɗi ɓoyayyiyar dukiya, 5 sa'an nan zaka san tsoron Yahweh zaka kuma sami sanin Allah. 6 domin Yahweh yana bada hikima, daga bakinsa ilimi da fahimta ke fitowa. 7 Yana tanada sahihiyar hikima domin waɗanda suka gamshe shi, kuma garkuwa ne ga waɗanda suke da aminci, 8 yana tsaron tafarkun adalci zai kuma kiyaye hanyoyin waɗanda suke bin sa da aminci. 9 Sa'an nan ne zaka fahimci abin da ke da adalci, da, gaskiya, da kowanne tafarki mai kyau. 10 Gama hikima zata shiga cikin zuciyarka, ilimi kuma zai ji wa ranka daɗi. 11 Hankali zai lura da kai, fahimta kuma zata kiyaye ka. 12 Zasu cece ka daga hanyar mugunta, daga kuma masu faɗar abubuwan saɓo, 13 waɗanda suka yi watsi da tafarkun gaskiya suna tafiya a hanyoyin duhu. 14 Suna farinciki sa'ad da suke yin mugunta, suna jin daɗi cikin aikata mugunta iri-iri. 15 Suna bin karkatattun tafarku, suna amfani da ruɗu sun ɓoye manufarsu. 16 Hikima da sanin dai-dai zasu cece ka daga mace mazinaciya, daga mace mai ƙazantar rayuwa daga maganganunta na zaƙin baki. 17 Takan yashe da abokinta na ƙuruciya ta manta da alƙawarin Allahnta. 18 Gama gidanta na bishewa zuwa mutuwa hanyoyinta zasu bishe ka zuwa gun waɗanda ke cikin kabari. 19 Duk masu tafiya wurinta ba zasu sake dawowa ba kuma ba zasu sami tafarkun rai ba. 20 Saboda haka zaka yi tafiya a hanyar mutanen kirki ka kuma bi tafarkun adalan mutane. 21 Domin adalai zasu kafa mazauni a ƙasar, amintattu kuma za a barsu a cikinta. 22 Amma za a datse mugaye daga ƙasar, marasa bangaskiya kuma za a datse su daga ita.

Sura 3

1 ‌Ɗana kada ka manta da umarnaina ka riƙe koyarwata a cikin zuciyarka, 2 domin za su ƙara maka tsawon kwanaki da shekarun rayuwa za su kuma ƙara maka salama. 3 Kada ka bari alƙawarin aminci da dogara su taɓa barinka, ka ɗaura su tare a wuyanka, rubuta su a allon zuciyarka. 4 Sa'an nan zaka sami tagomashi da suna mai kyau a gaban Allah da mutum. 5 Ka dogara ga Yahweh da dukkan zuciyarka kada ka jingina ga taka fahimta; 6 cikin dukkan hanyoyinka ka san da shi, shi kuwa zai maida tafarkunka miƙaƙƙu. 7 Kada ka zama da hikima a naka idanu; ka ji tsoron Yahweh ka guji mugunta. 8 Za ta zamar maka warkaswa ga naman jikinka da wartsakewa ga jikinka. 9 Ka girmama Yahweh da dukiyarka da nunar fari na dukkan aikinka, 10 sai rumbunanka su cika kuma matatsar ruwan 'ya'yan inabinka zasu yi ambaliya, su cika da ruwan inabi. 11 ‌Ɗana, kada ka rena koyarwar Yahweh kuma kada ka ƙi kwaɓarsa, 12 gama Yahweh yana horon wanda ya ke ƙauna, kamar yadda mahaifi ya ke tarbiyantar da ɗansa wanda ya ke gamsarsa. 13 Mai albarka ne wanda ya sami hikima; ya kuma sami fahimta. 14 Ribar da ka samu daga hikima ta fi abin da azurfa zata bayar a bisani kuma ribarta tafi zinariya. 15 Hikima tafi duwatsu masu ƙawa daraja kuma dukkan abin da kake marmari ba za a gwada su da ita ba a tamani. 16 Tana da tsawon kwanaki cikin hannun damarta a cikin hannun hagunta akwai arziki da ɗaukaka. 17 Hanyoyinta hanyoyin alheri ne kuma dukkan tafarkunta na salama ne. 18 Itacen rai ce ga waɗanda suka kamata, waɗanda suka riƙe ta suna da farinciki. 19 Ta wurin hikima Yahweh ya kafa duniya, ta wurin fahimta ya shimfiɗa sammai. 20 Ta wurin iliminsa zurfafa suka buɗe kuma giza-gizai suka zubo da raɓarsu. 21 Ɗana, ka riƙe hukuncin gaskiya da sanin dai-dai kada ka ɗauke ido daga gare su. 22 Za su zama rai a rayuwarka da kayan ado na alheri da zaka rataya zagaye da wuyanka. 23 Sa'an nan zaka yi tafiya a hanyarka lafiya ƙafarka ba zata yi tuntuɓe ba; 24 sa'ad da ka kwanta, ba zaka ji tsoro ba; lokacin da ka kwanta, zaka yi barci mai daɗi. 25 Kada ka ji tsoron masifar da zata zo farat ɗaya ko hallakarwar da mugaye suka haddasa, sa'ad da ta zo, 26 domin Yahweh za ya kasance tare da kai ya tsare kafafunka daga faɗawa cikin tarko. 27 Kada ka janye daga yin alheri ga waɗanda suka cancanta, yayin da kake da ikon aikatawa. 28 Kada ka cewa maƙwabcinka, "Tafi ka sake dawowa, gobe zan baka," alhali kuwa da kuɗin tare da kai. 29 Kada ka shirya cutar da maƙwabcinka - wanda ya ke kusa da kai ya kuma amince da kai. 30 Kada ka yi jayayya da mutum ba dalili, sa'an nan bai yi komai ba don ya cuce ka. 31 Kada ka ji ƙyashin ɗan ta'addar mutum ko ka zaɓi hanyoyinsa. 32 Domin masu aikata mugunta abin ƙyama ne ga Yahweh, amma yana karɓar mutum mai adalci ya amince da shi. 33 La'anar Yahweh tana kan gidan mugun mutum, amma yana sa albarka a gidan adalan mutane. 34 Yakan yi wa masu ba'a ba'a, amma yakan bada jinƙansa ga mutane masu tawali'u. 35 Mutane masu hikima sukan gãji girmamawa, amma za a ɗauke wawaye cikin kunyarsu.

Sura 4

1 Ku kasa kunne, 'ya'ya maza, ga koyarwar mahaifinku, ku maida hankali, domin ku san ko mene ne fahimta. 2 Ina baku koyarwa mai kyau; kada ku yi banza da koyarwata. 3 Sa'ad da nake ɗan yaron mahaifina, ina cikin ƙuruciya kuma ni kaɗai ne a gun mahaifiyata, 4 ya koyar da ni ya ce mani, "Bari zuciyarka ta riƙe maganganuna da kirki; ka kiyaye dokokina ka rayu. 5 Ka sami hikima da fahimta; kada ka manta kuma kada kuma ka ƙi maganganun bakina; 6 kada ka ƙyale hikima zata tsare ka; ka ƙaunaceta zata kiyaye lafiyarka. 7 Hikima ita ce mafificin abu, saboda haka ka sami hikima ka sayar da duk mallaƙarka don ka sami fahimta. 8 Ka ƙaunaci hikima za ta girmamaka; zata girmama ka sa'ad da ka rungume ta. 9 Zata ɗaura maka rawanin girmamawa a kanka; zata ba ka kambi mai kyau." 10 Ka kasa kunne, ɗana, ka maida hankali ga maganganuna, zaka kuma sami shekaru da yawa a cikin rayuwarka. 11 Ina nuna maka hanyoyin hikima; ina bishe ka a miƙaƙƙun tafarku. 12 Sa'ad da kake tafiya, ba wanda zai tsaya a hanyarka in kana gudu, ba zaka yi tuntuɓe ba. 13 Ka riƙe koyarwa, kada ka barta ta kubce; ka tsare ta, gama ita ce ranka. 14 Kada ka bi tafarkin mugaye kuma kada ka bi hanyoyin masu aikata mugunta. 15 Ka kauce mata, kada ka bi ta kanta; juya daga gare ta ka bi wata hanyar. 16 Domin ba sa iya barci sai sun aikata mugunta kuma sukan rasa barci sai sun sa wani ya yi tuntuɓe. 17 Domin sukan ci abincin mugunta su sha ruwan inabin ta'addanci. 18 Amma tafarkin adalan mutane kamar fitowar rana ne da ke ta ƙara haskakawa; hasken yana ta ƙara girma har tsakiyar rana ta zo. 19 Hanyar mugu kamar duhu take - ba su san yadda take ba suke tuntuɓe a kai. 20 ‌Ɗana, ka maida hankali ga maganganuna; ka bada kunnuwanka ga faɗata. 21 Kada ka bari su guje wa idanunka; ka ajiye su a zuciyarka. 22 Gama maganata rai ne ga waɗanda suka same ta lafiya ce kuma ga dukkan jikinsu. 23 Ka kiyaye lafiyar zuciyarka ka tsare ta da himma, domin daga cikinta maɓuɓɓugar rai ke zubowa. 24 Ka kawar da alfasha nesa daga gare ka ka kuma kawar da ruɓaɓɓar magana nesa daga gare ka. 25 Bari idanunka su dubi gaba sosai ka kuma kafa ƙurawarka miƙe a gaban ka. 26 Ka yi wa ƙafarka tafarkin da ke dai-dai; sa'an nan ne dukkan hanyoyinka zasu zama lafiyayyu. 27 Kada ka juya zuwa dama ko hagu; ka juyar da ƙafafunka daga mugunta.

Sura 5

1 ‌Ɗana, ka maida hankali ga hikimata; ka kasa kunne ga fahimtata, 2 domin ka koyi sanin abin da ke dai-dai leɓunanka zasu tsare ilimi. 3 Domin leɓunan mace mazinaciya suna ɗiga da zuma kuma bakinta yafi mai tabshi, 4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar shuwaka, tana yanka kamar takobi mai kaifi. 5 Kafafunta suna gangarawa zuwa mutuwa sawunta yana tafiya har Lahira. 6 Ba ta tunani game da hanyar rayuwa. Sawayenta sun ratse daga hanya; ba ta san inda zata ba. 7 Yanzu dai, 'ya'yana maza, ku saurare ni; kada ku juya baya ga barin jin maganganun bakina. 8 Bari tafarkinku ya yi nesa da ita kuma kada ku je kusa da ƙofar gidanta. 9 Da haka ba zaka bada girmamawarka ga waɗansu ba ko shekarun rayuwarka ga mugun mutum ba; 10 bãƙi ba zasu cinye dukiyarka ba; abin da ka yi wahala ka samu ba zai tafi gidan bãƙi ba. 11 A ƙarshen rayuwarka zaka yi nishi sa'ad da jikinka zai lalace. 12 Zaka ce, "Ai kuwa na ƙi jinin umarni kuma zuciyata ta wofintar da kwaɓa! 13 Na ƙi yin biyayya da malamaina na kuma ƙi in saurari umarnansu. 14 Na kusa lalacewa gaba ɗaya a tsakiyar taro, a cikin tattaruwar mutane." 15 Ka sha ruwa a cikin randar da ke taka ka kuma sha ruwa mai gudana daga taka rijiyar. 16 Ko ya kamata maɓuɓɓugarka ta yi ambaliya ko'ina kuma rafuffukan ruwanka su kwarara a bainar jama'a? 17 Bari su zama naka kaɗai ba kuma domin bãƙin da ke tare da kai ba. 18 Bari maɓuɓɓugarka ta zama da albarka kuma bari ka yi farinciki da matar kuruciyarka, 19 gama ita ƙaunatacciyar barewa ce kuma kurciya cike da alheri. Bari nonnanta su ƙosar da kai koyaushe; bari ka bugu da ƙaunarta kowanne lokaci. 20 Don mene ne, ɗana, zaka shaƙu da mazinaciya; donme za ka rungumi nonnan karuwar mace? 21 Yahweh yana ganin dukkan abin da mutum ke yi yana kuma lura da dukkan tafarkun da ya ɗauka. 22 Zunuban mugun mutum zasu cafke shi; igiyoyin zunubinsa zasu riƙe shi kam-kam. 23 Zai mutu domin ya rasa umarni; an ɓadda shi ta wurin wautarsa mai girma.

Sura 6

1 ‌Ɗana, idan ka ɗauki lamunin bashin da makwabcinka ya ci, idan ka yi alƙawari domin bashin wani da baka san shi ba, 2 to ka kafa wa kanka tarko ta wurin alƙawarin da ka yi an kuma kama ka da maganganun bakinka. 3 Sa'ad da an kama ka ta wurin maganganunka, ka yi wannan ka ceci kanka, tunda ka faɗa hannun makwabcinka; ka tafi ka ƙasƙantar da kanka ka faɗi wa makwabcinka abin da ya faru. 4 Kada ka ba idonka barci ko gyangyaɗi. 5 Ka tsirar da ranka kamar barewa daga hannun mafarauci, kamar tsuntsuwa daga hannun maharbi. 6 Dubi tururuwa, kai ragon mutum, ka yi la'akari da hanyoyinta, ka yi hikima. 7 Ba ta da hafsa, shugaba, ko mai mulki, 8 duk da haka tana shirya abincinta da kaka kuma a lokacin girbi ta kan tanada abin da za ta ci. 9 Har yaushe zaka yi ta barci, kai ragon mutum? Yaushe zaka tashi daga barcinka?‌ 10 "Ɗ‌an barci kaɗan, ɗan gyangyaɗi kaɗan, ɗan naɗe hannuwa don a huta" - 11 sai talaucinka ya zo maka kamar ɗanfashi buƙatunka kuma kamar jarumi mai makami. 12 Wofin taliki - mugun mutum - yana rayuwa ne ta wuri karkata maganarsa, 13 yana ƙifci da idanunsa, yana nuni da tafin ƙafarsa yana nuni da yatsunsa. 14 Yana shirya mugunta da ruɗi a ransa; kullum yana haddasa rashin jituwa, 15 Saboda haka masifarsa zata auko masa farat ɗaya; ba zato za a karairaye shi ba damar warkewa. 16 Akwai abu shida da Yahweh yaƙi, har ma bakwai da ya ke ƙyamar su. 17 Idanun taliki mai girman kai, harshe mai faɗar ƙarairayi, hannaye masu zub da jinin mutane marasa laifi, 18 zuciya mai ƙago mugayen shirye-shirye, ƙafafu masu saurin gudu su je su yi mugunta, 19 mashaidi mai furta ƙarairayi yana shuka husuma a tsakanin 'yan'uwa. 20 ‌Ɗ‌ana, ka yi biyayya da umarnin mahaifinka kada kuma ka watsar da koyarwar mahaifiyarka. 21 Kullum ka ajiye su a zuciyarka; ka ɗaura su zagaye da wuyanka 22 Sa'ad da kake tafiya zasu bishe ka; sa'ad da kake barci, zasu tsare ka; sa'ad da ka farka, zasu koyar da kai. 23 Gama umarnai fitila ce, koyarwa kuma haske ne; tsautawa da ke zuwa daga koyarwa hanyoyin rai ne. 24 Zata kiyaye ka daga muguwar mace, daga lallausar maganganun muguwar mace. 25 Kada ka yi sha'awar kyanta a zuciyarka kuma kada ka bari ta cafke ka da girar idanunta. 26 Kwana da karuwa tsadarsa kamar na kuɗin ɗan curin gurasa ne, amma matar wani zaka biya diyya da ranka. 27 Mutum zai iya ɗaukar wuta a ƙirjinsa har da ba zata ƙona masa kayan jikinsa ba? 28 Ashe mutum zai iya tafiya bisa garwashin wuta mai zafi ba tare da ya ƙona ƙafafunsa ba? 29 To haka ya ke da mutumin da ya kwana da matar maƙwabcinsa; wanda ya kwana da ita ba zai kuɓuta daga hukunci ba. 30 Mutane ba zasu rena ɓarawo ba idan ya yi sata domin biyan buƙatar yunwar cikinsa. 31 Amma idan an kama shi, zai biya riɓi bakwai na abin da ya sata; dole ya sadaukar da dukkan abubuwa masu daraja da ke cikin gidansa. 32 Wanda ya yi zina ba shi da hankali; wanda ya yi ta yana hallakar da kansa. 33 Raunuka da kunya su ne sakaiyarsa kuma ƙasƙancinsa ba za a iya sharesu ba. 34 Gama kishi yakan sa mutum ya husata; ba zai nuna jinƙai ba; sa'ad da zai ɗauki fansarsa. 35 Ba zai karɓi wata fansa ba, kuma ba za iya ba da toshiya ba ko da an bashi kyautai da yawa.

Sura 7

1 ‌Ɗana, ka adana maganganuna ka kuma ajiye dokokina a cikinka. 2 Ka kiyaye dokokina ka rayu ka kiyaye koyarwata kamar ƙwayar idonka. 3 Ka ɗaura su a yatsun hannunka; ka rubata su a allon zuciyarka. 4 Ka ce da hikima, "Ke 'yar'uwata ce," kuma ka kira fahimi danginka, 5 domin ka kiyaye kanka daga mace mazinaciya, daga karuwar mace da maganganunta masu zaƙi. 6 Ta tagar ɗakina ina leƙe ta labule. 7 Sai na duba wasu dolayen mutane, sai na lura cikin samari wani matashi wanda bashi da hankali. 8 Saurayin ya gangara wani titi kusa da saƙonta, ya nufi wajen gidanta. 9 Da maraice, wajen yammaci a ranar nan, a lokacin dare da duhu. 10 A can wata mata ta gamu da shi, ta yi shigar karuwa, mai zuciyar wayo. 11 Tana magana da ƙarfi da iskanci; ƙafafunta basu zauna a gida ba. 12 Yanzu tana titi, an jima tana kasuwa, a kowanne saƙo takan jira ta yi kwanto. 13 Sai ta kama shi kuma ta sumbace shi, da fuska mai yaudara ta ce masa, 14 "Na yi baikona da salama yau, na cika wa'adina, 15 shi yasa na fito in sadu da kai, da himma in biɗi fuskarka, na kuma same ka. 16 Na baza shimfiɗu a kan gadona, lilin masu launuka daga Masar. 17 Na fesawa gadona miyor da alos da kirfa. 18 Ka zo, mu sha ƙaunarmu mu ƙoshi har safiya; bari mu ji daɗi sosai cikin ayyukan ƙauna. 19 Gama mijina ba ya cikin gidansa; ya yi tafiya mai nisa. 20 Ya ɗauki jakkar kuɗi tare da shi; zai dawo in wata ya raba." 21 Da maganganu masu yawa ta sa shi ya ratso; da daɗin bakinta tasa shi ya karkace. 22 Nan da nan ya bi ta kamar san da ake kai shi wurin yanka, kamar barewar da aka kama a tarko, 23 har sai da kibiya ta tsire shi har zuwa hantarsa. Yana kama da tsuntsun da ya ke gaggautawa ya faɗa tarko. Bai san cewa zai sadaukar da ransa ba ne. 24 Yanzu dai, ɗana, ka kasa kunne gare ni; ka maida hankali ga maganganun bakina. 25 Kada zuciyarka ta kauce zuwa tafarkunta; kada ka bari a ɓadda kai zuwa tafarkunta. 26 Ta sa mutane da yawa sun faɗi sokakku; kasassunta da suka mutu na da yawan gaske. 27 Gidanta yana kan tafarkun Lahira; suna gangarawa ne zuwa ɗakunan kwanan mutuwa mai baƙin duhu.

Sura 8

1 Ba hikima na ƙwala kira ba? Ba fahimta na ɗaga muryarta ba? 2 A kan tsaunukan dutse a gefen hanya, a mararrabar hanya, Hikima ta ɗauki matsayinta. 3 A gaban ƙofofi, inda ake shiga cikin birni, a ƙofofin shiga cikin birni, tana ƙwala kira. 4 A gare ku, ku mutane, nake kira; muryata domin 'yan adam. 5 Ku marasa azanci, ku koyi hikima; ku kuma da kuke wauta, dole ku sami zuciya mai fahimta. 6 Ku saurara, domin zan yi magana a kan mafifitan al'amura, kuma sa'ad da bakina ya buɗe zan faɗi madaidaitan al'amura. 7 Gama bakina yana faɗin gaskiya, mugunta kuma abin ƙyama ce ga leɓunana. 8 Dukkan maganganun bakina na adalci ne; a cikinsu ba murɗiya ko karkatarwa. 9 Dukkansu miƙaƙƙu ne ga mutum mai fahimta; maganganuna dai-dai ne ga wanda ya sami ilimi. 10 Ka sami koyarwata maimakon azurfa; ka sami ilimi maimakon zinariya tsantsa. 11 Domin hikima tafi duwatsu masu ƙawa, ba wata dukiya da ta kai ta daraja. 12 Ni Hikima ina zaune da Hankali; Na kuma mallaki ilimi da sansancewa. 13 Tsoron Yahweh shi ne ƙin jinin mugunta. Na ƙi girman kai da alfarma, da muguwar hanya, da gamtsin baki, ina ƙinsu. 14 Ina da shawara mai kyau; da sahihiyar hikima; ni mai gani ce; ƙarfi nawa ne. 15 Ta wuri na sarakai suke sarauta, kuma masu mulki suke tsara dokoki masu adalci. 16 Ta wurina mahukunta ke mulki, hakimai, da dukkan masu mulki da adalci. 17 Ina ƙaunar masu ƙauna ta, kuma dukkan masu biɗata da himma, suna samu na. 18 A guna akwai wadata da daraja, dawwamammar dukiya da adalci. 19 'Ya'yana sun fi zinariya, koma sahihiyar zinariya ce; amfanina ya fi azurfa da aka tãce. 20 Ina tafiya a hanyar adalci, cikin tsakiyar tafarkun adalci. 21 Sakamakon wannan, nakan sa masu ƙaunata su gaji wadata; nakan cika rumbunansu taf. 22 "Yahweh ya hallice ni tun farko, ayyukansa na farko a lokacin. 23 Tun zamanun dãdã da suka wuce aka yini - daga farko, tun farkon duniya. 24 Kafin tekuna su kasance, aka haife ni - kafin maɓuɓɓugai masu yawan ruwa. 25 Kafin kafawar duwatsu kuma kafin tuddai, aka haife ni. 26 An haife ni kafin Yahweh ya hallici duniya ko jeji, kafin ma ƙura ta farko a duniya. 27 Ina nan sa'ad da ya kafa sammai, sa'ad da ya zana alamar zobe a sararin zurfi. 28 Ina nan sa'ad da ya kafa giza-gizai a sama da sa'ad da maɓuɓɓugai cikin zurfi suka kafu. 29 Ina nan sa'ad da ya sa wa teku iyaka, domin kada ruwaye su yi ambaliya su ƙetare umarninsa, da sa'ad da aka dasa iyakar harsashin busasshiyar ƙasa. 30 Ina gefensa, kamar gwanin masassaƙi, ni abin farincikinsa ne rana bayan rana, ina farinciki a gabansa koyaushe. 31 Ina ta murna da dukkan duniyarsa, kuma farincikina game da 'yan adam ne. 32 Yanzu dai, 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, domin waɗanda suka kiyaye tafarkuna za a albarkace su. 33 Ku kasa kunne ga koyarwata ku zama da hikima; kada ku ƙi ta. 34 Wanda ya saurareni za a albarka ce shi. Zai yi ta tsaro a ƙofofina kowacce rana, yana ta jira a dogaran ƙofofina. 35 Gama duk wanda ya same ni, ya sami rai, zai kuma sami tagomashin Yahweh. 36 Amma wanda ya kãsa, yana cutar ransa ne; dukkan masu ƙina mutawa suke ƙauna."

Sura 9

1 Hikima ta gina gidanta; ta sassaƙa ginshiƙai bakwai daga duwatsu. 2 Ta yanka dabbobinta; ta gauraya ruwan inabinta; kuma ta shimfiɗa teburinta. 3 Ta aiki barorinta; tana kira daga wurare masu tsayi na birni, 4 "Wane ne dolo? Bari ya ratso nan!" Tana magana da wanda ba shi da hankali. 5 Kazo, ka ci abincina, kuma ka sha ruwan inabi da na gauraya. 6 Ka bar ayyukan dolonci ka rayu; ka bi tafarkin fahimta. 7 Duk wanda ya hori mai reni za a zage shi, kuma duk wanda ya kwaɓi mugun mutum zai sami zargi. 8 Kada ka tsauta wa mai renako, domin zai ƙi jininka; ka tsauta wa mutum mai hikima, zai ƙaunace ka. 9 Ka bada hikima ga mutum mai hikima, zai ƙara hikima sosai. Ka koya wa adalin mutum, zai ƙaru cikin koyonsa. 10 Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, kuma sanin Mai Tsarkin nan shi ne fahimta. 11 Ta wurina za a tsawanta kwanakinka, shekarun rayuwa za a ƙara maka su. 12 Idan kana da hikima, domin kanka kake da hikimar, idan ka yi renako, zaka ɗauka kai kaɗai." 13 Wawuyar mace mai jahilci ce; ba a iya koyar da ita kuma bata san komai ba. 14 Takan zauna a bakin ƙofarta, a wurare mafi tsayi a gari. 15 Tana kiran masu wucewa a tituna, ga waɗanda ke tafiya a miƙe a hanyarsu. 16 "Bari wani dolo ya ratso wurin," takan cewa dolaye. 17 "Ruwan da aka sata ya fi daɗi, kuma abincin sirri yana da daɗi. 18 Amma bai sani ba matattu na wajen, cewa gayyatattunta suna cikin zurfin Lahira.

Sura 10

1 Misalai na Suleman. ‌Ɗ‌a mai hikima yakan sa mahaifinsa ya yi farinciki amma wawan ɗa yana kawo wa mahaifiyarsa baƙinciki. 2 Dukiyar da aka tara da mugunta bata da amfani, amma aikata abu nagari zai tsare ka daga mutuwa. 3 Yahweh ba ya barin ran mutum mai adalci ya yunwata, amma yana kaɓar da kwaɗayin mugaye. 4 Hannun da ke da ƙiyuwa sa mutum ya talauce, amma hannun ma'aikacin mutum yakan ribato arziƙi. 5 ‌Ɗa mai hikima yakan tattara amfani da kaka, amma abin kunya ne ya yi barci da kaka. 6 Alheran Allah suna kan mutum mai adalci, amma bakin mugu yana cike da ta'addanci. 7 Mutum mai adalci ya kan sa masu tunawa da shi su ji daɗi, amma sunayen mugaye zasu lalace. 8 Mutane masu hankali suna karɓar umarni, amma wawa mai surutai zai lalace. 9 Mai rayuwa cikin adalci zai yi tafiya lafiya, amma wanda ya maida tafarkunsa na maguɗi, za a kama shi. 10 Mai ƙibce da ido yana kawo baƙinciki, amma wawa mai surutai za a kã da shi. 11 Bakin mutum mai adalci maɓuɓɓugar ruwan rai ne, amma bakin mugu yana rufe da ta'addanci. 12 ‌̀‌Ƙiyayya tana haddasa tashin hankali, amma ƙauna tana rufe dukkan laifofi. 13 Hikima tana kan leɓen mutum mai basira, amma bulala domin bayan wanda ba shi da hankali ne. 14 Mutane masu hikima suna tara ilimi, amma bakin wawa yana kawo hallakarwa kusa. 15 Wadatar mutum attajiri shi ne tsararren birninsa; talaucin matsiyaci shi ne hallakarsa. 16 Ladan mutum mai adalci yana kai ga rai; ribar mugaye takan kai su ga zunubi. 17 Akwai tafarkin rai domin wanda ya ke bin tarbiya, amma wanda ya ƙi kwaɓa ya bijire ne. 18 Kowanne ya ɓoye ƙiyayya yana da leɓunan ƙarya, wanda ya baza tsegumi wawa ne. 19 Sa'ad da akwai maganganu dayawa, ba a rasa zunubi, amma wanda ya ke lura da abin da ya ke faɗa mai hikima ne. 20 Harshen mutum mai adalci azurfa ne tsantsa; babu wani abin amfani a zuciyar mugu. 21 Leɓunan mutum mai adalci sukan amfani mutane da yawa, amma wawaye sukan mutu saboda da rashin hankalinsu. 22 Alheran Yahweh masu kyau sukan kawo wadata kuma ba ya sa cutarwa a ciki. 23 Mugunta abu ne da wawa ya ke jin daɗi yana kuma wasa da ita, amma hikima abu ne na jin daɗi ga mutum mai fahimi. 24 Abin da mugu ke jin tsoro zai auka masa, amma za a biya muraɗin adilai. 25 Mugaye kamar hadari mai wargajewa ne, sai kawai ka ga basu kuma, amma adalai ginshiƙi ne da ya dawwama har abada. 26 Kamar abu mai tsami a hakori koma kamar hayaƙi a idanu, haka ma rago ya ke ga waɗanda suka aike shi. 27 Tsoron Yahweh ya kan tsawonta rai, amma shekarun mugaye za a gajarta su. 28 Begen mutane adilai shi ne murnarsu, amma shekarun mutane mugaye zasu gajarce. 29 Hanyar Yahweh ta kan tsare aminci, amma hallaka ce domin mugaye. 30 Ba za a taɓa kawar da mutum mai adalci ba, amma mugu ba zai zauna a ƙasar ba. 31 Daga bakin adilin mutum 'ya'yan hikima suke fitowa, amma za a sare harshe mai gatse. 32 Leɓunan mutum mai adalci sun san karɓaɓɓiyar magana, amma bakin mugu, sun san abin cutarwa kawai.

Sura 11

1 Yahweh yana ƙin ma'aunai da ba na gaskiya ba, amma yana murna da madaidaicin nauyi. 2 Sa'ad da girmankai yazo, daga nan ƙasƙanci ke zuwa, amma tare da tawali'u hikima ke zuwa. 3 Mutanen kirki mutuncinsu ke bishe su, amma hanyoyin zamba kan hallaka maciya amana. 4 Dukiya ba komai ba ce a ranar hukunci, amma yin abin da ke dai-dai zai hana ka mutuwa. 5 Halin kirkin amintaccen mutum kansa hanyarsa ta zama a sawwaƙe, amma mugu zai faɗi saboda muguntarsu. 6 Halin kirki na waɗanda suke gamsar Allah kan kiyaye su lafiya, amma marasa aminci haɗamarsu ce takan zamar masu tarko. 7 Sa'ad da mugun mutum ya mutu, sa zuciyarsa takan lalace sa zuciyar kuma da ke kan ƙarfinsa takan ɓace. 8 Akan kiyaye adalin mutum daga wahala kuma takan aukawa mugu a maimako. 9 Marar tsoron Allah da bakinsa yakan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin hikima adalai sukan sami tsaro. 10 Sa'ad da adalan mutane suka azurta, birni yakan yi farinciki; sa'ad da mugu ya lalace, akwai sowa ta murna. 11 Ta wurin kyautai masu kyau na waɗanda ke farantawa Allah rai, birni yakan ƙasaita; amma ta wurin maganganun mugaye, birni yakan ɓarke ƙasa. 12 Mutumin da ke rena abokinsa bashi da tunani, amma mutum mai fahimta yakan yi shiru. 13 Duk mai yawon yin tsegumi yakan bayyana asirai, amma amintaccen mutum yakan rufe al'amarin. 14 Wurin da babu jagoranci cikin hikima al'umma takan faɗi, amma nasara takan zo ta wurin tuntuɓar mashawarta masu yawa. 15 Duk wanda ya ɗaukar wa bãƙo lamuni lallai shi zai cutu, amma wanda ya ƙi bayarwa ta wurin ɗaukar alƙawari ya kuɓuta. 16 Mace cike da alheri takan sami girmamawa, amma azzalumai na haɗamar dukiya. 17 Mutum mai taimako yakan amfanawa kansa, amma macuci kansa ya ke cuta. 18 Mugun mutum yakan kwanta ya sami ladansa, amma wanda ya shuka abin da ke dai-dai yakan girbi sakamakon gaskiya. 19 Mutum mai gaskiya wanda ya yi abin da ke dai-dai zai rayu, amma wanda ke bin mugunta zai mutu. 20 Yahweh yana ƙin waɗanda tunaninsu mugaye ne, amma yana murna ga waɗanda hanyoyinsu marasa aibu ne. 21 Ku tabbatar da wannan - mugun mutum ba zai tafi ba tare da hukunci ba, amma zuriyar mutane masu adalci zasu zauna lafiya. 22 Kome kyaun mace idan bata da tunani tana kama da zoben zinariya a hancin alade. 23 Abin da adalan mutane suke so yakan jawo abu mai kyau, amma mugayen mutane zasu sa begensu ga hukunci kaɗai. 24 Akwai mai warwatsawa - zai samu ma da yawa; wani kuma yakan riƙe abin da zai bayar - yakan talauce. 25 Mutum mai bayarwa zai azurta kuma wanda ya ke bada ruwa ga waɗansu zai sami ruwa domin kansa. 26 Mutane sukan la'anta mutumin da yaƙi sayar da hatsi, amma kyaututtuka masu kyau sukan zama kambi akan mutumin daya sayar da nasa. 27 Mai la'akarin neman abu mai kyau yana neman tagomashi, amma mai neman mugunta zai same ta. 28 Masu dogara ga dukiyarsu zasu faɗi, amma kamar ganye, haka adalan mutane zasu azurta. 29 Wanda ya jawo wa iyalin gidansa wahala zai gãji iska wawa kuma zai zama bawan mai hikima a zuciya. 30 Adalin mutum zai zama kamar itacen rai, amma tashin hankali ya kan ɗauke rayuka. 31 Duba! Adalin mutum yana karɓar abin da ya dace da shi; balle ma mugu da mai zunubi!

Sura 12

1 Duk mai son horo yana son ilimi, amma wanda ya ke ƙin yarda da gyara wawa ne. 2 Mutumin kirki yakan sami tagomashi a wurin Yahweh, amma yakan hukunta mutum mai shirya miyagun dabaru. 3 Mutum ba zai kafu ta wurin mugunta ba, amma ba za a tuge adalan mutane ba. 4 Mace mai tsabtar rai kambi ce ga mijinta, amma ita mai kawo kunya tana kama da cuta mai ruɓar da ƙasusuwansa. 5 Shirye-shiryen adali adalci ne, amma shawarar mugu yaudara ce. 6 Maganganun miyagun mutane su ne ayi kwanto a jira domin a sami zarafin yin kisa, amma maganganun adalai sukan cece su. 7 Miyagun mutane ana kaɓantar da su kuma sun tafi, amma gidan adalin mutum zai tsaya. 8 Akan yabi mutum bisa ga yawan hikimar da ya ke da ita, amma za a rena wanda ya ke tunanin mugunta. 9 Gara baka da wani muƙami mai muhimmanci - kawai kana matsayin bawa - da kayi fankamar kai wani ne amma baka da abinci. 10 Adalin mutum yakan kula da buƙatun dabbobinsa, amma ko tausayin mugu zalunci ne. 11 Wanda ya yi aiki a gonarsa zai sami isasshen abinci, amma duk mai bin ayyuka marasa ma'ana ba shi da tunani. 12 Mugun mutum yana marmarin abin da mugayen mutane suka sato daga wurin waɗansu, amma ribar adalai sukan zo daga gare su ne. 13 Maganar mugun mutum takan zamar masa tarko, amma adalin mutum yakan kuɓuta daga wahala. 14 Mutum zai ƙoshi da abubuwa masu kyau ta wurin amfanin maganganunsa, kamar yadda aikin hannuwansa zai sãka masa. 15 Hanyar wawa a ganinsa dai-dai ce, amma mutum mai hikima yakan saurari shawara. 16 Wawa yakan nuna fushinsa nan da nan, amma mai yin watsi da zagi yana da hikima. 17 Wanda ke faɗin gaskiya yana faɗin abin da ke dai-dai, amma mai shaidar zur na faɗin ƙarairayi. 18 Maganganun mai faɗin magana cikin garaje na kama da saran takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa. 19 Leɓuna masu faɗin gaskiya sukan tabbata har abada, amma harshe mai yin ƙarya na ɗan lokaci ne. 20 Akwai yaudara cikin zukatan masu shirin aikata mugunta, amma murna takan zo wa masu shawarar salama. 21 Ba cutar da zata sami adalin mutum, amma mugayen mutane suna cike da wahaloli. 22 Yahweh yana ƙin leɓunan masu faɗar ƙarya, amma masu zama cikin aminci abin murnarsa ne. 23 Mutum mai hikima yakan ɓoye abin da ya sani, amma zuciyar wawaye takan yi shelar wauta. 24 Hannun mai ƙwazo zai yi mulki, amma ragayen mutane za a sa su aikin dole. 25 Damuwa cikin zuciyar mutum takan nawaita masa, amma maganganu masu kyau sukan sa shi ya yi murna. 26 Adalin mutum jagora ne ga abokinsa, amma hanyar miyagu takan bauɗar da su. 27 Ragayen mutane ba zasu iya gasa naman farautarsu ba, amma mutum mai ƙwazo zai sami dukiya mai tamani. 28 Waɗanda suka yi tafiya a hanyar da ke dai-dai sukan sami rai a cikin tafarkinsa babu mutuwa.

Sura 13

1 ‌Ɗ‌a mai hikima yakan saurari koyarwar mahaifinsa, amma shaƙiyi ba zai saurari tsautawa ba. 2 Mutum zai ci moriyar abubuwa masu kyau ta wurin amfanin bakinsa, amma marmarin mayaudara ta'addanci ne. 3 Mai tsaron bakinsa yana kare ransa, amma wanda ya wage bakinsa zai hallaka kansa. 4 Raggayen mutane na marmarin samu, amma ba sa samun komai, amma begen mutane masu ƙwazo zai sami ƙosarwa. 5 Mutum mai adalci ya kan ƙi ƙarairayi, amma mugun mutum yakan maida kansa abin ƙyama, kuma yakan yi abin kunya. 6 Adalci yakan tsare kamilai a cikin tafarkinsu, amma mugunta ta kan juyar da waɗanda suka aikata zunubi. 7 Akwai wani mai azurta kansa, amma ba shi da komai sam, kuma akwai wanda ba ya ba kansa komai, duk da haka yana da wadata da gaske. 8 Fãnsar ran mai arzaki dukiyarsa ce, amma matalauci baya jin razanarwa. 9 Hasken adalan mutane yakan yi murna, amma fitilar miyagun mutane za a ɓice ta. 10 Girmankai husuma kaɗai ya ke kawowa, amma akwai hikima ga waɗanda ke karɓar shawara. 11 Wadata zata ragu idan hanyar samunta ta banza ce, amma wanda ya sami kuɗi ta wurin yin aiki da hannunsa zai sa kuɗinsa su ƙaru. 12 Sa'ad da aka dakatar da bege, zuciya takan karaya, amma samun abin da aka sa zuciya itacen rai ne. 13 Duk wanda ya rena umarni yana jawowa kansa hallaka, amma mai mutunta doka za a sãka masa. 14 Koyarwar mai hikima maɓulɓular rai ce, da zasu juyar da kai daga tarkunan mutuwa. 15 Tunani mai kyau kan jawo tagomashi, amma hanyar mai cin amana bata da iyaka. 16 Mutane masu hikima sukan yi aikinsu bisa ga ilimi a cikin kowacce shawara, amma wawa yakan bayyana wawancinsa. 17 Mugun ɗan saƙo yakan faɗa cikin damuwa, amma amintaccen wakili yakan kawo sasanci. 18 Wanda ya ƙi koyarwa zai sami talauci da kunya, amma girmamawa zata zo ga wanda ya koya ta wurin gyara. 19 Samun abin da aka daɗe ana sauraro da daɗi ya ke ga rai, amma wawaye na ƙin juyawa daga mugunta. 20 Ka yi tafiya da masu hikima zaka zama mai hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai hallaka 21 Bala'i na bin masu zunubi, amma adalan mutane za a saka masu da abu mai kyau. 22 Nagarin mutum yakan bar gãdo domin 'ya'yan 'ya'yansa, amma a kan ajiye dukiyar mai zunubi domin adalin mutum. 23 Gonar talaka da ba'a nomawa akwai abinci da yawa, amma rashin adalci yakan kawar da shi. 24 Wanda baya horon ɗansa yana ƙinsa, amma mai ƙaunar ɗansa yana kula ya hore shi. 25 Adalin mutum yakan ci har sai ya ƙosadda marmarinsa, amma cikin mugu koyaushe yunwa ya ke ji.

Sura 14

1 Mace mai hikima takan gina gidanta, amma wawar mace takan rushe shi da hannuwanta. 2 Wanda ya ke tafiya cikin gaskiya yana tsoron Yahweh, amma wanda ba shi da gaskiya yana rena shi. 3 Daga bakin wawa tsiron girman kansa ke fitowa, amma leɓunan masu hikima zasu tsare su. 4 Wurin da babu dabbobi kwamin ciyar da dabbobi yakan zama da tsabta, amma isasshen abinci yakan zo ta wurin ƙarfin bajimi. 5 Amintaccen mashaidi ba yayin ƙarya, amma mai shaidar zur ƙarairayi ya ke furtawa. 6 Mai ba'a yakan nemi hikima amma ba zai samu ba, amma ilimi yakan zo a sauƙaƙe ga wanda ya ke da fahimta. 7 Ka guje wa wawan mutum, domin ba zaka sami ilimi daga maganganunsa ba. 8 Hikimar mutum mai fahimta shi ne ya gane hanyarsa, amma wautar wawaye itace yaudara. 9 Wawaye sukan yi ba'a sa'ad da aka miƙa hadayar laifi, amma a kan raba tagomashi tsakanin kamilai. 10 Zuciya tasan ɓacin ranta bata raba murnarta da bãƙo. 11 Za a hallaka gidan mugayen mutane, amma rumfar masu adalci zata yi albarka. 12 Akwai hanya wadda take dai-dai ga ganin mutum, amma ƙarshenta takan kai ga mutuwa kaɗai. 13 Zuciya na iya dariya amma ta kuma kasance cikin damuwa murna kuma kan iya zama baƙinciki. 14 Marar aminci zai sami abin da ya dace da hanyoyinsa, amma nagarin mutum zai sami abin da ke nasa. 15 Marar wayo yakan gaskanta kowanne abu, amma mutum mai himma yakan yi tunani game da takawarsa. 16 Mutum mai hikima yakan ji tsoro kuma ya rabu da mugunta, amma wawa da gangan yakan yi banza da gargaɗi. 17 Mai saurin fushi yakan yi abubuwan wauta, kuma mutum mai tsara mugayen dabaru a na ƙinsa. 18 Marasa wayo sukan gãji wauta, amma mutane masu himma a na masu kambi da ilimi. 19 Mugayen mutane zasu russuna a gaban waɗanda ke nagari masu mugunta kuma zasu russuna a ƙofofin masu adalci. 20 Matalauci har abokan hurɗansa ƙinsa suke, amma masu arziki suna da abokai da yawa. 21 Wanda ya rena maƙwabcinsa zunubi ya ke yi, amma wanda ke taimakon matalauci mai albarka ne. 22 Masu shirin mugunta ba ratse hanya suke yi ba? Amma masu shirin yin alheri zasu karɓi rabon amintacciyen alƙawari da karɓuwa. 23 Ta wurin aiki tuƙuru a kan sami riba, amma wurin da taɗi ne kawai, talauci yakan zo. 24 Rawanin masu hikima dukiyarsu ce, amma wautar wawaye takan ƙara kawo masu wawanci. 25 Mashaidi mai gaskiya yakan ceci rayuka, amma mai shaidar zur yakan furta ƙarairayi. 26 Sa'ad da wani yaji tsoron Yahweh, shi ma yana da gabagaɗi a cikinsa; waɗannan abubuwa zasu zama kamar wurin fakewa mai ƙarfi domin 'ya'yan wannan mutumin. 27 Tsoron Yahweh maɓulɓula ne na rai, domin mutum ya iya juyawa daga tarkunan mutuwa. 28 ‌Ɗaukakar sarki na cikin yawan mutanensa, amma rashin mutane ke hallaka yarima. 29 Mutum mai jinkirin fushi na da ganewa mai yawa, amma mutum mai garaje na ɗaukaka wauta. 30 Natsattsiyar zuciya rai ce ga jiki, amma kishi yakan ruɓar da ƙasusuwa. 31 Wanda ya zalunci matalauta yana la'anta Mahaliccinsa, amma wanda ya nuna tagomashi ga mabuƙata yana girmama shi. 32 Akan kãda mugun mutum ƙasa ta wurin mugayen ayyukansa, amma mai adalci na da mafaka ko a cikin mutuwa. 33 Hikima takan zauna cikin zuciyar mai fahimta, amma ko cikin wawaye takan bayyana kanta. 34 Aikata adalci na ɗaukaka al'umma, amma zunubi abin kunya ne ga kowacce jama'a. 35 Tagomashin sarki na tare da baran da ke aiki da himma, amma fushinsa na kan wanda ke aikata abin kunya.

Sura 15

1 Mayar da magana da taushi kan juyar da hasala, amma magana mai zafi na tada fushi. 2 Harshen mutane masu hikima na yabon ilimi, amma bakin wawaye yana zuba wauta. 3 Idanun Yahweh suna ko'ina, suna lura da mugaye da nagari. 4 Harshe mai warkarwa Itacen rai ne, amma harshe mai yaudara na karya ruhu. 5 Wawa yakan ƙi kulawa da umarnin mahaifinsa, amma wanda ke koya ta wurin gyara mai himma ne. 6 A cikin gidan adalin mutum akwai dukiya mai yawa, amma dukiyar mugun mutum na ba shi damuwa. 7 Leɓunan mutane masu hikima sukan baza ilimi, amma ba haka zukatan wawaye suke ba. 8 Yahweh yana ƙin hadayun mugayen mutane, amma yana murna da addu'ar adalai. 9 Yahweh ya ƙi hanyar mugayen mutane, amma yana ƙaunar wanda ke bin abin da ke dai-dai. 10 Horo mai zafi na jiran duk wanda yabar hanyar da ke dai-dai shi kuma wanda yaƙi tsautawa zai mutu. 11 Lahira da hallakarwa a buɗe suke a gaban Yahweh; to balle zukatan "yan adam? 12 Mai ba'a baya son gyara; ba zai je wurin mai hikima ba. 13 Zuciya mai murna takan sa fuska tayi murmushi, amma ciwon zuciya yakan karyar da ruhu. 14 Zuciya mai basira takan nemi ilimi, amma bakin wawa naci daga wawanci. 15 Mutanen da ke shan tsanani suna cikin takaici dukkan kwanakin ransu, amma zuciya mai farinciki zata yi buki marar matuƙa. 16 Gwamma a samu kaɗan tare da tsoron Yahweh da samun dukiya da yawa cikin ruɗami. 17 Cin abinci tare da 'ya'yan itatuwa a wurin da akwai ƙauna ya fi cin ɗan maraƙi mai ƙiba tare da ƙiyayya. 18 Mutum mai zafin rai yakan tãda husuma, amma mai jinkirin fushi na kwantar da rigima. 19 Hanyar rago na kama da wurin da aka shinge ta da ƙayayuwa, amma hanyar adali lafiyayya ce. 20 ‌Ɗa mai hikima na kawo farinciki ga mahaifinsa, amma wawa yana rena mahaifiyarsa. 21 Daƙiƙai na murna da mutumin da ba shi da tunani, amma mai fahimta na tafiya a hanyar da ke dai-dai. 22 Wurin da babu shawara shirye-shirye kan tafi ba dai-dai ba, amma zasu yi nasara inda akwai mashawarta da yawa. 23 Mutum yakan sami farinciki sa'ad da ya bada amsar da ta dace; magana a lokacin da ya dace abu mai kyau ne! 24 Tafarkin rai na kaiwa sama-sama ga mutane masu himma, domin su tsere daga Lahira ta ƙarƙashi. 25 Yahweh yana rushe gidan mai girmankai, amma yana kiyaye dukiyar gwauruwa. 26 Yahweh yana ƙin tunanin mugayen mutane, amma kalmomi masu daɗi tsabtatattu ne. 27 ‌Ɗ‌an fashi na kawo masifa cikin iyalinsa, amma mai ƙin cin hanci zai rayu. 28 Zuciyar adalin mutum takan yi tunani kafin ta bada amsa, amma bakin mugayen mutane na zuba dukkan muguntarsa. 29 Yahweh na nesa da mugayen mutane, amma yana jin addu'ar adalan mutane. 30 Fuska mai fara'a takan kawo murna ga zuciya kuma labari mai daɗi lafiya ce ga jiki. 31 Idan ka maida hankali sa'ad da wani ke maka gyara yadda zaka yi rayuwa, zaka zauna cikin mutane masu hikima. 32 Wanda yaƙi horo rena kansa ya ke yi, amma mai sauraron gyara zai sami fahimta. 33 Tsoron Yahweh na koyar da hikima kuma tawali'u kuma na zuwa kafin girmamawa.

Sura 16

1 Shirye-shiryen zuciya na mutum ne, amma daga harshen Yahweh amsa ke fitowa. 2 Dukkan hanyoyin mutum suna da tsarki a ganinsa, amma Yahweh ke auna ruhohi. 3 Ka miƙa ayyukanka ga Yahweh shirye-shiryenka kuma zasu yi nasara. 4 Yahweh ya yi kowanne abu da dalili, har da mugu domin ranar wahala. 5 Yahweh na ƙin kowanne mutum mai zuciya mai fahariya, amma ku tabbatar da wannan, ba zasu kuɓuta daga hukunci ba. 6 Ɗa amintaccen alƙawari da gaskatawa akan gafarta zunubi ta wurin tsoron Yahweh mutane suke juyawa daga mugunta. 7 Lokacin da hanyoyin mutum suka gamshi Yahweh, zai sa maƙiyan mutumin su zauna lafiya da shi. 8 Gwamma kaɗan da abin da ke na adalci, da dukiya mai yawa da ke ta rashin adalci. 9 A cikin zuciya mutum ke shirya hanyarsa, amma Yahweh ke bida sawayensa. 10 Ƙudurori masu zurfi na a leɓunan sarki, kada bakinsa ya munafunci adalci. 11 Ma'aunai na gaskiya na zuwa ne daga Yahweh; dukkan ma'aunai cikin jakka ayyukansa ne. 12 Sa'ad da sarakuna suka yi mugayen abubuwa, wannan abin ƙi ne, gama kursiyi na kafuwa ne ta wurin yin abin da ke dai-dai. 13 Sarki na murna da leɓunan da ke faɗin abin da ke dai-dai kuma yana ƙaunar mai magana kaitsaye. 14 Fushin sarki saƙon mutuwa ne amma mutum mai hikima zai yi ƙoƙarin kwantar da fushinsa. 15 A cikin fara'ar sarki rai ne kuma tagomashinsa na kama da hadari mai kawo ruwan sama a lokacin bazara. 16 Yafi kyau a sami hikima fiye da zinariya. A sami fahimta yafi neman azurfa. 17 Babbar hanyar adalan mutane na kauce wa mugunta; wanda ke kãre ransa na kula da hanyarsa. 18 Girmankai na zuwa kafin hallaka kuma ruhun fahariya kafin fãɗuwa. 19 Ya fi kyau ka zama mai tawali'u cikin matalauta da ka zama mai raba ganima tare da masu girmankai. 20 Duk wanda ke tunani a kan abin da aka koya masa zai sami abin da ke mai kyau, waɗanda kuma suka dogara ga Yahweh zasu yi albarka. 21 Mai hikima cikin zuciya za a ce da shi mai sansancewa kuma zaƙin maganarsa na inganta iya koyarwa. 22 Fahimta maɓuɓɓugar rai ce ga wanda ya ke da ita, amma umarnin wawaye wawancinsu ne. 23 Zuciyar mutum mai hikima na bada basira ga bakinsa ta kuma ƙara ikon rinjaya ga leɓunansa. 24 Kalmomi masu daɗi saƙar zuma ce - abin daɗi ga rai warkarwar kuma ga ƙasusuwa. 25 Akwai hanyar da ke dai-dai ga mutum, amma ƙarshenta hanyar zuwa ga mutuwa ce. 26 Marmarin ma'aikaci na yi masa aiki; yunwarsa na tura shi gaba. 27 Mutum marar amfani na haƙo da damuwa maganarsa kuma na kama da wuta mai ƙuna. 28 Mugun mutum na tãda tashin hankali magulmaci kuma na raba abokanai na kurkusa. 29 Mutum mai ta'addanci na yin ƙarya ga maƙwabcinsa ya kuma gangara dashi ga tafarki da ba dai-dai ba. 30 Mutum mai kaɗa ido abubuwan mugunta ya ke ƙullawa; waɗanda ke tsayar da leɓuna zasu kawo mugunta. 31 Furfura kambin daraja ce; a na samunta ne ta yin rayuwar data dace. 32 Ya fi kyau ka zama mai jinkirin fushi da ka zama jarumi kuma wanda ke mulkin ruhunsa ya fi wanda ke mamaye birni. 33 Akan jefa ƙuri'a a cikin cinya, amma yanke shawara daga wurin Yahweh ne.

Sura 17

1 Ya fi a ci busasshiyar gurasa rai kwance da gida cike da shagali tare da tashin hankali. 2 Bawa mai hikima zai yi mulki bisa ɗan da ke aikata abin kunya zai kuma sami rabon gãdo kamar ɗaya daga cikin 'yan'uwa. 3 Maƙera da tanderun wuta domin tãce azurfa da zinariya ne; amma Yahweh ke tace zukata. 4 Mai aikata mugunta na kasa kunne ga mugayen leɓuna; maƙaryaci na sauraren harshe mai hallakarwa. 5 Duk wanda ya yi wa matalauci ba'a Mahallicinsa ya ke zagi kuma wanda ke farinciki da hasara ba zai tsira ba tare da hukunci ba. 6 Jikoki kambin tsofaffi ne iyaye kuma suna kawo daraja ga 'ya'yansu. 7 Yin magana da ƙwarewa bata da daɗi ga wawa; balle leɓuna masu faɗin ƙarya ba dai-dai bane da masu mulki. 8 Cin hanci na kama da dutsen dabo ga wanda ya bada shi; duk inda ya juya, nasara ya ke yi. 9 Duk wanda ke yafe laifi yana neman ƙauna, amma wanda ke maimaita batu yana raba abokai na kurkusa. 10 Tsautawa kan shiga da zurfi cikin mutumin da ke da fahimta fiye da naushe-naushe ɗari ga jikin wawa. 11 Mugun mutum tawaye kaɗai ya ke nema, don haka za a aika masa da mugun manzo ya yi gãba da shi. 12 Ya fi kyau ka gamu da kerkeci wadda aka kwashe mata 'ya'yanta da ka gamu da wawa cikin wawancinsa. 13 Idan wani ya maida mugunta maimakon alheri, mugunta ba zata taɓa rabuwa da gidansa ba. 14 Mafarin jayayya na kama da wanda ya saki ruwa ko'ina, don haka ka kaucewa jayayya kafin ta ɓarke ko'ina. 15 Mutumin da ya baratar da mugun mutum da mutumin da ya kãda adalin mutum - dukkansu abin ƙi ne ga Yahweh. 16 Donme wawa zai biya kuɗi ya koyi hikima, ganin cewa ba shi da iyawar koyon ta? 17 A koyaushe aboki yana nuna ƙaunarsa ɗan'uwa kuma an haife shi ne domin kwanakin damuwa. 18 Sai mutum marar hankali ke ɗaukar zaunannun alƙawarai domin basusuwan maƙwabcinsa. 19 Duk wanda ke ƙaunar rikici yana ƙaunar zunubi; wanda ya sa bakin ƙofarsa tayi yawan tsayi zai haifar da karyewar ƙashi. 20 Mutumin da ke da gurɓatacciyar zuciya ba ya ganin abin da ke dai-dai; wanda ke da mugun harshe na faɗawa cikin bala'i. 21 Mahaifin da ɗansa wawa ne yakan jawowa kansa ɓacin rai; mahaifin wawa kuma ba shi da farinciki. 22 Zuciya mai farinciki magani ne mai kyau, amma karyayyen ruhu kan busar da ƙasusuwa. 23 Mugun mutum yakan karɓi cin hanci a ɓoye domin ya karkatar da hanyoyin adalci. 24 Mai fahimta yakan sa fuskarsa wajen hikima, amma idanun wawa a kafe suke har ga ƙarshen duniya. 25 Wawan ɗa abin baƙinciki ne ga mahaifinsa abin haushi ne kuma ga matar da ta haife shi. 26 Haka kuma, ba dai-dai ba ne a hukunta mutum mai adalci; kuma ba shi da kyau a bulali mutane masu daraja masu mutunci. 27 Wanda ke da ilimi yakan yi amfani da kalmomi kaɗan wanda kuma ke da fahimta yana da natsuwa. 28 Har wawa idan ya yi shiru za a zaci shi mai hikima ne; sa'ad da bai yi magana ba, ana masa kallon mai basira.

Sura 18

1 Wanda ya ware kansa muradin kansa ya ke nema yana kuma jayayya da dukkan hukunci mai kyau. 2 Wawa bai da mu da ya fahimta ba, amma ya da mu kaɗai ya bayyana abin da ke cikin zuciyarsa. 3 Sa'ad da mugun mutum yazo, reni yakan zo tare da shi - tare da kunya da ƙasƙanci. 4 Maganganun bakin mutum ruwaye ne masu zurfi; maɓulɓular hikima rafi ne mai gudãna. 5 Ba dai-dai ba ne a nuna son kai ga mugun mutum, ko a hana adalci ga mutum mai adalci. 6 Maganar wawa takan jawo masa tsatsaguwa bakinsa kuma na gayyatar dũka. 7 Bakin wawa ke lalatar da shi da leɓunansa kuma ya ke ɗana wa kansa tarko. 8 Maganganun magulmaci na kãma da loma mai daɗi sukan kuma gangara zuwa can cikin ciki. 9 Haka kuma, wanda ya yi sanyi cikin aikinsa ɗan'uwa ne da wanda ke lalatarwa sosai. 10 Sunan Yahweh ƙaƙƙarfar hasumiya ne; adalan mutum yakan ruga cikinsa ya kuma tsira. 11 Attajiri na zaton dukiyarsa ce zata kare shi kamar garu mai tsayi da ke kewaye da birni. 12 Kafin faɗuwarsa zuciyar mutum takan kumbura, amma tawali'u yakan zo kafin girmamawa. 13 Wanda ya amsa kafin ya saurara - wauta ce a gare shi da kunya. 14 Ruhun mutum zai jure rashin lafiya, amma wa zai daure da karyayyen ruhu? 15 Zuciyar mai ƙwazo takan sami ilimi kunnen mai hikima yana biɗarsa. 16 Kyautar mutum zata bude masa hanya ta kuma kai shi gaban mutum mai muhimmanci. 17 Wanda ya fara gabatar da damuwarsa za a ga shi ne da gaskiya har sai abokin ƙara ya zo ya ƙalubalance shi. 18 Jefa ƙuri'a takan dai-daita jayayya ta raba tsakanin masu iko da ke jayayya. 19 Ɗan'uwan da aka ɓata da shi ya fi birni mai ƙarfi wuyar shiryawa, tantankawa kuma na kama da makaran kagara. 20 Cikin mutum zai ƙoshi da amfanin bakinsa; zai gamsu da amfanin leɓunansa. 21 Mutuwa da rai harshe ne ke sarrafasu, waɗanda ke ƙaunar harshe zasu ci amfaninsa. 22 Wanda ya sami mata abin kirki ya samu yana kuwa samun tagomashi daga wurin Yahweh. 23 Fakirin mutum yakan roƙi jinƙai, amma mawadaci na amsa magana da kaushi. 24 Wanda ke taƙamar yana da abokai da yawa, sukan yashe shi ta wurinsu, amma akwai abokin da ke zuwa kusa fiye da ɗan'uwa.

Sura 19

1 Gara matalaucin mutum mai tafiya cikin mutuncinsa da mai maganar mugunta gashi kuwa wawa. 2 Kuma, ba shi da kyau a kasance da marmari ba tare da sani ba kuma wanda ke gudu da sauri yakan ɓata hanya. 3 Wautar mutum takan ɓata ransa zuciyarsa kuma tana fushi gãba da Yahweh. 4 Arziki na ƙara abokai da yawa, amma matalauci a ware ya ke da abokansa. 5 Mai shaidar zur ba zai tserewa hukunci ba mai furta ƙarairayi ba zai kuɓuta ba. 6 Mutane da yawa zasu roƙi tagomashi daga wurin mutum mai kyauta kuma kowanne mutum aboki ne ga mai bada kyautai. 7 Dukkan 'yan'uwan matalauci na ƙinsa; balle ma abokansa waɗanda suka yi nisa da shi! Ya kira su, amma sun tafi. 8 Wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; wanda ya kiyaye fahimta zai sami abin da ya ke da kyau. 9 Mai shaidar zur ba zai tsere wa hukunci ba, amma mai furta ƙarairayi zai hallaka. 10 Bai dace da wawa ya zauna cikin daula ba - balle bawa ya yi mulki bisa 'ya'yan sarakuna. 11 Mutum mai sanin ya kamata yakan yi jinkirin fushi kuma daraja ce a gare shi ya ƙyale laifi. 12 Hasalar sarki na kama da rurin ɗan zaki, amma alherinsa na kama da raɓa a bisan ciyawa. 13 Wawan ɗa masifa ce ga mahaifinsa mace mai tankiya ɗiɗɗigar ruwa ne koyaushe. 14 Gida da dukiya ana gãdonsu daga iyaye, amma mace mai hankali daga wurin Yahweh take. 15 Ragonci kan jefa mutum cikin barci mai zurfi, amma wanda bai son aiki zai sha yunwa. 16 Wanda ya kiyaye doka ransa ya ke kiyayewa, amma mutumin da baya tunani game da al'amuransa zai mutu. 17 Duk mai jin tausayin fakirai yana bada rance ga Yahweh kuma zai sãke biyansa da abin da ya yi. 18 Ka hori ɗanka tun da sauran bege kuma kada ka ƙallafa ranka ga kashe shi. 19 Mutum mai zafin rai za ya ɗauki alhaki; idan ka cece shi, sai ka sake yi karo na biyu. 20 Ka saurari shawara ka karɓi koyarwa, domin ka iya zama mai hikima a ƙarshen rayuwarka. 21 Shirye-shirye masu yawa ke a cikin zuciyar mutum, amma manufar Yahweh ce zata tabbata. 22 Biyayya ce ya kamata mutum ya yi marmari kuma gara matalauci da maƙaryaci. 23 Girmama Yahweh yakan jagoranci mutane ga rai; wanda ke da shi zai gamsu ba abin da zai cutar da shi. 24 Rago yakan tsoma hannunsa cikin kwano; ba zai ko iya dawo da shi bakinsa ba. 25 Ka bugi mai ba'a, mutum marar wayau zai zama mai tattali; ka hori mai fahimta, zai kuma ƙaru da ilimi. 26 Wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne mai kawo kunya da zargi. 27 Idan ka daina jin koyarwa, ɗana, zaka ratse daga zantattukan ilimi. 28 Gurɓataccen mashaidi ya kan yi wa adalci ba'a bakin mugu yakan haɗiye laifi. 29 A kan shirya hallakarwa domin masu ba'a bulala kuma domin bayan wawaye.

Sura 20

1 Ruwan inabi mai ba'a ne barasa kuma mai tankiya ce; duk wanda ya kauce ta wurin sha marar hikima ne. 2 Tsoron sarki kamar tsoron ɗan zaki ne mai ruri; wanda yasa shi ya yi fushi zai rasa ransa. 3 Abin darajantawane ga kowanne mutum da ya kauce wa husuma, amma kowanne wawa yakan yi tsalle cikin jayayya. 4 Ragon mutum baya huɗa lokacin bazara; yakan nemi hatsi a lokacin girbi amma ba zai sami komai ba. 5 Shawara cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai zurfi, amma mutum mai fahimta zai jawo ta waje. 6 Mutane da yawa suna shelar nasu alheri, amma mutum mai aminci wa ya iya samunsa? 7 Mutum mai aminci wanda ke tafiya cikin mutuncinsa, 'ya'yansa da suka bishi zasu zama masu albarka. 8 Sarkin da ya zauna a kan dakalin shari'a ya ke aikin alƙali da idanunsa ya ke sheƙar da dukkan muguntar da ke gabansa. 9 Wane ne zai ce, "Na tsabtace zuciyata; Ni tsarkakakke ne daga zunubina"? 10 Ma'auni daban-daban da mudun da ba dai-dai ba - Yahweh yaƙi su dukka. 11 Ko matashi a kan sanshi ta wurin ayyukansa, ko aikinsa mai tsabta ne ko dai-dai kuma. 12 Kunne mai ji da ido mai gani - Yahweh ne ya yi su dukka biyun. 13 Kada kaso barci domin kada ka talauce; ka buɗe idanunka da haka zaka sami isasshen abinci ka ci. 14 "Ba kyau! Ba kyau!" inji mai saye, amma sa'ad da ya tafi sai fahariya ya ke yi. 15 Akwai zinariya da duwatsu masu tsada, amma leɓuna masu sani duwatsu ne masu tamani. 16 Wanda ya tsayawa bãƙo ka karɓi rigarsa, ka karɓi jingina kuma daga hannun wanda ya tsayawa mace marar kintsuwa. 17 Gurasar da aka samu ta wurin yaudarar ɗanɗano mai daɗi ce, amma daga baya bakinsa zai cika da tsakuwa. 18 Shirye-shirye sukan kahu ta wurin shawara da jagorancin mai hikima kaɗai zaka yi yaƙi. 19 Mai tsegumi yakan bayyana asirai domin haka kada kayi hurɗa tare da mutane masu yawan magana. 20 Idan mutum ya la'anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, za a ɓice fitilarsa a cikin tsakiyar duhu. 21 Gãdon da aka samu cikin gaggawa da farko amma a ƙarshe ba zai zama da kyau ba. 22 Kada ka ce, "Zan rama wannan muguntar!" Ka jira Yahweh zai kuɓutar da kai. 23 Yahweh yana ƙin ma'aunin algus mizanan rashin gaskiya basu da kyau. 24 Al'amuran mutum Yahweh ke shugabantarsu; ta yaya zai fahimci tafarkinsa? 25 Tarko ne ga mutum ya yi magana cikin sauri, "Wannan abu mai tsarki," daga nan ya fara tunanin ma'anar bayan ya yi wa'adinsa. 26 Sarki mai hikima yakan sheƙe miyagu ya juyar da turmin chasa a kansu. 27 Ruhun mutum fitilar Yahweh ce, tana bincike dukkan sassan ciki. 28 Alƙawarin aminci da gaskiya suna tsare sarki; kursiyinsa an kintsa shi da ƙauna. 29 ‌Ɗ‌aukakar samari ƙarfinsu ne darajar tsofaffin mutane kuma furfurarsu ce. 30 Buge buge waɗanda ke sa rauni sukan tsarkake mugunta dũka kuma yakan sa sassan cikin jiki su tsarkaka.

Sura 21

1 Zuciyar sarki kamar tafki ce mai gudanowa a cikin hannun Yahweh kuma yana juya shi a duk inda ya ga dama. 2 Kowanne mutum na ganin hanyarsa dai-dai ne a idanunsa, amma Yahweh ke auna zukata. 3 Aikata abin da ke dai-dai da gaskiya abin karɓa ne ga Yahweh fiye da hadaya; 4 Idanun masu fahariya da zuciya mai girman kai - fitilar mugaye - zunubi ne. 5 Shirye-shiryen mai himma na kai wa ne kaɗai ga wadata, amma duk mai yawan sauri zai kai ga talauci. 6 Tãra dukiya da harshe na ƙarya kamar tururi ne mai wucewa kuma tarko ne mai kashewa. 7 Ta'addancin masu mugunta zai kwashe su ya tafi, domin sun ƙi aikata abin da ke dai-dai. 8 Hanyar marar gaskiya karkatacciya ce, amma mai gaskiya na aikata abin da ke dai-dai. 9 Ya fiye a zauna laɓe a lungun ɗaki da a zauna ɗaki ɗaya da mace mai yawan faɗace-faɗace. 10 Ƙishin mugu na marmarin aikata mugunta; maƙwabtansa baya samun tagomashi a idanunsa. 11 Lokacin da aka yiwa mai ba'a horo, marar wayau na samun hikima, kuma idan aka bai wa hikima umarni, yana tara ilimi. 12 Mutum mai adalci na lura da gidan mutum mai mugunta; yana kawo masu mugunta zuwa ga bala'i. 13 Duk wanda ya hana wa kunnensa jin kukan matalauta, haka zai yi kuka, amma ba za a amsa masa ba. 14 Kyauta a ɓoye na kwantar da fushi kuma asirtacciyar kyauta na kauda hasala mai girma. 15 Lokacin da aka shar'anta gaskiya, tana kawo farincikin ga mutum mai adalci, amma tana kawo fargaba ga masu aikata mugunta. 16 Wanda ya kauce daga hanyar fahimta, za shi zauna a cikin taron matattu. 17 Duk wanda ke ƙaunar annashuwa za shi talauce; wanda ke ƙaunar ruwan inabi da mai ba zai wadata ba. 18 Mugun mutum abin fansa ne domin mai adalci, maci amana kuma abin fansa ne domin nagargarun mutane. 19 Ya fiye a zauna cikin hamada da a zauna tare da mata mai yawan faɗace-faɗace da fushi. 20 Zaɓaɓɓun dukiya da mai an ajiye su a mazaunin masu hikima, amma mutum marar wayo yana haɗiye su dukka. 21 Wanda ke aikata adalci yana kuma kyautatawa - wannan mutum ya sami rai, da adalci, da kuma ɗaukaka. 22 Mutum mai hikima na tsallake birnin masu iko, kuma yana rusar da ƙaƙƙarfan wurin da suka dogara da shi. 23 Duk wanda ya kiyaye bakinsa da harshensa yana tsare kansa ne daga wahala. 24 Mai girman kai da mutum mai fahariya - "Mai ba'a" ne sunansa - yana ayyukansa da girmankai na kumburi. 25 Sha'awar rago tana kashe shi, gama hannunsa na ƙin yin aiki. 26 Dukkan yini yana marmari yana ƙara marmari, amma mutum mai adalci yana bayarwa kuma baya hanawa. 27 Hadayar mugaye ƙazanta ce; ƙazantar na yawaita idan ya kawo su da miyagun manufofi. 28 Mai shaidar ƙarya zai hallaka, amma wanda ya yi sauraro za ya yi magana a dukkan lokaci. 29 Mugun mutum na mai da fuskarsa da tauri, amma mai adalci na dai-daita tafarkunsa. 30 Babu hikima, babu fahimta, kuma babu shawara da ke iya gãba da Yahweh. 31 Ana shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara ta Yahweh ce.

Sura 22

1 Zaɓen suna mai kyau ya fi wadata mai yawa kuma tagomashi ya fi azurfa da zinariya. 2 Wannan na faruwa da masu arziƙi da matalauta - Yahweh ne mahallicinsu dukka. 3 Mutum mai ƙwazo na hangen wahala ya kuma ɓoye kansa, amma marasa cikakkiyar kula na wucewa har ga wahala. 4 Ladan tawali'u da tsoron Yahweh arziƙi ne, da ɗaukaka, da kuma rai. 5 Ƙayayuwa da tarkuna suna kan hanyar bijirarru; duk wanda ya kiyaye ransa zai yi nisa da su. 6 Ka koya wa yaro hanyar da zai bi kuma idan ya manyanta ba zai kauce daga wannan umarnin ba. 7 Masu arziki ne ke mulkin matalauta kuma mai cin bashi bawa ne ga mai bada bashi. 8 Shi wanda ya shuka rashin adalci za shi girbi masifa kuma sandar hasalarsa zata ƙare. 9 Shi wanda ke da ido na hannu sake za shi yi albarka, gama yana raba gurasarsa da talakawa. 10 Ka kori mai ba'a, husuma zata fita; faɗace-faɗace da zage-zage zasu ƙare. 11 Shi wanda ke ƙaunar tsabtacciyar zuciya wanda kuma kalamansa masu alheri ne, za shi zama abokin sarki. 12 Idanun Yahweh na bisa ilimi, amma yana rusar da maganganun maci amana. 13 Ragon mutum ya ce, "Akwai zaki a kan hanya! Za a kashe ni a buɗaɗɗun filaye." 14 Bakin karuwa rami ne mai zurfi; Fushin Yahweh na gãba da duk wanda ya faɗi cikinta. 15 Ana samun wawanci a zuciyar ɗan yaro, amma sandar horo na korarsa da nisa. 16 Wanda ke zaluntar matalauta don ya tara dukiyarsa, ko ya baiwa mutane masu arziki, zai talauce. 17 Ka kusanto da kunnuwanka ga maganganun masu hikima ka kuma miƙa zuciyarka ga ilimina, 18 gama zata zamar maka abin daɗi, idan ka adana su cikinka, idan dukkansu suna shirye cikin leɓunanka. 19 Domin dogararka ta kasance cikin Yahweh, na koyar da su gare ka yau - lallai a gare ka. 20 Bana rubuta maka talatin maganganun na umarni da ilimi bane, 21 domin na koyar da kai waɗannan amintattun maganganu, dominn ka bayar da amintattun amsoshi ga waɗanda suka aike ka ba? 22 Kada ka cuci matalauci wai don shi matalauci ne, ko ka murƙushe mabuƙaci a bakin ƙofa, 23 gama Yahweh zai yi magana a madadin su, kuma zai ƙwace ran wadda ya cuce su. 24 Kada ka yi abokantaka da wanda fushi ke mulkinsa kuma kada ka yi tafiya da wanda ke hucin fushi, 25 in ba haka ba zaka koyi halayensa da haka zaka ɗana wa ranka tarko. 26 Kada ka zama wanda ke buga hannu don ɗaukar alƙawari, ko mai tsayawa a madadi na basussuka. 27 Idan ka rasa hanyar biya, me zai hana wani ya ɗauke gadonka daga gare ka? 28 Kada ka matsar da dutsen iyaka na dã wanda ubanninka suka sa. 29 Ko ka ga mutum ƙwararre ga aikinsa? Zai tsaya a gaban sarakuna; ba zai tsaya a gaban mutane marasa daraja ba.

Sura 23

1 A lokacin da ka zauna cin abinci da mai mulki, ka kula da kyau abin da a ka ajiye a gaban ka, 2 ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka idan fa kai wani ne mai yawan son cin abinci mai yawa. 3 Kada ka yi marmarin kayan kwaɗayinsa, gama abincin ƙarya ne. 4 Kada ka wahalar da kanka garin neman arziki; ka sami hikimar sanin lokacin da ya kamata ka huta. 5 Ko zaka bar idanuwanka bisa arziki? Zai watse, gama lallai za shi ɗauki fuka-fukai kamar gaggafa ya tashi sama. 6 Kada ka ci abincin wanda ke da mugun ido - kuma kada ka yi marmarin kayan kwaɗayinsa, 7 gama shi irin mutum ne da ke ƙirgen farashin abincin. "Ka ci ka sha!" yana ce maka, amma zuciyarsa bata tare da kai. 8 Za ka yi aman abin da ka ci kuma kalaman abokancin ka su tafi a banza. 9 Kada ka yi magana a gaban wawa, gama zai rena hikimar maganganunka. 10 Kada ka matsar da daɗaɗɗen dutsen iyaka ko ka shige gonar marayu, 11 gama mai Fansarsu na da ƙarfi kuma zai yi magana a madadin su gãba da kai. 12 Ka kafa zuciyar ka ga umarni kuma kunnuwanka ga maganganu na ilimi. 13 Kada ka ƙi yiwa yaro umarni, gama idan ka yi masa horo, ba zai mutu ba. 14 Kai ne ya zama dole ka doke shi da sanda ka kuma ceci ransa daga Lahira. 15 Ya ɗa na, idan zuciyarka na da hikima, da haka kuma zuciyata za ta yi murna; 16 can cikin zuciyata za ta yi farinciki lokacin da leɓunan ka suka furta abin da ke dai-dai. 17 Kada ka bar zuciyarka ta yi kishin masu zunubi, amma ka ci gaba da tsoron Yahweh dukkan rana. 18 Tabbas akwai gobe kuma ba za a datse begen ka ba. 19 Ka ji - kai! - ɗa na, ka sami hikima ka kuma bida zuciyarka a hanyar. 20 Kada ka yi abokantaka da mashaya, ko masu cin abinci fiye da kima, 21 gama da mashayi da marar horo ga ci suna zama matalauta kuma gyangyadi za shi suturce su da tsummokara. 22 Ka saurari mahaifin ka wanda ya haife ka kuma kada ka rena mahaifiyar ka sa'ad da ta tsufa. 23 Ka sayi gaskiya, amma kada ka sayar da ita; sayi hikima, da umarni, da kuma fahimta. 24 Mahaifin mutum mai adalci za shi yi farinciki, kuma duk wanda ya haifi yaro mai hikima za shi yi murna dominsa. 25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna kuma bari ita da ta haife ka ta yi farinciki. 26 ‌Ɗana, ka ba ni zuciyarka kuma bari idanuwanka su kula da hanyoyi na. 27 Gama karuwa rami ne mai zurfi, kuma mace mai gurɓataccen hali rijiya ce ƙuntacciya. 28 Tana kwanciya kamar ɗan fashi tana kuma barbaza yawan munafunci cikin 'yan adam. 29 Wa keda waiyo? Wa ke da kaito? Wa keda faɗace-faɗace? Wa ke ƙorafi? Wa keda raunuka babu dalili? Wa keda jajayen idanuwa? 30 Waɗanda suka daɗe da ruwan inabi, waɗanda suka gwada gaurayayyen ruwan inabi. 31 Kada ka dubi ruwan inabi sa'ad da ya yi ja, lokacin da ya ke kumfa a cikin moda yana kuma kwararowa ƙasa a hankali. 32 A ƙarshe zai yi sãra kamar maciji ya kuma yi harbi kamar kãsa. 33 Idanunka zasu ga baƙon abubuwa kuma zuciyarka za ta furta gurɓatattun abubuwa. 34 Za ka zama kamar wanda ke kwanciya bisa tekuna ko kwantawa bisa rufin jirgi. 35 "Sun buge ni," za ka ce. "amma ban ji ciwo ba. Sun buge ni, amma ban ji zafi ba. Har yaushe zan farka? Zan nemi wani abin shan."

Sura 24

1 Kada ka yi ƙyashin masu aikata mugunta, ko ka yi marmarin yin abokantaka da su, 2 domin zuciyarsu na ƙirƙiro da ta'addanci kuma leɓunansu na zancen rigima. 3 Ta wurin hikima a ke gina gida ta wurin fahimta a ke kafa shi. 4 Ta wurin ilimi a ke cika ɗakunan da dukkan dukiya masu tamani da daraja. 5 Jarumi mai hikima na da ƙarfi, kuma mutum mai ilimi na ƙara ƙarfinsa; 6 domin ta wurin shawara na hikima zaka yi yaƙi kuma cikin shawarwari masu yawa akwai nasara. 7 Hikima na da tsawo ga wawa; a bakin ƙofa ba ya buɗe bakinsa. 8 Akwai wani wanda ke shirin aikata mugunta - mutane na kiransa shugaban dabaru. 9 Wawan shiri zunubi ne kuma mutane na ƙyamar mai ba'a. 10 Idan ka yi sanyi sabili da tsoro a ranar wahala, to ƙarfinka ƙalilan ne. 11 Ka ƙwaci waɗanda aka ɗauke ga mutuwa ka kuma hana waɗanda ke gangarawa zuwa yanka. 12 Idan ka ce, "Duba, ba mu san da komai game da wannan ba," shi wanda ke auna zuciya ba ya fahimci abin da kake faɗa ba? Wanda ke tsaron ranka, ba yana sane da haka ba? Allah ba zai saka wa kowanne abin da ya cancance shi ba? 13 Ya ɗana, ka ci zuma domin yana da kyau, domin ɗigo-ɗigon sakar zuma na da zaƙi a bakin ka. 14 Haka hikima take ga ranka - Idan ka same ta, gobe tabbas ne kuma begen ka baza a katse shi ba. 15 Kada ka yi kwanto kamar mugun mutum wanda ke kai farmaki ga gidan mutum mai adalci. Kada ka lalatar da gidansa! 16 Gama mutum mai adalci na faɗuwa ƙasa sau bakwai ya tashi kuma, amma ana kãda mugayen mutane ƙasa da bala'i. 17 Kada ka yi farinciki sa'ad da maƙiyin ka ya faɗi kuma kada zuciyarka ta ji daɗi sa'ad da ya yi tuntuɓe, 18 domin Yahweh zai gani ya kuma bayyana rashin yardarsa ya kuma juyar da hasalarsa daga gare shi. 19 Kada ka da mu saboda masu aikata mugunta, kuma kada ka yi ƙyashin mugayen mutane, 20 gama mugun mutum ba shi da tabbaccin gobe kuma fitilar mugaye za ta ɓice. 21 Ka ji tsoron Yahweh, ka kuma ji tsoron sarki, ya ɗana; kada ka yi abokantaka da waɗanda suka tayar masu, 22 gama ba zato azaba zata auko kuma wa ya sani girman lalatar da zata zo daga dukkan su biyun? 23 Haka ma waɗannan maganganu ne na masu hikima. Nuna bambanci cikin shari'a ba abu ne mai kyau ba. 24 Duk wanda ya cewa mugun mutum, "Kai mutum mai adalci ne," mutane zasu la'anta shi al'ummai kuma zasu ƙi shi. 25 Amma waɗanda suka hori mai mugunta zasu sami jin daɗi kuma kyautai na alheri zasu zo gare su. 26 Wanda ya ba da amsa mai kyau yana bada sumba ga leɓuna. 27 Ka shirya aikinka na waje, ka kuma shirya wa kanka komai cikin fili; bayan haka, sai ka gina gidanka. 28 Kada ka zama shaida gãba da maƙwabcinka babu dalili kuma kada ka ruɗar da leɓunanka. 29 Kada ka ce, "Zan yi masa abin da ya yi mani; Zan sãka masa abin da ya yi." 30 na ratsa ta cikin filin rãgo, ta gonar inabi na mutumin da ba shi da hankali. 31 Duk ƙayayuwa sun rufe ko'ina, ƙasar ta cika da sarƙaƙiya, kuma ganuwarta ta dutse ta rushe. 32 Sai na gani na kuma yi lura da ita; na duba na kuma karɓi umarni. 33 Yin barci kaɗan, da ɗan gyangyaɗi, da ɗan naɗe-naɗen hannuwa domin hutu - 34 da haka talauci za shi saukar maka, kuma buƙatarka kamar soja mai makami.

Sura 25

1 Waɗannan ƙarin karin magana na Suleman ne, wanda mutanen Hezekiya, sarkin Yahuda suka kwafa. 2 ‌Ɗ‌aukaka ta Allah ce ya ɓoye zance, amma ɗaukakar sarakuna su bincike shi. 3 Kamar yadda sammai suke da tsayi duniya kuma tana da zurfi, haka zuciyar sarakuna sun wuce gaban ganuwa. 4 Ka sheƙe azurfa gwani kuma za shi yi amfani da azurfar ga aikinsa. 5 Haka ma, ka cire mugayen mutane daga gaban sarki kursiyinsa kuma zai kafu ta wurin aikata adalci. 6 Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki kada kuma ka zauna a mazaunin da aka shirya wa mutane masu daraja. 7 Ya fi kyau shi da kansa ya ce maka, "Hauro zuwa nan," da shi ya kunyatar da kai a gaban mutum mai daraja. Abin da ka yi shaidar sa, 8 kada ka yi saurin kawo shi ga shari'a. Gama me zaka yi a ƙarshe idan maƙwabcinka yasa ka cikin kunya? 9 Ka yi jayayya bisa matsala tsakaninka da maƙwabcinka da kansa kada kuma ka fallasa wani asirin, 10 domin kada wanda ya ji ka yasa ka ji kunya kuma mugun rohota a kanka da ba za a iya tsayarwa ba. 11 'Ya'yan itacen aful na zinariya da aka yi masu jerin azurfa kamar magana ce da aka yi ta dai-dai. 12 Zobe na zinariya ko sarƙar da aka yi ta da zinariya mai kyau horo ne na hikima ga kunnuwan mai sauraro. 13 Kamar yadda sanyin ƙanƙara ya ke lokacin girbi haka ɗan aike mai aminci ke ga waɗanda suka aike shi; yana dawo da ran shugabanninsa. 14 Giza-gizai da iska amma babu ruwan sama ne wanda ke fahariya da kyautar da bai bayar ba. 15 Cikin hakuri ake rinjayar mai mulki kuma harshe mai taushi na iya karya ƙashi. 16 Idan ka sami zuma, kada kayi masa shan fitar hankali - in ba haka ba, idan ka sha dayawa, za ka amayas. 17 Kada ka cika zuwa gidan maƙwabcinka, yana iya gajiya da kai ya kuma ƙi ka. 18 Mutumin da ya yi shaidar ƙarya bisa maƙwabcinsa na kama da kulkin da aka yi amfani da shi a yaƙi, ko takobi, ko wani mãshi mai tsini. 19 Mutum marar amincin daka amince da shi a lokacin wahala na kama da ruɓaɓɓen haƙora ko tafiya da gurguwar ƙafa. 20 Kamar mutumin da ya kwaɓe rigarsa a yanayi mai tsananin sanyi, ko zuba inabi bisa ainihin gawayi na soda, haka wanda ke yin waƙoƙi ga zuciya mai nauyi. 21 Idan makiyinka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci, idan kuma yana jin ƙishi, ba shi ruwa ya sha, 22 gama zaka tula masa tarin garwashin wuta a bisa kansa Yahweh kuma zai baka lada. 23 Kamar yadda iskar arewa ke kawo ruwan sama, haka take da harshen da ke faɗin asirai yana hadasar da fuskoki masu fushi. 24 Gara a zauna a saƙon rufin ɗaki da a zauna gida ɗaya tare da mace mai yawan faɗace-faɗace. 25 Kamar yadda ruwan sanyi ke ga wanda ke ƙishi, haka ya ke ga labari mai daɗi da ke zuwa daga ƙasa mai nisa. 26 Kamar ƙazantacciyar maɓuɓɓuga ko gurɓatacciyar rijiya haka ya ke da mutum adali da ya yi sanyi a gaban mugayen mutane. 27 Ba shi da kyau a sha zuma da yawa; wannan kamar neman yabo ne bisa yabo. 28 Mutumin da bashi da kamun kai na kama da birnin da ke a buɗe kuma bashi da ganuwa.

Sura 26

1 Kamar garin ƙanƙara a lokacin zafi ko ruwan sama a lokacin girbi, haka ma yabo bai dace ga wawa ba. 2 Kamar tsuntsayen da ke shawagi a sama basu sauka ba, haka la'annar da ba a cancance ta ba baza ta sauka ba. 3 Tsumagiya domin doki ne, linzami domin jaki sanda kuwa domin bayan wawaye. 4 Kada ka bada amsa ga wawa bisa ga wawancinsa, in ba haka ba za ka zama kamar sa. 5 Ka bada amsa ga wawa sai ka ƙara masa wawancinsa, domin kada ya ɗauki kansa wani mai hikima ne. 6 Duk wanda ya aika da saƙo ta hannun mai wauta na datse ƙafafunsa ne yana kuma shan ta'addanci. 7 Kamar ƙafafuwa shanyayyu da ke rataye da ƙasa haka karin magana ya ke a bakin wawaye. 8 Kamar a gwada harba dutse a majajjawa haka ya ke a bada yabo ga wawa. 9 Kamar ƙaya data shiga hannun mashayin giya haka karin magana a bakin wawaye. 10 Kamar maharbin da yaji wa dukkan waɗanda ke kewaye da shi raunuka haka wanda ya yi hayar wawa ko hayar duk mai wucewa kan hanya. 11 Kamar yadda kare ke komawa ga abin da ya amayas, haka wawan da ke maimaita wawancinsa. 12 Ko ka ga wani wanda ke ganin kansa mai hikima ne? Ko wawa na da bege fiye da shi. 13 Ragon mutum ya ce, "Akwai zaki a kan hanya! Akwai zaki a tsakanin buɗaɗɗun wurare!" 14 Kamar yadda ƙofa ke juyawa a ƙyaurenta, haka ragon mutum bisa gadonsa. 15 Ragon mutum na sa hannunsa cikin abinci duk da haka ba shi da ƙarfin ɗaga shi zuwa bakinsa. 16 Ragon mutum a ganin sa mai hikima ne shi fiye da mazaje bakwai da suka bada dalilai masu kyau. 17 Kamar wadda ya riƙe kunnuwan kare, haka mai wucewa kan hanya da ya yi fushi ga shawarwarin da basu shafe shi ba. 18 Kamar mahaukacin da ke harba kibiya mai wuta, 19 haka wanda ya ruɗi maƙwabcinsa yana cewa, "Ba wasa kawai nake yi ba?" 20 Don rashin itace, wuta ke mutuwa; kuma duk inda babu magulmaci faɗace-faɗace na ɗaukewa. 21 Kamar yadda gawayi ke ga wuta maici itace kuma ga wuta, haka ya ke da mutum mai faɗace-faɗace wurin kunna husuma. 22 Maganganun magulmaci suna kama da abinci mai daɗi; suna shigewa can cikin jiki. 23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfa haka baki mai zafi da kuma zuciya mai mugunta. 24 Shi da ke ƙin mutane yana ɓoye yadda ya ke ji da leɓunansa kuma yana ajiyar munafunci cikinsa. 25 Zai yi maganar alheri, amma kada ka yarda da shi, Gama akwai ƙazanta guda bakwai cikin zuciyarsa. 26 Ko da ya ke rashin gaskiya ya ɓoye ƙiyayyarsa, za a bayyana muguntarsa a cikin taro. 27 Duk wanda ya haƙa rami zai faɗa cikinsa kuma dutsen zai gangaro wa wanda ya turo shi. 28 Maƙaryacin harshe na ƙin mutanen da ya ke murƙushewa kuma baki mai fahariya na kawo hasara.

Sura 27

1 Kada ka yi alfahari game da gobe, domin baka san me ranar ke iya kawo wa ba. 2 Bari wani ne ya yabe ka amma ba naka bakin ba; baƙo amma ba naka leɓunan ba. 3 Ka yi la'akari da yadda dutse ke da nauyi da kuma nauyin yashi - cakuna ta wawa tafi dukkansu biyu nauyi. 4 Akwai rashin imanin hasala da kuma ambaliyar fushi, amma wa zai iya tsayawa a gaban kishi? 5 Tsautawa a fili ta fi nuna ƙauna a ɓoye. 6 Har yanzu akwai aminci a cutar da tazo daga aboki, amma maƙiyi na iya sumbatarka babu iyaka. 7 Mutumin da ya ci abinci ya ƙoshi zai ƙi ko da ma saƙar zuma ne, amma ga mutum mai yunwa, kowanne abu mai ɗaci na da zaƙi. 8 Kamar tsuntsun da ke yawo daga sheƙarsa haka mutumin da ya kauce daga inda ya ke zama. 9 Kayan ƙamshi da turare suna sa zuciya ta yi farinciki, amma daɗin aboki na zuwa ne daga amintacciyar shawararsa. 10 Kada ka yi banza da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan'uwanka a ranar wahalar ka. Maƙwabcin da ke kusa da kai ya fiye maka da ɗan'uwanka mai nisa da kai. 11 Ka zama mai hikima, ya ɗana, ka sa zuciyata ta yi farinciki; sa'an nan zan bada amsa ga wanda ke yi mani ba'a. 12 Mutum mai cikakken hankali na ɓoyewa ne idan ya ga wahala, amma mutane masu halin baƙunci na tafiya kai-tsaye har su kuma shiga wahala. 13 Ka karɓe mayafin wanda ya tsaya wa baƙo, ka kuma riƙe shi a matsayin alƙawari sa'ad da ya tsayawa karuwar mace. 14 Duk wanda yasa wa maƙwabcinsa albarka da babbar murya da sassafe, wannan albarkar za a ganta kamar la'ana ce! 15 Mace mai yawan faɗace-faɗace na kama da yayyafi a ranar ruwan sama marar tsayawa; 16 hana ta na kama da hana iska ne, ko kuma yin ƙoƙarin riƙe mai cikin hannun damanka. 17 ‌Ƙarfe ke wãsa ƙarfe; haka nan kuma, mutum ke wãsa abokinsa. 18 Wanda ya yi noman zaitun zai ci 'ya'yan itacensa, kuma wanda ya tsare ubangidansa za a yabe shi. 19 Kamar yadda ruwa ke nuna fuskar mutum, haka zuciyar mutum ke bayyana mutumin. 20 Kamar yadda Lahira da Abaddon basu ƙoshi, haka idanun mutum basu taɓa ƙoshi. 21 Maƙera domin gwada azurfa ne tanderun wuta kuwa domin zinariya ne; mutum kuma ana gwada shi ne sa'ad da aka yabe shi. 22 Ko da zaka daka wawa da taɓarya - harɗe da hatsi - duk da haka wawancinsa ba zai bar shi ba. 23 Ka tabbatar ka san lafiyar tumakinka ka kuma nuna damuwarka ga garkenka, 24 gama dukiya ba ta har abada ba ce. Ko masarauta tana dawwama dukkan tsararraki? 25 Ka san lokacin da busasshiyar ciyawa ta ɗauke sabuwa kuma ta fito, da kuma lokacin da ciyawa daga bisa tuddai ke taruwa ciki. 26 Waɗannan tumakai zasu yi maka tanadin tufafin sawa haka kuma ragunan zasu yi tanadin kuɗi domin filin. 27 Za a sami madarar awaki domin abincinka - abinci domin iyalinka - kuma wartsakarwa domin 'yan matanka bayi.

Sura 28

1 Mugayen mutane na gudu babu wani mai korar su, amma masu adalci basu da tsoro kamar ɗan zaƙi. 2 Saboda kurakuran ƙasa, ta sami shugabanni da yawa, amma ga mutum mai fahimta da ilimi, zata dawwama na lokaci mai tsawo. 3 Matalaucin da ke zaluntar wasu matalautan mutane na kama da ruwan sama da baya bada abinci. 4 Waɗanda suka yi banza da shari'a na koma wa ga yabon mugayen mutane, amma waɗanda ke bin shari'a na gãba da su. 5 Mugayen mutane basu fahimtar hukunci, amma masu neman Yahweh na fahimtar komai. 6 Ya fiye wa matalaucin mutum mai tafiya cikin aminci, da mai arziƙi wanda ke tafiya cikin hanyoyinsa na rashin aminci. 7 Shi wanda ya kula da shari'a ɗa ne mai fahimta, amma abokin mashaya abin kunya ne ga mahaifinsa. 8 Duk wanda ya tara dukiyarsa ta hanyar zamba dukiyarsa zata tafi wurin wani wanda zai tausaya wa matalauta. 9 Idan wani ya juyar da kunnuwarsa daga sauraren shari'a, ko addu'arsa ma abin ƙyama ce. 10 Duk wanda ya ɓatas da mai gaskiya domin aikata mugunta zai faɗa cikin ramin da ya haƙa, amma mai gaskiya zai sami gãdo mai kyau. 11 Mai arziki na yi wa kansa kallon shi mai hikima ne, amma mai fahimta wanda ke matalauci zai tona masa asiri. 12 Lokacin da masu adalci ke mulki, akwai babbar ɗaukaka; amma sa'ad da mugaye suka tashi, ana tone asirin mutane. 13 Wanda ya ɓoye zunubansa ba za shi yi albarka ba, amma shi wanda ya furtasu ya kuma rabu da su za a yi masa jinƙai. 14 Shi wanda ke rayuwa cikin girmamawa mai albarka ne, amma wanda ya taurare zuciyarsa zai abka cikin wahala. 15 Kamar zaki mai ruri ko kamar dabbar kerkeci mai huci haka mugun shugaba a bisa mutane matalauta. 16 Shugaban da ba shi da fahimta azzalumi ne, amma wanda ya tsani zalunci zai daɗe da kwanakinsa. 17 Idan mutum ya yi laifi domin ya zubda jinin wani, zai zama mai gudun hijira har sai ya mutu kuma ba wanda zai taimake shi. 18 Duk wanda ya yi rayuwa cikin gaskiya zai zauna lafiya lau, amma wanda tafarkinsa karkataccc ne zai faɗi ba zato. 19 Shi wanda ya yi aiki cikin gonarsa zai sami abinci mai yawa, amma wanda ya bi wofi zai sami talauci mai yawa. 20 Mutum mai aminci zai sami albarka mai girma, amma wanda ya sami wadata cikin hanzari ba zai tsira daga hukunci ba. 21 Bai kamata a nuna sonkai ba, amma akan 'yar gurasa mutum kan iya aikata ba dai-dai ba. 22 Mutum mai rowa na hanzarin neman arziki, amma bai san da cewar talauci na zuwa bisansa ba. 23 Duk wanda ya yi ma wani horo, daga baya zai sami tagomashi daga gare shi fiye da wanda daga shi aka yi masa zaƙin baki. 24 Duk wanda ya zambanci mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuma ce, "Wannan ba zunubi bane," shi abokin wanda ke hallakarwa ne. 25 Mutum mai yawan son kansa na haddasar da rigima, amma wanda ya dangana da Yahweh zai yi albarka. 26 Shi wanda ya dangana ga tasa zuciya wawa ne, amma duk wanda ya yi tafiya cikin hikima zai yi nisa daga hatsari. 27 Wanda ya bayar ga matalauta ba za shi rasa komai ba, amma wanda ya rufe idanunsa gare su zai sami la'ana. 28 Lokacin da miyagu suka tashi, mutane na ɓoye kansu; amma idan suka lalace, masu adalci na ƙaruwa.

Sura 29

1 Mutumin da ya karɓi horo dayawa amma ya taurare wuyansa za a karya shi cikin ƙanƙanen lokaci da ba za shi warke ba. 2 Lokacin da masu adalci suka ƙaru, mutane na farinciki, amma lokacin da mugu ke shugabanci, mutane na ajiyar zuciya. 3 Duk wanda ya ƙaunaci hikima nasa mahaifinsa ya yi farinciki, amma wanda ya yi abokantaka da karuwai na lalatar da dukiyarsa. 4 Sarki na kafa ƙasar da adalci, amma wanda ya nemi cin hanci yana yayyaga ta dukka. 5 Mutumin da ya yi wa maƙwabcinsa daɗin yana shinfiɗa wa sawayensa tarko ne. 6 Cikin zunubin mugun mutum nan akwai tarko, amma mutum mai adalci yana waƙoƙi da farinciki. 7 Mutum mai adalci na sane da yancin talakawa; mugun mutum ba shi da wannan ilimin. 8 Masu ba'a sukan cinna wa birni wuta, amma waɗanda ke da hikima suna juyar da hasala. 9 Lokacin da mutum mai hikima ya yi jayayya da wawa, yana fusata yana kuma dariya, ba za a kuma sami hutawa ba. 10 Masu zubda jini suna tsanar masu gaskiya su kuma nemi ran kamilai. 11 Wawa yana bayyana dukkan haushinsa, amma mutum mai hikima na danne shi ya kuma kãme kansa. 12 Idan mai mulki ya saurari ƙarairayi, dukkan shugabanninsa zasu zama mugaye. 13 Matalauci da wanda ke azzalumi sun zama ɗaya, gama Yahweh ya bada haske ga idanunsu dukka. 14 Idan sarki ya shar'anta matalauta da gaskiya, kursiyinsa zai kafu har abada. 15 Sanda da tsautawa na bada hikima, amma ɗan da ba ya sami horo ba na kawo wa mahaifiyarsa kunya. 16 Yayin da mugayen mutane ke riƙe da iko, kurakurai na ƙaruwa, amma adalai zasu ga faduwar mugayen mutane. 17 Ka hori ɗanka zai kuma baka hutu; zai kawo wa ranka jin daɗi. 18 Inda babu furtacciyar ruya mutane kan yi yadda suka ga dama, amma wanda ya kula da shari'a mai albarka ne. 19 Bawa ba zai tsautu da magana kawai ba, ko da ya fahimta, ba zai juya ba. 20 Ko ka ga mutum mai saurin magana? Ya fiye a sa zuciya ga wawa da wannan. 21 Duk wanda ya shagwaɓa bawansa tun yana matashi, a ƙarshe akwai wahala. 22 Mutum mai fushi na garwaya husuma kuma mai hasala na aikata zunubai masu yawa. 23 Girman kan mutum ne ke kãda shi, amma wanda ke da ruhun saukin kai za a ba shi ɗaukaka. 24 Shi wanda ya yi tarayya da ɓarawo maƙiyin ransa ne; yana jin la'ana bai kuma ce komai ba. 25 Tsoron mutum tarko ne, amma wanda ya dogara ga Yahweh za a kiyaye shi. 26 Dayawa ne masu neman ganin fuskar mai mulki, amma daga wurin Yahweh adalci ke zuwa ga mutum. 27 Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga mutane masu adalci, amma wanda ke mai adalci abin ƙi ne ga mugun mutum.

Sura 30

1 Maganganun Agu ke nan ɗan Yãke - furcin: Wannan mutumin ya gaya wa Itiyel da Ukal: 2 Tabbas ni kamar wata dabba ce ba mutum ba kuma bani da fahimta irin na mutum. 3 Ban koyi hikima ba, bani kuma da ilimi game da Mai Tsarkin. 4 Wane ne ya haura cikin sama ya kuma sauko? Wane ne ya tattara iska cikin hannuwansa? Wane ne ya tattara ruwaye cikin mayafi? Wane ne ya kafa iyakokin dukkan duniya? Mene ne sunansa, kuma mene ne sunan ɗansa? Tabbas ka sani. 5 Kowacce maganar Allah gwadajjiya ce; garkuwa ce ga duk waɗanda ke ɓuya gare shi. 6 Kada ka ƙara a bisa maganarsa, domin kada ya hore ka, kuma za a iske ka maƙaryaci. 7 Abu guda biyu na tambaya gare ka, kada kuma ka hana mani kamin na mutu: 8 Kada ka bar wofi da ƙarya su kusance ni. Kada ka ba ni ko talauci ko arziki, ka dai ba ni abincin da nake buƙata. 9 Gama idan na samu dayawa, ina iya ƙaurace maka in ce, "Wane ne Yahweh?" Ko idan na zama matalauci, ina iya sata har in kawo reni ga sunan Allahna. 10 Kada ka zargi bawa a gaban ubangidansa, don kada ya la'anta ka kuma har a kama ka da laifi. 11 Akwai wata tsara da ke la'anta mahaifinsu kuma ba ta albarkatar mahaifiyarsu. 12 Akwai tsarar da ke ganin kanta mai tsarki ce a gaban idanun ta, amma duk da haka basu wanku daga ƙazantarsu ba. 13 Akwai tsarar da fuskarsu take ɗage sama, dubi yadda girar idanunsu ke ɗage can sama! 14 Akwai wata tsara wadda haƙoransu na takobi ne, kuma mataunansu kamar wuƙaƙe, domin su hallaka matalauta daga duniya mabuƙata kuma daga cikin 'yan adam. 15 Matsattsaku na da 'yan mata biyu: "Bayar kuma bayar" suke kuka. Akwai abu guda uku da basu ƙoshi, guda huɗu da basu cewa, "Ya isa": 16 Lahira; da mahaifar da bata ɗaukar ciki; da ƙasar da bata ƙoshi da ruwa; da kuma wutar da bata cewa, "Ya isa!" 17 Idanun da suka yi wa mahaifi ba'a ko suka rena rashin biyayya ga mahaifiya, hankakin kwari zasu ƙwaƙule idanunsa, kuma angulai zasu cinye namansa. 18 Akwai abubuwa guda uku masu ban mamaki gare ni, har huɗu da ban fahimce su ba: 19 hanyar gaggafa a sararin samaniya; hanyar macijiya a bisa kan dutse; hanyar jirgi a bisa kan teku; da hanyar ɗan saurayi tare da 'yar budurwa. 20 Ga hanyar mazinaciya: tana cin abinci ta kuma share baki tana cewa, "Ban yi wani abin da ke ba dai-dai ba." 21 A ƙarƙashin abubuwa guda uku duniya ke girgiza, kuma a ƙarƙashin guda huɗu bata iya jurewa: 22 lokacin da bawa ya zama sarki; yayin da wawa ya ƙoshi da abinci; 23 macen da aka ƙi lokacin data yi aure; baiwar da kuma ta gãji uwargijiyarta. 24 Akwai abubuwa huɗu cikin duniya 'yan ƙanƙanana ne amma suna da hikima sosai: 25 tururuwa hallitu ne marasa ƙarfi, amma suna tanadin abincinsu cikin rani; 26 remaye hallitu marasa ƙarfi, amma suna gina gidajensu cikin duwatsu. 27 Fãra basu da sarki, amma dukkansu suna cincirindo-cincirido. 28 Haka ma ƙadangare, kana iya riƙe shi cikin hannunka biyu, duk da haka kana samun su a cikin fadodi. 29 Akwai abubuwa uku suna da koƙari cikin ayyukansu haka ma huɗu da ke da takama a yadda suke tafiyarsu: 30 zaki, mai ƙarfi cikin namun jeji - ba shi juya baya daga kowanne abu, 31 zakara mai cara; bunsuru; da kuma sarkin da sojojinsa ke tsaye kusa da shi. 32 Idan ka yi wauta, kana ɗaukaka kanka, ko idan kana shirye-shiryen mugunta - ka ɗibiya hannuwanka a bakinka. 33 Kamar yadda kaɗaɗɗar madara ke fitar da mai da kuma kamar yadda hanci ke haɓo yayin da aka buge shi, haka ayyukan da aka aiwatar da su a cikin fushi.

Sura 31

1 Maganganun sarki Lemuwel - umarnin da mahaifiyarsa ta koya masa. 2 Mene ne, ya ɗana? Mene ne, ɗan mahaifata? Me kake so, ɗan alƙawarina? 3 Kada ka bada ƙarfinka ga mata, ko hanyarka ga waɗanda ke hallakar da sarakai. 4 Ba girman sarakai ba ne, Lemuwel, ba girman sarakuna bane su sha giya, ko masu mulki su yi kwaɗayin abin sha mai bugarwa, 5 domin lokacin da suka sha sukan manta da abin da aka umartar, su kuma juyar da yancin dukkan ƙuntattu. 6 Ka bada abin sha mai bugarwa ga wanda ke hallaka inabi kuma ga waɗanda ke cikin ƙunci. 7 Zaya sha ya manta da talaucinsa kuma ba za shi tuna da wahalarsa ba. 8 Ka yi magana a madadin waɗanda basu iya magana, don dalilin dukkan masu hallaka. 9 Ka yi magana a fili ka kuma shar'anta dai-dai da ma'aunin adalci ka kuma yi roƙo sabili da nawayar matalauta da mabuƙatan mutane. 10 Wa ke iya samun mace cikakkiya? Darajarta ta fi duwatsu masu daraja. 11 Zuciyar maigidanta ta yarda ya ita, kuma ba zai taɓa talaucewa ba. 12 Tana yin abubuwan alheri dominsa ba mugunta ba dukkan kwanakinta. 13 Takan nemi ulu da lilin, ta kuma yi aiki cikin jin daɗi da hannuwanta. 14 Tana kama da fataken jirage; tana kawo abincinta daga nesa. 15 Takan tashi da dare ta bai wa iyalinta abinci, tana kuma raba wa bayinta mata aikinsu. 16 Takan lura da gona ta kuma saya, da ribar hannuwanta takan dasa gonar inabi. 17 Tana yi wa kanta ado da ƙarfi ta kuma maida kafaɗunta ƙarfafa. 18 Takan san abin da zai zama riba mai kyau gare ta; dukkan dare fitilarta ba ta mutuwa. 19 Tana ɗora hannunta bisa mazarin sãƙa, kuma ta riƙe murɗaɗɗen zaren. 20 Tana miƙa hannuwanta zuwa ga matalauta; tana kuma miƙa hannuwanta zuwa ga mutane mabuƙata. 21 Bata tsoron sanyi ta dalilin iyalinta, gama dukkan iyalinta na sanye da kayan sanyi. 22 Tana yiwa gadonta shimfiɗa, tana kuma sanye da tufafi masu kyau na lilin masu laushi na shunayya. 23 Maigidanta sananne ne a ƙofofi, lokacin da ya ke zama da shugabannin ƙasar. 24 Takan ɗinka riguna ta sayar, tana kuma sayar da ɗamara ga fatake. 25 Tana yafe da ƙarfi da daraja, kuma tana yiwa lokaci mai zuwa dariya. 26 Tana buɗe bakinta cikin hikima kuma dokar alheri na a bakinta. 27 Tana lura da tafarkin iyalanta kuma bata cin abincin zaman banza. 28 Yaranta na tashi su kira ta mai albarka, kuma mijinta na yabonta, cewa, 29 "Mata dayawa sun aikata dai-dai, amma ke kin wuce su gaba ɗaya." 30 Kayan kwalliya abin yaudara ne, kyau abin banza ne, amma mace mai tsoron Yahweh, za a yabe ta. 31 Ka ba ta 'ya'yan hannuwanta kuma bari ayyukanta su yabe ta a bakin ƙofofi.

Littafin Mai Wa'azi
Littafin Mai Wa'azi
Sura 1

1 Waɗannan ne maganganun malami, zuriyar Dauda kuma sarki a Yerusalem. 2 Malami ya faɗi wannan. "Kamar turirin hayakin raɓa, kamar hurawa a cikin iska, komai na ɓacewa, su na barin tambayoyi masu yawa. 3 Wacce riba ce 'yan'adam suke samu daga dukkan aikin da suke yin aiki tuƙuru akai a ƙarƙashin rana? 4 Tsara ɗaya ta tafi, wata tsarar kuma ta zo, amma duniya ta tabbata har abada. 5 Rana na fitowa, kuma tana faɗuwa, tana kuma sake saurin komawa wurin da ta fito. 6 Iska na hurawa kudu tana kuma zagayawa kewaye zuwa arewa, koyaushe ta na tafiya kewaye bisa tafarkinta ta kuma sake dawowa. 7 Dukkan koguna suna gangarawa zuwa teku, amma teku bai taɓa cika ba. Inda koguna su ke tafiya, a can kuma suke sake tafiya. 8 Komai ya zama a gajiye, ba bu kuma wanda zai iya yin bayani. Ido bai ƙoshi da abin da ya ke gani ba, ko kuma kunne ya wadatu da abin da ya ke ji ba. 9 Duk abin da ya kasance shi ne zai kasance, duk kuma abin da aka taɓa yi shi ne za'a yi. Ba bu wani abu sabo a ƙarƙashin rana. 10 Akwai wani abu game da abin da za'a ce, 'Duba, wannan sabo ne'? Duk abin da ya wanzu ya riga ya wanzu da daɗewa, a lokacin shekarun da suka zo da daɗewa kafin mu. 11 Babu wanda ya ke kamar ya tuna da abubuwan da suka faru a zamanin dã, da abubuwan da suka faru daga bisani sosai da abin da zai faru a nan gaba bai yi kama da za'a tuna da shi ba ma." 12 Ni ne Malamin, kuma ni ne nake sarki a bisa Isra'ila a Yerusalem. 13 Na miƙa raina ga bincike da nemowa ta wurin hikima duk abin da ake yi a ƙarƙashin sama. Cewa nema gajiyayyen aiki ne da Allah ya ba 'ya'yan ɗan'adam suyi ta aiki da shi. 14 Naga dukkan ayyukan da ake yi a ƙarƙashin rana, kuma duba, dukkan su ɗungum turirin hayaƙi ne da bin iska. 15 Murɗaɗɗe ba za a iya miƙar da shi ba! Abin da ya ɓace ba za a iya ƙidaya wa ba! 16 Nayi magana da zuciyata cewa, "Duba, na sami hikima fiye da waɗanda suke kafin ni a Yerusalem. Raina yaga babbar hikima da ilimi." 17 Sai na miƙa zuciyata in san hikima da kuma hauka da wawanci. Sai na kai ga fahimtar cewa wannan ma wani yunƙuri ne na kiwon iska. 18 Gama a cikin yalwar hikima akwai ruɗewa sosai, shi kuma wanda ke ƙara ilimi yana ƙara baƙinciki.

Sura 2

1 Na cewa zuciyata, "Zo yanzu, zan gwada ki da murna. Sai ki more jin daɗinki." Amma duba, wannan ma 'yar taƙaitacciyar iska ce. 2 Game da dariya na ce, "Taɓin hankali ce," game da jin daɗi kuma, "Ina amfanin shi?" 3 Na nemo a zuciyata yadda zan biya buƙatar marmarina da ruwan inabi. Na bar raina ya bishe ni da hikima kodaya ke har wa yau ina riƙe da wawanci. Na so in samo abu mai kyau da mutane za suyi a ƙarƙashin sama a lokacin kwanakin rayuwarsu. 4 Na aiwatar da manyan abubuwa. Na gina gidaje domin kaina na kuma dasa garkunan inabi. 5 Na ginawa kaina lambuna da tashoshin shaƙatawa; na dasa dukkan ire-iren itatuwa masu ba da 'ya'ya a cikin su. 6 Na ƙirƙiro tafkunan ruwa domin su bada ruwa ga jejin da ake renon itatuwa. 7 Na sawo bayi maza da bayi mata; An haifa ma ni bayi a fãdata. Kuma ina da manyan garkunan shanu da garkunan tumaki da awaki, fiye da duk wani sarki da ya yi mulki kafin ni a Yerusalem. 8 Na kuma tarawa kaina azurfa da zinariya, dukiyar sarakuna da larduna. Na samar wa kai na mawaƙa maza da mata - abin farincikin 'ya'yan 'yan'adam - da ƙwaraƙwarai masu yawa. 9 Sai na zama mafi girma da dukiya fiye da dukkan waɗanda suke kafin ni a Yerusalem, kuma hikimata ta kasance tare da ni. 10 Duk abin da idanuna suka yi marmari, ban hana masu ba. Ban hana wa zuciyata duk wani jin daɗi ba, saboda zuciyata na farinciki cikin dukkan aikin ƙarfina kuma jin daɗi shi ne ladata domin dukkan aikina. 11 Daga nan na duba dukkan ayyukan da hannuwa na suka aiwatar, da aikin da nayi, amma kuma, kowanne abu turiri ne da yunƙurin kiwon iska. A ƙarƙashin rana babu wata riba a cikin su. 12 Daga nan na juya in yi la'akari da hikima, da kuma hauka da wawanci. Gama me sarki na gaba zai yi wanda zai zo bayan sarki, wanda ba a riga anyi ba? 13 Daga nan na fãra fahimtar cewa hikima na da daraja bisa wawanci, kamar yadda haske yafi duhu. 14 Mutum mai hikima ya kan yi amfani da idanunsa cikin kansa ya ga inda ya ke tafiya, amma wawa yana tafiya cikin duhu, ko da ya ke na san al'amura iri ɗaya ne ke faruwa da dukkan su. 15 Daga nan na ce a cikin zuciyata, "Abin da ya fãru da wawa, ni ma zai fãru da ni. To ina ban-banci idan ina da wayau sosai?" Sai na kammala a cikin zuciyata, "Wannan ma turirin hayaƙi ne kawai." 16 Domin mutum mai hikima, kamar wawa, ba a tunawa da shi har dogon lokaci sosai. A cikin kwanaki masu zuwa an riga an manta da komai. Mai wayau na mutuwa kamar yadda wawa ke mutuwa. 17 Sai rayuwa ta gundure ni saboda dukkan aikin da ake yi a ƙarƙashin rana mugunta ce a gare ni. Wannan kuwa saboda komai turiri ne kawai da yunƙurin kiwon iska. 18 Na ƙi jinin dukkan abin da na aiwatar wanda na aikata a ƙarƙashin rana saboda tilas in bar su baya ga mutumin da zai zo bayana. 19 Gama wa ya sani ko zai zama mutum mai hikima ko wawa? duk da haka zai zama shugaba bisa komai ƙarƙashin rana wanda aikina da hikimata suka gina. Wannan ma turirin hayaƙi ne. 20 Saboda haka zuciyata ta fãra razana bisa dukkan aikin da nayi a ƙarƙashin rana. 21 Domin za a sami wanda ya ke aiki tare da hikima, tare da ilimi, da ƙwarewa, amma zai bar duk abin da ya ke da shi ga mutumin da bai yi wani abu kamar sa ba. Wannan ma turirin hayaƙi ne da tsautsayi mai girma. 22 Domin wacce riba taliki ya samu wanda ya yi aiki tuƙuru kuma ya yi ƙoƙari a zuciyarsa ya kammala aikin ƙarfinsa a ƙarƙashin rana? 23 Kowacce rana aikin shi cike da ciwo da gajiya, sa'an nan da dare ransa ba ya samun hutawa. Wannan ma turirin hayaƙi ne. 24 Babu wani abin da ya fiye wa kowa baya ga ya ci ya sha ya ƙoshi da abin da ke mai kyau cikin aikinsa. Naga cewa wannan gaskiyar ta zo daga hannun Allah ne. 25 Gama wane ne zai iya ci ko ya sami wani irin jin daɗi idan ba daga Allah ba? 26 Domin ga dukkan wanda ya ke faranta masa rai, Allah na bayar da hikima da ilimi da farinciki. Duk da haka, ga mai zunubi yana bayar da aikin tattarawa da adanawa domin ya bayar da su ga wanda ya ke farantawa Allah rai. Wannan ma ɗungum turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.

Sura 3

1 Game da kowanne abu akwai tsaidajjen lokaci, da zamani domin kowanne dalili ƙarƙashin sama. 2 Akwai lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin dasawa da lokacin tuge dashe-dashen, 3 lokacin kashewa da lokacin warkarwa, lokacin yagawa da lokacin ginawa. 4 Akwai lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa, 5 lokacin zubar da duwatsu da lokacin tattara duwatsu, lokacin rungume wasu mutane da lokacin janyewa daga rungumewa. 6 Akwai lokacin dubawa domin abubuwa da lokacin tsayawa daga dubawar, lokacin ajiye abubuwa da lokacin zubar da abubuwa, 7 lokacin yaga sutura da lokacin gyara sutura, lokacin yin shiru da lokacin magana. 8 Akwai lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama. 9 Wacce riba ma'aikaci ke ci cikin aikin ƙarfinsa? 10 Naga aikin da Allah yaba talikai su kammala. 11 Allah ya yi kowanne abu ya dace domin nasa lokaci. Ya sa madawwamin lokaci a zukatansu. Amma 'yan'adam ba zasu fahimci ayyukan da Allah ya yi ba, daga farkonsu har ya zuwa ƙarshensu. 12 Nasan babu abin da ya fiye wa kowa baya ga ya yi farinciki ya kuma yi abin da ke mai kyau dukkan tsawon rayuwarsa - 13 kowa kuma ya ci ya sha, ya kuma fahimci yadda zai ji daɗin abin da ke zuwa daga dukkan aikinsa. Wannan kyauta ce daga Allah. 14 Nasan cewa dukkan abin da Allah ya yi yana dawwama har abada. Babu abin da za a ƙãra akai ko a ɗauke, saboda Allah ne ya yi domin mutane su kusance shi tare da girmamawa. 15 Kowanne abu da ke wanzuwa ya rigaya ya wanzu; kowanne abu da zai wanzu ya rigaya ya wanzu. Allah ya sa talikai su nemi ɓoyayyun abubuwa. 16 Na kalli muguntar da ke ƙarƙashin rana, inda ya kamata a yi hukunci, a gurbin adalci, mugunta ce ke wurin. 17 Na ce a zuciyata, "Allah zai shar'anta mai adalci da mugu a lokacin da ya dace domin kowanne al'amari da kowanne aiki." 18 Na ce a zuciyata, "Allah na gwada talikai ya nuna masu cewa kamar dabbobi suke." 19 Gama ƙaddarar ɗan'adam da ƙaddarar dabbobi ƙaddara ce iri ɗaya domin su. Mutuwar ɗaya kamar mutuwar ɗayan ce. Lumfashin iri ɗaya ne domin dukkan su. Babu wata daraja game da ɗan'adam fiye da ta dabbobi. Domin kowanne abu ba lumfashi ne kawai ba? 20 Kowanne abu na tafiya wuri ɗaya. Kowanne abu ya zo daga turɓaya, kuma kowanne abu zai koma ga turɓaya. 21 Wa ya sani ko ruhun ɗan'adam na tafiya sama kuma ruhun dabbobi na tafiya ƙasa cikin ƙasa? 22 Sai kuma na gane cewa babu abin da ya fiye wa kowa banda ya ji daɗin aikinsa, domin wannan ne hidimarsa. Wa zai maido da shi baya yaga abin da ke fãruwa bayansa?

Sura 4

1 Na sake yin tunani game da cutarwar da ke faruwa a ƙarƙashin rana. Duba kuma, hawayen mutanen da aka cuta, babu kuma wanda zai ta'azantar da su! Iko na hannun masu cutar da su, babu kuma wanda zai ta'azantar da su! 2 Sai na yi la'akari da cewa waɗanda suka mutu sun fi waɗanda ke da rai morewa, waɗanda har yau suna raye. 3 Duk da haka, wanda ya fisu dukka morewa shi ne wanda bai riga ya rayu ba, wanda bai riga ya ga ayyukan muguntar da ake yi ba ƙarƙashin rana. 4 Daga nan naga cewa kowanne aikata aiki da aikin ƙwarewa ya zama kishin maƙwabcin wa ni. Wannan shi ma turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska. 5 Wawa yana naɗe hannuwansa kuma baya aiki, domin wannan abincinsa jikinsa ne. 6 Amma gwamma riba kaɗan tare da aikin natsuwa da hannuwa biyu cike da aikin ƙoƙarin kiwon iska. 7 Daga nan na sake yin tunani game da ƙarin aikin wofi, ƙarin turirin hayaƙi mai ɓacewa a ƙarƙashin rana. 8 Akwai wani irin mutum da ya ke shi kaɗai. Bai da kowa, ba ɗa ko ɗan'uwa. Babu ƙarshe ga dukkan aikinsa, idanunsa ba su ƙoshi da neman wadata. Yana mamaki, "Domin wa nake wahala ina hana wa kaina jin daɗi?" Wannan ma turirin hayaƙi ne, al'amari marar kyau. 9 Mutum biyu za su yi aiki fiye da ɗaya; tare za su sami biya mai kyau game da aikinsu. 10 Domin idan ɗaya ya fãɗi, ɗayan zai iya ɗaga abokinsa. Duk da haka, baƙinciki na biye da wanda ke shi kaɗai sa'ad da ya fãɗi idan babu wanda zai iya ɗaga shi. 11 Idan biyu suka kwanta tare, za su iya jin ɗumi, amma ta yaya ɗaya zai ji ɗumi shi kaɗai? 12 Za a iya fin ƙarfin mutum ɗaya shi kaɗai, amma biyu za su iya yin tsayayya da hari, igiya uku a murɗe ba za su yi saurin tsinkewa ba. 13 Gwamma wani ya zama matashi talaka amma mai wayau da tsohon sarki wawa wanda ya daina sanin yadda ake sauraron kashedi. 14 Wannan gaskiya ne koda saurayin ya zama sarki daga kurkuku, ko kuma an haife shi talaka a masarautarsa. 15 Na kalli kowa wanda ya ke da rai kuma yana yawonsa a ƙarƙashin rana, tare da matashin da ke tasowa ya maye gurbinsa. 16 Babu ƙarshen dukkan mutanen da suke so suyi biyayya da sabon sarki, amma daga ba ya yawancin su ba zasu sake yabonsa ba. Tabbas wannan al'amari turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.

Sura 5

1 Ka kiyaye takawarka sa'ad da ka je gidan Allah. Ka matsa kusa ka saurara fiye da miƙa hadayar wawaye, waɗanda basu fahimci cewa suna yin abin da ba dai-dai ba. 2 Kada ka yi saurin magana da bakinka, kada kuma ka yi saurin barin zuciyarka ta fito da wani al'amari a gaban Allah. Allah na sama, amma kai ka na duniya, sai ka bari maganganunka su zama kaɗan. 3 Idan kana da abubuwa da yawa da za ka yi kuma ka da mu a kai, zai yiwu ka sami miyagun mafarkai. Kana ƙara yawan maganganun da zaka furta, kana ƙara yawan abubuwan shirme da zaka iya faɗa. 4 Sa'ad da ka ɗauki alƙawari ga Allah, kada ka yi jinkirin aikatawa, domin Allah ba ya jin daɗin wawaye. Ka yi abin da ka yi alƙawarin za ka yi. 5 Gwamma kada ka ɗauki alƙawari da ka ɗauki wanda ba ka aiwatar ba. 6 Kada ka bar bakinka yasa jikinka ya yi zunubi. Kada ka cewa manzon firist, "Wannan alƙawari kuskure ne." Meyasa za ka ba Allah haushi ta wurin alƙawarin ƙarya, kana tunzura Allah ya rushe aikin hannuwanka? 7 Gama a cikin yawan mafarkai, kamar a cikin yawan maganganu, akwai turirin hayaƙi marar ma'ana. Sai ka ji tsoron Allah. 8 Sa'ad da kaga ana zaluntar matalauci kuma ana karɓe masa hakkinsa da ke dai-dai a cikin lardinka, kada ka yi mamaki kamar cewa babu wanda ya sani, saboda akwai mutane da ke kan mulki waɗanda ke lura da waɗanda ke ƙarƙashinsu, akwai kuma waɗanda suka fisu iko sama da su. 9 Bugu da ƙari, amfanin ƙasar domin kowa ne, sarki kuma kansa yana ɗaukar amfani daga gonakin. 10 Duk wanda ke ƙaunar azurfa ba zai ƙoshi ba da azurfa, duk kuma wanda ke ƙaunar dukiya a koyaushe yana son ƙãri. Wannan, shi ma, turirin hayaƙi ne. 11 Yadda wadata ke ƙaruwa, haka ma mutanen da ke cin ta. Ina amfanin dukiya ga mai ita baya ga ya yi ta kallon ta da idanunsa? 12 Barcin ma'aikaci mai daɗi ne, ko ya ci kaɗan ko da yawa, amma dukiyar mai arziki bata barin shi ya yi barci sosai. 13 Akwai muguntar da na gani a ƙarƙashin rana: dukiyar da mai ita ya ɓoye, ita ce sakamakon azabarsa. 14 Sa'ad da mai arziki ya rasa dukiyarsa ta wurin rashin sa'a, ɗansa, wanda ya haifa, za a bar shi ba komai a hannuwansa. 15 Yadda mutum ya zo daga mahaifar mahaifiyarsa, haka ma zai tafi tsirara. Ba zai tafi da ko ɗaya daga cikin aikin ƙarfinsa ba cikin hannunsa. 16 Wani mugun abin kuma shi ne yadda mutum ya zo, haka ya ke tafiya. To wacce riba ce ke akwai game da shi wanda ya ke aiki domin iska? 17 A lokacin kwanakinsa ya ci tare da duhu kuma ya ƙuntata kwarai tare da ciwo da fushi. 18 Duba, abin da na ga yafi kyau da dacewa kuma shi ne mu ci mu sha mu kuma ji daɗin riba daga dukkan aikinmu, yayin da muke aiki tuƙuru ƙarƙashin rana a lokacin kwanakin rayuwarmu wadda Allah ya ba mu. Gama wannan ne hidimar mutum. 19 Duk wanda Allah ya ba arziki da dukiya da ikon karɓar rabonsa ya kuma yi farinciki cikin aikinsa - wannan kyauta ce daga Allah. 20 Domin ba ya yawan tunawa da kwanakin rayuwarsa, saboda Allah ya sa yana ta hidima da abubuwan da ya ke jin daɗin aiwatarwa.

Sura 6

1 Akwai wata mugunta da na gani a ƙarƙashin rana, kuma ta yi babban nauyi bisa mutane. 2 Allah zai iya ba mutum arziki, dukiya, da daraja yadda bai rasa wani abin da ya ke marmari ba domin kansa, amma daga nan Allah bai bashi ikon jin daɗin su ba. Maimako, wani daban ke amfani da abubuwansa. Wannan turirin hayaƙi ne, muguwar azaba. 3 Idan mutum ya zama mahaifin 'ya'ya ɗari kuma ya rayu shekaru masu yawa, yadda kwanakin shekarunsa masu yawa ne, amma idan zuciyarsa bata ƙoshi da abu mai kyau ba kuma ba a bizne shi ba, daga nan na ce gwamma jaririn da aka haifa matacce da shi. 4 Wannan irin jariri ma an haife shi a wofi kuma ya wuce cikin duhu, sunansa kuma ya rage ɓoyayye. 5 Ko da ya ke wannan ɗan bai ga rana ba ko kuma ya san wani abu, ya huta koda ya ke wancan mutum bai huta ba. 6 Koda mutum zai yi rayuwa shekaru dubu biyu amma bai koyi ya ji daɗin abubuwa masu kyau ba, yana tafiya wuri guda kamar kowa da kowa. 7 Dukkan aikin mutum domin bakinsa ne, duk da haka ɗanɗanonsa ba ya ƙoshi. 8 Tabbas, wacce moriya mai wayau ya ke da ita bisa wawa? Wacce moriya matalauci ya ke da ita koda ya san yadda zai aiwatar a gaban sauran mutane? 9 Gwamma a ƙoshi da abin da idanu ke gani da ayi marmarin abin da ɗanɗano ke sha'awa barkatai, wanda shi ma turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska. 10 Duk abin da ya wanzu an riga an ba shi sunansa, kamannin mutum kuma an riga an san shi. Sai ya zama marar amfani ayi saɓani da babban mai hukunta kowa. 11 Ana ƙãra maganganun da ake faɗa, ana ƙãra yawan aikin wofi, to ina moriyar wannan ga mutum? 12 Gama wa yasan abin da ke mai yau domin mutum a cikin rayuwarsa a lokacin, lissafin kwanakinsa na wofi ta inda ya ke wucewa kamar inuwa? Wa zai gayawa mutum abin da zai fãru a ƙarƙashin rana bayan da ya mutu?

Sura 7

1 Suna mai kyau ya fi turare mai tsada, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa. 2 Gwamma a je gidan makoki da a je gidan biki, domin makoki yana zuwa ga dukkan mutane a ƙarshen rayuwa, to mutanen da ke raye tilas su ɗauki wannan a zuciya. 3 ‌Ɓ‌acin rai ya fi dariya, domin bayan baƙinciki a fuska sai farinciki a zuciya ya zo. 4 Zuciyar mai hikima na gidan makoki, amma zuciyar wawaye na gidan biki. 5 Gwamma a saurari tsautawar mai hikima da a saurari waƙar wawaye. 6 Domin kamar ƙarar ƙayoyin da ke ƙonewa a ƙarƙashin tukunya, haka ma dariyar wawaye. Wannan, ma, turirin hayaƙi ne. 7 Babu shakka ƙwace na sa mutum mai hikima ya zama wawa, kuma cin hanci na ɓãta zuciya. 8 Gwamma ƙarshen al'amari da farkonsa; kuma mutane masu haƙuri a ruhu sun fi mutane masu girman kai a ruhu. 9 Kada ka yi saurin fushi a ruhunka, domin fushi na zama cikin zukatan wawaye. 10 Kada ka ce, "Me ya sa kwanakin dã suka fi waɗannan?" Domin ba saboda hikima ka yi wannan tambaya ba. 11 Hikima, kamar gãdo, mai kyau ce, waɗanda ke ganin rana na moriyar ta. 12 Domin hikima na bada kariya kamar yadda kuɗi ke bada kariya, amma darajar ilimi shi ne hikima na ba da rai ga duk wanda ke da ita. 13 Yi la'akari da ayyukan Allah: Wa zai miƙar da duk abin da ya tanƙwarar? 14 Sa'ad da lokutta ke da kyau, ka zauna da murna cikin kyaun nan, amma sa'ad da lokutta suka ɓaci, yi la'akari da wannan: Allah ya bar dukkan su su wanzu gefe da gefe. Domin wannan dalili, babu wanda zai san wani abu da ke zuwa bayansa. 15 Naga abubuwa masu yawa a cikin kwanakina marasa ma'ana. Akwai mutane masu adalci da ke hallaka duk da adalcinsu, akwai kuma mutane masu mugunta da ke yin tsawon rai duk da muguntarsu. 16 Kada ka zama mai adalcin kai, mai hikima a idanunka. Meyasa za ka hallakar da kanka? 17 Kada ka zama mai yawan mugunta ko wawanci. Meyasa za ka mutu kafin lokacinka? 18 Yana da kyau ka riƙe wannan hikimar, kuma kada ka saki adalci. Domin talikin da ke da tsoron Allah zai kiyaye dukkan farillansa. 19 Hikima na da ƙarfi sosai a cikin mutum mai wayau, fiye da shugabanni goma a cikin birni. 20 Babu mutum mai adalci a duniya da ke aikata nagarta kuma bai taɓa yin zunubi ba. 21 Kada ka saurari dukkan maganar da aka furta, saboda kana iya jin bawanka na la'antar ka. 22 Haka nan kuma, ka sani da kanka cewa a cikin zuciyarka kana yawan la'antar wasu. 23 Dukkan waɗannan na tabbatar ta wurin hikima, na ce, "Zan yi wayau," amma ya fi abin da zan iya zama. 24 Hikima na nesa kuma da zurfi sosai. Wa zai same ta? 25 Na juya zuciyata in koya kuma in jaraba kuma in biɗi hikima da bayanan zahiri, in kuma fahimci cewa mugunta sakarya ce kuma wawanci hauka ne. 26 Na gano cewa abin da yafi mutuwa ɗaci shi ne ko wacce mata wadda zuciyarta ke cike da tarkuna da tãrurruka, wadda kuma hannuwanta sarƙoƙi ne. Duk wanda ya gamshi Allah zai kucce daga gare ta, amma zata ɗauke mai zunubi. 27 "Yi la'akari da abin da na gãno," cewar Malamin. "Ina ta tãra gãnowa bisa gãnowa domin in samo bayanin zahiri. 28 Wannan ne har yanzu nake nema, amma ban same shi ba. A cikin dubu na sami namiji ɗaya mai adalci, amma a cikin dukkan waɗannan ban sami mace ɗaya ba. 29 Wannan ne kawai na gãno: Cewa Allah ya halicci 'yan'adam dai-dai, amma suka tafi neman wahalhalu da yawa."

Sura 8

1 Wane ne mutum mai hikima? Wanda ya san abin da al'amuran rayuwa ke nufi? Hikima a cikin mutum nasa fuskarsa ta haskaka, kuma taurin fuskarsa ya canza. 2 Ina ba ka shawara da ka yi biyayya da dokar sarki saboda rantsuwar Allah na kiyaye shi. 3 Kada ka yi garajen barin gabansa, kada kuma ka goyi bayan abin da ba dai-dai ba, domin sarki na yin abin da ya so. 4 Maganar sarki ke mulki, to wane ne zai ce masa, "Me ka ke yi?" 5 Duk wanda ke kiyaye dokar sarki yana kaucewa cutarwa. Zuciyar mutum mai hikima takan gane dai-dai lokacin daya dace a aiwatar da abu. 6 Domin ga kowanne al'amari akwai yadda ya dace da lokacin da ya dace, saboda matsalolin mutum manya ne. 7 Babu wanda ya san abin da ke zuwa a gaba. Wane ne zai gaya mashi abin da ke zuwa? 8 Babu wanda ke mulki bisa lumfashinsa yadda zai tsaida lumfashin, babu kuma wanda ke da iko bisa ranar mutuwarsa. Babu wanda ake sallama daga bataliyar sojoji a lokacin yaƙi, kuma mugunta ba ta kuɓutar da waɗanda ke bayinta. 9 Na gãno dukkan wannan; Na sanya zuciyata ga kowanne irin aiki da ake yi a ƙarƙashin rana. Akwai lokacin da wani taliki ke muzgunawa wani talikin domin cutarwar wannan taliki. 10 Sai naga ana bizne miyagu a sarari. An ɗauke su daga wuri mai tsarki aka kuma bizne su mutane kuma suka yabe su a cikin birni inda suka aiwatar da ayyukan muguntarsu. Wannan ma wofi ne. 11 Sa'ad da zartar da hukunci gãba da aikin mugunta ba a aiwatar dashi ba da sauri, yana jarabtar zukatan 'yan'adam da su aikata mugunta. 12 Koda ya ke mai zunubi yana aikata mugunta sau ɗari kuma duk da haka ya yi tsawon rai, duk da haka na sani cewa zai fi kyau ga waɗanda ke girmama Allah, ga waɗanda ke tsayawa a gabansa suna kuma nuna masa girma. 13 Amma ba zai zama da lafiya ba game da mugun mutum; rayuwarsa ba za tayi tsawo ba. Kwanakinsa kamar inuwa ce mai wucewa saboda ba ya darjanta Allah. 14 Akwai wani turirin hayaƙi marar amfani - wani abun kuma da ake yi a duniya. Abubuwa na faruwa da mutane masu adalci yadda suke faruwa da mutane masu mugunta, kuma abubuwa na faruwa da mutane masu mugunta yadda suke faruwa da mutane masu adalci. Na ce shi ma wannan turirin hayaƙi ne marar amfani. 15 Sai na shawarta murna, saboda mutum ba ya da wani abu a ƙarƙashin rana fiye da ya ci ya sha ya kuma yi murna. Murna ce za ta yi masa rakiya cikin aikin ƙarfinsa domin dukkan kwanakin rayuwarsa waɗanda Allah ya bashi a ƙarƙashin rana. 16 Sa'ad da na bada zuciyata in san hikima in kuma fahimci aikin da ake yi a duniya, aikin da yawanci ake yi ba bu barci domin idanu koda rana ko da dare, 17 daga nan na yi la'akari da dukkan ayyukan Allah, kuma da cewar mutum ba zai iya fahimtar aikin da ake yi ba a ƙarƙashin rana. Ko ta yaya mutum ya yi aiki tuƙuru domin ya sami amsoshi, ba zai same su ba. Koda ya ke mutum mai hikima zai bada gaskiyar cewa ya sani, lallai bai sani ba.

Sura 9

1 Gama na yi tunani game da dukkan wannan a raina in sami fahimta game da mai adalci da mutane masu hikima da ayyukansu. Dukkan su suna cikin hannuwan Allah. Babu wanda ya sani wataƙila ƙauna ko ƙiyayya zata zo ga wani. 2 Kowa na fuskantar ƙaddara ɗaya. ‌Ƙaddara ɗaya ce ke jiran mutane masu adalci da miyagu, masu kyau, masu tsarki da marasa tsarki, da mai miƙa hadayu da wanda ba ya hadaya. Kamar yadda masu kyau suke mutuwa, haka kuma mai zunubi. Kamar yadda mai rantsuwa zai mutu, haka kuma mutumin da ke jin tsoro ya ɗauki wa'adi. 3 Akwai muguwar ƙaddara ga kowanne abu da ake yi a ƙarƙashin rana, al'amari ɗaya ne ke faruwa da su dukka. Zukatan 'yan'adam na cike da mugunta, kuma hauka na cikin zukatansu yayin da suke raye. Sai bayan wannan su tafi wurin matattu. 4 Domin duk wanda ya ke tare da dukkan masu rai, akwai bege, kamar yadda kare mai rai yafi mataccen zaki. 5 Domin mutane masu rai sun san cewa za su mutu, amma matattu basu san komai ba. Basu da wani sakamako kuma saboda an manta da tunawa da su. 6 ‌Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu, da kishinsu, sun ɓace da daɗewa. Ba za su sake samun wuri ba kuma cikin kowanne abu da ake yi ƙarƙashin rana. 7 Ka yi tafiyar ka, ka ci gurasarka da farinciki, ka kuma sha ruwan inabinka da zuciya mai murna, domin Allah ya tabbatar da shagalin ayyuka masu kyau. 8 Bari suturunka koyaushe su zama farare kanka kuma shafaffe da mai. 9 Ka zauna da murna tare da matar daka ke ƙauna dukkan kwanakin rayuwarka marasa amfani, kwanakin da Allah ya baka a ƙarƙashin rana a zamanin kwanakinka marasa amfani. Wannan ne sakamakonka a rayuwa domin aikinka a ƙarƙashin rana. 10 Duk abin da hannunka ya samu ya yi, ka aikata shi da dukkan ƙarfinka, saboda babu aiki ko bayani ko ilimi ko hikima a Lahira, in da kake tafiya. 11 Na ga wasu abubuwa na burgewa a ƙarƙashin rana: Tseren ba na mutane masu sauri ba ne. Yaƙin ba na mutane masu ƙarfi ba ne. Gurasa ba ta mutane masu hikima ba ce. Arziki ba na mutane masu fahimta ba ne. Tagomashi ba na mutane masu ilimi ba ne. Maimako, lokaci da sarari ke shafar su dukka. 12 Tabbas, babu wanda ya san sa'ad da lokacinsa zai zo. Kamar yadda ake kama kifi cikin tãru mai haɗari, ko ake kama tsuntsaye cikin tarko, a na yi wa 'ya'yan 'yan'adam tarko da miyagun lokutta da ke faɗowa bisan su farat ɗaya. 13 Na kuma ga hikima a ƙarƙashin rana ta hanyar da na kalle ta babba a gare ni. 14 Akwai wani ƙaramin birni mai mutane ƙalilan a ciki, wani babban sarki kuma ya zo gãba da shi ya yi masa sansani ya kuma gina manyan ramukan sansani gãba da shi. 15 To a cikin birnin an sami matalauci, mutum mai wayau, wanda ta wurin hikimarsa ya ceci birnin. Duk da haka daga baya, babu wanda ya tuna da wannan mutum matalauci. 16 Sai na kammala, "Gwamma hikima da ƙarfi, amma aka rena hikimar mutumin nan matalauci, maganganunsa kuma ba a ji su ba." 17 Maganganun mutane masu hikima da aka furta a hankali an fi jin su fiye da kururuwar duk wani sarki cikin wawaye. 18 Hikima tafi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya zai lalata abubuwan nagarta masu yawa.

Sura 10

1 Kamar yadda mataccen ƙuda yana sa turare ya yi wãri, haka wawanci ƙarami zai iya shan ƙarfin hikima da daraja. 2 Zuciyar mai hikima na gusawa dãma, amma zuciyar wawa na gusawa hagu. 3 Sa'ad da wawa ke tafiya akan hanya, tunaninsa kasasshe ne, yana tabbatar wa da kowa cewa shi wawa ne. 4 Idan hankalin mai mulki ya tashi gãba da kai, kada ka bar aikinka. Natsuwa na iya kwantar da fushi mai girma. 5 Akwai muguntar da na gani a ƙarƙashin rana, wani irin kuskure da ke zuwa daga shugaba: 6 A na ba wawaye matsayin shugabanci, yayin da mutane na ƙwarai ake basu ƙasƙantattun matsayi. 7 Na ga bayi na hawa dawakai, kuma mutane na ƙwarai na tafiya kamar bayi bisa ƙasa. 8 Duk wanda ya ke ginin rami zai iya faɗawa a ciki, duk kuma sa'ad da wani ya fasa katanga, maciji na iya sarar sa. 9 Duk wanda ke yankan duwatsu za su iya ji masa rauni, kuma mutumin da ke sarar katako yana cikin haɗari dashi. 10 Idan bãkin ƙarfe ya dushe, kuma mutum bai wãsa shi ba, daga nan tilas ya yi amfani da ƙarfi sosai, amma hikima na bayar da mafita domin nasara. 11 Idan maciji ya yi sara kafin a yi masa makari, daga nan babu wani amfani domin mai makarin. 12 Maganganun bãkin mutum mai hikima na cike da alheri, amma leɓunan wawa na lanƙwame shi. 13 Sa'ad da maganganu suka fãra kwararowa daga bãkin wawa, wawanci na fitowa, a ƙarshe kuma bãkinsa na kwararowa da haukan mugunta. 14 Wawa yana ruɓanɓanya maganganu, amma babu wanda ya san abin da ke zuwa. Wane ne ya san abin da ke zuwa bayansa? 15 Aikin wawaye na gajiyar da su, yadda ba zasu san ma hanyar zuwa gari ba. 16 Kaiton ki, ƙasa, idan sarkin ki ƙaramin yaro ne, idan kuma shugabanninki suka fara shagali da safe! 17 Amma mai albarka ce ke, ƙasa, idan sarkin ki ɗa ne na ƙwarai, idan kuma shugabannin ki na cin abinci lokacin da ya dãce, domin ƙarfi, kuma ba domin buguwa ba! 18 Saboda ƙyuya rufin gida na ruftawa, kuma saboda hannaye marasa aiki gida na zuba. 19 Mutane na shirya abinci domin dariya, ruwan inabi yana kawo jin daɗi ga rayuwa, kuɗi kuma na cika buƙata domin komai. 20 Kada ka la'anci sarki, ko a tunaninka ma, kada kuma ka la'anci mutane masu arziki a cikin ƙuryar ɗakinka. Domin tsuntsuwar sararin sama na iya ɗaukar maganganunka; duk abin da ke da fukafukai zai iya baza al'amarin.

Sura 11

1 Ka aika da gurasar ka bisa ruwaye, domin za ka same ta kuma bayan kwanaki masu yawa. 2 Ka raba da bakwai, har ma da mutane takwas, domin baka san bala'o'in da ke zuwa bisa duniya ba. 3 Idan giza-gizai suka cika da ruwa, suna juye kansu bisa duniya, idan kuma itace ya fãɗi zuwa kudu ko zuwa arewa, inda itacen ya fãɗi, nan zai tsaya. 4 Duk wanda ke kallon iska ba zai yi shuka ba, duk kuma wanda ke kallon giza-gizai ba zai yi girbi ba. 5 Kamar yadda ba ka san tafarkin iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri ke girma a cikin mahaifar mai ciki, haka nan kuma ba za ka gãne aikin Allah ba, wanda ya halicci komai. 6 Da safe ka shuka irinka; har yamma, ka yi aiki da hannuwanka bisa ga buƙata, domin ba ka san wanda zai wadata ba, ko safe ko yamma, ko wannan ko wancan, ko dukkan su biyu zasu yi kyau. 7 Gaskiya haske yana da daɗi, kuma abu mai gamsarwa ne ga idanu su kalli rana. 8 Idan wani ya rayu shekaru masu yawa, bari ya yi murna cikin dukkan su, amma bari ya yi tunani game da kwanakin duhu masu zuwa, domin zasu zama da yawa. Kowanne abu da ke zuwa turirin hayaƙi ne mai wucewa. 9 Ka yi farinciki, saurayi, a cikin ƙuruciyarka, bari kuma zuciyarka ta yi farinciki cikin kwanakin ƙuruciyarka. Ka runtumi sha'awoyi masu kyau na zuciyarka, da duk abin da ke cikin ganin idanunka. Duk da haka, ka sani cewa Allah zai kawo ka cikin hukunci domin dukkan waɗannan abubuwa. 10 Ka kori fushi daga zuciyarka, ka kuma yi watsi da duk wani zafi a cikin jikinka, saboda ƙuruciya da ƙarfinta turirin hayaƙi ne.

Sura 12

1 Ka kuma tuna da mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin kwanaki masu wuya su zo, kafin kuma shekarun su iso waɗanda za ka ce, "Ba ni da marmari a cikin su," 2 ka yi wannan kafin hasken rana da na wata da na taurari su duhunta, baƙaƙen giza-gizai kuma su dawo bayan ruwan sama. 3 Wannan lokacin ne sa'ad da masu tsaron făda zasu yi rawar jiki, kuma a tanƙwarar da mazaje masu ƙarfi, mataye masu niƙa kuma su tsaya saboda basu da yawa, waɗanda kuma su ke dubawa ta taga sun dena gani sosai. 4 Wannan lokacin ne sa'ad da aka kulle ƙofofi cikin tituna, ƙarar niƙa kuma ta tsaya, sa'ad da mazaje ke firgicewa ta muryar tsuntsu, kuma muryoyin waƙoƙin 'yanmata suka dushe. 5 Wannan lokacin ne sa'ad da mazaje suka zama masu jin tsoron tuddai da haɗarorin da ke bisa hanya, sa'ad da kuma itacen almon ke yaɗo, sa'ad da kuma fãri suke jan kansu tare, sa'ad da kuma marmari na ɗabi'a ya karye. Daga nan mutum ya tafi madawwamin gidansa masu makoki kuma su gangara bisa tituna. 6 Ka tuna da mahaliccinka kafin a datse igiyar azurfa, ko a kwankwatse kwanon zinariya, ko tulu ya farfashe a rafi, ko gargaren murɗo ruwa ya fashe a rijiya, 7 kafin turɓaya ta koma ƙasa in da ta fito, kuma ruhu ya koma ga Allah wanda ya bayar dashi. 8 "A tsakiyar turirin hayaƙi," a faɗar Malamin, "komai turirin hayaƙi ne mai bajewa." 9 Malamin mai hikima ne kuma ya koyar da mutane ilimi. Ya yi bincike kuma ya yi juyayi kuma yasa misalai masu yawa a jere. 10 Malamin ya nemi ya rubuta kuma yana amfani da zahirin, cikakkun maganganun gaskiya. 11 Maganganun mutane masu hikima kamar zugazugai suke. Kamar ƙusoshin da ake bugawa da zurfi haka nan maganganun gwanayen da suka ƙware wajen tattara misalansu, wanda makiyayi ɗaya ya koyar. 12 ‌Ɗana, ka zama a faɗake game da wani abin kuma: yin litattafai da yawa, wanda bai da ƙarshe da yawan bincike yana kawo gajiyarwa ga jiki. 13 ‌Ƙarshen al'amari bayan an ji komai, shi ne tilas ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye dokokinsa, domin wannan gabaɗaya shi ne aikin ɗan'adam. 14 Domin Allah zai kawo kowanne aiki zuwa hukunci, tare da duk wani ɓoyayyen abu, ko mai kyau ne ko mugu.

Wa‌ƙar Suleman
Waƙar Suleman
Sura 1

1 Waƙar Waƙoƙi ta Suleman ce. Matar tana magana da kanta ne 2 Oh, da ma zai sumbace ni da sumbatar bakinsa, matar kuma tana yin magana da mutumin, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi. 3 Manka na shafawa yana da ƙanshi mai daɗi, sunanka na kama da turare mai kwararowa, zuwa ga 'yammatan da kake ƙauna. 4 Ka ɗauke ni mu yi gudu tare. Matar tana yin magana da kanta. Sarkin ya kawo ni cikin ɗakunansa. Matar tana yin magana da mutumin. Muna yin murna; muna farinciki game da kai; bari muyi bukin ƙaunarka; ta fi ruwan inabi. Dai-dai ne waɗansu mata su yi sha'awar ka. Matar tana magana da waɗansu matan. 5 Ni baƙa ce amma kyakkawa, ku 'yammatan Yerusalem - baƙaƙe kamar rumfunan Kedar, kyawawa kamar labulen Suleman. 6 Kada ku ƙyale ni saboda ni baƙa ce, saboda rana ta gasa ni. 'Ya'yan mahaifiyata suna fushi da ni; sun maida ni mai tsaron garka, amma ban iya tsare tawa garkar ba. Matar tana magana da mutumin. 7 Ka gaya mani, wanda raina ya ke ƙauna, ina kake kiwon garkenka? Ina kake sa garkenka su huta da tsakiyar rana? Me yasa zan zama kamar wadda take kai da kawo wa a kusa da garkunan abokanka? 8 Mutumin yana magana da matar. Idan baki sani ba, wadda ta fi sauran mataye kyau, ki bi sawun garkena, ki kiwaci 'yan awakinki kusa da rumfar makiyaya. 9 Ƙaunatacciyata, ina kwatanta ki da goɗiya a cikin dawakin karusar Fir'auna. 10 Kumatunki kyawawa ne masu ban sha'awa, wuyanki da sarƙoƙin lu'uluai. 11 Zamu yi maki kayan ado na zinariya da azurfa. Matar tana magana da kanta. 12 Sa'ad da sarkin ya ke kwance a kan shimfiɗarsa, yana jin daɗin ƙanshin turaren. 13 Ƙaunataccena yana kama da jakar mur sa'ad da ya kwanta a tsakanin nonnana. 14 Ƙaunataccena kamar fure ya ke a garkar En Gedi. Mutumin yana magana da matar. 15 Ki saurara, kina da kyau, ƙaunatacciyata; ki saurara, kina da kyau; idanunki suna sheki. 16 Matar tana magana da mutumin. Ka saurara, kana da kyau, ƙaunataccena. Shuke-shuke masu taushi sune gadonmu. 17 Kalankuwar gidanmu ta al'ul ce, raftarmu ta fir ce.

Sura 2

1 Ni furen kallo ce ta Sharon, fure na bakin kwari. Mutumin yana magana da matar. 2 Kamar fure a cikin ƙayoyi, haka ƙaunatacciyata take a cikin 'yammata. 3 Matar tana magana da kanta. Kamar itacen tsada a cikin itatuwan jeji, haka ƙaunataccena ya ke a cikin samari. Na kan zauna a cikin inuwarsa da jin daɗi mai yawa, ina jin daɗin 'ya'yan itatuwansa. 4 Ya kawo ni gida mai ruwan inabi, tutarsa a kaina ƙauna ce. Matar tana magana da mutumin. 5 Ka farfaɗo dani da waina ka wartsakar da ni da 'ya'yan tsada, gama ƙaunata ta kasa. Matar tana magana da kanta. 6 Na yi matashin kai da hannunsa na hagu, hannunsa na dama kuma ya rungume ni. 7 Matar tana magana da sauran mata. Ku 'yammatan Yerusalem, ina so ku yi rantsuwa, da bareyi da batsiyoyi na jeji, ba zaku farka da ƙauna ba sai ta gamsu. 8 Matar tana magana da kanta. Akwai motsin ƙaunataccena! Saurara, gashi yana zuwa, yana sassarfa a kan duwatsu, yana tsalle a kan tuddai. 9 Ƙaunataccena yana kama da barewa ko ɗan kishimi; duba, ga shi a tsaye bayan katangarmu, yana leƙowa ta taga, yana kallo cikin assabari. 10 Ƙaunataccena yayi magana da ni yace, "Tashi, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, ki zo mu fita. 11 Duba, hunturu ya wuce, ruwa ya ɗauke kuma ya tafi. 12 Furanni sun fito a kan ƙasa; lokacin aske itatuwa da kukan tsuntsaye ya zo, kuma an ji motsin kurciyoyi a ƙasarmu. 13 'Ya'yan ɓaure sun nuna, inabi kuma yana sheƙi; sun bayar da ƙanshinsu. Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, mu fita. 14 Kurciyata a kogon dutse, a cikin wani asirtaccen kogon dutse, bari in ga fuskarki. Bari in ji muryarki, gama muryarki tana da zaƙi, kuma fuskarki abin ƙauna ce." Matar tana magana da mutumin. 15 Ka kamo mana diloli, 'yan dilolin da suke ɓata gonaki, gama gonarmu tana sheƙi. 16 Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce; yana kiwo a cikin furanni na annashuwa. Matar tana magana da mutumin. 17 Ka tafi, ƙaunataccena, kafin iskar asubahi ta buso inuwoyi kuma su ɓace. Ka zama kamar barewa ko kamar 'yar batsiya a kan dutse mara laushi.

Sura 3

1 Ina jiran sa da dare a bisa gadona wato shi wanda raina ya ke ƙauna, na neme shi, amma ban same shi ba. 2 Na ce da kaina, "Zan tashi in shiga cikin birni, a kan hanyoyi da wuraren shaƙatawa; zan neme shi wato shi wanda raina ya ke ƙauna." Na neme shi amma ban same shi ba. 3 Masu gãdi suka same ni sa'ad da suke aikinsu na zagayawa a cikin birni. Na tambaye su, "Ko kun gan shi wanda raina ya ke ƙauna? 4 Na wuce su kenan sai na sami shi wanda raina ya ke ƙauna. Sai na riƙe shi na hana shi ya tafi sai da na kawo shi gidan su mahaifiyata, a cikin ɗakin wadda ta ɗauki cikina. 5 Matar tana magana da waɗansu matayen. Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, da bareyi da batsiyoyin jeji, ba zaku tashi ku nuna ƙauna ba sai ta yarda. 6 Matar tana magana da kanta. Mene ne wancan mai tahowa daga jeji kamar umudin hayaƙi, tare da kayan ƙanshi masu ƙăwa, tare da dukkan hodar da 'yan kasuwa ke sayarwa? 7 Duba, gadon Suleman ne; kewaye da mayaƙa sittin, sojoji sittin na Isra'ila. 8 Dukkan su gwanayen mãshi ne ƙwararru a wajen yaƙi. Kowanne mutum yana da mashinsa a gefe, shiryayye saboda ta'adanci cikin dare. 9 Sarki Suleman yayi wa kansa kujera ta alfarma da itacen Lebanon. 10 An yi ginshiƙanta da azurfa; bayanta kuma an yi shi da zinariya, da wurin zama na ƙyallen shunayya. Daga ciki 'yammatan Yerusalem sun yi mata ado na ƙauna. Matar tana magana da matayen Yerusalem. 11 Ku je waje, ku 'yammatan Sihiyona, ku hangi Sarki Suleman, yana ɗauke da rawani wanda mahaifiyarsa ta naɗa masa a ranar aurensa, a cikin ranar da ya ke farinciki a zuciyarsa.

Sura 4

1 Oh, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata; kina da kyau. Idanunki suna kama da kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki kamar garken awaki suna gangarowa daga Dutsen Giliyad. 2 Haƙoranki kamar kazganyar da a ka yi wa sabon aski, tana fitowa daga wurin yi mata wanka. Kowanne da na kusa dashi, ba wani a cikin su da ya faɗi. 3 Leɓunanki kamar jan zare; bakinki abin ƙauna ne. Kumatunki suna sheƙi da santsi a cikin lulluɓinki. 4 Wuyanki yana kama da hasumiyar Dauda da a ka gina da jerin duwatsu, wadda a ka rataye garkuwoyi dubu a kanta, dukkan garkuwoyin sojoji ne. 5 Nonnanki kamar bareyi biyu, tagwayen bareyi, suna kiwo cikin furanni. 6 Sai asuba ta yi inuwa ta ɓace, zan je dutsen mur da tudun kayan ƙanshi. 7 Ke kyakkyawa ce a kowanne sashi, ƙaunatacciyata babu inda kike da cikas. 8 Mu tafi tare daga Lebanon, amaryata. Mu tafi tare daga Lebanon; ki tawo daga ƙololuwar Dutsen Amana, daga ƙololuwar Dutsen Senir da Harmon daga kogon zakuna, daga kogon dutsen damisoshi. 9 'Yar'uwata, kin sace zuciyata, amaryata, kin sace zuciyata, da kika dube ni sau ɗaya kawai, da abin wuyanki guda ɗaya kaɗai. 10 'Yar'uwata, ƙaunarki tana da kyau, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi, ƙanshin turarenki yafi kowanne kayan ƙanshi. 11 Amaryata, leɓunanki suna ɗigo da zuma; zuma da madara suna ƙarƙashi harshenki; ƙanshin tufafinki yana kama da ƙanshin Lebanon. 12 'Yar'uwata, amaryata tana kama da lambun da a ka kulle, kullallen lambu, maɓulɓula wadda a ka hatimce. 13 Rassanki suna kama da rukunin itatuwa masu bada 'ya'ya na musamman, da itacen lalle da nardi, 14 Nardi da saffron da man ƙanshi da kalamus da kirfi da kayan yaji iri-iri da aloyis da dukkan kayan ƙanshi mafi kyau. 15 Ke maɓulɓular lambu ce, rijiya mai sabon ruwa, ƙorama mai gangarowa daga Lebanon. Matar tana magana da mutumin. 16 Ki taso iskar arewa; ki zo iskar kudu; ki busa a kan lambuna domin kayan yaji suba da ƙanshinsu. Dămă ƙaunataccena zai zo cikin lambunsa yaci zaɓaɓɓun 'ya'yan itatuwa.

Sura 5

1 Na shigo cikin lambuna, 'yar'uwata, amaryata; na tattaro mur da kayan ƙanshina. Ina shan zumana da saƙarsa; na sha ruwan inabina da madarata. Abokai suna yin magana da mutumin da matar, Ku ci, abokai, ku sha ku bugu da ƙauna. Matar tana magana da kanta. 2 Ina barci, amma zuciyata ba barci take yi ba. Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa yana cewa, "Ki buɗe mani, 'yar'uwata, abin ƙaunata, kurciyata, ke tawa marar cikas, gama kaina ya jiƙa da raɓa, sumata kuma da danshin dare." 3 Na tuɓe rigata; in sake maida ita ne? Na wanke ƙafafuna; in sake sawa su yi dauɗa?" 4 Ƙaunataccena yasa hannunsa a kan marfin ƙofa, kuma zuciyata tana wajensa. 5 Na tashi in buɗe ƙofa saboda ƙaunataccena; hannuwana nashe-nashe da mur, yatsuna da danshin mur, a kan mariƙin ƙofa. 6 Na buɗe ƙofar saboda ƙaunataccena, amma ƙaunataccena ya juya ya tafi. Zuciyata ta nutsa sa'ad da yayi magana. Na neme shi, amma ban same shi ba; na kira shi amma bai amsa mani ba. 7 Masu gadi suka tarar dani sa'ad da suke aikinsu na zagaya birni. Suka buge ni suka ji mani ciwo; masu gadin da ke kan ganuwa suka ɗauke gyalena daga gare ni. Matar tana magana da matan birni. 8 Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, idan kuka haɗu da ƙaunataccena - Me zaku sanar da shi? - ina ciwon ƙauna. Matan birni suna magana da matar. 9 Da me ƙaunataccenki ya fi wani ƙaunataccen, ke mafi kyau a cikin mata? Me yasa ƙaunataccenki ya fi wani ƙaunataccen, da kika ce mu ɗauki alkawari kamar wannan? 10 Matar ta na magana da matan birni. Ƙaunataccena wankan tarwaɗa ne yana sheƙi, fitacce ne shi a cikin dubu. 11 Kansa zinariya ce mai tsaftar gaske; sumarsa nannaɗe take baƙa wulik kamar hankaka. 12 Idanunsa kamar kurciyoyi a bakin ƙoramar ruwa, sun yi wanka da madara, sun tsaya kamar lu'ulu'ai. 13 Kumatunsa suna kama da kwamin kayan ƙanshi, yana bada ƙanshi mai gamsarwa. Leɓunansa abin kallo ne, nashe-nashe da ruwan mur. 14 Hannayensa kamar zinariyar da a ka yi wa dajiya da lu'ulu'ai; kwankwasonsa kamar hauren giwar da a ka dalaye da duwatsun saffayar. 15 Ƙafafunsa kamar ginshiƙan da a ka yi da zinariya tsantsa, fitowarsa kamar Lebanon, zaɓabbe kamar itacen sidar. 16 Bakinsa yana da zaƙin gaske; shi cikakkaken abin ƙauna ne. Wannan shi ne Ƙaunataccena, kuma wannan shi ne abokina, 'yammatan Yerusalem.

Sura 6

1 Ina ƙaunataccenki ya tafi, ke mafi kyau a cikin mata? Wacce hanya ƙaunataccenki ya bi, domin mu neme shi tare da ke? Matar tana magana da kanta. 2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, wurin kwamin kayan ƙanshi, domin yayi kiwo a lambu kuma ya ɗebo furen kallo. 3 Ni ta ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furanni da farinciki. Mutumin yana magana da matar. 4 Kina da kyau kamar Tirzah, abin ƙaunata, ƙauna kamar Yerusalem, mai ban sha'awa da gamsarwa kamar tutocin nasara na sojoji. 5 Ki juyar da idanunki daga wajena, gama suna ɗaukar mani hankali. Gashinki yana kama da garken awakin da ke gangarowa daga magangarin Giliyad. 6 Haƙoranki suna kama da tumakin da a ka yi wa aski suna fitowa daga wurin da a ka yi masu wanka. Kowacce da 'ya'uwarta ba wadda take baƙinciki. 7 Kumatunki sumul-sumul a cikin lulluɓinki. Mutumin yana magana da kansa. 8 Akwai sarauniyoyi sittin, ƙwaraƙwarai tamanin, 'yammata kuwa sun fi a ƙirga. 9 Kurciyata, marar aibi, ita kaɗai ce; ita kaɗai ce ɗiya a wurin mahaifiyarta; tana da tagomashi a wurin matar da ta haife ta. 'Yammata sun gan ta sun kira ta mai albarka; sarauniyoyi da ƙwaraƙwarai ma sun ganta sun yabe ta: Ga abin da sarauniyoyin da ƙwaraƙwaran suka ce, 10 "Wace ce wannan da ta fito kamar tauraron asubahi, kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai ban sha'awa kamar sojoji da tutocinsu?" Mutumin yana magana da kansa. 11 Na gangara cikin rukunin itatuwa domin in ga waɗanda suke yin girma a cikin kwari, in gani ko inabi sun yi lingaɓi, in gani ko itatuwan rumman suna yin fure. 12 Na yi murna sosai na ji kamar ina cikin karusar sarki. Ƙawayen matar suna magana da ita. 13 Ki dawo, ki dawo, ke sahihiyar mata; ki dawo, ki dawo domin mu kalle ki. Matar tana magana da ƙawayenta. Me yasa kuke kallon sahihiyar mata, kamar rawa a tsakanin sojoji biyu?

Sura 7

1 Ƙafafunki sun yi kyau sosai a cikin takalmanki, ɗiyar sarki! Tsarin cinyoyinki sun yi kama da lu'ulu'ai, aikin ƙwararre a sassaƙa. 2 Cibiyarki tana kama da bangaji; dãma kada ta rasa gaurayayyen ruwan inabi. Cikinki yana kama da tarin alkama kewaye da furen kallo. 3 Nonnanki biyu suna kama da tagwayen bareyi. 4 Wuyanki yana kama da hasumiyar hauren giwa, idanunki tafki ne cikin Heshbon a ƙofar Bat Rabbim. Hancinki kamar hasumiya ce cikin Lebanon wadda ta ke fuskantar Damaskus. 5 Kanki yana bisanki kamar Karmel; gashin kanki shunayya ne mai duhu-duhu. Kitsonki ya ɗauke hankalin sarki. 6 Ke kyakkyawa ce kuma abin ƙauna, ƙaunatacciyata, tare da jin daɗi! 7 Kina da tsawo kamar itacen dabino, nonnanki suna kama da kurshen 'ya'yan itace. 8 Na ce, "Ina so in hau wannan itacen dabino; zan kama rassansa." D‌ãmã nonnanki su zama kamar kurasan zaitun, damã ƙanshin hancinki ya zama kamar 'ya'yan tsada. 9 Dãmã kitsonki ya zama kamar ruwan inabi mafi kyau, ya malala a hankali domin ƙaunataccena, ya gangara leɓunan waɗanda suke yin barci. 10 Matar tana magana da mutumin. Ni ta ƙaunataccena ce, yana marmari na. 11 Kazo, ƙaunataccena, bari mu je ƙauye; bari mu kwana a can cikin ƙauyuka. 12 Bari mu tashi da sassafe mu tafi gonaki; bari mu gani ko inabi sun yi lingaɓi, ko furanninsu sun buɗe, mu gani ko itatuwan rumman sun yi fure. A can zan baka ƙaunata. 13 Tsiretsire suna ba da ƙanshinsu; akwai dukkan zaɓaɓɓun 'ya'yan itatuwa a ƙofar wurin da mu ke tsaye, da sabo da tsoho, waɗanda na ajiye saboda kai, ƙaunataccena.

Sura 8

1 Dãmã kai ɗan'uwana ne, wanda a ka yi renon sa da nonnan mahaifiyata. Daga nan duk inda na ganka a waje, sai na sumbace ka, kuma ba wanda zai rena ni. 2 Zan yi maka jagora in kawo ka gidan mahaifiyata - ita wadda ta koyar da ni. Dã na baka ruwan inabi mai ƙanshi ka sha da wani abin sha daga itatuwan rumman. Matar tana magana da kanta. 3 Na tãda kai da hannun hagunsa hannun damansa kuma yana rungume da ni. 4 Matar tana magana da waɗansu mata. Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, ba zaku shiga tsakani ku dame mu ba sai mun gama ƙaunarmu. 5 Matan Yerusalem suna magana. Wace ce wannan da ke fitowa daga cikin jeji, tana jingina da ƙaunataccenta? Matar tana magana da mutumin. Na tashe ka a ƙarƙashin itacen tsada; a can mahaifiyarka ta ɗauki cikin ka; a can ta haife ka, ita ta haife ka. 6 Ki sani kamar hatimi a zuciyarki, kamar hatimi a hannunki, gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa. Ƙarfin kishi kamar Lahira; harshensa yana ƙonewa; harshen wuta ne mai ci, harshen wutar ya fi kowacce wuta zafi. 7 Ruwa mai yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, ko rigyawa ma ba zata iya share ta ba. Koda mutum zai bayar da dukkan abin da ya mallaka a gidansa saboda ƙauna, za a rena abin da ya bayar. 8 'Yan'uwan matar suna magana da junansu. Muna da 'yar'uwa ƙarama, nonnanta ko fitowa basu yi ba. Me zamu yi wa 'yar'uwarmu sa'ad da za a ba da ita aure? 9 Inda ita ganuwa ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Inda ita ƙofa ce, da sai mu yi mata ado da katakon al'ul. 10 Matar tana magana da kanta. Ni ganuwa ce, amma nonnana yanzu suna kama da hasumiya ƙayatacciya; Ina kama da mai kawo salama a idanunsa. Matar tana magana da kanta. 11 Suleman yana da gona a Ba'al Hamon. Ya sa waɗansu su kula da ita. Kowannen su zai kawo masa kuɗi azurfa dubu daga 'ya'yan itatuwanta. 12 Gonata, tawa ce sosai, tana gabana; Suleman, kuɗi azurfa dubu naka ne, azurfa ɗari biyu kuma na masu kula da 'ya'yan itatuwan gonar ne. 13 Mutumin yana magana da matar. Ke da kike zaune a cikin lambuna, abokaina suna sauraren muryarki; bari nima in ji muryarki. 14 Matar tana magana da mutumin. Ka yi hanzari ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko batsiya a kan duwatsu inda kayan ƙanshi suke.

Littafin Ishaya
Littafin Ishaya
Sura 1

1 Wahayin Ishaya ɗan Amoz, wanda ya gani game da Yahuda da Yerusalem, a kwanakin Uziya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuda. 2 Ku saurara, ku sammai, ke duniya, ki kasa kunne; gama Yahweh ya yi magana: "Na yi renon 'ya'ya na girmar da su, amma sun tayar mani. 3 Sã ya san mai shi, jaki kuma ya san inda ubangijinsa ke ciyar da shi, amma Isra'ila ba ta sanni ba, Isra'ila ba ta fahimta ba," 4 Kaito! Al'umma, masu zunubi, mutanen da zunubi ya danne su ƙasa, zuriyar masu aikata mugunta, 'ya'ya masu aikin lalata! Sun yi watsi da Yahweh, sun rena Mai Tsarki na Isra'ila, sun ware kansu daga gare shi. 5 Donme a ke ta dukan ku har yanzu? Me ya sa kuke ta tayarwa akai akai? Dukkan kai yana ciwo, dukkan zuciya kuma ta yi rauni. 6 Tun daga tafin sawu har zuwa kai ba inda ba ciwo; sai ciwuka ne da ƙoƙƙojewa, da sababbin raunuka; ba'a rufe su ba, ba'a tsabtace su ba, ba'a naɗe su ba, ko kuma a sa masu mai. 7 Ƙasarku ta zama kufai; an ƙone biranenku; filayenku - a idonku, bãƙi na hallaka su - an yi watsi da su, an yi kaca-kaca da su ta hannun bãƙi. 8 ‌Ɗiyar Sihiyona an barta kamar 'yar bukka a garkar inabi, kamar 'yar rumfa a lambun kukumba, kamar birnin da aka yiwa sansani. 9 Idan dã Yahweh mai runduna bai bar mana ragowa ƙalilan ba, da mun zama Sodom, mun kuma zama kamar Gomora. 10 Ku ji maganar Yahweh, ku shugabannin Sodom; ku saurari shari'ar Allahnmu, ku mutanen Gomora: 11 "Mene ne yawan hadayunku a gare ni?" in ji Yahweh. Ina da isassun baye-bayen ƙonawa na raguna, da kitsen manyan dabbobi; da jinin bijimai, da raguna, ko awaki waɗanda bana jin daɗi. 12 Lokacin da kuka zo gare ni wa ya buƙaci wannan daga gare ku, don ku tattaka harabaina? 13 Kada ku ƙara kawo baye-bayenku marasa ma'ana, na ƙi ƙonennan turare, ba zan yarda da bukukuwanku na sabon wata ba da na Asabaci - Ba zan yarda da wannan taron ba. 14 Na ƙi bukukuwanku na sababbin watanni da keɓaɓɓun ranaku; sun zama nawaya a gare ni; Na gaji da jurewa da su. 15 Don haka lokacin da kuka buɗe hannuwanku kuna addu'a na ɓoye fuskata daga gare ku; koda ya ke kun yi addu'o'i da yawa, Ba zan ji ba; hannuwanku sun cika da jini. 16 Yi wanka ku tsabtace kanku; ku cire mugayen ayyukanku daga fuskata, ku dena mugunta; 17 Ku koyi yin abin kirki; ku nemi adalci, ku dena danniya, ku yi adalci ga marayu, ku kare gwauraye." 18 Sai ku zo mu tattauna tare," in ji Yahweh; koda zunubanku sun yi kamar jangarura za su yi fari kamar ƙanƙara; koda sun yi jawur kamar jini, za su zama kamar ulun auduga. 19 In kun yarda kuka yi biyayya za ku ci mafi kyau daga cikin ƙasar, 20 Amma idan kuka ƙi kuka yi tayarwa, to takobi zata haɗiye ku," domin bakin yahweh ne ya furta haka. 21 Yadda birni mai aminci ya zama karuwa! Ita da dã take cike da adalci, amma yanzu ta cika da masu kisan kai. 22 Zinariyarki ta zama marar tsarki, ruwan inabinki ya gauraye da ruwa. 23 Sarakunanki masu tayarwa ne da kuma abokan ɓarayi; kowa na ƙaunar cin hanci, yana gudu domin ya ci haram. Ba su kare marayu ba, ba su kuma yiwa gwauruwa shari'ar adalci ba a lokacin da ta zo gare su. 24 Saboda haka sai ku ji abin da Yahweh mai runduna ya faɗi, Mai Iko na Isra'ila: "Kaiton su! Zan ɗauki fansa a kan maƙiyana, in kuma nuna ramuwata a kan magabtana; 25 Zan juya hannuna gãba daku, zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe in kawar da ƙazantarku dukka. 26 Zan maido da mahukuntanku kamar farko, mashawartanku kuma kamar na can farko; bayan wannan za a kira ku birnin adalci, gari kuma mai aminci." 27 Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma ta wurin adalci. 28 Masu tayarwa da masu zunubi za a murje su tare, waɗanda suka yi watsi da Yahweh kuma za a kawar dasu. 29 Don za ku ji kunyar wurare masu tsarki na itatuwan rimi da kuke marmari, za a kuma kunyata ta wurin lambun da kuka zaɓa. 30 Gama za ku zama kamar itacen rimi wanda ya kaɗe, kamar kuma lambun da ba ruwa. 31 Ƙaƙƙarfan mutum zai zama kamar ƙeƙasesshe, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duk za a ƙone su tare, ba kuma mai kashe su."

Sura 2

1 Abubuwan da Ishaya ɗan Amoz ya ji a wahayi game da Yahuda da Yerusalem. 2 Zai zamana a kwanaki na ƙarshe za a kafa tsaunin gidan Yahweh a can ƙololuwar tsaunuka, za a tada shi bisa dukkan tuddai, dukkan al'ummai kuma za su kwararo gare shi. 3 Mutane da yawa za su zo su ce, "Ku zo mu je kan tsaunin Yahweh, zuwa gidan Allah na Yakubu, don ya koya mana waɗansu hanyoyinsa, mu kuma yi tafiya cikin tafarkunsa." Gama daga Sihiyona shari'a za ta fito maganar Yahweh kuma daga Yerusalem. 4 Zai hukunta tsakanin al'ummai ya kuma yanke shawara ga mutane da yawa; za su mayar da takkubansu garemani, mãsunsu kuma su maida su almakashin yanke rassa; al'umma ba za ta sake tayar da takobi gãba da al'umma ba, ko kuma su sake horar da kansu don yaƙi. 5 Gidan Yakubu, ku zo, sai muyi tafiya cikin hasken Yahweh. 6 Gama ka yi watsi da mutanenka, gidan Yakubu, saboda sun cika da al'adu daga gabas suna kuma karatun sihiri kamar Filistiyawa, suna kuma shan hannuwa da 'ya'yan băƙi. 7 Ƙasarsu ta cika da zinariya da azurfa, kuma wadatarsu ba ta da iyaka; ƙasarsu kuma ta cika da dawakai, karusarsu ba ta da iyaka. 8 Hakannan kuma ƙasarsu ta cika da gumaka; suna bautawa aikin hannun mutum na hannuwansu, abubuwan da yatsunsu suka yi. 9 Za a sunkuyar da mutane ƙasa, mutum zai faɗi ƙasa; don haka kada ka tada su tsaye. 10 Ku je wurare masu duwatsu ku ɓuya a ƙarƙashin ƙasa don ku ɓoye wa hukuncin Yahweh daga kuma ɗaukakar ikonsa. 11 Za a ƙasƙantar da kallon girman kan mutum, fahariyar mutune kuma za a ƙasƙantar da ita, Yahweh kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana. 12 Gama akwai ranar Yahweh mai runduna găba da duk masu girman kai da masu kumbura, găba kuma da duk marasa kunya - 13 kuma da dukkan itatuwan Labanon waɗanda suka yi girma sosai da kuma găba da dukkan itatuwan rimi na Bashan. 14 Waccan ranar ta Yahweh mai runduna za ta yi găba da dukkan dogayen tsaunuka, da tuddai da suka yi tsayi, 15 gãba kuma da doguwar hasumiya, gãba kuma da kowacce katanga marar gwami, 16 gãba kuma da dukkan jiragen ruwa na Tarshish, gãba kuma da dukkan kyawawan abubuwan tafiya a ruwa. 17 Za a saukar da girman kan mutum ƙasa, taƙamar mutum kuma zata fãɗi; Yahweh kaɗai za a ɗaukaka a waccan rana. 18 Gumakan za su shuɗe ɗungum. 19 Mutane za su shiga kogonnin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa, domin ɓuya daga razanar Yahweh, da kuma darajar ɗaukakarsa, a lokacin daya tashi domin ya razana duniya. 20 A ranar nan mutane za su watsar da gumakansu na azurfa da zinariya da suka yiwa kansu domin su bauta masu - za su watsar da su a gidan mujiya da jemagu. 21 Mutane za su shiga cikin matsin duwatsu da kuma cikin tsagar fasassun duwatsu domin su ɓuya daga hasalar Yahweh, kuma daga darajar martabarsa, a lokacin da ya tashi domin ya razana duniya. 22 Ku dena dogara ga mutum, wanda numfashinsa a ƙofofin hancinsa ya ke, domin kuwa wacce daraja ya ke da ita?

Sura 3

1 Duba, Ubangiji Yahweh mai runduna, yana gab da ya kawar da Yerusalem da kuma goyon bayansa daga Yahuda, da samar da gurasa da kuma ruwa, 2 mutum mai iko da mayaƙi, da mai hukunci, da annabi da masu dubarsu, da dattijo; 3 jagoran hamsin, da mazaunan birnin da ake girmamawa, da mashawarci, da shahararen masassaƙi, da gwanayen masu sihirinsu. 4 Zan sa matasa kawai su zama shugabanninsu, matashi kuma zai mulke su. 5 Za a tsanantawa mutane, za su tsananta wa junansu da kuma maƙwabtansu; yaro zai wulaƙanta dattijo, ƙasƙantattu kuma su ƙalubalanci masu martaba. 6 Mutum zai sami ɗan'uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, 'Kana da riga; ka yi mulkin mu, kuma bari wannan kangon ya kasance a hannuwanka,' 7 Ranar zai yi ihu ya ce, 'Ba zan iya zama mai warkarwa ba; ba ni da gurasa ko sutura. Ba za ku mai da ni shugaban mutane ba,'" 8 Gama Yerusalem ta yi tuntuɓe, Yahuda kuma ta faɗi, saboda maganganunsu da ayyukansu na gãba da Yahweh, suna rena idanunsa na ɗaukaka 9 Suka duba shaidunsu a fuskarsu suna gãba da su; suna maganar zunubansu kamar Sodom; ba su ɓoye shi ba. Kaiton su! Gama sun kammalawa kansu bala'i. 10 Faɗawa mai adalci cewa komai zai yi dai-dai, domin za su ci 'ya'yan ayyukansu. 11 Kaiton mugu! abin zai yi masa muni sosai, gama za'a sãka masa abin da ya aikata. 12 Mutanena 'ya'yansu su ne masu wahalshe su, mata ne kuma ke mulkinsu. Mutanena masu yi maku jagora suna ɓatar da ku suna kuma rikitar da hanyar tafarkinku. 13 Yahweh na tsaye domin ya faɗi laifin mutanensa; yana tsaye domin ya zarge su. 14 Yahweh zai zo da hukunci gãba da dattawan mutanensa da kuma shugabanninsu: "Kun lallatar da garkar inabi; ganimar matalauci na gidajenku. 15 Donme kuke ƙuje mutanena, kuke kuma musgunawa matalauta?" Wannan furcin Ubangiji Yahweh mairunduna ne. 16 Yahweh yace saboda 'yan matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya suna ɗaga wuya sama, suna kuma jujjuya idanunsu, suna rangwaɗa a lokacin da suke tafiya kayan adon ƙafafunsu na ƙãra. 17 Saboda haka Ubangiji zai saukar masu da ciwon ƙuraje a bisa kawunan 'yan matan Sihiyona, Yahweh kuma zai sa su yi saiƙo. 18 A wannan ranar Ubangiji zai cire masu kyawawan kayan adonsu na ƙafa, da maɗaurin kansu, da kayan adonsu masu siffofin wata, 19 da 'yankunne, da abin hannu, da kayan lulluɓi; 20 'yankwalaye, da sarkar ƙafa, da ɗamara; da akwatunan turare, da layunsu na neman sa'a. 21 Zai cire zobba da kayan adon hanci; 22 da suturun bukukuwa, da alkyabbobi, da mayanai, da jakkunan hannu; 23 da madubai na hannu, da linin mai kyau, da ƙyallayen kai, da kuma zannuwa. 24 A maimakon ƙanshin turare za su yi wari; a maimakon sarƙa kuma igiya; a maimakon gyararriyar suma kuma saiƙo, a maimakon sutura mai ƙawa kuma kayan makoki; tsaga maimakon kyau. 25 Mazajenku za su fãɗi da takobi, jarumawanku kuma za su fãɗi a wurin yaƙi. 26 Ƙofofin Yerusalem za su yi makoki da baƙinciki; za ta kuma zauna a ƙasa a kaɗaice.

Sura 4

1 A wannan rana mata bakwai za su riƙe namiji ɗaya su ce, "Mă ciyar da kanmu, mu yiwa kanmu suturar da za mu sa. Amma ka yarda a kira mu da sunanka domin a kawar mana da kunya." 2 A wannan ranar rassan Yahweh za suyi kyau da kuma ɗaukaka, 'ya'yan itatuwan ƙasar kuma za su yi zaƙi, da kuma jin daɗi ga waɗanda suka ragu a Isra'ila. 3 Zai kasance a wannan ranar da wanda ya ragu a Sihiyona da kuma wanda ya ragu a Yerusalem za a kira shi mai tsarki, da kuma duk wanda aka rubuta sunansa a matsayin mazaunin Yerusalem. 4 Wannan zai faru a lokacin da Ubangiji zai share tsaurin idon 'yan matan Sihiyona, ya kuma goge jinin da ya manne daga tsakiyar Yerusalem, ta wurin ruhun hukunci da kuma ruhun harshen wuta. 5 Sa'an nan dukkan sassan Tsaunin Sihiyona da kuma kan wuraren taruwarta, Yahweh zai yi girgije da hayaƙi da rana, da kuma hasken harshen wuta da dare; zai zama inuwa a kan dukkan ɗaukaka. 6 Za ta bada inuwa da rana daga zafi, da kuma mafaka da kuma maɓoya daga hadari da ruwan sama.

Sura 5

1 Sai in raira waƙa ga ƙaunataccena, waƙar ƙaunataccena game da garkar inabinsa. Wadda nake ƙauna sosai yana da garka a tudu mai dausayi. 2 Ya gyara ta, ya cire duwatsu, ya kuma shuke ta da irin inabi mai matuƙar daraja. Ya gina hasumiya a tsakiyar gonar, ya kuma kafa wurin matse ruwan inabi. ya jira ta bada 'ya'ya amma sai 'ya'yan inabin jeji kawai ta yi. 3 To yanzu, mazauna Yerusalem da mutanen Yahuda, ku yi hukunci tsakanina da garkar inabita. 4 Me kuma zan ƙara yi wa garkar inabita, da ban taba yi mata ba? Lokacin da na dube ta ta bada 'ya'ya me yasa ta bada 'ya'yan inabin jeji? 5 Yanzu zan fada maku abin da zan yi da garkata: Zan cire shingen, zan mayar da ita makiyaya, zan rushe garunta, za a kuma tattaketa ƙasa 6 Zan watsar da ita, ba zan yi mata noma ko kaftu ba. A maimakon haka ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro a cikin ta. Zan kuma umarci giza-gizai kada su yi ruwa a kanta. 7 Domin garkar inabin Yahweh mai runduna ita ce gidan Isra'ila, mutanen Yahuda kuma dashensa ne da ya ke jin daɗi; ya jiraci adalci, a maimakon haka sai kisa; a maimakon adalci kuma, sai ihun neman taimako. 8 Kaiton su masu yawo gida gida, waɗanda ke haɗa wurare daga wannan wuri zuwa wancan wuri, har sai ba ɗakunan da suka ragu sai kai kaɗai za a bari a cikin ƙasar! 9 Yahweh mai runduna ya faɗa mani, gidaje da yawa za su zama kufai, har ma da manyan gidajen nan masu ban sha'awa, ba mazauna. 10 Domin kadada goma ta garkar inabi za ta bada garwa ɗaya ne kacal, sannan mudun iri zai bada ɗangongoni ne kawai. 11 Kaiton masu tashi da asuba domin neman ƙaƙƙarfan ruwan inabi, waɗanda ba su kwantawa da wuri har sai ruwan inabi ya bugar da su. 12 Suna shagali da sarewa da garaya da tambari da algaita da ruwan inabi, amma ba su fahimci aikin Yahweh ba Ba su kuma yi la'akari da aikin hannuwansa ba. 13 Saboda haka mutanena suka tafi bautar talala saboda rashin fahimta; Shugabaninsu masu daraja suka zauna a cikin yunwa, talakawansu kuma ba su da wani abin sha. 14 Domin haka Lahira ta maida marmarinta babba ta kuma buɗe bakinta sosai; da masanansu da mutanensu da shugabanninsu da masu duba na cikinsu da kuma waɗanda ke murna a cikin su, sun ɗunguma Lahira. 15 Za a tilastawa mutum ya sunkuya ƙasa, Za'a ƙasƙantar da mutum; idanun masu taƙama za su wulaƙanta. 16 Yahweh mai runduna zai ɗaukaka cikin adalcinsa, Allah Mai Tsarki nan zai nuna kansa da tsarki cikin adalcinsa. 17 Bayan wannan sai tumakai su yi kiwo kamar a makiyayarsu, a kuma cikin kangaye, 'yan raguna za su yi kiwo kamar bãƙi. 18 Kaiton masu cire laifofinsu da sarƙoƙi marasa amfani da masu birgima cikin zunubi kamar an ɗaure su da igiya. 19 Kaiton masu cewa, "Bari Allah ya yi sauri, bari ya hanzarta ya yi aikinsa, domin mu ga ya faru; kuma bari shirye-shiryen Mai Tsarki na Isra'ila su zo, domin mu sansu." 20 Kaiton masu kiran mugunta nagarta, nagarta kuma mugunta; waɗanda suka mai da duhu haske, haske kuma duhu; suka kuma mai da ɗaci zaƙi, zaki kuma ɗaci! 21 Kaiton masu hikima a fuskarsu, masu daraja kuma a cikin fahimtarsu! 22 Kaiton shahararrun shan ruwan inabi, da waɗanda s ka shahara a wajen gauraya ruwan inabi mai ƙarfi; 23 Waɗanda suka ƙyale mugu saboda a biya su, suka kuma zalunci marar laifi a kan hakinsa! 24 Saboda haka kamar yadda harshen wuta ke lanƙwame kututture, kamar kuma yadda busasshiyar ciyawa ke shiga harshen wuta haka saiwarsu za ta mutu, kyansu kuma ya gushe kamar ƙura. Wannan zai faru saboda sun ƙi shari'un Yahweh mai runduna, saboda kuma sun rena maganar Mai Tsarki na Isra'ila. 25 Saboda haka fushin Yahweh yana kan mutanensa. Ya miƙa hannusa gãba da su ya kuma hore su. tsaunuka sun razana, gawawwakinsu sun zama kamar sharar da a ka zubar a bakin hanyonyi. A cikin duk waɗannan abubuwa fushinsa bai sauka ba; a maimakon haka hannunsa har yanzu yana miƙe. 26 Zai ɗaga alama ta tuta don al'ummai masu nisa zai kuma yi fĩto ga waɗanda ke ƙarshen duniya. Ku duba, za su zo a guje a kan lokaci kuma. 27 Ba yagewa ko tuntuɓe a cikinsu; babu masu rurrumi ko bacci. Ba su kuma kwance ɗammararsu ba, ko kuma shimfiɗar takalmansu da ta yage. 28 Kibawunsu na da tsini kuma dukkan bakkunansu a tanƙware; kofatan dawakansu kuma kamar curin dutse, gargaren karusarsu kuma kamar hadari ya ke. 29 Gurnaninsu kuma kamar na zãki; za su yi ruri kamar matasan zãki. Za su yi ruri su fizge abin da suka farauto su kuma ja shi su tafi, ba kuma wanda zai kuɓutar da su. 30 A wannan ranar za su yi ruri kamar yadda tekuna ke ruri. In wani ya dudduba ƙasar zai ga duhu da shan wuya; ko ma da haske za a mai da shi duhu ta wurin giza-gizai.

Sura 6

1 A cikin shekarar da sarki Uziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kursiyi; yana da tsayi da kuma martaba, gezar tufarsa kuma ta cika haikalin. 2 A sama da shi kuma da serafim; kowannen su yana da fuka-fukai shida; kowannen su yana rufe fuska da guda biyu, ya kuma rufe ƙafafu da guda biyu, yana kuma shawagi da guda biyu. 3 Suna kiran juna suna cewa, "Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki," shi ne Yahweh mai runduna! Dukkan duniya ta cika da ɗaukakarsa." 4 Harsashen ginin ƙofofinsa sun girgiza a lokacin da suka tada murya, sai kuma hayaƙi ya cika gidan. 5 Sa'an nan na ce "kaitona! Gama na hallaka domin ni mutum ne dake da leɓuna marasa tsarki, ina kuma rayuwa a cikin mutane marasa tsarkin leɓuna, saboda idanuna sun ga Sarki, Yahweh, Yahweh mai runduna!" 6 Daga nan sai ɗaya daga cikin serafim ɗin yawo shawagi wurina; yana da garwashi jawur a hannunsa, wanda ya ɗauko daga bagadi. 7 Sai ya taɓa bakina da shi ya kuma ce, "Duba wannan ya taɓa leɓunanka; an kawar da laifofinka, an kuma gafarta zunubanka." 8 Na ji muryar Ubangiji tana cewa, "Wa zan aika; wa kuma zai tafi dominmu?" Daga nan sai na ce, "Ga ni; ka aike ni." 9 Ya ce ka je ka faɗawa mutanen nan, za ku ji amma ba za ku gane ba; za ku gani amma ba za ku sani ba.' 10 Mai da zuciyarsu ta zama marar tunani, kunnuwansu kuma su kurmance, idanunsu kuma su makance. A maimakon haka za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su kuma fahimta da zuciyarsu, kuma daga nan su juyo su kuma warke." 11 Sai na ce Ubangiji har tsawon wanne lokaci? '"Ya amsa "Har sai birane sun zama kangaye ba mazauna a ciki, gidaje kuma sun zama ba mutane, ƙasar kuma ta zama yasasshiya, 12 Har sai Yahweh ya kora mutanen waje, kaɗaicin ƙasar kuma ya haɓaka. 13 Koda kashi ɗaya cikin goma na mutanen suka ragu a cikinsa, duk da haka za a ƙara hallaka shi; zai zama kamar ranar da aka datse itacen rimi wanda gungumensa ya ragu, iri mai tsarki na cikin kututture."

Sura 7

1 A kwanakin Ahaz ɗan Yotam ɗan Uziya, sarkin Yahuda, Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya da sarkin Isra'ila, suka je Yerusalem domin su yaƙe ta, amma ba su iya yin nasara da ita ba. 2 Sai aka sanar da gidan Dauda cewa Aram ya haɗa kai da Ifraim. Sai ya tsorata, haka ma zuciyar mutanensa, kamar yadda itatuwan jeji ke kaɗawa a cikin iska. 3 Sai Yahweh yace da Ishaya, "Ka tafi tare da ɗanka Shiya-Yashub ku sadu da Ahaz a ƙarshen kwararon babban wurin da aka datse ruwa, a kan hanya zuwa Filin masu wanki da guga. 4 Ka ce da shi, 'Ka lura, ka tsaya a natse, kada ka ji tsoro ko ka razana saboda waɗannan 'yan guma-gumai na wuta, ta wurin zafin fushin Rezin da Aram, da Feka ɗan Remaliya. 5 Aram, Ifraim da ɗan Remaliya sun ƙulla mugun abu găba da kai; sun ce, 6 "Bari mu kai wa Yahuda hari mu firgita ta, mu kuma fasa cikinta mu naɗa sarkinmu a can, wato ɗan Tabil." 7 Ubangiji Yahweh yace, "Ba zai faru ba; ba zai faru ba, 8 saboda shugabar Aram ita ce Damaskus, shugabar Damaskus kuma ita ce Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar, za'a watsa Ifraim kuma ba za su zama al'umma ɗaya ba 9 Shugabar Ifraim ita ce Samariya, shugaban Samariya kuma shi ne ɗan Remaliya. Idan ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya ba, tabbas ba za ku zama da kariya ba.""' 10 Sai Ubangiji ya sake yin magana da Ahaz, 11 "Ka roƙi alama daga Yahweh Allahnka; ka yi roƙonta ko a cikin zurfafa ko a can sama." 12 Amma Ahaz yace "ba zan yi tambaya, ko kuma in gwada Yahweh ba." 13 Domin haka Ishaya ya amsa, "Ku saurara, gidan Dauda. Ya ku mutane ashe bai isheku ba ku gwada haƙurin jama'a? Dole ne kuma ku gwada haƙurin Allahna? 14 Saboda haka Ubangiji da kansa zai ba ku alama, duba budurwa za ta yi juna biyu za ta haifi ɗa, za a kira sunansa Imanuwel. 15 Zai ci fãra da ruwan zuma a lokacin da ya ƙi mugunta ya kuma zaɓi nagarta. 16 Gama kafin yaron ya san ƙin mugunta da zaɓar nagarta, ƙasar sarakunan nan guda biyu da kuka ji tsoronsu za ta zama kufai. 17 Yahweh zai sauko maku da wata rana a kan mutanenku da gidan mahaifanku ranar da ba a taɓa ganin ta ba tun da Ifraim ya bar Yahuda - zai aiko maku da sarkin Asiriya." 18 A wannan lokacin Yahweh zai yi kira na tashi daga ƙoramu masu nisa na Masar, kuma da na zuma daga ƙasar Asiriya. 19 Duk za su zo su zauna a dukkan kwazazzabai, a cikin kogonnin duwatsu, a kan dukkan ƙayayuwa, da a kan dukkan makiyaya. 20 A wannan lokacin Ubangiji zai yi aski da rezar da aka yi haya daga hayin Kogin Yuferitis - sarkin Asiriya - da kai da gashin ƙafafu; za a kuma share gemu. 21 A wannan rana mutum zai yi kiwon 'yar karsana da tumaki guda biyu, 22 Kuma saboda yalwar madarar da za su bayar, zai ci cuku, ga duk waɗanda suka ragu a ƙasar za su ci cuku da ruwan zuma. 23 A wannan lokacin, a inda a kwai dubu na inabi da ya kai azurfa dubu, a wurin ba za a ga komai ba sai sarƙarƙiya da ƙayayuwa. 24 Mutane za su fita farauta da bãka, saboda dukkan ƙasar za ta cika da ƙaya da sarƙaƙiya. 25 Za su tsaya nesa da dukkan tuddan da aka nome da fartanya, domin tsoron sarƙaƙiya da ƙayayuwa; amma zai zama wurin da dabbobi da tumaki za su yi kiwo.

Sura 8

1 Yahweh yace mani, "Ka ɗauki babban allo ka yi rubutu a kansa, 'Maha-Shalal-Hash-Baz.' 2 Zan kira amintattun shaidu su tabbatar mani, Yuriya Firist, da Zakariya ɗan Yebirekiya." 3 Na je wurin annabiya, ta kuwa yi juna biyu ta haifi ɗa. Sai Yahweh yace mani, "Ka kira sunansa 'Maha-Shalal-Hash-Baz.' 4 Gama kafin yaron ya san yin kuka har ya furta, 'Babana da Mamata,' sarkin Asiriya zai kwashe dukiyar Damaskus da ganimar Samariya." 5 Sai Yahweh ya sake yi mani magana, 6 "Saboda waɗannan mutanen sunƙi tausassun ruwayen Shilowa, amma suna murna kan Rezin da ɗan Remaliya, 7 don haka Ubangiji ya kusa kawo ruwayen Kogi a kansu, masu ƙarfi da yawa, sarkin Asiriya da dukkan ɗaukakarsa. Za ya hau kan dukkan magudanansa ya yi ambaliya kan iyakokinsa. 8 Rafin zai shafe har zuwa cikin Yahuda, ambaliyar zata ratsa, har sai ta kai wuyanka. Miƙawar fikafikansa zai cika iya faɗin ƙasarka, Imanuwel." 9 Ku mutanen za a daddatsa ku gunduwa-gunduwa. Ku saurara, dukkan ku manisantan ƙasashe: ku yi ɗammara domin yaƙi za a kuwa daddatse ku, ku yi shiri za a kuwa gutsuttsuraku. 10 Ku yi shiri, amma bãza ku iya aiwatarwa ba; ku ba da umarni, ba za a kiyaye ba, gama Allah yana tare da mu. 11 Yahweh ya yi magana da ni, da hannunsa mai ƙarfi a kaina, ya dokace ni kada in yi tafiya cikin tafarkin mutanen nan. 12 Kada ku kira maƙida akan kowanne abin da mutanen nan suke kira maƙida, kada ku ji tsoron abin da suke tsoro, kada ku firgita kuma. 13 Amma Yahweh mai runduna za ku girmama a matsayin maitsarki; shi ne wanda dole za ku ji tsoro, shi ne dole zai zama abin razanar ku. 14 Zai zama wuri maitsarki; amma zai zama dutse abin bugu da pã abin sa tuntuɓe ga dukan gidajen Isra'ila, zai zama tarko da azargiya ga mutanen Yerusalem. 15 Mutane da yawa za su yi tuntuɓe a kansa su faɗi su karye, su zama azargiya kuma su kamu. 16 Ka ɗaure shaida ta, ka hatimce umarni na musamman, ka kuma bada su ga alma'jiraina. 17 Zan jira Yahweh, wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yakubu; Zan jira shi. 18 Duba, Ni da 'ya'yan da Yahweh ya bani domin alamu ne da al'ajibai cikin Isra'ila daga Yahweh mai runduna, wanda ya ke zaune akan Tsaunin Sihiyona. 19 Za su ce maku, "Ku tuntuɓi mãsu duba da bokaye" waɗanda suke kashe murya suna surkulle. Shin ko mutane ba za su tuntuɓi Allahnsu ba? za su tuntuɓi matattu a madadin masu rai? 20 Ga shari'a da kuma shaida! idan ba su faɗi waɗannan abubuwan ba, saboda ba bu hasken wayewar gari a garesu. 21 Za su ratsa ta cikin ƙasa da babbar damuwa da yunwa. Idan suna jin yunwa, za su yi fushi su la'anta sarkinsu da Allahnsu, yayin da suka ɗaga fuskokinsu sama. 22 Za su du bi duniya kuma za su ga wahala, duhu, da azabtarwa. Za a koresu zuwa cikin ƙasar duhu.

Sura 9

1 Amma za a kawar da baƙin duhun daga wurin ta wadda take cikin azaba a dã. A kwanakin da ya ƙasƙantar da ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, amma cikin kwanaki na ƙarshe zai ɗaukakata, ta hanyar teku, ƙetaren Yodan, Galili ta al'ummai. 2 Mutanen da suka yi tafiya cikin duhu sun ga babban haske; waɗanda suka zauna cikin ƙasa ta inuwar mutuwa, haske ya haskaka bisansu. 3 Ka riɓanya al'umma; ka ƙara farincikin su. Suna murna gaban ka kamar murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke raba ganima. 4 Gama karkiyar kayansa, katakon dake gicciye da kafaɗarsa, sandar mai azabta masa, ka rafke su kamar a ranar Midiyan. 5 Gama dukkan takalman mayaƙa cikin hayaniyar yaƙi da tufafi mirginannu cikin jini za a ƙone su, su zama abin rura wuta. 6 Gama a gare mu an haifi yaro, a gare mu an bada ɗa; mulki kuma zai kasance a kafaɗarsa; za a kira sunansa Al'ajibi Maishawara, Allah maigirma, Uba Madawwami, Sarkin Salama. 7 Ƙaruwar mulkinsa da salama bata da iyaka, ya yin da ya ke mulki kan kursiyin Dauda, da bisa mulkinsa, a kafa shi a kuma tabbatar dashi cikin gaskiya da adalci daga wannan lokaci har abada kuma. Himmar Yahweh Mairunduna zai yi wannan. 8 Sai Ubangiji ya aika da magana gãba da Yakubu, sai ta faɗo kan Isra'ila. 9 Dukkan mutane za su sani, har Ifraim da mazaunan Samariya, waɗanda suke magana cikin girmankai da taurin zuciya, 10 "Tubala sun faɗi, amma za mu sake gini da sassaƙaƙƙun duwatsu; an sare durumi ƙasa, amma zamu sa itatuwan sidas amadadinsu." 11 Domin haka Yahweh zai tayar masa da Rezin, abokin gabarsa, zai harzuƙa maƙiyansa, 12 Suriyawa daga gabas, da kuma Filistiyawa daga yamma. Da baki buɗe za su cinye Isra'ila. A cikin waɗannan duka, fushinsa bai juya ba; maimakon haka, hannunsa har yanzu a miƙe ya ke. 13 Duk da haka mutane ba za su juya wajen shi wanda ya buge su ba, ba kuwa za su nemi Yahweh mai runduna ba. 14 Domin haka Yahweh zai datse ma Isra'ila kai da wutsiya, reshen dabino da gazarinsa, cikin rana ɗaya. 15 Shugaba da mutum maidaraja su ne kai; da annabi mai koyar da ƙarya shi ne wutsiya. 16 Waɗanda ke shugabantar jama'ar nan sun karkataddasu, waɗanda suke binsu kuma an haɗiye su. 17 Domin wannan Ubangiji ba za ya yi murna da majiya karfinsu ba ba kuma zai tausayawa marayunsu da gwaurayensu ba, domin kowannensu marasa allahntaka ne da masu aikata mugunta, kowanne baki kuma yana faɗin wauta. Cikin waɗannan duka fushinsa ba zai juya ba; maimakon haka, hannunsa har yanzu a miƙe ya ke. 18 Mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa; tana ƙone ƙungurmin daji, wanda ke tashi cikin tuƙuƙin hayaƙi. 19 Ta wurin hasalar Yahweh mairunduna ƙasa ta ƙone, mutane kuma sun zama kamar abin rura wuta. Ba mutumin daya bar ɗan'uwansa. 20 Za su fizge abinci a hannun dama duk da haka za su ji yunwa, za su ci abinci a hannun hagu duk da haka ba za su ƙoshi ba. Kowanne zai ci naman dantsen hannunsa. 21 Manasse zai lanƙwame Ifraim, Ifraim kuma Manasse, tare kuma za su kaima Yahuda farmaki. Cikin waɗannan duka, fushinsa yana nan, maimakon haka, har yanzu hannunsa a miƙe ya ke.

Sura 10

1 Kaitonsu waɗanda ke zartar da hukuncin zalunci suke rubuta umarnan rashin gaskiya. 2 Suna hana wa mabuƙata adalci, mutanena suna yi masu ƙwace su hana masu haƙƙinsu, gwamraye sun zama ganimarsu, sun maida marayu ganimarsu! 3 Me za kuyi a ranar hukunci lokacin da hallakarwa ke zuwa daga nesa? wurin wa za ku gudu domin neman taimako, kuma ina za ku bar dukiyarku? 4 Ba abin daya rage, za ku laɓe ƙarƙashin 'yan sarƙa, ko ku faɗi tsakanin kisassu. Cikin dukkan waɗannan abubuwa, fushinsa ba zai sauka ba; maimakon haka, har yanzu hannunsa a miƙe ya ke. 5 Kaiton Asriyen, kulkin fushina, sandar hannunka a bin harzuƙata ne! 6 Na aike shi gãba da al'umma mai girmankai, gãba da mutane masu ɗauke da ambaliyar fushina. Na umarce shi ya ɗauki ɓãtattu, ya kwashi ganima, ya tattake su kamar laka cikin tituna. 7 Amma ba haka ya ke nufi ba, bai kuma yi tunanin haka ba. Amma shi a cikin zuciyarsa ne ya kawar da al'umma masu yawa. 8 Gama ya ce, "Shugabannina ba sarakuna ba ne dukkansu? 9 Kalno ba kamar Karkemish ba ce? Hamat ba kamar Arfad ba ce? Samariya ba kamar Damaskus ba ce? 10 Kamar yadda hannuna ya yi nasara da mulkokin tsafi, wanda ƙerarrun gumakansu sun fi na Yerusalem da Samariya, 11 kamar yadda na yi da Samariya da gumakanta marasa amfani, ba zan yi irin wannan kuma ga Yerusalem da gumakanta ba?" 12 Sa'ad da Ubangiji ya gama aikin sa akan Tsaunin Sihiyona da bisa Yerusalem, zan hukunta jawabin faɗin ran sarkin Asiriya da homarsa. 13 Domin yace, "Da karfina da hikimata Na yi aiki. Ina da fahimta, na kuma kawas da iyakoki na mutane. Na sace taskokin su, kamar sã na nakasadda mazauna nan wurin. 14 Hannuna ya tsaya, kamar sheƙa, dukiyar dangogi, kuma kamar wanda ya tattara ƙwan da aka ƙyale. Na tattaro dukkan duniya. Ba bu wanda ya motsa fiffike, ko ya buɗe baki balle suyi ƙara." 15 Ko gatari zai iya yiwa mai sara da shi alfahari? ko zarto zai iya ɗaukaka kansa bisa wanda ya ke yanka da shi? sai kace sanda zata iya ɗaga mai ɗaukar ta, ko kuma kulkin katako zai ɗaga mutum. 16 Domin haka Yahweh mai runduna zai aiko da ramewa cikin jarumawansa; ƙarƙashin ɗaukakarsa kuma za a kunna ƙonewa kamar wuta. 17 Hasken Isra'ila kuma zai zama wuta, Mai Tsarkin nasa kuma harshen wuta, za ya ƙone ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ya cinye su rana ɗaya. 18 Yahweh kuma zai cinye darajar kurminsa da gonarsa mai albarka, rai duk da jiki; zai zama kamar lokacin da ran marar lafiya ya suma. 19 Sauran itatuwan kurmin za su zama 'yan kaɗan, ƙaramin yaro zai iya ƙirga su. 20 A wannan rana, ringin Isra'ila, da iyalin Yakubu waɗanda suka tsira, ba za su dogara ga wanda ya ci nasara da su ba, amma lallai za su dogara ga Yahweh, MaiTsarkin nan na Isra'ila. 21 Ringi na Yakubu za su juya zuwa ga Allah mai iko. 22 Ko da shike mutanenka, Isra'ila, suna kama da yashin teku, sai ringi daga cikin su za su komo. An zartar da dokar Hallakarwa, kamar yadda adalci mai malalowa ya wajabta. 23 Gama Yahweh mai runduna, daf ya ke da hallakar da dukkan ƙasar kamar yadda ya ayyana. 24 Domin wannan Ubangiji Yahweh mai runduna yace, "Mutanena da suke zaune cikin Sihiyona, kada ku ji tsoron Asiriyen. Zai buge ku da sanda ya ɗaga kerensa ga bada ku, kamar yadda Masarawa suka yi. 25 "Kada ku ji tsoron sa, gama a cikin ɗan lokaci kaɗan fushina a kanku zai ƙare, fushi na zai kai ga hallakarwarsa." 26 Daga nan Yahweh mai runduna zai tayar da bulala akansu, kamar yadda ya fatattaki Midiyan a Tsaunin Oreb. Zai ɗaga sandarsa bisa teku ya ɗaga ta sama kamar yadda ya yi a Masar. 27 A wannan rana, nauyin kayansa an ɗauke shi daga kafaɗarki kuma karkiyarsa an ɗauke daga wuyanki, kuma karkiyarki zata lalace saboda ƙibar. 28 Maƙiyi ya zo Ayiyat ya ratsa ta Migron; a Mikmash ya ajiye abubuwan daya tanada. 29 Sun ƙetare suka sauka a Geba. Rema tana rawar jiki Gibiya ta Saul kuma ta gudu. 30 Ki yi kuka da ƙarfi, ɗiyar Galim! ki saurara, Laisha! ke talautattar Anatot! 31 Madmena tana gudu, mazaunan Gebim sun gudu domin su ɓuya. 32 A wannan rana zai sauka a Nob zai girgiza damtsensa a tsaunin ɗiyar Sihiyona, tudun Yerusalem. 33 Duba, Ubangiji Yahweh mai runduna zai sassare rassa da ban razana; itatuwan da suka fi tsawo za'a sare su, maɗaukaka kuma za'a ƙasƙantar dasu. 34 Za ya sassare kuramen jeji da gatari, Lebanon kuma cikin ɗaukakarsa zata faɗi.

Sura 11

1 Zai toho daga cikin kututturen Yesse, reshe kuma daga cikin sa zai bada 'ya'ya. 2 Ruhun Yahweh kuma zai zauna bisansa, Ruhun hikima da fahimta, da Ruhun umarni da iko, da Ruhun sani dana tsoron Yahweh. 3 Marmarin sa zai kasance tsoron Ubangiji; ba zaiyi shari'a bisa ga abin da idanunsa suka gani ba, ba kuwa zai yi hakunci bisa ga abin da kunnensa ya ji ba. 4 Maimakon haka zai shar'anta talakwa bisa ga adalci bisa ga dai-daita kuma zai yanke shawara ga masu tawali'u na duniya. Zai bugi duniya da sandar bakinsa, da numfashin leɓunansa kuma zai kashe miyagu. 5 Adalci zai zama ɗammarar ƙugunsa, aminci kuma ɗammara kewaye da kwatangwalonsa. 6 Kyarkeci zai zauna tare da rago, damisa kuma zata kwanta tare da ɗan'akuya, ɗan maraki da ɗan zaki tare da kiwataccen ɗan maraƙi, za su zauna tare, ɗan yaro kuwa zai bishe su. 7 Saniya da kerkeci za su yi kiwo tare, 'ya'yansu za su kwanta wuri ɗaya. Zaki zai ci ciyawa kamar sã. 8 Jariri zai yi wasa a bakin ramin maciji, yayayyen yaro kuma zai sa hannunsa a kogon maciji. 9 Ba za su cutar ko hallakar ba a ko'ina kan tsaunina mai tsarki; gama duniya za ta cika da sanin Yahweh, kamar yadda ruwaye suka rufe teku. 10 A wannan rana, tushen Jesse zai tsaya a matsayin tuta ga mutane. Al'ummai za su neme shi, wurin hutun sa kuma zai zama abin ɗaukaka. 11 A wannan rana, Ubangiji zai sake sa hannunsa domin ya fanshi sauran mutanensa da suka rage a Asiriya, Masar, Fatros, Kush, Ilam, Shina, Hamat, da tsibirai na teku. 12 Zaya kafa tuta domin al'ummai ya tattara korarru na Isra'ila warwatsattsu na Yahuda daga kusurwoyi huɗu na duniya. 13 Zai juyar da kishin Ifraim, masu azabtar da Yahuda kuma zai datse su. Ifraim ba zai yi kishin Yahuda ba, Yahuda kuma ba zai ƙara kishin Ifraim ba. 14 Maimakon haka zasu sauko bisa tuddan Filistiyawa a wajen yamma, tare za su washe 'ya'yan gabas. Za su kai hari ga Idom da Mowab Mutanen Ammon kuma za su yi masu biyayya. 15 Yahweh zai hallakar da dukkan kwarurruka na Tekun Masar. Da iskarsa mai ƙonewa zai karkaɗe hannunsa bisa kan Kogin Yufiretis zai raba su zuwa rafuffuka bakwai, domin a iya ƙetarewa da takalmi a ƙafa. 16 Zai kasance akwai karabka domin sauran mutanensa, waɗanda suka ragu za su dawo daga Asiriya, kamar yadda akayi ga Isra'ila cikin ranar da suka taso daga ƙasar Masar

Sura 12

1 A wannan rana za ka ce, "Zan gode maka, Yahweh. Koda shike ka yi fushi da ni, fushinka ya juya, ka kuwa yi mani ta'aziya. 2 Duba, Allah shi ne cetona; zan dogara, ba kuwa zan ji tsoro ba, gama Yahweh, hakika, ƙarfina ne da waƙata. Ya zama cetona," 3 Da farinciki za ku ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto. 4 A wannan rana za ku ce, "Kuyi godiya ga Yahweh ku kuma kira ga sunansa; ku bayyana ayyukan sa a wurin al'ummai, ku yi shelar sunansa maɗaukaki ne. 5 Ku raira ga Yahweh, gama ya aikata al'amura mafifita, bari wannan ya zama sananne ko'ina a duniya. 6 Ku tada murya ku yi sowa ta murna, ku mazaunan Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra'ila dake tsakiyarku mai girma ne."

Sura 13

1 Kenan game da Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa: 2 A bisa buɗaɗɗen tsauni ku ɗaga tutar alama, ku tada murya gare su, ku kaɗa hannu gare su domin su shigo ƙofofin hakimai. 3 Na umarci tsarkakana, I, Na kira masu iko na su aiwatar da fushina, su waɗanda nake fahariya da su da waɗanda aka ɗaukaka. 4 Hayaniyar mutane cikin duwatsu, sai kace na mutane da yawa! Hayaniya ta mulkokin al'ummai a tattare! Yahweh mai runduna yana tattara runduna domin yaƙi. 5 Sun zo daga ƙasa mai nisa, tun daga iyakacin sama. Yahweh kenan da kayan yakinsa na hukunci, domin hallaka dukkan ƙasa. 6 Ku yi kuka, gama ranar Ubangiji ta kusa; zata zo da hallakrwa daga Mai iko. 7 Domin haka dukkan hannuwa za su maƙale, kowacce zuciya kuma za ta narke. 8 Za su firgita; zafi da baƙinciki za su kama su, kamar mace cikin naƙuda. Za su dubi junansu cikin mamaki, fuskokinsu za su zama kamar gaushen wuta. 9 Duba, ranar Yahweh tana zuwa da hasala da fushi mai zafi, za'a maida ƙasar kango, za'a hallakar da masu zunubin daga cikin ta. 10 Taurarin sama ba za su bada haskensu ba. Rana za ta duhunta a lokacin fitowarta, wata kuma ba zai haskaka ba. 11 Zan hori duniya domin muguntarta da Miyagu domin zunubansu. Zan kawo ƙarshen alfarmar masu girmankai in ƙasƙantar da alfarmar mutane masu ban tsoro. 12 Zan sa maza su yi ƙaranci fiye da zinariya mai daraja, samun mutum kuma ya zama da wuya fiye da tsattsarkar zinariya ta Ofir 13 Domin wannan zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuma za ta girgiza ta gusa daga wurinta, ta wurin hasalar Yahweh mai runduna, da cikin ranar fushinsa mai zafi. 14 Kamar barewar da aka farauto ko tumakin da ba su da makiyayi, kowanne mutum ya juya ga bin mutanensa, zai gudu zuwa ƙasarsa. 15 Duk wanda aka samu za a kashe shi, duk wanda aka kama kuma zai mutu da kaifin takobi. 16 Jariransu kuma za a yayyanka su akan idanunsu. Gidajensu za a washesu, matan su kuma za a yi masu fyaɗe. 17 Duba, Ina gab da tayar da Medes domin su kai masu hari, waɗanda ba za su kula da azurfa ba, ba kuma za su yi murna saboda zinariya ba. 18 Mãsunsu za su soki samari. Ba za su tausayawa jarirai ba kuma ba zasu bar yara ba. 19 Daga nan Babila, mafi daraja a mulkoki, jamalin fahariyar Kaldiyawa, Allah zai juyadda su kamar yadda ya yi da Sodom da Gomora. 20 Ba za a zauna ciki ko rayuwa a ciki ba daga tsara zuwa tsara. Balarabe ba zai kafa rumfarsa a can ba, makiyaya kuma ba za su bar garken su su huta a can ba. 21 Amma namomin jeji za su kwanta a wurin. Gidajensu za su cika da mujiyoyi; Jiminai da Gadai za su yi ta tsalle can. 22 Kuraye za su yi kuka a cikin kagarorinsu, diloli kuma a cikin fadodinsu masu kyau. Lokacinta ya kusa, kwanakinta kuma ba za a jinkirtasu ba.

Sura 14

1 Yahweh zai ji tausayin Yakubu; zai sake zãɓen Isra'ila ya sake dawo da su cikin ƙasarsu, bãƙi za su haɗa kai da su, za su haɗa kansu da gidan Yakubu. 2 Al'ummai za su ɗauke su su kai su garinsu. Gidan Isra'ila zai ɗauke su ya kai su ƙasar Yahweh a matsayi bayi maza da mata. Za su bautadda waɗanda suka kwashe a dã, za su yi mulkin waɗanda suka ƙuntata masu. 3 A wannan rana Yahweh ya ba ku hutu daga baƙinciki da wahalarku kuma daga aiki mai wahala wanda aka sa ku yi, 4 za ku raira wannan waƙar ta habaici gãba da sarkin Babila, "Yadda ƙarshen mai azabtarwa ya zo, fushin masu girmankai ya ƙare! 5 Yahweh ya karya sandar mugu, ikon masu mulkin nan, 6 wanda ya bugi mutane cikin fushi da naushi kowanne lokaci, ya mallaki al'ummai da fushi, da harin da ba mai hanawa. 7 Dukkan duniya tana zaune cikin hutu kuma shiru; sun fara biki da raira waƙa. 8 Har itatuwan sayfres suna murna da kai tare da Sidas na Lebanon; suka ce, 'Tunda aka ƙasƙantar da kai, ba bu wani mai saran itace da ya zo ya sare mu ƙasa.' 9 Lahira daga ƙasa na marmarin saduwa da kai idan ka je can. Ta tayar da mattatu domin ka, dukkan sarakunan duniya an sa sun tashi daga kursiyinsu, dukkan sarakunan al'ummai. 10 Dukkansu za su yi magana su ce maka, 'Ka zama marar ƙarfi kamar mu. 11 Ka zama irin mu. An yi ƙasa da alfarmarka har Lahira duk da ƙarar amon tamburanka. An shimfiɗa tsutsotsi ƙarƙashinka, tsutsotsi sun rufe ka.' 12 Yadda ka faɗo daga sama, tauraron rana, ɗan asubahi! Yadda aka sãre ka ƙasa, kai wanda kayi nasara da al'ummai! 13 Sai ka ce a cikin zuciyarka, 'Zan hau cikin sama, Zan ɗaukaka kursiyina bisan taurarin Allah, zan zauna bisa tsaunin taruwar jama'a, cikin ƙarshen arewa. 14 Zan hau can bisa maɗaukakan gajimarai; Zan maida kaina kamar Allah Mai Iko.' 15 Yanzu angangaradda kai zuwa Lahira, zuwa ƙarshen rami. 16 Waɗanda suka ganka za su zuba maka ido kuma za su saurare ka. Za su ce, 'Ko shi ne mutumin da ya sa duniya ta yi rawa, wanda ya girgiza mulkoki, 17 wanda ya mai da duniya kamar jeji, wanda ya juyadda biranenta ya kuma hana 'yan yãrinsa komawa gida?' 18 Dukkan sarakunan al'ummai, dukkan su cikin daraja suke kwance, kowannen su cikin kabarinsa. 19 Amma kai an jefar da kai can waje da kushewarka kamar reshen da a ka jefar. Mattatu sun rufe ka kamar riga, waɗanda a ka sara da takobi, masu gangarowa zuwa ramin duwatsu. 20 Ba za ka bi su cikin jana'iza ba, saboda ka hallaka ƙasarka kuma ka kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaton zuriyar masu mugunta ba har abada." 21 Ka shira yanka domin 'ya'yansa, saboda zunubin kakanninsu, don kada su tashi su mallaki duniya su cika dukkan duniya da birane. 22 "Zan tashi in yi gãba da su"-wannan furcin Yahweh mai runduna ne. Zan datse wa Babila sũna, zuriya da tsãra" - wannan furcin Yahweh ne. 23 Zan maishe ta mallakar mujiyoyi, da kuma tabkunan ruwa, kuma zan share ta tsintsiyar hallakarwa" - wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna. 24 Yahweh mai runduna ya rantse ya ce, "Hakika, kamar yadda na ayyana, haka zai faru; kamar yadda na shirya haka zai faru: 25 Zan karya mutumin Asiriya cikin ƙasa ta kuma bisa kan duwatsu zan tattake shi ƙarƙashin sawu. Daga nan za a kawar da karkiyarsa daga gare su kayansa kuma daga kafaɗarsu." 26 Wannan shi ne shirin da a ka ƙadartawa dukkan duniya, wannan kuma shi ne hannun da a ka miƙar kan dukkan al'ummai. 27 Gama Yahweh mai runduna ya shirya haka; wa zai hana shi? hannun Sa a miƙe ya ke, wa za ya juyadda shi? 28 A cikin shekarar da sarki Ahaz ya mutu wannan furcin yazo: 29 Kada ku yi murna, dukkan ku Filistiyawa, cewa sandar da ya buge ki ya karye. Gama daga cikin tsatson maciji ƙasa mai dafi za ta fito, zuriyarsa kuma za ta zama wuta mai firiyar maciji. 30 Ɗ‌an farin talaka zai yi kiwon tumaki a makiyayata, mabuƙaci kuma zai kwanta cikin tsaro. Zan kashe tsatsonka da yunwa dukkan waɗanda suka tsira za su mutu. 31 Ki yi kururuwa, ƙofa, ki yi kuka, birni, dukkan ku za ku narke, Filistiya. Gama daga arewa girgije mai hayaƙi ke fitowa, ba kuma mai ratsewa cikin dagarsa. 32 Ta yaya za a amsa wa 'yan saƙon al'umman nan? Wato Yahweh ne ya kafa Sihiyona, daga cikin ta ne raunanan mutanensa za su sami mafaka.

Sura 25

1 Furci game da Mowab. Lallai, a dare ɗaya Ar ta Mowab ta zama marar amfani an hallaka ta, Lallai, a dare ɗaya Kir ta Mowab ta zama marar amfani an hallaka ta. 2 Sun hau saman masujada, mutanen Dibon sunje sammai don su yi kuka; Mowab na makoki kan Nebo da Medeba. Duk kawunansu an aske su kwal duk gemunsu kuma an yanke su. 3 A cikin titunansu suna saye da tsummoki; a kan benayen su da dandalinsu kowannensu yana koke-koke, sun narke da hawaye. 4 Heshbon da Ileyale sun yi kira domin taimako; a na jin muryarsu har Yahaz. Domin haka mayaƙa na Mowab suna kira domin neman taimako; su kadai suna rawar jiki. 5 Zuciyata tana kuka domin Mowab; sanannun ta suna gudu zuwa Zowa da Iglat Shelishiya. Sun hau zuwa wajen Luhit suna kuka; hanyar zuwa Horonayim sun tada murya da ƙarfi kan hallakarsu. 6 Ruwayen Nimrim sun bushe; ciyawa ta yi yaushi, sabuwar ciyawa ta mutu, ba sauran ɗanyen abu. 7 Yalwar abin da suka samar da wanda suka ajiye, za su ɗauka su haye kwazazzabon foflas. 8 Kukan ya zaga wajen iyakar Mowab; kuwwarta har ta fi Iglaim da Biya Ilim. 9 Domin ruwayen Dimon cike suke da jini; amma zan kawo wanda ya fi zafi akan Dimon. Zaki zai kai hari ga waɗanda suka tsira a Mowab da kuma sauransu da suka rage a cikin ƙasar.

Sura 16

1 Ku aika da raguna domin mulkin ƙasa daga Selah cikin jeji; zuwa tsaunin ɗiyar Sihiyona. 2 Kamar tsuntsaye masu yawo, kamar sheƙar da aka warwatsar haka matan Mowab a mishigan Kogin Arnon. 3 "Ka bada umarni, ka tabbatar da adalci; ka sa inuwa ta zama dare a cikin tsakiyar rana; ka ɓoye yasassu; kada ka bashe da waɗanda ba kome ba. 4 Ka barsu su zauna a cikin ku, 'yan gudun hijira daga Mowab; ka zama maɓuya gare su daga mai lalatarwa." Gama zalunci zai tsaya, hallakarwa kuma zata tsaya, waɗannan da suke tattaka mutane za su ɓace a ƙasar. 5 A cikin alƙawarin aminci kuma za'a kafa kursiyi, ɗaya kuma daga cikin rumfar Dauda da aminci zai zauna can, zai yi shari'a yana neman adalci, yana aikata gaskiya. 6 Mun ji labarin girmankan Mowab, girmankansa da fahariyarsa da fushinsa. Amma taƙamarsa duk bakomai ba ne. 7 Sai Mowab tayi koke-koke domin Mowab - dukkan su suna makoki, ku da a ka lalatar ɗungum, domin wainar kauɗar inabin Kir Hareset. 8 Gonakin Heshbon sun bushe duk da kuringar inabin Sibma. Sarakunan al'ummai sun tattake zaɓaɓɓun inabin da suka kai zuwa Yaza, da suka yaɗu zuwa cikin jeji. Rassanta sun yaɗu waje; sun fita zuwa ƙetaren teku. 9 Domin wannan zan yi kuka tare da Yaza domin kuringar Sibma. Zan dausayar da ku da hawaye na, Heshbon da Ileyale. Gama na kawo ƙarshen farincikinku game da amfanin gonakinku damina da na kaka. 10 Murna da farincikinku an ɗauke su daga 'ya'yan itatuwan kuramenku, ba sauran waƙa, ba sowa cikin gonakinku. Ba mai taka ruwan inabi a wurin matsewa, gama na kawo ƙarshen sowa ga mai takawar. 11 Domin haka zuciyata na tsãki kamar girayar Mowab, can cikina kuma domin Kir Hareset. 12 Sa'ad da Mowab ya gajiyar da kansa a wuri mai bisa kuma ya shiga masujada ya yi addu'a, addu'o'insa ba za su yi komai ba. 13 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗi game da Mowab da farko. 14 Yahweh ya sake yin magana, "Cikin shekara uku, ɗaukakar Mowab za ta ɓace; duk da yawan mutanensa, sauran da za su ragu za su zama 'yan kaɗan marasa amfani."

Sura 17

1 Furci game da Damaskus. 2 Biranen Arowa za su zama kufai. Za su zama inda garkuna za su riƙa kwanciya, ba kuwa mai tsoratar dasu. 3 Biranensu masu kagara za su ɓace daga Ifraim, mulki kuma daga Damaskus, da ringin Aram - za su zama kamar ɗaukakar mutanen Isra'ila - wannan furcin Yahweh mai runduna ne. 4 Zai zama kuma a ranar nan darajar Yakubu zata zama 'yar siririya, ƙibar jikinsa zata saɓe. 5 Zai zama kamar kwanakin da maigirbi ya tattara hatsin dake tsaye, hannunsa kuma yana yankan zangarku. zai zama kamar lokacin da mutum ke kalar zangarku cikin kwarin Refayim. 6 Za'a bar kala, duk da haka, kamar lokacin da itacen zaitun ke kakkaɓewa: biyu ko uku cikin reshe mafi bisa, huɗu ko biyar a cikin rassa mafi bisa na itace mai 'ya'ya - wannan furcin Yahweh ne, Allah na Isra'ila. 7 A wannan rana mutane za su dubi mahaliccinsu, idanunsu za su dubi Mai Tsarki na Isra'ila. 8 Za su dubu bagadai, aikin hannuwansu, ba kuwa za su dubi abin da yatsunsu suka yi ba, sandunan Ashera ko siffofin rana. 9 A wannan rana ƙarfafan biranensu za su zama kamar wuraren da aka bar su kufai cikin kurmi a ƙwanƙolin tsaunuka, da aka bar su saboda mutanen Isra'ila wannan zai zama hallaka. 10 Domin kun manta da Allah mai cetonku, kun kuma yi watsi da dutsen ƙarfinku. Kuna dasa tsire-tsiren da suka gamshe ku, kuna dasa rassan inabi da kuka karɓa wurin baƙo, 11 A cikin rana kayi dashe da shinge da noma. Bada daɗewa ba irinka zai yi girma, amma girbinka zai gaza a cikin ranar baƙinciki da matsananciyar azaba. 12 Kaito! ga hayaniyar mutane da yawa, wannan ruri na kama da rurin tekuna, da gudun al'ummai, suna gudu kamar gudun ruwaye masu girma! 13 Al'ummai za su yi ruri kamar gudun ruwaye masu yawa, amma Allah zai tsauta masu. Za su gudu nesa za'a runtume su kamar ƙai-ƙai a kan tsaunuka gaban iska, kamar guguwa kuma gaban hadari. 14 Da yamma, ga, razana! Kafin safiya kuma za su tafi! wannan shi ne rabon waɗanda suke yi mana sata, rabon waɗanda suke yi mana fashi.

Sura 18

1 Kaiton ƙasa ta motsin fukafukai wadda, take rafukan Kush. 2 Wadda take aika jakadu ta hanyar teku, a cikin ruwaye ta jiragen iwa Ku tafi ku, jakadu masu sauri, wurin dogayen al'ummai masu taushin fata, wurin mutanen da a ke tsoron su nesa da kusa, al'umma mai ban razana mai tattakewa, wadda ruwaye sun raba ƙasarta. 3 Dukkan ku mazaunan duniya da waɗanda ke zaune a duniya, idan kuka ga alama a kan duwatsu, ku duba; idan aka busa ƙaho, ku saurara. 4 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi mani, "A hankali zan lura daga gidana, kamar gumi cikin hasken rana, kamar hazon ƙyasashi a lokacin girbi. 5 Kafin girbi, ya zo sa'ad da fure ya kaɗe, huda tana zama nunannun 'ya'yan inabi, zai datse maɓulɓula da ƙugiya mai tsini, zai sare ya kuma kwashe rassan da suka barbaje. 6 Za a bar su tare saboda tsuntsayen duwatsu da dabbobin duniya. Tsuntsaye za su yi damina a kansu, kuma dukkan dabbobin duniya za su yi lokacin sanyi a kansu." 7 A wancan lokacin dogayen mutane masu taushin jiki za su kawo hadaya ga Yahweh, daga mutanen da a ke tsoro nesa da kusa, ƙarfafan al'ummai masu ban razana, waɗanda rafuka suka raba ƙasarsu, zuwa wurin da ya ke na sunan Yahweh mai runduna, zuwa Tsaunin Sihiyona.

Sura 19

1 Furci game da Masar. Duba, Yahweh ya hau girgije mai sauri ya taho Masar; gumakan Masar za su razana a gabansa, zuciyar masarawa za ta narke a cikin su. 2 "Zan haɗa masarawa gãba da masarawa: Mutum zai yi faɗa gãba da ɗan'uwansa, mutum gãba da maƙwabcinsa; birni kuma gãba da birni, mulki kuma gãba da mulki. 3 Ruhun Masar zai karaya daga ciki. Zan rushe shawararsa, koda ya ke sun nemi shawarar gumakai, da ruhun matattu, da masu duba, da masu aiki da ruhohi. 4 Zan bada masarawa a hannun mugun shugaba, sarki mai ƙarfi zai yi mulkin su - wannan shi ne furcin Yahweh Ubangiji mai runduna." 5 Ruwayen teku za su bushe, rafi zai bushe ya zama ba komai. 6 Rafuka za su yi wari; ƙoramun Masar kuma za su shanye su bushe; iwa da jema za su yi yaushi. 7 Iwar dake kusa da Nilu, da bakin gãɓar Nilu, da dukkan gonakin da a ka shuka a gefen Nilu za su bushe, za a kore su, kuma ba za su kasance ba. 8 Masunta za su yi kuka su yi makoki, da dukkan masu jefa ƙugiya cikin Nilu za su yi makoki, kuma masu jefa tãru za su yi baƙinciki. 9 Masu aikin tsifar zare da waɗanda ke saƙar farar tufa za su rame. 10 Za a murƙushe masu aikin tufafi na Masar; masu aikin lada za su yi baƙinciki a cikin su. 11 Sarakunan Zowan wawaye ne gaba ɗaya. Shawarar mashawartan Fir'auna mafiya wayo ta zama rashin hankali. Yaya za ka iya cewa da Fir'auna, "Ni ɗan mutane masu hikima ne, ni ɗan sarakunan dã ne?" 12 Ina mazajenka masu wayau suke? Bari su gaya maka su kuma sanasshe ka abin da Yahweh mai runduna ke shiryawa game da Masar. 13 Sarakunan Zowan sun zama wawaye, an ruɗi sarakunan Memfis; sun sa Masar ta bauɗe, su da suke duwatsun kusurwar kabilunta. 14 Yahweh ya sa ruhun lalacewa cikin tsakiyarta, suka kuma sa Masar ta bauɗe cikin dukkan abin da take yi, kamar mashayi mai tangaɗi cikin amansa. 15 Ba abin da wani zai iya yi domin Masar, ko kai ko wutsiya, ko rassan dabino ko iwa. 16 A wannan rana, Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki da tsoro saboda ɗagaggen hannun Ubangiji mai runduna a kansu. 17 Ƙasar Yahuda za ta zama sanadin tangaɗin Masar. Dukkan sa'ad da wani ya tuna masu da ita, za su ji tsoro, saboda shirin Yahweh, kan abin da ya ke shiryawa gãba da su. 18 A wannan rana za a sami birane biyar cikin ƙasar Masar da za su yi magana da harshen Kan'ana su yi rantsuwa su yi amana da Yahweh mai runduna. Ɗaya daga waɗannan za a kira shi Birnin Rana. 19 A wannan rana za a sami bagadin Yahweh a tsakiyar ƙasar Masar, da dutsen daya zama ginshiƙi na kan iyakar Yahweh. 20 Zai zama kamar alama da shaida ga Yahweh mai runduna a cikin ƙasar Masar. Idan suka yi kuka ga Yahweh saboda mai tsananta masu, zai aiko masu da mai ceto da mai kariya, zai kuma cece su. 21 Yahweh zai zama sananne a Masar, a wannan rana Masarawa za su san da kasancewar Yahweh. Za su yi sujada da hadayu da baye-baye, za su yi wa'adodi ga Yahweh, su cika su kuma. 22 Yahweh zai azabci Masar, yana azabtarwa da warkarwa kuma. Za su juyo ga Yahweh; zai ji addu'arsu ya warkar dasu. 23 A wannan rana za a sami karabka tsakanin Masar da Asiriya, Asiriye zai zo Masar, Bamasare kuma zai je Asiriya; Masarawa kuma za su yi sujada tare da Asiriyawa. 24 A cikin wannan rana, Isra'ila za ta zama ta uku tare da Masar da Asiriya, za su zama albarka a tsakiyar duniya; 25 Yahweh mai runduna zai albarkace su ya ce, "Mai albarka ce Masar, jama'ata; Asiriya, aikin hannuwana; da Isra'ila, abin gãdona."

Sura 20

1 A cikin shekarar da Tartan ya zo Ashdod, sa'ad da Sargon sarkin Asiriya ya aiko shi, ya yi faɗa gãba da Ashdod ya amshe ta. 2 A wannan lokaci Yahweh ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz yace, "Ka je ka tuɓe tsummokara daga ƙugunka, ka tuɓe takalma daga ƙafafunka." Ya yi haka, ya yi tafiya huntu ba takalma a ƙafafunsa. 3 Yahweh yace, "Kamar yadda bawana Ishaya ya yi tafiya huntu ba takalma a ƙafafunsa shekara uku, wannan alama ce da al'ajibi dangane da Masar da Kush - 4 ta haka sarkin Asiriya zai tafi da kamammu na Masar, da korarru na Kush, tsoho da yaro, huntu ba takalmi, da ɗuwawunsu a waje, domin Masar ta kunyata. 5 Za su karaya su ji kunya, saboda Kush begensu da Masar darajarsu. 6 Mazaunan wannan yanki a cikin wannan rana za su ce, 'Hakika, wannan shi ne tushen begenmu, inda mu kan ruga neman taimako domin a cece mu daga sarkin Asiriya, to yanzu, ta yaya za mu tsira?"'

Sura 21

1 Furci game da hamada ta wajan teku. Kamar guguwa mai sharewa ta bi ta Negeb, ta zo tana wucewa ta cikin jeji, daga ƙasa mai ban tsoro. 2 An ba ni ruya mai ban razana: mutum marar imani yana yin rashin imani, mai hallakarwa yana hallakarwa. Jeka ka kai hari, a kan Ilam; yi sansani, Midiya; zan tsaida dukkan rurinta. 3 Saboda haka kwankwasona ya cika da ciwo; ciwo kamar irin ciwon mace mai naƙuda ya kama ni; abin da na ji ya durƙusar da ni; abin da na gani ya tada hankalina. 4 Zuciyata tana bugawa; na kaɗu da tsoro. Hasken asuba lokacin da nike so, amma ya kawo razana a gare ni. 5 Sun shirya teburi, sun shimfiɗa dardumai, sun ci sun sha; ku tashi, yarimai, ku shafe garkuwoyinku da mai. 6 Gama abin da Yahweh yace da ni ke nan, "Jeka, ka sa mai tsaro; dole ya faɗi abin da ya gani. 7 Sa'ad da ya ga karusa, da tagwayen mahaya, a kan jakuna, da raƙuma, sai ya natsu ya yi lura sosai." 8 Mai tsaron ya yi kuka, "Ubangiji, a kan kagara nike tsaye dukkan yini, kullum, a kan aikina nike dukkan dare." 9 Ga karusa tana zuwa da mutum da tagwayen mahaya. Ya yi kira, "Babila ta faɗi, ta faɗi, dukkan sassaƙaƙƙun siffofin allolinta kuma sun ragargaje har ƙasa." 10 Masussukaina da sheƙaƙƙu, yaran masussukata! Abin da na ji daga Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, shi na furta maku. 11 Furci game da Duma. Wani ya kira ni daga Siya, "Mai tsaro, me ya rage na dare?" Mai tsaro, me ya rage na dare?" 12 Mai tsaro ya ce, "Safiya ta kan zo haka ma dare. Idan kana so ka yi tambaya, sai ka yi tambaya; ka sake dawowa kuma." 13 Furci game da Arebiya. A cikin jejin Arebiya za ku kwana, ku fataken Dedaniyawa. 14 Ku kawo ruwa saboda masu jin ƙishi; mazauna ƙasar Tema, ku kawo gurasa ga masu gudun hijira. 15 Gama sun gudo daga takobi, daga takobin da a ka zaro, daga bakan da ke a ɗane, kuma daga nawayar yaƙi. 16 Gama abin da Yahweh ya faɗa mani ke nan, "A cikin shekara ɗaya, kamar yadda ma'aikacin da a ka ɗauka domin shekara ɗaya zai gani, dukkan darajar Keda za ta ƙare. 17 Maharba kaɗan kawai, da jarumawan Keda 'yan kaɗan za su rage," gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi.

Sura 22

1 Furci game da Kwarin Wahayi: Mene ne dalilin da ya kai dukkan ku bisan gidaje? 2 Shi ne domin ka ji birni cike da hargowa, birni cike da bukukuwa? Matattunka bada takobi a ka kashe su ba, kuma ba a dãgar yaƙi suka mutu ba. 3 Dukkan masu mulkinku sun gudu tare, amma an kamo su ba tare da an yi amfani da baka ba; dukkan su an kamo su tare, koda ya ke sun gudu nesa. 4 Saboda haka sai na ce, "Kada ku dube ni, zan yi kuka mai zafi; Kada ku yi ƙoƙarin ta'azantar da ni game da hallakar ɗiyar mutanena." 5 Gama akwai ranar hargitsi, tana tattakowa, da ruɗami domin Ubangiji Yahweh mai runduna, a Kwari na Wahayi, da rushewar ganuwoyi, da mutane suna kuka ga duwatsu. 6 Ilam ya ɗauki kwãri, da mahayan karusai da mahayan dawakai, Kir kuma ya ajiye garkuwa a fili. 7 Zai zama zaɓaɓɓun kwarurrukan ku za su cika da karusai, masu hawan dawaki kuma za su ja dãgarsu a ƙofa. 8 Ya ɗauke kariyar Yahuda; a cikin wannan rana ka duba kayan yaƙi a Fada wadda ke Jeji. 9 Kun ga tsagogin birnin Dauda, suna da yawa, ku ka kuma ɗebo ruwa daga tafki na gangare. 10 Kun ƙirga gidajen Yerusalem, kun fasa gidaje domin ku ƙara ƙarfin ganuwa. 11 kun gina wurin tãra ruwa a tsakanin ganuwowin biyu na tsohon tafki. Amma ba ku kula da wanda ya yi birnin ba, wanda ya shirya shi tun da daɗewa. 12 Ubangiji Yahweh mai runduna ya yi kira a wannan rana domin kuka, domin makoki, domin aske kawuna, da sanya tsummokara. 13 Amma duba, maimakon haka, sai buki da annashuwa, da yanka shanu da tumaki, da cin nama da shaye-shayen ruwan inabi; bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu. 14 An bayyana mani haka a kunnuwana daga wurin Yahweh mai runduna: "Babu shakka ba za a gafarta maku wannan muguntar ba, ko kun mutu," inji Ubangiji Yahweh mai runduna. 15 Ubangiji Yahweh mai runduna, yace, "Jeka wurin shugaban nan, wurin Shebna, mai lura da gidan, ka ce, 16 "Me ka ke yi a nan, wane ne ya ba ka izini ka gina kabari domin kanka, sassaƙa kabari ya ke yi a wurare masu tsawo, yana sassaƙawa kansa wurin hutawa a cikin dutse?"' 17 Duba, Yahweh ya kusa jefar da kai, ƙaƙƙarfan mutum, ya kusa jefar da kai ƙasa; zai cafke ka da ƙarfi. 18 Ba shakka zai yi majaujawa da kai, kamar ƙwallo zai wurga ka a cikin ƙasa mai girma. Can za ka mutu, can kuma karusanka masu daraja za su kasance; za ka zama abin kunyar gidan shugabanka! 19 Zan tumɓuke ka daga matsayin ka daga wurin da kake aiki. Zan jawo ka har ƙasa. 20 Zai zama a wannan rana zan kira bawana Iliyakim ɗan Hilkiya. 21 Zan tufasantar da shi da alkyabbarka in ɗaura masa ɗamararka, zan maida muƙaminka a hannunsa. Za ya zama uba ga mazaunan Yerusalem da gidan Yahuda. 22 Zan ɗora mabuɗin gidan Dauda a kafaɗarsa; zai buɗe, kuma ba mai kullewa; zai kulle, kuma ba mai buɗewa. 23 Zan kafa shi, kamar ƙusa a wuri mai tsaro, zai zama mazaunin ɗaukaka domin gidan ubansa. 24 Za su rataya masa dukkan ɗaukakar gidan ubansa, 'ya'ya da zuriya-zuriya, kowanne ƙaramin wurin ajiya daga ƙoƙuna zuwa dukkan moɗaye. 25 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - ƙusar da a ka kafa a wuri mai ƙarfi za ta cire, ta karye, ta kuma faɗi, nauyin dake kanta kuma zai yanke - Gama Yahweh ya furta.

Sura 23

1 Furci game da Taya: Ku yi ruri, ku jiragen Tarshish; domin babu gida ko wurin tsayawa; daga ƙasar Sifuros an bayyana masu. 2 Ku yi shiru, ku mazauna bakin teku; 'yan kasuwar Sidon, masu tafiya kan teku, sun cika ku. 3 A kan manyan ruwaye ga hatsin Shiho, girbin Nilu ne amfaninta; kuma ta zama wurin cinikin al'ummai. 4 Ki ji kunya, ke Sidon; gama teku ya yi magana, babba na teku. Ya ce, "Ban yi naƙuda ba ban haihu ba, ban yi renon samari ba, ban tarbiyantar da 'yammata ba." 5 Sa'ad da rahoton ya zo ga Masar, za su yi baƙinciki saboda Taya. 6 Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka, ku mazauna bakin teku. 7 Wannan ya faru da ku ne, birni mai farinciki, wanda tushenta tun daga zamanin dã ne, wadda ƙafafunta sun kai ta can nesa zuwa bãƙin wurare ta zauna? 8 Wane ne ya shirya wa wannan gãba da Taya haka, mai bada rawwuna ce, wadda 'yan cinikinta yarimai ne, wanda dillalanta masu daraja ne na duniya? 9 Yahweh mai runduna ne ya shirya haka domin ya ƙasƙantar da girman kanta da dukkan darajarta, ya kunyatar da dukkan masu martabarta a duniya. 10 Ki nome gonarki, kamar mai noma a Nilu, ke ɗiyar Tarshish. Ba sauran wurin kasuwanci a Taya. 11 Yahweh ya kai hannunsa bisa teku, ya girgiza mulkoki; ya bada umarni game da Fonisiya, ta rushe ƙarfafan wurarensu. 12 Ya ce, "Ba za ki ƙara yin farinciki ba, ke mai shan tsanani ɗiyar budurwa ta Sidon; ki tashi, ki wuce zuwa Sifuros; Amma ko can ma ba za ki sami hutu ba." 13 Dubi ƙasar Kaldiyawa. Waɗannan mutane yanzu ba su; Asiriyawa sun maida ita daji domin dabbobin jeji. Sun kafa hasumiyoyin sansaninsu; sun rushe fãdojinta; sun maida ita tsibin kufai. 14 Ku yi ruri, ku jiragen Tarshish; gama an rushe mafakarku. 15 A wannan rana, za a manta da Taya har shekara saba'in, kamar kwanakin sarki. Bayan shekara saba'in ɗin wani abu zai faru da Taya kamar yadda ya ke a cikin waƙar karuwa. 16 Ɗauki molo, ki zagaya birnin, ke karuwar da a ka manta da ita; ki kaɗa su da kyau, ki yi waƙoƙi masu yawa, domin a tuna dake. 17 Zai zama bayan shekara saba'in, Yahweh zai taimaki Taya, za ta fara samun kuɗi ta wurin aikin karuwanci, za ta bada hidimarta ga dukkan mulkokin duniya. 18 Ribarta da abin da take samu za a keɓe shi ga Yahweh. Ba za a tara su ko a ajiye su a ma'aji ba, gama za a bada ribarta ga waɗanda suke zama a gaban Yahweh domin ayi amfani da su a ba su abinci isashshe saboda su sami tufafi mafi daraja.

Sura 24

1 Duba, Yahweh ya kusa mayar da duniya kango, ya lalata ta, ya ɓata fuskarta, ya watsar da mazauna cikinta. 2 Za ya zama cewa, kamar yadda ya ke da mutane, haka kuma firist; kamar yadda iyayengiji suke haka bayi za su zama, kamar yadda uwargijiya take, haka kuyangarta za ta zama, kamar yadda mai sayarwa ya ke, haka mai saye za ya zama; kamar yadda mai bada bashi ya ke, haka mai karɓar bashin za ya zama; kamar yadda mai karɓar bashi da ruwa ya ke, haka mai bada wa da ruwa. 3 Duniya za ta zama kango ta zama huntuwa sarai; gama Yahweh ya faɗi wannan magana. 4 Ƙasa za ta yanƙwane ta bushe, duniya za ta koɗe ta watse, sanannun mutane na duniya za su lalace. 5 Duniya ta ƙazamtu daga mazaunanta saboda sun karya dokoki, sun wofinta farillai, sun karya alƙawari na har abada. 6 Saboda haka, la'ana ta cinye duniya, an sami mazaunan ta da laifi. Mazauna duniya sun ƙone, mutane kuma kaɗan suka rage. 7 Sabon ruwan inabi ya bushe, kuringar ta yi yaushi, dukkan masu farinciki a zuciya suna nishi. 8 Ƙarar murna ta kacau-kacau ta ƙare, bukukuwan waɗanda suke farinciki; murnar masu garaya ta ƙare. 9 Ba sa shan ruwan inabi su yi waƙa, kuma barasa ta yi ɗaci ga masu shan ta. 10 An rushe birni mai ruɗani; an rufe kowanne gida ba kowa a ciki. 11 Ana kuka a kan hanyoyi saboda ruwan inabi; dukkan farinciki ya duhunta, murnar birnin ta shuɗe. 12 A cikin birnin sai kufai, an rushe birnin, an ɓalle ƙofarsa zuwa kango. 13 Domin haka zai kasance a dukkan duniya cikin al'ummai, kamar yadda a ke bugun itacen zaitun, kamar yadda a ke kãlar inabi bayan an gama girbi. 14 Za su tada muryoyi su yi sowa ga darajar Yahweh, kuma za su yi sowa ta murna daga teku. 15 Saboda haka daga gabas ku ɗaukaka Yahweh, a cikin tsibiran teku ku ɗaukaka sunan Yahweh, Allah na Isra'ila. 16 Mun ji waƙoƙi daga wuri mafi nisa na duniya, "Ɗaukaka ga mai tsarki!" Amma na ce, "Kaito na, na lalace, na lalace! Mazambata sun yi zamba; i, mazambata sun yi zamba ƙwarai." 17 Razana, da rami da tarko suna kanku, mazaunan duniya. 18 Shi wanda ya gudu saboda jin ƙarar razana zai faɗa rami, kuma shi wanda ya fito daga tsakiyar rami tarko zai kama shi. Tagogin sama za su buɗe, tussan duniya kuma za su girgiza. 19 Za a rushe duniya sarai, duniya zata tsage, duniya zata girgiza ƙwarai. 20 Duniya zata yi tangaɗi kamar mutum mashayi ta yi tangaɗi gaba da baya kamar bukka. Zunubinta zai yi mata nauyi zata faɗi ba zata ƙara tashi ba. 21 Zai zama a wannan rana, Yahweh zai hukunta rundunar sama a can sammai, sarakunan duniya kuma a duniya. 22 Za a tattara su tare, 'yan sarƙa a cikin rami, za a rufe su a cikin kurkuku; bayan kwanaki da yawa zai yi masu hukunci. 23 Sa'an nan rana zata ƙasƙanta wata kuma ya ji kunya, gama Yahweh zai yi mulki a Tsaunin Sihiyona da cikin Yerusalem a gaban dattawansa cikin daraja.

Sura 25

1 Yahweh, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka, zan yabi sunanka; saboda ka yi abubuwan ban mamaki, abubuwan da a ka shirya tun dã, cikin cikakken aminci. 2 Gama ka mayar da birnin juji, birni mai daraja ya zama kufai, wurin zaman baƙi ya zama ba birni ba kuwa. 3 Saboda haka ƙarfafan mutane za su ɗaukaka ka; birnin al'ummai 'yan ta'adda zai ji tsoronka. 4 Gama ka zama mafaka ga wanda ya ke matalauci, mafaka ga fakirai mabuƙata - wurin fakewa daga hadari, wurin fakewa daga zafin rana. Sa'ad da hucin marasa hankali ya ke kamar haɗari mai buga bango, 5 kamar zafi a busasshiyar ƙasa, ka sha ƙarfin hayaniyar bãƙi, kamar yadda inuwar giza-gizai sukan sha ƙarfin zafi, haka aka amsa waƙar 'yan ta'adda. 6 A kan wannan tsaunin Yahweh mai runduna zai yiwa dukkan mutane liyafa da abubuwa masu ƙiba, zaɓaɓen ruwan inabi, da nama mai taushi, liyafar ruwan 'ya'yan itace. 7 A kan wannan tsaunin zai rushe abin da ya rufe dukkan mutane, saƙaƙƙen mayafin lulluɓe dukkan al'ummai. 8 Zai haɗiye mutuwa har abada, Ubangiji Yahweh zai share hawaye daga dukkan fuskoki; zai ɗauke ƙasƙancin mutanensa daga duniya dukka, gama Yahweh ya faɗe shi. 9 A wannan rana za a ce, "Duba, wannan shi ne Allahnmu, mun jira shi, shi kuma zai cece mu. Wannan shi ne Yahweh, mun jira shi, za mu yi murna da farinciki cikin cetonsa." 10 Gama a wannan tsaunin Yahweh zai ɗora hannunsa; za a tattake Mowab daga wurinsa, kamar yadda ake tattake ciyawa cikin ramin dake cike da taki. 11 Za su buɗe hannuwansu a tsakiyarsa, kamar yadda mai iyo ya kan buɗe hannunsa ya yi iyo. 12 Amma Yahweh zai ƙasƙantar da girman kansu, duk da hikimar hannuwansu. Zai rushe hasumiyoyinsu mai tsawo har ƙasa ta zama turɓaya.

Sura 26

1 A wannan rana za a yi wannan waƙar a ƙasar Yahuda: Mu na da birni mai ƙarfi; Yahweh yasa ceto ya zama ganuwarsa da kagararsa. 2 A Buɗe ƙofofin, domin al'umma mai adalci da take riƙe gaskiya ta shiga ciki. 3 Wanda ya tsayar da hankalinsa a kanka, za ka riƙe shi cikin cikakkiyar salama, domin ya dogara gare ka. 4 Ku sa dogara cikin Yahweh, har abada; gama cikin Yah, Yahweh, dutse ne na har abada. 5 Gama waɗanda suke zama cikin girman kai zai ƙasƙantar da su; zai rushe tsararren birni, zai rushe shi har ƙasa; ya mayar da shi turɓaya. 6 Fakirai da matalauta za su tattake shi da ƙafafunsu har ƙasa. 7 Hanyar mai adalci an shirya ta, Mai Adalcin nan; ka shirya tafarkin mai adalci ka maishe ta miƙaƙƙa. 8 I, a tafarkin hukuncinka, Yahweh, za mu jira ka; sunanka da ɗabi'arka su ne marmarinmu. 9 Na ji marmarinka cikin dare; i, ruhuna a cikina ya neme ka da gaske. Gama sa'ad da hukucinka ya zo duniya, mazaunan duniya suna koyo game da adalci. 10 Bari a nuna wa mai mugunta tagomashi, amma ba zai koyi adalci ba. A cikin ƙasar masu tafiya dai-dai, shi mugunta ya ke yi kuma darajar Yahweh shi bai san ta ba. 11 Yahweh, an tada hannunka sama, amma su ba su lura ba, amma za su ga himmar ka domin mutane za su ji kunya, saboda wutar magabtanka za ta cinye su. 12 Yahweh, za ka kawo mana salama; gama hakika ka cika dukkan ayyukanmu domin mu. 13 Yahweh Allahnmu, waɗansu shugabanni baya ga kai sun yi mulki a kanmu; amma sunan ka kaɗai muke yabo. 14 Sun mutu, ba za su tsaya ba sun shuɗe, ba za su tashi ba. Hakika, ka zo cikin hukunci, ka hallaka su, ko tunawa da su ba a yi. 15 Ka sa al'umma ta ƙaru, Yahweh, al'umma ta ƙaru ta wurin ka; ka ɗaukaka, an darjantaka; ka faɗaɗa dukkan iyakokin ƙasar. 16 Yahweh, a cikin matsala suka dube ka, sai da horon ka ya zo kansu sa'an nan suka yi addu'a. 17 Kamar mace mai juna biyu sa'ad da lokacin haihuwar ta ya yi kusa, tana zafin ciwon naƙuda ta kuma yi kuka gare ka, haka muke a gaban ka, Ubangiji. 18 Muna da juna biyu, muna cikin naƙuda, amma ya zama kamar mun haifi iska. Ba mu kawo ceto ga duniya ba, kuma mazaunan duniya ba su faɗi ba. 19 Matattun ka za su rayu; jukkunan su da suka mutu za su tashi. Ku farka ku raira waƙar farinciki, ku mazauna cikin ƙura; gama raɓarku raɓar haske ce, ƙasa kuma za ta fito da matattunta. 20 Ku tafi ku mutanena, ku shiga ɗakunanku ku rufe ƙofofi; ku ɗan ɓoye kaɗan, har sai hasalar ta wuce. 21 Gama, duba, Yahweh ya kusa fitowa daga wurinsa ya hori mazaunan duniya saboda muguntarsu; ƙasa za ta buɗe zubar da jinin da ta yi, ba zata ƙara ɓoye waɗanda ta kashe ba.

Sura 27

1 A wannan rana Yahweh zai hori Lebiyatan macijin nan mai gudu da takobinsa mai girma, mai karfi, mai ban tsoro, Lebiyatan macijin nan mai tafiya a shagide, zai kashe babban dodon ruwa dake cikin teku. 2 A wannan rana: kuringar inabi, ta yi masa waƙa. 3 "Ni, Yahweh, ni ne mai kare shi; zan yi masa banruwa kowanne lokaci. zan yi tsaron sa dare da rana yadda ba wanda zai cuce shi. 4 Ban ji haushi ba, Oh, dãma akwai sarƙaƙiya da ƙaya! Zan far masu a filin daga in ƙone su tare duka; 5 sai dai idan sun nemi kariyata, sun nemi salama da ni; bari su nemi salama da ni. 6 A rana mai zuwa, Yakubu zai yi sauya; Isra'ila zaya bunƙasa ya yi fure; su cika sararin ƙasa da 'ya'ya." 7 Yahweh, ya kaiwa Yakubu da Isra'ila hari kamar yadda ya kaiwa al'umman da suka kai masu hari? An kashe Yakubu da Isra'ila kamar yadda aka kashe al'umman da suka kashe su? 8 Ka yi fama bisa mizanin da ya yi dai-dai, ka sallami Yakubu da Isra'ila suka tafi; ka kore su da iska mai ƙarfi sun tafi, a wannan rana ta iskar gabas. 9 Haka a wannan rana, za a rufe muguntar Yakubu, wannan shi ne cikakken 'ya'yan kawar da zunubi: sa'ad da zai farfasa duwatsun bagadi ya yi masu gutsu-gutsu kamar alli, ba za a sami sifofin Asheran ko bagadin turarenta a tsaye ba. 10 Gama birni mai ganuwa ya zama kufai, an watsar da mazauna a ciki an yashe su kamar jeji. A can ɗan maraƙi ya ke kiwo yana cin rassansa. 11 Sa'ad da ƙiraruwan suka bushe, za a kakkarye su. Mataye za su hura wuta da su, gama mutane ne marasa fahimta. Wanda ya yi su ba za ya ji tausayin su ba, shi wanda ya yi su ba za ya nuna masu jinƙai ba. 12 Rana zata zo inda Yahweh zai yi shiƙa tun daga Kogin Yuferitis har zuwa Wadi ta ƙasar Masar, ku kuma mutanen Isra'ila za a tattaro ku ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. 13 A wannan rana za a busa babban ƙaho; lalatattu na ƙasar Asiriya za su zo, da yasassu na ƙasar Masar, cikin Isra'ila za su yi sujada ga Yahweh a kan tsauni mai tsarki cikin Yerusalem.

Sura 28

1 Kaiton rawanin girman kai na fure da kowanne mashayan Ifraim ke sanye da shi, kyaun darajarsu na dushewa kamar yadda kyaun fure ke dushewa, haka ma rawanin dake kan waɗanda suka bugu da ruwan inabi a Kwari mai tãki, inda ruwan inabi ya rinjayi wasu! 2 Duba, Ubangiji yana aiko da wani babba, kuma ƙaƙƙarfa; kamar hadari mai ƙanƙara, da iska mai lalatarwa, kamar ruwan sama mai kwararowa da ambaliyar ruwaye; zai jefar da kowanne rawanin fure a ƙasa. 3 Masu rawanin girman kai na fure mashaya na Ifraim za a tattake a ƙarƙashin sawu. 4 Furen ɗaukakarsa mai ƙyau, dake kan kwari mai arziki, zai zama kamar nunannen ɓaure na fãri da damuna, zai zamana, sa'ad da wani ya dube shi, tun yana hannunsa, zai haɗiye su. 5 A ranar nan Yahweh mai runduna zai zama rawani mai daraja da kambi mai kyau ga sauran mutanensa da suka rage, 6 ruhun adalci ga mahukunta, ƙarfi kuma ga waɗanda suka kori abokan gãba daga ƙofofinsu. 7 Amma har ma waɗannan suna tangaɗi da ruwan inabi mai ƙarfi. Da firist da annabi suna tangaɗi da ruwa mai ƙarfi, ruwan inabi ya haɗiye su. Suna tangaɗi da ruwan inabi mai ƙarfi, suna tangaɗi a wahayi da rashin sanin abin yi. 8 Hakika duk teburorin sun ƙazantu da haraswa, har ma babu tsabtaccen wuri. 9 Su waye zai koya wa sani, kuma ga suwa zai fasara saƙon? Ga waɗanda aka yaye daga nono, ko kuma waɗanda a ka cire daga mama? 10 Gama doka ce bisa doka, doka bisa doka; ka'ida bisa ka'ida; nan ɗan-kaɗan can ɗan-kaɗan. 11 Hakika, da leɓunan ba'a da kuma bãƙon harshe zai yiwa mutanen nan magana. 12 A dã ya ce masu, "Wannan shi ne hutu, a bada hutu ga wanda ya gaji; wannan shi ne wartsakewa ɗin," amma ba za su kasa kunne ba. 13 Haka maganar Yahweh za ta zama ma su doka bisa doka, doka bisa doka; ka'ida bisa ka'ida, ka'ida bisa ka'ida; nan ɗan kaɗan, can ɗan kaɗan; domin su tafi da baya su faɗi, a karya su, a sa masu tarko, a kama. 14 Ku saurari maganar Yahweh, ku masu ba'a, ku da ke mulki bisa waɗannan mutane dake Yerusalem. 15 Wannan zai faru domin kun ce, "Mun yi alƙawari da mutuwa, da muka ƙulla yarjejeniya. Saboda haka lokacin da babbar bulala mai bin kan kowa zata ratsa, ba zai iso wurin mu ba. Gama mun mai da ƙarya mafaƙarmu, mun sami mafaka a rumfa cikin ƙarya." 16 Saboda haka Ubangiji Yahweh yace, "Duba: Zan kafa harsashin dutse a Sihiyona, dutsen da aka jaraba, dutsen kusurwa mai daraja, tabbataccen harsashi, duk wanda ya gaskata ba za ya kunyata ba. 17 Zan sa gaskiya ta zama sandar gwaji, adalci kuma igiyar awo. Ƙanƙara za ta share mafaƙar ƙarairayi, kuma rigyawa zai sha kan maɓuya. 18 Za a tada alƙawarin ku da mutuwa, yarjejeniyar da ku ka ƙulla da Lahira za a soke. Sa'ad da rigyawa mai ruri ke wucewa, za a sha kanku. 19 Duk lokacin da za su wuce, za su sha kanku, daga safiya zuwa safiya za su yi ta aukowa, kuma dare da rana za su wuce kuma da rana da dare zai zo. Sa'ad da aka fahimci saƙon, zai sa firgita. 20 Gama gadon ya gajarce da mutum ya miƙe a bisansa, bargon kuma bashi da fãɗin da zai isa ya rufe kansa." 21 Yahweh zai miƙe kamar a kan Dutsen Ferazim, zai tashi kansa kamar a cikin Kwarin Gibiyan domin ya yi aikinsa, bãƙon aikinsa, ya kuma yi bãƙon aikinsa. 22 Saboda haka kada ku yi ba'a, domin kada a karfafa sarƙarku. Na ji daga wurin Ubangiji Yahweh mai runduna, dokar hallaka a kan duniya. 23 Ku natsu ku saurari muryata; ku natsu ku saurari maganganuna. 24 Manomin dake huɗa dukkan rana domin shuka, ya kanyi huɗar ƙasar ne kawai? Zai yi ta huɗa ne kawai yana fasa ƙasa? 25 Lokacin da ya shirya ƙasar, ba yakan yafa tamba ba, ya warwatsa riɗi, sai ya sa alkama a jere, da bali a inda ya kamata, da kuma wasu irin a gefuffuka? 26 Allahnsa yana gaya masa abin yi; yana koya masa da hikima. 27 Bugu da ƙari 'ya'yan tamba ba a sussukasu da haƙoran ƙarfe, ba a kuma bin kan riɗi da tayar karusa; amma akan buga tamba da 'gora, riɗi kuma da sanda. 28 Akan niƙa tsaba domin abinci amma bada laushi ba, koda shike ƙafafun kekensa dana dawakansa sukan warwatsar da shi, dawakansa ba sa murƙushesu. 29 Wannan ma daga Yahweh mai runduna ya ke fitowa, shi kuwa mai al'ajibi ne a cikin bishewa mafifici cikin hikima.

Sura 29

1 Kaiton Ariyel, Ariyel birnin da Dauda ya kafa zango! A ƙara shekara kan shekara; bari bukukuwa su kewayo. 2 Amma zan kafa wa Ariyel dãga, zata yi ta makoki da kururuwa; kuma zata zamar mani kamar Ariyel. 3 Zan kafa dãga gãba dake in kewaye ki, zan yi maki kwanto gãba dake da kuma soro, zan kafa wuraren faƙo gãba dake. 4 Za a jawo ki ƙasa za ki yi magana daga ƙasa; muryarki zata dushe a cikin ƙura. Muryar ki zata zama kamar ta ruhu dake fitowa daga ƙasa, maganar ki kuma zata zama rarrauna daga cikin ƙura. 5 Yawan masu kawo maki hari za su zama kamar 'yar ƙura, ɗunbin mugayen nan kamar dusa dake wucewa. Zai faru, ba zato ba tsammani, farat ɗaya. 6 Yahweh mai runduna zai zo maki, da tsawa, da raurawar ƙasa, da ƙara mai tsanani, da babbar iska, da gawurtaccen hadari, da harshen wuta mai hallakarwa, 7 Zai zama kamar mafarki, wahayi da dare: Taron dukkan al'ummai za su yaƙi Ariyel da kagararta. Za su hare ta da ita da garunta domin su matsa mata. 8 Zai zama kamar lokacin da mayunwacin mutum ya ke mafarki yana cin abinci, amma da ya farka, cikininsa ba komai. Zai zama kamar lokacin da wani mutum yana jin kishin ruwa, sai ya yi mafarki yana shan ruwa, amma lokacin da ya farka, yana suma, kishin ruwansa ba a kashe ba. I, haka zai zama ga dukkan al'umman da za su yaƙi Dutsen Sihiyona. 9 Ku jiwa kanku mamaki, ku kuma yi mamaki; ku makantar da kanku, ku zama makafi! Ku bugu, amma bada ruwan inabi ba, amma bada giya ba. 10 Gama Yahweh ya kwararo maku ruhun barci mai nauwi. Ya rufe maku idanu, ku annabawa, ya lulluɓe kawunanku, masu gani. 11 Dukkan wahayi ya zamar maku kamar maganganun littafin da a ka kulle, wanda mutane za su ba masani, su ce, "Karanta wannan." Shi kuma zai ce, "Ba zan iya ba gama an kulle." 12 Idan an bada littafin ga wanda bai iya karatu ba, cewa,"Karanta wannan," zai ce, "Ban iya karatu." 13 Ubangiji yace, "Waɗannnan mutane suna kusatowa gare ni da bakunansu, suna kuma girmamani da leɓunansu, amma zuciyarsu tana nesa da ni. Girman da suke ba ni na dokokin mutane ne da a ka riga a ka koya. 14 Saboda haka, duba, zan ci gaba in yi abin ban mamaki cikin mutanen nan, al'ajibi kan al'ajibi. Hikimar masanansu zata lalace kuma fahimtar masu tattalinsu zasu ɓace." 15 Kaiton waɗanda suke ɓoye wa Yahweh shirye-shiryensu, waɗanda ayyukansu suke cikin duhu. Suna cewa, "Wa ke ganinmu, wa kuma ya san mu?" 16 Kuna juya abubuwa na sama zuwa ƙasa! Za a kwatanta mai ginin tukwane kamar yumɓu, har da abin da a ka yi zai ce game da wanda ya yi shi, "Ba shi ya yi ni ba," ko abin da a ka sarrafa ya cewa wanda ya sarrafa shi, "Bai fahimta ba"? 17 A ɗan lokaci kaɗan, za a maida Lebanon fili, filin kuma zai zama kurmi. 18 A ranar nan kurma zai ji maganganun littafi, idanun makafi kuma za su gani daga cikin duhu baƙiƙƙirin, 19 Waɗanda a ka murƙushe za su sake yin murna a cikin Yahweh, matalauta kuma a cikin mutane za su yi farinciki cikin Mai Tsarkin na Isra'ila. 20 Gama miyagu za su ƙare, masu ba'a za su ɓace. Za a datse dukkan masu ƙaunar aikata mugunta, 21 waɗanda ta wurin magana su kan maida mutum mai laifi. Suna kafa tarko ga mai neman a yi mashi adalci a ƙofa su kuma kãda mai adalci da holoƙan ƙarairayi. 22 Saboda haka ga abin da Yahweh ya faɗi game da gidan Yakubu - Yahweh wanda ya fanshi Ibrahim, "Yakubu ba zai ƙara jin kunya ba, ko kuma fuskarsa ta turɓune. 23 Amma sa'ad da zai dubi 'ya'yansa, aikin hannuwana, za su tsarkake sunana. Za su tsarkake sunan Mai Tsarki na Yakubu za su kafu cikin tsoron Allah na Isra'ila. 24 Waɗanda suka ɓata cikin ruhaniya za su sami fahimta, masu gunaguni za su koyi ilimi."

Sura 30

1 "Kaiton 'ya'yan tawaye," wannan ne furcin Yahweh. Suna shirye-shirye, amma ba daga gare ni ba; suna ƙulla yarjejeniya da wasu al'ummai, amma ba Ruhuna ya bishe su ba, saboda haka suna ƙara zunubi kan zunubi. 2 Sun kama hanya su gangara zuwa Masar, amma ba su nemi bishe wa daga gare ni ba. Suna neman kariya daga Fir'auna, sun nemi mafaƙa a inuwar Masar. 3 Saboda haka kariyar Fir'auna zata zama abin kunyarku, fakewa a inuwar Masar, zai zama ƙasƙancinku, 4 koda shike hakimansu suna Zowan, jakadunsu sun iso Hanes. 5 Dukkansu za su ji kunya domin mutanen da ba za su iya taimakonsu ba, waɗanda ba taimako ba ne ko tallafawa, amma abin kunya ne, har ma abin ƙasƙanci." 6 Furci game da dabbobin Negeb: Cikin ƙasar wahala da hatsari, da zakanya da kuma zaki, da kububuwa da miciji mai dafi yana shawagi, su kan labta arzikinsu bisa jakkai, da kayayyakinsu masu daraja bisa doron raƙuma, su kaiwa mutanen da ba za su iya taimaka masu ba. Gama taimakon 7 Masar na banza ne; Saboda haka na kirata Rahab, wadda ta zauna shuru. 8 Yanzu ka tafi, ka rubuta shi a gabansu a kan allo, ka maka shi a kan allon fata, domin a adana shi da kyau saboda lokaci mai zuwa ya zama shaida. 9 Gama mutanen nan 'yan tawaye ne, 'ya'ya maƙaryata, waɗanda ba za su ji umarnin Yahweh ba. 10 Sukan cewa masu duba, "Kar ku gani," ga kuma annabawa, "Kada ku faɗa mana annabcin gaskiya; ku faɗa mana maganganun wãsawa, annabcin ruɗami, 11 Kun kauce daga hanya, kun saki tafarki; kun sa Mai Tsarkin na Isra'ila ya daina magana a fuskarmu." 12 Saboda haka Mai Tsarki na Isra'ila yace, "Domin kun ƙi wannan magana, kun dogara ga zilama da ruɗi, kun jingina gare shi, 13 saboda haka wannan zunubi zai zamar maku kamar ɓangaren shashe dake shirin faɗuwa, kamar curi a kan bango mai tsayi wanda faɗuwarsa zata zo nan da nan, farat ɗaya." 14 Zai fasa shi kamar yadda tukunyar magini ke farfashewa; ba zai ƙyale ta ba, don kada a sami cikin farfasassun koda ɗan kaskon da za a ɗauko ɗan garwashin wuta daga sauran garwashin, ko a kwarfo ruwa daga cikin randa. 15 Gama wannan shi ne Ubangiji Yahweh, Mai Tsarki na Isra'ila yace, "Cikin komowa da hutu za ku tsira; cikin natsuwa da dogara ƙarfin ku zai tabbata. Amma ba ku yarda ba, 16 Kuka ce, 'A a, za mu gudu a kan dawakai,' haka za ku gudu; kuma, 'Za mu hau kan dawakai masu zafin gudu,' haka masu bin ku za su yi sauri. 17 Dubu za su gudu a tsoratawar mutum ɗaya; a tsoratawar biyar za ku gudu har sai sauranku da suka rage sun zama kamar sandar tuta a kan tsauni, ko kamar 'yar tuta a kan tudu." 18 Duk da haka Yahweh yana jira ya yi maku alheri, saboda haka a shirye ya ke ya nuna maku jinƙai. Gama Yahweh Allah ne mai adalci; masu albarka ne dukkan waɗanda suke jiransa. 19 Gama waɗansu mutane za su zauna a cikin Sihiyona, cikinYerusalem, ba za su ƙara yin kuka kuma ba. Hakika zai yi maku alheri da ya ji ƙarar kukan ku. Idan ya ji shi, zai amsa maku. 20 Koda shike Yahweh yana ba ku gurasar wahala da ruwan matsaloli, haka kuma, malaminku ba zai ƙara ɓoye kansa ba, amma za ku ga malamin ku da idanunku. 21 Kunnuwan ku za su ji magana a bayan ku, cewa, "Wannan ita ce hanya, yi tafiya a cikinta," sa'ad da kuka juya zuwa dama ko kuka juya zuwa hagu. 22 Za ku tozartar da sassaƙaƙƙun siffofin ku da a ka dalaye da azurfa da kuma sarrafaffun siffofinku na zinariya. Za ku zubar da su kamar ƙazamtattun tsunmokaran al'ada. Za ku ce masu, "Ku fita daga nan." 23 Zai bada ruwan sama domin iri lokacin da kuka yi shuka a ƙasa, da gurasa tare da yalwa daga ƙasa, amfani kuma zai zama da yawa. A ranar nan shanunku za su yi kiwo a makiyaya mai fãɗi. 24 Shanun noma da jakkai, da suke huɗa, za su ci gyararren abinci wanda aka sheƙe da cebur da matankaɗi. 25 Bisa kowanne dogon tsauni, da bisa kowanne dogon tudu, za a sami maɓuɓɓugai da rafuka masu gudanar da ruwa, a ranar gawurtaccen kisa sa'ad da hasumiyoyi za su faɗi. 26 Hasken wata zai zama kamar hasken rana, hasken rana zai ninka sau bakwai, kamar hasken kwana bakwai. Yahweh zai ɗaure karayar mutanensa ya warkar da ƙujewar raunin da ya yi masu. 27 Duba, sunan Yahweh ya zo daga wuri mai nisa, yana ƙũna da fushinsa kuma a cikin turmuƙin hayaƙi. Leɓunansa suna cike da zafi, harshensa kuma na kama da wuta mai cinyewa. 28 Numfashinsa yana kama da ambaliya wanda ruwansa ya kai har tsakiyar wuya, domin ya rairaye al'ummai da matankaɗin hallakarwa. Numfashinsa linzami ne a muƙamuƙan mutane yasa su warwatse. 29 Za ku sami waƙa da dare sa'ad da kuke biki mai tsarki, da murna a zuciya, kamar yadda wani zai tafi da sarewa bisa tsaunin Yahweh, zuwa ga Dutsen Isra'ila. 30 Yahweh zai sa aji muryarsa mai daraja, ya nuna motsin hannunsa cikin zafin fushinsa da harshen wuta, tare da guguwa, hadari, da ƙanƙara. 31 Gama da jin muryar Yahweh, Asiriyawa za su razana; zai fyaɗe su da sanda. 32 Kowanne dukkan sanda da Yahweh ya ƙaddara masu za a bi bayansa da waƙoƙin tambura da molo sa'ad da ya ke yaƙi da faɗa da su. 33 Domin an shirya wurin ƙũna tuntuni. Hakika, an shirya shi domin sarki, Allah ya shirya shi da zurfi da kuma faɗi. Tarin kuwa a shirye ne da wuta da kuma itace da yawa. Numfashin Yahweh, kamar rafin ƙibiritu ne da zai cinna masa wuta.

Sura 31

1 Kaiton waɗanda suke gangarawa zuwa Masar domin neman gudummuwa suna jingina ga dawakai, suna dogara ga karusai, (domin suna da yawa), da kuma mahayan dawakai (domin sun zarce ƙididdiga). Amma ba su damu da Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su kuma neman Yahweh! 2 Duk da haka yana da hikima, zai kuwa kawo masifa ba zai janye maganarsa ba. Zai tashi gãba da gidan mugunta, gãba kuma da kai gudummuwa ga masu aikata zunubi. 3 Masar mutum ne ba Allah ba, dawakansu kuma jiki ne ba ruhu ba. Lokacin da Yahweh zai miƙar da hannunsa, dukka da wanda ya yi gudummuwar zai yi tuntuɓe, wanda kuma a ka yiwa gudummuwar zai faɗi; su biyun za su hallaka tare. 4 Ga abin da Yahweh yace mani, "Kamar yadda zaki, har ma ɗan zaki ya kan yi ruri a kan dabbar da ya kashe, sa'ad da a ka kira ƙungiyar makiyaya a kansa, amma ba ya rawar jiki saboda muryoyinsu, ko ya sulale domin ƙararsu; haka Yahweh mai runduna zai sauko ya yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona, a kan tudun nan. 5 Kamar tsuntsaye masu shawagi bisa sheƙarsu, haka Yahweh mai runduna zai tsare Yerusalem; zai tsare ya kuma cece ta sa'ad da ya ke wuce wa bisanta ya kare ta. 6 Ki komo wurinsa shi wanda kika juya nesa daga gare shi, mutanen Isra'ila. 7 Domin a cikin wannan rana kowanne zai jefar da gumakansa na azurfa da gumakansa na zinariya wanɗanda hannuwanku ne cikin zunubi suka yi su. 8 Asiriya zata faɗi da kaifin takobi, takobin da ba mutum ne ya ke wurgawa ba zata hallaka shi. Zai gujewa takobi, matasanta za su yi aikin tilas. 9 Za su karai saboda razana, sarakunansu za su tsorata idan sun ga tutar yaƙin Yahweh - wannan furcin Yahweh ne - wanda wutarsa ke cikin Sihiyona, tanderun wutarsa kuma tana cikin Yerusalem.

Sura 32

1 Duba, wani sarki zai yi sarauta cikin adalci, yarimai kuma za su yi mulki da gaskiya. 2 Kowanne ɗayansu zai zama kamar wurin faƙewa daga iska da kuma mafaka daga hadari, kamar rafukan ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, kamar inuwar babban dutse a ƙasar gajiya. 3 Sa'an nan idanun waɗanda suke gani ba za su dushe ba, kuma kunnuwan waɗanda suke ji za su ji sarai. 4 Mai saurin baki zai yi tunani da kyau tare da ganewa, mai nauyin baki kuma zai yi magana da kyau da sauƙi kuma. 5 Ba za a ƙara kiran wawa nagari ba, ko a ce da mayaudari mai aminci. 6 Domin wawa yakan faɗi wauta, zuciyarsa takan shirya mugunta da mugayen ayyuka, yana kuma faɗar ƙarya akan Yahweh. Yakan tsiyatar da mayunwata, masu jin ƙishirwa kuma ya sa su rasa abin sha. 7 Dabarun mayaudari mugaye ne. Yakan ƙago mugayen shirye-shirye, domin ya lalatar da matalauta da ƙarairayinsa, koda matalaucin ya faɗi abin dake dai-dai. 8 Amma nagarin mutum yakan yi shiri nagari; kuma saboda nagargarun ayyukansa zai tsaya. 9 Ku tashi, ku matan dake zaman sake, ku saurari murya ta; ku 'ya'ya mata 'yan ba ruwanmu, ku saurare ni. 10 Gama nan gaba kaɗan da shekara guda ƙarfin halinku za a karya, ku mata masu zaman sake, gama ba za a sami girbin inabi ba, kuma ba amfanin da za a tattara a rumbuna. 11 Ku yi rawar jiki don tsoro, ku mata masu zaman sake; ku yi damuwa, ku masu ƙarfin hali; ku tuɓe ƙyawawan tufafinku, ku tsirance kanku; ku ɗaura tsummokin makoki a kwankwasonku. 12 Za kuyi kururuwa domin gonakinku masu yalwa, da inabinku masu 'ya'ya. 13 Ƙasar mutanena zata cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya, har ma a cikin dukkan gidaje da aka taɓa yin farinciki a birnin bukukuwa. 14 Gama za a yasar da fãda, birnin mai cincirindon mutane zai koma kango; da tudu da benen tsaro za su zama kogonni har abada, abin murna ga jakan jeji, wurin kiwo domin garkuna; 15 har sai an kwararo Ruhu a kanmu daga bisa, jeji kuma ya zama gonaki masu bada amfani, gonaki masu bada amfani kuma su zama kamar kurmi. 16 Sa'an nan hukunci za ya kasance a jeji; adalci kuma ya kasance a gonaki masu amfani. 17 Aikin adalci zai zama salama; sakamakon adalci, kwanciyar hankali da gabagaɗi har abada. 18 Mutanena za su zauna a cikin mazauni na salama, a cikin tsararrun gidaje, da natsattsun wuraren hutawa. 19 Amma koda an yi ƙanƙara ko kuma jeji duk ya ƙone, aka kuma rushe birnin gaba ɗaya, 20 ku da kuka yi shuka a bakin rafuffuka za a albarkace ku, da dukkan ku da kuke aika shanunku da jakai su yi kiwo.

Sura 33

1 Kaiton ka, mai ɓatawa ba a ɓata ka ba! Kaiton ka mai cin amanar waɗanda ba su ci amanarka ba! Lokacin da ka bar ɓatawa, za a ɓata ka. Lokacin da ka daina cin amana, za a ci amanar ka. 2 Yahweh, ka yi mana alheri; muna jiranka; ka zama damtsenmu kowacce safiya, cetonmu kuma a lokacin wahala. 3 Da jin ƙararka mai amo mutanen suka gudu; lokacin da ka tashi, al'ummai sai su watse. 4 Akan tara ganimarka kamar yadda fãri ke taruwa, kamar yadda fãri ke tsalle haka mutane ke tsalle a kanta. 5 Daukaka ga Yahweh, yana zaune a mafificin wuri. Zai cika Sihiyona da gaskiya da adalci. 6 Shi zai zama kafuwarmu a lokatanki, ceto a yalwace, hikima, da ilimi; da tsoron Yahweh shi ne dukiya mai tamani. 7 Duba, manzannin suna kuka a tituna; 'Jakadun masu begen salama, suna kuka mai zafi. 8 An yasar da karabku; ba bu sauran matafiya. Ana ta tada alƙawari, an wofintar da shaidu, kuma ba nuna bangirma ga ɗan adam. 9 Ƙasar tana makoki, duk ta yi yaushi; Lebanon ta kunyata ta kuma yi yaushi; Sharon kamar ƙasar filin hamada take; Bashan kuma da Kamel sun kakkaɓe ganyayensu. 10 "Yanzu ne zan tashi," inji Yahweh; "Yanzu ne za a ɗagani sama; yanzu za a fifita ni. 11 Kun ɗauki cikin ƙai-ƙai, kun haifi ciyawa; numfashinku wuta ce da zata cinye ku. 12 Mutanen za a ƙona su su zama danƙo, kamar yadda a ke sassare sarƙaƙƙiya a ƙone ta. 13 Ku da kuke nesa, ku ji abin da na yi; kuma ku da ke kusa, ku shaidi ƙarfina." 14 Masu zunubi a Sihiyona sun tsorata; makyarkyata ta kama marasa tsoron Allah. Wane ne a cikin mu zai iya zama da wuta mai ruruwa? Wane ne a cikin mu zai iya zaunawa da madawwamin ƙone-ƙone? 15 Shi wanda ya ke tafiya bisa adalci yana magana da gaskiya; wanda ke ƙin ribar zilama, yana ƙin karɓar toshi, ba ya shirye-shiryen ta'addanci; ba ya duban mugunta - 16 zai kafa gidansa a kan tuddai; Mafaƙarsa zai zama kagarar duwatsu; zai dinga samun abincinsa da ruwan shansa a kan kari. 17 Idanunku za su ga sarki cikin jamalinsa; za su ga babbar ƙasa. 18 Zuciyarka zata tuna da razanar da ta faru; ina magatakarda, ina mai auna kuɗi? Ina ya ke mai ƙididdiga hasumiyoyi? 19 Ba za ku ƙara ganin mutanen nan masu tawaye ba, mutane masu baƙon harshe, waɗanda ba ku fahimce su ba. 20 Dubi Sihiyona, birnin bukukuwanmu; idanunku za su ga Yerusalem kamar mazauni mai lafiya, rumfar da ba za a kawas ba, ƙusoshin ta ba za a tumbuƙe su ba, kuma igiyoyinta ba za a katse su ba. 21 Maimakon haka, Yahweh cikin daraja zai kasance tare damu, a wuri mai manyan koguna da rafuffuka. Ba jirgin ruwan yaƙi da zai bi ta cikinsa, ba kuma manyan jiragen da za su bi ta wurin. 22 Domin Yahweh ne alƙalinmu, Yahweh ne mai bamu shari'a; Yahweh ne sarkinmu; shi zai cece mu. 23 An kwance maɗaurinka, ba za su iya riƙe tirken tutar jirgin ruwa da ƙarfi ba; ba za su iya baza tutar jirgin ruwa ba; sa'ad da za a raba babbar ganima, har gurgu ma zai sami rabo. 24 Mazaunan wurin ba za su ce, "Ba ni da lafiya ba," mutanen dake zaune a can za a gafarta zunubansu.

Sura 34

1 Ku matso kusa, ku al'ummai, ku saurara; ku natsu, ku mutane! Duniya da dukkan cikarta dole su saurara, duniya, da dukkan abin da ke fitowa a cikinta. 2 Gama Yahweh yana fushi da dukkan al'ummai, da hasala ga dukkan rundunar yaƙin su; ya hallakar da su gaba ɗaya, ya bashe su ga yanka. 3 Za a jefar da gawawwakin matattunsu waje. Warin gawawwakin su zai bazu ko'ina; duwatsu kuma za su shanye jininsu. 4 Dukkan taurarin sama za su dushe, za a naɗe sammai kamar naɗaɗɗen littafi; dukkan taurarinsu za su dushe, kamar yadda ganyayen inabi suke karkaɗewa su faɗi daga itacen, kuma kamar yadda nunannun ɓaure ke faɗuwa daga jikin itacensa. 5 Sa'ad da takobina ya sha ya ƙoshi a sama; duba, yanzu zai gangara a kan Idom, akan mutanen da na keɓe domin hallakarwa. 6 Takobin Yahweh na ɗiɗɗigar da jini da kitse, tana ɗiɗɗigar da jinin 'yan raguna da na awaki, rufe da kitsen ƙodojin raguna. Gama Yahweh yana da hadaya a Bozra da kuma babban yanka a ƙasar Idom. 7 Za a kashe bijiman jeji tare da su, ƙananan bijimai tare da manyansu. Ƙasarsu za ta bugu da jini, ƙurarsu za ta yi ƙiba da kitse. 8 Gama zata zama ranar sãkayya ga Yahweh da shekarar kuma da zai sãka masu sabili da Sihiyona. 9 Kogunan Idom za a mai da su baƙin danƙo, ƙurarta kuma ta zama ƙibiritu, ƙasarta kuma ta zama baƙin danƙo mai cin wuta. 10 Zata ci wuta dare da rana; hayaƙinta zai tashi sama har abada; daga tsara zuwa tsara zata zama yasasshiyar ƙasa; ba wanda zai ratsa ta tsakiyarta har abada abadin. 11 Tsuntsaye jeji da dabbobi za su zauna a wurin; mujiya da hankaka za su yi sheƙar su a cikin ta. Kamar yadda mai gini ya ke amfani da igiyar gwaji haka zai auna ƙasar domin rusarwa da hallakarwa. 12 Ba za a bar wa shugabaninta komai da za su kira masarauta ba, kuma dukkan hakimanta ba za su zama komai ba. 13 ‌Ƙ‌ayayuwa za su cika fãdodinta, tsidau da dundu a wuraren tsaronta. Zai zama mazaunin diloli, farfajiyar jiminai. 14 Dabbobin jeji da kuraye za su tattaru a can, awakan jeji za su kira junansu da kuka. Dabbobin jeji masu yawon dare za su tare a nan su kuma samar wa kansu wurin hutawa. 15 Mujiyoyi za su yi sheƙa, za su nasa ƙwayayensu su ƙyanƙyashe, su ƙyanƙyashe su kuma tsare 'yan ƙananansu. I, a can hankaki za su taru, kowanensu da abokin tarayyarsa. 16 Ku binciko daga naɗaɗɗen littafin Yahweh; ba ko ɗayansu da za a rasa. Ba wanda zai rasa ɗan'uwan tarayyarsa; gama bakinsa ya umarta shi, ruhunsa kuma ya tattara su. 17 Ya jefa ƙuri'a domin mazaunansu, hannunsa kuwa ya auna masu shi da igiya. Za su mallaketa har abada; daga tsara zuwa tsara za su zauna a can.

Sura 35

1 Jeji da Hamada za su yi farin ciki; hamada kuma za ta yi murna ta faso da fure. Kamar tsire-tsire, 2 zata faso da furanni ainun ta yi murna da farin ciki da waƙa; za a ba shi darajar Lebanon, da kuma ɗaukakar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Yahweh, mafificiyar ɗaukakar Allahnmu. 3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku tsaida gwiwoyin masu kaɗuwa. 4 Ku ce wa matsorata, "Ku ƙarfafa, kada ku ji tsoro! Duba, Allahnku zai zo da ramako, da kuma sakamakon Allah. Zai zo kuwa ya cece ku." 5 Sa'an nan idanun makafi za su gani, kunnuwan kurame kuma za su ji. 6 Sa'an nan gurgu zai yi tsalle kamar barewa, bebe zai raira waƙa, gama ruwa zai malalo daga cikin Hamada, koguna kuma cikin jeji. 7 Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙasa mai ƙishin ruwa kuma zata zama maɓuɓɓugar ruwa; a mazaunin diloli, inda dă suka kwanta, za a tarar da ciyawa da iwa. 8 Wata karafka zata kasance a wurin ana kiran ta Hanya Mai Tsarki. Marar tsarki ba zai bi ta kanta ba. Amma zata kasance domin wanda ya yi tafiya a cikinta. Ba wawan da zai bi ta kanta. 9 Ba zakin da zai kasance a wurin, ba wata muguwar dabba da zata kasance a kanta; ba za a same su ba a can, amma fansassu ne za su yi tafiya a can. 10 Baratattun Yahweh za su komo za su taho suna waƙa zuwa Sihiyona, madawwamin farinciki zai kasance a kansu; murna da farinciki za su mamaye su; baƙinciki da ajiyar zuciya za su shuɗe.

Sura 36

1 A shekara ta goma sha huɗu ta sarki Hezekiya, Senakerib sarkin Asiriya, ya tasar wa dukkan biranen Yahuda da kagararsu ya kuma kame su. 2 Sai sarkin Asiriya ya aika da babban shugaban soja daga Lakish zuwa Yerusalem ga sarki Hezekiya tare da babban soja. Ya gabaci dai-dai magudanar kwarin da ya ke kawo ruwa, a babbar hanyar filin da masu wankin tufafi suka tsaya a kanta. 3 Shugabannin Isra'ilawa waɗanda suka fito wajen birnin su yi magana da su su ne Hilkiya ɗan Iliyakim, shugaba mai kula da fãda, Shebna sakataren sarki, da Yowa ɗan Asaf, wanda ke rubuta matakan gwamnati. 4 Sai shugaban sojoji yace da su, "Ku faɗawa Hezekiya babban sarki, sarkin Asiriya, yace, 'Me kake dogara da shi? 5 Ka na maganganun wofi marar amfani, cewa akwai shawara da ƙarfin yaƙi. To yanzu ga wa kake dogara? Wane ne ya baka ƙarfin zuciya da za ka yi mani tawaye? 6 Duba, kana dogora da Masar, da tsabgar da kake amfani da ita a matsayin sandar tafiya, amma duk mutumin da ya dogara da ita, zai karye ya soke hannunsa. Wannan shi ne Fir'auna sarkin Masar zai yiwa dukkan wanda ya dogara gare shi. 7 Amma idan ka ce da ni, "Mu na dogara ga Yahweh Allahnmu," ba shi ne wanda ya ke a manyan wurare da bagadai Hezekiya ya ɗauke, ya kuma ce Yahuda da Yerusalem, '"Dole ku yi sujada a wannan bagadi a Yerusalem ba"? 8 Saboda haka yanzu, zan ba ka abu mai kyau daga maigidana sarkin Asiriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, idan har za ka iya samin masu hawansu. 9 Ya ya zaka iya kaucewa ko ɗaya daga cikin barorin shugabana? Kana sa dogara ga karusai da mahaya dawakai na Masar! 10 To yanzu, na tafi can ba tare da Yahweh ba in tasar wa wannan ƙasar, har in lalatar da ita? Yahweh yace da ni, "Ka faɗawa wannan ƙasar har ka lalatar da ita.'"" 11 Sa'an nan Iliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce da babban shugaba, "Ka yi magana da barorinka a cikin harshen Aremiyanci, Aremaik, domin muna gane shi. Kada ka yi magana da mu da harshen Yahuda a kunnuwan mutane waɗanda suke a kan garu." 12 Amma babban kwamanda ya ce, "Babban sarki ya aiko ni ga shugabanku kuma ya faɗi waɗannan maganganu? Ba ya aiko ni ga jama'ar da suke a kan garu ba, waɗanda za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu tare da ku ba?" 13 Sai shugaban sojoji ya tsaya ya tada murya da ƙarfi a cikin Yahudanci, cewa, "Ku saurari magana daga babban sarki, sarkin Asiriya. 14 Sarki yace, 'Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, shi ba zai iya cetonku ba. 15 Kada kuma ku bari Hezekiya ya saku ku dogara ga Yahweh, cewa, '"Yahweh zai tabbatar da cetonku; wannan birni ba za a bada shi a hannun sarkin Asiriya ba.'" 16 Kada ku saurari Hezekiya, domin wannan shi ne abin da sarkin Asiriya yace: 'Ku nemi salama tare da ni kuma ku fito wuri na. Sai kowannenku ya ci daga cikin 'ya'yan inabin gonarsa, daga kuma itacen ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga rijiyon kansa. 17 Za ku yi wannan har saina zo na ɗauke ku zuwa wata ƙasa mai kama da irin ta ku, ƙasa mai hatsi da sabuwar inabi, ƙasa ta gurasa da kuringar inabi.' 18 Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, cewa, 'Yahweh zai kuɓutar da ku.' Ko akwai wasu allolin mutanen da suka cece su daga hannun sarkin Asiriya? 19 Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarwayim? Sun ceci Samariya daga ikona? 20 A cikin dukkan allolin waɗannan ƙasashe, akwai wani da ya ceci ƙasarsa daga ikona, ya ya kuke ganin kamar Yahweh zai ceci Yerusalem daga ikona? 21 Amma mutane suka tsaya tsit ba bu kuma wanda ya maida martani, don umarnin sarki, "Kada ku amsa masa." 22 Sai Iliyakim ɗan Hilkiya, wanda ya ke bisa iyalin, Shebna marubuci, da Yowa ɗan Asaf mai kula da tarihi, suka zo wurin Hezekiya da tufaffinsu a kekkece, kuma suka faɗa masa maganganun da shugaban mayaƙa ya faɗa.

Sura 37

1 Ya zamana a lokacin da sarki Hezekiya ya ji abin da suka faɗa, ya kekkece tufafinsa, ya rufe jikinsa da tsummoki, ya kuma shiga gidan Yahweh. 2 Ya aika Iliyakim, mai kula da fada, da Shebna marubucin shari'a, da dattawa firistoci, dukkansu suka rufe jikinsu da tsummoki, zuwa wurin Ishaya ɗan Amoz, annabi. 3 Suka ce da shi, "Hezekiya yace, 'Wannan rana ce ranar wahala da wulaƙanci da kunya, mun zama kamar lokacin da za a haifi yaro, amma uwar ba ta da ƙarfin da zata haifi yaron. 4 Watakila Yahweh Allahnka zai ji maganganun shugaban mayaƙansa, wanda sarkin Asiriya uban gidansa ya aiko domin ya wulaƙanta Allah mai rai, ya kuma tsawata wa maganganu waɗanda Yahweh Allahnka ya ji. Yanzu sai ka yi addu'a domin ringin da har yanzu suna nan.'" 5 Sa'ad da barorin sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, 6 sai Ishaya yace da su, "Ku faɗawa ubangidanku: 'Yahweh yace, "Kada ku ji tsoron irin maganganun da kuka ji, waɗanda dasu barorin sarkin Asiriya suka wulaƙanta ni. 7 Duba, zan sa ruhu a cikinsa, zai kuma ji jita-jitar da zata sa ya koma ƙasarsa. Zan sa shi ya faɗi ƙasa da takobi a cikin ƙasarsa.'"' 8 Sai shugaban mayaƙan ya koma ya kuma sami sarkin Asiriya yana yaƙi da Libna, domin ya ji sarki ya tafi daga Lakish. 9 Sa'ad da Senakerib ya ji Tirhaka sarkin Kush da Masar sun haɗu domin su yi yaƙi da shi, sai kuma ya aika da manzanni zuwa wurin Hezekiya tare da saƙo: 10 "Ka ce da Hezekiya, sarkin Yahuda, 'Kada ka bari Allahnka wanda kake dogara da shi ya ruɗe ka, cewa, 'Yerusalem ba zata faɗa hannun sarkin Asiriya ba." 11 Ku gani, ku kuma ji abubuwan da sarakunan Asiriya suka yiwa dukkan ƙasashe ta wurin lalata su ga baki ɗaya. Kuna tsammani za ku kuɓuta? 12 Ko allolin al'ummai sun kuɓutar da su, al'umman da ubannina suka lalata akwai Gozan, da Haran, Rezef, da kuma mutanen Iden a Tel-assa? 13 Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin biranen Sefarwayim, da Hena, da kuma Iwwa?'" 14 Hezekiya ya karɓi wannan wasiƙar daga hannun manzannin ya kuma karanta ta. Sai ya shiga gidan Yahweh ya baza ta gabansa. 15 Hezekiya ya yi addu'a ga Yahweh: 16 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, kai da ka zauna a sama da kerubim, kai kaɗai ne Allah a kan dukkan mulkokin duniya. Kai ka yi sammai da duniya. 17 Ka juyo da kunnuwanka, Yahweh, ka ji mu. Buɗe idanuwanka, Yahweh, ka gani, ka kuma ji maganar Senakerib, wanda ya aika don ya yi ba'a ga Allah mai rai. 18 I' gaskiya ne, Yahweh, sarakunan Asiriya sun lalata dukkan al'ummai da ƙasashensu. 19 Suka sa allolinsu a cikin wuta, domin su ba alloli ba ne amma ayyukan hannunwan mutane ne, itace da dutse ne kawai. 20 Saboda haka Asiriyawa sun lalata su. Yanzu dai, Yahweh Allahnmu, ka cece mu daga ikonsa, saboda dukkan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Yahweh." 21 Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wurin Hezekiya, cewa, "Yahweh, Allah na Israila yace, 'Domin ka yi addu'a gare ni a kan Senakerib sarkin Asiriya, 22 wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗa a kansa: "Akwai budurwar yariya ta Sihiyona ta rena ka kuma tana yi maka dariyar ba'a; budurwar Yerusalem tana girgiza kanta gare ka. 23 Wa ka rena ka kuma ci mutunci sa? Gãba da wa ka ɗaga muryarka, ka kuma ɗaga idanuwanka na girmankai? Gãba da Mai Tsarki na Isra'ila. 24 Ta wurin barorinka ka rena Ubangiji ka kuma ce, 'Da yawan karusaina har na kai ƙololuwar duwatsu, zuwa tsayin Lebanon. Zan sare dogayen itatuwan sida dana sifuros zaɓuɓɓu, na kuma kai wurare mafi nisa, na jeji mafi 'ya'ya. 25 Na gina rijiyoyi na kuma sha ruwa; Na busar da dukkan kogunan Masar ƙarƙashin sawayena.' 26 Baka ji yadda na ƙudura a yi haka tuntuni kuma na aiwatar tun zamanin ḍã? Yanzu ne nake cikawa. Kana nan ne domin ka mai da birane gagara-shiga zuwa tulin kango. 27 Mazaunan su, masu ƙaramin ƙarfi, sun warwatse da kunya. Sun zama tsire-tsire a gona, ɗanyar ciyawa, ciyawar dake kan rufi ko a fili, kafin iskar gabas. 28 Amma na san zaman ka, da fitar ka, da kuma zuwan ka, na san yadda ka harzuƙa gãba da ni. 29 Domin harzuƙar ka ta gãba da ni, kuma don girmankanka ya iso kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka, linzami na kuma a bakinka; zan komar da kai hanyar da ka biyo." 30 Wannan ita ce zata zama alama domin ka: A wannan shekara zaku ci gyauro, a kuma shekara ta biyu zaku shuka daga abin da ya tsiro daga gauron. Amma a shekara ta uku dole zaku yi shuka ku kuma girɓe shi, ku dasa kuringar inabi ku kuma ci 'ya'yanta. 31 Su da suke ringi na gidan Yahuda da waɗanda kuma suka tsira za su sake kafuwa su haifi 'ya'ya. 32 Domin daga Yerusalem ringin za su fito; daga Dutsen Sihiyona waɗanda suka tsira za su zo. Himmar Yahweh mai runduna zai yi wannan.'" 33 Saboda Yahweh ya faɗi wannan a kan sarkin Asiriya: "Ba zai shiga wannan birnin ba kuma ba zai harba kibiya a nan ba. Ba zai zo gare shi ba tare da garkuwa ko ya kafa sansanin tudu gãba da ita. 34 Ta hanyar da ya zo ta hanyar kuma zai koma; ba zai shiga wannan birni ba - wannan furcin Yahweh ne. 35 Zan kare wannan birnin zan kuma ceto shi, domin ni kaina da kuma bawa na Dauda." 36 Sai mala'ikan Yahweh ya fito ya fãɗa wa sansanin Asiriyawa, ya kashe sojoji 185,000. Da mutanen suka tashi da sassafe, sai suka ga jukunan matattu a kwakkwance ko'ina. 37 Senakerib sarkin Asiriya ya ƙyale Isra'ila ya koma gida ya zauna a Nineba. 38 Daga bisani, yayin da ya ke sujada a gidan Nisrok allahnsa, 'ya'yansa Adramelek da Shareza suka kashe shi da takobi. Sai suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Isahadon ɗansa ya yi sarauta a matsayinsa.

Sura 38

1 A kwanakin da Hezekiya ya ke ciwo har ya kusa mutuwa. Sai Ishaya ɗan Amoz, annabi, ya zo wurinsa, ya ce masa, "Yahweh yace, 'Ka kintsa komai dai-dai a gidanka; gama mutuwa za ka yi, ba za ka rayu ba,'" 2 Sai Hezekiya ya juya ya sa fuskarsa a bango ya yi addu'a ga Yahweh. 3 Ya ce, "Idan ka yarda Yahweh, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da dukkan zuciyata da aminci, yadda na yi abin da ke dai-dai a idanunka." Sai Hezekiya ya yi kuka da ƙarfi. 4 Sai maganar Yahweh ta zo wurin Ishaya, cewa, 5 "Tafi ka ce da Hezekiya, shugaban mutanena, 'Wannan shi ne abin da Yahweh, Allah na Dauda kakanka, ya ce: Na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka. Duba, ina shirin ƙara maka shekaru goma sha biyar nan gaba. 6 Daga nan zan cece ka da wannan birnin daga hannun sarkin Asiriya, kuma zan kãre wannan birni. 7 Wannan zai zama alama a gare ka daga Yahweh, zan yi abin da na alƙawarta. 8 Duba, zan komar da inuwa baya da taki goma na hawan benen Ahaz. Saboda haka inuwa ta koma baya da taki goma a kan hawan benen inda ta yi gaba. 9 Wannan ita ce rubutacciyar addu'ar Hezekiya sarkin Yahuda, lokacin da ya ke rashin lafiya daga nan kuma ya warke: 10 "Na ce tsakanin ƙarshen rayuwata zan koma daga ƙofofin Lahira; zan ƙarashe sauran shekaru a can. 11 Na ce ba zan ƙara ganin Yahweh, Yahweh a cikin ƙasar rayayyu ba; ba kuma zan ƙara duban wani mutum ko mazaunan duniya ba. 12 An datse raina an kuma tafi da shi daga gare ni kamar rumfar makiyayin tumaki; na naɗe raina kamar gado; kana sare ni daga masaƙa; tsakanin rana da dare zaka ƙarar da raina. 13 Na yi ta kuka har gari ya waye; kamar zaki yana kakkarya dukkan ƙasussuwana. Tsakanin rana da dare kana ƙarashe raina. 14 Kamar muryar ƙaramin tsuntsu; na yi kuka kamar kurciya; idanuna sun gaji don dubar sama. Ubangiji, an matsa mani; ka taimake ni. 15 Me zan iya faɗa? Ya yi magana da ni, ya yi haka, zan yi tafiya a hankali dukkan shekaruna sabili da baƙinciki ya rinjaye ni. 16 Ubangiji, wahalolin daka aiko suna da kyau a gare ni; ka dawo mani da raina; ka maido mani da raina da kuma lafiyata. 17 Domin amfani na ne na ji irin wannan baƙincikin. Ka cece ni daga kududufin hallaka; domin ka jefar da dukkan zunubaina bayanka. 18 Gama Lahira ba ta yi maka godiya; mutuwa ba ta yabonka; waɗanda suka tafi can cikin rami ba za su bege cikin amincinka ba. 19 Mutum mai rai, mutum mai rai, shi ne zai iya yi maka godiya, kamar yadda na ke yi a wannan rana, uba yana bayyanawa 'ya'ya irin amincinka. 20 Yahweh yana kusa da ceto na, za mu kuma yi buki tare da kaɗe-kaɗe da waƙoƙi dukkan ƙwanakin ranmu cikin gidan Yahweh." 21 Yanzu Ishaya yace, "Bari su ɗauki 'ya'yan ɓaure su cura a kuma sa shi akan marurun, zai kuma warke." 22 Hezekiya kuma ya ce, "Me zai zama alama da yasa zan iya zuwa gidan Yahweh?"

Sura 39

1 A wannan lokacin sai Maduk-Baladan ɗan Baladan, sarkin Babila, ya aika da wasiƙu tare da kyauta ga Hezekiya; domin ya ji cewa Hezekiya ya yi ciwo ya kuma sami lafiya. 2 Hezekiya kuwa ya ji daɗin waɗannan abubuwa; har ya kuma nuna wa manzannin ɗakin dukiyarsa - wato su azurfa, da zinariya, da kayan yaji, da mai mai daraja, da daƙin kayayyakinsa na yaƙi, da dukkan abin da ke cikin gidansa. Babu sauran wani abu da ya ke da shi a gidansa, ko cikin dukkan mulkinsa, wanda Hezekiya bai nuna masu ba. 3 Sai Ishaya annabi ya zo wurin sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi, "Me waɗannan mutane suka ce da kai? Daga ina suka zo?" Hezekiya yace, "Sun zo wuri na daga ƙasa mai nisa ta Babila." 4 Ishaya ya yi tambaya, "Me suka gani a gidanka?" Hezekiya ya amsa, "Sun ga dukkan abin da ya ke a gidana. Babu wani abu mai daraja da ban nuna masu ba." 5 Sai Ishaya yace da Hezekiya, "Saurari maganar da Yahweh mai runduna: 6 'Duba, ranaku sun kusa zuwa da za a kwashe komai a fadarka, abubuwan da kakaninka suka tara har ya zuwa yau, za a ɗauke su zuwa Babila. Ba abin da za a rage, in ji Yahweh. 7 'Ya'ya da aka haifa maka, waɗanda kai ka haife su - za a ɗauke su, kuma za su zama bãbãnni a fadar sarkin Babila.'" 8 Sai Hezekiya ya cewa Ishaya, "Maganar Yahweh wadda ka faɗa tana da kyau." Domin ya yi tunani, "Za a sami salama da kwanciyar rai a zamanina."

Sura 40

1 "Ta'aziya, ta'azanta mutanena," in ji Allahnka. 2 "Yi magana mai taushi ga Yerusalem; ka yi mata shela cewa yaƙinta ya zo ƙarshe, laifofinta kuma an gafarta mata, za ta sami ruɓi biyu daga hannun Yahweh domin dukkan zunubanta." 3 Wata murya ta koka, "A cikin jeji shirya hanyar Yahweh; a shirya ta miƙaƙƙiya a cikin Hamada doguwar hanya domin Allahnmu." 4 Kowanne kwari zai cika, za a baje kowanne tsauni da tudu; ƙasa mai kwazazzabai kuwa za ta zama sumul, wurare kuma masu gargada za su zama sarari; 5 kuma ɗaukakar Yahweh zata bayyana, dukkan mutane kuwa za su gan shi tare; gama bakin Yahweh ne ya faɗi haka. 6 Wata murya na cewa, "Yi kuka." Wata ta amsa, "Kukan me zan yi?" "Dukkan yan adam ciyawa ne, dukkan alƙawarinsu da amincinsu kamar furannin jeji. 7 Ciyawa ta kan bushe, furanni kuma su yanƙwane sa'ad da numfashin Yahweh ya hura a kansu; ba bu shakka mutane ciyawa ne. 8 Hakika ciyawa ta kan bushe, furanni kuwa kan yi yaushi, amma maganar Allahnmu zata tsaya har abada." 9 bisa tsauni mai tsayi, Sihiyona, mai ɗauke da labari mai daɗi. Ki yi kuwwa da ƙarfi, yaYerusalem. Ke da kika kawo labari mai daɗi, daga muryarki, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa biranen Yahuda, "Ga Allahnku!" 10 Duba, Ubangiji Yahweh yana zuwa kamar mayaƙi mai nasara, damtsensa mai ƙarfi zai yi masa mulki. Ga shi, da sakamako tare da shi, kuma waɗanda ya ceto sun sha gabansa. 11 Zai ciyar da garkensa kamar makiyayi, zai tattara 'yan tumakin a damtsensa, ya kuma ɗauke su kusa da zuciyarsa, kuma a hankali zai bida tumaki masu shayar da nono. 12 Wa ya taɓa auna ruwaye da tafin hannunsa, ko ya auna sararin sama da tafin hannunsa, ko ya iya riƙe ƙurar duniya a kwando, ko ya iya auna nauyi tsaunika a sikeli, ko tuddai a ma'auni? 13 Akwai wanda zai iya fahimtar tunanin Yahweh, ko ya ba shi umarni a matsayin mashawarcinsa? 14 Daga wurin wa ya taɓa karɓar umarni? Wane ne ya koya masa yadda zai yi abubuwa, ya kuma koya masa sani, ko ya nuna masa hanyar fahimta? 15 Duba, al'ummai na kamar digon ruwa a bokiti, kuma suna kama da ƙura a sikeli; duba, yana auna tsibirai kamar ɗan ɗigo. 16 Lebanon bata da isasshen fetur, ko dabbobin dajinta ba su isa baikon konawa ba. 17 Dukkan al'ummai ba isassu ba ne a gare shi; an ɗauke su ba a bakin komai bane a gare shi. 18 Da wa za ka iya ƙwatanta Allah? To da wanne gunki za ka kamanta da shi? 19 Gunki! Masassaƙi ne ya yi shi: makera suka dalaye da zinariya kuma suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa. 20 Domin miƙa baiko wani ya zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba; ya nemi ƙwararren maƙeri da zaya yi masa siffar gunkin da ba zaya fãɗi ba. 21 Ashe ba ka sani ba? Ashe ba ka ji ba? Ba a faɗa maka ba tun daga farko? Ba ka fahimta ba tun daga fara kafa harsashin duniya? 22 Shi wanda ya ke zaune a bisa bangon duniya; mazaunanta suna kama da fãri a gabansa. Ya miƙar da sammai kamar labule kuma ya baza su kamar rumfa domin a zauna ciki. 23 Yana maida masu mulki ba komai ba kuma yana maida masu mulkin duniya yadda ba a san da zamansu ba. 24 Suna kama da dashe kasafai, dashen da a ka shuka kasafai, dashen da bai yi ko saiwar da ta shiga ƙasa ba, sa'ad da ya hura a kansu sai su yi yaushi, kuma iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi. 25 "To, da wane ne za a kwatanta ni, ko akwai wani mai kama da ni?" in ji shi Mai Tsarki. 26 Dubi sararin sama a bisa! Wane ne ya halicce dukkan waɗannan taurarin? Shi ne wanda ya ke masu jagora kuma ya kira su bisa ga sunan kowa. Ta wurin ikonsa da girmansa da kuma ta wurin karfi da iko, ba ko ɗayansu da ya ɓace. 27 Me ya sa kuka ce, Yakubu, kuma kuka ce, Isra'ila, "Hanya ta a ɓoye take daga Yahweh, kuma Allahna bai damu da baratarwata ba"? 28 Ba ku sani ba? Ba ku kuma ji ba? Madawwamin Allah, Yahweh, shi ne mahaliccin ƙarshen duniya, ba ya taɓa jin gajiya ko kasala ba; ba shi da iyakar fahimta. 29 Yana ƙarfafa masu jin gajiya; masu kasala kuma ya kan sabunta ƙarfinsu. 30 Duk da matasa ma sukan ji kasala da gajiya, samari kuma sukan yi tuntuɓe su faɗi: 31 Amma waɗanda suke dogara ga Yahweh zai sabunta ƙarfinsu; za su tashi da fikafikai kamar gaggafa; za su yi gudu kuma ba za su gaji ba; za su yi tafiya amma ba za su suma ba.

Sura 41

1 "Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe; bari ƙasashe su sabunta ƙarfinsu; bari su matso kusa su yi magana; bari mu taru ga yin jayayya a kan saɓanin. 2 Wane ne wannan da ya motso wani daga gabas, ana kiransa cikin adalci ga aikinsa? Ya bada ƙasashe a gare shi ya kuma taimaka masa har ya yi nasara a kan sarakuna. Ya maida su ƙura da takobinsa, kamar ciyawar da iska ta hure da bakansa. 3 Yana biye da su har ma ya wuce lafiya, da sauri ƙwarai da ƙyar ƙafarsa take taɓa ƙasa. 4 Wane ne yasa wannan ya faru kuma su wane ne suka yi waɗannan ayyuka? Wane ne ya kirawo tsararraki tun daga farko? Ni, Yahweh, na farko, da na ƙarshe, Ni ne shi. 5 Tsibirai sun gani kuma sun ji tsoro; ƙarshen duniya ta girgiza; sun nufo har sun zo. 6 Kowanne ya taimaki makwabcinsa, kowanne kuma ya cewa ɗayan, 'Yi ƙarfin hali.' 7 Masassaki yana ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma wanda ya ke aiki da guduma yana ƙarfafa shi wanda ya ke aiki da tubalin ƙarfe, haka nan ya ke cewa mai walda, yana da kyau.' Suna buga ƙusoshi masu ƙarfi domin kada su tuntsure, 8 Amma kai, Isra'ila, bawana, Yakubu wanda na zaba, zuriyar Ibrahim abokina, 9 kai wanda na kawo ka daga maƙurar duniya, kuma wanda na kira daga wurare masu nisa, wanda na ce, 'kai ne bawana,' Na zaɓe ka ban kuma ƙi ka ba. 10 Kada ka ji tsoro, ina tare da kai. Kada ka damu da komai, ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka, zan kuma taimake ka, zan tallafe ka da hannunna na dama mai adalci. 11 Duba, za su ji kunya da ƙasƙanci, dukkan su da suke fushi da kai; za su zama ba komai ba za su kuma lalace, waɗannan da suke gãba da kai. 12 Za ka neme su amma ba za ku same su ba; wato waɗanda suke gãba da kai; za su zama kamar ba komai ba, ba bu shakka za su zama ba komai ba. 13 Gama Ni, Yahweh Allahnku, zan riƙe ka da hannun dama, ina faɗi maka, 'Ka da ka ji tsoro; ina taimakonka.' 14 Kada ka ji tsoro, kai tsutsa Yakubu, da ku mutanen Isra'ila; zan taimake ku - wannan furcin Yahweh ne, mai fansarku, Mai Tsarki na Isra'ila. 15 Duba, zan sa ku zama kamar ceburin sussuka mai kaifi, sabo mai baki biyu; za ku sussuke tsaunuka ku lalatar da su; za ku niƙe tuddai kamar ƙaiƙayi. 16 Za ku sheƙesu, iska kuma zata hure su; iska kuma zata warwatsa su. Za ku yi murna cikin Yahweh, za ku yi murna a cikin Mai Tsarki na Israi'la. 17 Waɗanda ake takurawa da mabuƙata za su nemi ruwa, amma ba bu, harsunansu za su bushe da ƙishi; Ni Yahweh, zan amsa addu'arsu; Ni Allah na Isra'ila, ba zan yashe su ba. 18 Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga gangare, maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a tsakiyar kwarurruka; zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa. 19 Zan sa itatuwan sida, da gawo su tsiro a jeji, da itacen ci-zaƙi, da itacen zaitun. Zan dasa siferas a hamada, tare da marke da wuraren renon itacen siferas. 20 Zan yi wannan domin mutane su gani, su sani, su kuma fahimta tare, hannun Yahweh ya yi wannan, Mai Tsarki na Isra'ila ya halitta shi. 21 "Faɗi maganarka," Inji Yahweh, "Faɗi jayayyarka mai kyau don gumakunka," inji Sarkin Yakubu. 22 Bari ku kawo ma na jayayyarku; ku zo ga ba ku furta ma na abin da da zai faru, saboda mu san waɗannan abubuwa sosai. Ku sa su faɗa mana yadda furcin za su zama, domin mu yi tunani a kansu mu kuma san yadda su ka cika. 23 Ku faɗa game da abubuwan da za su faru nan ga ba, domin mu san ko ku alloli ne; ku yi wani abu mai kyau ko bala'i, ko ma cika da jin tsoro ya kuma burgemu. 24 Ku duba, ku allolin wofi ne kuma ayyukan kuma na wofi ne; wanda ya zaɓe ku ma abin ƙyama ne. 25 Na ta da wani daga arewa, kuma ya zo; daga fitowar rana na kira shi wanda ya yi kira bisa sunana, wanda zai tattake masu mulki kamar laka, kamar yadda maginin tukwane ya ke tattake yumɓu. 26 Wa ne ne ya faɗa ma na wannan tun daga farko, ko ma sani? Kafin wannan lokaci, ko mu ce, "Ya yi dai-dai"? Babu ɗayansu da ya yi dokar haka, i, ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu. 27 Ni ne na farko da na ce da Sihiyona, "Duba ga su a nan;" Na aika manzo zuwa Urshalima. 28 Sa'ad da na duba, ba bu wani, ko ma a cikinsu wanda zai ba da shawara mai kyau, wanda idan Na yi tambaya, zai iya amsawa da magana. 29 Duba, dukkansu a wofi su ke, ayyukansu na wofi ne; zubin siffofinsu na ƙarfe adadin iska su ke, wofi ne kuma.

Sura 42

1 Duba, bawana, wanda na riƙe; zaɓaɓɓena, wanda na ke jindaɗin sa. Na sa Ruhuna a bisansa; za ya kawo hukunci ga al'ummai. 2 Ba za ya yi kuka ko sowa ba, ko ya sa a ji muryarsa a tituna ba. 3 Murzajjen kara ba za ya karya shi ba, lagwanin da ba ya ci sosai ba za ya ɓice shi ba: a cikin aminci za ya zartar da hukunci. 4 Ba za ya suma ba ko ya karaya har sai ya kafa hukunci a duniya; Ƙasashen tsibirai kuma suna jiran shari'arsa. 5 Ga abin da Allah Yahweh ya faɗa - shi wanda ya halicci sammai kuma ya shimfiɗasu, shi wanda ya yi duniya da dukkan abin da take fitarwa, shi wanda ya ke bayar da numfashi ga mutanen dake cikin ta da kuma rai ga waɗanda ke zaune a cikin ta: 6 "Ni, Yahweh, na kira ka cikin adalci kuma zan ri ƙe hannunka. Zan kiyayeka in sanya ka alƙawari domin mutane, haske kuma ga al'ummai, 7 Domin a buɗe idanun makafi, za a sako da 'yan kurkuku daga can cikin kogo da kuma waɗanda aka tsare a gidan tsaro waɗanda ke zaune a cikn duhu. 8 Ni ne Yahweh, sunana kenan; bazan raba ɗaukakata da wani ba ko yabona da sassaƙaƙƙun gumaka. 9 Duba, abubuwan da suka wuce sun faru, yanzu ina gaf da furta sabobbin al'amura. Kafin su fara afkuwa zan gaya maku game da su." 10 Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh, da kuma yabonsa daga ƙarshen duniya; ku waɗanda ke gangarawa zuwa teku, da dukkan abin da ke ciki, ƙasashen tsibirai da dukkan mazaunan cikin su. 11 Bari hamada da biranenta su koka, ƙauyuka kuma inda keda ke zaune, ku yi sowa ta farinciki! bari mazauna Sela su raira; bari su yi sowa daga ƙololuwar tsaunuka. 12 Bari su bada ɗaukaka ga Yahweh su kuma furta yabonsa a ƙasashen tsibirai. 13 Yahweh za ya fita a matsayin mayaƙi; a matsayin mutumin yaƙi za ya motsa himmarsa. Za ya yi sowa, I, za ya yi kururuwar koke-koken yaƙinsa; za ya nuna wa maƙiyansa ikonsa. 14 Na yi shiru na dogon lokaci; na tsaya cik na hana kaina; yanzu zan yi kuka kamar macen dake cikin naƙuda; zan yi nishi da huci. 15 Zan rusar da tsaunuka da tuddai in kuma sa ganyayensu su bushe; zan maida koguna tsibirai in kuma sa lakarsu su bushe. 16 Zan kawo makafi bisa hanyar da ba su sani ba; bisa tafarkun da ba su san zan bi da su ba. Zan mayarda duhu ya zama haske a gabansu, zan sa karkatattun wurare su miƙe. Zan yi waɗannan abubuwa, ba kuma zan yashe su ba. 17 Za a komar da su baya, za a san ya su cikin kunya gabaɗaya, wato su waɗanda suka sa dogararsu ga sassaƙaƙƙun siffofi, su waɗanda suke cewa sarrafaffun siffofin ƙarfe, "Ku ne allolinmu." 18 Ka saurara, kai kurma; ka duba, kai makaho, domin ka sami gani. 19 Wane ne makaho idan ba bawana ba? ko kurma kamar manzona wanda na aika? Wane ne ya yi makantar abokin alƙawarina, ko makaho kamar bawan Yahweh? 20 Kana ganin abubuwa da yawa, amma baka fahimta; kunnuwa a buɗe, amma ba bu mai ji. 21 Ya gamshi Yahweh ya yabawa hukuncinsa kuma yasa shari'arsa a bar ɗaukaka. 22 Amma waɗannan mutane ne waɗanda a ka yiwa fashi a ka kuma washe su; an datse su dukka a ramuka, sun zama abin washe wa ba bu kuma mai fansarsu, ba bu wanda kuma ya ce, "A maido da su!" 23 Wane ne a cikin ku za ya saurari wannan? Wane ne za ya saurara kuma ya ji a nan gaba? 24 Wane ne ya miƙa Yakubu ga ɗan fashi, Isra'ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Yahweh bane, wanda muka yiwa zunubi, wanda suka ƙi tafiya cikin hanyoyinsa, wanda kuma suka ƙi yin biyayya da shari'arsa? 25 Domin wannan ya zubo da fushinsa mai zafi a bisansu, da masifar yaƙi. Ya haska kewaye da su, amma ba su lura ba; ya ƙona su, amma ba su yi hattara ba a zukatansu.

Sura 43

1 Amma yanzu ga abin da Yahweh ya faɗa, shi wanda ya halicceka, Yakubu, shi wanda ya yi ka, Isra'ila: "Kada ka ji tsoro, gama na fansheka; na kiraka da sunanka, kai nawa ne. 2 Sa'ad da ka bi ta cikin ruwaye, zan kasance tare da kai; ta cikin koguna kuma, ba za su sha kanka ba. Sa'ad da ka yi tafiya ta cikin wuta ba za ka ƙone ba, harsashen wutar kuwa ba za ya lalatar da kai ba. 3 Gama ni ne Yahweh Allahnka, mai tsarki na Isra'ila, mai cetonka. Na ba da Masar diyya a kanka, Itiyofiya da Seba misanya dominka. 4 Tunda kana da tamani da muhimmanci a idanuna, ina ƙaunarka; saboda haka zan bayar da mutane misanya dominka, wasu mutanen kuma misanya domin rayuwarka. 5 Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; zan kawo zuriyarka daga gabas, in tattaro ka daga yamma. 6 Zan cewa arewa, 'Miƙosu,' kudu kuma, 'Kada ka riƙesu,' A kawo 'ya'yana maza daga ne sa, 'ya'yana mata kuma daga lungun sassan duniya, 7 dukkan wanda ake kira da sunana, wanda na halitta domin ɗaukakata, wanda na yi, I, wanda na halitta. 8 Fito da mutane makafi, koda ya ke suna da idanu, da kuma kurame, koda ya ke suna da kunnuwa. 9 Dukkan al'ummai ku tattaru wuri ɗaya, dukkan mutane kuma ku taru. Wane ne a cikinsu za ya furta wannan, ya kuma yi mana shelar al'amuran farko? Bari su kawo shaidunsu su tabbatar da gaskiyarsu, bari su saurara su kuma tabbatar, 'Gaskiya ne.' 10 Ku ne shaiduna," Yahweh ya furta, "Bawana kuma wanda na zaɓa, domin ku sani ku kuma gaskata da ni, ku kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu wani allah da a ka yi, kuma ba za ayi wani ba bayana. 11 Ni, ni ne Yahweh, kuma babu wani mai ceto sai ni. 12 Na furta, na ceto, kuma na yi shela, kuma babu wani allah a tsakaninku. Kune shaiduna," Yahweh ya furta, '"Ni ne Allah. 13 Daga wannan rana har zuwa nan gaba ni ne shi, kuma babu wanda za ya ceci wani daga hannuna. Na aikata, wane ne za ya canza?" 14 Wannan ne abin da Yahweh yace, Mai fansarku, Mai tsarki na Isra'ila: "Sabili da ku na yi aike a Babila na turasu dukka zuwa gudun hijira, na maida farincikin Babiloniyawa zuwa waƙoƙin makoki. 15 Ni ne Yahweh, Mai tsarkinku, Mahaliccin Isra'ila, Sarkinku." 16 Wannan shi ne abin da Yahweh yace (Wanda ya buɗe hanya ta cikin teku da kuma tafarki ta cikin manyan ruwaye, 17 wanda ya bida karusa da doki, sojoji da babbar runduna. Suka faɗi tare; ba za su sake tashi ba; an kawar da su, aka ɓice su kamar lagwanin da ke ci.) 18 Kada ku yi tunani akan waɗannan abubuwa da suka wuce, ko ku kula da abubuwan dã can. 19 Duba, ina gaf da yin sabon abu; yanzu ya fara faruwa; ba ku yi la'akari ba? zan yi hanya a hamada da magudanan ruwa a cikin jeji. 20 Dabbobin jeji za su girmamani, diloli da jiminai, saboda na bayarda ruwa a jeji, da koguna a hamada, domin zaɓaɓɓun mutanena su sha, 21 waɗannan mutane waɗanda na yi su domin kaina, domin su maimaita yabbaina. 22 Amma ba ku yi kira gare ni ba, Yakubu; kun gaji da ni, Isra'ila. 23 Ba ku kawo mani ko ɗaya daga cikin tumakinku ba a matsayin baye-bayen ƙonawa, ko kuka girmamani da hadayunku ba. Ban ɗora maku nauyin baye-bayen hatsi ba, ko na gajiyar daku da kawo turare. 24 Ba ku sawo mani ƙiraren ƙanshi da kuɗi ba, ko kuwa ku zubo mani kitsen hadayunku ba; amma kuna ɗoramani nauyin zunubanku, kun gajiyar da ni da miyagun ayyukanku. 25 Ni, I, Ni, Ni ne wanda na ke share kurakuranku sabili da ni; kuma bazan sake tunawa da zunubanku ba. 26 Ku tuna mani da abin da ya faru, bari mu yi mahawara tare; ku kawo ƙararku, domin a tabbatar da ku marasa laifi. 27 Ubanku na farko ya yi zunubi, kuma shugabanninku sun yi mani laifi. 28 Saboda haka zan gurɓata tsarkakan shugabanni; zan miƙa Yakubu ga lalacewa ɗungum, Isra'ila kuma ga wulaƙantaccen ƙasƙanci."

Sura 44

1 Ka saurara yanzu, bawana Yakubu, da Isra'ila, wanda na zaɓa: 2 Ga abin da Yahweh yace, shi wanda ya yi ka ya kuma nasa ka cikin mahaifa wanda kuma za ya taimake ka: "Kada ka ji tsoro, bawana Yakubu; da kai kuma, Yeshurun, wanda na zaɓa. 3 Gama zan zubo da ruwa a bisa ƙasa mai ƙishi, da magudanan ruwa a bisa busasshiyar ƙasa; zan zubo da Ruhuna a bisa zuriyarku, da albarkata a bisa 'ya'yanku. 4 Za su tsiro daga cikin ciyawa, kamar itatuwan kurmi dake gefen magudanan ruwa. 5 Wani za ya ce, 'Ni na Yahweh ne,' wani kuma za ya yi kira ga sunan Yakubu, wani kuma zaya rubuta a kan hannunsa, 'Na Yahweh ne,' ya kuma raɗawa kansa suna da sunan Isra'ila." 6 Wannan ne abin da Yahweh yace - Sarkin Isra'ila da mai fansarsa, Yahweh mai runduna: "Ni ne farko, ni ne kuma ƙarshe; babu kuma wani Allah sai ni. 7 Wane ne kamar ni? bari ya yi shela kuma ya yi mani bayanin al'amuran da suka afku tunda na kafa mutanen dã, bari kuma su yi bayanin al'amuran da za su zo. 8 Kada ku ji tsoro ko ku firgita. Ba na furta maku ba tuntuni, na kuma shelarda shi? Ku ne shaiduna: Akwai wani Allah baya gare ni? Babu wani Dutse; bansan da wani ba." 9 Dukkan masu sarrafa gumakai ba komai bane; abubuwan da suke jiwa daɗi wofi ne; shaidunsu basu gani ko sanin wani abu, kuma za a sa su sha kunya. 10 Wane ne za ya yi allah ko ya sarrafa gumaka da ke wofi? 11 Duba, dukkan abokan tarayyar shi za su sha kunya; masu sassaƙa shi mutane ne kawai. Bari su ɗauki matsayinsu tare; za su noƙe kuma za a sa su sha kunya. 12 Maƙeri na aiki da kayan aikinsa, ya yi su, ya zuga su a garwashi. Ya siffantashi da guduma ya aikatashi da ƙarfin damtsensa. Ya ji yunwa, ƙarfinsa ya ƙare; bai sha ruwa ba sai ya sume. 13 Kafinta yana gwada katako da abin gwaji, za ya yi mashi zane-zane da abin salo. Da kayan aikinsa zai yi masa siffofi, ya zãne shi da abin zãne. zai yi shi siffa-siffa bisa ga siffar mutum, kamar mutum mai ban sha'awa, domin ya zauna a cikin gida. 14 Yana saro itatuwan sida, ko ya zaɓo itatuwan sifares ko itacen rimi. Yana ɗaukowa kansa itatuwa daga jeji. Za ya dasa itacen fir ruwan sama kuma za ya sa ya yi girma. 15 Sai mutum ya yi amfani da shi ya kunna wuta kuma ya ji ɗumi. I, yana kunna wuta ya gargasa gurasa. Daga ciki kuma yana ɗauka ya yi wa kansa allah sai ya rusuna masa; ya yi wa kansa gumaka kuma ya rusuna masa. 16 Daga cikin katakan yana yin amfani da wasu ya kunna wuta, ya kuma gasa nama a kai. Ya ci ya ƙoshi. yana ɗunɗuma kansa sai ya ce, "Ah, na ji ɗumi, na ga wutar." 17 Sauran itatuwan da suka rage kuma sai ya yi allah da su, siffar da ya sassaƙa kuma; sai ya rusuna masa yana ba shi girma, sai ya yi addu'a gare shi yana cewa, "Cece ni, gama kai ne allahna." 18 Ba su sani ba, balle kuma su fahimta, domin idanunsu makafine ba su kuma gani, kuma zukatansu ba su ganewa. 19 Babu mai yin tunani, ko su yi nazari su ce, "Daga cikin katakon na yi abin wuta da wasu; I, kuma na gasa gurasa bisa garwashin. Na gasa nama bisa garwashin na ci. To ya ya zan ɗauki sauran katakon da ya rage in yi abin ƙazanta da shi domin sujada? Ya ya zan rusuna ga wani kututturen katako?" 20 Ya yi kamar toka ya ke ci; ruɗaɗɗiyar zuciyarsa ta sa ya kauce. Baya iya ceton kansa, ko kuwa ya ce, "Wannan abin da ke hannun damana ba allahn gaskiya ba ne." 21 Yi tunani a kan waɗannan abubuwa, Yakubu, da Isra'ila, domin kai bawana ne: na yi ka, kai bawana ne; Isra'ila bazan manta da kai ba. 22 Na share, ayyukan tawayenka sarai, kamar girgije mai kauri, kamar girgije kuma, zunubanka sun dawo mani, gama na fanshe ka. 23 Ku raira, ku sammai, gama Yahweh ya yi wannan; ku yi sowa, ku zurfafan duniya. Ku fashe da waƙa, ku tsunuka, kai daji da duk itatuwan da ke cikinka; gama Yahweh ya fanshi Yakubu, kuma za ya nuna ɗaukakarsa a Isra'ila. 24 Wannan ne abin da Yahweh yace, mai fansarka, wanda ya yi ka daga cikin mahaifa: "Ni ne Yahweh, wanda ya yi dukkan abubuwa, wanda shi kaɗai ya shimfiɗa sammai, shi kaɗai ya sarrafa duniya. 25 Ni wanda na lalata kayan tsafin masu maganar wofi na kuma wulaƙanta masu karanta kayan tsafin; Ni wanda na juyarda hikimar masu hikima na kuma maida shawararsu wawanci. 26 Ni, Yahweh, wanda ke tabbatarda maganganun bawansa wanda kuma ke sa hasashen manzanninsa su afku, wanda ya cewa Yerusalem, 'Za a sake zaunawa a cikinki,' da kuma garuruwan Yahuda, 'Za a sake ginaku, kuma zan ɗaga rusassun wurarensu'; 27 wanda ya ke cewa teku mai zurfi, 'Ki bushe, kuma zan busar da igiyoyinki.' 28 Yahweh ne ya faɗa game da Sairus, 'Makiyayina ne shi, za ya aiwatar da dukkan nufina; za ya zartar da doka game da Yerusalem, 'Za a sake ginata,' game da haikalin, 'Bari a sake kafa harsashensa.'"

Sura 45

1 Ga abin da Yahweh ya faɗi wa shafaffensa, ga Sairus, wanda nake riƙe da hannun damansa, domin inci ƙarfin al'ummai a gabansa, in tuɓe makaman sarakuna, in kuma buɗe ƙofofi a gabansa, domin ƙofofin su zauna a buɗe: 2 Zan shiga gabanka in rusar da duwatsu; zan farfasa ƙofofin tagullar in kuma dardatse sandunan ƙarfensu, 3 zan baka taskokan duhu da kuma dukiyoyin da a ka ɓoye, domin ka sani cewa Ni ne, Yahweh, wanda ya kira ka da sunanka, Ni, Allah na Isra'ila. 4 Saboda Yakubu bawana, da Isra'ila zaɓaɓɓena, na kira ka da sunanka: Ina baka daraja kaɗan, koda ya ke ba ka sanni ba. 5 Ni ne Yahweh, babu wani kuma; babu wani Allah sai ni. zan shirya ka domin yaƙi, koda ya ke ba ka sanni ba; 6 domin mutane susan cewa daga tasowar rana, daga kuma yamma, cewa babu wani allah sai ni: Ni ne Yahweh, babu kuma wani. 7 Ni na yi haske kuma na halicci duhu; Ina kawo salama in kuma ƙirƙiro bala'i; Ni ne Yahweh, wanda ke yin dukkan waɗannan abubuwa. 8 Ku sammai, ku kwararo ruwa daga sama! bari sararin sammai su kwararo da adalci. Bari duniya ta shanyesu, domin ceto ya tsiro, da adalci kuma su yi girma tare. Ni, Yahweh, na halicce su dukka. 9 Kaiton duk wani wanda ke gardama da wanda ya halicce shi, ga wanda ya ke kamar kowacce tukunyar yunɓu a cikin tukwanen yunɓu a ƙasa! yunɓun za ya iya cewa mai yin tukwanen, 'Me kake yi?' ko 'Aikin naka baya da abin riƙewa a jikinsa'? 10 Kaiton wanda za ya cewa Mahaifi, 'Mahaifin wa kake yi?' ko kuwa ga mace, 'Me kike haihuwa?' 11 Ga abin da Yahweh yace, Mai Tsarki na Isra'ila, Mahaliccinka: 'Me yasa kake tambayoyi game da abin da zan yi domin 'ya'yana? zaka gaya mani abin da zan yi game da aikin hannuwana?' 12 Ni na yi duniya kuma na halitta mutum a kanta. Hannuwana ne suka shimfiɗa sammai, kuma na umarci dukkan taurari su bayyana. 13 Na motsa Sairus cikin adalci, kuma zan miƙar da tafarkunsa dukka. Zai gina birnina; za ya bar mutanena 'yan gudun hijira su koma gida, ba kuma da farashi ba ko cin hanci,'" Yahweh mai runduna ya faɗa. 14 Ga abin da Yahweh ya faɗa, "Za a kawo maku cinikayyar Masar da fataucin Itiyofiya tare da Sabiyawa, mutane masu doguwar siffa. Za su zama naku. Za su biyo ku, tafe cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku suna roƙonku suna cewa, 'Tabbas Allah na tare daku, babu kuma wani sai dai shi.'" 15 Hakika kai ne Allah wanda ka ɓoye kanka, Allah na Isra'ila, Mai ceto. 16 Dukkansu za su kunyata su wulaƙanta tare; masu sassaƙa gumakai za su yi tafiya cikin ƙasƙanci. 17 Amma Yahweh za ya ceci Isra'ila da madawwamin ceto; ba za ku sake shan kunya ba ko ƙasƙanci. 18 Ga abin da Yahweh ya faɗa, shi wanda ya halicci sammai, Allahn gaskiya wanda ya ƙirƙiro duniya, ya halittata, ya kafa ta. Ya halittata, ba a matsayin jujiba, Ya zãna ta domin a zauna a cikinta: "Ni ne Yahweh, babu wani kuma. 19 Ban yi magana a asirce ba, a wani ɓoyayyen wuri; Ban cewa zuriyar Yakubu, 'Ku neme ni a wofi ba!' Ni ne Yahweh, Mai yin magana a gaskiya; Ina furta abubuwan da ke dai-dai. 20 Ku tattaro kanku ku zo! ku taru wuri ɗaya, ku 'yan gudun hijira daga cikin al'ummai! basu da Ilimi, su waɗanda ke ɗaukar sassaƙaƙƙun siffofi su kuma yi addu'a ga allolin da ba su iya ceto. 21 Ku zo kusa ku furta mani, ku kawo shaida! bari su yi mugun shirinsu tare. Wane ne ya nuna wannan tundã can? Wane ne ya yi shelar shi? Ba Ni ne ba, Yahweh? Babu wani Allah sai dai ni, Allah baratacce Mai ceto kuma; babu wani baya gare ni. 22 Ku juyo gare ni ku sami ceto, ku dukkan ƙarshen duniya; gama Ni ne Allah, babu wani kuma. 23 Na yi rantsuwa da kaina, maganar dokar adalci tawa, kuma ba za ta koma baya ba: 'A gare ni kowacce gwiwa zata durƙusa kuma kowanne harshe za ya rantse. 24 Za su ce mani, "A cikin Yahweh ne kawai akwai ceto da ƙarfi kuma.""' Ma su jin haushina kuma za su sha kunya. 25 A cikin Yahweh dukkan zuriyar Isra'ila za su barata; za su yi taƙama a cikinsa.

Sura 46

1 Bel ta rusuna, Nebo ta sunkuya; an ɗauke gumakansu a bisa dabbobi da bisashen ɗaukar kaya. Waɗannan gumakai da kuka ɗauko kaya ne masu nauyi a bisa dabbobin da suka gaji. 2 Gaba ɗaya sun sunkuya ƙasa, durƙushe a ƙasa; basu iya fanso siffofin, su kansu kuma sun tafi cikin bauta. 3 Ku saurareni, gidan Yakubu, dukkanku ragowar gidan Isra'ila, waɗanda nake ɗauke daku tun kafin a haifeku, a ɗauke tun daga mahaifa. 4 Har zuwa tsufanku Ni ne shi, kuma zan ɗaukeku har sai gashinku ya zama furfura. Na halicceku kuma zan riƙeku; zan ɗaukeku kuma zan fansheku. 5 Da wa za ku kwatantani? da wa kuke tunanin na yi kama, domin ku kwatantamu? 6 Mutane sukan zubo da zinari waje daga Jaka sukan kuma gwada azurfa a bisa ma'auni. Sai su yi hayar maƙeri, sai ya narka ya yi masu allah; sai su rusuna su kuma yi mashi sujada. 7 Za su ɗagashi su ɗora a kafaɗa su ɗaukeshi; sai su ajiye a wurin zamansa, zai tsaya a wurin zamansa ba kuma zai matsa daga wurin ba. Za su yi kuka zuwa gare shi, amma ba za ya iya amsawa ba ko kuwa ya ceci wani daga matsalarsa. 8 Ku yi tunani game da waɗannan abubuwa; kada ku yi watsi dasu, ku fitsararru! 9 Ku yi tunani game da abubuwan farko, na lokutan da suka wuce, gama Ni ne Allah, babu wani kuma, Ni ne Allah, babu wani kama da ni. 10 Ina sanar da ƙarshen tun daga farko, tukunna kuma abin da bai riga ya faru ba; Na faɗa, "Shirina za ya faru, kuma zan yi yadda nake so." 11 Na kira tsuntsun ganima daga gabas, mutumin dana zaɓa kuma daga ƙasa mai nisa; I, na faɗa; Zan kuma aiwatar da shi; ina da manufa, zan kuma aikata. 12 Ku saurareni, ku mutane marasa ji, waɗanda ke nesa da yin abin dake dai-dai. 13 Ina kawo adalcina kusa; baiyi nisaba, kuma cetona baya jira; zan bada ceto kuma ga Sihiyona kyauna kuma ga Isra'ila.

Sura 47

1 Sauko ki zauna cikin turɓaya, ke budurwa ɗiyar Babila; zauna ƙasa babu kursiyi, ɗiyar Kaldiyawa. Baza a sake kiranki mai kwarjini da taushi ba. 2 ‌Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; kware lulluɓinki, ki tuɓe doguwar rigarki, buɗe ƙafafunki, ki tsallake rafuffuka. 3 Za a buɗe tsiraccinki, I, za a ga kunyarki: I zan ɗauki fansa kuma bazan bar kowa ba. 4 Mai fansarmu, Yahweh mai runduna sunansa, Mai tsarki na Isra'ila. 5 Ki zauna shiru ki tafi cikin duhu, ke ɗiyar Kaldiyawa; domin ba za a sake kiranki sarauniyar masarautai ba. 6 Na yi fushi da mutanena; na lalata gãdona na miƙasu cikin hannunki, amma ba ki nuna masu jinƙai ba; ki ka ɗora kaya mai nauyi bisa tsofaffin mutanen. 7 Ki ka ce, "Zan yi mulki har abada a matsayin sarauniya ni kaɗai." ba ki yi la'akari da abubuwannan ba a zuciyarki, ba ki kuwa duba yadda za su kasance ba. 8 To yanzu saurari wannan, ke da kika ƙaunaci annashuwa kika zauna a tsare; ke da kika ce a zuciyarki, "Zan wanzu, babu kuma wani kamar ni; Bazan taɓa zaunawa kamar gwauruwa ba, ko in taɓa fuskantar rashin 'ya'ya ba." 9 Amma abubuwan nan biyu za su zo maki a lokaci guda a rana ɗaya: rashin 'ya'ya da gwauranci; da cikakken ƙarfi za su afko maki, duk da sihirinki da surkullen ki masu yawa da layunki. 10 Kin dogara ga muguntarki; ki ka ce, "Babu mai gani na"; hikimarki da iliminki sun kai ki ga hallaka, amma kika ce a zuciyarki, "Na wanzu, babu kuma wani kama da ni." 11 Bala'i za ya afko maki; ba za ki iya korar shiba da surkullenki. Lalacewa zata faɗo maki; ba za ki iya kawar da ita ba. Babbar hasara zata afko maki nan da nan, kafin ki farga. 12 Ki yi naciya wurin zuba magungunanki da sihirorinki mãsu yawa waɗanda kika yi aminci wurin nanatawa tun cikin kuruciyarki; watakila za ki yi nasara, watakila za ki kori bala'in. 13 Kin gaji da yawan zuwa wurin bokayenki; bari su waɗannan mutanen su tashi su ceceki - su waɗanda ke shawagi a sammai suna duba taurari, waɗanda ke furta sabobbin watanni - bari su ceceki daga abin da zaya faru dake. 14 Duba, za su zama kamar haki, wuta za ta cinye su. Ba za su ceci kan su ba daga cikin harsashen. Babu garwashin da za su ji ɗumi dashi babu kuma wutar da za su zauna a gefe! 15 Ga abin da za su zama a gare ki, su waɗanda kika yi aiki tare da su, kika yi saye da sayarwa tare da su da ki na yarinya, dukkansu kuma su ka ci gaba da aikata abubuwansu na wawanci; da kika yi kukan neman taimako kuma, ba bu wanda zai iya ƙwato ki."

Sura 48

1 Ku saurara, ya gidan Yakubu, waɗanda a ke kira da suna Isra'ila, waɗanda kuma kuka fito daga tsatson Yahuda; ku da kuka yi rantsuwa da sunan Yahweh kuka kuma tono Allahn Isra'ila, amma bada gaske ba ko kuma ta hanyar adalci. 2 Domin suna kiran kansu mutanen birni mai tsaki masu dogara kuma ga Allahn Isra'ila. Yahweh mai runduna ne sunansa. 3 Na furta abubuwa tunda daɗewa; sun fito daga bakina, na sa a sansu, sai nan da nan kuma na yi su, su ka kuma kasance. 4 Saboda na sani ku masu taurinkai ne, tsokar wuyanku ta cije kamar karfe, goshinku kuma kamar tagulla, 5 domin wannan na furta waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na sanardaku, domin kada ku ce, 'Gunkina ya yi wannan,' ko kuwa 'Sassaƙaƙƙen siffana ko sarrafaffen siffar ƙarfena ya ƙaddara waɗannan abubuwa.' 6 Kun ji game da waɗannan abubuwa; ku duba dukkan alamunnan; kuma ku, ba za ku yarda da cewa abin da na faɗi gaskiyane ba? Daga yanzu zuwa nan gaba, zan nunamaku sabobbin abubuwa, ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba. 7 Yanzu, ba daga baya ba, za su kasance, kuma kafin yau ba ku taɓa ji game da su ba, saboda haka ba za ku iya cewa, 'I, na san da su ba. 8 Ba ku taɓa ji ba; ba ku sani ba; ba a bayyana abubuwan nan a kunnuwanku ba kafin yanzu. Domin na san ku macutane sosai, kuma ku masu taurinkai ne tunda a ka haife ku. 9 Sabili da sunana zan yi jinkirin fushina, domin darajata kuma zan dakata daga lalatar daku. 10 Duba, na tãce ku, amma ba kamar azurfa ba; Na tsarkakeku cikin garwashin azaba. 11 Sabili da kaina, sabili da kaina zan aiwatar; domin tayaya zanbar sunana ya wulaƙanta? ba zan bayar da ɗaukakata ga wani dabam ba. 12 Ku saurareni, Yakubu, da Isra'ila, wanda na kira: Ni ne shi; Ni ne farko, Ni ne kuma ƙarshe. 13 I, hannuna ya kafa harsashen duniya, hannun damana kuma ya shimfiɗa sammai; Idan na yi kira gare su, suna tashi tsaye tare. 14 Ku tattara kanku, dukkanku, ku saurara! wane ne a cikinku ya yi shelar waɗannan abubuwa? Wanda Yahweh ya zaɓa za ya cika nufinsa a kan Babila. Za ya aiwatar da nufin Yahweh a kan Kaldiyawa. 15 Ni, na faɗa, I, na kiraye shi, na kawo shi, kuma za ya yi nasara. 16 Ku zo kusa da ni, ku saurari wannan: Tun daga farko ban yi magana a asirce ba; sa'ad da ya faru, ina nan." Yanzu Ubangiji Yahweh ya aike ni, da Ruhunsa kuma. 17 Ga abin da Yahweh, Mai fansarku, Mai tsarki na Isra'ila ya faɗa, "Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ke koya maku yadda za ku yi nasara, wanda ke bida ku a hanyar da za ku bi. 18 Inda ace kawai kunyi biyayya da dokokina! da salamarku da wadatarku sun malala kamar kogi, cetonku kuma kamar raƙuman teku. 19 Da yawan zuriyarku yakai kamar rairayi, 'ya'ya kuwa daga mahaifarku kamar ƙwayoyin rairayi; da baza a datse sunansu ba ko kuwa a gogesu daga gabana. 20 Ku fito daga Babila! ku tsere daga Kaldiyawa! da ƙarar kuka mai ƙaraurawa ku yi shelar shi! ku sanar da wannan, ku sa ya bazu zuwa iyakar duniya! Ku ce, 'Yahweh ya fanshi bawansa Yakubu.' 21 Ba su ji ƙishi ba da ya bida su ta cikin jeji; Ya sa ruwa ya kwararo daga dutse dominsu; Ya fasa dutse, ruwayen kuwa suka ɓulɓulo. 22 Babu salama ga mugu - inji Yahweh."

Sura 49

1 Ku saurare ni, ku dake gaɓar tekuna! ku kasa kunne gare ni, ku manisantan mutane. Yahweh ya kira ni tun da a ka haife ni da suna na, sa'ad da mahaifiyata ta kawo ni cikin duniya. 2 Ya maida bakina kamar takobi mai kaifi; ya ɓoye ni a inuwar hannunsa; ya maida ni gogaggiyar kibiya; a cikin kwarinsa ya ɓoye ni. 3 Ya ce mani, "Kai bawana ne, Isra'ila, wanda ta wurinka ne na nuna ɗaukakata." 4 Amma sai na ce, "Koda ya ke nayi zaton nayi aiki a banza, na ɓata karfina a banza, duk da haka adalcina yana ga Yahweh, kuma sakamakona na gun Allahna." 5 Yanzu Yahweh ya yi magana - wanda ya sifanta ni daga haihuwata in zama bawansa, za ya maida Yakubu kuma gare shi, domin a tattaro Isra'ila zuwa gare shi, gama an ɗaukaka ni a gaban Yahweh, kuma Allahna ya zama ƙarfina - 6 sai ya ce, "Abu mafi ƙanƙanta kai ka zama bawana da zan sa ya sake kafa kabilun Yakubu, ya kuma farfaɗo da tsirarrun Isra'ila. Zansa ka zama haske ga Al'ummai, domin ka zama cetona ga duk karshen duniya." 7 Wannan ne abin da Yahweh yace, mai 'Fansar Isra'ila, Mai Tsarkin Nan nasu, gare shi wanda a ka rena ransa, al'ummai suka ƙi shi, da kuma barorin masu mulki, "Sarakuna za su ganka su miƙe, kuma "hakimai za su ganka su rusuna, saboda Yahweh mai aminci ne, wato Mai Tsarkin nan na Isra'ila, wanda ya zaɓe ka." 8 Ga abin da Yahweh ya faɗi, "A lokacin dana shirya nuna tagomashina zan ba ka amsa, kuma a ranar ceto zan taimake ka; zan yi maka kariya, in kuma bada kai a matsayin alƙawari domin mutanen, domin a sake gina ƙasar, a kuma sake raba gãdon da ya lalace. 9 Za ka cewa 'yan kurkuku, 'Ku fito waje;' ga waɗanda ke ramuka masu duhu, 'Ku nuna kanku.' Za su yi kiwo a hanyoyi, kuma dukkan sararin gangare zai zama makiyayarsu. 10 Ba za su ji yunwa ko ƙishi ba, ko kuwa zafi ko rana ta buge su, domin shi mai yi masu jinƙai zai jagorance su; zai bishe su har ga maɓulɓulan ruwa. 11 Daga nan zan sa dukkan tsaunuka su zama hanya, in kuma sa karafku su zama miƙaƙƙu." 12 Duba, waɗannan za su zo daga nesa, waɗansu daga arewa da yamma; waɗansu kuma daga ƙasar Sinim. 13 Ku yi waƙa, sammai, da murna, duniya; fashe da waƙoƙi ku duwatsu! Gama Yahweh zai ta'azantar da mutanensa, ya kuma ji tausayin nãsa masu tsanancin wahala. 14 Amma Sihiyona ta ce, "Yahweh ya yashe ni, kuma Ubangiji ya manta da ni." 15 Mace za ta iya mantawa da jaririnta, da ke shan nononta, har ta rasa jin tausayin ɗan da ta haifa? I, za su iya mantawa, amma Ni ba zan manta daku ba. 16 Duba, na zana sunanki a tafin hannuwa na; katangunki na gabana a kowanne lokaci. 17 'Ya'yanki suna dawowa da sauri, yayin da waɗanda suka lalatar dake suna watsewa. 18 Duba kewaye ki gani, suna tattarowa suna zuwa gare ki. Lallai hakika idan ina raye - wannan Yahweh ne ya faɗa -za ki sa su kamar kayan ado, ki kuma sanya su kamar amarya. 19 Koda shi ke ke lalatacciya ce kuma kufai, ƙasa ce da dã a ka hallakar, yanzu za ki yiwa mazaunan ƙasar ƙanƙanta, kuma masu takura maki za su yi nisa dake. 20 'Ya'yan da a ka haifa a lokacin da a ka yi maki rashi za su faɗa a kunnuwanki, 'Wurin ya yi mana ƙanƙanta, a yi mana ƙãri, saboda mu zauna a nan.' 21 Sa'an nan za ki tambayi kanki, 'Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'yan domina? An yi mani rashi kuma ni bakarariya ce, mai gudun hijira da sakakkiya ni ke. Wane ne ya yi renon waɗannan yaran? Duba, ni kaɗai a ka bari; daga ina waɗannan suke?"' 22 Wannan ne abin da Ubangiji Yahweh yace, "Duba, Zan tayar da hannuna ga al'ummai; Zan tayar da tutar alamata ga mutane. Za su zo da 'ya'yanki maza a hannuwansu su kuma taho da 'ya'yanki mata a kafaɗunsu. 23 Sarakuna za su zama kamar ubanninki, kuma sarauniyoyinsu kamar masu renonki; za su rusuna maki da fuskokinsu ƙasa suna lasar ƙurar ƙafafunki; kuma za ki san cewa ni ne Yahweh; waɗanda suke jira na ba za su kunyata ba." 24 Za a iya karɓe ganima daga jarumi, ko a ƙubutar da kamammu daga 'yan ta'adda? 25 Amma ga abin da Yahweh yace, "I, za a karɓe kamammun daga jarumi, kuma a washe ganimar; Gama zan yi tsayayya da magabcinki in kuma ceci 'ya'yanki. 26 Zan ciyar da masu tsananta maku da naman jikinsu; kuma za su bugu da jininsu, kamar a ce ruwan inabin ne. Sai dukkan 'yan adam su sani cewa Ni, Yaweh, ne mai cetonku da mai fansarku, Maɗaukaki na Yakubu."

Sura 50

1 Wannan ne abin da Yahweh ya faɗi, "Ina takardar saki da na saki mahaifiyarku? ga waɗanne masu bina bashi na sayar daku? Duba, an sayar daku domin laifofinku ne, domin kuma tayarwarku, a ka kori mahaifiyarku. 2 Me yasa na zo amma babu kowa a wurin? Me yasa na yi kira amma babu wanda ya amsa? Hannu na ya gajarce ga fansar ku ne? Ko babu iko a gare ni da zan ƙuɓutar da ku? Duba, ga tsautawata na busar da teku; na maida koguna hamada; kifayensu suka mutu domin rashin ruwa suka ruɓe. 3 Na suturtar da sararin sama da duhu; Na rufe shi da tsummoki." 4 Ubangiji Yahweh ya bani harshe kamar na ɗaya daga cikin waɗanda a ka koyar dasu, saboda in yi maganar ƙarfafawa ga gajiyayyu; yana farkar da ni daga safiya zuwa safiya; ya kan tasar da kunnena ga saurarawa kamar waɗanda a ka koyar dasu. 5 Ubangiji Yahweh ya buɗe kunne na, kuma ban zama mai tayarwa ba, ban kuma koma baya ba. 6 Na bada bayana ga masu bugu na, kuncina kuma ga masu tuge mani gemu; ban ɓoye fuskata ba daga ayyukan ban kunya da tofa miyau ba. 7 Gama Ubangiji Yahweh zai taimake ni; saboda haka ba zan wulaƙanta ba; don haka na maida fuskata kamar dutsen ƙyastawa, domi na san ba zan kunyata ba. 8 Shi wanda zai yi mani adalci yana kusa, Wane ne zai yi jayayya da ni? Bari mu tsaya mu fuskanci juna. Wane ne mai tuhuma ta? Bari ya zo kusa da ni. 9 Duba, Ubangiji Yahweh zai taimake ni. Wane ne zai furta ni mai laifi ne? Duba za su koɗe kamar tufafi; ƙwaro mai cin kaya zai cinye su ɗungum. 10 Wane ne a cikinku ke tsoron Yahweh? Wane ne ke biyayya da muryar bawansa? Wa ke tafiya a cikin zurfafan duhu ba tare da haske ba? Sai ya dogara da sunan Yahweh ya kuma jingina ga Allahnsa. 11 Ku duba, dukkan ku masu kunna wuta, masu tanadawa kansu cociloli: ku yi tafiya cikin hasken wuta da harsunan wutar da kuka kunna. Wannan ne abin da ku ka karɓa daga gare ni: za ku kwanta a wurin azaba.

Sura 51

1 Ku saurare ni, ku da ke biɗar ayyukkan adalci, ku dake neman Yahweh: Ku dubi dutsen da aka sassaƙo ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka yanko ku. 2 Ku duba Ibrahim, mahaifinku, da Saratu wadda ta haife ku; gama tun yana mutum guda, na kirawo shi, na albarkace shi na maida shi mai yawa. 3 I, Yahweh zai ta'azantar da Sihiyona; zai ta'azantar da dukkan kufanta; jejinta ya maida kamar gonar Iden, kuma sararin hamadarta a gefen kogin Yodan ya maida kamar lambun Yahweh; za a sami farinciki da murna a cikinta, godiya, da ƙarar waƙa. 4 Ku kasa kunne gare ni, mutane na; ku kuma saurare ni mutane na. Gama zan zartar da doka, kuma zan sa hukuncina ya zama haske domin al'ummai. 5 Adalci na ya kusato; ceto na zai fito, kuma hannu na zai hukunta al'ummai; ƙasashen kurmi za su jira ni; domin damtsena za su jira ni da ɗoki. 6 Ku ɗaga idanuwanku ga sararin sama, sai ku kalli duniya a ƙasa, gama sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za ta shuɗe kamar tufa, kuma mazaunanta za su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai ci gaba har abada, gama adalcina ba zai taɓa daina aiki ba. 7 Ku saurare ni, ku da kuka san abin da ya ke dai-dai, ku dake da dokokina a zukatanku: kada ku ji tsoron zage-zagen mutane, ko ku karaya saboda wulaƙancinsu. 8 Gama ƙwaro mai cin kaya zai cinye su kamar tufafi, tsutsa kuma ta cinye su kamar ulu; amma adalci na zai dawamma har abada, cetona kuma ga dukkan tsararraki." 9 Farka, farka, ka suturtar da kanka da ƙarfi, damtsen Yahweh. Tashi kamar kwanakin dã, tsararraki na zamanan dã. Ba kai ba ne ka ragargaza Rahab, kai da ka soke dodon ruwa? 10 Ba kai ka busar da teku ba, ruwayen manyan zurfafa, ka kuma maida tsakiyar teku hanya domin wucewar tsararraki? 11 Waɗanda Yahweh ya fansa za su dawo su zo Sihiyona tare da kukan farinciki tare kuma da murna har abada a kawunansu; kuma murna da farinciki za su mallake su, baƙinciki da makoki za su tsere daga gare su. 12 Ni, Ni, ne shi wanda ke ta'azantar da ku. Me ya sa kuke tsoron mutane, waɗanda za su mutu, da 'ya'yan ɗan Adam, wanɗanda aka yi su kamar ciyawa? 13 Donme ku ka mance da Yahweh wanda ya yi ku, wanda ya miƙar da sammai ya kuma kafa harsasan duniya? Kun kasance a cikin fargaba kowacce rana saboda zafin fushin mai zalunci sa'ad da ya shirya ya yi hallaka. Ina hasalar mai zaluncin? 14 Wanda ya rusuna ƙasa, Yahweh zai hanzarta 'yantar da shi; ba zai mutu kuma ya je rami ba, ko ya rasa gurasa ba. 15 Gama Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ke motsa teku saboda raƙuman ruwa su yi ruri - Yahweh mai runduna ne sunan sa. 16 Na sa maganata a bakinka, kuma na rufe ka da inuwar hannuna, domin in dasa sammai, in kafa harsasan duniya, in kuma cewa Sihiyona, 'ku mutanena ne.'" 17 Farka, farka, tashi tsaye Yerusalem, ke da kika bugu a hannun Yahweh daga kwanon fushinsa; ke da kika bugu daga kwanon, har zuwa dago-dago daga ƙoƙon tangadi. 18 Babu kowa a cikin dukkan 'ya'yanta maza da ta haifa da zai yi mata jagora; babu kowa kuma daga cikin 'ya'yanta maza waɗanda ta rayar da su da zai riƙe hannunta. 19 Waɗannan matsalolin biyu sun faru dake - wa zai yi makoki tare dake? - kaɗaici da hallaka, da yunwa da takobi. Wane ne zai ta'azantar dake? 20 'Ya'yanki maza sun some; suna kwance a kowacce kwanar tituna, kamar barewa a tarko; suna cike da fushin Yahweh, da tsautawar Allahnki. 21 Amma yanzu ki ji wannan, ke da a ke muzguna wa ke bugaggiyar nan amma bada ruwan inabi ba 22 Ubangijinki Yahweh, Allahnki wanda ke kãriyar ki ya ce, "Duba, na ɗauki ƙoƙon tangaɗi daga hannun ki -kwanon, wadda shi ne ƙoƙon fushi na. domin kada ki sake shan sa kuma. 23 Zan sa shi a hannun masu ba ki wuya, waɗanda suka ce maki, 'Ki kwanta a ƙasa don mu yi tafiya bisan ki; kin maida bayanki kamar ƙasar da a ke takawa, kamar kuma tituna domin su yi tafiya akai."

Sura 52

1 Farka, farka, ki sa ƙarfinki, Sihiyona; ki sa sababbin tufafinki, Yerusalem, Birni mai tsarki, gama marasa kaciya da kazamtattu ba za su sake shigar ki ba. 2 Girgiza kanki daga ƙura; tashi ki zauna, Yerusalem; cire sarƙa daga wuyanki, ɗaurarriya, ɗiyar Sihiyona. 3 Gama ga abin da Yahweh ya faɗi, "An sayar dake a banza, kuma za a fanshe ki ba tare da ƙuɗi ba." 4 Gama ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi, "Da farko mutane na zun je can Masar domin zama na 'yan kwanaki; Asiriya bada dadewa ba ta muzguna masu. 5 Yanzu me nake da shi a nan - wannan furcin Yahweh ne - ganin an ɗauke mutane na babu dalili,? Waɗanda suke mulkinsu suka yi ba'a - Wannan furcin Yahweh ne - kuma aka ci gaba da saɓon suna na dukkan rana. 6 Saboda haka mutane na za su san sunana; za su sani a ranan nan cewa ni ne wanda ya ce, "I, Ni ne!" 7 Yaya kyaun sawayen manzo mai kawo labarai ma su daɗi ya ke akan duwatsu, wanda ke shelar salama. wanda ke riƙe da saƙonni masu daɗi, wanda ya shelar ceto, wanda ya cewa Sihiyona, "Allahnki na mulki!" 8 Ki saurara! masu tsaronki sun ɗaga muryoyinsu, tare suna sowa don murna, gama za su gani, kowanne idonsu, dawowar Yahweh zuwa Sihiyona. 9 Ku fashe da waƙoƙin farinciki tare, ku duk kufan Yerusalem; Gama Yahweh ya ta'azantar da mutanensa; ya fanso Yerusalem, 10 Yahweh ya buɗe damtsensa mai tsarki a gaban dukkan al'ummai; dukkan duniya za su ga ceton Allahnmu. 11 Tafi, tafi, fita daga nan; kar ki taɓa wani kazamtaccen abu; tafi daga cikinta; ku tsarkake kanku, ku da ke ɗauke da taskokin Yahweh. 12 Gama ba za ku tafi a cikin hanzari ba, ko ku tafi a cikin fargaba ba; gama Yahweh zai tafi gabanku; kuma Allah na Isra'ila zai kasance a bayanku. 13 Duba, bawana zai yi aiki da hikima; za ya zama da ɗaukaka sosai, kuma za a ɗaukaka shi, 14 Kamar yadda da yawa suka yi fargaba da kai - kamanninsa ya lalace fiye da kowanne mutum, kuma fasalinsa bai sake yin kama da wani abu na mutum ba. 15 Duk da haka, bawa na zai yayyafa al'ummai masu yawa sarakuna kuma za su rufe bakunansu saboda shi. Gama abin da ba a taɓa faɗa masu ba, za su gani, kuma abin da ba su taɓa ji ba, za su gane.

Sura 53

1 Wane ne ya gaskata da abin da ya ji daga gare mu, kuma ga wane ne aka bayyana hannun Yahweh? 2 Gama ya yi girma a gaban Yahweh kamar 'yar itaciya, kuma kamar tsiro daga cikin busasshiyar ƙasa; ba shi da wani kyakkyawan jamali ko daraja; sa'ad da muka ganshi, babu wani kyau da zai rinjaye mu. 3 Mutane suka rena shi suka kuma ƙi shi; mutumin baƙinciki, kuma wanda ya saba da raɗaɗi. Kamar wanda mutane ke ɓoye fuskarsu daga gare shi; aka rena shi; muka kuma ɗauke shi ba a bakin komai ba. 4 Amma tabbas ya sungumi cututtukanmu ya kuma ɗauke baƙincikinmu; duk da haka mun yi zaton cewa Allah ne ke hukunta shi, Allah ya mazge shi, ya kuma azabta. 5 Amma an soke shi saboda ayyukan tayarwarmu; aka ragargaje shi saboda zunubanmu. Hukunci domin salamarmu ya kasance a kansa, kuma ta wurin raunukansa muka warke. 6 Dukkanmu kamar tumaki muka bijire; kowannenmu ya juya zuwa hanyarsa, kuma Yahweh ya ɗora masa laifuffukanmu dukka. 7 An muzguna masa; duk da haka sa'ad da ya ƙasƙantar da kansa, bai buɗe bakinsa ba; kamar ɗan ragon da za'a kai yanka, kuma kamar tumakin dake tsaye shiru a gaban masu sausaya, haka shi ma bai buɗe bakinsa ba. 8 Ta wurin wulaƙantarwa da hukuntawa aka kayar da shi; wane ne daga wancan tsara ya sake yin tunani a kansa? Amma an datse shi daga ƙasar masu rai; saboda laifuffukan mutanena aka yanke masa hukunci. 9 Suka sa kabarinsa tare da ma 'yan ta'adda, tare da mai arziki a mutuwarsa, koda ya ke bai yi tawaye ba, ko kuwa wata ruɗarwa a bakinsa. 10 Duk da haka, nufin Yahweh ne a murkushe shi a sa shi ciwo. Sa'ad da ya mai da kansa baiko domin zunubi, zai ga 'ya'yansa, zai daɗa tsawon kwanakinsa, kuma dalilin Yahweh zai cika ta wurinsa. 11 Bayan wahalar rayuwarsa, zai ga haske kuma ya gamsu da saninsa. Bawana mai adalci zai baratar da mutane da yawa; zai ɗauki laifuffukansu. 12 Saboda haka zan ba shi nasa kason a cikin yawan mutane, kuma zai raba ganimar da mutane da yawa, domin ya sa kansa ga mutuwa, aka kuma ƙidaya shi tare da masu kurakurai. Ya ɗauki zunuban mutane da yawa ya kuma yi roƙo domin masu kurakurai.

Sura 54

1 "Yi waƙa, ke bakarariya, ke da ba ki haihu ba; ki fashe da waƙar farinciki ki yi kuka da karfi, ke da ba ki taɓa yin naƙudar haihuwa ba. Gama 'ya'yan yasassa sun fi na matar da aka aura," inji Yahweh. 2 Ki faɗaɗa girman rumfarki, ki baza labulen rumfarki da faɗi; bada ƙwauro ba; ki daɗa tsawon igiyoyinki; ki miƙar da dirkokinki, 3 Gama za ki bazu ta hannun dama da ta hagu, har sai zuriyarki sun mamaye al'ummai sun kuma sake kafa yasassun birane. 4 Kada ki ji tsoro domin ba za ki ji kunya ba, ko ki karaya ba gama ba za a wulaƙanta ki ba; za ki mance da abin kunyar kuruciyarki da wulaƙancin yashewarki. 5 Gama wanda ya Yiki shi ne mijinki; Yahweh mai runduna shi ne sunansa. Mai Tsarkin nan na Isra'ila shi ne mai Fansarki; Shi a ke kira Allahn dukkan duniya. 6 Gama Yahweh ya sake kirawo ki a matsayin matar da aka yasar da take kuma cikin ƙunci a ruhu. Kamar matar da a kuruciyarta aka aurota sa'an nan aka ƙi ta," inji Allahnki. 7 Gama na yashe ki na ɗan lokaci kaɗan, amma da tausayi mai girma zan tattara ki. 8 A sa'ad da na yi fushi mai zafi, na ɓoye fuskata daga gare ki na wani lokaci; amma da madawwamin alƙawari aminci zan yi maki jinƙai - inji Yahweh, wanda ya ƙubutar dake. 9 Gama wannan kamar ruwayen Nuhu ne a gare ni: kamar yadda na rantse cewa ruwayen Nuhu ba za su sake shan kan duniya ba, saboda haka na rantse cewa ba zan yi fushi dake ko in kwaɓe ki ba. 10 Koda shi ke tsaunuka za su iya faɗuwa kuma tuddai su girgizu, duk da haka madawwamiyar ƙauna ta ba zata rabu da ke ba, ko alƙawarin salamata ya girgiza ba - inji Yahweh, wanda ke yi maki jinƙai. 11 Mai ƙunci, wanda guguwa ke kora kuma marar ta'aziyya, ku duba, zan sa shiryayyar hanya da dutsen tukoyis, in kuma kafa harsashenki da saffiyes. 12 Zan sa sorayenki da duwatsu masu ƙawa ƙofofinki kuma da duwatsu masu walƙiya, da kuma katangarki ta waje da kyawawan duwatsu. 13 Sa'an nan Yahweh zai koyar da dukkan 'ya'yanku; kuma salamar 'ya'yanku zata yi yawa. 14 A cikin adalci zan sake kafa ku. Ba za ku ƙara fuskantar tsanantawa ba, gama ba za ku ji tsoro ba; kuma ba abin ban tsoro da zai yi kusa da ku ba. 15 Duba, idan wani ya tada rikici, ba zai zama daga gare ni ba, duk wanda ya tada rikici da ku, za ku yi nasara a kansa. 16 Duba na halici maƙeri, mai hura garwashin wuta ya ƙera makamai na aikinsa, Ni kuma na hallici mai hallakarwa domin ya hallakar. 17 Babu makamin da aka ƙera gãba da kai da zai yi nasara; kuma zan kayar da duk wanda ya tuhume ka. Wannan shi ne gădon bayin Yahweh, kuma kariyarsu daga gare ni take. wannan furcin Yahweh ne."

Sura 55

1 Ku zo, kowannen ku dake jin kishin ruwa, ku zo wurin ruwan, ku da baku da kuɗi, ku zo, ku saya, ku ci, ku zo ku sayi ruwan inabi da madara kyauta da arha kuma. 2 Me ya sa kuke auna azurfa domin abin da ba abinci ba, kuma me yasa kuke aiki domin abin da ba ya ƙosarwa? Ku saurare ni sosai ku ci abin dake da kyau, ku kuma yi farinciki cikin ƙoshi. 3 Ku juyo da kunnuwanku ku zo gare ni! Ku saurara, domin ku rayu! Zan yi madawwamin alƙawari da ku - ingantacce, amintacciyar ƙauna dana alƙawarta wa Dauda, 4 Duba, na sashi a matsayin shaida ga al'ummai, a matsayin shugaba da mai ba da umarni ga mutane. 5 Duba, za ku kira ga al'umman da baku san su ba; kuma al'umman da basu san ku ba za su rugo gunku saboda Yahweh Allahnku, Mai Tsarki na Isra'ila wanda ya ɗaukaka ku." 6 Ku nemi Yahweh tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa. 7 Bari mai mugunta ya bar tafarkinsa, haka nan mai zunubi ya bar tunane-tunanensa. Bari ya komo wurin Yahweh, sai ya yi masa jinƙai, da kuma Allahnmu wanda zai gafarta masa a yalwace. 8 Gama tunane-tunanena ba dai-dai ne da tunane-tunanenku ba, kuma hanyoyinku ba dai-dai da nawa ba - wannan furcin Yahweh ne - 9 gama kamar yadda sammai ke nesa da duniya, haka hanyoyina ke nesa da taku, haka kuma tunane-tunanena ke nesa da tunane-tunanenku. 10 Gama kamar yadda ruwa da ƙanƙara ke saukowa daga sama, kuma basu komawa sai sun jiƙa ƙasa, susa amfaninta su tsiro su bada 'ya'ya ga manomin da ya yi shuka ya kuma bada abinci ga mai ci, 11 haka nan ne maganata wadda ta fito daga bakina zata kasance - ba za ta komo gare ni a banza ba, amma zata yi nasara a kan abin da na aike ta ta aiwatar. 12 Gama za ku fita da farinciki, a kuma jagorance ku a cikin salama; Tsaunuka da tuddai za su farfashe da murnar ihu a gabanku, kuma dukkan itatuwan filaye za su tafa hannuwansu. 13 A maimakon ƙayoyin saura, itatuwa masu ganyaye za su fito; kuma a maimakon itacen ƙaya, itacen ganye mai kyau zai fito, kuma zai zama domin Yahweh, domin sunansa, kamar madawwamiyar alama da ba za a tsige ba."

Sura 56

1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi, "Ku yi abin dake dai-dai; ku yi abin da ya kamata; gama cetona ya yi kusa, kuma adalcina na gaf da bayyana. 2 Mai albarka ne mutumin dake yin wannan, wanda kuma ya riƙe shi kam-kam. Ya kiyaye ranar Asabaci, ba ya ƙazamtata, yana kuma kiyaye hannunsa daga aikin mugunta." 3 Kada bãƙon da ya zama mai bin Yahweh yace, "Yahweh zai tuge ni daga cikin mutanensa." Kada bãbã yace, "Duba, ni busasshen itace ne." 4 Gama wannan ne abin da Yahweh yace, "Ga bãbãnni da ke kiyaye Asabataina kuma suna zaɓen abin dake faranta mani rai, su kuma riƙe alƙawaraina kam-kam, 5 dominsu ne zan kafa alama a cikin gidana da ganuwata abin tunawa da yafi samun 'ya'ya maza da mata. Zan ba su madawwamin abin tunawa da ba za a taɓa datsewa ba. 6 Haka ma bãƙin da suka haɗa kansu da Yahweh - su ɓauta masa, waɗanda kuma suke son sunan Yahweh, su ɓauta masa, duk wanda ke lura da Asabaci, da wanda ke kãre kansa daga ƙazamta, da wanda ya riƙe alƙawari na kam-kam 7 - zan kawo su ga tsarkakken tsaunina in sa su yi farinciki a gidan addu'a ta; baye-bayensu na ƙonawa da hadayunsu za su samu karɓuwa a bagadina. Gama za'a kira gidana gidan addu'a domin dukkan al'ummai, 8 Wannan ne furcin Ubangiji Yahweh, wanda ya tattara korarrun Isra'ila - Zan sake tattaro waɗansu in haɗa tare da su." 9 Dukkanku namomin jeji na saura, ku zo ku lanƙwame, dukkan ku dabbobin cikin kurmi! 10 Dukkan matsaransu maƙafi ne, ba su fahimta ba. Su dukka karnuka dake shiru ne waɗanda ba su iya yin haushi. Suna mafarki, kuma a kwance suna ƙaunar yin barci. 11 Karnukan na da babban marmarin ci; Ba za su taba samun abin da ya ishe su ba; su makiyaya ne da ba su da ganewa; dukkansu sun juya ga ta su hanya, kowannensu na ƙyashin mugun ribar kansa. 12 "Zo," suka ce "bari mu sha ruwan inabi da barasa mai karfi," Gobe zai zama kamar yau, rana mai girma fiye da yadda a ke tsammani."

Sura 57

1 Adali ya hallaka, babu wanda ya kula, kuma mutanen amintaccen alƙawari sun taru a can, amma ba wanda ya gane cewa an ɗauke mai adalici ne daga mugunta. 2 Ya shiga cikin salama; suna hutawa a cikin gadajensu, waɗanda ke tafiya a cikin kamilcinsu 3 Amma ku zo nan, ku 'ya'yan masu sihiri, 'ya'yan mazinaciya da matar da ta karuwantar da kanta. Wane ne kuke yi masa ba'a da murna? 4 Gãba da wa kuke buɗe bakunanku kuke gwalo? Ku ba 'ya'yan tayarwa ba ne, 'ya'yan zamba? 5 Kuna ɗuma kanku ku da kuke kwance tare ƙarƙashin itacen rimi, ƙarƙashin kowanne koren itace, ku dake kashe 'ya'yanku a cikin rafuffukan da suka ƙone da ƙarƙashin duwatsu masu maratayi 6 A cikin abubuwa masu laushi na rafin gangare su ne aka ba ku. Wato kayan ibadarku. Kun zuba ruwan baikon abin sha gare su kuka kuma ɗaga baikon hatsi. A waɗannan abubuwan ne ya kamata in ji daɗi? 7 Kun shirya gadonku a ƙwanƙwolin tsauni; kun kuma tafi sama can domin ku miƙa hadayu. 8 A bayan ƙofa da ƙyaurayen kuka shirya alamunku; kun yashe ni, kun yi wa kanku tsiraici, sai kuka haura sama; kuka yi gadonku da faɗi. Kuka yi yerjejeniya da su; kuka ƙaunaci gadajensu; kuka ga tsiraicinsu. 9 Kun tafi wurin Molek da mai; kun ruɓanɓanya turare. Kun aika jakadunku nesa; kun gangara zuwa Lahira. 10 Kun gaji saboda doguwar tafiyarku, amma ba ku taɓa cewa, "babu bege ba." Kun sami rai a hannuwanku; saboda haka ba ku karaya ba. 11 Wane ne kuke damuwa dominsa? Wane ne kuke jin tsoronsa da yawa har ya sa kuka aikata abin ruɗi, harma kun manta da ni ko ku yi tunani akai na? Saboda na yi shiru na dogon lokaci, harma yanzu kun dena jin tsoro na. 12 Zan sanar da dukkan ayyukan adalcinku in kuma faɗi dukkan abin da kuka yi, amma ba za su taimake ku ba. 13 Sa'ad'da kuka yi kũka, bari tarin gumakanku su 'yantar daku. Maimakon haka iska za ta ɗauke su dukka, wani numfashi zai ɗauke su dukka. Duk da haka wanda ya yi mafaka a cikina zai gaje ƙasar ya kuma mallaki tsarkakken tsaunina. 14 Zai ce, 'Gina, gina! A shãre hanya! Cire dukkan abin sa tuntuɓe a hanyar mutanena!'" 15 Gama ga abin da mai girma maɗaukaki Kaɗai yace, wanda ke zaune har abada, wanda sunansa tsarki ne, "Ina zaune a maɗaukakin wuri mai tsarki, tare da shi kuma mai karyayye da ƙasƙantaccen ruhu, in falkar da ruhun masu ƙasƙantar da kai, in farkar da zuciyar masu tawali'u. 16 Gama ba zan yi zargi har abada ba, ko in yi fushi har abada ba, domin ruhun mutum zai some a gabana, rayyukan dana halitta, 17 Saboda da zunubinsa na ribar ƙwãce, Na yi fushi, Na kuma hukunta shi; Na ɓoye fuskata na kuma yi fushi, amma ya koma da baya cikin hanyar zuciyarsa. 18 Na ga hanyoyinsa, amma zan warkar da shi. Zan jagorance shi in kuma ta'azantar da shi in kuma ƙarfafa waɗanda ke makoki dominsa, 19 kuma ni na hallici diyan lebuna. Salama, salama, ga waɗanda ke nesa da na kusa - inji Yahweh - Zan warkar da su. 20 Amma miyagu suna kama da haukan teku, wanda ba zai huta ba, kuma ruwayen suna amayar da taɓo da laka. 21 Babu salama domin mugu - inji Allah."

Sura 58

1 Yi kuka da ƙarfi; kada ku dena. Ku ɗaga muryarku kamar kakaki. Ku ta'azantar da mutanena a kan tayarwarsu, da kuma gidan Yakubu a kan zunubansu. 2 Duk da haka suna nema na kullum suna kuma fahariya a sanin hanyoyina, kamar al'umma dake yin aɗalci da ba su yashe da dokokin Allahnsu ba. Suna tambayata hukuncin aɗalci; Suna jin daɗin tunani a kan Allah ya kusance su. 3 Me yasa muka yi azumi,' suka ce, 'amma ba ka gani ba? Me yasa muka ƙasƙantar da kanmu, amma ba ka kula ba?' Duba, a ranar azuminku, kuna neman jin daɗinku kuna kuma danne dukkan ma'aikatanku, 4 Duba, kuna azumi ku yi faɗace-faɗace, kuma ku bugu da hannun mugunta; ba za ku yi azumi yau wanda za ku sa a ji muryarku a sama ba. 5 Wannan shi ne lallai irin azumin da zan so: Ranar da wani zai ƙasƙantar da kansa, ya sunkuyar da kansa kamar ciyawa, kuma ya yafa tsummokara da toka a ƙarƙashinsa? Kun tabbata za ku kira wannan azumi, rana wadda ta gamshi Yahweh? 6 Wannan ba shi ne azumin dana zaɓa ba: A saki miyagun sarƙoƙi, a kwance igiyoyin karkiya, a sa waɗanda aka ragargaza su sami 'yanci, a kuma karya kowacce karkiya? 7 Ko kuma ku raba gurasarku da mayunwata ku kuma shigo da marasa mazauni cikin gidanku ba?" Idan ku ka ga wani tsirara, sai ku suturtar da shi; kuma kada ku ɓoye kanku daga 'yan'uwa. 8 Sa'an nan hasken ku zai faso a buɗe kamar fitowar rana, kuma warkewarku zata tsiro nan da nan; adalcinku zai sha gabanku, kuma ɗaukakar Yaweh zata biyo bayanku. 9 Sa'an nan ne za ku yi kira, kuma Yahweh zai amsa; za ku yi kukan neman taimako, kuma zai ce, "Ga ni nan." Idan har kuka ɗauke daga tsakiyarku karkiya, da zargi, da maganganun mugunta, 10 idan ku da kanku kuka tanada wa mayunwata kuma kuka biya buƙatun gajiyayyu; sa'an nan ne haskenku zai keto daga cikin duhu, kuma duhunku zai zama kamar rana tsaka. 11 Sa'an nan Yahweh zai jagoranceku a kullum kuma ya ƙosar da ku a wuraren da babu ruwa, ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambu mai laima, kuma kamar maɓulɓular ruwa, wanda ruwansa ba ya ƙarewa. 12 Waɗansunku za su sake gina lalatattun kufaye; za ku tada kufayen tsararraki da yawa; za a kira ku "Masu gyaran Garu," "Masu maido da titunan da za a zauna." 13 Dãma a ce kun juyo da ƙafafunku daga tafiya a ran Asabaci, kuma daga yin abin son ranku a ranata mai tsarki. Dãma a ce kun kira ranar Asabaci abin farinciki, kuma harma ku kira sha'anin Yahweh tsarki da martaba. Dãma a ce kun girmama ranar Asabacina wurin barin sha'anin kanku, ku kuma bar neman jin daɗin kanku da kuma kun ƙi faɗar maganganun kanku. 14 Sa'an nan za ku yi farinciki cikin Yahweh; kuma zan sa ku yi yawo a ƙwalƙwolin duniya; zan ciyar daku daga gãdon Yakubu mahaifinku - gama bakin Yahweh ya faɗa."

Sura 59

1 Duba, hannun Yahweh bai gajarce bada ba zai iya ceto ba; kunnensa bai kurmance ba, da ba zai iya ji ba. 2 Ayyukanku na zunubi, duk da haka, su suka raba ku daga Allahnku, kuma zunubanku sun sashi ya ɓoye fuskarsa daga gare ku daga kuma sauraronku. 3 Gama hannayenku sun haramtu da jini kuma yatsunku da zunubi. Leɓunanku na faɗin ƙarya kuma harsunanku na faɗin tsokana. 4 Babu mai kira cikin aɗalci, kuma babu mai gudanar da ƙararsa cikin gaskiya. Suna dogara da maganganun wofi, suna faɗin ƙarairayi; Suna ɗaukar cikin masifa su kuma haifi zunubi. 5 Suna ƙyanƙyashe ƙwayayen maciji mai dafi su kuma sãƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci daga ƙwansu zai mutu, kuma idan aka fasa ƙwan, zai ƙyanƙyashe maciji mai dafi. 6 sãƙarsu ba za a iya yin tufafi da su ba, kuma ba za su iya rufe kansu da ayyukansu ba. Ayyukansu ayyukan zunubi ne, kuma ayyukan ta'addanci na cikin hannayensu. 7 Kafafunsu na gudu gun mugunta, kuma suna gudu domin su zubar da jini. Tunaninsu tunanin zunubi ne; ta'addanci da hallakarwa ne hanyoyisu. 8 Ba su san tafarkin salama ba, kuma babu adalci a tafarkinsu. Sun ƙago karkatattun tafarkuna; Duk wanda ya yi tafiya kan waɗannan tafarku ba zai san salama ba. 9 Saboda haka adalci ya yi nesa daga gare mu, kuma ayyukan adalci ba su kai wurinmu ba. Mun jira haske, amma muna ganin duhu; muna neman haske amma muna tafiya a duhu. 10 muna laluɓar bango kamar maƙafi, kamar waɗanda basu gani. Mu na yin tuntuɓe da rana kamar da asussuba; a cikin jarumai muna kama da matattun mutane. 11 Muna ihu kamar damusai da makoki kamar kurciyoyi; muna jiran adalci amma babu ko ɗaya, domin kuɓutarwa, amma tana nesa da mu. 12 Gama yawan zunubanmu suna gabanmu, kuma zunubanmu na shaida gãba damu; gama laifofinmu na tare damu, kuma mun san zunubanmu. 13 Mun yi tayarwa, muna musanta Yahweh kuma mun juya daga bin Allahnmu. Mun faɗi yaudara da juyin baya, mun ɗauki cikin gunaguni daga zuciya da maganganun ƙarya. 14 An kori adalci baya, kuma ayyukan adalci sun tsaya nesa; gama gaskiya ta yi tuntuɓe a dandali, na gaske ba zai iya zuwa ba. 15 Aminci ya tafi, kuma wanda ya juya ga barin mugunta ya maida kansa abin zargi. Yahweh ya gani kuma bai ji daɗi ba cewa babu adalci. 16 Ya ga babu wani mutum, ya kuma yi mamakin cewa babu wanda zai shiga tsakani. Saboda haka damtsensa ya kawo ceto dominsa, kuma ayyukan adalcinsa suka tallafe shi. 17 Yasa ayyukan adalci su zamar masa sulke da ƙwalƙwalin ceto a kansa. Ya suturta kansa da rigunan ɗaukar fansa ya yafa himma ya zama alkyabbarsa. 18 Ya biya su gwargwadon abin da suka yi, hunkuncin fushi ga maƙiyansa, da ramako ga magabtansa, da kuma horo ga tsibirai wannan ne ladarsu. 19 Saboda haka za su ji tsoron sunan Yahweh daga yamma, da ɗaukakarsa daga fitowar rana; gama zai zo kamar rafi mai kwararowa, wand numfashin Yahweh ke tunkuɗawa. 20 Mai fansa zai zo Sihiyona, da kuma ga waɗanda suka juyo daga ayyukan tayarwarsu cikin Yakubu - wannan furcin Yahweh ne. 21 Ni dai, wannan shi ne alƙawari na da su - inji Yahweh - ruhuna wanda ya ke bisanku, da maganganuna waɗanda na sa a bakinku, ba za su bar bakinku ba, ko su fita daga bakin 'ya'yanku, ko su fita daga bakin 'ya'yan 'ya'yanku ba - inji Yahweh - daga wannan lokaci zuwa har abada."

Sura 60

1 Tashi, haskaka; gama haskenki ya iso, kuma ɗaukakar Yahweh ta taso a bisanki. 2 Koda shi ke duhu zai rufe duniya, kuma duhu mai kauri ga al'ummai; duk da haka Yahweh zai tashi bisanki, kuma za a ga ɗaukakarsa a bisanki. 3 Al'ummai za su zo ga haskenki, sarakuna kuma ga sheƙin haskenki dake tashi. 4 Duba ko'ina ki gani. Suna tattarowa domin su zo gare ki. 'Ya'yanki maza za su zo daga nesa, kuma 'ya'yanki mata za su ɗaukosu a hannuwansu. 5 Sa'an nan za ki duba ki cika da farinciki, kuma zuciyarki zata yi ambaliya, domin za a zuba maki yalwar teku, kuma arzikin al'ummai za su zo gare ki. 6 Ayarin raƙuma za su rufe ki, takarkaran Midiyan da Ifa; dukkansu za su zo daga Sheba; za su kawo zinari da kayan ƙanshi, kuma za su raira waƙar yabon Yahweh. 7 Dukkan garkunan Kedar za a tara maki, ragunan Nebayot za su biya buƙatunki; za su zama karɓaɓun baiko a kan bagadina; kuma zan darjanta gidana mai daraja. 8 Su wane ne waɗannan dake shawagi kamar girgije, kuma kamar kurciyoyi da za su mafaƙarsu? 9 Ƙasashen gãɓar tekuna suna nema na, kuma jiragen ruwa na Tarshish suna jagoranci, domin su kawo 'ya'yanki maza daga nesa, zinariyarsu da azurfarsu na tare da su, domin sunan Yahweh Allahnki, da kuma domin Mai Tsarkin Nan na Isra'ila, saboda ya daukaka ki. 10 'Ya'ya maza na bãƙi za su gina garunki, kuma sarakunanki za su yi maki bauta; koda ya ke a cikin fushina na hore ki, duk da haka a cikin alheri na zan yi maki jinƙai. 11 ‌Ƙofofinki ma zasu kasance a buɗe kullum; ba za a rufe su da rana koda dare ba, saboda a kawo arzikin al'ummai da sarakunansu dake masu jagora. 12 Hakika, al'ummai da masarautu da ba za su ɓauta maki ba za su lalace; waɗannan al'umman za su hallaka kakaf. 13 ‌Ɗaukakar Lebanon za ta zo gare ki, itatuwan fir da makamantansu za su ƙawata masujadata; kuma zan darjanta wurin sa ƙafafuna. 14 Za su zo gare ki su yi rusuna, 'ya'yan ki maza waɗanda suka ƙasƙantar dake; za su rusuna a ƙafafunki; za su kira ki Birnin Yahweh, Sihiyona ta Mai Tsarkin Nan na Isra'ila. 15 A maimakon ki ci gaba da zaman wadda aka yashe ta aka ƙita, ba kuma wanda ya wuce ta wurinki, zan maishe ki abin fahariya na har abada, abin murna daga tsara zuwa tsara. 16 Za ki kuma sha madarar al'ummai, kuma za a rene ki a kirjin sarakuna; za ki sani cewa Ni, Yahweh, ni ne Mai cetonki da mai Fansarki. Mai Girman nan na Yakubu. 17 A maimakon tagulla zan kawo maki zinariya, a maimakon ƙarfe zan kawo azurfa; a maimakon katako, tagulla, kuma a maimakon duwatsu, karfe. Zan sa salama ta zama gwamnoninki, adalci kuma masu mulkinki. 18 Ba za a ƙara jin tashin hankali a ƙasarki ba, ko hallakarwa ko aukawar ɓarna a yankin; amma za ki kira garunki Ceto, ƙofofinki kuma Yabo. 19 Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, ko hasken wata ya haskaka a kanki; amma Yahweh zai zama haskenki na har abada, Allahnki kuma shi ne darajarki. 20 Ranarki ba za ta ƙara faɗuwa ba, ko watanki ya dushe ya ɓace ba; Gama Yahweh zai zama haskenki har abada, kuma ranakun makokinki za su ƙare. 21 Dukkan mutanenki za su zama adalai; za su karɓi mallakar ƙasar na dukkan lokaci, reshen shuka ta da aikin hanuwana, domin a ɗaukaka Ni 22 ‌Ƙ‌arami ɗaya zai zama dubu, mafi ƙanƙanta guda kuma al'umma mai ƙarfi; Ni, Yahweh, zan aiwatar da waɗannan abubuwa da sauri idan lokacin ya yi.

Sura 61

1 Ruhun Ubangiji Yahweh na bisana, domin Yahweh ya shãfe ni in yi shelar labari mai da‌ɗi ga ƙuntattu. Ya aike ni in warkar da waɗanda suka karye a zuci, in yi shelar 'yanci ga kamammu, da kuma buɗewar kurkuku domin waɗanda suke a ɗaure. 2 Ya aike ni in yi shelar shekarar tagomashi ta Yahweh, ranar ramuwar gayya ta Allahnmu, in kuma ta'azantar da dukkan masu makoki. 3 Ya aike ni - in ba masu makoki cikin Sihiyona - in ba su rawani a maimakon toka, mai na farinciki a maimakon makoki, alƙyabba ta yabo a maimakon ruhun baƙinciki, domin a kira su rimayen adalci, dashen Yahweh, domin ya sami ɗaukaka. 4 Za su sạke gina rusassun birane nadã; za su gyara lalatattun wurare. Za su gyara rusassun birane, lalatattu tun daga tsararrakin da suka rigaya suka wuce. 5 Bãƙi za su tsaya su ciyar da garkunanki, 'ya'yan baƙi kuma za su yi maki aiki a gonakinki dana garkunan inabinki. 6 Za a kira ku firistocin Yahweh; za su kira ku bayi na Allahnmu. Za ku ci wadatar al'ummai, kuma za ku yi fahariya cikin arzikinsu. 7 A maimakon kunyar ki zaki sami riɓi biyu; kuma a maimakon ƙasƙanci za su yi farinciki da rabonsu. Haka za su sami riɓi biyu na rabon ƙasarsu; murna zata zama tasu har abada. 8 Gama Ni, Yahweh, ina kaunar shari'ar gaskiya, kuma na ƙi fạshi da shari'ar zalunci. Na tabbata zan sạka masu, kuma zan yi madawwamin alƙawari dasu. 9 Zuriyarsu za su zama sanannu a cikin dukkan al'ummai, kuma 'ya'yan tsatsonsu cikin mutane. Dukkan wanda ya gan su zai tabbatar da su, cewa su ne mutanen da Yahweh ya sawa albarka. 10 Zan yi farinciki sosai cikin Yahweh; cikin Allahna zan yi murna sosai. Gama ya suturce ni da mayafan ceto; ya suturceni da rigar adalci, kamar yadda ango ke ƙawata kansa da rawani, kuma kamar yadda amarya takan ƙawata kanta da kayan ado. 11 Gama kamar yadda ƙasa take fito da dashe-dashenta, kuma kamar yadda gona takan sa shuke-shukenta su tsiro, haka Ubangiji Yahweh zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukkan al'ummai.

Sura 62

1 Saboda Sihiyona ba zan yi shuru ba, saboda da kuma Yerusalem ba zan yi tsit ba, har sai adalcinta ya bayyana da haske sosai, kuma cetonta kamar fitila mai ci bal-bal. 2 Al'ummai za su ga adalcinki, dukkan sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki. Za a kira ki da sabon suna wanda Yahweh zai zaɓa. 3 Za ki zama kambi mai daraja cikin hannun Yahweh, kuma rawanin sarauta a cikin hannun Allahnki. 4 Ba za a ƙara ce dake, "Yasasshiya" ba; ko ƙasarki ba za a ce da ita, "Watsattsiya ba." Hakika, za a ce dake "Farincikina na cikin ta," ƙasarki kuma "Aurarra," gama Yahweh na farinciki dake, kuma ƙasarki za ta yi aure. 5 Hakika, kamar yadda saurayi matashi yakan auri 'yar budurwa, haka 'ya'yanki za su aure ki, kuma kamar yadda ango ke farinciki da amaryarsa, Allahnki zai yi farinciki dake. 6 Na sa masu tsaro a bisa ganuwarki, Yerusalem; ba za su yi shuru ba dare da rana. Ku da kuke tunasshe da Yahweh, kada ku tsagaita. 7 Kada ku ba shi hutu har sai ya sake kafa Yerusalem ya kuma maishe ta abin yabo a duniya. 8 Yahweh ya yi rantsuwa da hannunsa na dama da kuma hannunsa mai iko, "Hakika ba zan ƙara bada hatsinki ya zama abinci ga maƙiyanki ba. Bãƙi ba za su sha sabon ruwan inabinki ba, wanda ke kika aikinta ba. 9 Gama waɗanda suka yi girbin hatsinsu za su ci su kuma yabi Yahweh, kuma waɗanda suka tsinke 'ya'yan inabisu za su sha ruwan inabin a cikin wurarena masu tsarki." 10 Ku shigo, ku shigo ta cikin ƙofofi! Ku shirya hanya domin mutane! Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku tattara duwatsu! Ku tada tutar alama sama domin al'ummai! 11 Duba, Yahweh yana sanarwa zuwa ga iyakar duniya, "Ku cewa ɗiyar Sihiyona: Duba, Mai cetonki yana zuwa! Ki gani, ladarsa na tare da shi, kuma sakamakonsa ya sha gabansa." 12 Za su kira ki, "tsarkakakkiyar jama'a; fansassu na Yahweh," kuma za a kira ki "Biɗaɗɗiya; birnin da ba a yashe shi ba."

Sura 63

1 Wane ne wannan da ya ke zuwa daga Idom, yafe da jar tuffa daga Bozara? Wane ne shi cikin kayan sarauta, yana takawa da ƙarfin hali sabili da girman ƙarfinsa? Ni ne, ina maganar adalci da kuma ikon yin ceto. 2 Me yasa kayayyakinka suka yi jạ, kuma me yasa suka yi kamar ka daɗe kana tattaka 'ya'yan inabi a wurin matatsar inabi? 3 Na tattaka 'ya'yan inabi a matatsar inabi ni kaɗai, kuma babu wani daga cikin al'ummai da ya yi tare da ni. Na tattakesu a cikin fushina na kuma rugurgujesu cikin hasalata. Jininsu ya ɗiɗɗiga a kan kayana kuma ya ɓaɓɓata tufafina. 4 Gama ina hangen ranar ramuwa, kuma shekara domin fansata ta rigaya ta zo. 5 Na duba, kuma babu wani da zai yi taimako. Na yi mamaki cewa babu mai taimako, amma hannuna ya kawo mani nasara, kuma fushina mai tsanani ya iza ni. 6 Na tattake mutanen a cikin fushina na kuma sa sun bugu cikin hasalata, na kuma zubar da jininsu a fuskar ƙasa. 7 Zan faɗi amincin ayyukan alƙawarin Yahweh, ayyukan yabo na Yahweh. Zan faɗi dukkan abin da Yahweh ya yi mana, da kuma manyan alherinsa zuwa gidan Isra'ila. Wannan tausayi da ya nuna mana sabili da jinƙansa, da kuma ayyuka masu yawa na amintaccen alƙawarinsa. 8 Gama ya ce, "Hakika sụ mutanena ne, 'ya'ya masu biyayya." Ya zama Mai cetonsu. 9 Cikin dukkan wahalarsu, shima ya wahala, sai mala'ika daga gare shi ya cecesu. Cikin ƙaunarsa da jinƙansa ya cecesu, ya kuma ɗagasu sama ya kuma bishesu a cikin dukkan zamanan dã. 10 Amma suka yi tayarwa suka ɓata wa Ruhunsa Mai Tsarki rai. Saboda haka yạ zama abokin gạbarsu ya kuma yaƙesu. 11 Mutanensa suka yi tunani game da kwanakin dã na Musa. Suka ce, "Ina Allah, wanda ya fito da su daga teku da makiyayin garkensa? Ina Allah, wanda ya sanya Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu? 12 Ina Allah, wanda yasa darajar ikonsa ya tafiya tare da hannun daman Musa, ya kuma raba ruwa a gabansu, domin ya yiwa kansa suna na har abada? 13 Ina Allah, wanda ya bi da su ta cikin ruwa mai zurfi? Kamar doki mai gudu a hanya mai kyau, ba su yi tuntuɓe ba. 14 Kamar shanu da suke gangarawa zuwa cikin kwari, Ruhun Yahweh ya ba su hutuwa. Sai ka bida da mutanenka, domin ka yiwa kanka suna mai yabo. 15 Ka duba daga sama ka kuma kula daga wurinka mai tsarki da kuma maɗaukakin mazauni. Ina himmarka da kuma manyan ayyukanka? Tausayinka da ayyukan juyayinka an hana mana su. 16 Gama kai ne ubanmu, ko da shi ke Ibrahim bai sanmu ba, kuma Isra'ila bai fahimcemu ba, kai, Yahweh, kai ne ubanmu. 'Mai fansarmu' sunanka kenan tun zamanan dã. 17 Yahweh, me yasa ka sạmu muka bijire daga hanyoyinka ka kuma taurare zukatanmu, har ba mu yi maka biyayya ba? Ka dawo ta dalilin bayinka, kabilun gãdonka. 18 Mutanenka sun mallaki wurinka mai tsarki na ƙaramin lokaci, amma maƙiyanmu suka tattake ta. 19 Muka zama kamar waɗanda ba ka taɓa mulkinsu ba, kamar waɗanda ba a taɓa kiransu da sunanka ba."

Sura 64

1 Ai ya, dãma ace ka tsaga sammai ka sauko ƙasa! Da tsaunuka sun girgiza a gabanka, 2 kamar yadda wuta ke chinye ƙananan kurmi, ko wuta tasa ruwa ya tafasa. Ai ya, dãma dai sunanka ya zama sananne a wurin magabtanka, domin al'ummai su yi rawar jiki a gabanka! 3 A dã, da kayi abubuwan ban mamaki waɗanda ba mu zata ba, kạ sauko ƙasa, kuma tsaunuka suka girgiza a gabanka. 4 Tun a zamanin dã ba wanda ya taɓa ji ko ya fahimta ko ya gani da ido wani Allah in banda kai, wanda ya ke yin abubuwa ga wanda ya jira gare shi. 5 Ka kan zo ka taimaki waɗanda suke farinciki da aikata abin dake na adalci, su dake tunawa da hanyoyinka suna kuma yin biyayya dasu. Kạ yi fushi a lokacin da muka yi zunubi. Ta hanyoyinka kullum za a cecemu. 6 Gama dukkan mu mun zama kamar wanda ya ƙazamtu, kuma dukkan aikin adalcinmu kamar tsumman jinin haila. Dukkanmu mun yi yaushi kamar ganyaye; kurakuranmu, kamar iska, sun kwashe mu nesa. 7 Babu ko ɗaya mai kira bisa sunanka, wanda ya ke ƙoƙarin ya kama ka. Gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace a cikin hannun kurakuranmu. 8 Duk da haka, Yahweh, kai ne ubanmu; mu ne yimɓu. Kai ne maginin tukunya; kuma dukkanmu aikin hannunka ne. 9 Kada ka yi fushi sosai, Yahweh, kada koyaushe ka tuna da zunubanmu gãba damu. In ka yarda ka dube mu dukka, jama'arka. 10 Biranenka masu tsarki sun zama jeji; Sihiyona ta zama jeji, Yerusalem kuma kango. 11 Haikalinmu mai tsarki mai kyau, inda dã ubanninmu suka yabe ka, an rusar da su da wuta, kuma dukkan abin dake da muhimmanci yạna a lalace. 12 Ta ƙaƙa za ka jure wannan, Yahweh? Ta ƙaƙa za kayi shuru ka kuma ci gaba da ƙasƙantar damu?

Sura 65

1 "Na shirya da su same ni su waɗanda ba su tambaya ba; Na shirya domin su same ni su waɗanda ba su neme ni ba. Na ce, 'Ga ni nan! Ga ni nan!' ga al'ummar da ba su kira bisa sunana ba. 2 Na miƙa hannayena dukkan yini zuwa ga mutane masu taurin zuciya, masu tafiya a cikin tafarkin da ba dai-dai ba, waɗanda suka yi tafiya bisa ga tunaninsu da shirye-shiryensu! 3 Sụ jama'ane dake tozartani a koyaushe, suna miƙa hadayu a cikin gonaki, suna kuma ƙona turare bi sa ginin tuballa. 4 Sukan zauna cikin maƙabarta suna tsaro dukkan dare, suna kuma cin naman alade tare da romon ruɓaɓɓen nama a cikin kwanoninsu. 5 Suna cewa, "Tsaya nesa, kada ka zo kusa da ni, gama nafi ka tsarki.' Waɗannan abubuwa hayaƙi ne cikin hancina, wutar da take ƙonewa duk yini. 6 Duba, a rubuce ya ke a gabana: Ni ba zan yi shuru ba, gama zan yi masu sãkayya; zan sãka masu a cikin cinyarsu, 7 domin zunubansu da zunuban ubanninsu tare," Yahweh ya faɗa. "Zan sãka masu domin ƙona turare a bisa tsaunuka da kuma ba'ar da suke yi mani a bisa tuddai. Saboda haka zan auna masu ayyukansu na dã a cikin cinyarsu." 8 Ga abin da Yahweh ke cewa, "Kamar yadda a ke samun ruwan inabi daga nonon 'ya'yan inabi, lokacin da wani na cewa, 'Kada ka lalata shi, gama akwai abu mai kyau a cikinsa; Ga abin da zan yi domin barorina: Ba zan lallatar da su dukka ba. 9 Zan fito da zuriya daga Yakubu, kuma daga Yahuda waɗanda za su mallaki tsaunukana. Zaɓaɓɓuna za su mallaki ƙasar, kuma bayina za su zauna a wurin. 10 Sharon zata zama makiyaya domin garkena, kuma Kwarin Ako wurin hutawar garkuna, domin mutanena masu nema na. 11 Amma ku da kuka yashe da Yahweh, waɗanda suke mantawa da tsaunina mai tsarki, masu shirya teburi domin allahn Sa'a, su kuma cika moɗar ruwan inabi mai gauraye domin ‌Ƙaddara. 12 Zan ƙaddara ku ga takobi, kuma dukkanku za ku rusuna ga kisa, domin a lokacin da nayi kira, ba ku amsa ba; da nayi magana, ba ku saurara ba. Amma ku ka aikata abin dake mugu a gabana kuka kuma zaɓi ku aikata abin da ba zan ji daɗinsa ba." 13 Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ke faɗi, "Duba, bayina za su ci, amma ku za ku ji yunwa; duba, bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; duba, bayina za su yi murna, amma ku za ku kunyata. 14 Duba, bayina za su yi sowa da farinciki domin murnar zuciya, amma ku za ku yi kuka saboda da zafin zuciya, kuma za ku yi makoki saboda karayar ruhu. 15 Za ku bar sunanku abin la'antawa domin zaɓaɓɓuna su yi managa; Ni, Ubangiji Yahweh, zan kasheku; Zan kira bayina da wani suna. 16 Duk wanda ya furta albarka ga ƙasar zaiyi albarka ta wurina, Allah na gaskiya. Duk wanda ya yi rantsuwa a duniya zai rantse da ni, Allah na gaskiya, gama matsalolin dã za a manta da su, gama za su ɓoye daga idanuna. 17 Gama duba, ina dab da halitta sabobbin sammai da kuma sabuwar duniya; kuma al'amuran dã ba za a tuna dasu ba ko su zo ga rai. 18 Amma ku za kuyi murna da farinciki har abada a cikin abin da zan hallita. Ga shi, ina dab da halitta Yerusalem abin farinciki, mutanenta kuma abin fahariya. 19 Zan yi murna bisa Yerusalem in kuma ji daɗi bisa mutanena; kuka da ihu saboda matsala ba za a ƙara ji a cikinta ba. 20 Ba zai ƙara faruwa ba ɗan jinjiri ya rayu kwanaki kaɗan; ko tsohon mutum ya mutu kafin lokacinsa. Wanda ya mutu yana shekara ɗari za a ce da shi matashi. Duk wanda ya kãsa kaiwa shekara ɗari za a ɗauke shi la'ananne ne. 21 Za su gina gidaje su kuma zauna ciki, kuma za su shuka garkunan inabi su ci amfaninsu. 22 Ba za su ƙara gina gida wani daban ya zauna ciki ba; ba za su shuka, wani ya ci ba; gama kamar kwanakin itatuwa haka zai zama kwanakin jama'ata. Zaɓaɓɓuna za su kere ayyukan hannuwansu a shekaru. 23 Ba za su yi aiki a banza ba, ko su haifi kaito. Gama sụ 'ya'yan waɗanda Yahweh yasa masu albarkata ne, kuma da zuriyarsu tare da su. 24 Kafin su kira, Zan amsa; kuma a lokacin da suke magana, Zan ji. 25 Damisa da ɗan rago za su yi kiwo tare, kuma zaki zai ci ciyawa kamar sã; amma ƙura ce za ta zama abincin maciji. Ba za su ƙara cutarwa ko su hallakar a kan dukkan tsaunina mai tsarki," inji Yahweh.

Sura 66

1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya ke cewa, "Sama kursiyina ne, ƙasa kuma matashin sawuna. To ina gidan da za ku gina mani? Ina wurin da zan iya hutawa? 2 Hannuwana suka yi dukkan waɗannan abubuwa; haka waɗannan abubuwa suka zo suka kasance - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta. Wannan shi ne mutumin dana zaɓa, karyayye da tawali'u a ruhu, kuma wanda ya ke rawar jiki ga maganata. 3 Shi wanda ya yanka rago ya kuma kashe mutum; shi wanda ya yi hadayar ɗan rago ya kuma karya wuyan kare; shi wanda ya miƙa baikon hatsi ya miƙa jinin alade; shi wanda ya miƙa turare na tunawa shima yasa wa mugunta albarka. Sun zaɓi hanyoyin kansu, kuma suna fahariya da aikin ƙazamtarsu. 4 Ni ma haka zan zaɓi masu horonsu; zan kawo a bisansu abin nan da suke tsoro, domin a lokacin dana yi kira, ba bu wanda ya amsa; dana yi magana, ba bu wanda ya saurara. Suka aikata abin da ke mugu a gabana, suka zaɓi su yi abin dake ɓata mani rai." 5 Ku saurara ga maganar Yahweh, ku da kuke rawar jiki da maganarsa, "Yan'uwanku da suka ƙi ku suka ware ku sabili da sunana suka ce, 'Bari Yahweh ya ɗaukaka, sa'an nan za mu ga murnar ku'; amma za a kunyatar dasu. 6 Hayaniyar yaƙi na fitowa daga birnin, hayaniya daga haikali, hayaniyar Yahweh yana sãka wa maƙiyansa. 7 Kafin ta shiga naƙuda, ta haihu; kafin zafi ya abko mata, ta haifi ɗa namiji. 8 Wane ne ya taɓa jin abu kamar haka? Wane ne ya taɓa ganin abubuwa kamar haka? Ana iya haihuwar al'umma a rana ɗaya? Al'umma tana iya haihuwa a ɗan ƙanƙanin lokaci? Duk da haka da Sihiyona ta shiga naƙuda, nan da nan ta haifi 'ya'yanta. 9 Zan kawo jinjiri a cikin ƙofar fita in kuma hana a haifi jaririn?- Yahweh yana tambaya. Ko ina kawo jariri lokacin haihuwa amma sai in hana shi fitowa?- Allahnka na tambaya." 10 Ku yi farinciki da Yerusalem ku yi murna dominta, dukkanku masu ƙaunarta; ku yi farinciki da ita, dukkanku da kuke makoki a kanta! 11 Gama za kuyi reno ku kuma ƙoshi; da nonnanta za ku ta'azantu; Gama za ku sha ku ƙoshi ku kuma ji daɗin yalwar ɗaukakarta. 12 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Ina gab da zubo wadata bisanta kamar kogi, kuma arzikin al'ummai kamar ambaliyar kogi. Za kuyi reno kusa da ita, a ɗauke ku cikin hannuwanta, a karkaɗa ku da murna a gwuiwarta. 13 Kamar yadda mahaifiya ke ta'azantar da ɗanta, haka ni ma zan ta'azantar daku, kuma za ku ta'azantu a cikin Yerusalem." 14 Za ku ga wannan, kuma zuciyarku za tayi farinciki, kuma ƙasusuwanku za su tsiro kamar 'yan ciyayi. Za a bayyana hannun Yahweh ga bayinsa, amma zai nuna fushinsa gãba da maƙiyansa. 15 Gama duba, Yahweh yana zuwa da wuta, kuma karusansa suna zuwa kamar guguwar iska domin ta kawo zafin fushinsa da kwaɓarsa tare da harshen wuta. 16 Gama Yahweh yana shar'anta 'yan adam da wuta da kuma takobinsa. Waɗanda Yahweh ya kashe za su yi yawa. 17 Sun keɓe kansu suna tsabtace kansu, domin su shiga gonaki, suna bi ta tsakiyar waɗanda suke cin naman alade da abubuwan ban ƙyama kamar kũsu. "Za su kawo ga ƙarshe - wannan shi ne furcin Yahweh. 18 Gama na san ayyukansu da tunaninsu. Lokaci na zuwa da zan tara dukkan al'ummai da yarurruka. Za su zo su ga ɗaukakata. 19 Zan sa gaggarumar alama a tsakaninsu. Sa'an nan zan aiko da masu tsira daga gare su zuwa ga al'ummai: Zuwa ga Tarshish, Fut, da Lud, masu harbi da suke jan bakansu, zuwa ga Tubal, da Yaban, da kuma zuwa iyakar ƙasashen bakin ruwa da ke nesa inda ba su taɓa ji game da ni ko suka ga ɗaukakata ba. Za su furta ɗaukakata a tsakiyar al'ummai. 20 Za su dawo da dukkan 'yan'uwanku daga cikin al'ummai, abin baiko ga Yahweh. Za su zo bisa dawakai, da karusai, da cikin kekunan shanu, da bisa jakuna, da kuma bisa raƙuma, zuwa ga tuduna mai tsarki Yerusalem - inji Yahweh. Gama jama'ar Isra'ila za su kawo baiko na hatsi a cikin kwanuka masu tsabta cikin gidan Yahweh. 21 Zan zaɓi wasu daga cikinsu su a matsayin firistoci da kuma Lebiyawa - inji Yahweh 22 Gama kamar yadda sabuwar sammai da sabuwar duniya da zan halitta za su dawwama a gabana - wannan shi ne furcin Yahweh - haka zuriyarku za su dawwama. 23 Daga wata ɗaya zuwa na gaba, kuma daga wannan Asabaci zuwa na gaba, dukkan mutane za su zo su rusuna mani - inji Yahweh. 24 Za su fito waje su dubi gawawakin jama'ar da su ka yi mani tayarwa, gama tsutsotsin da za su ci su ba za su mutu ba, kuma wutar da za ta haɗiyesu ba za ta ɓice ba; kuma za su zama abin ƙi ga dukkan masu rai."

Littafin Irmiya
Littafin Irmiya
Sura 1

1 Waɗannan su ne kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistocin Anatot cikin ƙasar Benyamin. 2 Maganar Yahweh ta zo gare shi a kwanakin Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda, cikin shekara ta goma sha uku ta mulkinsa. 3 Ta kuma zo cikin kwanakin Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, har sai watan biyar na shekara goma sha ɗaya ta Zedekiya ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, lokacin da aka kwashe mutanen Yerusalem a matsayin 'yan fursuna. 4 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 5 "Kafin In sifanta ka a cikin ciki, Na zaɓe ka; kafin ka fito daga cikin ciki Na keɓe ka; Na sa ka zama annabi ga al'ummai." 6 Sai na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh!" Na ce, "Ni ban san yadda zan yi magana ba, gama ni yaro ne." 7 Amma Yahweh yace mani, "Kada ka ce 'Ni ƙaramin yaro ne.' Dole ka tafi duk inda Na aike ka, kuma ɗole ka faɗi duk abin da Na umarce ka! 8 Kada ka ji tsoron su, gama Ina tare da kai domin in cece ka - wannan furcin Yahweh ne." 9 Daga nan sai Yahweh ya miƙa hanunsa ya taɓa bakina, yace mani, "Yanzu, Nasa maganata a cikin bakinka. 10 Yau na sanya ka bisa kan al'ummai da kan mulkoki, ka tunɓuke ka kuma rushe, ka hallakar, ka kuma juyar, ka gina ka dasa." 11 Sai maganar Yahweh ta zo wurina, cewa, "Me ka gani, Irmiya?" Na ce, "Na ga reshen almond." 12 Yahweh yace mani, "Ka gani da kyau, gama ina kiyaye maganata domin in cika ta." 13 Maganar Yahweh ta sake zuwa wuri na karo na biyu, cewa, "Me ka gani? Na ce, "Na ga tukunya mai zafi, wadda fuskarta na ɓullowa, tana kaucewa daga arewa. 14 "Yahweh ya ce mani, "Bala'i zai fito daga arewa akan dukkan mazaunan ƙasar nan. 15 Gama ina kiran dukkan kabilun mulkokin arewa, inji Yahweh. Zasu zo, kowanne ɗayan su zai kafa kursiyin sa a ƙofofin shiga Yerusalem, gãba da dukkan ganuwar da ta kewaye ta, kuma gãba da dukkan biranen Yahuda. 16 Zan furta hukunci gãba da su domin dukkan muguntarsu cikin yãshe ni, ta wurin ƙona turare ga waɗansu alloli, cikin kuma yin sujada ga abubuwan da suka ƙera da hannuwansu. 17 Ka shirya kanka! Ka tashi ka faɗa masu duk abin da na umarce ka. Kada ka firgita a gaban su, ko in firgitar da kai a gabansu! 18 Duba! Yau, na maishe ka tsararren birni, ginshiƙin ƙarfe, da bangaye na tagulla gãba da dukkan ƙasar - gãba da sarakunan Yahuda, da hakimansu, firistocinsu, da mutanen ƙasar. 19 Zasu yi yaƙi gãba da kai, amma ba zasu yi nasara da kai ba, gama zan kasance tare da kai in cece ka - wannan furcin Yahweh ne."

Sura 2

1 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 2 "Kaje ka yi shela ga kunnuwan Yerusalem. Ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Na tuna a madadin ki da alƙawarin aminci cikin ƙuruciyarki, ƙaunarki a lokacin da muna tashe, lokacin da kika bi ni cikin jeji, ƙasar da ba'a taɓa shuka ba. 3 An keɓe Isra'ila ga Yahweh, nunan farin girbinsa! Dukkan waɗanda suka ci daga nunan farin sun ɗauki laifinsu; bala'i ya afko masu - wannan furcin Yahweh ne."' 4 Kuji maganar Yahweh, ya gidan Yakubu, dukkanku iyalin gidan Isra'ila. 5 Yahweh ya faɗi haka, "Wanne laifi ubanninku suka iske tare da ni, da suka yi nisa daga bi na? Da suka bi alloli marasa amfani su kansu kuma suka zama marasa amfani? 6 Basu ce, "Ina Yahweh, wanda ya fito da mu daga ƙasar Masar ba? Ina Yahweh, wanda ya bishe mu cikin jeji, zuwa cikin ƙasar Araba da ramummuka, a cikin ƙasar fari da duhu mai zurfi, ƙasa wadda ba wanda ke ratsawa ba kuma wanda yake zama ciki?' 7 Amma na kawo ku cikin ƙasar Kamel, domin ku ci 'ya'yan itatuwanta, da sauran abubuwa masu kyau! amma da kuka zo, kuka ƙazantar da ƙasata, kun maida abin gãdona ya zama abin ƙyama! 8 Firist bai ce, 'Ina Yahweh ba?' masanan shari'a kuma basu da mu da ni ba! Makiyaya sun yi mani laifi. Annabawa suka yi annabci domin Ba'al suka kuma bi al'amura marasa amfani. 9 Saboda haka har yanzu zan zarge ku - wannan furcin Yahweh ne - kuma zan zargi 'ya'yan 'yayanku. 10 Domin ƙetarewa zuwa gaɓar Kittim ku kuma duba. Ku aika da manzanni zuwa Kedar ku bincika ku gani ko an taɓa yin wani abu irin wannan. 11 Ko al'umma ta musanya allolinta, ko da shike su ba alloli ba ne? Amma mutane na sun musanya darajarsu da abin da ba zai taimakesu ba. 12 Ku girgiza, sammai, saboda wannan! ku yi rawar jiki ku kuma firgita - wannan furcin Yahweh ne. 13 Gama mutanena sun aikata mugayen abubuwa biyu gãba da ni: Sun yi watsi da maɓuɓɓugan ruwayen rai, sun gina wa kansu randuna, hudaddun randuna waɗanda ba zasu iya riƙe ruwa ba. 14 Ko Isra'ila bawa ne? An haife shi a gidan ubangidansa? To don me ya zama abin washewa? 15 'Yan zakuna sun yi masa ruri. Suna surutai da yawa sun kuma mai da ƙasarsu wurin tsoratarwa. An lalatar da biranensu ba sauran mazauna a ciki. 16 Kuma, mutanen Memfis da Tafanhes zasu aske ƙoƙon kanku. 17 Ba ku ne kuka yi wa kanku wannan ba lokacin da kuka yashe da Yahweh Allahnku, yayin da yake bishe ku a hanya? 18 Yanzu fa, me ya kai ku hanyar Masar kuka kuma sha ruwayen Shihor? Don me kuka bi hanyar zuwa Asiriya kuma kuka sha ruwayen kogin Yufiratis? 19 Muguntarku ta tsauta maku, rashin bangaskiyarku kuma ya hore ku. Don haka ku yi tunani akai, kuma ku fahimci cewa mugunta ce kuma da ɗaci idan kuka yashe da Yahweh Allahnku, kuma baku da tsoro na - wannan furcin Ubangiji Yahweh mai runduna ne. 20 Gama na karye karkiyar da kake da ita tun zamanin dã; na yanke sarƙƙoƙinka. Duk da haka ka ce, 'Ba zan yi bauta ba!' da shike ka russuna wa kowanne tudu mai tsawo da gindin kowanne itace mai ganye, kai mazinaci. 21 Na dasa ka a matsayin zaɓaɓɓen inabi, cikakke daga iri marar aibi. Amma ta yaya ka canza kan ka zuwa gurɓatacce, inabi marar amfani. 22 Gama ko da ka wanke kanka cikin kogi ko ka wanke da sabulu mai ƙarfi, zunubinka ya ɓata ka a gaba na - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 23 Ta yaya zaka ce, 'Ban ƙazantu ba! Ban bi Ba'aloli ba?' Dubi abin da ka yi a cikin kwarurruka! Yi la'akari da abin da kayi, kai raƙumi ne mai gaggawar tafiya mai gudu nan da can, 24 jakar jeji wadda ta saba da zaman jeji, a cikin zuffarta tana numfasa iska! Wa zai tsai da sha'awarta? Babu daga cikin mazajen da ke buƙatar ya gajiyar da kansa wajen binta; a lokacin barbararsu zasu same ta. 25 Dole ka tsaida ƙafafunka daga zama marar takalmi kuma maƙogwaronka daga jin ƙishi! Amma ka ce, 'Ba bege! A'a, Ina ƙaunar bãƙi kuma zan bi su!' 26 Kamar yadda ɓarawo yake jin kunya idan an kama shi, haka gidan Isra'ila zai ji kunya - su, da sarakunansu, hakimansu, da firistocinsu da annabawa! 27 Waɗannan su suke cewa itace, 'Kai ubana ne,' ga dutse kuma, 'Kai ka haife ni.' Gama bayansu ke fuskanta ta ba fuskokinsu ba. Duk da haka a kwanakin matsaloli zasu ce 'Ka tashi ka cece mu!' 28 Duk da haka ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su tashi in sun ga dama su cece ku a lokacin damuwarku, gama yawan allolinku yawan biranenku, ya Yahuda! 29 To don me kuke zargi na a kan yi ba dai-dai ba? Dukkan ku kun yi mani zunubi - wannan furcin Yahweh ne. 30 A banza na hukunta mutanenku. Ba zasu karɓi horo ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai hallakarwa! 31 Ku 'yan wannan tsara! Ku saurari maganata, maganar Yahweh! Na zama jeji ga Isra'ila? Ko ƙasa mai baƙin duhu? Don me mutanena zasu ce, 'Bari mu yi yawo mu zagaya, ba zamu ƙara zuwa wurin ka ba?' 32 Zai yiwu budurwa ta manta da kayan adonta na zinariya ko amarya da kayan lulluɓin ta? Duk da haka mutanena sun manta da ni kwanaki ba iyaka! 33 kin shirya hanyarki da kyau don ki nemi ƙauna. Kin koyar da halayenki ga mugayen mata. 34 A cikin tufafinki an iske jinin ran marasa laifi, mutane talakawa. Waɗannan mutane ba a same su cikin ayyukan sata ba. 35 Amma kin ce, 'Ni mara laifi ce; lallai fushinsa ya juya daga gare ni.' Amma duba! zan kawo hukunci a kan ki domin kin ce, 'Ban yi zunubi ba.' 36 Don me kike ɗauka da sauƙi haka batun canza hanyoyinki? Masar zata kunyatar da ke kamar yadda Asiriya ta yi maki. 37 Kema za ki fita daga can a wulaƙance, da hannayen ki a kanki, gama Yahweh ya ƙi waɗanda kika dogara gare su, don haka ba za ki sami taimako daga gare su ba."

Sura 3

1 "Idan mutum ya saki matarsa, ta fita daga wurinsa ta kuma zama matar wani, zai sake komawa wurinta kuma? ‌Ƙ‌asar ba zata ƙazantu ba gaba ɗaya? Kin zama kamar karuwa mai masoya da yawa; yanzu kuma kina so ki sake dawowa wurina? - wannan furcin Yahweh ne. 2 Ki ɗaga idanun ki sama ki duba tsaunuka! ko akwai wurin da ba kiyi lalata ba? A bakin hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kamar Balarabe cikin jeji. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da kuma mugunta. 3 Don haka an hana ruwan bazara ruwan kaka kuma bai zo ba. Amma fuskar ki akwai girmankai, kamar fuskar karuwa. Ba ki jin kunya. 4 Ba yanzu kika kira gare ni ba: 'Ubana! Abokina na kurkusa tun daga ƙuruciyata! 5 Koyaushe zai yi ta fushi? Kullum zai riƙe fushinsa har ƙarshe?' Duba! Wannan shi ne abin da kika ce, amma kin yi dukkan muguntar da kika iya yi!" 6 A kwanakin sarki Yosiya sai Yahweh ya ce mani, "Ka ga abin da Isra'ila marar amana ta aikata? Ta hau bisa kan kowanne tudu mai tsawo ƙarƙashin kowanne itace mai ganyaye, a can ta zama kamar karuwa. 7 Na ce, 'Bayan ta yi dukkan waɗannan al'amura, zata koma wurina,' amma bata komo ba. Daga nan sai 'yar uwarta mai cin amana Yahuda ta ga waɗannan abubuwa. 8 Sai na ga haka, Isra'ila maci amana ta aikata zina na kore ta na bata takardar kisan aure, 'yar uawrta maci amana Yahuda bata ji tsoro ba; ita ma ta fita ta aikata kamar karuwa. 9 Karuwancinta ba wani abu ba ne a gare ta; ta ƙazantar da ƙasa, ta kuma aikata zina da duwatsu da itatuwa. 10 Daga nan bayan dukkan waɗannan, 'yaruwarta maci amana Yahuda ta komo wurina, amma ba da dukkan zuciyarta ba, amma da ƙarya - wannan furcin Yahweh ne." 11 Daga nan sai Yahweh ya ce mani, "Adalcin Isra'ila ya fi na Yahuda maci amana! 12 Ka je kayi shelar waɗannan maganganu zuwa ga arewa. 'Ki dawo, ya Isra'ila mai cin amana! - wannan furcin Yahweh ne - ba kulluyaumin zan yi fushi da ke ba. Tun da ni mai aminci ne-wannan furcin Yahweh ne - ba zan zauna cikin fushi ba har abada. 13 Ki yarda da zunubinki, gama kin aikata laifuffuka gãba da Yahweh Allahnku; kin raba hanyoyin ki da bãƙi ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa! Gama baki saurari muryata ba! - wannan furcin Yahweh ne. 14 Ku juyo, mutane maciya amana! - wannan furcin Yahweh ne - mijinki ne! zan ɗauke ki, ɗaya daga cikin birni, biyu daga cikin iyali, zan kawo ki Sihiyona! 15 Zan baku makiyaya gwargwadon zuciyata, kuma zasu yi kiwon ku da sani da fahimta. 16 Sa'annan zai kasance a sa'ad da zaku riɓanɓanya ku bada 'ya'ya a waɗannan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne - daga nan ba zasu ƙara cewa, "Sanduƙin akwatin alƙawari na Yahweh ba!" Wannan al'amarin ba zai ƙara zuwa cikin zuciyarsu ba, gama ba zasu ƙara tunawa ko su yi kewarsa ba. Kuma ba za a ƙara yin wani ba.' 17 A lokacin nan za su yi shela game da Yerusalem, 'Wannan shi ne kursiyin Yahweh,' daga nan sauran al'ummai za su taru a Yerusalem a cikin sunan Yahweh. Ba za su ƙara yin tafiya cikin taurin kai da muguntar zuciyar su ba. 18 Cikin kwanakin nan, gidan Yahuda zai yi tafiya da gidan Isra'ila. Tare za su zo daga kasar arewa zuwa ƙasa wadda na ba kakannin ku a matsayin gãdo. 19 Amma ni, Nace, Yadda nake so in girmamaku a matsayin ɗa in baku ƙasa mai daɗi abin gãdo wanda ya fi kyau fiye da wanda ke cikin sauran al'ummai!' Da sai in ce, 'Zaku kira ni "baba na". 'Ba zaku juya daga bina ba. 20 Amma kamar mace mai cin amanar mijinta, kun yashe ni, ku gidan Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne." 21 An ji murya bisan filaye, kuka da godon mutanen Isra'ila! Gama sun canza hanyoyinsu; sun manta da Yahweh Allahnsu, 22 "Ku juyo, ku mutane maciya amana! Zan warkar da yaudarar ku!" Duba!! Zamu zo wurin ka, gama kai ne Yahweh Allahnmu! 23 Hakika ƙarairayi sun zo daga tuddai, muryoyi masu ruɗar wa daga duwatsu; hakika Yahweh Allahnmu shi ne ceton Isra'ila. 24 Duk da haka gumaka abin kunya sun cinye abin da kakanninmu suka yi wahalarsa - garkunansu na shanu da na awaki, 'ya'yansu maza da mata! 25 Bari mu kwanta cikin kunya. Bari kunyar mu ta rufe mu, gama mun yi zunubi ga Yahweh Allahnmu! Mu da kakanninmu, tun daga lokacin ƙuruciyar mu har zuwa yau, bamu saurara ga muryar Yahweh Allahnmu ba!"

Sura 4

1 Idan kuka juyo, Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - zai zama gare ni zaku juyo. Idan kuka kawar da ƙazantattun abubuwa daga gabana kuma baku ƙara bari na ba, 2 Dole ku zama da gaskiya, marasa aibi, da masu adalci lokacin da kuke rantsuwa, 'Da ran Yahweh.' Sa'annan ne al'ummai za su albarkaci kansu a cikinsa, kuma a cikinsa zasu yi ɗaukaka." 3 Gama Yahweh ya faɗi haka ga kowanne mutum da ke cikin Yahuda da Yerusalem: 'Ku yi huɗar ƙasarku, kada kuma ku yi shuka cikin ƙayayuwa. 4 Kuyi wa kanku kaciya ga Yahweh, ku cire loɓar zuciyarku, mazajen Yahuda da mazaunan Yerusalem, in ba haka ba fushina zai fita kamar wuta, ya ƙone har ba wanda zai kashe shi, saboda muguntar ayyukanku. 5 Ka sanar cikin Yahuda, bari a ji a Yerusalem. Ka ce, "A busa ƙaho cikin ƙasar." Ayi shela a ce, "Mu taru. Bari mu shiga zuwa birane masu kagara." 6 A ɗaga alamar tuta kuma ta fuskanci wajen Sihiyona, ku gudu don ku tsira! kada ku tsaya, gama zan kawo bala'i daga arewa da babbar faɗuwa. 7 Zaki yana zuwa daga cikin kurminsa wani kuma wanda zai hallakar da al'ummai yana shirin fita. Zai bar wurinsa ya kawo tsoratarwa a ƙasarku, zai mai da biranenku su zama kangaye, inda ba mai zama ciki. 8 Saboda haka, ku yi ɗammara da tsummoki, ku yi makoki kuna kururuwa. Gama ƙarfin fushin Yahweh bai juya daga gare mu ba. 9 Zai zama kuma a ranar nan - wannan furcin Yahweh ne. a ranar nan, zuciyar sarki da hakimansa zata mutu. Firistoci zasu tsorata annabawa kuma zasu razana." 10 Sai nace, "Ah! Ubangiji Yahweh. Lallai ka ruɗi waɗannan mutane da Yerusalem ta wurin cewa, 'Zaku sami salama.' Duk da haka takobi tana sara gãba da ransu." 11 A wannan lokaci za'a ce da waɗannan mutane da Yerusalem, "Iska mai ƙuna daga wajen filayen hamada, zata yi wajen ɗiyar mutanena. Ba zata sheƙe ba ko kuwa ta tsarkake su. 12 Iska da ta fi wannan ƙarfi zata zo bisa ga umarni na, yanzu kuma zan furta shari'a a kansu. 13 Duba, yana kai hari kamar giza-gizai, karusansa kuma suna kamar hadari. Dawakansa sunfi gaggafa sauri. Kaiton mu, gama zamu zama hallakakku! 14 Ki wanke zuciyar ki daga mugunta ya Yerusalem, domin ki tsira. Har yaushe zuzzurfan tunaninki zai kasance yadda za a yi zunubi? 15 Gama murya na kawo labari daga Dan, an ji zuwan masifa daga tuddan Ifraim. 16 Kasa al'ummai su yi tunani akan wannan: Duba, ka sanar da Yerusalem cewa magewaya suna zuwa daga ƙasa mai nisa su tada muryar yaƙi akan biranen Yahuda. 17 Zasu zama kamar masu tsaron nomammiyar gona gãba da ita kewaye, domin tayi mani tayaswa wannan shi nefurcin Yahweh - 18 halinki da ayyukanki ne suka yi maki waɗannan abubuwa. Wannan zai zama hukuncinki. Zai zama da muni! Zai buga har zuciyarki. 19 Ya zuciyata! Zuciyata! Ina cikin baƙin ciki a zuciyata, zuciyata tana binbini a cikina. Ba zan iya yin shiru ba, gama na ji ƙarar ƙaho, gangamin yaƙi. 20 Bala'i na bin bala'i; gama dukkan ƙasar ta zama kango. Farat ɗaya rumfunana an hallaka su, labulena kuwa nan da nan. 21 Har yaushe zan ga tutar? Zan ji ƙarar ƙaho? 22 Saboda wautar mutanena - basu sanni ba. Mutane ne masu halin wauta basu da fahimta. Masu azanci ne wajen mugunta, amma basu da sanin yin abu mai kyau. 23 Na duba ƙasar. Duba! ta zama wofi da fanko. Gama babu haske domin sammai. 24 Na duba duwatsu. Duba, suna rawar jiki dukkan tsaunuka suna girgiza. 25 Na duba. Duba, babu ko ɗaya, kuma dukkan tsuntsayen sammai sun gudu. 26 Na duba. Duba, fadamun sun zama jeji dukkan biranenta sun rurrushe a gaban Yahweh, da zafin fushinsa." 27 Ga abin da Yahweh yace, "Dukkan ƙasar zata zama kango, amma ba zan hallakar da ita dungum ba. 28 Saboda wannan dalili, ƙasar zata yi makoki, sammai daga bisa kuma zasu duhunta. Gama na sanar da manufofi na; ba zan sake nufi na ba; ba kuwa zan juya ga barinsa ba. 29 Kowanne birni zai gudu daga ƙarar mahayan dawakai da maharba; zasu ruga cikin kurmi. Kowanne birni zai hau sama cikin wurare masu duwatsu. Za a bar biranen, ba za a sami wanda zai zauna cikinsu ba. 30 Yanzu da kika zama kango, me za ki yi? Ko da kike sa tufafi na mulufi, kike ado da kayan zinariya, kina sa idanunki su zama manya saboda shafe shafe, mazan da suka yi sha'awar ki yanzu sun yashe ki. Maimakon haka, suna ƙoƙarin ɗaukar ranki. 31 Na ji sautin baƙin ciki, wahala kamar a lokacin haihuwar ɗan fari, sautin muryar ɗiyar Sihiyona. Tana haki. Ta baza hannayenta, ta ce, 'Kaitona! Ina suma saboda waɗannan masu kisan kai."

Sura 5

1 "Yi gudu ta titunan Yerusalem; yi bincike cikin dandalin birninta, kuma. Daga nan ka duba kayi tunani akan wannan: Ko za a sami mutum ɗaya ko akwai wanda ya ke aikata adalci yana ƙoƙarin aikata aminci, daga nan zan yafewa Yerusalem. 2 Kodashike suna cewa, 'Mun rantse da ran Yahweh,' duk da haka suna rantsuwa kan ƙarya." 3 Yahweh, idanunka ba aminci suke kallo ba? Ka bugi mutanen, duk da haka basu ji zafi ba, ka hallaka su gaba ɗaya, amma duk da haka sunƙi kaɓar horo. Sun sa fuskokinsu sun taurare fiye da dutse, gama sun ƙi tuba. 4 Sa'annan nace, "Hakika waɗannan mutane talakawa ne. Su wawaye ne, gama basu san tafarkun Yahweh ba, ko umarnan Allahnsu ba. 5 Zan tafi wurin muhimman mutane domin in sanar da saƙonnin Allah gare su. Gama sun san hanyoyin Yahweh, da umarnan Allahnsu." Amma dukkan su sun karya karkiyarsu tare, sun tsintsinke sarƙoƙin da suka ɗaure su ga Allah. 6 Domin wannan zaki daga cikin kurmi zai kai masu hari. Kyarkeci daga Araba zai lalata su. Damisa za ta zo gãba da biranensu. Duk wanda ya fita daga cikin birninsa za a yayyage shi. Gama laifofinsu sun ƙaru. Ayyukan rashin amincinsu kuwa basu da iyaka. 7 Don me zan gafarta wa waɗannan mutane? 'Ya'yansu sun yashe ni kuma sunyi rantsuwa ga waɗanda ba alloli ba ne. Na ciyar dasu sun ƙoshi, amma sun aikata zina, sun riƙa tafiya suna cincirindo zuwa gidajen karuwai. 8 Dawakai ne su cikin zafi. Suna yawo suna jira a haɗu, kowanne mutum yana neman matar maƙwabcinsa. 9 Don haka ba zan hukunta su ba? - wannan furcin Yahweh ne - kuma ba zan ɗaukar wa kai na fansa a kan irin wannan al'ummar ba? 10 Ku hau sama gun garkunan inabinta ku gano ku hallaka. Amma kada ku hallakar da ita duka. Ku gyara inabinsu, gama waɗannan inabin ba daga Yahweh suke ba. 11 Gama gidajen Isra'ila dana Yahuda sun bashe ni gaba ɗaya - wannan furcin Yahweh ne. 12 Sun faɗi ƙarya game da Yahweh kuma suka ce, "Ba zai yi kome ba; ba wata cuta da zata zo kanmu, ba kuwa zamu ga takobi ko yunwa ba. 13 Annabawa zasu zama iska, maganar bata cikin su, bari duk abin da suka faɗi ayi masu." 14 Yahweh, Allah mai runduna ya faɗi wannan, "Saboda ka faɗi haka, duba, duba zansa maganata cikin bakinka. Zata zama kamar wuta, mutanen nan kuma zasu zama kamar itace! Gama zata cinyesu. 15 Duba!! zan kawo wata al'umma daga nesa, ya gidan Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - al'ummace wadda ta wanzu, kuma daɗaɗɗiyar al'umma! Al'umma ce wadda baka san yaren su ba, ba kuwa zaka fahimci abin da suke faɗi ba. 16 Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne. Dukkansu sojoji ne. 17 Zasu cinye amfanin da ka girbe, haka 'ya'yanka maza da mata, da abincinka. Zasu cinye garken tumakinku da na awaki da kuma garken shanunku; zasu cinye kuringar anab naka dana ɓaure. Zasu rurrushe biranenka masu ganuwa da takobi waɗanda ka dogara gare su. 18 Amma ko a cikin waɗancan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne - bani da nufin in hallakar da ku baki ɗaya. 19 Zai faru idan ku, Isra'ila da Yahuda, kun ce, 'Don me Yahweh Allahnmu ya yi mana dukkan waɗannan abubuwa?' Sai kai, Irmiya, kace masu, 'Kamar yadda kuka yashe da Yahweh kuka yi sujada ga baƙin alloli a cikin ƙasarku, haka kuma dole ku bauta wa baƙi a cikin ƙasar da ba taku bace. 20 Ka sanar da wannan a gidan Yakubu bari a ji a gidan Yahuda. Kace, 21 'Ku ji wannan ku wawayen mutane waɗanda basu da fahimta; kuna da idanu amma baku gani, kuna da kunnuwa amma ba ku ji. 22 Baku ji tsoro na ba - wannan furcin Yahweh ne - ko kuyi rawar jiki a fuskata ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, bisa madauwamin umarni wanda ba zai ƙetare ba - koda shike teku yana tashi ya na faɗuwa, duk da haka bai karya shi ba, ko da sun yi ruri ba zasu ƙetare ba. 23 Amma waɗannan mutane suna da kangararriyar zuciya. Sun yi tayarwa sun tafi abinsu. 24 Gama a cikin zuciyarsu ba su ce, "Bari mu ji tsoron Yahweh Allahnmu, wanda yake bada ruwa na farko da na ƙarshe a lokacinsu ba, ya ke tabbatar mana da makonnin girbl." Laifofinku sun hana waɗannan faruwa. 25 Zunubanku sun hana abubuwa masu kyau su zo gare ku. 26 Gama an sami miyagun mutane tare da mutanena. Suna fako kamar yadda wani ke laɓewa ya kama tsuntsaye; suna ɗana tarko su kama mutane. 27 Kamar yadda keji yake cike da tsuntsaye, haka gidajensu suke cike da ha'inci da ruɗi. Don haka sun yaɗu sun zama masu arzaki. 28 Sun yi ƙiba; suna ƙyalli da lafiyarsu. Suna keta haddin kowacce mugunta. Basu sauraron roƙon mutane ko dalilin marayu. Sun azurta duk da ba sa nuna adalci ga masu bukata. 29 Bazan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba - wannan furcin Yahweh ne - kuma ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba? 30 Abubuwan banƙyama da tsoratarwa sun faru a cikin ƙasar. 31 Annabawa suna anabci da ha'inci, firistoci suna mulki da ikonsu. Mutanena kuma suna son haka, amma me zai faru a ƙarshe?"'

Sura 6

1 Ku nemi mafaka, mutanen Benyamin, ta wurin fita daga Yerusalem. Ku busa ƙaho cikin Tekowa. Ku tada tuta kan Bet Hakkerem, tun da mugunta tana bayyana daga arewa; babbar hallakarwa na zuwa. 2 Za a hallaka ɗiyar Sihiyona, kyakkyawar mace 'yar lele. 3 Makiyaya da garkunansu zasu tafi wurinsu; zasu kafa rumfunansu kewaye dasu; ko wannen su zai yi kiwo tare da hannunsa. 4 Ka miƙa kanka ga allolin domin yaƙin. Mu tashi, bari mu kai hari da rana. Bashi da kyau gama hasken rana yana dushewa, inuwoyin yamma suna faɗuwa. 5 Amma bari mu tashi da dare mu kai hari mu hallaka matsaranki." 6 Gama Yahweh mai runduna ke faɗar haka: Ku sare itatuwanta, ayi tudu da aikin kewaye gãba da Yerusalem. Wannan shi nebirnin daya cancanci a kai wa hari, domin cike yake da zalunci. 7 Kamar yadda rijiya take bada ruwa, haka birnin yake sarrafa mugunta. Ana jin tashin hankali da rashin lafiya a cikinta, cuta da rauni kullum suna gabana. 8 Ki karɓi horo ya Yerusalem ko in juya daga gareki in sa ki cikin hallaka, ƙasar da babu mai zama ciki. 9 Yahweh mai runduna ya faɗi wannan, "Hakika zasu yi kalar waɗanda suka ragu a Isra'ila kamar kuringar inabi. Ka sake sa hanunka ka tsinki inabi daga kuringa. 10 Ga wa zan sanar in kuma yi gargaɗi domin su ji? Duba! Kunnuwansu marasa kaciya ne; ba su iya saurarawa! Duba! Maganar Yahweh tazo gare su domin ta kwaɓesu, amma basu so ba." 11 Amma na cika da hasalar Yahweh. Na gaji da daurewa a cikinta, Yace mani, "Ka zuba ta kan yara cikin tituna, da kan taron majiya ƙarfi. Gama kowanne miji za a ɗauke shi da matarsa; da kowanne tsoho mai yawan shekaru. 12 Za a ɗauki gidajensu aba waɗansu, gonakinsu da matansu gaba ɗaya. Gama zan kai hari ga mazaunan ƙasar da hannuna - wannan furcin Yahweh ne. 13 Yahweh ya furta cewa daga ƙaraminsu zuwa babbansu, dukkansu suna haɗama wajen cin ƙazamar riba. 14 Daga annabi zuwa Firist, kowannensu yana aikata yaudara. Sun warkar da raunukan mutane na sama sama, suna cewa, 'Salama, Salama,' alhali kuwa ba salamar. 15 Suna jin kunya lokacin da suka aikata abin ƙyama? Basu jin kunya; basu san yadda zasu juye ba, Don haka zasu faɗi cikin masu faɗowa; za a kawo su ƙasa lokacin hukuncinsu, inji Yahweh. 16 Yahweh yace, "Ka tsaya a mararrabar hanya ka duba, ka tambayi daɗaɗɗun tafarkun hanyoyi. 'Ina wannan hanya mai kyau take?' kayi tafiya kanta ka samarwa kanka wurin hutu. Amma mutane suka ce, 'Ba zamu je ba' 17 Na sa maku matsara ku saurari muryar ƙaho. Amma suka ce, 'Ba zamu saurara ba.' 18 Don haka ku saurara, al'ummai! ku duba, ku zama shaidar abin da zai same su. 19 Ki ji, ke duniya! Zan kawo masifa kan mutanen nan - 'ya'yan tunaninsu. Ba su saurari maganata ko dokata ba, amma sun ƙi ta." 20 "Mene ne ma'anar wannan turare mai ƙanshi na lubban da ake kawowa daga sheba a gare ni? ko wannan ƙanshi mai daɗi daga ƙasa mai nisa? ƙonannun hadayunku ba abin karɓa ba ne a gareni ko sadakokinku. 21 Domin wannan Yahweh yace, 'Duba, zan sa sanadin tuntuɓe akan waɗannan mutane. Za suyi tuntuɓe a kan sa - Ubanni da 'ya'ya maza tare. Mazaunan tare da maƙwabtansu kuma zasu hallaka.' 22 Yahweh yace, 'Duba, al'umma tana zuwa daga ƙasar arewa. Za a zuga babbar al'umma su taso daga ƙasa mai nisa. 23 Zasu ɗauki kibau da mãsu. Masu mugunta ne basu da tausayi. ‌Ƙ‌ararsu na ruri kamar teku, suna kuma hawan dawakai, sun fita a jere kamar mayaƙan mutane, gãba da ke, ɗiyar Sihiyona.'" 24 Mun ji rahotanni game dasu hannuwanmu kuma sun yi sanyi cikin azaba. Azaba ta kama mu kamar mace mai naƙuda. 25 Kada ku fita zuwa filaye, kada ku yi tafiya kan hanyoyi, gama takubban abokan gaba da tsoratarwa suna koina. 26 Ɗiyar mutanena, ki sanya tsummoki ki kuma yi birgima cikin toka; ki yi makoki da kuka mai zafi kamar na tilon ɗa, gama mai hallakarwar zai zo kanmu ba zato. 27 "Irmiya, Na maishe ka mai gwada mutanena, kamar mai gwada ƙarfe, zaka duba suka auna hanyoyinsu. 28 Mutane ne da suka fi kowa rashin ji, suna yawon ɓata waɗansu. Dukkansu jan karfe da baƙin ƙarfe suke, masu aikata cin hanci. 29 Mazuga suna zuga da wutar dake ƙonesu; dalma tana cinyewa cikin harshen wuta. Tacewar ta ci gaba tsakaninsu, amma bashi da amfani, saboda ba a kawar da muguntar ba. 30 Za a kira su azurfar da aka ƙi, gama Yahweh ya ƙi su."

Sura 7

1 Maganar da ta zo ga Irmiya daga Yahweh, cewa, 2 Ka tsaya a ƙofar gidan Yahweh ka shaida wannan maganar! Kace, 'Ji maganar Yahweh, dukkan kuna Yahuda, ku da kuke shiga waɗannan ƙofofin kuyi ma Yahweh sujada. 3 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa haka: Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku da kyau, haka kuwa zan ƙyale ku ku ci gaba da zama a nan wurin. 4 Kar ku miƙa kanku ga maganganun ƙarya ku kuma ce, "Haikalin Yahweh! Haikalin Yahweh! Haikalin Yahweh!" 5 Gama idan kun tabbatar da ayyukanku da hanyoyinku da kyau; idan kun aiwatar da adalci da gaskiya tsakanin mutum da makwabcinsa - 6 idan baku zalunci wanda ke zaune a ƙasar ba, da maraya da gwauruwa kuma baku zubar da jini a banza a nan wurin ba, kuma baku bi waɗansu allolin da zasu yi maku illa ba - 7 sa'annan zan ƙyale ku ku zauna a nan wurin, a ƙasar dana bayar ga kakanin ku daga zamanin zamanai da zuwa har abada. 8 Duba!! kun amince da maganganu na ruɗami da ba zasu taimake ku ba. 9 Kuna sata da kisan kai da zina? kuna rantsuwar ƙarya da kuma miƙa turare ga Baal kuma kuna bin waɗansu allolin da baku sani ba? 10 Sa'annan sai kuzo ku tsaya a gabana a wannan gidan da ake kira da sunana kuma a ce, "An cece mu," saboda kawai kuyi dukkan waɗannan abubuwan banƙyama? 11 Wannan gidan dake ɗauke da sunana, ya zama ƙogon mafasa a idanunku? Amma duba, Na gani - wannan furcin Yahweh ne.' 12 Saboda haka ku je wuri na dake shiloh, inda na bar sunana ya zauna nan da farko, kuma duba abin da nayi da ita saboda muguntar mutanena Isra'ila. 13 Don haka yanzu, ta dalilin yin waɗannan ayyuka - wannan furcin Yahweh ne - Nayi magana da ku lokuta zuwa lokuta, amma baku ji ba. Na kira ku amma baku amsa ba. 14 Saboda haka, abin da nayi a Shilo, Zan kuma yi ma gidan nan da ake kira da sunana, gidan da kuka amince, wannan wuri da na baku da kakaninku. 15 Gama zan aikar da ku waje daga gare ni kamar yadda na aikar da dukkan 'yan uwanku, dukkan zuriyar Ifraim.' 16 Kai kuwa, Irmiya, kar ka yi wa mutanen nan addu'a, kuma kar ka ɗaga muryar makoki ko ka faɗi addu'a a madadinsu, kuma kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba. 17 Baka ga abin da suke yi a biranen Yahuda da titunan Yerusalem ba? 18 Yaran na tattara katako kuma Ubanin na kunna wuta! Matayen na ƙwaba ƙullu don yin gurasa domin sarauniyar sammai kuma suna zubo da hadayun ruwan inabi ga waɗansu alloli domin su tsokane ni. 19 Da gaske tsokana ta suke yi? - wannan furcin Yahweh ne - ba kansu suke tsokana ba, har kunya ta kasance a kansu? 20 Hakika Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'duba, fushina da hasalata zasu kwararo a wannan wurin, a kan mutum da dabba, a itatuwa na fili da 'ya'yan itace na ƙasa. Zata ƙone kuma ba za a ɓice ta ba.' 21 Yahweh mai runduna, Allahn Isra'ila ya faɗi haka, 'Ku ƙara baye -bayen ƙonawa akan hadayarku da naman daga garesu. 22 Gama sa'adda na fito da kakaninku daga ƙasar Masar, ban nemi komai daga gare su ba. Ban basu ko umurni a kan zancen baye - baye na ƙonawa da hadayu ba. 23 Na basu wannan umurnin ne, "Ku saurare muryata, sai in zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Saboda haka kuyi tafiya a hanyoyin da nake umurtar ku, don ya tafi maku dai-dai." 24 Amma basu saurara ko su kula ba. Sun rayuwa ta bishewar shirye-shiryen taurin zuciyarsu, saboda haka suka koma baya, maimakon gaba. 25 Tun daga ranar da kakaninku suka fito daga ƙasar Masar har zuwa wannan ranar, Na aike kowanne ɗaya daga cikin barorina da annabawa na a gare ku. Nayi naciya yayin da nake aikar da su. 26 Amma basu saurare ni ba. Basu kula ba. Maimako, suka taurare wuyansu. Sun ma fi kakanninsu mugunta.' 27 Saboda haka ka sanar da waɗannan maganganun gare su, amma ba zasu saurare ka ba. Faɗi waɗannan abubuwan a gare su, amma ba zasu ba ka amsa ba. 28 Kace masu Wannan ce al'ummar da ba zata saurari muryar Yahweh Allahnta ba kuma bata karɓi horaswa ba. An hallaka an datse gaskiya daga bakunansu. 29 Ku yanke gashinku ku kuma yi wa kanku aski, ku kuma zubar da gashin kanku. Ku raira waƙar jana'iza a kan buɗaɗɗun wurare. Gama Yahweh ya ƙi kuma ya watsar da wannan tsara a cikin hasalarsa. 30 Gama 'ya'ya maza na Yahuda sun yi mugunta a idona - wannan furcin Yahweh ne - Sun sa abubuwan ƙyamarsu a cikin gidan da ake kira da sunana, domin su ƙazamtar dashi. 31 Sa'annan suka gina babban wurin Tofet wanda ke cikin kwarin Ben Hinom. Sun yi haka don su ƙone 'ya'yansu maza da mata a wuta - abin da ban umurta ba, ko ya shiga zuciyata ba, 32 Saboda haka duba, rana na zuwa - Wannan furcin Yahweh ne - yayin da ba za'a ƙara kiran wurin Tofet ko kwarin Ben Hinnom ba. Zai zama kwarin yanka; za a binne jikkuna a Tofet har sai babu wurin da ya rage. 33 Gawawwakin waɗannan mutanen zasu zama abincin tsuntsayen sararin sama da dabbobin duniya, kuma babu wanda zai tsoratar da su. 34 Zansa ƙarshen titunan Yahuda da na Yerusalem, ƙarar murna da ƙarar farin ciki, ƙarar ango da amarya, gama ƙasar zata zama lalatacciya."

Sura 8

1 Wannan ne furcin Yahweh - a lokacin nan zasu fitar da kasusuwan sarakunan Yahuda da ofisoshinsu, kasusuwan firistoci da annabawa, da kasusuwan mazaunan Yerusalem daga kaburbura. 2 Sa'annan zasu shimfiɗa su a waje a hasken rana da wata da dukkan tauraron sararin sammai; waɗannan abubuwan na sararin sama da suka bi suka kuma bauta masu, da suka kuma bisu suka nemesu, kuma suka yi masu sujada. Baza a binne ko a tattara kasusuwan kuma ba, zasu zama kamar kashin dabba a fili. 3 A dukkan ragowar wuraren da na kore su zuwa, zasu zaɓi mutuwa a maimakon rai domin kansu, dukkan waɗanda aka bar su daga wannan muguwar al'umma - Wannan ne furcin Yahweh mai runduna. 4 Saboda haka ka faɗa masu, 'Yahweh yace haka: Akwai wanda ya faɗi kuma bai tashi ba? Akwai wanda ya ɓace da bai yi ƙoƙarin dawowa ba? 5 Meyasa waɗannan mutanen, Yerusalem, suka juya baya da daɗewa cikin rashin bangaskiya? Sun rungume yaudara kuma sun ƙi su tuba. 6 Na kula na kuma saurara, amma basu yi maganan dai - dai ba; ba wanda ke nadama da muguntarsa, ba wanda yace, "Mene ne na yi?" Dukkansu sun tafi wurin da suke so, kamar dokin da ke sauri zuwa fagen fama. 7 Ko shamuwar sama ma ta san lokutan da suka dace; kurciyoyi kuma, da dila da zalɓe. Suna kiyaye lokacin ƙaurarsu, amma mutanena ba su san dokokin Yahweh ba. 8 Yaya zaku ce, "Mu masu hikima ne, don umurnin Allah na tare da mu"? Hakika ku duba! alƙalamin ƙarya na magatakarda ya ƙirƙiro ƙarya. 9 Mutane masu hikima zasu ji kunya. Zasu tsorata su kuma cafku. Duba! Sun ƙi maganar Yahweh, to mene ne amfanin hikimarsu? 10 Saboda haka zan bada matayensu ga waɗansu, filayensu kuma ga waɗansu su mallaka, don daga mafi ƙanƙantarsu zuwa babbansu, kowannensu ya na haɗamar cin ƙazamar riba! Daga annabi zuwa firist, dukkansu suna aikata ha'inci. 11 Sun warkar da raunin mutanena sama - sama, suna cewa, "Salama, Salama," sa'adda babu salama. 12 basu ji kunya ba ne a sa'adda suke ayyukan banƙyama? Basu ji kunya ba; basu san yadda zasu kunyata ba! Saboda haka zasu faɗi cikin faɗaɗɗu; za a kawo su ƙasa sa'adda ake horar da su, inji Yahweh. 13 Zan tuge su kakaf - wannan furcin Yahweh ne - baza a sami inabi a itacen inabi ba, ko 'ya'ya a itacen ɓaure ba, gama ganyen zai bushe, kuma abin da na basu zai ƙuɓuce masu. 14 Me yasa muke zama a nan? kuzo mu taru; bari mu je garuruwa masu garu, kuma mu yi shiru a can cikin mutuwa. Gama Yahweh Allahnmu zai sa muyi tsit. Zai sa mu sha guba, tunda mun yi masa laifi. 15 Muna fatan salama, amma babu wani abu mai kyau. Muna fatan lokacin warkarwa, amma duba, za a sami razana. 16 Firjin dawakansa aka ji daga Dan. Dukkan duniya ta girgiza saboda haniniyar ingarmun ƙarfafan dawakansa. Gama zasu zo su cinye ƙasar da wadatarta, birni da masu zama cikinsa. 17 Gama ku duba! Ina aikar da macizai a cikinku, kãsayen da ba zaku samu makarinsu ba. Zasu cije ku -Wannan furcin Yahweh ne."' 18 Baƙincikina ba shi da ƙarshe, kuma zuciyata na ciwo. 19 Duba!! Muryar ihun ɗiyar mutanena daga ƙasa mai nisa! Babu Yahweh a Sihiyona ne? Ko ba sarkin a cikinta? Me ya sa suke cakuna ta zuwa fushi da sassaƙaƙƙun sifofinsu da banzayen bãƙin gumakansu? 20 Girbi ya ƙare, damuna kuma ta wuce. Amma ba a cece mu ba. 21 Na raunana saboda raunin ɗiyar mutanena. Nayi makokin a kan abubuwan tsoron da suka same ta; Na tsorata. 22 Babu wani magani a Giliyad ne? Babu mai warkarwa a can ne? Me zai hana warkarwar ɗiyar mutanena ta faru?

Sura 9

1 Da ma kaina zai ɓullo da ruwa, kuma idanuna su zama maɓuɓɓular hawaye! Gama ina tunanin yin kuka rana da dare domin waɗanda ke cikin ɗiyar mutanena da aka kashe. 2 Da ma wani zai bani wuri domin matafiya a hamada su zauna, inda zan je in rabu da mutanena. Da ma zan iya barin su, tunda dukkansu mazinata ne, ƙungiyar maciya amana! 3 Yahweh ya furta, "Sun tanƙwasa bakkunan ƙarerayinsu da na harsunansu, amma ba don wani amincinsu ne ya sa suka yi ƙarfi a duniya ba. Suna ta ci gaba daga aikin mugunta ɗaya bayan ɗaya. Basu san ni ba." 4 Kowannen ku, yayi hankali da maƙwabcinsa kuma kada ya amince da kowanne irin ɗan'uwa. Gama kowanne ɗan'uwa hakika mayaudari ne, kuma kowanne maƙwabci mai kushe ne. 5 Kowanne mutum yana yiwa maƙwabcisa ba a kuma ba ya faɗin gaskiya. Harsunansu na koyar da abubuwan ƙarya. Sun rafke daga aikata laifi. 6 Zamanku na cikin ruɗu; a cikin yaudararsu sun ƙi su shaida ni - Wannan furcin Yahweh ne." 7 Yahweh mai runduna ya faɗi haka, "Duba, Ina gab da tsabtace su in kuma gwada su, gama me zan iya yi, saboda abin da mutanena suka yi? 8 Harsunansu kibiyoyi masu kaifi ne; suna faɗin abubuwan rashin aminci. Da bakunansu suna shaida salama ga maƙwabtansu, amma da zukatansu suna shirya masu maƙarƙashiya. 9 Ba zan hukuntasu saboda waɗannan abubuwan ba - wannan shi ne furcin Yahweh - kuma ba zan rama wa al'umma irin wannan ba? 10 Zan raira waƙar makoki da kururuwa saboda duwatsu, kuma za a raira wakar jana'iza domin wuraren kiwo. Gama an ƙone su don kar kowa ya wuce ta wurinsu. Ba zasu ji kukan wata dabba ba. Tsuntsaye da namomin daji sun gudu sun tafi. 11 Saboda haka Zan maida Yerusalem tsibin kufai, maɓoyar diloli. Zan maida biranen Yahuda kufai inda ba mazauna." 12 Wanne mutum ne ke da isasshiyar hikima ya gane wannan? Ga wane ne bakin Yahweh yayi magana, kuma zai faɗe shi? Me yasa ƙasar ta lalace an kuma hallakar da ita kamar hamadar da ba wanda zai iya wucewa ta cikinta? 13 Sai Yahweh yace, "Saboda sun ƙi dokokin da na shirya a gare su, saboda basu saurari muryata ko su yi aiki da ita ba. 14 Saboda sun yi tafiya da taurarrar zuciyarsu suka kuma bi Ba'aloli kamar yadda ubanninsu suka koya masu suyi. 15 Saboda haka Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da sa mutanen nan suci abinci mai ɗaci da ruwan dafi. 16 Sa'annan zan watsar dasu cikin al'ummar da basu sani ba da su da kakaninsu. Zan aikar da takobi ya bi su har sai na hallaka su kakaf."' 17 Yahweh mai runduna ya faɗi haka, "Kuyi tunani a kan wannan: Ku kira masu waƙar jana'iza; bari su zo. Ku aiko a kira matayen da suka ƙware a makoki; bari suzo. 18 Bari su yi sauri su raira waƙar makoki a kanmu, saboda idanuwanmu su iya zubar da hawaye kuma girar idanuwanmu ta malalo da ruwa. 19 Gama an jin muryar kuka a Sihiyona, 'Yaya muke lalacewa. Mun ji kunya sosai, gama mun yi watsi da ƙasar tun da suka rurrushe gidajenmu.' 20 Saboda haka ku mataye, ku ji maganar Yahweh; ku kula da saƙonni dake zuwa daga bakinsa. Sa'annan ku koyar da 'ya'yanku mata waƙar makoki, kuma kowacce mace maƙwabciya waƙar jana'iza. 21 Gama mutuwa ta iso ta tagoginmu; ta shigo cikin fãdodinmu. Ta hallaka yara daga waje, da 'yan maza a dandalin biranen. 22 Ka faɗi haka, 'Wannan furcin Yahweh ne - gawawwakin mutane zasu faɗo kamar kashin dabbobi a gonaki, kuma kamar dammunan masu girbi, kuma babu wanda zai tara su."' 23 Yahweh ya faɗi haka, "Kada ka bar mutum mai hikima yayi taƙama da hikimarsa, ko jarumi a cikin ƙarfinsa. Kada ka bar mai arziki yayi taƙama da arzikinsa. 24 Gama idan mutum yayi taƙama da wani abu, bari ya zama a wannan, cewa yana da fahimta kuma ya san ni. Gama ni ne Yahweh, wanda yake aiki da alƙawarin aminci da adalci da ayyukan adalci a duniya. Gama a cikin waɗannan ne nake murna - wannan furcin Yahweh ne." 25 Duba, kwanaki na zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'adda zan horar da dukkan masu kaciya a jiki kawai. 26 Zan horar da Masar da Yahuda da Idom da mutanen Ammon da Mowab da dukkan mutanen da ke yanke gashin kansu suna sanƙo. Domin dukkan waɗannan al'umman marasa kaciya ne, kuma dukkan gidan Isra'ila suna da zuciya marar kaciya."

Sura 10

1 "Ku ji maganar da Yahweh yake sanar daku, ya gidan Isra'ila. 2 Yahweh ya faɗi haka, 'Kar ku koyi hanyoyin al'ummai, kuma kada ku da mu da alamun cikin sammai, domin al'ummai na damuwa da waɗannan ne. 3 Gama al'adun addinin mutanen nan na banza ne. Suna sare itace a cikin jeji, kuma gwanayen sassaƙa na sassaƙa katako. 4 Sa'annan suka ƙayata shi da azurfa da zinari. Sun inganta ƙarfin shi da guduma da ƙusa don kada ya faɗo. 5 abin da suka yi da hanuwansu yana kama da mutummutumi a gonar kukumba, saboda su, ma, ba zasu iya cewa komai ba, kuma ɗaukarsu ake yi domin ba zasu iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu, gama ba zasu iya jawo mugunta, ko kuma su iya yin wani abu maiƙyau ba."' 6 Babu wani kamarka, Yahweh. Kai mai girma ne, kuma sunanka na da girma cikin iko. 7 Wane ne ba ya jin tsoron ka, sarkin al'ummai? Don ka cancanci haka, gama babu wani kamar ka a cikin dukkan mazaje masu hikima na al'ummai ko dukkan mulkokinsu masu martaba. 8 Dukkansu iri ɗaya ne, su daƙiƙai da wawaye ne, almajiran gumaka da ba kome ba ne sai itace. 9 Suna kawo sarafaffiyar azurfa daga Tarshish da zinariya daga Ufaz waɗanda ƙwararru suka yi, da hannuwan maƙera. Tufafinsu na mulifi da shunayya ne. Gwanayensu ne suka yi dukkan waɗannan abubuwan. 10 Amma Yahweh shi ne Allah na gaskiye. Shi ne Allah mai rai da madawamin sarki. Fushinsa yakan girgiza duniya, kuma al'ummai ba zasu jure fushinsa ba. 11 Zaka yi magana da su kamar haka, "Allolin da basu yi sammai da duniya ba zasu lalace daga duniya kuma daga ƙarƙashin waɗannan sammai." 12 Amma shi ne wanda yayi duniya ta ikonsa, ya kuma kafa ta ta wurin hikimarsa, kuma ta fahimtarsa ya miƙar da sammai. 13 Muryarsa ta yi ƙugin ruwa a sammai, ya kuma kawo hayaƙi daga kurewar duniya. Yakan yi walƙiyoyi domin ruwan sama ya kuma aikar da iska daga taskokinsa. 14 Kowanne mutum ya zama jahili da marar ilimi. Kowanne maƙerin zinariya zai sha kunya ta dalilin gumakansa. Gama ƙerarrun siffofinsu ƙarya ne; Babu rai a cikinsu. 15 Basu da amfani, aikin masu ba'a; zasu lalace a lokacin horonsu. 16 Amma Allah, madogarar Yakubu, ba haka yake ba, gama shi ne yayi dukkan abubuwa. Isra'ila kabilar gãdonsa ne; Yahweh mai runduna ne sunansa. 17 Ku tattara kayayyakinku ku bar ƙasar, ku mutanen dake zaune a wuraren dake kewaye da yaƙi. 18 Gama Yahweh ya faɗi haka, "Duba, Ina gab da jefar da mazaunan ƙasar waje a wannan lokacin. Zan kawo masu ƙunci, kuma zasu kuwa same shi a hakan." 19 Kaito na! Saboda karyayyun ƙasusuwana, raunina ya sami lahani. Saboda haka na ce, "Tabbas wannan azaba ce, amma zan jure." 20 An lalatar da rumfata, kuma dukkan igiyoyin rumfata an yanke su biyu. An ɗauke 'ya'yana daga gare ni, saboda haka basu nan. Babu wanda zai yi shimfiɗa a rumfata ko mai ɗaga labulolin rumfata. 21 Gama makiyayan wawaye ne kuma ba sa biɗar Yahweh; saboda haka basu wadata ba, kuma dukkan garkensu an warwatsar. 22 Rohotonin labarai sun iso, "Duba! Tana zuwa, babbar girgizar ƙasa tana zuwa daga ƙasar arewaci ta sa biranen Yahuda su zama kufai, maɓuya domin diloli." 23 Na sani, Yahweh, cewa hanyar mutun ba daga kansa take fitowa ba. Babu mutumin dake jagorar tafiyarsa da takawar kansa. 24 Ka tsauta mani, Yahweh, da adalci, ba a cikin fushinka ba domin kada ka hallaka ni. 25 Ka kwarara hasalarka ga al'umman da basu san ka ba, da iyalan da basu kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yakubu sun kuma haɗiye shi saboda su hallakar da shi kakaf su kuma rushe mazauninsa.

Sura 11

1 Maganar da tazo ga Irmiya daga Yahweh, cewa, 2 "Ka saurari maganganun wannan alƙawari, kuma ka furta su ga kowanne mutum a Yahuda da kuma ga mazaunan Yerusalem 3 Ka ce masu, 'Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗi haka: La'ananne ne duk wanda ba ya sauraron maganganun wannan alƙawari. 4 Wannan shi nealƙawarin da na umurci kakaninku su cika a ranar dana fito da su daga ƙasar Masar, Daga tanderun sarrafa ƙarfe. Nace, "Ku saurari muryata ku kuma yi dukkan waɗannan abubuwan kamar yadda na umurce ku, gama zaku zama mutane na ni kuma In zama Allahnku." 5 Kuyi mani biyayya saboda in cika rantsuwar da na yi ma kakaninku, rantsuwar cewa zan ba su ƙasar dake kwararo da madara da zuma, inda kuke zama a yau." Sa'annan Ni Irmiya, na amsa nace, "I, Yahweh!" 6 Yahweh yace mani, "Kayi shelar waɗannan abubuwan a cikin biranen Yahuda da titunan Yerusalem. Kace, Ku saurari maganganun wannan alƙawari ku kuma aikata su. 7 Gama na yi ta bayar da tsarkakan umarnai na ga kakaninku daga ranar da na fitar dasu daga ƙasar Masar har zuwa wannan lokacin, nayi ta faɗakar da su cewa, "Ku saurari muryata." 8 Amma basu saurara ko su kula ba. Kowanne mutum yana tafiya a cikin taurarriyar muguntar zuciyarsa. Saboda haka na kawo dukkan la'anonin cikin wannan alƙawarin da na umurta su zo gare su. Amma mutanen basu yi biyayya ba duk da haka." 9 Biye da haka Yahweh yace mani, "An gano tawaye a cikin mutanen Yahuda da mazunan Yerusalem. 10 Sun juya zuwa zunuban kakaninsu na farko, waɗanda sun ƙi su saurari maganata, maimakon haka suka bi waɗansu alloli suka bauta masu. Gidan Yahuda da na Isra'ila sun karya alƙawarina da na kafa da kakaninsu. 11 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da kawo bala'i a kansu, bala'in da ba zasu iya kuɓutar da kansu ba. Sa'annan zasu yi kira gare ni, amma ba zan saurare su ba. 12 Biranen Yahuda da mazaunan Yerusalem zasu je su yi kira ga allolin da suka bada baye-baye gare su, amm hakika ba zasu sami ceto ta wurinsu a lokacin bala'insu ba. 13 Gama ke Yahuda, allolinki sun ƙaru dai - dai da yawan biranenki. Kin yi yawan bagadanki masu ban kunya a Yerusalem, da turaren bagadai domin Ba'al, dai - dai da yawan titunanta. 14 Saboda haka kai kanka, Irmiya, kada kayi wa mutanen nan addu'a. Kada kayi kuka ko addu'a a madadin su. Gama ba zan saurara ba sa'adda suka kira ni a lokacin bala'insu. 15 Me ya sa ƙaunatacciyata, wadda take da mugayen ƙudurori da yawa, take ta aikata su a gidana? Naman hadayunki ba zasu iya taimakonki ba. Kina farinciki saboda mugayen ayyukanki. 16 A baya Yahweh ya kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakyawa mai 'ya'yan da ake so. Amma zai cinna wuta a kanta wadda zata yi ƙara kamar iskar guguwa; rassanta zasu kakkarye. 17 Gama Yahweh mai runduna, shi wanda ya dasa ku, ya furta bala'i gãba da ku saboda mugayen ayyukan da gidan Isra'ila da na Yahuda suka yi - sun sa na husata ta wurin yiwa Ba'al baye-baye."' 18 Yahweh ya sa na san waɗannan abubuwan, saboda haka na sansu. Kai, ya Yahweh, ka sa na ga ayyukansu. 19 Ina kama da ɗan rago mai sauƙin kai wanda ake ja zuwa mayanka. Ba ni da sanin cewa sun yi maƙarƙashiya gãba da ni, "Bari mu lalatar da itacen da 'ya'yansa! Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai saboda kada a sake tunawa da sunansa." 20 Duk da haka Yahweh mai runduna Mai yin shari'ar adalci ne wanda yake bincike zuciya da tunani. Zan shaidi sakayyarka game da su, gama na danƙa maganata a gare ka. 21 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka game da mutanen Anatot dake biɗar ranka, "Suka ce, 'Kada ka kuskura kayi annabci da sunan Yahweh, ko ka mutu ta hannun mu.' 22 Domin haka Yahweh mai runduna ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da hukunta su. Samarinsu masu ƙarfi zasu mutu ta takobi. 'Ya'yansu maza da mata zasu mutu saboda yunwa. 23 Babu waninsu wanda za a bari, domin Ina tahowa da masifa gãba da mutanen Anatot, a shekarar hukuncinsu."'

Sura 12

1 Kai adali ne, Yahweh, duk lokacin dana kawo rashin jituwata a gare ka. Hakika zan faɗa maka dalilin ƙarata: Me yasa hanyoyin mugaye suke yin nasara? Dukkan marasa bangaskiya suna cin nasara? 2 Ka dasa su kuma suka yi saiwa. Sun ci gaba da bada 'ya'ya. Kana kusa da su a cikin bakunansu, amma nesa daga zuciyarsu. 3 Duk da haka kai, Yahweh, ka san ni. Kana gani na kuma kana gwada zuciyata gare ka. Ka ɗauke su kamar tunkiyar da ake kaiwa mayanka, ka ware su domin ranar yanka! 4 Yaushe ƙasar zata ci gaba da bushewa, kuma tsire-tsiren kwace gona ke yaushi saboda muguntar mazaunanta? Dabbobi da tsuntsaye an ɗauke. Hakika, mutanen sun ce, "Allah ba zai ga abin da zai faru da mu ba." 5 Yahweh yace, "hakika, idan kai, Irmiya, kayi tsere da sojojin ƙafa suka kuma gajiyar da kai, to yaya zaka yi gasa gãba da dawakai? Idan ka faɗi a lafiyayyar karkara, ƙaƙa zaka yi a kurmin Yodan. 6 Gama ko 'yan'uwanka da gidan mahaifinka sun basheka sun kuma ƙi ka ƙiri-ƙiri. kada ka amince da su, ko sun faɗi maka abubuwa masu daɗi. 7 Na yashe da gidana; Na rabu da gãdona. Na bada ƙaunatacciyata cikin hannuwan maƙiyanta. 8 Abar gãdona ta zamar mani kamar zaki a kurmi; ta kafa kanta gãba da ni da muryarta, saboda na ƙi jininta. 9 Ashe mallakar da nake ji da ita ta zama dabbare-dabbaren tsuntsu, wacce manyan tsuntsaye ke farauta gãba da ita a kewaye? Tafi ka tattaro dukkan namomin jeji ka kuma kawo su su lanƙwameta. 10 Makiyaya da yawa sun lalatar mani da garkar inabi. Sun tattake kan dukkan nawa rabon ƙasar; sun maida kyakkyawan rabona hamada da kufai. 11 Sun maida ita ba komai. Ina makoki domin ta; ba ta da komai. Dukkan ƙasar an maida ita kango, gama ba wanda ya ɗauke abin a zuciya. 12 Masu hallakarwa sun zo gãba da dukkan tsaunukan cikin hamada, gama takobin Yahweh tana hallakarwa daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan. Babu kwanciyar hankali a ƙasar domin kowacce hallita mai rai. 13 Sun shuka alkama sun girbi ƙayayuwa. Sun gaji da aiki amma basu samu ribar komai ba. Saboda haka ku ji kunyar ribarku saboda fushin Yahweh." 14 Yahweh ya faɗi haka a kan dukkan maƙwabtana, mugayen da suka taɓa mallakar dana sa mutanena Isra'ila suka gada, "Duba, Nine wanda ke gab da tumɓuke su daga ƙasarsu, kuma zan jawo gidan Yahuda daga cikinsu. 15 Sa'annan bayan na tumɓuke waɗancan al'ummai, zai zamana zan sake jin tausayinsu in kuma komo da su; Zan komar da su - kowanne mutum ga gãdonsa da ƙasarsa. 16 Zai kuwa zamana idan waɗancan al'umman zasu himmantu su koyi hanyoyin mutanena, su yi rantsuwa da sunana 'In dai Yahweh na raye' kamar dai yadda suka koya ma mutanena suyi rantsuwa da Ba'al, to su ma zasu ginu a cikin mutanena. 17 Amma idan ba wanda ya saurara, sai in tumɓuke wannan al'ummar. Hakika za a tumɓuke ta a kuma hallakata - wannan furcin Yahweh ne."

Sura 13

1 Yahweh yace da ni haka, "Jeka ka sayi lilin na yin ɗamara kuma ka sa shi kewaye da kwankwasonka, amma kar ka sa shi a ruwa da farko" 2 Saboda haka na sayi ɗamarar kamar yadda Yahweh ya jagorance ni, sai na rataya kewaye da kwankwasona. 3 Daga nan maganar Yahweh ta zo a gare ni karo na biyu, cewa, 4 "Ka ɗauki ɗamarar da ka saya wadda ke kewaye da kwankwasonka, ka tashi ka tafi yanzu zuwa Ferat. Ka ɓoye ta nan a ƙogon tsaguwar dutse." 5 Sai na tafi na ɓoye ta a Ferat, kamar yadda Yahweh ya umarce ni. 6 Bayan kwanaki da yawa, Yahweh yace mani, "Tashi ka koma Ferat. Ka ɗauki ɗamarar da na ce ka ɗauka daga wurin da ka ɓoye." 7 Sai na koma Ferat na kuma haƙo ɗamarar a inda na ɓoye ta, kuma duba, ta lalace dukka kuma babu amfani. 8 Sai maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 9 Yahweh ya faɗi haka: Ta dai wannan hanyar zan hallakar da gagarumin kumbura kan Yahuda a Yerusalem. 10 Waɗannan miyagun mutanen da suka ƙi su raurari maganata, waɗanda ke tafiya a cikin taurin zuciyarsu, waɗanda ke bin bayan waɗansu alloli suyi masu sujada suka kuma russuna masu - zasu zama kamar wannan ɗamarar da ba ta da amfani. 11 gama kamar yadda ɗamarar nan ta ke manne wa ƙwanƙwason wani, haka na maida gidan Isra'ila da dukkan gidan Yahuda su manne mani - wannan furcin Yahweh ne - su zama mutanena, su kawo mani shahara, a ko'ina da yabo, da girmamawa. Amma ba su saurare ni ba. 12 Saboda haka, dole ka faɗa masu wannan magana, 'Yahweh, Allah na Isra'ila, yace: Za a cika kowanne gora da ruwan inabi.' Zasu ce da kai, "Ashe bamu sani hakika cewa kowanne gora za a cika shi da ruwa ba?' 13 Sai kace da su, Yahweh ya faɗi haka: Duba, Ina gab da cika dukkan mazaunan wannan ƙasa da buguwa, sarakunan dake zaune a kursiyin Dauda da firistoci da annabawa da mazaunan Yerusalem. 14 Sa'annan zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu tare - wannan shi ne furcin Yahweh - Ba zan ji tausayinsu ko juyayinsu ba, kuma ba zan kiyaye su daga hallaka ba."' 15 Ku saurara ku kuma natsu. Kada ku kumbura kai, gama Yahweh yayi magana. 16 Ku girmama Yahweh Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin kuma yasa ƙafafunku su yi tuntuɓe akan duwatsu da hasken asuba. Gama kuna begen haske, amma zai maishe da wurin duhu baƙƙi ƙirin, zuwa baƙin girgije. 17 Saboda haka idan ba zaku saurara ba, zan yi kuka ni kaɗai saboda kumbura kanku. idanuwa na zasu yi kuka ƙwarai kuma su zub da hawaye, domin an ɗauke garken Yahweh zuwa bauta. 18 Kace da sarki da kuma mahaifiyar sarki, 'Ku sauko daga bisa kursiyoyinku, gama rawwunanku masu daraja sun faɗi daga kawunanku.' 19 Biranen cikin Negeb za a rufe su, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a ɗauke Yahuda zuwa bauta, dukkan ƙasar zuwa bauta. 20 Ku ta da idanuwanku ku ga waɗanda ke tahowa daga arewa. Ina garken da ya baku, garken dake kyakkyawa a gare ku? 21 Me zaku ce sa'adda Allah ya naɗa a kanku shugabanin da kuka koyar su zama muhimman aminanku? Ashe ba waɗannan ba ne mafarin zafin azabai da zasu mamaye ku kamar mace mai naƙuda? 22 Sa'annan zaku iya cewa a zuciyarku, 'Me yasa waɗannan abubuwan suke faruwa da ni?' Zai zama domin yawan zunubanku ne shi yasa an ɗaga ɗantofinku kuma an wulaƙanta ku. 23 Mutanen Kush zasu iya sake launin fatarsu, ko kuwa damisa zata iya sake dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, to ku kanku, duk da dai kun saba da yin mugunta, zaku iya yin nagarta. 24 Saboda haka zan watsar da su kamar ƙaiƙayi da kan lalace a iskar hamada. 25 Wannan shi ne abin da na baku, rabon da nayi doka dominku - wannan Furcin Yahweh ne - saboda kun mance da ni kun dogara ga ruɗu. 26 Saboda haka kuma Ni kaina zan kware ɗantofinku, kuma za a ga tsiraicinku. 27 Na ga zinarki da haniniyarki, da muguntar karuwancinku akan tuddai da cikin gonaki, na kuma ga waɗannan abubuwa masu ban ƙyama! kaiton ki, Yerusalem! Har tsawon wanne lokaci ne zaki sake wankuwa kuma?"

Sura 14

1 Wannan ita ce maganar Yahweh da tazo wurin Irmiya game da fari, 2 "Bari Yahuda ta yi makoki; bari ƙofofinta su lalace. Suna kuka domin ƙasar; kukansu domin Yerusalem ta hau sama. 3 Manyansu sun aiki barorinsu su ɗebo ruwa. Da suka je maɓuɓɓuga, sun tarar ba ruwa. Sai dukkansu suka koma ba tare da samun kome ba, sun lulluɓe kawunansu don kunya da ƙasƙanci. 4 Domin wannan ƙasar ta tsage, domin babu ruwan sama a ƙasar. Manoma sun sha kunya har sun lulluɓe kawunansu. 5 Ko dama barewa ma a saura ta kan gudu ta bar 'ya'yanta sabuwar haihuwa, don ba ciyawa. 6 Jakunan jeji sukan tsaya akan huntun sararinsu na haki kamar diloli. Idanuwansu ba sa gani, domin ba abinci." 7 Ko da yake zunubanmu suna shaida gãba da mu, Yahweh, kayi taimako saboda sunanka. Gama rashin amincinmu yayi yawa; mun yi maka zunubi. 8 Kai ne begen Isra'ila, mai cetonta a lokacin wahala, ƙaƙa zaka zama kamar baƙo a ƙasar, kamar mai tafiyar yawon buɗe ido wanda ya kwanta a gefen hanya don ya kwana ɗaya? 9 Ƙaƙa zaka zama kamar jarumin da ya kãsa iya ceton kowa? Duk da haka kana nan a tsakiyarmu, Yahweh, da sunanka ake kiranmu. Kada ka barmu! 10 Yahweh yace wannan akan waɗannan mutanen: "Tun da suna ƙaunar yawace-yawace, basu iya daina wa ba." 11 Yahweh ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da laifofinsu ya kuma hukunta zunubansu. Yahweh yace mani, "Kada kayi addu'a domin lafiyar waɗannan mutane. 12 Ko da sun yi azumi, ba zan saurare kukansu ba, kuma ko da sun mika hadaya ta ƙonawa da hadayar abinci, ba zan karɓe su ba. Amma zan kawo ƙarshensu da takobi, yunwa, da annoba." 13 Sai na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh! Duba!! Annabawa suna gayawa mutane, 'Ba zaku ga takobi ba; babu yunwa domin ku, amma zan baku dawwamammen tsaro a wannan wuri.'" 14 Yahweh yace mani, "Annabawa suna annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ko kuwa in basu wani umarni ko kuma in yi magana da su. Amma ƙarairayi da wahayin ƙarya ne, ƙaryar duba da suke yi marar amfani suna fitowa daga tunaninsu waɗanda suke annabcin ƙarya ne." 15 Saboda haka ga abin da Yahweh yace, "Akan annabawan da suke yin annabci da sunana amma ba ni ne na aikesu ba - waɗanda suka ce baza a yi takobi ko yunwa ba a ƙasar. Waɗannan annabawa zasu hallaka da takobi da yunwa. 16 Kuma mutanen da suka yi wa annabci za a jefar dasu waje cikin titunan Yerusalem domin yunwa da takobi, har ma babu wanda zai binne su - su, da matayensu da 'ya'yansu maza da mata - don zan sa muguntarsu a kansu. 17 Faɗa masu wannan magana: 'Bari idanuna suyi ta zub da hawaye, dare da rana. Kada su daina, saboda akwai babbar aukawar budurwa 'yar mutane na -babban rauni marar warkewa. 18 Idan na tafi cikin saura, akwai su da yawa da aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga cikin birni, akwai cututtukan da yunwa ta kawo. Gama annabi da firist yawace-yawace suke ta yi a ƙasar, kuma basu sani ba.'" 19 Ka ƙi Yahuda kenan dungum? Kana ƙin Sihiyona ne? Me yasa zaka azabtar da mu sa'adda babu warkarwa domin mu? Muna begen salama, amma ba wani abin kirki - don lokacin warkewa, amma ku gani, sai dai tsoro kaɗai. 20 Mun yarda, Yahweh, laifofinmu da muguntarmu da ta kakanninmu, gama mun yi maka zunubi. 21 Kada ka ƙi mu! Saboda darajar sunanka, kada kuma ka ƙasƙantar da darajar kursiyinka. Ka tuna kada kuma ka karya alƙawarinka da mu. 22 A cikin gumakan al'ummai marasa amfani akwai mai iya sa sammai su bada ruwa? Ba kai kaɗai ba ne, Yahweh Allahnmu, wanda yayi wannan? Mun sa bege a gare ka, gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa dukka.

Sura 15

1 Sai Yahweh yace da ni, "Ko da Musa ko Sama'ila zasu tsaya a gabana, duk da haka ba zan nuna wa waɗannan mutanen tagomashi ba. Ka kore su daga gabana, don su yi tafiyarsu. 2 Zaya zama sa'ad da suka ce da kai, 'Ina zamu tafi?' Sai ka faɗa masu, Yahweh ya faɗi wannan: Waɗanda an ƙaddara su mutu su tafi ga mutuwa; waɗanda suke na takobi su tafi ga takobi. Waɗanda suke na yunwa su tafi ga yunwa; kuma waɗanda suke na bauta su tafi ga bauta.' 3 Zansa su kasance kashi huɗu - wannan furcin Yahweh ne - takobi na kisan wasu ne, karnuka su yayyaga wasu, tsutsaye sararin sama da dabbobin duniya don su cinye su kuma hallakar da wasu. 4 Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukkan mulkokin duniya, saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, sarkin Yahuda, ya aikata a Yerusalem. 5 Amma wa zai ji tausayinki, Yerusalem? Wa zai yi baƙinciki domin ki? 6 Kun yashe ni - wannan furcin Yahweh ne - kun koma baya daga gare ni. Saboda haka zan buge ku da hannuna in kuma hallaka ku. Ni na gaji da nuna maku jinƙai. 7 Saboda haka zan sheƙe su da abin shiƙa a ƙofofin garuruwan ƙasar. Zansa su makoki. Zan hallaka mutanena tun da ba zasu juyo daga mugayen hanyoyinsu ba. 8 Zan yawaita gwaurayensu fiye da yashi a bakin teku. Game da uwayen samari zan aika da hallakarwa da tsakar rana. Zan sa azaba da razana su auko masu farat ɗaya. 9 Uwar da ta haifi 'ya'ya baƙwai zata yi yaushi ta suma. Faɗuwar ranarta zata zo tun da rana. Zata ji kunya da wulaƙanci, don zan bada waɗanda suka ragu ga takobi a gaban abokan gãbarsu -wannan furcin Yahweh ne." 10 Kaito na, mahaifiyata! Domin ke kika haife ni, ni ne mutum mai jayayya da gardama cikin dukkan ƙasar. Ban bada rance ba, ko wani ya bani rance, duk da haka dukkansu suna zagina. 11 Yahweh yace: "Ba zan ceto ka domin alheri ba? Babu shakka zansa abokan gãbarka su roƙi taimako a lokacin bala'i da masifa. 12 Wani zai iya karya ƙarfe? Musamman ƙarfe daga arewa wanda aka haɗa da tagulla? 13 Zan bada wadatarku da dukiyarku ganima kyauta ga abokan gãbarku. Zan yi wannan saboda dukkan zunubanku da kuka aikata a dukkan iyakarku. 14 Zansa ku bautawa abokan gãbarku a cikin ƙasar da ba ku sani ba, gama wuta zata kama, zata kunnu a cikin fushina gãba da ku." 15 Yahweh, ka sani! Ka tuna da ni ka kuma taimake ni. Ka kawo mani fansa ka kuma sãka wa waɗanda suke tsananta mani. Kai mai haƙuri ne, amma kada ka bar su su tafi da ni; ka sani na sha wahala saboda kai. 16 An sami magangaanunka, na kuwa cinyesu. Maganganunka sun zamar mani abin murna da farincikin zuciyata, gama ana kira na da sunanka, Yahweh, Allah mai runduna. 17 Ban zauna cikin ƙungiyar waɗanda suke annashuwa ko murna ba. Na zauna ni kaɗai saboda hannunka mai iko, gama ka sa na cika da haushi. 18 Me yasa azabata ta ƙi ƙarewa kuma raunukana ba sa warkewa? Zaka yaudare ni kamar ruwaye, ruwaye masu ƙafewa? 19 Domin wannan ga abin da Yahweh yace, "Idan ka tuba, Irmiya, sai in komo da kai, sa'annan zaka tsaya a gabana ka kuma bauta mani. Gama idan ka ware abubuwan dake banza daga abubuwa masu daraja, zaka zama kamar bakina. Sai mutanen su dawo wurinka, amma kai ba zaka koma wurinsu ba. 20 Zan maishe ka kamar garun tagulla da ba za a iya hudawa ba ga waɗannan mutane, zasu yi yaƙi da kai. Amma ba zasu yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in cece ka kuma in kuɓutar da kai -wannan furcin Yahweh ne - 21 gama zan kuɓutar da kai daga hannun mugaye kuma zan fanshe ka daga hannun marasa tausayi."

Sura 16

1 Sai maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 2 "Kada ka auri mata domin kanka, kuma kada ka sami 'ya'ya maza da 'ya'ya mata domin kanka a wannan wuri. 3 Gama Yahweh yace waɗannan 'ya'ya maza da mata waɗanda za a haifa a wannan wuri, da kuma iyayensu mata waɗanda zasu haife su, da iyayensu maza da zasu sa a haife su a wannan ƙasa, 4 'Zasu mutu da muguwar cuta. Baza a yi makoki ko a bisne su ba. Zasu zama kamar juji a ƙasa. Gama ƙarshe zai kasance ta wurin takobi da yunwa, kuma gawarwakinsu zasu zama abincin tsuntsayen sararin sama da nanamomin ƙasar.' 5 Gama maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 'Kada ka shiga gidan da ake makoki. Kada kayi makoki ko ka nuna damuwa dominsu, gama na ɗauke salamata daga waɗannan mutanen, da ƙaunata da jinƙaina - wannan furcin Yahweh ne. 6 Babba da yaro zasu mutu a wannan ƙasa. Baza a bizne su ba kuma ba wanda zai yi makoki domin su ko su tsattsage jikinsu ko su aske kansu ƙwal domin su. 7 Tilas kada wani ya raba abinci a cikin makoki don ya ta'azantar da su saboda matattu, tilas kuma kada wani ya bada ƙoƙon ta'aziya ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa don ya ta'azantar da su. 8 Tilas kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ka ci ka sha tare da su.' 9 Gama Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, 'Duba, a gaban idanunka, da zamaninka a kuma wannan wuri, na kusa kawo ƙarshen muryar murna da muryar farinciki, data ango data amarya.' 10 Zai kasance idan ka bayyana dukkan waɗannan maganganu ga waɗannan mutane, zasu kuwa ce maka, 'Me yasa Yahweh ya furta dukkan wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu da zunubin da muka yi wa Yahweh Allahnmu?' 11 Sai kace da su, 'Domin kakanninku sun rabu da ni - wannan furcin Yahweh ne - sun bi wasu alloli har sun bauta masu sun kuma sunkuya sun yi masu sujada. Sun rabu da ni, kuma basu kiyayye dokokina ba. 12 Gama ku kuma kun kawo mugunta fiye da ta kakanninku, ku gani, kowannenku yana tafiyar taurinkai da mugun nufi a zuciyarsa; ba wanda yake saurare na. 13 Saboda haka zan jefar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku baku sani ba, a can zaku bauta wa wasu alloli dare da rana, gama ba zan nuna maku wani tagomashi ba.' 14 Saboda haka, duba, kwanaki suna zuwa - wannan furcin Yahweh ne - da baza a ƙara cewa, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar ba.' 15 amma, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar arewa kuma daga ƙasashen da ya warwatsa su.' Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu. 16 Duba!! Zan aika domin masunta da yawa - wannan furcin Yahweh ne - zasu kuwa kama mutane su fitar waje. Bayan wannan zan aika domin mafarauta da yawa don su farauto su daga dukkan tsaunuka da tuddai, da cikin kogunan dutse. 17 Gama idona yana dukkan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke ba a gare ni. Muguntarsu kuma ba a ɓoye take ba daga idanuwana. 18 Zan fara saka masu ruɓi biyu domin laifinsu da zunubi domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun siffofin gunkinsu, kuma domin sun cika gãdona da gumakansu na banƙyama." 19 Yahweh, kai ne kagarata da mafakata, wurin tsarona a ranar wahala. Al'ummai zasu zo gunka daga ƙurewar duniya za a kuma ce, "Babu shakka kakanninmu sun gãji yaudara. Su fanko ne; babu riba a cikinsu. 20 Mutane zasu iya yiwa kansu alloli?' amma su ba alloli ba ne." 21 Saboda haka duba!! Zansa su sani a wannan lokacin, zansa su san hannuna da ikona, don haka zasu sani cewa sunana Yahweh ne.

Sura 17

1 "Zunubin Yahuda a rubuce yake da alƙalamin ƙarfe mai bakin lu'u-lu'u. An zana shi a allon zuciyarsu da ƙahon bagadinku. 2 Har 'ya'yansu masu na tunawa da bagadansu da sandunan Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa shimfiɗe akan kuma tuddai masu tsayi. 3 Dutsena a buɗaɗɗiyar ƙasar, dukiyarku da dukkan wadatarku zan bada su ganima, tare da wuraren tsaunukanku, saboda zunubin da kuka aikata a dukkan ƙasashen. 4 Zaku rasa gãdon da na baku. Zansa ku bautawa abokan gãbarku a ƙasar da baku sani ba, gama kun kunna wuta cikin fushina, wadda zata yi ta ci har abada." 5 Yahweh yace, "Mutumin dake dogara ga ɗan adam la'ananne ne; wanda ya maida jiki ƙarfinsa wanda ya juya zuciyarsa daga Yahweh. 6 Gama zai zama kamar ƙaramin jeji a Hamada ba kuma zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a wurare masu duwatsu a cikin daji, ƙeƙasarshiyar ƙasar da ba mazauna. 7 Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Yahweh, gama Yahweh ne dalilin madogararsa. 8 Domin yana kamar itacen da aka dasa gefen rafi, wanda saiwoyinsa suka bazu zuwa cikin rafin. Ba zai ji tsoron zafi ba a duk lokacin da yazo, domin kullum ganyensa kore ne. Ba zai da mu da shekarar fari ba, ba kuma zai fasa yin 'ya'ya ba. 9 Zuciya ta fi kome rikici. Cuta gare ta matuka; wa zai iya gane ta? 10 Ni ne Yahweh, wanda yake binciken tunani, wanda yake gwada zukata. Ina ba kowane mutum gwargwadon al'amuransa, da kuma gwargwadon ayyukansa. 11 Makwarwar da ta ƙwanta kan ƙwan da ba ita ta saka ba. Mutum zai iya zama mai arzaƙi ta rashin gaskiya, amma lokacin da yayi rabin shekarunsa sun yi, wannan arzaƙin zai bar shi, a ƙarshe zai zama wawa." 12 "Wurin haikalinmu kursiyi ne mai daraja, an ɗaukaka shi tun daga farko. 13 Yahweh shi ne begen Isra'ila. Dukkan waɗanda suka rabu da kai zasu ji kunya. Waɗanda suke cikin ƙasar waɗanda suka juya daga gare ka za a rubuta su akan ƙura. Domin sun rabu da Yahweh, maɓuɓɓugar ruwan rai. 14 Warkar da ni, Yahweh, zan kuwa warke! Ka cece ni, zan kuwa cetu. Gama kai ne waƙar yabona. 15 Duba!, suna ce mani, 'Ina maganar Yahweh take? Tazo mana!' 16 Amma ni, ban gudu daga zama makiyayi da yake binka ba. Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba. Ka kuwa san abin da ya fito daga leɓunana. An yi su a gabanka. 17 Kada ka zamar mani abin ban razana. Kai ne mafakata a ranar masifa. 18 Bari waɗanda suke runtumata su kunyata, amma kada ka barni in kunyata. Bari su karaya, amma kada ka bar ni in karaya. Ka aika masu da ranar masifa gãba da suka kuma rugurkujesu da hallaka riɓi biyu." 19 Yahweh ya faɗa mani wannan: "Ka tafi ka tsaya a ƙofar jama'a wadda sarakunan Yahuda suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukkan ƙofofin Yerusalem. 20 Ka ce da su, 'Ku ji maganar Yahweh, ku sarakunan Yahuda da dukkan ku mutanen Yahuda, da kowanne mazaunin Yerusalem waɗanda ke shiga ta waɗannan ƙofofi. 21 Yahweh ya faɗi wannan: "Kuyi hankali saboda rayukanku kada ku kuma ɗauki kaya a ranar Asabar ku kawo su ta ƙofofin Yerusalem. 22 Kada ku kawo kaya daga gidajen ku a ranar Asabar. Kada ku yi kowanne irin aiki, sai dai ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarce kakanninku su yi.'" 23 Basu saurara ba ko su mai da hankali, amma suka taurare wuyansu don kada su ji ni ko su karɓi horaswa. 24 Zai kasance idan dai kun saurare ni - wannan furcin Yahweh ne - kada ku kawo kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar amma maimako ku tsarkake ranar Asabar ta Yahweh kada kuma ku yi kowanne irin aiki a cikinta, 25 sa'an nan ne sarakuna, da 'ya'yan sarakuna, da waɗanda ke zaune akan kursiyin Dauda za su shiga ta ƙofofin wannan birni su na hawan karusai da dawakai, su da shugabaninsu, da mutanen Yahuda da mazauna Yerusalem, wannan birni kuma za a zauna cikinsa har abada. 26 Zasu zo daga biranen Yahuda daga kuma dukkan kewayen Yerusalem, daga ƙasar Benyamin da ta kwarurruka, daga duwatsu, da ta Negeb, suna kawo baye-bayen na ƙonawa da hadayu, baye-bayen hatsi da na turare, baye-bayen godiya ga gidan Yahweh. 27 Amma idan baku saurare ni ba - ku kiyaye ranar Asabar ba kuma ku ka ɗauki kaya masu nauyi kuka shiga ta ƙofofin Yerusalem a ranar Asabar ba - sai in cinna wa ƙofofin wuta, zata kuwa cinye tsararrun wurare na Yerusalem, ba kuwa zata kasu ba."

Sura 18

1 Maganar da ta zo ga Irmiya daga Yahweh, cewa, 2 "Tashi ka tafi gidan maginin tukwane, domin a can zaka ji maganata. 3 Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, duba yana aikin tukwane akan na'urar ginin tukwanen. 4 Amma abin da yake mulmulawa da yunɓu ya lalace a hannunsa, sai ya canja tunaninsa ya sake wani abu dabam wanda yake gani yana da kyau a idanunsa. 5 Sa'annan maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 6 "Ba zan iya yin haka da ku ba kamar wannan maginin tukwanen, gidan Isra'ila? -wannan furcin Yahweh ne. Duba! Kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane - haka nan kuke a hannuna, gidan Israi'la. 7 A lokaci ɗaya, zan iya yin shela wani abu akan al'umma ko mulki, cewa zan kora ta, in kakkaryata, ko hallaka ta. 8 Amma idan al'umma wadda na yi magana a kanta ta juyo daga muguntarta, sai in janye masifar da nayi niyyar kawo mata. 9 A wani lokaci, zan iya yin shelar wani abu akan wata al'umma ko mulki, cewa zan gina ko in kafa ta. 10 Amma idan ta aikata mugunta a idanuna ta wurin rashin sauraron muryata, daga nan zan janye abu mai kyau da na ce zan yi domin su. 11 To yanzu, yi magana da jama'ar Yahuda da mazaunan Yerusalem ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da shirya masifa gãba da ku. Ina gab da tsara wata dabara gãba da ku. Ku tuba, kowanne mutum daga muguwar hanyarsa, da haka hanyoyinku da ayyukanku zasu kawo maku alheri. 12 Amma zasu ce, 'Wannan bashi da amfani. Zamu yi kamar yadda muka tsara. Kowanne ɗayan mu zai yi bisa ga muguntarsa, da tattaurar zuciyarsa take marmari.' 13 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, 'Tambayi al'ummai, wane ne ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila ta yi mugun abu ƙwarai. 14 Dusar ƙanƙara Lebanon ta taɓa rabuwa da tsaunuka a gefenta? Ko rafuffukan duwatsu masu gangarowa daga nesa sun taɓa lalacewa, waɗannan rafuffuka masu sanyi? 15 Duk da haka mutanena sun manta da ni. Suna baye-baye ga gumaka marasa amfani waɗanda aka sasu tuntuɓe a cikin tafarkunsu; sun bar tsofaffin tafarku don suyi tafiya a tafarku masu sauƙi. 16 ‌Ƙasarsu zata zama abar banƙyama, ta zama abin tsaki har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kuma kaɗa kansa. 17 Zan warwatsa su gaban maƙiyansu kamar iskar gabas. Zan nuna masu bayana, amma ba fuskata ba, a ranar masifarsu.'" 18 Sai mutanen suka ce, "Kuzo, mu shirya maƙarƙashiya akan Irmiya, tun da yake shari'a bata lalace daga wurin firist ba, ko shawara daga mutane masu hikima ba, ko maganganu daga annabawa ba. Kuzo, mu kai ƙararsa ta wurin maganarmu kada mu yarda ko mu kula da duk wani abin da zai faɗa." 19 Ka saurare ni, Yahweh, ka saurari murya abokan gãbata. 20 Lallai ne masifa daga gare su ta zama ladana don yin abin kirki gare su? Duk da haka sun gina rami domina. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka na yi magana akan lafiyarsu, da zai sa a janye fushinka daga gare su. 21 Saboda haka ka miƙa 'ya'yansu ga yunwa, ka kuma bashe su a hannun masu amfani da takobi. Bari matansu su zama masu makoki da gwauraye, mazajensu a kashe su, samarinsu a kashe su da takobi a yaƙi. 22 Bari a ji kururuwa daga gidajensu, don maharan da ka aika masu farat ɗaya. Gama sun haƙa rami don su kama ni sun kuma kafa wa ƙafafuna tarkuna. 23 Amma kai, Yahweh, ka san dukkan maƙarshiyarsu a kaina don su kashe ni. Kada ka gafarta masu muguntarsu da zunubansu. Kada kuma ka shafe zunubansu daga gabanka. A maimakon haka, bari a jefar da su a gabanka. Ka yi gãba dasu a lokacin fushinka.

Sura 19

1 Yahweh ya faɗi wannan, "Tafi ka sayo tulun yumɓu a wurin maginin tukwane sa'ad da kana tare da dattawan mutane da kuma firistoci. 2 Sai ku tafi Kwarin Ben Hinnom na ƙofar Kasko, a wurin zaka yi shelar maganar da zan faɗa maka. 3 Ka ce, 'Ku ji maganar Yahweh, sarakunan Yahuda da mazaunan Yerusalem! Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Ku gani, na kusa kawo masifa akan wannan wuri, duk kuma kunuwan kowanne da zai ji zai karkaɗa. 4 Zan yi wannan domin mutanen sun rabu da ni sun ƙazantar da wannan wuri. A wannan wuri sun miƙa hadayu ga wasu alloli da basu san su ba. Kakaninsu, da sarakunan Yahuda sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi. 5 Sun ginawa Ba'al bagadi don su ƙona 'ya'yansu maza a matsayin baye-bayen ƙonawa gare shi - abin da ban umarta ba, ko in furta, ban ma yi tunanin haka ba. 6 Saboda haka, ku gani, rana tana zuwa - wannan furcin Yahweh ne - wadda wannan wuri baza a ƙara kiransa Tofet, Kwarin Ben Hinnom ba, domin zai zama Kwarin Yanka. 7 A wannan wuri zan wofinta shirin Yahuda da na Yerusalem. Zansa a kashe su da takobi a gaban abokan gãbarsu ta hannun waɗanda suke neman ransu. Sa'annan zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsutsayen sammai da na namomin jeji. 8 Zan mai da wannan birni kango da kuma abin tsaki, domin duk wanda ya wuce wurin zai yi mamaki da tsaki, akan dukkan annobar. 9 Zansa su ci naman 'ya'yansu maza da mata; kowanne mutum zai ci naman maƙwbcinsa cikin damuwa da azaba akan abin da ya faru da su daga wurin abokan gãbarsu da waɗanda suke neman ransu.'" 10 Sa'annan sai ka fasa tulun yumɓun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai. 11 Ka kuwa ce masu, 'Yahweh mai runduna yace wannan: Haka zan yi wannan abu ga waɗannan mutane na wannan birni - wannan furcin Yahweh ne - kamar yadda Irmiya ya fashe tulun yumɓun yadda ba wanda zai iya gyara shi kuma. Mutane zasu bizne matattu a Tofet har sai an rasa wurin da ya rage da za a sake bizne matattu kuma. 12 Wannan shi ne abin da zan yi da wannan wuri da mazaunansa idan na maida wannan birni kamar Tofe -wannan furcin Yahweh ne - 13 saboda haka gidajen Yerusalem da na sarakunan Yahuda zasu zama kamar Tofet - dukkan gidajen waɗanda akan rufinsu ne ƙazaman mutane suke sujada ga dukkan taurarin sararin sama da suke zuba abin sha na baye baye ga wasu alloli.'" 14 Sai Irmiya ya komo daga Tofet, inda Yahweh ya aike shi don yayi annabci. Ya tsaya a filin gidan Yahweh, yace da dukkan mutane. 15 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, y faɗi wannan, 'Ku gani, na kusa auka wa wannan birni da dukkan garuruwansa da dukkan masifu da na ambata gãba da shi, tun da sun taurare wuyansu sun kuma ƙi jin maganganuna.'"

Sura 20

1 Fashur ɗan Immer firist - shi babban jami'i ne - ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan maganganu a gaban gidan Yahweh. 2 Saboda haka Fashur ya bugi annabi Irmiya sa'annan ya sa shi cikin turu wanda ke ƙofar bisa ta Benyamin a gidan Yahweh. 3 Ya zamana kashegari sa'adda Fashhur ya fitar da Irmiya daga turun. Sai Irmiya yace da shi, "Yahweh bai kira sunanka Fashhur ba, amma ya baka suna Magor Missabib. 4 Domin Yahweh ya faɗi wannan, 'Duba, zan maishe ka abin tsoro, kai da dukkan waɗanda kake ƙauna, amma zasu mutu da takobi ta wurin abokan gãbarsu idanunka kuma zasu gani. Zan kuma bada dukkan jama'ar Yahuda a hannun sarkin Babila. Shi kuwa zai maida dasu bayi a Babila ko kuwa ya kai masu hari da takobi. 5 Zan ba shi dukkan dukiyar wannan birni da kuma dukkan arzikinta da dukkan abubuwa masu tamani da dukkan dukiyar sarakunan Yahuda. Zan miƙa waɗannan abubuwa a hannun abokan gãbarsu zasu kuma washe su. Zasu ɗauke su su kuma kai su Babila. 6 Amma kai, Fashhur, da dukkan mazauna gidanka zasu tafi bauta. Kai zaka tafi Babila a can zaka mutu. Kai da dukkan waɗanda kake ƙauna kuma kayi masu annabcin ƙaryar waɗannan abubuwa a wurin za a bizne ka.'" 7 Yahweh, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu. Ka fi ni ƙarfi, ka kuma rinjaye ni. Na zama abin dariya dukkan yini, kowa yana ta yi mani ba'a. 8 Amma duk lokacin da zan yi magana, na kan kira da murya in yi magana da ƙarfi, 'Hargitsi da hallakarwa.' Sai maganar Yahweh ta zama abin zargi da abin ba'a a dukkan yini. 9 Idan na ce, 'Ba zan ƙara yin tunani akan Yahweh ba. Ba kuwa zan ƙara yin magana da sunansa ba.' Sai in ji kamar wuta a cikin zuciyata, an sa ta a cikin ƙasusuwana. Sai in yi ƙoƙarin danne ta amma ba zan iya jurewa ba. 10 Na kan ji jita-jita ta banrazana daga wurin mutane da yawa a dukkan kewaye. 'Dole mu bada rahoto!' Waɗanda ke kusa da ni su dubawa su gani ko zan faɗi. 'Watakila za a ruɗe shi. Idan haka ne, sa'annan ma iya rinjayarsa har mu ɗauki fansarmu a kansa.' 11 Amma Yahweh yana tare da ni kamar jarumi mai iko, don haka masu runtumata zasu yi tangaɗi. Baza su ci nasara da ni ba. Zasu ji kunya ƙwarai domin ba zasu yi nasara ba. Ba zasu daina jin kunya ba, kuma ba za a manta ba. 12 Amma kai, Yahweh mai runduna, mai gwada adali wanda yake ganin zuciya da tunani. Bari in ga sakayyar da zaka yi masu tun da na kawo ƙarata a gare ka. 13 Raira waƙa ga Yahweh! A yabi Yahweh! Gama ya kuɓutar da rayukan waɗanda ake zalunta daga hannun mugaye. 14 Bari ranar da aka haife ni ta zama la'ananniya. Kada ka bar ranar da uwata ta haife ni ta yi albarka. 15 Bari mutumin da ya kai wa mahaifina labari ya zama la'annane, wanda yace, An haifa maka ɗa namiji,' don yasa ka farin ciki. 16 Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Yahweh ya kaɓantar ba tare da ya ji tausayinsu ba. Bari ya ji kuka don neman taimako da wayewar gari, da rana kuma ya ji gangamin yaƙi, 17 domin bai kashe ni tun ina ciki ba, ya sa uwata ta zama kabarina, cikin mahaifar da zata dawwama har abada. 18 Me yasa na fito daga cikin mahaifa in ga damuwa da azaba, don kwanakina su cika da kunya?"

Sura 21

1 Wannan ita ce maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh lokacin da sarki Zadakiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da Zafaniya ɗan Ma'aseya firist gare shi. Suka ce da shi, 2 "Nemi shawara daga Yahweh a madaddin mu, don Nebukadnezza sarkin Babila yana kawo ma na yaƙi. Me yiwuwa Yahweh zai yi abin ban al'ajabi domin mu, kamar yadda ya saba a lokatan baya, wanda ya sa shi ya janye daga wurin mu." 3 Sai Irmiya ya ce da su, "Wannan shi ne abin da dole za ku ce da Zadakiya, 4 Yahweh, Allah na Israila, ya faɗi wannan: Duba, zan juya baya ga kayan yaƙin da su ke hannunka, waɗanda ka ke yaƙi da su gãba da sarkin Babila da Kaldiyawa waɗanda suke kusa da ku daga wajen garun! Gama zan tara su a cikin tsakiyar wannan birnin. 5 Ni kaina zan yi faɗa da kai da duk ƙarfina, da kuma hasalata da zafin fushina. 6 Gama zan faɗawa mazaunan wannan birnin, mutum da dabba. Za su mutu da babbar annoba. 7 Bayan wannan - wannan shi ne furcin Yahweh - Zadakiya sarkin Yahuda, da bayinsa da mutanen, da duk wanda ya rage a cikin wannan birni bayan annoba, da takobi da kuma yunwa, zan bashe su dukka a hannun Nebukadnezza sakin Babila, da kuma hannun abokan gãbarsu, da hannun waɗanda suke neman rayukansu. Daga nan shi kuma zai kashe su da kaifin takobi. Ba zai ji tausayinsu ba, ko ya rage su, ko kuma ya yi juyayinsu ba.' 8 Game da waɗannan mutane dole ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba ina kusa da sa hanyar rai da hanyar mutuwa a gabanku. 9 Shi wanda ya zauna a wannan birnin zai mutu da takobi, da yunwa da kuma annoba; amma shi wanda ya fita zai ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suka kewaye ku gãba da ku zai rayu. Zai tserar da ransa. 10 Gama na ƙudura zan yi gãba da wannan birni in kuma kawo masa masifa ba alheri ba - wannan furcin Yahweh ne. An ba da shi a hannun sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.' 11 A game da gidan sarkin Yahuda kuwa, ku ji maganar Yahweh. 12 Ya gidan Dauda, Yahweh ya ce, 'Ku aikata adalci kowace safiya. Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace daga hannun mai tsananta masa, ko kuma hasalata ta fita kamar wuta ta yi ƙuna, harma ba mai iya kashe ta, saboda mugayen ayyukanku. 13 Duba, mazaunan kwari! Ina gãba da ku, dutsen da ya ke a fili - wannan furcin Yahweh ne - ina gãba da wanda yake cewa, "Wane ne zai iya saukowa ƙasa don ya yi gãba da mu?" Ko kuwa "Wane ne zai iya shiga gidajenmu?" 14 Na sa sakamakon ayyukanku su yi gãba da ku - wannan furcin Yahweh ne - kuma zan kunna wuta a cikin kurmin, za ta cinye duk abin da ya ke kewaye da ita.'"

Sura 22

1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya ce, "Ka gangara zuwa gidan sarkin Yahuda ka faɗa ma sa wannan magana a can. 2 Ka ce, 'Sarkin Yahuda, ka saurari maganar Yahweh - kai da ke zaune akan gadon sarautar Dauda - da kai, da barorinka, da mutanenka da ke shigowa ta waɗannan ƙofofi. 3 Yahweh ya faɗi wannan, "Ku aikata gaskiya da adalci, kuma duk wanda aka yi masa ƙwace - ku cece shi daga hannun masu zalumtarsa. Kada ku wulaƙanta wani baƙon da ke ƙasarku, ko maraya ko kuwa gwauruwa. Kada a yi ta'addanci ko a zubar da jinin marar laifi a wannan wurin. 4 Domin idan hakika ku ka yi waɗannan abubuwa, sarakunan da ke zaune kan kursiyin Dauda za su shiga cikin ƙofofin gidan nan haye cikin karusa da dawakai, shi, da barorinsa, da jama'arsa! 5 Amma idan ba ku kasa kunne ga waɗannan zantattuka waɗanda na yi shelar su ba - wannan furcin Yahweh ne - to wannan masarauta za ta zama kufai.'" 6 Gama Yahweh ya faɗi wannan game da gidan sarkin Yahuda, 'Kai kamar Giliyad ka ke, kamar ƙolƙolin Lebanon ka ke a gare ni. Duk da haka zan maisheka jeji, da kuma birane da ba mazauna. 7 Gama zan ƙaddara masu lalatarwa su tashi gãba da ku! Mutane da makamansu za su daddatse itatuwan sidarku mafi kyau su kuma zuba su a wuta. 8 Sa'annan al'ummai da yawa za su shige ta wannan birni. Kowanne mutum zai ce wa na kusa da shi, "Me ya sa Yahweh ya yi haka game da wannan babban birni?" 9 Sa'annan ɗayan zai amsa, "Saboda sun yi watsi da alƙawarin Yahweh Allahnsu suka russuna wa waɗansu alloli suka yi masu sujada." 10 Kada ku yi kuka domin wanda ya mutu ko ku yi makoki dominsa; amma ku yi kuka mai zafi sabili da wanda ya kusa tafiya, domin ba zai ƙara dawowa ya ga ƙasar asalinsa ba.' 11 Domin Yahweh ya faɗi haka game da Yehoahaz ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wanda ya gaji sarauta a madadin ubansa Yosiya, 'Ya tafi daga nan wurin ba zai sake komowa ba. 12 Zai mutu a can inda suka kai shi zaman talala, kuma ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.' 13 Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, benayensa kuma ta hanyar rashin gaskiya, ya sa makwabcinsa ya yi masa aiki a banza, bai kuma bashi al'bashinsa ba; 14 yana cewa, 'Zan gina wa kaina babban gida mai manyan ɗakuna a sama.' Sai ya sa masu manyan tagogi, ya kuma rufe su da itacen sida, ya kuma yi masu jan shafe. 15 Wannan ne zai maishe ka sarki mai adalci, da ka ke son ka sami katakan sida? Ko mahaifinka bai ci ya sha ba, duk da haka ya yi gaskiya da adalci? Sai komai ya tafi dai - dai da shi. 16 Ya shari'anta da alheri ga matalauta da fakirai. Ya yi kyau a lokacin nan. Wannan ba shi ne ma'anar sanina ba? - wannan ne furcin Yahweh. 17 Amma ba kome a zuciyarka da idanunka sai dai damuwa domin muguwar ribarka da kuma domin zubar da jinin marasa laifi, da aikata danniya da murƙushe waɗansu. 18 Sabili da wannan Yahweh ya faɗi haka game da Yehoiyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda: Ba za su yi makoki domin sa ba, suna cewa, 'Kaito, ɗan'uwana!' ko, 'Kaito, 'yar'uwata!' Ba za su yi makoki dominsa ba, suna cewa, 'Kaito, ubangida!' ko, 'Kaito, mai martaba!' 19 Za a binne shi kamar yadda ake binne jaki, a janye shi a jefar nesa da ƙofofin Yerusalem. 20 Ku haura kan duwatsun Lebanon ku yi ihu. Ku tada muryarku a Bashan. Ku yi ihu daga duwatsun Abarim, gama duk abokanku za a hallaka su. 21 Na yi maku magana sa'ad da ku ke zaune lafiya, amma kun ce, 'Ba za mu kasa kunne ba.' Al'adarku ce wannan tun kuna samari, gama ba ku saurari muryata ba. 22 Iska za ta kora dukkan makiyayanku, abokanku kuma za su tafi bautar talala. Sa'annan lallai za ku kunyata ku ƙasƙantu ta wurin miyagun ayyukanku. Ku da kuke zaune cikin 'Lebanon,' 23 ku da ku ke shaƙatawa cikin ginin itatuwan sida, za ku zama abin tausayi sa'ad da azabar naƙuda ta afko maku, azaba kamar ta mace mai naƙudar haifuwa!" 24 "Na rantse da zatina - wannan furcin Yahweh ne - ko da kai, Yehoiyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda, zoben hannun damana ne, zan cire ka. 25 Gama na bashe ka a hannun masu neman ranka da kuma hannun waɗanda ka ke jin tsoro a gabansu, wato hannun Nebukaneza sarkin Babila da Kaldiyawa. 26 Zan jefar da kai da mahaifiyarka wadda ta haife ka cikin wata ƙasa, ƙasar da ba nan aka haife ka ba, kuma can za ka mutu. 27 Game da ƙasar nan da suke so su koma, ba za su dawo nan ba. 28 Wannan ita ce tukunyar da aka rena aka kuma farfasa? Wannan shi ne mutumin nan Yehoiyacin tukunyar da ba ta gamshi kowa ba? Me ya sa suka jefar da shi waje da shi da zuriyarsa, kuma suka zubar da su cikin ƙasar da ba su santa ba? 29 Ƙasa, Ƙasa, ƙasa! Ki ji maganar Yahweh! 30 Yahweh ya faɗi wannan, "Rubuta akan mutumin nan Yehoiyacin: Ba zai haifu ba. Ba zai yi albarka ba a kwanakinsa, ba kuma wani a zuriyarsa da zai ci nasara ko kuma ya ƙara zama a kursiyin Dauda ya yi mulki bisa Yahuda ba."

Sura 23

1 "Kaiton makiyayan da ke lalatarwa suke kuma warwatsar da tumakin makiyayata - wannan furcin Yahweh ne." 2 Saboda haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da makiyayan da ke kiwon mutanensa, "Kun warwatsar da garkena kun kore su nesa. Ba ku lura da su ba. Sabili da haka na kusa in hukunta ku saboda muguntar da ku ka aikata - wannan ne furcin Yahweh. 3 Ni da kaina zan tattara ragowar garkena daga dukkan ƙasashen da na kora su, zan kuma dawo da su wurin kiwo, inda za su hayayyafa su kuma ƙaru. 4 Sa'anna zan tanada makiyaya bisansu waɗanda za su yi kiwon su domin kada su ƙara tsorata ko su zama karyayyu. Ba za a rasa ko ɗayansu ba - wannan furcin Yahweh ne. 5 Duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da zan tada wa Dauda reshe mai adalci. Shi zai yi mulki kamar sarki; zai yi aiki da hikima ya sa gaskiya da adalci su kasance a ƙasar. 6 A kwanakinsa Yahuda zai tsira, Isra'ila zai zauna lafiya. Ga sunan da za a kira shi da shi: Yahweh shi ne adalcinmu. 7 Saboda haka duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da ba za su ƙara cewa, "Na rantse da ran Yahweh wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar ba.' 8 Maimakon haka za su ce, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fitar ya kuma dawo da zuriyar gidan Isra'ila daga ƙasar arewa da dukkan ƙasar da aka kora su.' Sa'annan za su zauna a ƙasar da ke tasu." 9 A game da annabawan, zuciyata ta karai, dukkan ƙasusuwana su na kaɗuwa, na zama kamar bugaggen mutum, kamar mutumin da ruwan inabi ya rinjaye shi, saboda Yahweh da kuma zantattukansa masu tsarki. 10 Domin ƙasar ta cika da mazinata. Sabili da waɗannan ne ƙasar ta bushe. Wuraren kiwo a jeji sun ƙeƙashe. Tafarkun annabawan nan mugaye ne; ba su mori ikonsu yadda ya kamata ba. 11 Gama da annabawan da firstocin dukka biyu sun ƙazamtu. Har ma na ga muguntarsu a cikin gidana! - wannan ne furcin Yahweh - 12 Sabili da haka tafarkinsu zai zama kamar wuri mai santsi cikin duhu. Za a ture su ƙasa. Za su faɗa a cikinta. Gama zan aiko da masifa găba da su a shekarar da zan hukunta su - wannan ne furcin Yahweh. 13 Gama na ga annabawan da ke cikin Samariya su na yin abin kyama: sun yi annabci da Ba'al sun karkatar da jama'ata Isra'ila. 14 A cikin annabawan da ke Yeruselem na ga mugayen abubuwa: Su na yin zina su na aikata ƙarya. Su na ƙarfafa hannun miyagu; ba wanda yake juyowa daga muguntarsa. Dukkan su sun zama kamar Soduma a gareni, mazamnan su kuma kamar Gwamarata!" 15 Saboda haka Ubangiji mai runduna ya faɗi wannan game da annabawan, "Duba, na kusa in sa su su ci abu mai ɗaci su sha ruwa mai dafi, gama ƙazamta ta bazu daga annabawa da ke cikin Yeruselem har zuwa dukkan ƙasar." 16 Ubangiji mai runduna ya ce, "Kada ku saurari maganganun annabawan da ke yi maku annabci. Sun zurma ku! Suna sanar da wahayi daga nasu tunani, ba daga bakin Yahweh ba. 17 Kullum su na faɗa wa waɗanda su ka rena ni, 'Yahweh ya ce akwai salama dominku,' Gama kowanne mai tafiya a cikin tattaurar zuciyarsa ya kan ce, 'Masifa ba za ta auko kanmu ba.' 18 Duk da haka wa ya tsaya a majalisar Yahweh? Wa ya gani ya kuma ji maganarsa? Wa ya natsu ya kasa kunne ya saurari maganarsa? 19 Duba, akwai hadarin da ke dannowa daga Yahweh! Hasalar sa na fita, guguwa kuma na juyawa ko'ina. Tana zagayawa kewaye da kan mugaye. 20 Fushin Yahweh ba zai huce ba sai ya gama aiwatawa da cika nufin zuciyarsa. A ƙarshen kwanaki, za ku gane shi. 21 Ban aiki waɗannan annabawan ba. Haka kawai su ka bayyana. Ban shaida masu kome ba, amma duk da haka su ka yi annabci. 22 Inda sun kasance a majalisar shawarata, da sun sa jama'ata su ji maganata; da sun sa su su juyo daga mugayen maganganunsu da kuma mugayen ayyukansu. 23 Ni Allah ne na kusa kaɗai - wannan ne furcin Yahweh - ba kuma Allah na nesa ba? 24 Akwai wani da zai iya ɓoye wa a wurin da ba zan ganshi ba? - wannan ne furcin Yahweh - ko ni ban cika sammai da ƙasa ba? - wannan ne furcin Yahweh. 25 Na ji abin da annabawan su ka faɗi, waɗanda suke annabcin ƙarya cikin sunana. Sukan ce, 'Na yi mafarki! 'Na yi mafarki! 26 Har yaushe za a ci gaba da haka, annabawa masu annabcin ƙarya daga tunaninsu, da kuma annabci daga ruɗun da ke cikin zuciyarsu? 27 Su na shirin sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkan da su ka sanar, kowanne ga maƙwabcinsa, kamar dai yadda kakaninsu su ka manta da sunana su ka so sunan Ba'al. 28 Annabin da ya ke da mafarki, bari ya sanar da mafarkin. Amma ga wanda na sanar da shi wani abu, bari ya sanar da maganata da gaskiya. Me ya haɗa ciyawa da al'kama? - wannan ne furcin Yahweh - Maganata ba kamar wuta ta ke ba? - wannan ne furcin Yahweh - 29 kuma kamar guduma mai farfasa duwatsu gutsu - gutsu? 30 To ku duba, ina găba da annabawan - wannan ne furcin Yahweh - da kowanne ɗayan da ya saci magana daga wani mutum ya kuma ce maganar ta zo daga gareni. 31 Duba, ina găba da annabawan - wannan ne furcin Yahweh - masu amfani da harshensu su yi shelar annabci. 32 Duba, ina găba da annabawa da ke mafarkan ƙarya - wannan ne furcin Yahweh - sa'annan su yi shela da haka su ke ɓad da mutanena da ƙarairayinsu da kuma fariya. Ina găba da su, gama ban aike su ba ko in ba su umarni. Saboda haka lallai, ba za su taimaki mutanen nan ba - wannan ne furcin Yahweh. 33 Lokacin da waɗannan mutane, ko annabi, ko firist ya tambayeku, 'mene ne nawaiyar Yahweh?' za ka ce masu, 'Ku ne nawaiyar, kuma zan jefar da ku - wannan ne furcin Yahweh. 34 Game da annabawan, da firistoci, da kuma mutanen da ke cewa, 'Wannan shi ne nawaiyar Yahweh' zan hukunta wannan mutum da gidansa. 35 Kuna ci gaba da cewa, kowanne mutum ga makwabcinsa da kuma kowanne mutum ga ɗan'uwansa, 'Me Yahweh ya amsa?' kuma 'Me Yahweh ya furta? 36 Amma ka da ku ƙara yin magana akan 'nawayar Yahweh,' gama nawaiyar ita ce maganar kowanne mutum, kuma kun karkatar da maganganun Allah mai rai, Ubangiji mai runduna, Allahnmu. 37 Ga abin da za ku ce wa annabi, 'Wace amsa ce Yahweh ya ba ku? ko kuma, 'Me Yahweh ya ce?' 38 Amma idan kun ce, 'Nawaiyar Yahweh,' wannan shi ne abin da Yahweh ya ce: 'Sabili da kun faɗi wanɗannan maganganu, 'Nawaiyar Yahweh,' lokacin da na aika maku, cewa, 'Ba za ku ce, "Nawaiyar Yahweh,"' ba. 39 saboda haka, duba, na kusa ɗaukar ku in jefar da ku nesa da ni, tare da birnin dana ba ku da kakanninku. 40 Sa'annan zan sa maku madawwamiyar kunya da zargi a kanku wanda ba za a taɓa mantawa ba.'"

Sura 24

1 Yahweh ya nuna mani wani abu. Duba, ga kwanduna biyu na 'ya'yan baure a gaban haikalin Yahweh. (Wannan wahayi ya faru bayan da Nebukadnezza, sarkin Babila, ya kai waɗannan mutane bautar talala: Yehoyacin ɗan Yehoyakim, sarkin Yahuda, da shugabannin Yahuda, da masassaƙa, da masu ƙira da kwasao daga Yerusalem ya kawo su Babila.) 2 Ɗaya kwandon ɓauren na da ƙyau sosai, kamar nunar fari na ɓaure, amma ɗaya kwandon ɓauren ba shi da kyau ko kaɗan har ma ba za a iya cin su ba. 3 Yahweh ya ce mani, "Me ka gani, Irmiya?" Na ce, '"Ya'yan ɓaure. 'Ya'yan ɓaure masu kyau sosai da marasa kyau har ma ba za a iya cinsu ba." 4 Sai maganar Yahweh ta zo gareni, cewa, 5 "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Zan dubi 'yan bautar talala na Yahuda da tagomashi, kamar kyawawan 'ya'yan ɓauren nan, 'yan bautar talala waɗanda na kore su daga nan zuwa ƙasar Kaldiya. 6 Zan kafa idanuna a kansu domin in yi masu alheri, in kuma dawo da su wannan ƙasar. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan dasa su, ba zan tumbuƙe su ba. 7 Sa'annan zan ba su zuciyar da za su sanni, gama ni ne Yahweh. Za su zama mutanena, zan kuma zama Allahnsu, haka za su juyo gareni da dukkan zuciyarsu. 8 Amma kamar 'ya'yan ɓauren nan marasa kyau har da ba za a iya cinsu ba-ga abin da Yahweh ya ce - Zan yi haka da Zedekiya, sarkin Yahuda, da shugabanninsa, da kuma sauran da ke a Yerusalem waɗanda suka rage a cikin ƙasar nan ko kuwa su ka tafi su zauna cikin ƙasar Masar. 9 Zan maishe su abin tsoro, abin masifa, a idanun dukkan mulkokin duniya, abin kunya abin zargi da karin magana, da dariya, da la'ana a duk wuraren da na warwatsa su. 10 Zan aika da takobi, yunwa, da annoba găba da su, har sai an hallakasu daga ƙasar da na basu da kakanninsu."

Sura 25

1 Wannan ita ce maganar da ta zo wurin Irmiya game da dukkan mutanen Yahuda. Ya zo ne a shekara ta huɗu ta Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda. Wannan ita ce shekara ta fari ta Nebukadnezza, sarkin Babila. 2 Annabi Irmiya ya yi shelar wannan ga dukkan mutanen Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem. 3 Ya ce, "Shekaru ashirin da uku, tun daga shekara ta sha uku ta Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda, har zuwa yau, maganar Yahweh ta na ta zuwa gare ni, ni kuma na yi maku magana akai-akai, amma ba ku kasa kunne ba. 4 Yahweh ya aika maku dukkan bayinsa annabawa akai-akai, amma ba ku saurare su ba ko ku kasa kunne. 5 Waɗannan annabawa sun ce, 'Bari kowanne mutum ya juyo daga hanyar muguntarsa da lalatattun ayyukansa ya dawo ƙasar da Yahweh ya bayar a zamanin dã ga kakanninku da ku kuma, a matsayin madawwamiyar kyauta. 6 Saboda haka kada ku bi waɗansu alloli ku yi masu sujada ko ku russuna masu, kuma kada ku cakune shi da ayyukan hannuwanku domin kada ya azabtar da ku.' 7 Amma ba ku saurare ni ba - wannan ne furcin Yahweh - haka ku ka cakune ni da aikin hannuwanku in cutar da ku. 8 Domin haka Ubangiji mai ruduna ya faɗi wannan, 'Saboda ba ku saurari maganganuna ba, 9 duba, ina gaf da aiko da umarni domin a tara dukkan mutanen arewa - wannan ne furcin Yahweh - da Nebukadnezza bawana, sarkin Babila, zan kawo su gãba da ƙasar nan da mazaunanta, gãba kuma da dukkan al'umman da ke kewaye da ku. Gama zan keɓe su domin halakarwa. Zan mai da su abin tsoro, abin yi wa tsaki, da kuma kufai har abada. 10 Zan kawo ƙarshen ƙarar murna da ƙarar farinciki, ƙarar ango da ƙarar amarya, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila. 11 Sa'annan dukkan wannan ƙasa za ta zama kufai da abin tsoro, kuma waɗannan al'ummai za su bauta wa sarkin Babila shekaru saba'in. 12 Za ya zama kuwa bayan shekaru saba'in sun cika, zan hukunta sarkin Babila da al'umman nan, ƙasar Kaldiyawa - wannan ne furcin Yahweh - saboda kurakuransu in maishe ta kango marar matuƙa. 13 Sa'anan kuma zan yi wa ƙasar nan abin gãba bisa ga dukkan maganar da na faɗi, da kuma dukkan abin da aka rubuta a cikin wannan littafi wanda Irmiya ya yi annabci gãba da dukkan al'ummai. 14 Kuma wasu al'umman da yawa da manyan sarakuna za su bautar da waɗannan al'ummai. Zan sãka masu bisa ga abin da su ka aikata da kuma ayyukan hannuwansu."' 15 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗa mani wannan, "Ka ƙarɓi wannan ƙoƙon ruwan inabi na hasalata daga hannuna ka sa dukkan al'umman da na aike ka gun su su sha shi. 16 Gama za su sha sa'anan su yi tuntuɓe ko ina su sheƙa da gudu daga takobin da nake aikowa cikinsu." 17 Sai na ƙarɓi ƙoƙon daga hannun Yahweh, na kuma să dukkan al'umman da Yahweh ya aike ni su sha shi: 18 Yerusalem, biranen Yahuda da sarakunanta da shugabanninta-a maida su kufai da abin tsoro, da kuma abin tsaki da la'antarwa, kamar yadda suke a yau. 19 Sauran al'ummai dole su sha shi: Fir'auna Sarkin Masar da barorinsa; shugabanninsa da dukkan mutanensa; 20 dukkan baƙin mutane ruwa biyu da dukkan sarakunan da ke ƙasar Uz; dukkan sarakunan da ke ƙasar Filistiya - Ashkelon, Gaza, Ekron, da ragowar Ashdod; 21 Idom da Mowab da mutanen Ammon. 22 Sarakunan Taya da Sidon, sarakunan gãɓar tsallaken teku, 23 Dedan, Tema, da Buz da dukkan waɗanda suke aske gashin gefen kawunansu suma sai da suka sha shi. 24 Waɗannan mutanen suma dole suka sha shi: dukkan sarakunan Arebiya da dukkan sarakunan mutane masu ruwa biyu da ke zaune a jeji; 25 dukkan sarakunan Zimri, da dukkan sarakunan Elam, da dukkan sarakunan Madayana; 26 dukkan sarakunan arewa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa - kowanne da ɗan'uwansa da dukkan masarautar da ke duniya da ke a fuskar ƙasa. A ƙarshe, sarkin Babila zai sha a bayansu. 27 Yahweh ya ce mani, "Yanzu dole ka faɗa masu, 'Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Ku sha ku bugu, sa'anan ku haras, ku faɗi ƙasa, kada ku tashi kafin in aiko da takobi a tsakanin ku.' 28 Idan kuwa sun ƙi su ƙarɓi ƙoƙon daga hannunka su sha, za ka ce masu, 'Yahweh mai runduna ya faɗi wannan, Dole ne lallai ku sha shi. 29 Ku duba, na kusa kawo masifa akan birnin da ake kira da sunana, to ku da kanku ya kamata a tsirar da ku daga horo ne? Ba za ku tsira ba, gama ina kawo takobi gãba da dukkan mazaunan ƙasar! - wannan ne furcin Yahweh mai runduna.' 30 Dole ka yi annabcin dukkan waɗannan maganganu gãba da su, kuma ka ce masu, 'Yahweh zai yi ruri daga sammai zai yi ihu da muryarsa daga wurin zamansa mai tsarki, zai yi ruri da ƙarfi gãba da nasa; kuma zai yi ihu, kamar waɗanda suke matse 'ya'yan inabi gãba da dukkan mazaunan duniya. 31 Zizar yaƙi zata buga ta kai dukkan bangon duniya, gama Yahweh yana kawo ƙara gãba da dukkan al'ummai, zai kuma kawo hukunci kan dukkan talikai. Zai ba da mugaye ga takobi - wannan ne furcin Yahweh.' 32 Ubangiji mai runduna ya faɗi wannan, 'Duba, masifa tana tasowa daga al'umma zuwa al'umma, kuma babban hadari ya danno daga manisantan wurare na duniya. 33 Sa'anan waɗanda Yahweh ya kashe za su zama daga wannan bangon duniyan zuwa wan can; ba kuma za a yi makokinsu ba, ko a tattarasu, ko kuma a binne su. Za su zama kamar taki a ƙasa. 34 Ku yi makoki, makiyaya, ku yi ihu domin taimako! Ku yi birgima a cikin ƙura, ku iyayengijin garke, gama ranar da za a yanka ku ta zo; za a warwatsa ku sa'ad da ku ka faɗi kamar kyawawan tukwane. 35 Babu mafaka domin makiyaya, ba sauran mafita domin iyayengijin garke. 36 Ku ji koke-koken makiyaya da makokin iyayengijin garke, gama Yahweh yana lalatar da makiyayarsu. 37 Haka makiyayarsu mai salama za a lalatar da ita sabili da zafin fushin Yahweh. 38 Kamar ɗan zaki, da ya baro maɓuyarsa, gama ƙasarsu zata zama abin ban tsoro saboda fushin mai tsanantawa, saboda kuma zafin fushinsa.'"

Sura 26

1 A farkon mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, wannan maganar ta zo daga Yahweh cewa, 2 "Yahweh ya faɗi wannan: Ka tsaya a filin haikalina ka yi magana akan dukkan biranen Yahuda waɗanda suke zuwa su yi sujada a gidana. Yi shelar dukkan maganganun da na umarce ka ka faɗa masu. Kada ka rage ko wata kalma! 3 Mai yiwuwa su kasa kunne, har kowanne mutum ya juyo ya bar mugayen hanyoyinsa, nima in janye masifar da nake niyyar saukar masu saboda mugayen ayyukansu. 4 Saboda haka dole ka ce masu, 'Yahweh ya faɗi wannan: Idan baku kasa kunne gare ni kun yi biyayya da dokokina da na sa agabanku ba - 5 Idan baku kasa kunne da maganar bayina annabawa waɗanda na ke aiko maku-amma ba ku ji ba! - 6 to zan maida gidan nan kamar Shiloh; zan maida birnin nan la'ana a idanun dukkan al'umman da ke a duniya.'" 7 Da firistoci, da annabawa da dukkan jama'a sun ji annabi Irmiya yana shelar waɗannan maganganu a haikalin Yahweh. 8 Ananan da Irmiya ya gama shelar dukkan maganar da Yahweh ya umarce shi ya faɗa wa dukkan mutane, sai firistoci, da annabawa da dukkan mutane suka kama shi suka ce, "Zaka mutu lallai! 9 Me yasa ka yi annabci a cikin sunan Yahweh ka ce wannan gida zai zama kamar Shiloh kuma wannan birni zai zama kufai, har ba mazauna?" Gama dukkan mutanen sun tada tarzoma gãba da Irmiya a cikin haikalin Yahweh. 10 Daganan sai shugabannin Yahuda suka ji waɗannan maganganu suka tashi daga gidan sarki su ka tafi gidan Yahweh. Su ka zauna a ƙofa a Sabuwar Ƙofa ta haikalin Yahweh. 11 Sai firistoci da annabawa suka yi wa shugabanni da dukkan mutane magana. Suka ce, "Dai-dai ne mutumin nan ya mutu, domin ya yi annabci gãba da birnin nan, kamar yadda kuka ji da kunnuwanku!" 12 Sai Irmiya ya yi magana da dukkan shugabanni da dukkan mutane yace, "Yahweh ya aiko ni in yi annabci gãba da haikalin nan da kuma birnin nan, in faɗi dukkan maganganun nan da kuka ji. 13 Saboda haka yanzu fa, sai ku gyara al'amuranku da kuma ayyukanku, ku saurari muryar Yahweh Allahnku domin ya janye masifar da ya yi shela gãba da ku. 14 Ni da kaina-ku dube ni! - ina hannunku. Ku yi mani abin da kuka ga yayi dai-dai a idanunku. 15 Amma lallai ya kamata ku sani idan ku ka kashe ni, kuna jawo wa kanku al'hakin jinin marar laifi da kuma wannan birni da mazaunan da ke a cikinsa, gama lallai Yahweh ya aiko ni wurinku in yi shelar waɗannan maganganu a kunnuwanku." 16 Daga nan shugabannin da dukkan mutane suka cewa firistoci da annabawa, "Ba dai-dai ba ne mutumin nan ya mutu, gama ya yi mana shelar abubuwa a cikin sunan Yahweh Allahnmu." 17 Sai wasu maza suka tashi daga cikin dattawan ƙasar suka yi wa dukkan taron mutanen magana. 18 Suka ce, "Mika Ba-morashe ya yi annabci a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya yi wa dukkan mutanen Yahuda magana yace, 'Yahweh mai runduna yace: Za a huɗa Sihiyona kamar gona, Yerusalem za ta zama tsibin juji, dutsen haikali zai zama dutsen da ciyayi suka sha kansa.' 19 To, Hezekiya sarkin Yahuda da dukkan Yahuda sun kashe shi ne? Ashe bai ji tsoron Yahweh ya nemi alheri a fuskar Yahweh domin Yahweh ya janye masifar da ya faɗa masa ba? Ko dai-dai ne muyi mugunta mafi girma gãba da rayyukanmu?" 20 Ananan wani mutum kuma ya yi annabci cikin sunan Yahweh - Yuriya ɗan Shemaya daga Kiriyat Yarim-shi ma ya yi annabci gãba da birnin nan da kuma ƙasannan, ya amince da dukkan maganganun Irmiya. 21 Amma da sarki Yehoyakim da dukkan sojojinsa da shugabanninsa suka ji maganarsa sai sarki ya yi ƙoƙari ya kashe shi, amma da Yuriya ya ji sai ya tsorata, ya gudu ya tafi Masar. 22 Sai sarki Yehoyakim ya aiki mutane su tafi Masar - Elnatan ɗan Akbor da waɗansu mutanen aka aike su su bi Yuriya zuwa Masar. 23 Suka ɗauko Yuriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoiyakim. Sai Yehoiyakim ya kashe shi da takobi ya aika gawarsa makabartar da ke waje inda ake rufe mutane marasa galihu. 24 Amma hannun Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bada shi ga hannun mutane su kashe ba.

Sura 27

1 A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, wannan magana ta zo ga Irmiya daga Yahweh. 2 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa mani, "Ka yiwa kanka karkiyar itace. Ka sa su a wuyanka. 3 Sa'annan ka aika su wurin sarkin Idom, sarkin Mowab, sarkin mutanen Ammon, sarkin Taya, da kuma sarkin Sidon. Ka aika da su ta hannun jakadun sarki da suka zo Yerusalem gun Zedekiya sarkin Yahuda. 4 Ka ba su umarni domin iyayengijinsu ka ce, 'Ubangiji mai runduna, Allah na Isra'ila ya ce: Wannan shi ne abin da zaku ce da iyayengijinku, 5 Ni da kaina na yi duniya ta wurin ƙarfina mai girma da miƙaƙƙen hannuna. Ni ne nayi mutane da dabbobi a kan fuskar duniya, nakan kuma ba da ita ga wanda na ga ya dace a idanuna. 6 Saboda haka yanzu, ina bada dukkan ƙasar nan a cikin hannun bawana, Nebukadnezza, sarkin Babila. Kuma ina bada abubuwa masu rai na jeji su bauta masa. 7 Gama dukkan al'ummai za su bauta masa, da ɗansa da kuma jikokinsa, har sai lokaci domin ƙasarsa ya zo. Sa'annan al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su ci ƙarfinsa. 8 Saboda haka duk al'umma da mulkin da bai bauta wa Nebukadnezza, sarkin Babila ba, bai kuma ba da wuyansa ya yi karkiya da sarkin Babila ba-zan hukunta wannan al'umma da takobi, yunwa, da annoba - wannan furcin Yahweh ne-har sai na hallaka ta ta hannunsa. 9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu mafarkanku, masu dubanku, masu sihiri, da matsubbata, waɗanda suke ta yi maku magana suna cewa, 'Kada ku bauta wa sarkin Babila,' 10 Gama suna yi maku annabcin ƙarya domin su kora ku nesa da ƙasarku, gama zan kore ku, zaku kuma mutu. 11 Amma al'ummar da ta bada wuyanta ta yi karkiya da sarkin Babila, ta kuma bauta masa, zan bar su su huta a ƙasarsu - wannan furcin Yahweh ne-zasu kuma noma ta su gina mazauninsu a ciki.""' 12 Sai na yi magana da Zedekiya sarkin Yahuda na ba shi wannan saƙon, 'Ku ba da wuyanku ku yi karkiya da sarkin Babila ku bauta masa da shi da mutanensa, zaku kuwa rayu. 13 Donmi zaku mutu-da kai da mutanenka-da takobi, yunwa da annoba, kamar yadda na faɗa game da al'ummar da ta ƙi ta bauta wa sarkin Babila? 14 Kada ku saurari maganganun annabawan da suka ce maku, 'Kada ku bauta wa sarkin Babila,' gama suna yi maku annabcin ƙarya ne. 15 Gama ni ban aikesu ba-wannan furcin Yahweh ne - gama annabcin ƙarya suke yi cikin sunana domin in kore ku ku tafi ku hallaka, da ku da annabawan da suke maku annabci." 16 Na yi shelar wannan ma firistoci da dukkan mutane na ce, "Yahweh ya faɗi wannan yace: Kada ku kasa kunne ga maganganun annabawaku da su kayi maku annabci suka ce, 'Duba! ana dawo da kayayyakin gidan Yahweh daga Babila yanzu!' Annabcin ƙarya suke yi maku, 17 Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babila ku rayu. Don me wannan birni zai zama kufai? 18 Idan su annabawa ne, kuma idan lallai maganar Yahweh ta zo gare su, to su roƙi Yahweh mai runduna kada ya aika kayan haikalinsa da suka rage, na gidan sarkin Yahuda, da na Yerusalem zuwa Babila. 19 Yahweh mai runduna ya faɗi haka game da ginshiƙai da babban daro da aka sani a matsayin "Tekun" da mazauninta, da sauran kayayyakin da suka rage a wannan birni - 20 kayayyakin da Nebukadnezza sarkin Babila bai ɗauka ba lokacin da ya tafi da Yehoyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda bautar talala daga Yerusalem zuwa Babila tare da dukkan hakiman Yahuda da na Yerusalem. 21 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da kayayyakin da suka rage a gidan Yahweh, da gidan sarkin Yahuda da Yerusalem, 22 'Za a kawo su Babila, kuma za su kasance a can har sai ranar da na aza a zo domin su - wannan ne furcin Yahweh - sa'annan zan komo da su in maido su a wannan wuri."'

Sura 28

1 Sai ya kasance a cikin shekarar nan, a farkon mulkin Zedekaya sarkin Yahuda, a shekara ta huɗu kuma a wata na biyar, Annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibiyon, yayi magana da ni a gidan Yahweh a gaban firistoci da dukkan mutane. Yace, 2 "Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan: Na karya karkiyar da sarkin Babila ya ɗora maku. 3 A cikin shekara biyu a wannan wuri zan maido da dukkan kayayyakin gidan Yahweh wanda Nebukadnezza sarkin Babila ya ɗauke daga wannan wuri ya tafi dasu Babila. 4 Daga nan kuma a wannan wurin zan maido da Yehoiyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda, da dukkan kamammun Yahuda waɗanda aka aika Babila - wannan furcin Yahweh ne - Gama zan karya karkiyar sarkin Babila." 5 Sai Annabi Irmiya yayi magana da Annabi Hananiya a gaban firistoci da dukkan mutanen dake tsaye a gidan Yahweh. 6 Irmiya Annabi yace, "Bari Yahweh yayi haka! bari Yahweh ya tabbatar da maganganun daka anabta a wannan wuri ya maido da kayayyakin gidan Yahweh, da dukkan kamammu daga Babila. 7 Duk da haka, ka saurari maganar da nake shelarwa a kunnuwanka da kunnuwan dukkan mutane. 8 Annabawan da suka wanzu da daɗewa kafin ni da kai sunyi anabci game da al'ummai masu yawa gãba da manyan masarautu, game da yaƙi, da yunwa, da annoba. 9 Hakanan Annabin da yayi anabcin za a yi salama - Idan maganarsa ta tabbata, to za a sani cewa lallai annabi ne wanda Yahweh ya aiko." 10 Amma annabi Hananiya ya tashi ya ɗauki karkiyar dake wuyan annabi Irmiya ya karya ta. 11 Daga nan sai Hananiya yayi magana a gaban dukkan mutanen yace, "Yahweh ya faɗi haka: kamar dai haka, cikin shekara biyu zan karya kowace karkiya daga wuyan dukkan al'ummai wanda Nebukadnezza sarkin Babila ya ɗora masu." Daga nan annabi Irmiya yayi tafiyarsa. 12 Bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar dake wuyan annabi Irmiya, sai maganar Yahweh tazo ga Irmiya, cewa, 13 "Kaje kayi magana da Hananiya kace, 'Yahweh ya faɗi haka: ka karya karkiyar itace, a maimako zan yi karkiyar ƙarfe.' 14 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: na ɗora karkiyar ƙarfe a bisa wuyan dukkan waɗannan al'ummai domin su bauta wa Nebukadnezza sarkin Babila, kuma zasu bauta mashi. Na kuma bashi bisashen jeji dake cikin gonaki domin yayi mulki a kansu." 15 Kuma annabi Irmiya ya cewa annabi Hananiya, "Ka saurara Hananiya! Yahweh bai aiko ka ba, amma kai da kanka kasa mutanen nan su gaskata ƙarya. 16 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan: duba, ina gab da aika ka daga wannan duniya. A wannan shekarar zaka mutu, tunda kayi shelar tawaye ga Yahweh." 17 A cikin watan bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.

Sura 29

1 Waɗannan ne maganganun dake cikin littafin da annabi Irmiya ya aika daga Yerusalem zuwa ga ragowar dattawan daga cikin kamammun da kuma firistoci, da annabawa, da dukkan mutanen da Nebukadnezza ya tura bauta daga Yerusalem zuwa Babila. 2 Wannan ya faru ne bayan da aka aika da sarki Yehoyacin, da mahaifiyar sarki, da manyan dagatai, da shugabannin Yahuda da Yerusalem, da masu sana'o'in hannu daga Yerusalem. 3 Ya aika da wannan littafi ne ta hannun Elasa ɗan shafan da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Hezekaya, sarkin Yahuda, ya aika ga Nebukadnezza sarkin Babila. 4 Littafin yace, "Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan ga dukkan kamammu waɗanda nasa suka tafi bauta daga Yerusalem zuwa Babila, 5 'Ku gina gidaje ku zauna a cikinsu. Ku shuka gonaki kuci amfaninsu. 6 Ku auri mataye ku haifi 'ya'ya maza da mata. Ku aurowa 'ya'yanku maza mataye, ku aurar da 'ya'yanku mata ga mazaje. Bari su haifi 'ya'ya maza da mata kuma ku ƙaru ta haka ba zaku zama 'yan kaɗan ba. 7 Ku biɗi salamar birnin da na aika daku bauta, ku yi roƙo gare ni a madadinsa tunda zaku kasance da salama idan yana cikin salama.' 8 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan, 'Kada ku bar annabawanku dake zaune a tsakaninku da masu sihirinku su ruɗe ku, kada kuma ku saurari mafarke-mafarken da ku da kanku kuke yi. 9 Gama suna ruɗin ku cikin anabcin da suke yi a cikin sunana. Ban aike su ba - wannan furcin Yahweh ne.' 10 Gama Yahweh ya faɗi wannan 'Idan Babila ta yi mulkinku har shekaru saba'in, zan taimake ku in aiwatar da maganata mai nagarta game da ku in sake maido da ku a wannan wuri. 11 Gama ni da kaina na san irin shirye-shiryen da nake da su dominku - wannan furcin Yahweh ne- shirye-shirye na salama ba na bala'i ba, domin in baku gaba mai kyau da bege. 12 Daga nan zaku yi kira a gare ni, zaku je ku yi addu'a a gare ni, zan kuma saurare ku. 13 Gama zaku neme ni ku kuma same ni, tunda zaku neme ni da dukkan zuciyarku. 14 Daga nan zan samu gare ku - wannan furcin Yahweh ne - zan kuma maido da kadarorinku; zan tattaro ku daga cikin dukkan al'ummai da wuraren da na warwatsar da ku - wannan furcin Yahweh ne - gama zan maido da ku wannan wuri daga inda nasa kuka tafi bauta.' 15 Tunda kunce Yahweh ya tado maku da annabawa a Babila, 16 Yahweh ya faɗi wannan game da wanda ke zaune bisa kursiyin Dauda da dukkan mutanen da ke zaune a cikin birnin, 'yan'uwanku waɗanda basu tafi tare da ku cikin bauta ba - 17 Yahweh Mai runduna ya faɗi haka, 'Duba, ina gab da aiko da takobi, da yunwa da cuta a kansu. Gama zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓauren da ba a iya ci. 18 Daga nan zan runtume su da takobi, da yunwa, da annoba in maida su abin tsoratarwa ga dukkan mulkokin duniya.-abin ƙyama, abin la'ana da tsãki, abin kunya cikin dukkan al'ummai inda na warwatsa ta. 19 Wannan saboda basu saurari maganata ba ne - wannan furcin Yahweh ne-wanda na aika masu ta wurin bayina annabawa. Na aike su sau da yawa, amma baku saurara ba-wannan furcin Yahweh ne.' 20 Domin wannan ku da kanku ku saurari maganar Yahweh, dukkanku 'yan bautar da ya kora daga Yerusalem zuwa Babila, 21 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da Ahab ɗan Kolaiya da Zedekaya ɗan Ma'ãseya, waɗanda suke yi maku anabcin ƙarya a cikin sunana: Duba, ina gab da sanya su cikin hannun Nebukadnezza sarkin Babila. Zaya kashe su a kan idanun ku. 22 Daga nan za a furta la'ana game da waɗannan mutane daga bakin ɗaurarrun Yahuda da ke Babila. La'anar zata ce: Dãma Yahweh ya maida kai kamar Zedekaya da Ahab, waɗanda sarkin Babila ya gashe cikin wuta. 23 Wannan zaya faru ne saboda abubuwan kunya da suka aikata a Isra'ila da suka yi zina da matayen maƙwabtansu suka kuma furta maganganun ƙarya a cikin sunana, abubuwan da ban taɓa umurtar su ba su faɗa. Gama Ni ne na sani; Ni ne shaida-wannan furcin Yahweh ne."' 24 Game da Shemaiya Nehelamiye, ka faɗi wannan: 25 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Domin ka aika da wasiƙu a cikin sunanka zuwa ga dukkan mutanen Yerusalem, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma'ãseiya firist, da dukkan firistoci, kãce, 26 Yahweh ya maida kai firist a maimakon Yehoaida firist, domin kayi shugabancin gidan Yahweh. Kai ne ke mulkin dukkan mutanen dake girgije-girgije suna maida kansu annabawa. Sai ka sanya su a turu da sarƙoƙi. 27 To yanzu, me yasa baka tsautawa Irmiya na Anatot ba, wanda ya maida kansa annabi mai tsayayya da kai? 28 Gama ya aika mana a Babila yana cewa, 'Lokaci ne mai tsawo za ayi. Ku gina gidaje ku zauna a ciki, ku shuka gonaki ku ci amfaninsu.""' 29 Zefanaya firist ya karanta wannan wasiƙa a kunnen annabi Irmiya. 30 Sai maganar Yahweh tazo ga Irmiya, cewa, 31 "Ka aika magana ga dukkan 'yan bauta kace, 'Yahweh ya faɗi wannan game da Shemaiya Nehelamiye: Saboda Shemaiya yayi maku anabci wanda Ni da kaina ban aike shi ba, kuma yasa kun gaskata ƙarya, 32 Domin wannan Yahweh ya faɗi haka: Duba, Ina gab da horon Shemaiya Nehelamiye da zuriyarsa. Ba za a sami wani mutum da zaya tsaya masa ba a cikin mutanen nan. Ba zai ga alherin da zan yiwa mutanena ba - wannan furcin Yahweh ne - Gama yayi shelar tawaye gãba da Yahweh."'

Sura 30

1 Maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh, cewa, 2 "Ga abin da Yahweh, Allah na Isra'ila, yace, 'Ka rubutawa kanka a littafi dukkan maganganun dana furta maka a littafi. 3 Gama duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da zan maido da kaddarorin mutanena, Isra'ila da Yahuda. Ni, Yahweh, Na faɗi wannan. Gama zan maido da su ƙasar da na ba kakanninsu, zasu kuma mallake ta."' 4 Waɗannan ne maganganun da Yahweh ya furta game da Isra'ila da Yahuda, 5 "Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Munji muryar rawar jiki da fargaba bata salama ba. 6 Ku yi tambaya ku ji ko Namiji na haihuwar ɗa. To yaya naga kowanne mutum mai ƙuruciya da hannu a kwankwaso kamar macen da zata haihu? Yaya fuskokinsu suka koɗe? 7 Kaito! Gama wannan rana babba ce, babu wata kamar ta. Zata zama lokacin fargaba domin Yakubu, amma za a cece shi daga ita. 8 Gama zaya kasance a wannan rana - wannan furcin Yahweh ne Mai runduna - zan karya karkiyar daga wuyan ku, zan ɓalle sarƙoƙinku, domin bãƙi ba zasu sake bautar da ku ba. 9 Amma zasu yi sujada ga Yahweh Allahnsu su kuma bautawa Dauda sarkinsu, wanda zan naɗa sarki a kansu. 10 To kai, Yakubu bawana, kada kaji tsoro - wannan furcin Yahweh ne - kada kuma ka firgita, Isra'ila. Gama duba, Ina gaf da maido da kai daga nesa, Zuriyarka kuma daga ƙasar bauta. Yakubu zai dawo ya zauna cikin salama; za a kãre shi, kuma babu sauran tsoratar wa. 11 Gama ina tare da ku - wannan furcin Yahweh ne - domin in cece ku. Daga nan zan kawo cikakken ƙarshen dukkan al'ummai inda na warwatsar da ku. Amma tabbas bazan kawo ƙarshenku ba, koda yake na horar da ku bisa adalci kuma tabbas bazan barku babu horo ba.' 12 Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Rauninku ba ya warkuwa; rauninku ya sami lahani. 13 Babu wanda za yayi roƙo domin ku; babu wani magani da zai warkar da rauninku. 14 Masoyanku dukka sun manta da ku. Ba zasu neme ku ba, gama na yi maku rauni da raunin maƙiyi da kuma horon ubangida mai mugunta saboda kurakuranku masu yawa da zunubanku marasa ƙirguwa. 15 Me yasa kuke neman taimako domin rauninku? zafinku baya warkuwa. Saboda kurakuranku masu yawa da zunubanku marasa ƙirguwa, na yi maku waɗannan abubuwa. 16 Domin wannan duk waɗanda ke cinye ku za a cinye su, kuma dukkan magabtanku zasu tafi cikin bauta. Domin dukkan waɗanda suka washe ku za su zama abin washewa, kuma dukkan waɗanda suka maida ku ganima zan maida su ganima. 17 Gama zan kawo warkarwa gare ku; zan warkar da ku daga raunukanku - wannan furcin Yahweh ne - zan yi wannan saboda sun kira ku: Yasassu. Babu wanda ya kula da wannan Sihiyonar."' 18 Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, Ina gab da maido da kaddarorin rumfunan Yakubu in kuma ji tausayin gidajensu. Daga nan za a gina birni a bisa rusassun wurarensu, mafaka mai ƙarfi kuma zata kasance inda take a dã. 19 Daganan waƙar yabo da ƙarar shagulgula zasu fito daga gare su, gama zan ƙãra su ba kuma zan rage su ba; zan darjanta su domin kada su wulaƙanta. 20 Daga nan mutanensu zasu zama kamar dã, taronsu kuma zaya tabbata a gabana yayin da zan horar da masu tsananta masu a yanzu. 21 Shugabansu zaya fito daga cikin su. Zaya ɓullo daga cikin su yayin da zan jawo shi kusa yayin da kuma ya matso gare ni. Idan ban yi haka ba wane ne zai iya zuwa kusa da ni? - wannan furcin Yahweh ne. 22 Daganan zaku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku. 23 Duba, iskar fushin Yahweh, da hasalarsa, tana fita waje. Iska ce marar tsaitsayawa. Zata yi guguwa bisa kawunan mutane masu mugunta. 24 Fushin Yahweh ba zai dawo ba har sai ya aiwatar kuma ya haifar da nufe-nufen zuciyarsa. A ranakun ƙarshe, zaku fahimci wannan."

Sura 31

1 "A wannan lokaci - wannan furcin Yahweh ne- Zan zama Allahn dukkan iyalan Isra'ila, su kuma zasu zama mutanena." 2 Yahweh ya faɗi wannan, "Mutanen da zuka tsira daga takobi sun sami tagomashi a jeji; zan fita in bayar da hutawa ga Isra'ila." 3 Yahweh ya bayyana gare ni a baya kuma yace, "Na ƙaunace ka, Isra'ila, da madawwamiyar ƙauna. Saboda haka na jawoka zuwa gare ni da amintaccen alƙawari. 4 Zan sake gina ki domin ki ginu, budurwa Isra'ila. Zaki sake ɗaukar tamburanki ki fita da raye-rayen murna. 5 Zaki sake dasa gonakin inabi a tsaunukan samariya; manoman zasu dasa kuma suyi amfani da 'ya'yan. 6 Gama rana tana zuwa wadda masu tsaron tsaunukan Ifraim zasu yi shela, 'Ku tashi, mu tafi Sihiyona ga Yahweh Allahnmu.' 7 Gama Yahweh ya faɗi wannan, "Ku yi sowa ta farinciki game da Yakubu! Ku yi sowa cikin jindaɗi game da manyan mutanen al'ummai! Bari aji yabo. Ku ce, 'Yahweh ya ceci mutanensa, ragowar Isra'ila.' 8 Duba, ina gab da kawo su daga ƙasashen arewa. Zan tattaro su daga sassan duniya mafi nisa. Makaho da gurgu zasu kasance a cikin su; Mataye masu ciki da waɗanda ke kusa da haihuwa zasu kasance tare da su. Babban taro ne zaya dawo a nan. 9 Za su zo da kuka; zan bishe su yayin da sukeyin roƙo. Zansa suyi tafiya zuwa maɓulɓulan ruwa a bisa miƙaƙƙiyar hanya. Ba zasu yi tuntuɓe akai ba, gama zan zama Uba ga Isra'ila, Ifraim kuma zaya zama ɗan farina." 10 Ku saurari maganar Yahweh, al'ummai. Ku yi rahoto har ga ƙasashen kurmi dake nesa. Ku al'ummai dole ku ce, 'Wanda ya warwatsa Isra'ila yana tattara ta kuma yana tsaronta kamar yadda makiyayi ke tsaron tumakinsa.' 11 Gama Yahweh ya ceto Yakubu ya kuma fanso shi daga hannun wanda yafi ƙarfinsa sosai. 12 Daga nan zasu zo su yi farinciki bisa tuddan Sihiyona. Fuskokinsu zasu haskaka saboda alherin Yahweh, bisa hatsi da ruwan inabi, bisa mai da 'ya'yan garken awakinsu da na tumaki da kuma na shanu. Gama rayuwarsu zata zama kamar fadamar da ake yiwa banruwa, ba kuma zasu ƙara jin baƙinciki ba daɗai. 13 Daga nan budurwai zasu yi farinciki da rawa, samari kuma da tsofaffi zasu kasance tare. Domin zan canza makokinsu zuwa bukukuwa. Zan ji tausayin su insa su yi farinciki a maimakon baƙinciki. 14 Daga nan zan mamaye rayuwar firistoci da yalwa. Mutanena zasu cika kansu da nagartata-wannan ne furcin Yahweh." 15 Yahweh ya faɗi wannan: "An ji murya a Ramah, kururuwa da kuka mai ɗaci. Rahila ce ke kukan 'ya'yanta. Taƙi ta ta'azantu game da su, gama basu a raye." 16 Yahweh ya faɗi wannan, "Ki tsai da muryarki daga kuka idanunki kuma daga hawaye; gama akwai sakamako game da aikinki - wannan ne furcin Yahweh - 'ya'yanki zasu dawo daga ƙasar maƙiya. 17 Akwai bege domin gabanki - wannan furcin Yahweh ne- zuriyarki zasu dawo cikin kan iyakokinsu." 18 Babu shakka naji bakincikin Ifraim, 'Ka horar da ni, kuma na horu kamar maraƙin da ba horarre ba. Ka maido da ni kuma zan sami maiduwa, gama kai ne Yahweh Allahna. 19 Gama bayan na juyo zuwa gare ka, nayi nadama; bayan na horu, na mari cinyata. Na ji kunya kuma na ƙasƙantu, gama na ɗauki tsarguwar ƙuruciyata.' 20 Ifraimu ba ɗa na ne mai daraja ba? Ba ƙaunataccena ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Gama duk sa'ad da na yi maganar tsayayya da shi, babu shakka ina tunawa da shi a raina da ƙauna. Ta haka zuciyata ke marmarin sa. Babu shakka zanji tausayin sa - wannan furcin Yahweh ne." 21 Ku kafawa kanku alamun hanya. Ku sanyawa kanku alamun jagora. Ku shirya tunaninku a tafarki mai kyau, hanyar da zaku bi. Ku dawo, budurwan Isra'ila! Ku dawo cikin waɗannan biranen naku. 22 Har yaushe zaki ci gaba da shakka, ɗiya marar aminci? Gama Yahweh ya halicci wani sabon abu a duniya - mace ta kewaye namiji maji ƙarfi. 23 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Idan na maido da mutanen zuwa cikin ƙasarsu, zasu faɗi wannan cikin ƙasar Yahuda da kuma biranenta, 'Bari Yahweh ya albarkace ka, kai wuri mai adalci inda ya ke zaune, kai dutse mai tsarki.' 24 Gama Yahuda da biranenta zasu zauna tare a wurin, kamar yadda manoma da waɗanda suka fita da garkunansu. 25 Gama zan bada ruwa ga gajiyayyu domin su sha, kuma zan cika dukkan sumammu." 26 Bayan wannan sai na farka, sai na lura da cewa barcina ya wartsakar da ni. 27 Duba, ranaku suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - Inda zan shuke gidajen Isra'ila dana Yahuda da zuriyoyin mutane dana bisashe. 28 A baya, Na keɓe su ciki tsaro domin in tunɓuke su in yage su, in tuntsurar, in lalatar, in kuma kawo masu bala'i. Amma a kwanaki masu zuwa, zan lura da su, domin in gina su in kuma dasa su - wannan furcin Yahweh ne. 29 A cikin waɗannan kwanaki babu wanda zaya sake cewa, 'Ubanni sun ci inabi masu tsami, amma haƙoran 'ya'ya ne suka dãsashe.' 30 Gama kowane mutum zaya mutu cikin kurakuransa; Duk wanda ya ci inabi masu tsami, haƙoransa ne zasu dãsashe. 31 Duba, kwanaki suna zuwa - wanna furcin Yahweh ne - inda zan kafa sabon alƙawari tare da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuda. 32 Ba zaya zama kamar alƙawarin dana kafa da Ubanninsu ba a kwanakin da na ɗauko su na kamo hannusu na fito da su daga ƙasar masar. Waɗannan kwanakin ne inda suka karya alƙawarina, duk da cewa ni miji ne a gare su - wannan furcin Yahweh ne. 33 Amma wannan ne alƙawarin da zan kafa da gidan Isra'ila bayan waɗannan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne: Zan sanya shari'ata a cikinsu in rubuta ta a zukatansu, gama zan zama Allahnsu, zasu kuma zama mutanena. 34 Daganan babu sauran wani mutum ya koyawa maƙwabcinsa, ko wani mutum ya koyawa ɗan'uwansa ya ce, 'Ka san Yahweh!' gama dukkan su, daga mafi ƙanƙantarsu har ya zuwa mafi girmansu, zasu san ni - wannan furcin Yahweh ne - Gama zan gafarta kurakuransu ba kuma zan sake tunawa da zunubansu ba." 35 Yahweh ya faɗi wannan - shi ne wanda yake sanya rana ta haskaka da rana ya kuma jejjera wata da taurari su haskaka da dare. Shi wanda ke sanya teku na motsi raƙuman ruwanta kuma na ruri. Sunansa Yahweh Mai runduna. 36 Sai idan waɗannan dawwamammun abubuwan sun ɓace daga gare ni - wannan furcin Yahweh ne- ko zuriyar Isra'ila zasu daina zama al'umma a gabana." 37 Yahweh ya faɗi wannan, "Sai idan za a iya ɗaukar gwajin sammai dake nesa, sai kuma idan za a iya gano harsashin duniya dake can ƙasa, shi ne zan iya yashe da dukkan zuriyar Isra'ila saboda dukkan abin da suka yi - wannan furcin Yahweh ne." 38 Duba, kwanaki suna zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'ad da za a sake gina birnin domina, daga hasumiyar Hananel zuwa ‌Ƙ‌ofar kwana. 39 Daga nan layin gwajin zai fita ya ƙara nisa, zuwa tuddun Gerab da kewayen Goya. 40 Dukkan kwarin gawawwaki da tokarsu, da dukkan filayen kurmi har ya zuwa Kwarin Kidron har zuwa kwanar ‌Ƙofar Doki da ke gabas, za a keɓe domin Yahweh. Ba za a sake rusarwa ko tuntsurar da birnin ba, har abada."

Sura 32

1 Wannan ce maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh a shekara ta goma ta sarautar sarki Zedekiya na Yahuda, a shekara ta sha takwas ta Nebukadnezza. 2 A wannan lokaci, sojojin sarkin Babila sun yi wa Yerusalem sansani, Annabi Irmiya kuma yana cikin kurkukun harabar 'yan tsaro dake cikin gidan sarkin Yahuda. 3 Zedekiya sarkin Yahuda ya sanya shi cikin kurkuku ya kuma ce, "Me yasa kake anabci kana cewa, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da miƙa wannan birni cikin hannun sarkin Babila, kuma zaya ci shi da yaƙi. 4 Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kubce ba daga hannun Kaldiyawa, gama babu shakka za a miƙa shi cikin hannun sarkin Babila. Bakinsa kuma za ya yi magana da bakin sarkin, idanunsa kuma zasu ga idanun sarkin. 5 Za ya ɗauki Zedekiya zuwa Babila, zaya zauna a can har sai na gama horar da shi - wannan furcin Yahweh ne. Koda yake za ka yi yaƙi da Kaldiyawa, ba zaka yi nasara ba."' 6 Irmiya ya ce, "Maganar Yahweh tazo gare ni, tana cewa, 7 'Duba, Hanamel ɗan Shallum kawunka na zuwa wurin ka kuma zai ce, "Ka saiwa kanka gonata da ke Anatot, domin kai ne ka ke da 'yancin sayen ta.""' 8 Daga nan, kamar yadda Yahweh ya furta, Hanamel, ɗan-ɗan kawuna, Yazo wuri na a harabar 'yan tsaro, sai ya ce da ni, "Ka sayi gonata dake a Anatot cikin ƙasar Benyamin, domin kai ne ke da 'yancin gãdo, kuma 'yancin saye na gare ka. Ka sai wa kanka." Daga nan na sani cewa wannan maganar Yahweh ce. 9 Sai na sayi gonar da ke Anatot daga wurin Hanamel, ɗan-ɗan kawuna, sai na gwada mashi azurfar, shekel sha bakwai a nauyi. 10 Sai na rubuta a takarda na hatimce ta, na kuma kawo shaidu su shaida. Sai na gwada mashi azurfar a ma gwaji. 11 Sai na ɗauki takardar kammala saye da aka hatimce, bisa ga shari'a da ka'idoji, da kuma takardar kammala saye da ba a hatimce ba. 12 Sai na bada hatimtacciyar takardar ga Baruk ɗan Neriya ɗan Masiyya a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da kuma shaidun da suka sa hannu a hatimtacciyar takardar, a kuma gaban Yahudawan da ke zaune a harabar 'yan tsaron. 13 Sai na bada umarni ga Baruk a gaban su. Nace, 14 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Karɓi takardunnan, dukkan takardun kammala sayen da wannan da aka hatimce da waɗannan da ba a hatimce ba, sai ka sanya su a cikin tukunyar ƙasa domin suyi ƙarko na dogon lokaci. 15 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Za a sake sayen gidaje, da gonaki, da garkunan inabi a cikin wannan ƙasar." 16 Bayan da na bada rasiɗin saye ga Baruk ɗan Neriya, sai nayi addu'a ga Yahweh nace, 17 Kaito, Ubangiji Yahweh! Duba! Kai ka ɗai ka halitta Sammai da duniya ta wurin babban ƙarfinka da ɗagaggen hannunka. Babu abin da ka faɗa wanda zai gagare ka ka yi. 18 Kana nuna amintaccen alƙawarinka ga dubbai kana kuma zubo da tsarguwar mutane bisa cinyoyin 'ya'yansu bayansu. Kai ne mai girma Allah mai iko kuma; Yahweh Mai runduna ne sunanka. 19 Kai babba ne a hikima mai girma kuma cikin ayyuka, idanunka a buɗe suke ga dukkan hanyoyin mutane, domin kaba kowanne mutum abin da ya cancanci halinsa da ayyukansa. 20 Ka yi alamu da al'ajibai a ƙasar Masar. Har yazuwa yau a nan ƙasar Isra'ila da kuma cikin dukkan 'yan adam, kasa sunanka ya zama sananne. 21 Gama ka fito da mutanenka Isra'ila daga ƙasar Masar da alamu da al'ajibai, da hannu mai ƙarfi, da ɗagaggen hannu, da kuma babbar razana. 22 Daga nan ka basu wannan ƙasar - wanda ka rantsewa Ubanninsu zaka basu - ƙasar dake zubo da madara da zuma. 23 Sai suka shiga suka mallake ta. Amma ba su yi biyayya da muryarka ba ko suka zauna cikin biyayya da shari'arka ba. Ba su yi komai ba game da abin da ka umarce su su yi, sai ka kawo dukkan wannan bala'i a kansu. 24 Duba! Tarin sansanin ya kai har birnin domin ya ci shi da yaƙi. Gama saboda Takobi, da yunwa, da annoba, an bayar da birnin cikin hannun Kaldiyawa da suke yaƙi da shi. Gama abin da kace zaya faru yana faruwa, kuma duba, kana kallo. 25 Daga nan kai da kanka kace mani, "Ka sai wa kanka gona da azurfa kuma ka kawo shaidu su shaida, duk da cewar ana bayar da wannan birni a hannun Kaldiyawa." 26 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, tana cewa, 27 Duba! Ni ne Yahweh, Allahn dukkan 'yan adam. Akwai abin da ya gagare ni in yi? 28 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, ina gab da bayar da wannan birni cikin hannun Kaldiyawa da Nebukadnezza, sarkin Babila. Za ya ci shi da yaƙi. 29 Kaldiyawan da ke yaƙi da birnin nan za su zo su cinna mashi wuta su ƙone shi, tare da gidajen da ke kan rufin wuraren da mutane ke yiwa Ba'al sujada suke kuma zuba baye-bayen shayarwa ga wasu alloli domin su cakune ni. 30 Gama mutanen Isra'ila da Yahuda babu shakka mutane ne da ke ta aikata mugunta a gaban idanuna tun daga ƙuruciyarsu. Babu shakka mutanen Isra'ila sun ɓata mani rai ta wurin ayyukan hannuwansu - wannan furcin Yahweh ne. 31 Yahweh ya furta cewa wannan birni na tunzura fushina da hasalata tun daga ranar da aka gina shi. Haka yake har zuwa wannan rana. To zan kawar da shi daga fuskata 32 saboda dukkan muguntar mutanen Isra'ila da ta Yahuda, abubuwan da suka yi domin su cakune ni - su, da sarakunansu, da dagatansu, da firistocinsu, da annabawansu, da kuma kowane mutum a Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem. 33 Sun juya mani bayansu a maimakon fuskokinsu, koda yake da ɗoki na koyar da su. Nayi ƙoƙari in koyar da su, amma babu wani cikinsu da ya saurara domin ya ɗauki gyara. 34 Suka jera haramtattun gumakansu a cikin gidan da ake kira da sunana, suka gurɓata shi. 35 Suka gina dogayen wurare domin Ba'al a kwarin Ben Hinnom domin su sanya 'ya'yansu maza da mata cikin wuta domin Molek. Ban umarcesu ba. Bai taɓa shiga tunanina ba cewa zasu aikata wannan abin ƙyama su sa Yahuda ya yi zunubi.' 36 To saboda haka yanzu, Ni, Yahweh, Allah na Isra'ila, Na faɗi wannan game da birnin, birnin da kuke cewa, 'An bayar da shi cikin hannun sarkin Babila ta wurin takobi, da yunwa, da annoba. 37 Duba, ina gab da tattaro su daga kowace ƙasa inda na kora su cikin fushina, da hasalata, da babban jin haushina, Ina gab da maido su cikin wannan wuri in kuma sa su iya zama cikin tsaro. 38 Daga nan zasu zama mutanena, Ni kuma in zama Allahnsu. 39 Zan basu zuciya ɗaya da hanya ɗaya na girmama ni kullum domin ya zama alheri a gare su da kuma zuriyarsu bayansu. 40 Daga nan tare da su zan kafa madawwamin alƙawari, cewa bazan juya daga yi masu alheri ba. Zan sa girmamawa domi na a zukatansu, ta haka ba zasu sake juyawa daga gare ni ba. 41 Daga nan zan yi farinciki wurin yi masu alheri. Da aminci zan dasa su cikin ƙasar nan da dukkan zuciyata da dukkan raina. 42 Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Kamar yadda na kawo dukkan wannan babban bala'i a bisa mutanen nan, haka zan kawo masu dukkan abubuwan alherin da nace zan yi domin su. 43 Daga nan za a sayi gonaki a cikin wannan ƙasar, wadda kuke cewa, "Wannan busasshiyar ƙasa ce, wadda babu mutum balle dabba. An bayar da ita cikin hannun Kaldiyawa." 44 Za su sayi gonaki da azurfa su kuma rubuta cikin hatimtattun takardu. Zasu tattara shaidu a cikin ƙasar Benyamin, a dukkan kewayen Yerusalem da biranen Yahuda, a cikin birane a cikin garuruwan tudu da kuma ƙasashen kwari, da kuma biranen Negeb. Gama zan maido da kaddarorinsu - wannan furcin Yahweh ne."'

Sura 33

1 Daga nan maganar Yahweh ta zo ga Irmiya karo na biyu, yayin da yake kulle a harabar 'yan tsaro, cewa, 2 "Yahweh mahalicci, ya faɗi wannan - Yahweh, wanda yake halittawa domin ya tabbatar-Yahweh ne sunansa, 3 Ku kira gare ni, Ni kuma zan amsa maku. Zan nuna manyan abubuwa a gare ku, asirai da baku fahimta ba.' 4 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da gidajen da ke cikin wannan birni da gidajen sarakunan Yahuda waɗanda suka rushe saboda mamayewar sansani da takobi, 5 Kaldiyawa suna zuwa su yi yaƙi su kuma cika waɗannan gidaje da gawawwakin mutane waɗanda zan kashe cikin fushina da hasalata, yayin da na ɓoye fuskata daga wannan birni saboda dukkan muguntarsu. 6 Amma duba, Ina gab da kawo warkarwa da lafiya, zan warkar da su in kawo masu yalwa, salama da aminci. 7 Gama zan maido da kaddarorin Yahuda da Isra'ila; Zan kuma gina su kamar da farko. 8 Daga nan zan tsarkake su daga dukkan kurakuran da suka yi a gare ni. Zan gafarta dukkan kurakuran da suka yi a gare ni, da kuma dukkan hanyoyin da suka yi tsayayya a gare ni. 9 Gama wannan birni zai zame mani abin farinciki, waƙar yabo da girmamawa daga dukkan al'umman duniya waɗanda zasu ji dukkan abubuwan alheri da zan yi domin shi. Daga nan zasu ji tsoro su girgiza saboda dukkan abubuwan alheri da salama da zan bayar a gare su. 10 Yahweh ya faɗi wannan, 'A wannan wurin wanda yanzu kuke cewa, "Kufai ne, wurin da babu mutum balle dabba," a biranen Yahuda da kuma titunan Yerusalem waɗanda suke kufai babu mutum balle dabba, da za a sake ji a ciki 11 ‌Ƙarar farinciki da ƙarar murna, ƙarar ango, da ƙarar amarya, ƙarar waɗanda suka ce, yayin da suke kawo baye-bayen godiya ga gidan Yahweh, "Ku bada godiya ga Yahweh Mai runduna, gama Yahweh nagari ne, kuma ƙaunarsa marar kasawa ta dawwama har abada!" Gama zan maida kaddarorin ƙasar nan kamar yadda suke a dã,' inji Yahweh. 12 Yahweh Mai runduna ya faɗi wannan: 'A wannan kufan wuri, inda yanzu babu mutum balle dabba-a dukkan biranen za a sami saura inda makiyaya zasu hutar da garkunansu. 13 A cikin biranen da ke ƙasar tudu, da kwari, da kuma Negeb, a cikin ƙasar Benyamin da dukkan kewayen Yerusalem, da kuma cikin biranen Yahuda, garkuna kuma zasu sake bi ta ƙarƙashin hannuwan masu ƙirga su,' inji Yahweh. 14 Duba! kwanaki na zuwa - wannan furcin Yahweh ne-inda zan aikata abin da na yi alƙawari game da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuda. 15 A cikin waɗannan kwanaki da kuma cikin wannan lokaci zan sa reshen adalci ya tsiro domin gidan Dauda, zaya aiwatar da hukunci da kuma adalci a cikin ƙasar. 16 A waɗannan kwanaki za a ceci Yahuda, Yerusalem kuma zata zauna cikin tsaro, gama ga yadda za a kira ta, "Yahweh ne adalcinmu."' 17 Gama Yahweh ya faɗi wannan: 'Daga zuriyar gidan Dauda ba za a taɓa rasa mutum da zaya zauna a kursiyin gidan Isra'ila ba, 18 ko kuwa a rasa mutum daga Lebiyawa firistoci da zaya tsaya a gabana ya ɗaga baye-baye na ƙonawa ba, ya ƙona baye-bayen abinci ba, ya kuma aiwatar da baye-baye na hatsi a dukkan lokaci."' 19 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa, 20 Yahweh ya faɗi wannan: 'Idan zaku iya karya alƙawarina da rana da dare yadda ba za a sake yin rana ko dare ba a lokuttansu, 21 to zaku iya karya alƙawarina da Dauda bawana, yadda ba za a sake samun ɗan da zai zauna a kursiyinsa ba, da kuma alƙawarina da Lebiyawa Firistoci bayina. 22 Kamar yadda baza a iya ƙirga rundunar sama ba, ko kuma a iya gwada yashin da ke bakin teku, hakanan zan kawo ƙaruwa ga zuriyar Dauda bawana da kuma Lebiyawa da ke bauta a gabana."' 23 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa, 24 "Ba ku yi la'akari da abin da mutanen nan suka furta ba da suka ce, 'Iyalai biyu da Yahweh ya zaɓa, yanzu ya watsar da su'? Ta wannan hanya sun wulaƙanta mutanena, suna cewa ba al'umma ba ce kuma a gaban mu. 25 Ni, Yahweh, Na faɗi wannan, 'Idan da ban kafa alƙawarin rana da dare ba, ban kuma kafa dokokin sama da duniya ba, 26 to shi ne zan watsar da zuriyar Yakubu da Dauda bawana, har da ba zan kawo wani daga gare su ba da za ya yi mulki bisa zuriyar Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ba. Gama zan maido da kaddarorinsu in nuna masu jinƙai."'

Sura 34

1 Maganar da ta zo wurin Irmiya daga Yahweh, lokacin da NebuKadnezza sarkin Babila da dukkan rundunarsa, tare da dukkan sarakunan duniya, su harabobin da ke a ƙarkashin ikonsa, kuma dukkan mutanensu suna zuwa yaƙi gãba da Yerusalem da dukkan biranenta, cewa: 2 'Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Jeka ka yi magana da Zedekiya sarkin Yahuda ka kuma ce masa, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da miƙa wannan birni cikin hannun sarkin Babila. Zai ƙone shi. 3 Ba zaka tsira daga hannunsa ba, gama lallai za a kama ka a miƙa ka a cikin hannunsa. Idanunka za su dubi idanun sarkin Babila; zai yi magana da kai fuska da fuska yayin da kake tafiya zuwa Babila.' 4 Saurari maganar Yahweh, Zedekiya sarkin Yahuda! Yahweh ya faɗi wannan game da kai, 'ba za ka mutu ta hanyar takobi ba. 5 Za ka mutu cikin salama. Kamar yadda aka yi wa kakanninka jana'izar ƙonawa, sarakuna magabatan ka, haka za su ƙone jikinka. Za su ce, "kaito, shugaba!" Za su yi maka makoki. Yanzu dai na faɗi_ wannan furcin Yahweh ne." 6 Sai Irmiya annabi ya furta wa Zedekiya sarkin Yahuda dukkan waɗannan maganganu a Yerusalem. 7 Rundunar sarkin Babila suka yi yaƙi da Yerusalem da dukkan sauran biranen Yahuda: Lakish da Azeka. Waɗannan biranen Yahuda sun kasance kamar birane masu tsaro mai ƙarfi. 8 Maganar da ta zo ga Irmiya daga wurin Yahweh bayan da Zedekiya sarki ya yi alƙawari da dukkan mutanen Yerusalem, domin ya furta 'yanci gare su da 9 cewa bari kowane ya 'yantar da bawansa Bayahude, namiji da ta mace, wato mutum na iya ɗaukan bawa Ba-yahude, wanda ya ke ɗan uwansa. 10 Sai dukkan shugabanni da mutanen suka ɗauki alƙawari kowannensu da cewa su 'yantar bayinsu maza da mata domin kada su sake zama bayi. Suka yi biyayya su ka 'yantar su. 11 Amma bayan haka sai suka canza zuciyarsu. Suka dawo da bayin da suka 'yantar. Suka tilasta masu su sake zama bayi. 12 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa, 13 "Yahweh, Allah na Isra'ila, yana cewa, 'Ni da kaina na yi alƙawari da ubanninku a ranar da na fito da su daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. A wannan lokaci ne na ce, 14 A duk ƙarshen kowacce shekara bakwai, kowanne mutum dole ya 'yantar da ɗan'uwansa, BaIbrane wanda ya sayar da kansa gare ka ya kuma yi maka bauta na shekaru shida. Ka sake shi ya tafi cikin 'yanci." Amma ubanninku ba su saurare ni ba ko su ba da kunnuwansu gare ni. 15 Yanzu ku da kanku kuka tuba ku ka fara ayyukan da ke dai-dai a gabana. Ku ka furta yanci, kowanne mutum ga maƙwabcinsa, kuma ku ka yi alƙawari a gabana a wannan gida da ake kiransa da sunana. 16 Amma kuka juya ku ka ƙazamtar da sunana; kuka sa kowanne mutum ya dawo da bayinsa maza da mata, waɗanda kuka 'yantar domin su tafi inda ransu ke so. Ku ka tilasta masu su sake zama bayinku.' 17 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, 'Ku da kanku ba ku saurare ni ba. Dama kun furta 'yanci, kowannen ku, zuwa ga 'yan'uwanku da dangi Isra'ilawa. Don haka duba! Ina dab da furta 'yanci gare ku--- wannan furcin Yahweh ne- 'yanci ga takobi, ga annoba, da yunwa, gama zan maishe ku abin tsoro a fuskar kowacce masarauta a duniya. 18 Sa'an nan zan hori mutanen da suka karya alƙawarina, waɗanda suka ƙi su kiyaye maganganun wannan alƙawari wanda suka ɗauka a gabana a lokacin da suka yanka bajimi kashi biyu suka kuma ratsa tsakanin kason, 19 daga nan sai shugabannin Yahuda da na Yerusalem, da bãbãnni da kuma firistoci, da kuma dukkan mutanen ƙasar suka ratsa tsakanin bajimin. 20 Zan ba da su cikin hannun maƙiyansu da kuma cikin hannun waɗanda suke neman rayukansu. Jikkunansu zasu zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namomin jeji a duniya. 21 Haka zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da shugabanninsa cikin hannun makiyansu da kuma cikin hannun waɗanda suke neman ransu, da kuma cikin hannun rundunar sarkin Babila da ya tashi tsaye gãba da ku. 22 Duba, ina dab da bãda ummarni--- wannan furcin Yahweh ne-- kuma zan dawo da su zuwa ga wannan birni su kuma yaƙe shi su kuma karɓe shi, su kuma ƙona shi. Gama zan juyar da birnin Yahuda zuwa yasassun kufai inda ba za a sami mazauna cikinsa ba."

Sura 35

1 Maganar da ta zo wurin Irmiya daga wurin Yahweh a kwanakin Yehoiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, cewa, 2 "Jeka wurin iyalin Rekabawa ka yi magana da su. Sai ka kawo su zuwa gidana, cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke can, sai ka ba su inabi su sha." 3 Sai na ɗauki Ya'azaniya ɗan Irmiya ɗan Habazziniya tare da 'yan'uwansa, dukkan 'ya'yansa, da dukkan iyalin Rekabawa. 4 Sai na kawo su zuwa gidan Yahweh, zuwa cikin ɗakunan 'ya'yan Hanan ɗan Igdaliya, mutumin Allah. Waɗannan ɗakunansu na kurkusa da ɗakunan shugabanni, wanda ke sama da ɗakin Ma'aseiya ɗan Shallum, mai tsaron ƙofa. 5 Sai na ajiye kwanuka da kofuna cike da inabi a gaban Rekabawa na ce masu, "Ku sha inabi." 6 Amma suka ce, "ba za mu sha inabi ba, gama kakanmu, Yonadab ɗan Rekab, ya umurcemu, 'Kada ku sha kowanne inabi, ko ku ko zuriyarku, har abada. 7 Kuma, kada ku gina gidaje, ko ku shuka iri, ko ku shuka gonakin inabi; wannan ba na ku ba ne. Gama dole ku zauna cikin bukkoki dukkan kwanakinku, domin ku rayu da kwanaki masu yawa a cikin ƙasar da kuke zaman baƙunci.' 8 Mun yi biyayya da muryar Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, cikin dukkan abin da ya umurce mu, da kada mu sha inabi a duk kwanakinmu, mu, da matayenmu, da 'ya'yanmu, da kuma 'ya'ya matanmu. 9 Ba zamu taɓa gina gidaje mu zauna ciki ba, ko mu yi gonar inabi, ko fili, ko mu ajiye iri wurinmu. 10 Mun daɗe da zama a cikin bukkoki kuma mun yi biyayya mun kuma aiwatar da dukkan abin da Yonadab kakanmu ya umurce mu. 11 Amma da Nebukadnezza sarkin Babila ya kawo farmaki ga ƙasar, muka ce, 'Zo, dole ne mu je Yerusalem domin mu tsira daga rundunar Kaldiyawa da Aremiyawa.' Shi ya sa mu ke zama a Yerusalem." 12 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa, 13 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Ka je ka ce da jama'ar Yahuda da mazauna Yerusalem, "Ba za ku karɓi gyara ku kuma saurari maganata ba?--- wannan shi ne furcin Yahweh. 14 Maganganun Yonadab ɗan Rekab da ya yi wa 'ya'yansa a matsayin umurni, kada su sha kowanne inabi, an yi la'akari da haka har zuwa yau. Sun yi biyayya da umurnin kakansu. Amma a nawa, Ni da kai na ina ta naciya wurin shaida maku, amma ba ku saurare ni ba. 15 Na aika zuwa gare ku dukkan bayina, su annabawa. Na yi naciya da aiken su su ce, 'Bari kowanne mutum ya juyo ga barin muguwar hanyarsa ya kuma aikata ayyuka na gari; kada wani ya sake yin tafiya bisa ga tafarkin wasu alloli ko ya kuma yi masu sujada. A maimakon haka, ku dawo zuwa ga ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.' Duk da haka ku ka ƙi ku saurare ni ko ku bada hankalinku gare ni. 16 Domin zuriyar Yonadab ɗan Rekab sun kula da umurnin kakansu da ya ba su, amma waɗannan jama'a suka ƙi su saurare ni." 17 Sai Yahweh, Allah mai runduna da kuma Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Duba, Ina kawo masifa bisa Yahuda da kuma bisa kowanne mai zama cikin Yerusalem, dukkan masifar da na furta game da su domin na yi magana da su, amma ba su saurara ba; Na yi kira gare su, amma ba su amsa ba."' 18 Irmiya ya cewa iyalin Rekabawa, "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, na faɗin haka: Kun saurari umurnan Yonadab kakanku kuka kuma yi biyayya da su dukka- kun yi biyayya da dukkan abin da ya dokace ku ku yi- 19 sai Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, 'A kullum za a sami wani daga zuriyar Yonadab ɗan Rekab da zai bauta mani."'

Sura 36

1 Sai ya kasance a cikin shekara ta huɗu ta Yehoyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, da wannan maganar ta zo ga Irmiya daga Yahweh, ya kuma ce, 2 "Ka ɗaukar wa kanka naɗaɗɗen littafi ka rubuta dukkan maganar da na faɗa maka game da Is'raila da Yahuda, da kowacce al'umma. Ka yi haka da duk abin da na faɗa tun daga zamanin Yosiya har zuwa yau. 3 Watakila jama'ar Yahuda za su saurara da dukkan masifar da na yi niyyar kawo wa bisan su. Watakila kowanne zai juyo daga barin muguwar hanyarsa, da haka zan gafarta kurakuransu da zunubansu." 4 Sai Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, sai kuma Baruk ya yi rubutu cikin naɗadɗen littafi, sa'ada da Irmiya ya ke magana, dukkan maganganun Yahweh da aka faɗa masa. 5 Bayan wannan Irmiya ya bada umurni ga Baruk. Ya ce, "Ina cikin kurkuku kuma ba zan iya zuwa gidan Yahweh ba. 6 Saboda haka sai ka tafi ka karanta daga cikin naɗaɗɗen littafin da ka rubuta daga maganar da na faɗa. A ranar azumi, dole ne ka karanta maganganun Yahweh jama'a suna sauraro cikin gidansa, haka kuma a cikin kunnuwan dukkan Yahuda waɗanda suka fito daga birane. Furta waɗannan maganganu a gare su. 7 Wataƙila roƙonsu na jinkai kai zuwa ga Yahweh. Wataƙila kowannen su zai juyo daga muguwar hanyarsa, da yake fushi da hasalar da Yahweh ya furta game waɗannan mutane masu zafi ne." 8 Sai Baruk ɗan Neriya ya aiwatar da dukkan abin da Irmiya annabi ya doka ce shi ya yi. Ya karanta maganganun Yahweh da babbar murya a cikin gidan Yahweh. 9 Sai ya zama kuma a cikin shekara ta biyar ga watan tara na Yehoiyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, sai dukkan jama'ar Yerusalem da kuma mutanen da suka zo Yerusalem daga biranen Yahuda suka yi shelar azumi don girmama Yahweh. 10 Sai Baruk ya karanta maganganun Irmiya da ƙarfi a cikin gidan Yahweh, daga cikin ɗakin Gemariya ɗan Shafan marubuci, a cikin harabar da ke bisa, dab da mashigin ƙofa ta gidan Yahweh. Ya yi wannan a kunnuwan dukkan jama'a. 11 Yanzu Mikaiya ɗan Gemaraya ɗan Shafan ya ji dukkan maganganun Yahweh daga cikin naɗaɗɗen littafi. 12 Ya gangara zuwa gidan sarki, zuwa ga ɗakin sakatare. Duba, dukkan shugabanni na nan zaune: Elishama sakatare, da Delaya ɗan Shemaya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemaraya ɗan Shafan, da kuma Zedekiya ɗan Hananiya, da dukkan shugabanni. 13 Sai Mikaiya ya kawo masu rahoton dukkan maganganun da ya ji Baruk ya karanta da ƙarfi jama'a suna saurare. 14 Sai dukkan shugabanni suka aiki Yehudi ɗan Netanaya ɗan Shelemaya ɗan Kushi, zuwa ga Baruk. Yehudi ya ce wa Baruk, "Ɗauki naɗaɗɗen littafin cikin hannunka, naɗaɗɗen littafin da ka karanta ga sauraron jama'a, ka kuma zo." Sai Baruk ɗan Neraya ya ɗauki naɗaɗɗen littafin cikin hannunsa ya tafi wurin shugabannin. 15 Sai suka ce masa, "Zauna ka kuma karanta muna jinka." Sai Baruk ya karanta naɗaɗɗen littafin. 16 Sai ya zama sa'ad da suka ji dukkan waɗannan maganganu, kowanne mutum ya juya yana kallon na kusa da shi cikin tsoro suka ce wa Baruk, "Dole ne mu kai rohoton dukkan waɗannan maganganu ga sarki." 17 Sai su ka tambayi Baruk, "Gaya mana, ta yaya ka rubuta dukkan waɗannan maganganu daga bakin Irmiya? 18 Baruk ya ce masu, "Ya furta dukkan maganganun gare ni, ni kuma na rubuta su da tawada cikin wannan naɗaɗɗen littafi." 19 Sai shugabannin su ka cewa Baruk, "Ka tafi, ka ɓoye kanka, da Irmiya, kuma. Kada ka bar wani ya san inda ku ke." 20 Sai su ka ajiye naɗaɗɗen littafin a cikin ɗakin Elishama sakatare, kuma suka tafi wurin sarki cikin haraba suka kuma faɗawa sarki komai. 21 Sa'annan sarki ya aiki Yehudi ya kawo naɗaɗɗen littafin. Yehudi ya ɗauko shi daga ɗakin Elishama sakatare. Sa'annan ya karanta wa sarki da dukkan shugabanni da suke tsayawa kusa da shi. 22 Yanzu sarki na zama a gida lokacin hunturu a cikin wata na tara, kuma wutar kasko na ci a gaban shi. 23 Ya zama kuwa da Yehudi ya karanta shafi uku ko huɗu, sarkin za ya datse su da wuƙa ya jefa cikin wuta cikin kaskon wuta har dukkan naɗaɗɗen littafin ya ƙare. 24 Amma babu wani ko sarki ko wani daga cikin bayinsa da ya ji dukkan waɗannan maganganun ya kuma tsorata, basu kuma yayyage tufafinsu ba. 25 Elnatan, da Delaya, da kuma Gemariya sun riga sun roƙi sarki da kada ya ƙona naɗaɗɗen littafin, amma ya ƙi ya sauraren su. 26 Sai sarkin ya umarci Yeramil, na dangi, da Seraya ɗan Aziriyel, da kuma Shelemiya ɗan Abdil domin su damƙe Baruk sakatare da kuma Irmiya annabi, amma Yahweh ya riga ya ɓoye su. 27 Sai maganar Yahweh ta zo wa Irmiya bayan sarki ya ƙona naɗaɗɗen littafin da kuma maganganun da Baruk ya rubuta daga furcin bakin Irmiya, cewa, 28 "Ka koma, ka ɗaukar wa kanka wani naɗaɗɗen littafi, ka kuma rubuta cikin sa dukkan maganganun da suke a cikin naɗaɗɗen littafin na farko, wanda Yehoyakim sarkin Yahuda ya ƙona. 29 Sa'annan dole ka faɗi wannan ga Yehoyakim sarkin Yahuda: 'Ka ƙona wannan naɗaɗɗen littafi, kana cewa, 'Don me ka yi rubutu a cikinsa, 'Sarkin Babila lallai zai zo ya hallakar da wannan ƙasar, gama za ya hallakar da mutum da kuma dabba a cikinta'?""' 30 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan game da kai, Yehoiyakim sarkin Yahuda: "Babu zuriyarka da za ta taɓa zama a kan kursiyin Dauda. Game da kai, gawarka za a jefa ta a waje cikin zafin rana da kuma cikin sanyin dare. 31 Gama zan yi maka horo, da zuriyarka, da kuma bayinka domin kurakuranku duka. Zan kawo a bisanka, da bisan dukkan mazamnan Yerusalem, da kuma a bisa kowanne mutum cikin Yahuda dukkan masifun da na tsoratar daku da su, amma baku ba da hankali ga wannan ba." 32 Sai Irmiya ya ɗauko wani naɗaɗɗen littafi ya kuma miƙa shi ga Baruk ɗan Neriya marubuci. Baruk ya rubuta ciki daga bakin Irmiya dukkan maganganun da suka kasance a cikin naɗaɗɗen littafin da Yehoyakim sarkin Yahuda ya ƙona. Bugu da ƙari kuma, aka ƙara maganganu da yawa makamantan waɗannan cikin wannan naɗaɗɗen littafin.

Sura 37

1 Yanzu Zedekiya ɗan Yosiya ya yi sarauta a madadin Yehoiyacin ɗan Yehoyakim. Nebukadnezza sarkin Babila ya naɗa Zedekiya sarki bisa ƙasar Yahuda. 2 Amma Zedekiya, da bayinsa, da mutanen ƙasa ba su saurari maganganun Yahweh da ya furta ta hannun Irmiya annabi ba. 3 Sai sarki Zedekiya, da Yehukal ɗan Shelemiya, da kuma Zefanaya ɗan Maseya firist ya aika saƙo zuwa ga Irmiya annabi. Su ka ce, "Yi addu'a a madadinmu ga Yahweh Allahnmu." 4 Yanzu Irmiya na shigowa da fitowa a cikin mutanen, gama ba a rigaya an saka shi cikin kurkuku ba. 5 Rundunar Fir'auna suka fito daga Masar, sai kuma Kaldiyawa waɗanda suke kafa wa Yerusalem sansani suka ji labari game da su sai kuma su ka bar Yerusalem. 6 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya annabi, cewa, 7 "Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗi wannan: Ga abin da za ka faɗi wa sarkin Yahuda, domin ya aike ka neman shawara wurina, 'Duba, rundunar Fir'auna, wacce ta kawo maku taimako, tana dab da komawa Masar, ƙasarta. 8 Su Kaldiyawa za su dawo. Za su yaƙi wannan birni, su karɓe shi, su kuma ƙona shi.' 9 Yahweh ya faɗi wannan: Kada ku ruɗi kanku kuna cewa, 'Hakika Kaldiyawan na tafiya suna barin mu,' domin ba za su tafi ba. 10 Ko da ace kun ci dukkan rundunar Kaldiyawan da yaƙi da ke yaƙi da ku da har ace raunannun mutane ne aka bari cikin runfunansu, za su tashi sama su kuma ƙone wannan birnin." 11 Haka ya zama lokacin da rundunan Kaldiyawa su ka bar Yerusalem lokacin da rundunar Fir'auna ke gabatowa, 12 sai Irmiya ya fito Yerusalem domin ya tafi kasar Beyamin. Ya bukaci ya mallaki wani ɗan fili a nan a tsakanin mutanensa. 13 Sa'ad da ya ke a bakin ‌Ƙ‌ofar Benyamin, wani shugaban matsara na wurin. Sunansa Iriya ɗan Hananiya. Ya riƙe annanbi Irmiya gama kuma ya ce, "Kana zanzarewa zuwa ga Kaldiyawa." 14 Amma Irmiya ya ce, "Wannan ba gaskiya ba ne. Ba zanzarewa na ke yi ba zuwa ga Kaldiyawa." Amma Iriya ya ƙi ya saurare shi. Ya ɗauki Irmiya ya kawo shi wurin shugabanni. 15 Shugabannin suka ji haushin Irmiya. Suka yi ma sa duka suka sa shi cikin kurkuku, wanda ya ke cikin gidan Yonatan marubuci, gama sun maishe shi kurkuku. 16 Sai aka sa ka Irmiya cikin kurkuku na ƙarƙashin ƙasa, inda ya zauna ranaku da yawa. 17 Sai sarki Zedekiya ya aika da wani wanda ya kawo shi zuwa ga fada. A gidansa, sarkin ya tambaye shi a asirce, "Akwai wata magana daga Yahweh?" Irmiya ya amsa, "Akwai magana: Za a miƙa ka cikin hannun sarkin Babila." 18 Sai Irmiya ya ce wa sarki Zedekiya, "Ta yaya na yi maka zunubi, ko bayinka, ko waɗannan mutane da har ka saka ni cikin kurkuku? 19 Ina annabawanka, waɗanda suka yi maka anabci kuma suka ce sarkin Babila ba zai zo gãba da kai ko gãba da wannan birnin ba? 20 Amma ka saurara yanzu, shugabana sarki! Bari roƙona shi zo gare ka. Kada ka maida ni zuwa ga gidan Yonatan marubuci, don kada in mutu a can." 21 Sai sarki Zedekiya ya ba da umarni. Bayinsa suka tsare Irmiya cikin harabar matsara. Aka ba shi curin gurasa kowace rana daga layin matoya, har sai da dukkan gurasar ta ƙare cikin birnin. Haka Irmiya ya zauna cikin harabar matsaran.

Sura 38

1 Shefatiya ɗan Matan, da Gedaliya ɗan Fashhur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da kuma Fashhur ɗan Malkiyah su ka ji maganganun da Irmiya ya ke furtawa ga dukkan mutanen. Yana cewa, 2 "Yahweh ya faɗi haka: Duk mai zama cikin wannan birni za a kashe shi da takobi, da yunwa, da kuma annoba. Amma kowanne da ya fita zuwa ga Kaldiyawa za shi rayu. Zai tsira da ransa, shi rayu. 3 Yahweh ya faɗi wannan: Wannan birni za a ba da shi ga hannun rundunar sarkin Babila, kuma za ya karɓe shi." 4 Sai shugabannin suka ce wa sarkin, "Bari wannan mutum shi mutu, gama ta wannan hanya yana raunanar da hannuwan mazaje mayaƙa waɗanda suka rage a wannan birni, da kuma hannun dukkan mutane. Ya na furta waɗannan maganganu, gama wannan mutum bai kula da lafiyar waɗannan mutane ba, sai dai bala'i." 5 Sai sarki Zedekiya ya ce, "Duba, yana cikin hannunku da shi ke babu sarkin da ya isa shi yi tsayayya da ku." 6 Sai su ka ɗauki Irmiya su ka jefa shi cikin ramin Malkiyah, ɗan sarki. Ramin na cikin harabar masu tsaro. Suka zurara Irmiya ƙasa da igiyoyi. Babu ruwa cikin ramin, amma taɓo ne, sai kuma ya nutse ƙasa cikin taɓon. 7 Yanzu Ebed Melek Ba-Kushi yana cikin ubanni na gidan sarki. Ya ji cewa an jefa Irmiya cikin rami. Yanzu sarkin yana zama a Kofar Benyamin. 8 Sai Ebed Melek ya tafi daga gidan sarki ya yi magana da sarki. Ya ce, 9 "Shugabana sarki, waɗannan mutane sun aikata mugunta ta yadda suka yi da Irmiya annabi. Sun jefar da shi cikin rami domin ya mutu cikinsa da yunwa, tun da babu wani abincin da ya rage cikin birnin." 10 Sai sarkin ya bada umurni ga Ebed Melek Ba-Kushe. Ya ce, "Ka ɗauki shugabancin mutane talatin daga nan ka kuma ciro annabi Irmiya daga ramin kamin ya mutu." 11 Sai Ebed Melek ya ɗauki shugaban waɗannan mutanen ya tafi gidan sarki, zuwa ga ɗakin ajiyar kaya na ƙarƙashin gidan. Daga nan ne ya ɗauko tsummokara da kuma koɗaɗɗun kaya sai kuma ya zurara su da igiyoyi ga Irmiya cikin ramin. 12 Ebed Melek mutumin Kush ya cewa Irmiya, "Sanya tsummokaran da koɗaɗɗun kayan a ƙarƙashin hannunka da kuma bisa igiyoyin." Irmiya kuwa ya yi haka. 13 Sai suka jawo Irmiya da igiyoyin. Da haka suka fito da shi daga cikin ramin. Irmiya kuma ya zauna cikin harabar masu tsaro. 14 Sai sarki Zedekiya ya aika magana ya kuma kawo Irmiya annabi wurin sa, zuwa cikin mashigi na uku cikin gidan Yahweh. Sarkin ya cewa Irmiya, "Ina so in tambaye ka wani abu. kada ka hana mani amsar." 15 Irmiya ya ce da Zedekiya, "Idan na amsa maka, lallai ba za ka kashe ni ba? Amma idan na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba." 16 Amma sarki Zedekiya ya rantse wa Irmiya a asirce ya kuma ce, "Na rantse ga Yahweh mai rai, wanda ya yi mu, ba zan kashe ka ba ko in miƙa ka cikin hannuwan waɗannan mutanen nan da suke neman ranka ba." 17 Sai Irmiya annabi ya cewa sarki Zedekiya, "Yahweh, Allah mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Idan ka fita zuwa ga shugabannin Babila za ka rayu kuma ba za a kone wannan birni ba. Kai da iyalin ka za ku rayu. 18 Amma idan ka ƙi fita zuwa ga shugabannin sarkin Babila, to za a miƙa wannan birnin cikin hannun Kaldiyawa. Za su kona shi, kai kuma ba za ka tsira daga hannun su ba." 19 Sarki Zedekiya ya cewa Irmiya, "Amma ina jin tsoron mutanen Yahuda waɗanda suka ƙaurace zuwa ga sansanin Kaldiyawa domin ana iya miƙa ni cikin hannuwansu, domin su wulaƙanta ni sosai." 20 Irmiya ya ce, "Ba zasu miƙa ka cikin hannuwansu ba. Kai dai ka yi biyayya da saƙon Yahweh da nake faɗa maka, domin komai ya zamar maka lafiya lau, domin kuma ka rayu. 21 Amma idan ka ƙi ka fita, wannan shi ne abin da Yahweh ya nuna mani. 22 Duba! Dukkan matayen da aka rage a gidanka, sarkin Yahuda, za a fito da su zuwa ga shugabannin sarkin Babila. Waɗannan matayen za su ce maka, 'Abokananka sun ruɗe ka; sun rusar da kai. ‌Ƙafafunka yanzu sun nutse cikin taɓo, kuma abokanka za su gudu.' 23 Gama dukkan matayen ko da 'ya'yanka ma za a fito da su zuwa ga Kaldiyawa, kai kuma da kanka ba za ka tsira daga hannunsu ba. Za a kama ka ta hannun sarkin Babila, kuma za a ƙona wannan birnin." 24 Sai Zedekiya ya cewa Irmiya, "Kada ka sanar da kowa game da wannan maganganu, don kada ka mutu. 25 Idan shugabannin suka ji labari na yi magana da kai, idan kuma suka zo su ka ce maka, "Ka faɗi mana abin da ka faɗi wa sarki kuma kada ka ɓoye mana, ko mu kashe ka, 26 sa'annan dole za ka amsa masu da cewa, na yi roƙo ne da zuciya ɗaya ga sarki da kada ya komar da ni gidan Yonatan don kada in mutu a can." 27 Sai dukkan shugabannin suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi abin da ya gaya wa sarki, shi kuma sai ya amsa masu yadda sarki ya umarce shi da ya faɗi. Sai suka daina magana da shi, domin ba su ji tattaunawar da aka yi tsakanin Irmiya da sarkin ba. 28 Sai Irmiya ya zauna a cikin harabar masu tsaro har zuwa ranar da aka karɓe Yerusalem.

Sura 39

1 A shekara ta tara na watan goma na Zedekiya sarkin Yahuda, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo da dukkan rundunarsa gãba da Yerusalem ya kuma kafa mata sansani. 2 A shekara ta sha ɗaya da kuma wata na huɗu na Zedekiya, a rana ta tara ga wata, aka rusar da birnin. 3 Sai dukkan shugabannin sarkin Babila suka zo suka zauna a ƙofa ta tsakiya: Nagal Shareza, da Samgar Samgal Nebo, da kuma Sarsekim, shugaba mai muhimmanci. Nagal Shareza shugaba ne babba kuma dukkan sauran sun zama shugabannin sarkin Babila. 4 Sai ya zamana da Zedekiya sarkin Yahuda, da dukkan mayaƙan sa suka gan su, suka gudu. Suka fita da dare daga birnin ta hanyar gonar gidan sarki, ta cikin ƙofa ta tsakanin ganuwa biyun. Sarkin ya fita ta bangon hanyar Araba. 5 Amma rundunar Kaldiyawa suka runtume su suka kuma cimma Zedekiya a cikin filin Kogin Yodan kwari kusa da Yeriko. Sai suka cafko shi suka kawo shi wurin Nebukadnezza, sarkin Babila, a Ribla cikin ƙasar Hamat, inda Nebukadnezza ya yanke masa hukunci. 6 Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zedekiya a fuskarsa a Ribla. Ya kuma kashe dukkan muhimman mutanen Yahuda. 7 Sai ya cire idanuwan Zedekiya ya kuma ɗaure shi da sarƙoƙin jan karfe domin ya tafi da shi Babila. 8 Sai Kaldiyawan suka ƙone gidan sarki da gidajen mutane. Suka kuma rushe ganuwar Yerusalem. 9 Nebuzaradan, hafsan masu tsaron sarki, ya kwashe sauran mutanen waɗanda aka rage cikin birnin zuwa bauta. Wannan ya haɗa har da waɗanda suka yi ƙaura zuwa ga Kaldiyawa da kuma sauran mutanen waɗanda aka rage cikin birnin. 10 Amma Nebuzaradan babban hafsan masu tsaron sarki ya bar sauran mutanen waɗanda suke fakirai waɗanda basu da wani abu na kansu su zauna a cikin Yahuda. Ya kuma ba su gonakin inabi da filaye a wannan rana. 11 Nebukadnezza sarkin Babila ya ba da umarni game da Irmiya ga Nebuzaradan hafsan masu tsaron sarki. Ya riga ya ce, 12 "Ka ɗauke shi ka kula da shi. Kada ka ji ma sa rauni. Yi ma sa duk abin da ya ce ma ka. 13 Sai Nebuzaradan hafsan masu tsaron sarki, Nebushazban babban bãbãn, Nagal Shareza babban shugaba, da dukkan muhimman shugabannin sarkin Babila su ka aiki mutane waje. 14 Mutanensu su ka ɗauki Irmiya daga harabar masu tsaro su ka miƙa shi cikin hannun Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan, ya kai shi gida, sai Irmiya ya zauna a tsakanin mutanen. 15 Yanzu dai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya tun ya na a tsare a cikin harabar masu tsaro, cewa, 16 "Yi magana da Ebed Melek mutumin Kush ka ce, "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Duba, ina dab da cika maganganuna da na furta game da wannan birni bala'i kuma ba alheri ba. Gama za su faru dukka a idanunka a wannan rana. 17 Amma zan cece ka a wannan rana- wannan ne furcin Yahweh- kuma ba za a bashe ka cikin hannun mutanen da ka ke jin tsoronsu ba. 18 Gama babu shakka zan tsirar da kai. Ba za ka faɗi ga takobi ba. Za ka tsira da ranka, tun da ka yarda da ni- wannan shi ne furcin Yahweh."

Sura 40

1 Maganar ta zo wurin Irmiya daga wurin Yahweh bayan da Nebuzaradan babban hafsan masu tsaron sarki ya sa ke shi a Rama. Ya sami Irmiya a ɗaure da sarƙoƙi a tsakiyar dukkan 'yan sarƙar Yerusalem da Yahuda waɗanda aka kwashe zuwa ga ƙasar bauta a Babila. 2 Shugaban matsara ya ɗauki Irmiya ya kuma ce ma sa, "Yahweh Allahnka ya umarta wannan masifar domin wannan wurin. 3 Don haka Yahweh ya kawo hakan. Ya aikata kamar yadda ya umarta, tun da ku mutanen nan kun yi ma sa zunubi kuma ba ku yi biyayya da muryar sa ba. Shi ya sa wannan abu ya faru da ku mutanen nan. 4 Amma yanzu duba! Na sa ke ka yau daga sarƙokin da ke hannuwanka. Idan ka ga ya dace a idanunka ka bi ni zuwa Babila, sai ka bi ni, ni kuwa zan kula da kai. Amma idan ba ya dace a idanunka ba da ka biyo ni zuwa Babila, to kada ka yi haka. Duba dukkan ƙasar da ke a gabanka. Ka tafi duk inda ya ke da kyau da kuma dai - dai a idanunka ka tafi." 5 Da Irmiya ba ya amsa ba, Nebuzaradan ya ce, "Tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan, wanda sarkin Babila ya ɗora wa haƙin kula da biranen Yahuda. Ka zauna da shi a tare da sauran mutanen ko ka tafi ko inda da ya yi ma ka kyau a idanunka ka tafi." Sai hafsan masu tsaron sarki ya bashi abinci da 'yar kyauta, daga nan ya sallame shi. 6 Sai Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa. Ya zauna tare da shi a tsakiyar mutanen da aka bari cikin kasar. 7 Yanzu wa su hafsoshin Yahuda waɗanda har yanzu su na a cikin harabar-- su da mutanensu-- su ka ji cewa sarkin Babila ya ɗora Gedaliya ɗan Ahikam, gwamna bisa ƙasar. Sun kuma sa ke ji cewa ya sa shi a matsayin mai kula da mazajen, mataye, da yara waɗanda su ne fakiran mutane a cikin ƙasar, waɗanda ba a kwashe ga hijira zuwa ƙasar Babila ba. 8 Sai su ka tafi wurin Gedaliya a Mizfa. Waɗannan mutane su ne Ishmayel ɗan Netaniya; Yohanan da Yonatan, 'ya'yan Kariya; da Seraya ɗan Tanhumet; su 'ya'yan Ifai mutumin Netofatiyawa; da Ya'azaniya ɗan Ma'akatiyawa-- su da mutanensu. 9 Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan ya ɗauki alƙawari da su da 'ya'yansu ya ce masu, "Ka da ku ji tsoro da za ku bauta wa shugabannin Kaldiyawa. Ku zauna a cikin ƙasar ku kuma bauta wa sarkin Babila, da haka komai zai yi maku dai - dai. 10 Duba, ina zama a Mizfa domin in sami ganin Kaldiyawa da su ka zo gare mu. Sai ku girbe inabi, da kayan itatuwa na damuna, da kuma mai ku adana su a cikin dururruka. Ku zauna a biranen da ku ka mallaka." 11 Sai dukkan mutanen Yahuda da ke a Mowab, a tsakanin mutanen Ammon, da kuma cikin Idom, da kuma a kowacce ƙasa su ka ji cewa sarkin Babila ya bar ragowar Yahuda su zauna, har ya aza Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan bisan su. 12 Saboda haka dukkan mutanen Yahuda su ka dawo daga dukkan wuraren da aka tarwatsa su. Su ka dawo zuwa ga ƙasar Yahuda, zuwa ga Gedaliya a Mizfa. Su ka girbe inabi da amfanin itatuwa na damina mai yawan gaske. 13 Yohanan ɗan Kareya da dukkan shugabannin rundunar da su ke baje cikin ƙasar su ka zo wurin Gedaliya a Mizfa. 14 Su ka ce ma sa, "Ko ka sa ni da cewa Balis sarkin mutanen Ammon ya aiko Ishmel ɗan Netaniya da ya kashe ka?" Amma Gedaliya ɗan Ahikim bai yarda da su ba. 15 Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi magana a asirce da Gedaliya a Mizfa kuma ya ce, "Ka bar ni in tafi in kashe Ismayel ɗan Netaniya. Babu wanda zai sani. Don me za shi kashe ka? Don me za a bar Yahuda da aka tara maka su wartwatsu kuma ragowar Yahuda su hallaka? 16 Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, "Kada ka aikata wannan abu, gama ka na faɗin ƙarya ne bisa Ismayel."

Sura 41

1 Amma ya kasance a wata na bakwai Ismayel ɗan Netaniya ɗan Elishama, daga gidan sarauta, da waɗansu shugabanni na sarki, su ka zo su goma tare da shi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, Mizfa. Su ka ci abinci tare a can Mizfa. 2 Amma Ismayel ɗan Netaniya da mutanen nan goma da ke tare da shi su ka tashi suka farmaki Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan da takobi. Ismayel ya kashe Gedaliya, wanda sarkin Babila ya sa ya mulki ƙasar. 3 Daga nan sai Ismayel ya kashe dukkan mutanen Yahudiya da ke goyon bayan Gedaliya a Mizfa da mayaƙan Kaldiyawan da ya samu a can. 4 To a rana ta biyu bayan kisan Gedaliya, amma ba wanda ya sani. 5 Waɗansu mutane su ka zo daga Shekem, da kuma Shilo, da Samariya su tamanin waɗanda su ka aske gemunsu, su ka kuma kece tufafinsu, su ka yayyanka jikkunansu - ɗauke da baye - baye na abinci da turaren itacen lubban a hannuwansu don su je gidan Yahweh. 6 Sai Ismayel ɗan Netaniya ya tafi daga Mizfa don ya sadu da su akan hanyarsu ta komawa, suna tafe su na kuka. A lokacin da ya gansu sai ya ce da su, "Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam!" 7 Sai ya zamana bayan sun zo birnin, sai Ismayel ɗan Netaliya ya yayyanka su ya zura su cikin rami, tare da mutanen da ke tare da shi. 8 Amma akwai mutane goma daga cikinsu da su ka ce da Ismayel," kada ka kashe mu, don muna da tanaji a filin: da alkama, da sha'ir da mai da ruwan zuma." Don haka bai kashe su tare da abokan tafiyarsu ba. 9 Rijiyar da Ismayel ya zuba gawawwakin waɗanda ya kashe ta na da girma ita ce rijiyar da sarki Asa ya haƙa don kariya daga sarkin Ba'asha na Isra'ila. sai Ismayel ɗan Netaniya ya cikata da gawawwaki. 10 Abu na gaba shi ne Ismayel ya kame dukkan mutanen da ke a Mizfa, da 'ya'yan sarki 'yan mata da duk sauran mutanen da su ka ragu a Mizfa waɗanda Nebuzzradan shugaban masu tsaro ya ba Gedaliya ɗan Ahikam. To sai Ismayel ɗan Netaniya ya kame su ya tafi ya ƙetare da suzuwa wurin mutanen Ammon. 11 Amma Yohannan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi suka ji dukkan muguntar da Ismayel ɗan Netaniya ya yi. 12 To sai su ka kwashi dukkan mutane don su yaƙi Ismayel ɗan Netaniya. su ka same shi a babban kwarin Gibeyon. 13 Sai ya zamana a lokacin da dukkan mutanen da ke tare da Ismayel su ka ga Yohanan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi, sai suka yi murna. 14 Sai dukkan mutanen da Ismayel ya kame a mizfa su ka juya suka koma ga Yohannan ɗan Kareya. 15 Amma Ismayel ɗan Netaniya ya gudu tare da mutane takwas daga Yohannan. Ya je wurin mutanen Ammon. 16 Sai Yohannan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi su ka kwashe mutanen daga Mizfa, suka kuɓutar da su daga Ismayel ɗan Netaniya. Hakan ya faru ne bayan Ismayel ya kashe Gedaliya ɗan Ahikan. Yohannan da abokan tafiyarsa su ka ɗauki ƙarfafan mazaje, da mayaƙa, da mata da yara, da bãbãnni waɗanda aka kuɓutar a Gibeyon. 17 Daga nan sai su ka je su ka ɗan tsaya a Gerut Kimham, wanda ke kusa da Betelehem. Su na tafiya don su je Masar 18 saboda Kaldiyawa. Suna tsoron su tunda yake Ismayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babila ya sa ya yi mulkin ƙasar.

Sura 42

1 Daga nan dukkan hafsoshin da Yohanan ɗan Keriya, da Yezaniya ɗan Hoshayiya, da dukkan mutanen tun daga ƙanana ya zuwa manya suka zo wurin annabi Irmiya. 2 Su ka ce da shi, "bari kukanmu ya zo gareka. 3 Kayi addu'a zuwa ga Yahweh Allahnka a madadinmu da muka ragu tun da ya ke ba mu da yawa, kamar yadda ka gani. Ka roƙi Yahweh Allahnka ya faɗa mana abin da za mu yi da kuma hanyar da za mu bi" 4 Annabi Irmiya ya ce da su, "Na ji ku. Duba, zan yi addu'a ga Yahweh Allahnku kamar yadda ku ka bukata. Kuma duk amsar da Yahweh ya bayar zan faɗa muku. Ba zan ɓoye muku komai ba." 5 Su ka cewa Irmiya, "Dama Yahweh ya zama amintaccen shaida na gaskiya a tsakaninmu, idan ba mu yi duk abin da Yahweh Allahn ka ya ce mu yi ba. 6 Ko da mai kyau ne ko kuma mara kyau, za mu yi biyayya da muryar Yahweh Allahnmu, wanda mu ke aiken ka wurinsa, don komai ya yi mana dai - dai a lokacin da muka yi biyayya da muryar Yahweh Allanmu." 7 Bayan kwana goma, maganar Yahweh ta zo wurin Irmiya. 8 Sai Irmiya ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi, da kuma dukkan mutane daga ƙanana zuwa manya. 9 Sai ya ce da su, "Wannan shi ne abin da Yahweh Allah na Isra'ila - wanda ku ka aike ni wurin sa don in kai roƙonku gare shi - ya ce, 10 Idan kun koma wannan ƙasar ku ka zauna to zan gina ku ba zan keta ku ba; Zan dasa ku ba zan tuge ku ba, don zan kawar da masifar da na aukar a kan ku. 11 Kada ku ji tsoron sarkin Babila, wanda ku ke jin tsoro. Kada ku ji tsoron sa - wannan shi ne abin da yahweh ya furta - da shi ke Ina tare da ku don in cece ku in kuma kuɓutar da ku daga hannunsa. 12 Gama zan yi maku jinkai. Zan kuma ji tausayinku, zan kuma dawo da ku ƙasarku. 13 Amma in kun ce "ba za mu zauna a wannan ƙasa ba" - in ba ku saurari muryata ba, muryar Yahweh Allanku. 14 In kun ce, "A a! Za mu je ƙasar Masar, inda ba za mu ga wani yaƙi ba, inda ba za mu ji ƙarar ƙaho ba, kuma ba zamu ji yunwa domin abinci ba, can za mu zauna." 15 Yanzu sai ku saurari muryar Yahweh, ku da ku ka rage a Yahuda. Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan, 'In dai har ku ka je Masar, don ku je ku zauna a can, 16 To takobin da ku ke jin tsoro za ta kashe ku a can ƙasar Masar. Yunwar da ku ke damuwa a kanta yanzu za ta kora ku zuwa Masar, kuma za ku mutu a can. 17 Don haka duk waɗanda su ka gudu Masar don su zauna a can za su hallaka ta wurin takobi, da yunwa, ko annoba. Kuma ba wanda zai tsira daga wannan masifar da zan aukar masu. 18 Domin Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Kuma kamar yadda fushina ya yi ƙuna a kan mazauna Yeruselem, hakanan zan saukar da matsanancin fushina a kanku in ku ka je Masar. Za ku zama abin la'ana da reni, abin la'antawa, da abin ƙasƙantarwa, kuma ba za ku ƙara ganin wannan wurin ba.'" 19 Sai Irmiya ya ce,'" Yahweh ya faɗi wannan a kanku - ku da ku ka rage a Yahuda. Kada ku je Masar! Don tabbas kun san ni sheda ne a kanku a yau. 20 Domin kun yaudari kanku sosai a lokacin da ku ka aike ni ga Yahweh Allahnku ku ka ce, ka yi addu'a ga Yahweh Allahnmu dominmu. Duk abin da Yahweh Allahnmu ya ce, ka faɗa mana, za mu yi shi.' 21 Domin yau na ba ku rahoto, amma ba ku saurari muryar Yahweh Allahnku ko kuma duk abin da ya aiko ni wurinku. 22 To yanzu sai ku san cewa tabbas zaku mutu ta wurin takobi, da yunwa, da annoba, a wurin da kuke son ku tafi ku zauna."

Sura 43

1 Sai ya zamana bayan Irmiya ya gama shaidawa mutane dukkan maganar Yahweh Allahnsu wadda Yahweh Allahnsu ya faɗi masa ya faɗa. 2 Azariya ɗan Hosheya, Yohanan ɗan Kareya, da dukkan mutane kangararru su ka ce da Irmiya, '"ƙarya ka ke faɗi. Yahweh Allanhmu bai aiko ka ka faɗi cewa kada ku je Masar ku zauna a can ba' 3 Domin Baruk ɗan Neriya ya na zuga ka ka bada mu a hannun Kaldiyawa, don kaima ka jawo mana mutuwa ka kuma mai da mu kamammu a Babila." 4 Domin haka Yohannan ɗan Kareya, da dukkan shugabannin mayaƙa da dukkan mutane su ka ƙi sauraron muryar Yahweh da ta ce su zauna a Yahuda. 5 Yohanan ɗan Kareya da shugabannin mayaƙa su ka kwashe dukkan waɗanda su ka rage a Yahuda waɗanda su ka dawo daga dukkan al'uman da aka warwatsa su su zauna a cikin ƙasar Yahuda. 6 Su ka kwashe maza da mata, da yara da 'ya'ya mata na sarki, da duk wanda Nebuzaradan, hafsan sarki da matsaran sarki, ya sa suka kasance tare da Gedeliya ɗan Ahikam ɗan Shafan. Hakannan su ka ɗauki Annabi Irmiya da Baruk ɗan Neriya. 7 Su ka tafi zuwa ƙasar Masar, a Tafenhes, saboda ba su saurari muryar Yahweh ba. 8 To sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya a Tafanhes, cewa, 9 "Ka ɗauki manyan duwatsu a hannunka, da kuma a gaban mutanen Yahuda, ka ɓoye su a kankare a gefen hanyar zuwa ƙofar gidan Fir'auna a Tafanhes." 10 Daga nan sai ka ce da su, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila ya faɗi wannan, 'Duba ina gab da aika manzannina zuwa Babila a matsayin bayina. Zan kafa mulkinsa akan waɗannan duwatsu wanda kai Irmiya ka binne. Nebukadzza zai kafa daularsa a kansu. 11 Domin zai zo ya kawo hari ga ƙasar Masar. Duk wanda aka ƙaddara ga mutuwa zai mutu. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta za a ɗauke shi zuwa bauta. Duk wanda aka ƙaddara ga takobi za a bada shi ga takobi. 12 Daga nan zan kunna wuta a haikalun allolin Masar. Nebukadnezza zai ƙone su ko kuma ya kwashe su. Zai tsarkake ƙasar Masar kamar yadda makiyaya ke tsabtace tufafinsu. Zai fita daga wurin nan da ɗaukaka. 13 Zai karye ginshiƙan nan na dutse na Heliyofolis a ƙasar Masar. Zai ƙone haikalun allolin Masar.'"

Sura 44

1 Maganar ta zo ga Irmiya game da dukkan mutanen Yahudiya da ke zaune a ƙasar Masar, waɗanda ke zaune a Migdol, da Tafenhas, da Memfis, da ƙasar Fatros. 2 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Ku da kan ku kun ga duk waɗannan masifu da na aukar a Yeruselem da dukkan biranen Yahuda. Duba, yau sun zama kangaye. Ba wanda zai zauna a cikinsu. 3 Wannan saboda miyagun abubuwan da su ka yi domin su yi mani laifi ta wurin zuwa su ƙona turare da kuma bautawa waɗansu alloli. Waɗannan alloli ne da ko su da kansu, ko ku, ko kakanninku ba su sani ba.' 4 Don haka na dinga aikawa da dukkan bayina annabawa gare su. Na aike su su ce, 'Ku dena aikata abubuwan ban ƙyamar da na ke ƙi.' ba su saurara ba. 5 Amma sun ƙi saurare. Suka ƙi maida hankali ko su juyo daga muguntarsu ta wurin ƙona turare ga wasu alloli. 6 Sai razanata da fushina su ka yi ƙuna a kan biranen Yahuda da titunan Yerusalem. Don haka suka zama kango da abin banzatarwa, kamar yadda ya ke a yau' 7 To yanzu Yahweh, Allah mai runduna Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Don me ku ke aikata babbar mugunta gãba da kanku? Don me ku ke jawowa kanku abin da zai sa a datse ku daga cikin Yahuda - mazaje da mataye, yara da jarirai? Ba za a rage ko ɗayanku ba. 8 Ta wurin aikin muguntarku kun yi ma ni laifi ta wurin ayyukan hannuwanku, ta ƙona turare ga waɗansu alloli a ƙasar Masar, inda ku ka je ku zauna. Kun je can ne don a hallaka ku, don ku zama la'antattu da abin reni a cikin dukkan al'umman duniya. 9 Kun manta da ayyukan muguntar da kakanninku su ka yi da muguntar da sarakunan Yahuda da matansu su ka yi? Kun manta da muguntar da ku da kanku da matanku ku ka aikata a cikin ƙasar Yahuda da titunan Yerusalem? 10 Har ya zuwa yau, ba su yi tawa'li'u ba. Ba su girmama shari'una ba ko dokokina da na sanya a gabansu ba, su da kakanninsu, ba su kuma yi tafiya a cikinsu ba.' 11 Don haka Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Duba, ina gab da sa fuskata gãba da ku don in kawo muku masifa in kuma hallakar da dukkan Yahuda. 12 Don zan kwashe sauran mutanen Yahuda waɗanda su ka je Masar su zauna a can. Zan yi wannan don dukkan su su hallaka a ƙasar Masar. Za su faɗi ta wurin takobi da yunwa. Tun daga ƙaraminsu har zuwa babbansu za su faɗi ta wurin takobi da yunwa. Za su mutu su kuma zama abin reni da abin ƙyama. 13 Don zan hori mutanen dake zaune a ƙasar Masar kamar yadda na hori mutanen Yeruselem da takobi, da yunwa. da annoba, 14 yadda ba wani ragowar Yahuda waɗanda su ka tafi su zauna a cikin ƙasar Masar da zai kucce ko ya tsira ko ya dawo ƙasar Yahuda, wadda su ke marmari su dawo su zauna; Ba waninsu da zai dawo, sai dai 'yan kima da su ka kutto a nan.'" 15 Daga nan duk waɗanda su ka san matansu na ƙona turare ga waɗansu alloli, da kuma dukkan matayen da ke a babbar taruwa, da dukkan mutanen da ke zaune a ƙasar Masar ta kwari da tudu, a Fatros su ka amsa wa Irmiya. 16 Su ka ce, "Game da maganar da ka faɗa, mana a cikin sunan Yahweh ba za mu saurare ka ba. 17 Don hakika za mu yi duk abin da mu ka ce za mu yi - ƙona turare ga sarauniyar sama da zuba baye - baye na sha a gabanta Kamar yadda kakanninmu, da sarakunanmu, da shugabanninmu su ka yi a titunan Yerusalem. Daga nan za mu ƙoshi da abinci mu wadatu, ba tare da fuskantar wata masifa ba. 18 Sa'ad da mu ka dena yin waɗannan wato ƙin miƙa baiko ga sarauniyar sama da kuma ƙin miƙa baye - baye na sha a gare ta, duk za mu talauce mu kuma mutu ta wurin takobi da yunwa." 19 Sai matayen suka ce, "lokacin da mu ke yin baye - baye na turare a gaban sarauniyar sama da zuba baye - baye na sha a gare ta, ashe saɓawa mazanmu muka yi da muka aikata waɗannan abubuwa, yin waina a cikin siffarta da kuma zuba baye - baye na sha gare ta?" 20 Daga nan sai Irmiya ya ce da dukkan mutanen -ga maza da mata, kuma dukkan mutanen da su ka amsa masa - ya yi shela ya ce, 21 "Ashe Yahweh bai tuna da turaren da ku ka ƙona a biranen Yahuda da titunan Yerusalem - ku da kakanninku, da sarakunanku da shugabanninku, da kuma mutanen ƙasar ba? Domin Yahweh ya tuna da wannan; ya fãɗo cikin tunaninsa. 22 Daga nan ba zai ƙara jurewa da shi ba saboda miyagun ayyukanku da ku ka yi, saboda ayyukan ban ƙyamar da ku ka aikata. Sai ƙasarku ta zama yassashiya, da abin reni, da la'anta ta zama ba wanda ke zaune a cikinta har ya zuwa yau. 23 Saboda kun ƙona turare kun kuma yi zunubi ga Yahweh, don kun ƙi sauraron muryarsa, da shari'unsa ba da kuma ƙa'idojinsa ba, ko alƙawaransa ba, da dokokinsa ba shi ya sa wannan masifar ta same ku kamar yadda ya ke a yau." 24 Sai Irmiya ya ce da dukkan taron mutanen da kuma dukkan matayen, "Ku ji maganar Yahweh, dukkan mutanen Yahuda da ke ƙasar Masar. 25 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila ya faɗi wannan, 'Ku da matayenku duk kun furta da bakinku kun kuma ɗauki duk abin da ku ka ce,"Hakika za mu aiwatar da alƙawuran da mu ka yi cewa za mu yi sujada ga sarauniyar sama, mu kuma zuba baye-baye na sha a gareta." Yanzu sai ku cika alƙawuranku, ku kuma aikatasu.' 26 Don haka ku ji maganar Yahweh, ku dukkan mutanen Yahuda da ke a ƙasar Masar, duba na rantse da sunana mai girma - in ji Yahweh. Ba za a sa ke kiran sunana ta bakin wani daga cikin mutanen Yahuda ba a dukkan ƙasar Masar, ku da yanzu ke cewa, "Na rantse da ran Ubangiji Yahweh." 27 Duba, ina lura da su don in aukar masu da masifa ba abu na gari ba. Duk wani mutumin Yahuda da ke a Masar zai hallaka ta wurin takobi da yunwa har sai dukkan su sun ƙare. 28 Daga nan sai waɗanda su ka tsira daga takobin su dawo daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuda, 'yan kimansu kawai. Da haka dukkan waɗanda su ka ragu a Yahuda da suka je Masar don su zauna a can za su san ko maganar waye zata zama gaskiya - tawa ko tasu. 29 Wannan zai zamar maku alama - wannan shi ne furcin Yahweh - da na ke shirya maku a wannan wurin, don ku san cewa maganata tabbas za ta hare ku tare da masifa.' 30 Yahweh ya faɗi wannan, duba ina gab da in bada Fir'auna Hofra sarkin Masar ga hannun maƙiyansa da kuma hannun masu so su hallaka shi. Zai zama kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga sarki Nebukadnezza sarkin Babila, maƙiyinsa wanda ya biɗi ransa.'"

Sura 45

1 Wannan ita ce maganar annabi Irmiya da ya faɗawa Baruk ɗan Neriya. Wannan ya faru a lokacin da ya rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi wanda Irmiya ya yi masa shifta - wannan ya faru a watan huɗu na sarautar Yahoaikim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sai ya ce, 2 Yahweh Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan a gareku, ina faɗa maka wannan Baruk: 3 Ku ka ce, 'Kaito na, domin Yahweh ya ƙara ƙunci ga raɗaɗina. Da nishe - nishena sun gajiyar da ni; ban sami hutu ba.' 4 Wannan shi ne abin da tilas za ka faɗa masa; Dubi abin da na gina, yanzu ina rushewa. Abin da na dasa, yanzu ina tumɓukewa - Zan yi wannan a dukkan duniya. 5 Amma ko kana begen manyan abubuwa domin kanka? Kada ka yi begen haka. Don duba, masifa za ta aukowa dukkan mutane - wannan furcin Yahweh ne - amma zan ba ka ranka a matsayin ganimarka a duk inda ka je.'"

Sura 46

1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo wurin Irmiya annabi game da al'ummai. 2 Game da Masar: "Wannan game da sojan Fir'auna Neko ne, sarkin Masar da ke Karkemish a wajan kogin Yuferetis. Wannan shi ne sojan Nebudkadnezza sarkin Babila ya cinye a yaƙi a shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda: 3 A sami ƙananan garkuwoyi da manyan garkuwoyi a shirya su ka fita ka yi yaƙi. 4 Ka sa linzamin doki; Ka ɗaura sirdi ka kuma sa hular kwano; ka wasa mãshi ka ɗaura kayan yaƙi. 5 Me nake gani a nan? sun cika da fargaba suna kuma guduwa, don an yi nasara da sojojinsu. Suna gudu don neman tsira basa kuma waigen baya. Fargaba na ko'ina - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta - 6 masu hanzari baza su iya gudu ba, sojojin kuma ba za su tsira ba. Sun yi tuntuɓe a arewa suka faɗi a gefen Kogin Yuferetis. 7 Wane ne wannan da ya tashi kamar Nilu, wanda ruwayensa ke tunbatsa sama da ƙasa kamar koguna? 8 Masar na tashi kamar Nilu, kamar kogunan da suke tumbatsa sama da ƙasa. Masar ta ce Zan tashi in rufe duniya. Zan hallakar da birane da mazaunansu. 9 Ku dawakai ku hau sama ku yi fushi, ku karusai. Bari sojoji su fita waje, Kush da Fut, mutanen da ke fasaha da garkuwa, da mutanen Ludim, mutanen da suka shahara a tanƙwara bakkunansu.' 10 Wannan ranar zata zama ranar ramako ce ga Ubangiji Yahweh mai runduna, zai kuma sakawa kansa akan magaftansa. Takobi za ta ci ta ƙoshi. zata ƙoshi da jininsu. Don za a yi hadaya ga Yahweh Ubangiji mai runduna a arewacin ƙasar a gefen Kogin Yuferetis. 11 Ku je Gileyad ku sami magani, budurwan Masar. A banza kuke sawa kanku magani mai yawa. Ba za ku warke ba. 12 Al'ummai sun ji labarin kunyarku. Duniya ta cika da makokinku, don sojoji suna tuntuɓe da juna, dukkansu su ka fãɗi tare." 13 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗawa annabi Irmiya bayan Nebukadnezza sarkin Babila ya kawo wa Masar hari: 14 "Ka sanar a Masar, ka kuma yi shela a Migdol, da Memfis, da Tafanhes. Ku sami wurinku ku shirya kanku, don takobi zai haɗiye waɗanda ke kewaye da ku.' 15 Don me jarumawanki fuskarsu a sunkuye ƙasa? Ba za su tsaya ba, saboda Ni, Yahweh, na ture su ƙasa. 16 Ya ƙara yawan waɗanda su ka yi tuntuɓe. Kowanne soja ya fãɗi kusa da ɗan uwansa. Su na cewa, 'Ku tashi. Bari mu tafi gida. Bari mu koma wurin mutanenmu, zuwa ainahin ƙasarmu. Bari mu bar wannan takobin da ya ke doddoke mu ƙasa.' 17 Su ka yi shela a can, 'Fir'auna sarkin Masar mai kwakazo ne kawai, wanda ya bar zarafinsa ya sille.' 18 Na rantse da zatina inji Sarki, wanda sunansa shi ne Yahweh mai runduna - wani zai zo mai kama da Dutsen Tabor da Dutsen Karmel na bakin teku. 19 Ku kwaso wa kanku jakkuna don za ku tafi hijira, ku da ku ke zaune a Masar. Domin Memfis zata zama wofi, zata zama kango, ba kuma wanda zai zauna a can. 20 Masar kyakkyawar maraƙa ce, amma ƙwaro mai harbi na zuwa daga arewa. Yana zuwa. 21 Sojojin hayar da ke cikinta kamar bijimi mai ƙiba suke, amma su ma za su juya su gudu. Ba za su iya tsayuwa tare ba, don ranar masifarsu na zuwa gãba da su, lokacin horonsu ne. 22 Masar ta fito kamar maciji tana kuma rarrafawa, don maƙiyanta suna tattaki gãba da ita. Suna tunkararta kamar masu yankan katako da gatura. 23 Za su sassare dazuzzuka - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta-duk da yake abin ya na da ban razana. Domin magabta za su zama da yawa sosai fiye da fara ba za su ƙidayu ba. 24 Za a kunyatar da Masar. Za a miƙa ta ga hannun mutane daga arewa." 25 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, "Duba, ina gab da in hori Amon na Tebes, da Fir'auna, da Masar da allolinta, da sarakunanta wato masu mulkinta, da masu dogara da su. 26 Zan miƙa su ga wanda ke neman rayukansu, da kuma hannun Nebukadnezza sarkin Babila da bayinsa. Daga nan bayan wannan za a sake zama a Masar kamar a kwanakinta na can baya - wannan furcin Yahweh ne 27 Amma kai, bawana Yakubu, kada ka ji tsoro. Kada ka razana, Isra'ila, don duba, Ina gab da in komo da ku daga manisanta wurare, zuriyarku kuma daga ƙasar bautarsu. Daga nan sai Yakubu ya dawo, ya sami salama, ya kuma sami tsaro, kuma ba sauran wanda zai razana shi. 28 Kai, bawana Yakubu, kada ka ji tsoro - wannan shi ne furcin Yahweh - don ina tare da kai, kuma zan halakar da dukkan al'ummai a inda na warwatsa ku. Amma ba zan hallaka ku dukka ba. Duk da haka zan hore ku da adalci hakika ba zan bar ku ba horo ba."

Sura 47

1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo ga annabi Irmiya game da Filistiyawa. Wannan maganar ta zo gare shi kafin Fir'auna ya kai wa Gaza hari. 2 Yahweh ya faɗi wannan: Duba, tunbatsar ruwa na tasowa daga arewa. Zai zama kamar ambaliyar koguna! Daga nan za su share ƙasar da duk abin da ke cikinta, da biranenta da mazaunanta! Saboda haka kowa zai yi kukan neman taimako, kuma dukkan mazaunan ƙasar za su yi makoki. 3 Da jin motsin sawayen ƙarfafan dawakansu 'kofatansu na ruri akan karusansu da kuma ƙarar gargarensu, ubanni ba za su taimaki 'ya'yansu ba saboda rashin ƙarfinsu. 4 Domin rana na zuwa da zata warwatsa dukkan Filistiyawa, ta datse daga Taya da kuma Sidom da kuma daga duk wanda ya tsira ya ke kuma so ya taimake su. Don Yahweh yana warwatsa Filistiyawa, waɗanda su ka ragu a tsibirin Kafto. 5 Saiƙo zai aukawa Gaza. Ashkelon kuma mutanen da aka bari a kwarurrukansu za a sa su su yi shiru. Makokinku zai kai wanne lokaci? 6 Kaito, takobin Yahweh! Har yaushe za ta kasance har sai kun yi shiru? Ku koma ga watsewarku! Ku dena ku yi shiru. 7 Ta yaya zai huta, sa'ad da Yahweh ya umarce shi. Sa'ad da ya umarta a kaiwa Ashkelon hari da kuma ƙasashen da ke gefen teku?"

Sura 48

1 Ga Mowab, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Kaiton Nebo, domin an warwatsa ta. An cinye KIriyata an ƙasƙantar da ita. An ɓalle hasumiyarta an wulaƙanta ta. 2 Mowab ba ta da sauran wata daraja. Maƙiyansu a Heshbon sun shirya mata masifa. Sun ce Ku zo mu hallakar da ita a matsayinta na ƙasa. Mahaukatanta suma za su hallaka - takobi za ta bi bayanku.' 3 Ku saurara! Ƙarar kururuwa na tafe daga Horoniyam, inda akwai kango da kuma babbar hallakarwa. 4 An hallakar da Mowab. 'Ya'yanta sun yi kuka har aka ji su. 5 Sun je kan tsaunukan Luhit suna kuka, Domin akan hanya zuwa Horoniyam, an ji ƙara mai ban razana saboda hallakarwa. 6 Tsere! Ku ceci rayukanku ku zama kamar dajin yunifa a jeji. 7 Domin saboda dogararku ga ayyukanku da dukiyarku, kuma za a kame ku. Daga nan sai Kemosh ya tafi zaman bauta, tare da firistocinsa da shugabanninsa. 8 Domin mai hallakarwa zai zo kowanne birni; ba birnin da zai tsira. Don haka kwari zai lalace, filin ƙasa kuma za a ɓaɓɓata shi, Kamar yadda Yahweh ya faɗa. 9 Ku bada fukafukai ga Mowab, don tilas ne ta tashi ta gudu. Biranenta za su zama ɓatattun ƙasashe, inda ba mai zama a cikinsu. 10 Dama duk wanda ke ragwanci cikin aikin Yahweh ya zama la'ananne! Dama duk wanda ya janye takobinsa daga zubar da jini ya zama la'annanne! 11 Mowab tana jin tana da tsaro tun tana matashiya. Ta zama kamar ruwan inabin da ba a taba canja masa gora ba. Ba ta taɓa zuwa bauta ba. Don haka yana jin komai dai - dai ne kamar dã; ɗanɗanonsa bai canza ba. 12 To duba, ranaku na zuwa - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta - lokacin da zan aika masa da waɗanda za su juye shi su kuma juye dukkan tukwanensa su kuma farfasa butocinsa. 13 Daga nan sai Mowab su ji kunyar Kemosh kamar yadda ya faru ga gidan Isra'ila, yadda su ka ji kunyar Betel, abin dogararsu. 14 Yaya za ku ce 'Mu sojoji ne, jarumawan yaƙi'? 15 Za a washe Mowab za kuma a kai wa biranenta hari. Don kyawawan matasanta sun gangara mayanka. Wannan furcin sarki ne! Sunansa Yahweh mai runduna ne. 16 Masifar Mowab na gab da auko mata; bala'i ya kusa sauka da sauri. 17 Dukkan ku da ke kewaye da Mowab, ku yi kuka; da ku da kuka san ƙarfinta, ku yi sowar wannan, Kaiton, sanda mai ƙarfi, sandar daraja, an karye ta.' 18 Sauko daga wurinki mai daraja ki zauna a busasshiyar ƙasa, ke ɗiya mai zama a Dibon. Domin wanda zai hallaka Mowab yana kawo ma ki hari, wanda zai hallakar da madogaranki. 19 Ku tsaya akan hanya ku yi tsaro, ku mutanen da ke a Arowa. Ku yi tambaya ga wanda ya ga wanda ke gudu don ya tsira. ku ce Me ya faru?' 20 Mowab ta kunyata, don an warwatsa ta. Ku kaɗa kai ku yi makoki; Ku yi ihun neman taimako. Ku faɗawa mutanen yankin kogin Arnon cewa an hallakar da Mowab. 21 Yanzu horo ya sauko kan ƙasa mai duwatsu, ga Holon, da Jakza, da Mefat, 22 ga Dibon, ga Nebo, da Bet diblataim, 23 ga Kiriyataim, da Bet Gamul, da Bet Meyon, 24 ga Keriyot da Bozra, da kuma ga dukkan biranen da ke ƙasar Mowab - da manisanta, da biranen da ke nesa da kusa. 25 An kawar da ƙahon Mowab; an karya damtsenta - wannan furcin Yahweh ne.+ 26 Ka sa ya bugu, don ya yi girman kai gãba da Yahweh. Bari Mowab ta yi birgima a kan hararwarta, ka sa ta zama abin ba a. 27 Domin ko Isra'ila bata zama abin dariya a gare ku ba? An same shi cikin ɓarayi, saboda haka ku ka kaɗa kanku gare shi ku ka yi kuma ta yin magana a kansa? 28 Ku yi watsi da birane ku tattaru a gefen gari, ku mazaunan Mowab. Ku zama kamar kurciyar da ke sheƙa a bakin rami a cikin duwatsu. 29 Mun ji labarin girman kan Mowab - da tayarwarta, da kumbura kanta, yadda ta ke ɗaukaka kanta da mugayen tunane tunanenta na zuciya. 30 Wannan furcin Yahweh ne - Ni da kaina na san maganganunsa na banza, waɗanda ba komai ba ne, kamar ayyukansa. 31 Don haka zan kawo makoki ga Mowab, zan kuma tada muryar makoki ga dukkan Mowab zan yi makoki saboda mutanen Kir Hareset. 32 Zan yi kuka dominku fiye da yadda na yi don Yazer, da kuringar Sibmah! Rassanki sun zarce ƙetaren Tekun Gishiri sun kai har Yazer. masu hallakarwa sun kawo hari ga 'ya'yan itatuwan inabinki na damina. 33 Don an kawar da biki da farinciki daga 'ya'yan itace da kuma ƙasar Mowab. Na kawo ƙarshen ruwan inabi daga wurin matsawarsu. Ba zasu matse su da sowace - sowacen farinciki ba. Duk wani sowace - sowace ba zai zama sowace - sowacen murna ba. 34 Daga sowace - sowace a Heshbon tun daga can Eleyele, an jiwo ƙararsu a Yahaz, daga Zowar har zuwa Horoniyaim da Eglat Shelishiya, tun daga ma can rafuffukan Nimrim da suka bushe. 35 Don zan kawo ƙarshen kowa a Masar wanda ke miƙa hadayu a manyan wurare da ƙona turare ga allolinsa - wannan furcin Yahweh ne. 36 Don haka zuciyata tana makoki domin Mowab kamar sarewa. Zuciyata tana makoki kamar gungume saboda mutanen Kir Hereset. Dukiyar da suka ribato ta ƙare. 37 Don dukkan kawuna sun yi saiƙo an kuma aske duk wani gemu. Tsage - tsage yana a kowanne hannu, sun kuma yafa tufafin makoki a kwankwasonsu 38 A kwai makoki a ko'ina, a cikin dukkan gine-ginen Mowab da kuma Cibiyoyin kasuwancin Mowab. Don na hallakar da Mowab kamar tukwanen da ba wanda ke so - wannan furcin Yahweh ne. 39 Yadda aka farfasa su! Yadda su ka yi ruri cikin makokinsu! Mowab ta juya bayanta cikin kunya! Don haka Mowab zata zama abin ba a da firgita ga dukkan waɗanda suka kewaye shi." 40 Gama Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, maƙiyi zai zo yana jewa kamar gaggafa, yana buɗe fuka-fukansa a kan Mowab. 41 An kame Keriyot da dukkan hasumiyoyinta an ƙwance su. Don a waccan ranar zukatan sojojin Mowab za su zama kamar na zukatan matan da ke naƙuda a lokacin haihuwa. 42 Don haka za a hallakar da Mowab ta zama ba sauran mutane, don ya mai da kansa ya zama babba gãba da yahweh. 43 Masifa da rami, da tarko suna zuwa kanku, ku mazauna Mowab - wannan furcin Yahweh ne. 44 Duk wanda ya gudu saboda firgita zai faɗa rami, kuma duk wanda ya fito daga rami tarko zai kama shi, don zan aukar masu da wannan a shekarar fushina na ramako a kansu - wannan furcin Yahweh ne. 45 Waɗanda su ka tsere za su tsaya a inuwar Heshbon ba tare da wani ƙarfi, ba don wuta za ta tashi daga Heshbon, da harshen wuta daga tsakiyar Sihon. Zata cinye goshin Mowab da tsakiyar kawunan mutane masu ɗaga kai. 46 Kaiton ki, Mowab! an hallakar da mutanen Kemosh, Don an kwashe 'ya'yanki maza a matsayin bayi, 'yan matanki kuma zuwa bauta. 47 Amma zan dawo da nasarar Mowab a kwanaki masu zuwa - wannan furcin Yahweh ne." Hukuncin Mowab ya ƙare a nan.

Sura 49

1 Ga abin da Yahweh ya ce, game da mutanen Ammon, Isra'ila ba ta da 'ya'ya ne? Babu wanda zai gãji wani abu a Isra'ila? Me ya sa Molek ya ke zaune a Gad, mutanen sa kuma su na zaune a cikin biranen sa? 2 To duba, kwanaki su na zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'ad da zan ba da alamar yaƙi gãba da Rabbah a cikin mutanen Ammon, za ta zama yasasshen tsibi kuma a ƙone ƙauyukanta da wuta. Gama Isra'ila zai mallaki waɗanda su ka mallake shi." cewar Yahweh. 3 Yi ruri cikin makoki, da Heshbon, gama za a ragargaza Ai! Ɗiyar Rabba, ki yi kururuwa! Sa kayan makoki. Yi makoki da kai da kawowa a wofi, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da shuganninsa. 4 Me ya sa ki ke fahariya da kwarurrukanki, kwarurrukan masu ba da 'ya'ya sosai, ke kangararriyar ɗiya? Ke da ki ke dogara da dukiyarki kuma kin ce, "wane ne za ya iya zuwa ya yi gãba da ni?' 5 Duba, na kusa kawo maki tsoro, wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh Mai Runduna - wannan abin tsoro zai zo daga dukkan waɗanda su ke maƙwabtanki. Zai watsar da kowanne ɗayan ku. Ba wanda zai tattaro waɗanda suka gudu. 6 Amma bayan haka zan dawo da kaddarorin mutanen Ammon - wannan shi ne furcin Yahweh." 7 A kan Idom, Yahweh mai runduna ya ce haka, "Ba sauran hikimar da za a samu a Teman? Shawara mai amfani ta ƙare daga masu fahimta? Hikimar su ta lalace? 8 Ku gudu! Ku koma baya! Ku jira cikin ramummuka cikin ƙasa, mazauna Dedan. Gama zan kawo hallaka ga Isuwa, a kan shi lokacin da zan hore shi. 9 Idan masu girbin inabi su ka zo wurin ku, ba za su rage kaɗan ba? Idan ɓarayi ne da daddare, ba za su saci abin da su ke so ba? 10 Amma na tuɓe Isuwa ya zama huntu, na tono wuraren ɓoyon sa domin kada ya ƙara ɓoye wa. 'ya'yansa da 'yan uwansa da maƙwabtansa an hallakar da su, shi kuma ya tafi. 11 Ku bar marayunku, zan lura da su rayukansu, gwaurayenku su dogara gare ni." 12 Gama Yahweh ya faɗi haka, "Duba waɗanda ba su cancanta ba tabbas za su sha daga cikin ƙoƙon. Kai da kanka, ka na tsammani za ka tafi ba tare da horo ba? Ba zai yi wu ba, domin tabbas zaka sha. 13 Gama na rantse da kaina, wannan furcin Yahweh ne - Bozra za ta zama abin tsoro, abin reni, lalatatta, da abin la'antarwa. Dukkan biranenta za su lalace har abada. 14 Na ji magana daga wurin Yahweh, an aika da manzo zuwa ga al'ummai, 'ku taru ku kai mata hari, ku yi shiri domin yaƙi.' 15 Duba, idan an gwada da sauran al'ummai na mai da ke 'yar ƙarama, abin reni ga mutane. 16 Saboda tsoron ka, girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, mazauna can ƙoli, ku da ku ke a can bisa tsaunuka masu tsawo domin ka sa sheƙar ka can sama kamar gaggafa. Zan dawo da kai ƙasa daga can - wannan ne furcin Yahweh. 17 Idom za ta zama abin tsoro ga dukan mai wuce ta. Kowanne mutum zai yi rawar jiki da tsaki saboda dukkan masifunta. 18 Kamar yadda aka kaɓantar da Sodom da Gomora da maƙwabtansu," Yahweh ya faɗi, "ba wanda zai zauna a can; ba wanda zai tsaya a can. 19 Duba, zai tashi kamar zaki daga jejin Yodan zuwa wuraren kiwo masu kyau. Domin nan da nan zan sa Idom ta gudu daga wurin ta, zan sa wani zaɓaɓɓe ya lura da ita. Gama wanene kama da ni, wane ne kuma zai yi mani sammaci? Akwai makiyayin da zai iya yin tsayayya da ni?" 20 Ji shirye-shiryen da Yahweh ya yi gãba da Idom, shirye-shiryen da ya yi gãba da mazaunan Teman. Ba shakka za a janye su har ɗan ƙaramin garken dabbobi. Wuraren kiwon su za su zama rusasssun wurare. 21 Duniya za ta girgiza da ƙarar faɗuwar su. An ji sowace - sowacen ƙunci daga Tekun Iwa. 22 Duba, wani zai kawo hari kamar gaggafa, ya kawo su-ra ya buɗe fuka-fukansa a kan Bozra. Daga nan a wannan rana zuciyar sojojin Idom za ta zama kamar zuciyar macen da ke cikin naƙuda." 23 Game da Damaskus: "Hamat da Arfad za su ji kunya, saboda sun ji labarin hallaka. Sun narke! hankalin su ya ta shi kamar tekun da ya kasa kwantawa. 24 Damaskus ta raunana ƙwarai, ta juya ta gudu; tsoro ya kama ta. ‌Ƙ‌unci da ciwo ya kama ta kamar mace mai hafuwa. 25 Yaya birnin yabo ba a yashe shi ba, garin farincikina? 26 Saboda haka samarinta za su faɗi a wuraren cinikaiyarsu, jarumawanta za su hallaka a rannar- wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna" 27 "Gama zan kunna wuta a kan ganuwar Damsakus, za ta cinye kagara mai ƙarfi ta Ben Hadad." 28 Game da Kedar da mulkokin Hazor, ga abin da Yahweh ya ce da Nebukadnezza, (gama Nebukadnezza sarkin Babila zai kai wa waɗannan wurare hari): "Tashi ka kai wa Kedar hari ka hallaka waɗannan mutanen na gabas. 29 Za a kwashe bukkokinsu da garkunansu, duk da labulen bukkokinsu da kayan aikinsu; za a kore raƙumansu daga wurinsu, mazaje za su yi masu ihu su ce, "Ga abin tsoro a kowanne gefe!" 30 Ku gudu! Ku yi ragaita can nesa! Ku tsaya a cikin ramuka a ƙasa ku mazauna Hazor - wannan furcin Yahweh ne. Gama Nebukadnezza sarkin Babila ya ƙulla shiri gãba da ku. Ku gudu! Ku koma baya! 31 Tashi ka kai wa al'ummar da ke zaune lafiya hari cikin sauƙi, "Yahweh ya ce" Ba su da ƙofofi ko makarai, mutanen hakanan suke zaune su kaɗai. 32 Gama raƙumansu za su zama ganima, kayansu masu yawa za su zama ganimar yaƙi. Sa'annan zan sa iska ta watsar da su, su waɗanda ke aske gefen gashinsu, zan kawo masu hallaka daga kowanne gefe - haka Yahweh ya furta. 33 Hazor za ta zama wurin kwanciyar diloli, ta lalace har abada. Ba wanda zai zauna a wurin, ba mutumin da zai tsaya a can. 34 Wannan ce maganar Yahweh da ta zo ta wurin Irmiya annabi game da Elam. Wannan ya faru a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda, ya ce, 35 "Yahweh Mai runduna ya faɗi wannan: Duba, na kusa karya 'yan baka na Elam, a karfinsu mafi yawa. 36 Gama zan kawo iskoki huɗu daga kusurwoyi huɗu na sammai, zan watsar da mutanen Elam ga dukkan waɗannan iskokin. Waɗanda su ka watse daga Elam babu al'ummar da za su je. 37 Zan ragargaza Elam a gaban abokan gãbar su da waɗanda ke neman ransu. Domin zan kawo masu hallaka da zafin fushina - haka Yahweh ya furta - Zan aika takobi a bayansu har sai na hallakar da su. 38 Sa'annan zan kafa kursiyina a Elam in hallakar da sarkinta da shugabanninta daga can - abin da Yahweh ya furta kenan - 39 Zai zama a cikin kwanaki masu zuwa zan dawo da martabar Elam - abin da Yahweh ya furta kenan."

Sura 50

1 Ga abin da Yahweh ya furta game da Babila, ƙasar Kaldiyawa, ta hannun Irmiya annabi, 2 "Faɗawa al'ummai kuma ka sa su, su saurara. Ka sa alama kuma ka sa su saurara. kada ka rufe ta. Ka ce, 'An ɗauke Babila, an kuyatar da Bel. Marduk ta razana, an sa gumakanta cikin kunya; siffofinta sun razana. 3 Wata al'umma daga arewa zata taso mata, domin ta mayar da ƙasarta kango. Ba wanda zai zauna cikinta ko mutum ko dabba, duk za su gudu. 4 Ga abin da Yahweh ya furta a cikin waɗannan kwanaki da wannan lokaci, mutanen Isra'ila da na Yahuda - zasu taru su je suna neman Yahweh Allahnsu da kuka. 5 Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su nufi wurin ta suna cewa, za mu je mu haɗa kanmu da Yahweh da dauwamamman alƙawarin da ba za a manta ba." 6 Mutane na sun zama garken da ya ɓace, makiyayansu sun bauɗar da su cikin duwatsu; suna juya su daga wannan tudu zuwa wancan. Sun tafi sun mance wurin da suka fito. 7 Kowa ya je wurin su yana cinye su. Abokan gãbar suna cewa, 'Ba mu yi zunubi ba gama sun yi zunubi ga Yahweh, gidansu na gaskiya -Yahweh begen kakanninsu. 8 Ku fita daga tsakiyar Babila; ku fice daga ƙasar Kaldiyawa; ku zama kamar dan akuyan da ya tafi kafin sauran garke. 9 Duba, na kusa ta da ruɗami, in tada wata ƙungiya ta manyan al'ummai daga arewa su yi gãba da Babila. za su haɗa kan su gãba da ita. Za a ci Babila da yaƙi daga can. Kibiyoyinsu kamar na babban maharbin da ba ya dawowa hakanan. 10 Kaldiya za ta zama ganima. Dukkan waɗanda suka washe ta za su gamsu - haka Yahweh ya furta. 11 Kun yi farinciki, kun yi shagali sa'ad da aka washe abin gãdona, kun yi tsalle kamar ɗan maraki a wurin kiwonsa, kun yi haniniya kamar ƙaƙƙarfan doki. 12 Saboda haka mahaifiyarku zata ji kunya ƙwarai; za a ƙasƙantar da wadda ta haife ku. Zata zama mafi ƙanƙanta cikin al'ummomi, ta zama jeji ta zama busasshiyar ƙasa ta zama hamada. 13 Saboda Yahweh ya yi fushi, Babila za ta zama kufai mai zama a cikinta, za ta lalace sarai. Dukkan wanda ya wuce zai yi mamakin lalacewar Babila, ya yi tsaki saboda dukkan raunukanta. 14 Ku da ke kewaye da ita, ku shirya ku kai wa Babila hari. Dukkan wanda ya ɗana baka dole ya harbe ta, kada ku mayar da kibiyoyinku, gama ta yi wa Yahweh zunubi. 15 Ku yi mata ihu a ko'ina! Ta ba da kai, hasumiyoyinta sun faɗi; an rushe ganuwoyinta, wannan fansa ce da Yahweh ya ɗauka. Ku ɗauki fansa a kanta! Ku yi mata kamar yadda ta yi. 16 Ku hallaka manoma, da wanda ya shuka iri da wanda ya yi amfani da lauje a lokacin girbi cikin Babila. Bari kowanne mutum ya koma wurin mutanensa ya gudu daga takobin mai azabtarwa; bari su gudu su koma ƙasarsu. 17 Isra'ila tumaki ne da suka watse zakuna suka kore su. Da farko sarkin Asiriya ya cinye shi; sa'annan Nebukadnezza sarkin Babila ya karya ƙasusuwansa. 18 Saboda haka Yahweh Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Duba, na kusa in hori sarkin Babila da ƙasarsa, kamar yadda na hori sarkin Asiriya. 19 Zan dawo da Isra'ila ƙasarsa; zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Sa'annan za ya ƙoshi a ƙasar kan tudu ta Ifraim da Giliyad. 20 Yahweh ya ce, a cikin waɗanan kwanaki da wannan lokaci, za a nemi laifi a Isra'ila, amma ba za a samu ba. Zan biɗi zunubi game da Yahuda, amma ba zan samu ba, gama zan gafartawa waɗanda na keɓe." 21 "A tasar wa ƙasar Meratayim, gãba da ita da mazaunan Fekod. Sa masu takobi, kuma a keɓe su domin hallakarwa - abin da Yahweh ya furta kenan-- ku yi dukkan abin da nake umurtarku. 22 Zizar yaƙi da mummunar hallakarwa suna cikin ƙasar. 23 Yadda aka datse gudumar dukkan ƙasashe kuma aka hallakar. Yadda Babila ta zama rusasshen wuri cikin al'ummai. 24 Na ɗana maki tarko kuma kin kamu, ke Babila, kuma baki sani ba! An same ki kuma an kama ki, domin kin yi tsayayya da Yahweh. 25 Yahweh ya buɗe wurin ajiyar kayan yaƙinsa kuma yana fito da kayan yaƙin domin aiwatar da fushinsa. Akwai aiki domin Ubangiji Yahweh mai runduna a ƙasar Kaldiyawa. 26 Ku kai ma ta hari daga nesa. Ku buɗe rumbunanta ku tara ta kamar tsibin hatsi. Ku keɓe ta domin hallakarwa. kada ku rage ma ta komi. 27 Ku kashe dukkan bijimanta, ku kai su wurin yankawa. Kaiton su, ranarsu ta zo - lokacin horonsu. 28 Akwai motsin waɗanda suke gujewa, waɗanda suka rage, daga ƙasar Babila. Waɗannan za su ba da labarin ɗaukar fansa da Yahweh Allahnmu ya yi domin Sihiyona, da ɗaukar fansa domin haikalinsa." 29 A kira maharba gãba da Babila - dukkan waɗanda su ka ɗana bakkunansu. Ku yi zango gãba da ita, kuma kada kowa ya tsira. Ku sãka mata kamar yadda ta yi. ku yi mata bisa ga ma'aunin da ta yi amfani da shi. Gama ta rena Yahweh, Mai Tsarki na Isra'ila. 30 Haka samarinta za su faɗi a cikin dandalin birni, kuma dukkan mayaƙanta zasu hallaka a wannan rana - Wannan shi ne furcin Yahweh." 31 Duba, Ina gãba da ke, ke mai takama - wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh mai runduna - gama ranarki ta zo, ke mai taƙama, lokacin da zan hore ki. 32 Domin masu taƙama su yi tuntuɓe su faɗi. Ba wanda zai tashe su. Zan kunna wuta a cikin biranensu; za ta cinye komi da komi da ke kewaye da shi. 33 Yahweh mai runduna ya ce wannan: An tsanantawa mutanen Isra'ila, tare da mutanen Yahuda. Dukkan waɗanda suka kamasu su na riƙe da su; sun hana su su tafi. 34 Mai kuɓutar da su mai ƙarfi ne. Yahweh mai runduna ne sunansa. Lallai zai duba matsalar su da gaskiya, domin ya kawo hutu a ƙasar, ya kuma kawo husuma ga mazaunan Babila. 35 Takobi na gãba da Kaldiyawa, haka Yahweh ya furta, da kuma Babila da mazaunanta da shuganninta da masu hikimarta. 36 Takobi na gãba da masu faɗar maganganun banza! Za su zama wawaye! Takobi na gãba da sojojinta! za su cika da tsoro. 37 Takobi yana zuwa gãba da dawakansu, da karusansu da dukkan mutane mazauna cikin tsaƙiyar Babila, domin su zama kamar mataye. Takobi ya na zuwa gãba da ɗakunan ajiyarta, kuma za a washe su. 38 Fari ya na zuwa kan ruwayenta domin su bushe. Domin ta zama ƙasar gumaka lalatattu, sun yi kamar mutane marasa hankali ta wurin gumakansu. 39 Ta zama hamada inda namun daji za su zauna da diloli da 'ya'yan jimina su zauna a cikinta. Ba lokacin da za a ƙara zama a cikinta. Ba za a ƙara zama cikinta ba daga tsara zuwa tsara. 40 Kamar yadda Yahweh ya kaɓantar da Sodom da Gomora da maƙwabtansu - abin da Yahweh ya furta ke nan - ba wanda zai zauna a can; ba mutumin da zai tsaya cikinta." 41 Duba, wasu mutane suna zuwa daga arewa; babbar al'umma da sarakuna masu yawa an izo su daga manisantan wuraren duniya. 42 Zasu ɗauko bakkuna da mãsu. Su masu masifa ne ba su da tausayi. Tafiyar su tana kama da rurin teku, sun haye bisa dawakai, a jere bisa layi kamar mutane domin yaƙi, gaba da ke, ɗiyar Babila. 43 Sarkin Babila ya ji rahoto game da su, sai hannayensa suka yi sanyi cikin ƙunci. Azaba ta kama shi kamar mace mai haihuwa. 44 Duba! Ya fito kamar zaki daga tuddan Yodan zuwa wuraren kiwo. Gama nan da nan zan sa su gudu daga wurin, kuma zan sa wani zaɓaɓɓe ya lura da wurin. Gama wane ne kama da ni, kuma wa za ya ba ni sammaci? Wanne makiyayi ne zai iya tsayayya da ni? 45 To saurari shirye-shiryen da Yahweh ya yi gãba da Babila, shirye-shiryensa da ya shirya gãba da ƙasar Kaldiyawa. Lallai za a janye su, har ma da ɗan karamin garke. Wuraren kiwon su za su zama kango. 46 Duniya za ta girgiza da rurin yaƙin yin nasara da Babila, al'ummai za su ji kukansa na ƙunci."

Sura 51

1 Ga abin da Yahweh ya faɗi: Duba, na kusa tado da iskar mai hallakaswa a kan Babila da mazauna cikin Leb Kamai. 2 Zan aika da baƙi ga Babila, za su warwatsar da ita su lalata kasarta, gama za su auko mata ta kowanne gefe a ranar hallakarwa. 3 Kada ku bari maharba su ɗana bakkunansu; kada ku bari su sa kibiya. Kada ku ƙyale samarinta, ku keɓe dukkan sojojinta domin hallakarwa. 4 Gama mutanen da suka sami rauni za su faɗi a ƙasar Kaldiyawa; matattu za su faɗi a cikin titunanta. 5 Gama Isra'ila da Yahuda Allah bai yashe su ba, Yahweh mai runduna, ko da yake ƙasar ta na cike da laifofin da a ka yi wa Mai Tsarki na Isra'ila. 6 Ku gudu daga cikin Babila, kowa ya tsira da kansa. Kada ku hallaka cikin muguntarta. Gama lokacin ɗaukar fansar Yahweh ne. Zai rama komai a kanta. 7 Dã Babila ƙoƙon zinari ce a hannun Yahweh wadda ta sa dukkan duniya suka bugu; dukkan al'ummai suka sha ruwan inabinta suka sami taɓin hankali. 8 Ba da jimawa ba Babila za ta fadi za a hallaka ta. Ku yi makoki dominta! Ku ba ta magani domin ciwonta; ko ƙila zata warke. 9 Mun so mu warkar da Babila, amma ba ta warke ba. Bari mu barta, mu tafi kasarmu. Gama muguntarta ta kai har sama, ta taru a cikin giza-gizai. 10 Yahweh ya ce mu ba mu da laifi. Ku zo, mu faɗi ayyukan Yahweh Allahnmu a cikin Sihiyona.' 11 Ku wãsa kibiyoyi ku kuma ɗauki garkuwoyi. Yahweh ya na zuga ruhun sarkin Medes a kan shirin hallaka Babila. Wannan fansa ce ta Yahweh, fansa saboda hallaka haikalinsa. 12 Ku tada tuta a kan ganuwoyin Babila, ku tsananta tsaro; ku sa masu tsaro ku shirya kwanton ɓauna; gama UBANGIJI zai aikata abin da ya ce game da mazaunan Babila. 13 Ku mutanen da ke zaune a bakin rafuka masu ruwa da ku mutane masu arzikin dukiya, ƙarshenku ya zo. An rage tsawon zaren rayuwarku. 14 Yahweh mai ruduna ya rantse da ran sa, ' zan cika ku da mutane, kamar cincirindon fara, za kuma su tãda muryar yaƙi gãba da ku.' 15 Ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa. Ta wurin fahiminsa ya shimfiɗa sammai. 16 Idan ya yi tsawa, sai ruwaye su yi ruri a cikin sammai, gama ya kan kawo turiri daga ƙarshen duniya. Ya kan yi walƙiya domin ruwa ya kuma aiki iska daga cikin taskokinsa. 17 Kowanne mutum ya zama marar fahimi, marar sani. Kowanne maƙerin tama gumakansa sun kunyatar da shi. Gama sifofinsa na zubi ƙarya ce kawai babu rai a cikin su. 18 Ba su da amfani, aikin ruɗi ne kawai, za su lalace a ranar horonsu. 19 Amma Yahweh, rabon Yakubu ba kamar waɗannan ya ke ba, gama shi ne ya cura dukkan abu. Isra'ila ne harshen gãdonsa; Yahweh mai runduna ne sunansa. 20 Kai ne gudumata da kayan yaƙina. Da kai zan ragargaza al'ummai in hallaka mulkoki. 21 Da kai zan ragargaza dawakai da mahayansu; da kai zan ragargaza karusai da masu tuƙa su. 22 Da kai zan ragargaza kowanne mutum da kowacce mace. Da kai zan ragargaza tsoho da yaro. Da kai zan ragargaza samari da budurwai. 23 Da kai zan ragargaza makiyayi da garkensa. Da kai zan ragargaza manoma da ƙungiyarsu, Da kai zan ragargaza gwamnoni da jami'ansu. 24 Kana gani zan sakawa Babila da dukkan mazauna Kaldiya, bisa ga dukkan muguntar da suka yi a cikin Sihiyona - abin da Yahweh ya furta kenan. 25 Duba, ina gãba da kai, dutsen hallakarwa - abin da Yahweh ya furta kenan - wanda ke hallaka dukkan duniya. Zan miƙa hannuna gãba da kai in gangarar da kai daga can ƙoli, in mai da kai ƙonannen dutse. 26 Yadda ba za su ɗauki wani dutse daga wurinka su kafa tushen gini da shi ba. Za ka lalace sarai har abada - haka Yahweh ya furta. 27 A kafa tuta bisa duniya. A busa ƙaho bisa al'ummai, a kira al'ummai su kai mata hari: Ararat, Minni da Ashkenaz. A sa wani jarumi ya kai mata hari, a zo da dawakai kamar cincirindon fãri. 28 A shirya al'ummai su kai mata hari: Sarkin Medes da gwamnoninsa, da dukkan jami'ansa da dukkan ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkinsa. 29 Gama ƙasar za ta girgiza ta kasance cikin azaba, tun da shirye - shiryen Yahweh ya ci gaba a kan Babila, domin ya maida ƙasar Babila lalatacciyar ƙasa inda ba mazauna. 30 Sojojin da ke Babila sun dena faɗa; sun koma cikin maɓoyarsu. ‌Ƙ‌arfinsu ya ƙare; sun zama mata - gidajenta suna cin wuta, an kakkarya makaran ƙofofinta. 31 Wani manzo ya tafi ya yi shela ga wani manzo, wani mai gudu ya tafi ya gaya wa wani mai gudu ya kai wa sarkin Babila rahoton an ƙwace birninsa tun daga ƙarshe har zuwa ƙarshe. 32 An ƙwace magangarin rafi an ƙone ciyawar fadamu, kuma mayaƙan Babila sun rikice. 33 Gama Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: ‌Ɗ‌iyar Babila ta zama kamar masussuka. Lokaci ya yi da za a tattake ta ƙasa. Da jimawa kaɗan lokacin girbi zai zo mata. 34 Nebukadnezza sarkin Babila ya lanƙwame ni; ya kore ni cikin ruɗami ya kuma maishe ni tukunyar da ba komi a ciki. Ya haɗiye ni kamar dodo, ya cika cikinsa da abinci na mai kyau, ya share ni sarai.' 35 Shi wanda ya ke zaune a Sihiyona zai ce, '‌Ta'addancin da a ka yi mani da jikina ya koma kan Babila.'Yerusalem za ta ce, ' Bari jinina ya zauna a kan Kaldiya.' 36 Saboda haka ga abin da Yahweh ya ce: Duba, ina kusa da goya ma ki baya cikin matsalar ki in ɗauki fansa domin ki. Duba zan busar da ruwayen Babila, in sa mabulbulolinta su ƙafe. 37 Babila za ta zama juji, kogunan diloli, wurin jin tsoro, abin tsãki, inda ba kowa a ciki. 38 Mutanen Babila za su yi ruri tare kamar 'yan zakoki. Za su yi ƙara kamar 'ya'yan zaki. 39 Sa'ad da su ka ji zafi saboda haɗama, zan shirya masu liyafa; zan sa su bugu domin su yi murna, sa'annan su yi barci wanda ba za su ƙara tashi ba - abin da Yahweh ya furta kenan - 40 Zan tura su kamar ragunan yanka, kamar raguna da bunsura. 41 An ci Babila da yaƙi! An kame yabon dukkan duniya. Abin da mamaki yadda Babila ta zama kango a cikin al'ummai. 42 Teku ya zo kan Babila! Rurin balalloƙan ruwa ya cika ta. 43 Biranenta sun zama lalatattu, ƙasa busasshiya da kuma jeji, ƙasar da babu mai zama a ciki, ba talikin da ke wucewa ta wurin. 44 Saboda haka zan hori Bel cikin Babila; zan fitar daga bakinsa abin da ya haɗiye, al'ummai ba za su ƙara gangarowa wurinsa da baye - bayensu ba. Ganuwoyin Babila za su faɗi. 45 Mutanena, ku fice daga cikin tsakiyarta. Bari kowanne ɗayanku ya tsira da ransa daga fushin hasalata. 46 Kada ku bari zuciyarku ta yi suwu saboda labarin da ku ka ji cikin ƙasar, gama labaran za su zo shekara ɗaya. Bayan wannan shekara mai zuwa akwai labarai, tashin hankali zai zo cikin ƙasar. Mai mulki zai yi gãba da mai mulki. 47 Saboda haka, duba, kwanaki za su zo inda zan hori sassaƙaƙƙun gumaka na Babila. Dukkan ƙasarta za ta ji kunya, dukkan waɗanda a ka yanka za su faɗi cikin tsakiyarta. 48 Sa'annan sama da ƙasa, da dukkan abin da ke cikin su za su yi farin ciki a kan Babila. Gama masu hallakarwa za su zo dominta daga arewa - haka Yahweh ya furta. 49 Kamar yadda Babila ta kashe mutane su ka faɗi a Isra'ila, haka kuma za a kashe mutane su faɗi a cikin tsakiyar Babila. 50 Masu tsira daga takobi, ku tafi! Kada ku tsaya cik. Ku tuna da Yahweh daga nesa; bari Yerusalem ta zo cikin lamirinku. 51 Mun ji kunya, domin mun ga wulaƙanci; kunya ta rufe fuskokinmu, gama bãƙi sun shiga wurare masu tsarki na gidan Yahweh. 52 Domin haka, duba, kwanaki suna zuwa - haka Yahweh ya furta - sa'ad da zan hukunta sassaƙaƙƙun gumakanta, waɗanda suka ji rauni zasu yi nishi cikin ƙasarta dukka. 53 Ko da Babila zata hau cikin sammai ta inganta hasumiyarta, masu hallakarwa zasu auko mata daga wurina - haka Yahweh ya furta. 54 Kukan baƙinciki ya fito daga Babila, babbar ribɗewa ta fito daga ƙasar Kaldiyawa. 55 Gama Yahweh ya na hallakar da Babila. Yana sa muryarta mai ƙara ta lalace. Abokan gabarsu su na ruri kamar balalloƙan ruwaye masu yawa; ƙarar su ta yi ƙarfi ƙwarai. 56 Gama masu hallakarwa sun zo kanta - a kan Babila! - kuma an kama jarumawanta. An kakkarya bakkunansu, gama Yahweh Allah ne mai ɗaukar fansa; ba shakka zai ɗauki fansa. 57 Zan sa hakimanta da masu mulkinta da sojojinta su bugu, su yi barcin da ba za su tashi ba - wannan furcin sarki ne: Yahweh mai runduna ne sunansa. 58 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ganuwar Babila mai kauri za a rushe ta sarai, za a ƙone dogayen ƙofofinta. Sa'annan mutane masu kawo mata ɗauki za su yi aikin wofi; dukkan abin da al'ummai su ka yi ƙoƙarin yi mata za a ƙone shi." 59 Wannan ita ce maganar da Irmiya annabi ya umurtawa Seraya dan Neriya dan Maseya, sa'ad da ya tafi da Zedekiya sarkin Yahuda zuwa Babila a cikin shekara ta hudu ta mulkinsa. A lokacin Seriya shi ne babban jami'i. 60 Irmiya ya riga ya rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi dukkan hallakar da za ta zo a kan Babila - dukkan waɗannan maganganu da aka rubuta game da Babila. 61 Irmiya ya ce da Seraiya, "Sa'ad da ka je Babila za ka gani kuma za ka karanta waɗannan maganganu da ƙarfi. 62 Sa'annan za ka ce, 'Yahweh, kai da kanka ka furta cewa za ka hallaka wannan wuri, kuma ba mutum ko dabba da zai zauna a cikinta, za ta zama lalatacciya har abada.' 63 Sa'ad da ka gama karanta wannan naɗaɗɗen littafi, ka ɗaura masa dutse ka jefa shi cikin tsakiya Ifratis. 64 Ka ce, 'Haka Babila zata nitse. Ba zata tashi ba saboda bala'in da na ke aiko wa gãba da ita, kuma za su faɗi."' Nan maganganun Irmiya suka tsaya.

Sura 52

1 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki a Yerusalem shekara goma sha ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ne; ita ɗiyar Irmiya ce daga Libna. 2 Ya yi mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abin da Yohoaikim ya yi. 3 Ta wurin fushin Yahweh dukkan waɗannan abubuwa suka faru a Yerusalem da Yahuda, har sai lokacin da ya kore su daga gabansa. Sa'annan Zedekiya ya yi wa sarkin Babila tawaye. 4 Ya zama a cikin shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, a cikin wata na goma, a cikin rana ta goma ga watan, Nebukadnezza sarkin Babila, ya zo da dukkan mayaƙansa gãba da Yerusalem. Suka yi zango daura da ita, suka kafa sansanin yaƙi kewaye da ita. 5 Suka kewaye birnin ba shiga ba fita, har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya. 6 A cikin wata na hudu, a kan rana ta tara ga watan yunwa ta yi tsanani a cikin birnin har ma ba abin da mutane za su ci a ƙasar. 7 A ka ɓalle birnin aka shiga, dukkan mayaƙa su ka gudu su ka fice daga cikin birnin ta hanyar da ke tsakanin ganuwa biyu a cikin dare, ta lambun sarki, duk da ce wa Kaldiyawa su na kewaye da birnin. Su ka tafi wajen Arabah. 8 Amma sojojin Kaldiyawa su ka bi sarki su ka cimma Zedekiya a filin Kogin Yodan kusa da sararin kwarin Yariko. Dukkan mayaƙansa su watse daga wurinsa. 9 Suka kama sarki suka kawo shi wurin sarkin Babila a Riblah cikin ƙasar Hamat, inda ya yanke ma sa hukunci. 10 Sarkin Babila ya yanka 'ya'yan sarki Zedekiya maza ya na gani, kuma a Riblah ya yanka dukkan shugabannin Yahuda. 11 Sa'annan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya ɗaure shi da sarƙa ta jan ƙarfe ya kawo shi Babila. Sarkin Babila ya sa shi a kurkuku har zuwa ranar mutuwarsa. 12 To, a cikin wata na biyar, a kan rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha tara ta mulkin Nebukadnezza sarki, sarkin Babila, Nebuzaradan ya zo Yeruselem. Shi ne jami'in masu tsaron sarki, shi kuma bawan sarkin Babila ne. 13 Ya ƙone gidan Yahweh, da fadar sarki da dukkan gidajen Yerusalem; ya kuma ƙone kowanne gini mai mahimmanci. 14 Ganuwar da ta kewaye Yerusalem kuma, mayaƙan Babiloniyawa da ke tare da jami'in masu tsaron sarki suka rushe su. 15 Su marasa galihu da sauran mutanen da su ka ragu a cikin birni, waɗanda su ka bijire su ka tafi wurin sarkin Babila da sauran masu aikin hannu - Nebuzaradan jami'in masu tsaron sarki ya kwashe su ya kai su bauta. 16 Amma Nebuzaradan jimi'in masu tsaron sarki ya bar waɗansu cikin marasa galihu a ƙasar domin su yi aiki a garkar inabi da gonaki. 17 Game da ginshikai na tagulla da ke na gidan Yahweh kuwa, da diraku, da babban bangaji na tagulla da ake kira "Teku" da su ke cikin gidan Yahweh, Kaldiyawa su ka kakkarya su gutsu - gutsu suka kwashe dukkan tagullan suka koma da su Babila. 18 Tukwanen, da ceburan, da tsinkunan gyara fitilu, da bangazai, da dukkan kayan aikin na tagulla waɗanda firistoci suka yi hidima da su a haikali - Kaldiyawa suka kwashe su dukka suka tafi da su. 19 Daruka da tasoshin ƙona turare, da bangazai, da tukwane, da maɗorin fitilu, da kaskuna, da darurruka da aka yi da su zinariya da waɗanda aka yi su da azurfa - jami'in masu tsaron sarki ya kwashe su dukka. 20 Ginshiƙai guda biyu, da babban bangajin tagulla da aka sa ni da "Teku," da bijimai guda goma sha biyu na tagulla da su ke karkashin dirakun, abubuwan da Sulaiman ya yi domin gidan Yahweh, ɗauke da tagulla da ta wuce gaban aunawa. 21 Ginshikan kamu sha takwas ne kowannen a tsayi, da layikan da su ke kewaye da su kuma kowanne kamu goma sha biyu ne. Kowannen su kaurin yatsu hudu ne masu rami. 22 Akwai gammon tagulla a bisan sa. Gammon tsawon kamu biyar ne, an yi masa aikin dajiya da siffofin 'ya'yan manta'uwa waɗanda a ka yi da tagulla. Ɗaya ginshikin da nashi 'ya'yan manta uwar dai - dai su ke da na farin. 23 Don haka akwai manta'uwa tasa'in da shida bisa gefen gammunan, da manta'uwa guda ɗari a bisa kewayen aikin dajiyar. 24 Jami'in masu tsaron sarkin ya dauki Seraiya babban firist tare da Zafaniya da firist na biyu da masu tsaron ƙofa su uku a matsayin 'yan kurkuku. 25 Daga cikin birni kuwa ya kama jami'in da ke kula da sojoji da mutane bakwai masu ba sarki shawara, waɗanda suke cikin birni har wannan lokaci. Ya kuma kama jami'in sojojin sarki wanda shi ne ke shigar da mutane aikin soja, tare da waɗansu mahimmam mutane guda sittin waɗanda su ke cikin birni. 26 Sai Nebuzaradan jami'in masu tsaron sarki ya ɗauko su ya kawo su wurin sarkin Babila a Ribla. 27 Sarkin Babila ya kashe su a Ribla cikin ƙasar Hamat. Ta haka Yahuda ta fita daga ƙasarta ta tafi bauta. 28 Waɗannan su ne mutanen da Nebukadnezza ya kai bauta cikin shekara ta bakwai, mutanen Yahuda su 3,023. 29 A cikin shekara ta takwas ta Nebukadnezza, ya ɗauki mutane 832 daga Yerusalem. 30 A cikin shekara ta ashirin da uku ta Nebukadnezza, Nebuzaradan, jami'in masu tsaron sarki ya ɗauki mutum 745 cikin mutanen Yahudiya ya kai su bauta. Dukkan waɗanda a ka kai bauta su ne mutum 4,600. 31 Ya zama kuma a cikin shekara ta talatin da bakwai ta hijira Yehoyacin, sarkin Yahuda, a cikin wata na goma sha biyu, a kan rana ta ashirin da biyar ga wata, sai Awel-Marduk, sarkin Babila ya saki Yehoyacin sarkin Yahuda daga kurkuku. Wannan ya faru ne a cikin shekarar da Awel-Marduk ya fara mulki. 32 Ya yi masa maganar alheri, ya ba shi wurin zama da ya fi na sauran sarakunan da suke tare da shi daraja a Babila. 33 Awel-Marduk ya cire wa Yehoiyacin kayan 'yan sarƙa. Yehoyacin ya yi ta cin abinci a teburin sarki dukkan sauran rayuwarsa, 34 a kan ba shi kuɗin cin abinci kullum har mutuwarsa.

Littafin Makoki
Littafin Makoki
Sura 1

1 Ƙasar da dã ke cike da mutane yanzu tana zaman kaɗaici. Ta zama kamar gwauruwa ko da ya ke babbar al'umma ce dã. Dã gimbiya ce a cikin al'ummai, amma yanzu an sa ta aikin bauta na dole. 2 Tana kuka da koke-koke da dare, kuma hawayenta sun rufe kumatunta. Babu masoyinta da ke yi mata taimako. Dukkan abokananta sun yashe ta. Sun zama maƙiyanta. 3 Bayan talauci da ƙunci, Yahuda ta tafi zaman bauta. Tana zaune a cikin al'ummai kuma ta rasa samun hutawa. Dukkan masu korarta a guje sun wuce ta a cikin damuwarta. 4 Hanyoyin Sihiyona na makoki saboda babu waɗanda suka zo bukukuwan da aka shirya. Dukkan ƙofofinta sun zama yasassu. Firistocinta na nishi. 'Yanmatanta na cikin da baƙinciki kuma ita kanta tana cikin cikakken ƙunci. 5 Magabtanta sun zama iyayengijinta; maƙiyanta sun azurta. Yahweh ya ƙuntata mata domin yawan zunubanta. An kai ƙananan 'ya'yanta bauta ga magabcinta. 6 Kyau ya rabu da ɗiyar Sihiyona. 'Ya'yan sarakunanta sun zama kamar bareyin da ba za su iya samun abinci ba, kuma suna tafiya da ƙyar a gaban masu farautarsu. 7 A kwanakin ƙuncinta da rashin wurin zamanta, Yerusalem zata tuna da dukiyoyinta masu daraja wadda take da su a kwanakin dã. Sa'ad da mutanenta suka faɗi a hannun abokan gãba, babu wanda ya taimaketa. Abokan gãba sun gan ta sun kuma yi dariya ga hallakarta. 8 Yerusalem ta yi zunubi ƙwarai, saboda haka ta zama abin ƙi kamar wani abin ƙyama. Dukkan waɗanda ke girmama ta sun yashe ta tun da suka ga tsiraicinta. Tana nishi tana ƙoƙarin juyawa. 9 Ta zama marar tsabta a karkashin zannuwanta. Ba ta yi tunani a kan kwanakinta masu zuwa ba. Faɗuwarta abin takaici ne. Babu wanda zai ta'azantar da ita. Ta yi kuka cewa "Dubi wuyar da nake sha, Yahweh, gama makiyana sun ƙaru da yawa!" 10 Abokin gãba yasa hannunsa a dukkan dukiyoyinmu masu daraja. Ta ga al'ummai sun shigo wurinta mai tsarki, ko da ya ke ka umarcesu kada su shiga wurin taruwar jama'arka. 11 Dukkan mutanenta sun yi nishi sa'ad da suke neman abinci. Sun ba da dukiyoyinsu masu daraja domin abincin da zai rayar da su. Yahweh, ka dube ni ka kula da ni, gama na zama marar daraja. 12 Wato a wurinku ba komai ba ne, dukkanku da ke wucewa? Ku duba ku gani ko akwai wani mai shan azaba kamar ni, tun da Yahweh ya azabtar da ni a ranar fushinsa mai zafi. 13 Daga can bisa ya aiko da wuta a ƙasusuwana, kuma ta cinye su. Ya yafa raga domin ƙafafuwana ya kuma maida ni baya. Ya maida ni kullum a yashe da somewa. Karkiyar laifofina a ɗaure suke a hannunsa. 14 An ɗaura su tare an sa su a kan wuyana. Ya sa ƙarfina ya ƙare. Ubangiji ya bashe ni a hanun maƙiyana, kuma ba zan iya tsayawa ba. 15 Ubangiji ya tura majiya ƙarfina gefe waɗanda ke yi mani kariya. Ya kira taron jama'a găba da ni don su murƙushe jarumawana. Ubangiji ya tattake ɗiyar Yahuda budurwar nan, a wurin matse ruwan inabi. 16 Saboda waɗannan abubuwa na yi kuka. Idanuwana, ruwa na zubowa ƙasa daga Idanuwana tun da mai ta'azantar da ni wanda zai 'yantar da raina yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace saboda maƙiyin ya yi nasara. 17 Sihiyona ta shinfiɗa hannuwanta da făɗi; ba wanda zai ta'azantar da ita. Yahweh ya umarci waɗanda ke kusa da Yakubu su zama abokan găbarsa. Yerusalem ta zama abin rashin tsabta a garesu. 18 Yahweh mai adalci ne, gama na tayar wa dokokinsa. Ku ji, dukkan mutane, ku kuma ga damuwata. Budurwaina da jarumawana sun tafi bauta. 19 Na yi kira ga abokaina, amma sun zama maciya amana a gareni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin, sa'ad da suke neman abinci na ceton ransu. 20 Duba, Yahweh, gama ina cikin kunci; cikina ya ɗuri ruwa, sai na damu a cikin zuciyata, gama ni mai tayarwa ne sosai. A waje, takobi ya sa uwa makoki, a cikin gida kuma babu kome sai mutuwa. 21 Sun ji nishina, amma ba mai ta'azantar da ni. Dukkan maƙiyana sun ji batun matsalata kuma sun yi murna cewa kai ka yi haka. Kã kawo ranar da ka alƙawarta; yanzu bari su zama kamar ni. 22 Bari dukkan muguntarsu ta zo gabanka. Ka yi masu yadda ka yi mani saboda laifofina. Nishe-nishe na da yawa kuma zuciyata ta some.

Sura 2

1 Ubangiji yã rufe ɗiyar Sihiyona a karkashin gizagizan fushinsa. Ya jefar da darajar Isra'ila ƙasa daga sama zuwa duniya. Bai tuna da matashin sawunsa a ranar fushinsa ba. 2 Ubangiji yã haɗiye yã kuma ƙi jin tausayin dukkan garurruwan Yakubu. A ranar fushinsa ya jefar da ƙayatattun biranen ɗiyar Yahuda a ƙasa; a cikin rashin girmamawa ya saukar da mulkin da shugabaninsa ƙasa. 3 Da zafin fushinsa ya datse kowanne ƙaho na Isra'ila. Ya cire hannun damansa daga gaban maƙiyi. Ya ƙone Yakubu kamar harshen wuta da ke cinye dukkan abin da ke kewaye da shi. 4 Kamar maƙiyansa ya ɗana bakansa gare mu, ya yi shirin harbi da hannun damansa. Ya yayyanke dukkan masu faranta masa rai a rumfar ɗiyar Sihiyona; Ya zuba fushinsa kamar wuta. 5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi. Ya haɗiye Isra'ila. Ya haɗiye dukkan fadodinta. Ya hallakar da wuraren mafakarta. Ya ƙara baƙinciki da makoki cikin ɗiyar Yahuda. 6 Ya kai wa rumfar sujadarsa hari kamar bukkar gona. Ya rusa wurin tsattsarkan taron jama'a. Yahweh yasa a mance da tattsarkar Asabar da taron jama'a a Sihiyona, gama ya wofintar da sarki da firist cikin zafin fushinsa. 7 Ubangiji ya ƙi bagadinsa ya kuma musanci tsarkakan haikalinsa. Ya ba da bangayen fadodinta ga hannun maƙiyi. Sai suka ta da ihu a gidan Yahweh, kamar ranar ayyanannen idi. 8 Yahweh ya ƙudura ya hallakar da garun birnin ɗiyar Sihiyona. Ya miƙar da igiyar gwaji kuma bai ɗauke hannunsa daga rusar da garun ba. Ya sa kagara da garu suyi makoki; ya wofintar da su tare. 9 Ƙofofinta sun lume cikin ƙasa; ya rusar ya kuma karya shingayen kofofinta. Sarkinta da 'ya'yan sarkinta na cikin al'ummai, babu doka kuma, har anabawanta sun rasa wahayi daga Yahweh. 10 Dattawan ɗiyar Sihiyona na zaune shiru a ƙasa. Sun watsa ma kawunansu ƙasa suna kuma sanye da tufafin makoki. 'Yan matan Yerusalem sun russunar da kawunansu ƙasa. 11 Hawayen idanuwana sun gaji da zubowa; cikina ya kiɗime, dukkan raina na cike da baƙinciki saboda rushewar ɗiyar mutanena, yara da jarirai sun some a titunan birnin. 12 Suka cewa uwayensu, "Ina hatsi da ruwan inabi?" sa'ad da suka some kamar mutumin da ya ji ciwo a titunan birnin, rayukansu suka kasance cikin baƙinciki a hannuwan uwayensu 13 Me zan ce maki, ɗiyar Yerusalem? Me zan kwatanta ta'aziyar da zan yi maki 'yar Sihiyona? Ciwonki na da girma kamar teku. Wa zai iya warkar da ke? 14 Anabawanki sun gano wahayin ƙarya dana wofi domin ki. Ba su fallasar da laifofinki har da farfaɗo da ke daga hasarar bauta ba, amma suka fitar da maganganun ƙarya dana kaucewa daga hanya. 15 Dukkan waɗanda suka wuce a hanya suna tafa maki hannuwansu. Suna tsãki suna kaɗa kai gãba da 'yar Yerusalem suna cewa, "Ba wannan ne birnin da ake kira 'Cikakken Kyau,' 'Farin Cikin dukkan Duniya' ba?" 16 Dukkan maƙiyanki sun buɗe bakunansu suna maki ba'a. Suna gwalo da cizon baki da cewa, "Mun haɗiye ta! Wannan ce ranar da muke jira! Muna jiran ganinta!" 17 Yahweh ya aikata abin da ya shirya zai yi. Ya cika maganarsa. Ya tumɓuke ki da rashin tausayi, gama ya bai wa maƙiya dama su yi farinciki a kan ki; ya ɗaga ƙahon maƙiyanki. 18 Zuciyarsu ta yi kuka ga Ubangiji, garun 'yar Sihiyona! Ki sa hawayenki su kwararo ƙasa kamar kogi dare da rana. Kar ki ba kanki da idanunki hutu, 19 Tashi, yi kuka da dare, sau da yawa da almuru! Ki zubo da zuciyarki kamar ruwa a gaban fuskar Ubangiji. Ki ɗaga hannuwanki gareshi domin rayukan 'ya'yanki waɗanda suka some da yunwa a kowanne gefen titi. 20 Duba, Yahweh, ka kula da waɗanda ka yi masu haka. Shin mata zasu iya cinye 'ya'yan cikinsu, 'ya'yan da suka yi renonsu? Yana yiwuwa a kashe firist da annabi a rumfar sujada ta Ubangiji? 21 Matasa da tsofaffi na kwance a ƙurar titunan. "Yan mata da samari sun făɗi ta takobi; kã yanka su ba tare da tausayinsu ba. 22 Kã yi kira, kamar yadda kake kiran mutane a ranar idi, ina fargaba a kowanne gefe, a ranar fushin Yahweh, babu wanda zai kuɓuta ko ya rayu; waɗanda na lura na kuma tasar da su, maƙiyana sun hallakar da su.

Sura 3

1 Ni ne mutumin da yaga wuya a ƙarƙashin sandar fushin Yahweh. 2 Ya kore ni waje ya kuma sanya ni in yi tafiya cikin duhu a maimakon haske. 3 Hakika ya juye hannuwansa gãba da ni ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba a dukkan rana. 4 Ya maida naman jikina da fatar jikina banza; ya karya kassusuwana. 5 Ya kewaye ni kamar birnin da aka kawo masa hari, ya kuma kewaye ni da baƙinciki da matsananciyar wahala. 6 Yasa na zauna a wurare masu duhu, kamar waɗanda suka mutu da daɗewa. 7 Ya gina garu kewaye da ni kuma ba zan iya kuɓuta ba. Yasa sarƙoƙina sun nawaita 8 kuma ko da na yi kiran neman taimako, sai ya ƙi jin addu'ata 9 Ya tare hanyata da garun sassaƙaƙƙun duwatsu; ya maida hanyoyina karkatattu. 10 Ya yi kamar damisa da ke mani kwanto, Zaki na boyewa; 11 ya bauɗar da hanyoyina, ya yashe ni. 12 Ya ja bakansa ya sa na zama abin da kibiyarsa zata harba. 13 Ya soke ƙodojina da kiɓiyoyin kwarinsa. 14 Na zama abin dariya ga dukkan mutane, wani abin yi wa zambo a dukkan yini. 15 Ya cika ni da ɓacin rai ya kuma tilasta ni sha ruwan ɗaci. 16 Ya haƙorana niƙa da tsakuwa; ya tura ni ƙasa cikin ƙura. 17 An raba raina da salama; Na mance da mene ne ma farinciki. 18 Saboda haka na ce, "jimirina ya ƙare haka kuma begena ga Yahweh" 19 Tuna da azabata da yawace-yawacena, ɗacin rai da baƙinciki. 20 Ina ci gaba da tunawa da ita ina kuma russunawa ƙasa a cikin rai na. 21 Amma ina nazarin wannan a zuciyata saboda haka ina da bege: 22 Kaunar Yahweh madawwamiya ba ta ƙarewa kuma tausayinsa baya zuwa ga ƙarshe, 23 suna sabuntuwa kowacce safiya; amincinka mai girma ne. 24 "Yahweh ne gãdona". Na ce, saboda haka zan yi bege a cikinsa. 25 Yahweh managarci ne ga waɗanda ke jiransa, kuma ga mai nemansa. 26 Ya yi kyau a yi shiru a jira ceton Yahweh. 27 Abu nagari ne mutum ya jure karkiya a cikin ƙuruciyarsa. 28 Bari ya zauna shiru shi kaɗai sa'ad da aka ɗora masa shi. 29 Bari ya sa bakinsa a ƙura - mai yiwuwa akwai bege. 30 Bari ya ba da kuncinsa ga mai marinsa, kuma bari ya cika da abin kunya. 31 Gama Ubangiji ba zai ƙi mu har abada ba, 32 Amma koda ya ke ya jawo ɓacin zuciya, zai ji tausayinmu bisa ga yawan kaunarsa marar ƙarewa, 33 Gama ba ya ƙuntatawa daga zuciyarsa, ko cakuna ga 'yan adam. 34 Domin a rugurguza a karkashin kafafunsa dukkan ɗaurarrun duniya, 35 a hana yiwa mutum adalci a gaban maɗaukaki, 36 a hana adalci ga mutum - Ubangiji ba zai amince da abubuwa haka ba. 37 Wa ya yi magana kuma ta cika, idan ba Ubangiji ya umarta ta ba? 38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne masifu da nagargarun abubuwa ke fitowa ba? 39 Ta yaya wani rayayye zai yi gunaguni? Ta yaya mutum zai yi gunaguni game da hukuncin zunubansa? 40 Bari mu auna hanyoyinmu mu gwada su, mu kuma juyo ga Yahweh. 41 Bari mu daga zukatanmu da hannuwanmu ga Allah a sammai. 42 "Mun yi laifofi da tayarwa, kuma baka gafarta ba. 43 Ka rufe kanka da fushi ka kuma kore mu, ka kashe kuma ba ka keɓe mu ba. 44 Ka rufe kanka da giza-gizai yadda babu addu'ar da zata wuce ciki. 45 Ka maishe mu kamar ƙazantaccen juji na wofi a cikin al'ummai. 46 Dukkan maƙiyanmu sun la'anta mu, 47 fargaba da tsoro da lalacewa da hallaka sun auko mana. 48 Idanuwana na fitar da maɓulɓulan hawaye saboda mutanena da aka hallaka. 49 Idanuwana za su zubar da hawaye marar ƙarewa; babu tsayawa, 50 har sai ya dubo ƙasa kuma Yahweh zai duba daga sama. 51 Idanuwana sun sa ni matsananciyar wahala saboda dukkan 'yan matan birnina. 52 Maƙiyana na farauta ta kamar waɗanda ke kamun tuntsu; suna ta farauta ta ba dalili. 53 Sun jefa ni cikin rami suka kuma jefe ni da dutse, 54 har ruwa ya zuba a bisa kaina. Na ce, "An datse ni!' 55 Yahweh, na kira sunanka daga rami mai zurfi. 56 Ka ji muryata sa'ad da na ce, 'Kada ka rufe kunnuwanka ga kukana na neman taimako.' 57 Ka zo kusa a ranar da na kira ka; ka ce, 'kada kaji tsoro.' 58 Ubangiji, ka yi mani kariya, ka cece ni! 59 Yahweh, ka ga abu marar kyau da aka yi mani; ka zama alƙalina. 60 Ka ga zagi da ƙulle-ƙullen da suke yi mani. 61 Ka ji reninsu, Yahweh, da dukkan shirin da suke yi a kai na. 62 Leɓunan waɗanda suke yi mani tayarwa, da zarginsu sun zo gãba da ni dukkan rana. 63 Duba yadda suke zama da tashi; suna yi mani ba'a da waƙoƙinsu. 64 Yahweh, ka rama mani bisa ga abin da suka yi. 65 Za ka bar zukatansu a rashin kunya! Da ma hukuncinka ya auka masu! 66 Ka rarakesu a cikin fushinka ka hallaka su daga ƙarƙashin sammai, Yahweh!"

Sura 4

1 Zinariyar ta zama gurbatacciya; tatacciyar zinariyar ta sake kamanni! An watsar da tsarkakakkun duwatsu a kwanar kowanne titi. 2 'Yan mazan Sihiyona masu daraja sun cancanci nauyin tacacciyar zinariya, amma yanzu ba suma cancanci tulunan yumɓu ba, aikin hannuwan maginin tukwane! 3 Har ma diloli kan iya ba 'ya'yansu nono amma ɗiyar mutanena ta zama mai mummunan hali irin na garken jiminai da ke hamada. 4 Harshen jariri saboda ƙishin ruwa ya liƙe a dasashinsa; yaran na neman abinci amma babu kome dominsu. 5 Waɗanda suka saba da idin abinci mai tsada sun gamu da yunwa a tituna; waɗanda aka san su da sa kyawawun kaya, yanzu suna kwance a juji wofi. 6 Hukuncin ɗiyar mutanena ya fi na Sodom, wadda aka kawar da ita a ɗan lokaci kaɗan kuma babu wanda ya tada hannu na taimakonta 7 Shugabaninta sun ɗara dusar ƙanƙara rashin aibi, sun kuma fi madara fari; jikunansu sun fi murjani kyau, fasalinsu kamar shudin saffiya. 8 Yanzu kammaninsu yafi kunkunniya baƙi. Ba sa ganuwa a tituna. Fatarsu ta liƙe a kasusuwansu; ta zama busasshiya kamar katako. 9 Waɗanda aka kashe su da takobi suna da farinciki fiye da waɗanda aka kashe da yunwa, wanɗanda su ne suka zama lalatattun da aka sokesu da rashin wani girbi daga gona. 10 Hannuwan mata masu tausayi sun dafa 'ya'yansu; suka zamar masu abinci a lokacin da ake hallakar da ɗiyar mutanena. 11 Yahweh ya nuna dukkan fushinsa; ya zubo zafin fushinsa. Ya kunna wuta a Sihiyona da ta cinye tushenta. 12 Sarakunan duniya, ba su amince ba, da haka ma dukkan mazaunann duniya ba su amince ba cewa maƙiyan ko masu adawa za su iya shiga ƙofofin Yerusalem. 13 Wannan ya faru ne saboda zunuban annabawanta da laifofin firistocinta waɗanda suka zubar da jinin adalai a cikinta. 14 Sun yi ta gararamba cikin makanta a tituna. Sun zama ƙazantattu sosai ta wurin jini da babu wanda aka yarda ya taba tufafinsu. 15 "Fita! Marar tsabta!" mutane na ta ihun kiransu. "Fita! Fita! Kar ku taɓa!" Haka suke gararamba; mutane faɗi a cikin al'ummai, "Ba za su ƙara zama a nan kuma ba." 16 Yahweh da kansa ya watsar da su; bai sake kula da su kuma ba. Ba su girmama firistoci ba, kuma ba su nuna wani alheri ga dattawa ba. 17 Idanuwanmu sun gaji da neman taimako a banza; daga wurin duban maƙiyanmu mun dubi al'ummar da ba za ta iya kuɓutar da mu ba. 18 Suka bi duk inda muka nufa, bamu iya tafiya a titunanmu ba. Ƙarshenmu ya kusato kuma an lisafta kwanakinmu, ƙarshenmu ya zo. 19 Masu fafarar mu sun fi gaggafan sararin sama sauri. Suna korar mu zuwa duwatsu kuma suna yi mana kwanton ɓauna a cikin jeji. 20 Numfashin hancinmu - keɓaɓɓu na Yahweh - shi ne wanda aka cafko a ramukansu; wanda aka ce game da shi, "a ƙarkashin inuwarsa ne za mu zauna cikin al'ummai." 21 Ki yi farinciki da murna, ɗiyar Idom, ke da kike zaune a ƙasar Uz. Amma a gare ki kuma za a fara shan ƙoƙon; za ki bugu har sai kin tuɓe kanki tsirara. 22 Ɗiyar Sihiyona, hukuncinki zai kawo ga ƙarshe, ba zai ƙara kwanakin bautarki ba. Amma zai hukunta ɗiyar Idom, zai hukunta; zai buɗe zunubanki

Sura 5

1 Tuna, Yahweh, da abin da ya same mu. Ka duba ka ga abin ban kunyarmu. 2 Gãdonmu an bayar ga bãƙi, gidajenmu ga bãƙi. 3 Mun zama marayu, marasa ubanni, kuma waɗanda uwayensu sun zama kamar gwauraye. 4 Dole mu biya zinariya don ruwan shanmu, kuma dole mu biya zinariya kafin mu samu abincinmu. 5 Waɗanda suke rarakarmu sun matso kusa da mu. mun gaji kuma ba mu samu hutu ba. 6 Mun ba da kanmu ga Masar da Asiriya don mu samu isasshen abinci. 7 Ubanninmu sun yi zunubi, kuma yanzu basu nan, kuma muna ɗaukar alhakin laifofinsu. 8 Bãyi suna mulki a kanmu, kuma babu wanda zai kuɓutar da mu daga hannunsu. 9 Muna samun abincinmu ta sadaukar da ranmu ne kawai, saboda takobin cikin jeji. 10 Zafin fatarmu kamar zafin tanderu don tsananin yunwa. 11 Ana yi wa mata fyaɗe a Sihiyona, har da 'yan mata ma a biranen Yahuda. 12 'Ya'yan sarakuna na rataya kansu da hannuwansu, kuma ba a nuna girmamawa ga dattawa. 13 An sa samari su yi niƙan hatsi dole da dutsen niƙa, samari kuma suna jiri da kayan itace masu nauyi. 14 Dattawa sun bar kofar birnin kuma samarin sun bar raira waƙoƙinsu. 15 Farincikinmu ya ƙare kuma rawarmu ta koma makoki. 16 Rawani ya faɗo ƙasa daga kanmu; kaiton mu, don mun yi zunubi! 17 Domin wannan, zuciyarmu ta kamu da ciwo, kuma idanuwanmu sun dushe, saboda wannan idanuwanmu sun rage ƙarfi. 18 gama Tsaunin Sihiyona ya zama ƙango, diloli ke yawo a kansa. 19 Amma kai, Yahweh, mulkinka har abada ne, kuma za ka zauna a kan kursiyinka daga tsara zuwa tsara. 20 Meyasa ka mance da mu har abada? Meyasa ka bar mu har tsawon kwanaki da yawa? 21 Ka komo da mu zuwa gare ka ya Yahweh, kuma zamu komo. ka sabunta kwanakinmu kamar yadda suke a dã - 22 har sai in ka ƙi mu ɗungum kuma ka yi fushi da mu fiye da misali.

Littafin Ezekiyel
Littafin Ezekiyel
Sura 1

1 A cikin shekara ta talatin, a wata na huɗu, rana ta biyar ga wata, ya kasance kuwa ina zaune cikin 'yan bauta a bakin Kogin Keba. Sai sammai suka buɗe, kuma Na ga wahayoyin Allah. 2 A rana ta biyar a wannan watan - shekara ta biyar kenan ta mijirar sarki Yehoyacin. 3 Maganar Yahweh ta zo ga Ezekiyel ɗan Buzi firist, a cikin ƙasar Kaldiyawa a hanyar Kogin Keba, hannun Yahweh kuma yana kansa a wurin. 4 Daga nan sai na duba, sai ga iskar hadari na tasowa daga arewa; babban girgije mai wuta na haskakawa kewaye da shi da kuma a cikinsa, haske na kewaye da shi da cikinsa, kuma wutar tana da launin rawaya cikin girgijen. 5 Daga cikin tsakiyarsa siffar waɗansu masu rai huɗu. Wannan shi ne bayyanuwar su: suna da kamannin mutum, 6 amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, kowacce halittar kuma nada fikafikai huɗu. 7 Ƙafafunsu a miƙe suke, amma tafin sawayensu kamar kofaton ɗan maraƙi yana sheƙi kamar gogaggiyar tagulla. 8 Duk da haka suna da hannayen mutane a ƙarƙashin kowanne sashi huɗu na fukafukansu, dukkan su huɗun, fuskokinsu da fukafukansu haka suke: 9 fukafukansu na taɓa fukafukan ɗaya halittar, a cikin tafiyarsu ba su juyawa; maimakon haka, kowannensu a miƙe yake ɗoɗar. 10 Kamannin fuskokinsu na kama da fuskar mutum. Su huɗun suna da fuskar zaki a sashin dama, su huɗun suna da fuskar bijimin sã sashin hagu. Su huɗun kuma suna da fuskar gaggafa. 11 Fukafukansu haka suke, fukafukansu kuma a shimfiɗe suke a sama, domin kowacce halitta nada fiffike biyu da ke taɓa fiffiken halittar, kuma fukafukan biyu sun rufe jikkunansu. 12 Kowanne ɗayansu ya tafi ɗoɗar, domin duk inda ruhu ya jagorance su suje, suna tafiya ba tare da sun juya ba. 13 Game da kamannin rayayyun halittun nan kuwa, bayyanuwarsu na kama da garwashin wuta mai ci, kamar bayyanar cociloli; hasken wuta kuma na kai da komowa tsakanin halittun, kuma akwai haskawar walƙiya. 14 Rayayyun halittun nan suna matsawa da sauri gaba da baya, bayyanarsu kuma kamar walƙiya take! 15 Daga nan sai na dubi rayayyun halittun nan, sai ga wani gargare a ƙasa a gefen rayayyun halittun tare da fuskokinsu huɗu. 16 Wannan shi ne bayyanuwa da tsarin gargarorin; kowanne gargare na kama da dutse mai tamani, dukkan su huɗun kamannin su ɗaya ne; bayyanuwarsu da ƙirarsu sai ka ce gargare mai ratsawa ta wani gargaren. 17 Yayin da suke matsawa, suna tafiya ta kowanne kusurwarsu huɗu, ba tare da sun juya ba yayin da suke tafiya. 18 Zancen gammon gargarensu, masu tsawo ne da kuma ban tsoro, domin gammon gargaren na cike da idanu a kewaye. 19 Duk sa'ad da rayayyun halittan nan suke matsawa, gargarorin na matsawa a gefensu. Sa'ad da rayayyun halittar suka tashi daga duniya, gargarorin suma su kan tashi sama. 20 Duk inda Ruhu zai tafi, sukan tafi, sai gargarorin su tashi a gefensu, gama ruhun rayayyun halittun yana cikin gargarorin. 21 Duk sa'ad da halittun suke matsawa, gargarorin suma suna matsawa; idan kuma halittun suka tsaya cik, gargarorin suma sukan tsaya cik; idan halittun suka tashi daga ƙasa, gargarorin sukan tashi a gefensu, saboda ruhun rayayyun halittun yana cikin gargarorin. 22 A bisa kawunan rayayyun halittun nan akwai kamannin miƙaƙƙen sarari; yana kama da abu mai banmamaki da ƙyalli a miƙe bisa kawunansu sama. 23 A ƙarƙashin sararin, kowanne fukafukan halittun a miƙe suke sak kowanne yana taɓa fukafukan ɗaya rayayyen halittar. Kowannen rayayyen halittar kuma yana da fiffike biyu domin su rufe kansu; kowanne yana da biyu domin ya rufe jikinsa. 24 Daga nan sai naji ƙarar fikafikansu. Kamar ƙarar ruwaye masu yawa. Kamar muryar mai Iko dukka a duk sa'ad da suke matsawa. Kamar ƙarar iskar hadari. Kamar ƙarar rundunar sojoji. Duk sa'ad da suka tsaya cik, sukan saukar da fukafukansu. 25 Sai murya ta zo daga saman sararin sama da kansu duk sa'ad da suka tsaya cik suka kuma sãki fukafukansu. 26 A bisa sararin nan da ke sama da kansu akwai kamannin kursiyi da ke kama da bayyanuwar dutsen tama, a bisa kamannin kursiyin kuma akwai kamannin da ya yi kama da bayyanuwar mutum. 27 Na ga siffa da bayyanuwar ƙarfe mai haskakawa da wuta a cikinsa tun daga bayyanuwar kwankwasonsa har sama; naga kuma daga bayyanuwar kwankwasonsa har zuwa ƙasa sai ka ce bayyanuwar wuta da haske ko'ina kewaye. 28 Kamar bayyanuwar bakangizo cikin giza-gizai a ranar da aka yi ruwa haka bayyanuwarar sheƙin hasken da ke kewaye da shi yake. Wannan kamar bayyanuwarar kamannin ɗaukakar Yahweh ne. Sa'ad da na gani, Na faɗi bisa fuskata, sai na ji murya tana magana.

Sura 2

1 Ya ce mani, "Dan mutum, tashi bisa sawayenka; daga nan zan yi magana da kai." 2 Daga nan, da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya shiga cikina, yasa na tsaya bisa sawayena, na kuma ji shi yana magana da ni. 3 Ya ce mani, "Dan mutum, ina aiken ka zuwa wurin mutanen Isra'ila, ga al'ummai masu tayarwa, da suka tayar mani. - da su da kakanninsu sun yi mani zunubi har ya zuwa yau! 4 Zuriyarsu masu tsaurin fuskoki ne zukatansu kuma kangararru ne. Ina aiken ka wurinsu, kuma za ka ce masu, 'Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya ce.' 5 Ko su saurara ko kada su saurara. Gama su gida ne mai tayarwa, amma a ƙalla za su sani cewa akwai annabi a tsakiyarsu. 6 Kai, ɗan mutum, kada ka ji tsoron su ko maganganunsu. Kada ka ji tsoro, koda yake kana tare da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa koda yake kuma kana zaune da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka damu da irin fuskokinsu, da shike su gida ne mai tayarwa. 7 Amma za ka faɗi maganganuna a gare su, ko su ji ko kada su ji, gama suna cika da tayarwa. 8 Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da nake faɗa maka. Kada kayi tayarwa kamar wannan gidan mai tayarwa. Ka buɗe bakinka kaci abin da Na ke shirin ba ka!" 9 Daga nan Na duba, sai a ka miƙo mani hannu; cikin sa rubutaccen littafi ne naɗaɗɗe. 10 Ya baza shi a gaba na; yana da rubutu cikinsa da bayansa, abubuwan da aka rubuta a kai sune koke-koke da makoki da kuma kaito.

Sura 3

1 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka ci abin da ka samu. Ka ci littafin nan, daga nan ka tafi ka yi magana da gidan Isra'ila." 2 Sai na buɗe bakina, ya kuma ciyar da ni da littafin. 3 Ya ce mani, "Dan mutum, ka ciyar da tunbinka ka kuma ƙosar da cikinka da littafin da Na ba ka!" Sai na ci shi, a cikin bakina yana da zaƙi kamar zuma. 4 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka tafi gidan Isra'ila ka faɗi maganganu na a gare su. 5 Gama ba'a aike ka wurin mutane masu bãƙon harshe ba, ko waɗanda harshensu yake da wahala ba, amma zuwa gidan Isra'ila - 6 ba wurin mutane masu yawa ba da bãƙon harshe ko waɗanda harshensu keda wuya ba, waɗanda ba za ka iya fahimtar kalmominsu ba. Tabbas idan da na aike ka wurinsu, da za su saurare ka. 7 Amma, gidan Isra'ila ba za su yadda su saurare ka ba, gama ba su yadda su saurare ni ba. Gama dukkan gidan Isra'ila masu taurinkai ne masu taurin zuciya kuma. 8 Duba! Na sa fuskarka ta taurare kamar fuskokinsu girarka kuma ta taurare kamar girarsu. 9 Na maida girarka kamar lu'u-lu'u, yafi tsagewar dutse! kada ka ji tsoron su ko ka karaya da irin fuskokinsu, tunda gida ne mai tayarwa." 10 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, dukkan kalmomin dana sanar da kai ka ɗauke su cikin zuciyarka ka kuma ji su da kunnuwanka! 11 Daga nan ka tafi wurin 'yan bauta mutanenka, ka yi magana da su. Ka ce masu, 'Wannan ne abin da Ubangiji Yahweh ya ce,' ko su ji ko kada su ji." 12 Daga nan sai Ruhu ya ɗaga ni sama, a baya na kuma sai na ji babbar muryar girgizar ƙasa: "Albarka ta tabbata ga ɗaukakar Yahweh daga wurinsa!" 13 ƙarar fukafukan masu ran nan ne yayin da suke taɓa junansu, da ƙarar gargarorin da ke tare da su, da ƙarar babbar girgizar ƙasa. 14 Sai Ruhu ya ɗauke ni sama ya tafi da ni, na kuma tafi da ɓacin rai cikin ruhuna da zafin fushi, gama hannun Yahweh yana danne ni da iko! 15 Sai na tafi wurin 'yan bauta a Tel-abib waɗanda suke zama a bakin kogin Keba, na zauna cikinsu har kwana bakwai, zugum cikin mamaki. 16 Daga nan ya kasance bayan kwanaki bakwai ɗin sai maganar Yahweh ta zo gare ni, tana cewa, 17 "Ɗan mutum, Na maida kai mai tsaro domin gidan Isra'ila, domin haka sai ka ji maganar bakina, ka kuma ba su gargaɗi na. 18 Sa'ad da na ce da mugu, 'Hakika za ka mutu' kai kuma ba ka gargaɗe shi ba ko ka yi maganar gargaɗi ga mugu a kan miyagun ayyukansa ba, domin ya rayu - mugun za ya mutu saboda zunubinsa, amma zan biɗi haƙƙin jininsa a hannunka. 19 Amma idan ka gargaɗi mugun, kuma bai juya daga muguntarsa ba ko yabar miyagun ayyukansa ba, zai mutu domin zunubinsa, amma kai za ka ceci ranka. 20 Kuma idan adali ya juya daga adalcinsa ya aikata ba abin da dai-dai ba, kuma na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Saboda ba kagargaɗe shi ba, zai mutu cikin zunubansa, ba kuwa zan tuna da ayyukansa na adalci da ya yi ba, amma zan biɗi haƙƙin jininsa a hannunka. 21 Amma idan ka gargaɗi adalin mutum ya daina yin zunubi shi kuwa bai ƙãra yin zunubi ba, lallai zai rayu tun da shi ke an gargaɗe shi; kai kuma ka ceci ranka." 22 Hannun Yahweh yana kaina a wurin, sai ya ce mani, "Tashi! Ka fita zuwa sarari, a can kuma zan yi magana da kai!" 23 Sai na tashi na fita zuwa cikin sarari, a can ne ɗaukakar Yahweh na tsayawa, kamar ɗaukakar dana gani a gefen Kogin Keba; sai na faɗi a bisa fuskata. 24 Sai Ruhu ya sauko mani ya tsaida ni bisa sawayena; sai ya yi magana da ni, ya ce mani, "Jeka ka kulle kanka cikin gidanka, 25 domin yanzu, ɗan mutum, za su sa igiyoyi a kanka su ɗaureka domin kada ka iya fita cikinsu. 26 Zan sa harshenka ya liƙe wa rufin bakinka, za ka kasa yin magana, ba za ka iya tsauta masu ba, da shi ke su gidane masu tayarwa. 27 Amma sa'ad da na yi magana da kai, Zan buɗe bakinka za ka ce masu, 'Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi,' Wanda ya ji, ya ji, Wanda ya ƙi ji ya ƙi ji, gama su gida ne mai tayarwa!"

Sura 4

1 "Amma kai, ɗan mutum, sai ka ɗaukarwa kanka tubali ka sa a gabanka. Ka sassaƙa birnin Yerusalem a kansa. 2 Daga nan kayi sansani kewaye da shi, sai ka gina kagarai gãba da ita. A kuma tayar da masu kai mata hari, a kuma sa mata sansani kewaye da ita. 3 Daga nan ka ɗaukarwa kanka faifan ƙarfe ka kuma yi amfani da shi a matsayin katangar ƙarfe tsakaninka da birni ka kuma sa fuskarka gãba dashi, gama za a yi masa sansani, kuma kai zaka sa sansanin gãba dashi. Wannan zai zama alama ga gidan Isra'ila. 4 Daga nan, sai ka kwanta a gefen hannunka na hagu sai ka sa zunubin gidan Isra'ila a kansa; za ka ɗauki zunubinsu bisa ga yawan kwanakin da kake kwantawa gãba da gidan Isra'ila. 5 Ni da kaina na sanya maka kwana ɗaya ya wakilci shekara ta hukuncinsu: kwanaki 390! Ta haka nan, za ka ɗauki zunubin gidan Isra'ila. 6 Idan ka gama waɗannan kwanaki, sai ka sake kwanciya a sashin hannunka na dama kuma, gama za ka ɗauki zunubin gidan Yahuda har kwana arba'in. Na sanya maka kwana ɗaya domin shekara guda. 7 Ka sa fuskarka wajen sansanin Yerusalem, da hannunka marar rufi ka yi anabci gãba da ita. 8 Duba! I na sanya maɗaurai a kanka yadda ba za ka juya daga wannan sashi zuwa wancan ba har sai lokacin da ka gama kwanakin sansaninka. 9 Ka ɗaukar wa kanka alkama, bali, wake, acca, gero da maiwa; ka sa su cikin tukunya ɗaya ka yi gurasa da su bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a sashinka. Za ka ci su har kwanaki 390. 10 Abincin da za ka ci zai zama bisa ga awo, shekel ashirin kowacce rana, za ka ci bisa ga lokutan da a ka ƙaiyade kowacce rana. 11 Daga nan za ka sha ruwa, bisa ga aunawa sau shida bisa ga ka'ida za ka sha. 12 Za ka ci a matsayin waina ta bali, amma za ka toya ta a kan idonsu da kãshin da ke fitowa daga jikin mutum!" 13 Gama Yahweh ya ce, "Wato abincin da 'ya'yan Isra'ila za su ci zai zama marar tsabta, a can cikin al'ummai inda na kora su." 14 Amma, Na ce, "Kaito! Ubangiji Yahweh! Ban taɓa ƙazantuwa ba! Ban taɓa cin mushe ba ko abin da namun jeji suka kashe, tun ina matashi har yanzu, kuma ba wani ƙazantaccen nama da ya taɓa shiga bakina!" 15 Sai ya ce mani, "Duba, na baka kãshin shanu maimakon kãshin mutum a kansa za ka shirya abincinka." 16 Ya sake ce mani, "Ɗan mutum! Duba! Ina karya sandar abincin da ke cikin Yerusalem, za su ci abinci suna aunawa cikin juyayi za kuma su sha ruwa lokacin da suke aunawa cikin rawar jiki. 17 Saboda za su rasa abinci da ruwa, kowanne mutum zai dubi ɗan'uwansa da damuwa su kuma lalace saboda laifinsu."

Sura 5

1 "Daga nan kai, Ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi kamar askar mai aski domin kanka, ka aske kanka da gemunka, daga nan ka ɗauki ma'auni ka raba gashin kanka uku. 2 Ka ƙone kashi ɗaya cikin wuta a tsakiyar birnin lokacin da kwanakin yiwa birnin sansani suka cika, ka ɗauki kashi ɗaya na gashin ka buge shi da takobi ko'ina kewayen birnin. Daga nan sai ka watsar da kashi ɗaya a iska, daga nan zan zare takobi in runtumi mutanen. 3 Amma ka ɗibi gashi kaɗan daga cikinsu ka ɗaure su cikin rigarka. 4 Daga nan sai ka ɗebi gashi mafi yawa ka jefa cikin tsakiyar wuta; ka ƙone su cikin wuta; daga nan wuta za ta fito ta shiga dukkan gidan Isra'ila." 5 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, "Wannan ita ce Yerusalem na sanya ta a tsakiyar al'ummai, na kuma kewaye ta da sauran ƙasashe. 6 Amma ta ƙi shari'ata yayin da ta aikata mugunta fiye da yadda sauran ƙasashe suka yi, ta tayarwa umarnaina fiye da ƙasashen da ke kewaye da ita. Mutanen sunƙi hukuntaina ba su kuma yi tafiya cikin farillaina ba." 7 Domin wannan Yahweh ya ce, "Saboda kunfi al'ummai waɗanda ke kewaye daku taurinkai ba ku yi tafiya cikin umarnaina ba kuma ba ku kiyaye dokokina ba ko ma dokokin al'umman da ke kewaye daku," 8 domin wannan Yahweh ya ce, "Duba! nima ina gãba da ke. Zan aiwatar da hukuntai a tsakiyarki domin al'ummai su gani. 9 Zan yi maku abin da ban taɓa yi ba da kuma irin wanda ba zan sake yin irin sa ba, saboda dukkan ayyukan banƙyamarku. 10 Domin wannan a tsakiyarki ubanni za su ci naman 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su ci naman iyayensu, da shi ke zan aikata hukunci a kanku zan kuma watsar da dukkanku da kuka rage ko ina 11 Na rantse da raina - Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - hakika saboda kun tozartar da wurina mai-tsarki da dukkan kayanku na banƙyama da al'amuranku na banƙyama, domin wannan Ni da kaina zan rage yawanku; idona kuma ba zai dube ku da rahama ba, ba kuma zan bar ku ba. 12 Kashi ɗaya cikin ukunku za su mutu da annoba, da yunwa kuma za su ƙare a tsakiyarku. Kashi ɗaya cikin ukunku kuma za su faɗi da kaifin takobi kewaye daku. Sulusin na ukun kuma zan watsar da su a kowanne sashi, in kuma zare takobi in fafare su. 13 Daga nan fushina zai kammala, zan kuma sa zafin hasalata akansu ya huce. Zan gamsu, kuma za su sani cewa Ni, Yahweh na yi magana cikin fushina sa'ad da na gama aikin hasalata gãba da su. 14 Zan maishe ku kango abin raini ga al'umman da ke kewaye daku, a kan idon duk wanda ke wucewa. 15 Hakan nan Yerusalem za ta zama wani abin wulaƙantarwa da ba'a ga mutane, abin gargaɗi da tsoratarwa ga al'ummai da ke kewaye daku. Zan zartar da hukuntai gãba daku cikin fushi da hasala, da tsautawa mai zafi - Ni, Yahweh na furta wannan! 16 Zan aikar da kibau masu zafi na yunwa gãba daku da za su zama dalilin da zan hallaka ku. Zan ƙara maku yunwa zan kuma datse abincin da kuke dogara da shi. 17 Zan aikar da yunwa da bala'o'i gãba daku za ku zama marar 'ya'ya. Annoba da jini za su ratsa ta tsakiyarku, zan kawo takobi gãba daku - Ni, Yahweh na furta wannan."

Sura 6

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka sa fuskarka gãba da tsaunukan Isra'ila ka yi anabci a kansu. 3 Ka ce, "Tsaunukan Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Yahweh! Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan ga tsaunuka da tuddai ga rafuffuka da kwarurruka: Duba! Zan kawo takobi gãba da ku, zan kuma hallaka wurarenku masu daraja. 4 Daga nan bagadanku za su zama kangaye ginshiƙansu za a hallakar da su, zan jefar da gawarwakinku gaban gumakansu. 5 Zan jera gawarwakin mutanen Isra'ila a gaban gumakansu, in warwatsar da ƙasusuwanku wajen bagadanku. 6 Duk inda kuka zauna, biranen za su zama marasa amfani, wuraren bisa kuma za su zama kufai, domin bagadanku su zama kufai su zama kangaye. Daga nan za'a farfashe su kuma za su ɓace, za a datse ginshiƙanku ayyukanku kuma za a shafe su kaf. 7 Matattu za su faɗi a tsakiyarku kuma za ku sani Ni ne Yahweh. 8 Amma zan tsare ringi daga cikin ku, waɗansu kuma za su tsere wa takobi daga cikin al'ummai, sa'ad da aka warwatsar da ku ko'ina cikin ƙasashe. 9 Daga nan su da suka tsira za su tuna da ni cikin al'ummai inda za a kai su bauta, za su tuna yadda zuciyata tayi ƙũna ta wurin zuciyarsu mazinaciya wadda ta juya daga gare ni, ta idanunsu kuma da ke ƙara sasu bin gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu suna duban dukkan muguntar da suka aikata da dukkan ƙazantarsu. 10 Za su sani cewa Ni ne Yahweh. Saboda wannan dalilin Na ce Zan kawo wannan muguntar a gare su. 11 Ubangji Yahweh ya ce: Ka tãɓa hannayenka ka buga ƙafarka! Ka ce, 'Kaito!' saboda dukkan miyagun ayyukan ƙazanta na gidan Isra'ila! Gama za su faɗi ta kaifin takobi da yunwa da annoba. 12 Na nesa za su mutu ta annoba, na kusa zai faɗi ta wurin takobi. Waɗanda suka rage suka rayu za su mutu da yunwa. Ta haka ne zan cika hasalata a kansu. 13 Daga nan za ku sani ni ne Yahweh, sa'ad da matattunsu suka kwanta wurin gumakansu, kewaye da bagadansu, a kan kowanne tudu mai bisa - kan dukkan ƙwanƙoli tsaunuka, da ƙarƙashin kowanne itace mai inuwa kuma da rimi mai kauri - da wurare inda suke ƙona turare ga dukkan gumakansu. 14 Da hannuna zan kai sãra in maida ƙasar kango da kufai, tun daga jeji har zuwa Dibla, ko'ina a dukkan wuraren zamansu. Daga nan za su sani cewa Ni ne Yahweh."

Sura 7

1 Kalmar Yahweh ta zo wurina, cewa, 2 "Kai, Ɗan mutum - Ubangiji Yahweh ya faɗi haka ga ƙasar Isra'ila." 'ƙarshe! ƙarshe ya zo ga iyakoki huɗu na ƙasar. 3 Yanzu ƙarshenki yana kanki, gama ina aikar da fushina a kanki, zan shar'anta ki bisa ga ayyukanki; zan kuma kawo dukkanharamtattun ayyukanki a kanki. 4 Gama idanuna ba za su tausaya maki ba, ba kuma zan keɓe ki ba. Maimakon haka, Zan kawo al'hakin al'amuranki a kanki, haramtattun ayyukanki kuma a cikinki, domin ki sani cewa Ni ne Yahweh. 5 Ubangiji Yahweh ya ce: Bala'i! Bala'i na musamman! Duba, yana zuwa. 6 Lallai matuƙa tana zuwa. Matuƙa ta farka a kanki. Duba, tana zuwa! 7 hukuncinku zai zo maku ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya zo; ranar hallaka ta kusa, tsaunuka kuma ba za su ƙara yin murna ba. 8 Yanzu bada daɗewa ba zan zuba maku hasalata in cika fushina a kanku lokacin da nake hukunta ku bisa ga al'amuranku in kuma kawo dukkan al'hakin ƙazantarku a kanku. 9 Gama idanuna ba za su tausaya ba, ba kuma zan keɓe ku ba. Kamar yadda kuka yi haka zan yi maku; haramtattun ayyukanku za su kasance a tsakiyarku domin ku sani cewa Ni ne Yahweh wanda yake hukuntaku. 10 Duba, ranar! Duba, tana zuwa! hukunci ya fita waje! Sandar tayi fure, girmankai ya yi toho! 11 Tashin hankali ya yi girma zuwa cikin sandar mugunta - babu wani daga cikinsu, ko wani daga cikin taronsu, ko daga cikin wadatarsu, babu wani abu nasu mai muhimmanci da zai dawwama! 12 Lokaci na zuwa; lokaci ya zo kusa. Kada ka bari mai saye ya yi farinciki, ko mai sayarwa ya yi makoki, tunda fushina yana kan dukkan taronsu! 13 Gama mai sayarwa ba zai dawo ƙasar da ya yi sayarwa ba muddan dukkansu suna raye, saboda wahayin game da dukkan taron ba za a sauya ba; kuma saboda zunubansu, ba waninsu da zai ƙarfafa! 14 Sun busa ƙaho sun shirya komai, amma ba bu mai takawa zuwa yaƙi; tunda fushina yana kan dukkan taron jama'ar. 15 Takobi na waje, yunwa kuma da annoba suna cikin ginin. Waɗanda ke cikin saura za su mutu da takobi, yayin da yunwa da annoba kuma za su cinye waɗanda ke cikin birnin. 16 Amma waɗansu za su tsira daga cikinsu, za su gudu zuwa tsaunuka. Kamar kurciyoyin kwarurruwa, dukkansu za su yi makoki - kowanne mutum saboda laifinsa. 17 Kowanne hannu zai zama raunanne kowacce gwiwa kuma za ta zama marar ƙarfi kamar ruwa, 18 za su sa tsummoki, tsoro kuma zai rufe su; kunya za ta kasance a kowacce fuska, saiƙo kuma a dukkan kawunansu. 19 Za su jefar da azurfarsu cikin karafku zinariyarsu kuma za ta zama kamar juji. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Yahweh. Rayukansu ba za su tsira ba, ba za a ƙosar da yunwarsu ba, domin laifofinsu sun zama dalilin tuntuɓe. 20 A cikin taƙamarsu suka ɗauki Kyaun kayan duwatsun adonsa, da su kuma suka yi siffofinsu na gumaka da ƙazantattun abubuwansu. Domin wannan, Ina maida waɗannan abubuwa su zama marasa tsarki a gare su. 21 Daga nan zan bada waɗannan abubuwa a cikin hannun bãƙi a matsayin ganima ga kuma miyagun duniya a matsayin ganima, za kuma su ƙazantar da su. 22 Daga nan zan juyar da fuskata daga gare su sa'ad da suka ƙazantar da ƙaunataccen wurina; 'yan adawa za su shiga su ƙazantar da shi. 23 Kayi sarƙa, saboda ƙasar ta cika da hukuncin jini, birnin kuma na cike da tashin hankali. 24 Domin in kawo ƙasashe mafi mugunta, za su kuma mallaki gidajensu, zan kuma kawo ƙarshen girmankan masu ƙarfi, gama za a ƙazantar da wurarensu masu tsarki! 25 Tsoro zai auko! Za su nemi salama, amma ba za a samu ba. 26 Masifa biye da masifa za ta zo, kuma za a samu jita-jita bayan jita-jita. Sa'an nan za su nemi wahayi daga wurin annabi, amma shari'a za ta lalace daga Firist shawara kuma daga wurin dattawa. 27 Sarki zai yi makoki yarima kuma zai rufe kansa da fargaba, yayin da kuma hannayen mutanen ƙasar makyarkyata cikin tsoro. Bisa ga hanyoyinsu zan aikata masu wannan! Zan hukunta su bisa ga matakinsu har sai sun sani cewa Ni ne Yahweh.'"

Sura 8

1 Ana nan a shekara ta shida cikin wata na shida, a rana ta biyar ga watan, Ina zaune cikin gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, sai hannun Yahweh ya sake saukowa a kaina a wurin. 2 Sai na duba, sai ga alamar wani mai kama da bayyanuwar mutum. Daga bayyanuwar ƙugunsa zuwa ƙasa akwai wuta. Daga kuma ƙugunsa zuwa sama akwai bayyanuwar wani abu mai ƙyalli, kamar ƙarfe mai sheƙi. 3 Daga nan sai ya miƙa abu mai kama da hannu, ya ɗauke ni ta gashin kaina; Ruhun kuma ya ɗaga ni tsakanin duniya da sama, a kuma cikin wahayoyi daga wurin Allah, sai ya kawo ni Yerusalem, zuwa wurin shiga ƙofar arewa ta ciki, inda gunki mai cakuno babban kishi ke tsayawa. 4 Daga nan duba, ɗaukakar Allah na Isra'ila na wurin, bisa ga wahayin da na gani a sarari. 5 Daga nan sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka zuwa arewa." Sai na ɗaga idanuna zuwa arewa, daga arewacin ƙofar da ke bida wa zuwa bagadi, a ƙofar shigar, gunkin kishi ne. 6 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga abin da suke yi? Waɗannan sune haramtattun ayyuka masu girma da gidan Isra'ila ke yi da nufin su sani in tafi nesa da wurina mai tsarki. Amma za ka juya ka ga waɗansu haramtattun ayyukan mafi girma." 7 Daga nan sai ya kawo ni bakin ƙofar farfajiya, sai na duba, sai kuma ga rami a jikin bango. 8 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka yi gini cikin bangon nan" Sai na gina cikin bangon, sai ga wata ƙofa. 9 Daga nan sai ya ce mani, "Je ka ka ga haramtattun ayyukan muguntar da suke yi a nan." 10 Sai na shiga ciki na duba, kuma duba! Akwai kowanne abu mai rarrafe da ƙazantattun bisashe! Kowanne gunki na gidan Isra'ila an sasssaƙa siffarsa a jikin bangon kewaye ko'ina. 11 Dattawa saba'in na gidan Isra'ila suna wurin, Yãzaniya ɗan Shafan kuma na tsaye a tsakiyarsu. Suna tsaye a gaban siffofin, kowanne mutum na riƙe da kaskon ƙona turare a hannunsa yadda ƙanshin girgijen turaren kuma ya hau sama. 12 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga abin da dattawan gidan Isra'ila ke aikatawa a cikin duhu? Kowannesu na aikata wannan a cikin ɓoyayyen wurin ɗakin gunkinsa, gama sun ce, 'Yahweh ba ya ganin mu! Yahweh ya yi watsi da ƙasar." 13 Daga nan sai ya ce mani, "Ka sake juyawa ka ga waɗansu manyan haramtattun ayyuka da suke yi." 14 Gaba kuma sai ya kawo ni wajen ƙyauren ƙofar gidan Yahweh wadda ke gefen arewa, kuma duba! Mata na zaune suna makoki domin Tamuz. 15 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga wannan? Ka sake juyawa za ka ga manyan haramtattun ayyuka fiye da waɗannan." 16 Ya kawo ni cikin farfajiya ta cikin gidan Yahweh, duba kuma! A ƙofar shiga haikalin Yahweh tsakanin harabar da bagadi, akwai maza ashirin da biyar sun juyawa haikalin Yahweh baya fuskokinsu na fuskantar gabas, suna kuma yiwa rana sujada. 17 Sai ya ce mani, Ɗan mutum, ka ga wannan? Wannan ƙaramin abu ne ga gidan Yahuda, su yi waɗannan haramtattun ayyuka da suke yi a nan? Gama sun cika ƙasar da tashin hankali sun sake juyawa kuma sun cakune ni ga yin fushi, suna sanya reshe cikin hancinsu. 18 Ni ma zan yi aiki a cikinsu; Idanuna ba za su tausaya masu ba, ba kuwa zan raga masu ba. Koda za su yi kuka da babbar murya a kunnuwana, Ba zan ji su ba."

Sura 9

1 Sa'an nan sai ya yi kuka da babbar murya a kunnena, ya ce, "Bari matsara su taso zuwa birni, kowanne da makamin hallakarwarsa a hanunsa." 2 Daga nan duba! Mutane shida suka zo daga hanyar ƙofa ta bisa, wadda ke fuskantar arewa, kowanne mutum da makamin yankansa a hanunsa. Akwai mutum ɗaya a tsakiyarsu saye da tufafin linin a jikinsa da abin rubutu a gefensa. Suka shiga ciki suka tsaya wajen bagadi na tagulla. 3 Daga nan sai ɗaukakar Allah na Isra'ila ta hau daga wurin kerubim inda take a dã har zuwa bakin ƙofar gidan. Sai ya kira mutumin da ke saye da tufafun linin wanda yake da kayan rubuta a gefensa. 4 Yahweh ya ce masa, "Ka ratsa ta tsakiyar birnin - ta tsakiyar Yerusalem - ka sa shaida a goshin mutanen da ke nishi da tsaki game da dukkan haramtattun ayyukan da ake yi cikin tsakiyar birnin." 5 Daga nan na ji ya yi magana da sauran ya ce, "Ku ratsa birnin ku bi bayansa ku yi kisa. Kada ku bari idanunku su tausaya, kada kuma ku raga wa kowa. 6 Ko tsoho, ko saurayi, ko budurwa, ko ƙananan yara, ko mata. Ku kashe dukkan su! Amma kada ku kusanci kowanne mutum da ke da shaida a goshinsa. Ku fara daga wurina mai tsarki!" Sai suka fara da dattawa waɗanda ke a gaban gidan. 7 Sai ya ce masu, "Ku ƙazantar da gidan, ku cika harabunsa da matattu. Ku zarce gaba" Sai suka fita waje suka kai wa birnin hari. 8 Yayin da suke kai masa harin, sai na sami kaina ni kaɗai sai na faɗi a fuskata na yi kuka na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh, za ka hallakar da dukkan sauran Isra'ila cikin hasalar fushin da kake zubawa kan Yerusalem?" 9 Sai ya ce mani, "Zunubin gidan Isra'ila da na Yahuda ya ƙasaita ƙwarai. Ƙasar cike take da jini kuma birnin cike yake da ayyukan ƙazanta, tun da suka ce, 'Yahweh ya manta da ƙasar,' kuma Yahweh ba ya gani!' 10 To daga nan, ni ma idanuna ba za su duba da tausayi ba, kuma ba zan raga masu ba. Maimakon haka, zan kawo masu duk alhakinsu a kansu." 11 Duba! Mutumin da ke saye da tufafin linin wanda ke da kayan rubutu a gefensa ya dawo. Ya kawo rahoto ya ce, "Na aiwatar da dukkan abin da ka umarta."

Sura 10

1 Da na duba ta sararin da yake bisan kawunan kerubobin; wani abu ya bayyana a samansu kamar yakutu da bayyanuwa mai kamannin kursiyi. 2 Daga nan Yahweh ya yi magana da mutumin da ke saye da tufafin linin ya ce, "Jeka tsakaningargarorin da ke ƙarƙashin kerubobin, ka cika hannuwanka biyu da garwashin wuta mai zafi daga tsakanin kerubobin ka watsa su bisa birnin." Daga nan mutumin ya tafi ni yayin da nake kallo. 3 Kerubobin suna tsaya a gefen dama na gidan sa'ad da mutumin ya shiga ciki, sai girgije ya cika harabar da ke can ciki. 4 Ɗaukakar Yahweh ta taso daga kerubobin ta tsaya a ƙyauren gidan. ta cika gidan da girgijen, kuma harabar ta cika da hasken ɗaukakar Yahweh. 5 Aka kuwa ji ƙarar fukafukan kerubobin har can wajen harabar, kamar muryar Allah maɗaukaki sa'ad da yake magana. 6 Ana nan kuma, sa'ad da Allah ya umarce mutumin da ke saye da tufafin linin ya ce, "Ka ɗebi wuta daga tsakanin gargarorin da ke tsakanin kerubobin," mutumin ya je ciki ya tsaya a gefen gargare ɗaya. 7 Kerubim ɗaya ya miƙa hannunsa tsakanin kerubobin zuwa wutar da ke tsakanin kerubobin, ya ɗiba ya zuba a hannun wanda ke saye da tufafin linin. Mutumin ya karɓa ya tafi waje. 8 Na kuwa gani a kerubobin wani abu kamar hannun mutum a ƙarƙashin fukafukansu. 9 Saboda haka na duba, sai ga! gargarori huɗu a gefen kerubobin - gargare ɗaya a gefen kowanne kerubim guda - kuma fasalin gargarorin na kamar dutse mai daraja. 10 dukka huɗun fasalinsu dai-dai yake, kamar gargare na gittawa cikin wani gargaren. 11 Sa'ad da suke matsawa, suna tafiya a dukkan shiyyoyi huɗun. kuma ba tare da juyawa ga wata shiyyar ba, Maimakon haka, duk inda kan yake fuskanta, nan suke bin shi. Ba su kuwa juyawa ga wata shiyya sa'ad da suke tafiya. 12 Dukka jikinsu - haɗe da bayansu da hannuwansu da fukafukansu - na rufe da idanuwa, kuma idanuwan sun rufe gargarori huɗun dukka kewaye kuma. 13 Sa'ad da nake saurarawa, gargarorin suna kira, "guguwa." 14 Kowanne ɗayansu na da fuskoki huɗu; fuska ta fari ta Kerubim ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuma ta gaggafa ce 15 Daga nan kerubobin - waɗannan ne hallitu masu rai da na gani ta Kogin Keba - suka taso. 16 Duk sa'ad da Kerubobin suka matsa, gargarorin za su bi su gefensu, kuma duk sa'ad da kerubobin suka ɗaga fukafukansu su tashi daga ƙasa, gargarorin ba su juyewa. Suna dai tsaye a gefensu. 17 Sa'ad da kerubobin suka tsaya cik, gargarorin suma sai su tsaya cik, kuma idan suka tashi sama, gargarorin suma sai su tashi tare da su, gama ruhun halittar mai rai na cikin gargarorin. 18 Sa'an nan ɗaukakar Yahweh ta fita daga ƙyauren gidan ta tsaya a kan kerubobin. 19 Kerubobin suka ɗaga fukafukansu suka tashi daga ƙasa a fuskata sa'ad da suka fita, gargarorin kuma suka yi kamarsu a gefensu. Suka tsaya a bakin kofar shiga ta wajen gabas, ta gidan Yahweh, sai ɗaukakar Allah na Isra'ila ta zo gare su daga sama. 20 Waɗannan ne halittu masu rai dana gani a ƙarƙashin Allah na Isra'ila ta Kogin Keba, shi yasa na sani cewa su keruubobi ne! 21 Kowannen su na da fuskoki huɗu da fukafukai huɗu, da kamannin hannuwan mutum a ƙarƙashin fukafukansu, 22 kuma kamannin fuskokinsu na kama da wadda na gani a ruya a Kogin Keba, kuma kowannen su ya tafi gaba kai tsaye.

Sura 11

1 Sai Ruhun ya ɗago ni sama ya kawo ni ƙyauren gabas na gidan Yahweh, yana kuma fuskantar gabas, a bakin ƙofar akwai mutum ashirin da biyar. Na ga Yãzaniya ɗan Azzu da Felatiya ɗan Benayya shugabanin mutanen, a cikinsu. 2 Allah ya ce mani, "Ɗan mutum, waɗannan ne mutanen da ke ƙirkiro zunubai da kuma yin miyagun shirye-shirye a wannan birnin. 3 Suna cewa, 'Ba yanzu ne lokacin gina gidaje ba, wannan birnin shi ne tukunyar, kuma mu ne naman.' 4 Saboda haka ka yi annabci gãba da su. Ɗan mutum, ka yi annabci." 5 Sai Ruhun Yahweh ya sauko mani ya kuma ce mani, "Ka ce: Ga abin da Yahweh ya ce, "Gidan Isra'ila wannan shi ne abin da kuke cewa; gama na san abin da ke tafiya a zuciyarku. 6 Kun yawaita mutanen da kuka kashe a wannan birnin kuma kun cika karafku da su. 7 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Mutanen da kuka kashe, waɗanda kuka sa jikunansu a tsakiyar UYerusalem, su ne naman, kuma wannan birnin ne tukunyar. Amma za a fitar daku daga tsakiyar wannan birnin. 8 Kun ji tsoron takobi, saboda haka ina tahowa da takobi a kanku - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh. 9 Zan fitar daku daga cikin birnin, in sa ku a hannun bãƙi, gama zan kawo hukunci a kanku. 10 Za ku faɗi ta takobi. Zan hukunta ku a cikin iyakar Isra'ila domin ku sani cewa Ni ne Yahweh. 11 Wannan Birnin ba zai zama tukunyar dahuwarku ba, ko ku zama naman cikinta ba. Zan hukunta ku a kan iyakar Isra'ila. 12 Sa'an nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh, wanda kuka ƙi yin tafiya bisa ga tafarkinsa wanda kuma kuka ƙi aikata umarninsa. Maimakon haka, sai kuka aikata dokokin al'umman da ke kewaye daku." 13 Hakanan kuma sa'ada da nake annabci, Felatiya ɗan Benayya, ya rasu. Sai na faɗi fuskata a ƙasa na yi kuka da murya mai ƙarfi na ce, "Kash, ya Ubangiji Yahweh, za ka hallakar da ragowar Isra'ila ne kakaf?" 14 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 15 "Ɗan mutum, 'yan'uwanka! 'Yan'uwanka! Mutanen danginka da dukkan gidan Isra'ila! Dukkansu ne waɗanda a ka yi magana game da su ta wurin waɗanda ke zama cikin Yerusalem, 'Su na nesa da Yahweh! Wannan ƙasar an bada ita gare mu a matsayin mallakarmu.' 16 Saboda haka ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Koda shi ke na kai su nesa tsakanin al'ummai, kuma na warwatsar da su cikin ƙasahe, duk da haka na zama haikali a gare su na ɗan lokaci ƙaɗan cikin ƙasashen da suka tafi.' 17 Saboda haka ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Zan tattaro ku daga mutane daban-daban, in jera ku daga ƙasashen da kuka warwatse, sai in ba ku ƙasar Isra'ila. 18 Sa'an nan za su je wurin su cire dukkan abin banƙyama da dukkan ayyukan banƙyama daga wancan wurin. 19 Zan ba su zuciya ɗaya, kuma zan sa sabon ruhu a cikin su. Zan ɗauke zuciyar dutse daga jikinsu in ba su zuciyar tsoƙa, 20 domin su yi tafiya cikin tafarkina, za su kiyaye ka'idodina su kuma aikata su. Sa'an nan za su zama mutanena, Ni kuma in zama Allahnsu. 21 Amma ga waɗanda ke tafiya tare da sha'awar abin ƙyamarsu da taƙaicinsu, Zan kawo masu ayyukansu ga kawunansu - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh." 22 Kerubobin suka ɗaga fukafukansu da gargarorinsu da ke a gefensu, ɗaukakar Allah na Isra'ila kuma ta kasance a can sama bisansu. 23 Sa'an nan ɗaukakar Yahweh ta fito daga cikin tsakiyar birnin ta kuma tsaya a tsauni ta gabashin birnin. 24 Ruhun ya ɗago ni ya kawo ni cikin Kaldiya, gun 'yan zaman ɓauta, a wahayi daga Ruhun Allah, kuma wahayin da na gani ya fito daga gare ni. 25 Sai na furtawa masu zaman bautar dukkan abubuwan Yahweh da na gani.

Sura 12

1 Maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 2 "Ɗan mutum, kana zama a cikin gidan tayarwa, inda suna da idanuwan gani amma ba su gani; inda kuma suna da kunnuwan ji amma ba su ji. Saboda su gidan tayarwa ne. 3 Saboda haka kai ma, ɗan mutum, ka shirya kayanka domin zaman bauta, kuma ka tashi da rana a fuskarsu, domin zan sa kaje zaman bauta a fuskarsu daga wurin da kake zuwa wani wurin. Watakila za su fara gani, koda shi ke su gidan tayarwa ne 4 Za ka fitar da kayayyakinka na zaman bauta da rana a fuskarsu; jeka waje da yamma a fuskarsu a hanyar da kowa ke zuwa zaman bauta. 5 Ka huda rami a bango a fuskarsu, kuma ka fita ta wurin. 6 A fuskarsu, ka ɗauki kayayyakinka kan kafaɗarka, ka kawo su waje a cikin duhu. Ka rufe fuskarka, gama lallai ba za ka ga ƙasar ba, tunda na sa ka kamar alama ne ga gidan Isra'ila." 7 Sai na yi hakan, kamar dai yadda aka umarce ni. Na kawo kayan zaman bautata da rana, kuma da yamma na huda rami da hannu a bango. Na fitar da kayana waje a duhun, sai na sa su a kafaɗata na ɗaga sama a fuskarsu. 8 Sai maganar Yahweh ta zo mani da safe, cewa, 9 "Ɗan mutum, ko gidan Isra'ila, gidan tayarwar nan, ba su tambaya, 'me ka ke yi?' 10 Ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan aikin annabcin ya shafe ɗan sarki a Yerusalem ne, da dukkan gidan Isra'ila wanda a cikinsa suke.' 11 Ka ce, 'Ni ne alama a gare ku. Kamar yadda na yi, haka za a yi masu; za su je zaman bauta da zaman talala. 12 Ɗan sarkin da ke a cikinsu zai ɗauki kayansa a kafaɗarsa da duhu, kuma ya fice ta bango. Za su huda bango su fita da kayansu. Zai rufe fuskarsa domin kar ya ga ƙasar da idanuwansa. 13 Zan shimfiɗa ragata a kansa kuma zai kamu a tarkona; sa'an nan zan kawo shi Babila, da ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan su ba. Zai mutu a can. 14 Ta kowacce shiyya kuma zan warwatsar da dukkan waɗanda ke kewaye da shi da za su taimaka masa da dukkan sojojinsa, kuma zan aikar da takobi biye da su. 15 Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, idan na warwatsar da su cikin al'umma na kuma tarwatsar da su ko'ina a ƙasashe. 16 Amma zan bar kaɗan daga cikinsu daga takobin da yunwa da annoba, saboda su bada rohoton dukkan abin ƙyamar da ke cikin ƙasar inda na ɗauke su, domin su sani Ni ne Yahweh."' 17 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 18 "Ɗan mutum, ka ci gurasarka a giggice, ka kuma sha ruwanka da rawar jiki da damuwa. 19 Sa'an nan sai ka ce da mutanen ƙasar, ' Ubangiji Yahweh ya ce haka game da mazaunan Yerusalem, da ƙasar Isra'ila: Za su ci abincinsu da rawar jiki kuma su sha ruwa cikin fargaba, tun da za a washe ƙasar da dukkan abin da ke ciki saboda hargitsin dukkan waɗanda ke zaune a ciki. 20 Domin haka Biranen da ke da mazauna za su zama kufai, kuma ƙasar za ta zama kango; To za ku sani cewa Ni ne Yahweh."'" 21 Karo na biyu kuwa, maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 22 "Ɗan mutum, Mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra'ila da ke cewa, 'Kwanakin na da tsawo, kuma dukka wahayin bai gudana ba'? 23 Saboda haka, ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Zan kawo ƙarshen wannan karin maganar, kuma mutanen Isra'ila ba za su ƙãra amfani da ita ba.' Ka ce masu, 'Kwanakin sun kusato sa'ad da dukkan wahayoyin za su cika. 24 Gama ba za ƙãra samun wahayoyin ƙarya ba ko dũba ta neman suna cikin gidan Isra'ila ba. 25 Gama Ni ne Yahweh! Nakan faɗa, kuma ina aikata abin da na faɗa. Ba za a ƙãra ɓata lokaci a kan batun ba. Gama zan faɗi wannan magana a kwanakinku, gidan tayarwa, kuma tabbas zan aiwatar da shi! - wannan ne Ubangiji Yahweh ke furtawa."' 26 Haka kuma maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 27 "Ɗan mutum! Duba, gidan Isra'ila ya ce, 'Wahayoyin da yake gani na kwanaki da yawa ne daga yanzu, kuma yana annabcin lokutta masu nisa ne.' 28 Saboda haka ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya ce: Maganganuna ba za su ƙãra yin jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta cika - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.

Sura 13

1 Bugu da ƙari, maganar Yahweh ta zo mani, cewa. 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci gãba da annabawan da ke annabci a Isra'ila, kuma ka faɗa wa waɗanda ke annabci daga tsammace-tsammacensu, ' Ku saurari maganar Yahweh. 3 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton wawayen annabawan da ke bin ruhun kansu, amma ba su ga komai ba! 4 Isra'ila, annabawanki sun zama kamar diloli a watsattsun gonaki. 5 Ba ku je wurin tsagogin bango da ke kewaye da gidan Isra'ila domin ku gyara shi ba, domin ku yi tsayayya a yaƙi a ranar Yahweh ba. 6 Mutanen na ganin wahayoyin ƙarya kuma su na yin annabcin ƙarya, waɗanda ke cewa, "Wannan da wancan ne furcin Yahweh." Yahweh bai aike su ba, amma ko kaɗan ba su bar sanya mutane begen saƙonninsu za su zama gaskiya ba. 7 Ba ku yin wahayin ƙarya da annabcin ƙarya, ku da ke cewa, "abu kaza da abu kaza ne furcin Yahweh" sa'ad da Ni kaina ban yi magana ba? 8 Saboda haka Ubangiji Yaweh ya faɗi wannan, 'Domin kun yi ƙarairayi a kan karɓar wahayi - Saboda haka Ubangiji Yahweh ya yi furcin gãba da ku: 9 Hannuna zai yi gãba da annabawa masu wahayoyin ƙarya da annabcin ƙarya. Ba za su kasance a taruwar jama'ata ba, ko a sa su a cikin lissafin gidan Isra'ila ba; Ba za su tafi ƙasar Isra'ila ba. Gama za ku san cewa Ni ne Ubangiji Yahweh! 10 Domin wannan, kuma saboda sun sa mutanena su kauce daga hanya da cewa, "Salama!" sa'ad da babu salama, suna gini a bangon da za su shafa farar ƙasa.' 11 Ka cewa waɗanda ke shafen bangon da farar ƙasar,' zai faɗo ƙasa; za a yi ruwan sama, kuma zan aiko da guguwar da za ta sa ya faɗi, da iska mai ƙarfi da za ta rushe bangon. 12 Duba, bangon zai faɗo. Waɗansu ba su ce maku, "Ina farar ƙasar da kuka shafa wa bangon ba?" 13 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya ce: Zan kawo guguwar iska a fushina, kuma za a samu ambaliyar ruwan sama a hasalata! ƙurar fushina za ta hallaka shi kakaf. 14 Gama zan rushe bangon da kuka shafe da farar ƙasa, kuma zan ragargaza shi har ƙasa in bar ginshiƙan a fili. Domin ya faɗo, kuma ku hallaka a tsakiyarsa. Za ku kuwa sani cewa Ni ne Yahweh. 15 Gama cikin fushina zan hallakar da bangon da waɗanda ke shafa masa farar ƙasa. 16 wato annabawan Isra'ila da ke yin annabci a kan Yerusalem waɗanda kuma ke ganin wahayoyin salama dominta. Amma babu salama!- wannan furcin Ubangiji Yaweh ne."' 17 Saboda haka, ɗan mutum, ka sa fuskarka gãba da 'ya'ya mata na mutanenka da ke annabci daga nasu tunanin, kuma ka yi annabci gãba da su. 18 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton matayen da ke ɗinka layun dabo a dukkan ɓangarorin hannunsu suna kuma yin gyalulluka domin kawunansu da kowanne irin fasali, suna amfani da shi a farautar mutane. Za ku farauci mutanena amma ku ceci ranku? 19 Kun ɓãta ni a cikin mutanena domin a ba ku ɗan danƙin bali da gutsiren gurasa, ku kashe mutanen da bai dace su mutu ba, da kuma barin waɗanda bai dace su rayu ba su rayu, saboda karairayi da kuke yiwa mutanena da ke jinku. 20 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ina gãba da dabo da layun da kuka yi aiki da su domin ku yiwa rayukan mutane tarko kamar tsuntsaye. Hakika zan yayyage su daga hannuwanku; kuma mutanen da kuka cafko kamar tsuntsaye - Zan sake su su tafi. 21 Zan yayyage gyalullukanku na tsafi in ceci mutanena daga hannunku, saboda ka da su ƙara faɗawa a tarkon hannuwanku. Za ku kuwa sani cewa Ni ne Yahweh. 22 Saboda kun karya zuciyar mutum mai adalci da ƙarairayi, koda yake Ni ban yi niyyar karya zuciyarsa ba, kuma domin kun ƙarfafa wa mugu gwiwa domin kar ya juyo daga hanyarsa ya ceci ransa - 23 to ba za ku ƙara ganin wahayoyin ƙarya ko ku ci gaba da yin annabcin ƙarya ba, gama Zan ceci mutanena daga hannunku. Za ku sani cewa Ni ne Yahweh,"'

Sura 14

1 Waɗansu daga cikin dattawan Isra'ila suka zo wurina suka zauna a gabana. 2 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 3 "Ɗan mutum waɗannan mazajen sun ɗauki gumakansu cikin zukatansu sun kuma sa tuntuɓen zunubansu a gaban fuskokinsu. Za su ma roƙe ni wani abu kuwa? 4 Saboda haka ka sanar da wannan gare suka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duk mutumin gidan Isra'ila wanda ya ɗauki gumaka ya sa a zuciyarsa, ko ya sa tuntuɓen zunubansa a gaban fuskarsa, kuma ya zo gun Annabi - Ni, Yahweh, zan amsa masa bisa ga yawan gumakansa. 5 Zan yi wannan domin Zan iya ɗauke gidan Isra'ila daga cikin zukatansu da ke nesa da ni ta dalilin gumakansu.' 6 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila. 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ku tuba ku juyo daga gumakanku! Ku juya fuskokinku baya daga dukkan haramtattun ayyukanku. 7 Domin duk wanda yake daga gidan Isra'ila da duk wanda ke cikin bãƙin da ke zaune a Isra'ila da suka rabu da ni, wanda ke ɗauke da gumaka cikin zuciyarsa ya sa abin tuntuɓe na zunubansa a furkarsa, kuma ya zo gun annabi ya roƙe ni - Ni, Yahweh, zan amsa masa da kaina. 8 Saboda haka zan sa fuskata gãba da mutumin nan in maida shi alama da karin magana, gama zan yanke shi daga tsakiyar mutanena, kuma za ku sani cewa Ni ne Yahweh. 9 Idan a ka ruɗi annabi ya faɗi sãƙo, daga nan Ni, Yahweh, zan ruɗi annabin nan; Zan miƙa hannuna gãba da shi kuma in hallaka shi daga tsakiyar mutanena Isra'ila. 10 Za su ɗauki laifofinsu; laifin annabi zai zama dai-dai da laifin wanda ke zuwa nema daga gare shi. 11 Saboda wannan, gidan Isra'ila ba zai ƙara bijirewa ba daga bi na ko su ƙazamtar da kansu ta wurin bin dukkan laifofinsu. Za su zama mutanena, Ni kuma zan zama Allahnsu - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne,"' 12 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 13 "Ɗan mutum, Idan ƙasa ta yi zunubi gãba da ni ta aikata laifi har Na fitar da hannuna gãba da ita na karya sandar gurasarta, kuma Na aiko yunwa a kanta kuma na datse mutum da dabba daga ƙasar; 14 to ko mutanen nan guda uku - Nuhu da Daniyel da Ayuba - suna cikin tsakiyar ƙasar, za su dai iya ceton ransu ne kawai ta ayyukansu na adalci - wannan furcin Yahweh ne. 15 Idan na aiko miyagun bisashe ta ƙasar na maida ita bakarariya saboda ta zama kufai inda ba mutum da zai iya wucewa saboda bisashen, 16 daga nan ko waɗannan mutum ukun kuma na ciki - Muddin ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - ba za su iya su ceto ko da "ya'yansu maza ko mata ba; Rayukansu ƙadai za su iya cetowa, amma ƙasar za ta zama watsattsiya. 17 Ko idan na kawo takobi gãba da ƙasar na ce, 'Takobi, je ta cikin ƙasar ki datse mutum da dabba daga cikinta, 18 daga nan ko waɗannan mutane ukun suna tsakiyar ƙasar- muddin Ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - ba za su iya su ceto ko da ma 'ya'yansu maza ko mata ba; rayukansu ƙaɗai za su iya cetowa. 19 Ko idan na aiko da annoba gãba da ƙasar nan kuma na zubo fushina gãba da ita ta wurin zubda jini, saboda in datse mutum da bisã, 20 daga nan ko da Nuhu da Daniyel da Ayuba na cikin ƙasar - muddin ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - Ba za su iya su ceto ko da ma 'ya'yansu maza da mata ba; rayukansu ne kawai za su iya cetowa ta wurin ayyukan adalcinsu. 21 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Zan maida abubuwa su fi haka ɓaci tabbas ta wurin aikowa da hukuntaina - yunwa da takobi da namomin jeji, da annoba - gãba da Yerusalem domin in datse mutum da bisã daga cikinta. 22 Duba! duk da haka, Za a bar ragowa a cikinta, waɗanda suka rayu da za su fito da 'ya'ya maza da mata. Duba Za su fita zuwa wurinku, kuma za ku ga hanyoyinsu da ayyukansu sai ku ƙarfafa game da horon da Na aiko a Yerusalem, da a kan komai da na aiko gãba da ƙasar. 23 Waɗanda suka rayu za su ta'azantar da ke sa'ad da kika ga hanyoyinsu da ayyukansu, saboda ku san dukkan waɗannnan abubuwan da na yi gãba da ita, cewa ban yi su a banza ba! wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 15

1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, yaya kuringar inabi ta fi kowanne itace mai rassa da ke kurmi kyau? 3 Mutane na ɗaukar katako daga kuringar inabi su yi wani abu da shi? Ko kuwa su yi maratayi daga gare ta su rataya wani abu a kai? 4 Duba! Idan aka jefa ta cikin wuta kuma idan wutar ta ƙone dukka sassa biyu na ƙarshenta da kuma na tsakiya, za a iya yin wani amfani? 5 Duba! Sa'ad da ta kai ƙarshe, ba za ta iya yin komai ba; tabbas, sa'ad da wutar ta ƙona ta, to ba za ta yi wani abin amfani ba. 6 Domin haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ba kamar itatuwan dazuzzuka ba, Na ba da kuringar inabi ta zama abin ƙonawa ga wuta; Kamar haka zan yi ga mazaunan Yerusalem. 7 Gama zan sa fuskata gãba da su. koda yake sun fito daga wutar, duk da haka wutar ba za ta cinye su ba; da haka za ku sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na sa fuskata gãba da su. 8 Sa'an nan zan maida ƙasar watsattsen kufai domin sun aikata zunubi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 16

1 Maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka sanar da Yerusalem game da haramtattun ayyukanta, 3 ka kuma furta, 'Ubangiji Yahweh faɗi wannan ga Yerusalem: Farkonki da haihuwarki sun faru a ƙasar Kan'ana ne; Mahaifinki Ba'amore ne, mahaifiyarki Bahitiya ce. 4 A ranar haihuwarki, mahaifiyarki bata yanke cibiyarki ba, balle ta tsabtace ki a ruwa ko ta shafe ki da gishiri, ko ta rufe ki da tsumma. 5 Babu idon da ya tausaya maki ya yi wani abu daga cikin waɗannan domin ki, ya ji tausayinki. Aranar da aka haife ki, domin ƙin jininki, an jefa ki waje a fili. 6 Amma na bi ta wurinki, kuma na ga kina motsi cikin jininki; sai Na ce da ke a cikin jininki, "Ki rayu!" Na ce da ke a cikin jininki, "Ki rayu!" 7 Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yawaita kin kuma zama da girma, kika zama abin ƙauna sosai kuma kin kai ga sa kayan ado. Nonnanki sun tsaya tantsan-tantsan, kuma gashin kanki ya yi kauri, koda shi ke ki na tsirara tumɓur. 8 Na bi ta wurin da kike kuma, na kuma gan ki. Duba! lokacin ƙauna ya zo maki, sai na rufe ki da bargo na rufe tsiraicinki. sa'an nan na yi maki rantsuwa na kawo ki ga alƙawari - kika kuma zama tawa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 9 Sai na wanke ki da ruwa, na kuma wanke ki daga jini, sai na shafe ki da mai. 10 Na suturta ki da ɗinkakken tufafi na sa maki takalman fãta a ƙafafunki. Na naɗe ki da linin mai kyau na rufe ki da silki. 11 Biye da haka na yi maki ado da sarƙoƙi masu daraja, sai na sa maki sarƙar hannu, da sarƙa kewaye da wuyanki. 12 Na sa zoben hanci a hancinki, da 'yan kunne a kunnuwanki, da kambi a kanki. 13 Saboda haka an yi maki ado da zinariya da azurfa, kuma an suturta ki da linin mai kyau da silki da ɗinkakkun kaya; kin ci gari mai kyau da zuma da mai, kuma kika zama kyakkyawa, sai kika zama sarauniya. 14 Shahararki ta kai ga al'ummai saboda kyaunki, gama cikakkiya ce a cikin darajar da na ba ki - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 15 Amma kin dogara ga kyaunki, kuma kin yi kamar karuwa saboda shahararki; kin zubo ayyukan karuwancinki ga duk wanda ke wucewa, saboda kyaunki ya zama nasa. 16 Sa'an nan kika ɗauki tufafinki kuma da su kika yiwa kanki masujadai masu ado da launuka daban-daban, a wurin kuma kika yi kamar karuwa. Bai kamata hakan ya faru ba. ko irin wannan abin ya kasance. 17 Kin ɗauki kyawawan kayan adonki na zinariya da azurfa da na ba ki, sai kika yiwa kanki siffofin mazaje, sai ki ka yi da su kamar yadda karuwa ke yi. 18 Kika ɗauki tufafinki da a ka yi aikin ɗinki mai kyau kika rufe su, sai kika ajiye maina da turarena a gabansu. 19 Gurasata na ba ki - wanda aka yi da lallausan gari da maida zuma - kin ajiye su domin kamshi mai daɗi, gama abin da ya faru kenan - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 20 Sa'an nan kuka ɗauki 'ya'yanku maza da mata da kuka haifa mani, kuka kuma yi hadaya da su ga siffofin domin su lanƙwame kamar abinci. Ayyukan karuwancinku ƙaramin abu ne? 21 Kun yanka 'ya'yana kuka sa su a cikin wutar. 22 A cikin dukkan abin ƙyamarku da ayyukan karuwancinku ba ku yi tunani a kan kwanakin kuruciyarku ba, a sa'ad da kuke tsirara tumɓur sa'ad da kuke birgima cikin jininku. 23 Kaito! Kaitonki! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda haka, a kan dukkan wannan muguntar, 24 kin gina wa kanki sãƙon tsafi a kowanne wurin taruwar jama'a. 25 Ki ka gina wurin tsafi a kan kowacce hanya kuma kin wulaƙanta kyaunki, gama kin bada kanki ga kowanne mai wucewa kuma kika ƙara yin ayyukan karuwanci. 26 Kika yi kamar karuwa tare da Masarawa, makwabtanki masu sha'awace-sha'awace, kika kuma aikata ayyukan karuwanci da yawa, ki na ta sani fushi. 27 Duba! Zan cake ki da hannuna in yanke abincinki. Zan miƙa ranki ga maƙiyanki, 'yan matan Filistiyawa, waɗanda suka ji kunyar halinki na lalata. 28 Kin yi kamar karuwa tare da Asiriyawa saboda ba ki ƙoshi ba. Ki ka yi kamar karuwa amma dai ba ki ƙoshi ba. 29 Kin ƙara aikata ayyukan karuwanci da yawa a ƙasar attajiran Kaldiya, kuma ko wannan ma bai ƙosar da ke ba. 30 Yaya ciwon zuciyarki yake - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - cewa za ki yi dukkan waɗannan abubuwan, ayyukan bankunya na karuwanci? 31 Kin gina wurin tsafinki a kan dukkan tituna kuma ki ka sa sãƙon tsafinki a dukkan wurin taruwar jama'a. Duk da haka ke ba kamar karuwa ba ce saboda kin ƙi karbar biya. 32 Ke mazinaciyar mace, kin amince da kwartaye a maimakon mijinki. 33 Mutane na biyan kowacce karuwa, amma ke kina bada ladarki ga dukkan masoyanki kina kuma ba su cin hanci su zo wurin ki daga ko'ina domin ayyukan karuwancinki. 34 Saboda haka akwai bambanci tsakaninki da waɗancan matayen, tun da ba mai zuwa wurinki ya sa ki kwana da shi, a maimakon haka kina biyan su. Babu mai biyan ki. 35 Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Yahweh. 36 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Saboda kin zubo sha'awace-sha'awacenki waje kika kuma buɗe tsiraicinki ta wurin ayyukan karuwanci da dukkan masoyanki da dukkan ƙazaman gumakanki, kuma saboda jinin 'ya'yanki da kika miƙawa gumakanki, 37 saboda haka, Duba! Zan tara dukkan masoyanki da kika sadu da su, dukkan waanda kike so da waɗanda kike ƙi, kuma zan tara su gãba da ke a ko'ina. Zan fallasa tsiraicinki wurinsu domin su ga dukkan tsiraicinki. 38 Gama zan hukunta ki saboda zina da zubda jini, kuma zan kawo maki zubda jinin fushina da shauƙi. 39 Zan bada ke a hannunsu saboda su jefar da sãƙon tsafiinki ƙasa su kuma rurrushe wuraren tsafinki su kuma tuɓe maki tufafinki su ɗauki dukkan kayan adonki. Za su bar ki tsirara tumɓur. 40 Sa'an nan za su tara maki jama'a gãba da ke su jejjefeki da duwatsu, kuma su daddatsa ki da takkubansu. 41 Za su ƙone gidajenki su yi abubuwan hukuntawa da yawa a kanki a gaban mata da yawa, gama zan tsayar da karuwancinki, ba za ki kuma biya masoyanki ba. 42 Sa'an nan ne zan kwantar da fushina a kanki; fushina zai bar ki, gama zan gãmsu, kuma ba zan ƙara yin fushi ba. 43 Saboda ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba kuma kin sa na girgiza da fushi saboda dukkan waɗannan abubuwan, Domin haka, Duba! Ni kaina zan aiko hukunci a kanki domin abin da kika yi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. Ba za ki ƙara karuwanci da dukkan sauran kazamtattun ayyukanki ba? 44 Duba! Duk mai faɗin karin magana game da ke zai ce, "Kamar yadda uwa take, haka ma 'yarta take." 45 Ke ɗiyar mahaifiyarki ce, wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta, kuma ke 'yar'uwar 'yan'uwanki ne waɗanda suka ƙi mazajensu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahitiya ce, kuma mahaifinki Ba'amore ne. 46 Yãyarki Samariya ce 'ya'yanta mata kuma su ne ke zama a Arewa, ƙanwarki kuma ita ce wadda ke zama a kudu da ke, wato Sodom da 'ya'yanta mata. 47 Ba tafiya a hanyarsu da bin halayensu da ayyukansu kawai kika yi ba, amma a dukkan hanyoyinki kin zama fiye da yadda suke. 48 Da dawwamata - wannan furcin Yahweh ne - Yar'uwarki Sodom da 'ya'yanta mata, ba su yi yawan mugunta kamar yadda ke da 'ya'yanki mata suka yi ba. 49 Duba! Wannan ne zunubin 'yar'uwarki Sodom: ta na da kumbura kai a cikin wadataccen jin daɗi da zaman sangarcewa da rashin kulawa da komai. Ba ta ƙarfafa hannun talakawa da masu buƙata ba. 50 Ta zama mai kumbura kai da aikata ayyukan ƙyama a gabana, saboda haka na ɗauke su kamar yadda kuka gani. 51 Ko Samariya bata aikata rabin zunubanki ba; maimakon haka ma, kin yi ayyukan ƙyama da yawa fiye da yadda suka yi, kuma kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kirki saboda dukkan abubuwan ƙyama da kika yi! 52 Ke musamman, kin nuna kunyar kanki; a wannan hanyar kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kyau, saboda laifofin da kika aikata a dukkan hanyoyin banƙyaman nan. 'Yan'uwanki yanzu sun nuna alamar fin ki kyau. Ke musamman, kin nuna kunyar kanki, gama a wannan hanyar kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kyau. 53 Gama zan komo da wadatarsu - wadatar Sodom da'ya'yanta da wadatar Samariya da 'ya'yanta; amma wadatarki zata kasance a cikinsu. 54 A game da waɗannan abubuwan kuwa za ki nuna kunyarki; za a wulaƙanta ki saboda dukkan abubuwan da kika yi, kuma a sa'an nan ne za ki zama mai ta'azantarwa a gare su. 55 Saboda haka 'yar'uwanki Sodom da 'ya'yanta mata za a komo da su kamar yarda suke a dã. Samariya kuma da 'ya'yanta mata za a komo masu da matsayinsu na dã. 56 Ba ki ambato 'yar'uwarki Sodom da bakin ki ba a kwanakin da kike fahariya. 57 kafin muguntarki ta bayyanu. Amma yanzu kin zama abar zargi ga 'ya'ya mata na Idom da kuma dukkan 'ya'ya mata na Filistiyawa kewaye da ita. Dukkan mutanen da ke kewaye na raina ki. 58 Za ki nuna kunyarki da aikin banƙyamarki! wannan furcin Yahweh ne! 59 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan yi da ke yadda kika cancanta, ke da kika raina rantsuwarki ta wurin karya alƙawari. 60 Amma ni da kaina zan tuna da alƙawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki, kuma zan kafa madawamin alƙawari da ke. 61 Sa'an nan ne za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya a sa'ad da kika ƙarɓi yãyarki da ƙanwarki. Zan ba ki su a matsayin 'ya'yanki mata, amma ba saboda alƙawarinki ba 62 Ni da kaina zan ƙulla alƙawarina da ke, kuma za ki san cewa ni ne Yahweh. 63 Saboda waɗannan abubuwan, za ki tuna da komai ki kuma ji kunya, saboda haka ba za ki sake buɗe bakinki ki yi magana ba saboda kunya, sa'ad da na gafarce ki a kan dukkan abin da kika yi - wannan furcin Yahweh ne."'

Sura 17

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, faɗi kacici-kacici da kuma misali ga mutanen Isra'ila. 3 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: Wani babban gaggafa mai manyan fikafikai da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ya je Lebanon ya kama saman kan itacen sida. 4 Ya karya kan tohonsa mafi tsawo ya ɗauko su zuwa ƙasar Kan'ana; ya shuka su a birnin fatake. 5 Sai kuma ya ɗauki wani iri na ƙasar ya dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa kamar itacen warɗi. 6 Sai ya yi toho ya zama kuringa mai yaɗuwa har ƙasa. Rassansa suka tanƙwasa wajensa, saiwoyinsa suka kama ƙasa sosai. Domin haka ya zama kuringa ya yi rassa da toho. 7 Amma akwai wani babban gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuringa ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen gaggafan, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajensa tun daga inda aka dasa ta domin ya rika yi ma ta ban ruwa. 8 An dasa ta a wuri mai kyau da danshi inda akwai ruwa da yawa domin ta yi rassa ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kuringar inabi ta ƙwarai.' 9 Ka cewa mutanen, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: Ko za ta wadatu? Ba za a iya cire ta a kuma ɗebe 'ya'yanta domin kada su yi yaushi, kuma dukkan ganyayenta masu kyau su yanƙwane ba? Babu wani abu ko mutane masu yawa da a ke buƙata da su cire ta daga jijiyoyinta. 10 To duba! bayan an sake dasa ta, za ta sake yin girma? Ba za ta yanƙwane ba idan iskar gabas ta hura ta? Babu shakka za ta yanƙwane ga baki ɗaya daga tushenta.'" 11 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 12 "Ka yi magana da 'yan tawayen gidan, 'Ba ku san mene ne waɗannan abubuwa ke nufi ba? Duba! Sarkin Babila ya zo Yerusalem ya kuma tafi da sarkinta da yarimanta ya kai su zuwa gare shi Babila. 13 Sai ya ɗauki wani daga zuriyar sarauta, ya yi alƙawari da shi, ya kuma ɗauki rantsuwa da shi. Ya ɗauke mutane na ƙasar masu iko, 14 domin mulkin ya zama da rauni har ƙasar ta kasa ɗaga kanta. Ta wurin kiyayye alƙawarinsa ƙasar za ta tsira. 15 Amma sarkinYerusalem ya yi masa tawaye ta wurin aikawa da jakadai zuwa Masar domin a ba shi dawakai da sojoji. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin waɗannan abubuwa zai tsira? Idan ya karya alƙawari, zai iya tsira? 16 Da dawwamata -wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - babu shakka zai mutu a cikin ƙasar sarki wanda ya naɗa shi sarauta, sarkin da ya rena rantsuwarsa, wanda kuma ya karya alƙawarinsa. Zai mutu a tsakiyar Babila. 17 Fir'auna da sojojinsa masu ƙarfin yaƙi da kuma jama'arsa masu yawa domin yaƙi ba za su tsare shi ba a wannan yaƙin, sa'ad da Babilawa suka gina hasumiyoyi da kagarai don su kashe rayuka masu yawa. 18 Gama sarkin bai cika rantsuwar alƙawarinsa ba. Duba ya miƙa hannunsa ga yin alƙawari duk da haka ya aikata dukkan waɗannan abubuwa. Ba zai kuɓuta ba. 19 Domin haka ni Ubangiji Yahweh na faɗi wannan: Da dawwamata, ba rantsuwata da alƙawarina ya rena ya kuma karya ba? Saboda ha ka zan ɗora hukuncinsa a kansa! 20 Zan kafa masa tarko in kama shi, kuma za a kama shi a tarkon farautata. Sa'an nan zan kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda cin amana da kuma tayawar da ya yi mani! 21 Dukkan 'yan gudun hijira cikin sojojinsa za a kashe su da takobi, sauran da suka ragu za a watsar da su ko'ina. A sa'an nan ne za su sani cewa Ni ne Yahweh; Na furta wannan zai faru." 22 Ubangjji Yahweh ya faɗi wannan, 'Saboda haka ni kaina zan cire toho a kan itacen sida mai tsawo, zan kuma sake dasa shi daga sashen jikin rassansa. Zan karye shi, ni da kaina kuma zan dasa shi a tsauni mai tsayi. 23 Zan dasa shi a kan tsaunukan Isra'ila domin ya fito da rassa, ya bada 'ya'ya, ya kuma zama itacen sida na gaske saboda kowanne tsuntsu mai fiffike ya zauna a ƙarƙashinsa. Za su yi sheƙa a cikin inuwar rassansa. 24 Sa'an nan dukkan itatuwan jeji za su sani cewa Ni ne Yahweh. Na kan kawo manyan itatuwa ƙasa sa'an nan in tada ƙananan itatuwa sama. Zan sa ɗanyen itace ya bushe in kuma sa busashen itace ya zama ɗanye. Ni ne Yahweh, Na furta wannan zai faru; na kuma yi shi.

Sura 18

1 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni, cewa, 2 "Me kuke nufi, ku da kuka yi amfani da wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa, 'Mahaifa sun ci 'ya'yan inabi masu tsami, hakoran 'ya'yansu kuma sun dakushe'? 3 Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba za a ƙara samun wani dalili da za ka sake amfani da wannan karin magana a Isra'ila ba. 4 Ga shi! Kowanne rai nawa ne - ran mahaifi duk da na ɗan, dukka nawa ne! Wanda ya yi zunubi shi zai mutu! 5 Me za a ce a kan mutum wanda yake shi adali ne yana kuma aikata shari'a da adalci-- 6 idan ba ya cin abinci a kan tsaunuka ko ya sa idanunsa a kan allolin da ke gidan Isra'ila, bai kuma kwana da matar maƙwabcinsa ba, ko ya Kwana da mace a lokacin hailarta, wannn mutum adali ne? 7 Me za a ce a kan mutum wanda ba ya ƙuntatawa kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace amma ya kan bada abinci ga mayunwanci, yakan ba huntu tufa, wannan mutum adali ne? 8 Me za a ce da mutumin da ba ya bada bashin kuɗi da ruwa; ko tare da wani ƙari a kan abin da ya sayar? Haka yake ce da shi yana goyon bayan gaskiya a tsakanin masu gaskiya, yana kuma tabbatar da adalci a tsakanin mutane. 9 Amma idan mutumin yana tafiya cikin farillaina yana kuma bin ka'idodina da gaskiya, daga nan alƙawarin wannan mutum mai adalci shi ne: hakika zai rayu! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 10 Amma da a ce yana da ɗa wanda ya zama ɗan fashi mai kisankai yana kuma yin waɗannan abubuwa masu yawa kamar yadda a ka nuna su a nan, 11 koda mahaifinsa ba ya yin ɗaya daga waɗannan abubuwa, amma yana cin abinci a kan tsaunuka ya kuma kwana da matar maƙwabcinsa, me za a ce game da shi? 12 Wannan mutum yana cin zalin matalauta da masu buƙata, yana kuma yin ƙwace da fashi, ba ya mayar da abin da a ka jinginar masa, yana bautawa gumaka yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama, 13 yana bada rancen kuɗi da ruwa, yana cin riba ta fitar hankali a kan abin da ya sayar, shin wannan mutum zai rayu? Babu shakka ba zai tsira ba! Lallai ne zai mutu kuma alhakin jininsa yana a kansa domin ya yi munanan abubuwa. 14 Amma idan akwai mutum da ya haifi ɗa, kuma ɗan nasa ya ga dukkan zunuban nan da mahaifinsa ya yi, koda ya gan su, amma shi bai yi waɗannan abubuwa ba. 15 Wannan ɗa bai ci abinci a kan tsaunuka ba, bai kuma sa idanunsa ga gumakan gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, me za a ce game da shi? 16 Wannan ɗa bai ci zalin kowa ba, ko ya ƙarbi jingina, ko ya saci wasu abubuwa, amma a maimakon haka yana bada abincinsa ga mayunwaci, yana ba huntu tufafi. 17 Wannan ɗan ba ya zaluntar kowa ko ya bada bashi da ruwa ko kuma ya ci ƙazamar riba a kan bashin, amma yana bin ka'idodina, yana kuma tafiya bisa ga farillaina; wannan ɗa ba zai mutu ba saboda zunubin mahaifinsa: Lallai za ya rayu. 18 Mahaifinsa kuwa, da yake ya ƙuntatawa wasu ta wurin zaluntarsu, ya yiwa ɗan'uwansa ƙwace, ya kuma aikata abubuwa marasa kyau a cikin mutanensa - zai mutu saboda muguntarsa. 19 Amma kun ce, 'Me ya sa ɗa ba zai ɗauki laifin mahaifinsa ba?' Domin ɗan ya bi shari'a da adalci kuma ya bi dukkan umarnaina; ya yi su dai-dai. Babu shakka za ya rayu! 20 Shi wanda ya yi zunubi, shi ne wanda zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki laifin mahaifinsa ba, haka nan mahaifi ba zai ɗauki laifin ɗansa ba. Adalcin wanda ya yi dai-dai ai nasa ne, muguntar azzalumi zata kasance a kansa. 21 Amma idan mugu ya juya daga dukkan zunubansa wanda ya aikata ya kiyaye umarnaina ya bi shari'a da adalci, lallai za ya rayu ba zai mutu ba. 22 Dukkan muguntar da ya aikata ba za a neme su a kansa ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi. 23 Ina murna da mutuwar mugu ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba juyowa daga muguwar hanyarsa ba domin ya rayu? 24 Amma idan adalin mutum ya bar yin adalcinsa, ya aikata haramtattun ayyuka kamar dukkan haramtattun ayyuka waɗanda wannan mugun mutum ya aikata, daga nan sai ya rayu? Dukkan adalcin da ya aikata ba za a tuna da su ba idan ya ci amanata da laifin da ya aikata. To zai mutu a cikin zunuban da ya aikata. 25 Amma kun ce, 'Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce!' Ku ji ya ku gidan Isra'ila! Hanyata ba dai-dai ba ce? Ashe ba hanyarku ce ba dai-dai ba? 26 Sa'ad da mutum adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda su, zai mutu a cikin muguntar da ya aikata. 27 Amma idan mugun mutum ya bar muguntar da ya yi ya zo ya aikata gaskiya da adalci, za ya rayu. 28 Domin ya gani kuma ya bar dukkan laifofin da ya aikata. Babu shakka za ya rayu, ba zai mutu ba. 29 Amma gidan Isra'ila suka ce, 'Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce! Gidan Isra'ila yãyã hanyata ta zama ba dai-dai ba? Ai hanyarku ce ba dai-dai ba. 30 Saboda haka zan shar'anta kowanne mutum a cikinku gwargwadon ayyukansa, ya gidan Isra'ila! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. Ku tuba daga dukkan muguntarku domin kada su zamar maku dalilin hallaka. 31 Ku rabu da dukkan laifofin da kuka aikata; ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon ruhu. Me ya sa za ku mutu, gidan Isra'ila? 32 Gama ba na murna da mutuwar wanda ke mutuwa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda haka sai ku tuba domin ku rayu!"

Sura 19

1 "Yanzu kai, sai ka yi makoki a kan shugabanin Isra'ila 2 ka ce, 'Wace ce mahaifiyarka? Zakanya, tana zaune tare da ɗan zaki; a cikin tsakiyar 'yan zakoki, ta yi renon 'ya'yanta. 3 Ita ce ta goyi ɗaya daga cikin 'ya'yanta ya zama ɗan zaki wanda ya koyi kamun nama, har ya cinye mutane. 4 Sai al'ummai suka ji labarinsa. Sai aka kama shi cikin tarkonsu, suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar. 5 Daga nan ta ga cewa koda yake ta jira dawowarsa, sa begenta a kansa yanzu ya ƙare, sai ta ɗauki ɗaya daga cikin 'ya'yanta, ta goye shi ya zama sagari. 6 Wannan sagari yana ta kai da kawowa a cikin zakoki. Ya zama sagari yana kuma koyan kamun nama; ya cinye mutane. 7 Ya lalatar da kagarunsu ya kuma maida biranensu kufai. ƙasar da mazaunan cikinta an bar su saboda jin rurinsa 8 Amma al'ummai suka kafa masa tarko daga kowanne waje; suka baza masa tarunsu a kansa. Suka kama shi cikin tarkunansu. 9 Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka kawo shi ga sarkin Babila. Suka kawo shi cikin matsaran wurare domin kada a ƙara sake jin muryarsa a kan tsaunuka Isra'ila. 10 Mahaifiyarka tana kamar kuringar inabi da aka dasa a cikin jininka a gefen ruwa. Ta yi 'ya'ya da rassa da yawa saboda isasshen ruwa. 11 Tana da rassa masu ƙarfi da a ke amfani da su domin sandunan masu mulki, tsayinta zuwa sama da dukkan rassan, ta yi tsayi sosai daga nesa ana iya hangen ganyenta. 12 Amma aka tumɓuke kuringar inabin da fushi aka jefar da ita a ƙasa, iskar gabas ta busar da ita. Rassanta masu ƙarfi suka kakkarye suka bushe, wuta kuwa ta cinye su. 13 Yanzu an dasa ta a cikin jeji, cikin busasshiyar ƙasa mai ƙishi da fari. 14 Sai wuta ta fito daga manyan rassanta ta kuwa cinye 'ya'yanta, babu reshe mai ƙarfi a kanta, babu sandar da zan yi mulki.' Wannan makoki ne, kumaza a raira shi a matsayin makoki."

Sura 20

1 Ya zamana a kan shekara ta bakwai, a rana ta goma ga watan biyar, sai dattawan Isra'ila suka zo domin su yi roƙo a wurin Yahweh suka kuma zauna a gabana. 2 Daga nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 3 "Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Kun zo ku yi roƙo a wurina? Da dawwamata, ba za ku taɓa tuntuɓa ta ba! -wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.' 4 Za ka shar'anta su? Za ka shar'anta, ɗan mutum? Bari su san haramtattun ayyukan da ubanninsu suka aikata. 5 Ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: A ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna na rantse wa zuriyar gidan Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su cikin ƙasar Masar, sa'ad da na ta da hannun rantsuwa a gare su. Na ce, "Ni ne Yahweh Allahnku"- 6 a wannan rana na ta da hannuna na rantsuwar alƙawari a gare su cewa zan fito da su daga ƙasar Masar zuwa cikin ƙasar dana zaɓa dominsu. Mai malalowa da madara da zuma; tana da abubuwa masu kyau da babu irinsu a dukkan ƙasashe. 7 Na ce da su, "Bari kowanne ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama daga idanunsa, da gumakan Masar. Kada ku ƙazantar da kanku; Ni ne Yahweh Allahnku." 8 Amma sun yi mani tawaye, ba su da niyyar sauraro na. Kowanne mutum ya ƙi watsi da abubuwan banƙyama daga idanunsa ko ya rabu da gumakan Masar, sai na shirya zan zubo masu da fushina domin in cika hasalata a cikinsu a kuma tsakiyar ƙasar Masar. 9 Amma saboda sunana ban yi haka ba a idanun al'ummai da suke zama a cikinsu. Na sanar da kaina a gare su, a idanunsu, ta wurin fito da su daga ƙasar Masar. 10 Sai na fitar da su daga ƙasar Masar na kawo su cikin jeji. 11 Sa'an nan na ba su farillaina na sa su san ka'idodina a gare su, waɗanda idan mutum ya kiyaye su zai rayu. 12 Na kuma ba su Asabatai a matsayin alama tsakanina da su, domin kuma su sani cewa Ni ne Yahweh wanda ke tsarkake su. 13 Amma gidan Isra'ila suka tayar mani a cikn jeji. Suka ƙi su yi tafiya cikin farillaina; maimakon haka, sai suka ƙi ka'idodina, waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu idan ya yi biyayya da su. Sun ɓata Asabataina ƙwarai, saboda haka na ce zan zubo masu da fushina a cikin jeji domin in ƙarar da su. 14 Amma sabili da sunana ban yi haka ba saboda kada a saɓi sunana a idanun al'ummai, waɗanda a kan idanunsu ne na fitar da su daga ƙasar Masar. 15 Sai na kuma tada hannuna na rantse masu a cikin jeji ba zan kai su cikin ƙasar da na ba su ba, ƙasar da ta ke cike da yalwar madara da zuma, wadda tafi kyau a cikin dukkan ƙasashe. 16 Nayi rantsuwa a kan wannan domin sun ƙi ka'idodina kuma sun ƙi yin tafiya cikin farillaina, sun ɓata Asabataina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumakai. 17 Amma na kawar da idanuna daga hallakasu ban kuma hallakar da su a cikin jeji ba. 18 Sai na ce da 'ya'yansu a jeji, "Kada ku yi tafiya a kan farillan ubanninku; ko ku kiyaye sharuɗɗansu ko ku ɓata kanku da gumakansu. 19 Ni ne Yahweh Allahnku, ku yi tafiya a kan farillaina, ku kuma kiyaye ka'idodina, ku yi biyayya da su. 20 Ku kiyaye Asabataina da tsarki domin su zama alama tsakanina da ku, domin ku sani cewa Ni ne Yahweh Allahnku." 21 Amma 'ya'yansu maza da mata suka tayar mani, ba su yi tafiya a cikin farillaina ko su kiyaye ka'idodina ba, ta haka idan mutum ya yi biyayya da su zai rayu. Sai kuma suka ɓata Asabataina, domin haka na yi tunani zan zubo masu da fushina a kansu in kuma huce fushina a kansu a jeji. 22 Amma na yi hakuri sabili da sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban idanun al'ummai waɗanda a idanunsu ne na fito da Isra'ilawa. 23 Ni da kaina na ɗaga hannuna bisa na rantse masu a jeji, zan warwatsar da su cikin al'ummai in kuma raba su a sauran ƙasashe. 24 Na yi shawara zan yi wannan domin sun ƙi yin biyayya da ka'idodina, sun kuma ƙi bin farillaina, sun lalata Asabar ɗina. Idanuwansu na mamarin bauta wa gumakan kakanninsu. 25 Sai kuma na ba su farillai waɗanda ba su da kyau, da ka'idodi marasa amfani da ba za susa su rayu ba. 26 Na furtasu ƙazantattu ta wurin kyaututtukansu - sunyi hadayunsu na kowanne ɗan fãri daga mahaifa sunsa su ratsa ta cikin wuta - domin in cika su da fargaba su kuma sani cewa Ni ne Yahweh!" 27 Saboda haka, ɗan mutum, yi magana da gidan Israila ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wannan kuma ubanninku suka saɓe ni ta wurin rashin aminci a gare ni. 28 Sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, daga nan kuma dukkan sa'ad da suka hango wani tudu da itace mai ganye, sai su miƙa hadayunsu, suka tsokane ni ta wurin baye-bayensu, a wurin kuma suka ƙona turare mai ƙanshi da zuba baye-bayensu na sha. 29 Daga nan na ce da su, "Wanne wurin ne wannan da kuke miƙa baye-baye a can?" Domin haka aka kira sunan wurin Bama har zuwa wannan rana.' 30 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Me ya sa kuka ƙazantar da kanku da hanyoyin ubanninku? To me ya sa kuke haka kamar karuwai, ku na neman abubuwan banƙyama? 31 Duk sa'ad da ku ke miƙa kyaututtukanku - kuma duk sa'ad da kuke sanya 'ya'yanku maza su bi ta cikin wuta - har ya zuwa wannan rana kuna ƙazantar da kanku ta wurin dukkan gumakanku. To me ya sa zan barku ku neme ni, gidan Isra'ila? Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba zan bari ku neme ni ba. 32 Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku ba zai faru ba. Kuka ce, "Bari mu zama kamar sauran al'ummai, kamar dangogin sauran ƙasashe waɗanda ke bauta wa katako da dutse." 33 Da dawwamata - wannan furcin Yahweh ne - tabbas zan yi mulki a bisan ku da hannu mai ƙarfi, da ɗagaggen damtse, da fushina zan zubo a kanku. 34 Zan fitar da ku daga sauran mutane zan kuma tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsar da ku. Zan yi wannan da ikona ta wurin fushina mai zafi. 35 Sa'an nan zan kawo ku cikin jejin mutane, a wurin ne zan yi maku shari'a fuska da fuska. 36 Kamar yadda na yi wa ubanninku shari'a a jeji a ƙasar Masar, haka nan kuma zan yi maku shari'a - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 37 Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sandata, in kuma sa ku yi biyayya da abubuwan da alƙawari ya wajabta. 38 Zan fitar da 'yan tawaye daga cikinku da waɗanda ke yi mani laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune kamar bãƙi, gama ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Sa'an nan ne za ku sani cewa Ni ne Yahweh. 39 To ku, gidan Israila, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: kowannen ku zai tafi wurin bautar gukinsa. Ku bauta ma sa tun da ya ke ba za ku saurare ni ba, amma ba za ku sake ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku. 40 Gama a kan dutsena mai tsarki, a bisa ƙwanƙolin dutsen Israila--wannan furcin Yahweh ne--dukkan gidan Israila za su bauta mani a ƙasar. Zan yi murna in bukaci hadayunku a wurin, da kuma nunar 'ya'yan farin gandunku na dukkan abubuwanku masu tsarki. 41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fito da ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsar da ku. Zan nuna kaina mai tsarki a cikinku domin sauran al'ummai su gani. 42 Gama idan na kawo ku a ƙasar Isra'ila, a ƙasar da na ɗaga hannuna sama na rantse zan bada ita ga ubanninku, za ku sani cewa Ni ne Yahweh. 43 A nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da dukkan ayyukanku da kuka ɓata kanku da su, za ku ji ƙyamar kanku a idanunku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata. 44 Za ku sani cewa Ni ne Yahweh sa'ad da na yi maku wannan saboda sunana, ba kuma saboda gurɓatattun ayyukanku ba, ya gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'" 45 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa. 46 "Ɗan mutum, ka fuskanci ƙasashen kudu, ka yi maganar gãba da kudu; ka yi annabci a kan kurmin Negeb. 47 Ka cewa kurmin Negeb, 'Wannan furcin Yahweh ne - Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba, zan kunna wuta a cikinka. Za ta kuwa cinye kowanne ɗanyen itace da kowanne busashen itace da ke cikinta. Ba za a iya kashe harshen wutar ba, kowacce fuska daga kudu da arewa za su ƙone. 48 Gama dukkan masu rai za su sani cewa Ni ne Yahweh idan na sa wutar, ba kuma za a iya kashewa ba. 49 Sai na ce, "Ya Ubangiji Yahweh, suna cewa da ni, wannan ba maganar misalai kawai yake yi ba?'"

Sura 21

1 Sai maganar Yahweh ta zo ga gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka fuskanci Yerusalem, ka yi maganar gãba da masujadarta; ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila. 3 Ka ce da ƙasar Isra'ila, 'Yahweh ya faɗi wannan: Ina gãba da ita! Zan zare takobina daga cikin kubanta in datse adalin mutum da mugun mutum daga cikinta! 4 Da yake ni zan daddatse adalai da mugaye daga gare ki, takobina zata fito daga cikin kubenta gãba da dukkan mutane daga kudu da kuma arewa. 5 Dukkan mutane kuwa za su sani Ni, Yahweh, na zare takobina daga kubenta. Ba kuwa za a sake mayar da ita a kubenta ba!' 6 Kai kuma, ɗan mutum, sai ka yi nishi da ajiyar zuciya yayin da ƙugunka ya karye! cikin ɗacin rai kayi nishi a gaban idanunsu! 7 Idan har za su tambaye ka, 'Donme ya sa kake nishi?' Sai ka ce masu, 'Saboda labarin abin da ke zuwa, domin kowacce zuciya za ta narke, kuma kowanne hannu zai yi lakwas! Kowanne ruhu zai some, kuma kowace gwiwa zata malale kamar ruwa. Duba! Abin yana zuwa kuma zai kasance kamar haka! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'" 8 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 9 "Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji ya faɗi haka: "Ka ce Takobi! Takobi! Za a wãsa ta sosai a kuma goggoge ta! 10 Za a wãsa ta domin a yi babban kisa, an goge ta domin ta yi walwal kamar walƙiya! Shin mũyi murna a kan sandar girma ta ɗana? Takobi mai zuwa na gãba da kowacce sanda! 11 Saboda haka za a bada takobin a goge ta, sa'an nan a cafke ta da hannu! Takobin an wãsa ta an kuma goge ta za a kuma bada ita a hannun wanda ke yin kisa!""' 12 Ɗan mutum ka yi kiran neman taimako da makoki! Gama takobi ta zo ta yi gãba da mutanena! Ta na gãba da dukkan shugabannin Isra'ila. An bada su ga takobi tare da mutanena. Saboda haka, ka buga cinyarka! 13 Gama akwai gwaji, amma idan sandar girman bata daɗe ba fa? - wannan furcin Yahweh ne. 14 Yanzu kai, ɗan mutum, ka yi annabci ka buga hannuwanka biyu tare, don takobi zata kai hari har sau uku! Takobi domin waɗanda za a yanka! Ita ce takobin da zata datse mutane da yawa, za a yi masu gunduwa-gunduwa a ko'ina! 15 Domin a narkar da zukatansu a kuma ruɓanya faduwarsu, na aika da takobi domin yanka a ƙofofinsu. Ah! An yi ta kamar walƙiya, an cafko ta domin yanka! 16 Ke, takobi! ki sara dama! ki kuma sara hagu! Ki kuma je duk inda kika juya fuskarki. 17 Gama ni ma zan buga hannuwana biyu, Sa'an nan kuma zan kwantar da fushina, Ni, Yahweh na furta haka. 18 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni, cewa, 19 "Yanzu kai, ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu domin takobin sarkin Babila ta zo. Hanyoyin biyu kuwa za su fara a ƙasar, alama kuma za ta nuna ɗaya daga ckinsu da ke kaiwa zuwa birnin. 20 Ka kuma sa alamar ɗaya hanyar domin sojojin Babila da za su zo Rabba, birnin Ammonawa. Ka kuma sa ɗaya alamar ta kai sojoji Yahuda da kuma birnin Yerusalem, wadda aka katange. 21 Gama sarkin Babila zai tsaya a mararrabar hanyoyi, inda hanyar ta rabu biyu, domin ya yi tsãfi. Yana girgiza waɗansu kiɓau yana kuma neman bayani daga waɗansu gumaka zai kuma binciki hanta. 22 A hannun damarsa zai riƙe wani abun sihiri game da Yerusalem, zai kafa mata dundurusai, ya buɗe bakinsa domin ya bada umarnin yanka, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta ya kuma gina mahaurai da gina hasumiyoyin sansani. 23 Zai kasance kamar abin banza ne a idanuwan waɗanda suke a Yerusalem, waɗanda suka rantse ga Babiloniyawa! Amma sarkin zai zarge su da karya yarjejeniyarsu domin mamaye su! 24 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Saboda kun sa a tuna da laifinku, kuka kuma sa a bayyana kurakuranku, domin a ga zunubanku a dukkan ayyukanku - saboda kun yi haka za a kame ku a hannu. 25 Kai kuma, ƙazantacce da mugun shugaban Isra'ila, wanda ranar hukuncinsa ta zo, wanda kuma lokacin aikata laifofinsa ya zo karshe, 26 Ubangiji Yahweh ne ya faɗi haka zuwa gare ka: Ka cire rawani ka kuma cire kambi! Abubuwa ba za su sake zama dai-dai ba! A ɗaukaka marasa martaba a kuma ƙasƙantar da masu girmankai! 27 Kufai! Kufai! Zan maida ita kufai! ba za a komar da ita ba, har sai shi wanda aka sa ya zartar da hukunci ya zo. 28 To Kai, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan ga mutanen Ammonawa a kan zuwan kaskancinsu: Takobi! an zare takobi! An wãsa ta domin yanka domin ta lanƙwame, haka zata zama kamar walƙiya! 29 Annabawa kuma suna ganin holoƙan wahayoyi domin ku, sa'ad da suke yin bukukuwan addini domin su zo maku da karairayi, wannan takobin zata kwanta a wuyan mai mugunta wanda aka kusan kashewa, wanda ranar hukuncinsa ta zo wanda kuma lokacin zunubinsa ya kusa ƙarewa. 30 Maida takobi a cikin kubenta. A wurin da aka hallice ka, a cikin ƙasarka ta ainihi, zan hukunta ka! 31 Zan zubo da hasalata a kanka! Zan kunna wutar fushina gãba da kai in kuma sa ka a cikin hannun mugayen mutane masu dabarar hallakarwa! 32 Za ka zama abincin wuta! Jininka zai kasance a tsakiyar ƙasar. Ba za a tuna da kai ba, gama Ni, Yahweh na furta wannan!'"

Sura 22

1 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa 2 "Yanzu, kai ɗan mutum, za ka shar'anta? Za ka shar'anta birni mai jini? Kasa ta san dukkan ayyukanta na banƙyama. 3 Dole ne ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan shi ne birnin da ke zubar da jini a tsakiyarsa domin lokacinsa ya zo; birnin da ya yi gumaka domin ya kazantar da kansa. 4 Ka zama mai laifi ta wurin jinin da ka zubar, ka ƙazantar da kanka ta wurin gumakan da ka yi. Domin ka jawo kwanakinka kusa, ƙarshen shekarunka kuma ya zo. Domin haka zan maida kai abin reni ga dukkan al'ummai, abin ba'a kuma a dukkan ƙasashe. 5 Da waɗanda ke kusa da waɗanda ke nesa da kai za su yi maka ba'a, kai ƙazantaccen birni - da aka sani a ko'ina cike da rudami. 6 Duba! Masu mulki na Isra'ila, kowannen su da ikonsa, ya zo wurin ka domin ya zubar da jini. 7 Sun rena ubanni da uwaye a cikin ka, kuma suka yiwa baƙi danniya a cikin tsakiyar ka. 8 Sun wulaƙanta marayu da gwauraye a cikinka ka rena abubuwana masu tsarki, ka tozarta Asabataina. 9 Masu yankan baya sun zo cikin ka domin su zubar da jini, kuma sun ci abinci a kan tsaunuka. Sun yi mugunta a tsakiyarka. 10 Mazaje sun buɗe tsiraicin mahaifinsu a cikin ka. Sun kuma tozarta mata masu haila a cikin ka a lokacin hailarsu. 11 Mutanen da suka yi aikin kazanta da matan makwabtansu, mutanen da suka sa surukansu cikin kunya da kazanta; mazajen da suka ɓata 'yan'uwansu mata - 'ya'ya matan ubanninsu - dukkan waɗannan suna cikin ka. 12 Waɗannan mutane sun karɓi toshi a cikin ka domin su zubar da jini. Ka karɓi kuɗinka da ruwa, kaci riba mai yawa, ka ɓata maƙwabtanka da danniya, ka mance da ni - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 13 Duba! Da hannuna na bugi kazamar ribar da kaci, da kuma zubar da jinin da ke a tsakiyarka. 14 Zuciyarka zata tsaya, hannuwanka suyi ƙarfi a kwanakin da ni da kaina zan ɗauki mataki a kan ka? Ni Yahweh ni ne ke furta wannan, kuma zan aikata. 15 Zan watsar da kai cikin al'ummai in sa ka ɗaiɗaice cikin ƙasashe. Ta haka zan wanke ƙazantarka. 16 Ta haka za ka zama mai ƙazanta a cikin al'ummai. Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh." 17 Sai kuma maganar Yahweh ta zo gare ni cewa, 18 "Ɗan mutum, gidan Isra'ila sun zama a yamutse a gare ni. Dukkan su sun zama ragowar tagulla da tãma da ƙarfe da dalma a cikin tsakiyar ka. Za su zama kamar gurɓatacciyar azurfa a cikin kaskonka. 19 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya ce, 'Saboda ku dukka kun zama kamar gauraye, duba, saboda haka na kusa tattara ku a cikin tsakiyar Yerusalem. 20 Kamar yadda mutane ke tara azurfa da tagulla da ƙarfe da tãma da dalma a maƙera su narke, su kuma hura wuta a kan su domin su narkar da su, to haka zan tattara ku cikin fushina da hasalata, zan kuma sa ku a wurin in narkar da ku. 21 Zan tattara ku in hura wutar hasalata a kanku, za ku kuma narke a cikin tsakiyarta. 22 Kamar yadda a ke narka azurfa a cikin tsakiyar maƙera, za ku narke a cikin ta, sa'an nan za ku sani cewa Ni, Yahweh na zubo da hasalata a kan ku. 23 Maganar Yahweh ta zo gare ni cewa, 24 "Ɗan mutum ka ce da ita ke ƙasa ce wadda ba a tsabtace ba. Ba ruwan sama a cikin ranar hasala! 25 Akwai haɗaɗɗiyar maƙida ta annabawanta a cikinta kamar zaki mai ruri yana yaga nama. Suna kashe rai su kwashi dukiya mai daraja, suka sa gwauraye su yi yawa a cikin ta! 26 Firistocinta suna yiwa shari'ata tayarwa, sun ɓata abubuwa masu tsarki. Ba su banbanta abu mai tsarki da lalatacce ba, bãsa koyar da banbanci tsakanin abu mai tsabta da marar tsabta. Sukan kawar da idanunsu daga ranakun Asabar ɗina, saboda haka suka tozarta ni a cikin su. 27 Hakiman da ke cikin ta kamar kerketai suke lokacin da suke yayyaga nama. Sukan kashe rai, su zubar da jini domin suci riba ta rashin gaskiya. 28 Annabawanta sun shafe su da farar ƙasa; suna ganin wahayoyin ƙarya suna kuma faɗa masu ƙarya. Sukan ce, "Ubangiji Yahweh ya faɗi haka" Sa'ad da Yahweh bai yi magana ba. 29 Mutanen ƙasar suna yin zalunci, suna karɓar toshi, suna yin fashi, suna wulaƙanta mabuƙata da masu talauci, suna ƙwarar bãƙo da rashin adalci. 30 Sai na nemi mutum ɗaya a cikin su wanda zai gina ganuwa, ya tsaya a gabana a cikin tsagar domin kada in hallaka ta, amma ban samu ba. 31 Saboda haka zan zuba fushin hasalata a kan su. Zan gama da da su da fushin hasalata in maida masu ayyukansu a kansu - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 23

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, akwai mata guda biyu, mahaifiyarsu kuma ɗaya. 3 Sun yi aikin karuwanci a Masar sa'ad da suke matasa. Sun yi aikin karuwanci a can. A can aka lagwaigwaita nonnansu, aka daƙuna kan nonnan budurcinsu. 4 Sunayensu su ne Ohola - ita ce babba - da Oholiba kuma ƙanwarta. Daga nan suka zama nawa suka haifi 'ya'ya maza da mata. Ga ma'anar sunayensu: Ohola tana nufin Samariya, Oholiba tana nufin Yerusalem. 5 Ohola ta yi karuwanci ko sa'ad da take tawa; ta yi sha'awar masoyanta, su Asiriyawa waɗanda suke da yawa a wurin. 6 Gwamna mai saye da shuɗi, da jami'ansa kyawawa majiya ƙarfi, da dukkan waɗanda ke a kan dawakai. 7 Ta bayar da kanta karuwa a gare su, da dukkan mahimman mazaje na Asiriya, ta ƙazantar da kanta da dukkan waɗanda ta yi sha'awar su - da dukkan gumakansu. 8 Gama ba ta bar halinta na karuwanci a Masar ba, sa'ad da suka kwana da ita lokacin da take yarinya, sa'ad da suke taɓa nonnanta na kuruciya, lokacin da suka fara zuba mata halinsu na lalata. 9 Saboda haka na miƙa ta a hannun masoyanta, a hannun Asiriyawa waɗanda ta yi sha'awar su. 10 Suka yi mata tsirara sun kwashe 'ya'yanta maza da mata, kuma suka kashe ta da kaifin takobi, ta zama abin kunya ga sauran mata, suka yi mata hukunci. 11 Oholiba 'yar'uwarta ta ga haka, amma ta yi sha'awa fiye da ita, ta yi aikin karuwanci fiye da 'yar'uwarta. 12 Ta yi sha'awar Asiriyawa da gwamnoni da jami'ai waɗanda suke sa kaya masu kyau, masu hawan dawaki. Dukkan su kyawawa ne kuma ƙarfafan mutane ne. 13 Na ga ta kazamtar da kanta. Dukkan su sun zama ɗaya. 14 Sai kuma ta ƙaru cikin karuwancinta, ta ga sifofin mazaje a kan ganuwa, waɗanda a ka zãna da siffar Kaldiyawa da jar kala, 15 suna ɗaure da ɗamara a gindinsu, da rawunna masu lilo a kansu. Dukkan su sun yi kama da jami'ai masu karusai, kamanninsu na 'ya'yan Babiloniyawa ne, waɗanda asalin ƙasarsu Kaldiya ce. 16 Da dai idanunta suka gan su, sai ta yi sha'awar su, sai ta aiki waɗansu wurin su a cikin Kaldiya. 17 Sai Babiloniyawa suka zo wurin ta, wurin gadon sha'awarta, suka kazantar da ita da lalatarsu. Abin da ta yi ya kazantar da ita, sai ta ɓatar da kama ta rabu da su. 18 Ta bayyana aikin karuwancinta ta nuna tsiraicinta, raina ya yi ƙyamar ta kamar yadda raina ya yi kyamar 'yar'uwarta. 19 Sa'an nan ta ƙara tunawa da aikin karuwanci, kamar yadda ta yi kwanakin ƙuruciyarta, sa'ad da ta zama kamar karuwa a cikin ƙasar Masar. 20 Ta yi sha'awar masoyanta waɗanda mazakuttarsu ke kamar na jakuna, waɗanda kuma maniyinsu kamar na dawaki ne. 21 Haka ki ka yi aikin kunya a lokacin ƙuruciyarki, sa'ad da Masarawa suka taɓa kan nonnanki suka lagwaigwaita nonnanki da ke tsaye. 22 Saboda haka, Oholiba, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Duba! Zan sa mãsu ƙaunar ki su yi gãba da ke. Waɗanda kika gudu daga wurin su, za su taso maki daga kowanne sashi: 23 Babiloniyawa da dukkan Kaldiyawa da Fekod da Shoya da Koya da dukkan Asiriyawa tare da su da ƙarfafa da kyawawan mutane da gwamnoni da jami'ai, dukkan su jami'ai ne da mazaje masu muƙami, dukkan su suna kan dawakai. 24 Za su auko maki da kayan yaƙi, da karusai da kekuna da taron mutane da yawa. Za su ta da garkuwoyi manya da ƙanana da hulunan ƙarfe kewaye da ke ko'ina. Zan ba su zarafi su hore ki, za su hore ki da ayyukansu. 25 Gama zan sa kishin fushina a kan ki, za su lallasa ki da fushinsu. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka tsira kuma za su faɗi da kaifin takobi. Za su kwashe 'ya'yanki maza da mata, waɗanda suka tsira kuma wuta za ta cinye su. 26 Za su tuɓe kayanki su bar ki tsirara, su kwashe kayan adonki dukka. 27 Ta haka zan cire halinki na abin kunya da aikin karuwancinki daga ƙasar Masar. Ba za ki ƙara ɗaga idonki wajen su da marmarin ki gan su ba, ba za ki ƙara yin tunanin Masar ba. 28 Gama Ubangiji ya faɗi haka. Duba! zan bayar da ke a hannun waɗanda kika ƙi su, ki koma hannun waɗanda kika juyawa baya. 29 Za su azabtar da ke cikin zafin ƙiyayya, za su ɗauke dukkan kayayyakinki su bar ki huntuwa. Huntancinki na karuwanci zai bayyana, halinki na kunya da lalatarki za su bayyana. 30 Za a yi maki waɗannan abubuwa saboda aikinki na karuwanci, sha'awarki ta al'ummai wadda ta ƙazamtar da ke da gumakansu. 31 Kin yi tafiya cikin hanyar 'yar'uwarki, saboda haka zan sa ƙoƙon horona a cikin hannunki.' 32 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Za ki sha ƙoƙon 'yar'uwarki mai faɗi da zurfi. Za ki zama abin dariya da abin ba'a - cikin wannan ƙoƙon akwai abubuwa da yawa. 33 Za ki cika da maye da baƙinciki, ƙoƙon fargaba da lalacewa; ƙoƙon 'yar'uwarki Samariya. 34 Za ki shanye shi dukka ki farfasa shi ki tsattsaga nononki da gutsattsarinsa. Gama na furta shi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 35 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Saboda kin manta da ni kin jefar da ni bayanki, ke kuma za ki ɗauki alhakin halinki na kunya da lalata." 36 Yahweh ya ce da ni, "Ɗan mutum, za ka hukunta Ohola da Oholiba? To ka nuna masu ayyukansu na banƙyama, 37 tun da yake sun yi zina, tun da yake akwai jini a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu, sun sa 'ya'yansu cikin wuta, a matsayin abinci ga gumakansu. 38 Sa'an nan sun ci gaba da yi mani haka, sun ɓata gidana mai tsarki, sun tozarta Asabataina. 39 Gama sa'ad da suka yanka 'ya'yansu ga gumakansu, rannan kuma suka zo gidana mai tsarki suka ɓata shi! To duba! Wannan shi ne abin da suka yi a tsakiyar gidana. 40 Kin yi aike wurin mutanen da suka zo daga nesa, an aika manzanni - duba yanzu. To sun zo su waɗanda kika yi wanka domin su, kin yi wa idanunki kwalliya kin sa kayan adonki. 41 Can kika zauna a kan gado mai kyau wanda aka shirya teburi a gabansa inda kika ajiye turarena da maina. 42 To ga hayaniyar babban taro kewaye da ita; ciki akwai mutane iri-iri har da masu maye daga cikin jeji, sun sa sarƙoƙi a hannuwansu da kambuna kyawawa a kawunansu. 43 Sa'an nan na ce da ita, ita wadda ta tsofe a wurin karuwanci, 'Yanzu za su ƙazantu da zinarta, ita kuma da su.' 44 Suka je wurin ta suka kwana da ita kamar yadda mutum zai je wurin karuwa. Ta wannan hanya suka kwana da Ohola da Oholiba, kazantattun mata. 45 Amma mazaje masu adalci za su yi masu hukuncin mazinata, kuma za su yi masu hukunci na mãsu zubar da jini, saboda su mazinata ne kuma jini yana hannuwansu. 46 To Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: zan sa taron mutane su auko masu da ta'addanci su washe su. 47 Sa'an nan waɗannan mutane za su jejjefe su da duwatsu su daddatsu da takubbansu. Za su karkashe 'ya'yasu maza da mata, su ƙone gidajensu. 48 Gama zan cire halayen kunya daga ƙasar, in hori dukkan mataye domin kada su ƙara yin rayuwa kamar karuwai. 49 Haka za su sa maki halinki na kunya. Za ki ɗauki hakin zunubanki da gumakanki, ta haka za ki sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."

Sura 24

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni a cikin shekara ta tara, a cikin wata na goma, a kan rana ta goma ga watan, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka rubuta wa kanka sunan wannan rana, ranar nan ta yau, gama a dai-dai wannan ranar ne sarkin Babila ya ƙwace Yerusalem. 3 To sai ka yi magana da misali gãba da wannan gida mai tayarwa, a misali. Ka ce da su Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ɗora tukunyar girki. Ɗora ta ka zuba ruwa a cikin ta. 4 Ka tattara gutsattsarin abinci a cikin ta, kowanne yanka mai kyau - kamar su cinya da karfata - ka cika ta da ƙasusuwa zaɓaɓɓu. 5 A cikin garke ka ɗauki dabba zaɓaɓɓiya ka jera kasusuwan a ƙarƙashin ta. Ka sa ta tafasa ka dafa ƙasusuwan a cikin ta. 6 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton birni mai jini, tukunyar girki mai tsatsa kuma tsatsar ba za ta fita daga cikin ta ba. Ka ɗauki yanka bayan yanka daga cikin ta, amma kada ka jefa ƙuri'a kan ta. 7 Gama jininta yana cikin tsakiyarta, ta sa shi a kan dutse mai laushi; ba ta zubar da shi a ƙasa ta rufe shi da turɓaya ba, 8 ta kawo hasala dai-dai ta ɗaukar fansa. Na sa jininta a kan dutse mai laushi domin kada ya rufu. 9 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Kaiton birni mai jini. Zan ƙara sa itace da yawa. 10 Iza itacen ka sa wuta. Ka dafa naman ya dafu sosai ka gauraye da kayan yaji ka kuma bari kasusuwan su gashe. 11 Sa'an nan ka ɗora tukunyar a kan garwashi ba komai a ciki, domin ta yi zafi tagullarta ta rikiɗe, domin ƙazantar da ke cikinta ta narke, tsatsarta ta ƙone. 12 Ta zama gajiyayya saboda aiki, amma tsatsarta ba ta fita daga cikin ta da wuta ba. 13 Halinki na kunya yana cikin ƙazantarki. Saboda nayi ƙoƙari in tsabtace ki amma har yanzu ba ki tsabtatu daga ƙazantarki ba, ba za ki sake tsabtatuwa ba sai na ƙosar da fushina a kan ki. 14 Ni, Yahweh, na furta, kuma zan aikata. Ba zan janye ba, ba zan huta ba. Yadda hanyoyinki suke, yadda kuma ayyukanki suke, su za su hukunta ki! - Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne." 15 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 16 "Ɗan mutum! Duba zan ɗauke maka muradin idanunka daga gare ka da annoba, amma kada ka yi baƙinciki ko kuka, kada hawayenka su zubo. 17 Ka yi nishi a hankali. kada kayi jana'izar matattu. Ka ɗaura rawaninka a jikinka ka sa takalmanka a ƙafafunka, amma kada ka lulluɓe gashin bakinka, kada ka ci gurasar waɗanda ke makoki saboda sunyi rashin matayensu." 18 Domin haka na yiwa mutane magana da safe, da yamma kuma matata ta mutu. Da safe na yi abin da aka umarce ni in yi. 19 Mutanen suka tambaye ni, "Ba za ka gaya mana ma'anar waɗannan abubuwa ba, abubuwan da kake yi?" 20 To sai na ce da su, "Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 21 'Ka ce da gidan Isra'ila, ga abin da Ubangiji Yahweh ya fadi: Duba! Zan ƙaskantar da gidana mai tsarki - girmankan ikonku da muradin idanunku, da marmarin ranku da na 'ya'yanku maza da mata da kuka baro, za su faɗi da kaifin takobi. 22 Sa'an nan za ku yi dai-dai yadda na yi: Ba za ku lulluɓe kanku ba, ba za kuci gurasar mazajen da ke yin makoki ba! 23 Maimakon haka rawunanku za su kasance a kan ku takalmanku kuma a ƙafafunku; ba za ku yi baƙinciki ka kuka ba, gama za ku narke cikin muguntarku, kowanne mutum zai yi nishi saboda ɗan'uwansa. 24 Domin haka Ezekiyal za ya zamar maku misali, yadda idan wannan abu ya zo za ku yi dukkan abin da ya yi. Sa'an nan za ku sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh." 25 "Amma kai ɗan mutum, ran da na ƙwace haikalinsu, wanda shi ne farincikinsu, da fahariyarsu da abin da suke gani suna jin daɗi - sa'ad da kuma na ɗauke 'ya'yansu maza da mata - 26 a wannan rana mai gudun hijira zai zo ya ba ka labari! 27 A wannan rana ne bakinka zai buɗe ga wannan mai gudun hijira za ka yi magana - ba za ka ƙara yin shiru ba. Za ka zama misali a gare su domin su sani cewa Ni ne Yahweh."

Sura 25

1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka sa fuskar ka gãba da mutanen Amon ka yi anabci gãba da su. 3 Ka ce da mutanen Amon, 'Ku ji maganar Yahweh. Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi: Saboda kun ce, "Aha!" a kan wurina mai tsarki sa'ad da aka ɓata shi, da kuma gãba da ƙasar Isra'ila sa'ad da ta zama kango, da kuma gidan Yahuda sa'ad da suka tafi bauta, 4 saboda haka, duba, zan bashe ku ga mutanen gabas su mallake ku. Za su kafa sansani gãba da ku su kafa rumfuna a cikin ku. Za su ci 'ya'yan itatuwanku su sha madararku. 5 Zan maida Rabba wurin kiwon raƙuma mutanen Amon kuma saura domin garkuna. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh. 6 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Da yake kun tafa hannuwanku kun buga ƙafafunku kun yi farinciki da ƙiyayya a cikin ku gãba da ƙasar Isra'ila. 7 Saboda haka, duba! Zan buge ku da hannuna in bashe ku ganima ga al'ummai. Zan datse ku daga cikin mutane in sa ku lalace daga cikin al'ummai! Zan hallaka ku, kuma za ku sani cewa Ni ne Yahweh.' 8 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Saboda Mowab da Siya sun ce, "Duba! Gidan Yahuda ya zama kamar kowacce al'umma." 9 Saboda haka, Duba! Zan buɗe magangarin Mowab in fara daga biranensa a kan iyaka - martabar Bet Yeshimot, Ba'al Miyon da Kiriyattayim - 10 domin mutanen gabas waɗanda ke gãba da mutanen Amon. Zan bayar da su a mallake su yadda ba za a ƙãra tunawa da mutanen ba a cikin al'ummai. 11 Haka zan yi hukunci a kan Mowab, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh. 12 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Idom ta ɗauki fansa a kan gidan Yahuda kuma ba ta yi dai-dai ba da ta yi haka. 13 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan bugi Idom da hannuna in hallaka kowanne mutum da kowacce dabba a can. Zan maida su kufai, yasasshen wuri tun daga Teman har zuwa Dedan. Za su faɗi da kaifin takobi. 14 Zan ɗora ramakona a kan Idom ta hannun mutanena Isra'ila, za su yi wa Idom bisa ga fushina da hasalata, kuma za su gane ramako na ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.' 15 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Tun da Filistiyawa sun ɗauki fansa da reni a cikin su, sun yi ƙoƙari su rushe Yahuda ba sau ɗaya ba. 16 To ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Zan kai hannuna a kan Filistiyawa, zan datse Keretiyawa in hallaka waɗanda suka rage a gefen teku. 17 Gama zan ɗauki fansa a kan su da fushi mai zafi da horo, saboda su sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na ɗauki fansata a kan su."

Sura 26

1 Ya zama a cikin wata na goma sha ɗaya, a kan rana ta fari ga watan, Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, saboda Taya ta ce, 'Aha! A kan Yerusalem, ƙofofin mutanen yanzu an ɓalle su! ta dawo wurina; zan cika saboda ta zama kango.' 3 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Duba! Ina gãba da ke Taya, zan taso da al'ummai da yawa a kan ki kamar yadda teku ya kan tada raƙuman ruwansa. 4 Za su rushe ganuwoyin Taya, su farfasa hasumiyoyinta. Zan share ƙurarta in sa ta zama kamar huntun dutse. 5 Za ta zama wurin da a ke shimfiɗa taru ya bushe a tsakiyar teku, tun da shi ke na furta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - kuma za ta zama ganima ga al'ummai. 6 'Ya'yanta waɗanda suke cikin gona za a datse su da takobi; kuma za su sani cewa Ni ne Yahweh.' 7 Gama wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi: Duba, daga arewa zan kawo Nebukadnezza sarkin Babila, sarkin sarakuna gãba da Taya, da dawakai da karusai da masu hawan dawakai da mutane da yawa. 8 Za ya kashe 'ya'yanki mata a gona. Ya kafa sansani ya gina wuraren hawan ganuwarki ya tada garkuwoyi gãba da ke. 9 Zai sa mabugi ya bubbuge ganuwarki, ya rushe hasumiyoyinka da kayan aikinsa. 10 Dawakinsa za su yi yawa har ƙurar su za ta rufe ki. Ganuwarki za ta girgiza da ƙarar mahayan dawakai da kekunan yaƙi da karusai. Sa'ad da zai shiga ƙofofinki zai shiga kamar yadda mutane ke shiga birnin da aka rushe ganuwarsa. 11 Kofatun dawakinsa za su yi tafiya a cikin dukkan hanyoyinki. Zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki na dutse masu ƙarfi za su faɗi har ƙasa. 12 Za su kwashe dukiyarki da kayan cinikinki, za su farfasa ganuwarki su rushe gidajenki na jin daɗi. Duwatsunki da katakonki da ɓaragwazanki za su zubar da su a cikin ruwaye. 13 Zan tsayar da ƙarar waƙoƙinki. Ba za a ƙara jin ƙarar molayenki ba. 14 Zan maida ke huntun dutse, za ki zama wurin da za a shanya taru ya bushe. Ba za a sake gina ki ba, gama Ni, Ubangiji Yahweh na faɗi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 15 Ubangiji Yahweh ya faɗawa Taya haka, 'Tsibirai ba za su girgiza ba da ƙarar faɗuwarki, da nishin waɗanda aka yiwa rauni sa'ad da wannan kisa mai muni ya zo cikin ki? 16 Sa'an nan dukkan yarimai na bakin teku za su sauka daga mulkokinsu su tuɓe tufafinsu, su jefar da rigunansu masu aiki. Za su rufe kansu da rawar jiki, za su zauna a ƙasa suna rawar jiki kowanne lokaci, kuma za su yi nukura saboda ke. 17 Za su yi makoki a kanki su ce da ke, yaya haka, ke da kike wurin zaman masu tukin jirgin ruwa aka rushe ki. Sanannen birni mai ƙarfin gaske - yanzu ba shi a bakin teku. Su da suke zaune cikin ta suka baza labarin fargabarsu ga waɗanda ke zaune kusa da su. 18 Yanzu ƙasashen tudu sun girgiza da ranar faɗuwarki. Tsibirai na cikin teku sun firgita saboda kin rabu da wurin ki.. 19 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Sa'ad da na mayar da ke kangon birni, kamar biranen da ba kowa. Sa'ad da na taso da zurfafa a kan ki, sa'ad da manyan ruwaye suka rufe ki, 20 sa'ad da zan saukar da ke wurin mutanen dã, kamar waɗanda suka gangara cikin rami; gama zansa ki zauna can ƙarƙashin ƙasa kamar irin kango na zamanin dã. Saboda haka ba za ki ƙara dawowa ki tsaya a cikin ƙasar masu rai ba. 21 Zan saukar maki da masifa, kuma ba za ki ƙara wanzuwa ba har abada. Sa'an nan za a neme ki, kuma ba za a ƙara samun ki ba - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 27

1 Kuma maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni cewa, 2 "Yanzu kai, ɗan mutum, sai ka soma makoki game da Taya, 3 ka kuma cewa Taya, wadda take zama kurkusa da ƙofofin teku, masu kasuwancin mutane ne ga Tsibirai da yawa, Ubangiji Yahweh ya faɗa maki haka: Taya, Kin ce, 'Ni kammalalliya ce mai kyau.' 4 Iyakokinki suna cikin tsakiyar zuciyar tekuna; maginanki sun kamalla kyaunki; 5 Sun yi katakan ki da siferas daga Tsaunin Hamon; sun ɗauko sida daga Lebanon domin su yi maki sandar tukin jirgi. 6 Sun sarrafa sandar tukin jirginki da itace na Bashan; suka yi matakalar ki da katakan siferas daga Saifrus, suka kuma lulluɓe ta da hauren giwa. 7 Mayafanki mayafai masu ƙawa ne daga Masar da ke a matsayin tutarki; launin shuɗi da shunayya daga gaɓar Elisha a na amfani da su domin kare jirgin ruwanki. 8 Waɗanda suka zauna cikin Sidon da Abad su ne matuƙanki; masu hikima na Taya na cikin ki; su ne masu yi maki jagora. 9 Ƙwararru masana masu aikin hannu daga Baibilos sun gyarta tsagaggun wurarenki; dukkan jiragen teku da matuƙansu da ke cikin ki suna ɗaukar kayan fatauci domin kasuwanci. 10 Fãsha da Lidiya da kuma Libiya suna cikin rundunarki, mayaƙãnki sun rataye garkuwa da ƙwalƙwali a cikin ki; suka bayyana darajarki. 11 Mazajen Abad da Helek da ke cikin rundunarki sun zama katanga zagaye da ke, kuma mutanen Gammad su ne hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu a kan katangu zagaye da ke! Suka kammala kyaunki. 12 Tarshish abokiyar kasuwancinki ce saboda yawan wadatar dukiyarki ta sayarwa: da azurfa, da baƙin ƙarfe, da tãma, da dalma. Suka saya suka kuma sayar da kayayyakin ki! 13 Yaban da Tubal da kuma Meshek-sun sayar da bayi da kuma kayayyaki na tagulla. Suka sarrafa kayan fataucinki. 14 Bet Togama ta tanadi dawakai, da dawakan yaƙi da alfadarai a matsayin kayan fataucinki. 15 Mazajen Rodes suka zama yan kasuwarki a tsibirai masu yawa. Fatauci na cikin hannunki; suka kuma aiko maki ƙaho da hauren giwa da katakai masu ƙarfi a matsayin kyautai. 16 Aram babbar 'yar kasuwa ce da kayayyakin ki masu yawa; suka tanada koren dutse mai daraja da shunayya, kaya mai launuka, da yãdi mai kyau da tsakiya da sauran kayan ado a matsayin kayan fataucinki. 17 Yahuda da Isra'ila abokan kasuwancin ki ne. Suka tanada alkama daga Minit, waina da zuma, da mai, da ƙãro a matsayin kayan fataucinki. 18 Dimaskus dillaliyar dukkan kayayyakin da kika sarrafa ce, ta hamshaƙiyar dukiyarki, da kuma ruwan inabi na Helbon da ulun Zaha. 19 Dan da Yaban daga Izal suka yi maki fataucin ɗanyen ƙarfe da ɓawon ƙirya, da ƙansa-ƙansa. Wannan ya zama abin fatauci domin ki. 20 Dedan ce mai samar maki da mashinfiɗai na sirdin dawakai masu kyau. 21 Arebiya da dukkan shugabannin Keda suna ciniki da ke; sun samo maki 'yan raguna da raguna da awaki. 22 'Yan kasuwa na Sheba da Rama suka zo su sayar maki da kowanne irin kayan ƙamshi mafiya daraja da kowanne irin dutse mai daraja; suka yi safarar zinariya domin fataucinki. 23 Haran da Kane da Iden su ne abokan kasuwancinki, tare da Sheba da Ashu da kuma Kilmad. 24 Waɗannan su ne dillalanki waɗanda ke sayar da kayan ƙawa (kayayyaki masu daraja na sãƙaƙƙun kayan ãdo), da kuma cikin barguna masu zane iri-iri da sãƙaƙƙun kaya a cikin kasuwannin ki. 25 Jiragen ruwa na Tarshish su ne masu kawo maki kayayyakin fataucinki! Domin haka ki ka cika, aka loda maki kaya masu nauyi a tashoshin jiragen ruwanki. 26 Matuƙan jiragen ruwanki suka kawo ki ga manyan tekuna; iskar gabas ta karya ki a tsakiyar su. 27 Dukiyarki, da abin fataucinki da kuma kayan kasuwancinki; matuƙan jiragenki, da mãsassaƙa jiragen ruwa; abokan cinikinki da dukkan mayaƙan da ke cikin ki da dukkan ma'aikatan jiragenki- za su nutse cikin zurfin teku a ranar hallakarki. 28 Biranen kusa da teku za su yi rawar jiki da jin ƙarar kukan masu yin jagoran jiragen ruwanki; 29 Dukkan matuƙan jiragen za su sauko daga jiragensu; ma'aikata da majayan hanya za su sauka su tsaya kan ƙasa. 30 Sa'an nan za susã ki saurari muryarsu za su kuma yi kuka mai zafi; za su watsa ƙura a kawunansu. Za su kwanta suna birgima cikin toka. 31 Za su aske sumar kansu dominki su kuma ɗaure kansu da tsummokin makoki, kuma za su yi kuka mai zafi su kuma tãda murya ƙwarai. 32 Za su tãda muryarsu ta makoki mai zafi dominki su kuma furta kalamai na habaici a kanki, wane ne kamar Taya, wadda yanzu aka sa tayi shiru a tsakiyar teku? 33 A lokacin da fataucinki ya kai bakin teku, yana biyan buƙatar mutane masu yawa; kin azurtar da sarakunan duniya da dukiyarki da fataucinki! 34 Amma lokacin da teku ya ragargaza ki, ta zurfafan ruwaye, fataucinki da dukkan ma'aikatanki suka nutse! 35 Mazaunan tsibirai suka gan ki suka tsorata da ke, kuma sarakunansu suka yi rawar jiki mai ban razana! Fuskokinsu suka gigice! 36 Fatake suka yi maki tsãki, kin zama abin razana, kuma ba za a sake ganin ki ba har abada."

Sura 28

1 Sai maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka yi magana da shugaban Taya, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zuciyarka tunƙaho! Kãce, 'Ni allah ne! zan zauna a cikin mazaunin alloli a tsakiyar tekuna!" koda shi ke kai mutum ne ba allah ba, ka maida zuciyarka kamar ta allah; 3 kana tunanin ka fi Daniyel hikima, kuma babu asirin da ke ba ka mamaki! 4 Ka maishe da kanka mawadaci da hikima da fasaha, ka kuma tara zinariya da azurfa cikin ma'ajin ka! 5 Ta wurin babbar hikima da kuma kasuwanci, ka ruɓanɓanya wadatarka, sai zuciyarka ta kumbura saboda dukiyarka. 6 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: domin ka maida zuciyarka kamar zuciyar allah, 7 Zan kawo bãƙi gãba da kai, Mazaje masu ban razana daga waɗansu al'ummai. Za su kawo takubba gãba da kyakkawar hikimarka, kuma za su wulaƙanta darajarka. 8 Za su tura ka cikin rami, kuma za ka mutu mutuwa irin ta masu mutuwa cikin tsakiyar tekuna. 9 Ka iya cewa, 'Ni allah ne' a fuskar mai kashe ka? Kai mutum ne ba Allah ba, kuma za ka zama a hannun wanda yake caccakar ka. 10 Za ka yi mutuwar marasa kaciya ta hannun bãƙi, gama na furta haka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne." 11 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni karo na biyu, cewa, 12 "Ɗan mutum, ka tãda makoki domin sarkin Taya kace da shi, "Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: ka zama misalin kammala, cike da hikima da kammalanlen kyau. 13 Kana cikin Iden, lambun Allah. Kowanne dutse mai daraja ya rufeka; da rubi, da tofaz, da imeral, da kiraisolet, da oniks, da yasfa, da saffiya, da tokwayis, da beril. Tsare-tsarenka da haɗuwarka anyi su ne da zinariya. A ranar da aka hallice ka ne aka shirya su. 14 Na ajiye ka a bisa tsauni mai tsarki na Allah a matsayin kerubim da na shafe domin ya yi tsaron 'yan adam. Kana cikin tsakiyar dutse ma wuta inda ka yi yawo. 15 Kana da aminci a tafarkunka tun daga ranar da aka hallice ka har sai da aka sami rashin adalci cikin ka. 16 Ta wurin girman kasuwancinka ka cika da ta'addanci, domin haka ka yi zunubi. Saboda haka sai na jefar da kai daga tsaunin Allah, kamar wadda ya ƙazanta, kuma sai na hallakar da kai, kerubim mai tsaro, na kore ka daga cikin duwatsu masu wuta. 17 Zuciyarka ta cika da tunƙaho domin kyaunka; ka wofintar da hikimarka saboda darajarka. Na koro ka ƙasa. Na sanya ka a gaban sarakuna domin su gan ka. 18 Saboda zunubanka masu yawa da kuma rashin amincin kasuwancinka, ka ƙazantar da wurarenka masu tsarki. Domin haka na sa wuta ta fito daga gare ka; zata cinye ka. Zan maishe ka toka a fuskar dukkan waɗanda suke kallon ka. 19 Dukkan waɗanda suka san ka cikin mutanen za su girgiza kai; za su yi fargaba, kuma ba za a sake ganinka ba har abada."' 20 Sai maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 21 "Ɗan mutum, ka sa fuskar ka gãba da Sidon ka kuma yi annabci gãba da ita. 22 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Ina gãba da ke, Sidon! Gama za a ɗaukaka Ni a tsakiyarki domin mutanenki su sani cewa Ni ne Yahweh a lokacin da zan zartar da adalci a cikin ki. Za a nuna ni mai tsarki cikin ki. 23 Zan aika da annoba cikin ki da jini cikin titunanki, kuma waɗanda aka kashe za su faɗi a tsakiyarki. A lokacin da takobin zata tashi gãba da ke ta ko'ina, sa'an nan za ki sani cewa Ni ne Yahweh. 24 Daga nan ba za a sami wata sarƙaƙiya da ƙaya mai azaba domin gidan Isra'ila ba daga dukkan waɗanda ke zagaye da ita waɗanda ke raina mutanenta ba, haka za su sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh!' 25 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Lokacin da na tara gidan Isra'ila daga cikin mutane waɗanda aka tarwatsa su, kuma lokacin da na keɓe cikin su, domin al'ummai su gani, sa'an nan za su gina gidajensu a cikin ƙasar da zan ba bawana Yakubu. 26 Sa'an nan za su zauna lafiya cikin ta su kuma gina gidaje, su shuka gonakin inabi, su kuma zauna lafiya a lokacin da zan shar'anta dukkan waɗanda suka rena su yanzu daga dukkan kewaye; Da haka za su sani Ni ne Yahweh Allahnsu!"'

Sura 29

1 A cikin shekara ta tara, a watan goma a ran sha biyu ga wata, maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka juya fuskar ka gãba da Fir'auna, sarkin Masar; ka yi annabci gãba da shi da kuma gãba da dukkan Masar. 3 Ka furta ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Ina gãba da kai, Fir'auna, sarkin Masar. Kai, babbar dabbar teku da ke ɓuya cikin tsakiyar kogi, da ke cewa, "Kogi nawa ne. Na yi shi domin kaina." 4 Gama zan sa ƙugiya a cikin bakinka, kuma kifaye na cikin Nilunka za su liƙe bisa ɓawonka; Zan tãda kai sama tare da dukkan kifayen kogin da suka manne wa ɓawonka. 5 Zan jefar da kai cikin hamada, kai da dukkan kifaye daga koginka. Zaka faɗi a buɗaɗɗen fili; ba za a tãra ka ko a tãda kai sama ba. Zan bada kai abinci ga hallitun ƙasa da kuma tsuntsayen sammai. 6 Sa'an nan dukkan mazaunan Masar za su sani cewa Ni ne Yahweh, domin sun zama sandar matsala ga gidan Isra'ila. 7 A lokacin da suka riƙe ku da hannunsu, kun karye kun kuma yage kafaɗarsu; da suka jingina a kanku, sai kuka karye, sai kuma kuka sa ƙafafunsu suka kasa tsayawa. 8 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Zan kawo takobi gãba da kai. Zan datse mutum da dabba daga gare ka. 9 Sai ƙasar Masar ta zama yasasshiya da kuma kufai. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, domin dabbar teku ta ce, "Kogin nawa ne, gama ni na yi shi." 10 Domin haka, duba! Ina gãba da kai kuma ina gãba da koginka, don haka zan bayar da ƙasar Masar ga hallakarwa da lalacewa, kuma za ta zama lalatacciyar ƙasa daga Migdol zuwa Sãyin da kuma iyakokin Kush. 11 Babu ƙafafun mutum da za shi wuce ta cikin ta, kuma babu ƙafar naman jeji da za shi wuce cikin ta. Ba za a zauna cikin ta ba har shekaru arba'in. 12 Gama zan maida Masar ƙango a tsakiyar ƙasar da ba a zama cikin ta, kuma biranenta a tsakiyar lalatattun birane za su zama kufai har shekaru arba'in; sa'an nan zan tarwatsa Masar cikin al'ummai, in kuma watsa su cikin ƙasashe. 13 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: a ƙarshen shekara arba'in zan tara Masar daga cikin mutanen da aka watsar da su. 14 Zan dawo da abin da ke na Masar in kuma dawo da su zuwa ga yankin Fatros, zuwa ga ƙasar su ta asali. Sa'an nan za su zama masarauta marar muhimmanci a can. 15 Zata zama ƙasƙantacciyar masarauta cikin masarautu, kuma ba za a ɗaga ta sama ba cikin al'ummai. Zan ƙasƙantar da su domin kada su yi mulkin al'ummai. 16 Masarawa ba za su ƙara zama dalilin ƙarfin zuciya ga gidan Isra'ila ba. Maimakon haka, za su zama abin tunawa da zunubin da Isra'ila ta aikata a lokacin da suka juya ga Masar neman taimako. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."' 17 Sai ya zama a cikin shekara ta ashirin da bakwai a ranar farko ta watan ɗaya, maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 18 "Ɗan mutum, Nebukadneza sarkin Babila ya shirya rundunarsa su yi aiki mai wuya gãba da Taya. Kowanne kai an murje shi har sai ya yi saiƙo, kuma kowacce kafaɗa ta gogu. Duk da haka shi da rundunarsa ba su karɓi lada daga wurin Taya domin aiki mai wuyar da ya yi gãba da ita ba. 19 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: 'Duba! Ina bayar da Masar ga sarki Nebikadneza sarkin Babila, kuma zai kwashe dukiyarta, ya kwashe mallakarta, ya tafi da duk abin da ya iske a can; wannan zai zama ladar rundunarsa. 20 Na ba shi ƙasar Masar domin aikin da suka yi mani - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 21 A wannan rana zan sa ƙaho ya taso domin gidan Isra'ila, kuma na sa ku yi magana a tsakiyarsu, domin su san cewa Ni ne Yahweh."

Sura 30

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ku yi kururuwa, "Kaiton ranar mai zuwa." 3 Ranar ta kusa. Ranar ta gabato domin Yahweh. Za ta zama rana ce ta hadarai, lokaci na masifa ga al'ummai. 4 Sa'an nan takobi zata zo gãba da Masar, kuma za a yi ƙunci a cikin Kush a lokacin da mutanen da aka kashe suka fǎɗi a Masar - a lokacin da suka ɗauki dukiyarsu, da kuma lokacin da ginshiƙanta aka warwatsar. 5 Kush da Libiya, da kuma Lidiya, da dukkan Arebiya, tare da mutanen da ke na alƙawari - dukkan su za su fãɗi ta dalilin takobi. 6 Yahweh ya faɗi wannan: Waɗanda suka tsaya tare da Masar za su fǎɗi, kuma girman ƙarfin ta zai fǎɗi ƙasa. Daga Migdol zuwa Siyen sojojinsu za su fǎɗi da takobi - wannan furcin Yahweh ne. 7 Za su zama wofi a tsakiyar yasassun ƙasashen, kuma biranen su za su zama cikin dukkan rusassun biranen. 8 Sa'an nan za su san cewa Ni ne Yahweh, yayin da na cinna wuta cikin Masar, kuma lokacin da aka hallaka dukkan mataimakanta. 9 A wannan ranar 'yan saƙo za su fito daga gare ni cikin jirage su addabi tsararrar Kush, kuma za a yi azaba a cikin su a wannan rana ta azabar Masar. Duba! Tana zuwa. 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan kawo ƙarshen taron jama'ar Masar ta hannun Nebukadneza, sarkin Babila. 11 Shi da rundunarsa tare, ta'addar al'ummai, za a hallakar da ƙasar; za su zare takobinsu gãba da Masar su kuma cika ƙasar da gawawwakin mutane. 12 Zan maishe da rafuffuka busassun ƙasa, zan kuma sayar da ƙasar cikin hannun mugayen mutane. Zan maishe da ƙasar da dukkan cikarta kufai ta hannun bãƙi- Ni, Yahweh, na yi magana. 13 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zan hallakar da gumaka, kuma zan kawo iyakar gumakan Memfis marasa amfani. Ba za a sake samun yarima cikin ƙasar Masar ba, kuma zan sa ta'adda a bisa ƙasar Masar. 14 Sa'an nan zan sa Fatros ta zama kufai in kuma cinna wuta a Zowan, kuma zan aiwatar da ayyukan shari'a a kan Tebes. 15 Gama zan zubo da fushi na a bisa Felusiyom, kangararren wuri na Masar, in kuma datse taron jama'ar Tebes. 16 Sa'an nan zan cinna wuta a Masar; Felusiyom za ta zama da azaba mai tsanani, Tebes za ta kakkarye, Memfis kuma za ta fuskanci magabta a kowacce rana. 17 Majiya ƙarfi cikin Heliyofolis da Bubastis za su fǎɗi ta takobi, kuma birninsu zai tafi bauta. 18 A Tafahes, rana za ta ƙi bada haskenta sa'ad da na karya karkiyar Masar a nan, za a ƙarar da alfarmar ikonta. Girgije zai rufe ta, kuma 'ya'yanta mata za su tafi bauta. 19 Zan aiwatar da ayyukan shara'a a Masar, domin su sani cewa Ni ne Yahweh.'" 20 Sai ya kasance a cikin shekara ta sha ɗaya, cikin wata na farko, a cikin kwana na bakwai na watan, da maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 21 "Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, sarkin Masar. Duba! Ba a rigaya an ɗaure masa ciwon ba, ko a shirya shi ya warke da bandeji, saboda ya yi ƙarfi ya kama takobi. 22 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: 'Duba, ina gãba da Fir'auna, sarkin Masar. Gama zan karya hannunsa, da mai ƙarfin da wanda aka karye, kuma zan sa takobin ya fǎɗi daga hannunsa. 23 Sa'an nan zan tarwatsa su cikin Masar cikin al'ummai in kuma watsa su cikin ƙasashe. 24 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila in kuma ɗibiya takobina a cikin hannunsa domin in hallaka hannun Fir'auna. Zai yi nishi a gaban sarkin Babila da nishi kamar na mutum mai mutuwa. 25 Gama zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila, amma hannun Fir'auna zai faɗi. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, a lokacin da zan sa takobina cikin hannuwan sarkin Babila; gama zai kai wa Masar farmaki da ita. 26 Don haka zan watsar da Masar cikin al'ummai In kuma tarwatsa su a cikin ƙasashe. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh."'

Sura 31

1 Sai ya zama a cikin shekara ta sha ɗaya, a wata na uku, a rana ta farko ta watan, da maganar Yahweh ta zo mani, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka ce da Fir'auna, sarkin Masar, da kuma ga taron jama'arsa da ke kewaye da shi, 'girman kujerarka, kama da wa kake? 3 Duba! Asiriya ta zama sida a cikin Lebanon da kyawawan rassa, ta na bada inuwa ga jejin, kuma doguwa ce, kuma rassanta suka zama ƙoƙuwar itace. 4 Ruwaye masu yawa suka sa tayi tsayi; zurfafan ruwaye suka sa tayi faɗi. Rafuka suka gangara dukka kewaye da sashenta, gama hanyoyinsu sun bi ta dukkan hanyoyi zuwa ga dukkan itatuwan fili. 5 Tsawonsa mai girma yafi sauran itatuwa da ke a filin, kuma rassanta sun zama da yawa; rassanta suka yi tsayi sabili da ruwaye masu yawa sa'ad da suke girma. 6 Kowanne tsuntsun sammai na zama cikin rassanta, haka kuma kowacce halita mai rai na cikin filin suna haifar 'ya'yansu a ƙarƙashin inuwarsa. Dukkan al'ummai masu yawa suna zama a ƙarƙashin inuwarsa. 7 Gama yana da kyau a cikin girmansa da kuma tsayi a rassansa, gama saiwarsa na cikin ruwaye masu yawa. 8 Sida na cikin gonar Allah ba su kai shi ba. A cikin itatuwan gora babu waɗanda suka kai rassansa, kuma itacen durumi bai kai shi rassa ba. Babu wani itace a cikin lambun Allah da ke kamar sa cikin kyaunsa. 9 Na yi shi da kyau da rassansa masu yawa kuma dukkan itatuwan Iden da ke cikin lambun Allah suka yi kishinsa. 10 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Saboda yana da tsawo, kuma ya sa dogayen rassansa a tsakanin rassansa, ya ɗaukaka zuciyarsa sabili da tsawonsa. 11 Na rigaya na bayar da shi cikin hannuwan jarumi na al'ummai, ya yi masa dai-dai da muguntarsa. Na wurga shi waje. 12 Bãƙi waɗanda ke ta'addanci a dukkan al'ummai suka datse shi suka bar shi ya mutu. Rassansa suka fãɗi a kan tsaunuka da kuma dukkan kwari, rassansa suka kakkarye a cikin dukkan magudanun ruwaye na ƙasar. Sai dukkan al'ummai na duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka kuma tafi suka bar shi. 13 Dukkan tsuntsayen sararin sama suka sauka bisa tushen itacen da ya fãɗi, kuma kowacce dabba ta fili ta zo rassansa. 14 Wannan ya faru ne domin kada wata itaciyar ta tsiro kusa da ruwayen ta ɗaga ganyayesu zuwa ga itatuwa mafiya tsawo, kuma kada waɗansu itatuwa su yi girma gefen ruwayen su kai tsayinta. Dukkan su an sa sun mutu, a can ƙasa, a cikin 'ya'yan mutane, tare da waɗanda suka gangara cikin rami. 15 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A ranar da sida ya gangara zuwa Lahira na kawo makoki cikin duniya. Na rufe zurfafan ruwaye bisanta, na kuma tsayar da ruwayen teku. Na tsai da ruwaye masu girma, na kuma kawo makoki ga Lebanon dominsa. Saboda haka dukkan itatuwan saura suka yi makoki sabili da shi. 16 Na kawo rawar jiki ga al'ummai ta dalilin ƙarar faɗuwarsa, a lokacin da na wurga shi cikin lahira tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin rami. Sai na ta'azantar da dukkan itatuwan da ke a Iden a cikin wuraren duniya a ƙasa. Waɗannan su ne da zaɓaɓɓu da kuma mafi kyaun itatuwa na Lebanon; itatuwan da suka sha ruwan. 17 Gama suma suka gangara tare da shi zuwa Lahira, zuwa ga waɗanda aka kashe da takobi. Waɗannan su ne ƙarfin hannunsa, waɗannan al'umman da suka zauna cikin inuwarsa. 18 Wacce itaciya ce dai-dai da ke a ɗaukaka da girma? Gama za a kawo ki ƙasa tare da itatuwan Iden zuwa ƙarkashin ƙasa a tsakanin marasa kaciya; za ka zauna tare da waɗanda aka kashe da takobi.' Wannan shi ne Fir'auna tare da dukkan taronsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 32

1 Sa'an nan ya kasance a cikin wata na sha biyu ta shakara ta sha biyu, a rana ta farko ga watan, da maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, tãda makoki domin Fir'auna sarkin Masar; ka ce masa, 'Ka na kamar ɗan zaki a cikin al'ummai, amma ka zama kama da dodon ruwa na cikin teku; ka na dama ruwa, ka na dãma ruwaye da ƙafafunka ka kuma yamutsa ruwayensu. 3 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Haka zan warwatsa tãruna bisan ka cikin mutane da yawa, kuma za su ɗaga ka cikin tãruna. 4 Zan yashe ka cikin ƙasar. Zan wurga ka cikin fili in kuma sa dukkan tsuntsayen sammai su zauna bisanka; yunwar dukkan dabbobi masu rai a duniya za su ƙoshi ta wurin ka. 5 Gama zan sa naman ka a bisa tsaunuka, zan kuma cika kwarurruka da gawarka cike da tsutsotsi. 6 Sa'an nan zan watsar da jininka a bisa tsaunuka, ruwayen ƙarƙarshin ƙasa za su cika da jininka. 7 Bayan na katse ka, Zan rufe sammai in kuma baƙantar da taurarinsu; Zan rufe rana da giza-gizai, wata kuma ba zai bada haskensa ba. 8 Dukkan haske masu haskakawa a sammai zan baƙanta su bisan ka, zan kuma sa duhu bisa ƙasarka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 9 Da haka zan tsoratar da zuciyar mutane da yawa a cikin ƙasashen da ba ka sani ba, a lokacin da na kawo rushewarka a tsakiyar al'ummai, cikin ƙasashen da ba ka sani ba. 10 Zan firgita mutane da yawa saboda kai; sarakunansu za su girgiza cikin tsoro saboda kai a lokacin da zan jujjuya takobina a gabansu. A kowacce sa'a kowa zai yi rawar jiki saboda kai, a ranar faɗuwar ka. 11 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Takobin sarkin Babila zai auko gãba da kai. 12 Zan sa taron jama'arka mutanenka su faɗi ta hannun takobin jarumi - kowanne jarumi ɗan ta'adda ne ga al'ummai. Waɗannan jarumawa za su lalatar da fahariyar Masar su kuma lalata dukkan tarurrukanka. 13 Gama zan lalatar da dukkan garkunan da ke a bakin magudanun ruwaye masu yawa; tafin ƙafar mutum ba zai ƙara dãma ruwan ba, ko kuma kofatun dabbobi su dãma su. 14 Sa'an nan zan kwantar da ruwansu in sa ƙogunansu su zubo kamar mai - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 15 A sa'ad da na maida Masar yasasshiyar ƙasa, lokacin da aka maida ƙasar abin wofi sarai da dukkan cikarta, bayan na kai hari ga mazaunanta, za su san cewa Ni ne Yahweh. 16 Za a yi makoki; 'ya'ya mata na al'ummai za su yi makoki domin ta; za su yi makoki domin Masar, domin dukkan taruwar jama'arta za su yi makoki - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."' 17 Hakanan ya faru a cikin shekara ta sha biyu, a ranar sha biyar ga wata, da maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 18 "Ɗan mutum, ka yi kuka domin taron jama'ar Masar ka kuma jawo su ƙasa - ita da 'ya'yanta mata masu daraja na al'ummai-- zuwa cikin ƙarƙashin ƙasa tare da sụ waɗanada suke gangarawa cikin rami. 19 'Ki na da kyau fiye da wani? Je ƙasa ki kwanta da marasa kachiya.' 20 Za su faɗi daga cikin waɗanda aka kashe da takobi. An zare takobin! An miƙa ki ga takobin; za su kama ta tare da taron jama'arta. 21 Mafi ƙarfi daga cikin jarumawa a Lahira zai yi magana game da Masar da kuma abokan amanarta. Sun gangaro zuwa nan! Za su kwanta tare da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.' 22 Asiriya ta na can tare da dukkan jama'arta. Kaburburanta suna zagaye da ita; dukkansu an kashe su da takobi. 23 Su waɗanda kaburburansu na can cikin wuri mai zurfin rami su na can, da dukkan jama'arta. Kaburburanta sun zagaye dukkan waɗanda aka kashe, su da suka faɗi ta wurin takobi, su da suka jawo masifa a bisa ƙasar masu rai. 24 Ilam na wurin tare da dukkan taron. kaburburanta na zagaye da ita; dukkan su aka kashe su. Waɗanda suka faɗi ta wurin takobi, su da suka gangara ƙasa babu kaciya zuwa wurin zurfafa na iyakar ƙasa, su da suka kawo ta'addancin su bisa ƙasar masu rai kuma su waɗanda suke ɗauke da kunyarsu, tare da waɗanda suke gangarawa cikin rami. 25 Suka shirya wa Ilam makara da dukkan taron ta cikin tsakiyar waɗanda aka kashe; kaburburanta sun zagaye ta. Dukkan su marasa kaciya ne, an sha zararsu da takobi, domin sun kawo ta'addancinsu cikin ƙasar masu rai. Domin haka suna ɗauke da kunyarsu, tare da su waɗanda suke gangarawa zuwa cikin rami a tare da dukkan waɗanda aka kashe, waɗanda suke gangarawa zuwa cikin rami. Ilam na cikin dukkan waɗanda aka kashe. 26 Meshek, Tubal, da dukkan taron suna wurin! Kaburburansu na kewaye da su. Dukkansu marasa kaciya ne, aka kashe da takobi, domin sun kawo ta'addancinsu cikin ƙasar masu rai. 27 Ba su kwanta da jarumawan da suka faɗi na marasa kaciya waɗanda suka gangara zuwa Lahira da dukkan makamansu na yaƙi ba, kuma da dukkan makamansu ƙarƙashin kawunansu da kuma kurakuransu bisa ƙasusuwansu. Gama su ne 'yan ta'adda na jarumawa a cikin ƙasar masu rai. 28 To ke, Masar, za a kakkarya ki a cikin takiyar marasa kaciya! Za ki kwanta tare da waɗanda aka sare su da takobi. 29 Idom na wurin tare da sarkinta da kuma dukkan shugabanninta. An sanya su cikin ƙarfinsu tare da waɗanda aka kashe da takobi. Tare da marasa kaciya suka kwanta, tare da waɗanda suka gangara cikin rami. 30 Sarakunan arewa suna wurin - dukkansu da kuma dukkan Sidoniyawa waɗanda suka gangara ƙasa tare da waɗanda aka sare su. Suna da matuƙar karfi kuma suka sanya waɗansu jin tsoro, amma yanzu suna wurin cikin kunya, marasa kaciya tare da waɗanda aka sare da takobi. Sun ji kunyarsu, tare da waɗanda suke gangarawa cikin rami. 31 Fir'auna zai gani ya kuma karfafa game da dukkan taron jama'arsa waɗanda aka sare da takobi - Fir'auna tare da dukkan sojojinsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 32 Na sa shi a matsayin mai ban tsoro a cikin ƙasar masu rai, amma za a ajiye shi ƙasa a tsakiyar marasa kaciya, cikin waɗanda aka sare da takobi, Fir'auna da dukkan taron jama'arsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 33

1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Dan mutum, ka faɗa wa mutanenka wannan; ka ce masu, 'Sa'ad da na kawo takobi gãba da wata ƙasa, sai mutanen wannan ƙasar suka ɗauki ɗaya da ga cikin su suka maishe shi mai tsaro domin su. 3 Zai riƙa duba idan takobi ya taso wa ƙasar sai ya busa ƙahonsa ya faɗakar da mutane! 4 Idan mutanen suka ji ƙarar ƙaho amma ba su yi lura ba, idan kuma takobi ya zo ya kashe su, to kowanne ɗayansu alhakin jininsa na kansa. 5 Idan wani ya ji ƙarar ƙaho amma ya ƙyale, alhakin jininsa na kansa; amma idan ya kula, zai ceci na sa ran. 6 Idan kuwa, mai tsaro ya ga takobi yana tasowa, amma bai busa ƙaho ba, sakamakon bai faɗakar da mutane ba, takobi ya zo ya ɗauki ran wani, wannan mutum ya mutu cikin zunbinsa, zan biɗi alhakin jininsa daga hannun mai tsaro.' 7 Yanzu kai da kanka, ɗan mutum! Na saka ka zama mai tsaron gidan Isra'ila; za ka ji maganganu daga bakina kayi gargaɗi a madadi na. 8 Idan na cewa mugun mutum, 'Kai mugu, hakika za ka mutu!' Amma idan ba ka faɗakar da wannan ba domin a gargaɗi mugu game da hanyarsa, mugun nan zai mutu cikin zunubinsa, amma zan biɗi alhakin jininsa a hannun ka! 9 Amma idan kai, ka gargaɗi mugu game da hanyarsa, domin ya juyo ya bar ta, idan bai juyo yabar hanyarsa ba, to zai fa mutu cikin zunubinsa, amma kai da kanka ka riga ka ceci ranka. 10 Saboda haka, ɗan mutum, ka cewa gidan Isra'ila, 'Kuna cewa haka, 'Kurakuranmu da zunubanmu suna kanmu, muna kuma ruɓewa a cikin su! Ƙaƙa za mu rayu?'" 11 Ka ce masu, 'Muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba na farinciki da mutuwar mugu, domin idan mugu ya tuba daga hanyarsa, zai rayu! Ku Tuba! Ku Tuba daga mugayen hanyoyinku! Donme ne ne za ku mutu, gidan Isra'ila?' 12 Yanzu kai, ɗan mutum, ka cewa mutanenka, 'Ayyukan adalcin adali ba zai cece shi ba idan ya yi zunubi! Muguntar mugun mutum ba za ta sa shi ya hallaka ba, idan ya tuba daga zunubinsa! Domin mai adalci ba zai iya rayuwa ba saboda adalcinsa idan ya yi zunubi. 13 Idan na cewa adali, "Ba shakka za ka rayu!" idan kuwa ya dogara ga adalcinsa sa'an nan ya aikata rashin gaskiya, ba zan tuna da adalcinsa ba ko guda ɗaya. Zai mutu saboda muguntar da ya yi. 14 Idan na cewa mugu, "Ba shakka za ka mutu," amma kuma sai ya tuba daga zunubinsa ya aikata abin adalci da gaskiya - 15 idan ya mayar da ƙwacen da ya yi da sunan jingina, ko kuma ya mayar da abin da ya sata, kuma idan ya yi tafiya a cikin farillan rai ya dena yin laifi - ba shakka zai rayu. Ba zai mutu ba. 16 Ba za a kuma tuna masa da laifofinsa waɗanda ya aikata ba. Gama ya aikata gaskiya da adalci, saboda haka, zai rayu! 17 Amma mutanenka suka ce, "Hanyar Ubangiji ba dai-dai take ba!" alhali hanyoyinku ne ba dai-dai ba! 18 Sa'ad da adali ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu cikinsa! 19 Sa'ad da mugu ya juya ya bar muguntarsa ya yi abin da ke gaskiya da adalci, zai rayu saboda waɗannan abubuwa! 20 Amma ku mutane kun ce, '"Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce!" Zan shar'anta kowannenku bisa ga hanyarsa, gidan Isra'ila.'" 21 Wannan ya faru a shekara ta goma sha biyu, a rana ta biyar ga watan goma na bautar talalarmu, wani ɗan gudun hijira ya zo guna da ga Yerusalem ya ce, "An ci birnin!" 22 Hannun Yahweh yana bisana da maraice kafin ɗan gudun hijiran ya zo, bakina kuma ya rigaya ya buɗe kafin lokacin zuwansa da safe. Bakina kuwa ya buɗe; ban ƙara yin shuru ba! 23 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 24 "Ɗan mutum, waɗanda suke zaune cikin kango a ƙasar Isra'ila suna magana suna cewa, 'Ibrahim kaɗai ne ya gaji ƙasar, amma mu, muna da yawa! An riga an ba mu ƙasar a matsayin mallaka.' 25 Saboda haka ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi: Kuna cin nama da jini, kuna bautar gumakanku sa'an nan kuna zubda jinin mutane. Lallai sai kun mallaki ƙasar? 26 Kun kafa dogararku ga takubba, kunyi abubuwan banƙyama; kowannenku yana zina da matar maƙwabcinsa. Ya kamata ku mallaki ƙasar kenan?' 27 Za ka faɗa masu haka, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Muddin ina raye, 'hakika waɗanda ke kufai za a kashe su da takobi, zan kuma bada waɗanda ke jeji ga hallitu masu rai su zama abincinsu, waɗanda ke cikin kagaru da koguna annoba za ta kashe su. 28 Sa'an nan zan maida ƙasar kufai da kuma abin tsoro, ƙarfinta na taƙama zai ƙare, gama za a bar duwatsun Isra'ila, ba wanda zai ratsa ta cikinsu.' 29 Gama za su sani Ni ne Yahweh, sa'ad da na maida ƙasar kufai a lalace saboda dukkan abubuwan banƙyamar da suka aikata. 30 Yanzu kai, ɗan mutum - mutanenka suna faɗin abubuwa game da kai a jikin garu da ƙofofin gidaje, suna cewa junansu - kowanne mutum ga ɗan'uwansa, 'Bari mu je mu saurari maganar annabi wadda ta zo daga Yahweh!' 31 Mutanena za su zo wurinka, kamar yadda suka saba yi, za su zauna a gabanka su saurari maganganunka, amma ba za su yi biyayya da su ba. Maganganu masu kyau suna bakinsu, amma zukatansu na bin ƙazamar riba. 32 Gama kai kamar waƙa mai daɗi ne a gare su, ƙyakkyawar murya da a ke rairawa a kan garaya, lallai za su kasa kunne ga maganarka, amma ba ko ɗaya da zai yi biyayya da ita. 33 Saboda haka idan duk waɗannan sun faru - duba! haka kuwa zai faru! - sa'an nan ne za su sani annabi ya kasance a tsakanin su."

Sura 34

1 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci gãba da makiyayan Isra'ila. Yi annabci ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya cewa makiyaya: Kaiton makiyayan Isra'ila masu kiwon kansu. Bai kamata masu kiwo su tsare garke ba? 3 Kuna cin rabo mai tsoka kuna kuma sa tufafi na ulu. Kuna yanka masu ƙiba cikin garke. Baku yin kiwo ko kaɗan. 4 Ba ku ƙarfafa waɗanda ke da cututtuka ba, ko ku warkar da marasa lafiya. Waɗanda suka karye, ba ku ɗori su ba, waɗanda aka kora ba ku dawo da su ba ko ku nemo ɓatattu. Maimakon haka, kun mallaƙesu ƙarfi da yaji. 5 Sai suka warwatse saboda ba makiyayi, suka zama nama ga kowanne mai rai a jeji bayan an warwatsar da su. 6 Tumakina suka yi makuwa a kan duwatsu da tsaunuka, suka kuma warwatsu a dukkan faɗin duniya. Duk da haka ba wanda ya ke neman su. 7 Saboda haka, makiyaya, ku ji maganar Yahweh: 8 Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda tumakina sun zama ganima da abinci ga kowanne naman jeji, saboda rashin makiyayan kirki, kuma masu kiwon garkena ba su nemo tumakin ba, amma makiyayan sun kãre kansu, ba su yi kiwon garkena ba. 9 Saboda haka, makiyaya, ku ji maganar Yahweh: 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ina găba da masu kiwon tumakina, zan nemi tumaki na a hannunsu. Sa'an nan zan sallame su daga kiwon garkena; makiyayan ba za su ƙara kiwon kansu ba tunda zan ƙwace garkena daga bãkinsu, domin kada tumakina su ƙara zama abincinsu. 11 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ni da kaina zan nemo garkena in kuma lura da su, 12 kamar yadda makiyayi yakan nemi tumakinsa da suka watse daga cikin garkensa. Haka zan nemo tumakina, zan kuma cecesu daga dukkan wuraren da aka warwatsa su a ranar hadari da duhu. 13 Sa'an nan zan fito da su daga cikin al'ummai; zan tattaro su daga ƙasashe dabam dabam in kawo su ƙasarsu. Zan saukar da su a wurin kiwo mai dausayi a gefen duwatsu na Isra'ila, a maɓugɓugai, a dukkan wuraren da mutane ke zaune a ƙasar. 14 Zan sa su a makiyaya mai kyau; manyan duwatsun Isra'ila za su zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, inda akwai ciyawa da yawa, za su yi kiwo a tsaunukan Isra'ila. 15 Ni da kai na zan yi kiwon garkena, Ni da kaina kuma zan sa su kwanta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - 16 Zan nemo ɓatattu in kuma dawo da waɗanda aka watsar da su. Zan ɗora karyayyun tumaki, in warkar da marasa lafiya amma masu ƙiba da ƙarfafa zan hallaka su. Zan yi kiwo da adalci. 17 Yanzu dai ku, garkena - ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗa - duba, zan shar'anta tsakanin tunkiya da tunkiya, tsakanin raguna da bunsurai. 18 Bai isa ba ku ci ciyawa mai ƙyau, sai kun tattake ragowar da ƙafafunku; ku kuma sha ruwa mai kyau, sai kuma kun gurɓata rafin dukka da ƙafafunku? 19 Dole ne tumakina suci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku? 20 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗa masu haka: Duba! Ni da kaina zan shar'anta tsakanin tumaki masu ƙiba da ramammu, 21 domin kun tunkuɗe su da kwankwasonku da kuma kafaɗunku, kun kuma tunkuɗe dukkan marasa ƙarfi da ƙahonninku har sai da kuka warwatsar da su daga ƙasar. 22 Zan ceci garkena ba za su ƙara zama ganima ba, zan shar'anta tsakanin tunkiya da tunkiya! 23 Zan ɗora makiyayi guda a bisansu, bawana Dauda. Shi zai yi kiwon su, zai ciyar da su, zai kuma zama makiyayinsu. 24 Gama Ni, Yahweh, zan zama Allahnsu, kuma bawana Dauda zai zama sarki a cikin su - Ni, Yahweh, na furta wannan. 25 Sa'an nan zan yi alƙawarin salama da su in fitar da mugayen dabbobi a ƙasar, domin su zauna lafiya a jeji su kuma yi barci lafiya a kurmi. 26 Zan kuma kawo albarku a bisan su da kuma wurare kewaye da tuddaina, domin zan aiko da ruwan sama a lokacinsa. Zai zama ruwan albarka. 27 Sa'an nan itatuwan saura za su bada 'ya'yansu, ƙasa za ta bada amfaninta. Tumakina za su zauna lafiya a ƙasarsu; sa'an nan ne za su sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da zan karya gungumen kãrkiyarsu, in kuma cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su. 28 Ba za su ƙara zama ganima ga al'ummai ba, mugayen namomin jeji a bisa ƙasa ba za su cinye su ba. Gama za su zauna lafiya, ba kuma wanda zai tsoratasu. 29 Gama zan ƙebe masu mazaunin salama domin kada a ƙara zama da yunwa a cikin ƙasar, al'ummai kuma ba za su kawo zargi a kansu ba. 30 Sa, an nan za su sani cewa Ni, Yahweh Allahnsu, ina tare da su. Su jama'ata ne, gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 31 Gama ku tumakina ne, garken makiyayata, mutanena, ni kuma Allahnku ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'"

Sura 35

1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 '‌Ɗan mutum, kasa fuskarka gãba da Tsauna Seyir ka yi annabci gãba da shi. 3 Ka ce masa, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ina gãba da kai, Tsauni Seyir, kuma zan buge ka da hannuna in maishe ka kufai abin watsarwa. 4 Zan maida biranenka kufai, kai kuma da kanka za ka zama kango; sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh. 5 Domin kullum kana ƙiyayya da mutanen Isra'ila, kuma domin ka bashesu a hannun takobi a lokacin ƙuncinsu, a lokacin da hukuncinsu yake da zafi. 6 Saboda haka, Muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zan shiryaka domin zubar da jini, alhakin jini zai bi ka! Tun da ba ka ƙi zubar da jini ba, alhakin jini zai bi ka. 7 Zan maida Tsaunin Seyir kufai gaba ɗaya sa'ad da na datse mai shiga cikinsa da mai fita. 8 Sa'an nan zan cika duwatsunsa da gawawwakinsa. Da tuddansa da kwarurukansa da dukkan rafuffukansa, waɗanda aka kashe da takobi za su fǎɗa. 9 Zan sa ka yi ta zama kufai. Ba za a zauna cikin biranenka ba, amma za ka sani cewa Ni ne Yahweh. 10 Ka ce, "Waɗannan al'ummai biyu da ƙasashen nan biyu za su zama nawa, zan kuma mallakesu," koda yake Yahweh yana tare da su. 11 muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zan sãka maka gwargwadon fushinka da gwargwadon kishi da ƙiyayyar da ka yiwa Isra'ila, kuma zan bayyana kaina gare su sa'ad da na shar'anta ka. 12 Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh. Na ji ɓatancin da ka yi gãba da duwatsun Isra'ila, sa'ad da ka ce, "An lalatar da su; an rigaya an ba mu su mu cinye." 13 Ka ɗaukaka kanka gãba da ni da abin da ka faɗa, ka yi maganganu da yawa gãba da ni; na kuma ji su dukka. 14 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Zan maishe ka kufai, dukkan duniya za suyi murna. 15 Kamar yadda ka yi murna da gãdon mutanen Isra'ila saboda ta zama kufai, kai ma zan yi haka da kai. Za ka zama kufai, Tsaunin Seyir da dukkan Idom - dukkanta! Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh."'

Sura 36

1 Yanzu dai, ɗan mutum, ka yi annabci ga tsaunukan Isra'ila ka ce, "Tsaunukan Isra'ila, ku saurari maganar Yahweh. 2 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Magabci ya ce a kanka, "Aha!" kuma "Daɗaɗɗun tuddai na dã sun zama mallakarmu.'" 3 Saboda haka ka yi annabci kace, Ubangiji Yahweh ya ce: Saboda an maishe ka kufai an kuma murƙushe ka ta kowacce fuska, ka zama abin mallaka ga sauran al'ummai; ka zama abin ɓatanci a leɓuna da harsuna, a kuma labaran mutane. 4 Saboda haka, Tsaunukan Isra'ila, ku kasa kunne ga maganar Ubangiji Yahweh: Ubangiji Yahweh ya faɗi haka ga tsaunuka, da tuddai, da rafuffuka da kwarurruka, da kufafan da ba kowa da yasassun biranen da aka washe su sun zama ganima da abin ba'a ga sauran al'umman da ke kewaye da su - 5 saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Hakika nayi magana cikn zafin fushina da hasalata gãba da sauran al'ummai, gãba da Idom da dukkan waɗanda suka ƙwace ƙasata suka maisheta mallakarsu, gãba da dukkan masu murna a zuciyarsu ko reni a ruhunsu, yadda suka ƙwace ƙasata domin su mallaki wuraren kiwo su zama nasu.' 6 Saboda haka, ka yi annabci a kan ƙasar Isra'ila ka cewa tsaunuka da kuma tuddai, da rafuffuka da kwarurruka, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duba! A cikin fushina da hasalata nake furta wannan domin ka jure da zage-zagen al'ummai. 7 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ni da kaina zan ɗaga hannuna in rantse cewa al'ummai da ke kewaye daku tabbas za su sha tasu kunyar. 8 Amma ku, tsaunuka Isra'ila, za ku yi rassa ku haifi 'ya'ya domin mutanena Isra'ila, domin bada daɗewa ba za su komo wurinku. 9 Ku duba, Ni naku ne, na yi maku tagomashi; za a huɗe ku a kuma shuke ku da iri. 10 Saboda haka zan ruɓanya maku yawan mutanenku, koda dukkan gidan Isra'ila ne. Birane za su kasance da mazauna, za a sake gina rusassun wurare. 11 Zan riɓaɓɓanya mutum da dabba a kanku ku tsaunuka saboda su ruɓaɓɓanya su hayayyafa. Sa'an nan Zan sa a zauna a cikin ku kamar yadda kuke dã, zan sa ku yalwata fiye da dã, domin ku sani cewa Ni ne Yahweh. 12 Zan kawo mutane, jama'ata Isra'ila, su tattaka ku. Za su mallakeku, za ku zama gãdonsu, ba za ku ƙara sa 'ya'yansu su mutu ba. 13 Ubangiji Yaweh ya faɗi haka: Saboda suna ce maku, "Ku na cinye mutane, kuna sa 'ya'yan al'ummarku suna mutuwa," 14 saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba za ku ƙara sa al'ummarku ta yi makokin mutuwarsu ba. Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 15 Ba zan ƙara bari ku sake sauraren zage-zagen al'ummai ba, ba za ku ƙara jin kunyan mutane ba ko ku sa al'ummarku ta faɗi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'" 16 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo wuri na, cewa, 17 "‌Ɗan mutum, sa'ad da gidan Isra'ila suka gaji ƙasarsu, suka ƙazamtar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Hanyoyinsu a gabana kamar ƙazantar hailar mace suke. 18 Saboda haka na zuba hasalata gãba da su, domin zubar da jini da suka yi a ƙasar da kuma ƙazantarsu ta wurin gumakansu. 19 Na warwatsa su cikin al'ummai; suka warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon hanyoyinsu da ayyukansu. 20 Sai suka tafi cikin al'ummai, duk inda suka tafi, sai suka ɓata sunana mai tsarki sa'ad da mutane suka ce masu: 'Da gaske waɗannan mutanen Yahweh ne? Gama an fitar da su daga ƙasarsa.' 21 Amma ina da juyayi saboda sunana mai tsarki wanda gidan Isra'ila ya ƙazantar cikin al'ummai lokacin da suka tafi can. 22 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: 'Ba saboda ku nake wannan ba, gidan Isra'ila, amma saboda sunana mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al'ummai dukkan inda kuka tafi. 23 Gama zan sa sunana mai girma ya zama da tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al'ummai - a tsakiyar al'ummai, kuka ɓata shi. Sa'an nan al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh - wannan furcin Ubagiji Yahweh ne - sa'ad da za ku ga Ni mai tsarki ne. 24 Zan kwasoku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga kowacce ƙasa, zan kawo ku ƙasarku. 25 Sa'an nan zan yayyafa maku tsabtataccen ruwa domin ku tsarkaka daga dukkan ƙazantarku, zan kuma tsarkake ku daga gumakanku. 26 Zan ba ku sabuwar zuciya da sabon ruhu a cikinku, zan ɗauke zuciyar dutse daga cikinku. Gama zan ba ku zuciyar tsoka. 27 Zan sa Ruhuna a cikinku in sa ku kuyi tafiya a cikin farillaina da kiyaye umarnaina, domin ku yi su. 28 Sa'an nan za ku zauna a ƙasar da na ba kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku. 29 Gama zan ceceku daga dukkan ƙazantarku. Zan sa hatsi ya yawaita. Ba zan ƙara nawaitaku da yunwa ba. 30 Zan yawaita 'ya'yan itatuwa da amfanin gona domin kada ku ƙara jin kunya a wurin al'ummai saboda yunwa. 31 Sa'an nan za ku yi tunani a kan mugayen hanyoyinku da ayyukanku masu banƙyama, za ku nuna naɗama a fuskokinku sabili da zunubanku da kuma mugayen ayyukanku. 32 Ba dominku nake yin wannan ba - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - yakamata ku san wannan. Saboda haka, ku kunyata ku ƙasƙanta, saboda hanyoyinku ku gidan Isra'ila. 33 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: A ranar da na tsarkake ku daga dukkan kurakuranku, zan sa ku zauna a birane, ku kuma gina rusassun wurare. 34 Gama za ku noma ƙasa wadda take kufai a dã masu wucewa wurin ba za su gane ta ba. 35 Sa'an nan za su ce, "Wannan ƙasa wadda dă kufai ce yanzu ta zama kamar lambun Iden; rusassun birane da rusassun wurare waɗanda suka zama kufai an yi masu garu a na kuma zama a cikin su." 36 Sa'an nan sauran al'ummai da ke kewaye daku za su sani cewa Ni ne Yahweh, mai gina rusassun wurare da mai zaunar da mutane a yasassun wuri. Ni ne Yahweh. Ni na faɗi haka, zan kuma aiwatar da shi. 37 Ubangiji Yahweh ya faɗi: Gidan Isra'ila za su roƙe ni in yi masu haka, in riɓaɓɓanya su kamar garken mutane. 38 Kamar garken da aka keɓe domin hadayu, kamar garke a Yerusalem a lokacin bukukuwan idi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh."'

Sura 37

1 Hannun Yahweh yana bisa na, ya fito da ni waje ta wurin Ruhun Yahweh kuma ya zaunar da ni a tsakiyar wani kwari; yana cike da ƙasusuwa. 2 Daga nan ya sani na bi ta tsakiyar su ina ta zagayawa, Duba! Da yawansu birjik suna cikin kwarin. Duba! Ga su busassu ƙayau. 3 Sai ya ce mani, "'Dan mutum, ƙasusuwan nan za su iya rayuwa kuma?" Sai na ce, "Ubangiji Yahweh, kai kaɗai ka sani." 4 Daga nan ya ce mani, "'Ka yi annabci a kan waɗannan ƙasusuwa ka ce masu, 'Busassun ƙasusuwa. Ku saurari maganar Yahweh. 5 Ubangiji Yahweh ya cewa ƙasusuwan nan: Duba! Zan sa numfashi a cikinku, za ku kuma rayu. 6 Zan sa jijiyoyi a jikkunanku in kuma sa tsoka. Zan rufe ku da fata in hura numfashi a cikinku domin ku rayu. Daga nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh.'" 7 Sai na yi anabci kamar yadda ya umarce ni; da na ke anabcin, duba, sai wata ƙara ta fito, mai girgiza. Sai ƙasusuwan suka marmatso ga junansu - ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu. 8 Da na duba, ai kuwa, sai ga jijiyoyi a kansu, tsoka kuma ta fito fata kuma ta rufe su. Amma ba numfashi a cikinsu tukuna. 9 Daga nan Yahweh ya ce mani, "Yi anabci a kan numfashi, yi anabci, ɗan mutum, ka ce da numfashi, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Numfashi, ka zo daga kusurwai huɗu, ka hura a kan waɗannan da aka kashe, domin su rayu.'" 10 Sai na yi anabci kamar yadda aka umarce ni; numfashi ya shiga cikinsu suka rayu. Daga nan suka miƙe a kan ƙafafunsu, babbar rundunar mayaƙa. 11 Daga nan Yahweh ya ce da ni, "Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwan gidan Isra'ila ne dukka. Duba! Suna cewa, 'Kasusuwanmu sun bushe, zuciyarmu ta karai. An datse mu.' 12 Saboda haka ka yi anabci ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duba! Zan buɗe kabarbarunku in tashe ku daga cikinsu, ya ku mutane na. Zan dawo daku ƙasar Isra'ila. 13 nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na buɗe kabarbarinku na tashe ku daga cikin su, mutane na. 14 Zan sa Ruhuna a cikin ku domin ku rayu, zan sa ku huta a ƙasarku sa'ad da kuka sani ni ne Yahweh. Ni na faɗa kuma zan aikata - wannan furcin Yahweh ne.'" 15 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 16 "Yanzu dai, ɗan mutum, ka ɗauki sanda guda domin kanka ka yi rubutu a kan sa, 'Domin Yahuda da mutanen Isra'ila abokan tarayya.' Sa'an nan ka ɗauki wata sandar ka yi rubutu a kansa, 'Domin Yosef reshen Ifraim kuma domin dukkan mutanen Isra'ila, abokan tarayya.' 17 Haɗa biyun su zama sanda guda, domin su zama ɗaya a hannunka. 18 Sa'ad da mutanenka za su yi maka magana, su ce, 'Ba za ka gaya mana abin da kake nufi da waɗannan ba?' 19 sai ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya ce: Duba! Ina ɗauke reshen Yosef da ke hannun Ifraim da kabilar Isra'ila abokan tarayyarsa domin in haɗa shi da Yahuda, domin su zama sanda guda, za su kuma zama ɗaya a hannuna.' 20 Ka riƙe sandunan da ka yi rubutu a kansu a hannunka a kan idanunsu. 21 Ka furta masu, Ubangiji Yahweh yafaɗi wannan: Duba! Ina gab da fitar da mutanen Isra'ila daga cikin al'ummai inda suka tafi. Zan tattaro su daga ƙasashen kewaye in kuma dawo da su ƙasarsu. 22 Zan tattaro su al'umma ɗaya a ƙasar, a kan tsaunukan Isra'ila, sarki guda ne zai yi sarauta bisansu dukka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba. Ba za a ƙara raba su zuwa masarautai biyu ba. 23 Daga nan ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumakansu ba, da abubuwansu na ban ƙyama, ko kowanne irin zunubansu ba. Gama zan cece su daga dukkan ayyukan rashin aminci waɗanda da su suka yi mani zunubi, zan kuma tsarkake su, domin su zama mutanena ni kuma in zama Allahnsu. 24 Bawana Dauda zai zama sarki bisansu. Domin su kasance da makiyayi ɗaya a bisansu dukka, za su yi tafiya bisa ga dokokina su kuma kiyaye farillaina su yi biyayya da su. 25 Za su zauna a ƙasar da na ba bawana Yakubu, inda ubanninku suka zauna. Za su zauna cikin ta har abada - da su, da 'ya'yansu, da jikokinsu, gama bawana Dauda zai zama sarkinsu har abada. 26 Zan kafa alƙawarin salama da su. Zai zama madawwamin alƙawari ne da su. Zan kafa su in ruɓanɓanya su, in kuma kafa wurina mai tsarki a tsakaninsu har abada. 27 Mazaunina zai kasance tare da su; zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena. 28 Daga nan al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh da na ƙeɓe Isra'ila da bam, sa'ad da wurina mai tsarki yana cikinsu har abada.'"

Sura 38

1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 2 Ɗan mutum, ka juya ka fuskanci Gog, ƙasar Magog, babban yariman Meshek da Tubal; ka kuma yi anabci gãba da shi. 3 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! ina gãba da kai, Gog, babban yariman Meshek da Tubal. 4 Domin in juya ka in kuma sa maka ƙugiya a muƙamuƙinka; Zan fitar da kai da dukkan sojojinka, da dawakai, da mahaya dawakan, dukkansu sun sa kayan yaƙi sosai, babbar runduna da manyaan garkuwoyi da ƙananan garkuwoyi, dukkan su suna riƙe da takubba! 5 Fasiya, Kush, da Libiya suna tare da su, dukkan su da garkuwoyi da hulunan kwano! 6 Goma da dukkan rundunarta, da Bet Togama, daga arewa mafi nisa, da dukkan rundunarta! Mutane da yawa na tare da kai! 7 shiri!, ka shirya kanka da tawagarka da suka yi layi tare kai, ka zama kwamandansu. 8 Bayan waɗansu kwanaki da waɗansu za a kiraka, kuma bayan waɗansu shekaru za ka je wata ƙasa da ta farfaɗo daga takobi wadda kuma aka tattaro daga mutane masu yawa, tattare aka koma tsaunin Isra'ila wanda ya ci gaba da zama kango. Amma mutanen ƙasar za a fito da su daga mutanen, kuma za su zauna cikin tsaro, dukkan su! 9 Saboda za ka tashi sama kamar yadda hadari ke yi; za ka zama kamar girgijen da yake rufe ƙasar, da duk rundunar sojojinka, da sojoji masu yawa da ke tare da kai. 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zai kuma faru a wannan ranar da aka tsara wannan shiri a zuciyarka, kuma za ka ɓata mugayen shirye-shirye.' 11 Daga nan za ka ce, zan je can buɗaɗɗiyar ƙasa; zan je wurin mutane masu natsuwa da ke zama cikin tsaro, dukkan su da ke rayuwa a inda babu garu ko danga, inda babu ƙofofin birane. 12 Zan kwaso kayayyaki in saci ganima, domin in kawo hannuna gaba da kangayen da yanzu mutane suka fara zama, da kuma gaba da al'ummai waɗanda ke samun dabbobi da kayayyaki, waɗanda kuma ke zama a tsakiyar duniya.' 13 Sheba da Dedan, da 'yan kasuwar Tarshish haɗe da matasan mayaƙanta za su ce da kai, Kun zo ne domin ku kwashi ganima? Kun tattara sojoji ne domin ku kwashi ganima, domin ku kwashi azurfa da zinariya, ku kuma kwashi dabbobinsu da kayayyaki ku kuma kwashi garar ganimar yaƙi?' 14 Saboda haka, ɗan mutum ka yi anabci, ka ce da Gog, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wannan rana, lokacin da mutanena Isra'ila na zama cikin tsaro, ba za ku koyi wani abu ba game da su? 15 Za ku fito daga wurarenku a can arewa mafi nisa tare da babbar rundunar sojoji, dukkan su suna kan dawakai, babbar runduna, manyan mayaƙa. 16 Za ka kai hari ga mutanena Isra'ila kamar girgijen da ya rufe ƙasar. A kwanaki masu zuwa zan kawo ka gãba da ƙasata, domin ƙasashe su san ni a lokacin da na nuna kaina ta wurinka, Gog, ka zama da tsarki a idanunsu. 17 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ba ku ba ne waɗanda na yi magana a kan ku a waɗancan kwanaki ta hannun bayina, annabawan Isra'ila, waɗanda suka yi anabci a nasu lokuttan game da shekarun da zan kawo ku gãba da su? 18 Haka zai faru a waɗancan kwanaki bayan Gog ya kai hari ƙasar Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - fushina zai yi ƙuna a cikin hasalata. 19 A cikin himmata da kuma cikin wutar fushina, na furta cewa za'a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra'ila. 20 Za su girgiza a gabana - da kifayen teku da tsuntsayen sama, da dabbobin saura, da dukkan dabbobi masu rarrafe a duniya, da kowanne mutum da ke a doron ƙasa. Za'a ragargaza duwatsu ɓallin zai faɗi, har sai kowacce kusurwa ta faɗi a kan duniya. 21 Zan kawo takobi a kansu a kan dukkan duwatsu -wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh - kowanne mutum zai juya takobinsa gãba da ɗan'uwansa. 22 Bayan wannan zan hukunta shi da annoba da jini; da kuma ambaliyar ruwa da aman duwatsu da tattatsin wuta zan saukar a kansa shi da rundunarsa da dukkan al'umman da ke kewaye da shi. 23 Domin zan nuna girmana da tsarkina zan kuma sa al'ummai da yawa su san ni, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh.'"

Sura 39

1 "Yanzu, kai ɗan mutum, ka yi annabci gãba da Gog ka ce, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! ina gãba da kai Gog, sarkin Meshek da Tubal. 2 Zan juya ka in bi da kai; Zan kawo ka daga can arewa in kawo ka tsaunukan Isra'ila. 3 A sa'an nan ne zan bugi bakanka daga hannunka na hagu in kuma sa kibiya ta faɗi daga hannunka na dama. 4 Za ka fãɗi ƙasa matacce a kan tsaunukan Isra'ila -kai da tawagar da ke tare da kai da kuma sojojin da ke tare da kai. Zan miƙa ka ga tsuntsayen sama da dabbobin dawa ka zama abincinsu. 5 Za ka faɗi ƙasa a saura, domin ni da kaina na furta haka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 6 Daga nan zan aika da wuta a kan Magog a kan kuma masu zama cikin tsaro a wurare masu nisa, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh. 7 Domin zan sa su san sunana mai tsarki a tsakiyar mutanena Isra'ila, kuma ba zan taɓa yadda sunana ya ɓaci ba; al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh, mai Tsarki na Isra'ila. 8 Duba! Rana na zuwa, kuma za ta zo - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 9 Masu zama a biranen Isra'ila za su fita za su mori makamai su kunna wuta su ƙone su - ƙananan garkuwoyi, da manyan garkuwoyi, da bakkuna, da kibau, da kwarin mashi; za su wuta da su har tsawon shekaru bakwai. 10 Ba za su tattara itatuwa daga saura ba ko su sassaro bishiyoyi daga dawa, tun da ya ke za su ƙona makamansu; za su ɗauka daga wurin waɗanda ke son su ɗauka daga gare su; za su baje waɗanda suka so su baje su - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne." 11 Kuma zai zamana a wannan rana zan tanada wuri domin Gog - maƙabarta a Isra'ila, kwari ga waɗanda ke tafiya cikin gabashin kwarin teku. Zai toshe waɗanda ke son ƙetarewa su haye. A can za su binne Gog da dukkan mutane masu yawa da ke tare da shi. Za su kira shi kwarin Hamon Gog. 12 Har tsawon watanni bakwai gidan Isra'ila za su binne su domin su tsarkake ƙasar. 13 Domin dukkan mutanen ƙasar za su binne su; za su zama abin tunawa a gare su a lokacin da na sami ɗaukaka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 14 A sa'an nan ne za su keɓe mutanen da za su ci gaba da tafiya a cikin ƙasar, domin su sami waɗanda ke tafiya a ciki, amma waɗanda suka mutu gangar jukkunansu kuma na waje a ƙasar za su iya su binne su, domin su tsarkake ƙasar. A ƙarshen shekarun nan bakwai za su fara bincikensu. 15 A lokacin da mutanen nan ke tafiya a cikin ƙasar, bayan sun ga ƙashin mutum za su sa alama a gefenta, har sai masu haƙar kabari sun zo domin su binne su a kwarin Hamon Gog. 16 Za'a sami wani birni a can ta wurin sunan Hamona. A wannan hanya za su tsarkake ƙasar. 17 Yanzu a gare ka, ɗan mutum, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ka faɗi wannan ga dukkan tsuntsayen sama da dukkan dabbobin daji, 'Ku taru wuri ɗaya ku zo. Ku tattaru daga ko'ina ku kewaye hadayar da ni kaina nake miƙawa a kan tsaunukan Isra'ila, domin ku ci gangar jiki ku kuma sha jini. 18 Za ku ci jikkunan mayaƙa ku kuma sha jinin shugabannin duniya; za su zama raguna, da 'yan raguna, da awaki. da bijimai, duk sun yi ƙiba a Bashan. 19 Daga nan za ku ci wadataccen kitse ku ci ku ƙoshi; ku kuma sha jini har sai kun bugu; wannan ita ce hadayar da zan yanka dominku. 20 A kan teburina za ku ƙoshi da dawakai, da karusai, da mayaƙi, da dukkan jaruman yaƙi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.' 21 Zan sa ɗaukakata a cikin al'ummai, kuma dukkan al'ummai za su ga hukuncina da nayi da kuma hannuna da na sa nake gãba da su. 22 Gidan isra'ila za su sani cewa Ni ne Yahweh Allansu daga wannan rana zuwa gaba. 23 Al'ummai za su sani cewa gidan Isra'ila sun je bauta saboda laifofinsu wanda ta wurinsu suka bashe ni, domin haka na ɓoye fuskata daga gare su, na kuma miƙa su ga abokan gãbarsu domin a hallaka dukkan su da takobi. 24 Na yi masu gwargwadon ƙazantarsu da zunubansu, a lokacin da na kawar da fuskata daga gare su. 25 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan; Yanzu zan komo da damar Yakubu, kuma zan ji tausayin dukkan gidan Is'raila, a lokocin da na yi haka da himmar sunana mai tsarki. 26 A lokacin za su sha kunyarsu a cikin dukkan cin amanar da suka bashe ni. Za su manta da duk wannan a lokacin da suka huta a cikin ƙasarsu cikin tsaro, inda ba wanda zai firgita su. 27 lokacin da na komo da su daga cikin jama'a na kuma tattaro su daga ƙasar maƙiyansu, zan nuna kaina a matsayin mai tsarki a idon al'ummai masu yawa. 28 Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh Allahnsu, domin na aika su zuwa bauta a cikin al'ummai, amma zan sake tattara su a ƙasarsu. Ba zan rage ko ɗaya daga cikinsu ba a cikin al'ummai. 29 Ba zan sake ɓoye fuskata daga garesu ba a lokacin da na huro Ruhuna a kan gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 40

1 A cikin shekara ta ashirin da biyar ta bautar talalarmu a farkon shekara a rana ta goma ga wata, A shekara ta sha huɗu bayan an kame birnin a wannan dai ranar, hannun Yahweh na bisana ya kuma ɗauke ni zuwa can. 2 A cikin wahayai daga Allah sai ya kawo ni zuwa ƙasar Isra'ila. Ya kawo ni in huta a kan tsauni mai tsawo sosai; a ɓangaren kudu inda abin da ya bayyana ya zama gine-ginen birni. 3 Sai ya kawo ni can. Sai ga wani mutum! Bayyanuwarsa kamar bayyanuwar tagulla. Yana ɗauke da igiyar linin da sandar awo a hannunsa, sai ya tsaya a bakin ƙofar birnin. Mutumin ya ce da ni, 4 "Dan mutum, ka duba da idanunka ka kuma saurara da kunnuwanka, ka kuma maida hankali ga dukkan abin da nake bayyana maka, domin an kawo ka nan ne domin in bayyana maka su. Ka bada rahoton duk abin da za ka gani ga gidan Isra'ila." 5 Akwai katangar da ta kewaye haikali. Tsawon sandar awon a hannun mutumin kamu shida ne. Dukkan mizanan tsawonsu iri ɗaya. Sai ya auna katangar; ta kai kamu ɗaya da rabi na tsawon sandar awon. 6 Daga nan sai ya tafi ƙofar haikali da ke fuskantar gabas. Sai ya hau kan matakansa ya auna ginshiƙin ƙofar tsawonsa shi ne dai-dai tsawon sandar gwajin a zurfi. 7 Ɗakunan tsaron dukkan su kamun sandar awon ɗaya a tsawo kuma ɗaya ne a fãɗi; akwai tsawon kamu biyar a tsakanin kowanne ɗakuna biyu, kuma daga dankarin shirayin haikalin akwai kwararo mai tsayi da aka kafa ƙasa. 8 Sai ya auna kwararon ƙofar; faɗinsa ya kai kamu guda na sandar awon. 9 Ya auna kwararon ƙofar. Zurfinsa ya kai kamu guda na sandar awo. Madogaran ƙofofin sun kai kamu biyu a fãɗi. Wannan shi ne kwararon ƙofar da ke fuskantar haikali. 10 Akwai ɗakunan tsaro guda uku a kowacce kwana a ɓangaren gabas, kuma dukkan su suna da awo iri ɗaya ne, kuma katangar da ta raba su ita ma awo iri ɗaya ne. 11 Daga nan mutumin ya auna faɗin ƙofar shiga - aka sami kamu goma; kuma faɗin ƙofar shiga - ya kai kamu goma sha uku. 12 Sai ya auna katangar da ke iyaka da ɗakuna na gaba - tsayinta kamu guda ne. Aka auna ɗakunan kowannen su ya kai kamu shida a kowanne gefe. 13 Daga nan sai ya auna ƙofar shiga daga rufin ɗaya daga cikin ɗakin har zuwa ɗaki na gaba - aka sami kamu ashirin da biyar, daga ƙofar farko ta shiga ɗakin har ya zuwa ta biyun. 14 Daga nan ya auna katangar da ta bi ta tsakanin ɗakunan tsaron - tsawonsu ya kai kamu sittin; ya auna har ya zuwa kwararon ƙofar. 15 Mashigi daga ƙofar gaba har ya zuwa kwararon ƙofar ƙarshen kamu hamsin. 16 Akwai kullallun tagogi a kusa da ɗakunan da kuma kusa da madogaran da ke cikin dukkan ƙofofin da ke kewayen; hakannan kuma zaurukan. Akwai tagogin da ke kewaye a ciki, kuma kowanne ƙyaure an yi masa ado da itacen kwakwa. 17 Sai mutumin ya kawo ni harabar waje da haikalin. Duba, ga ɗakuna, akwai gefen hanya a harabar, da kuma ɗakuna sittin a gaban harabar, da ɗakuna talatin gaba da gefen hanyar. 18 Gefen hanyar ya bi ta gefen ƙofofin, kuma fasalinsu ɗaya ne da tsawon ƙofofin. Wannan shi ne gefen hanya mafi kwari. 19 Sai mutumin ya auna nisan daga gaban ƙaramar ƙofa zuwa gaban ƙofofi na ƙurya; kamu ɗari ne daga bangon gabas, haka kuma yake a bangon arewa. 20 Daga nan sai ya auna tsawo da fadin ƙofar da ke arewa a can cikin harabar waje 21 Akwai ɗakuna guda uku a kowanne gefe na ƙofar, ƙofar da kwararonta duk suma an auna su kamar yadda aka auna babbar ƙofar - tsawonta dukka kamu hamsin ne sai fadinta kuma kamu ashirin da biyar ne 22 Tagogin, da kwararon, da ɗakunan, da bishiyoyin dabinon da aka sa a ƙofar da ke fuskantar gabas. Taki bakwai su ne suka kai kwararonsa. 23 Akwai kuma wata ƙofar daga ciki wadda ke fuskantar arewa, kamar dai yadda akwai ƙofa a gabas; mutumin ya auna daga ƙofa ɗaya zuwa ƙofa ɗaya - ya sami kamu dari na nisa. 24 A gaba sai mutumin ya kawo ni ƙofar shiga ta kudu, kusurwarta da tsawonta suma ya auna su kamar yadda ya auna sauran ƙofofin. 25 Akwai tagogi da ke a kulle a kan hanyar ƙofar da kwararonta kamar dai irin na waccan ƙofar. Kofar kudu da kwararonta tsawonta kamu hamsin ne faɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. 26 Akwai kuma ƙofa zuwa can ƙuryar harabar daga bangon kudu tsawonta kamu ɗari ne. 27 Akwai matakai bakwai da ake hawa zuwa ƙofar da kwararonta akwai kuma itacen dabino da aka kewaye katangar da su a kowanne gefe. 28 Sai mutumin ya kawo ni ƙuryar harabar ta hanyar ƙofarsa ta kudu, wadda ke da awo irin na sauran ƙofofin. 29 da bangayen, da kwararon duk awonsu dai-dai ne da na sauran ƙofofin; kuma akwai tagogi a ko'ina a kwararon. ƙofar ciki da girmanta kamu hamsin ne na tsawo kuma faɗinta kamu ashirin da biyar ne. 30 Kuma akwai kwararo da suka kewaye katangar ta ta ciki a ko'ina; waɗannan ne ma su kamu ashirin da biyar a tsawo da kuma kamu biyar na faɗi. 31 Wannan kwararo ya fuskanci harabar waje da aka kewaye da sassaƙaƙƙun itatuwan dabino a bangonta kuma akwai matakai takwas da a ke takawa a hau samanta. 32 Daga nan sai mutumin ya kawo ni cikin haraba ta ƙurya ta bangon gabas ya kuma auna ƙofar, ita ma awonsu ɗaya da sauran ƙofofin. 33 Ɗakunansa, da bangayen, da kwararon suma an auna su kamar yadda aka auna sauran ƙofofin, kuma awonsu dai-dai, kuma akwai tagogi a kewaye a ko'ina. Ƙofar ciki da kwararonta an auna tsawonsu kamu hamsin, faɗinsu kuma kamu ashirin da biyar. 34 Kwararonta na fuskanci harabar waje; kuma tana da itatuwan dabino a kowanne gefe kewaye da matakai takwas na hawa bisansa. 35 A gaba sai mutumin ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta; awonta dai-dai ne da sauran ƙofofin. 36 Ɗakunanta, da bangayenta, da kwararonta duk ɗaya suke da sauran ƙofofin, akwai kuma tagogi a kewaye a ko'ina. ƙofar shiga da kwararonta an auna kamu hamsin na tsawo, sai kamu ashirin da biyar na faɗi. 37 Kwararonta na fuskantar harabar waje; tana kuma da itatuwan dabino a kowacce kusurwarsa da kuma matakai takwas na hawa samansa. 38 Akwai ɗaki da ƙofa a kowanne gefe na hanyoyin shiga da ke ciki. Wannan ne wurin da suke ɗauraye baye-baye na ƙonawa. 39 Da tebura guda biyu a kowanne gefen kowanne kwararo, inda a ke yanka baikon ƙonawa a kai, haka kuma baiko na zunubi da kuma baiko na laifi. 40 Bangon harabar, da ya bi ta ƙofa zuwa arewa, akwai tebura guda biyu. Hakan nan a ɗaya gefen shi ma akwai tebura guda biyu a kwararon ƙofar. 41 Akwai kuma tebura guda huɗu a kowanne gefe wurin ƙofa; su na yanka dabbobi a kan teburan nan guda takwas. 42 Akwai kuma tebura huɗu na yakkakken dutse domin baye-baye na ƙonawa, tsawonsu kamu ɗaya da rabi, sanan faɗinsa rabin kamu ne, tsayinsa kuma kamu guda ne. A kansu suke ɗora kayayyakin da suke yanka baye-baye na ƙonawa da su. 43 Aka kakkafa matsirai guda biyu tsawonsu kamun hannu ne a kwararon kewaye da ko'ina, domin a dinga ƙyafe naman baye-bayen da za'a miƙa a kan teburan. 44 A waje da ƙofar ciki, a cikin harabar ciki, akwai ɗakuna na mawaƙa, ɗaya daga gefen arewa yana fuskantar kudu, ɗayan kuma daga gefen kudu yana fuskantar arewa. 45 Bayan haka sai mutumin ya ce da ni, "Wannan ɗakin da ke fuskantar kudu domin firistoci ne waɗanda ke kan aiki a cikin haikali. 46 Ɗakin da ke duban arewa na firistocin da ke kan aiki ne a bagadi. Waɗannan sune 'ya'yan Zadok da suka zuwa kusa da Yahweh domin su bauta masa; suna cikin 'ya'yan Lebi." 47 A gaba sai ya auna harabar - tsawo kamu dari faɗi kuma kamu ɗari ne, tare da bagadi a gaban gidan. 48 Sai mutumin ya ɗauko ni ya kawo ni kwararon gidan ya kuma auna madogaran ƙofofin - kaurinsu ya kai kamu biyar a kowanne gefe. Hanyar shiga ita kanta kuma sha huɗu ne a faɗi, kuma bangayen kowanne gefe faɗinsu kamu uku ne. 49 Tsawon kwararon ya kai kamu ashirin, kuma zurfinsa ya kai kamu sha ɗaya. Akwai matakai da suka nufe shi sama da lungunan da ke a kowanne gefen gini.

Sura 41

1 Sai mutumin ya kawo ni cikin wuri mai tsarki na haikali, sai ya auna madogaran ƙofofin - faɗinsa kamu shida ne ta kowanne gefe. 2 faɗin hanyar ƙofar ya kai kamu goma; bagon a kowanne gefe ya kai kamu biyar a tsawo. Daga nan sai mutumin ya auna fasalin wuri mai tsarki - tsawonsa kamu arba'in da faɗinsa kamu ashirin. 3 Daga nan mutumin ya tafi ya shiga wuri mafi tsarki ya auna madogaran hanyar ƙofar - aka sami awo biyu, hanyar ƙofar kuma kamu shida ne faɗinsa. Bangayen ta kowanne gefe kamu bakwai ne a faɗi. 4 Daga nan sai ya auna tsawon ɗaki - awo ashirin ne. Faɗinsa kuma - kamu ashirin ne zuwa gaban sararin haikalin. Daga nan sai ya ce mani, "Wannan shi ne wuri mafi tsarki." 5 Sai mutumin ya auna bangon gidan - kaurinsa kamu shida ne. Faɗin kowanne gefen ɗaki kewaye da gidan kamu huɗu ne a faɗi. 6 Akwai ɗakuna a gefe bisa hawa ku, ɗaki ɗaya bisa ɗaya, akwai ɗakuna talatin a kowanne hawa. Akwai ginshiƙai kewaye da bangon gidan, domin su zama makarai na dukkan ɗakunan da ke gefe, domin babu makarin da aka sa a bangon gidan. 7 To ɗakunan gefen suka faɗaɗa suka kewaya suka nufi sama, domin gidan ya zama bene kan bene a kewaya; ɗakunan suna faɗaɗa yayin da gida ke yin sama, hawan benen ya hau zuwa mataki mafi bisa, ta cikin mataki na tsakiya. 8 Sa'an nan na ga sashen da aka ɗaga dukkan kewayen gidan, da harsashe domin ɗakunan gefe; an auna shi kamun tsayin sanda - wato awo shida. 9 Faɗin bangon ɗakunan gefe ta waje awo biyar ne. Akwai kuma wuri buɗaɗe a wajen waɗannan ɗakunan a masujada. 10 A ɗaya gefen na wannan buɗaɗɗen fili akwai ɗakunan firistoci da ke waje; wannan filin faɗinsa ya kai awo ashirin a dukkan kewayen masujadar. 11 Akwai ƙofofi a cikin ɗakunan gefe daga wani buɗaɗɗen filin -akwai kuma wata hanyar ƙofar daga bangon arewa, da kuma wata daga kudu. Faɗin wannan buɗɗaɗen fili dukka kamu biyar ne. 12 Ginin da ya fuskanci harabar daga yamma ya kai kamu saba'in a faɗi. Bangonsa kuma da aka auna ya kai kamu biyar a kauri a kewaye da ko'ina, tsawonsa kuma ya kai kamu tasa'in. 13 Daga nan sai mutumin ya auna masujadar - tsawonsa kamu ɗari ne. Ginin da ke ware, da bangonsa, da harabar duk suma an auna su tsawonsu kuma ya kai kamu ɗari. 14 Faɗin gaban harabar a gaban masujadar shi ma kamu ɗari ne. 15 Sai mutumin ya auna tsawon ginin da ke bayan masujadar, zuwa yammacinsa, da ɗakunan ajiya da ke a dukkan gefen - aka sami awo ɗari. Wuri mai tsarki da kwararon, 16 da bangayen ciki da tagogi da duk da ƙananan tagogi, da ɗakunan ajiya kewaye da dukkan hawa ukunnan, duk an ƙayata su da katako 17 A saman hanyar shiga zuwa masujada ta ciki da kuma filin da ke wurin shi ma duk an auna shi. 18 An yi masa ado da kerubim da itatuwan dabino a tsakanin kowanne kerubim da kerubim, kuma kowanne kerubim na da fuskoki biyu: 19 fuskar mutum na duban itacen dabino ta gefe ɗaya da kuma fuskar sagarin zaki da ke duban ɗaya gefen. Sun kewaye ko'ina na gidan, 20 Doga ƙasa har zuwa saman hanyar ƙofa, an kewaye shi da kerubim da kuma itatuwan dabino a dukkan bangon gidan 21 Madogaran ƙofar wuri mai tsarki an yi masu zagaye. Kammanninsu kamar kamannin 22 bagadin katako ne a gaban wuri mai tsarki, wanda bisansa kamu uku ne, tsawonsa kuma kamu biyu ne ta kowanne gefe. Madogaran kusurwa, da harsashen, da matokaranta, da katako aka yi su. Sai mutumin ya ce da ni, "Wannan shi ne teburin da ke tsaye a gaban Yahweh." 23 Akwai ƙofofi ruɓi biyu manne domin wuri mai tsarki da kuma wuri mafi tsarki. 24 Waɗannan ƙofofin suna da maƙalatun ƙofa guda biyu, maƙalatun ƙofa biyu domin kowacce ƙofa. 25 Aka sassaƙa a kansu - a kan ƙofofin wuri mai tsarki - kerubim ne da itatuwan dabino, kamar dai yadda aka yi wa bango ado, kuma an yi rufin katako a kan kwararon daga gaba. 26 Akwai kuma tagogi da itatuwan dabino a gefen kwararon waɗannan su ne ɗakunan da ke gefen gidan, suma kuma suna da rufi a sama.

Sura 42

1 A gaba sai mutumin ya aike ni waje zuwa harabar ciki daga wajen arewa, sai ya kawo ni ɗakuna a gaban harabar waje da kumabangon waje daga kudu. 2 Waɗannan ɗakunan sun kai kamu ɗari a tsawonsa a gaba sai kuma kamu hamsin na faɗi. 3 Waɗansu daga cikin ɗakunan sun fuskanci harabar ciki nisansu daga masujadar ya kai kamu ashirin. Akwai ɗakuna hawa uku waɗanda ke sama suna duban ƙasa na waɗanda ke ƙasa da su, an kuma bubbuɗe masu ƙofofin da a ke bi. Waɗansu ɗakunan kuma suna duban haikalin. 4 Sararin wucewa kamu goma ne na faɗi da kuma kamu ɗari na tsawo su ne a gaban ɗakunan. Ƙofofin ɗakunan na duban arewa. 5 Amma ɗakunan taro na sama ƙanana ne daga nan ne a ke samun hanyar wucewa, ƙofofin suna da faɗi fiye da filin da ke a ƙasa da kuma tsakiyar matakai na ginin. 6 Domin ɗakunan taron da ke hawa na uku ba su da shingaye. Ba kamar harabar ba, da ke da shingaye. To benayen da ke can sama ƙanana ne in kwatanta da girman ɗakunan da ke ƙarƙas da kuma benaye na hawan tsakiya. 7 Bangon da ke waje ya bi ta kusa da harabar ciki, harabar da ke gaban ɗakunan. Wannan bangon ya kai kamu hamsin a tsayi. 8 Tsawon ɗakunan ya kai kamu hamsin, ɗakunan da ke fuskantar masujada kamunsu kamu ɗari ne a tsawo. 9 Akwai hanyar shiga ta ɗakunan da ke kwari da ke gefen gabas, da suka fito daga wajenharabar waje. 10 A gefen bangon harabar waje da ke gefen gabas da harabar waje, a gaban harabar ciki na masujada, akwai kuma waɗansu ɗakunan 11 da hanyar wucewa a gabansu. Suna kama da bayyanuwar ɗakunan a gefen arewa. Suna da tsawo da faɗi iri ɗaya kuma kasancewar iri ɗaya ne da jerin da ƙofofin. 12 A gefen kudu akwai ƙofofin zuwa cikin ɗakuna waɗanda suke dai-dai da da na gefeb arewa. Sararin wucewa daga ciki yana da ƙofa bisa kansa, kuma sararin wucewar ya buɗe zuwa cikin ɗakuna daban-daban. A gefen gabas akwai hanya da ke zuwa sararin wucewar a ƙarshe ɗaya. 13 Daga nan sai mutumin ya ce da ni, "Ɗakunan da ke arewa da kuma ɗakunan da ke kudu waɗanda ke a gaban harabar waje ɗakuna ne masu tsarki inda firistocin da ke aiki kusa da Yahweh za su iya cin abinci mafi tsarki. Za su ajiye abubuwa mafiya tsarki a can - baiko na abinci, da baiko na zunubi, dabaiko na laifi - domin wannan wuri mai tsarki. 14 Sa'ad da firistoci suka shiga can, ba za su fita daga wuri mai tsarki ba zuwa harabar waje, ba tare da sun ajiye tufafin da suea yin hidima da su ba, tun da ya ke waɗannan masu tsarki ne. To dole ne su sa waɗansu tufafin na da ban kafin su kusanci mutane." 15 Mutumin ya gama auna gida na ciki daga nan sai ya ɗauke ni zuwa waje zuwa ƙofar da ke duban gabas ya auna dukkan filayen da ke kewaye a can. 16 Ya auna gefen gabas da sandar awo - ya sami kamu ɗari biyar da sandar awon. 17 Ya auna gefen arewa - awo ɗari biyar da sandar awo. 18 Hakannan ya auna gefen kudu - awo ɗari biyar da sandar awo. 19 Ya kuma juya ya auna gefen yamma - awo ɗari biyar da sandar awo. 20 Ya auna sassan guda huɗu. Akwai bango a kewaye da shi tsawonsa kamu ɗari biyar, da kuma kamu ɗari biyar a faɗi, domin ya raba tsakanin wuri mai tsarki da kuma dandali.

Sura 43

1 Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da ta buɗe zuwa gabas. 2 Duba! ɗaukakar Allah na Isra'ila na zuwa daga gabas; muryarsa kamar rurin ruwaye masu yawa, duniya kuma ta haskaka da ɗaukakarsa. 3 Bisa ga bayyanuwar wahayin dana gani ne, bisa ga wahatin dana gani sa'ad da yazo domin ya lalatar da birnin, wahayoyin kuma sun yi kama da wahayin dana gani a Kogin Keba - sai na faɗi da fuskata. 4 Sai ɗaukakar Yahweh ta zo gidan daga ƙofar da ta buɗe zuwa gabas. 5 Sai Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin harabar ciki. Duba! ɗaukakar Yahweh ta cika gidan. 6 Mutumin na tsaye a gefena, sai na ji muryar wani mutumin da ban na magana da ni daga gidan. 7 Ya ce mani, "‌Ɗan mutum, wannan ne wurin kursiyina da kuma wurin sawayen ƙafafuna, inda zan zauna a tsakiyar mutanena Isra'ila har abada. Gidan Isra'ila ba za su ƙara rena sunana mai tsarki ba - su ko sarakunansu - da rashin amincinsu ko kuma da gawayen sarakunansu bisa dogayen wurarensu ba. 8 Ba za su sake rena sunana mai tsarki ba ta wurin kafa dankarin gidansu, da dankarin gidana ba, da kuma madogaran ƙofofinsu da madogaran ƙofofina ba, babu wani abu sai katanga kawai tsakanina da su. Suka rena sunana mai tsarki da ayyukansu na ƙazanta, sai na cinye su cikin fushina. 9 Yanzu bari su kawar da rashin amincinsu da gawarwakin sarakunansu daga gabana, daga nan in zauna a tsakiyarsu har abada. 10 ‌Ɗan mutum, kai da kanka dole ka gaya wa gidan Isra'ila game da wannan gida domin su ji kunyar kurakuransu. Su yi tunani game da wannan kwatancin. 11 Gama idan suka ji kunyar abin da suka yi, dagaan sai ka bayyana masu zanen gidan, da dukkan abin da ya ƙunsa, da wanzuwarsa, da hanyoyin shiga cikinsa, dukkan dokoki da ka'idodinsa. Daga nan sai ka rubuta wannan a gaban idanunsu domin su kiyaye dukkan tsarinsa da dukkan dokokinsa, domin su yi biyayya da su. 12 Wannan ne ka'idar gidan: Daga ƙololuwar tudu zuwa dukkan kewayen kan iyakar da ta kewaye shi, za ya zama mafi tsarki. Duba! wannan ce ka'idar gidan. 13 Waɗannan ne za su zama gwaje-gwajen bagadin bisa ga kamu-kamun kuwa dai-dai kamun tafin hannu a tsawonsa. To ramin da ke kewaye da bagadin zurfinsa za ya zama kamu ɗaya, faɗin sama kamu ɗaya. Kan iyakar da ke kewaye da gefensa zaya zama taƙi daya. Wannan ne za ya zama ƙasan bagadin. 14 Daga ramin daɓen ƙasa zuwa hawa na farko na bagadin kamu biyu ne, hawa na farkon kansa faɗinsa kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin hawan kuma zuwa babban hawan bagadin kamu huɗu ne, babban hawan kuma faɗinsa kamu ɗaya ne. 15 Murhun bagadin kuma domin baye-baye na ƙonawa bisansa kamu huɗu ne, akwai kuma ƙahonni huɗu da suka fuskanci sama a bisa murhun. 16 Tsawon murhun kamu sha biyu ne faɗinsa kuma kamu sha biyu ne, a kewaye. 17 Kan iyakarsa kuma tsawonsa kamu sha huɗu fadinsa kamu sha huɗu a fannoninsa huɗu, gefensa kuma rabin kamu a faɗi. Ramin kuwa faɗinsa kamu ɗaya ne a dukkan kewayen da matakalunsa na fuskantar gabas. 18 Daga nan sai ya ce mani, "‌Ɗan mutum, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Waɗannan ne ka'idoji domin bagadi a ranar da aka yi su, domin ɗaga baikon ƙonawa a kansa, da kuma yayyafa jini a kansa. 19 Za ku bada maraƙi daga cikin garken shanu a matsayin baikon zunubi domin Lebiyawa firistoci waɗanda ke na zuriyar Zadok, waɗanda ke zuwa kusa da ni su yi mani bauta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 20 Sai ka ɗauki jinin ka sa a ƙahonnin huɗu na bagadin, da fannoni huɗu na hawan da kewayen gefen kuma; za ka tsaftace shi ka kuma yi kaffara domin sa. 21 Sai ka ɗauki maraƙin baikon zunubin ka ƙona a wurin da aka zaɓa a sashen harabar haikalin da ke waje da masujadar. 22 A rana ta biyu sai ka miƙa bunsuru marar aibi daga garken awaki a matsayin baikon zunubi; Firistocin za su tsaftace bagadin da shi kamar yadda suka tsaftace shi da maraƙin. 23 Idan kuka gama tsaftace shi, sai ku miƙa maraƙi marar aibi daga garken shanu da rago marar aibi daga garken tumaki. 24 Ku miƙa su a gaban Yahweh; Firistocin za su barbaɗa masu gishiri su ɗaga su sama a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh. 25 Dole ku shirya bunsuru a matsayin baikon zunubi kullum har kwanaki bakwai, Firistoci kuma dole su shirya maraƙi marar aibi daga garken shanu da rago marar aibi daga garken tumaki. 26 Dole su yi kaffara ta kwana bakwai domin bagadin su tsarkake shi, ta wannan hanya dole su keɓe shi. 27 Dole su kammala waɗannan kwanaki, a rana ta takwas kuma da nan gaba za ya kasance Firistocin za su shirya baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a kan bagadin, kuma zan karɓe ku - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 44

1 Sai mutumin ya dawo da ni ƙofar masujadar da ke fuskantar gabas; an rufe ta gam. 2 Yahweh ya ce mani, "An datse wannan ƙofar gam; ba za a buɗe ta ba. Babu wanda za ya bi ta cikin ta, gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bi ta cikin ta, domin haka an rufe ta gam. 3 Shugaban Isra'ila za ya zauna a kai ya ci abinci a gaban Yahweh. Za ya shiga ta rumfar ƙofar ya kuma fita ta cikin ta." 4 Daga nan sai ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa da ke fuskantar gidan. Sai na gani na kuma duba, ga ɗaukakar Yahweh ta cika gadan Yahweh, sai na faɗi bisa fuskata. 5 Sai Yahweh ya ce mani, "‌Ɗan mutum, ka shirya zuciyarka ka kuma duba da idanunka ka saurara kuma da kunnuwanka dukkan abin da na ke furta maka. Ga dukkan farillai na gidan Yahweh da dukkan ka'idodin. Yi tunani game da ƙofofin shiga gidan dana fitarsa. 6 Sai ka faɗa wa kangararrun nan, gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Bari dukkan ayyukanku na ƙazanta su ishe ku, gidan Isra'ila - 7 Da kuka kawo baƙi marasa kaciyar zuciya da kaciyar jiki su kasance a Haikalina, suna rena gidana, yayin da kuke miƙa mani abinci, kitse da Jini - Kun karya alƙawarina da dukkan ayyukanku na ƙazanta. 8 Ba ku aiwatar da ayyukanku ba game da abubuwana masu tsarki, amma kuka zaɓi wasu suyi ayyukanku, kuka kuma sanyasu su lura da wurina maitsarki. 9 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ba bu wani baƙo, marar kaciyar zuciya da jiki, a cikin dukkan waɗanda ke zaune tare da mutanen Isra'ila, da za ya shiga wurina mai tsarki. 10 Amma Lebiyawa suka tafi nesa da ni - suka kauce daga gare ni, suka tafi ga gumakansu - amma za su biya domin zunubinsu. 11 Su bayi ne a haikalina, suna lura da ƙofofin gidan suna kuma yin bauta a cikin gidan suna kuma yanka baye-baye na ƙonawa da hadayun mutane, za su tsaya a gaban mutane su bauta masu. 12 Amma saboda sun miƙa hadayu ga gumakansu, sai suka zama abin sa tuntuɓe domin zunubi ga gidan Isra'ila. Saboda haka zan ɗaga hannuna in furta rantsuwa game da su - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zasu ɗauki nauyin horonsu. 13 Ba za su zo kusa da ni ba su yi aikin firistoci ko kuma su kusanci abubuwana masu tsarki, abubuwa mafi tsarki ba. Maimako haka, za su ɗauki zarginsu da laifofinsu domin ayyukan ƙazanta da suka aiwatar. 14 Amma zan maishe su masu tsaron aikin cikin gidan, domin dukkan ayyukansa da dukkan abin da a ke yi a cikinsa. 15 Daga nan su Lebiyawa firistoci, su waɗannan 'ya'ya maza na Zadok waɗanda suka cika ayyukan masujadata sa'ad da mutanen Isra'ila suke bauɗewa daga gare ni - za su zo kusa da ni su yi mani sujada. Za su tsaya a gabana su miƙa mani kitse da jini - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 16 Za su zo masujadata; za su kusanci teburina su yi mani sujada su kuma cika ayyukansu a gare ni. 17 Hakanan za ya kasance sa'ad da suka zo ƙofofin harabar ciki, dole su yi sutura da kayan linin, dole ne kuma ba za su zo cikin ƙofofin harabar ciki da gidansa ba a cikin suturar ulu. 18 Za su sa rawwunan linin a kawunansu da kuma bujen linin a kwankwasonsu. Ba za su yi sutura da kayan da za susa su yi zufa ba. 19 Idan suka fita zuwa harabar waje, zuwa harabar waje domin suje wurin mutanen, dole su tuɓe kayan da suka sa sa'ad da suke yin hidima; dole su tuɓe su su kuma ajiye su a cikin ɗaki mai tsarki, domin kada su maida sauran mutane masu tsarki ta wurin shafar suturarsu ta musamman. 20 Dole ne kuma ba za su aske kawunansu ba ko su bar gashinsu a rataye ba yana lilo, amma dole su yiwa gashin kawunansu saisaya. 21 Kada wani firist ya sha ruwan inabi idan za ya shiga harabar ciki, 22 ko kuma ya ɗaukarwa kansa gwauruwa ko bazawara a matsayin matar aure, sai dai budurwa kaɗai daga zuriyar gidan Isra'ila ko kuma gwauruwar da ta auri firist. 23 Gama za su koyawa mutanena bambanci tsakanin abu mai tsarki da abun reni; za su sanya su su san abu mai tsafta daga marar tsafta. 24 A wurin saɓani za su tsaya su yi hukunci da dokokina; dole su kasance masu adalci. Za su kiyaye shari'ata da farillaina a cikin kowanne buki, kuma su yi shagalin Asabataina masu tsarki. 25 Ba za su je ga wanda ya mutu ba domin su zama marasa tsarki, sai dai ko mahaifinsu ne ko mahaifiyarsu, ko ɗa ko ɗiya, ko ɗan'uwa ko 'yar'uwar da ba ta taɓa kwana da namiji ba; idan kuwa ba haka ba, za su zama marasa tsafta. 26 Bayan da firist ya zama marar tsafta, za su lissafa warewar tsawon kwana bakwai domin sa. 27 A ranar da za ya shiga wuri mai tsarki, a cikin harabar ciki domin ya yi bauta a wuri mai tsarki, dole ne ya kawo baikon zunubi domin kansa - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh. 28 Wannan za ya zama gãdonsu: Ni ne gãdonsu, tilas kuma ba za ku ba su kaddara ba a Isra'ila; Ni ne zan zama kaddararsu! 29 Za su ci baye-baye na abinci, da baye-baye na zunubi, da kuma baye-baye na laifi, da kuma dukkan abin da aka keɓe domin Yahweh a Isra'ila, za ya zama nasu. 30 Mafi kyau na 'ya'yan fari na dukkan abubuwa da kuma dukkan baiko, kowanne abu daga dukkan baye-baye za ya zama na firistoci, za ku kuma bayar da mafi kyau na baye-bayen abincinku ga firistoci domin albarka ta sauka bisa gidanku. 31 Firistoci kuma ba za su ci wani mushe ba ko dabbar da naman daji ya yaga, ko tsuntsu ne ko bisa ne.

Sura 45

1 Idan kuka jefa ƙuri'u domin raba ƙasar a matsayin gãdo, dole ku bayar da baiko domin Yahweh; wannan baiko za ya zama fanni mai tsarki na ƙasar, kamu dubu ashirin da biyar a tsawonsa, faɗinsa kuma kamu dubu goma. Za ya zama mai tsarki, da dukkan lardin da ke kewaye da shi. 2 Daga wannan za a ɗibi wuri kamu ɗari biyar na tsawo da kamu ɗari biyar na faɗi a kusurwa huɗu kewaye da wuri mai tsarki, da kuma kewayen kan iyakarsa kamu hamsin a faɗinsa. 3 Daga wannan lardin za ka ɗibi wuri kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kamu dubu goma a faɗi; shi ne za ya zama masujada, wuri mafi tsarki. 4 Za ya zama wuri mai tsarki a ƙasar domin firistoci da ke yiwa Yahweh bauta, waɗanda ke zuwa kusa da Yahweh su bauta masa. Za ya zama wuri domin gidajensu da kuma lardi mai tsarki domin wuri mai tsarki. 5 Saboda haka za ya zama kamu dubu ashirin da biyar a tsawonsa da kamu dubu goma a faɗinsa, za ya kuma zama garurruka domin Lebiyawa da ke bauta a gidan. 6 Zaku keɓe lardi domin birnin, kamu dubu biyar a faɗi da kamu dubu ashirin da biyar a tsawo, wanda zaya zama a gaba da lardin da aka keɓe domin wuri maitsarki; wannan birni zaya zama na dukkan gidan Isra'ila. 7 ‌Ƙasar shugaban zata kasance a ɓarayi biyu na lardin da aka keɓe domin wuri maitsarki da kuma birnin. Zaya zama a yamma da su da kuma gabas da su. Tsawonsa zaya zama dai-dai da tsawon ɗaya daga cikin wuraren da aka keɓe, daga yamma zuwa gabas. 8 Wannan ƙasa zata zama kaddarar shugaba a Isra'ila. Shugabannina ba zasu sake muzgunawa mutanenaba; Maimako, zasu bayar da ƙasar ga gidan Isra'ila, domin kabilunsu. 9 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ya isheku, shugabannin Isra'ila! Ku kawar da ta'addanci da rigima; kuyi hukunci da adalci! ku daina kawar da mutanena! - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh. 10 Dole kuyi ma'aunai na gaskiya, da jarka ta gaskiya, da daro na gaskiya! 11 Awon jarkar da daron su zama ɗaya, saboda daro ɗaya ya zama kashi ɗaya cikin goma na durom; jarkar kuma ta zama kashi ɗaya cikin goma na durom. Ma'auninsu zaya zama dai-dai da durom. 12 Shekel zaya zama gerori ashirin; shekel sittin zaya zama maina a gare ku. 13 Wannan ne baikon da ya zama tilas ku gabatar: kashi shida na jarka domin kowanne durom na alkama, zaku kuma bayar da kashi shida na jarka domin kowanne durom na bãli. 14 Baikon ka'ida na mai zaya zama kashi goma na daro wanda ya ke durom ɗaya (wanda ya ke darurruka goma), ko kuma kowanne durom, tunda ya ke durom ɗinma darurruka goma ne. 15 Tunkiya ɗaya ko akuya ɗaya daga cikin garken kowanne dabbobi ɗari biyu daga shiyyoyin ruwa na Isra'ila za a yi amfani da su domin baikon ƙonawa da baikon salama ayi kaffara domin mutanen - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh. 16 Dukkan mutanen ƙasar zasu bayar da wannan baiko ga shugaban Isra'ila. 17 Zaya zama aikin shugaban ya shirya dabbobin domin baye-baye na ƙonawa, da baye-baye na hatsi, da baye-baye na abin sha a lokacin shagulgula da bukukuwan sabon wata, da ranakun asabaci - dukkan kafaffun shagulgulan gidan Isra'ila. Zaya bayar domin baye-baye na zunubi, da baye-baye na hatsi, da baye-baye na ƙonawa, da baye-baye na salama domin kaffara a madadin gidan Isra'ila. 18 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wata na farko, a rana ta farko ga watan, zaku ɗauki maraƙi marar cikas daga garke kuyi baikon zunubi domin masujadar. 19 Firist zaya ɗiba daga cikin jinin baikon zunubin sai ya sanya a dawakan ƙofar gidan da kuma kusurwa hudu na kan iyakar bagadin, da kuma dawakan ƙofar shiga harabar ciki. 20 Zakuyi wannan a rana ta bakwai na watan domin zunubin kowanne mutum da a kayi cikin kuskure ko jahilci; ta wannan hanya zakuyi kaffara domin haikalin. 21 A cikin wata na farko a rana ta sha huɗu ga watan, akwai shagali dominku, shagali na kwana bakwai. Za kuci gurasa marar gami. 22 A wannan rana, shugaban zaya shiryawa kansa da dukkan mutanen maraƙi a matsayin baikon zunubi. 23 A kwanaki bakwai na bukin, shugaban zaya shirya baiko na ƙonawa ga Yahweh: maraƙai bakwai da raguna bakwai marasa cikas kowacce rana har ranaku bakwai, da kuma bunsuru kowacce rana a matsayin baikon zunubi. 24 Daga nan shugaban za ya yi baikon abinci na jarka ɗaya domin kowanne maraƙi da kuma jarka ɗaya domin kowanne rago da gwajin mai domin kowacce jarka. 25 A cikin wata na bakwai a rana ta sha biyar ga watan, a wurin shagalin, shugaban za ya yi baye-baye cikin waɗannan kwanaki bakwai: baye-baye na zunubi, baye-baye na ƙonawa, baye-baye na abinci, da baye-baye na mai.

Sura 46

1 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: ‌Ƙofar harabar ciki, da ke fuskantar gabas, za a rufe ta a cikin kwanaki shida na aiki, amma a ranar Asabaci za a buɗe ta, ranar sabon wata kuma za a buɗe ta. 2 Shugaban za ya shiga harabar waje ta hanyar ƙofar da rumfarta da ke waje, za ya kuma tsaya a dawakan ƙofa na ƙofar ciki yayin da firistocin ke shirya masa baikon ƙonawa da baikon salama. Daga nan sai ya yi sujada a dankarin ƙofar ciki sai ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma. 3 Mutanen ƙasar kuma za suyi sujada a gaban Yahweh a wurin shiga wannan ƙofa a ranakun asabaci da sabobbin watanni. 4 Baikon ƙonawa da shugaban zaya miƙa ga Yahweh a ranar asabaci zaya zama 'yan tumaki shida marasa cikas da kuma rago ɗaya marar cikas. 5 Baikon hatsi tare da ragon zaya zama jarka ɗaya, baikon hatsin dana 'yan ragunan zaya bayar bisa ga ra'ayinsa, da kuma gwajin mai ga kowacce jarkar hatsin. 6 A ranar sabon wata tilas ne ya miƙa maraƙi marar cikas daga garke, 'yan tumaki shida, da rago marar cikas. 7 Tilas ya miƙa baikon hatsi na jarka ɗaya domin maraƙin da kuma jarka ɗaya domin ragon, da abin da ya yi niyyar bayar wa domin 'yan tumakin, da kuma gwajin mai ga kowacce jarkar hatsi. 8 Idan shugaban ya shiga ta hanyar ƙofar da rumfarta, tilas ya fita ta hakan. 9 Amma idan mutanen ƙasar suka zo gaban Yahweh a lokacin shagulgulan da aka kafa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa domin ya yi sujada tilas ya fita ta ƙofar kudu; duk kuma wanda ya shiga ta ƙofar kudu tilas ya fita ta ƙofar arewa. Babu wanda za ya koma baya ta ƙofar da ya shiga, tilas ya miƙe ya fita ta gabansa. 10 Tilas shugaban ya kasance a tsakanin su; yayin da suke shiga, tilas ya shiga, yayin da suke fita, tilas ya fita. 11 A lokacin shagulgulan, baikon hatsin tilas ya zama jarkar hatsi ɗaya domin maraƙin da jarka ɗaya domin ragon, da kuma duk abin da ya yi niyyar bayarwa domin 'yan tumakin, da gwajin mai domin kowacce jarka. 12 Idan shugaban ya bayar da baikon yaddar rai, kodai baiko na ƙonawa ko baiko na salama ga Yahweh, za a buɗemashi ƙofar da ke fuskantar gabas. Zaya miƙa baikonsa na ƙonawa da baikonsa na salama kamar yadda ya ke yi a ranar asabaci. Daga nan tilas ya fita, bayan kuma daya fita sai a kulle ƙofar. 13 Bugu da ƙari, za ku bayar da ɗan rago marar cikas ɗan shekara ɗaya a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh kullum; za ku yi wannan safiya bayan safiya. 14 Za ku bayar da baikon hatsi tare da shi safiya bayan safiya, ka shi shida na garwar da kashi uku na gwajin mai domin a murtsike garin baikon hatsin ga Yahweh, bisa ga madawwamin farilla. 15 Za su shirya ɗan ragon, da baikon hatsin, da kuma mai safiya bayan safiya, baikon ƙonawa madawwami. 16 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: idan shugaban ya bayar da kyauta ga ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza, gãdonsa ne. Za ya zama kadarar 'ya'yansa maza, gãdo ne. 17 Amma idan ya bayar da kyauta daga gãdonsa ga ɗaya daga cikin bayinsa, za ya zama na bawannan har zuwa shekarar 'yantarwa, sai kuma a maida shi ga shugaban. Gãdonsa lallai za ya zama na 'ya'yansa maza ne. 18 Shugaban ba za ya ɗauke gãdon mutanen daga kadararsu ba; dole ya bayar ga 'ya'yansa maza daga kadararsa domin kada mutanena su warwatse, kowanne mutum daga kadararsa."' 19 Daga nan sai mutumin ya kawo ni ta hanyar shiga ɗakuna masu tsarki domin firistoci, masu fuskantar arewa duba kuma! Akwai wani wuri kuma zuwa yamma. 20 Ya ce mani, "Wannan ne wurin da tilas firistoci su dafa baikon laifofi da baikon zunubi inda kuma tilas su gasa baikon hatsi. Tilas kuma ba za su kawo baye-bayen ba zuwa harabar waje, domin mutanen za su zama keɓaɓɓu." 21 Daga nan ya kawo ni harabar waje ya bida ni na bi ta kusurwoyi huɗu na harabar, sai kuma na ga cewa a kowacce kusurwar harabar akwai wata harabar. 22 A kusurwoyi huɗu na harabar waje akwai waɗansu ƙananan harabai huɗu, kamu arba'in a tsawo da kamu talatin a faɗi. Dukkan harabobin huɗu gwajinsu ɗaya ne. 23 Akwai layin da aka yi da dutse kewaye da dukkan su huɗun, kuma murahun girki na ƙarƙashin dutsen. 24 Sai mutumin ya ce mani, "Waɗannan ne wuraren da bayin haikali za su dafa hadayun mutane."

Sura 47

1 Sai mutumin ya maida ni baya hanyar shiga haikalin, sai ga ruwa na ɓulɓulowa daga ƙarƙashin dankarin haikalin gidan zuwa gabas - gama gaban haikalin na fuskantar gabas - kuma ruwan na ɓulɓulawa ɓangaren kudu na haikalin, zuwa dama da bagadin. 2 Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa ya kuma bi da ni zagaye da ƙofar da ke fuskantar gabas, a nan ruwan yana ta malalawa daga wannan ƙofa zuwa kudu da ita. 3 Yayin da mutumin ke tafiya zuwa gabas, yana riƙe da magwaji a hannunsa; sai ya gwada kamu dubu ya kuma kawo ni ta cikin ruwan inda zurfinsa ya kai idon ƙafa. 4 Ya sake gwada kamu dubu ya kuma kawo ni ta cikin ruwan inda zurfinsa yakai gwiwa; ya sake gwada kamu dubu ya kuma kawo ni inda zurfin ruwan ya kai kwankwaso. 5 Sai ya sake gwada wani kamu dubu, amma ruwan ya zama kogi wanda bazan iya bi ta cikin ba gama ruwan ya taso sama zurfinsa kuma ya isa ayi iwo a ciki - ya zama kogin da ba a iya ƙetarewa. 6 Daga nan mutumin ya ce mani, "‌Ɗan mutum, ka ga wannan?" sai ya fito da ni waje ya kuma sa na tafi na koma baya ina tafiya ta gefen kogin. 7 Yayin da nake komawa baya sai na ga gefen kogin nada itatuwa da yawa a wannan gefe da kuma wancan gefe. 8 Mutumin ya ce mani, "Wannan ruwan na tafiya lardin gabas ne da ƙasa zuwa Araba; wannan ruwan yana gudu ne zuwa cikin tekun gishiri za ya kuma sabunta ta. 9 Za ya zama kuma duk wata halitta mai rai da ke iwo za ta kasance inda ruwan ya tafi; za ayi kifaye masu yawa, gama wannan ruwan za ya malala zuwa can. Za ya maida ruwan gishirin mai daɗi. Komai za ya rayu a duk inda ruwan ya je. 10 Daga nan za ya kasance masu kamun kifi na Engedi za su tsaya bakin ruwan, za a sami wurin shanya tarurrukan kamun kifin su bushe a En Egilayim. Za a sami kifaye daban-daban a Tekun Gishiri, kamar kifayen babbar teku domin tsananin yawansu. 11 Amma kududdufai da tafkunan Kogin Gishirin ba za a maida su masu daɗi ba; za su zama wurin samun gishiri. 12 Gefen wannan kogin a bakunansa, a gefensa biyu, itatuwa daban-daban masu bada abinci za su fito. Ganyayensu ba za su yi yaushi ba kuma ba za su taɓa dena bada 'ya'ya ba. Kowanne wata itatuwan za su bada 'ya'ya, saboda ruwa daga haikalin yana malalawa zuwa gare su. 'Ya'yansu za su zama domin abinci, ganyayensu kuma za su zama domin warkaswa. 13 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan ce hanyar da za ku raba ƙasar ga kabilu sha biyu na Isra'ila: Yosef za ya sami kaso biyu. 14 Za ku raba dai-dai abin da na ɗaga hannu na rantse wa ubanninku zan ba su. Wannan ƙasa za ta zo maku a matsayin gãdo. 15 Wannan ne za ya zama kan iyakar ƙasar a gefen arewa dagaBabbar Teku zuwa hanyar Hetlon, daga nan kuma zuwa Zedad. 16 Daga nan kan iyakar za ya tafi Berota, da Sibirayim, wadda ke tsakanin Damaskus da Hamat, daga nan kuma zuwa Haza Hattikon, wadda ke gefen kan iyakar Hauran. 17 Saboda haka kan iyakar za ya tafi daga teku zuwa Haza Enan kan iyaka da Damaskus da Hamat zuwa arewa. Wannan ne za ya zama ɓarayin arewa. 18 A gefen gabas, a tsakanin Hauran da Damaskus da kuma tsakanin Giliyad da ƙasar Isra'ila za ya zama Kogin Yodan. Tilas ka gwada daga kan iyaka zuwa tekun gabas; dukkan wannan za ya zama kan iyakar gabas. 19 Daga nan gefen kudu kan iyakar zai kama daga Tama zuwa ruwayen Meriba Kadesh, gulbin Masar zuwa BabbarTeku. Wannan zai zama kan iyakar gefen kudu. 20 Daga nan kan iyakar yamma za ya zama daga BabbarTeku zuwa inda ya tafi daura da Hamat. Wannan ne za ya zama gefen yamma. 21 Ta wannan hanyar za ku raba ƙasar a tsakaninku, domin kabilun Isra'ila. 22 Sai ku rarraba gãdon domin ku da kuma baƙin da ke zaune a tsakanin ku, su waɗanda suka haifi 'ya'ya a tsakanin ku, tare daku, kamar haihuwar 'yan asalin mutanen Isra'ila. Za ku jefa ƙuri'u domin gãdo a tsakanin kabilun Isra'ila. 23 Daga nan za ya zama cewa baƙo za ya kasance tare da kabilar da ke zaune tare da su. Tilas ku ba shi gãdo - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."

Sura 48

1 Waɗannan ne sunayen kabilun. Kabilar Dan za su karɓi kaso ɗaya na ƙasar; Kan iyakarsu za ya tafi dai-dai da kan iyakar Isra'ila ta arewa ta hanyar Hetlon da Lebo Hamat. Kan iyakar za ya tafi har zuwa Hazar Enan ya kuma tafi kan iyaka da Damaskus zuwa arewa daga nan har zuwa Hamat. Kan iyakar Dan za ya tafi daga gabas har zuwa Babbar Teku. 2 Haɗe da kan iyakar Dan, daga gefen gabas zuwa yamma, Asha za ya sami kaso ɗaya. 3 Haɗe da kan iyakar Asha, daga gefen gabas zuwa yamma, Naftali za ya sami kaso ɗaya. 4 Haɗe da kan iyakar Naftali daga gefen gabas zuwa yamma, Manasse za ya sami kaso ɗaya. 5 Haɗe da kan iyakar Manasse daga gefen gabas zuwa yamma, Ifraim za ya sami kaso ɗaya. 6 Haɗe da kan iyakar Ifraim daga gefen gabas zuwa yamma, Ruben za ya sami kaso ɗaya. 7 Haɗe da kan iyakar Ruben daga gefen gabas zuwa yamma, Yahuda za ya sami kaso ɗaya. 8 Baikon ƙasa da zaku bayar za ya kasance daga kan iyakar Yahuda ya zarce daga gefen gabas zuwa gefen yamma; Faɗin ta za ya zama kamu dubu ashirin da biyar. Tsawonta kuma za ya zama dai-dai da kason kabila ɗaya daga gefen gabas zuwa gefen yamma, Haikalin kuma za ya kasance a tsakiyarsa. 9 Wannan ƙasa da za ku miƙa baiko ga Yahweh za ta zama kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kuma kamu dubu goma a fãɗi. 10 Waɗannan ne za su zama ayyukan kason wannan ƙasa mai tsarki: za a ɗeba wa firistoci ƙasar a gwada kamu dubu ashirin da biyar bisa gefen arewa; kamu dubu goma a fãɗi bisa gefen yamma; kamu dubu goma a fãɗi bisa gefen gabas; kamu dubu ashirin da biyar kuma bisa gefen kudu, tare da wuri mai tsarki na Yahweh a tsakiyarta. 11 Wannan za ya zama domin keɓewar firistoci zuriyar Zadok, waɗanda suka bauta mani da aminci ba su kuma kauce ba a lokacin da mutanen Isra'ila suka kauce, yadda Lebiyawa suka yi. 12 Baiko dominsu za ya kasance kason wannan ƙasa mafi tsarki, ya zarce zuwa kan iyakar Lebiyawa. 13 ‌Ƙasar Lebiyawa da ke kan iyaka da ƙasar firistoci za ta kasance kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kamu dubu goma a fãɗi. Tsawon gabaɗaya na tsagawar ƙasar biyu za ya kasance kamu dubu ashirin da biyar da kuma kamu dubu ashirin a fãɗi. 14 Dole ba za su sai da ba ko su yi musanya da ita; 'Ya'yan fari na ƙasar Isra'ila dole ba za a taɓa ware su ba daga waɗannan karkasawar, gama dukkan ta mai tsarki ce ga Yahweh. 15 Sauran ƙasar, kamu dubu biyar a fãɗi da kamu dubu ashirin da biyar a tsawo, za ta zama abin amfanin birnin gabaɗaya, da gidajen, da saurar kiwo, birnin za ya kasance a tsakiya. 16 Waɗannan ne za su zama gwaje-gwajen birnin: Gefen arewa za ya zama kamu 4,500 a tsawo; gefen kudu za ya zama 4,500 a tsawo; gefen gabas za ya zama 4,500 a tsawo; gefen yamma za ya zama 4,500 a tsawo. 17 Za a fidda saura domin birnin wajen arewa, kamu 250 a zurfi; wajen kudu, kamu 250 a zurfi; wajen gabas, kamu 250 a zurfi; wajen yamma, kamu 250 a zurfi. 18 Sauran lardin domin baiko mai tasrki za ya zarce ya kai kamu dubu goma zuwa gabas da kamu dubu goma zuwa yamma. Za ta zarce har zuwa kan iyaka da baiko mai tsarki, amfanin ta kuma za ya zama abinci domin masu aiki cikin birnin. 19 Mutanen da ke aiki cikin birnin, mutanen da suka fito daga dukkan kabilun Isra'ila, za su noma wannan ƙasar. 20 Dukkan ƙasar baikon za a gwada kamu dubu ashirin da biyar da kamu dubu ashirin da biyar. Ta wannan hanyar za ku bada baikon mai tsarki da ƙasa, domin birnin. 21 Sauran ƙasar daga kowanne gefe na baiko mai tsarki da lardin birnin za ya zama domin shugaban. Tsagin ƙasar shugaban zuwa gabas za ta zarce ta kai kamu dubu ashirin da biyar daga kan iyakar baiko mai tsarki zuwa gabashin kan iyakar - tsagin nasa kuma daga yamma za ta zarce ta kai kamu dubu ashirin da biyar zuwa yammacin kan iyakar. Tsakiyar za ta zama baiko mai tsarki, wuri mai tsarki kuma na haikalin za ya kasance a tsakiyarta. 22 ‌Ƙasar za ta zarce daga kadarar Lebiyawa da kuma lardin birnin da ke tsakiya zaya zama na shugaban; za ta kasance tsakanin kan iyakar Yahuda da kuma kan iyakar Benyamin - wannan ƙasa za ta zama ta shugaban. 23 Sauran kabilun kuwa, na su kashi-kashinsu ma za ya fara daga gefen gabashi zuwa gefen yamma. Benyamin za ya karɓi kaso ɗaya. 24 Haɗe da kan iyakar Benyamin daga gefen gabas zuwa yamma, Simiyon za ya sami kaso ɗaya. 25 Haɗeda kan iyakar Simiyon daga gefen gabas zuwa yamma, Issaka za ya sami kaso ɗaya. 26 Haɗe da kan iyakar Issaka daga gefen gabas zuwa yamma, Zebulun za ya sami kaso ɗaya. 27 Daga kudancin kan iyakar Zebulun, ya kamo daga gefen gabas zuwa yamma, za ya zama ƙasar Gad - kaso ɗaya. 28 Kan iyakar kudancin Gad za ya zarce daga Tama zuwa Meriba Kadesh da kuma nesa daga tafkin Masar, daga nan kuma zuwa babbar teku. 29 Wannan ce ƙasar da za ku jefa ƙuri'u; za ta zama gadon kabilun Isra'ila. Waɗannan ne za su zama rabonsu. Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 30 Waɗannan ne za su zama wuraren fita daga birnin: a gefen arewa, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, 31 za ya zama ƙofofi uku, waɗanda za a yi wa suna domin kabilun Isra'ila: ƙofa ɗaya domin Ruben, ƙofa ɗaya domin Yahuda, ƙofa ɗaya kuma domin Lebi. 32 A gefen gabas, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Yusufu, ƙofa ɗaya domin Benyamin, ƙofa ɗaya kuma domin Dan. 33 A bangon kudu, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Simiyon, ƙofa ɗaya domin Issaka, ƙofa ɗaya kuma domin Zebulun. 34 A gefen yamma, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Gad, ƙofa ɗaya domin Asha, ƙofa ɗaya kuma domin Naftali. 35 Tazarar kewaye da birnin za ya zama kamu dubu sha takwas; daga ranar nan zuwa nan gaba, sunan birnin za ya zama "Yahweh yana wurin."

Littafin Daniyel
Littafin Daniyel
Sura 1

1 A cikin shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo Yerusalem ya kewaye birnin domin ya yanke dukkan abin da zai shigo cikinsa. 2 Ubangiji ya ba Nebukadnezza nasara akan Yehoyakim sarkin Yahuda, ya ba shi waɗansu keɓaɓun abubuwa daga gidan Allah. Ya kawo su cikin ƙasar Babila, zuwa gidan allahnsa, kuma ya sa keɓaɓun abubuwan a cikin ma'ajin allahnsa. 3 Sarkin ya yi magana da Ashfenaz, baban jami'insa, ya kawo waɗansu daga cikin mutanen Isra'ila, waɗanda su ke daga iyalin sarauta da kuma manyan mutane - 4 samari waɗanda ba su da cikas, kyawawa, ƙwararru a kowacce hikima, cike da ilimi da ganewa, waɗanda suka cancanci su yi aiki a fãdar sarki. Shi ne zai koya masu adabin mutanen Babila da harshensu. 5 Sarki ya ɗibar masu abinci daga abincinsa da ruwan inabi wanda ya ke sha. Za a horar da waɗannan samari har shekaru uku, bayan haka, za su yi wa sarki hidima. 6 A cikin su akwai Daniyel da Hananiya da Mishayel da Azariya, daga cikin mutanen Yahuda. 7 Babban jami'in ya ba su sunaye, Daniyel ya kira shi Beltishazza, ya kira Hananiya Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak Azariya kuma ya kira shi Abednego. 8 Amma Daniyel ya yi niyya a ransa, cewa ba zai ɓata kansa da abincin sarki ba ko da ruwan inabin da ya ke sha. Sai ya roƙi alfarma daga wurin babban jami'in saboda ba ya so ya ɓata kansa. 9 Sai Allah ya ba Daniyel tagomashi da tausayi daga babban jami'in ta wurin girmamawar da da ya ke yi masa. 10 Babban jami'in ya ce da Daniyel, "Ina jin tsoro shugabana sarki. Ya bada ummurni akan abincin da za ku ci da abin shan da za ku sha. Me ya sa zai gan ku da rãma da samari abokanku? Sarki zai fille kaina saboda ku." 11 Sa'annan Daniyel ya yi magana da mai aikin da babban jami'in ya sa ya kula da su Daniyel, Hananiya, Meshayel da Azariya. 12 Ya ce, "Idan ka yarda ka gwada mu bayinka na kwana goma, ka riƙa ba mu kayan lambu mu ci da kuma ruwa mu sha. 13 Sa'annan ka gwada baiyanarmu da baiyanar samarin da ke cin abincin sarki, ka yi mana mu bayinka, bisa ga abin da ka gani." 14 Sai mai hidimar ya yarda ya yi haka, ya gwada su kwana goma. 15 A ƙarshen kwanaki goman sai baiyanarsu ta fi lafiya, kuma suka fi duk samarin da ke cin abincin sarki annuri. 16 Sai mai hidimar ya ɗauke abincinsu da ruwan inabinsu ya ba su kayan lambu kawai. 17 Waɗannan samari huɗu, Allah ya ba su ilimi da ganewa da fahimtar dukkan adabi da hikima, Daniyel kuma ya na iya gane kowanne irin wahayi da mafarkai. 18 Da lokacin da sarki ya bayar a kawo su wurinsa ya yi, sai babban mai hidimar ya kawo su ciki gaban Nebukadnezza. 19 Sarki ya yi magana da su, a cikin dukkan taron babu wanda za a iya kwatanta shi da Daniyel, Hananiya, Meshayel da Azariya. Suka tsaya a gaban sarki, a shirye su yi masa hidima. 20 A cikin kowacce tambaya ta hikima da ganewa da sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukkan masu dũba da masu magana da kurwa waɗanda ke cikin dukkan mulkinsa har sau goma. 21 Daniyel ya zauna can har shekara ta fari ta Sairus.

Sura 2

1 A cikin shekara ta biyu ta mulkin Nebukadnezza, sai ya yi mafarkai. Hankalinsa ya tashi, bai iya yin barci ba. 2 Sarki ya umarta cewa masu dũba da masu cewa suna magana da kurwa su zo. Haka kuma ya kira masu sihiri da mutane masu hikima. Ya so su ba shi bayanin mafarkansa. Sai suka zo suka tsaya a gaban sarki. 3 Sarki ya ce da su, "Na yi mafarki, kuma raina ya ƙagara ya san ma'anar mafarkin." 4 Sai mutanen masu hikima suka yi wa sarki magana cikin harshen Aremiyanci, "Ranka ya dade ya sarki! Ka gaya mana mafarkin, bayinka kuwa za su baiyana maka ma'anarsa." 5 Sai sarki ya amsawa masu hikimar da cewa, "Wanann maganar a yanke take. Idan ba ku baiyana mani mafarkin da fassararsa ba, za a yayyaga jukkunanku a mayar da gidajenku kufai. 6 Amma idan kun baiyana mani mafarkin da ma'anarsa, za ku karɓi kyautai daga gare ni, da lada da ɗaukaka. To sai ku gaya mani mafarkin da ma'anarsa." 7 Suka sake amsawa suka ce, "Bari sarki ya gaya mana mafarkin, mu bayinsa mu kuwa za mu baiyana maka ma'anarsa." 8 Sai sarki ya amsa, "Tabbas na sani kuna bukatar ƙarin lokaci, saboda kun ga shawarata ta yi tsauri akan wannan abu. 9 Amma idan ba ku faɗa mani mafarkin ba, hukunci ɗaya ne a kanku. Kun shirya ku gaya mani ƙaryar da kuka shirya ku ka yarda a kanta da maganganu na ruɗi, har sai na canza shawarata. To ku gaya mani mafarkin, sa'annan zan sani za ku ba ni bayaninsa." 10 Masu hikima suka amsa wa sarki, "Ba wani mutum a duniya da zai iya biyan bukatar sarki. Ba wani babban sarki mai iko da ya taɓa bukatar irin wannan abu daga masu dũba, ko daga wani mai magana da kurwa, ko mutum mai hikima. 11 Abin da sarki ya ke bukata yana da wuya, ba wanda zai iya gaya wa sarki shi sai dai alloli, su kuma ba a cikin mutane suke zama ba." 12 Wannan ya sa sarki ya ji haushi ya hasala ƙwarai, ya bada ummurni a hallaka dukkan masu hikima na Babila. 13 Shela ta fita a kashe dukkan waɗanda aka sani su masu hikima ne. Saboda wannan doka, aka nemo Daniyel da abokansa domin a kashe su. 14 Sai Daniyel cikin ladabi da hikima ya amsa wa Ariyok shugaban masu tsaron sarki, wanda ya zo ya kashe dukkan waɗanda aka san masu hikima ne a cikin Babila. 15 Daniyel ya tambayi jami'in sarkin, "Me ya sa shelar sarki ta zo da sauri haka?" Ariyok ya gaya wa Daniyel abin da ya faru. 16 Sai Daniyel ya roƙi a ba shi lokaci ya zo wurin sarki domin ya kawo wa sarki fassara. 17 Sai Daniyel ya koma gida ya gaya wa su Hananiya, Meshayel da Azariya, abin da ya faru. 18 Ya roƙe su su nemi jinƙai daga Allah na sama akan wannan asiri domin kada a kashe su tare da sauran mutanen Babila waɗanda aka sani saboda da hikimarsu. 19 A wannan daren a ka baiyana wa Daniyel asirin a cikin ruya. Sa'annan Daniyel ya yabi Allah na sama 20 ya ce, "A yabi sunan Allah har abada abadin; gama hikima da iko nasa ne. 21 Shi ne mai canza lokatai da zamanai; ya kan cire sarakuna ya sa waɗansu sarakunan akan mulkokinsu. Ya kan ba da hikima da ilimi ga masu fahimta. 22 Yakan baiyana ɓoyayyun abubuwa masu zurfi gama shi ya san abin da ke cikin duhu, haske kuwa tare da shi ya ke zama. 23 Allah na ubannina, na gode maka na yabe ka saboda hikima da iko da ka ba ni. Yanzu ka sanar da ni abin da muka roƙe ka; ka kuma sa mun san abin da ya dami sarki." 24 Sai Daniyel ya shiga wurin Ariyok (wanda sarki ya sa ya kashe kowanne mai hikima a cikin Babila). Ya je ya ce masa, "Kada ka kashe masu hikima na cikin Babila. Ka kai ni wurin sarki zan nuna masa fassarar mafarkinsa." 25 Nan da nan kuwa Ariyok ya kawo Daniyel gaban sarki ya ce, "Na samo wani daga cikin 'yan bauta na Yahuda wanda zai baiyana wa sarki ma'anar mafarkinsa." 26 Sarki ya cewa Daniyel (wanda a ke kira Beltishazza), "Ko ka iya gaya mani mafarkin da na gani da ma'narsa?" 27 Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, "Asirin da sarki ya tambaya game da shi masu hikima ba zasu iya baiyana shi ba, ko masu magana da kurwa da masu dũba, ko masana taurari. 28 Duk da haka, akwai Allah wanda ya ke zaune a cikin sammai, wanda ya ke baiyana asirai, kuma ya sanar da kai, ya sarki Nebukadnezza, abin da zai faru a cikin kwanaki masu zuwa. Wannan shi ne mafarkinka da ruyar ranka lokacin da ka ke kwance akan gadonka. 29 Amma kai, ya sarki, zace-zacenka sa'ada ka ke kan gadonka game da abubuwan da zasu faru nan gaba ne, kuma shi wanda ya ke baiyana asirai ya sanar da kai abin da ya kusa faruwa, 30 A gare ni ba a baiyana mani wannan asiri domin na fi kowanne mutum da ke rayuwa hikima ba. An baiyana mani asirin ne domin, kai, sarki ka gane ma'anar, domin kuma ka gane zurfin tunanin da ke cikin tunane-tunanenka da ke da zurfi a cikinka. 31 Sarki, ya dubi sama ya ga siffa mai girma. Wannan siffa mai girma da haske, ta tsaya a gabanka. Haskenta yana da ban tsoro. 32 Kan sifar an yi shi da zinariya mai kyau. Ƙirjinta da hannuwanta na azurfa ne. Tsakiyarta da cinyoyinta an yi su da tagulla, 33 ƙafafunta kuma an yi su da ƙarfe. Tafin sawunta kuma an yi su rabi da ƙarfe rabi da yumɓu. 34 Da ka duba sama, an saro wani dutse, ko da ya ke ba da hannun mutum ba ne, ya kuma bugi siffar ya farfasa ƙafafunta na ƙarfe da na yumɓu. 35 Sa'annan ƙarfen da yumɓun da baƙin ƙarfen da azurfar da zinariyar aka farfasa su gaba ɗaya suka zama kamar ɗan maraƙi a masussuka lokacin kaka. Iska ta kwashe su ba ta rage komai ba. Amma dutsen da ya faɗo ya farfasa siffar ya zama babban dutse ya cika duniya. 36 Wannan shi ne mafarkinka. Yanzu zamu gaya maka ma'anarsa. 37 Kai, sarki, kai ne sarkin sarakuna waɗanda Allah na sama ya ba su mulki, da iko da ƙarfi da martaba. 38 Ya bayar da wurin da mutane ke zaune a hannunka. Ya kuma bada dabbobi da tsuntsayen sama a cikin hannunka, ya sa ka yi mulki akan su dukka. Kai ne kan zinariya na siffar nan. 39 Bayanka, wani mulki zai taso wanda bai kai kamar ka ba, daga nan mulki na uku na baƙin ƙarfe zai yi mulkin dukkan duniya. 40 Mulki na huɗu zai zo, mai ƙarfi kamar ƙarfe, saboda ƙarfe ya farfasa kome ya lalata su. Zai farfasa duk waɗannan abubuwa ya lalata su. 41 Kamar yadda ka gani an yi tafin ƙafafun rabi da yumɓu rabi da ƙarfe, mulkin zai rabu kenan; wani sashi zai sami ƙarfi kamar ƙarfe, kamar yadda ka ga an gauraya ƙarfe da yumɓu mai taushi. 42 Kamar yadda aka yi yatsun ƙafafun rabi da ƙarfe, rabi da yumɓu, haka mulkin zai zama wani sashi da ƙarfi wani sashi da rauni. 43 Kamar yadda ka ga ƙarfe gauraye da yumɓu mai taushi, haka mutanen za su zama a gauraye; ba za su tsaya tare ba kamar yadda ƙarfe ba zai gaurayu da yumɓu ba. 44 A cikin kwanakin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai tayar da wani mulkin da ba za a iya rushe shi ba, waɗansu mutane ba zasu iya cin nasara akan sa ba. Zai farfasa sauran mulkokin gutsu-gutsu ya kawo ƙarshensu, shi kuwa zai kasance har abada. 45 Kamar yadda ka ga an saro dutse daga babban dutse, amma ba da hannuwan mutum ba. Ya farfasa ƙarfen da baƙin ƙarfe da yumɓu da azurfa da zinariya gutsu-gutsu. Allah Mai Girma ya sanar da kai, ya sarki, abin da zai faru bayan wannan. Mafarkin gaskiya ne, wannan bayanin kuma tabbas ne." 46 Nebukadnezza sarki ya faɗi da fuskarsa a ƙasa a gaban Daniyel ya girmama shi; ya ba da ummurni a yi bayarwa dominsa a ba shi turare. 47 Sarkin ya cewa Daniyel, "Hakika Allahnka shi ne Allahn alloli, Ubangijin sarakuna, wanda ya ke baiyana asirai, gama ka iya ka baiyana wannan asiri." 48 Sai sarki ya sa Daniyel ya zama mai martaba sosai, ya ba shi kyautai da yawa na mamaki. Ya mai da shi mai mulki a bisa dukkan gundumar Babila. Daniyel ya zama babban gwamnan masu hikima na Babila. 49 Daniyel ya roƙi sarki, sarkin kuma ya naɗa Shadrak, Meshak da Abednego su zama masu gudanarwa a gundumar Babila. Amma Daniyel ya zauna a fãdar sarki.

Sura 3

1 Nebukadnezza sarki ya yi siffa ta zinariya wadda tsawonta ƙafa tasa'in ne fadinta kuma ƙafa tara, ya ƙafa ta a Filin Dura wanda ke a gundumar Babila. 2 Sai Nebukadnezza ya aika da 'yan kai saƙo, a tattaro shugabanni, masu riƙe da sassa da yankuna da gundumomi da masu ba da shawara da masu ajjiya da masu shari'a da alƙalai da dukkan manyan jami'an gundumomi, su zo wurin ƙaddamar da siffar da ya kafa. 3 Sai shugabannin sassa da yankuna da gundumomi da masu bada shawara da masu ajjiya da masu shari'a da alƙalai da dukkan manyan jami'an gundumomi, suka tattaru domin ƙaddamar da siffar da Nebukadnezza ya kafa. Suka tsaya a gaban siffar. 4 Sa'annan aka yi shela mai ƙarfi, "An ummurce ku, ku mutane da al'ummai da harsuna, 5 a lokacin da ku ka ji ƙarar kahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, sai ku faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda Nebukadnezza sarki ya kafa. 6 Duk wanda bai faɗi ya yi sujada ba, a wannan lokacin, za a jefa shi cikin tanderu mai ci da wuta." 7 To lokacin da dukkan mutane suka ji ƙarar ƙahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, dukkan mutane da al'ummai da harsuna suka faɗi warwas a wurin siffar zinariya wadda Nebukadnezza sarki ya kafa. 8 To sai waɗansu Kaldiyawa suka zo suka kawo sãra akan Yahudawa. 9 Suka ce da Nebukadnezza sarki, "Ranka ya daɗe, ya sarki! 10 Kai sarki, kai ne ka ba da ummurni, dukkan wanda ya ji ƙarar ƙahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, dole ya faɗi warwas a gaban siffar zinariya. 11 Duk wanda bai faɗi ya yi sujada ba, dole za a jefa shi cikin tanderu mai ci da wuta. 12 To akwai waɗansu Yahudawa da ka naɗa su lura da harkokin gundumar Babila; sunayensu kenan, Shadrak, Meshak da Abednego. Sarki, waɗannan mutane ba su damu da kai ba. Ba za su yi wa allolinka sujada ba, balle su bauta masu, ko kuma su faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda ka kafa." 13 Sai Nebukadnezza cike da fushi da hasala, ya ummurta a kawo su Shadrak, Meshak da Abednego a wurin sa. Sai aka kawo waɗannan mutane gaban sarki. 14 Nebukadnezza yace da su, "Ko kun yi shawara, ya Shadrak, Meshak da Abednego, ba za ku yi sujada ga allolina ba ko ku faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda na kafa ba? 15 Yanzu idan kuna shirye -lokacin da ku ka ji ƙarar ƙahonni da sarewa da giraya da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa - ku faɗi warwas a gaban siffa wadda na kafa, ba komai. Amma idan ba za ku yi sujada ba, yanzun nan za a jefa ku cikin tanderu mai ci da wuta. Wanne allah ne zai iya kuɓutar da ku daga hannuna?" 16 Shadrak, Meshak da Abedinego suka amsa wa sarki, "Nebukadnezza, ba mu da bukata mu amsa maka a kan wannan magana. 17 Idan da wata amsa ita ce, Allahn da muke bauta wa zai iya tsare mu lafiya daga cikin tanderu mai ci da wuta, kuma zai kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki. 18 Amma idan ma ba haka ba, bari ka sani ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka ba, kuma ba za mu faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda ka kafa ba." 19 Sai Nebukadnezza ya cika da hasala; yanayin fuskarsa ya canza game da Shadrak, Meshak da Abednego. Ya ba da ummurni a zuga tanderun har sau bakwai fiye da yadda aka saba zugawa. 20 Sa'annan ya ummurci waɗansu ƙarfafa cikin sojojinsa su ɗaure su Shedrak, Meshak da Abedinego, su jefa su cikin tanderun mai ci da wuta. 21 Aka ɗaure su saye da tufafinsu da alkyabbunsu da rawunansu da sauran kayan jikinsu, aka jefa su cikin tanderun mai ci. 22 Saboda ummurnin sarki ya yi tsauri kuma haka aka yi, tanderun ya yi zafi ƙwarai, harshen wuta ya kashe mutanen da suka ɗauki su Shedrak da Meshak da Abednego. 23 Waɗannan mutane uku, wato, Shedrak, Meshak da Abednego, suka faɗa a cikin tanderun mai ci da wuta a ɗaure. 24 Sai Nebukadnezza ya cika da mamaki, ya tashi da sauri. Ya tambayi mashawartansa, "Ba mutane uku mu ka jefa a ɗaure cikin wuta ba?" Suka amsa wa sarki suka ce, "Tabbas haka ne, ya sarki." 25 Ya amsa ya ce, "Na ga mutane huɗu ba a ɗaure ba suna yawo a cikin wutar, kuma ba abin da ya same su. Hasken na huɗun kamar na ɗan alloli." 26 Sai Nebukadnezza ya zo kusa da ƙofar tanderun mai ci da wuta ya yi kira, "Shedrak, Meshak, da Abednego bayin Allah Mafi Ɗaukaka, ku fito! Ku zo nan!" Sai su Shadrak, Meshak da Abednego suka fito daga cikin wutar. 27 Shugabannin sassa da yankuna da gundumomi da suka taru a wurin suka ga waɗannan mutane. Wuta ba ta ƙona jukkunansu ba; gashin kansu bai taɓu ba; kuma ba abin da ya sami tufafinsu; kuma babu ƙaurin wuta a jikinsu. 28 Nebukadnezza yace, "Bari mu yabi Allah na Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko ɗan saƙonsa ya ba bayinsa saƙo. Sun gaskata da shi lokacin da ba su bi dokata ba, sun ba da jikkunansu a maimakon su yi sujada ga wani allah ko su faɗi warwas a gabansa sai dai Allahnsu kaɗai. 29 Saboda haka na ba da ummurni ko dukkan mutane ko al'umma ko harshen da ya yi magana gãba da Allah na Shadrak, Meshak da Abednego dole za a yayyaga su a mai, da gidajensu juji saboda ba wani allah da zai iya yin ceto kamar wannan." 30 Sa'annan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a cikin gundumar Babila.

Sura 4

1 Sarki Nebukadnezza ya aika wannan umarni ga dukkan mutane da al'ummai, da harsuna waɗanda ke zaune a duniya: "Bari salamarku ta ƙaru. 2 Na ga ya yi kyau in faɗa maku akan waɗansu abubuwan alamu da al'ajabai da Maɗaukaki ya yi mani. 3 Ya ya girman alamunsa, kuma ya ya girman al'ajabansa! Sarautarsa har abada ce kuma mulkinsa daga zamani zuwa zamani ne." 4 Ni, Nebukadnezza ina zaune cike da murna a cikin gidana, ina nishaɗi a fãdata. 5 Sai na yi mafarki wanda ya sa na ji tsoro. lokacin da na ke kwance, kamanni da wahayin da na gani ya dami tunanina ƙwarai. 6 Saboda haka sai na ummarta a kirawo mani dukkan masu hikima na Babila don su yi mani fassarar mafarkin. 7 Sai masu sihiri da waɗanda ke cewa suna magana da matattu da masu hikima da masu duba suka zo. Na faɗa masu mafarkin, amma ba su iya fassara mani ba. 8 Sai daga baya Daniyel ya zo - wanda a kira Beltishazza wato irin sunan allahna, a gare shi kuwa akwai ruhun alloli tsarkaka-- na faɗa masa mafarkin. 9 Beltishazza, shugaban masu sihiri, na sani ruhun alloli tsarkaka yana cikinka kuma ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ka faɗa mani mene ne na gani a mafarkina kuma me ya ke nufi. 10 Waɗannan su ne alamun da na gani a cikin tunanina lokacin da nake kwance akan gadona: Na duba, akwai wani itace a tsakiyar duniya, yana da tsayi ƙwarai da gaske. 11 Itacen ya yi girma ya zama mai ƙarfi. ƙwanƙolinsa ya kai sammai, kuma ana iya ganinsa har duk ƙarshen duniya. 12 Yana da ganyaye masu kyau, 'ya'yansa kuwa suna da yawa, a kansa kuma akwai abinci domin kowa. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukkan masu rai suna ci daga gare shi. 13 A tunaninna da nake kwance akan gadona na ga wani tsattsarkan mai saƙo ya sauko daga sammai. 14 Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, 'A sare itacen, a kuma daddatse rassansa, a zage ganyayensa kakaf, a kuma warwatsar da 'ya'yansa. Bari namomin jeji su yi gudu daga ƙarƙashinsa, tsutsaye kuma su tashi daga rassansa. 15 A bar kututturen da saiwoyinsa a cikin ƙasa, ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla, a cikin tsakiyar ɗanyar ciyawar saura. A bar shi ya jiƙe da raɓa daga sammai. A bar shi ya zauna da namomi a cikin tsirai na ƙasa. 16 Bari tunaninsa ya canja daga tunanin mutum, a kuma ba shi tunanin irin na dabba zai zauna a wannan hali har shekaru bakwai. 17 Wannan ita ce shawara da hukuncin da ɗan saƙon ya faɗa. Shawarar da masu tsarki suka zartar don waɗanda ke da rai su sani Maɗaukaki ne ke sarautar mulkokin 'yan adam, ya kan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama a maimakonsu, har ma da mutane masu tawali'u.' 18 Ni, sarki Nebukadnezza, na yi wannan mafarki. Yanzu kai, Beltishazza, ka faɗa mani ma'anarsa, domin dukkan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗa mani ma'anar ba. Amma kai za ka iya yi, gama ruhun alloli tsakaka yana cikinka." 19 Sai Daniyel, wanda aka lakaba wa suna Beltishazza, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki yace, "Beltishazza, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro." Beltishhazza ya amsa, "Ya shugabana, bari mafarkin ya zama domin waɗanda ke gãba da kai ne; bari ma'anarsa kuma ta zama ta masu gãba da kai. 20 Itacen nan da ka gani - wanda ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, wanda ƙwanƙolinsa kuma ya kai sammai, har ma wanda za a iya ganinnsa daga ko'ina a duniya - 21 wanda ke da ganyaye masu kyau, wanda kuma har ya yi 'ya'ya jingim, don a cikinsa akwai abinci domin kowa, har ma namomin jeji sun sami inuwa a ƙarƙashinsa, wanda tsuntsaye sammai kuma suka zauna a kai - 22 wannan itacen kuwa kai ne, ya sarki, kai ne ka yi girma ka ƙasaita. Girmanka kuma ya kai har sammai, mulkinka kuma ya kai har iyakar duniya. 23 Kai, sarki, ka ga tsattsarkan ɗan saƙo na saukowa daga sama yana cewa, 'A sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa, a ɗaure da sarƙar ƙarfe da kuma tagulla, a tsakiyar ɗanyar ciyawar saura. A bar shi can ya jiƙe da raɓa daga sammai. Bari ya zauna tare da namomin jeji har shekaru bakwai.' 24 Wannan ita ce fassarar, sarki. Wannan hukunci ne na Maɗaukaki ya same ka, shugabana sarki. 25 Za a kore ka daga cikin mutane, zaka kuma zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, zaka jiƙe da raɓa daga sammai, har shekaru bakwai sun cika lokacin nan za ka sani Maɗaukaki ne ke sarautar mulkin 'yan adam, kuma ya kan ba da ita ga kowa yadda ya ga dama. 26 Kamar yadda aka ummarta a bar kututturen itace da saiwoyinsa, a wannan hanyar mulkinka zai dawo gare ka daga lokacin da ka san Mai sama ne ke mulki. 27 Saboda haka, ya sarki, bari shawarata ta sami karɓuwa gare ka. Ka daina zunubi, ka yi abin da ke da kyau. Ka juyo daga muguntarka ta wurin aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara maka tsawon kwanakinka da salama." 28 Dukkan waɗannan abubuwa sun kasance ga sarki Nebukadnezza. 29 Bayan wata goma sha biyu lokacin da ya ke tafiya akan benen fãdar Babila, 30 sai ya ce, "Ashe wannan ba ita ce babbar Babila ba, wadda ni da kaina na gina domin zama fãdar sarauta, don darajar ɗaukakata ba?" 31 Lokacin da kalmomi ke fita daga leɓunan sarki, sai ga murya daga sama: "Sarki Nebukadnezza, ana sanar da kai an ɗauke wannan mulkin daga gare ka. 32 Za a kuma kore ka daga cikin mutane, gidanka kuwa zai kasance tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa. Shekaru bakwai cur zasu wuce sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne ke mulkin mulkokin mutane, yana kuma ba da su ga wanda ya ga dama." 33 Wannan hukuncin akan Nebukadnezza ya tabbata nan take. An kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa, jikinsa kuwa ya jiƙe da raɓa daga sammai. Gashinsa kuma ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, farotansa kuma suka yi tsawo kamar na shaho. 34 A ƙarshen kwanakin ni, Nebukadnezza, sai na ɗaga idanuna sama, hankalina ya komo gare ni. "Na ɗaukaka Maɗaukaki, na yi yabo na kuma ɗaukaka shi wanda ke rayayye har abada. Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, sarautarsa kuwa daga dukkan zamanai zuwa zamanai ne. 35 Dukkan mazaunan duniya yana ɗaukan su kamar ba a bakin kome suke a gare shi ba; yakan yi yadda ya nufa a cikin rundunar sama da mazaunan duniya abin da ya yi masa dai-dai. Babu wanda zai iya hana wa ko ya ƙalubalance shi. Ba wanda zai ce da shi, 'Me ya sa ka yi wannan?" 36 A lokacin nan hankalina ya komo gare ni, an mayar mani da sarautata da darajar mulkina. 'Yan majalisata da fãdawana suka dawo da mutuncina. Aka maido ni kan gadon sarautata, har ma an darajanta ni fiye da dã. 37 Yanzu ni, Nebukadnezza, na ba da yabo da girma da ɗaukaka ga Sarkin samaniya, domin dukkan abubuwan da ya aikata masu kyau ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Ya kan ƙasƙantar da waɗanda ke da girmankai.

Sura 5

1 Sarki Belshazza ya yi babban liyafa domin manyan mutanensa, ya kuwa sha ruwan inabi a gaban dukkan su su dubu. 2 A lokacin da Belshazza ya kurɓi ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezza ubansa ya ɗauko daga cikin haikali a Yerusalem, daga waɗanda shi kansa, da manyan mutanensa da matansa da ƙwaraƙwaransa za su sha. 3 Barorinsa kuwa suka ɗauko waɗannan kayyayaki da aka kwaso su daga cikin haikali, gidan Allah, a Yerusalem. Sarki da manyan mutanensa da matansa da ƙwaraƙwarnsa suka sha a cikin su. 4 Sun sha ruwan inabin sun yabi allolinsu waɗanda aka yi da zinariya da azurfa da tagulla da baƙin ƙarfe da katako da kuma dutse. 5 A dai- dai wannan lokaci sai ga yatsun hannun mutum suka bayyana a gaban fitila da rubutu a kan shafen bangon fadar sarki. Sarki ya ga rabin hannun na rubutu. 6 Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa ya razanar da shi; gaɓoɓinsa kuwa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna. 7 Sarki ya yi umarni da babbar murya a kawo masu cewa suna iya magana da matattu, da masu dabo da bokaye, da masu duba. Sarki ya ce da waɗannan da aka san su masu hikima ne a Babila, "Wanda duk ya bayyana wannan rubutu ya kuma faɗi ma'anarsa za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. Zai zama da iko ya kuma zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar." 8 Sai dukkan waɗanda aka san masu hikima na sarki ne suka shigo, amma babu wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma'anarsa. 9 Sarki Belshazza kuwa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune. Fãdawansa kuma duk suka ruɗe. 10 Yanzu da sarauniya ta zo wurin babban liyafa domin abin da sarki da manyan fãdawansa suka ce. Sarauniya ta ce "Ran sarki, ya daɗe! Kada ka bar tunaninka ya sami damuwa. Kada kuma ka bar fuskarka ta turɓune. 11 Ai, akwai wani mutum a cikin mulkinka wanda ke da ruhun alloli tsarkaka. A kwanakin ubanka, an iske haske da fahimi da hikima da ganewa kamar na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezza, ubanka sarki, ya naɗa shi shugaba na masu sihiri, da kuma shugaban masu magana da matattu, da bokaye da masu dũba. 12 Ya na da ruhu nagari, da ilimi da ganewa da fassarar mafarkai da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya - waɗannan ƙwarewa aka sami wannan mutum wato Daniyel da su, wanda sarki ya lakaɓa wa suna Beltishazza. Yanzu sai ka kirawo Daniyel, shi kuwa zai faɗa maka ma'anar abin da aka rubuta." 13 Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya cewa Daniyel, "Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauko a Yahuda, wanda ubana sarki ya kawo daga Yahuda. 14 Na ji labarinka, ruhun alloli tsarkaka na cikinka, haske da ganewa da mafificiyar hikima aka samu a cikinka tare. 15 Yanzun nan mutanen da aka san su da hikima da waɗanda ke magana da matattu an kawo su gabana don su karanta wannan rubutu su kuma yi mani fassara, amma sun kasa faɗar ma'anar rabutun. 16 Amma na ji kai kana iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Yanzu idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya faɗa mani ma'anarsa, za a sa maka rigar shunayya, a kuma sa maka sarƙar zinariya a wuyanka, za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar." 17 Sai Daniyel ya amsa a gaban sarki, "Bar kyautarka don kanka, ka ba wani ladan. Duk da haka zan karanta rubutun a gare ka, ya sarki, zan kuma faɗa maka ma'anarsa. 18 Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezza ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba. 19 Saboda girman da Allah ya ba shi, dukkan mutane, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suna rawar jiki a gabansa. Ya kashe duk waɗanda ya ke so ya kashe, ya kuma bar waɗanda ya ke so ya bar su su rayu. Haka nan kuma ya kan ɗaukaka waɗanda ya ke so, ya kuma ƙasƙantar da waɗanda ya ga dama. 20 Amma sa'ad da zuciyarsa ta kumbura, ruhunsa kuma ya taurare don haka sai ya yi girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. 21 Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hali irin na dabba, ya kuma zauna tare da jakunan jeji. Yana ta cin ciyawa kamar sã. Jikinsa ya jiƙe da raɓa daga sammai har zuwa lokacin da ya gane ashe Allah Maɗaukaki ne ke mulkin 'yan'adam, ya kan kuma ba da shi ga wanda ya ga dama. 22 Kai kuma ɗansa, Belshazza, ba ka ƙasƙantar da zuciyarka ba, duk da ka san wannan dukka, 23 Sai ka ɗaukaka kanka kana nuna wa Ubangiji na sama girmankai. Tun daga gidansa suka kawo maka waɗannan abubuwa kai da fãdawanka, da matanka da ƙwaraƙwaranka ku ka sha ruwan inabi daga ciki, kuna yabon gumakan da aka yi da zinariya da na azurfa da na tagulla da baƙin ƙarfe da itace da dutse - gumakan da ba sa gani, ba su ji, ko su gane kome. Ba ka girmama Allah wanda ya ke riƙe da numfashinka a hannunsa ba, wanda kuma ya san dukkan hanyoyinka. 24 Saboda haka ne Allah ya aiko da hannun da ya yi wannan rubutun. 25 Wannan shi ne rubutun da aka yi: 'Mene, Mene, Tekel, da Pharsin.' 26 Wannan ita ce ma'anar: 'Mene,' 'Allah ya sa kwanakin mulkinka sun ƙare.' 27 'Tekel' 'an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kasa.' 28 'Peres,' 'an raba mulkinka, an kuma ba Mediyawa da Fashiyawa.'" 29 Sai Belshazza ya ba da umarni, suka sawa Daniyel rigar shunayya. Aka sa masa sarkar zinariya a wuyansa, sarki kuma ya yi shela a kansa cewa yanzu shi ne mai iko na uku cikin masu mulkin ƙasar. 30 A wannan dare aka kashe Belshazza, sarkin Babila, 31 Dariyos Bamediye ya karɓi mulkin ya na da shekaru sittin da biyu.

Sura 6

1 Ya gamshi Dariyos ya naɗa dagatai 120 a masarautar domin su yi mulkin dukkan masarautar. 2 Sama da su kuma ya naɗa manyan hakimai uku, Daniyel kuma na ɗaya daga cikin su. Waɗannan manyan hakimai an zaɓe su ne domin su riƙa duba ayyukan dagatan, domin kada sarki ya yi asara. 3 Daniyel ya yi fice daga cikin manyan hakiman da kuma dagatan saboda yana da nagartaccen ruhu. Sarki yana shirin ya sanya shi bisa dukkan masarautar. 4 Sai manyan hakiman da dagatan suka duba domin su sami kuskure a cikin aikin da Daniyel ya ke yiwa masarautar, amma ba su sami wata rashawa ko kasawa ba saboda shi mai aminci ne. Ba a sami wani kuskure ko watsi da aiki a cikinsa ba. 5 Sai waɗannan mutane suka ce, "Bamu sami wani dalilin da zamu yi ƙarar wannan Daniyel ɗin ba sai dai ko mu sami wa ni abin tsayayya da shi game da shari'ar Allahnsa." 6 Daga nan waɗannan hakimai da Dagatai suka kawo wani shiri a gaban sarki. Suka ce da shi, "Sarki Dariyos, ranka ya daɗe! 7 Dukkan manyan hakiman masarautar, da dagatan gudumomi, da dagatan lardi, da mashawarta, da gwamnoni sun yi shawara a tsakaninsu sun ɗauki mataki cewa kai, sarki, ka fito da doka kuma ka tilastata, yadda duk wanda ya yi wani roƙo ga wa ni allah ko mutum cikin kwana talatin, sai dai gare ka kaɗai, sarki, wannan mutum tilas a jefa shi cikin ramin zakuna. 8 Yanzu dai, sarki, ka fito da doka ka kuma sanya hannu a takardar yadda ba za a iya canza ta ba, kamar yadda aka umarta bisa ga shari'un Medeyawa da Fashiyawa, domin baza a iya sauya ta ba." 9 Sai sarki Dariyos ya sa hannu a takardar ya maida dokar ta zama shari'a. 10 Da Daniyel ya fahimci cewa an sanya hannu a takardar ta zama shari'a, sai ya tafi cikin gidansa (tagoginsa dai a buɗe suke a ɗakinsa na saman bene suna fuskantar Yerusalem), sai ya durƙusa bisa gwiwoyinsa, yadda ya saba sau uku a rana, ya yi addu'a ya kuma bada godiya a gaban Allahnsa, yadda ya ke yi a dã. 11 Daga nan waɗannan mutane waɗanda suka shirya makircin tare suka ga Daniyel yana yin roƙe-roƙe da neman taimako wurin Allah. 12 Sai suka zo wurin sarki suka yi masa magana game da dokarsa: Ashe ba ka kafa doka ba cewa duk wanda ya yi roƙo ga wani allah ko mutum a cikin kwanaki talatin, in ba gare ka kaɗai ba, ya sarki, tilas a jefa shi cikin ramin zakuna?" Sarkin ya amsa, "Al'amarin zaunannne ne, kamar yadda aka umarta bisa ga shari'ar Medeyawa da Fashiyawa; baza a iya sokewa ba." 13 Sai suka amsa wa sarki, "Wannan Daniyel ɗin, wanda ke ɗaya daga cikin 'yan bauta da daga Yahuda, bai kula da kai ba, sarki, ko dokar da ka sa hannu. Yana addu'a ga Allahnsa sau uku a rana." 14 Da sarkin ya ji haka, sai hankalinsa ya tashi sosai, sai ya ƙudura a ransa ya ceci Daniyel daga wannan hukunci. Ya yi ƙoƙari har zuwa faɗuwar rana ya ga ya ceci Daniyel. 15 Sai waɗannan mutane waɗanda suka shirya makircin suka tattaru tare da sarki suka ce masa, "Ka sani, sarki, cewa shari'a ce ta Medeyawa da Fashiyawa, cewa babu wata doka ko umarni da sarki ya fito da shi da za a iya canzawa." 16 Daga nan sarkin ya bada umarni, sai aka kawo Daniyel, aka kuma jefa shi cikin ramin zakunan. Sarkin ya cewa Daniyel, "Bari Allahnka, wanda ka ke bautawa babu fasawa, ya kuɓutar da kai." 17 Aka kawo dutse aka rufe ramin, sai sarkin ya hatimce shi da zobensa na sanya hannu da kuma zobunan sanya hannun 'yan, majalisarsa yadda babu wani abin da za a canza game da Daniyel. 18 Daga nan sarki ya koma fãdarsa ya yi azumi tsawon dare. Babu wani abin annashuwa da aka kawo a gabansa, barci kuma ya guje daga gare shi. 19 Da gari ya waye sarkin ya tashi da sauri ya tafi ramin zakunan. 20 Da ya matso kusa da ramin, ya yi kira ga Daniyel da muryar baƙinciki, "Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahnka, wanda ka ke bautawa babu fasawa, ya iya cetonka daga zakunan?" 21 Daga nan Daniyel ya ce da sarki, "Ran sarki, ya daɗe! 22 Allahna ya aiko da manzonsa ya rufe bakunan zakunan, ba su kuma cutar da ni ba. Gama an same ni marar laifi a gabansa da kuma gabanka, sarki, ban kuma cutar da kai ba." 23 Daga nan sarki ya yi murna ƙwarai. Ya bada umarni a fito da Daniyel daga ramin. Sai aka ciro Daniyel daga ramin. Babu wani abin cutarwa da ya same shi, saboda ya dogara ga Allahnsa. 24 Sarkin ya bada umarni, sai aka kawo mutanen nan da suka zargi Daniyel aka kuma jefa su cikin ramin zakunan - dukka, da 'ya'yansu, da kuma matansu. Kafin su kai ƙasa, zakunan suka sha ƙarfinsu suka kakkarya ƙasusuwansu suka yi ragargaza su. 25 Sai Sarki Dariyos ya rubuta zuwa ga dukkan mutane, da al'ummai da kuma harsuna da ke zaune a cikin dukkan duniya: "Bari salama ta ƙaru gare ku. 26 Yanzu na kafa doka a dukkan mulkin masarautata mutane su yi rawar jiki su kuma ji tsoro a gaban Allahn Daniyel, gama shi ne Allah mai rai kuma ya dawwama har abada, sarautarsa kuwa ba za a rushe ba; mulkinsa kuwa za ya kasance har ƙarshe. 27 Yana kiyaye mu yana kuɓutar da mu, yana yin alamu da al'ajibai a sama da kuma duniya; Ya kiyaye Daniyel daga ƙarfin zakuna." 28 Daniyel kuwa ya wadata a zamanin mulkin Dariyos da mulkin Sairus bafashiye.

Sura 7

1 A shekara ta farko ta Belshazza sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki da wahayoyi a ransa da ya ke kwance bisa gadonsa. Sai ya rubuta abin da ya gani a mafarkin. Ya rubuta al'amura mafi muhimmanci: 2 Daniyel ya bayyana cewa, "A cikin wahayina na dare sai na ga iskokin sama huɗu suna motsa babban teku. 3 Manyan dabbobi huɗu, kowanne ya sha daban da ɗayan, suka fito daga cikin tekun. 4 ‌Ɗayan ya yi kama da zaki amma yana da fukafukai kamar gaggafa. lokacin da nake kallo, sai aka yage fukafukansa aka kuma ɗaga shi sama aka sa ya tsaya bisa ƙafafu biyu, kamar mutum. 5 Daga nan akwai dabba ta biyu, kamar damisa, a sunkuye kuma; tana da haƙarƙari uku a tsakiyar haƙoranta a cikin bakinta. Aka ce mata, 'Tashi ki lanƙwame mutane da yawa.' 6 Bayan wannan na sake dubawa. Akwai wata dabbar kuma, kamanninta kamar damisa. Bisa bayanta tana da fukafukai huɗu kamar fukafukan tsuntsu, tana kuma da kawuna huɗu. Aka ba ta ikon yin mulki. 7 Bayan wannan kuma na gani a wahayina na dare dabba ta huɗu, mai ban razana, da ban tsoro, kuma mai ƙarfi ƙwarai. Tana da babban haƙorin ƙarfe; tana haɗiyewa, tana karyawa rugu-rugu, tana kuma tattake abin da ya rage da ƙafafunta. Ta bambanta da sauran dabbobin, kuma tana da ƙahonni goma. 8 Yayin da nake yin la'akari da ƙahonnin, dana duba sai naga wani ƙaho ya fito daga cikinsu, ƙaramin ƙaho. Uku daga cikin ƙahonnin aka daga jijiyoyinsu. A wannan ƙaho na ga idanu kamar idanun mutum da kuma bakin da ke fahariya game da manyan abubuwa. 9 Da na duba, sai na ga an shirya kursiyoyi a waje ɗaya, sai Mai dogon zamani ya zauna. Suturarsa fari fat kamar ƙanƙara, gashin kansa kuwa kamar farin ulu. Kursiyinsa harsunan wuta ne, gargarensu kuwa suna ci da wuta. 10 ‌Ƙoramar wuta na fitowa daga gabansa; miliyoyi na bauta masa, miliyan ɗari kuma na tsaye a gabansa. Ana zaman kotu, aka kuma buɗe litattafai. 11 Na ci gaba da dubawa saboda maganganun fankama da ƙahon ke furtawa. Ina kallo lokacin da aka kashe dabbar, aka lalatar da jikinta, aka kuma miƙa ta domin a ƙone ta. 12 Sauran dabbobin huɗu kuwa, ikonsu na yin mulki aka ɗauke shi, amma aka ƙarawa rayukansu tsawon kwanaki na wani lokaci. 13 A cikin wahayoyina na daren nan, sai na ga wani na zuwa da gizagizan sama kamar ɗan mutum; ya zo wurin Mai dogon zamani ya gabatar da kansa a gabansa. 14 Ikon yin mulki da ɗaukaka da ikon sarauta aka bayar a gare shi yadda dukkan mutane, da al'ummai, da harsuna zasu bauta masa. Ikonsa na mulki madawwamin iko ne da ba zai shuɗe ba, masarautarsa kuwa ba za a taɓa iya rusawa ba. 15 Ni kuwa, Daniyel, ruhuna ya damu a cikina, wahayoyin da na gani kuwa a cikin raina suka dame ni. 16 Sai na kusanci ɗaya daga cikin waɗanda ke tsaye a wurin na kuma tambaye shi ya nuna mani ma'anar waɗannan abubuwa. 17 Waɗannan manyan dabbobin, guda huɗu, sarakuna huɗu ne da zasu taso a duniya. 18 Amma tsarkakan mutanen Mafi Girma zasu karɓi masarautar, zasu kuma mallake ta har abada abadin.' 19 Sai kuma na so in ƙara sani game da dabbar nan ta huɗu - ta bambanta sosai da sauran kuma tana da ban razana da haƙoranta na ƙarfe da kofatun tagulla; tana cinyewa, tana karyawa rugu-rugu, ta kuma tattake abin da ya rage da ƙafafunta. 20 Na so in sami sani game da ƙahonnin goma da ke a kanta, game kuma da ƙahon ɗaya da ya tsiro, wanda kuma a gabansa ƙahonni uku suka faɗi. Na so in sami sani game da ƙahon da ke da idanu da kuma game da bakin da ke fahariyar manyan abubuwa wanda kuma ya ke ganin kamar ya fi abokan tarayyarsa girma. 21 Lokacin da nake kallo, sai wannan ƙaho ya yaƙi tsarkakan mutane yana kuma kayar da su 22 har sai da Mai dogon zamani ya zo, an kuma bayar da hukunci ga tsarkakan mutane na Mafi Girma. Daga nan lokaci ya zo inda tsarkakan mutanen suka karɓi sarautar. 23 Wannan ne abin da mutumin nan ya faɗa, 'Dabbar nan ta huɗu kuwa, zata kasance masarauta ta huɗu a duniya wadda zata sha bamban da dukkan sauran masarautun. Za ta cinye dukkan duniya, ta tattake ta ta kuma karya ta rugu-rugu. 24 ‌Ƙahonnin goma kuwa, daga cikin wannan masarauta sarakuna goma ne za su taso, wani kuma zai taso bayan su. Zai sha bamban da waɗanda suka wuce, zai kuma yi nasara da sarakunan uku. 25 Zai furta maganganun tsayayya da Mafi Girma zai kuma tsananta wa tsarkaka mutanen Allah Mafi Girma. Zai yi ƙoƙarin canza shagulgula da kuma shari'a. Za a bayar da waɗannan abubuwa cikin hannunsa har shekara ɗaya, shekaru biyu, da kuma rabin shekaru. 26 Amma zaman kotu zai ci gaba, za a kuma ɗauke ikon sarautarsa domin a gama da shi a kuma lalatar da shi a ƙarshe. 27 Masarautar da mulkin, da kuma girman masarautun da ke ƙarƙashin dukkan sama, za a bayar ga mutane waɗanda ke tsarkakan mutanen Mafi Girma. Masarautarsa madawwamiyar masarauta ce, dukkan sauran masarautu kuma za su bauta masa su kuma yi masa biyayya.' 28 Ga ƙarshen al'amarin. Ni kuwa, Daniyel, tunane-tunanena sun motsa ni sosai fuskata kuwa ta canza kamanni. Amma na ajiye waɗannan abubuwa a gare ni."

Sura 8

1 A cikin shekara ta uku ta mulkin Sarki Belshazza, Ni, Daniyel, wahayi ya bayyana a gare ni (baya ga wanda ya bayyana a gare ni da farko). 2 A cikin wahayin na gani, yayin da nake dubawa, cewa ina cikin fãdar Susa a gundumar Ilam. Na gani a wahayi cewa ina bakin Rafin Ulai Kanal. 3 Na duba sama sai na ga rago a gabana mai ƙahonni biyu, yana tsaye bakin rafin. ‌Ƙaho ɗaya ya fi ɗaya tsawo, amma wanda ya fi tsawon girmansa a hankali ne fiye da gajeren har ya zo ya zarce shi a tsawo. 4 Sai na ga ragon na bankawa yamma, daga nan arewa, daga nan kuma kudu; babu wata dabbar da ke iya tsayawa a gabansa. Babu waninsu da ke iya kuɓuto da wani daga hannunsa. Yana yin abin da ya ga dama, ya kuma zama babba. 5 Yayin da nake tunani game da wannan, sai na ga bunsuru ya fito daga yamma, wanda ya tafi cikin sararin dukkan duniya, yana gudu da sauri, ya yi kamar baya taɓa ƙasa. Bunsurun yana da babban ƙaho a tsakanin idanunsa. 6 Ya zo wurin ragon mai ƙahonni biyu - naga ragon yana tsayawa a bakin rafin - bunsurun kuwa ya ruga wurin ragon cikin matsanancin fushi. 7 Na ga bunsurun ya zo kusa da ragon. Yana cikin fushi sosai da ragon, sai kuma ya tunkuyi ragon ya ɓalle masa ƙahonnin biyu. Ragon kuwa bai da ƙarfin tsayawa a gabansa. Bunsurun ya fyaɗa shi ƙasa ya take shi. Babu wani da ke iya kuɓuto da ragon daga ikonsa. 8 Sai bunsurun ya zama mai girma sosai. Amma da ya zama mai ƙarfi, sai babban ƙahon ya ɓalle, a gurbinsa kuwa ƙahonni manya huɗu suka fito suka fuskanci kusurwoyin iskoki huɗu na sammai. 9 Daga kan ɗaya daga cikin su wani ƙahon ya tsiro, da farko dai ƙarami ne, amma ya zama babba sosai a kudu, a gabas, a kuma ƙasa mai kyau. 10 Ya yi girma sosai har ya shiga yaƙi da mayaƙan sama. Waɗansu daga cikin mayaƙan da waɗansu daga cikin taurarin aka watso su ƙasa cikin duniya, ya kuma tattake su. 11 Ya maida kansa ya zama da girma kamar shugaban mayaƙan. Ya ɗauke baiko na ƙonawa da aka saba yi, wurin haikalinsa kuma aka gurɓata shi. 12 Saboda tawaye za a miƙa mayaƙan ga ƙahon bunsurun, kuma za a tsai da baikon ƙonawa. ‌Ƙahon zai watsar da gaskiya ƙasa, zai kuma yi nasara cikin dukkan abin da ya yi. 13 Sai na ji wani mai tsarki na magana wani kuma mai tsarkin na amsa masa, "Har yaushe waɗannan abubuwa za su kasance, wannan wahayin game da baikon ƙonawa, zunubin da ya kawo rusarwa, miƙawar haikalin, da kuma tattakawar mayaƙan sama?" 14 Ya ce mani, "Za su kasance har yamma-yamma da safiya-safiya 2,300. Bayan wannan za a maido da haikalin dai-dai." 15 Lokacin da ni, Daniyel, na ga wahayin, na yi ƙoƙari in fahimce shi. Sai ga wani ya tsaya a gabana mai kamannin mutum. 16 Sai na ji muryar mutum na kira daga tsakiyar bakin Rafin Ulai. Ya ce, "Jibra'il, ka taimaki mutumin nan ya fahimci wahayin." 17 Sai ya zo kusa da inda na tsaya. Da ya zo, sai na tsorata na rusuna ƙasa. Ya ce mani, "Ka fahimta, ɗan mutum, wahayin domin lokacin ƙarshe ne." 18 Da ya yi mani magana, sai na faɗa cikin barci mai nauyi da fuskata a ƙasa. Daga nan ya taɓa ni ya sa na miƙe a tsaye. 19 Ya ce, "Duba, zan nuna maka abin da zai faru daga bisani a lokacin hasala, saboda wahayin ya shafi zaɓaɓɓen lokacin ƙarshe. 20 Game da ragon da ka gani, wanda ke da ƙahonni biyu - sune sarakunan Mediya da Fashiya. 21 Bunsurun shi ne sarkin Girka. Babban ƙahon tsakanin idanunsa shi ne sarkin farko. 22 Game da ƙahon da ya ɓalle kuwa, wanda a gurabunsa huɗu kuma suka taso - masarautai huɗu ne za su taso daga al'ummarsa, amma bada babban ikonsa ba. 23 A ƙarshen lokacin waɗannan masarautai, lokacin da masu kurakurai suka ƙure iyakarsu, wani sarki marar sakin fuska, mai basira sosai, zai taso. 24 Ikonsa zai zama babba - amma ba da ikonsa ba. Zai zama da ban mamaki cikin abin da ya ke rusarwa; zai aikata ya kuma yi nasara. Zai lalatar da manyan mutane, mutane daga cikin tsarkakan. 25 Da dabararsa zai sa yaudara ta yi nasara a hannunsa. Zai zama babba a cikin tunaninsa. Kamar yadda aka zata zai lalatar da mutane da yawa. Zai kuma yi tsayayya da Sarkin sarakuna, za a kuma karya shi, amma ba da hannun mutum ba. 26 Wahayi game da yammaci da safiya da aka faɗa gaskiya ne. Amma ka rufe wahayin, gama yana magana ne akan kwanaki masu yawa nan gaba." 27 Daga nan ni, Daniyel, aka sha ƙarfina na kwanta da kasala har kwanaki da yawa. Daga nan na tashi, na kuma ci gaba da hidimomin sarki. Amma na razana game da wahayin, babu kuma wani wanda ya fahimce shi.

Sura 9

1 Dariyos ɗan Ahazurus ne, daga zuriyar Medeyawa. Ahazurus ne aka naɗa sarki a dukkan ƙasar Babiloniyawa. 2 To a shekara ta farko ta mulkin Dariyos ni, Daniyel, ina binciken litattafai da ke ɗauke da maganar Yahweh, maganar da tazo wa Irmiya annabi. Sai na lura za ayi shekaru saba'in har watsarwar Yerusalem ta kai ƙarshe. 3 Sai na juya fuskata ga Ubangiji Allah, na biɗe shi cikin addu'a da roƙe-roƙe, tare da azumi, ina sanye da tsumma, ina zaune kuma cikin toka. 4 Nayi addu'a ga Yahweh Allahna, na kuma furta zunubanmu. Na ce, "Ina roƙon ka, Ubangiji - kai ne Allah Mai Girma Mai Ban mamaki - kai ne mai riƙe alƙawari kana kuma da aminci da ƙaunar masu ƙaunarka suna kuma kiyaye dokokinka. 5 Mun yi zunubi kuma mun yi abin da ba dai-dai ba. Mun aikata mugunta kuma mun kangare, mun kauce daga umarnanka da dokokinka. 6 Ba mu saurari bayinka annabawa ba waɗanda suka yi magana cikin sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da ubanninmu, da kuma dukkan mutanen ƙasar. 7 A gare ka, Ubangiji, adalci ya tabbata. Ko da ya ke, a gare mu yau, kunya ce ta tabbata a fuskokinmu-ga mutanen Yahuda, da mazauna Yerusalem, da kuma dukkan mutanen Isra'ila. Wannan ya haɗa da waɗanda ke kusa da waɗanda ke nesa a cikin dukkan ƙasashen da ka warwatsa su. Wannan ya zama haka saboda babban tawayen da muka yi maka. 8 A gare mu, Yahweh, kunya a fuskokinmu ta tabbata-ga sarakunanmu, ga shugabanninmu, ga kuma ubanninmu - saboda mun yi maka zunubi. 9 Jinƙai da gafartawa sun tabbata ga Ubangiji Allahnmu, gama mun yi maka tawaye. 10 Ba mu yi biyayya ga muryar Yahweh Allahnmu ba ta wurin tafiya bisa ga shari'unsa waɗanda ya ba mu ta wurin bayinsa annabawa ba. 11 Dukkan Isra'ila sun karya shari'arka su ka juya gefe ɗaya, suka ƙi biyayya da muryarka. La'ana da rantsuwar da aka rubuta cikin shari'ar Musa, bawan Allah, an zubo ta a kanmu, gama mun yi masa zunubi. 12 Yahweh ya tabbatar da maganganun da ya furta game da mu da kuma masu mulki a kanmu, ta wurin kawo babban bala'i a kanmu. Gama a ƙarƙashin sama dukka babu wani abu da za a iya kwatantawa da abin da a kayi wa Yerusalem. 13 Kamar yadda aka rubuta a shari'ar Musa, duk wannan bala'i ya sauka akan mu duk da haka ba mu roƙi jinƙai ba daga wurin Yahweh Allahnmu ta wurin kaucewa daga laifuffukanmu da mai da hankali ga gaskiyarka. 14 Saboda haka Yahweh ya ajiye bala'i a shirye ya kuma kawo shi a kanmu, gama Yahweh Allahnmu mai adalci ne cikin dukkan abin da ya yi, duk da haka ba mu yi biyayya da muryarsa ba. 15 Yanzu, Ubangiji Allahnmu, ka fito da mutanenka daga ƙasar Masar da hannu mai iko, ka yi wa kanka sanannen suna, kamar yadda ya ke a yau. Amma duk da haka mun yi zunubi; mun yi abubuwan mugunta. 16 Ubangiji, domin dukkan ayyukanka na adalci, bari fushinka da hasalarka su kawu daga birninka Yerusalem, tsauninka mai tsarki. Saboda zunubanmu, saboda kuma laifuffukan ubanninmu, Yerusalem da mutanenka sun zama abin ba'a ga dukkan waɗanda ke kewaye da mu. 17 Yanzu, Allahnmu, ka saurari addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa domin jinƙai; Ubangiji, ka sa fuskarka ta haskaka akan haikalinka da ya zama kufai. 18 Allahna, ka buɗe kunnuwanka ka saurara; ka buɗe idanunka ka duba. Mun wulaƙantu; kalli birnin da ake kira da sunanka. Ba muna roƙon taimakonka ba ne saboda adalcinmu, amma saboda jinƙanka mai girma. 19 Ubangiji, ka saurara! Ubangiji, ka gafarta! Ubangiji, ka kula ka ɗauki mataki! Saboda kai, kada ka yi jinkiri, Allahna, saboda birninka da kuma mutanenka ana kiran su da sunanka." 20 Yayin da na ke magana - ina addu'a da furta zunubina da zunubin mutanena Isra'ila, ina kuma gabatar da roƙe-roƙena a gaban Yahweh Allahna a madadin dutsen Allah mai tsarki - 21 yayin da nake addu'a, mutumin nan Jibra'il, wanda na gani a wahayin da farko, ya taso zuwa wurina da gaggawa, a lokacin hadayar maraice. 22 Ya ba ni fahimi ya kuma ce mani, "Daniyel, yanzu na zo in ba ka masaniya da fahimta. 23 Da ka fara roƙo domin jinƙai, an bayar da umarni na kuma zo in faɗa maka amsar, gama an ƙaunace ka sosai. Domin haka ka yi la'akari da wannan magana ka fahimci wahayin. 24 Bakwai-bakwai sau saba'in na shekaru aka zartar domin mutanenka da birninka mai tsarki domin a kawo ƙarshen laifofi a kuma kawo ƙarshen zunubi, a yi kaffara domin mugunta, a kuma kawo madawwamin adalci, a kuma aiwatar da wahayin da anabcin, a kuma keɓe wuri mafi tsarki. 25 Ka sani kuma ka fahimci cewa daga zartar da umarnin maidowa da sake ginin Yerusalem har ya zuwan shafaffen nan (wanda za ya zama shugaba), za a sami bakwai-bakwai sau bakwai da kuma bakwai sittin da biyu. Za a sake gina Yerusalem da tituna da ramin ganuwa, duk da cewa lokutan tsanani ne. 26 Bayan bakwai-bakwai sittin da biyu na shekaru, za a rugurguza shafaffen zai zama kuma zama ba komai. Mayaƙan shugaba mai zuwa za su rugurguza birnin da kuma wuri mai tsarki. ‌Ƙarshen shi zai zo da ambaliya, za a kuma yi yaƙi har zuwa ƙarshe. An zartar da abubuwan ban ƙyama. 27 Zai tabbatar da alƙawari da mutane da yawa na bakwai ɗaya. A tsakiyar bakwai ɗin zai kawo ƙarshen hadaya da baiko. A tsakiyar haramtattun al'amura wani mai hallakarwa zai zo. Cikakkken ƙarshe da rusarwa aka zartar da za a zubo akan wanda ya kawo hallakarwar."

Sura 10

1 A cikin shekara ta uku ta Sairus sarkin Fasiya, an bayyana wa Daniyel wani saƙo, wanda kuma ake kira Beltishazza. Wannan saƙon gaskiya ne. Game da babban yaƙi ne. Daniyel ya gane saƙon ya kuma sami fahimta daga wahayin 2 A cikin waɗannan kwanaki ni, Daniyel ina cikin makoki har sati uku. 3 Ban ci abincin da nake marmari ba, ban ci nama ba, ban sha ruwan inabi ba, ban kuma shafe kaina da mai ba har sai da mako uku ɗin suka cika. 4 A rana ta ashirin da huɗu ga watan fari, lokacin da nake bakin babban kogi (wato Tigris), 5 Sai Na duba sama sai ga mutum saye cikin linin, ƙugunsa na ɗaure da ɗammara na tsattsarkar zinariya daga Ufaz. 6 Jikinsa na kama da tofaz, fuskarsa tana kamar walƙiya. Idanunsa kamar fitilu na wuta, ƙafafunsa da hannuwan sa kamar gogagiyar tagulla. Muryar kalmominsa tana kama da muryar babban taro. 7 Ni, Daniyel, kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da ke tare da ni ba su ga wahayin ba. Duk da haka, babban tsoro ya sauko masu, suka ruga don su ɓoye kansu. 8 Ni kaɗai aka bari sai na ga wannan babban wahayin. Babu sauran ƙarfi da ya rage a cikina; bayyanata mai haske ta juya ta za ma kallon lalatarwa, ba sauran ƙarfi da ya rage a cikina. 9 Daga nan sai na ji kalmominsa - da na ji su, sai na faɗi kan fuskata cikin barci mai nauyi da fuskata a ƙasa. 10 Sai hannu ya taɓa ni, ya sa jikina ya yi ta rawa a cikin gwiwoyina da dantsen hannuwana. 11 Mala'ika ya ce mani, "Daniyel, ƙaunataccen mutum na ƙwarai, Ka fahimci maganar da nake faɗa maka. Ka tashi tsaye, gama an aiko ni wurin ka." Sa'ad da ya faɗa mani wannan saƙon, na miƙe tsaye, ina rawar jiki. 12 Daga nan sai ya ce mani, "Kada ka ji tsoro, Daniyel. Tun ran da ka fara ƙwallafa ranka ka fahimta kuma ka ƙasƙantar da kanka gaban Allahnka, an ji maganganunka, nima na zo ne saboda maganganunka. 13 Sarkin mulkin Fasiya ya yi mani tsayayya, an ajiye ni a can tare da sarakunan Fasiya har kwanaki a shirin da ɗaya. Amma Makyal, ɗaya daga cikin manyan sarakuna, ya zo domin ya taimake ni. 14 Yanzu na zo in taimake ka fahimtar abin da zai faru da mutanenka a kwanakin ƙarshe. Gama wahayin domin kwanakin da ba su zo ba ne tukuna." 15 Lokacin da ya ke magana da ni yana morar waɗannan kalmomin, sai na juya fuskata wajen ƙasa ban iya yin magana ba. 16 Wani mai kama da 'ya'ya maza na mutum ya taɓa laɓunana; sai na buɗe bakina na yi magana da shi wanda ke tsaye a gabana. "Ya shugabana, I na cikin tsanani saboda wahayin nan; Ba ni da sauran ƙarfi. 17 Ni bawanka ne. Ta ya ya zan yi magana da shugabana? Gama ba ni da ƙarfi, kuma ba sauran numfashin da ya ragu a cikina." 18 Har yanzu sai shi mai bayyana irin ta mutum ya taɓa ni ya ƙarfafa ni. 19 Ya ce, "Kada ka ji tsoro, ƙaunataccen mutum na ƙwarai, Salama a gareka! Ka yi ƙarfin hali yanzu, ka yi ƙarfin hali!" Lokacin da ya ke magana da ni, Na sami ƙarfi, Na ce, "Bari shugabana ya yi magana, gama ka ƙarfafa ni." 20 Ya ce, "Ko ka san dalilin da ya sa na zo gare ka? Ba da jimawa zan dawo in yaƙi sarkin Fasiya. Idan na tafi, sarkin Girka zai zo. 21 Amma zan faɗa maka abin da a ka rubuta cikin Littafin Gaskiya. Ba wanda ya nuna kansa cewa yana da ƙarfi tare da ni gãba da su, sai Makyal sarkinku."

Sura 11

1 Cikin shekara ta fari ta Dariyos Bamedeya, ni da kaina na zo domin in goyi baya in kuma kãre Makyal. 2 Yanzu kuma zan bayyana maka gaskiya. Sarakuna uku zasu tashi daga cikin Fasiya na huɗun zai fi sauran wadata nesa. Yayin da ya sami iko ta wurin wadatarsa, zai zuga mutane su tayarwa mulkin Girka. 3 Sarki mai girma zai tashi wanda zai yi mulkin masarauta mai girma, zai kuma aikata bisa ga yadda ya so. 4 Sa'ad da ya tashi sama, mulkinsa zai karye za a raba su wajen iskoki huɗu na sama, amma ban da zuriyarsa, ba kuma zai zama da iko kamar lokacin da ya ke mulki ba. Gama za a tunɓuke mulkinsa a raba shi ga waɗansu ba ga zuriyarsa ba. 5 Sarkin kudu zai zama da ƙarfi, amma ɗaya daga cikin jarumawansa zai fi shi ƙarfi zai yi mulkin masarautarsa da babban iko. 6 Bayan 'yan shekaru idan lokaci ya yi, za su yi ƙawance. ‌Ɗiyar sarkin kudu za ta zo wurin sarkin arewa domin tabbatar da yarjejiniyarsu. Amma ba za ta riƙe da ƙarfin hanunta ba shi kuwa ba zai tsaya ba ko 'ya'yansa. Za a yãshe ta - tare da waɗanda suka kawo ta, da mahaifinta, da shi wanda ya goyi bayanta a waɗancan kwanaki. 7 Amma reshe daga cikin sauyoyinta zai tashi a maimakonta. Zai kai wa rundunar hari ya shiga sansanin sarkin Arewa. Zai yaƙe su, kuma zai yi nasara da su. 8 Za ya ɗauke su ya kai su Masar bauta. allolinsu da siffofinsu na zubi tare da kyawawan kayansu na azurfa da na zinariya. Har waɗansu shekaru zai janye da ga sarkin Arewa. 9 Daga nan sarkin Arewa zai mamaye daular sarkin Kudu, amma zai janye ya koma ƙasarsa. 10 'Ya'yansa za su yi shiri su kuma tara babbar rundunar yaƙi. Za su ci gaba da zuwa su yi ambaliyar kowanne abu; za su ratsa ta duk hanyar zuwa kagararsa. 11 Daga nan sarkin Kudu zai ji haushi ƙwarai; zai je ya yi yaƙi da shi, wato sarkin Arewa. Sarkin Arewa zai tara manyan mayaƙa, amma za a bayar da rundunar a cikin hanunsa. 12 Za a kwashe rundunar, zuciyar sarkin kudu kuma za ta ɗaukaka, zai sa dubbun-dubbai su faɗi amma ba zai yi nasara ba. 13 Daga nan sarkin Arewa zai tãda wata rundunar, da suka fi ta fari girma. Bayan waɗansu shekaru, lallai sarkin Arewa zai zo da babbar runduna waɗanda sun tănaji kayayyaki masu yawa. 14 Cikin waɗancan lokatai da yawa za su ṭashi gãba da sarkin kudu. 'Yan tada zaune tsaye daga cikin mutanenka za su shirya kansu domin su cika wahayin, amma za su faɗi. 15 Sarkin Arewa zai zo, zai zuba ƙasa kewaye domin yin matakalu, ya kuma ci birni tare da sansanonin. Ko zaɓaɓɓun sojojinsu. Ba su da sauran karfin tsayawa. 16 Maimakon haka, shi wanda ya zo zai aikata bisa ga manufofinsa gãba da shi; Ba wanda zai tsaya cikin hanyarsa. Zai tsaya cikin ƙasa mai kyau, hallakarwa kuwa zata kasance cikin hanunsa. 17 Sarkin Arewa zai ƙudurta ya zo da dukkan ƙarfin mulkinsa, tare da shi kuma zai zama akwai yarjejeniya da sarkin Kudu. Zai ba shi 'ya mace ya aura domin ya lalata mulkin Kudu. Amma dabarar ba za ta taimake shi ba ba kuwa zai yi nasara ba. 18 Bayan wannan, sarkin Arewa zai maida hankali ga ƙasashen bakin teku zai kama da yawa daga cikin su. Amma wani Jarumi zai kawo ƙarshen girmankansa zai sa girmankansa ya koma kansa. 19 Sa'annan zai mai da hankalinsa ga sansanoni na ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe ya faɗi; ba za a ƙara ganinsa ba. 20 Amma wani zai tashi a madadinsa zai sa mai karɓar haraji ya ratsa saboda darajar mulkinsa. Amma cikin kwanaki masu zuwa za a karya shi, ba cikin fushi ko cikin yaƙi ba. 21 A maimakonsa kuma wani zai tashi mutum abin raini wanda mutane ba za su ba shi darajar sarauta ba; zai zo ba tsammani zai karɓi mulki ta wurin yaudara. 22 Za a share rundunar yaƙi kamar ambaliya a gabansa. Dukan su da rundunar yaƙi da shugaban alƙawari za a hallakar da su. 23 Daga lokacin da a ka yi ƙawance da shi, zai yi aikin yaudara; da kimanin mutane 'yan kaɗan zai yi ƙarfi. 24 Ba tare da gargaɗi ba zai zo cikin waɗansu lardunan da suka fi wadata, zai yi abin da mahaifinsa ko kakansa bai yi ba. Zai baza wa mabiyansa ganima, ganimar yaƙi, da dukiya. Zai shirya juyar da sansanoni, amma na ɗan lokaci ne. 25 Zai ta da ikonsa da zuciyarsa gãba da sarkin Kudu da babbar rundunar yaƙi. Sarkin Kudu kuma zai ja dagar yaƙi, da babbar rundunar yaƙi, ba zai iya tsayawa ba saboda waɗansu zasu shirya masa makirci. 26 Har su da suke cin abincisa mai kyau za su yi ƙoƙarin hallaka shi. Rundunarsa za'a share su kamar ambaliya, da yawan su zasu faɗi kisassu. 27 Dukansu sarakunan nan, da zukatansu da ke nufin mugunta gãba da juna, za su zauna a teburi ɗaya suna yiwa juna ƙarya, amma ba za ta zama da amfani ba. Gama matuƙa za ta zo a ƙayadadden lokaci. 28 Sa'an nan sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai yawa, ya sa zuciyarsa ta yi gãba da alƙawari mai tsarki. Zai aikata abin da ya so daga nan ya koma ƙasar sa. 29 A cikin sanyayyen lokaci zai sake dawowa gaba da Kudu. Amma a wannan lokacin ba zai zama kamar na farin ba. 30 Gama jiragen Kittim za su kawo masa hari, zai tsorata kuma ya koma baya. Zai ji haushin alƙawari mai tsarki, zai nuna amincewa ga waɗanda suka watsar da alƙawari mai tsarki. 31 Dakarunsa zasu tashi su tozartar da kagarun wuri mai tsarki. Zasu kawar da baikon ƙonawa na kullum, za kuma su kafa abin banƙyama da zai sa hallakarwa. 32 Gare su da suke aikata mugunta saɓanin alƙawari, zai yaudare su ya ɓata su. Amma mutanen da suka san Allahnsu zasu yi ƙarfi su kuma ɗauki mataki. 33 Su da ke da hikima cikin mutane zasu sa da yawa su fahimta. Amma zasu faɗi ta kaifin takobi da harshen wuta; zasu faɗi cikin bauta da yi masu fashi kwanaki da yawa. 34 Cikin faɗuwarsu, za a taimake su da taimako ƙanƙane. Cikin munafunci da yawa za su haɗa kai da su. 35 Daga cikin masu hikima waɗansu zasu faɗi domin a tace su, a wanke su, a tsarkake su, har kwanakin ƙarshe. Amma lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna. 36 Sarki zai aikata bisa ga son ransa. zai ɗaukaka kansa ya maida kansa babba bisan kowanne allah. Zai faɗi abubuwan ban mamaki gãba da Allahn alloli, zai yi nasara har lokacin da fushi ya cika. Gama abin da aka wajabta zai faru. 37 Ba zai kula da allolin kakanninsa ba ko allahn da mata ke marmari. Ba zai kula da kowanne allah ba. Gama zai maida kansa babba a bisa kowannen su. 38 Maimakon waɗannan, zai girmama allahn ganuwoyi. Shi ne allahn da ubanninsa ba su sani ba zai girmama shi da zinariya da azurfa da duwatsu masu daraja da kyaututtuka masu amfani. 39 Zai kai hari ga ganuwoyi masu ƙarfi ta wurin taimakon baƙon allah. Ga duk wanda ya yarda da shi, zai ƙara mai ɗaukaka. Zai maishe su masu mulkin mutane da yawa. Zai raba masu ƙasa a matsayin lada. 40 A kwanakin ƙarshe kuma sarkin Kudu zai kai hari. Sarkin Arewa kuma zai tasar masa da karusan yaƙi da mahaya dawakai, da jirage da yawa. Zai shiga cikin ƙasashe, ya kwarara, ya ratsa. 41 Zai shiga cikin ƙasa mai kyau dubbun-dubban Isra'ilawa za su faɗi. Amma waɗannan zasu tsira daga hanunsa: Idom, Mowab da sauran mutanen Amon. 42 Zai ƙara miƙa hanunsa cikin ƙasashen; ƙasar Masar ba za ta tsira ba, 43 Zai sami iko bisa kan taskar zinariya da azurfa da kan dukkan wadatar Masar; Libiyawa da Kushawa zasu bi tafin sawayensa. 44 Amma labari daga gabas da arewa zai tsoratar da shi, zai fita da babbar hasala domin ya hallakar gaba ɗaya ya kuma keɓe da yawa domin hallaka. 45 Zai kafa rumfar fãdarsa tsakanin teku da kyakkyawan dutse mai tsarki. Zai kawo ƙarshen sa, ba kuwa mai taimakon sa.

Sura 12

1 "A wannan lokaci Makyal, babban yarima mai kare mutanenka, zai tashi. Za a yi kwanakin wahala irin waɗanda ba a taɓa yi ba tun da aka yi kowacce al'umma har ya zuwa lokacin nan. A lokacin nan za a ceci mutanenka, duk wanda aka iske sunansa a cikin littafi. 2 Da yawa waɗanda suke barci cikin turɓayar ƙasa za su tashi, waɗansu zuwa rai na har abada waɗansu kuma zu wa kunya da ƙasƙanci marar matuƙa. 3 Waɗanda suke da hikima zasu haskaka kamar walƙiya ta sararin sama, waɗanda suka juya mutane da yawa zuwa ga adalci za su haskaka kamar taurari har abada abadin. 4 Amma kai Daniyel, ka kulle maganganun nan; ka hatimce littafin har sai kwanakin ƙarshe. Da yawa zasu yi ta gudu nan da can, ilimi kuma zai ƙaru". 5 Sa'an nan, ni, Daniyel, na duba, akwai waɗansu biyu suna tsaye. ‌Ɗaya yana tsaye a bakin kogi ɗaya kuma yana tsaye a bakin ƙetaren wancan kogin. 6 ‌Ɗ‌aya daga cikin su ya ce da mutumin da ke saye da linin, wanda ya ke kan magudanar kogin ya ce, "Har yaushe zai zama ƙarshen waɗannan al'amura na al'ajabi?" 7 Na ji mutumin da ke sanye da linin, wanda ya ke bisa magudanar kogin - ya ɗaga hanunsa na dama da na hagu sama ya yi rantsuwa ga shi wanda ya ke rayuwa har abada za a yi lokaci da lokatai, da rabin lokaci. Sa'ad da ikon mutane masu tsarki ya karye a ƙarshe, dukkan waɗannan al'amura zasu cika. 8 Na ji amma ban fahimta ba. Sai na tambaya, "Ya shugabana, ina mafitar waɗannan al'amura?" 9 Ya ce, "Tafi yi tafiyarka, Daniyel, gama an kulle maganganun nan an hatimce su har sai kwanakin ƙarshe. 10 Waɗansu da yawa zasu tsarkaka, tsabtattu, su zama tatattu, amma miyagu za su aikata mugunta. Babu wani a cikin mugaye da zai fahimta, amma masu hikima zasu fahimta. 11 Daga lokacin da aka kawar da baiko na ƙonawa aka kuma kafa abin ƙyama mai sa hallakarwa, za'a yi kwanaki 1,290. 12 Mai albarka ne shi wanda ya jira har ƙarshen kwanaki 1,335. 13 Dole ka yi tafiyarka har ƙarshen, kuma za ka huta. Za ka tashi a cikin wurin da aka keɓe maka, a ƙarshen kwanaki."

Littafin Hosiya
Littafin Hosiya
Sura 1

1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo wurin Hosiya ɗan Biri a kwanakin Uziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da kuma kwanakin Yerobowam ɗan Yoash, sarkin Isra'ila. 2 Sa'ad da Yahweh ya yi magana da fari ta wurin Hosiya, ya ce masa, "Jeka ka ɗaukar wa kanka mata wadda karuwa ce. Za ta sami 'ya'ya ta wurin karuwancinta. Domin ƙasar tana aikata matuƙar karuwanci ta wurin yashe da Yahweh." 3 Sai Hosiya ya tafi ya auro Gomar ɗiyar Diblayim, sai ta yi ciki ta haifa masa ɗa namiji. 4 Yahweh ya cewa Hosiya, "Ka kira sunansa Yeziril, gama a ɗan lokaci kaɗan zan hukunta gidan Yehu saboda ya zubda jini a Yeziril, zan kuma kawo ƙarshen mulkin gidan Isra'ila. 5 Wannan zai faru randa zan karya bakãr Isra'ila a Kwarin Yeziril." 6 Sai Gomar ta sake yin ciki ta haifi 'ya mace. Sai Yahweh yace wa Hosiya, "Ka raɗa mata suna Lo Ruhama, gama ba zan ƙara yi wa gidan Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta masu. 7 Duk da haka zan yi wa gidan Yahuda jinƙai, zan cece su ni da kaina, Yahweh Allahnsu. Ba zan cece su da baka, da takobi, da yaƙi, da dawakai da mahayansu ba," 8 Bayan da Gomar ta yaye Lo Ruhama, sai ta yi ciki ta haifi ɗa namiji kuma, 9 Sa'an nan Yahweh yace, "Ka raɗa masa suna, Lo Ammi, domin ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne. 10 Duk da haka yawan mutanen Isra'ila za su zama kamar yashi a bakin teku, wanda ba za a iya aunawa ko ƙirgawa ba. Zai zamana inda aka ce masu, 'Ku ba mutanena ba ne, za a ce masu, "Ku mutanen Allah mai rai ne.' 11 Mutanen Yahuda da mutanen Isra'ila za su taru wuri ɗaya. Za su naɗa wa kansu shugaba ɗaya, za su haura su tafi daga ƙasar, gama ranar Yezril zata zama da girma.

Sura 2

1 Ku cewa 'yan'uwanku maza, 'Mutanena!' ga 'yan'uwanku mata, 'An ji tausayin ku.'" 2 Ku kawo ƙarar mahaifiyarku, ku kawo ƙara, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ta kawar da karuwancinta daga gare ta da halinta na zina daga tsakanin nonnanta. 3 Idan ba haka ba, zan maishe ta tsirara in nuna tsiraicinta kamar a ranar da aka haife ta. Zan maishe ta kamar hamada, kamar busasshiyar ƙasa, in sa ta mutu da ƙishiruwa. 4 Ba zan nuna jinƙai kan 'ya'yanta ba ko kaɗan, gama 'ya'yan fasikanci ne. 5 Domin uwarsu dăma karuwa ce, ita wadda ta ɗauki cikinsu ta yi abin kunya. Ta ce, "Zan bi masoyana, domin suna bani abincina, da ruwa, da ulu, da gyale, da mai da abin sha." 6 Sabo da haka zan gina shinge in tare hanyarta da ƙayayuwa. Zan gina katanga gãba da ita don kada ta gane hanyarta. 7 Zata bi masoyanta, amma ba za ta cim masu ba. Zata neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'annan za ta ce, "Zan koma wurin mijina na farko, gama a dã ya fiye mani da yanzu." 8 Gama ba ta sani dama ni ne na ba ta hatsi ba, da sabon ruwan inabi da mai, na kuma yawaita ta da azurfa da zinariya, wanda suke amfani da shi ga Ba'al. 9 Saboda haka zan karɓe hatsinta da kaka, da sabon ruwan inabina a lokacin girbi. Zan karɓe uluna da gyaluluwana da aka mora don a rufe tsiraicinta. 10 Zan buɗe tsiraicinta a idanun masoyanta, ba wanda zai cece ta daga hannuna. 11 Zan sa dukkan shagulgulanta su ƙare - bukukuwanta, shagalin tsayawar sabon wata, Asabatai, da dukkan ayyanannun bukukuwa. 12 "Zan lalatar da kuringar inabinta da itatuwan ɓaurenta, da ta ce, "Waɗannan su ne ladar da masoyana suka bani.' Zan maishe su jeji, namun jeji kuma za su cinye su. 13 Zan hore ta domin ranakun bukukuwan Ba'aloli, lokacin da ta ƙona masu turare, sa'ad da ta yiwa kanta ado da zobba da duwatsu masu daraja, ta bi masoyanta ta manta da ni -- wannan shi ne furcin Yahweh." 14 Saboda haka zan lallashe ta in dawo da ita. Zan kai ta cikin jeji in yi mata tattausar magana. 15 Zan mayar mata da gonakin inabinta, Kwarin Akor zai zama kofar bege. Nan za ta amsa mani kamar kwanakin ƙuruciyarta, kamar ranar da ta fito daga ƙasar Masar. 16 "Zaya zamana a ranan nan - wannan furcin Yahweh ne - za ki kira ni, 'Mijina,' kuma ba za ki ƙara kira na 'Ba'al Nawa' ba. 17 Gama zan fitar da sunayen Ba'aloli daga bakinta, ba za a ƙara tunawa da sunayensu ba." 18 A ranan nan zan yi alƙawari domin su da namun jeji, da tsuntsayen sama, da masu rarrafe a ƙasa. Zan kori bakã, da takobi, da kuma yaƙi daga ƙasar, in sa ku zauna lafiya. 19 Zan yi alƙawari in zama mijinki har abada. Zan yi alƙawari in zama mijinki cikin gaskiya, da adalci, da alƙawarin aminci, da jinƙai. 20 Zan ɗaukar wa kaina alƙawarin aminci da ke, za ki kuma san Yahweh. 21 A ranar nan zan amsa - wannan furcin Yahweh ne - Zan amsa wa sammai, su kuma za su amsa wa ƙasa. 22 Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, za su amsa wa Yeziril. 23 Zan dasa ta domin kaina a ƙasar, zan nuna jinkai akan Lo Ruhama, Zan cewa Lo Ammi, 'Ke ce Ammi Attah,' sa'annan za su ce mani, 'Kai ne Allahnmu."'

Sura 3

1 Yahweh yace mani, "Jeka har wa yau, ka ƙaunaci wata mata wadda kaunatacciya ce ga mijinta, amma mazinaciya ce. Ka ƙaunaceta kamar yadda Ni, Yahweh, na ke ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake sukan juya zuwa ga bin waɗansu alloli, suna ƙaunar wainar 'ya'yan itatuwa." 2 Sai na saye ta domin kaina a bakin azurfa sha biyar da hatsi tiya guda da rabin bali. 3 Na ce mata, "Dole ne ki zauna da ni kwanaki da yawa. Ba za ki zama karuwa ba, ko ki zama ta wani mijin ba. Haka nima kuma zan kasance a gare ki." 4 Gama mutanen Isra'ila za su kasance kwanaki da yawa ba sarki, ba kuma ɗan sarki, ba hadaya, ba bagadin dutse, ba falmara ko gumakan gida. 5 Daga baya mutanen Isra'ila za su juyo su nemi Yahweh Allahnsu da sarkinsu Dauda, kuma a kwanakin ƙarshe, za su zo da rawar jiki gaban Yahweh da alheransa.

Sura 4

1 Ku ji maganar Yahweh, ku mutanen Isra'ila. Yahweh yana da ƙara game da mazaunan ƙasar, domin babu gaskiya ko alƙawarin aminci, babu sanin Allah a ƙasar. 2 Akwai la'antarwa, ƙarya, kisa, sata da zina. Mutanen sun zarce dukkan iyaka, ana zubda jini kan zubda jini. 3 Saboda haka ne ƙasar take bushewa, dukkan mazaunanta kuma suna yanƙwanewa; dabbobin jeji da tsuntsayen sama, har ma da kifayen dake a teku, ana kawar dasu. 4 Amma kada ka bari ko guda ɗaya ya kawo ƙara; kada ka bari wani ya zargi wani. Domin ku firistoci kune nake zargi. 5 Ku firistoci za ku yi tuntuɓe da rana, annabawa kuma za su yi tuntuɓe tare da ku da dare, zan kuma hallaka mahaifiyarku. 6 Ana hallaka mutanena saboda rashin ilimi. Saboda ku firistoci kun ƙi ilimi, nima zan ƙi ku zama firistocina. Domin kun manta da dokokina, ko da yake ni Allahnku ne, nima zan manta da 'ya'yanku. 7 Yadda firistocin suke ƙaruwa, haka ma zunuban da suke yi mani. Sukan misanya ɗaukakarsu da kunya. 8 Suna ci daga zunuban mutanena; suna da zarin mugunta da yawa. 9 Zai zama ɗaya saboda mutane da kuma firistoci: Zan hukunta su dukka saboda al'amuransu, zan saka masu saboda ayyukansu. 10 Za su ci amma ba zai ishe su ba; za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba, domin sun yi nisa da Yahweh. 11 Suna ƙaunar fasiƙanci, ruwan inabi, da sabon ruwan inabi, wanda yake ɗauke fahimtarsu. 12 Mutanena suna neman shawara daga gumakun itacensu, sandar tafiyarsu kuma na basu anabce - anabce. Domin tunanin fasiƙanci ya ɓadda su, sun aikata karuwanci maimakon su zama da aminci ga Allahnsu. 13 Suka miƙa hadayu a ƙwanƙolin duwatsu, suka ƙona turare bisa tuddai, ƙarƙashin rimaye, foflas da tsamiya, domin inuwar tana da daɗi. Sai 'ya'yanki mata suka yi lalata, surukanki mata kuma suka yi zina. 14 Bazan hori 'ya'yanki mata ba sa'ad da suka zaɓi suyi fasiƙanci, ko surukanki mata idan suka yi zina. Domin maza ma suna bada kansu ga karuwai, suna miƙa hadayu domin su yi lalata da keɓaɓɓun karuwai. Waɗannan mutane da basu da ganewa zan fyaɗa su ƙasa. 15 Koda yake Isra'ila kin yi zina, bari Yahuda ma kada ta yi saɓo. Ku mutane, kada ku tafi Gilgal, kada ku haye zuwa Bet Aben, kada kuma ku rantse kuna cewa, "Yahweh hakika mai rai ne." 16 Gama Isra'ila ta yi taurin kai, kamar karsana mai gardama. Ƙaƙa Yahweh zai kawosu makiyaya kamar 'yan tumaki wurin kiwo? 17 Ifraim ya haɗa kansa da gumaka; ku ƙyale shi. 18 Harma idan barasarsu ta ƙare, sukan ci gaba da zinarsu, masu mulkinsu suna amincewa da kunyarsu ƙwarai. 19 Iska za ta nannaɗe ta cikin fukafukanta; za su kuma ji kunya saboda hadayunsu.

Sura 5

1 Ku ji wannan ku firistoci! Ku natsu, gidan Isra'ila! Ku kasa kunne, gidan sarki! Domin hukunci na zuwa bisa kanku dukka. Kun zama tarko a Mizfa tarun da aka baza akan Tabor. 2 'Yan tawaye sun dage da hallakarwa, amma zan hukunta dukkansu. 3 Na san Ifraim, Isra'ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba. Ifraim yanzu kin zama kamar karuwa; Isra'ila ta ƙazantu. 4 Ayyukansu ba za su barsu su juyo ga Allah ba, domin tunanin zina yana cikinsu, ba su kuwa san Yahweh ba. 5 Girman kan Isra'ila yana shaida a kansu, saboda haka Isra'ila da Ifraim za suyi tuntuɓe cikin laifinsu. Yahuda ma zai yi tuntuɓe tare dasu. 6 Zasu tafi tare da garkunansu na tumaki dana shanu su biɗi Yahweh, amma baza su same shi ba, gama ya rigaya ya janye kansa daga gare su. 7 Sunyi rashin aminci ga Yahweh, domin sun haifi 'ya'yan haram. Yanzu bukukuwan sabon wata zai cinyesu dasu da gonakinsu. 8 Ku busa ƙaho a Gibiya, da kakaki a Rama. Ku tada kururuwar yaƙi a Bet Aben: 'Za mu bi ki Benyamin!' 9 Ifraim zata zama kango a ranar hukuncinta. Na yi shelar abin da zai faru lallai a cikin ƙabilar Isra'ila. 10 Shugabannin Yahuda suna kama da masu kawar da dutsen kan iyaka, zan zuba hasalata a kansu kamar ruwa. 11 An murƙushe Ifraim; an danne shi a shari'a domin da yardar rai ya bi gumaka. 12 Saboda haka zan zama kamar asu ga Ifraim, kuma kamar tsatsa ga gidan Yahuda. 13 Da Ifraim ya ga cutarsa, Yahuda ma ya ga rauninsa, sai Ifraim ya tafi Asiriya, Yahuda kuwa ya aiki jakadu wurin babban sarki. Amma bai iya warkar da mutanen ku ba, bai kuma iya warkar da raunukanku ba. 14 Saboda haka zan zama kamar zaki ga Ifraim, kuma kamar dan zaki ga gidan Yahuda. Ni, I, Ni' kaina zan kekketasu in yi tafiya ta; zan kwashe su; ba kuma wanda zai cecesu' 15 Zan tafi in koma wurina, har sai sun yarda su karɓi laifinsu su kuma biɗi fuskata, sai kuma sun biɗe ni da aniya cikin ƙuncinsu."

Sura 6

1 "Zo, mu koma gun Yahweh, gama ya yayyaga mu, amma zai warkar da mu; ya ji mana rauni, amma zai ɗaure mana raunukanmu. 2 Bayan kwana biyu, zai farkar da mu; zai tashemu a rana ta uku, zamu rayu kuma a gabansa. 3 Bari mu san Yahweh, bari mu ƙara nacewa mu san Yahweh. Zuwansa tabbataccene kamar wayewar gari. Zai zo wurinmu kamar ruwan sama, kamar ruwan ƙarshe mai jiƙa ƙasa. 4 Ifraim me zan yi da ke? Yahuda, me zan yi da ke? Amincinki kamar gajimaren safe ne, kamar raɓar da take kaɗewa da wuri. 5 Saboda haka na daddatse su ta wurin annabawansu, na kashesu da maganganun bakina. Umarninka kamar haske ne mai sheƙi. 6 Gama ina biɗar aminci ne ba hadaya ba, da kuma sanin Allah fiye da hadayun ƙonawa. 7 Kamar Adamu sun karya alƙawari; sun yi mani rashin aminci. 8 Giliyad birnin mugaye ne mai sawun jini. 9 Kamar yadda taron mafasa suke wa mutum kwanto haka ƙungiyar firistoci suke haɗa kai su yi kisa a hanya zuwa Shekem; sun aikata laifofi masu ban kunya. 10 A cikin gidan Isra'ila na ga mummunan abu; karuwancin Ifraim na nan, Isra'ila kuma ta ƙazantu. 11 Ke kuma, Yahuda, an ƙaddara miki girbi, sa'ad da zan mayar wa mutanena albarkunsu.

Sura 7

1 Duk lokacin da nake so in warkar da Isra'ila, sai zunuban Ifraim su bayyana, haka kuma mugayen ayyukan Samariya, domin suna shirya yaudara; ɓarawo ya kan shigo, mafasa kuwa su kai hari a titi. 2 Basu sani ba a zukatansu ina sane da dukkan mugayen ayyukansu. Yanzu ayyukansu sun kewayesu; suna nan a fuskata. 3 Da muguntarsu suke faranta wa sarki rai, hakimai kuma da ƙarairayi. 4 Dukkansu mazinata ne, kamar tanderun wuta da mai tuya ya dena zuga wutar daga lokacin kwaɓa curi zuwa lokacin sa gami. 5 A ranar sarki, hakimai suka sa wa kansu ciwo da ƙunar barasa. Ya miƙa hannunsa ga masu yin ba'a. 6 Da zuciya kamar tanderu suna ƙirƙiro dabarun ƙarya. Fushinsu; na ƙuna da dare, da safe yakan tashi kamar harshen wuta. 7 Duk suna da zafi kamar tanderu, suna kuma hallakar da masu mulkinsu. Dukkan sarakunansu sun faɗi; ba wanda yake kira na. 8 Ifraim ya na cuɗanya da al'umma. Ifraim waina ne mai faɗi da ba a juya shi ba. 9 Bãƙi sun cinye ƙarfinsa, amma bai sani ba. An yayyafa furfura a kansa, amma bai sani ba. 10 Girman kan Isra'ila na shaida gãba akansa a; duk da haka basu dawo ga Yahweh Allahnsu ba, basu kuma neme shi ba duk da waɗannan abubuwa. 11 Ifraim kamar kurciya yake, mara wayo, ba hankali, yana kiran Masar yana firiya zuwa Asiriya. 12 Sa'ad da suka tafi, zan baza ragata a kansu, zan jawo su ƙasa kamar tsutsayen sama. Zan hukunta su a tarayyarsu. 13 Kaiton su! Domin sun gudu daga gare ni. Hallaka tana zuwa kansu! Sun yi mani tawaye! Dã na cece su, amma sun yi mani ƙarya. 14 Basu yi mani kuka da dukkan zuciyarsu ba, amma a kan gadajensu suke rusa kuka. Suna taruwa domin hatsi da sabon ruwan inabi, sun juya daga gareni. 15 Ko da yake ni na koyar dasu na kuma ƙarfafa hannuwansu, amma yanzu suna ƙulla mani mugunta. 16 Sun dawo, amma ba su dawo wurina ba, Mafi ‌Ɗaukaka. Suna kama da bakan da ya saki. Hakimansu za su fãɗi da kaifin takobi, saboda hasalar harshensu. Wannan zai jawo masu ba'a cikin kasar Masar.

Sura 8

1 Ka sa ƙaho a leɓunanka! Gaggafa na zuwa bisa kan gidan Yahweh domin mutane sun karya alƙawarina sun kuma bijirewa dokokina. 2 Sun yi kuka gare ni, 'Ya Allahna, mu a Isra'ila mun san ka.' 3 Amma Isra'ila taƙi abin dake mai kyau, maƙiyi kuma zai tasar masa. 4 Sun naɗa sarakuna, amma ba dani ba, sun yi hakimai, amma bada sani na ba. Da zinariyar su da azurfa suka yi wa kansu gumakai, amma lallai za a datse su." 5 "An ƙi ɗan maraƙinki ya Samariya. Fushina yana ƙuna akan waɗannan mutane. Har yaushe zasu kasance cikin laifi? 6 Gama wannan gunki daga wurin Isra'ila ya fito; mutum ne yayi shi; ba Allah ba ne! Za a farfashe ɗanmaraƙin Samariya. 7 Gama mutane sun shuka iska sun girbe guguwa. Hatsin dake tsaye ba shi da tsaba; bai bada gari ba. Ko da ya nuna, bãƙi ne zasu cinye shi. 8 An haɗiye Isra'ila; yanzu sun kwanta tare da ƙasashe sai kace abin da ba shi da amfani. 9 Gama sun hau zuwa Asiriya kamar jakin jeji shi ka ɗai. Ifraim tayi hayar masoya domin kanta. 10 Ko da zasu yi hayar masoya daga cikin al'ummai, yanzu zan tara su. Zasu fara lalacewa, saboda danniyar sarkin sarakuna. 11 Saboda Ifraim ya ruɓanya bagadai domin miƙa baye-baye na zunubi, amma a maimakon haka sai suka zama bagadan aikata zunubi. 12 Ko da zan rubuta masu dokata sau dubu goma, zasu dube ta a matsayin baƙon abu a gare su. 13 Game da maganar hadayun baye-bayena, suna hadaya da nama su kuma ci. Amma ni, Yahweh, ban karɓe su ba. Yanzu zan tuna da muguntarsu in hukunta zunubansu. Za su koma Masar. 14 Isra'ila ya manta da ni, Mahaliccinsa, ya kuma gina masarautai. Yahuda ya gina garu masu yawa, amma zan aikar da wuta bisa biranen su; zai hallakar da kagara.

Sura 9

1 Isra'ila, kada ka yi farinciki, tare da murna kamar sauran mutane. Gama ka yi ta rashin aminci, ka yashe da Allahnka. Kana son biyan haƙƙoƙin karuwa a dukkan masussukai. 2 Amma masussuka da wurin matsewar inabi ba zasu ciyar da su ba; sabon ruwan inabi kuma zai ƙare. 3 Ba zasu ci gaba da zama a ƙasar Yahweh ba; maimakon haka, Ifraim zai koma Masar, wata rana zasu ci ƙazantaccen abinci a Asiriya. 4 Ba zasu zuba hadayun inabi ga Yahweh ba, ba kuma zasu zama abin karɓa gare shi ba. Hadayunsu zasu zama kamar abincin makoki: duk wanda ya ci shi zai ƙazantu. Domin abincinsu zai zama nasu ne kaɗai; ba zai zo cikin gidan Yahweh ba. 5 Me za ku yi a ranar da aka keɓe don taruwa, a ranar idi ta Yahweh? 6 Gama, duba, idan sun kubcewa hallaka, Masar zata tara su, Memfis kuma za ta bizne su, kayayyakin daraja na azurfa - abubuwa masu tsini zasu mallake su, ƙayayuwa kuma za su cika rumfunansu. 7 Kwanakin hukunci suna zuwa; kwanakin sakamako suna zuwa. Bari dukkan Isra'ila su san waɗannan abubuwa. Annabin wawa ne, masanin kuma taɓaɓɓe ne, saboda girman muguntarka da yawan zafin ranka. 8 Annabi mai tsaro ne domin Allahna akan Ifraim. Amma tarkon tsuntsu yana kan dukkan hanyoyinsa, rashin jituwa kuma na cikin gidan Allahnsa. 9 Sun ƙazantar da kansu ƙwarai kamar a cikin kwanakin Gibiya. Allah zai tuna da muguntarsu, zai kuma hukunta zunubansu. 10 Yahweh yace, "Lokacin da na samo Isra'ila, kamar samun 'ya'yan inabi ne a cikin jeji. Kamar nunan farin itacen ɓaure a lokacinsa, na samo ubanninku. Amma suka je wurin Ba'al Fiyo, suka kuma miƙa kansu ga wannan gunki abin kunya. Suka zama abin ƙyama kamar gunkin da suke ƙauna. 11 Amma ga Ifraim darajarsu zata tashi kamar tsuntsu. Ba mai haihuwa, ba mai juna biyu, ko mai daukar ciki. 12 Ko da yake sun goyi 'ya'ya, zan ɗauke su daga gare su ba wanda zai ragu. Kaiton su sa'ad da na juya daga gare su! 13 Na ga Ifraim, kamar Taya, an dasa ta a wuri mai dausayi, amma Ifraim zai kawo 'ya'yansa wurin wani wanda zai yayyanka su." 14 Ka ba su, Yahweh - me zaka ba su? Ka ba su mahaifa mai yin ɓari, da nonon da baya ba da madara. 15 "Saboda muguntarsu a Gilgal, a can ne na fara ƙinsu. Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga cikin gidana. Bazan ƙara ƙaunarsu ba; dukkan shugabanninsu 'yan tawaye ne. 16 Ifraim na da cuta, sauyarsa kuma ta bushe; basu ba da 'ya'ya. Ko da zasu sami 'ya'ya, zan kashe ƙaunattatun 'ya'yansu." 17 Allahna zai ƙi su saboda ba suyi masa biyayya ba. Zasu zama masu kai wa da komowa cikin al'ummai.

Sura 10

1 Isra'ila kuringa ce mai yabanya dake ba da 'ya'yansa. Gwargwadon yawan 'ya'yansa gwargwadon yawan gina bagadansa. Bisa ga albarkar ƙasarsa, yakan inganta ginshiƙansa. 2 Zuciyarsu da yaudara; yanzu dole su ɗauki laifinsu. Yahweh zai rushe bagadansu; zai lalatar da ginshiƙansu. 3 Sa'annan zasu ce, "Bamu da sarki, domin ba mu jin tsoron Yahweh, sarki kuma -- me zai yi mana?" 4 Maganganunsu na wofi ne, su kan ɗauki wa'adodi ta wurin rantsewa kan ƙarya. Domin wannan adalci ya tsuro kamar tsire - tsire masu dafi cikin gona. 5 Mazaunan Samariya zasu tsorata saboda 'yan'maruƙan Bet Aben. Mutanenta zasu yi makoki a kanta, kamar yadda mazinatan firistoci suka yi murna a kansu da darajarsu, amma yanzu ba su nan. 6 Za a kai su Asiriya a matsayin kyauta ga babban sarki. Za a kunyatar da Ifraim, Isra'ila kuma za ta ji kunya saboda gumakanta. 7 Za'a hallakar da sarkin Samariya, kamar sassaƙen itace a bisa ruwa. 8 Za a hallakar da wurin zaman mugunta. Wannan shi ne zunubin Isra'ila! Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya zasu fito bisa bagadansu. Mutane zasu cewa duwatsu, "Ku rufe mu!" tuddai kuma, "Ku faɗo mana!" 9 Isra'ila kayi zunubi tun kwanakin Gibiya; a can ka tsaya. Ko yaƙi ba zai iske 'ya'yan kurakurai a Gibiya ba? 10 A lokacin da na so, zan horar dasu. Al'ummai zasu taru su ɗaure su saboda laifofinsu. 11 Ifraim horarriyar karsana ce dake son sussukar hatsi, zan sa karkiya a bisa kyakkyawan wuyanta. Zan sa karkiya a wuyan Ifraim; Yahuda zai yi huɗa; Yakubu kuma zai ja garma da kansa. 12 Ku shuka wa kanku adalci, za ku girbi ɗiyan alƙawarin aminci. Kuyi kaftun saurar ƙasarku, gama lokaci ya yi da za a nemi Yahweh, har lokacin da zai zo ya zuba adalci a kanku. 13 Kun shuka mugunta; kun girbe rashin adalci. Kun ci 'ya'yan yaudara saboda kun dogara ga shirye-shiryenku da kuma yawan sojojinku. 14 Domin wannan hargitsin yaki zai tashi daga cikin mutanenku, za a kuma lalatar da dukkan garuruwanku masu kagara, zai za ma kamar yadda Shalman ya lalatar da Bet Arbel a ranar yaƙi, aka datse uwaye da 'ya'yansu gunduwa-gunduwa. 15 Haka zai faru dake, Betel, saboda muguntar ki mai yawa. Da wayewar gari za a datse sarkin Isra'ila gaba ɗaya."

Sura 11

1 Lokacin da Isra'ila yake yaro na ƙaunace shi, na kuma kira ɗana daga cikin Masar. 2 Yawan kiran su, yawan gujewar su daga gare ni. Sun miƙa hadaya ga Ba'aloli, suka ƙona turare ga gumaka. 3 Duk da haka ni na koyawa Ifraim tafiya. Ni ne na ɗaga su da hannuwansu, duk da haka basu sani na kula dasu ba. 4 Na bishe su da linzamin mutune, da ragamar ƙauna. Na zama kamar mai kwance masu karkiya a muƙamuƙinsu, na sunkuya masu na ciyar dasu kuma. 5 Baza su koma ƙasar Masar ba? Ko Asiriya ba za suyi mulkinsu saboda sunƙi juyowa gare ni ba? 6 Takobi zai faɗa wa biranensu ya hallaka ƙarafan ƙofofinsu; zai hallaka su saboda shirye-shiryensu. 7 Mutanena sun ƙudurta juyawa daga gareni. Ko da sun yi kira ga Maɗaukaki, ba wanda zai taimake su. 8 Ta yaya zan iya rabuwa da kai, ya Ifraimu? Ta yaya zan mika ka, ya Isra'ila? ‌‌‌Ƙaƙa zan maishe ka kamar Adma? Yaya zan maishe ka kamar Zeboyim? A gare ni zuciyata ta canza; dukkan jinƙaina ya harzuƙa. 9 Bazan tabbatar da zafin fushina ba; bazan hallakar da Ifraim ba. Gama Ni Allah ne ba mutum ba; Ni ne Mai Tsarki wanda ke tsakiyar ku, ba kuwa zan zo cikin hasala ba. 10 Zasu bi Yahweh; shi kuma zai yi ruri kamar zaki. Idan yayi ruri, 'ya'yansa za su zo suna rawar jiki daga yamma. 11 Zasu zo da rawar jiki kamar tsuntsu daga Masar, kamar kurciya daga ƙasar Asiriya. Zan maishe su su zauna a gidajensu - wannan furcin Yahweh ne. 12 Ifraim ya kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra'ila kuma da yaudara. Amma Yahuda har yanzu yana tare da ni, Allah, yana yi mani aminci, Mai Tsarkin nan."

Sura 12

1 Ifraim yana ci daga iska, ya na bin iskar gabas. Kullum yana yawaita ƙarairayi da ta'addanci. Sun yi alƙawari da Asiriya suna ɗaukar man zaitun zuwa Masar. 2 Yahweh kuma yana da ƙara gãba da Yahuda kuma zai hukunta Yakubu saboda abin da ya yi; zai sãka masa gwargwadon ayyukansa. 3 A cikin ciki Yakubu ya kama duddugen ɗan'uwansa, a cikin balagarsa kuma yayi kokowa da Allah. 4 Yayi kokowa da mala'ika kuma ya yi nasara. Ya yi kuka ya roƙi tagomashinsa. Ya sadu da Allah a Betel; a can Allah yayi magana da shi. 5 Wannan shi ne Yahweh, Allah Mai runduna; "Yahweh" shi ne sunansa da za a dinga kira 6 Domin wannan ka juyo wurin Allahnka. Ka kiyaye alƙawarin jinƙai da adalci, kana cigaba da sauraron Allahnka. 7 'Yan kasuwa na riƙe da ma'aunin algus a hannunsu; suna son yin algus. 8 Ifraim yace, "Hakika na zama mai arzaƙi sosai; na samarwa kaina dukiya. A cikin dukkan aikina ba za a sami laifi a ciki na ba, ko duk wani abin da zai zama zunubi." 9 "Ni ne Yahweh Allahnku tun daga ƙasar Masar. Zan kuma sa ku sake zama cikin rumfuna, kamar cikin kwanakin ayyanannen idi. 10 Na yi magana da annabawa, na kuma basu wahayi da yawa domin ku. Ta hannun annabawa kuma na ba da misalai." 11 Idan akwai mugunta a Giliyad, hakika mutane sun zama marasa amfani. A Gilgal sun yi hadayar bajimai; bagadansu zasu zama kamar tsibi -tsibin dutse a cikin gonaki. 12 Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra'ila ya yi aiki domin ya sami mata; ya yi kiwon garkunan tumaki domin ya sami mata. 13 Yahweh ya fitar da Isra'ila daga Masar ta wurin annabi, ta hannun annabi kuma ya kula dasu. 14 Ifraim ya baƙanta wa Yahweh rai. Domin wannan Ubangijinsa zai bar jininsa a kansa, zai kuma sãka masa akan duk abin kunyarsa.

Sura 13

1 "Sa'ad da Ifraim ya yi magana, akwai razanarwa. Ya ɗaukaka kansa a Isra'ila, amma ya zama da laifi wajen bautar Ba'al, kuma ya mutu. 2 Yanzu, sai ƙara zunubi suke tayi, suna yiwa kansu sifofi na zubi daga azurfarsu, gumaka ne da masu hikima suka ƙera, dukkan su aikin gwanayen masu sana'a ne. Mutane suka ce masu, 'Waɗannan mutane masu miƙa hadaya sunyiwa 'yanmaruƙa sumba.' 3 Domin wannan zasu zama kamar gizagizan safe, kamar raɓa mai kaɗewa da sauri, kamar ƙai-ƙayi wanda iska ke hurewa daga masussuka, kamar hayaƙi daga cikin mafitarsa. 4 Amma ni ne Yahweh Allahnka tun daga ƙasar Masar, dole ka sani cewa ba bu wani Allah sai ni, dole kuma ka amince cewa banda ni babu wa ni mai ceto. 5 Na san ka a cikin jeji, cikin ƙasa mai tsananin fari. 6 Da kuka sami makiyaya, kun zama ƙosassu; amma bayan da kuka ƙoshi, kun ɗaukaka kanku. Saboda wannan dalili kuka manta da ni. 7 Zan zama kamar zaki a gare su; kamar damisa zan yi fako a kan hanya. 8 Zan faɗa masu kamar damisa da aka ƙwace mata 'ya'yanta, zan tsaga haƙarƙarin ƙirjin su, a can ne zan cinye su kamar zaki, kamar naman jeji zan yayyage su gunduwa-gunduwa. 9 Zan hallaka ku, ya Isra'ila; wanene zai iya taimakon ku? 10 Yanzu ina sarkinku, da za ya iya ceton ku daga cikin dukkan biranenku? Ina shugabanninku waɗanda kuka ce mani, 'Ka bamu sarki da hakimai'? 11 Na baku sarki cikin fushina, na kuma kawar da shi cikin hasalata. 12 Laifin Ifraim a ajiye yake; an kuma ajiye kurakuransa, 13 Zafin naƙudar haihuwa za ta afko masa, amma ɗa ne mara hikima, domin idan lokacin haihuwarsa ya yi, ba zai fita daga cikin mahaifa ba. 14 ̀̀̀̀̀Zan cece su daga hannun Lahira? Zan cece su daga mutuwa? Mutuwa, ina, annobanki? Lahira, ina hallakarwarki? Babu sauran tausayi daga idanuna." 15 Koda Ifraim ya azurta cikin 'yan'uwansa, iskar gabas za ta zo; guguwar Yahweh za ta buga daga hamada. Maɓulɓular Ifraim za ta bushe, rijiyarsa ba zata ba da ruwa ba. Abokan gãbarsa zasu washe ɗakin ajiyar dukkan kayansa masu daraja. 16 Samariya za ta ji kunya, domin ta tayarwa Allahnta. Zasu faɗi ta kaifin takobi; ƙananan 'ya'yansu za a yayyankasu, matansu masu ciki za a farke su.

Sura 14

1 Isra'ila, ka juyo wurin Yahweh Allahnka, gama ka faɗi saboda laifinka. 2 Ka ɗauki maganganun tare da kai ka juyo wurin Yahweh. Ka ce masa, "Ka kawar da dukkan laifinmu ka kuma karɓi abin da ke mai kyau, domin mu iya miƙa maka ɗiyan leɓunanmu. 3 Asiriya ba za su cece mu ba; ba za mu hau dawakai mu yi yaƙi ba. Ba kuwa zamu ƙara ce da aikin hannuwanmu, 'Ku ne allolinmu,' gama a cikinku marayu ke samun jinƙai." 4 "Zan warkar da bauɗewarsu; zan ƙaunacesu a yalwace, domin na kawar da fushina daga gare shi. 5 Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila; zai yi fure kamar auduga, ya kuma kafu kamar itacen sida a Lebanon. 6 Rassansa zasu yaɗu waje; kyaunsa zai zama kamar itatuwan zaitun, ƙanshinsa kuma kamar itatuwan sida a Lebanon. 7 Mutanen da ke zaune ƙarƙashin inuwarsa zasu dawo; zasu farfaɗo kamar hatsi zasu yi fure kamar kuringar inabi. Shahararsa za ta zama kamar inabin Lebanon. 8 Ifraim, me zan yi kuma da gumaka? Zan amsa masa in lura da shi. Ni kamar itacen bakin rafi ne wanda kullum ganyayensa kore ne; daga wurina kuke samun 'ya'ya." 9 Wane ne mai hikima da zai fahimci waɗannan abubuwa? Wane ne ya fahimci waɗannan abubuwa domin ya san su? Gama hanyoyin Yahweh dai-dai suke, adali kuwa zaya yi tafiya cikinsu, amma masu tayarwa zasu faɗi a cikinsu.

Littafin Yowel
Littafin Yowel
Sura 1

1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo ga Yowel ɗan Fetuwel. 2 Ku ji wannan ku dattawa, ku kuma kasa kunne dukkan ku mazauna ƙasar. Ko wannan ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin iyayenku? 3 Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa, 'ya'yanku kuma su fada wa tsara mai zuwa. 4 Abin da bãbe ya rage fara ta ci; abin da da fara ta bari burdunnuwa ta ci; abin da burdunnuwa ta rage; ganzari ya cinye. 5 Ku mashaya, ku tashi, ku yi ta kuka! Ku yi ta baƙin ciki, ku dukkan mashayan ruwan inabi, don an datse inabinku mai zaƙi daga gare ku. 6 Don wata al'umma ta zo kan ƙasata, ƙaƙƙarfa mara ƙidayuwa. Haƙoransu haƙoran zãki ne, kuma suna da haƙoran zãkanya. 7 Sun mayar da kuringar inabina abar wofi. Sun yayyage dangar itacen ɓaurena, sun yayyage dangar sun watsar; rassan sun koɗe sun yi fari. 8 Ku yi makoki kamar amaryar da ke makokin mutuwar angonta. 9 An dena miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Yahweh. Firistoci, bayin Yahweh suna makoki. 10 Filaye sun bushe, ƙasa tana makoki saboda an hallakar da hatsi. Sabon ruwan inabi ya ƙare, mai ya kasa. 11 Ku manoma ku ji kunya, ku yi baƙinciki, hakan nan ku wuraren matse ruwan inabi, saboda alkama da sha'ir. Don abin da aka girbe ya lalace. 12 Inabi sun kaɗe, itatuwan ɓaure kuma sun bushe, itacen ruman, da kuma na dabino, da gawasa duk da sauran itatuwa sun bushe. Don farinciki ya ƙare daga cikin mutane 13 Ku firistoci ku sa tufafin makoki, ku firistoci ku yi bakin ciki, ku masu hidima a bagadi ku kwanta cikin tufafin makoki har safiya, ku bayin Allahna. Don an hana miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Allahnku. 14 Ku yi kira a yi azumi mai tsarki, ku kuma yi kira a yi tattaruwa mai tsarki. Ku tattara dattatawa da dukkan mazaunan ƙasar zuwa gidan Yahweh Allahnku, ku yi kuka ga Yahweh. 15 Kaito saboda ranar! Gama ranar Yahweh ta ƙarato. Tare da ita akwai hallakarwa daga Mai iko dukka. 16 Ba a ɗauke abinci daga gabanmu ba, an kuma ɗauke farinciki da fara'a daga gidan Allahnmu ba? 17 Iri ya lalace a kofensa, an wulaƙanta hatsi, an banzantar da wuraren ajiya don hatsi ya yanƙwane. 18 Yaya dabbobi ke nishi! Makiyayan dabbobi kuma ke shan wahala saboda ba wurin kiwo. Hakannan kuma garken tumaki na shan wahala. 19 Yahweh, ina kuka gare ka. Don wuta ta cinye makiyayar dake jeji, harshen wuta kuma ya ƙone bishiyoyin dake cikin filayen. 20 Har da dabbobin jeji suna yi maka kuka, don ƙoramun ruwa sun bushe, wuta kuma ta cinye makiyayar jeji.

Sura 2

1 Ku hura ƙaho a Sihiyona, ku kuma kaɗa kararrawa a kan duwatsuna masu tsarki! Bari dukkan mazaunan ƙasar su gigice don tsoro, Don hakika ranar Yahweh tana tafe, hakika ta kusa. 2 Rana ce ta duhu baƙiƙƙirin, rana ce ta giza-gizai da baƙin duhu. Kamar yadda duhu ke rufe duwatsu, babbar rundunar sojoji tana kusantowa. Ba a taɓa samun soja kamarta ba, ba kuma za a sake samun kamar ta ba, Koma a bayan tsararraki da yawa. 3 Wuta na cinye duk abin da ke gabanta, bayanta kuma harshen wutar yana ƙuna. ƙasar ta zama kamar gonar Adnin a gabanta, amma a bayanta akwai jejin da ba komai. Ba kuma abin da zai tsira daga gare ta. 4 Bayyanuwar sojojin kamar ta dawakai ce, kuma su na gudu kamar mahayan dawakai. 5 Suna tsalle da ƙara kamar na masu karusa a kan duwatsu, kamar kuma ƙarar wutar da ke cin tarin yayi, kamar ta Sojoji masu iko dake shirye domin yaƙi. 6 A gabansu jama'a na cikin ƙunci, dukkan fuskokinsu kuma suka yi suwu. 7 Suna gudu kamar na jarumawa masu iko; suka hau katanga kamar sojoji; suna tafiya a jere kowanne dai-dai a kan sawu, basu kauce matsayinsu ba. 8 Ba wanda ya tunkuɗe wani a gefe, kowa yana tafiya a gefensa, suka kutsa ta cikin kariyar basu kuma kauce layi ba. 9 Suka ruga kan birnin, suna gudu a kan ganuwa, suka haura cikin gidaje, suka shiga ta tagogi kamar ɓarayi. 10 Duniya ta girgiza a gabansu, sammai kuma suka firgita, rana da wata sun duhunta, taurari kuma sun dena haskakawa. 11 Sai Yahweh ya tada muryarsa a gaban sojojinsa, don sojojinsa suna da yawa sosai, suna kuma da ƙarfi, waɗanda ke karɓar umarninsa. Don ranar Yahweh tana da girma da kuma ban tsoro sosai. Wa zai iya jure mata? 12 "Amma ko yanzu ma, "Yahweh yace, "Ku juyo wurina da dukkan zuciyarku. Ku yi azumi da kuka, da makoki." 13 Ku keta zuciyarku ba tufafinku kawai ba, ku komo wurin Yahweh Allahnku. Don shi mai alheri ne da jinƙai, marar saurin fushi kuma ya na cike da alƙawari mai aminci, kuma zai so ya kawar da aiwatar da hukunci. 14 Wa ya sani? Ko zai juyo ya ji tausayi, ya kuma sa masa albarka, da baiko na hatsi da na abin sha saboda Ubangiji Allahnku? 15 A hura ƙaho a Sihiyona, a kira ayi azumi mai tsarki, a kuma yi kira ayi tattaruwa mai tsarki. 16 A tattara jama'a don tattaruwa mai tsarki, a tattara dattawa, a tattara 'yan yara da jarirai masu shan nono. Sai anguna su fito daga ɗakunansu, amare kuma daga kagararsu ta amarcinsu. 17 Sai firistoci bayin Yahweh su yi kuka a tsakanin bagadi da shirayi. Sai su ce, "Ya Yahweh, ka ceci mutanenka, kada kuma ka mai da gãdonka abin ba a, har al'ummai su yi musu ba a. Me ya sa za su faɗa a cikin al'umai cewa, 'Ina Allahnsu?'" 18 Sai ya yi kishin ƙasarsa, ya kuma ji tausayin mutanensa. 19 Yahweh ya amsa wa mutanensa, "Duba zan aiko maku da hatsi, da sabon ruwan inabi, da mai. Zasu wadace ku, kuma ba zan ƙara mai da ku abin wulaƙanci ba a cikin al'ummai. 20 Zan kawar da maharan nan na arewa daga gare ku, kuma za ku kore su zuwa yasassun wurare. jagoran sojojinsu zai fuskanci gabashin teku. Bãshinta zai tashi, mumunan warinta kuma zai tashi.' Hakika, ya yi manyan abubuwa. 21 Ƙasa kada ki tsorata, ki yi murna da farinciki, domin Yahweh zai yi manyan abubuwa. 22 Kada ku ji tsoro, namomin jejin da ke cikin saura, gama tsire-tsiren dake cikin saura zasu tohu, itatuwa zasu bada 'ya'ya, kuma itacen ɓaure da na inabi za su bada "ya'yansu sosai. 23 Mutanen Sihiyona ku yi murna, kuma ku yi farinciki cikin Yahweh Allanhnku. Don zai baku ruwan sama da bazara ya kuma buɗe sakatun sama dominku, ruwan bazara da na koramunku kuma kamar dã. 24 Masussuka za ta cika da alkama, wurin matsar inabi kuma zai cika da sabon ruwan inabi da mai. 25 "Zan komo maku da shekarun da kuka yi asarar hatsinku wanda fãra ta cinye wato wannan farar mai hallakarwa da na aiko cikinku. 26 Za ku ci ku ƙoshi sosai, ku yabi sunan Yahweh Allahnku, wanda ya aikata abubuwan al'ajabi a cikinku, kuma ba zan taɓa sake kawo abin kunya akan mutane na ba. 27 Za ku san cewa ina cikin Isra'iila, kuma ni ne Yahweh Allahnku, kuma babu wani sai ni, kuma ba zan ƙara kawo kunya akan mutanena ba. 28 Bayan wannan kuma zan zubo da Ruhuna ga dukkan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci. Tsofaffinku zasu yi mafarkai, samarinku kuma zasu ga wahayi. 29 Kuma ga bayi da mata bayi, a waɗancan kwanaki zan zubo musu da Ruhuna. 30 Zan nuna al'ajabai a sama da kuma a duniya, jini, da wuta, da murtukewar hayaƙi. 31 Rana zata duhunta, wata kuma zai zama jini, kafin babbar ranar nan ta Ubangiji mai ban tsoro ta zo. 32 Zai zama kuma dukkan wanda ya yi kira ga sunan Yahweh zai tsira. Don a dutsen Sihiyona da kuma a cikin Yerusalem za a sami waɗanda suka tsira, kamar yadda Yahweh ya ce, da kuma cikin waɗanda suka rayu, wato waɗanda Yahweh ya kira.

Sura 3

1 A waɗannan kwanaki da lokatai, sa'ad da na komar da masu zaman talalar Yahuda da Yerusalem, 2 Zan tattara dukkan al'ummai in kuma kawo su kwarin Yehoshafat. A can zan yi masu shari'a, saboda jama'ata da abin gãdona Isra'ila, waɗanda suka warwatsar cikin al'ummai, saboda kuma sun raba ƙasata. 3 Sun kuma jefa ƙuri'a kan mutanena, sun sayar da yaro saboda da karuwa, sun kuma sayar da yarinya saboda ruwan inabi don su sha. 4 Yanzu don me kuke fushi da ni, ku Taya, da Sidon da dukkan yankin Filistiya? Ko za ku sãka mani? Ko da ma kun sãka mani nan da nan zan komo muku da ramuwarku a kanku. 5 Don kun ɗauke zinariyata da azurfata, kun kuma kawo kayayyakina masu daraja zuwa cikin masujadanku. 6 Kun sayar da mutanen Yahuda da na Yerusalem ga Girkawa, don ku cire su can nesa da ƙasarsu. 7 Duba, ina gab da in tayar da su, daga inda kuka sayar dasu, ku ne kuma za ku biya kuɗin fansa da kanku. 8 Zan sayar da 'ya'yanku maza da mata ta hannun mutanen Yahuda. Za su sayar da su ga Sabiyawa, ga al'umma mai nisa, Don Yahweh ne ya furta. 9 Yi wannan shela a cikin al'ummai, 'Ku shirya kanku domin yaƙi, ku horar da manyan mutane, ku bar su su zo kusa, ku bar dukkan jarumawan yaƙi su hauro nan. 10 Ku mayar da dumɓayen garemaninku takkuba, ku kuma mayar da wuƙaƙenku mãsu. Sai raunana su ce "muna da ƙarfi." 11 Ku yi sauri ku zo ku makusantan ƙasashe, ku tara kanku wuri ɗaya a can. Yahweh ya kawo ƙarshen mayaƙanku masu iko.' 12 Bari al'ummai su tada kansu tsaye su zo kwarin Yehoshafat. Don a can zan zauna don in yi wa dukkan al'umman da ke kewaye shari'a. 13 Ku ɗauki lauje don girbi ya nũna. Ku zo, ku mãtsi abin sha, don tulunan ruwan inabi sun cika. sun cika suna zuba, saboda muguntarsu tana da yawa sosai." 14 Akwai hayaniya, a cikin Kwarin Hukunci. Gama ranar Yahweh ta kusa a cikin Kwarin Hukunci. 15 Rana da wata sun zama baƙi, taurari kuma sun dena bada haskensu. 16 Yahweh zai yi ruri daga Sihiyona, ya kuma tada murya daga Yerusalem. Duniya da sammai za su girgiza, amma Yahweh zai zama mafaka ga mutanensa, da kuma kagara ga mutanen Isra'ila. 17 "Da haka za ku sani cewa ni ne Yahweh Allahnku wanda ke a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Daga nan Yerusalem zata tsarkaka, kuma ba wani sojan da zai ƙara ratsa ta. 18 A wannan rana kuma duwatsu zasu cika da ruwan inabi mai zaƙi, tuddai kuma za su kwararo da madara, dukkan ƙoramun Yahuda za su ɓulɓulo da ruwa, magudanu za su zo daga gidan Yahweh su jiƙe kwarin Shittim. 19 Masar zata zama yasasshiya, Idom kuma ta zama jejin da a ka yi watsi da shi, saboda tayarwar da a ka yi wa mutanen Yahuda, saboda an zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu. 20 Gama za a zauna a Yahuda har abada, Yerusalem kuma zata zama wurin zama na dukkan zamanai. 21 Zan yi ramuwar da ban yi ba tukuna a kan jininsu," don Yahweh yana zaune a Sihiyona.

Littafin Amos
Littafin Amos
Sura 1

1 Waɗannan sune abubuwa game da Isra'ila wanda Amos, ɗaya daga cikin makiyaya a Tekowa ya karɓa a wahayi. Ya karɓa waɗannan abubuwa a kwanakin da Azariya ke mulkin Yahuda, da kuma kwanakin Yerobowam ɗan Yehowash ke sarautar Israila, shekaru biyu kafin girgizar ƙasa. 2 Ya ce, "Yahweh zai yi ruri daga Sihiyona; zai yi tsawa da murya mai ƙarfi daga Yerusalem. Wuraren kiwo na makiyayan za su bushe; ƙwanƙolin Karmel zai yi yaushi." 3 Wannan shi ne abin da Yahweh yace: "Domin zunubai uku na Damasku, har don huɗu ma, Ba zan janye hukuncin ba, domin sun zalunci mutanen Gileyad da maƙamai na ƙarfe. 4 Zan aika da wuta a kan gidan Hazael, kuma za ta cinye kagarar Ben-hadad. 5 Zan karya makaran kyamran Damasku zan kuma kau da mutumin da ke rayuwa a Kwarin Aben, da kuma mutumin da yake rike da sandar girma a Bet Iden. Mutanen Aram za su tafi bauta a Kir," inji Yahweh. 6 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Domin zunubai uku na Gaza har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, domin su ne suka ɗauke kamammun mutane dukka, don su miƙa su ga mutanen Idom. 7 Zan aika da wuta akan garun Gaza, za ta kuma lakume kagarorinta. 8 Zan yanke mutumin da yake rayuwa a Ashdod da kuma mutumin da ya ke riƙe da sandar girma daga Ashkelon. Zan juya hannu na gãba da Ekron, kuma sauran Filistiyawa za su hallaka," inji Ubangiji Yahweh. 9 Wannan shi ne abin da Yahweh yace: "Domin zunubai uku na Taya, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, don sun miƙa dukkan mutanen zuwa Idom, kuma sun karya yarjejeniyar yan'uwantakarsu. 10 Zan aika da wuta akan garun Taya, kuma za ta ƙone kagarorinta." 11 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, Domin zunubai uku na Idom, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, don ya farauci 'ɗan'uwansa da takobi ya kuma kawar da dukkan tausayi. Ya cigaba da fushi, fushinsa ya ɗore har abada. 12 Zan aika da wuta akan Teman, kuma za ta cinye fadodin Bozra." 13 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Domin zunubai uku na mutanen Ammon, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, don sun farke mata masu ciki na Gileyad, saboda su ƙara faɗaɗa yankinsu. 14 Zan kunna wuta a garun Rabba, kuma za ta cinye fadodin, tare da ihu a ranar yaƙi, tare da rugugin hadari a ranar guguwar. 15 Sarkinsu zai tafi zuwa bauta, tare da sauran jami'ansa," inji Yahweh.

Sura 2

1 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Domin zunubai uku na Mowab, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, don ya ƙone ƙasusuwan sarkin Idom zuwa toka. 2 Zan aika da wuta akan Mowab, kuma za ta cinye kagarorin Keriyot. Mowab zai mutu a hargitsi, tare da sowa da kuma busa ƙaho. 3 Zan lalata mai shari'a a cikinta, zan kuma kashe dukkan 'ya'yan sarki tare da shi," inji Yahweh. 4 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Domin zunubai uku na Yahuda, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, domin sun ƙi dokar Yahweh kuma sun ƙi dokokinsa. Ƙarerayinsu sun jawo su yin tafiya ba dai dai ba, kamar yadda ubanninsu su ka yi tafiyar. 5 Zan aika da wuta akan Yahuda, kuma za ta cinye kagarorin Yerusalem." 6 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Domin zunubai uku na Isra'ila, har ma don huɗu, ba zan janye hukuncin ba, domin sun sayar da salihai don azurfa da kuma masu bukata akan takalma. 7 Sun tattake kawunan talakawan kamar mutane na taka ƙura a ƙasa; suna ture matalauta a gefe. Mutum da ubansa su kwanta a wurin budurwa ɗaya kuma su na ɓata sunana mai tsarki. 8 Sun kwanta a gefen kowanne bagadi akan tufafin da aka bayar jingina don bashi, kuma a cikin gidajen Allahnsu sukan sha ruwan inabin waɗanda aka yi wa tãra. 9 Ga shi na hallakar da Ba'amore a gaban ku, dogaye masu tsawo kamar itatuwan sida; ya na da ƙarfin kamar rimaye. Ga shi na lalata 'ya'yan itatuwansa na sama da jijiyoyin ƙasa. 10 Kuma na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma bi da ku a cikin daji shekaru arba'in, na kuma ba ku ƙasar Amoriyawa. 11 Na ta da annabawa daga cikin 'ya'yanku, waɗansu kuma daga cikin samarin sun zama Naziriyawa. Ko ba haka ba ne, ya ku mutanen Israila? Yahweh ne ya faɗa 12 Amma kun sa Naziriyawa shan ruwan inabi kun kuma umarci annabawa da kada su yi anabci. 13 Duba, zan ragargaza ku kamar yadda amalanke cike da hatsi yake ragargaza mutum. 14 Ko wani mai gudu ma ba zai tsere ba, mai ƙarfi ba zai ƙara wa kansa ƙarfi ba; ko mai iko ya ceci kansa. 15 Mai baka ba zai iya tsayawa ba; mai saurin gudu ba zai tsira ba; mahayin doki ba zai ceci kansa ba. 16 Ko ma sojojin da suka fi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan - wannan furcin Yahweh ne.

Sura 3

1 Ku saurari maganar da Yahweh ƙe faɗa akan ku, ku mutanen Isra'ila, akan dukkan iyalinku, na fito da ku daga ƙasar Masar. Ku kaɗai na zaɓa daga kowanne iyalai a duniya. 2 "Saboda haka zan hukunta ku don zunubanku." 3 Zan yiwu mutanen biyu su yi tafiya tare, ba tare da yarda ba? 4 Zai yiwu zaki yayi ruri a daji ba tare da ya sami kome ba? Zai yiwu ƙaramin zaki yayi gurnani a kogonsa idan bai kama kome ba? 5 Zai yiwu tsuntsu ya faɗi akan ƙasa idan ba a kafa masa tarko ba? Zai yiwu tarko ya zargu daga ƙasa idan bai kama wani abu ba? 6 Zai yiwu mutane su rasa firgita idan suka ji ƙarar ƙaho a birni? Zai yiwu wata masifa ta auko wa birnin amma Yahweh bai aiko ta ba? 7 Hakika Ubangiji Yahweh ba zai aikata komai ba ba tare da ya baiyana wa bayinsa annabawa ba. 8 Zaki yayi ruri wane ne ba zai ji tsoro ba? Ubangiji Yahweh yayi magana; wane ne ba zai yi anabci ba? 9 A yi shelar wannan a kagarar Ashdod da kuma kagarar ƙasar Masar; a ce, "Ku tara kanku akan duwatsun Samariya ku ga babban shashanci a cikinta, da kuma irin danniyar da ke cikinta. 10 Domin ba su san abin da ya ke dai dai ba - wannan furcin Yahweh ne. Sun cika da tashin hankali da barnar kagarorinsu." 11 Saboda haka, wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh yace, "Abokin gãba zai kewaye ƙasar. Zai nuna ƙarfinsa ya rushe kagarorinka." 12 Wannan ne abin da Yahweh yace: "Kamar yadda makiyayi ya kan ceci ƙafafu biyu kadai na tunkiya daga bakin zaki, ko gutsarin kunne, hakanan kuma ke ma daga cikin mutanen Isra'ila wanda yake zama cikin Samariya, a gefen taragon jirgi kaɗai ko a gefen gado." 13 Ku ji ku kuma shaida game da gidan Yakubu - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne, Allah mai runduna, 14 "A ranar da zan hukunta Isra'ila saboda zunubai, zan kuma hukunta bagadodin Betel. ƙahonin bagadi za su kakkarye su kuma fadi a ƙasa. 15 Zan lalata gidan hunturu tare da na bazara. Gidajen da aka yi da hauren giwa zasu lalace, babban gidan shi ma zai lalace, - wannan furcin Yahweh ne.

Sura 4

1 Ku ji wannan maganar, ku shanun Bashan, ku na cikin dutsen Samariya, ku dake danne matalauta, ku dake hallaka mabukata, ku dake cewa da mazajenku, "Kawo mana abin sha." 2 Ubangiji Yahweh ya rantse da sunansa mai tsarki, "Ku duba, ranaku na zuwa akan ku da za a tafi da ku da ƙugiya, na ƙarshenku tare da fatsar kifi. 3 Za ku fita ta wurin da ya tsage a jikin garun birnin, kowannenku zai tafi ta cikin tsaguwar, za a jefar da ku waje wajen Harmon - wannan furcin Yahweh ne." 4 Ku tafi Betel ku yi zunubi, tafi Gilgal ku ƙara zunubi, ku kawo hadayarku kowacce safiya, zakkarku kowane kwanaki uku. 5 Ku mika gurasarku shaidar haɗayar godiya; ku yi shelar baikon yaddar rai, ku sanar da su, wannan dai dai ne, gare ku mutanen Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. 6 Na ba ku tsabtatattun hakora a cikin dukkan biraninku da kuma ƙarancin gurasa a dukkan wurarenku. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba - wannan furcin Yahweh ne. 7 Na kuma hana ruwan sama daga gare ku a lokacin da akwai sauran watanni uku a yi girbi. Na sa a yi ruwa a birni daya, kuma na sa ka da a yi ruwa a wani birnin. Ɗaya daga cikin sashen ƙasar an yi ruwa amma ɗaya sashen ba a yi ruwa ba ya bushe. 8 Birane biyu ko uku suna ƙishi har ma sun tafi neman ruwa a birnin, amma ba su ƙoshi ba. Amma duk da haka ba ku komo wurina ba - wannan furcin Yahweh ne. 9 Na sa ma ku ƙunci tare da darɓa da raɓa. Yawan lambunanku da gonakin inabinku da itatuwan ɓaurenku da itatuwan zaitun ɗinku fari sun laƙume su dukka. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba - wannan furcin Yahweh ne. 10 Na aika ma ku da annoba irin wanda na aika wa Masar. Na kashe samarinku da takobi, an ɗauke dawakanku, an cika hancinku da ɗoyi. Amma duk da haka kun ki juyo wa gare ni - wannan furcin Yahweh ne. 11 Na hallakar da biraninku kamar yadda Allah ya hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sandar da aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba - wannan furcin Yahweh ne. 12 Domin haka zan yi wani abu mummuna a kanki, ya Isra'ila; shirya don ki sadu da Allahnki, Isra'ila! 13 Ku duba, wanda ya yi duwatsu ya kuma halicci iska, ya baiyana tunaninsa ga mutum, ya maida safiya duhu, ya auna wurare na Duniya. Yahweh, Allah mai runduna, shi ne sunansa."

Sura 5

1 Ku ji wannan maganar dana ɗauke ta kamar ta makoki da zan yi a kanku, gidan Israi'la. 2 Budurwa Isra'ila kin faɗi, ba za ki ƙara tashi ba, an yasheta a ƙasarta; ba wanda zai ta da ita. 3 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Birnin da ya fita tare da dubu zai dawo da ɗari kaɗai, kuma wanda ya tafi da ɗari amma goma kaɗai za su rage na gidan Isra'ila." 4 Wannan shi ne abin da Yahweh ya ce da gidan Isra'ila: "Ku neme ni ku kuma tsira! 5 Kada ku nemi Betel; ko ku shiga Gilgal; ka da ku tafi Biyasheba. Gama babu shakka ita ma za ta tafi bauta, kuma Biyasheba za ta zama wofi. 6 Ku nemi Yahweh ku rayu, ko ya taso ma gidan Yosef kamar wuta. Zai kuwa laƙume, ba kuma wanda zai kashe ta a Betel. 7 Mutanen nan na juya adalci zuwa abu mai ɗaci kuma suna jefar da ayyukan adalci a ƙasa!" 8 Allah ya yi manyan taurari tare da haskensu; ya maida duhu haske; ya maida rana dare shi ne kuma ya kira ruwan teku; ya ƙwararo shi a fuskar duniya. Sunansa Yahweh ne! 9 Ya kawo hallaka a kan ƙarfafa don lalacewar ta kai kan kagarori. 10 Ku na ƙin duk wanda ya ƙwabe ku a ƙofar birnin, kuma tare da duk wanda zai faɗi gaskiya. 11 Domin kun matsa wa talakawa kuna ƙwace alkama daga gare su - koda yake kun gina gidajenku da dutse, ba za ku zauna a cikinsu ba. Kuna sha'awar gonakin inabinsu, kuma ba za ku sha ruwan inabin ba. 12 Domin na san yawan laifofinku, kuma da girman zunubanku - kuna wulakanta masu kirki, ku na karɓar rashawa ku na hanawa talakawa adalci a wurin shari'a. 13 Saboda haka mai hikima shiru yake a waɗanan lokatai, don mugun lokaci ne. 14 Ku nemi yin nagarta ba mugunta ba, saboda ku rayu. Don Yahweh, Allah mai runduna, ya kasance tare da ku, kamar yadda ku ka ce ya ke. 15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, ku yi adalci a cikin majalisa. Watakila Yahweh, Allah mai runduna, zai yi wa sauran da su ka ragu na Yosef alheri. 16 Saboda haka wannan shi ne abin da Yahweh yace, Allah mai runduna, Ubangiji, "Za a yi kuka da kururuwa a kowanne wurin taruwa za su kuma ce a dukkan tituna, 'Kaito! Kaito!' Za su kira manoma su yi makoki kuma masu makokin su yi kuka mai zafi. 17 A cikin dukkan gonakin inabinku za a yi kuka da kururuwa, don zan wuce a tsakiyar ku," inji Yahweh. 18 Kaito ga ku dake marmarin zuwan ranar Yahweh! Me ya sa ku ke jiran ranar Yahweh? 19 Za ta zama baƙa bakikirin kuma babu haske, kamar wanda ya gujewa zaki ya fada a bakin damisa, ko kuwa kamar wanda ya komo gida ya sa hannunsa a bango, maciji kuma ya sare shi. 20 Ko ranar Yahweh za ta zama haske ne ba duhu ba? Almuru ne ba haske ba? 21 Na ki bukukuwanku ba na murna da tarurukanku. 22 Ko da ya ke kun kawo mani baikon ƙonawa da baikonku na hatsi ba zan karɓe su ba, ba kuma zan dubi tarurukan baye-bayenku na manyan dabbobinku ba. 23 Ku kawar mani da hargowar waƙoƙinku; ba zan saurari kaɗe-kaɗenku da bushe-bushenku ba. 24 Maimakon haka ku sa adalci ya kwararo kamar ruwa, adalci kuma ya zama kamar kogin da ba ya ƙafewa. 25 Gidan Isra'ila ko kun kawo mani hadaya da baye-baye a cikin jeji har shekaru ariba'in? 26 Duk da haka ku ka ɗauki siffofin Sakkut sarkinsu da Kaiwan, allolinku na taurari- gumakan da kuka yi wa kanku. 27 Saboda haka zan sa ku yi ƙaura gaba da Damaskus," inji Yahweh, wanda sunansa Allah mai runduna ne.

Sura 6

1 Kaiton waɗanda ke zama sake a Sihiyona, da ke da kariya a tudun ƙasar Samariya, da ku da kuke sanannun mutane da suka fi na kowacce al'umma, ga waɗanda gidan Isra'ila ke zuwa don taimako! 2 Shugabaninku sun ce, "Mu je Kalne mu duba, daga wurin ku je Hamat, babban birnin, sa'an nan har zuwa Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkokinku biyu daraja ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku ne?" 3 Kaiton waɗanda suka kawar da ranar masifa suka kuma sa mulkin hargitsi ya zo kusa. 4 Suna kwance kan gadajen hauren giwa suna jin daɗin miƙe jiki a dogayen kujerunsu. Sun ci naman 'yan raguna daga garke da naman 'yan maruƙa daga turke. 5 Suna raira waƙokin wofi da giraya; kuna amfani da kayan aiki kamar Dauda. 6 Suna shan ruwan inabi daga manyan kwanoni sa'an nan su shafe jikinku da mai mafi kyau, amma ba su yin makoki saboda lalacewar Yosef. 7 To yanzu sune na fari da zasu tafi bauta, kuma bukukuwanku da shagulgulanku zasu wuce. 8 Ni, Ubangiji Yahweh na rantse da kai na - wannan furcin Ubangiji Yahweh, Allah mai runduna, na ƙi girman kan Yakubu; ba na son kagaransa. Saboda haka zan miƙa birnin da duk abin dake ciki. 9 Ko da zai zama mutane goma ne suka rage a gida ɗaya, zasu mutu dukka. 10 Sa'ad da dangin mamacin ya zo don ya ɗauki gawar mamatan -wanda zan ƙone su bayan ya fitar da gawarwaki daga gidan - sai yayi kira ga wanda ya ke a cikin gidan, ko akwai wani kuma a nan? Idan wannan mutum zai ce, "A'a." Sai ya ce, "Ka yi shuru, don ba za mu ambaci sunan Yahweh ba." 11 Duba, Yahweh zai ba da umarni, babban gida buge shi za a yi ya ragargaje, ƙaramin gida kuma ya rushe. 12 Dawakai sukan yi gudu a ƙonƙolin duwatsu? ko da wanda zai iya huɗa da shanu a can? Duk da haka ku ka mai da adalci dafi kuma ku ka mai da nagarta mugunta. 13 Ku da kuke murna akan Lo Dibar, wanda yace, "Ba mu ɗauke Karnaim ta wurin ƙarfinmu ba?" 14 Ku duba zan ta da wata al'umma ta yi gãba da ku, gidan Isra'ila -- wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh, Allah mai runduna. Zasu ƙuntata ma ku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba."

Sura 7

1 Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya nu na mani. Duba, ya sa fari sun yi cincirindo lokacin da aka fara yankan hatsi, duba lokacin girbin baya ne bayan an cire na sarki. 2 Bayan sun gama cinyen kowanne ɗanyen ganye a ƙasar, sai na ce, "Ubangiji Yahweh, idan ka yarda ka yi gafara, yaya Yakubu zai tsira? Don shi ƙarami ne ainun." 3 Yahweh kuwa ya dakatar da nufinsa. Ya ce, "Ba zai faru ba." 4 Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya nuna mani: Duba, Ubangiji Yahweh ya yi kira akan wuta ta shari'a. An busar da fili mai yawan gaske, ruwa mai zurfi a ƙarƙashin duniya an kuma lalata ƙasa. 5 Amma na ce, "Ubangiji Yahweh, idan ka yarda ka tsaya; Yaya Yakubu zai tsira? Don shi ƙarami ne." 6 Yahweh kuwa ya dakatar da wannan. "Wannan ma ba zai faru ba," inji Ubangiji Yahweh. 7 Wannan shi ne abin da aka nuna mani: Duba, Ubangiji ya tsaya gefen bango, yana rike da magwaji a hannunsa. 8 Yahweh yace da ni, "Amos, me ka gani? Sai na ce, "Magwaji." Sai Ubangiji yace, "Duba, zan sa magwaji a wurin mutanena Isra'ila. Ba zan sake barin su ba. 9 Wurare masu bisa na Ishaku za a lalace, wuraren sujada na Israila za su zama kufai, kuma zan yi gãba da gidan Yerobowam da takobi." 10 Sai Amaziya, firist na Betel, ya aika da saƙo zuwa Yerobowam sarkin Isra'ila: "Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin gidan Isra'ila. Ƙasa ba za ta iya ɗaukan dukkan maganganunsa ba. 11 Wannan shi ne abin da Amos yace, 'Yerobowam zai mutu ta takobi, kuma babu shakka Isra'ila zai tafi bauta daga ƙasarsa.'" 12 Amaziya yace da Amos, "Mai gani, tafi da gudu. koma ƙasar Yahuda, a can za ka nemi gurasa ka ci ka kuma yi annabci. 13 Amma kada ka ƙara yin annabci a nan Betel don nan wurin yin sujadar sarki ne kuma gidan sarauta ne." 14 Sai Amos yace wa Amaziya, "Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi. Ni makiyayi ne, kuma mai lura da itatuwan ɓaure. 15 Amma Yahweh ya ɗauke ni daga kiwo sai ya ce da ni, 'Tafi, yi annabci ga mutanena Isra'ila.' 16 Yanzu ji maganar Yahweh. Ka ce; "Ka da ka yi annabci gãba da Isra'ila, kuma kada ka yi magana gãba da gidan Ishaku.' 17 Saboda haka ga abin da Yahweh yace, 'Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka maza da mata da takobi; ƙasarka za a gwada ta a kuma rarraba; kai kanka za ka mutu a cikin ƙasa marar tsarki, kuma babu shakka Isra'ila zai tafi bauta daga ƙasarsa.'"

Sura 8

1 Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya nuna mani. Duba, ga kwandon itacen ɓaure na kaka! 2 Ya ce, "Me ka gani, Amos?" Na ce "Kwandon itacen ɓaure na bazara." Sai Yahweh yace da ni, "ƙarshen mutanena Israila ya zo; Ba zan sake barin su ba. 3 Waƙoƙin haikali za su zama na makoki. A wannan rana -- wannan furcin Ubangiji Yahweh ne -- gawawwaki zasu yawaita, a ko'ina za a jefar dasu waje. Shuru!" 4 Ku saurari wannan, ku da ku ke tattake masu bukata ku na fitar da matalautan ƙasar. 5 Sun ce, yaushe ne sabon wata zai wuce, saboda ko ma sake sayar da amfanin? Yaushe ne Asabar za ta ƙare, ko ma sake sayar da alkama? Za mu rage girman ma'aunin mu kuma ƙara farashi, yayin da muke zalunci da ma'aunin ƙarya. 6 Wannan zai sa mu sayar da alkama mara kyau, mu saye talakawa da zinariya, kuma masu bukata da takalma." 7 Yahweh ya rigaya ya rantse ta wurin fahariyar Yakubu, "Babu shakka ba zan manta da kowanne aikinsu ba. 8 Shin ƙasar ba za ta girgiza a kan wannan ba, dukkan wanda ke cikinta zai yi baƙinciki? Dukkan ƙasar za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu, kuma za ta juya ta kuma sake dulmiyewa, kamar kogin Masar. 9 Za ya zama kuwa a wannan rana - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zan mai da rana ta faɗi da tsakar rana, zan kuma sa duniya ta duhunta a rana kata. 10 Zan mai da bukukuwanku makoki kuma waƙoƙinku su zama makoki. Zan sa maku tufafin makoki, in kuma sa kowa ya aske kansa. Zan sa ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa ɗan su tilo, kuma ranar mai daci ce har karshen ta. 11 Duba, ranaku na zuwa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - da zan aiko da yunwa a ƙasar, ba yunwa don gurasa ba, ko kishin ruwa, amma domin rashin samun sakon magana daga wurin Yahweh. 12 Zasu yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku; zasu yi gudu daga arewa zuwa gabas suna neman sakon maganar Yahweh, amma ba kuma zasu samu ba. 13 A wannan rana kyawawan 'yan'mata da samari zasu faɗi saboda ƙishi. 14 Waɗanda suka yi rantsuwa da zunubin Samariya suka kuma ce, 'Muddin allahnku na raye, Dan,' 'Muddin hanyar zuwa Biyasheba nanan' -- za su faɗi kuma ba zasu ƙara tashi ba."

Sura 9

1 Na ga Ubangiji tsaye wajen bagadi, sai yace, "Bugi saman ginshiƙan don harsasan dukka su girgiza. Farfasa su gunduwa-gunduwa akan kowannen su, ni kuma zan kashe su da takobi. Babu ɗaya daga cikinsu da zai tsere. 2 Ko da za su nutse cikin Lahira, can hannu na zai kamo su. Ko da sun hau sama, zan sauko da su. 3 Ko da sun ɓuya a bisa kololuwar Karmel, can ma zan neme su in cafko su. Ko da sun ɓoye daga ganina a karkashin teku, can ma zan bada umarni ga maciji, shi kuma zai sare su. 4 Ko da sun tafi bauta ta hannun abokan gãbarsu, can ma zan bada umarni ga takobi, takobi kuwa za ya kashe su. Zan sa idanuna a kansu don azaba ba nagarta ba." 5 Ubangiji Yahweh mai runduna ya taɓa ƙasa har ta narke, dukkan waɗanda suke cikinta suna baƙinciki; dukkan abin da ke cikinta zasu tashi kamar Kogi, za ta kuma nutse kamar kogin Masar. 6 Shi ne ya gina matakansa a sammai, ya kafa maɓoyarsa a bisa duniya. Ya kira ruwan teku ya ƙwararo a bisa fuskar duniya, sunansa Yahweh ne. 7 "Ku ba kamar mutanen Kush ba ne gare ni, mutanen Isra'ila? - wannan furcin Yahweh ne. Ba na fito da Isra'ila daga ƙasar Masar da Filistiyawa daga Krit da Aramiyawa kuma daga Kir ba? 8 Duba, idanuwan Ubangiji Yahweh suna kan mulkin nan mai zunubi, kuma zan lalata su daga fuskar duniya, sai dai ba zan hallaka gidan Yakubu kakaf ba -wannan furcin Yahweh ne. 9 Duba, zan ba da umarni, zan kuma rairayi gidan Isra'ila a cikin al'ummai, kamar wanda yake tankaɗan hatsi, don kada a rage ko ɗan ƙaramin dutse ya faɗi a ƙasa. 10 Dukkan masu zunubi daga cikin mutanena za su mutu ta wurin takobi, waɗansu za su ce, 'Masifa ba za ta auko mana ko ta kusan ce mu ba!' 11 A wannan rana zan ta da rumfar Dauda wanda ta faɗi, zan toshe kafafe. Zan ta da lalatattun wurarenta, in kuma sake gina ta kamar kwanakin dă. 12 Ta haka zasu ci nasara ga waɗanda su ka ragu a Idom, da kuma dukkan al'ummai da suke kira da sunana - wannan furcin Yahweh ne - shi ne ya yi wannan. 13 Duba, kwanaki na zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'ad da mai huɗa zai riga mai girbi, mai matse ruwa inabi kuma zai riga mai shuka iri nan da nan. Duwatsu zasu zubo da ruwan inabi mai zaƙi, dukkan tuddai kuma su kwararo da shi. 14 Zan dawo da mutanena Isra'ila daga bauta. Za su giggina biranensu da su ka rurrushe su kuma zauna a ciki, zasu dasa gonakin inabi su kuwa sha ruwan inabinsu, za su yi lambuna su kuma ci amfanin 'ya'yansu. 15 Zan dasa su a ƙasarsu, ba kuwa za a ƙara tumbuke su daga ƙasar da na ba su ba," inji Yahweh Allahnku.

Littafin Obadiya
Littafin Obadiya
Sura 1

1 Wahayin Obadiya. Ubangiji Yahweh ya faɗi haka a kan Idom: Mun ji bayani daga wurin Yahweh cewa an aika da jakada a cikin al'ummai, da cewa, "Tashi tsaye! Bari mu tashi mu kai mata hari!" 2 Ga shi zan mayar dake 'yar ƙarama a cikin al'ummai, za a rena ki ƙwarai. 3 Girman kai na zuciyarki ya ruɗe ki, ke da ki ke zaune a can cikin kogunan dutse, cikin ƙayataccen gidanki; a cikin zuciyarki, kin ce, "Wane ne zai saukar da ni can ƙasa?" 4 Ko da zaki tashi sama kamar gaggafa, ko da zaki kai sheƙarki cikin taurari, zan sauko dake ƙasa, inji Yahweh. 5 Idan ɓarayi suka zo wurinki, idan 'yan fashi suka zo wurinki da daddare - dubi yadda za a maishe ki kufai! - ba za su saci abin da suke buƙata ba ne kawai? Idan masu tattara inabi suka zo, ba zasu rage kala ba? 6 Yadda aka bincike Isuwa, harma da abin da ya ɓoye dukka an bincike! 7 Dukkan mazajen da suka ƙulla amana da ke zasu kore ki har kan iyaka, mazajen da suke zaune lafiya da ke sun ruɗe ki, sun ci nasara a kan ki. Waɗanda suka ci abincinki sun ɗana maki tarko. Babu fahimta a cikinsa. 8 Yahweh yace a waccan rana, "Ba zan ce a hallaka ma su hikima daga cikin Idom ba, da masu ganewa daga cikin dutsen Isuwa ba?" 9 Jarumawanki zasu karaya, Teman, domin a datse kowanne mutum daga dutsen Isuwa ta wurin yankawa. 10 Saboda ta'addancin da aka yi wa ɗan'uwanki Yakubu, kunya za ta rufe ki, za a datse ki har abada. 11 A ranar da ki ka tsaya a ware ke kaɗai, a ranar da bãƙi suka kwashe dukiyarsa, bãƙi suka shiga ƙofofinsa, suka jefa ƙuri'a a kan Yerusalem, kema ki na kamar su. 12 Amma kada ki yi murna a cikin ranar ɗan'uwanki, a ranar da ya yi asara, kuma kada ki yi farinciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu; kada ki yi fahariya a ranar baƙincikinsu. 13 Kada ki shiga ƙofar mutanena a ranar masifarsu; kada ki yi murna a cikin ƙuncinsu a ranar bala'insu; kada ki washe dukiyarsu a ranar rushewarsu. 14 Kada ki tsaya a mararrabar hanyoyi, domin ki datse masu neman tsira da miƙa kuɓutattun mutanensa a ranar ƙuncinsu. 15 Gama ranar Yahweh ta kusa a kan dukkan al'ummai. Kamar yadda ki ka yi, haka za a yi maki, abin da kika yi zai dawo kanki. 16 Kamar yadda kika sha a kan dutsena mai tsarki, haka dukkan al'ummai za suyi ta sha. Za su sha su haɗiye su zama kamar basu taɓa kasancewa ba. 17 Amma a Dutsen Sihiyona za a sami waɗanda suka tsira, kuma zai zama da tsarki; gidan Yakubu kuma zasu mallaki mallakarsu. 18 Gidan Yakubu zai zama wuta, gidan Yosef kuma zai zama harshen wuta mai ci, gidan Isuwa kuma zai zama tattaka, za a ƙone su a hallakar da su. Ba wanda zai tsira daga gidan Isuwa, gama Yahweh ya faɗi." 19 Waɗanda suke daga Negeb zasu mallaki dutsen Isuwa, na Sefilah kuma za su mallake ƙasar Filistiyawa. Za su mallaki ƙasar Ifraim da ƙasar Samariya; shi kuma Benyamin zai mallaki Giliyad. 20 Masu zaman bauta na mutanen Isra'ila masu yawa zasu mallaki ƙasar Kan'ana har zuwa Zerefat. Masu zaman bauta na Yerusalem, waɗanda ke Sefarad zasu mallaki biranen Negeb. 21 Masu kuɓutarwa za su hau zuwa Dutsen Sihiyona za su yi mulki a ƙasar kan tudu ta Isuwa, mulkin kuma zai zama na Yahweh.

Littafin Yona
Littafin Yona
Sura 1

1 Maganar Yahweh ta zo ga Yona ɗan Amittai, cewa, 2 "Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi magana gãba da shi, saboda muguntarsa ta zo gare ni." 3 Amma Yona ya tashi ya gudu daga gaban Yahweh ya tafi Tarshish. Ya tafi Yofa ya sami jirgin da zai tafi Tarshish. Ya biya kuɗin tafiya Tarshish. Domin ya gudu daga fuskar Yahweh. 4 Amma sai Yahweh ya aika da babbar iska a kan teku wadda ta zama hadari mai ƙarfi ta sa jirgin ya yi ta kaɗawa kamar zai fashe. 5 Sai masu tuƙin jirgin su ka ji tsoro sosai mutanen suka yi ta addu'a kowanne ga allahnsa. Sai suka zubar da kayan da ke cikin jirgin a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Amma Yona yana can cikin ƙarshen jirgi yana barci mai nauyi. 6 Sai mai tuƙin jirgin ya zo ya same shi yace da shi, "Barci ka ke yi? Tashi! Ka kira ga allahnka! Ko allahnka zai ji ya cece mu daga hallaka." 7 Sai suka ce da junansu, "Ku zo mu jefa ƙuri'a mu gani ko wane ne ya sa muka shiga wannan masifa." Da suka jefa ƙuri'a sai ta faɗa kan Yona. 8 Sai suka ce da Yona, "In ka yarda ka gaya mana wane ne ya sa wannan masifa ta same mu. Mene ne aikinka, daga ina ka ke? Daga wacce ƙasa ka ke, kai ɗan wacce kabila ne?" 9 Yona yace da su, "Ni Ba'ibrane ne; kuma ina jin tsoron Yahweh, Allah na sama, wanda ya halitta sama da teku da busasshiyar ƙasa." 10 Sai mutanen suka ƙara jin tsoro suka ce da Yona, "Me ka yi kenan?" Sun sani cewa ya gudu ne daga wurin Yahweh, gama ya faɗa masu. 11 Sai suka ce da Yona, "Me za mu yi maka domin tekun ya kwanta?" Saboda tekun na ƙara yin hauka. 12 Sai Yona yace masu, "Ku ɗauke ni ku jefa cikin tekun. Tekun kuwa zai yi shiru domin ku, gama na sani saboda ni ne wannan babban hadari ya same ku." 13 Amma duk da haka, mutanen suka yi ta ƙoƙari domin su mallako jirgin ya dawo bakin gãɓa, amma suka kasa saboda tekun yana ta ƙara yi masu hauka. 14 Sai suka yi kuka ga Yahweh suka ce, "Mun roƙe ka, Yahweh, mun roƙe ka, kada ka bari mu hallaka saboda wannan mutum, ya Yahweh, kada ka ɗora alhakin mutuwarsa a kan mu, saboda kai Yahweh ka yi adalci ka kuma yi kamar yadda ya gamshe ka." 15 Sai suka ɗauki Yona suka jefa shi cikin teku sai tekun ya daina hauka. 16 Sai mutanen suka ji tsoron Yahweh ƙwarai da gaske. Suka miƙa hadayu ga Yahweh suka kuma yi alƙawura. 17 Yahweh kuwa ya shirya wani babban kifi don ya haɗiye Yona, Yona kuma ya kasance a cikin cikin kifi har yini uku da kwana uku.

Sura 2

1 Daga can cikin kifi sai Yona ya yi addu'a ga Yahweh Allahnsa. 2 Ya ce, "Na yi kira ga Yahweh game da ƙuncina ya kuwa amsa mani; daga can cikin Lahira na yi kuka na neman taimako! Ka ji muryata. 3 Ka jefa ni can cikin ƙarƙashin ƙasa, cikin zurfin tekuna, rigyawa da ambaliya, raƙuman ruwa sun bi ta kaina. 4 Na ce, 'An kore ni daga fuskarka; amma duk da haka zan sake duban haikalinka mai tsarki.' 5 Ruwaye sun sha kaina har zuwa wuyana; zurfi ya kewaye ni ta ko'ina, rigyawa ta sha kaina. 6 Na shiga ƙarƙashin duwatsu; duniya da makullanta sun rufe ni har abada. Amma duk da haka ka tsamo raina daga rami, Yahweh, Allahna! 7 Lokacin da raina ya sume a cikina, sai na tuna da Yahweh a cikin raina; sai addu'ata ta zo gare ka, a haikalinka mai tsarki. 8 Waɗanda suka juya ga alloli marasa amfani sukan ƙi amincinka zuwa gare su. 9 Amma ni zan miƙa maka hadaya da murya ta godiya, zan cikasa abin da na alƙawarta. Daga wurin Yahweh ceto yake zuwa!" 10 Sai Yahweh ya yi magana da kifin, sai kifin ya amayar da Yona a gãɓar tekun.

Sura 3

1 Maganar Yahweh ta zo wurin Yona karo na biyu, cewa, 2 "Ka tashi, ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi shelar saƙon da na umarce ka ka bayar." 3 Sai Yona ya tashi, ya tafi Nineba ya yi biyayya da maganar Yahweh. Nineba dai birni ne babba, kuma tafiya ce ta kwana uku. 4 A yini guda Yona ya fara shiga birnin ya yi kira ya ce, "A cikin kwana arba'in za a rushe Nineba." 5 Mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka yi shelar yin azumi. Dukkan su suka sanya tsummokara, daga manyansu har ya zuwa ƙananansu. 6 Nan da nan labari ya kai ga sarkin Nineba. Shi kuwa ya tashi daga kursiyinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya rufe kansa da tsummokara, ya zauna cikin toka. 7 Sai ya aika ayi shelar cewa, "A cikin Nineba, bisa ga ikon sarki da majalisarsa, kada wani mutum ko dabba, ko garken shanu da tumaki, ko na awaki ya ɗanɗana wani abu. Kada su ci abinci ko su sha ruwa. 8 Amma sai mutum da dabba su rufa da tsummokara kuma su yi kuka mai ƙarfi zuwa ga Allah. Sai kowanne mutum ya juya daga hanyarsa ta mugunta da kuma ta'addancin dake cikin hannuwansa. 9 Wa ya sani? Ko Allah zai iya yin jinkiri kuma ya canza ra'ayinsa ya kuma juya daga fushinsa mai zafi domin kada mu hallaka." 10 Allah ya ga abin da suka yi, yadda suka juya daga hanyoyinsu na mugunta. Sai Allah ya canza ra'ayinsa game da hukuncin da ya ce zai zartar a kansu, bai kuma zartar da shi ba.

Sura 4

1 Amma hakan bai yi wa Yona daɗi ba, sai ya ji haushi ƙwarai. 2 Saboda haka, Yona ya yi addu'a ga Yahweh ya ce, "Yahweh, ashe ba abin da na ce ba kenan tun ban baro ƙasata ba? Shi ya sa tun da farko na yi ƙoƙarin gudu zuwa Tarshish - domin na san kai Allah ne mai alheri, mai tausayi, mai jinkirin fushi, cike da aminci, ka kan kuma fasa aiko da bala'i. 3 Saboda haka yanzu, Yahweh, na roƙe ka, ka ɗauke raina daga gare ni, gama ya fiye mani in mutu, da in rayu." 4 Yahweh yace, "Ya dace da ka yi fushi haka?" 5 Sai Yona ya fita daga birnin ya zauna daga gabas da birnin. Can ya yi rumfa ya kuma zauna a ƙarƙashinta domin ya ga abin da zai faru da birnin. 6 Yahweh Allah ya shirya wata 'yar itaciya ya sa ta yi girma ta kere Yona, domin ta zama inuwa a saman kansa ta sauƙaƙa ƙuncinsa. Yona kuwa ya yi murna sosai sabo da wannan 'yar itaciyar. 7 Amma Allah ya shirya tsutsa da gari ya waye rana ta ɗaga. Tsutsar kuwa ta kawo hari ga 'yar itaciyar, ta cinye 'yar itaciyar, 'yar itaciyar kuma ta bushe. 8 Kashegari sa'ad da rana ta fito, Allah ya shirya wata iska daga gabas mai zafin gaske. Ranar kuwa, ta yi zafi matuƙa bisa Yona har ya some. Sai Yona ya gwammace ya mutu. Ya ce wa kansa, "Gara ma in mutu da in rayu." 9 Sai Allah yace wa Yona, "Ya dace da ka yi fushi game da 'yar'itaciyar? Sai Yona yace, "Ya dace da in yi fushi, har ma ga mutuwa." 10 Yahweh yace, "Ka ji tausayin 'yar itaciyar, wadda ba ka yi aiki a kai ba, ba ka kuma sa ta yi girma ba. 'Yar Itaciyar ta yi girma cikin dare ɗaya ta kuma mutu cikin dare ɗaya. 11 To ashe, Ni, ba zan tausayawa Nineba, wannan babban birni, wanda akwai fiye da mutane dubu ɗari da ashirin, da ba su san bambanci tsakanin hannunsu na dama da hannunsu na hagu ba, da kuma dabbobi masu yawan gaske?"

Littafin Mika
Littafin Mika
Sura 1

1 Wannan ita ce maganar Yahweh wadda ta zo wurin Mika, Bamorashtite a cikin kwanakin Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuda, abin da ya gani game da Samariya da Yerusalem. 2 Dukkan jama'a ku saurara, ke duniya ki saurara da dukan abin dake cikinki. Bari Ubangiji Yahweh ya zama shaida a kan ki daga haikalinsa mai tsarki. 3 Duba, Yahweh ya sauko daga kursiyinsa, zai bi ta wurare masu tudu a bisa ƙasa. 4 Duwatsu zasu narke a ƙarƙashinsa, kwarurruka kuma zasu farfashe kamar saƙar zuma a gaban wuta, kamar an zubar da ruwa a kan wuri mai tsauri. 5 Dukkan wannan saboda tawayen Yakubu ne, kuma saboda zunubin gidan Isra'ila ne. Mene ne dalilin tawayen Yakubu? Ba Samariya ba ce? Mene ne dalilin wurare masu tsawo na Yahuda? Ba Yerusalem ba ce? 6 "Zan maida Yahuda ta zama kamar kufai kawai kamar wurin dasa itatuwan inabi. Zan tura gininta na duwatsu cikin rami, zan kware harsasanta. 7 Za a farfasa sifofinta, dukkan kyaututtukanta za a ƙone su. Dukkan gumakanta zan rushe su. Gama daga wurin karuwancinta ta tattara su, zasu zama kamar abin da aka biya ta saboda karuwanci." 8 Domin wannan zan yi makoki in yi kuka, zan fita tsirara ba takalma; zan yi kuka kamar dila, zan yi makoki kamar mujiya. 9 Domin rauninta marar warkewa, domin ta zo Yahuda. Ta kawo ƙofar mutanena, wato Yerusalem. 10 Kada a yi maganar ta a Gat; kada a yi mata kuka. A Bet Lefra na yi birgima a ƙura. 11 Ki wuce ta mazaunan Shafir, a tsiraice cikin kunya. Mazauna Za'ana basu fito waje ba. Bet Ezel tana makoki saboda an ɗauke kariyarta. 12 Mutanen Marot suna da marmarin jin labari mai daɗi, saboda masifa daga Yahweh ta zo har ƙofofin Yerusalem. 13 Ku mutanen Lakish ku haɗa karusai na dawaki. Ke, Lakish, ke ce kika zama sanadin zunubin ɗiyar Sihiyona, saboda an sami kurakuran Isra'ila a cikinki. 14 To za ki bada kyauta ta ban kwana ga Morashet Gat; garin Akzib zai ba sarakunan Isra'ila kunya. 15 Zan sake kawo wanda zai mamaye ku, ku mazaunan Maresha, martabar Isra'ila zata dawo Adullam. 16 Ki aske kanki ki share gashinki saboda 'ya'yan da ki ke jin daɗin su. Ki sa kanki ya yi saiƙo kamar na gaggafa, domin 'ya'yanki za su tafi bauta daga wurinki.

Sura 2

1 Kaiton masu shirya mugunta, ga waɗanda ke shirya mugunta a kan gadajensu. Idan gari ya waye sukan aikata ta domin suna da iko. 2 Sukan yi sha'awar gonaki su kuma ƙwace su; sukan yi sha'awar gidaje su kuma ƙwace su. Suna tsanantawa mutum da gidansa, da kuma abin gãdonsa. 3 Saboda haka Yahweh yace, "Duba, na kusa kawo bala'i ga wannan kabila, wadda ba zaku cire kanku daga ciki ba. Ba zaku yi tafiya da taƙama ba, gama zaya zama mugun lokaci. 4 A wannan rana abokan gãbarku zasu rera waƙa game da ku, zasu yi makoki da makoki mai zafi. Zasu yi waƙa, 'Mu Isra'ilawa mun hallaka sarai, Yahweh ya canza gundumar mutanena.' Ya ya zaya ɗauke shi daga wurina? Ya bayar da filayanmu ga maciya amana!"' 5 Saboda haka, ku masu arziki baza ku sami zuriyar da za a raba gundumominku a cikin taruwar mutanen Yahweh ba. 6 "Sun ce, "kada ka yi anabci." "Ba zasu yi anabcin waɗannan abubuwa ba; reni ba zaya zo ba." 7 Ko lallai za a iya faɗin gidan Yakubu, "Ko Ruhun Yahweh ya ji haushi ne?" Ko waɗannan su ne ainihin ayyukansa?" Ko kalmomina ba su yi wani aikin kirki ga kowa ba ne? 8 A makare mutanena suka tashi kamar abokan gãba. Kun tuɓe sutura, da riga, daga masu wucewa ba tare da tsarguwa ba, kamar sojoji suna dawowa daga yaƙi zuwa wurin da suke tsammani lafiyayye ne. 9 Kun kori matan mutanena daga gidajen da suke jin daɗi, kun ɗauke albarkuna daga wurin 'ya'yansu har abada. 10 Tashi ka tafi, nan ba wurin da za ka iya zama ba ne, saboda rashin tsafta; hallakakke ne sarai. 11 Idan wani ya zo da ruhun ƙarya ya yi ƙarya ya ce, "Zan yi maka anabci a kan ruwan inabi da abin sa maye," zasu ɗauke shi annabi domin wannan jama'a. 12 Tabbas, zan tattara dukkan ku, Yakubu. Tabbas zan tattara sauran mutanen Isra'ila. Zan kawo su kamar garken tumaki a cikin tsakiyar wurin kiwonsu. Saboda yawan mutanen za a ji ƙara mai ƙarfi. 13 Wanda ya fara ɓalle ƙofa shi ne zai yi masu jagora. Sun ɓalle ƙofa sun fita; sarkinsu zai wuce gabansu. Yahweh zai kasance a gabansu.

Sura 3

1 Na ce, "Yanzu ku saurara, ku shugabannin Yakubu da masu mulki na gidan Isra'ila: Ashe ba dai-dai ba ne a gare ku ku fahimci adalci? 2 Ku da ke ƙin nagarta kuke kuma ƙaunar mugunta? Ku da ke yayyage fatarsu, da namansu daga ƙasusuwansu -- 3 ku da ke cin naman mutanena, kun yage fatarsu, kun kakkarya ƙashinsu, kun daddatsa su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya, kamar nama domin dafawa. 4 Sa'an nan ku shugabanni zaku yi kuka ga Yahweh, shi kuwa ba zai amsa maku ba. Zai ɓoye fuskarsa daga gare ku, da yake kun yi aikin mugunta. 5 Yahweh ya faɗi haka, "Game da annanbawan da suke ɓatar da mutanena, idan wani ya basu wani abu su ci, sukan yi shelar 'Salama'. Amma ga waɗanda ba su sa komi a bakinsu ba, sai su fara yaƙi da su. 6 Saboda haka zai zama duhu a gare ku, babu ruya domin ku, zai zama duhu sosai har da ba zaku yi duba ba. Rana za ta faɗi a kan annabawa, yini zai yi masu duhu. 7 Masu duba zasu ji kunya, masu sihiri zasu rikice. Dukansu zasu rufe leɓunansu, domin babu amsa daga gare ni." 8 Amma ni ina cike da iko ta wurin Ruhun Yahweh, kuma ina cike da adalci da ƙarfi, don in furtawa Yakubu kuskurensa, Isra'ila kuma zunubinsa. 9 Yanzu ku ji wannan, ku shugabanni na gidan Yakubu, da masu mulki na gidan Isra'ila, ku da ke ƙyamar adalci, kuna wulaƙanta kowanne abu mai kyau. 10 Kun gina Sihiyona da jini, Yerusalem kuma da mugunta. 11 Shugabanninku suna hukunci da cin hanci, firistocinku suna koyarwa don a biya su, kuma annabawanku suna dubã saboda kuɗi. Duk da haka kun dogara ga Yahweh kun ce, "Ba Yahweh yana tare da mu ba? Ba masifa da za ta same mu." 12 Domin haka, saboda ku za a huɗe Sihiyona kamar gona, Yerusalem za ta zama juji, tudun haikali zai zama tsaunin daji.

Sura 4

1 Amma zaya zama a rana ta ƙarshe dutsen gidan Yahweh zaya kafu a bisa sauran duwatsu. Zai ɗaukaka bisa sauran tuddai mutane kuma za su yi tururuwa wurinsa. 2 Al'ummai da yawa zasu ce, "Ku zo, mu je bisa dutsen Yahweh, zuwa gidan Allah na Yakubu. Zaya koya mana hanyoyinsa, kuma zamu yi tafiya cikin tafarkunsa." Gama daga Sihiyona shari'a zata fito, maganar Yahweh kuma daga Yerusalem. 3 Shi zaya hukunta tsakanin mutane da yawa, ya kuma yanke hukunci a kan mulkoki masu yawan gaske masu nisa kuma. Zasu maida takubbansu su zama garmuna mãsun su kuma su zama lauzuna. Wata al'umma baza ta ɗaga takobi gãba da wata al'umma ba, baza su ƙara koyar da yaƙi ba. 4 Maimakon haka kowanne mutum zai zauna ƙarƙashin kuringar inabinsa ko ƙarƙashin itacen ɓauransa. Ba wanda zai ƙara basu tsoro, gama bakin Yahweh mai runduna ne ya faɗi. 5 Gama dukkan mutane suna tafiya, kowanne ɗaya cikin sunan allahnsu. Amma mu zamu yi tafiya cikin sunan Yahweh Allahnmu har abada abadin 6 "A waccan ranar" - wannan furcin Yahweh ne - "Zan tattaro guragu da korarru, da waɗanda na tsanantawa. 7 Zan sa guragun su zama su ne saura, waɗanda a ka kora su zama al'umma mai ƙarfi, ni kuma Yahweh zan yi mulki a bisansu, a kan Dutsen Sihiyona daga yanzu da har abada. 8 Ke fa, hasumiya ta tsaron garke, tsaunin ɗiyar Sihiyona, mallakarki ta dã za ta dawo gare ki, da mulki na ɗiyar Yerusalem. 9 Yanzu, me yasa kuke ihu da ƙarfi haka? Babu sarki a cikinku ne? Mai shawararku ya mutu ne? Wannan shi ne yasa ciwo ya kama ku kamar mace mai naƙuda? 10 Ki zama da ciwo da naƙuda ta haifuwa, ke ɗiyar Sihiyona, kamar mace mai naƙuda. Gama yanzu ke zaki fita waje daga birnin, ki zauna a waje, kuma ki tafi Babila. A can za a kuɓutar da ke. A can Yahweh zaya kuɓutar da ke daga hannun abokan gãbarki. 11 Yanzu al'ummai da yawa sun taru gãba da ke; sun ce, 'Bari ta ƙazance; bari idanunmu su yi murna a kan Sihiyona' 12 Basu san tunanin Yahweh ba, basu gane shirye-shiryansa ba, gama ya tara su kamar dammai a masussuka. 13 Tashi ki yi shiƙa ɗiyar Sihiyona, gama zan maida ƙahonki ya zama ƙarfe, kofatanki kuma su zama jan ƙarfe. Zaku hallaka mutane da yawa kuma zaku miƙa dukiyarsu ta zilama ta zama ta Yahweh, mallakarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya."

Sura 5

1 Yanzu ku taru da shirin yaƙi, ɗiyan sojoji; sojoji sun yi sansani sun kewaye birni, zasu bugi alƙalin Isra'ila da sanda a kunci. 2 Amma ke Betlehem Ba'ifrata, ko da yake ke ƙanƙanuwa ce a cikin dangi Yahuda, wani daga cikinki zaya zo gare ni ya yi mulkin Isra'ila, wanda farkonsa tun daga lokacin dã ne, tun daga can farko. 3 Saboda haka zaya bashe su, har sai wadda ta ke naƙuda ta haifi ɗa, kuma sauran 'yan'uwansa su dawo wurin mutanen Isra'ila. 4 Zaya tashi ya yi kiwon mutanensa cikin ƙarfin Yahweh, a cikin darajar sunan Yahweh Allahnsa. Zasu kasance, sa'annan shi zaya zama babba har iyakar duniya. 5 Zaya zama salamarmu. Sa'ad da Asiriyawa suka shigo cikin ƙasarmu, sa'ad da suka yi gangami gãba da kagarunmu, sa'an nan zamu tashi gãba da su, makiyaya bakwai da shugabanni takwas a kan mutane. 6 Zasu kiwaci ƙasar Asiriya da takobi, ƙasar Nimrod kuma a cikin ƙofofinta. Zaya kuɓutar da mu daga Asiriyawa, sa'ad da suka shiga cikin ƙasarmu, sa'ad da suka yi gangami cikin iyakokinmu. 7 Waɗanda suka rage na wajen Yakubu zasu zama cikin tsakiyar mutane da yawa, kamar raɓa daga wurin Yahweh, kamar ruwa a kan ciyawa, wadda ba mutum take jira ba, ba kuma 'ya'yan mutane take jira ba. 8 Waɗanda suka rage na wajen Yakubu zasu zama a cikin al'ummai, cikin mutane da yawa, kamar zãki a cikin namomin jeji masu yawa, kamar ɗan zaki a cikin garken tumaki. Sa'ad da ya shiga cikinsu zai tattaka su, ya daddatsa su, ba wanda zaya cece su. 9 Za a ɗaga hannunka gãba da abokan gãbarka, zaya kuma hallaka su. 10 "Haka zaya kasance a wannan rana" - wannan furcin Yahweh ne -- "zan hallakar da dawakanka a gabanka in narkar da karusanka. 11 Zan hallakar da biranen ƙasarka in lalatar da wuraren ɓoyewarka dukka. 12 Zan hallakar da maita da ke wurinka, baza ka ƙara samun masu duba ba. 13 Zan hallakar da sassaƙaƙƙun sifofinka da ginshiƙai na duwatsu daga wurinka. Baza ka ƙara bautawa aikin hannuwanka ba. 14 Zan tumɓuke ginshiƙan Asherarka daga wurinka, kuma in hallakar da biranenka. 15 Zan ɗauki fansa cikin fushi da hasala a kan al'umman da basu saurara ba."

Sura 6

1 Yanzu ji abin da Yahweh ya faɗi, "Ka tashi ka kai ƙararka ga duwatsu; bari tsaunuka su ji muryarka. 2 Ku ji ƙarar Yahweh, ku duwatsu, da ku ginshiƙan duniya masu juriya. Gama Yahweh yana da shari'a da mutanensa, zai yi faɗa da Isra'ila a kotu." 3 Mutanena, me na yi ma ku? Ta yaya na gajiyar da ku? Ku faɗi laifin da na yi! 4 Gama na fito da ku daga ƙasar Masar na kuɓutar da ku daga gidan bauta. Na aiki Musa da Haruna da Miriyam zuwa wurinku. 5 Mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla, da yadda Bala'am ɗan Biyo ya amsa masa sa'ad da kuke tafiya daga Shittim zuwa Gilgal, ta haka za ku san aikin adalci na Yahweh." 6 Me zan kawo gaban Yahweh, sa'ad da na durƙusa gaban Allah mai girma? Na zo da hadayu na ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya? 7 Yahweh zai yi murna da dubban raguna, ko da dubban rafukan mai? Zan ba da ɗan farina saboda laifina, ɗiyan jikina domin zunubina? 8 Ya dai gaya maka, mutum, abin da ke mai kyau, abin da Yahweh ke nema daga wurinka: Aikin adalci, jinƙai da tafiya cikin tawali'u tare da Allahnka. 9 Yahweh, yana yin furci da muryarsa zuwa ga birnin - ko yanzu hikima ta san sunanka: "Ku saurari sandar, da wanda ya ajiye ta a wurin. 10 Akwai dukiya a gidajen masu mugunta wannan rashin aminci ne, mudun ƙarya abin ƙyama. 11 Ko zan lura da mutumin daya yi amfani da ma'auni mara kyau, da bahu wanda nauyinsa na cuta ne? 12 Masu arziki sun zama cike da ta'addanci, mazaunan sun faɗi ƙarairayi, kuma harshensu da bakinsu na cike da ruɗi. 13 Saboda haka na buge ku da ciwo mai zafi, na mai da ku kango saboda zunubanku. 14 Za ku ci ba za ku ƙoshi ba, yunwarku za ta zauna a cikinku, za ku ajiye kayayyaki amma ba za ku adana su ba, abin da kuka adana zan bayar ga takobi. 15 Za ku yi shuka amma ba za ku yi girbi ba; za ku sawo zaitun amma ba za ku shafe kanku da mai ba; za ku matse kuringar inabi amma ba za ku sha ruwan ba. 16 Farillan da Omri ya bayar an kiyaye su, haka kuma dukkan abin da gidan Ahab suka yi. Kun yi tafiya bisa ga shawararsu. To haka zan mai da birnin kango, mazauna ciki kuma abin ƙi, ku mazaunan za ku yi ta fama da ba'a a matsayinku na mutanena."

Sura 7

1 Kaito na! Gama a gare ni ya zama kamar an riga an gama girbi na kaka, har ma da kalar abin da ya rage na kuringar inabi a gonaki: Ba sauran 'ya'yan itatuwan da za a samu, babu nunar fari na 'ya'yan ɓaure waɗanda rai na ke so. 2 Babu sauran amintattun mutane a ƙasar, babu sauran na kirki a cikin dukkan 'yan adam. Dukkan su sun yi kwanto domin su zãbar da jini, kowanne ɗayansu yana farautar ɗan'uwansa da tãru. 3 Hannayensu sun iya yin ɓarna sosai: sarki yana nema a ba shi kuɗi, alƙali yana shirye ya karɓi cin hanci, ƙaƙƙarfan mutum yana gaya wa waɗansu abin da yake so ya samu. Haka suke rigima tare. 4 Mafi kyau a cikinsu kamar laka yake, mafi aminci a cikinsu yana kamar shingen ƙaya. Dãma masu tsaronmu sun yi magana a kan wannan rana, ranar da za a hore ku. Ranar ruɗewarsu ta zo. 5 Kada ka amince da kowanne maƙwabci, kada ka dogara ga kowanne aboki. Ka yi hankali da abin da za ka faɗi ko ma ga matar da ke kwance a kafaɗunka. 6 Gama ɗa yana rena ubansa, ɗiya kuma tana tayarwa uwatta, suruka tana tayarwa uwar mijinta. Abokan gabar mutum, mutanen gidansa ne. 7 Amma ni zan duba wajen Yahweh, zan jira ga Allah na cetona, Allahna zai ji ni. 8 Kada ka yi murna a kaina kai maƙiyina, ko na faɗi zan tashi. Sa'ad da na zauna cikin duhu, Yahweh zai zama haske a gare ni. 9 Saboda na yi wa Yahweh zunubi, zan jure da fushinsa har yayi mani shari'a, yayi mani hukunci. Zai kawo ni cikin haske, zan gan shi yana kuɓutar da ni cikin adalcinsa. 10 Sa'an nan maƙiyina zai gani, kunya za ta rufe wanda yake ce da ni, "Ina Yahweh Allahnka?" Idanuna zasu gan ta, za a tattake ta kamar taɓo a kan hanyoyi. 11 Ranar da za ka gina ganuwarka tana zuwa; a ranar nan za a faɗaɗa iyakokinka da nisa ƙwarai. 12 A ranar nan mutanenka zasu zo wurinka daga Asiriya da biranen Masar, daga Masar har zuwa babban Kogi, daga teku zuwa teku, daga dutse zuwa dutse. 13 Waɗancan ƙasashen za a watsar da su saboda mutanen da ke zaune, a wurin yanzu, saboda sakamakon ayyukansu. 14 Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garke abin gãdonka. Suna zaune su kaɗai a jeji, a tsakiyar fadama. Bari su yi kiwo a Bashan da Giliyad kamar kwanakin dã. 15 Kamar rana da ka fito daga kasar Masar, zan basu mamaki. 16 Al'ummai zasu gani su ji kunya a kan dukkan ikonsu. Zasu sa hannuwansu a bakinsu, kunnuwansu zasu toshe. 17 Zasu lashi ƙasa kamar macizai, kamar hallittun dake rarrafe a ƙasa. Zasu fito daga cikin kogunansu da tsoro, zasu zo wurinka da tsoro, Yahweh Allahnmu, kuma za su ji tsoro saboda kai. 18 Wane ne Allah kamar ka, kai da kake ɗauke zunubi, wanda yake ƙetare kurakuran mutanensa da suka rage, abin gãdonsa? Ba ka riƙe fushinka har abada, saboda kana ƙaunar ka nuna mana amincin alƙawarinka. 19 Za ka sake jin tausayinmu, kuma; za ka take muguntarmu a ƙarƙashin sawayenka. Za ka jefa dukkan zunubanmu cikin zurfin teku. 20 Za ka bada gaskiya ga Yakubu alƙawari da aminci kuma ga Ibrahim, kamar yadda ka rantsewa kakanninmu tun kwanakin dã.

Littafin Nahum
Littafin Nahum
Sura 1

1 Furci game da Nineba. Littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh. 2 Yahweh Allah Mai kishi ne da sakayya; Yahweh mai sakayya ne da fushi mai zafi; Yahweh na ɗaukar fansa a kan abokan gãbarsa, kuma yana ci gaba da fushinsa a bisa maƙiyansa. 3 Yahweh na da jinkirin fushi da iko mai girma; ba zai ƙyale miyagu ba hukunci ba. Yahweh na shirya hanyarsa a cikin guguwa da hadari, gizagizai kuma ya maishe su ƙurar tafin sawayensa. 4 Yana tsauta wa teku ya kuma busar da ita; ya busar da dukkan koguna. Bashan ta yi rauni, haka kuma Karmel; furannin Lebanon sun yi yaushi. 5 Duwatsu suna girgiza a gabansa, tuddai kuma suna na narkewa; duniya tana rushewa a gabansa, hakika, dukkan duniya da mazaunanta. 6 Wane ne zai iya tsayawa a gaban hasalarsa? Wane ne zai iya tsayayya da zafin fushinsa? Hasalarsa na zubowa kamar wuta, kuma yana farfasa duwatsu. 7 Yahweh nagari ne, mafaka ne mai ƙarfi a ranar masifa; mai aminci ne kuma ga dukkan masu fakewa a cikinsa. 8 Amma zai hallakar da maƙiyansa kakaf da babbar ambaliya; zai kora su can cikin duhu. 9 Ku mutane mene ne ku ke shiryawa gãba da Yahweh? Zai kawo ƙarshensa dukka; Masifa ba za ta sake tasowa karo na biyu ba. 10 Gama zasu zama a harɗe kamar sarƙaƙiya; abin shansu zai gundure su; wuta zata cinye su sarai kamar busasshiyar ciyawa. 11 Wani ya tashi daga cikin ki, Nineba, wanda ya yi shirin mugunta game da Yahweh, wani wanda ya haɓaka aikin mugunta. 12 Ga abin da Yahweh ya faɗi, "Ko da suna cike da ƙarfinsu da kuma yawansu, duk da haka za a datse su; jama'arsu za su ƙare sarai. Amma kai, Yahuda; ko da ya ke na wahalshe ka, ba zan ƙara wahalsheka ba. 13 Yanzu zan karya karkiyar mutanen nan daga gare ka; Zan tsinke sarƙoƙinka." 14 Nineba, Yahweh ya ba da umarni game da ke; "Babu wata sauran zuriyar da za a kira ta da sunanki. Zan datse sassaƙaƙƙun gumaka da kuma gumakan ƙarfe daga gidajen allolinki. Zan haƙa kaburburanki, gama ke abin raini ce." 15 Duba, a bisa duwatsu, akwai sawayen wani mai kawo labarai masu daɗi, wanda ya ke shelar salama! Yahuda, yi murnar bukukuwanka, ka kuma cika wa'adodinka, gama mugu ba zai ƙara mamaye ka ba, don an datse shi sarai.

Sura 2

1 Shi wanda zai daddatsa ku yana zuwa gãba da ku. Ku tsare ganuwar birnin, ku yi tsaron hanyoyi. Ku ƙarfafa kan ku, ku shirya sojojinku. 2 Don Yahweh zai dawo da darajar Yakubu, kamar darajar Isra'ila, ko da ya ke maharan sun washe su sun kuma ɓaɓɓata rassan kuringar inabinsu. 3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, kuma sojojinsa sun sa jajayen tufafi, ƙarafan karusansu na walƙiya tun ranar da a ka shirya su, kuma suna karkaɗa mãsunsu masu ƙotar katako a iska 4 Karusai na ta yin gudu a tituna suna kai wa suna kawowa a manyan tituna. Suna kama da harsunan wuta, kuma suna gudu kamar walƙiya. 5 Wanda zai daddatsa ku gutsu-gutsu ya kira jarumawansa, cikin tafiyarsu suna cin karo da juna, su na sauri don su kawo hari a kan ganuwar birnin. An shirya babbar garkuwa don ta kare masu kawo hari. 6 An buɗe ƙofofin bakin koguna ta ƙarfi da yaji, fadar kuma ta zama kufai. 7 An tuɓe wa Huzzab tufafinta an kuma tafi da ita; bayinta mata suna makoki kamar kurciyoyi, suna bugun ƙirjinsu. 8 Nineba ta zama kamar tafki mai maguda, tare da mutanenta suna gudu kamar ruwa mai kwarara. Waɗansu na ihu "ku tsaya, ku tsaya", amma ba wanda ya waiga baya. 9 Ku ɗauki ganimar azurfa, ƙu ɗauki ganimar zinariya don bata da iyaka, kan dukkan abubuwa kyawawa masu daraja na Nineba. 10 Nineba ta zama kango da kufai. Zuciyar kowa ta karaya, gwiwoyin kowa na gugar juna, kowa na cikin baƙinciki; fuskokinsu sun yanƙwane. 11 Yanzu kuma ina kógon zakokin, inda ake ciyar da 'ya'yan zăki, wurin da zãki da zãkanya ke tafiya da 'ya'yansu ba su tsoron komai? 12 Zãki ya yayyaga abin da ya kama don 'ya'yansa, ya murɗe abin da ya kamo wa zãkanyarsa, ya cika kógonsa da waɗanda ya kamo, ya cika raminsa da yagaggen mushen waɗanda ya yayyaga. 13 "Duba, ina gãba da ku - wannan furcin Yahweh mai runduna ne. Zan ƙone karusanku, a cikin hayaƙi, takobi kuma zai cinye ƙananan zakunanku. Zan datse ganima daga ƙasarku, kuma ba za a ƙara jin muryoyin masu kawo saƙonku ba."

Sura 3

1 Kaiton birni wanda ke cike da jini! Wanda ke cike da ƙarairayi da kayan sata; a kullum waɗanda aka ƙwara suna cikinsa. 2 Ƙarar bulala na cikinsa, da ƙarar karusan yaƙi da haniniyar dawakai da sukuwar karusai. 3 Akwai mahayan dawakai masu kawo hari, da walƙiyar takubba da ƙyallin mãsu da tarin gawaye da tsibin jukkuna. Gawarwaki ba su da iyaka; maharan sun yi tuntuɓe a kan su. 4 Wannan na faruwa ne saboda mummunar sha'awa ta ayyuka kyakkyawar karuwar, ƙwararriya a maita, mai sayar da al'ummai ta wurin karuwancinta, ta wurin ta kuma mutane na aikata maitanci. 5 "Duba, ina gãba da ke - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - Zan kware zanen ki in sa ki zama tsirara a gaban al'ummai, ki zama abin kunya ga masarautu. 6 Zan kawo ƙazanta a kan ki, in sa ki zama abin reni; zan mayar dake abin kallo. 7 Zai zama dukkan wanda ya dube ki zai koma da baya, ya ce 'Nineba ta rushe; wa zai yi kuka domin ta?' Ina zan sami wanda zai yi maki ta'aziya?" 8 Nineba, kin fi Tebes ne wadda aka gina ta kusa da Kogin Nilu, wadda ruwaye ke kewaye da ita, wadda kariyarta teku ne, wadda teku ta yi mata dajiya? 9 Kush da Masar ne ƙarfinta, kuma ba shi da iyaka; Fut da Libiya suka yi amana da ita. 10 Duk da haka an kwashe Tebes, ta tafi bauta; an fyaɗa 'ya'yanta a ƙasa a kan hanyoyi, abokan gabarta sun jefa ƙuru'u a kan manyan mutanenta, kuma an ɗaure ƙarfafan mutanenta da sarƙoƙi. 11 Ke ma za ki bugu, za ki yi ƙoƙarin ɓoyewa ki nemi mafaka daga abokan gãbarki. 12 Dukkan hasumiyoyinki zasu zama kamar itacen ɓauren da yake da 'ya'yan fari: idan an girjiza su, zasu faɗo a bakin mai cinyewa. 13 Duba, mutanen dake tare dake mata ne; ƙofofinki suna bude ga abokan gãbarki; wuta ta cinye makaranki. 14 Ki je ki ɗebo ruwa domin za a kewaye ki, ki ƙarawa kagarorinki ƙarfi, ki je wurin magina ki samo yunɓu ki yi tubula. 15 Wuta zata same ki a wurin, takobi zai hallaka ki. Zai cinye ki kamar yadda fãra ta kan cinye komi da komi. Ki maida kanki kamar 'ya'yan fãra, ki yi yawa kamar fãrin da suka yi ƙwari sosai. 16 Kin riɓanya abokan cinikayyarki da yawa kamar taurarin sammai; amma suna kamar 'ya'yan fãri sukan washe ƙasa su tashi. 17 'Ya'yan sarakunanki suna da yawa kamar fãrin da suka yi girma sosai, jarumawanki kuma na kamar fãrin da suka yi cincirindo a bango lokacin sanyi. Amma idan rana ta yi sai su tashi su tafi wurin da ba'a sani ba. 18 Sarkin Asiriya, masu tsaronka sun yi barci; masu mulkinka sun kwanta suna hutawa. Mutanenka sun warwatsu a kan duwatsu ba wanda za ya tattarosu. 19 Raunukanka ba zasu warke ba. Raunukanka sun yi zafi sosai. Dukkan wanda ya ji labarinka zai tafa hannu domin murna a kanka. Wane ne ya tserewa muguntarka ta ko yaushe?

Littafin Habakuk
Littafin Habakuk
Sura 1

1 Saƙon da annabi Habakuk ya karɓa, 2 "Yahweh, har yaushe zan yi kukan neman taimako, ba za ka ji ni ba? Na yi kuka gareka cikin 'husuma'! amma ba za ka cece ni ba. 3 Donme kake bari na in kalli mugunta, in kuma dubi rashin gaskiya? Hallaka da tashin hankali na gabana; akwai jayayya, kuma gardama ta taso. 4 Saboda haka shari'a ta yi rauni, adalci kuma bai ɗore ba ko da na ɗan lokaci. Domin muguye sun kewaye masu adalci; shi yasa shari'a ta karkace." Yahweh ya amsa wa Habakuk. 5 Ka dubi al'ummai ka bincike su; ka yi mamaki da al'ajibi! Domin lallai na kusa in yi wani abu a kwanakin ka da ba za ka gaskata ba idan an faɗa maka. 6 Ka duba! Na kusa ta da Kaldiyawa - waɗannan al'ummai - masu zafin rai da kuma garaje - zasu ratsa dukkan faɗin ƙasar, su ƙwace wurare da ba nasu ba. 7 Masu ban razana ne da kuma ban tsoro; hukunci da darajassu daga gare su suke fitowa. 8 Dawakansu sun fi damisa gudu, sun fi kyarketan maraice sauri. Dawakan su su na tattakawa, mahayansu sun zo daga nesa sosai - Su kan tashi kamar gaggafar da ke niyyar ci. 9 Duk sun zo domin husuma; rundunarsu sukan tafi kamar iskar hamada, sukan tara bayi kamar yashi. 10 Suna yi wa sarakuna ba'a, masu mulki kuma abin ba'a ne a gare su. Suna ma duk kagara dariya, domin sukan tula ƙasa su hau su washe su. 11 Sa'an nan iska za ta buga mugayen mutane ta wuce da sauri, waɗanda ƙarfinsu allahnsu ne." Habakuk ya sake tambayar Yahweh 12 "Kai ba tun fil'azal ka ke ba, Yahweh Allahna, Mai Tsarkin nan? Ba za mu mutu ba. Yahweh ya ƙaddara su ga hukunci, kai kuma, Dutse, ka kafa su domin gyara. 13 Idanuwanka masu tsarki ne ba za su duba mugunta ba, ba za ka kuma dubi mugun aiki da tagomashi ba; to don me kake duban masu cin amana da tagomashi? Don me ka yi shuru sa'ad da mugaye suke haɗiye waɗanda suka fi su adalci? 14 Ka maida mutane kamar kifi a teku, kamar abubuwa masu rarrafe da basu da shugaba. 15 Ya kan kawo su dukka da ƙugiyar kamun kifi; yakan ja mutane a tarun kifi su tara su a tãrunsu. Wannan ne ya sa suke murna suna sowa mai yawa. 16 Shi ya sa suke miƙa hadayu ga tarun kama kifinsu suna ƙona wa tarunsu turare, domin dabbobi masu ƙiba ne rabonsu, nama mai kitse ne abincinsu. 17 Saboda wannan ne zasu juye tarun kama kifinsu su ci gaba da yanka al'ummai, ba jin tausayi?"

Sura 2

1 Zan tsaya wurin tsarona in kuma tsaya kan hasumiya, in duba da kyau in ji abin da dai zai faɗi mani da yadda zan amsa masa game da ƙarata. 2 Yahweh ya amsa mani ya ce, "Ka rubuta wannan ruyar, ka rubuta ta da kyau a kan alluna domin duk wanda ke karanta su ya gudu. 3 Domin ruyar lokacinta ya na gaba a ƙarshe lallai za ta cika ba zata fasa ba. Ko da ta yi jinkiri, ku jira. Tabbas zata zo ba za ta yi jinkiri ba. 4 Duba! Shi wanda sha'awace sha'awacensa ba dai-dai suke a cikinsa ba hurarra ne. Amma adali ta wurin bangaskiyarsa zai rayu. 5 Gama ruwan inabi abin yaudara ne ga mutum mai fahariya domin kada ya kiyaye, amma ya yawaita marmarinsa, kamar kabari, kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi. Ya kuma tattara wa kansa kowacce ƙasa ya kuma tattaro wa kansa dukkan mutane. 6 Ashe ko waɗannan ba zasu sa a ƙirƙiro masa maganganun reni da waƙa da zanbo suna cewa, 'Kaiton wanda yake ƙarawa kansa abin da ba nasa ba! Har yaushe zaka yi ta ƙara wa kanka nauyin al'ƙawuran da ka ɗauka?' 7 Masu cizonka ba zasu tashi farad ɗaya ba, su da ke tsoratar da kai sun farka? Za ka zama ganima a gare su. 8 Saboda ka washe mutane da yawa, dukkan sauran al'ummai za su washe ka. Saboda ka zubar da jinin mutane tare da tashin hankali a ƙasa, da birane da duk waɗanda ke zaune a cikinsu. 9 'Kaitonsa mai cin ƙazamar riba domin gidansa, yakan gina sheƙarsa a sama domin ya tsare kansa daga hanun mugunta.' 10 Ka jawo wa gidanka kunya ta wurin dạtse mutane da yawa, ka kuma yi wa kanka zunubi. 11 Gama daga cikin katanga duwatsu zasu tada murya, katako kuma daga cikin itatuwan jinka zai amsa masu, 12 'Kaiton wanda ya gina birni da jini, da wanda ya kafa gari da mugunta.' 13 Ashe ba daga Yahweh mai runduna ba ne mutane ke wahala domin su sami wuta, sauran ƙasashe kuma suna gajiyar da kansu domin abin wofi? 14 Har yanzu ƙasar zata cika da sanin darajar ɗaukakar Yahweh, kamar yadda ruwaye ke rufe teku. 15 'Kaiton wanda ke tilasta maƙwabcinsa ya sha, ka na nuna fushinka, kana kuwa sa su bugu, domin ka dubi tsiraicinsu.' 16 Maimakon ɗaukaka za ka cika da kunya. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha zaka kuma bayyana tsiraicinka. Ƙoƙon hannun dama na Yahweh zai juyo gare ka, kunya kuma zata rufe darajarka. 17 Tashin hankalin da aka yi wa Lebanon zai komo maka, hallakar dabbobi kuma zata tsoratar da kai. Domin ka zubar da jinin mutane, ka aikata tashin hankali gãba da ƙasa, da birane, da waɗanda ke zaune a cikinsu. 18 Ina amfanin sassaƙaƙƙiyar siffa a gare ka? Ko gare shi wanda ya sassaƙa ta, gunki na zubi, mai koyar da ƙarairayi; gama ya na sa dogararsa ga aikin hannuwansa sa'ad da ya ke yin waɗannan alloli bebaye. 19 'Kaiton wanda ke ce wa itace, 'Ka farka!' Ko ya ce wa beben dutse, 'Ka tashi!' Waɗannan abubuwa suna koyarwa ne? Duba, an dalaye su da zinariya da azurfa amma ba numfashi ko kaɗan a cikinsa. 20 Amma Yahweh yana cikin haikalinsa mai-tsarki! Ku yi shiru dukkan ƙasa a gabansa."

Sura 3

1 Addu'ar annabi Habakuk a waƙance: 2 Yahweh na ji labarinka, kuma na tsorata. Yahweh, ka farfaɗo da aikinka a cikin waɗannan lokatai; a cikin waɗannan lokatai ka bayyana shi; ka tuna da yin tausayi cikin fushinka. 3 Allah ya zo daga Teman, kuma Mai Tsarki daga Dutsen Faran. Selah. Ɗaukakarsa ta rufe sammai, kuma duniya na cike da yabonsa. 4 Sheƙi biyu na hannunsa na haskakawa kamar walƙiya, inda ƙarfinsa yake a ɓoye. 5 Cuta mai hallakarwa ta tafi a gabansa, annoba kuma ta biyo sawunsa. 6 Ya tsaya ya auna duniya; ya duba kuma ya girgiza al'ummai. Harma daɗaɗɗun duwatsu suka rugurguje, madawwaman tsaunuka kuma suka rusuna ƙasa. Tafarkinsa madawwami ne. 7 Na ga runfunan Kushan cikin ƙunci, kuma bargunan runfunan cikin ƙasar Midiyan suna raurawa. 8 Yahweh ya fusata da kogunan ne? fushinka a kan kogunan ne, ko hasalarka kan teku ne, da ka yi sukuwa bisa dawakanka da karusanka masu nasara? 9 Kã fito da bãkanka a ɗane; kạ sa kibiyoyinka ga băkanka! Selah. Kạ raba duniya da koguna. 10 Duwatsu sun gan ka sun murɗe cikin zafi. Ambaliyar ruwa ta bi ta kansu; Teku mai zurfi ya yi ruri. Ya yi tsalle da raƙuman ruwansa. 11 Rana da wata suka tsaya cik can sama wurarensu masu nisa suka gudu daga hasken kibiyoyinka, daga kuma hasken walƙiyar sheƙin mashinka. 12 Ka tattaka duniya da zafin fushi. A cikin fushi ka sussuke al'ummai. 13 Ka fita domin ceton mutanenka, domin ceton zaɓaɓɓenka. Ka rugurguza kan gidan mai mugunta domin a kware shi daga ƙasa har zuwa wuyansa. Selah. 14 Da kibiyoyinsa ka soke kan mayaƙansa tun da sun taho kamar hadari domin su watsar da mu, marmarinsu kamar masu lanƙwame matalauta a ɓoyayyen wuri ne. 15 Ka yi tafiya zuwa ƙetaren teku da dawakanka, ka kuma tattara manyan ruwaye. 16 Na ji, kuma can cikin gaɓoɓina na yi rawar jiki! Da jin ƙarar leɓunana sun girgiza. Ruɓewa ta shigo cikin ƙasusuwana, a cikina ina rawar jiki yayin da nake jira shiru domin ranar ƙunci da zata zo a kan mutanen da suka mamayemu. 17 Koda itacen ɓaure bai yi toho ba kuma inabi bai ba da 'ya'ya ba; kuma itacen zaitun bai ba da amfani mai kyau ba kuma gonaki basu ba da abinci ba; koda a ce garke ya tsinke babu shanu a maɗauri, ga abin da zan yi. 18 Duk da haka, zan yi farinciki cikin Yahweh. Zan cika da murna saboda Allahn cetona. 19 Ubangiji Yahweh shi ne ƙarfina ya kuma maida sawayena kamar na barewa. Yana sa in tafi gaba bisa wurarena na ɗaukaka. - Ga shugaban mawaƙa, bisa kayan kaɗe-kaɗena masu tsarkiya.

Littafin Zafaniya
Littafin Zafaniya
Sura 1

1 Wannan maganar Yahweh ce da ta zo ga Zafaniya ɗan Kushi ɗan Gedaliya ɗan Amariya ɗan Hezekiya, a kwanakin Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda. 2 "Zan hallakar da kome da kome daga doron duniya - wannan furcin Yahweh ne. 3 Zan hallakar da mutum da dabba; Zan hallakar da tsuntsayen sammai da kuma kifayen teku, rusasssun wurare tare da miyagu. Domin zan datse mutum daga sararin duniya - wannan furcin Yahweh ne. 4 Zan miƙa hannuna kan Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem. Zan datse kowanne ragowar Ba'al daga wannan wurin da kuma sunayen masu bautar gumaka daga cikin firistoci, 5 mutanen da a saman gidaje suke bautawa hallitun sammai, da mutanen da ke sujada da rantsuwa ga Yahweh amma kuma suna rantsuwa ta wurin sarkinsu. 6 Zan kuma datse waɗanda suka juye baya daga bin Yahweh, waɗanda basu neman Yahweh basu kuma neman bishewarsa." 7 Ku yi shiru a gaban Ubangiji Yahweh! Gama ranar Yahweh ta kusato; Yahweh ya shirya hadaya ya kuma keɓe baƙinsa. 8 "Zai zama kuma a ranar hadayar Yahweh, zan hori hakimai da 'ya'yan sarakuna, da duk wanda ke sanye da baƙin tufafi. 9 A ranan nan zan hukunta masu tsallake dankarin ƙofa, masu cika gidan shugabansu da ta'addanci da yaudara. 10 Haka zai zama a ranar nan - wannan furcin Yahweh ne - lallai za a ji kukan baƙinciki daga Kofar Kifi, da ƙarar kuka daga Gundumar Biyu, da gagarumar ƙarar farfashewa daga tuddai. 11 Kuyi kuka da ƙarfi, ku mazaunan Gundumar Kasuwa, gama za a rugurguje dukkan fatake; za a datse dukkan masu awon azurfa. 12 Zai zama a gabatowar lokacin nan ne zan binciki Yerusalem da fitilu in kuma hukunta mutanen da suka kafu a kan ruwan inabinsu suka ce a zuciyarsu, 'Yahweh ba zai yi kome ba, ko nagari ko mugu.' 13 Dukiyarsu zata zama ganima, kuma gidajensu za a maida su kufai da aka yi watsi da shi! Zasu gina gidaje amma baza su zauna a cikinsu ba, zasu dasa gargunan inabi amma baza su sha ruwansu ba. 14 Babbar ranar Yahweh ta yi kusa, tayi kuma kurkusa da sauri! ‌Ƙarar ranar Yahweh zata zama kukan mayaƙi na ɓacin rai! 15 Ranar nan zata zama ranar tsananin fushi, ranar damuwa da baƙinciki, ranar baƙin hadari da rushewa, ranar duhu da baƙin ƙunci, ranar giza-gizai da baƙin duhu. 16 Zata zama ranar hura kakaoki da ƙararrawa gãba da ƙayatattun birane masu manya manyan wuraren ɓuya da ganuwoyi. 17 Gama zan kawo ƙunci ga mutane, saboda suyi tafiya kamar makafin mutane tunda sun yiwa Yahweh zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, a kuma cire kayan cikinsu kamar kashin dabba. 18 A ranar hasalar Yahweh zinariyarsu ko azurfarsu ba zasu iya kuɓutar dasu ba. A cikin wutar kishinsa dukkan duniya zata hallaka, gama zai kawo cikakken mummunan ƙarshen dukkan mazaunan duniya."

Sura 2

1 Ku jero kanku tare ku taru, al'umma marar kunya - 2 kafin ranar aiwatar da dokokin kuma waccan ranar ta wuce kamar ƙaiƙayi, kafin zafin fushin hasalar Yahweh ta auko muku, kafin ranar hasalar Yahweh ta zo kanku. 3 Ku nemi Yahweh, ku mutane masu tawali'u da biyayya ga dokokinsa! ku nemi adalci Ku nemi tawali'u, ko wataƙila a yi maku kariya a ranar hasalar Yahweh. 4 Gama za a yashe da Gaza, kuma Ashkelon zata zama rusasshiya. Zasu kori Ashdod da rana, kuma zasu tunɓuke Ekron! 5 Kaiton mazaunan gaɓar teku, al'ummar Kiritiyawa! Yahweh ya yi magana gãba da ku, Kan'ana, ƙasar Filistiyawa. Zan hallakar dake har sai ba mazaunan da suka ragu. 6 Yankin gaɓar teku zai zama saurar makiyaya da makwantar dabbobi. Yankin gaɓar zai zama na ragowar mutanen gidan Yahuda, waɗanda zasu yi kiwon garkensu a wurin. 7 Da yamma mutanensu zasu kwanta a gidajen Ashkelon, gama Yahweh Allahnsu zai lura da su ya kuma mayar masu da mallakarsu. 8 Na ji cakunar Mowab da wulaƙancin mutanen Amon sa'ad da suke cakunar mutanena suna ci masu kan iyaka. 9 Don haka na rantse da kaina - wannan ne furcin Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, - Mowab zai zama kamar Saduma, mutanen Amon kuma kamar Gomora; wurin ciyayi masu dafi da ramin gishiri da aka yi watsi da shi har abada. Amma ragowar mutanena zasu washe su, ragowar al'ummata kuma zasu mallake su." 10 Wannan zai faru da Mowab da Amon saboda girman kansu, tunda suka cakuni suka kuma yi ba'a ga mutanen Yahweh mai runduna. 11 Sa'an nan zasu ji tsoron Yahweh, don zai cakuni dukkan allolin duniya. Kowannensu zai yi masa sujada, kowanne daga wurinsa, daga kowacce gaɓar teku. 12 Ku Kushiyawa kuma za a soke ku da takobina, 13 Hannun Allah kuma zai kawo hari ga arewa ya hallaka Asiriya, don Nineba zata zama rusasshen wurin da aka watsar, busshiya kuma kamar hamada. 14 Sai garkuna su kasance kwance a nan, kowacce dabba ta kowacce al'umma, mujiyar hamada da mujiya mai tsuwwa ma zasu huta a samman ginshiƙanta. Za a yi waƙoƙin kira daga tagogi; Juji zai kasance a bakin ƙofofin; sassaƙaƙƙun ginshiƙanta na sidar za a bayyana su. 15 Wannan ne maɗaukakin birnin da ya zauna cikin rashin tsoro, da yace a zuciyarsa," Ni ne kuma ba wanda ya kai ni." To Yaya ya zama mafi muni, wurin da dabbobin jeji ke kwance ciki. Duk wanda ya wuce ta wurinsa zai yi tsaki ya kaɗa kai.

Sura 3

1 Kaiton ki birni mai tayarwa! Birni mai ta'addanci ya ƙazantu. 2 Bata saurari muryar Allah ba, ko ta karɓi gyara daga Yahweh. Bata dogara ga Yahweh ba kuma ba zata kusanci Allahnta ba. 3 Sarakunanta zakuna ne masu ruri a tsakiyarta. Alƙalanta kyarketan yamma ne da basa barin abin yin tuƙa da safe. 4 Annabawanta marasa biyayya ne masu cin amana. Firistocinta sun wulaƙanta abin da ke mai tsarki kuma sun yi ta'addanci ga shari'a. 5 Yahweh adali ne a cikinta. Ba zai yi kuskure ba. Daga safiya zuwa safiya zai aiwatar da adalci! Ba zai ɓoyu ba cikin haske, duk da haka mutane marasa adalci basu san kunya ba. 6 Na hallakar da al'ummai; an lalatar da kagarorinsu. Na mai da titunansu kufai, don kar kowa ya bi kan su. An hallakar da biranensu har babu mutumin dake zaune cikinsu. 7 Na ce, 'Hakika zaku ji tsoro na. Ku karɓi gyara don kada a datse ku daga gidajenku ta wurin dukkan abubuwan da na shirya in yi maku.' Amma suna ƙagara su fara kowacce safiya da lalata ayyukansu. 8 Saboda haka ku jira ni - wannan furcin Yahweh ne. Har sai ranar da zan tashi domin ƙwace wahalallun. Gama ƙudurina shi ne in tara al'ummai, in taro masarautu, in kuma zuba masu fushina-dukkan hasalata mai zafi; domin a cikin wutar kishina za a cinye dukkan duniya. 9 Amma zan bada leɓuna masu tsarki ga mutanen, a kira dukkan su cikin sunan Yahweh su bauta mani suna tsaye kafaɗa da kafaɗa. 10 Daga ƙetaren kogin Kush masu yi mani sujada - mutanena dake warwatse - zasu kawo baye-bayen dake nawa. 11 A ranan nan baza ku kunyata ba game da dukkan abubuwan da kuka yi mani. Tun da a wannan lokaci zan kawar da waɗanda suka yi bikin girman kanku daga cikinku, saboda kuma baza ku ƙara yin rashin hankali ba a bisa dutsena mai tsarki. 12 Amma zan bar ku ƙaskantattu matalautan mutane, zaku kuma fake a cikin sunan Yahweh. 13 Ragowar Isra'ila kuma baza su ƙara aikata rashin adalci ba ko su faɗi ƙarairayi ko kuma a sami yaudara a bakin su ba; saboda haka zasu yi kiwo su kwanta, babu kuma wanda zaya tsoratar dasu." 14 Yi waƙa 'ɗiyar Sihiyona! Yi ihu, Isra'ila. Yi murna da farinciki da dukkan zuciyarki, ɗiyar Yerusalem. 15 Yahweh ya ɗauke hukuncinki; Ya kori maƙiyanki! Yahweh shi ne sarkin Isra'ila a tsakiyarku. Baza ki ƙara jin tsoron mugunta ba! 16 A ranar nan zasu cewa Yerusalem, "Kada ki ji tsoro, Sihiyona. Kada ki bari hannuwanki suyi sanyi. 17 Yahweh Allahnku yana tsakiyarku, mai ƙarfin nan da zai cece ku. Zai ji daɗin ku da farinciki kuma zai yi shuru a kanku cikin ƙaunarsa. Zai yi murna a kanku kuma zai yi sowa ta farinciki a kanku, 18 Zan tattara waɗanda ke ɓacin, waɗanda baza su iya kasancewa a zaɓaɓɓun bukukuwa ba, domin haka baza ku ƙara jin kunya dominsa ba. 19 Duba, Ina gab da horon masu tsananta maku. A lokacin nan, zan ƙwato guragu in tattaro waɗanda aka watsar. Zan maishe su kamar yabo, zan musanya kunyarsu zuwa sanannu a dukkan duniya. 20 A lokacin nan zan bi daku; a lokacin nan zan tara ku tare. Zan sa dukkan al'umman duniya su girmama su kuma yabe ku, lokacin kuka gana dawo da ku," inji Yahweh.

Littafin Haggai
Littafin Haggai
Sura 1

1 A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyos, a wata na shida, a rana ta fari ga watan, maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai ga gwamnan Yahuda, wato Zerubabel ɗan Shiltiyel, da kuma babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak cewa 2 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Waɗannan mutanen na cewa, 'lokaci bai yi ba da za mu zo ko mu gina wa Yahweh gida.'" 3 Sai maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai, cewa, 4 "Lokaci ya yi da za ku zauna a shiryayyun gidajenku, amma kuma wannan gidan na kwance a lalace? 5 To Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ku lura da hanyoyinku! 6 Kun shuka iri da yawa amma kun girbi kaɗan, kun ci amma bai ishe ku ba, kun sha amma ba ku ƙoshi ba. Ku na sa tufafi amma ba ku ji ɗumi ba, kuma mai ƙarbar albashi yana ƙarba kawai ya sa shi cikin jakka mai hudoji! 7 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: "Ku lura da hanyoyinku! 8 Ku hau bisa tudu, ku kawo katako ku gina mani gida, ta haka zan ji daɗi, kuma za a ɗaukaka ni!- in ji Yahweh." 9 "Kun nema da yawa amma duba kun kawo gida kaɗan, don na hure shi! Don me?" Yahweh mai runduna ya furta. "Saboda gidana na kwance a lalace, alhali kowanne ɗayan ku na aiki a nasa gidan. 10 Saboda haka sammai sun riƙe raɓa, ƙasa kuma ta riƙe amfaninta, 11 Ni na kawo ƒãri ga ƙasar kuma ga tuddai, ga ƙwayar hatsi, kuma ga sabon ruwan inabi, ga mai kuma ga girbin ƙasa, ga mutane da kuma ga dabbobi, kuma ga dukkan ayyukan hannuwanku!" 12 Sai Zarubabel ɗan Shaltiyel da babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, tare da dukkan sauran mutanen, suka yi biyayya da muryar Yahweh Allahnsu da kuma kalmomin annabi Haggai, saboda Yahweh Allahnsu ya aiko shi kuma mutanen sun ji tsoron fuskar Yahweh. 13 Sai Haggai, mai kawo saƙon Yahweh, ya faɗi saƙon Yahweh zuwa ga mutanen ya ce, "Ina tare da ku! - wannan furcin Yahweh ne!" 14 Yahweh ya zuga ruhun gwamnan Yahuda, wato Zerubabel ɗan Shiltiyel, da kuma ruhun babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, da kuma ruhun dukkan sauran mutanen, domin haka suka je su ka yi aiki a gidan Yahweh mai runduna, Allahnsu 15 a rana ta ashirin da hudu ta watan shida, a shekara ta biyu ta mulkin sarki Dariyos.

Sura 2

1 A wata na bakwai ranar ashirin da ɗaya a watan, maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai, cewa, 2 "Yi magana da gwamnan Yahuda, Zerubabel ɗan Shiltiyel, da babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, da dukkan mutane da aka rage. Ka ce, 3 "Wa ya rage a cikinku wanda ya ga wannan gida da darajarsa ta dã? Ya ya ku ka ganshi a yanzu? Shin kamar ba kome ya ke a idanunku ba? 4 Yanzu, sai ka yi ƙarfin hali, Zerubabel! - wannan furcin Yahweh ne, kai ma Yoshuwa ɗan Yehozadak babban firist sai ku yi ƙarfin hali, dukkan mutanen cikin ƙasar! - wannan furcin Yahweh ne, kuma ku yi aiki, domin ina tare da ku! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne. 5 Wannan shi ne alƙawarin da na yi da ku sa'ad da kuka fito daga ƙasar Masar, kuma Ruhuna na tare da ku. Kada ku ji tsoro! 6 Domin Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Ba da jimawa ba zan girgiza sammai da ƙasa, da teku da duk abin da ke a busarshiyar ƙasa! 7 Zan kuma girgiza kowacce al'umma, kuma kowacce al'umma za ta kawo abubuwa ma su daraja a gare ni, kuma zan cika wannan gidan da ɗaukaka, in ji Yahweh mai runduna. 8 Azurfa da zinariya nawa ne! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne. 9 Ɗaukakar wannan gidan ta zama da girma a nan gaba fiye da farkonsa, inji Yahweh mai runduna, zan ba da salama ga wannan wuri! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne." 10 A rana ta ashirin da hudu ga watan tara a shekara ta biyu ta Dariyos, maganar Yahweh ta zo ga annabi Haggai cewa, 11 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: A tambayi firistoci a kan shari'a, a ce, 12 "Idan mutum ya ɗauki nama da aka keɓe don Yahweh a rigarsa, sa'an nan ta taɓa gurasa, ko miya, ko ruwan inabi ko mai, ko kowanne irin abinci, ko wannan zai sa abin ya tsarkaka?" Firistoci suka amsa suka ce, "A'a." 13 Sai Haggai yace, "Idan wani wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin waɗannan, sun zama ƙazantattu? Sai firistoci suka amsa suka ce, "I sun ƙazantu. 14 Sai Haggai ya amsa yace, "Haka ya ke da mutane da al'umma da ke gabana! - wannan furcin Yahweh ne - haka ya ke game da dukkan abin da suke yi da hannuwansu. Da kuma abin da suke miƙawa a gare ni marar tsarki ne! 15 To yanzu, sai ku yi tunani a cikin lamirinku a kan abin da ya wuce har zuwa wannan rana. Kafin a ɗora dutse a kan dutse na haikalin Yahweh, 16 yaya ya ke? Lokacin da ku ka zo tarin da aka auna maku mudu ashirin na hatsi, sai aka iske mudu goma kaɗai; idan kuma kun zo wurin matsar ruwan inabi don a ɗebo mudu hamsin, sai aka tarar da mudu ashirin kawai. 17 Na aika maku da bala'i a aikin hannuwanku ta wurin darɓa da raɓa amma duk da haka ba ku komo wurina ba - wannan furcin Yahweh ne. 18 Lura tun daga wannan rana zuwa gaba, daga rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin haikalin Yahweh. Ku lura da shi! 19 Akwai sauran iri a rumbun? Inabin da itacen ɓauren, da ruman, da itacen zaitun ba su bada amfani ba! Amma daga wannan rana zan albarkace ku!" 20 Sai maganar Yahweh ta zo a karo na biyu ga Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan ya ce, 21 "Yi magana da gwamnan Yahuda, Zerubabel, ka ce, 'Zan girgiza sammai da ƙasa. 22 Zan kuma hamɓare kursiyin mulkoki in kuma lalata ƙarfin mulkokin al'ummai! Zan kuma hamɓare karusai da mahayansu; dawakai da mahayansu zasu faɗi ƙasa, kowanne saboda takobin ɗan'uwansa. 23 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - Zan ɗauke ka, Zerubabel ɗan Shiltiyel, bawana - wannan furcin Yahweh ne. Zan mai da kai kamar zoben hatimi, gama na zaɓe ka!' - wannan furcin Yahweh mai runduna ne!"

Littafin Zakariya
Littafin Zakariya
Sura 1

1 A cikin wata na takwas na shekara ta biyu na mulkin Dariyos maganar Yahweh ta zo ga Zakariya ɗan Berekaya ɗan Iddo, annabi, yana cewa, 2 "Yahweh ya ji haushin ubanninku ƙwarai! 3 Ka faɗi masu, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: ku juyo gare ni! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - ni ma zan dawo gare ku, Yahweh mai runduna ya faɗa. 4 Kada ku zama kamar ubanninku waɗanda Annabawa suka yi wa shela a lokatan baya, suna cewa, "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ku juyo daga miyagun hanyoyinku da ayyukanku na mugunta!" Amma basu ji ba ko kuma su saurare ni - wannan ne furcin Yahweh.' 5 Ubanninku, ina suke? Ina Annabawan, suna nan ne har abada? 6 Amma maganganuna da dokokina da na umarci bayina Annabawa, ba sun zarce ubanninku ba? Sai suka tuba suka ce, 'Kamar yadda Yahweh mai runduna ya shirya ya yi mana abin da ya yi wa hanyoyinmu da ayyukanmu dai-dai, hakanan ya yi da mu.'" 7 A cikin rana ta ashirin da huɗu na watan sha ɗaya, wanda shi ne watan Shibat, cikin shekara ta biyu na mulkin Dariyos, maganar Yahweh tazo wurin Annabi Zakariya ɗan Berekaya ɗan Iddo, cewa, 8 "Da dare na gani, na duba kuma! ga mutum na sukuwa bisa jan doki, yana tsakiyar itatuwan cizaƙi dake cikin kwari; bayan shi kuma akwai dawakai da ja da jaja-jaja-ruwan ƙasa-ƙasa da kuma farare." 9 Na ce, "Ubangiji mene ne waɗannan?" Sai mala'ikan da ke magana da ni yace mani, "zan nuna maka ko mene ne waɗannan." 10 Sai mutumin dake tsaye tsakiyar itatuwan cizaƙi ya amsa yace, "Waɗannan su ne Yahweh ya aika su yi yawo cikin duniya duka." 11 Suna ba da amsa ga mala'ikan Yahweh wanda ke tsaye a tsakiyar itatuwan cizaƙi; suna ce masa, "Muna ta yawatawa cikin duniya dukka; duba, dukkan duniya na zaune tsit kuma cikin hutawa." 12 Sai mala'ikan Yahweh ya amsa yace, "Yahweh mai runduna, har yaushe ne ba za ka nuna tausayi ga Yerusalem ba da kuma biranen Yahuda da suka sha wahalar zafin fushi shekarun nan saba'in?" 13 Yahweh ya amsa wa mala'ikan da ya yi magana da shi, da kalmomi masu daɗi, kalmomin ta'aziya. 14 Sai mala'ikan dake magana da ni yace mani, "Ka yi kira ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ina kishi game da Yerusalem da Sihiyona da babban kishi! 15 Ina jin haushi ƙwarai game da al'umman dake zaune cikin hutu. Yayin da haushina kaɗan ne game da su, sai suka maida bala'in ya zama da tsanani. 16 Saboda haka Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Na komo ga Yerusalem tare da jinkai. Za a sake gina gidana cikinta - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - kuma za a ja layin gwaji bisa Yerusalem!' 17 Ka sake kira, kuma, ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Biranena zasu sake malala da nagarta, Yahweh kuma zai sake yi wa Sihiyona ta'aziya, zai kuma sake zaɓen Yerusalem.'" 18 Sai na ɗaga idanuna na ga ƙahonni huɗu! 19 Sai na yi magana da mala'ikan dake magana da ni, "Mene ne waɗannan?" Ya amsa mani, "Waɗannan ne ƙahonnin da suka warwatsa Yahuda, da Isra'ila, da Yerusalem." 20 Sai Yahweh ya nuna mani masassaƙa huɗu. 21 Na ce, "Me waɗannan mutanen suka zo yi?" Ya amsa, yace, "Waɗannan ne ƙahonnin da suka warwatsa Yahuda har ba mai iya ɗaga kansa. Amma waɗannan mutane sun zo ne su kore su, su kakkarya ƙahonnin al'ummai waɗanda suka ɗaga ƙahon tsayayya da ƙasar Yahuda domin watsar da ita."

Sura 2

1 Daga nan na ɗaga idanuna sai na ga mutum da ma'auni a hannunsa. 2 Na ce, "Ina zaka?" Sai ya ce mani, "Domin in auna Yerusalem, a tantance faɗinta da tsawonta." 3 Sai mala'ikan da yake magana da ni ya yi tafiyar sa sai wa ni mala'ika kuma ya tafi domin ya same shi. 4 Mala'ikan na biyu yace masa, "Yi gudu ka yi magana da saurayin can; ka ce, 'Yerusalem zata zauna a buɗaɗɗiyar ƙasa saboda yawan mutane da dabbobi dake cikinta. 5 Gama ni - wannan furcin Yahweh ne - zan zama katangar wuta kewaye da ita, kuma zan zama ɗaukakar dake cikinta. 6 Tashi! Tashi! Ku gudu daga ƙasar arewa - wannan furcin Yahweh ne - gama na warwatsa ku kamar kusurwoyin iska huɗu a sasarin sama! - wannan furcin Yahweh ne. 7 Tashi! Ku tsere zuwa Sihiyona, ku da kuke zaune tare da ɗiyar Babila!'" 8 Gama bayan da Yahweh mai runduna ya darajantani ya kuma aike ni ga al'umman nan da suka washe ku - gama duk wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idon Allah! - bayan da Yahweh ya yi wannan, sai ya ce, 9 "Ni da kaina zan girgiza hannuna a bisansu, kuma za a washe su domin bayinsu. "Daga nan zaku sani Yahweh mai runduna ne ya aiko ni. 10 "Ki raira waƙa domin farinciki, ke ɗiyar Sihiyona, gama ni da kaina ina gaf da zuwa in kafa sansani a cikinki! - wannan ne furcin Yahweh." 11 Daga nan manyan al'ummai zasu haɗu da juna zuwa ga Yahweh a wannan rana. Ya faɗi, "Daga nan zaku zama mutanena; kuma zan kafa sansani a cikinku," daga nan kuma zaku sani Yahweh mai runduna ya aiko ni zuwa gare ku. 12 Gama Yahweh zai gãji Yahuda a matsayin mai 'yancin gãdonta cikin ƙasa mai tsarki kuma zaya sake zaɓen Yerusalem domin kansa. 13 Ku yi tsit, dukkanku masu rai, a gaban Yahweh, domin an zugo shi daga wurinsa mai tsarki!

Sura 3

1 Sai Yahweh ya nuna mani Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala'ikan Yahweh ga kuma Shaiɗan a tsaye a hannun damansa domin ya zarge shi da zunubi. 2 Mala'ikan Yahweh yace da Shaiɗan, "Bari Yahweh ya tsauta ma, Shaiɗan; bari Yahweh, wanda ya zaɓi Yerusalem, ya tsauta maka! Wannan ba reshe ba ne da aka ciro daga wuta?" 3 Yoshuwa dai na sanye da ƙazantattun tufafi yayin da yake tsaye a gaban mala'ikan. 4 Sai mala'ikan ya yi magana yace da waɗanda ke tsaye a gabansa, "Ku tuɓe ƙazantattun tufafin daga jikinsa." Sai yace da Yoshuwa, "Duba! na sa laifuffukanka su kawu daga gare ka kuma zan sanya maka kaya masu tsafta." 5 Sai yace, "Bari a sa rawani mai tsafta a bisa kansa!" Sai suka sa rawani mai tsafta a bisa kan Yoshuwa kuma suka sanya masa tufafi masu tsafta yayin da mala'ikan Yahweh ke tsaye tare dasu. 6 Daga nan sai mala'ikan Yahweh ya yi umarni mai juyayi ga Yoshuwa yace, 7 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Idan za ka yi tafiya cikin hanyoyina, ka kuma kiyaye dokokina, to za ka yi mulkin gidana kuma ka yi tsaron harabaina, domin zan ba ka dama ka shiga ka fita a tsakiyar waɗannan dake tsayawa a gabana. 8 Ka saurara, Yoshuwa babban firist, kai da masu tarayya da kai dake zaune tare da kai! Domin waɗannan mutane alama ne, gama ni da kaina zan taso da bawana Reshen. 9 Yanzu ka duba dutsen da na sa a gaban Yoshuwa. Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse ɗaya, kuma zan sassaƙa hatimi -wannan ne furcin Yahweh mai runduna - kuma zan cire zunubin daga wannan ƙasa a rana ɗaya. 10 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - kowanne mutum zai gayyaci maƙwabcinsa ya zauna a gindin inabinsa da gindin itacen ɓaurensa."

Sura 4

1 Sai mala'ikan dake magana da ni ya juya ya farko da ni kamar mutumin dake farkarwa daga barci. 2 Ya ce da ni, "Me ka gani?" na ce, "Na ga mazaunin fitila da aka yi da zinariya baki ɗaya, da kwano a bisansa. Yana da fitilu bakwai a bisansa da kuma lagwanin fitilu bakwai a kan kowacce fitila. 3 Akwai itatuwan zaitun biyu a kowanne gefensa, ɗaya na gefen dama da kwanon ɗaya kuma na gefen hagu." 4 Sai na ƙara magana da mala'ikan dake magana da ni. Na ce, "Mene ne ma'anar waɗannan abubuwa ya shugabana?" 5 Mala'ikan dake magana da ni ya amsa yace da ni, "Baka san ma'anar waɗannan abubuwa ba?" Na ce, "A'a, ya shugabana." 6 Sai ya ce ma ni, "Wannan ce maganar Yahweh ga Zerubabel: Ba ta ƙarfi ba, ba ta iko ba amma ta Ruhuna, Yahweh mai runduna ya faɗa. 7 Kai wane ne, babban dutse? A gaban Zerubabel za ka zama sarari, zai kuma kawo dutsen dake sama tare da sowace - sowacen 'Alheri! Alheri a gare shi!'" 8 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa, 9 "Hannun Zerubabel ya ɗora harsashen ginin wannan gida hannunsa kuma zai kammala shi. Daga nan zaku sani Yahweh mai runduna ya aiko ni gare ku. 10 Wane ne ya rena ranar ƙananan abubuwa? Waɗannan mutane zasu yi farinciki kuma zasu ga dunƙulen dutsen a hannun Zerubabel. (Waɗannan fitilu bakwai idanun Yahweh ne dake dubawa ko ina cikin duniya)." 11 Daga nan na tambayi mala'ikan, "Mene ne waɗannan itatuwan zaitun biyu dake hagu da dama na mazaunin fitilar?" 12 Na sake tambayar shi kuma, "Mene ne waɗannan rassan zaitun biyu dake gefen bututun zinari biyu dake ɓulɓulo da mạn zinariya daga cikinsu?" 13 Sai ya ce ma ni, "Baka san ko mene ne waɗannan ba?" Na ce, "A'a, ya shugabana." 14 Sai ya ce, "Waɗannan 'ya'ya maza ne na sabon man zaitun dake tsaye a gaban Ubangijin dukkan duniya."

Sura 5

1 Daga nan na juya na ɗaga idanuna, sai na gani, duba, ga littafi naɗaɗɗe na shawagi a sama! 2 Sai mala'ikan yace mani, "Me ka gani?" Na amsa, "Na ga littafi naɗaɗɗe na shawagi a sama, tsawonshi kamu ashirin fadinshi kamu goma." 3 Sai ya ce da ni, "Wannan ce la'anar dake yawo a fuskar dukkan ƙasar, za a datse kowanne ɓarawo bisa ga yadda ya faɗa a gefe ɗaya, dukkan wanda kuma ya yi rantsuwa da alƙawarin ƙarya za a datse shi bisa ga yadda ya faɗa a gefe ɗayan, bisa ga maganganunsu. 4 "Zan aika da ita - wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna - saboda haka zata shiga gidan ɓarawo da gidan wanda ya yi rantsuwar ƙarya da sunana. Zata zauna a gidanshi ta cinye katakan da duwatsun." 5 Daga nan sai mala'ikan dake magana da ni ya fita ya ce mani, "Ɗaga idanunka ka ga abin dake tahowa!" 6 Sai na ce, "Mene ne?" Ya ce, "Wannan kwando ne dake ɗauke da garuwa dake zuwa. Wannan laifuffukansu ne cikin dukkan ƙasar." 7 Sai aka ɗauke murfin ƙarfen dake rufe da kwandon sai ga wata mace a cikinsa zaune! 8 Mala'ikan yace, "Wannan mugunta ce!" Sai ya sake jefa ta cikin kwandon, kuma ya sake rufe shi da murfin ƙarfen. 9 Na ɗaga idanuna sai na ga mata biyu na zuwa wurina, kuma iska na cikin fukafukansu - gama suna da fukafukai kamar fukafukan shamuwa. Suka ɗaga kwandon nan tsakanin duniya da sama. 10 Sai na ce da mala'ikan nan dake magana da ni, "Ina zasu kai kwandon?" 11 Ya ce da ni, "Zasu gina mashi haikali a ƙasar Shina, domin idan suka gama ginin haikalin, sai su ɗora kwandon a dai-dai wurinda suka shirya dominshi."

Sura 6

1 Sai na juya na hango karusai huɗu suna zuwa sun fito daga tsakanin duwatsu biyu; duwatsun nan biyu kuwa an yi su daga tagulla ne. 2 Karusa na farko dawakansa jajaye ne, karusa na biyu dawakansa baƙaƙe ne, 3 karusa na uku dawakansa farare ne, karusa na huɗu dawakansa dabbare - dabbaren ruwan toka ne. 4 Sai na amsa na ce da mala'ikan dake magana da ni, "Mene ne waɗannan, ya shugabana?" 5 Sai mala'ikan ya amsa yace ma ni, "Waɗannan su ne iskoki huɗu na sararin samaniya waɗanda ke fitowa daga wurin da suke tsayawa a gaban Ubangijin dukkan duniya. 6 Mai baƙaƙen dawakai na tafiya zuwa ƙasar arewa; fararen dawakan na tafiya zuwa ƙasar yamma; dawakai masu dabbare-dabbaren ruwan toka na tafiya zuwa ƙasar kudu." 7 Waɗannan dawakai masu ƙarfi suka tafi suka nemi su kewaye dukkan duniya, sai mala'ikan yace, "Ku tafi ku kewaye bisa duniya!" Sai suka tafi domin dukkan duniya. 8 Sai ya kira ni ya yi magana da ni ya ce, "Dubi waɗanda ke tafiya zuwa ƙasar arewa; zasu tausar da ruhuna game da ƙasar arewa." 9 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 10 "Ka karɓi baiko daga 'yan gudun hijirar - daga Heldai, da Tobiya, da Yedaya - sai ka tafi dai-dai cikin wannan ranar ka kai cikin gidan Yosaya ɗan Zafaniya, wanda ya zo daga Babila. 11 Sai ka ɗauki azurfar da zinarin, sai ka yi rawani dasu ka ɗora bisa kan Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. 12 Ka yi magana da shi ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Wannan mutum, sunansa Reshe! Zai yi girma inda ya ke sa'an nan kuma ya gina haikalin Yahweh! 13 Shi ne wanda zai gina haikalin Yahweh sa'an nan ya ɗaga darajarsa; daga nan zai zauna ya yi mulki akan kursiyinsa. Zai zama firist a bisa kursiyinsa kuma fahimtar salama za ta kasance tsakanin su biyun. 14 Za a bayar da rawani ga Heldai, da Tobiya da Yedaya da Hen ɗan Zakariya a matsayin abin tunawa a cikin haikalin Yahweh. 15 Daga nan waɗanda ke daga nesa zasu zo su gina haikalin Yahweh, domin ku sani Yahweh mai runduna ne ya aiko ni zuwa gare ku; wannan zai faru idan da gaske kun saurari muryar Yahweh Allahnku!'"

Sura 7

1 Da sarki Dariyos ya yi mulki shekaru huɗu, a ranar huɗu ga watan Kisleb (wanda shi ne watan tara), maganar Yahweh ta zo ga Zakariya. 2 Mutanen Betel suka aika da Shareza da Regem Melek da kuma mazajensu domin su yi roƙo gaban fuskar Yahweh. 3 Suka yi magana da firistocin dake gidan Yahweh mai runduna da kuma annabawan; suka ce, "Ko zan yi makoki cikin watan biyar ta wurin yin azumi, kamar yadda na yi cikin shekarun nan masu yawa?" 4 Sai maganar Yahweh mai runduna ta zo gare ni, cewa, 5 "Yi magana da dukkan mutanen ƙasar da firistocin ka ce, 'Da kuka yi azumi da makoki watan biyar da watan bakwai cikin shekarun nan saba'in, da gaske ni kuka yi wa azumi? 6 Da kuka ci ku ka sha, ba don kanku ku ka ci kuka sha ba? 7 Waɗannan ba sune maganganun da Yahweh ya yi shela ba ta bakin annabawan dã, sa'ad da kuke zaune a Yerusalem da biranen kewaye cikin wadata kuma kuka yi zamanku a Negeb, da gefen tsaunukan yamma?'" 8 Maganar Yahweh ta zo wurin Zakariya, cewa, 9 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka, 'Ku zartar da hukunci mai gaskiya, da amintaccen alƙawari, da kuma jinƙai. Bari kowanne mutum ya yi wa ɗan'uwansa haka. 10 Game da gwauruwa da maraya, da kuma baƙo, da matalauci-- kada ku ƙuntata masu, kada kuma wani ya shirya wani mugun abu game da ɗan'uwansa a cikin zuciyarsa.' 11 Amma suka ƙi maida hankali kuma suka ɗaga kafaɗunsu cikin taurinkai. Suka toshe kunnuwansu domin kada su ji. 12 Suka maida zukatansu taurara kamar dutse domin ka da su ji shari'a ko maganganun Yahweh mai runduna. Ya aika da saƙonnin nan ga mutanen ta wurin Ruhunsa a lokatan farko, ta bakin annabawa. Amma mutanen suka ƙi saurare, domin wannan Yahweh mai runduna ya ji haushin su ƙwarai. 13 Sai ya kasance da ya yi kira, basu saurara ba. Ta haka kuma," Yahweh mai runduna yace, "Zasu yi kira zuwa gare ni, amma ba zan saurare su ba. 14 Gama zan warwatsasu da guguwa cikin dukkan al'umman da basu taɓa gani ba, ƙasar za ta zama kufai bayansu. Gama ba wanda zai iya ratsawa ta cikin ƙasar ko ya dawo gareta tun da mutanen sun maida ƙasarsu ta farinciki zuwa watsartsiyar ƙasa."

Sura 8

1 Maganar Yahweh mai runduna ta zo gare ni cewa, 2 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Ina kishi domin Sihiyona da kuma babban kishi da hasala mai zafi ƙwarai! 3 Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Zan komo wurin Sihiyona in kuma zauna a tsakiyar Yerusalem, gama za a kira Yerusalem Birnin Gaskiya kuma dutsen Yahweh mai runduna za a ce da shi Dutse Mai Tsarki! 4 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Tsofaffi maza da mata zasu ƙara kasancewa a titunan Yerusalem, kowannensu za shi buƙaci sanda a hannunsa domin yạ tsufa. 5 Titunan birnin zasu cika da matasa maza da mata, masu wasanni a cikinsu. 6 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Idan wani al'amari ya zama mai wuya a ganin mutanen nan da suka rage, a wannan kwanaki, shi ma za shi zama abu mai wuya a idanuna? -- wannan furcin Yahweh ne. 7 Yahweh mai runduna ya fa‌ɗ‌i wannan; Duba, Ina gaf da kuɓutar da mutanena daga ƙasashe na fitowar rana da na faɗuwar rana! 8 Gama zan dawo dasu, kuma zasu zauna a tsakiyar Yerusalem, haka zasu zama mutanena kuma, ni kuma zan zama Allahnsu cikin gaskiya da adalci! 9 Yahweh mai runduna ya fa‌ɗi haka: Ku da kuka ci gaba da sauraron maganganuna daga bakin annabawa tun farkon kafa harsashen ginin wannan haikali, - wannan gida nawa, Yahweh mai runduna: Ku ƙarfafa hannayenku domin a gina haikalin. 10 Domin kamin wannan lokaci babu hatsin da aka tara daga wurin wani, babu wata riba domin mutum ko dabba, kuma ba a sami salama ba daga magabci ko ga mai shiga ko mai fita. Na maishe da kowanne mutum magabci ga makwabcinsa. 11 Amma yanzu baza shi kasance kamar kwanakin baya ba, zan zauna tare da mutanena wa‌ɗ‌anda suka rage - wannan ne furcin Yahweh mai runduna. 12 Gama za a shuka irin salama; kuringa mai haurawa sama zata ba da 'ya'ya, duniya kuwa zata ba da amfanin ƙasa; sammai zasu ba da raɓarsu, gama zan sa sauran jama'ar da suka rage su gãji dukkan waɗannan abubuwa. 13 Kun zama misali na la'ana ga al'ummai, gidan Yahuda da na Isra'ila. Yanzu fa zan kuɓutar da ku da haka kuma zaku zama albarka. Kada ku ji tsoro; amma bari hannuwanku su ƙarfafa! 14 Gama Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: kamar yadda na shirya yi maku lahani a lokacin da kakanninku suka cakuneni - Yahweh mai runduna ya fadi wannan - kuma bai fasa ba, 15 haka kuma zan yi shiri mai kyau a wannan kwanaki zuwa ga Yerusalem da kuma gidan Yahuda! Kada ku ji tsoro! 16 Ga abubuwan da dole ku aikata: ku faɗi gaskiya, kowanne mutum ga makwabcinsa. Ku yi shari'a da gaskiya, da adalci, da kuma salama a ƙofofinku. 17 Kada ku yi shirin aikata mugunta a cikin zuciyarku ga junanku, kuma kada ku ƙaunaci alƙawaran ƙarya -- gama waɗannan sune abubuwan da na ƙi! - wannan furcin Yahweh ne." 18 Sa'an nan maganar Yahweh mai runduna ta zo gareni, cewa, 19 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, duk zasu zama lokatan farinciki, da jin daɗi, da bukukuwan murna na gidan Yahuda! Saboda haka ku ƙaunaci gaskiya da salama! 20 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Mutane zasu sake zuwa, harma da waɗanda suke zama a birane daban - daban. 21 Mazaunan birni ɗaya zasu je wani birnin su ce, "Mu yi sauri mu je mu yi roƙo a gaban fuskar Yahweh mu kuma nemi Yahweh mai runduna! Mu ma zamu tafi da kanmu. 22 Mutane dayawa da manyan al'umma zasu zo Yerusalem su nemi Yahweh mai runduna kuma su roƙi tagomashin Yahweh! 23 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: A wannan kwanakin, maza goma daga kowanne harshe da kuma al'umma zasu kama haɓar rigarku su ce, "Bari mu tafi tare da ku, gama mun ji cewa Allah na tare da ku!"'

Sura 9

1 Wannan furcin maganar Yahweh ne game da ƙasar Hadrak da Damaskus. Gama idanun Yahweh na bisan dukkan 'yan'adam, da kuma bisa dukkan kabilun Isra'ila. 2 Furcin nan kuma ya shafi Hamat wadda take maƙwabciya da Damaskus, ta kuma shafi Taya da Sidon, ko da shi ke suna da hikima ƙwarai. 3 Taya ta gina wa kanta mafaka mai karfi ta kuma lafta azurfa kamar ƙura da kuma tatacciyar zinariya kamar laƙa a bisa titunanta. 4 Duba! Ubangiji za ya kawar da ita ya kuma lallata karfinta na teku, da haka zata hallaka da wuta. 5 Ashkelon zata gani ta kuma ji tsoro! Gaza kuma zatayi rawar jiki ƙwarai! Ekron, begenta ba zai tabbata ba! Sarkin zaya hallaka daga Gaza, ba kuma za a sake zama cikin Ashkelon ba! 6 Baƙi zasu gina gidaje a Ashdod, zan kuma datse girman kan Filistiyawa. 7 Gama zan fitar da jininsu daga bakinsu, abubuwan banƙyamarsu kuma daga tsakiyar haƙoransu. Da haka zasu zama ragowa ga Allahnmu kamar zuriya a Yahuda, Ekron kuma zata zama kamar Yebusawa. 8 Zan kafa sansani kewaye da ƙasata gãba da sojojin maƙiya domin kada wani ya ratsa ta cikinta ko ya je ko ya dawo, domin ba bu mai tsanantawar da zai ƙara shigowa ta cikin ƙasata. Yanzu dai zan kula da ƙasata da idanuna! 9 Yi sowa da farinciki mai girma, ɗiyar Sihiyona! Yi sowa da murna, ɗiyar Yerusalem! Duba! Sarkinki na zuwa gare ki da adalci yana kuma kuɓutar dake. Mai tawali'u ne yana bisa kan jaki, a bisa kan ɗan jaki. 10 Daga nan zan datse karusa daga Ifraimu doki kuma daga Yerusalem, Za a kuma datse baka daga yaƙi; gama za ya yi maganar salama ga al'ummai, mulkinsa kuma za ya zama daga teku zuwa teku, kuma daga ‌Ƙogi har zuwa ƙarshen duniya! 11 Amma ke, saboda jinin alƙawarina dake, zan fitar da 'yan sarƙarki daga ramin da babu ruwa. 12 Ku dawo cikin mafaka mai ƙarfi dukkan ku 'yan kurkukun bege! Ko yau ina shaida maku zan maido maku ruɓi biyu, 13 gama na lanƙwasa Yahuda kamar baka na. Na cika ƙwarina da Ifraimu. Na motso da 'ya'ya mazanki, Sihiyona, gãba da 'ya'ya mazanki, Giris, kuma na yi ki, Sihiyona, kamar takobin mayaƙi! 14 Yahweh za ya bayyana gare su, kuma kibiyoyinsa zasu harba kamar walƙiya! Gama Ubangijina Yahweh za ya busa ƙahon kuma za ya cigaba cikin hadari daga Teman. 15 Yahweh mai runduna zai kare su, zasu kuma haɗiyesu, su kuma ci nasara da duwatsun majaujawa. Sa'an nan zasu sha suna sowa kamar mutanen da suka bugu da ruwan inabi, zasu kuma cika da ruwan inabi kamar dãro, kamar kusurwoyin bagadi. 16 Yahweh Allahnsu zai cece su a wannan rana; zasu zama kamar garke mai ɗauke da mutanensa, gama zasu zama duwatsun kambi, wanda aka ɗaukaka bisa ƙasarsa. 17 Duba yadda zasu zama da kyau da kuma ban sha'awa! Samarin zasu yalwata kan hatsi, budurwan kuma bisa inabi mai zaƙi!

Sura 10

1 Ku roƙi Yahweh ruwan sama a lokacin bazara -Yahweh shi ne mai yin hadarun-aradu -- kuma yana ba da ruwan sama ga kowa da kuma dukkan tsire tsiren gona. 2 Gama ƙarya kawai gumakan gãdo ke faɗi; masu sihiri kuma suna ƙirƙiro ƙarya; suna faɗin mafarkai na ruɗani su kuma yi ta'aziyar wofi, da haka suke yawo kamar tumaki suna shan azaba domin babu makiyayi. 3 Fushina na ƙuna akan makiyayan; sune bunsuran -- shugabannin -- waɗanda zan hora. Yahweh mai runduna za ya kuma lura da garkensa, gidan Yahuda, za ya mai dasu kamar dokin yaƙinsa a yaƙi! 4 Daga gare su dutsen kusurwar gini zaya fito; daga gare su turken rumfar za ya fito; bakan yaƙi za shi fito daga nan; daga can dukkan shugabanni zasu fito tare. 5 Zasu zama kamar jarumawa masu tattaka maƙiyansu a cikin laka a bisa titunansu a yaƙi; zasu ja dagar yaƙi, gama Yahweh na tare da su, zasu kuma kunyatar da mahayan dawakan yaƙi. 6 Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yosef; gama zan maido dasu in kuma nuna masu jinƙai. Ba za su yi kamar na yashe su ba, gama ni ne Yahweh Allahnsu, kuma zan amsa masu. 7 Daga nan Ifraim zaya zama kama da mayaƙi, zuciyarsu kuma zata yi farinciki kamar da inabi; 'Ya'yansu zasu gani su yi farinciki. Zuciyarsu zata yi farinciki a ciki na! 8 Zan yi masu busa in kuma tara su, gama zan kuɓutar dasu, kuma zasu zama da girma kamar yadda suke a dã! 9 Na shuka su cikin al'ummai amma zasu tuna da ni a ƙasashe masu ni sa, su da 'ya'yansu zasu rayu su kuma dawo gida. 10 Gama daga Asiriya zan tattara su in kuma maido dasu daga Masar. Zan dawo dasu ƙasar Giliyad da Lebanon har sai ba sauran wuri dominsu. 11 Zan bi ta cikin tekun azabarsu; Zan tsautawa igiyoyin tekun nan in kuma busar da dukkan zurfafun Nilu. Za a saukar da ƙasaitar Asiriya, sandar mulkin Masar kuma zata tafi daga Masarawa. 12 Zan ƙarfafa su a cikina, za su yi tafiya kuma cikin sunana - wannan furcin Yahweh ne.

Sura 11

1 Ki buɗe ƙofofinki, Lebanon, don wuta ta cinye itatuwanki na sida! 2 Yi makoki, itatuwan siferes, gama itatuwan sida sun faɗi! Abin da yake ƙasaitacce ya lalace sarai! Yi makoki, ku rimaye na Bashan, gama babban kurmi dukka ya faɗi. 3 Makiyaya suna ta kururuwa, gama an lalatar da ɗaukakarsu! Muryar 'ya'yan zakuna na ruri, gama an lallatar da fahariyar Kogin Yodan! 4 Wannan ne abin da Yahweh Allahna ya faɗi: "Kamar makiyayi, mai kiwon garken da aka ƙaddara domin yanka! 5 (Su waɗanda suka sayesu suka yankasu kuma ba a yi masu horo ba, kuma waɗanda suka sayar da su sukace; "Mai albarka ne Yahweh! Na zama mai arziƙi! gama makiyayan dake yi wa masu garken aiki basu jin tausayinsu). 6 Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasar ba! --- wannan furcin Yahweh ne. Duba! Ni da kaina ina gaf da bayar da kowanne mutum cikin hannun makwabcinsa da kuma cikin hannun sarkinsa, zasu kuma lallatar da ƙasar ba bu wanda zan kuɓutar daga hannunsu." 7 Don haka na zama makiyayin garken da aka ƙaddara domin yanka, ga masu cinikin tumaki. Na ɗauko sanduna biyu; ɗaya na kira ta "tagomashi" ɗayar kuma na kira ta "haɗin kai." da haka na yi kiwon garken. 8 A cikin wata ɗaya na hallaka makiyayan uku, gama hakurina ya gaza a kansu, haka su ma suka ƙi ni. 9 Sai na cewa masu garken, "Ba zan sake yi maku aikin makiyayi ba. Tumakin da ke mutuwa-- bari su mutu; tumakin da ke hallaka --- bari su hallaka. Bari tumakin dasu ka rage kowanne ya ci naman maƙwabcinsa." 10 Sai na ɗauki sandata "tagomashi" sai na karyata domin in karya alƙawarina da nayi da dukkan kabiluna. 11 A wannan ranar aka karya alƙawarin, masu cinikin tumaki da waɗanda ke kallona suka sani cewa Yahweh ya yi magana. 12 Na ce masu, "Idan kun ga ya dace ku biya ni ladata. Amma idan ba haka ba, kada kuyi." Sai suka auna mani ladata --- sulallan azurfa talatin. 13 Sai Yahweh yace dani, "Zuba azurfar cikin ma'aji, darajar farashin da aka kimantaka!" Sai na ɗauki sulallan azurfar talatin na zuba su cikin ma'aji a gidan Yahweh. 14 Sa'an nan na karya sandata ta biyu "Haɗin kai," domin a karya 'yan'uwantakar dake tsakanin Yahuda da Isra'ila. 15 Yahweh yace da ni, "Ka sake, ɗaukarwa kanka kayan aiki irin na wawan makiyayi, 16 gama duba, ina gaf da naɗa makiyayi a ƙasar. Ba za ya kula da tumakin dake hallaka ba. Ba za ya tafi neman ɓatattun tumaki ba, ko ya warkar da tumakin da suka gurgunce ba. Ba zaya ciyar da lafiyayyun tumakin ba, amma za ya cinye naman tumaki masu ƙiba, ya kuma saɓe ƙofatunsu. 17 Kaiton makiyayi mara amfani da ya yi watsi da garken! Bari takobi ta yi tsayayya da hannusa da kuma idonsa na dama! Bari hannunsa ya shanye idonsa na dama ya makance!"

Sura 12

1 Wannan furcin maganar Yahweh game da Isra'ila - furcin Yahweh, shi wanda ya shimfiɗa sararin sammai ya kuma kafa harsashen duniya, wanda ya sa ruhun ɗan adam cikin mutum, 2 "Duba, ina gaf da sa Yerusalem ta zama kofi mai sa maƙwabtanta tangaɗi. Haka kuma za shi zama ga Yahuda a lokacin da aka yiwa Yerusalem sansani. 3 A wannan rana, Zan maida Yerusalem dutse mai nauyi domin dukkan mutane. Duk wanda ya yi ƙoƙarin ɗaga wannan dutse za ya ji wa kansa rauni mai tsanani, dukkan al'umman duniya kuma zasu tattaru yin gãba da wannan birni. 4 A ranan nan --- wannan ne furcin Yahweh --- zan bugi kowanne doki da firgita da kuma kowane mahayi da hauka. Zan dubi gidan Yahuda da tagomashi in kuma bugi kowanne dokin sojojin da makanta. 5 Daga nan shugabannin Yahuda zasu ce cikin zuciyarsu, 'Mazaunan Yerusalem sune ƙarfinmu saboda Yahweh mai runduna, Allahnsu.' 6 A wannan rana zan mai da shugabannin Yahuda kamar tukunyar wuta a tsakiyar itatuwa da kuma fitila mai ci balbal a cikin hatsin dake tsaye, gama zasu hallaka dukkan mazauna kewaye dasu dama da hagu. Yerusalem zata sãke zaunawa a wurinta." 7 Yahweh zai ceci rumfunan Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dauda da kuma na mazaunan Yerusalem su fi na sauran mazaunan Yahuda. 8 A wannan ranar Yahweh zaya zama kariyar mazaunan Yerusalem, kuma a wannan ranar, waɗanda basu da ƙarfi cikinsu zasu zama kamar Dauda, yayin da gidan Dauda zaya zama kamar Allah, kamar mala'ikan Yahweh a gabansu. 9 "A ranan nan da zan fara hallaka dukkan al'umman dasu ka yi tsayayya da Yerusalem. 10 Amma zan zubo da ruhun tausayi da na roƙo a bisa gidan Dauda da mazaunan Yerusalem, domin su dube ni, wanda suka soke. Zasu yi makoki domina, kamar wanda ke makoki domin tilon ɗansa; za su yi matuƙar makoki dominsa kamar waɗanda su ke makokin mutuwar ɗan fari. 11 A wannan ranar makokin cikin Yerusalem za shi zama kamar makokin da aka yi cikin Hadad Rimon cikin kwarin Megido. 12 Ƙasar zata yi makoki, kowacce zuriya daban da wasu zuriyoyin. Zuriyar gidan Dauda zata zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware daga mazajen. Zuriya daga gidan Natan zasu zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware da mazajen. 13 Zuriyar gidan Lebi zasu zama a ware, matayensu kuma a ware da mazajen. Zuriyar Shimeyawa zasu zama a ware matayensu kuma a ware daga mazajen. 14 Kowacce zuriya ta sauran zuriyar da suka ragu - kowacce zuriya zata zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware daga mazajen."

Sura 13

1 "A wannan rana za a buɗe wa gidan Dauda magudanar ruwa da kuma mazaunan Yerusalem, saboda zunubansu da rashin tsarkinsu. 2 A wannan ranar -- wannan furcin Yahweh mai runduna ne - cewa zan datse sunayen gumaka daga ƙasar don kada a ƙara tunawa dasu. Zan kuma sa dukkan annabawan ƙarya da ƙazamin ruhunsu su fita daga ƙasar. 3 Idan wani mutum ya ci gaba da yin annabci, mahaifinsa da mahaifiyarsa waɗanda suka haifeshi zasu ce masa, 'Ba za ka rayu ba, don kana ƙarya da sunan Yahweh! Sa'an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa waɗanda suka haife shi zasu soke shi yayin da yake anabce-anabce. 4 A wannan ranar kowanne annabi zayaji kunyar wahayinsa yayinda yake gaf da yin annabci. Waɗannan annabawan ba zasu ƙara sanya rigar gashi ba don su ruɗi jama'a. 5 Gama kowanne zai ce, 'Ni ba annabi ba ne! Ni manomi ne, na fara aikin gona tun ina yaro!' 6 Amma wani zai ce masa, 'ina ka samo waɗannan raunukan a hannuwanka? shi kuwa za ya amsa, 'An yi mani rauni tare da waɗanda ke gidan abokaina."' 7 "Takobi! Motsa kanki gãba da makiyayina, mutumin da ya tsaya kusa da ni -- wannan furcin Yahweh ne - mai runduna. Bugi makiyayin, tumakin kuma zasu warwatse! Gama zan juya hannuna gãba da ƙasƙantattun. 8 Daga nan zaya kasance game da wannan a cikin dukkan ƙasar --- wannan furcin Yahweh ne --- kashi biyu cikin uku za a datse! Waɗannan mutane zasu hallaka; kashi ɗaya cikin uku kawai zaya rage a wurin. 9 Kashi ɗayan da ya rage zan bi dasu ta cikin wuta in tãcesu kamar yadda ake tãce azurfa; zan gwada su kamar yadda ake gwada zinariya. Zasu kira bisa sunana, ni kuwa zan amsa masu in ce, 'Waɗannan mutanena ne!' su kuma zasu ce, 'Yahweh ne Allahna!"'

Sura 14

1 Duba! Ranar Yahweh na zuwa da za a raba ganimarku a tsakiyarku. 2 Gama zan tattara dukkan al'umma tsayayya da Yerusalem domin yaƙi kuma za a ci birnin. Za a warwashe gidajensu kuma za a yiwa matayensu fyaɗe. Rabin birnin za ya tafi zuwa bautar talala, amma ragowar mutanen ba za a datse su ba daga birnin. 3 Amma Yahweh zaya fita ya kuma jãdagar yaƙi da waɗannan al'ummai kamar yadda ya jãgadar yaƙi a ranar yaƙi. 4 A wannan rana tafin sawayensa zasu tsaya bisa Dutsen Zaitun, wanda yake gefen Yerusalem maso gabas. Za a raba Dutsen Zaitu kashi biyu tsakanin gabas da yamma ta kwari mai girma kuma sashe ɗaya na dutsen za shi janye zuwa arewa ɗaya sashen kuma za shi janye zuwa kudu. 5 Sa'an nan zaku tsere zuwa cikin kwarin tsakanin duwatsun Yahweh, domin kwarin dake tsakanin duwatsun za ya kai har Azel. Zaku yi ta gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzaya, sarkin Yahuda. Sa'an nan Yahweh Allahna za ya zo kuma dukkan tsarkaka zasu kasance tare dashi. 6 A wannan ranar da ba za a sami haske ba, babu sanyi ko ƙanƙara. 7 A wannan ranar, Yahweh kaɗai ya san ta, ba za a sake yin rana ko dare ba, gama maraice za ya zama lokacin haske. 8 A wannan rana ruwayen rai za su ɓulɓulo daga Yerusalem. Rabin ruwan za shi yi gudu zuwa tekun gabas rabin kuwa zuwa tekun yamma, damina da lokacin sanyi. 9 Yahweh zai zama sarki a bisa dukkan duniya. A wannan rana Yahweh kaɗai zai zama, Allah ɗaya, babu wani suna sai na sa. 10 Dukkan ƙasa za ta zama kamar Arabah, daga Geba har zuwa Rimon kudu da Yerusalem. Yerusalem zata ci gaba da haurawa bisa a mazamninta, daga Ƙofar Benyamin zuwa inda kofar ta ke a dã, zuwa Ƙofar Kusurwa, kuma zuwa Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsewar ruwan inabin sarki. 11 Mutane zasu zauna cikin Yerusalem kuma babu sauran hallaka da zata zo gare su daga wurin Allah. Yerusalem zata zauna cikin kariya. 12 Wannan ita ce annobar da Yahweh zai hari dukkan al'umman da suka tayarwa Yerusalem da yaƙi: Naman jikinsu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye bisa sawayensu. Idanunsu zasu ruɓe cikin kwarminsu kuma harsunansu zasu ruɓe daga cikin bakunansu. 13 A wannan rana babban tsoro daga Yahweh za shi abko masu. Kowannensu zai kama hannun wani, kuma hannun wani zai ɗaga hannunsa domin tsayayya da hannun wani. 14 Yahuda kuma zai yi yaƙi da Yerusalem. Zasu tara dukiya daga al'umman dake zagaye dasu - zinariya, da azurfa da kuma kyawawan riguna tuli. 15 Annoba zata faɗo wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakai, da dukkan dabbobin da suke a sansaninsu zasu wahala da wannan annobar. 16 Za shi zama kuma dukkan waɗanda suka rage cikin ƙasashen da suka zo yaƙi da Yerusalem a maimako zasu zo kowacce shekara domin su yi wa sarki sujada, Yahweh mai runduna, sụ kuma kiyaye Idin Bukkoki. 17 Za shi zama kuma idan wani daga cikin al'umman duniya ya kasa zuwa Yerusalem don ya yi sujada ga sarki, Yahweh mai runduna, daga nan Yahweh kuma ba zai aiko masu da ruwan sama ba. 18 Idan al'ummar Masar basu je ba, to ba zasu sami ruwan sama ba. Annoba daga Yahweh zata abko wa duk mutanen dasu ka ƙi zuwa domin su yi Bikin Idin Bukkoki. 19 Wannan zai zama horon da za a yi wa Masar da kuma horo ga kowacce al'ummar da ba ta zo Yerusalem ta halarci Bikin Idin Bukkoki ba. 20 Amma a wannan ranar, ƙararrawar dawakai zasu ce, "ku keɓe ga Yahweh," kuma darurrukan da suke gidan Yahweh zasu zama kamar darurruka a gaban bagadi. 21 Gama kowacce tukunya a Yerusalem da Yahuda za a ƙeɓeta ga Yahweh mai runduna kuma duk wanda zai kawo hadaya zai ci daga cikinsu ya kuma tafasa a cikinsu. A wannan rana 'yan kasuwa ba zasu ƙara kasancewa a cikin gidan Yahweh mai runduna ba.

Littafin Malakai
Littafin Malakai
Sura 1

1 Furcin maganar Yahweh ga Isra'ila ta hannun Malakai. 2 "Na ƙaunace ku," inji Yahweh. Amma ku kun ce, "Ta yaya ka ƙaunace mu?" 3 "Ashe Isuwa ba ɗan'uwan Yakubu ba ne?" Yahweh ya furta. "Amma na ƙaunaci Yakubu, na ƙi Isuwa. Na maida tuddansa banza abin ƙi, kuma na maida gãdonsa muhallin diloli na daji." 4 Idan Idomawa suka ce, "An buge mu har ƙasa, amma za mu sake tashi," Yahweh mai runduna zai ce, "Zasu sake tashi kuma su gina, zan kuma sake rushewa. Wasu zasu kirasu, 'Ƙasar masu mugunta' kuma 'Mutanen da Yahweh ya la'anta har abada.' 5 Idanuwanku zasu ga wannan, kuma zaku ce, Yahweh mai girma ne har ma a gaban iyakokin Isra'ila.'" 6 Ɗa yana girmama ubansa, kuma bawa yana girmama ubangijinsa. Idan ni uba ne, ina ku ka girmama ni? Idan ni ubangijinku ne, me yasa ba ku ba ni daraja, inji Yahweh mai runduna ga ku firistoci, da ku ka rena sunana. "Amma kun ce ta yaya mu ka rena sunanka?' 7 Ta wurin miƙa ƙazantacciyar gurasa da kuke kawo wa bagadina. Amma kun ce, "Ta yaya mu ka ƙazantad da kai?"' Ta cewa teburin Yahweh marar daraja ne. 8 A lokacin da kuka miƙa hadayun makafin dabbobi ashe wannan ba mugunta ba ce? Duk lokacin da ku ka miƙa hadayun guragun dabbobi da marasa lafiya, wannan ba mugun abu ba ne? Kwa ba da wannan ga gwamnanku! Zai karɓa ko zaku sami tagomashi a wurinsa?" inji Yahweh mai runduna. 9 Yanzu kuna ta neman fuskar Allah, domin ya yi mana alheri. Amma Yahweh mai runduna yace da irin wannan baikon a hannunku, zaku sami tagomashinsa? 10 "Kash, ina ma da akwai wani daga cikinku wanda zai rufe ƙofofin haikali, don kada ku kunna wuta akan bagadina a banza! Domin ba na jin daɗinku," inji Yahweh mai runduna, "kuma ba zan karɓi kowanne baiko daga hannunku ba. 11 Daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta sunana zai zama da girma a cikin al'ummai a dukkan wuraren da ake ƙona turare da kuma baye-baye masu tsabta da za a miƙa da sunana. Domin sunana zai zama da girma a cikin al'ummai," inji Yahweh mai runduna. 12 Amma kuna ɓata shi sa'ad da kuka ce teburi na Ubangiji ya ƙazance, kuma 'ya'yan itacensa da abincinsa abin reni ne. 13 Kun kuma ce, 'kai wannan abin gajiyarwa ne,' kuma kun wulaƙanta shi," inji Yahweh mai runduna. "kun kawo dabbar da naman daji ya kama ko gurguwa ko marar lafiya; kuma wannan ku ka kawo a matsayin hadayarku. Ko zan karɓi wannan daga hannunku? inji Yahweh. 14 "Bari mayaudari ya zama la'ananne wanda ke da dabba namiji a garkensa kuma ya yi wa'adi zai bayar da ita gare ni, amma duk da haka, Ni da na ke Ubangiji, ya kawo mani hadayar nakasashiya! Gama ni babban sarki ne," inji Yahweh mai runduna, "kuma za a girmama sunana a cikin al'ummai."

Sura 2

1 Yanzu ku firistoci, wannan umurni domin ku ne. 2 "Idan ba zaku saurara ba, kuma in ba zaku yi niyya a zuciyarku ku bani girma ba," inji Yahweh mai runduna, "lallai zan aiko da la'ana zuwa gare ku, kuma zan la'anta albarkunku. Hakika, na la'antar da su, domin ba ku sa dokokina a zuciyarku ba. 3 Duba, ina shirin tsauta wa zuriyarku, kuma zan watsa kashin dabbobi a fuskokinku, wato kashin dabbobin bukukuwanku, kuma zan kore ku daga gare ni. 4 Za ku sani cewa ni na aiko da wannan umarni gare ku, kuma alƙawarina zai ci gaba da kasancewa tare da Lebi," inji Yahweh mai runduna. 5 Alƙawarina da shi na rai da salama ne, kuma ni na ba dasu gare shi; Na sa ya girmama ni, kuma ya ji tsoro na, kuma ya darajanta sunana. 6 Umurnin gaskiya ya kasance a bakinsa, kuma ba a sami ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya da ni a cikin salama da daidaituwa kuma ya juyo da yawa ga tuba daga zunubi. 7 Domin ya kamata leɓunan firist su kasance da sani kuma mutane su nemi koyarwa daga bakinsa, domin shi ɗan saƙon Yahweh mai runduna ne. 8 Amma kun kauce daga hanyar gaskiya. Kun sa da yawa sun yi tuntuɓe game da koyarwar shari'a. Kun karya alƙawarin Lebiyawa," inji Yahweh mai runduna. 9 Haka ni ma na maishe ku marasa daraja kuma abin reni ga dukkan mutane, domin baku bi hanyoyina ba, maimakon haka kuka nuna son kai game da abin da aka umurta." 10 Ashe dukkanmu ba uba ɗaya muke ba? Ba Allah ɗaya ne ya hallicce mu ba? Me ya sa muka zama marasa aminci kowanne ga ɗan'uwansa, mu na ƙazantar da alƙawarin iyayenmu? 11 Yahuda ya kasance marar aminci. An aikata mummunan abu cikin Isra'ila da Yerusalem. Gama Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Yahweh da yake ƙauna, kuma ya aure 'yar baƙon allah. 12 Bari Yahweh ya datse irin wannan mutum daga alfarwar Yakubu, ko wane ne shi, ko da ma mai kawo hadaya ga Yahweh mai runduna ne. 13 Kuna kuma yin wannan: wato kuna rufe bagadin Yahweh da hawaye da kuka da ajiyar zuciya, domin ba ya kula da hadayunku ko karɓar su daga hannunku da tagomashi. 14 Amma ku ka ce "Don me ya ƙi?" Domin Yahweh shaida ne tsakaninka da matarka ta ƙuruciya, wadda ka yi mata rashin aminci, ko da yake abokiyar tarayyarka ce da matarka ta alƙawari. 15 Ba shi ne ya yi su ɗaya daga ruhunsa ba? To me yasa ya maishe ku ɗaya? Saboda ya na neman 'ya'ya daga Allah. Don haka ku lura da kanku a cikin ruhunku, kada ka zama marar aminci ga matarka ta ƙuruciya. 16 "Gama na ƙi kisan aure," inji Yahweh, Allah na Isra'ila, "da kuma wanda ya rufe tufafinsa da husuma," inji Yahweh mai runduna. "To sai ku yi lura da kanku cikin ruhu don kada ku zama marasa aminci." 17 Kun gajiyar da Yahweh da maganganunku. Amma kun ce "Ta yaya muka gajiyar da shi?" Ta cewa "Duk wanda ya yi mugunta managarci ne a idanun Yahweh, kuma yana jin daɗin su, ko "Ina Allah na adalci?"

Sura 3

1 "Duba, na kusa aiko da manzona, kuma zai shirya mani hanya a gabana. Sa'an nan Ubangiji da kuke nema, zai zo haikalinsa ba zato. Manzon da aka alƙawarta, da kuke farinciki da shi, duba, zai zo," inji Yahweh mai runduna. 2 Amma wa zai jure ranar zuwansa? Wa zai iya tsayawa sa'ad da ya bayyana? Domin zai zama kamar wutar maƙera, kamar sabulun wanki. 3 Zai zama kamar mataci mai tace azurfa, zai tsarkake 'ya'yan Lebiyawa. Zai tace su kamar zinariya da azurfa, sa'an nan ne zasu kawo baikon adalci ga Yahweh. 4 Sa'an nan ne baikon Yahuda da na Yerusalem zai gamshi Yahweh, kamar a kwanakin dă, a shekarun baya. 5 "Sa'an nan zan zo gare ku domin hukunci. Nan da nan zan zama shaida gãba da masu sihiri, da mazinata, da masu shaidar zur, da masu zaluntar ma'aikata wajen albashinsu, da masu cutar gwauraye, da marayu, da masu korar baƙi, da marasa girmama ni," inji Yahweh mai runduna. 6 Domin ni Yahweh ban canza ba; saboda haka ne ku 'zuriyar Yakubu ba ku ƙare ba. 7 Tun daga zamanin ubanninku kun kauce daga bin farillaina ba ku kuma kiyaye su ba. Ku dawo gare ni, ni ma zan dawo gare ku," inji Yahweh mai runduna, "Amma kun ce, 'Ƙaƙa zamu dawo?' 8 Mutum zai iya yi wa Allah fashi? Duk da haka kuna yi mani fashi. Amma kun ce, 'Ta yaya muka yi maka fashi?' A zakkoki da baye-baye. 9 La'anannu ne ku da la'ana, domin kuna yi mani fashi, dukkan al'umma. 10 Ku kawo dukkan zakka a cikin ma'aji, domin a sami abinci a cikin gidana, ku gwada ni a wannan," inji Yahweh mai runduna, "idan ba zan buɗe maku tagogin sama, in zubo da albarku a kan ku, har ba wurin tara su. 11 Zan kwaɓi masu ɓarnata maku amfani domin su dena lalatar maku da amfanin ƙasarku. Gonakin inabinku ba zasu kakkaɓe 'ya'yansu ba, inji Yahweh mai runduna. 12 "Dukkan al'ummai zasu ce da ku masu albarka. Zaku zama ƙasa mai ban sha'awa," inji Yahweh mai runduna. 13 "Maganganunku a kaina suna da ƙarfi," inji Yahweh. "Amma kuka ce, 'Me muka ce a tsakaninmu gãba da kai?' 14 Kun ce, "Ba amfani a bauta wa Allah. Wacce riba ce muka samu da yin biyayya da dokokinsa ko kuma da tafiya rai ɓace a gaban Yahweh mai runduna? 15 Yanzu muna kiran masu girman kai masu albarka. Masu aikata mugunta bama azurta kaɗai suke ba, amma har ma suna gwada Allah su kuɓuta."' 16 Sai waɗanda ke jin tsoron Yahweh suka yi magana da junansu. Yahweh kuma ya ji su ya saurare su, sai aka rubuta littafin tunawa a gabansa game da waɗanda ke jin tsoron Yahweh masu girmama sunansa. 17 "Zasu zama nawa," inji Yahweh mai runduna, dukiyata mai tamani, a ranar da zan yi wannan. Zan yi masu jinƙai, kamar yadda uba ya kan yi wa ɗansa jinƙai wanda yake bauta masa. 18 Sa'an nan ne kuma zaku bambance tsakanin adalai da miyagu da tsakanin masu bauta wa Allah da marasa bauta masa.

Sura 4

1 Duba rana na zuwa, mai ƙuna kamar tanderu, inda dukkan masu girman kai da masu aikata mugunta zasu zama tattaka. Ranar dake zuwa zata ƙone su, "inji Yahweh mai runduna, "Baza ta bar masu tushe ko reshe ba" 2 Amma a gare ku ku dake tsoron sunana, ranar adalci zata fito da warkarwa a fukafukanta. Zaku fita, ku yi ta tsalle kamar 'yan maruka a dangwali. 3 A wannan rana zaku tattake mugaye, zasu zama tattaka a ƙarƙashin sawayenku a ranar da zan aikata wannan", inji Yahweh mai runduna. 4 "Ku tuna da koyarwar bawana Musa wadda na ba shi a Horeb domin dukkan Isra'ila, farillai ne da dokoki. 5 Duba, zan aiko ma ku da annabi Iliya kafin babbar ranar nan mai tsoratar wa ta Yahweh. 6 Zai juyar da zuciyar ubanni zuwa wajen 'ya'ya, da zuciyar 'ya'ya zuwa ga ubanninsu, domin kada in kawo hari in hallakar da ƙasar ɗungum."

Matiyu
Matiyu
1

1 Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. 2 Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. 3 Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. 4 Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. 5 Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, 6 Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya. 7 Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. 8 Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya. 9 Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. 10 Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. 11 Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. 12 Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel. 13 Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. 14 Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu 15 Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. 16 Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. 17 Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne 18 Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19 Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce. 20 Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, "Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. 21 Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu." 22 Duk wannan ya faru ne domin a cika abinda aka fada ta bakin annabin, cewa, 23 "Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel"-ma'ana, "Allah tare da mu." 24 Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. 25 Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu.

2

1 Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2 "Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada." 3 Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. 4 Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, "Ina za a haifi Almasihun?" 5 Suka ce masa, "A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, 6 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'" 7 Sai Hirudus ya kira masanan a asirce ya tambaye su aininhin lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Ya aike su Baitalami, ya ce, "Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada." 9 Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi matukar farin ciki. 11 Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur. 12 Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. 13 Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, "Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi." 14 A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar. 15 Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, "Daga Masar na kirawo Da na." 16 Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. 17 A lokacin ne aka cika fadar Annabi Irmiya, 18 "An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. 19 Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce, 20 "Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu." 21 Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila. 22 Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili 23 sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.

3

1 A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa, 2 "Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa." 3 Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, "Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa." 4 Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji. 5 Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa. 6 Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu. 7 Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, "Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? 8 Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku. 9 Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. 10 Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta. 11 Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 12 Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba." 13 Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. 14 Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, "Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?" 15 Yesu ya amsa masa ya ce, "Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci." Sai Yahaya ya yarje masa. 16 Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa. 17 Duba, wata murya daga sammai tana cewa, "Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai."

4

1 Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. 2 Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3 Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa." 4 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, "A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'" 5 Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, 6 ya ce masa, "In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.'" 7 Yesu ya ce masa, "kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'" 8 Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce masa, "Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada." 10 Sai Yesu ya ce masa, "Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'" 11 Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima. 12 To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili. 13 Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali. 14 Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa, 15 "Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! 16 Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu." 17 Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, "Ku tuba domin mulkin sama ya kusa." 18 Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 19 Yesu ya ce masu, "Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane." 20 Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi. 21 Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. 22 Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi. 23 Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. 24 Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su. 25 Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.

5

1 Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. 2 Ya bude bakinsa kuma ya koyar da su, yana cewa, 3 "Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne. 4 Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su. 5 Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. 6 Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su. 7 Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai. 8 Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah. 9 Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah. 10 Albarka ta tabbata ga wadanda ake tsananta masu saboda adalci, domin mulkin sama nasu ne. 11 Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni. 12 Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku. 13 Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane. 14 Ku ne hasken duniya, birnin da ke kan tudu ba shi boyuwa. 15 Mutane ba za su kunna fitila su sa ta karkashin kwando ba, sai ko a dora ta a mazaunin ta, domin ta ba da haske ga kowa da ke gidan. 16 Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama. 17 Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su. 18 Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura. 19 Saboda haka duk wanda ya karya mafi kankanta daga cikin dokokin nan ko kuwa ya koya wa wasu su yi haka, za a kira shi mafi kankanta a cikin mulkin sama. Amma dukan wanda ya kiyaye su ko kuwa ya koyar da su, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama. 20 Gama ina gaya maku cewa idan adalcin ku bai zarce adalcin marubuta da Farisawa ba, babu yadda za ku shiga mulkin sama. 21 Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.' 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. 23 Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai, 24 ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon. 25 Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku. 26 Gaskiya ina gaya maka, ba za ka taba fita daga can ba sai ko ka biya dukan kudin da ya ke binka. 27 Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'. 28 Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa. 29 Idan idonka na dama zai sa ka tuntube, kwakule shi ka jefar daga gareka. Don gara daya daga cikin gabobinka ya halaka, da a jefa dukan jikin ka a jahannama. 30 Ko kuwa idan hannunka na dama zai sa ka tuntube, ka yanke shi ka jefar daga gare ka. Domin gara daya daga cikin gabobin ka ya halaka, da a jefa dukan jikinka a jahannama. 31 An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' 32 Amma ina gaya maku ko wa ya saki matarsa, idan ba a kan laifin lalata ba, ya mai da ita mazinaciya kenan. Kuma duk wanda ya aure ta bayan sakin, ya yi zina kenan. 33 Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.' 34 Amma ina gaya maku, kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama domin kursuyin Allah ne; 35 ko kuwa da duniya, domin mazaunin kafafunsa ne, ko da Urushalima, domin birnin babban sarki ne. 36 Ko ma ace ku yi rantsuwa da kanku, domin ba za ku iya mai da gashin kanku baki ko fari ba. 37 Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. 38 Kun dai ji an ce, "Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.' 39 Amma ina gaya maku, kada ku yi jayayya da wanda ke mugu, a maimakon haka, ko wa ya mare ku a kuncin dama, ku juya masa dayan ma. 40 Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma. 41 Duk wanda ya tilasta ku ga tafiyar mil daya, ku je da shi biyu. 42 Ku ba kowa da ya tambaye ku, kuma kada ku hana kowa da ke neman rance a wurinku. 43 Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.' 44 Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku, 45 domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi. 46 Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba? 47 Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba? 48 Saboda haka, lalle ne ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.

6

1 Ku yi hankali kada ku yi ayyukan adalcinku gaban mutane domin su ganku, idan kun yi haka, ba za ku sami sakamako a wurin Ubanku da yake sama ba. 2 Saboda haka, in za ku yi sadaka, kada ku busa kaho yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma akan tituna domin mutane su yabesu. Gaskiya ina gaya maku, sun samu ladansu. 3 Amma in za ku yi sadaka, kada hannunku na hagu ya san abin da hannunku na dama yake yi, 4 domin sadakarku ta zama a asirce. Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. 5 Sa'adda za ku yi addu'a kuma, kada ku zama kamar munafukai, domin sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'unsu da kuma a gefen tituna, domin mutane su gansu. Gaskiya ina gaya maku, sun sami ladarsu kenan. 6 Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. 7 Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu. 8 Domin haka, kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatar ku tun kafin ku roke shi. 9 Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka. 10 Bari mulkinka shi zo. Bari nufinka ya yiwu a duniya kamar yadda ake yi a sama. 11 Ka ba mu yau abincinmu na kullum. 12 Ka gafarta mana basussukanmu, kamar yadda mu ma muke gafarta ma wadanda muke bi bashi. 13 Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' 1 14 Domin in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na Sama shima zai yafe maku. 15 In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba." 16 Haka kuma, in za ku yi azumi, kada ku zama da fuska kamar masu makoki yadda munafukai ke yi, domin sukan yankwane fuskokinsu, domin su bayyana ga mutane kamar suna azumi. Gaskiya, ina gaya maku, sun sami ladansu ke nan. 17 Amma in kuna azumi, ku shafa mai a ka, ku kuma wanke fuska, 18 don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku." 19 "Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke batawa, inda barayi kuma ke fasawa su yi sata. 20 Maimakon haka, ku tara wa kanku dukiya a sama, inda babu asu da tsatsa da za su bata, inda kuma ba barayi da za su fasa su yi sata. 21 Domin inda dukiyar ka take, a nan zuciyar ka ma take. 22 Ido shi ne fitilar jiki. Saboda haka, idan idonka na da kyau, dukan jiki na cike da haske. 23 Amma in idonka na da lahani, dukan jiki na cike da duhu. Saboda haka, in hasken da yake cikinka duhu ne, ina misalin yawan duhun! 24 Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya, ko kuma ya amince wa dayan ya raina dayan. Ba dama ku bauta wa Allah da kuma dukiya. 25 Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba? 27 Kuma wanene a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko taki ga tsawon rayuwarsa? 28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya. 29 Duk da haka ina gaya maku, ko Sulaimanu ma, cikin dukan daukakar sa bai yi ado kamar daya daga cikin wadannan ba. 30 Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya? 31 Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' 32 Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Amma ku nemi mulkinsa da farko da adalcinsa, kuma dukan wadannan abubuwa za a baku. 34 "Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe za ta damu da kanta. Kowace rana ta na cike da wahalarta".


1Mafi kyawun kwafin kwafi ba su da Gama mulki da iko da daukaka naka ne har abada. Amin .

7

1 Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku. 2 Mudun da kukan auna, da shi za a auna maku. 3 Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? 4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? 5 Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka. 6 Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku. 7 Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku. 8 Ai duk wanda ya roka, zai karba, kuma duk wanda ya nema zai samu, wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa. 9 Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji? 11 Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? 12 Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa. 13 Ku shiga ta matsattsiyar kofa, don kofar zuwa hallaka na da fadi, hanyar ta mai saukin bi ce, masu shiga ta cikin ta suna da yawa. 14 Domin kofar zuwa rai matsattsiya ce, hanyar ta mai wuyar bi ce, masu samun ta kuwa kadan ne. 15 Ku kula da annabawan karya, wadanda su kan zo maku da siffar tumaki, amma a gaskiya kyarketai ne masu warwashewa. 16 Za ku gane su ta irin "ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? 17 Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. 18 Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba. 19 Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20 Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su. 21 Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama. 22 A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' 23 Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' 24 Saboda haka, dukan wanda yake jin maganata, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidan sa a bisa dutse. 25 Da ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fadi ba, domin an gina shi bisa dutse. 26 Amma duk wanda ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutum da ya gina gidansa a kan rairayi. 27 Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa." 28 Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29 Domin yana koya masu da iko, ba kamar marubuta ba.

8

1 Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi. 2 Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, "Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni." 3 Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, "Na yarda, ka tsarkaka." Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. 4 Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? 5 Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi, 6 Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai." 7 Yesu ya ce masa, "Zan zo in warkar da shi." 8 Sai hafsan, ya ce, "Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke. 9 Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi," 10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, "Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. 11 Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. 12 Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora." 13 Yesu ya ce wa hafsan, "Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi," A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. 14 Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi. 15 Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima. 16 Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17 Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, "Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu." 18 Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. 19 Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, "Malam, zan bi ka duk inda za ka je." 20 Yesu ya ce masa, "Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta." 21 Wani cikin almajiran ya ce masa, "Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina." 22 Amma Yesu ya ce masa, "Bari matattu su binne matattunsu." 23 Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24 Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, "Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!" 26 Yesu ya ce masu, "Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?" Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. 27 Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, "Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?". 28 Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. 29 Sai suka kwala ihu suka ce, "Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?" 30 To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su. 31 Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, "In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan." 32 "Yesu ya ce masu, "To, ku je." Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. 33 Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun. 34 Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.

9

1 Yesu ya shiga jirgi ya haye ya je birninsa. 2 Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka." 3 Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, "Wannan mutum sabo yake yi." 4 Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, "Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? 6 Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya,..." Sai ya ce wa shanyayyen, "Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida." 7 Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida. 8 Da taron suka ga haka sai suka yi mamaki, suka daukaka Allah, wanda ya ba mutane irin wannan iko. 9 Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, "Ka biyo ni." Ya tashi ya bi shi. 10 Sa'adda kuma Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. 11 Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, "Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?" 12 Amma da Yesu ya ji haka ya ce, "Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 13 Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi. 14 Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, "Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?" 15 Sai Yesu ya ce masu, "Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi." 16 Babu mutumin da zai sa sabon kyalle a kan tsohuwar tufa, domin kyallen zai yage daga tufar, har ma yagewar ta fi ta da. 17 Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan." 18 Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, "Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu." 19 Sai Yesu ya tashi ya bi shi tare da almajiransa. 20 Sai ga kuma wata mace wadda ta yi shakaru goma sha biyu tana zubar da jini sosai, ta rabo ta bayan Yesu, ta taba gezar mayafinsa. 21 Domin ta ce a ran ta, "Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke." 22 Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '"Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke." Nan take matar ta warke. 23 Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya sosai. 24 Sai ya ce, "Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi." Sai suka yi masa dariyar raini. 25 Sa'adda aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta shi. 26 Labarin kuwa ya bazu a duk yankin. 27 Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, "Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu." 28 Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, "Kun gaskata ina da ikon yin haka?" Sai suka ce masa. "I, ya Ubangiji." 29 Sai Yesu ya taba idanunsu, ya ce, "Ya zama maku gwargwadon bangaskiyarku." 30 Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, "Kada fa kowa ya ji labarin nan." 31 Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk yankin. 32 Da makafin biyu suka tafi, sai aka kawo wa Yesu wani bebe mai aljani. 33 Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, "Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!" 34 Amma sai Farisawa suka ce, "Ai, da ikon sarkin aljanu ya ke fitar da aljanu." 35 Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala kuma sun karaya. Suna nan kamar tumaki da babu makiyayi. 37 Sai ya ce wa almajiransa, "Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne. 38 Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa."

10

1 Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da kazaman ruhohi, su warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya. 2 To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; 3 Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; 4 Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi. 5 Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, "Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6 Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila. 7 Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta. 9 Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku. 10 Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa. 11 Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi. 12 In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku. 13 Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku. 14 Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku. 15 Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. 16 "Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi. 17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu. 18 Za su kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku bada shaida a gabansu, da kuma gaban al'ummai. 19 Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin. 20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21 Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su. 22 Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira. 23 In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. 24 Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa. 25 Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! 26 Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28 Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama. 29 Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. 30 Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake. 31 Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa. 32 "Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama. 33 Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama." 34 "Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35 Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. 36 Zai zama na kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37 Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38 Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39 Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne. 40 "Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan. 41 Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci. 42 Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba."

11

1 Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi. 2 Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa. 3 Ya ce masa. "Kai ne mai zuwa"? ko mu sa ido ga wani. 4 Yesu ya amsa ya ce masu, "Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji. 5 Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara. 6 Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni. 7 Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, "Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? 8 Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna. 9 Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. 10 Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'. 11 Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12 Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi. 13 Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya. 14 kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo. 15 Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji. 16 Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna 17 suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba. 18 Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, "Yana da aljannu". 19 Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. 20 Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba. 21 "Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. 22 Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku. 23 Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. 24 Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku." 25 A wannan lokaci Yesu ya ce, "Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. 26 I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka. 27 An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa. 28 Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa. 29 Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi."

12

1 A wannan lokaci, Yesu ya tafi a ranar Asabaci, ya bi cikin gonar hatsi. Almajiransa na jin yunwa, sai suka fara zagar hatsi suna ci. 2 Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. "Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci." 3 Amma Yesu ya ce masu, "Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? 4 Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci? 5 Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba? 6 Amma ina tabbatar maku da cewa, wani wanda ya fi haikali girma yana nan. 7 In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. 8 Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci." 9 Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su. 10 Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, "Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?" Domin su zarge shi a kan zunubi. 11 Yesu ya ce masu, "Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba? 12 Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci." 13 Sai Yesu ya ce wa mutumin nan "Mika hannun ka." Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa. 14 Amma Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri domin sa. Su na neman hanyar da za su kashe shi. 15 Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka. 16 Ya dokace su da kada su bayyana shi ga kowa, 17 domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa, 18 "Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai. 19 Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku. 20 Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara. 21 Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa. 22 Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana. 23 Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, "Ko wannan ne Dan Dawuda?" 24 Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, "Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne." 25 Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. "Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe. 26 Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya? 27 Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. 28 Amma idan ina fitar da aljannu da Ruhun Allah ne, hakika mulkin Allah ya zo gare ku. 29 Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa. 30 Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne. 31 Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba. 32 Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada. 33 Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa. 34 Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana. 35 Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta. 36 Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi. 37 Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku." 38 Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, "Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka." 39 Amma Yesu ya amsa ya ce masu, "Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa. 40 Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa. 41 Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan. 42 Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan. 43 Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba. 44 Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta. 45 Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani. 46 Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi. 47 Sai wani ya ce masa, "Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai". 48 Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, "Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?" 49 Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, "Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana! 50 Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata."

13

1 A waccan rana Yesu ya fito daga gida ya zauna a gefen teku. 2 Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun. 3 Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, "Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka. 4 Da yayi shukar, wadansu irin suka fadi a kan hanya, sai tsunsaye suka zo suka cinye su. 5 Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi. 6 Amma da rana ta taso, sai suka yankwane domin ba su yi saiwa ba, suka kuwa bushe suka zube. 7 Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su. 8 Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin. 9 Duk mai kunnen ji, bari ya ji. 10 Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, "Don me ka ke yi wa taron magana da misali?" 11 Yesu ya amsa ya ce masu, "An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba. 12 Domin wanda yake da shi, za a kara masa, zai kuma samu dayawan gaske. Amma duk wanda ba shi da shi, sai a dauke har ma abin da yake dashi. 13 Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta. 14 A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, "Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. 15 Domin zuciyar mutanen nan ta duhunta, sun taurare ga saurare, kuma sun rufe idanunsu domin kada su gani da idanunsu, ko kuwa su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zukatansu, saboda su juyo kuma in warkar da su'. 16 Amma idanunku masu albarka ne, domin sun gani, haka ma kunnuwanku, domin sun ji. 17 Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba. 18 Ku saurari misalin nan na mai shuka. 19 Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya. 20 Shi wanda aka shuka akan duwatsu, shine wanda ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan. 21 Duk da haka, bai yi karfi cikin ta ba kuma nan ba da dadaiwa ba. Da wahala da tsanani suka taso saboda maganar, sai ya yi tuntube nan da nan. 22 Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. 23 Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin." 24 Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa "Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona. 25 Amma da mutane suka yi barci, magabcin sa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar, ya kuwa yi tafiyarsa. 26 Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana. 27 Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi? 28 Ya ce masu, "Magabci ne ya yi wannan". Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' 29 Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar. 30 Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, "Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'" 31 Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa "Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa. 32 Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa." 33 Yesu ya sake fada masu wani misali. "Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi." 34 Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba. 35 Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, "Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya." 36 Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, "Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar" 37 Yesu ya amsa kuma ya ce, "Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne. 38 Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun, 39 magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. 40 Saboda haka, kamar yadda aka tara ciyayin aka kona su da wuta, haka ma zai faru a karshen duniya. 41 Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta. 42 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 43 Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji. 44 Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin. 45 Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja. 46 Da ya sami lu'ulu'u daya mai darajar gaske, ya je ya sayar da dukan mallakarsa ya kuma saye shi. 47 Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri. 48 Da ya cika, sai masuntan suka jawo shi bakin tekun. Sai suka zauna suka tara kyawawan abubuwan a taska, amma munanan abubuwan, suka watsar da su. 49 Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. 50 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 51 Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, "I". 52 Sai Yesu ya ce masu, "Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa." 53 Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin. 54 Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, "Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai? 55 Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba? 56 Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa? 57 Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, "Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa. 58 Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

14

1 A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu. 2 Ya ce wa barorinsa, "Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa". 3 Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus. 4 Ya ce masa, "Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba." 5 Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi. 6 Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus. 7 Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta. 8 Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, "Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire. 9 Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka. 10 Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku. 11 Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta. 12 Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu. 13 Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen. 14 Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu. 15 Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, "Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci." 16 Amma Yesu ya ce masu, "Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci." 17 Suka ce masa, "Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai." 18 Yesu ya ce, "Ku kawo mani su." 19 Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron. 20 Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike. 21 Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara. 22 Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. 23 Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai. 24 Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su. 25 Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku. 26 Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, "Fatalwa ce," suka yi kururuwa cikin tsoro. 27 Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, "Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro." 28 Bitrus ya amsa masa cewa, "Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan." 29 Yesu yace, "Zo" Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu. 30 Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, "Ubangiji, ka cece ni!" 31 Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, "Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?" 32 Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa. 33 Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, "Hakika kai Dan Allah ne." 34 Da suka haye, sun iso kasar Janisarata. 35 Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya. 36 Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.

15

1 Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce, 2 "Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci." 3 Yesu ya amsa masu ya ce, "Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku? 4 Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu. 5 Amma kun ce, "Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, "Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'" 6 wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku. 7 Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce, 8 " Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni. 9 Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu." 10 Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, "Ku saurara ku fahimta, 11 ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum." 12 Sai al'majiran suka zo suka ce masa, "Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?" 13 Yesu ya amsa ya ce, "Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta. 14 Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami." 15 Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, "Ka bayyana wannan misali a garemu," 16 Yesu ya ce, "Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? 17 Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga? 18 Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. 19 Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage. 20 Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum." 21 Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon. 22 Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce," Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani." 23 Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, "Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu." 24 Amma Yesu ya amsa ya ce, "Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila." 25 Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, "Ubangiji ka taimake ni." 26 Ya amsa ya ce, "Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka. 27 Ta ce, "I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida." 28 Sai Yesu ya amsa ya ce mata, "Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so." 'Yarta ta warke a lokacin. 29 Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can. 30 Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su. 31 Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila. 32 Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, "Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya." 33 Almajiran suka ce masa, "A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan." 34 Yesu ya ce masu, "Gurasa nawa ku ke da ita?" Suka ce, "Bakwai da 'yan kifi marasa yawa." 35 Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa. 36 Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron. 37 Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike. 38 Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara. 39 Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.

16

1 Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama. 2 Amma ya amsa ya ce masu, "Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' 3 Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba. 4 Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa." Daga nan sai Yesu ya tafi. 5 Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa, 6 Yesu ya ce masu, "Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa." 7 Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, "Ko saboda bamu kawo gurasa bane." 8 Yesu yana sane da wannan sai ya ce, "Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? 9 Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba? 10 Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba? 11 Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa." 12 Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa. 13 A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, "Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? 14 Suka ce, "Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa." 15 Ya ce masu, "Amma ku wa kuke ce da ni?" 16 Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai." 17 Yesu ya amsa ya ce masa, "Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama. 18 Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. 19 Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama," 20 Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu. 21 Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku. 22 Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, "Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba." 23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, "Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane." 24 Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, "Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni. 25 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi. 26 Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa? 27 Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa. 28 Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa."

17

1 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai. 2 Kamanninsa ya canja a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli fal. 3 Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi. 4 Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya." 5 Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, "Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi." 6 Da almajiran suka ji haka, suka fadi da fuskokinsu a kasa, saboda sun tsorata. 7 Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, "Ku tashi, kada ku ji tsoro." 8 Amma da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kadai. 9 Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, "Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu." 10 Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, "Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?" 11 Yesu ya amsa ya ce, "Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. 12 Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. 13 Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne. 14 Da suka iso wurin taron, wani mutum ya zo gunsa, ya durkusa a gaban sa, ya ce, 15 "Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa. 16 Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba." 17 Yesu ya amsa ya ce, "Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina." 18 Yesu ya tsauta masa, sai aljanin ya fita daga cikinsa. Yaron ya warke nan take. 19 Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, "Me ya sa muka kasa fitar da shi?" 20 Yesu ya ce masu, "Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. 21 1 22 Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, "Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. 23 Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi." Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai. 24 Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, "Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?" 25 Sai ya ce, "I." Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, "Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?" 26 Sai Bitrus ya ce, "Daga wurin baki," Yesu ya ce masa, "Wato an dauke wa talakawansu biya kenan. 27 Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka.


1Mafi kyawun kwafin kwafi ba su da. 21, Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu'a da azumi .

18

1 Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, "Wanene mafi girma a mulkin sama?" 2 Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu, 3 ya ce, "Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama. 4 Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni. 6 Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku. 7 Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo! 8 Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka. 9 Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu. 10 Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama. 11 1 12 Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba? 13 In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba. 14 Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka. 15 Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan. 16 Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da 'yan'uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma. 17 In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji. 18 Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama. 19 Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi. 20 Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su." 21 Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, "Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?" 22 Yesu ya amsa ya ce masa, "Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in. 23 Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa. 24 Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma. 25 Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da 'ya'yansa da duk mallakarsa, domin a biya. 26 Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, "Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba." 27 Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran. 28 Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.' 29 Amma dan'uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.' 30 Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan'uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan. 31 Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka. 32 Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, "Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni. 33 Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?' 34 Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa. 35 Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba."


1Mafi kyawun kwafin Girkanci ba su da jumlar da wasu fassarori suka haɗa da, Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata .

19

1 Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun. 2 Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin. 3 Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, "Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?" 4 Yesu ya amsa ya ce, "Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace? 5 Shi wanda ya yi su kuma ya ce, "Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?" 6 Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba." 7 Sai suka ce masa, "To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?" 8 Sai ya ce masu, "Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba. 9 Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina." 10 Almajiran suka ce wa Yesu, "Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba." 11 Amma Yesu yace masu, "Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta. 12 Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa'annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba." 13 Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu'a, amma almajiran suka kwabe su. 14 Amma Yesu ya ce masu, "Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne." 15 Ya sa hannuwa akan su, sa'annan ya bar wurin. 16 Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, "Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?" 17 Yesu ya ce masa, "Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin." 18 Mutumin ya ce masa, "Wadanne dokokin?" Yesu ya ce masa, "Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur, 19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka." 20 Saurayin nan ya ce masa, "Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?" 21 Yesu ya ce masa, "Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni." 22 Amma da saurayin nan ya ji abin da Yesu ya fada, ya koma da bakin ciki, domin shi mai arziki ne kwarai. 23 Yesu ya ce wa almajiransa, "Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama. 24 Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah." 25 Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, "Wanene zai sami ceto?" 26 Yesu ya dube su, ya ce, "A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne." 27 Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, "Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?" 28 Yesu ya ce masu, "Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila. 29 Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, mahaifi, mahaifiya, 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. 30 Amma dayawa dake farko yanzu, za su zama na karshe, dayawa dake karshe kuma, su zama na farko.

20

1 Gama mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da asuba ya nemi 'yan kwadago da za su yi aiki a gonarsa. 2 Bayan sun shirya kudin da zai biya ma'aikata kimanin dinari daya a kowanne yini, sai ya aike su gonarsa suyi aiki. 3 Misalin sa'a ta uku sai ya sake fita, sai ya ga wasu ma'aikata suna tsaye a bakin kasuwa, babu aiki. 4 Sai ya ce masu, 'Kuzo kuyi aiki a gonar, duk abinda ya wajaba, zan ba ku,' Sai suka tafi su yi aikin. 5 Sai ya sake fita a sa'a ta shida ya kuma sake fita a sa'a ta tara, ya sake yin hakan din. 6 Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?' 7 Sai suka ce masa, 'Ai babu wanda ya dauke mu aiki, shi yasa.' Sai ya ce masu, 'ku ma, kuje cikin gonar. 8 Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa manajansa, 'Ka kira ma'aikatan nan ka biya su hakkin su, amma ka fara da wadanda suka zo a karshe, zuwa na farkon.' 9 Sa'adda wadanda suka fara aiki da yamma suka zo, an biya su daidai yadda ake biya a yini. 10 Da wadanda suka fara aiki tun safe suka zo, suna tsammani za a ba su fiye da wadanda sun zo daga baya, amma aka ba kowannensu dinari daya. 11 Da suka karbi hakkinsu, suka yi gunaguni game da mai gonar. 12 Suka ce, 'Wadannan da suka zo a karshe, sa'a guda ce kadai suka yi aiki, amma ka ba su daidai da mu, mu da muka yi fama da aiki cikin zafin rana.' 13 Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba? 14 Ku karbi abin da ke na ku, ku tafi. Ganin dama ta ne, in ba wadannan da suka zo a karshe daidai da ku. 15 Ashe, ba daidai bane a gare ni, in yi abin da na ga dama da mallaka ta? Ko kishi ne kuke yi saboda kirki na?' 16 Haka yake, na karshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na karshe." 1 17 Da Yesu zai tafi Urushalima, ya dauki sha-biyun nan a gefe, yayin da suke tafiya, sai ya ce masu, 18 "Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa, 19 za su kuma bada shi ga al'ummai don suyi masa ba'a, su bulale shi, su kuma gicciye shi. Amma a rana ta uku, za a tada shi." 20 Sai uwar 'ya'yan Zabadi ta zo wurin Yesu tare da 'ya'yanta. Ta rusuna a gabansa tana neman alfarma a wurinsa. 21 Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?" Sai ta ce masa, "Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka. 22 Amma Yesu ya amsa, ya ce, "Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?" Sai suka ce masa, "Zamu iya." 23 Sai ya ce masu, "In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne." 24 Sa'anda sauran almajirai goma suka ji haka, sun yi bacin rai da 'yan'uwan nan biyu. 25 Amma Yesu ya kira su wurin sa, ya ce, "Kuna sane da cewa, sarakunan al'ummai suna gwada masu mulki, manyan-gari kuma na nuna masu iko. 26 Ba zai kasance haka a tsakanin ku ba. A maimakon haka, duk wanda ke da marmari ya zama da girma a tsakanin ku, ya zama baran ku. 27 Wanda kuma ke da marmari ya zama na farko a cikin ku, ya zama baran ku. 28 Kamar dai yadda Dan mutum bai zo don a bauta masa ba, amma yayi bauta, ya kuma bada ransa fansa domin mutane dayawa." 29 Da suka fita daga Yariko, babban taro suka bi shi. 30 Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, "Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai." 31 Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, "Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai." 32 Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, "Me kuke so in yi maku?" 33 Sai suka ce masa, Ya Ubangiji, muna so mu sami ganin gari." 34 Sai Yesu yayi juyayi a cikin sa, ya taba idanunsu. Nan da nan, suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.


1Mafi kyawun kwafin kwafi ba su da An kira dayawa, amma kadan ne zababbu .

21

1 Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu, 2 yace masu, "Ku shiga kauyen da yake gaban ku zaku iske wata jaka da aholaki tara da ita. Ku kwance su ku kawo mani su. 3 Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan." 4 Anyi wannan kuwa domin a cika annabcin anabin. Yace, 5 "Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne." 6 Sai almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7 Suka kawo jakar da dan aholakin, suka sa tufafinsu akai, Yesu kuwa ya zauna akan tufafin. 8 Yawancin jama'a kuwa suka baza tufafinsu akan hanya, wasu kuma suka yanko ganye daga bishiyoyi suka shimfida su a hanya. 9 Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, "Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!" 10 Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, "Wanene wannan?" 11 Sai jama'a suka amsa, "Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili." 12 Sai Yesu ya shiga haikalin. Ya kori duk wadanda ke saye da sayarwa a cikin ikiilisiya. Ya birkice teburan masu canjin kudi da kujerun masu sayar da tantabaru. 13 Ya ce masu, "A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi." 14 Sai makafi da guragu suka zo wurin sa a haikalin, ya warkar da su. 15 Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, "Hossana ga dan Dauda," sai suka ji haushi. 16 Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?" Yesu ya ce masu, "I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?" 17 Sai Yesu ya bar su, ya fice daga birnin zuwa Betaniya ya kwana a wurin. 18 Washegari da safe yayin da yake komawa birnin, sai yaji yunwa. 19 Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, "Kada ki kara yin 'ya'ya har abada." Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. 20 Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, "Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?" 21 Yesu ya amsa yace masu, "Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, "Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance. 22 Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu." 23 Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, "Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?" 24 Yesu ya amsa yace masu, "Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. 25 Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?" Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, "In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' 26 Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne." 27 Sai suka amsa ma Yesu suka ce, "Bamu sani ba." Shi ma yace masu, "Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. 28 Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.' 29 Yaron ya amsa yace, 'bazan yi ba,' amma daga baya ya canza tunaninsa ya tafi. 30 Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba. 31 Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?" Suka ce, "na farkon." Yesu ya ce masu, "Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. 32 Gama Yahaya ya zo maku a hanyar adalci, amma ba ku gaskata da shi ba, a yayinda masu karbar haraji da karuwai suka gaskata da shi. Ku kuwa, bayan kun ga abin da ya faru, baku ma tuba daga baya ba don ku gaskata da shi. 33 Ku saurari wani misalin. Anyi wani mutum, mai gona. Yayi shuka a gonar, ya shinge ta, ya gina ramin matse inabi a cikin gonar, ya kuma gina wata hasumiyar tsaro, sai ya bada hayar gonar ga wadansu manoma. Sai ya tafi wata kasa. 34 Da kakar inabi ta yi, sai ya aiki wadansu bayi su karbo masa amfanin gonar. 35 Amma manoman suka kama bayin, suka doddoki dayan, suka kashe dayan, suka jejjefe dayan da duwatsu. 36 Sai mai gonar ya sake aika wadansu bayinsa da suka fi na farko, amma manoman suka yi masu kamar yadda suka yi wa sauran. 37 Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.' 38 Amma da manoman suka ga dan, sai suka ce a tsakanin su, 'wannan shine magajin. Kuzo, mu kashe shi mu gaji gonar.' 39 Sai suka dauke shi, suka jefar da shi daga cikin gonar, suka kashe shi. 40 To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman? 41 Suka ce masa, "Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna." 42 Yesu yace masu, "Baku taba karantawa a nassi ba," 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?' 43 Saboda haka ina gaya maku, za a karbe mulkin Allah daga wurin ku a ba wata al'umma da zata bada amfaninsa. 44 Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike." 45 Da manyan firistocin da farisawan suka ji wannan misalin, sai suka gane da su yake. 46 Da suka nemi kama shi, sai suka ji tsoron taron, saboda mutanen sun dauke shi annabi.

22

1 Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace, 2 "Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure. 3 Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa. 4 Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, "Ku gaya wa wadanda aka gayyata, "Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren." 5 Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa. 6 Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su. 7 Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su. 8 Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9 Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.' 10 Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki. 11 Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba. 12 Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.' 14 Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba."' 15 Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa. 16 Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, "Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. 17 To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?" 18 Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, "Don me kuke gwada ni, ku munafukai? 19 Ku nuna mani sulen harajin." Sai suka kawo masa sulen. 20 Yesu yace masu, "Hoto da sunan wanene wadannan?" 21 Suka ce masa, "Na Kaisar." Sai Yesu ya ce masu, "To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah." 22 Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi. 23 A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi, 24 cewa, "Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. 25 Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa. 26 Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai. 27 Bayan dukansu, sai matar ta mutu. 28 To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta." 29 Amma Yesu ya amsa yace masu, "Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba. 30 Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama. 31 Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa, 32 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu." 33 Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa. 34 Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu. 35 Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- 36 "Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?" 37 Yesu yace masa, "Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.' 38 Wannan itace babbar doka ta farko. 39 Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' 40 Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya." 41 Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya. 42 Yace, "Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?" Suka ce masa, "Dan Dauda ne." 43 Yesu yace masu, "To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa, 44 "Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka." 45 Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?" 46 Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.

23

1 Sai Yesu yayi wa taron da alamajiransa magana. 2 Ya ce, "Marubuta da Farisawa suna zaune a mazaunin Musa. 3 Don haka, duk abinda suka umarceku kuyi, kuyi wadannan abubuwa ku kuma kiyaye su. Amma kada kuyi koyi da ayyukansu, gama suna fadar abubuwa amma kuma ba su aikata su. 4 I, sukan daura kaya masu nauyi, masu wuyar dauka, daga nan su dauka su jibga wa mutane a kafada. Amma su kan su baza su mika danyatsa ba su dauka. 5 Duk ayyukan su suna yi ne don mutane su gani, suna dinka aljihunan nassinsu da fadi, suna fadada iyakokin rigunansu. 6 Su na son mafifitan wuraren zama a gidan biki, da mafifitan wuraren zama a majami'u, 7 da kuma gaisuwar musamman a wuraren kasuwanci, a kuma rika ce da su 'mallam.' 8 Amma ba sai an kira ku 'mallam, ba' domin malami daya kuke da shi, ku duka kuwa 'yan'uwan juna ne. 9 Kada ku kira kowa 'Ubanku' a duniya, domin Uba daya ne ku ke da shi, kuma yana sama. 10 Kada kuma a kira ku malamai, saboda malamin ku daya ne, shi ne Almasihu. 11 Amma wanda yake babba a cikin ku zaya zama bawanku. 12 Duk wanda ya daukaka kansa za a kaskantar dashi. Duk wanda ya kaskantar da kansa kuma za a daukaka shi. 13 Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba. 14 kaiton ku marubuta da Farisawa, domin kuna hallaka gwauraya - 15 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta. 16 Kaiton ku, makafin jagora, kuda kuke cewa, Kowa ya rantse da Haikali, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, rantsuwarsa ta daure shi.' 17 Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18 Kuma, 'Kowa ya rantse da bagadi, ba komai bane. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka dora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.' 19 Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah? 20 Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagadi, ya rantse da shi da duk abinda ke kansa. 21 Kuma duk wanda ya rantse da Haikali ya rantse dashi da kuma wanda yake cikin sa. 22 Kuma duk wanda ya rantse da sama, ya rantse da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune akai. 23 Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba. 24 Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi! 25 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta. 26 Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka. 27 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri. 28 Haka nan kuke a idanun mutane ku adalai ne, amma a ciki sai munafunci da mugun aiki. 29 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai. 30 Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.' 31 Domin haka kun shaida kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa. 32 Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku! 33 macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta? 34 Saboda haka, duba, ina aiko maku da annabawa, da masu hikima da marubuta. Za ku kashe wadansun su kuma ku gicciye su. Zaku yiwa wasu bulala a majami'un ku, kuna bin su gari gari. 35 Sakamakon hakan alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya ya komo a kan ku, tun daga jinin Habila adali har ya zuwa na Zakariya dan Barakiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikali da bagadi. 36 Hakika, Ina gaya maku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani. 37 Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki. 38 Ga shi an bar maku gidan ku a yashe! 39 Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji."'

24

1 Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali. 2 Amma ya amsa masu yace, "kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba." 3 Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, "me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?" 4 Yesu ya amsa yace dasu, "Ku kula kada wani yasa ku kauce." 5 Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, "ni ne almasihu," kuma za su sa da yawa su kauce. 6 Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna. 7 Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. 8 Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai. 9 Bayan haka za'a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al'ummai za su tsane ku saboda sunana. 10 Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna. 11 Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce. 12 Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi. 13 Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto. 14 Za'a yi wa'azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al'ummai. Daganan karshen zai zo. 15 Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta), 16 bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu, 17 Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa, 18 kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa. 19 Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin! 20 Ku yi addu'a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci. 21 Domin za'ayi tsanani mai girma, wanda ba'a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a'a ba za ayi irin shi ba kuma. 22 In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin. 23 Sa'annan idan wani yace maku, duba, "ga Almasihu a nan!" ko, "ga Almasihu a can!" kar ku gaskata. 24 Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. 25 Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo. 26 Saboda haka, idan suka ce maku, "ga shi a jeji," kar ku je jejin. Ko, "ga shi a can cikin kuryar daki," kar ku gaskata. 27 Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama. 28 Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa. 29 Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza. 30 Sa'annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma. 31 Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen. 32 Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa. 33 Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa. 34 Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru. 35 Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba. 36 Amma game da ranan nan ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai. 37 Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum. 38 A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin, 39 ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su_ haka ma zuwan Dan Mutun zai zama. 40 Sa'annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya. 41 Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar. 42 Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba. 43 Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba. 44 Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa'ar da ba ku yi zato ba. 45 To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci? 46 Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo. 47 Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi. 48 Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, "maigida na ya yi jinkiri," 49 sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya, 50 uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba. 51 Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.

25

1 Sa'annan mulkin sama zai zama kamar budurwai goma da suka dauki fitilunsu domin su taryi ango. 2 Biyar daga cikin su masu hikima ne biyar kuma wawaye. 3 Sa'adda wawayen budurwai suka dauki fitilunsu, ba su dauki karin mai ba. 4 Amma budurwai masu hikimar suka dauki gorar mai tare da fitilunsu. 5 To da angon ya makara, dukkan su sai suka fara gyangyadi sai barci ya dauke su. 6 Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa. 7 Sai dukka budurwan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8 Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.' 9 "Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku. 10 Sa'adda suka tafi sayan man, sai angon ya shigo, kuma wadanda suke a shirye su ka shiga tare da shi bukin auren, sai aka rufe kofar. 11 Bayan dan lokaci kadan sauran budurwan suka dawo suna cewa, 'Mai gida, mai gida, bude mana kofar.' 12 Amma ya amsa ya ce, 'A gaskiya ina gaya maku, ni ban san ku ba.' 13 Don haka sai ku lura, don baku san rana ko sa'a ba. 14 Domin yana kama da wani mutum da zai tafi wata kasa. Ya kira barorinsa ya ba su dukiyar sa. 15 Ga wani ya ba shi talanti biyar, ga wani ya ba shi biyu, ga wani kuma ya ba shi talanti daya. kowa an bashi gwargwadon iyawarsa, sai wannan mutum ya yi tafiyar sa 16 nan da nan sai wanda ya karbi talanti biyar ya sa nasa a jari, ya sami ribar wasu talanti biyar. 17 Haka ma wanda ya karbi talanti biyu ya sami ribar wasu biyu. 18 Amma bawan da ya karbi talanti dayan ya yi tafiyar sa, ya haka rami, ya binne kudin mai gidansa. 19 To bayan tsawon lokaci sai ubangidan barorin nan ya dawo, domin yayi lissafin kudinsu. 20 Bawan da ya karbi talanti biyar, ya kawo nasa da ribar wasu biyar. Yace, 'Maigida, ka bani talanti biyar, gashi na samo ribar karin talanti biyar.' 21 Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' 22 Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.' 23 Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' 24 Sai bawan da ya karbi talanti daya ya zo yace, 'Maigida, na san kai mai tsanani ne. Kana girbi inda baka yi shuka ba, kuma kana tattarawa inda ba ka watsa ba. 25 Na ji tsoro, don haka sai na je na boye talantinka a rami. Duba, ga abinda yake naka.' 26 Amma ubangidansa ya amsa yace, kai mugu malalacin bawa, ka san cewa ni mai girbi ne inda ban shuka ba kuma ina tattarawa inda ban zuba ba. 27 To da ba sai ka kai kudina a banki ba, da bayan na dawo da sai in karbi abina da riba. 28 Saboda haka ku kwace talantin daga gare shi ku baiwa mai talanti goman nan. 29 Gama ga wanda yake da shi za'a kara masa har ma a yalwace za'a kara bashi. Amma ga wanda bashi da komai abinda ke nasa ma za'a kwace. 30 Ku jefa wannan mugun bawan marar amfani, cikin duhu mai zurfi, inda ake kuka da cizon hakora.' 31 Sa'adda Dan mutum zai zo cikin daukakarsa da dukan Mala'iku tare da shi, sa'annan zai zauna kursiyinsa na daukaka. 32 A gabansa za'a tattara dukkan al'ummai, zai rarraba mutanen daya'daya, kamar yadda makiyayi yake rarraba tumaki daga awaki. 33 Zai sa tumakin a hannunsa na dama, amma awakin a hannunsa na hagu. 34 Sa'annan sarkin zai ce wa na hannun damarsa, 'Ku zo ku da Ubana ya albarkata, ku gaji mulkin da aka shirya maku kafin a kafa duniya. 35 Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki; 36 Na yi huntanci kuka tufasar dani; Na yi ciwo kuka kula dani; Ina kurkuku kuka ziyarceni.' 37 Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha? 38 Kuma yaushe muka ganka kana bakunci har muka baka masauki? Ko kuma kana huntanci da muka tufatar da kai? 39 Yaushe kuma muka ganka kana ciwo ko a kurkuku har muka ziyarce ka?' 40 Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.' 41 Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa, 42 domin ina jin yunwa baku bani abinci ba; ina jin kishi ba ku bani ruwa ba; 43 Ina bakunci amma baku bani masauki ba; ina huntanci, baku tufasar da ni ba; ina ciwo kuma ina kurkuku, baku kula da ni ba.' 44 Sa'annan suma zasu amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa, ko kishin ruwa, ko kana bakunci, ko kana huntanci, ko ciwo, kuma a kurkuku, da bamu yi maka hidima ba?' 45 Sa'annan zai amsa ya ce masu, 'Ina gaya maku hakika abin da baku iya yiwa mafi karanta daga cikin wadannan ba, ba ku yi mani ba.' 46 Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami."

26

1 Yayin da Yesu ya gama fadi masu wadannan maganganu, sai ya cewa almajiransa, 2 "Kun sani sauran kwana biyu idin ketarewa ya zo, kuma za'a bada Dan mutum domin a gicciye shi. 3 Sa'annan manyan firistoci da dattawan jama'a suka taru a fadar babban firist, mai suna Kayafa. 4 Suka shirya yadda zasu kama Yesu a boye su kuma kashe shi. 5 Amma suna cewa, "Ba a lokacin idin ba, domin kada tarzoma ta tashi daga cikin mutane." 6 Sa'adda Yesu yake Baita'anya a gidan Saminu Kuturu, 7 daidai lokacin da ya zauna a gefen teburin cin abinci, sai wata mata ta shigo da kwalbar mai, mai tsada, ta zuba wa Yesu a kansa. 8 Amma da almajiransa suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, "Ina dalilin yin irin wannan asara? 9 Ai da an sayar da wannan mai da kudi mai yawa a rabawa talakawa." 10 Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, "Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina. 11 Kuna da talakawa tare da ku koyaushe, amma ni ba zan kasance da ku ba koyaushe. 12 Don a sa'adda ta zuba man nan a jikina, ta yi haka ne don jana'iza ta. 13 Hakika Ina gaya maku, duk inda za ayi wannan bishara a dukan duniya, abin da matar nan tayi za'a rika ambatar da shi don tunawa da ita." 14 Sai daya daga cikin sha biyun, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya tafi wurin manyan firistocin, 15 yace, "Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?" Suka auna masa azurfa talatin. 16 Daga wannan lokacin yayi ta neman zarafi da zai bada shi a wurinsu. 17 To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, "Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?" 18 Yace, "Ku shiga cikin birnin zaku sami wani mutum sai kuce masa, 'Mallam yace, "lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina."'" 19 Almajiran suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su, suka shirya abincin idin ketarewar. 20 Da yamma ta yi, sai ya zauna domin ya ci tare da almajiransa goma sha biyu. 21 Sa'adda suke ci, yace, "Hakika ina gaya maku, daya daga cikin ku zai bada ni." 22 Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, "Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?" 23 Sai ya amsa, "Wanda ke sa hannu tare da ni cikin kwano daya shi ne zai bada ni. 24 Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba." 25 Yahuza da zai bada shi yace, "Mallam ko ni ne?" Yace masa, "Ka fada da kanka." 26 Yayin da suke ci, sai Yesu ya dauki gurasa, ya sa albarka, ya karya. Ya ba almajiran yace, "Ku karba, ku ci, wannan jiki nane." 27 Sai ya dauki kokon yayi godiya, Ya ba su yace, "Ku sha, dukanku. 28 "Gama wannan jinina ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa. 29 Amma ina gaya maku, ba zan kara shan ruwan inabin nan ba, sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a cikin mulkin Ubana." 30 Da suka raira waka, sai suka ka tafi dutsen zaitun. 31 Sai Yesu yace masu, "Dukan ku zaku yi tuntube a wannan dare sabili da ni, gama a rubuce yake, "Zan bugi makiyayin, garken tumakin kuma za su watse.' 32 Amma bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa Galili." 33 Amma Bitrus yace masa, "Ko dama duka zasu fadi sabili da kai, ni kam bazan fadi ba." 34 Yesu yace masa, "Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku." 35 Bitrus yace masa, koda zan mutu tare da kai, bazan yi musunka ba." Sai sauran almajiran suma suka fadi haka. 36 Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, "Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a." 37 Ya dauki Bitrus da kuma 'ya'ya biyu na Zabadi tare da shi, sai ya fara damuwa da juyayi. 38 Sai yace masu, "Raina na cikin damuwa sosai har ga mutuwa. Ku kasance anan kuna tsaro tare da ni." 39 Ya dan taka zuwa gaba kadan, sai ya fadi a fuskarsa, yayi addu'a. Yace, "Ya Ubana, in zai yiwu, bari kokon nan ya wuce ni. Duk da haka, ba nufina za'a bi ba, amma naka nufin." 40 Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, "Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya? 41 Ku yi tsaro kuma, kuyi addu'a domin kada ku fada cikin jaraba. Ruhu dai ya yarda amma, jiki ba karfi." 42 Sai ya koma karo na biyu yayi addu'a, Yace, "Ya Ubana, in wannan kokon ba zai wuce ba sai na sha shi, bari nufinka ya kasance." 43 Ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi. 44 Sai ya sake barinsu ya tafi. Ya koma karo na uku yana addu'a yana fadin kalmomi iri daya. 45 Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, "Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi. 46 Ku tashi mu tafi. Duba, wanda zai badani ya kusato." 47 Sa'adda yana cikin magana Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya zo. Babban taro ya zo tare da shi daga wurin manyan firistoci da dattawan jama'a. Suna rike da takubba da kulake. 48 To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, "Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi." 49 Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, "Gaisuwa, Mallam!" sai ya sumbace shi. 50 Yesu kuwa yace masa, "Aboki, kayi abin da ya kawo ka." Sai suka iso suka sa hannuwansu kan Yesu suka kama shi. 51 Nan take, daya daga cikin wadanda suke tare da Yesu ya mika hannunsa, ya zare takobinsa, ya sare wa bawan babban firist din kunne. 52 Sai Yesu yace, masa, "Ka maida takobinka cikin kubensa, domin duk wadanda suka dauki takobi su ma ta wurin takobi za su hallaka. 53 Ko kana tunanin ba zan iya kiran Ubana ba, ya kuma aiko da rundunar Mala'iku fiye da goma sha biyu? 54 Amma to tayaya za'a cika nassi, cewa dole wannan ya faru?" 55 A wannan lokacin Yesu yace wa taron, "Kun zo da takubba da kulake ku kama ni kamar dan fashi? Ina zaune kowace rana a haikali ina koyarwa, amma baku kama ni ba. 56 Amma duk wannan ya faru ne don a cika abinda annabawa suka rubuta." Bayan haka sai dukkan almajiran suka bar shi suka gudu. 57 Wadanda suka kama Yesu, suka kai shi wurin Kayafa babban firist, inda marubuta da duttawan jama'a suka taru. 58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har zuwa farfajiyar babban firist din. Ya shiga ya zauna da masu tsaro domin ya ga abinda zai faru. 59 A wannan lokaci manyan firistoci da duk 'yan majalisar suka fara neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi. 60 Amma ba su samu ko daya ba, ko dayake an samu shaidun karya dayawa da suka gabata. Amma daga baya sai wasu su biyu suka fito 61 sukace "Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.'" 62 Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, "Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?" 63 Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, "Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah." 64 Yesu ya amsa masa, "Ka fada da bakin ka. Amma ina gaya maka, daga yanzu zaka ga Dan mutun na zaune a hannun dama na iko, ya na zuwa akan gizagizai na sama." 65 Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, "Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon. 66 Menene tunaninku?" Suka amsa sukace, "Ya cancanci mutuwa." 67 Sai suka tofa masa yawu a fuska, suka kuma yi masa duka, suka kuma mammare shi da tafin hannuwansu, 68 sukace, "Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka. 69 To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, "Kaima kana tare da Yesu na Galili." 70 Amma ya yi musun haka a gaban su duka, yace, "Ban ma san abinda kike magana akai ba." 71 Da ya fita zuwa bakin kofa, nan ma wata yarinyar baiwa ta gan shi tace wa wadanda suke wurin, "Wannan mutumin ma yana tare da Yesu Banazare." 72 Sai yayi musun haka kuma, har da rantsuwa, yace, "Ban san mutumin nan ba." 73 Bayan dan lokaci kadan wadanda suke a tsaye suka zo wurin Bitrus suka ce masa, "Hakika kai daya daga cikin su ne, gama harshen ka ya tonaka." 74 Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, "Ban san wannan mutumin ba," nan da nan zakara yayi cara. 75 Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya fada, "Kafin carar zakara zaka yi musun sani na sau uku." Sai ya fita waje yayi kuka mai zafi."

27

1 Da gari ya waye, duk manyan firistoci da dattawan jama'a suka shirya yadda zasu kulla makirci domin su kashe shi. 2 Suka daure shi, suka mika shi ga gwamna Bilatus. 3 Sa'adda Yahuza, wanda ya bashe shi, ya ga an zartarwa Yesu hukuncin kisa, ya nemi tuba ya kuma mayar da azurfar talatin ga manyan firistocin da dattawan, 4 yace, "Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi." Amma sukace, "Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?" 5 Sai ya jefar da kwandalolin azurfar a kasa cikin haikalin ya kuma bar su, ya tafi ya rataye kansa. 6 Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, "Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne." 7 Sai suka tattauna al'amarin a tsakanin su, kudin kuma suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki. 8 Dalilin wannan ne ake kiran wurin, "Filin jini" har yau. 9 Sai abin da aka fada ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, "Suka dauki tsabar azurfa talatin na farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa, 10 suka bayar domin sayen filin mai tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni." 11 Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, "Kai sarkin Yahudawa ne?" Yesu ya amsa, "Haka ka fada." 12 Amma da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi, bai ce komai ba. 13 Sai Bilatus yace masa, "Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?" 14 Amma bai ce masa ko kalma guda ba, sai gwamna yayi matukar mamaki. 15 To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba. 16 A wannan lokacin suna da wani sanannen dan kurkuku mai suna Barabbas. 17 To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, "Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?" 18 Saboda ya san sun kawo shi ne domin kishi. 19 Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, "Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi." 20 A lokacin nan manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a kashe Yesu. 21 Sai gwamna ya tambayesu, "Wa kuke so a sakar maku?" Sukace, "Barabbas." 22 Bilatus yace masu, "Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?" Sai duka suka amsa, "A gicciye shi." 23 Sai yace, "Don me, wane laifi ya aikata?" Amma suka amsa da babbar murya, "A gicciye shi" 24 Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, "Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama." 25 Duka mutanen sukace, "Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu." 26 Sai ya sakar masu da Barabbas amma yayi wa Yesu bulala ya mika shi garesu domin su gicciye shi. 27 Sai sojojin gwamna suka dauki Yesu zuwa farfajiya suka kuma tara dukan rundunar sojoji. 28 Suka yi masa tumbur sa'annan suka sa masa jar alkyabba. 29 Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, "Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!" 30 Suka kuma tofa masa yawu, suka kwace sandar suka buga masa a ka. 31 Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi. 32 Da suka fito waje, sai suka iske wani Bakurame mai suna Saminu, wanda suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya dauki gicciyen. 33 Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,"Wurin kwalluwa." 34 Suka bashi ruwan inabi da aka gauraya da wani abu mai daci. Amma da ya 'dan-'dana shi sai ya ki sha. 35 Bayan da suka gicciye shi, suka kada kuri'a a kan rigarsa. 36 Suka kuma zauna suna kallonsa. 37 A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce, "Wannan shine sarkin Yahudawa." 38 An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa. 39 Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai, 40 suna kuma cewa, "Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!" 41 Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa, 42 "Ya ceci wasu amma ya kasa ceton kansa. Shi ne sarkin Isra'ila. Ya sauko mana daga kan gicciyen, sai mu ba da gaskiya gareshi. 43 Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, "Ni dan Allah ne." 44 Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi. 45 To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma. 46 Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, "Eli, Eli lama sabaktani?" wanda ke nufin, "Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?" 47 Da wadanda suke tsaye kusa suka ji haka, sai sukace, "Yana kiran Iliya." 48 Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha. 49 Sai sauran sukace, "Rabu da shi mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi." 50 Sai Yesu ya ta da murya mai karfi yayi kuka sai ya saki ruhunsa. 51 Sai labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa. Kasa kuma ta girgiza, duwatsu suka farfashe. 52 Kaburbura suka bude, tsarkaka kuwa wadanda suke barci da yawa suka tashi. 53 Suka fito daga kaburbura bayan tashinsa, suka shiga birni mai tsarki suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, "Hakika wannan Dan Allah ne" 55 Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa. 56 A cikin su akwai Maryamu Magadaliya, Maryamu uwar Yesu da Yusufu, da uwar 'ya'yan Zabadi. 57 Da yamma sai wani attajiri mutumin Armatiya ya zo, mai suna Yusufu wanda shi ma almajirin Yesu ne. 58 Ya je wurin Bilatus ya roka a bashi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a bashi. 59 Yusufu ya dauki jikin, ya rufe shi da likafani mai tsabta, 60 sai ya sa shi a cikin sabon kabarinsa da ya sassaka cikin dutse. Sai ya mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin ya tafi. 61 Maryamu Magadaliya da dayan Maryamun suna nan zaune akasin kabarin. 62 Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus. 63 Sukace, "Mai gida, mun tuna lokacin da mayaudarin nan yake da rai, yace, "Bayan kwana uku zan tashi." 64 Saboda haka, ka bada umarni a tsare kabarin na kwana uku. In ba haka ba almajiransa zasu zo su sace shi, kuma su ce wa mutane, "Ya tashi daga mattatu." Kuma yaudarar karshe zata fi ta farko muni." 65 Bilatus yace masu, "Ku dauki masu tsaro. Kuyi tsaro iyakar karfin ku." 66 Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka hatimce dutsen, suka sa masu tsaro.

28

1 Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin. 2 Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai. 3 Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno. 4 Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane. 5 Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, "Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye. 6 Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi. 7 Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku." 8 Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa. 9 Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, "A gaishe ku." Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada. 10 Sai Yesu yace masu, "Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni." 11 Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru. 12 Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin 13 Sukace masu, "Ku gaya wa sauran cewa, "Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci." 14 Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa." 15 Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau. 16 Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu. 17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka. 18 Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, "Dukan iko dake sama da kasa an ba ni. 19 Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. 20 Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani."

Markus
Markus
1

1 Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah. 2 kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya. 3 Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta. 4 Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai. 5 Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu. 6 Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma. 7 Yana wa'azi, ya ce "akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. 8 Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki". 9 Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. 10 Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya. 11 Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, "Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai". 12 Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji. 13 Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima. 14 Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah. 15 Yana cewa, "Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara". 16 Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 17 Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane". 18 Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi. 19 Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. 20 Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi. 21 Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu. 22 Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba. 23 A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi. 24 Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah". 25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, "Ka yi shiru ka fita daga cikinsa". 26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa. 27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!" 28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. 29 Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. 30 Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima. 32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu. 33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa. 34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi. 35 Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua. 36 Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi. 37 Suka sa me shi, sai su ka ce masa, "kowa yana nemanka". 38 Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan". 39 Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu. 40 Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, "in ka yarda kana iya warkar da ni. 41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa "Na yarda. Ka sarkaka". 42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa. 43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi. 44 Ya ce masa "ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida. 45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.

2

1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida. 2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana. 3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi. 4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai. 5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, "Da, an gafarta maka zunuban ka". 6 Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu. 7 Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi "sai Allah kadai?" 8 Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, "Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku? 9 Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? 10 Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen, 11 "Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka." 12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, "suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba." 13 Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu. 14 Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, "Ka biyo ni." Ya tashi, ya bi shi. 15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi. 16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, "Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?" 17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, "Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi." 18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, "Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?" 19 Sai Yesu yace masu, "Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba. 20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi. 21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa. 22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka." 23 A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi, 24 Sai Farisawa su ka ce masa, "Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?" 25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi? 26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi?" 27 Yesu yace, "Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba. 28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar."

3

1 Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu. 2 Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi. 3 Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun " Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa." 4 Sai ya ce wa mutane, "Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? "Amma suka yi shiru. 5 Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi. 6 Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi. 7 Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya 8 Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa. 9 Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi. 10 Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi. 11 Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne." 12 Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi. 13 Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa. 14 Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, 15 Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu. 16 Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus. 17 Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa, 18 da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, 19 da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi. 20 Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, 21 Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, "Ai, baya cikin hankalinsa " 22 Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce "Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu." 23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, "Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan? 24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba. 25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba. 26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan. 27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa. 28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, 29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada." 30 "Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu," 31 Sa'an nan uwatasa, da "Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka." 33 Ya amsa masu, "Dacewa su wanene uwa-ta da "yan'uwa na?" 34 Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, "Ga uwa-ta da yan-uwana anan! 35 Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta."

4

1 Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun. 2 Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu, 3 "ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5 Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa. 6 Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe. 7 Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba. 8 Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari". 9 Sai ya ce, Duk mai kunnen ji, ya ji," 10 Sa'adda Yesu yake shi kadai, wadanda suke kusa dashi tare da sha biyun suka tambaye shi ma'anar misalan. 11 Sai ya ce masu, "ku an yardar maku, ku san asirin mulkin Allah, amma ga wadanda ba su cikinku, komai sai a cikin Misalai, 12 don gani da ido sun gani, amma ba su gane ba. ji kuma, sun ji, amma ba su fahimta ba, don kada su juyo a gafarta masu," 13 Ya ce masu, "Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran? 14 Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa. 15 Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16 Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki. 17 Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube. 18 Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar, 19 amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani. 20 Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari." 21 ya ce masu, "Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta. 22 Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba. 23 Bari mai kunnen ji, ya ji!" 24 Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka. 25 Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi." 26 Sai ya ce, "Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa. 27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba. 28 Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko, 29 Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan." 30 Ya kuma ce, "Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31 Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya. 32 Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta." 33 Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu, 34 ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu. 35 A ranan nan da yama ta yi yace masu "Mu haye wancan ketaren." 36 Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi. 37 Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika. 38 Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa "Malam za mu hallaka ba ka kula ba?" 39 Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, "Ka natsu! ka yi shiru!" Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru. 40 Ya ce masu, "Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?" 41 Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, "wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?"

5

1 Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa. 2 Sa'adda Yesu ya sauko daga cikin jirgin ruwan sai wani mutum mai aljanu ya fito daga cikin kaburbura ya tarbe shi. 3 Mutumin yana zama a cikin kaburbura. An daure shi da sarkoki da mari 4 An daure shi da sarkoki da mari sau da yawa, amma ya tsuntsunke sarkoki da marin. har ma ba wanda zai iya daure shi kuma. 5 Dare da rana a cikin kabarbarun da duwatsu mutumin ya na ihu ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi. 6 Sa'adda ya hango Yesu daga nesa, sai ya tarbi Yesu ya durkusa a gabansa. 7 Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala, 8 Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa." 9 Ya tambaye shi, "Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa. 10 Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar. 11 Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni. 12 Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun. 13 Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa. 14 Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru 15 Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata. 16 Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun. 17 Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu. 18 Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi. 19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka. 20 Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki. 21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun. 22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa. 23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, "Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu." 24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi. 25 Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu. 26 Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi. 27 Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa. 28 Domin ta ce "Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke." 29 Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta. 30 Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce "wanene ya taba rigata?" 31 Almajiransa suka ce, "a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?" 32 Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi. 33 Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya. 34 Sai ya ce da ita, "Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki". 35 Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce "Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?" 36 Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, "kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai." 37 Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu. 38 Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai. 39 Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane "Me ya sa kuke damuwa da kuka?" Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi. 40 Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke. 41 Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita "Tilatha koum" wato yarinya na ce ki tashi" 42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya (gama shekarun ta sun kai goma sha biyu). Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske. 43 Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.

6

1 Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi. 2 Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa? 3 Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu. 4 Yesu ya ce, "Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa." 5 Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su. 6 Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa. 7 Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu, 8 ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu, 9 sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu. 10 Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi. 11 Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin. 12 Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu. 13 Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su. 14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa. 15 Wadansu kuma suna cewa, "Iliya," Har yanzu wadansu suna cewa daya "daga cikin annabawa ne na da can." 16 Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, "Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi." 17 Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta. 18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba. 19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba. 20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi. 21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. 22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, "ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi". 23 Ya rantse mata da cewa"Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne" 24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, "me zan ce ya bani?" Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma. 25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, "Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire." 26 Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a. 27 Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku. 28 Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta. 29 Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari. 30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar. 31 Sai ya ce da su "ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan," domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci 32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai. 33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo. 34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa. 35 Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, "wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi. 36 Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci. 37 Amma sai ya ba su amsa ya ce,"Ku ku basu abinci su ci mana". Sai suka ce da shi, "ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?" 38 Sai ya ce dasu, "Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani." Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu." 39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa. 40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin. 41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka. 42 Dukansu suka ci suka koshi. 43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin. 44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar. 45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen. 46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a. 47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai. 48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su. 49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu, 50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, "Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!" 51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai. 52 Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare. 53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka. 54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne. 55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa. 56 Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.

7

1 Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima. 2 Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba, 3 (Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa. 4 Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.) 5 Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, "Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?" 6 Amma ya amsa masu cewa, "Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni. 7 Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'". 8 Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane. 9 Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane. 10 Koda shike Musa ya rubuta cewa, "ka girmama Ubanka da Uwarka", kuma, "duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take". 11 Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, "duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)"'. 12 Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu. 13 Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi." 14 Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, "ku kasa kunne gareni, kuma ku gane. 15 Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi" 16 Bari mai kunnen ji, ya ji. 17 Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali. 18 Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba, 19 domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga". Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta. 20 Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi 21 Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa, 22 zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci. 23 Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi." 24 Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba. 25 Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa. 26 Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. 27 Sai ya ce mata, "Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba". 28 Sai ta amsa masa cewa, "I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan." 29 Ya ce mata, "domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki." 30 Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta. 31 Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis. 32 Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa. 33 Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa. 34 Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, "Ifatha", wato, "bude!" 35 Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau. 36 Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina. 37 kuma suna ta mamaki cewa, "Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana."

8

1 A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu, 2 "Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci. 3 Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa." 4 Almajiransa suka amsa masa cewa, "A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?" 5 Ya tambaye su, "gurasa nawa kuke da su?" Sai suka ce, "Bakwai." 6 Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu. 7 Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen. 8 Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai. 9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su. 10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta. 11 Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi. 12 Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, "Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar." 13 Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin. 14 A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan. 15 Ya gargade su, "ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus." 16 Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, "Saboda ba mu da gurasa ne." 17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, "Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?" 18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba? 19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, "Goma sha biyu." 20 Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, "bakwai." 21 Ya ce masu, "har yanzu baku gane ba?" 22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi. 23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi "kana ganin wani abu kuwa?" 24 Ya daga ido sai ya ce, "ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa." 25 Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau. 26 Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, "kada ka shiga cikin garin" 27 Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, "Shin wanene mutane ke ce da ni?" 28 Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, "Iliya". wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa". 29 Ya tambaye su, "Amma me ku ke ce da ni?" Bitrus ya ce, "Kai ne Almasihu." 30 Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi. 31 Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu. 32 Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa. 33 Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, "Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba." 34 Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, "Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni. 35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi. 36 Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa. 37 Me mutum zai bayar amaimakon ransa? 38 Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki."

9

1 Sai ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko." 2 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu. 3 Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya. 4 Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu. 5 Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya, 6 Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.) 7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, "ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi. 8 Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. 9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu. 10 Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu "mene ne tashin matattu" ke nufi. 11 Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?" 12 Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi? 13 Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa." 14 Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura. 15 Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16 Ya tambayi almajiransa, "Wacce muhawara ce kuke yi da su?" 17 Daya daga cikin taron ya amsa masa"malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani. 18 Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa. 19 Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi. 20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. 22 Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu. 23 Yesu ya ce masa, "In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata. 24 Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. 25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, "kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa. 26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, "Ai, yaron ya mutu. 27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye. 28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?" 29 Ya ce masu, "Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a." 30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. 31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi. 32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? 34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma. 35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka. 36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu. 37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni." 38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu. 39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu. 40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne. 41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba. 42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku. 43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. 44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. 46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. 48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa. 49 Domin da wuta za a tsarkake kowa. 50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.

10

1 Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa. 2 Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, "dai dai ne mutum ya saki matarsa?" Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi. 3 Ya amsa ya ce, menene Musa ya umarce ku? 4 Suka ce, "Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita." 5 "Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar," Yesu ya ce masu. 6 Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.' 7 Domin wannan dalilin ne mutum zai rabu mahaifinsa da mahaifiyarsa ya mannewa matarsa. 8 Su biyu kuwa sun zama jiki daya, ba biyu ba, 9 Saboda haka abinda Allah ya hada kada mutum ya raba." 10 Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana. 11 Ya ce da su. Dukan wanda ya saki matarsa ya kuma auro wata matar yayi zina da ita kenan. 12 Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan." 13 Mutane suka kawo masa 'ya'yansu kanana don ya taba su, sai almajiransa suka kwabe su. 14 Da Yesu ya gani, ya ji haushi, ya ce masu. Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su domin mulkin Allah na irinsu ne. 15 Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba. 16 Sai ya rungume su ya sa masu albarka. 17 Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya "Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?" 18 Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai. 19 Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka." 20 Sai mutumin ya ce masa Malam ai na kiyayye duk wadannan abubuwa tun ina yaro. 21 Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni. 22 Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai. 23 Yesu ya dubi almajiransa ya ce. "Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!" 24 Almajiransa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ce masu, ya ku ya'ya'na yana da wuya kamar me a shiga mulkin Allah. 25 Zai zama da sauki ga rakumi yabi ta kafar allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah. 26 Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, "to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?" 27 Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne. 28 Bitrus ya ce masa, "to gashi mu mun bar kome, mun bika". 29 Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara, 30 sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami. 31 Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko. 32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi. 33 "Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai. 34 Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi." 35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, "Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka" 36 Ya ce masu. "Me ku ke so in yi maku?" 37 Suka ce, "ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka." 38 Yesu ya ce masu. "Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?" 39 Suka fada masa, "Zamu iya." Yesu ya ce masu, "kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku." 40 Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne." 41 Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya. 42 Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, "kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko. 43 Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44 Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa. 45 Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa." 46 Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya. 47 Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, "Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina" 48 Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!" 49 Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. "Albishrinka, ta so! Yana kiranka." 50 Makahon ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51 Yesu ya tambaye shi, ya ce, "me ka ke so in yi maka?" Makahon ya ce, "Malam in sami gani." 52 Yesu ya ce masa. "Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare.

11

1 Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu 2 ya ce masu, "ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani. 3 In wani ya ce maku, "Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan."' 4 Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5 sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, "Don me kuke kwance aholakin nan? 6 Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi. 7 Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau. 8 Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen. 9 Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, "Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. 10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!" 11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. 12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa. 13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne. 14 Sai ya ce wa bauren, "Kada kowa ya kara cin "ya'yanka har abada!" Almajiransa kuwa sun ji maganar. 15 Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. 16 Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin. 17 Sai ya koyar da su cewa, "Ashe ba rubuce yake ba, "Za a kira gidana gidan addu'a na dukan al'ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi". 18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa. 19 Kowace yamma kuma, sukan fita gari. 20 Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe. 21 Bitrus kuwa ya tuna ya ce "Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe." 22 Yesu ya amsa masu ya ce, "ku gaskata da Allah." 23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. 24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku. 25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi." 26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.) 27 Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa, 28 suka ce masa, "Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu?" 29 Sai Yesu ya ce masu, "Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan. 30 Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa". 31 Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, "in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, "To, don me ba ku gaskata shi ba? 32 In kuwa muka ce, "amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. 33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, "Ba mu sani ba" Yesu ya ce masu, "Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba."

12

1 Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. "Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa. 2 Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar. 3 Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza. 4 Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi. 5 Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu. 6 Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma. 7 Amma manoman nan suka ce wa juna, "ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu." 8 Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9 To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar. 10 Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ' Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci. 11 Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu."' 12 Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama'a. Don haka suka kyele shi, suka tafi. 13 Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa. 14 Da suka zo, suka ce masa, "Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. "Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?" 15 AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, "Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani." 16 Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, "Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, "Na Kaisar ne." 17 Yesu ya ce, "to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai. 18 Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce, 19 "Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.' 20 To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba. 21 Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka. 22 Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. 23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta". 24 Sai Yesu ya ce, "Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba? 25 Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama. 26 Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? "Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'? 27 Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure ". 28 Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, "Wanne Umarni ne mafi girma dukka?" 29 Yesu ya amsa yace, "mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. 30 Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka. 31 ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan." 32 Sai malamin attaura ya ce masa, "Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi. 33 A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa." 34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, "Ba ka nesa da mulkin Allah." Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu. 35 Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce "Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne? 36 Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'. 37 Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?" Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna. 38 A koyarwa sa Yasu ya ce, "ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa, 39 da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa. 40 Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani." 41 Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kudi a ciki. 42 Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon. 43 Ya kira almajiransa, ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka. 44 Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi."

13

1 da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa "malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!" 2 Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba." 3 Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce. 4 Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?" 5 Yesu ya ce masu, "ku kula, kada kowa ya rudeku. 6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa. 7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. 8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne. 9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su. 10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara. 11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne. 12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su. 13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu. 14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse. 15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu. 16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa. 17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin. 18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina. 19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada. 20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin. 21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. 22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki. 23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin. 24 Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba. 25 Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 26 Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka. 27 Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama. 28 "Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan. 29 Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke. 30 Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 31 Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 32 Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai. 33 Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba. 34 Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake. 35 To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne. 36 Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci. 37 Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!"

14

1 Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi. 2 Suna cewa amma "Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane". 3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa. 4 wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa 5 "Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci? 6 Sai Yesu yace masu "Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata, 7 ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba. 8 Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza. 9 hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba." 10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu, 11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su. 12 A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa "Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa? 13 Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa "Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa. 14 Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace "ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?"' 15 Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can." 16 Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar. 17 Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun. 18 Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce "Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni". 19 Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa "Hakika bani bane ko?" 20 Yesu ya amsa masu da cewa "Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar". 21 Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! "zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba". 22 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa "Wannan jikinana ne". 23 Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon. 24 Ya ce "Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane". 25 Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah." 26 Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun. 27 Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa "Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse; 28 Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili. 29 Bitrus ya ce masa "ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni". 30 Yesu yace masa "Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku". 31 Amma Bitrus ya sake cewa "Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba". Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari. 32 Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa "Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a". 33 Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai. 34 Sai ya ce masu "Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake". 35 Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne "A dauke masa wannan sa'a daga gare shi. 36 Ya ce "Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka". 37 Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba? 38 Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne. 39 Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko. 40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome. 41 Ya sake komowa karo na uku yace masu "har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi". 42 Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato." 43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su. 44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa "Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare. 45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce "Ya malam!". Sai ya sumbace shi. 46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi. 47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne. 48 Sai Yesu ya ce "kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni? 49 Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada." 50 Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere. 51 Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka. 52 Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara. 53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa. 54 Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta. 55 Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba. 56 Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba. 57 Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce. 58 "Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba". 59 Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba. 60 Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace "Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka? 61 Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa "To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki? 62 Yesu ya ce "Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare". 63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace "Wacce shaida kuma zamu nema? 64 Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa. 65 Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa "Yi annabci" Dogaran kuma suka yi ta marinsa. 66 Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo. 67 Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce "Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu". 68 Amma ya musa ya ce "Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta". Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara. 69 Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, "Wannan ma daya daga cikinsu ne". 70 Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus "Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai". 71 Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa "Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba". 72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa "Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku". Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.

15

1 Da sassafe, sai manyan firistoci suka hadu da dattawa da manyan malamai, da majalisa suka daure Yesu, suka sa shi gaba suka mika shi ga Bilatus. 2 Bilatus ya tambaye shi, kaine sarkin Yahudawa? ya amsa ya ce "haka ka ce" 3 Sai manyan firistochi suka kawo zargi iri iri a kan Yesu. 4 Bilatus ya sake tambayarsa, ba ka da abin cewa? ka lura da yawan zargi da ake yi maka. 5 Amma Yesu baya sake yi masa magana ba. wannan ya ba shi mamaki. 6 A lokacin idi, Bilatus ya kan sakar masu da dan bursuna wanda jama'a suka bukaci a saka, 7 A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, da masu kisan kai, akwai wani mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas. 8 Sai Jama'a suka zo wurin Bilatus ya yi masu kamar yadda ya saba yi. 9 Bilatus ya amsa masu ya ce, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa? 10 Yayi wannan domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa, 11 Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu. 12 Bilatus ya sake yi masu tambaya "Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?" 13 sai suka amsa da kuwwa" a "giciye shi!" 14 Bilatus ya ce masu menene laifinsa sai suka kara ihu, "a giciye shi." 15 Bilatus don yana son ya farantawa jama'a zuciya sai ya sakar masu da Barrabbas sai ya yi wa Yesu bulala, sannan ya mika shi a giciye shi. 16 Sojoji suka kai shi cikin kagara, suka tara rundunan soja, 17 Suka sa masa tufafin shulaiya suka nada masa rawanin kaya, 18 Suna masa kirari na ba'a suna cewa, "A gaida sarkin Yahudawa!" 19 Sai suka buge shi a kai da kulki suka kuma tofa masa yau a fuska, suka kuma durkusa suna yi masa sujadar ba'a. 20 Bayan sun gama yi masa ba'a sai suka cire masa tufafin shunnaiya, sai suka maida masa tasa tufafinsa, sai suka fitar dashi don su giciye shi. 21 Suna cikin tafiya sai suka hadu da wani, mai suna Saminu Bakairawani (wato uban Alizanda da Rufus); suka tillasta shi ya dauki gijiyen Yesu. 22 Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai) 23 Suka bashi ruwan inabi hade da mur, amma ya ki ya sha. 24 Sai suka giciye shi, suka kuma raba tufafinsa suka kuma jefa kuri'a domin kowanne soja ya sami rabonsa. 25 A sa'a ta uku aka giciye shi. 26 Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa "Ga Sarkin Yahudawa" 27 Suka kuma giciye shi tare da wadansu yan fashi guda biyu. 28 Daya a hannun damansa daya a hannun hagunsa. Domin a cika abinda nassi ya fada. 29 suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, "Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30 ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!" 31 Haka ma manyan firistoci da malamai, suka yi masa ba'a suna cewa "Ya ceci wadansu amma bai iya ceci kansa ba" 32 Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka daga giciye. Domin mu gaskata shi, sai wadanda aka giciye shi tare dasu, suma suka yi masa ba'a. 33 sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina, 34 A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?" Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?" 35 Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, "Duba, yana kiran Iliya." 36 Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi. 37 Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu. 38 Sai labulen haikalin ya rabu kashi biyu daga sama har kasa. 39 Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce "hakika, wannan mutum Dan Allah ne." 40 Akwai kuma mata wadanda ke dubawa daga nesa. Daga cikinsu akwai Maryamu Magadala, da Maryamu( Uwar Yakubu da Yusufu) da Salome. 41 Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi. 42 Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce. 43 Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu. 44 Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu. 45 Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu. 46 Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi. 47 Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.

16

1 Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza. 2 Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana. 3 Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?" 4 Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma. 5 Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki. 6 Sai ya ce masu, "Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi. 7 Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku." 8 Suka fita daga cikin kabarin da gudu suna rawar jiki da mamaki, ba su cewa kowa komai ba domin suna jin tsoro. 9 Da safiyar ranar farko ta mako ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magadaliya wadda ya kori aljannu guda bakwai daga cikinta. 10 Sai ta tafi ta shaida wadanda suke tare da shi suke makoki da kuka. 11 Sai suka ji cewa ya tashi kuma ta ganshi, amma basu gaskata ba. 12 Bayan wadannan al'amura ya bayana kansa ta wata siffa ga mutum biyu sa'ilin da suke tafiya akan hanya. 13 Sai suka tafi suka gaya wa sauran almajiransa, duk da haka basu gaskata ba. 14 Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu. 15 Sai ya umarcesu cewa "Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta. 16 Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka. 17 Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna. 18 Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa." 19 Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah. 20 Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.

Luka
Luka
1

1 Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu, 2 kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon. 3 Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas. 4 Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne. 5 A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne. 6 Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji. 7 Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai. 8 Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa. 9 Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare. 10 Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren. 11 A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren. 12 Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi. 13 Amma mala'ikan ya ce masa, "Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya. 14 Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa. 15 Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa. 16 Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu. 17 Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa." 18 Zakariya ya ce wa mala'ikan, "Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa." 19 Mala'ikan ya amsa ya ce masa, "Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. 20 Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin." 21 Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali. 22 Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana. 23 Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa. 24 Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce, 25 "Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a." 26 A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, 27 zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu. 28 Ya zo wurin ta ya ce, "A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke. 29 Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan. 30 Mala'ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah. 31 Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'. 32 Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda. 33 Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka." 34 Maryamu ta ce wa mala'ikan, "Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?" 35 Mala'ikan ya amsa ya ce mata, "Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah. 36 Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya. 37 Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah." 38 Maryamu ta ce, "To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka." Sai mala'ikan ya bar ta. 39 Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya. 40 Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu. 41 Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki. 42 Ta daga murya, ta ce, "Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki. 43 Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni? 44 Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna. 45 Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika. 46 Maryamu ta ce, "Zuciyata ta yabi Ubangiji, 47 kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na." 48 Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka. 49 Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne. 50 Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi. 51 Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu. 52 Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu. 53 Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi. 54 Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai 55 (kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada." 56 Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta. 57 Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji. 58 Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita 59 Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa "Zakariya" kamar sunan ubansa, 60 amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, "A'a, za a kira shi Yahaya." 61 Suka ce mata, "Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna." 62 Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna. 63 Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, "Sunansa Yahaya." Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan. 64 Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah. 65 Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya. 66 Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, "To me wannan yaro zai zama ne?" Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. 67 Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa, 68 "Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su." 69 Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa, 70 kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai. 71 Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu. 72 Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73 rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim. 74 Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba, 75 a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu. 76 I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa, 77 domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu. 78 Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu, 79 domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama. 80 Yaron ya yi girma ya kuma zama kakkarfa a cikin ruhu, yana kuma cikin jeji sai ranar bayyanuwarsa ga Isra'ila.

2

1 Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya. 2 Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya. 3 Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan. 4 Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne. 5 Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu. 6 Ya zama sa'adda suke can, lokaci ya yi da za ta haifi danta. 7 Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin. 8 A cikin wannan yankin, akwai makiyaya wadanda suke zama a sarari suna tsaron garken tumakinsu da dare. 9 Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai. 10 Sai mala'ikan ya ce masu, "Kada ku ji tsoro, domin na kawo maku labari mai dadi da zai kawo murna da yawa ga dukan mutane. 11 Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji! 12 Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi." 13 Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa, 14 "Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu." 15 Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, "Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana." 16 Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin. 17 Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro. 18 Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu. 19 Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta. 20 Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu. 21 Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa. 22 Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji. 23 Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, "Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji." 24 Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, "Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu." 25 Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa. 26 An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji. 27 Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata, 28 sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce, 29 "Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka. 30 Domin idanuna sun ga cetonka, 31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane: 32 Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila." 33 Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa. 34 Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, "Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta. 35 Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana." 36 Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta, 37 sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana. 38 A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima. 39 Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat. 40 Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa. 41 Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa. 42 Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance. 43 Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba. 44 Suna tsammani yana tare da sauran mutane da suke tafiya tare, sai suka yi tafiya na kwana daya. Suka fara neman sa a cikin danginsu da abokansu. 45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima suna cigiyar sa a can. 46 Ya zama bayan kwanaki uku, su ka same shi a cikin haikali, yana zama a tsakiyar malamai, yana sauraron su yana kuma yi masu tambayoyi. 47 Dukan wadanda suka ji shi suna ta mamakin fahimtar sa da amsoshin sa. 48 Da suka gan shi, suka yi mamaki kwarai. Mahaifiyarsa ta ce masa, "Da na, don me ka yi mana haka? Ka ji, mahaifinka da ni muna ta neman ka rai a bace." 49 Ya ce masu, "Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?" 50 Amma ba su gane abin da yake nufi da kalmomin nan ba. 51 Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu. 52 Amma Yesu ya ci gaba da hikima da girma, ya kuma karu da tagomashi wurin Allah da mutane.

3

1 A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya, 2 kuma zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, maganar Allah ta zo wurin Yahaya dan Zakariya, a cikin jeji. 3 Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai. 4 Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, "Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! 5 Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada, 6 kuma dukan mutane za su ga ceton Allah." 7 Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, "Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8 Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. 9 Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta." 10 Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, "To me za mu yi?" 11 Ya amsa ya ce masu, "Idan wani yana da taguwa biyu, sai ya ba wanda bashi da ita daya, kuma wanda yake da abinci ya yi haka nan." 12 Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, "Malam, me za mu yi?" 13 Ya ce masu, "Kada ku karba kudi fiye da yadda aka umarce ku." 14 Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, "To, mu fa? Yaya za mu yi?" Ya ce masu, "Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku." 15 Ana nan da mutane ke sauraron zuwan Almasihu, kowa yana ta tunani a zuciyar sa game da Yahaya, ko shi ne Almasihu. 16 Yahaya ya amsa ya ce masu duka, "Game da ni dai, na yi maku baftisma da ruwa, amma akwai wani tafiye wanda ya fi ni iko, ban ma isa in kwance maballin takalmansa ba. Shi zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. 17 Kwaryar shikarsa na hanun sa domin ya share masussukarsa da kyau ya kuma tara alkama a cikin rumbunsa. Amma zai kona buntun da wuta marar mutuwa. 18 Da gargadi masu yawa ya yi wa mutanen wa'azin bishara. 19 Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi. 20 Amma Hirudus ya kara yin wani mugun abu. Ya sa an kulle Yahaya a cikin kurkuku. 21 Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude, 22 kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa a kamanin kurciya, sai wata murya ta fito daga sama, "Kai ne kaunataccen Da na. Ina jin dadin ka." 23 Ana nan Yesu da kansa, da ya fara, yana kimanin shekara talatin. Shi dan (kamar yadda ake tsammani) Yusufu ne, dan Heli, 24 dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu, 25 dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya, 26 dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda, 27 dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri, 28 dan Malki, dan Addi, dan Kosama, dan Almadama, dan Er, 29 dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi, 30 dan Saminu, dan Yahuda, dan Yusufu, dan Yonana, dan Aliyakima, 31 dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda, 32 dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, 33 dan Amminadab, dan Adimi, dan Arama, dan Hezruna, dan Feresa, dan Yahuda, 34 dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor, 35 dan Serug, dan Reyu, dan Feleg, dan Abiru, dan Shela, 36 dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek, 37 dan Metusela, dan Anuhu, dan Yaret, dan Mahalel, dan Kainana, 38 dan Enosh, dan Shitu, dan Adamu, dan Allah.

4

1 Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji 2 kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin. 3 Shaidan ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa." 4 Yesu ya amsa masa, "A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'" 5 Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci. 6 Shaidan ya ce masa, "Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama. 7 Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka." 8 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, "A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa." 9 Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan. 10 Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,' 11 kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse." 12 Yesu ya amsa masa cewa, "An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'" 13 Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci. 14 Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin. 15 Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa. 16 Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi. 17 An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta, 18 "Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci, 19 in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji." 20 Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa. 21 Sai ya fara masu magana, "Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku." 22 Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, "Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?" 23 Yesu ya ce masu, "Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'" 24 Ya sake cewa, "Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa. 25 Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar. 26 Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon. 27 Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai. 28 Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka. 29 Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa. 30 Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa. 31 Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a. 32 Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko. 33 A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya, 34 "Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!" 35 Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, "Yi shiru ka fita daga cikinsa!" Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba. 36 Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, "Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita." 37 Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin. 38 Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta. 39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima. 40 Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su. 41 Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, "Kai ne Dan Allah!" Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu. 42 Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su. 43 Amma ya ce masu, "Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan." 44 Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.

5

1 Ya zama sa'adda mutane sun taru a wurin Yesu suna sauraron maganar Allah, yana kuma yana tsaye a bakin tabkin Janisarata. 2 Ya ga jiragen ruwa biyu tsaye a bakin tabkin. Masu kamun kifin kuwa sun fita daga cikin jiragen suna wanke tarunsu. 3 Yesu ya shiga daya daga cikn jiragen wanda shike na Bitrus ne, sai ya umarce shi ya dan zakuda da jirgin daga bakin tabkin kadan zuwa cikin ruwa. Sai ya zauna ya kuma koya wa mutane daga cikin jirgin. 4 Da ya gama magana, ya ce wa Siman, "Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu." 5 Siman ya amsa ya ce, "Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun." 6 Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa. 7 Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa. 8 Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, "Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne." 9 Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama. 10 Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, "Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane." 11 Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi. 12 Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, "Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni." 13 Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, "Na yarda. Ka tsarkaka." Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi. 14 Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, "Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu." 15 Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu. 16 Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a. 17 Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa. 18 A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu. 19 Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu. 20 Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, "Maigida, an gafarta zunubanka." 21 Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, "Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?" 22 Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, "Don me kuke sukar wannan a zuciyarku? 23 Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?" 24 Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'" 25 Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah. 26 Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, "Yau mun ga abubuwan al'ajibi." 27 Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, "Ka biyo ni." 28 Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi. 29 Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su. 30 Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, "Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?" 31 Yesu ya amsa masu, "Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita. 32 Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba." 33 Sun ce masa, "Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?" 34 Yesu ya ce masu, "Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su? 35 Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi." 36 Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. "Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba. 37 Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace. 38 Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna. 39 Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, "Tsohon ya fi sabon."

6

1 Ana nan wata Asabaci Yesu yana ratsawa cikin gonar hatsi, almajiransa kuma na karyar zangarkun hatsin, suna murtsukawa a hanayensu suna ci. 2 Amma wasu daga cikin Farisawa suka ce, "Saboda me kuke yin abin da bai halatta a yi a ranar Asabaci ba?" 3 Yesu ya amsa masu, ya ce, "Ba ku karanta abin da Dauda ya yi a lokacin da yake jin yunwa ba, shi da mutanen da ke tare da shi? 4 Ya je cikin gidan Allah, ya dauki gurasar alfarwa ya kuma ci daga ciki, ya kuma ba mazajen da ke tare da shi su ci, ko da shike ya halarta ga Firistoci ne kadai su ci." 5 Sai ya ce masu, "Dan Mutum shi ne Ubangijin asabaci." 6 Ya kasance a wata ranar Asabaci ya shiga cikin majami'a ya kuma koya wa mutane a can. Wani mutum na can wurin wanda hannun damansa ya shanye. 7 Marubuta da Farisawa na kallonsa su ga ko zai warkar da wani a ranar Asabaci, domin su samu dalilin zarginsa da yin abin da bai cancanta ba. 8 Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, "Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a." Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan. 9 Yesu ya ce masu, "Ina tambayar ku, ya halatta a ranar Asabaci a yi nagarta ko mugunta, a ceci rai ko a hallaka shi? 10 Sai ya dube su duka, ya kuma ce wa mutumin, "Mika hannunka." Ya yi haka, sai hannunsa ya koma lafiyayye. 11 Amma suka fusata kwarai, suka yi shawara da junansu game da abin da za su yi da Yesu. 12 Ya zama a kwanakin nan, ya hawo bisan dutse domin ya yi addu'a. Ya ci gaba dukan dare yana addua'a ga Allah. 13 Da safiya ta yi, ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya kuma zabi goma sha biyu daga cikinsu, wadanda ya kira su "Manzanni." 14 Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus, 15 Matta, Toma, Yakubu dan Halfa, Siman, wanda ake kira Zaloti, Yahuda dan Yakubu, 16 da Yahuda dan Iskariyoti, wanda ya zama maci amana. 17 Sai Yesu ya gangaro daga dutsen tare da su, suka kuma tsaya a sarari. Almajiransa da yawa na nan a wurin, tare da mutane da yawa daga Yahudiya da Urushalima, da kuma bakin tekun Taya da Sidon. 18 Sun zo domin su ji shi, da kuma su sami warkarwa daga dukan cututukansu. Mutane waddan da ke fama da kazaman ruhohi ma sun sami warkarwa. 19 Dukan taron jama'ar suna kokarin su taba shi domin ikon warkarwa yana fitowa daga wurinsa, ya kuma warkar da su duka. 20 Sai ya dubi almajiransa ya ce, "Masu albarka ne ku matalauta, gama Mulkin Allah naku ne. 21 Masu albarka ne ku masu yunwa yanzu, domin za a kosar da ku. Masu albarka ne ku masu kuka a yanzu, domin za ku yi dariya. 22 Masu albarka ne ku idan mutane sun ki ku, suka nuna maku wariya suna mai da sunayen ku na mugunta, domin Dan Mutum. 23 Za ku yi farin ciki a ranan nan kuna tsalle domin murna, domin hakika za ku samu lada mai girma a sama, domin haka kakannin-kakannin su suka yi wa annabawa. 24 Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku. 25 Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba. 26 Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya. 27 Amma ina ce maku ku masu saurare na, ku kaunaci magabtanku, ku kuma aikata nagarta ga wadanda suke kinku. 28 Ku albarkaci masu zaginku, ku kuma yi addu'a ga wadanda suke wulakanta ku. 29 Wanda ya mare ku a wannan kunci, ku juya masa dayan. Idan wani ya dauki mayafinka, kada ka hana masa taguwarka. 30 Ku bayar ga duk wanda ya roke ku. Idan wani ya dauki wani abu da ke naku, kada ku bidi ya mayar da shi. 31 Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan. 32 Idan ka kaunaci masoyan ka ne kadai, me wannan zai amfane ka? Ko masu zunubi ma na kaunar masoyan su. 33 Idan kuna nuna alheri ga wadan da ke maku alheri kadai, menene ladan ku a nan? Ko masu zunubi ma na yin hakan nan. 34 Idan kun ba da rancen abubuwa ga mutanen da kuna sa zuciya zasu mayar maku ne kadai, menene ribar ku a nan? Ko masu zunubi suna ba masu zunubi rance, suna kuma sa zuciya a mayar masu dadai gwargwado. 35 Amma ku kaunaci magabtan ku, ku kuma nuna masu alheri. Ku basu rance, kada ku sa zuciya a maido maku, kuma sakamakon ku zai zama da girma. Za ku zama yayan Mafifici, domin shi da kansa yana nuna jinkai ga marasa godiya da miyagun mutane. 36 Ku zama masu jinkai, domin Ubanku mai jinkai ne. 37 Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku. 38 Ku bayar ga wasu, ku ma za a ba ku da yawa. Magwaji dankararre, girgizajje har ya cika yana zuba, za su zuba har cinyarku. Domin duk ma'aunin da ku ka yi amfani da shi, da shi za a auna maku. 39 Sai ya sake basu wani misali, "Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Idan ya yi haka, dukansu biyu za su fada cikin rami, ko ba haka ba? 40 Almajiri baya fin Malaminsa, amma duk wanda ya samu horo sosai zai zama kamar malaminsa. 41 Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? 42 Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. 43 Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya. 44 Domin ana iya sanin ko wani itace ta wurin 'ya'yan da yake bayarwa. Domin mutane basu kan tsinki 'ya'yan baure a jikin kaya, ko kuwa su dibi inabi daga jikin sarkakkiya. 45 Mutumin kirki, daga wadatar zuciyarsa ya kan ba da yaya masu kyau, kuma mugu daga cikin muguwar ajiyar zuciyarsa yake aikata mugunta. Domin daga cikar zuciyarsa ne bakinsa yakan yi magana. 46 Don me kuke ce da ni, 'Ubangiji, Ubangiji', amma ba ku yin biyayya da magana ta? 47 Duk wanda ya zo wurina ya ji kalmomina ya kuma yi biyayya da su, zan gaya maku yadda yake. 48 Yana kama da mutum da ke gina gida, wanda ya haka da zurfi zuwa cikin kasa ya kuma gina harshashin gidan sa a kan dutse. Da rigyawa ta zo, sai ruwa ya buga gidan, amma bai iya girgiza shi ba, domin an gina shi da kyau. 49 Amma duk mutumin da ya ji kalmomina ya kuma ki biyayya da su, yana kamar mutum wanda ya gina gidansa a kan kasa, babu harshashi. Amma da ambaliyan ruwa ta buga gidan, nan take ya rushe, ragargajewar gidan kuma da girma take.

7

1 Bayan da Yesu ya gama fadar dukan abubuwan da zai fadi a jin kunnen dukan mutanen, sai ya shiga Kafarnahum. 2 Bawan wani jarumi, wanda yake kauna, ba shi da lafiya har ma ya kusa mutuwa. 3 Amma da ya ji labarin Yesu, jarumin ya aiki wadansu dattawan Yahudawa, ya ce a roki Yesu ya zo ya ceci bawansa daga mutuwa. 4 Sa'adda su ka zo kusa da Yesu, su ka roke shi da gaske, cewa, "Wannan ya isa ka yi masa haka, 5 saboda shi mai kaunar kasar mu ne, kuma shi ne ya gina mana majami'a. 6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, "Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba. 7 Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke. 8 Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi." 9 Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, "Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba" 10 Daga nan wadanda a ka aika, suka dawo gida suka tarar da bawan cikin koshin lafiya. 11 Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa. 12 Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita. 13 Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, "Kada ki yi kuka." 14 Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi." 15 Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta. 16 Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, "An ta da wani annabi mai girma a cikinmu" kuma "Allah ya dubi mutanensa." 17 Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye. 18 Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa. 19 Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, "Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?" 20 Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, "Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, "Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?" 21 A cikin wannan lokaci, ya warkar da mutane da yawa daga cututtuka da matsaloli da miyagun ruhohi. Makafi da yawa sun sami ganin gari. 22 Yesu, ya amsa ya ce masu, "Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi. 23 Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi." 24 Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. "Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa? 25 Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna. 26 Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi. 27 Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, "Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka. 28 Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma. 29 Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma. 30 Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu. 31 Sa'annan Yesu ya ce, "Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama? 32 Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, "Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba." 33 Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa. 34 Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi! 35 Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta." 36 Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci. 37 Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi. 38 Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare. 39 Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, "In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce." 40 Yesu ya amsa ya ce masa, "Siman, ina so in gaya maka wani abu." Ya ce, "malam sai ka fadi!" 41 Yesu ya ce, "wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin. 42 Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?" 43 Siman ya amsa ya ce, "Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa." Yesu ya amsa ya ce masa, "Ka shari'anta dai dai." 44 Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, "Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta. 45 Kai ba ka yi ma ni sumba ba, amma ita ta yi, tun sa'adda na shigo nan ba ta dena sumbatar kafafuna ba. 46 Kai ba ka shafe kai na da mai ba, amma ita ta shafe kafafuna da turare. 47 Saboda haka, ita wadda ta ke da zunubi da yawa ta bayar da mai yawa, ta kuma nuna kauna mai yawa. Amma shi wanda aka gafarta wa kadan, ya kuma nuna kauna kadan." 48 Daga nan sai ya ce mata, "An gafarta zunubanki." 49 Wadanda su ke a nan zaune tare da shi suka fara magana da junansu, "Wanene wannan wanda har yake gafarta zunubai? 50 Sai Yesu ya ce da matar, "Bangaskiyarki ta cece ki. Ki tafi da salama."

8

1 Bayan haka, Yesu da almajiransa goma sha biyu, su ka zagaya cikin birane da kauyuka dabam dabam, suna wa'azi da shelar labari mai dadi game da mulkin Allah, 2 mata da yawa wadanda Yesu ya warkar daga aljanu da cututtuka iri iri suna tafiya tare da su. A cikinsu akwai Maryamu wadda a ke ce da ita Magadaliya, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta, 3 da Yuwana matar Kuza wakilin Hirudus, da Suzanatu da kuma wasu mata da yawa. Daga abin hannunsu suka tanada masu. 4 Wata rana aka tara taron mutane da yawa, saboda mutane su na zuwa daga birane da yawa domin su ga Yesu. Ya yi magana dasu cikin misali. 5 "Wani mai shuka ya tafi domin ya shuka iri. Sa'adda ya ke yafa iri, wadansu iri suka fada a kan hanya. Sai mutane suka tattake su, tsuntsaye kuma suka tsince wadansu suka cinye. 6 Wadansu kuma suka fada a kan duwatsu inda babu kasa da yawa. Da suka tsaro suka fara girma, sai nan da nan suka bushe saboda babu laima a wurin. 7 Wadansu irin kuma suka fada inda yake da kayayuwa. Tsiretsiren kayayuwan suka fito tare da irin da aka shuka, suka shake su yadda basu iya yin girma ba. 8 Amma wadansu irin suka fada a kan kasa mai kyau, suka yi girma sosai suka ba da anfani da yawa, har rubi dari." Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi kira gare su, "Duk mai kunnen ji, bari ya ji." 9 Sai almajiran Yesu suka tambaye shi ya gaya ma su ma'anar labarin. 10 ya ce da su, "Ku aka ba dama ku gane boyayyun abubuwa, na mulkin Allah. Amma ga sauran mutane ina yi masu magana cikin misalai, 'Domin ko da sun gani ba za su gane ba, kuma ko da sun ji ba za su fahimta ba." 11 To ga ma'anar misalin. Irin shi ne maganar Allah. 12 Irin da ya fada a kan hanya sune mutanen da suka ji maganar Allah amma daga baya sai shedan ya zo ya dauke maganar daga cikin hankulansu, domin kada su bada gaskiya su tsira. 13 Sa'annan, wadanda suka fada kan duwatsu sune mutanen da, da zarar sun ji maganar, sukan karbe ta da murna, amma ba su da sauyu; su kan bada gaskiya na dan lokaci kadan kawai, da zaran gwaji ya same su sai su ridda. 14 Irin da suka fada cikin kayayuwa, sune mutanen da suka ji maganar, amma da suka ci gaba da rayuwa, sai suka bari matsalolin rayuwa kamar dukiya da jin dadin rayuwa suka fi karfinsu, sai ya zama ba su iya bada 'ya'yan da suka yi girma ba. 15 Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya. 16 Ba mai kunna fitila, ya rufe ta da kasko, ko su sa ta a karkashin gado. Amma sai a sa ta a wurin zaman ta domin duk wanda ya shigo ya iya ganin hasken ta. 17 Babu abin da yake a boye wanda ba za a tone shi ba, ko wani asiri da ba za ya fito fili a san shi ba. 18 Ku yi hankali da yadda kuke ji, domin duk mai abu, shi za a kara wa, kuma duk mara abu, dan kadan da yake tunani yana da shi ma, za a dauke." 19 Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a. 20 Sai wani ya gaya masa, "Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka." 21 Amma Yesu ya amsa ya ce ma su, "Mahaifiyata da 'yan'uwana sune wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita." 22 Wata rana kuma Yesu ya shiga cikin jirgin ruwa, shi da almajiransa. Ya ce masu, "Ina so mu je dayan ketaren tafkin." Sai su ka fara tafiya domin su ketare tafkin. 23 Amma sa'adda su ke tafiya sai Yesu ya yi barci, sai wata iska mai karfi ta taso cikin tafkin, nan da nan sai jirgin ya fara cika da ruwa, kuma su na cikin hatsari. 24 Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, "Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!" Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit. 25 Daga nan sai ya ce da su, "Ina bangaskiyar ku?" Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, "Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?" 26 Suka zo yankin Garasinawa, wanda ke kusa da Gallili. 27 Sa'adda Yesu ya sauka kasa, sai wani mutum daga wannan yankin ya tarbe shi. Wannan mutum kuwa yana da aljanu. Mutumin ya dade ba ya sa tufafi, kuma ba ya zama a gida. Maimakon haka, sai a cikin kabarbura ya ke zama. 28 Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, "Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!" 29 Domin Yesu ya umarci aljanun su fita daga cikinsa, domin sau da dama aljanun sukan kama shi. Ko an daure mutumin da sarkoki an kuma tsare shi, yakan tsuttsunke su, kazaman ruhohin sukan kora shi cikin jeji. 30 Sa'annan Yesu ya tambaye shi, "Yaya sunanka?" Sai ya ba da amsa, "Suna na dubbai." Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum. 31 Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi. 32 Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu. 33 Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse. 34 Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen. 35 Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 36 Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi. 37 Sai dukan mutane wadanda suke cikin yankin Garasinawa da wadanda suke kewaye, suka roki Yesu da ya fita daga cikin yankin kasarsu domin sun ji tsoro kwarai da gaske. Daga nan Yesu da almajiransa suka shiga cikin jirgin ruwa suka koma. 38 Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, "Ka barni in tafi tare da kai!" Amma Yesu ya sallame shi cewa, 39 "Ka koma gida ka gaya wa mutanen ka abubuwa masu girma wadanda Allah ya yi maka." Daga nan sai mutumin ya tafi yana ta gayawa dukan mutanen birnin game da abubuwan da Yesu ya yi masa. 40 Sa'adda Yesu ya dawo, mutanen suka marabce shi, gama, dukansu suna jiransa. 41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, daya daga cikin shugabannin majami'a, ya zo kusa da Yesu ya rusuna da kansa a kasa. Ya roke shi domin ya zo gidansa, 42 saboda diyarsa mai kimanin shekara goma sha biyu ta na bakin mutuwa, kuma ita kadai ce diya a gare shi. Amma sa'adda yake tafiya, taron mutane da yawa suna matsa shi. 43 Akwai wata mace a nan wadda take zubar jini har shekara goma sha biyu. Ta kashe kudinta duka a wurin likitoci, domin su warkar da ita amma ba wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta biyo ta bayan Yesu ta taba habar rigarsa. Nan take sai zubar jinin ya tsaya. 45 Yesu ya ce, "Wanene ya taba ni?" Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, "Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai." 46 Amma Yesu ya ce, "Na sani, wani ya taba ni, domin iko ya fita daga wurina." 47 Sa'adda matar ta gane cewa ba za ta iya boyewa ba, sai ta zo wurinsa cikin tsoro. Ta durkusa a gaban Yesu, ta fada a gaban dukan jama'a dalilin da ya sa ta taba shi kuma nan da nan ta warke. 48 Sai ya ce da ita, "Diya, bangaskiyarki ta warkar da ke. Tafi cikin salama." 49 Yana cikin yin magana, wani daga cikin gidan shugaban majami'ar ya zo, ya ce, "Diyarka ta riga ta mutu, kada ka dami malam." 50 Amma sa'adda Yesu ya ji haka, sai ya ce da shi, "Kada ka ji tsoro. Ka bada gaskiya za ta rayu." 51 Sa'adda ya zo gidan, bai bar kowa ya shiga gidan tare da shi ba sai Bitrus da Yahaya da Yakubu, da mahaifiyar yarinyar da babanta. 52 Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, "Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!" 53 Mutanen suka yi ma sa dariyan reni, saboda sun sani yarinyar ta mutu. 54 Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, "Yarinya, na ce ki tashi!" 55 Nan da nan ruhun ta ya dawo jikin ta sai ta tashi. Ya ce masu su ba ta wani abu ta ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma Yesu ya ce da iyayen kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

9

1 Ya kira almajiransa goma sha biyu, ya ba su iko su fitar da kowanne irin aljani, su kuma warkar da cututtuka daga mutane. 2 Ya aike su, su yi wa'azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3 Ya ce masu, "Kada ku dauki komi tare da ku domin wannan tafiya. Kada ku dauki sanda, ko jakar matafiyi, ko gurasa, ko kudi - Kada ma ku dauki taguwa biyu. 4 Dukan gidan da ku ka shiga, ku zauna a gidan har zuwa lokacin da za ku tafi daga wannan yankin. 5 Dukan wadanda ba su marabce ku ba, sa'adda ku ke barin wannan gari, ku karkabe kurar kafufunku a matsayin shaida a kansu." 6 Daga nan sai almajiran suka tafi zuwa cikin kauyuka, suka yi ta shelar bishara, su na warkar da mutane a ko'ina. 7 Ana nan Hirudus, mai mulki, ya ji labarin dukan abubuwan da su ke faruwa. Ya yi mamaki saboda wadansu mutane suna cewa Yahaya mai yin Baftisma ne ya sake dawowa da ransa. 8 Wadansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sake bayyana, wadansu kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai. 9 Hirudus ya ce, "Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?" Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu. 10 Sa'adda manzannin suka dawo daga tafiyarsu, suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Daga nan sai ya dauke su domin su tafi tare da shi zuwa garin Baitsaida. 11 Amma sa'adda taron suka ji inda Yesu ya tafi, sai suka bi shi can. Ya marabce su ya yi masu jawabi a kan mulkin Allah, kuma ya warkar da wadanda su ke bukatar warkarwa. 12 Da yake yamma ta fara yi, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce da shi, "Idan ka yarda ka sallami wannan babban taron mutane dominsu shiga cikin kauyuka, da ke kewaye da gonaki, dominsu sami abinci da wuraren da za su kwana, da yake mu na nan a wurin da ba kowa." 13 Amma sai ya ce da su, "Ku ba su abin da za su ci." Suka amsa masa, "Dukan abin da muke da shi shine, 'Yan dunkulen gurasa biyar da 'yan kifaye guda biyu, ba za mu iya zuwa mu sawo abincin da zai ishi mutanen nan su duka ba." 14 Mutanen da suke wurin sun kai kimanin mazaje dubu biyar. Sai Yesu ya ce da almajiran, "Ku ce da mutanen su zauna kungiya-kungiya, mutane hamsin a kowacce kungiya." 15 Sai almajiran suka yi haka, dukan mutanen suka zauna. 16 Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa'annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane. 17 Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika! 18 Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, "Wa mutane suke cewa da ni?" 19 Suka amsa, "Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai." 20 Ya tambaye su, "Ku fa? Wa kuke cewa da ni?" Bitrus ya amsa, "Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah." 21 Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna. 22 Sa'annan ya ce, "Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai." 23 Sai ya ce da su duka, "Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni. 24 Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi. 25 Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? 26 Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki. 27 Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah." 28 Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu'a a can. 29 Sa'anda ya ke yin addu'a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya. 30 Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya. 31 Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima. 32 Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi. 33 Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, "Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya." Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba. 34 Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su. 35 Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, "Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi." 36 Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan. 37 Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa. 38 Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, "Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni. 39 Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi. 40 Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!" 41 Yesu, ya amsa, ya ce, "Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? "Kawo yaronka anan." 42 Sa'adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa'annan ya mika yaron wurin mahaifinsa. 43 Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa'anda suke ta yin mamaki a kan dukan al'ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa, 44 "Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane." 45 Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi. 46 Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu. 47 Amma Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya kawo dan karamin yaro ya tsaya a kusa da shi, 48 sai ya ce da su, "Idan wani ya karbi dan karamin yaro kamar wannan saboda ni, dai dai yake da ya karbe ni. Idan kuma wani ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni kenan. Wanda yake mafi kankanta a cikinku, shi ne mafi mahimmanci." 49 Yahaya ya amsa yace, "Ya shugaba, mun ga wani mutum yana ba miyagun ruhohi umarni su fita daga cikin mutane da sunanka. Sai muka ce da shi ya dena yin haka saboda baya tare da mu." 50 Amma Yesu ya ce, "Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku." 51 Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima. 52 Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can. 53 Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi. 54 Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, "Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?" 55 Amma, ya juya ya tsauta masu. 56 Sai suka tafi wani kauye dabam. 57 Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, "Zan bi ka dukan inda za ka tafi." 58 Yesu ya amsa masa, "Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta." 59 Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, "Ka biyo ni." Amma mutumin ya ce, "Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna." 60 Amma Yesu ya ce masa, "Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina." 61 Wani kuma ya ce, "Ubangiji zan tafi tare da kai, amma bari in je gida inyi ban kwana da mutanena tukuna." 62 Yesu ya ce da shi, "Dukan wanda ya fara huda a gonarsa idan ya dubi baya, bai isa ya shiga mulkin Allah ba."

10

1 Bayan wadannan abubuwa, Ubangiji ya sake nada wadansu saba'in ya aike su biyu biyu, domin su tafi kowanne birni da wurin da yake niyyan zuwa. 2 Ya ce da su, "Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan sun yi kadan. Saboda haka kuyi addu'a sosai ga Ubangijin girbin, domin ya aiko da ma'aikata cikin gonarsa. 3 Ku tafi, duba na aike ku kamar 'yan raguna cikin kyarkyetai. 4 Kada ku dauki jakan kudi, ko jakar matafiyi, ko takalma, kada ku gai da kowa a kan hanya. 5 Dukan gidan da ku ka shiga, ku fara cewa, 'Bari salama ta kasance a wannan gida.' 6 Idan akwai mutum mai salama a gidan, salamar ku za ta kasance a kansa, amma idan babu, salamar ku za ta dawo wurinku. 7 Ku zauna a wannan gidan, ku ci ku sha abin da suka tanada maku. Gama ma'aikaci ya wajibci ladansa. Kada ku bi gida gida. 8 Dukan birnin da ku ka shiga kuma sun karbe ku, ku ci abin da suka sa a gabanku. 9 Ku warkar da marasa lafiyar da ke wurin. Ku ce da su, 'Mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 10 Amma dukan birnin da ku ka shiga, idan ba su karbe ku ba, ku tafi cikin titunansu, ku ce, 11 'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 12 Na gaya maku, a ranar shari'a Saduma za ta fi wannan birni samun sauki. 13 Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki. 14 Amma a ranar shari'a Taya da Sidon za su fi ku samun sauki. 15 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani har zuwa sama za a daukaka ki? Babu, za a gangarar dake har zuwa hadas. 16 Wanda ya saurare ku ya saurare ni, wanda ya ki ku, ya ki ni, kuma wanda ya ki ni, ya ki wanda ya aiko ni." 17 Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, "Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka." 18 Sai Yesu ya ce masu, "Na ga Shaidan yana fadowa daga sama kamar walkiya. 19 Duba, na ba ku iko ku taka macizai da kunamai, da kuma kan dukan ikon magabci, kuma ba zai iya yin illa a gareku ba ko kadan. 20 Amma duk da haka kada ku yi murna a kan wannan kadai cewa ruhohi suna yi maku biyayya, amma ku yi murna domin an rubuta sunayenku a cikin sama." 21 Cikin wannan lokacin, ya yi farin ciki kwarai cikin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, "Na ba ka girma, ya Uba, Ubangijin sama da kasa. Domin ka rufe wadannan abubuwa daga masu hikima da ganewa, ka bayyana su ga wadanda ba koyayyu ba ne, kamar kananan yara. I, Uba gama haka ne ya gamshe ka." 22 Dukan abu, Ubana ya damka su gare ni, kuma babu wanda ya san Dan, sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Dan. Sai kuma wanda Dan ya yi niyyar ya bayyana Uban a gareshi." 23 Ya juya wajen almajiran, ya ce da su a kadaice, "Masu albarka ne su wadanda suka ga abin da kuke gani. 24 Na fada maku, annabawa da yawa, da sarakuna da yawa sun so da sun ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Kuma sun so da sun ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji su ba." 25 Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, "Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?" 26 Sai Yesu ya ce masa, "Yaya kake karanta abin da aka rubuta cikin shari'a?" 27 Ya amsa ya ce,"Dole ne ka kaunaci Ubangiji Allah da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka, da dukan lamirinka. Ka kuma kaunaci makwabcinka kamar kanka." 28 Yesu ya ce ma sa, "Ka amsa daidai, idan ka yi haka za ka rayu." 29 Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, "To, wanene makwabcina?" 30 Ya amsa ya ce, "Wani mutum yana tafiya daga Urushalima za shi Yariko. Sai ya fada hannun mafasa, suka tube shi, suka kwace dukan abin da ya ke da shi, suka yi masa duka, suka bar shi kamar matacce. 31 Ya zama sai ga wani firist ya na bin wannan hanya, da ya gan shi sai ya bi ta gefe daya ya wuce. 32 Haka kuma sai ga wani Balawi, sa'adda ya zo wurin, ya gan shi sai ya bi ta wani gefe ya wuce shi. 33 Amma wani Basamariye, ya na tafiya sa'adda ya zo wurin da mutumin yake, sa'adda ya ga mutumin sai tausayi ya kama shi. 34 Ya zo inda mutumin yake, ya daure masa raunukan da aka ji masa, yana shafa masu mai da ruwan inabi. Ya dora shi a kan dabbarsa ya kawo shi wurin kwana, ya kula da shi 35 Washegari ya kawo dinari biyu, ya ba mai wurin kwanan ya ce 'Ka kula da shi, idan ma ka kashe fiye da haka, idan na dawo zan biya ka.' 36 A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?" 37 Sai malamin ya ce, "Wannan da ya nuna masa jinkai" Sai Yesu yace masa, "Ka je kai ma ka yi haka." 38 Sa'adda suke tafiya, sai ya shiga cikin wani kauye, sai wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kafafun Ubangiji tana jin abin da yake fadi. 40 Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, "Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni." 41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, "Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa, 42 amma abu daya ne ya zama dole. Maryamu ta zabi abu mafi kyau, wanda ba za a iya kwace mata ba."

11

1 Wani lokaci, Yesu yana yin addu'a a wani wuri, sai daya daga cikin almajiransa yace da shi, "Ubangiji, ka koya mana yin addu'a kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa." 2 Yesu ya ce ma su, "Sa'anda ku ke yin addu'a ku ce, 'Uba a tsarkake sunanka. Mulkin ka ya zo. 3 Ka ba mu abin da za mu ci a kowacce rana. 4 Gafarta mana zunubanmu, kamar yadda muke gafarta ma wadanda suke mana laifi. Kada ka kai mu cikin jaraba.'" 5 Yesu ya ce masu, "Wanene a cikinku idan yana da aboki, za ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, "Aboki, ka ba ni rancen dunkulen gurasa guda uku, 6 da ya ke wani abokina ya iso yanzu daga tafiya, kuma ba ni da abin da zan ba shi ya ci,' 7 Sai wanda yake ciki, ya amsa, ya ce, 'Kada ka dame ni. Na riga na rufe kofa ta, kuma ni da yarana mun riga mun kwanta. Ba zan iya tashi in ba ka gurasa ba.' 8 Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata. 9 Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku. 10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa. 11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi? 12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama? 13 To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?" 14 Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki! 15 Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, "Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu." 16 Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama. 17 Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, "Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi. 18 Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba. 19 Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a. 20 Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku. 21 Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira. 22 Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa. 23 Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi. 24 Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro. 25 Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf. 26 Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni." 27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, "Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha." 28 Sai shi kuma ya ce, "Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita." 29 Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, "Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa. 30 Domin kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Neneba, haka kuma Dan Mutum za ya zama alama ga wannan tsara. 31 Sarauniyar Kudu, za ta tsaya ta yi shari'a da mutanen wannan tsara, kuma za ta kashe su, gama ta zo daga wuri mai nisa domin ta saurari hikimar Sulaimanu. Kuma ga wani wanda ya fi Sulaimanu a nan. 32 Mutanen Neneba, za su tsaya shari'a da matanen wannan tsara, kuma za su kashe su. Gama sun ji wa'azin Yunusa sun tuba. Kuma ga wani wanda ya fi Yunusa a nan. 33 Ba wanda zai kunna fitila ya boye ta, ko kuwa ya sa ta a karkashin kasko, amma zai sa ta a mazaunin ta domin dukan wanda ya shiga dakin ya ga haske. 34 Idon ku shine fitilar jikinku. Idan idonku yana gani sosai, jikinku zai cika da haske. Amma idan idonku ba ya gani sosai, jikinku zai cika da duhu. 35 Ku yi hankali fa, domin kada hasken da ya ke wurinku ya zama duhu. 36 Idan dukan jikinku yana cike da haske, babu duhu ko kadan, to sai dukan jikinku ya zama kamar fitilar da take bada haskenta a bisanku." 37 Sa'adda ya gama jawabi, sai wani Bafarise ya ce da shi ya zo gidansa ya ci abinci, sai Yesu ya shiga ya zauna. 38 Sai Bafarisen ya yi mamaki da ganin bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba. 39 Amma sai Ubangiji ya ce da shi, "Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta. 40 Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba? 41 Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta. 42 Amma kaitonku Farisawa, gama kuna karbar zakka da daddoya da karkashi da kowanne irin ganye na lambu, amma kun watsar da adalci da kaunar Allah. Dole ne a yi adalci, a kaunaci Allah, a yi sauran abubuwan kuma. 43 Kaitonku Farisawa, domin kuna so a ba ku wuraren zama masu kyau a cikin masujadai, a kuma yi maku gaisuwar bangirma a cikin kasuwanni. 44 Kaiton ku, gama kuna kama da kabarbarun da ba yi masu shaida ba, mutane kuwa suna tafiya akansu ba tare da saninsu ba." 45 Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, "Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma." 46 Sai Yesu ya ce, "Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba. 47 Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su. 48 Ya zama kenan kuna sane da ayyukan kakanni-kakanninku, domin sune suka kashe annabawan da kuke tunawa da su. 49 Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, "Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.' 50 Wannan tsarar, za ta dauki alhakin jinin dukan annabawan da aka kashe tun kafuwar duniya. 51 Tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya wanda aka kashe tsakanin bagadi da wuri mai tsarki. I, na gaya ma ku za a nemi hakin su a wurin wannan tsarar 52 Kaitonku malaman shari'a na Yahudawa, domin kun dauke mabudin sani, ku da kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana masu shiga su shiga." 53 Bayan da Yesu ya bar nan wurin, Marubuta da Farisawa suka yi gaba da shi, suka yi jayayya da shi a kan abubuwa da yawa, 54 suna kokari su kafa masa tarko domin su kama shi a cikin kalmomin da yake fadi.

12

1 Da jimawa kadan, bayan da mutane da yawa suka taru kwarai har suna tattaka junansu. Sai ya fara yin magana da almajiransa. "Ku yi lura da yisti na Farisawa, wanda shine manufunci. 2 Amma ba abin da ke rufe wanda ba za a tone ba, ba kuma abin da ke boye wanda ba za a sani ba. 3 Saboda haka ba abin da za ku fadi a asirce wanda ba za a ji shi a cikin sarari ba. Abin da ku ka fadi da rada cikin lungu, za a yi shelarsa a ko'ina. 4 Ina gaya maku abokaina, kada ku ji tsoron wanda da za su kashe jiki. Bayan haka kuma ba abin da za su iya yi. 5 Bari in gargade ku a kan wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron shi wanda bayan ya kashe zai iya jefa ku cikin jahannama. I, ina ce maku ku ji tsoronsa. 6 Ba a kan sayar da 'yan tsuntsaye biyar a kan anini biyu ba? Duk da haka, Allah ba zai manta da ko daya daga cikinsu ba. 7 Har ma gashin da ke kan ku ya san yawan su. Kada ku ji tsoro, ku kun fi tsuntsaye daraja a wurinsa. 8 Ina gaya maku, dukan wanda za ya shaida ni a gaban mutane, Dan Mutum kuma za ya shaida shi a gaban mala'kun Allah. 9 Kuma dukan wanda ya ki ni a gaban mutane, za a ki shi a gaban mala'ikun Allah. 10 Dukan wanda ya yi magana gaba da Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma shi wanda ya yi sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11 Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce. 12 Gama Ruhu Mai Tsarki zai koya maku abin da za ku fadi a wannan lokaci." 13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, "Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni 14 Yesu ya ce masa, "Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?" 15 Sai kuma ya ce masu, "Ku yi lura kada ku zama masu hadama, gama ba abin da mutum ya mallaka ne ya fi mahimmanci a cikin rayuwar sa ba." 16 Sa'annan Yesu ya fada masu wani misali, ya ce, "Gonar wani mutum ta bada amfani sosai, 17 ya yi tunani, ya ce, 'Me zan yi, domin ba ni da wurin da zan iya ajjiye amfanin gonata?' 18 Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa. 19 Sai in ce da raina, "Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna." 20 Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?' 21 Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah." 22 Yesu, ya ce da almajiransa, "Saboda haka ina cewa da ku, kada ku damu da rayuwarku, wato, abin da za ku ci, ko abin da za ku sa a jikinku. 23 Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja! 25 Wanene a cikinku ta wurin sha'awarsa za ya iya karawa kansa kwanaki? 26 Idan ba ku iya yi wa kanku dan karamin abu ba, me ya sa za ku damu da sauran abubuwa? 27 Ku dubi furanni a daji - yadda suke yin girma. Ba su kan yi aiki ba, ba su kan yi kadi ba. Ina gaya maku, ko Sulaimanu, a cikin darajarsa, bai sa tufafin da suka fi nasu kyau ba. 28 Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya! 29 Kada ku damu da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kuma kada ku yi alhini. 30 Gama dukan al'umman duniya suna neman wadannan abubuwa, kuma Ubanku ya san kuna bukatar wada nan abubuwan. 31 Amma ku bidi mulkinsa, wadannan abubuwa kuma za a kara maku su. 32 Kada ku ji tsoro, ku 'yan kanana, domin da murna Ubanku zai ba ku mulkin. 33 Ku sayar da abin da ku ke da shi ku ba matalauta. Kuyi wa kanku jakukkuna wadanda ba za su lalace ba, ku yi ajjiya cikin sama inda abin ba ya karewa, inda barayi ba za su iya zuwa ba, kwari kuma ba za su iya lalatawa ba. 34 Domin inda dukiyarka take, can zuciyarka za ta kasance kuma. 35 Ku rage tsawon tufafinku, ku yi dammara, ya zama fitilarku tana ci koyaushe, 36 ku kuma zama kamar wadanda suke jiran mai gidansu ya dawo daga gidan buki, domin duk sa'adda ya zo ya kwankwasa kofa, nan da nan za su bude masa. 37 Masu albarka ne wadannan bayi, wadanda ubangijinsu za ya tarar suna jiran dawowar sa. Gaskiya ni ke gaya ma ku, zai yi dammara yasa su zazzauna ya ba su abinci shi da kansa. 38 Ko da ubangijinsu ya zo da dare, ko da tsakar dare, ya tarar da su a shirye suna jiransa. Masu albarka ne wadannan bayi. 39 Kuma ku san wannan, da mai gida ya san lokacin da barawo zai zo, ba zai bari a fasa masa gida a shiga ba. 40 Sai ku zauna da shiri fa domin ba ku san lokacin da Dan Mutum zai dawo ba." 41 Sai Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?" 42 Sai Ubangiji ya ce, "Wanne shugaba ne, mai aminci, mai hikima kuma wanda ubangijinsa za ya damka bayinsa a hannunsa, domin ya kula da su, ya ba su abincinsu a kan lokaci? 43 Mai albarka ne wannan bawa, wanda ubangijinsa za ya tarar da shi yana yin abin da aka sa shi ya yi. 44 Hakika, ina gaya maku, zai danka dukan malakarsa a gareshi. 45 Amma idan wannan bawa, ya ce a cikin zuciyarsa, 'Ubangiji na yayi jinkirin dawowa,' sai ya fara dukan bayin, maza da mata abokan bautarsa, ya ci ya sha, ya bugu, 46 ubangijin bawan nan zai dawo a lokacin da bawan bai sa tsammani ba, kuma a cikin lokacin da bai sani ba, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ya kuma hada shi da marasa aminci. 47 Bawan nan, ya san halin ubagijinsa, amma bai shirya yayi abin da ubangijinsa yake so ba. Zai sha duka da bulala da yawa. 48 Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi. 49 Na zo domin in sa wuta a duniya, na so da ta riga ta kama. 50 Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta! 51 Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa. 52 Daga yanzu za a sami mutane biyar a cikin gida daya, kuma za su rarrabu, mutane uku suna gaba da biyu, biyun kuma suna gaba da ukun. 53 Da da mahaifi za su yi gaba da juna, dan zai yi gaba da mahaifinsa. Mahaifiya za ta yi gaba da diyarta, diya kuma gaba da mahafiyarta; uwar miji za ta yi gaba da matar danta, matar da kuma gaba da uwar mijinta." 54 Yesu, ya kuma gaya wa taron, "Da kun ga hadari ya taso daga yamma, nan da nan sai ku ce za a yi ruwa, haka kuwa ya kan zama. 55 Idan iska tana busowa daga kudu sai ku ce za a yi zafi mai tsanani, haka kuwa ya kan faru. 56 Munafukai, kun iya fasarta yanayin kasa da sama, amma baku iya fasarta abin da yake faruwa yanzu ba? 57 Me ya sa ba ku iya gane abin da zai tamake ku? 58 Idan kuna tafiya wurin shari'a da abokin husumarka, ka yi kokari ku daidaita tun a kan hanya domin kada ya kai ka wurin mai shari'a. Domin kada mai shari'a ya mika ka ga mai tsaron kurkuku, shi kuwa mai tsaron kurkuku ba zai nuna maka sani a cikin kurkuku ba. 59 Na gaya maka, ba za ka iya fitowa ba sai ka biya dukan kudin da a ke binka?

13

1 A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu. 2 Sai Yesu ya amsa masu yace "Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka? 3 A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu. 4 Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5 Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka" 6 Yesu ya fada wannan misali, "Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba. 7 Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, "ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza? 8 Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki. 9 In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!"' 10 Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci. 11 Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta." 13 Sai Yesu ya dora hannunsa a kanta, nan da nan sai ta mike a tsaye ta fara daukaka Allah. 14 Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, "Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba." 15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, "Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci? 16 Ashe wannan 'yar gidan Ibrahim, wanda shaidan ya daure ta shekara goma sha takwas, wato ba za a iya kwance ta a ranar Asabaci kenan ba? 17 Da ya fada wadannan abubuwa, dukansu da suka yi adawa da shi suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwa masu daraja da yayi. 18 Sai Yesu ya ce, "Yaya za a misalta mulkin Allah, kuma da me zan kwatanta shi? 19 Yananan kamar kwayar mastad, wanda wani mutum ya dauka ya jefa ta a lambunsa, ta kuma yi girma ta zama gagarumin itace, har tsuntsaye suka yi shekarsu a rassanta." 20 Ya sake cewa, "Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21 Yana kamar yisti wanda wata mace ta dauka ta cuda da mudu uku na garin alkama don ya kumburar da shi." 22 Yesu ya ziyarci kowanne birni da kauye, a hanyar sa ta zuwa Urushalima yana koyar da su. 23 Sai wani ya ce masa, "Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?" Sai ya ce masu, 24 "Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa, domin na ce maku, mutane dayawa za su nemi shiga amma ba za su iya shiga ba. 25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.' 26 Sannan za ku ce, 'Mun ci mun sha a gabanka, ka kuma yi koyarwa a kan titunanmu.' 27 Amma zai amsa ya ce, "Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!' 28 Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje. 29 Za su zo daga gabas, yamma, kudu, da arewa, za su ci a teburin abinci a mulkin Allah. 30 Ku san da wannan, na karshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na karshe." 31 Nan take, wadansu farisiyawa suka zo suka ce masa, "Ka tafi daga nan domin Hirudus yana so ya kashe ka." 32 Yesu ya ce, "Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.' 33 Ko da kaka, dole ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don bai dace a kashe annabi nesa da Urushalima ba. 34 Urushalima, Urushalima masu kisan annabawa, masu jifan wadanda aka aiko gare ku. Sau nawa ne ina so in tattara 'ya'yanki kamar yadda kaza take tattara 'ya'yanta a cikin fukafukanta, amma ba ki so wannan ba. 35 Duba, an yashe gidanki. Ina kwa gaya maku ba za ku kara ganina ba sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.'"

14

1 Wata ranar Asabaci, ya shiga gidan wani daya daga cikin shugabanin Farisawa domin cin abinci, mutane kuwa suna sa masa idanu. 2 Sai ga wani a gabansa mai ciwon fara. 3 Yesu ya tambaye masanan attaura da Farisawa, "Ya halata a wakar a ranan Asabaci, ko a'a?" 4 Amma suka yi shiru. Yesu kuwa ya kama shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5 Sai yace masu, "Wanene a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya fadi a rijiya ran Asabaci, ba zai fitar da shi nan da nan ba?" 6 Sai suka kasa ba da amsar wadannan abubuwa. 7 Sa'adda Yesu ya lura da yadda wadanda aka gayyato sun zabi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali yana ce masu, 8 "Sa'adda wani ya gayyace ka zuwa bikin aure, kada ka zauna a wuri mai daraja, domin yana yiwuwa an gayyaci wani wanda ya fi ka daraja. 9 Sa'adda wanda ya gayyace ku duka biyu ya zo, zai ce maka, 'Ka ba mutumin nan wurinka,' sa'annan a kunyace za ka koma mazauni mafi kaskanci. 10 Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi. 11 Duk wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, wanda ya kaskantar da kansa, kuma daukaka shi za a yi". 12 Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, "Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka. 13 Amma idan za ka kira biki sai ka gayyace matalauta, da nakasassu, da guragu, da makafi, 14 za ka kuwa sami albarka da yake ba su da hanyar saka maka. Gama za a saka maka a ranar tashin masu adalci." 15 Da daya daga cikin wadanda ke zama akan teburi da Yesu ya ji wadannan abubuwa, sai ya ce masa, "Albarka ta tabbata ga wanda zai ci abinci a mulkin Allah!" 16 Amma Yesu ya ce masa, "Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa ya ce wa wadanda aka gayyata, "Ku zo, duk an shirya kome." 18 Sai dukansu, suka fara kawo dalilai. Na farko ya ce masa, 'Na sayi gona, lalle ne in je in gan ta. Ina rokonka ka dauke mani.' 19 Sai wani ya ce, 'Na sayi shanu garma biyar, ina so in gwada su. Ina ronkan ka, ka dauke mani.' 20 Wani mutum kuma ya ce, 'Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.' 21 Da bawan ya zo ya fadi wa maigidansa wadannan abubuwa, sai maigidan yayi fushi, ya ce wa bawansa, jeka da sauri ka bi cikin titunan birni da kwararo-kwararo, ka kawo gajiyayyu, da nakasassu, da makafi, da guragu.' 22 Sai bawan ya ce, 'Maigida, abin da ka umarta an gama, amma har yanzu da sauran wuri." 23 Sai maigidan ya ce wa bawan, 'Jeka, ka bi kwararo-kwararo da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24 Gama ina gaya maku, babu ko daya daga cikin mutanen da na gayyata da farko da zai dandana bikina." 25 Ana nan, taron suna tafiya tare da shi, sai ya juya ya ce masu, 26 "Duk mai zuwa wurina amma bai ki mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa maza da mata ba - I, har da ransa ma, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Duk wanda bai dauki gijiyensa ya biyo ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Wanene a cikinku wanda yake niyyar gina bene, da ba zai zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba tun da farko, ko yana da ishashen kudi da zai iya kare aikin? 29 Kada ya zama bayan da ya sa harsashin ginin, ya kasa gamawa, har duk wadanda suka gani su fara yi masa ba'a, 30 su rika cewa, ga mutumin nan ya fara gini amma ya kasa gamawa.' 31 Ko kuwa wanne sarki ne, in za shi je yaki da wani sarki, da ba zai zauna da farko ya yi shawara ya ga ko shi mai jarumawa dubu goma zai iya karawa da dayan sarkin mai jarumawa dubu ashirin ba? 32 In kuwa ba zai iya ba, to tun wancan yana nesa, sai ya aiki wakili ya kuma tambayo sharudan salama. 33 Haka ma, ba wani a cikinku wanda bai rabu da duk abin da ya mallaka ba, da zai iya zama almajirina." 34 "Gishiri abu ne mai kyau, amma idan gishiri ya sane, da me za a dadada shi? 35 Ba shi da wani anfani a kasa, ko ya zama taki. Sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji."

15

1 To sai duk masu karbar haraji da masu zunubi suna ta zuwa wurin Yesu suna sauraronsa. 2 Dukan Farisawa da Marubuta suna ta gunaguni da junansu, cewa, "Wannan mutum yana karbar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci." 3 Yesu ya fadi wannan misali, ya ce, 4 "Idan waninku yana da tumaki dari, sai dayarsu ta bace, wato ba zai bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta bata gudan nan har sai ya same shi ba? 5 Idan kuwa ya same ta, sai ya dauke ta a kafadarsa yana farin ciki. 6 In ya dawo gida, sai ya kira abokansa da makwabta, yace masu, 'Ku taya ni murna don na samo tunkiyata da ta bata.' 7 Ina gaya maku, haka kuma za a yi farin ciki a sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu adalci tassa'in da tara wadanda ba su bukatar tuba. 8 Ko kuwa wacce mace ce, in tana da kudi azurfa guda goma, in ta batar da daya, ba za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta neman shi har sai ta same shi ba? 9 In kuwa ta same shi sai ta tara kawayenta da makwabtanta, ta ce, 'Ku taya ni farin ciki don na sami kudin nan nawa da ya bace.' 10 Haka nake gaya maku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah idan mai zunubi guda ya tuba." 11 Sai Yesu ya ce, "Akwai wani mutum mai 'ya'ya biyu maza, 12 sai karamin ya ce wa mahaifinsa, 'Baba, bani rabona daga cikin dukiyarka.' Sai mahaifinsa ya raba masu dukiyarsa tsakaninsu. 13 Bayan 'yan kwanaki kadan, sai karamin dan ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa wata kasa mai nisa. A can ya batas da kudinsa, yana sayan abubuwan da ba ya bukata, ya kuma batas da kudinsa a wajen masha'a. 14 Bayan da ya batas da duk abin da ya ke da shi, sai aka yi babbar yunwa a kasar, sai ya shiga fatara. 15 Ya je ya mika kansa domin aiki ga wani dan kasar, sai ya aike shi cikin gonakinsa domin ya rika ba aladu abinci. 16 Har yayi marmarin ya ci daga cikin barbashin da aladu suke ci, domin babu wanda yake ba shi wani abu ya ci. 17 Amma da hankalinsa ya dawo, ya ce, 'Barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe, amma ina nan a nan, ina mutuwa sabili da yunwa! 18 Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, "Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. 19 Ban cancanci a kara kira na danka ba; ka mai da ni kamar daya daga cikin barorinka.'" 20 Sai ya tashi, ya taho wurin mahaifinsa. Amma tun yana daga nesa, sai mahaifinsa ya hango shi tausayi ya kama shi, ya ruga a guje, ya rungume shi, ya yi ta sumbatar sa. 21 Dan kuma ya ce masa, 'Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. Ban isa a kara kira na danka ba.' 22 Amma mahaifinsa ya ce wa bayinsa, 'Ku yi hamzari ku kawo riga mafi kyau, ku yafa masa. Ku sa masa zobe a hanunsa da takalma a kafafunsa. 23 Sa'annan a kawo kiwataccen marakin nan, a yanka. Mu yi buki! 24 Gama da na ya mutu a da, amma yanzu yana a raye. Ya bata a da, amma a yanzu an same shi.' Sai suka fara liyafa. 25 A wannan lokacin, babban dansa yana gona. Da ya kai kusa da gida, ya ji ana kade-kade da raye-raye. 26 Sai ya kira wani bawan gidan, ya tambayi manufar wadannan abubuwa. 27 Bawan ya ce masa, 'Dan'uwanka ne ya dawo gida, mahaifinka kuma ya yanka kiwataccen marakin nan, saboda ya dawo gida lafiya.' 28 Amma dan'uwan ya yi fushi, ya ki ya shiga ciki, mahaifinsa kuwa ya fito, ya roke shi. 29 Amma babban dan ya amsa wa ubansa ya ce, 'Duba, duk yawan shekarun nan da nake bauta maka, ban taba karya umarnin ka ba, duk da haka ba ka taba bani ko dan taure da zan yi shagali tare da abokaina ba, 30 amma da dan nan naka ya zo wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ka yanka masa kiwataccen marakin nan. 31 Sai mahaifin ya ce masa, 'Dana, ai kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. 32 Amma, daidai ne a yi murna da farinciki, don dan'uwan nan naka da ya mutu, amma yanzu yana da rai, da ya bata, amma yanzu an same shi.'"

16

1 Yesu ya kuma ce wa almajiransa, "Akwai wani mai arziki da yake da wakili, sai aka yi karan sa da cewa wannan wakili yana fallasar masa da dukiya. 2 Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, 'Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.' 3 Sai wakilin ya ce a ransa, 'Kaka zan yi, da yake maigida na zai karbe wakilci daga hannuna? Gashi, ba ni da karfin noma ina kuwa jin kunya in yi roko. 4 Na san abin da zan yi domin idan an fitar da ni daga wakilcin, mutane su karbe ni a gidajensu. 5 Sai wakilin ya kira kowanne daya da maigidansa ke bi bashi, yace wa na farkon, 'Nawa maigida na yake bin ka?' 6 Ya ce, 'Garwan mai dari.' Sai ya ce masa, 'Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.' 7 Ya kuma ce wa wani, 'Nawa ake binka?' Ya ce, 'Buhu dari na alkama.' Ya ce masa, 'Ga tarkardarka, ka rubuta tamanin.' 8 Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama 'ya'yan zamanin nan a ma'ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi 'ya'yan haske wayo. 9 Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama. 10 Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya? 12 Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku? 13 Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba." 14 Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a. 15 Sai ya ce masu, "Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah. 16 Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta. 17 Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude. 18 Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina. 19 Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana. 20 Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne, 21 Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa. 22 Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi, 23 yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa. 24 Sai ya yi kira ya ce, 'Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li'azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.' 25 Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26 Banda haka ma, akwai rami mai zurfi, domin wadanda suke son ketarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ketaro zuwa wurinmu daga can.' 27 Sai mai arziki ya ce, 'To ina rokonka, Baba Ibrahim, ka aike shi zuwa gidan mahaifina - 28 domin ina da 'yan'uwa maza biyar, ya je ya yi masu gargadi kada su ma su zo wurin azaban nan.' 29 Amma Ibrahim ya ce, 'Suna da Musa da annabawa; bari su saurare su.' 30 Sai mai arziki ya amsa, 'A'a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.' 31 Amma Ibrahim ya ce masa, 'In dai har basu saurari Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su rinjayu ba.'"

17

1 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, 'Babu shakka akwai sanadodin tuntube da za su sa mu yin zunubi amma kaiton wanda shine sanadin su! 2 Zai gwammaci a rataya masa dutsen nika a wuyansa, a jefar da shi a cikin teku fiye da wanda zai zama sanadiyar tuntube ga wadannan kananan. 3 Ku kula da kanku. Idan dan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa, in kuwa ya tuba ka yafe masa. 4 Idan ya yi maka laifi sau bakwai a rana daya sa'annan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, 'Na tuba,' ya wajabta ka yafe masa!" 5 Sai Manzannin suka ce wa Ubangiji, 'Ka kara mana bangaskiya.' 6 Ubangiji kuwa ya ce, "In kuna da bangaskiya kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan durumin, 'Ka tuge, ka kuma dasu a cikin teku,' zai yi biyayya da ku. 7 Amma wanene a cikinku, idan yana da bawa mai yin masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, 'Maza zo ka zauna ka ci abinci'? 8 Ba zai ce masa, 'Ka shirya mani wani abu domin in ci ka kuma yi damara, ka yi mini hidima har in gama ci da sha. Bayan haka sai ka ci ka sha'? 9 Ba zai yi wa bawan nan godiya ba domin ya yi biyayya da abubuwan da aka umarce shi ya yi, ko zai yi haka? 10 Haka kuma, idan kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, 'Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibi ne kurum.'" 11 Wata rana yana tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili. 12 Yayin da yana shiga wani kauye kenan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi suna tsaye daga nesa da shi 13 sai suka daga murya suka ce, "Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai." 14 Da ya gan su, ya ce masu, "Ku je ku nuna kanku a wurin firistoci." Ya zama sa'adda suke tafiya, sai suka tsarkaka. 15 Daya daga cikinsu da ya ga an warkar da shi, ya koma, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi. 16 Ya fadi a gaban Yesu, yana masa godiya. Shi kuwa Basamariye ne. 17 Yesu ya amsa ya ce, "Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina sauran taran? 18 Babu wani da ya dawo ya girmama Allah sai wannan bakon kadai?" 19 Sai ya ce masa, "Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai." 20 Da Farisawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai bayyana, Yesu ya amsa masu ya ce, "Mulkin Allah ba lura ake yi da shi ba. 21 Ba kuwa za a ce, 'Gashi nan!' Ko kuwa, 'Ga shi can ba!' domin mulkin Allah yana tsaknaninku." 22 Yesu ya ce wa almajiran, "Kwanaki na zuwa da za ku yi begen ganin rana daya cikin ranakun Dan Mutum, amma ba zaku gani ba. 23 Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su. 24 Kamar yadda walkiya take haskakawa daga wannan bangaren sararin sama zuwa wancan bangaren, haka ma dan mutum zai zama a ranar bayyanuwarsa. 25 Amma lalle sai ya sha wahaloli dabam dabam tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ki shi. 26 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Dan Mutum. 27 Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har zuwa ga ranar da Nuhu ya shiga jirgi - ruwan tufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28 Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine. 29 Amma a ranar da Lutu, ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da kibiritu daga sama, aka hallaka su duka. 30 Haka kuma zai zama a ranar bayyanuwar Dan Mutum. 31 A ranar nan fa, wanda yake kan soro kada ya sauka domin daukan kayansa daga cikin gida. Haka kuma wanda yake gona kada ya dawo. 32 Ku tuna fa da matar Lutu. 33 Duk mai son ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai same shi. 34 Ina gaya maku, a wannan dare za a sami mutum biyu a gado daya. Za a dauka daya, a kuma bar dayan. 35 Za a sami mata biyu suna nika tare. Za a dauka daya a bar daya." 36 1 37 Sai suka tambaye shi, "Ina, Ubangiji?" Sai ya ce masu, "Duk in da gangar jiki yake, a nan ungulai sukan taru."


1Luka 17:36 mafi kyawun tsoffin kwafi ba su da aya 36, Za a ga mutum biyu a gona. Za a dauki daya a bar daya .

18

1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a kada kuma su karaya, 2 yace, "A wani gari an yi wani alkali mara tsoron Allah, kuma baya ganin darajan mutane. 3 Akwai wata mace gwauruwa a wannan garin, wadda ta rika zuwa wurinsa, tana ce masa, 'Ka taimake ni yanda zan sami adalci a kan abokin gaba na.' 4 An dade bai so ya taimaka mata, amma daga baya sai ya ce a ransa, 'ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma darajanta mutane, 5 duk da haka saboda gwauruwar nan ta dame ni, zan taimake ta domin ta sami adalci, yadda ba za ta gajiyar da ni da zuwanta wurina ba.'" 6 Sai Ubangiji ya ce, "Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya fada. 7 A yanzu Allah ba zai biya wa zababbunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne? 8 Ina gaya maku, zai biya masu hakkin su da wuri. Amma sa'adda Dan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya?" 9 Ya sake ba da misalin nan ga wadansu masu amincewa da kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, 10 "Wadansu mutane biyu suka shiga haikali domin yin addu'a - daya Bafarise, dayan kuma mai karbar haraji ne. 11 Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin. 12 Duk mako ina azumi sau biyu. Nakan bayar da zakkar dukan abin da na samu.' 13 Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.' 14 Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi." 15 Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su. 16 Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, "Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne. 17 Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba." 18 Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce "Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?" 19 Yesu ya ce masa, "Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai. 20 Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka." 21 Sai shugaban ya ce, "Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta." 22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, "Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni." 23 Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai. 24 Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, "Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah! 25 Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah." 26 Wadanda suka ji wannan magana suka ce, "Idan hakane wa zai sami ceto kenan?" 27 Yesu ya amsa, "Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah." 28 Sai Bitrus ya ce, "To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka." 29 Yesu ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah, 30 sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa." 31 Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, "Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata. 32 Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau. 33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi." 34 Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba. 35 Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara, 36 da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene. 37 Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa. 38 Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, "Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai." 39 Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, "Dan Dauda, ka yi mani jinkai." 40 Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi, 41 "Me kake so in yi maka?" Ya ce, "Ubangiji, ina so in samu gani." 42 Yesu ya ce masa, "Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai." 43 Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

19

1 Yesu ya shiga Yariko ya na wucewa cikinta. 2 Sai ga wani mutum a wurin mai suna Zakka. Shugaba ne na masu karban haraji, kuma mai arziki ne. 3 Yana kokarin ya ga ko wanene Yesu, amma bai iya gani ba sabo da yawan jama'a, domin shi gajere ne. 4 Sai ya ruga gaba ya hau itacen baure domin ya gan shi, saboda Yesu zai wuce ta wannan hanya. 5 Sa'adda Yesu ya zo wurin, ya kalli sama sai ya ce masa, "Zakka, ka sauko da sauri, domin yau dole in sauka a gidanka." 6 Sai ya sauko da sauri, ya karbe shi da farin ciki. 7 Sa'adda dukansu suka ga wannan, sai suka yi gunaguni, cewa, "Ya ziyarci mutum mai zunubi." 8 Zakka ya tsaya ya ce wa Ubangiji, "Duba, Ubangiji, zan ba matalauta rabin arzikina, idan kuma na cuci wani a kome, zan mai da adadinsa sau hudu." 9 Yesu ya ce masa, "Yau ceto ya shigo wannan gida, domin shi ma dan Ibrahim ne. 10 Gama Dan Mutum ya zo ne domin ya nemi, ya kuma ceci batattun mutane." 11 Da suka ji wadannan abubuwan, ya cigaba da magana, sannan ya fada masu wani misali, domin yana kusa da Urushalima, sai suka yi tsamani mulkin Allah za ya bayyana nan da nan. 12 Sai ya ce, "Akwai wani mutum mai sarauta wanda ya tafi wata kasa mai nisa domin ya karba wa kansa mulki sa'annan ya dawo. 13 Sai ya kira bayinsa guda goma, ya ba su fam goma, sai ya ce masu, 'Ku yi kasuwanci da wannan har sai na dawo.' 14 Amma mutanensa suka ki shi sai suka aiki jakadu bayansa, cewa, 'Ba za mu yarda wannan mutum ya yi mulki a kanmu ba.' 15 Anan nan sa'adda ya koma kuma, bayan da ya sami mulkin, sai ya ba da umarni a kira masa bayin da ya basu kudi, domin ya san ribar da suka samu wajen kasuwancin da suka yi. 16 Na farkon ya zo wurinsa, cewa, 'Ubangiji, fam nan na ka ya yi riban fam goma.' 17 Masaraucin ya ce masa, 'Madalla, bawan kirki. Domin ka yi aminci a karamin abu, za a baka iko kan birane goma.' 18 Na biyun ya zo, yana cewa, 'Fam na ka, Ubangiji, ya yi ribar fam biyar.' 19 Sai masarauncin yace masa, 'Ka dauki mulkin birane biyar.' 20 Wani kuma ya zo, yana cewa, 'Ubangiji, ga fam naka da na ajjiye shi da kyau cikin kaya, 21 gama na ji tsoronka, domin kai mutum mai tsanani ne. Kana daukar abu da baka ajiye ba, kana kuma girbin abin da ba ka shuka ba.' 22 Masarauncin ya ce masa, 'Da kalmominka zan shari'antaka, kai mugun bawa. Ka sani cewa ni mutum mai tsanani ne, ina daukan abinda ban ajiye ba, ina kuma girbin abinda ban shuka ba. 23 To don me ba ka kai kudi na wurin masu banki ba, saboda bayan da na dawo zan karbe shi da riba?' 24 Masaraucin ya ce wa wadanda suke a tsaye a wurin, 'Ku karba fam da ke a wurinsa, ku ba mai fam goman nan.' 25 Suka ce masa, 'Ubangiji, yana da fam goma.' 26 'Ina ce maku, duk wanda yake da abu za a kara masa, amma wadda bai da shi, za a karba sauran da ke wurinsa. 27 Amma wadannan abokan gabana, wadanda ba sa so in yi mulki bisansu, a kawo su nan a kashe su a gaba na.' 28 Da ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi gaba, yana tafiya zuwa Urushalima. 29 Ananan sa'adda ya zo kusa da Baitfaji da Baitanya, a kan tudu da a ke kira Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, cewa, 30 cewa, "Ku tafi cikin kauye da ke gabanku. Sa'adda ku ka shiga, za ku same dan aholaki da ba a taba hawansa ba. Ku kwance sai ku kawo mani shi. 31 Idan wani ya tambaye ku, 'Don me ku ke kwance shi?' Ku ce, 'Ubangiji ne ke bukatarsa." 32 Wadanda aka aike su suka je sun sami aholakin kamar yadda Yesu ya gaya masu. 33 Sa'adda suna kwance aholakin, sai masu shi suka ce masu, "Don me ku ke kwance aholakin?" 34 Suka ce, "Ubangiji yana bukatar sa." 35 Suka kawo wa Yesu, suka shimfida tufafinsu akan aholakin sai suka dora Yesu akansa. 36 Da yana cikin tafiya, suka shimfida tufafinsu akan hanya. 37 Da ya yi kusa da gangaren tudun Zaitun, sai dukan taron almajiransa suka fara yin murna suna kuma yabon Allah da murya mai karfi domin dukan ayukan al'ajibi da suka gani, 38 cewa, "Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!" 39 Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, "Malam, ka tsauta wa almajiranka." 40 Yesu ya amsa ya ce, "Ina gaya maku gaskiya, in wadannan sun yi shiru, duwatsu za su yi shewa." 41 Sa'adda Yesu yana kusatowa, sai ya yi kuka akan birnin, 42 cewa, "Da kun san wannan rana, ko ku ma, abubuwan da ke kawo maku salama! Amma yanzu an boye su daga idanunku. 43 Gama rana zata ta zo a gareki, da makiyan ki zasu gina ganuwa a kewaye da ke, su kuma fada maki daga kowace gefe. 44 Za su sare ki kasa tare da 'ya'yanki. Ba za su bar wani dutse akan dan'uwansa ba, domin ba ki lura da lokacin da Allah ya na kokarin ceton ki ba." 45 Yesu ya shiga Haikalin sai ya fara korar masu sayarwa, 46 ya na ce masu, "A rubuce yake, 'Gida na zai zama wurin addu'a,' amma kun mayar da shi kogon mafasa." 47 Yesu yana nan yana koyarwa kowace rana a cikin haikali. Amma manyan firistoci da marubuta da shugabanin jama'a suna so su kashe shi, 48 amma ba su sami hanyar yin wannan ba, domin mutane suna sauraron sa sosai.

20

1 Ana nan wata rana, Yesu yana kan koyarwa a haikali da wa'azin bishara, sai shugaban firistoci da marubuta suka zo wurinsa da dattawa. 2 Suka yi magana, su na ce masa, "Gaya mana da wanne iko ne ka ke yin wadannan abubuwan? Ko wanene ya baka wannan ikon?" 3 Ya amsa sai ya ce masu, "Ni ma zan yi maku tambaya. Gaya mani game 4 da baptisman Yahaya. Daga sama take ko kuwa daga mutane ne?" 5 Sai suka yi mahawara da junansu, suna cewa, "In mun ce, 'Daga sama,' zai ce, 'To don me ba ku ba da gaskiya gareshi ba?' 6 Amma in mun ce, 'Daga mutane ne,' dukan mutane za su jejjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata a ransu Yahaya annabi ne." 7 Sai suka amsa cewa ba su san ko daga ina ne take ba. 8 Yesu yace masu, "To haka ni ma ba zan gaya maku ko da wanne iko nake yin wadannan abubuwan ba." 9 Ya gaya wa mutane wannan misali, "Wani mutum ya dasa gonar inabi, ya ba wadansu manoma jinginarta, sai ya tafi wata kasa har ya dade. 10 Da lokacin girbi ya yi sai ya aiki wani bawansa zuwa wurin manoman, saboda su bashi daga cikin anfanin gonar. Amma manoman suka doke shi, sai suka kore shi hannu wofi. 11 Ya aike wani bawa kuma sai suka daddoke shi, suka kunyatar da shi, suka kore shi hannu wofi. 12 Ya kuma sake aike na uku suka yi masa rauni, suka jefar da shi a waje. 13 Sai mai gonar inabin ya ce, 'Me zan yi? Zan aiki kaunattacen dana. Watakila zasu ba shi daraja.' 14 Amma sa'adda manoman suka gan shi, suka yi shawara a tsakaninsu, cewa, 'Wannan ne magajin. Bari mu kashe shi, saboda gadon ya zama namu.' 15 Suka jefar da shi waje daga gonar, suka kashe shi. Menene ubangijin gonar inabin zai yi da su? 16 Zai zo ya halakar da wadannan manoma, sai ya ba wadansu gonar." Da suka ji wannan, suka ce, "Allah ya sawake!" 17 Amma Yesu ya kalle su, sai yace, "Menene ma'anar wannan nassi? 'Dutsen da magina suka ki, an mayar da shi kan kusurwa'? 18 Duk wanda ya fadi kan dutsen zai farfashe. Amma duk wanda dutsen ya fadi a kansa, zai rugurguza shi." 19 Sai marubutan da manyan firistocin suka so su kama shi a wannan sa'a, domin sun sani ya yi wannan misali a kansu ne. Amma sun ji tsoron mutane. 20 Suna fakonsa, suka aiki magewaya, wadanda suke kamar masu adalci, saboda su sami kuskure cikin maganarsa, don su mika shi ga hukumci da kuma ikon gwamna. 21 Suka tambaye shi, cewa, "Malam, mun sani da cewa kana fada da koyar da abin ke daidai, kuma ba wanda yake cusa maka ra'ayi, amma kana koyar da gaskiya game da hanyar Allah. 22 Wai shin doka ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?" 23 Amma Yesu ya gane makircinsu, sai ya ce masu, 24 "Nuna mani dinari. Sifar wanene da kuma rubutun wanene akan sa?" Suka ce, "Na Kaisar ne." 25 Sai ya ce masu, "To sai ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma ba Allah, abin da ke na Allah." 26 Marubutan da manyan firistocin ba su sami abin zargi cikin maganarsa, a gaban mutane ba. Suka yi mamakin amsar sa, ba su kuma ce komai ba. 27 Sa'adda wadansu Sadukiyawa suka zo wurinsa, wadan da suka ce babu tashin mattatu, 28 suka tambaye shi, cewa, "Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro. 29 Akwai 'yan'uwa guda bakwai kuma na farin ya yi aure, sai ya mutu babu da, 30 haka ma na biyun. 31 Na ukun ya aure ta, haka nan na bakwai ma bai bar yaya ba, har suka mutu. 32 Daga baya sai matar ma ta mutu. 33 To a ranar tashin mattatu, matar wa za ta zama? Domin duka bakwai din sun aure ta." 34 Yesu ya ce masu, "'Ya'yan duniyan nan suna aure, ana kuma ba da su ga aure. 35 Amma wadanda aka ga cancantarsu a waccan tsara, sun isa su sami tashin mattatu, ba za suyi aure ko a aurar da su ba. 36 Gama ba za su mutu kuma ba, domin suna daidai da mala'iku kuma su 'ya'yan Allah ne, da shike su 'ya'yan tashin matattu ne. 37 Amma batun tashi matattu, ko Musa ma ya nuna wannan, a cikin jeji, inda ya kira Ubangiji, Allah na Ibrahim da kuma Allah na Ishaku da Allah na Yakubu. 38 Yanzu shi ba Allahn matattu ba ne, amma na masu rai, saboda duka suna raye a wurinsa." 39 Wadansu marubuta suka amsa, "Malam, ka amsa da kyau." 40 Gama ba su sake yi masa wadansu tambayoyi ba. 41 Yesu ya ce masu, "Yaya suke cewa Almasihu dan Dauda ne? 42 Gama Dauda da kansa ya ce a cikin littafin Zabura, Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, 'Zauna a hannun dama na, 43 sai na maida makiyanka a karkashin tafin sawunka.' 44 Dauda ya kira Kristi 'Ubangiji', to ta yaya ya zama dan Dauda?" 45 Dukan mutane suna ji ya ce wa almajiransa, 46 "Ku yi hankali da marubuta, wadanda suna son tafiya da manyan riguna, suna kuma son a gaishe su a cikin kasuwanni, da mayan wuraren zama a cikin majami'u, da kuma manyan wurare a wurin bukukkuwa. 47 Suna kuma kwace wa gwamraye gidaje, suna kuma badda kama ta wurin yin doguwar addu'a. Wadannan za su sha hukumci mai girma."

21

1 Yesu ya tada ido sai ya ga mutane masu arziki wadanda suke saka baikonsu a cikin ma'aji. 2 Ya ga wata gwauruwa matalauciya tana saka anini biyu a ciki. 3 Sai ya ce, "Gaskiya ina gaya maku, wannan matalauciyar gwauruwa ta saka fiye da dukansu. 4 Duka wadannan sun bayar da baikonsu daga cikin yalwarsu. Amma wannan gwauruwan, daga cikin talaucin ta, ta saka dukan iyakar kudinta na zaman gari da take da shi." 5 Kamar yadda wadansu suke maganan haikali, yadda aka yi masa ado da duwatsu masu daraja da bayebaye, ya ce, 6 "Game da wadannan abubuwa da ku ke gani, rana tana zuwa da ba dutse ko daya da zai zauna kan dan'uwansa da ba za a rushe kasa ba." 7 Sai suka yi masa tambaya, cewa, "Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?" 8 Yesu ya amsa, "Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su. 9 Sa'adda ku ka ji game da yakoki da hargitsi, kada ku firgita, dole ne wadannan abubuwa su faru tukuna, amma karshe ba zai faru nan da nan ba." 10 Sa'annan ya ce masu, "Al'umma za ta tasar ma al'umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki. 11 Za a yi babbar girgizan kasa, a wurare dabam dabam kuma za a yi yunwa da annoba. Za a yi al'amura masu ban tsoro da manyan alamu daga sama. 12 Amma kafin abubuwan nan duka, za su kama ku, su kuma tsananta maku, suna mika ku ga majami'u da kuma gidajen kurkuku, za su kawo ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana. 13 Zai zamar maku zarafin shaida. 14 Saboda haka ku kudurta a ranku kada ku shirya yadda za ku amsa, 15 gama ni zan ba ku kalmomi da hikima, wadda dukan makiyanku ba za su yi tsayayya ko su karyata ku ba. 16 Amma har da mahaifa da 'yan'uwa da dangi da abokai za su bashe ku, su kuma kashe wadansun ku. 17 Kowa zai ki ku saboda sunana. 18 Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka. 19 A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku. 20 Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa. 21 Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki. 22 Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika. 23 Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan. 24 Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika. 25 Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa. 26 Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai. 27 Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma. 28 Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato." 29 Yesu ya bada misali, "Duba itacen baure, da duka itatuwa. 30 Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma. 31 Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa. 32 Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru. 33 Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 34 Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri 35 kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya. 36 Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum." 37 Da rana yana koyarwa a cikin haikali, dukan dare kuma yakan tafi dutsen da a ke kira zaitun. 38 Dukan mutane suka rika zuwa wurinsa da sassafe domin su ji shi a haikali.

22

1 Anan nan idin gurasa mara yisti ya yi kusa, wanda a ke kira Idin ketarewa. 2 Manyan firistoci da marubuta suka yi shawara yadda za su kashe Yesu, gama suna jin tsoron mutane. 3 Shaidan ya shiga Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin goma sha biyun. 4 Yahuza ya je ya yi shawara da manyan firistoci da Jarumawa yadda zai ba da Yesu a garesu. 5 Suka yi farin ciki, suka yarda su ba shi kudi. 6 Sai ya yarda, sai ya nimi dama yadda zai ba da shi garesu a lokacin da babu taro. 7 Ranar idin gurasa mara yisti ya yi, da dole za a yi hadayan rago na Idin ketarewa. 8 Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce masu, "Ku je ku shirya mana abincin Idin ketarewa, domin mu ci." 9 Suka tambaye shi, "A ina ka ke so mu shirya?" 10 Ya amsa masu, "Ku ji, sa'adda ku ka shiga birnin, wani mutum mai dauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bishi zuwa cikin gidan da za ya shiga. 11 Sai ku gaya wa mai gidan, 'Malam ya ce, "Ina dakin baki, inda zan ci abincin Idin ketarewa da almajirai na?'" 12 Zai nuna maku babban bene wanda yake a shirye. Ku shirya a can." 13 Sai suka tafi, suka sami komai kamar yadda ya gaya masu. Sai suka shirya abincin Idin ketarewan. 14 Sa'adda lokacin ya yi, ya zauna da almajiran. 15 Sai ya ce masu, "Ina da marmari matuka in ci wannan abincin Idin ketarewa da ku kamin in sha wahala. 16 Gama na ce maku, ba zan ci shi kuma ba, sai dai an cika shi a mulkin Allah." 17 Sai Yesu ya dauki koko, sa'adda ya yi godiya, sai yace, "Karba wannan, ku rarraba a tsakaninku. 18 Gama ina ce maku, ba zan sha wannan ruwan inabi kuma ba, sai dai mulkin Allah ya zo." 19 Sai ya dauki gurasa, sa'adda ya yi godiya, ya kakkarya shi, sai ya ba su, cewa, "Wannan jikina ne wanda aka bayar dominku. Ku yi wannan domin tunawa da ni." 20 Sai ya dauki kokon kuma bayan jibi, cewa, "Wannan koko sabon alkawari ne cikin jinina, wanda aka zubar dominku. 21 Amma ku yi lura. Wanda zai bashe ni yana tare da ni a teburi. 22 Gama Dan Mutum zai tafi lallai kamar yadda aka kaddara. Amma kaiton wannan mutum da shine za ya bashe shi!" 23 Sai suka fara tambaya a tsakaninsu, wanene a cikinmu da zai yi wannan abu. 24 Sai gardama ta tashi a tsakaninsu game da wanene mafi girma. 25 Ya ce masu, "Sarakunan al'ummai suna nuna iko akansu, kuma wadanda suke da iko a kansu ana ce da su masu mulki da daraja. 26 Amma kada ya zama haka da ku. A maimakon haka, bari wanda ya ke mafi girma a cikinku ya zama mafi kankanta. Bari wanda yafi muhimmanci kuma ya zama kamar mai hidima. 27 Gama wanene yafi girma, wanda ya zauna a teburi, ko kuwa wanda yake yin hidima? Ba wanda ya zauna a teburi ba? Duk da haka ina kamar mai hidima a tsakaninku. 28 Amma ku ne wadanda ku ke tare da ni a cikin jarabobina. 29 Na baku mulki, kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, 30 domin ku ci ku kuma sha a teburi na mulkina. Za ku zauna a kan kursiyai kuna shari'anta kabilun nan goma sha biyu na Israila. 31 Siman, Siman, ka yi hankali, shaidan ya nemi izini a bada kai domin ya tankade ka kamar alkama. 32 Amma na yi maka addu'a, saboda kada bangaskiyarka ta fadi. Bayan da ka juyo kuma, ka karfafa 'yan'uwanka." 33 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa." 34 Yesu ya amsa masa, "Ina gaya maka, Bitrus, kamin caran zakara a yau, za ka yi musu na sau uku cewa ba ka sanni ba." 35 Sa'annan Yesu ya ce masu, "Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, "Babu." 36 Ya kuma ce masu, "Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda. 37 Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika." 38 Sai suka ce, "Ubangiji, duba! Ga takuba biyu." Sai ya ce masu, "Ya isa." 39 Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi. 40 Sa'adda suka iso, ya ce masu, "Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba." 41 Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a, 42 yana cewa "Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance." 43 Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi. 44 Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini. 45 Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu, 46 sai ya tambaye su, "Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba." 47 Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba, 48 amma Yesu ya ce masa, "Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?" 49 Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, "Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?" 50 Sai daya daga cikinsu ya kai wa bawan babban firist sara a kunne, sai ya yanke masa kunnensa na dama. 51 Yesu ya ce, "Ya isa haka." Sai ya taba kunnensa, sai ya warkar da shi. 52 Yesu yace wa manyan firistoci, da masu tsaron haikali, da dattawa wadanda suke gaba da shi, "Kun fito kamar za ku kama dan fashi, da takuba da sanduna? 53 Sa'adda nake tare da ku kowace rana a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan shine lokacinku, da kuma ikon duhu." 54 Suka kama shi, sai suka tafi da shi, suka kawo shi cikin gidan babban firist. Amma Bitrus yana binsa daga nesa. 55 Bayan da suka hura wuta a tsakiyar gidan da suka zazzauna tare, Bitrus ya zaune a tsakaninsu. 56 Sai wata baranya ta ganshi ya zauna a hasken wuta, sai ta zura masa ido ta ce, "Wannan mutum ma yana tare da shi." 57 Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, "Mace, ban san shi ba." 58 Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, "Kaima kana daya daga cikinsu." Amma Bitrus ya ce, "Mutumin, ba ni ba ne." 59 Bayan sa'a daya sai wani mutum ya nace da cewa, "Gaskiya wannan mutum yana tare da shi, gama shi dan Galili ne." 60 Amma Bitrus ya ce, "Mutumin, ban san abin da kake fada ba." Sai nan da nan, da yana cikin magana, sai zakara ta yi cara. 61 Yana juyawa, sai Ubangiji ya dubi Bitrus. Sai Bitrus ya tuna kalmar Ubangiji, sa'adda ya ce masa, "Kafin zakara ya yi cara yau za ka musunce ni sau uku." 62 Da fitowarsa waje, Bitrus ya yi kuka mai zafi. 63 Sai mutanen da ke tsare da Yesu suka yi masa ba'a da bulala kuma. 64 Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, "Ka yi annabci! Wa ya buge ka?" 65 Suka yi wadansu miyagun maganganu na sabo game da Yesu. 66 Da gari ya waye, sai dattawa suka hadu tare, da manyan firistoci da marubuta. Sai suka kai shi cikin majalisa 67 suka ce, "Gaya mana, in kai ne Almasihu." Amma yace masu, "Idan na gaya maku, ba za ku gaskanta ba, 68 idan na yi maku tambaya, ba za ku amsa ba. 69 Amma nan gaba, Dan Mutum zai zauna a hannun dama na ikon Allah." 70 Suka ce masa, "Ashe kai Dan Allah ne?" Sai Yesu ya ce masu, "Haka kuka ce, nine." 71 Suka ce, "Don me muke neman shaida? Gama mu da kanmu munji daga bakinsa."

23

1 Sai duk taron suka tashi, suka kawo Yesu gaban Bilatus. 2 Suka fara saransa, cewa "Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki." 3 Bilatus ya tambaye shi, cewa "Shin kaine Sarkin Yahudawa?" Sai Yesu ya amsa masa ya ce, "Haka ka ce." 4 Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, "Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba." 5 Amma suka yi ta cewa, "Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri." 6 Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline. 7 Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin. 8 Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi. 9 Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba. 10 Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi. 11 Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus. 12 Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne). 13 Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar, 14 sai ya ce masu, "Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba. 15 Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa, 16 saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi." 17 1 18 Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, "A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!" 19 Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai. 20 Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu. 21 Amma suka yi ihu, cewa, "A giciye shi, a giciye shi." 22 Sai ya sake ce masu sau na uku, "Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi." 23 Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus. 24 Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so. 25 Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu. 26 Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu. 27 Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa. 28 Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, "Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku. 29 Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.' 30 Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.' 31 Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?" 32 Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su. 33 Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu. 34 Yesu yace, "Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba." Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa. 35 Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, "Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan." 36 Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami, 37 suna cewa, "Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka." 38 Akwai wata alama bisansa, "Wannan shine Sarkin Yahudawa." 39 Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, "Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu." 40 Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, "Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa? 41 Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba." 42 Sai ya kara, "Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka." 43 Yesu ya ce masa, "Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi." 44 Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara 45 sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa. 46 Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, "Uba, na mika Ruhu na a hannunka." Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu. 47 Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, "Lallai wannan mutumin mai adalci ne." 48 Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu. 49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa. 50 Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne 51 (bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah. 52 Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu. 53 Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba. 54 Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato. 55 Matan da suka taho da shi tun daga Galili, suka biyo baya, su ga kabarin da inda aka ajiye shi. 56 Suka koma, sai suka shirya kayan kamshi da mai. Suka kuma huta a ranar Asabaci bisa ga doka.


1Mafi kyawun kwafin tsoffin ba su da Luka 23:17, Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin .

24

1 Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya. 2 Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin. 3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba. 4 Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya. 5 Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, "Don me kuke neman mai rai ciki matattatu? 6 Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili, 7 cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma" 8 Sai matan suka tuna da kalmominsa, 9 suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran. 10 Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan. 11 Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba. 12 Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru. 13 A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima. 14 Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru. 15 Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su. 16 Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba. 17 Yesu ya ce masu, "Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?" Suka tsaya a wurin suna bakin ciki. 18 Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, "Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?" 19 Yesu ya ce masu, "Wadanne abubuwa?" Suka amsa masa, "Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane. 20 Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi. 21 Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru. 22 Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe. 23 Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai. 24 Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba." 25 Yesu ya ce masu, "Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada! 26 Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?" 27 Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai. 28 Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su. 29 Amma suka tilasta shi, cewa, "Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa." Sai Yesu ya tafi ya zauna da su. 30 Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su. 31 Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu, 32 Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?" 33 Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su, 34 cewa, "Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman." 35 Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa. 36 Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, "Salama a gareku." 37 Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa. 38 Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku? 39 Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su." 40 Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa. 41 Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, "Kuna da wani abinci?" 42 Sai suka bashi gasasshen kifi. 43 Yesu ya karba, ya ci a gabansu. 44 Sai ya ce masu, "Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika." 45 Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai. 46 Ya ce masu, "A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku. 47 Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima. 48 Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan. 49 Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama." 50 Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su. 51 Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama. 52 Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa. 53 Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.

Yahaya
Yahaya
1

1 A cikin farko akwai Kalma, Kalmar kuma tana tare da Allah, wannan Kalma kuwa Allah ne. 2 Shi kuwa tare da Allah yake tun farko. 3 Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta sai ta wurin sa. 4 A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane. 5 Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba. 6 Akwai wani mutum wanda Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7 Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa. 8 Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken. 9 Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya. 10 Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba. 11 Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba. 12 Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah. 13 Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah. 14 Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya. 15 Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, "Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'" 16 Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri. 17 Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu. 18 Babu lokacin da wani ya taba ganin Allah, shi wanda shi kadai ne Allah, wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana shi. 19 Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, "Wanene kai?" 20 Ya fada dalla dalla, kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa, "ba nine Almasihu ba." 21 Sai suka tambaye shi, "To kai wanene? Kai Iliya ne?" Yace, "Ba ni ba ne." Suka ce, "Kai ne anabin?" Ya amsa, "A'a". 22 Sai suka ce masa, "Kai wanene, domin mu bada amsa ga wadanda suka aiko mu? Me kake fadi game da kanka?" 23 Yace, "Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada." 24 Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa, 25 "To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?". 26 Yahaya ya amsa masu, cewa, "Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba, 27 shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba." 28 Wadannan abubuwa sun faru ne a Baitanya, a dayan ketaren Urdun, a wurin da Yahaya ke Baftisma. 29 Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, "Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya! 30 Wannan shine wanda na fada maku cewa, "Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.' 31 Ban san shi ba, amma saboda a bayyana shi ga Isra'ila ne nazo ina baftisma da ruwa." 32 Yahaya ya shaida, cewa, "Na ga Ruhu yana saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. 33 Ban gane shi ba, amma shi wanda ya aiko ni in yi baftisma cikin ruwa ya fada mani cewa, 'duk wanda ka ga Ruhun ya sauka kuma ya zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.' 34 Na gani, na kuma shaida cewa wannan shine Dan Allah." 35 Kuma, washegari, da Yahaya na tsaye da biyu daga cikin almajiransa, 36 suka ga Yesu na wucewa, sai Yahaya ya ce, "Duba, ga Dan rago na Allah!" 37 Sai almajiransa biyu suka ji ya fadi haka, suka kuwa bi Yesu. 38 Da Yesu ya waiwaya ya gan su suna bin sa, sai ya ce masu, "Me kuke so?" Suka amsa, "Rabbi (wato 'Mallam'), ina kake da zama?" 39 Yace masu, "Zo ku gani." Sai suka zo suka ga inda yake zama; suka zauna da shi ranan nan, gama wajen sa'a ta goma ne. 40 Daya daga cikin wadanda suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu shine Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus. 41 Ya fara neman dan'uwansa Siman yace masa, "Mun sami Almasihu" (wanda ake kira 'Kristi'). 42 Ya kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi yace, "Kai ne Siman dan Yahaya. Za a kira ka Kefas," (ma'ana, 'Bitrus'). 43 Washegari, da Yesu yana shirin tafiya zuwa Galili, sai ya sami Filibus, ya ce masa, "ka biyo ni." 44 Filibus dan asalin Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus. 45 Filibus ya sami Natana'ilu yace masa, "Mun same shi, shi wanda Musa ya rubuta shi a cikin attaura, da annabawa: Yesu Dan Yusufu, Ba-Nazarat." 46 Natana'ilu ya ce masa, "za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?" Filibus yace masa, "Zo ka gani." 47 Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, "Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa." 48 Natana'ilu yace masa, "Ta yaya ka san ni?" Sai Yesu ya amsa masa yace, "Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'adda kake a gindin baure, na gan ka." 49 Natana'ilu ya amsa, "Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!" 50 Yesu ya amsa masa yace, "Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma." 51 Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum."

2

1 Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin. 2 An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren. 3 Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, "basu da ruwan inabi." 4 Yesu yace mata, "Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna". 5 Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, "Ku yi duk abin da yace maku." 6 To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda. 7 Yesu yace masu, "Cika randunan da ruwa". Sai suka cika randunan makil. 8 Sai yace wa ma'aikatan, "Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki." Sai suka yi hakannan. 9 Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango 10 yace masa, "Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu." 11 Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi. 12 Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki. 13 To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima. 14 Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin. 15 Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu. 16 Yace wa masu sayar da tantabaru, "Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci." 17 Almajiransa suka tuna a rubuce yake, "Himma domin gidanka za ta cinye ni." 18 Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?" 19 Yesu ya amsa, "Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi." 20 Sai shugabanin Yahudawa suka ce, "An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?" 21 Amma yana nufin haikali na jikinsa ne. 22 Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada. 23 Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi. 24 Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka, 25 saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.

3

1 akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa. 2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, "Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi." 3 Yesu ya amsa masa, "Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba." 4 Nikodimu ya ce masa, "Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?" 5 Yesu ya amsa, "Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba. 6 Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.' 8 Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu." 9 Nikodimu ya amsa yace masa, "Yaya wannan zai yiwu?" 10 Yesu ya amsa yace masa, "Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba? 11 Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba. 12 Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama? 13 Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum. 14 Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum 15 domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada. 16 Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa. 18 Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba. 19 Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne. 20 Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu. 21 Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu. 22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma. 23 Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma, 24 domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna. 25 Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa. 26 Suka je wurin Yahaya suka ce, "Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa." 27 Yahaya ya amsa, "Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama. 28 Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.' 29 Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan. 30 Dole shi ya karu, ni kuma in ragu. 31 Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa. 32 Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa. 33 Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne. 34 Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba. 35 Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa. 36 Shi wanda ya bada gaskiya ga Dan ya na da rai madawwami, amma wanda ya ki yiwa Dan biyayya ba zai ga rai ba, amma fushin Allah na kansa.

4

1 Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya 2 (ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne), 3 ya bar Yahudiya ya koma Galili. 4 Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya. 5 Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu. 6 Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne. 7 Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, "Ba ni ruwa in sha." 8 Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci. 9 Sai ba-Samariyar tace masa, "Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?" Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa. 10 Sai Yesu ya amsa yace mata, "In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai." 11 Matar tace masa, "Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai? 12 Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?" 13 Yesu ya amsa yace mata, "duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi, 14 amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami." 15 Matar tace masa, "Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba." 16 Yesu ya ce mata, "Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare." 17 Matar ta amsa tace masa, "Ba ni da miji." Yesu yace, "Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,' 18 domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne." 19 Matar tace masa, "Mallam, Na ga kai annabi ne. 20 Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada." 21 Yesu ya ce mata, "Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima. 22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada. 24 Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya." 25 Matar ta ce masa, "Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu. 26 Yesu ya ce mata, "Ni ne shi, wanda ke yi maki magana." 27 A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, "Me kake so?" Ko kuma, "Don me ka ke magana da ita?" 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen, 29 "Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?" 30 Suka bar garin suka zo wurinsa. 31 A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, "Mallam, ka ci." 32 Amma ya ce masu, "ina da abinci da ba ku san komai akai ba." 33 Sai almajiran suka ce da junansu, "Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?" 34 Yesu ya ce masu, "Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi. 36 Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare. 37 Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.' 38 Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu. 39 Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, "Ya gaya mani duk abinda na taba yi." 40 To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu. 41 Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa. 42 Suka cewa matar, "Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya." 43 Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili. 44 Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa. 45 Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin. 46 Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa. 48 Yesu yace masa, "Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba." 49 Ma'aikacin ya ce masa, "Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu." 50 Yesu yace masa, "Je ka. Dan ka ya rayu." Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa. 51 Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye. 52 Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, "Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi." 53 Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, "Jeka, danka na raye." Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya. 54 Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.

5

1 Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima. 2 To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar. 3 Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin. 1 4 2 5 Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas. 6 Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, "Ko kana so ka warke?" 7 Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, "Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni." 8 Yesu ya ce masa," Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi." 9 Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce. 10 Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, "Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba." 11 Sai ya amsa ya ce, "Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi." 12 Suka tambaye shi, "wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?" 13 Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin. 14 Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, "ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka." 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi. 16 To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar. 17 Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, "Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki." 18 Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah. 19 Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi. 20 Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki. 21 Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa. 22 Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan, 23 domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi. 24 Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai,. 25 Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu. 26 Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa. 27 Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum. 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa, 29 su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci. 30 Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31 Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba. 32 Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce. 33 Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya. 34 Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto. 35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan. 36 Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni. 37 Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa. 38 Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39 Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40 kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai. 41 Ba na karbar yabo daga wurin mutane, 42 amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku. 43 Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah? 45 Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa. 46 Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni. 47 Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?"


1Mafi kyawun kwafin tsoffin ba su da jumlar, suna jira a dama ruwan .
2Mafi kyawun kwafin kwafi ba su da aya 4, Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita .

6

1 Bayan waddannan abubuwa, Yesu ya ketare tekun Galili, wanda a ke kira tekun Tibariya. 2 Sai taro mai yawa suka bi shi domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya. 3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4 (Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.) 5 Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, "Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?" 6 (Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.) 7 Filibus ya amsa masa, "gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba." 8 Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa, 9 "Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?" 10 Yesu ya ce, "ku sa mutane su zauna."( wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar. 11 Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su. 12 Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara." 13 Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci. 14 Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, "Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya. 15 "Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa. 16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku. 17 Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.) 18 Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa. 19 Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita. 20 Amma ya ce masu, "Ni ne! kada ku firgita." 21 Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci. 22 Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai. 23 Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya. 24 Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu. 25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, "Mallam, yaushe ka zo nan?" 26 Yesu ya amsa masu, da cewa, "hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi. 27 Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa." 28 Sai suka ce Masa, "Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah? 29 Yesu ya amsa, "Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko." 30 Sai suka ce masa, "To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka? 31 Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, "Ya ba su gurasa daga sama su ci." 32 Sa'an nan Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama. 33 Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya," 34 Sai suka ce masa, "Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe." 35 Yesu ya ce masu, "Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba. 36 Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan. 38 Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe. 40 Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe. 41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, "Nine Gurasar da ta sauko daga sama." 42 Suka ce, "Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'? 43 Yesu ya amsa, ya ce masu, "Kada ku yi gunaguni a junanku. 44 Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe. 45 A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni. 46 Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban. 47 Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami. 48 Ni ne Gurasa ta rai. 49 Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu. 50 Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba. 51 Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya." 52 Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, "Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci? 53 Sai Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba. 54 Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe. 55 Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya. 56 Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa. 57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni. 58 Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada." 59 Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum. 60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, "Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?" 61 Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, "Wannan ya zamar maku laifi? 62 Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da? 63 Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai. 64 Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi. 65 Ya fada cewa, "shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban." 66 Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba. 67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, "ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba? 68 Bitrus ya amsa masa ya ce, "Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami. 69 Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah." 70 Yesu ya ce masu, "Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?" 71 Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.

7

1 Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi. 2 To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa. 3 Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, "ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma. 4 Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya. 5 Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba. 6 Yesu ya ce dasu, "lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne. 7 Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau. 8 Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna. 9 Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili. 10 Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba. 11 Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa "Ina yake?" 12 Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, "shi mutumin kirki ne." Wadansu kuma suna cewa,"A'a yana karkatar da hankalin jama'a." 13 Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa. 14 Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa. 15 Yahudawa suna mamaki suna cewa,"Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba." 16 Yesu ya ba su amsa ya ce,"Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce." 17 Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina. 18 Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa. 19 Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni? 20 Taron suka ba shi amsa, "Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?" 21 Yesu ya amsa ya ce masu, "Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi. 22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya. 23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar? 24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci." 25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, "wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?" 26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba? 27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito." 28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, "Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba. 29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni." 30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna. 31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,"Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?" 32 Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi. 33 Sa'annan Yesu yace ma su," jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba." 35 Yahudawa fa su ka cewa junan su, "Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa? 36 Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?" 37 To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, "Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha. 38 Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo." 39 Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba. 40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, "Wannan lallai annabi ne." 41 Wadansu suka ce, "Wannan Almasihu ne." Amma wadansu suka ce, "Almasihu zai fito daga Gallili ne? 42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito? 43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi. 44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu. 45 Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce," me yasa ba ku kawo shi ba?" 46 Jami'an su ka amsa, "Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka." 47 Farisawa suka amsa masu, "kuma an karkatar da ku? 48 Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa? 49 Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne." 50 Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa), 51 " Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?" 52 Suka amsa masa suka ce,"kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili." 53 Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.

8

1 Yesu ya je Dutsen Zaitun. 2 Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu. 3 Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya. 4 Sai su ka ce da shi, "Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina. 5 A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?" 6 Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa. 7 Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, "shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse." 8 Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa. 9 Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su. 10 Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, "mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki? 11 Ta ce, "Ba kowa, Ubangiji" Yesu ya ce, "Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi." 12 Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, "Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai. 13 Farisawa suka ce masa, "Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce." 14 Yesu ya amsa ya ce masu, "Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba. 15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba. 16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni. 17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce. 18 Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta. 19 Su ka ce da shi, "Ina ubanka?" Yesu ya amsa ma su ya ce, "baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma." 20 Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna. 21 Ya kara cewa da su,"Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba". 22 Yahudawa su ka ce,"Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?" 23 Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne. 24 Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku. 25 Sai kuma suka ce da shi,"Wanene kai?" Yesu ya ce masu, "Abin da na gaya maku tun daga farko. 26 Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya." 27 Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban. 28 Yesu ya ce, "Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa. 29 Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai." 30 Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi. 31 Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, "Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya, 32 Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku." 33 Suka amsa masa, "Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?" 34 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne. 35 Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin. 36 Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai. 37 Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku. 38 Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku." 39 Suka amsa suka ce masa, "Ibrahim ne ubanmu" Yesu ya ce masu, "Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi. 40 Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba. 41 Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, "mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah." 42 Yesu ya ce masu, "Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni. 43 Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne. 44 Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma. 45 Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba. 46 Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba? 47 Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane," 48 Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?" 49 Yesu ya amsa, "Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni." 50 Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa. 51 Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba." 52 Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, ' dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'. 53 Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?." 54 Yesu ya amsa, "Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku. 55 Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa. 56 Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna." 57 Yahudawa su ka ce masa, "Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?" 58 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE." 59 Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.

9

1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi, "Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?" 3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa. 4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki. 5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya." 6 Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar. 7 Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike)." Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani. 8 Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, "Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?" 9 Wadansu suka ce, "shi ne." Wadansu suka ce, "A'a, amma yana kama da shi." Amma shi ya ce, "Ni ne wannan mutum." 10 Suka ce masa, "To yaya aka bude maka idanu?" 11 Sai ya amsa, "Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani." 12 Suka ce masa, "Ina yake?" Ya amsa, "Ban sani ba." 13 Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa. 14 A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu. 15 Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, "Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani." 16 Wadansu daga cikin farisawa suka ce, "Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. "Wadansu suka ce, "Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?" Sai rabuwa ta shiga tsakanin su. 17 Sai suka tambayi makahon kuma, "Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?" Makahon ya ce, "shi annabi ne." 18 Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin. 19 Su ka tambayi iyayen, "Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?" 20 Sai iyayen suka amsa masu, "Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi. 21 Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa." 22 Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a. 23 Domin wannan ne, iyayensa suka ce, "Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi." 24 Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, "Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne." 25 Sai wannan mutum ya amsa, "Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani." 26 Sai su ka ce masa, "Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?" 27 Ya amsa, "Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne? 28 Sai suka kwabe shi suka ce, "kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne. 29 Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba." 30 Mutumin ya amsa masu ya ce, "Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu. 31 Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa. 32 Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba. 33 In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba." 34 Suka amsa suka ce masa, "an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?" Sai suka fitar da shi. 35 Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, "Kana bada gaskiya ga Dan Allah?" 36 Sai ya amsa masa yace, "Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?" 37 Yesu yace masa, "Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai." 38 Mutumin ya ce, "Ubangiji, Na bada gaskiya." Sai ya yi masa sujada. 39 Yesu ya ce, "Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi." 40 Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, "Muma makafi ne?" 41 Yesu ya ce masu, "Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.

10

1 "Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi. 2 Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin. 3 Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje. 4 Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa. 5 Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba." 6 Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba. 7 Sai Yesu ya ce masu kuma, "Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki. 8 Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba. 9 Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo. 10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace. 11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa. 12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su. 13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba. 14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni. 15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin. 16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya. 17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma. 18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana." 19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin. 20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?" 21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?" 22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo. 23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu. 24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, "Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla." 25 Yesu ya ce masu, "Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina. 26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27 Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na. 29 Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban. 30 Ni da Uban daya ne." 31 Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa masu, "Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?" 33 Sai Yahudawa suka amsa masa, "ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah." 34 Yesu ya amsa masu, "Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, "ku alloli ne"'?" 35 In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba), 36 kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'? 37 In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni. 38 Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban." 39 Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu. 40 Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin. 41 Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,"Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne." 42 Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.

11

1 To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta. 2 Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya. 3 'Yan'uwannan mata suka aika sako wurin yesu, cewa, "Ubangiji, duba, shi wanda kake kauna yana rashin lafiya". 4 Da Yesu ya ji, sai ya ce "Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta". 5 Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru. 6 Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke. 7 Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, "Bari mu je Yahudiya kuma." 8 Sai almajiransa suka ce masa, "Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?" 9 Yesu ya amsa, "Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya. 10 Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi. 11 Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, "Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci". 12 Sai almajirai suka ce masa, "Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka." 13 Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu. 14 Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, "Li'azaru ya mutu. 15 Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa." 16 Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, "Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu." 17 Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari. 18 Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su. 19 Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu. 20 Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida. 21 Matta ta ce wa Yesu, "Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba". 22 Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka. 23 Yesu ya ce mata, "Dan'uwanki za ya rayu kuma. 24 Sai Matta ta ce masa, "Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe." 25 Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu; 26 Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?" 27 Sai ta ce masa, "I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya. 28 Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, "mallam ya iso, kuma yana kiran ki." 29 Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa. 30 Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi. 31 Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari. 32 Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, "Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba". 33 Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma; 34 sai ya ce, "A ina kuka kwantar da shi?" Sai suka ce masa, "Ubangiji, zo ka gani." 35 Yesu ya yi kuka. 36 Sai Yahudawa suka ce, "Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!" 37 Amma wadansun su suka ce, "Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba? 38 Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse. 39 Sai Yesu ya ce, "A kawar da dutsen." Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, "Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa". 40 Yesu ya ce mata, "Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?" 41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, "Uba, na gode maka domin kana ji na." 42 Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni." 43 Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, "Li'azaru, ka fito!" 44 Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, "Ku kwance shi, ya tafi". 45 To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi; 46 amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi. 47 Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, "menene za mu yi?" Mutumin nan yana alamu masu yawa. 48 Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu. 49 Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, "baku san komai ba". 50 Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka." 51 Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar; 52 kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya. 53 Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu. 54 Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa. 55 Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su. 56 Suka shiga neman Yesu, suna magana da junan su yayin da suke tsaitsaye a haikali, cewa "me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?" 57 Babban firist da farisawa sun rigaya sun ba da umurni cewa duk inda aka ga Yesu a zo a shaida domin su kama shi.

12

1 Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu. 2 Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu. 3 Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren. 4 Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, " 5 "Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?" 6 Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi. 7 Yesu ya ce, "Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta. 8 Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba. 9 To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu. 10 Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima; 11 domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu. 12 Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima, 13 Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, "Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila. 14 Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta, 15 "Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki". 16 Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa. 17 Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida. 18 Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama. 19 Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa "Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa. 20 Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin. 21 Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, "Mallam, muna so mu ga Yesu. 22 Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu. 23 Yesu ya amsa masu ya ce, "sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum. 24 Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa. 25 Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada. 26 Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi. 27 Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a. 28 Uba, ka daukaka sunanka". Sai wata murya daga sama ta ce, "Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi. 29 Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, "Mala'ika ya yi magana da shi". 30 Yesu ya amsa ya ce, "wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku." 31 Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan. 32 Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni". 33 Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi. 34 Taro suka amsa masa cewa, "Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?" 35 Yesu ya ce masu, "Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba. 36 Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske". Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu. 37 Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba. 38 Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana? 39 Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa, 40 ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su. 41 Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi. 42 Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a. 43 Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah. 44 Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, "Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni, 45 kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni. 46 Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba. 47 Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya. 48 Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe. 49 Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi. 50 Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi."

13

1 Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe. 2 Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu. 3 Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah. 4 Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi. 5 Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi. 6 Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,"Ubangiji, za ka wanke mani kafa?" 7 Yesu ya amsa ya ce, "Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta." 8 Bitrus ya ce masa, "Ba za ka taba wanke mani kafa ba." Yesu ya amsa masa ya ce, "In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni". 9 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina." 10 Yesu ya ce masa, "Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba." 11 (Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, "Ba dukanku ne ke da tsarki ba.") 12 Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, "Kun san abin da na yi muku? 13 kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake. 14 Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu. 15 Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku. 16 Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba. 17 Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su. 18 Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'. 19 Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne. 20 Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni. 21 Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, "Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni." 22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana. 23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu. 24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, "ka fada mana ko akan wa ya ke magana." 25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, "Ubangiji, wanene?" 26 Sannan Yesu ya amsa, "Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi." Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti. 27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, "Abinda kake yi, ka yi shi da sauri." 28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan. 29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, "Ka sayi abinda muke bukata don idin", ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu. 30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa. 31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, "Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa. 32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan. 33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan. 34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna." 36 Siman Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ina za ka?" Yesu ya amsa ya ce, "Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya." 37 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka." 38 Yesu ya amsa ya ce, "Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku."

14

1 "Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni. 2 A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri. 3 In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance. 4 Kun san hanya inda zan tafi." 5 Toma ya ce wa Yesu, "Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?" 6 Yesu ya ce masa, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7 Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi." 8 Filibus ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu." 9 Yesu ya ce masa, "Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'? 10 Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa. 11 Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu. 12 "Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba. 13 Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan. 14 Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi. 15 "Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina. 16 Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada. 17 Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku. 18 Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku. 19 Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu. 20 A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku. 21 Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi." 22 Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, "Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?" 23 Yesu ya amsa ya ce masa,"Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take. 25 Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku. 26 Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku. 27 Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata. 28 Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma. 29 Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata. 30 Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na, 31 amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.

15

1 "Nine itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomin. 2 Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya. 3 Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku. 4 Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada 'ya'ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na. 5 Ni ne itacen inabi, ku ne rassan. Wanda ya zauna ciki na, ni kuma cikin sa, yana bada 'ya'ya dayawa, gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6 Wanda kuma bai zauna a ciki na ba, akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe, kuma sukan tattara rassan su jefa a wuta, su kone. 7 In kun zauna a ciki na, maganata kuma ta zauna a cikin ku, sai ku roki duk abinda kuke so, za a kuwa yi maku. 8 Ta haka ake daukaka Ubana: cewa ku bada 'ya'ya dayawa, kuma cewa ku almajiraina ne. 9 Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku; Ku zauna cikin kaunata. 10 Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa. 11 Ina gaya maku wadannan al'amura domin farincikina ya kasance a cikin ku, kuma domin farincikinku ya zama cikakke. 12 "Wannan shine umarnina, cewa ku kaunaci juna kamar yadda na kaunace ku. 13 Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa. 14 Ku abokaina ne idan kuna yin abubuwan da na umarce ku. 15 Nan gaba ba zan kara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abinda Ubangijinsa ke yi ba. Na kira ku abokaina, domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku. 17 Na baku wannan umarni: domin ku kaunaci juna. 18 In duniya ta ki ku, ku sani cewa ta kini kafin ta ki ku. 19 Da ku na duniya ne, da duniya ta kaunace ku kamar nata. Amma saboda ku ba na duniya bane, na kuma zabe ku daga duniya, don haka duniya take kin ku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku, 'Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba.' Idan sun tsananta mani, ku ma za su tsananta maku; Idan sun kiyaye maganata, za su kuma kiyaye maganarku. 21 Za su yi maku duk wadannan abubuwa saboda sunana, don basu san wanda ya aiko ni ba. 22 Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu. 23 Duk wanda ya ki ni ya ki Ubana. 24 Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma yanzu sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari'arsu, ' Sun ki ni ba dalili.' 26 Sa'adda Mai Ta'aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na. 27 Ku ma kuna bada shaida saboda kuna tare da ni tun daga farko.

16

1 "Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube. 2 Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi. 3 Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba. 4 Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku." Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku. 5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?' 6 Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku. 7 Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9 Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba, 10 Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba, 11 game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci. 12 "Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba. 13 Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru. 14 Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku. 15 Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku. 16 "Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni." 17 Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, "Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?" 18 Saboda haka sukace, "Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba." 19 Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, "Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, "Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'? 20 Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki. 21 Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya. 22 To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki. 23 A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi. 24 Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke." 25 "Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba. 26 A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba, 27 domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28 Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba." 29 Almajiransa sukace, duba, "Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba! 30 Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito." 31 Yesu ya amsa masu yace, "Ashe, yanzu kun gaskata? 32 Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni. 33 Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,"

17

1 Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka, 2 kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi. 3 Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu. 4 Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi. 5 Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci. 6 Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka. 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake, 8 don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni. 9 Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne. 10 Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu. 11 Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya. 12 Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika. 13 Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 15 Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 17 Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce. 18 Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya. 19 Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya. 20 Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu, 21 Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni 22 Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya; 23 ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni. 24 Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya. 25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni. 26 Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,

18

1 Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa. 2 Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa. 3 Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai. 4 Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, "Wa kuke nema" 5 Suka amsa masa su ka ce, "Yesu Banazare" Yesu yace masu, Ni ne" Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin. 6 Sa'adda ya ce masu, "Ni ne", suka koma da baya, suka fadi a kasa. 7 Ya sake tambayarsu kuma, "Wa ku ke nema?" su ka ce, "Yesu Banazare." 8 Yesu ya amsa, "Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;" 9 Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, "Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba." 10 Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne. 11 Yesu ya ce wa Bitrus, "Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'? 12 Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi. 13 Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan. 14 Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane. 15 Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu; 16 Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17 Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, "kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?" Yace "bani ba." 18 To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin. 19 babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma. 20 Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba. 21 Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada. 22 Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, "Kana amsa wa babban firist haka." 23 Yesu ya amsa masa yace, "Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?" 24 Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist. 25 To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, "Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?" Sai yayi musu yace, "A'a, ba na ciki." 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, "Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba? 27 Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara. 28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa. 29 Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, "Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan? 30 "Sai suka amsa suka ce, "idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka" 31 bilatus yace masu, "Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!" Sai Yahudawa su kace masa, "Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa." 32 Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi. 33 Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, "kai sarkin Yahudawa ne?" 34 Yesu ya amsa, "wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?" 35 Bilatus ya amsa "Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?" Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. "Me ka yi?" 36 Yesu ya amsa, "Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba." 37 Sai Bilatus yace masa, "Wato ashe, sarki ne kai?" Yesu ya amsa, "Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata." 38 Bilatus yace masa, "Menene gaskiya?" Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, "Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba. 39 Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?" 40 Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, "A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas." Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.

19

1 Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala. 2 Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata. 3 Suka zo wurin sa sukace, "Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi. 4 Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, "Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba", 5 Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace "Ga mutumin nan". 6 Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa "A gicciye shi, A gicciye shi" Sai Bilatus yace masu, "ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba". 7 Sai Yahudawan sukace mashi, "Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah". 8 Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai. 9 Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, "Daga ina ka fito?" amma Yesu bai amsa mashi ba. 10 Sai Bilatus yace masa "Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka? 11 Yesu ya amsa masa, "Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi". 12 Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, "In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar". 13 Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira "Dakalin shari'a," a Yahudanci kuma, "Gabbata." 14 To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan "Ga sarkin ku!" 15 Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu "In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace "Ba mu da wani sarki sai Kaisar". 16 Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi. 17 Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira "Wurin kwalluwa" da Yahudanci kuma "Golgota". 18 Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya. 19 Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, "YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA". 20 Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci. 21 Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace "Ni ne sarkin Yahudawa"'. 22 Bilatus kuwa ya amsa, "Abinda na rubuta na rubuta kenan." 23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa. 24 Sai sukace wa junansu, "Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa "Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata. 25 Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu. 26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, "Mace, dubi, dan ki!" 27 Sai yace wa almajirin, "Dubi, mahaifiyarka!" Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa. 28 Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace "Ina jin kishi. 29 A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace "An gama" Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa. 31 Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su. 32 Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu. 33 Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba. 34 Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito. 35 Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata. 36 Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, "Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya". 37 Kuma wani nassin yace, "Zasu dube shi wanda suka soka." 38 Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin. 39 Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari. 40 Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa. 41 To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba. 42 Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.

20

1 To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin. 2 Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, "Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba." 3 Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin, 4 dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin, 5 Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba. 6 Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye. 7 sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban. 8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya. 9 Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba. 10 Sai almajiran suka sake komawa gida kuma. 11 Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin. 12 Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu. 13 Sukace mata, "Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, "Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba. 14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane, 15 Yesu yace mata, "Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, "Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi." 16 Yesu yace mata, "Maryamu". Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci "Rabboni!" wato mallam. 17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku". 18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, "Na ga Ubangiji" Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa. 19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace "Salama Agareku". 20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki. 21 Yesu ya sake ce masu, "salama agareku. "Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku". 22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, "Ku karbi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu." 24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana. 25 Sauran almajiran sukace masa "Mun ga Ubangiji". Sai yace masu, "In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba. 26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, "Salama agareku". 27 Sa'an nan yace wa Toma, "Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya". 28 Toma ya amsa yace "Ya Ubangijina da Allahna!" 29 Yesu yace masa, "Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya. 30 Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba. 31 Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.

21

1 Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa: 2 Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu. 3 Saminu Bitrus yace masu, "Zani su." sukace masa "Mu ma za mu je tare da kai." Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba. 4 To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane. 5 Sai Yesu yace masu, "Samari, kuna da wani abinda za a ci?" Suka amsa masa sukace "A'a". 6 Yace masu, "Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu." Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin. 7 Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, "Ubangiji ne fa!" Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun. 8 Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi. 9 Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa. 10 Yesu ya ce masu "Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu". 11 Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba. 12 Yesu yace masu, "Ku zo ku karya kumallo". Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa "Ko shi wanene?" Domin sunsani Ubangiji ne. 13 Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu. 15 Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, "Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?" Bitrus yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka" Yesu yace masa "Ka ciyar da 'ya'yan tumakina". 16 Ya sake fada masa karo na biyu, "Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?" Bitrus Yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka". Yesu yace masa, "Ka lura da Tumakina". 17 Ya sake fada masa, karo na uku, "Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, "Kana kaunata" Yace masa, "Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka." Yesu yace masa "Ka ciyar da tumaki na. 18 Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba." 19 To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni. 20 Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace "Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?" 21 Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu "Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?" 22 Yesu yace masa, "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni." 23 Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?" 24 Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne. 25 Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.

Ayyukan Manzanni
Ayyukan Manzanni
1

1 Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar, 2 har zuwa ranar da aka karbe shi zuwa sama. Wannan kuwa bayan da ya ba da umarni ga zababbun manzanninsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 3 Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah. 4 Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, "Kun ji daga gare ni, 5 cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan." 6 Sa'adda suna tare suka tambaye shi, "Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?" 7 Ya ce masu, "Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa. 8 Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya." 9 Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu. 10 Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi. 11 Suka ce, "Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama." 12 Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne. 13 Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra'ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu. 14 Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa. 15 A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce, 16 " 'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu 17 Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima," 18 (Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje. 19 Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu "Akeldama" wato, "Filin Jini.") 20 "Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,'kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.' 21 Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu, 22 farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa." 23 Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas. 24 Su ka yi addu'a suka ce, "Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan 25 Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje" 26 suka jefa kuri'a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.

2

1 Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya. 2 Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune. 3 Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu. 4 Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana. 5 A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama. 6 Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa. 7 Suka yi mamaki matuka; suka ce, "Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne? 8 Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu? 9 Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya, 10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma, 11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah." 12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, "Menene ma'anar wannan?" 13 Amma wasu suka yi ba'a suka ce, "Sun bugu ne da sabon ruwan inabi." 14 Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, "Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata. 15 Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai. 16 Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel. 17 Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai. 18 Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci. 19 Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije. 20 Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo. 21 Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto. 22 Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani. 23 Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi. 24 Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi. 25 Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita. 26 Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi. 27 Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba. 28 Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki. 29 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau. 30 Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa. 31 Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.' 32 Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne. 33 Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji. 34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, "Zauna hannun dama na, 35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.'" 36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu. 37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '"Yan'uwa me za mu yi?" 38 Sai Bitrus ya ce masu, "Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki. 39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira." 40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, "Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara." 41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku. 42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i. 43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin. 44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne, 45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita. 46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya; 47 Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.

3

1 Sa'adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu'ar karfe uku. 2 Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin. 3 Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka. 4 Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, "Ka dube mu." 5 Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su. 6 Amma Bitrus ya ce, "Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya" 7 Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi. 8 Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah. 9 Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah. 10 Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru. 11 Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai. 12 Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, "Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?" Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu? 13 Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi. 14 Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai. 15 Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al'amari. 16 Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka. 17 Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi. 18 Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika. 19 Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo; 20 domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu. 21 Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka. 22 Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku. 23 Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.' 24 I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki. 25 Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.' 26 Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa."

4

1 Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu. 2 Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu. 3 Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi. 4 Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya. 5 Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima. 6 Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist 7 Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, "Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?" 8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, "Ku shugabanni da dattawan jama'a, 9 idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya? 10 Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye. 11 Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini. 12 Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto." 13 Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu. 14 Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi. 15 Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu. 16 Suka ce, "Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka. 17 Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna." 18 Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu. 19 Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, "Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta. 20 Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba." 21 Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru. 22 Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in. 23 Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu. 24 Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, "Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu, 25 kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza? 26 Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.' 27 Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe. 28 Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru. 29 Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi. 30 Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu." 31 Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi. 32 Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne. 33 Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu. 34 Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar 35 sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa. 36 Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya). 37 Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.

5

1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu, 2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin. 3 Amma Bitrus ya ce, "Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin? 4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa." 5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu 6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi. 7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba. 8 Sai Bitrus ya ce mata, "ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?" Sai ta amsa, "ta ce kaza ne." 9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, "Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu." 10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta. 11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura. 12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu, 13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a. 14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata, 15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu. 16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka. 17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka 18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku. 19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce, 20 "Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai." 21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin. 22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto, 23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba. 24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar. 25 Sai wani ya zo ya ce masu, "Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a." 26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu. 27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su, 28 cewa "Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu." 29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, "Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba. 30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace, 31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai. 32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi." 33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin. 34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci. 35 Sai ya ce masu "Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan, 36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu. 37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse. 38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace. 39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah." Sai suka rinjayu. 40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi. 41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan. 42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.

6

1 A wadannan kwanaki, yawan almajiran ya ci gaba da ribanbanya, sai Yahudawan da suke zama a kasar Helanawa suka fara gunaguni game da Yahudawan Isra'ila, domin basu damu da gwamrayensu, wajen raba abinci da ake yi kullum. 2 Manzannin nan sha biyu suka kira taron almajiran suka ce masu, "Bai kamata mu bar maganar Allah mu shiga hidimar rabon abinci ba. 3 Don haka ku zabi 'yan'uwa maza daga cikinku, mutane bakwai wadanda a ke ganin su da daraja, cike da Ruhu da kuma hikima, wadanda za mu zaba suyi wannan hidima. 4 Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar." 5 Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci. 6 Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu. 7 Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya. 8 Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a. 9 Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus. 10 Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi. 11 Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, "Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah." 12 Sai suka zuga mutanen, har da dattawa da marubuta suka tunkari Istifanus, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa. 13 Suka kawo masu shaidar karya suka ce, "Wannan mutumin har yanzu bai dena maganganun gaba akan wannan wuri mai tsarki da kuma shari'a ba. 14 Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa." 15 Dukan wadanda suke zaune a majalisar suka zuba masa ido, sai suka ga fuskarsa kamar ta mala'ika.

7

1 Sai babban firist ya ce, "Wadannan al'amura gaskiya ne?" 2 Sai Istifanus ya amsa ya ce, "Ya 'yan'uwa da ubanni, ku saurare ni, Allah Madaukaki ya bayyana ga ubanmu Ibrahim tun yana can kasar Mesofotamiya, kafin ma ya zauna a kasar Haran; 3 ya ce masa, 'Ka bar kasarka da danginka, ka tafi kasar da zan nuna maka.' 4 Sa'annan ya bar kasar Kaldiyawa ya zo ya zauna a Haran; daga can, bayan rasuwar mahaifinsa, sai Allah ya kira shi zuwa wannan kasa da kuke ciki. 5 Amma Allah bai ba shi kasar gado ba tukuna, ko da misalin tafin sawunsa. Amma ya alkawarta - ko da yake bai riga ya haifi da ba tukuna - wanda zai ba shi kasar gado, shi da zuriyarsa, a bayansa. 6 Allah ya yi magana da shi kamar haka, cewa zuriyarsa za su yi bakonci a wata kasa wadda ba tasu ba, mutanen wannan kasar kuwa za su gwada masu bakar azaba su kuma bautar da su har shekaru dari hudu. 7 'Kuma zan hukunta wannan al'umma da ta bautar da su,' Allah ya ce, 'Bayan haka za su fito daga wannan kasa su bauta mini a wannan wuri.' 8 Allah ya ba Ibrahim alkawarin kaciya, sai Ibrahim ya haifi Ishaku ya yi masa kaciya a rana ta takwas; Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi ubanni Isra'ila su goma sha biyu. 9 Wadannan 'yan'uwa suka yi kyashin danuwansu Yusifu suka sayar da shi bauta zuwa Masar. Amma Allah na tare da shi. 10 Ya kuwa cece shi daga dukan sharin da yan uwansa suka kulla masa, Allah kuwa ya ba shi tagomashi da hikima a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Fir'auna kuwa ya mai da shi mai mulki a dukan kasar Masar da kuma dukan mallakarsa. 11 Sai aka yi babbar yunwa a dukan kasar Masar da ta Kan'ana, iyayenmu suka sha wuya saboda rashin abinci. 12 Amma lokacin da Yakubu ya ji akwai hatsi a kasar Masar, sai ya aiki ubannimu a karo na farko. 13 Da suka je a karo na biyu, sai Yusifu ya bayyana kansa ga yanuwansa; a wannan lokaci ne Fir'auna ya gane da yanuwan Yusufu. 14 Yusufu ya aiki yanuwansa su kawo Yakubu ubansu da dukan mallakarsu da iyalansu zuwa Masar, Dukansu mutane saba'in da biyar ne. 15 Yakubu ya tafi ya zauna a Masar; shi da zuriyarsa har mutuwar su. 16 Aka dauke su zuwa Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kudin azurfa daga hannun yayan Hamor a Shekem. 17 Yayin da alkawarin Allah ya kusato wanda Allah ya fada wa Ibrahim, mutanen suka karu suka hayayyafa kwarai a Masar, 18 Sai a ka yi wani sarki a Masar wanda bai san Yusifu ba, 19 Wannan sarki ya yaudari kakkaninmu ya yi masu mugunta kwarai da gaske, har ma ya kai ga suna barin jariransu cikin hasari don su ceci rayukansu. 20 A wannan lokaci ne aka haifi Musa, kuma kyakkyawan yaro ne sai aka yi renon sa tsawon wata uku a gidan mahaifinsa a asirce. 21 Yayin da aka jefar da shi, sai diyar Fir'auna ta dauke shi ta rene shi kamar danta. 22 Aka ilimantar da Musa da dukan ilimi irin na Masar; kuma ya shahara cikin fasahar magana da kuma ayyukansa. 23 Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa. 24 Sai ya ga wani na cin zalin Ba Isra'ile, Musa kuwa ya taimaki wanda ake kwara ta wurin murkushe Bamasaren: 25 zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba. 26 Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?' 27 Amma shi wanda ake kwarar makwabcinsa ya ture Musa a gefe guda, ya ce, 'Wa ya nada ka shugaba ko alkali akanmu? 28 Kana so ka kashe ni ne, kamar yadda ka kashe Bamasaren nan jiya?' 29 Da jin haka sai Musa ya gudu, zuwa kasar Midinawa, a matsayin dan gudun hijira. Anan ya haifi "ya'ya biyu maza. 30 Bayan da shekaru arba'in suka wuce, sai mala'ika ya bayyana gare shi a jeji, kusa da dutsen Sinai, a cikin harshen wuta a cikin jeji. 31 Sa'adda Musa ya ga wutar, mamaki ya kama shi; sai ya maso kusa don ya kara dubawa, sai ya ji muryar Ubangiji na cewa, 32 'Nine Allah na ubanninka, Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.' Musa ya razana har ma bai sake daga kai ya duba ba. 33 Ubangiji ya ce masa, 'Tube takalminka, domin in da kake tsaye wuri mai tsarki ne. 34 Ba shakka na ga wahalar da mutane na ke sha a Masar, kuma na ji nishinsu, don haka na zo in cece su, yanzu fa sai ka zo, in aike ka zuwa Masar.' 35 Wannan fa shine Musan da suka ki, harma da cewa, 'Wanene ya nada ka alkali ko shugaba a kanmu?' Shine kuma wanda Allah ya aiko masu a matsayin shugaba da kuma mai ceto. Allah ya aiko shi ta hannun mala'ikan da ya gani a daji. 36 Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain. 37 Wannan shine Musan da ya cewa Isra'ilawa, 'Ubangiji zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin Yan'uwan ku.' 38 Wannan shine mutumin da ke tare da mutane a jeji. Karkashin jagorancin mala'ikan da ya yi magana da shi a dutsen Sinai. Wannan ne mutumin da ke tare da ubannen mu, wannan shi ne mutumin da ya ba mu maganar Allah mai rai. 39 Wannan shine mutumin da ubannenmu suka ki su yi masa biyayya; su ka fitar da shi daga cikinsu, suka kudurta a zuciyarsu za su koma masar. 40 A lokacin ne suka cewa Haruna, 'ya yi masu allolin da za su jagorance su zuwa masar. Domin kuwa ga zancen Musan nan da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.' 41 Sai suka kera dan maraki suka kawo wa gunkin hadaya, suka yi murna da abin da hannayensu suka kera. 42 Allah ya bashe su su bauta wa tauraran sama, kamar yadda yake a rubuce cikin littattafafan annabawa, 'Kun mika mani hadayu na yankakkun dabbobi a jeji ne a shekaru arba'in din nan ya ku Isra'ilawa?' 43 Kun yarda da haikalin Molek da kuma tauraron allahn nan Rafem, da kuma siffofin nan da kuka kera don ku yi masu sujada; don haka zan kai ku bauta har gaba da Babila.' 44 Kakkaninmu suna da alfarwa ta sujada domin shaida a cikin jeji, kamar yadda Allah ya umarta yayin da ya yi magana da Musa, cewa ya yi shi bisa ga salon da aka nuna mashi. 45 Wannan shine Alfarwar da kakkaninmu suka zo da shi, a lokacin Joshuwa. Wannan ya faru ne yayin da suka mallaki wannan kasa ta al'ummai da Allah ya kora a gaban kakkaninmu. Haka abin yake har ya zuwa zamanin Dauda, 46 wanda ya sami tagomashi a wurin Allah; don ya gina masujada domin Allah na Yakubu. 47 Amma Sulaimanu ne ya gina Gidan Allah. 48 Sai dai Madaukaki ba yakan zauna a gidan da hannaye suka gina ba, kamar yadda annabin ya ce, 49 'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne. To wane irin gida za ku gina mani? inji Ubangiji: ko kuwa ina ne wurin da zan huta? 50 Ko ba hannayena ne suka yi dukan wadannan ba?' 51 Ku mutane masu taurin kai masu zuciya mara kaciya da kunnuwa marasa ji, kullum kuna gaba da Ruhu Mai Tsarki, kuna aikata abin da kakkaninku suka aikata. 52 Wane annabi ne kakkaninku ba su tsanantawa ba? Sun kashe annabawan da suka rigayi zuwan Mai Adalcin nan, kuma kun zama wadanda suka kasance masu bashe shi da masu kashe shi, 53 kune mutanen da kuka karbi shari'a wadda mala'iku suka bayar, amma ba ku kiyaye ta ba". 54 Yayin da majalisar suka ji wannan, sai ransu ya baci kwarai, har suna cizon hakoransu don gaba da Istifanus. 55 Amma shi, cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya daga idonsa sama, ya ga daukakar Allah; ya kuma hango Yesu na tsaye a hannun daman Allah. 56 Istifanus ya ce, "Duba, ina ganin sama ta bude, ga Dan Mutum na tsaye a hannun dama na Allah." 57 Amma yan majalisar suka daga murya da karfi, suka yi ihu, suka kuma toshe kunnuwansu, gaba dayansu suka afka masa; 58 suka fitar da shi bayan gari, suka jejjefe shi da duwatsu, don shaida sai suka tube manyan rigunansu suka ajiye a gaban wani matashi da ake ce da shi Shawulu. 59 Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, "Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na." 60 Ya durkusa ya daga murya da karfi, ya ce, "Ya Ubangiji, kada ka rike wannan zunubi a kansu." Yayin da ya fadi wannan, sai ya yi barci.

8

1 Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari. 2 Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi. 3 Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku. 4 Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar. 5 Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu. 6 Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi. 7 Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke. 8 Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin. 9 Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci. 10 Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, "Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma." 11 Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa. 12 Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata. 13 Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki. 14 Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya. 15 Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki. 16 Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu. 17 Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki. 18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi. 19 Ya ce, "Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki." 20 Amma Bitrus yace masa, "Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi. 21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba. 22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka. 23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi." 24 Siman ya amsa ya ce, "Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni." 25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa. 26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, "Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza" (wannan hanyar yana cikin hamada.) 27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada. 28 Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya. 29 Ruhun ya ce wa Filibus, "Ka je kusa da karussar nan." 30 Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, "Ka fahimci abin da kake karantawa?" 31 Bahabashen ya ce. "Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?" Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi. 32 Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, "An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba. 33 Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya." 34 Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, "Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?" 35 Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu. 36 Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, "Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?" 37 Filibus ya ce," Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma." Sai Bahabashen ya ce, "Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah." 38 Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma. 39 Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna. 40 Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.

9

1 Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist 2 kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami'un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure. 3 Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi; 4 Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, "Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?" 5 Shawulu ya amsa, "Wanene kai, Ubangiji?" Ubangiji ya ce, "Nine Yesu wanda kake tsanantawa; 6 amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi. 7 Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba. 8 Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku. 9 Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha. 10 Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, "Hananiya." Sai ya ce, "Duba, gani nan Ubangiji." 11 Ubangiji ya ce masa, "Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a; 12 kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude." 13 Amma Hananiya ya amsa, "Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima. 14 An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka." 15 Amma Ubangiji ya ce masa, "Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila; 16 Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana." 17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, "Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki." 18 Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma; 19 kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa. 20 Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah. 21 Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce "Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci." 22 Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu. 23 Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi. 24 Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi. 25 Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga. 26 Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba. 27 Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku. 28 Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu 29 kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi. 30 Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus. 31 Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane. 32 Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda. 33 A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado. 34 Bitrus ya ce masa, "Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka." Nan take sai ya mike. 35 Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji. 36 Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana "Dokas." Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata. 37 Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene. 38 Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, "Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba." 39 Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su. 40 Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, "Tabita, tashi." Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna, 41 Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa'annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu. 42 Wannan al'amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji. 43 Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.

10

1 An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya. 2 Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah. 3 Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, "Karniliyas!" 4 Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce "Menene, mai gida?" mala'ikan ya ce masa, "Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah, 5 "Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. 6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku. 7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima. 8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa. 9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a. 10 Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi. 11 Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu. 12 A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama. 13 Sai murya ta yi magana da shi; "Tashi, Bitrus, yanka ka ci " 14 Amma Bitrus ya ce "Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba." 15 Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; "Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce." 16 Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama. 17 A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan, 18 Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan. 19 A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, "Duba, mutane uku na neman ka." 20 Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su." 21 Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, "Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?" 22 Suka ce, "Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka." 23 Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi. 24 Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa. 25 Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada. 26 Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, "Tashi tsaye! Ni ma mutum ne." 27 A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya. 28 Ya ce masu, "Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce. 29 Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo." 30 Karniliyas ya ce "Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske. 31 Ya ce, "Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai. 32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku. 1 33 Don haka nan da nan na aika a kira ku. Kuna da kirki da kuka zo. Yanzu haka, duk muna nan a gaban Allah, don jin duk abin da Ubangiji ya umarce ku da ku faɗi.” 2 34 Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, "Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci. 35 Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi. 36 Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka. 37 Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi. 38 Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi. 39 Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace. 40 Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne, 41 ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu, 42 Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu. 43 Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.` 44 Sa'adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa'azin sa. 45 Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al'ummai. 46 Domin sun ji al'umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa, 47 "Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?" 48 Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.


1Wasu tsoffin kwafi sun ƙara: Idan ya zo, zai yi magana da kai .
2Maimakon Ubangiji ya umarce ya faɗi, wasu tsoffin kwafi sun yi, Allah ya umarce ya faɗi .

11

1 Yanzu Manzani da 'yan'uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al'ummai ma sun karbi maganar Allah 2 Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi; 3 suka ce, "Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!" 4 Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce, 5 Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana. 6 Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama. 7 Sai na ji murya tana ce da ni, "Tashi, Bitrus, yanka ka ci." 8 Na ce, "Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina." 9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, "Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki." 10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama. 11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni. 12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin. 13 Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa "Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus. 14 Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka." 15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko. 16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,"Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki." 17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah? 18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce "Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai." 19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai. 20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu. 21 Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji. 22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya. 23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su. 24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji. 25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu. 26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista. 27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya. 28 Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya. 29 Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa 'yan'uwa da ke Yahudiya da taimako. 30 Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu.

12

1 A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu. 2 Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi. 3 Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma. 4 Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa. 5 To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa. 6 Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun. 7 Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, "Tashi da sauri." Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa. 8 Mala'ikan ya ce masa, "Yi damara ka sa takalmanka." Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, "Yafa mayafinka, ka biyo ni." 9 Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne. 10 Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi. 11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, "Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato." 12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a. 13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar. 14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa. 15 Suka ce mata, "Kin haukace." Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, "Mala'ikansa ne." 16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai. 17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, "Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru." Sai ya bar su, ya tafi wani wuri. 18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus. 19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can. 20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne. 21 A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi. 22 Mutanen suka yi ihu, "Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!" 23 Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu. 24 Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya. 25 Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne.

13

1 A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu. 2 Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su". 3 Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su. 4 Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus. 5 Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu. 6 Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya. 7 Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah. 8 Amma Elimas "mai tsafi" (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya. 9 Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido. 10 Sai ya ce, "Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba? 11 Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci." Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora. 12 Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji. 13 Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima. 14 Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna. 15 Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, "'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi." 16 Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, "Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji. 17 Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta. 18 Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in. 19 Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado. 20 Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo. 21 Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in. 22 Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'. 23 Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi. 24 Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila. 25 Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.' 26 Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto. 27 Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi. 28 Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi. 29 Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari. 30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu. 31 Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu. 32 Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu. 33 Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: "Kai da na ne yau na zama mahaifinka." 34 Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: "Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu." 35 Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.' 36 Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba, 37 amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba. 38 'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai. 39 Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba. 40 Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku: 41 'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku." 42 Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa. 43 Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah. 44 Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji. 45 Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi. 46 Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, "Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai. 47 Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'" 48 Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba. 49 Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin. 50 Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu. 51 Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya. 52 Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

14

1 A lokacin da Bulus da Barnaba sun shiga garin Ikoniya suka shiga majami'an Yahudawa suka yi wa'azi yadda har mutane da yawa daga cikin Yahudawa da Hellinawa suka ba da gaskiya. 2 Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan. 3 Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba. 4 Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin. 5 Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su, 6 da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su, 7 a can suka yi wa'azin bishara. 8 A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa. 9 Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, "Tashi ka tsaya akan kafafunka" 10 Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo. 11 Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, "Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane." 12 Suna kiran Barnaba da sunan "Zafsa," Bulus kuwa suka kira shi da sunan "Hamisa" domin shine yafi yin magana. 13 Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya. 14 Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen. 15 Suna ta cewa, "Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu. 16 A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama. 17 Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki." 18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya. 19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu. 20 Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba. 21 Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya. 22 Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, "Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala." 23 Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi. 24 Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya. 25 Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya. 26 Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu. 27 Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya. 28 Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.

15

1 Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, "Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba." 2 Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana. 3 Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa. 4 Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu. 5 Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, "Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa." 6 Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari. 7 Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, "'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya. 8 Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana; 9 kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya. 10 To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba? 11 Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke." 12 Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai. 13 Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, "'Yan'uwa, ku ji ni. 14 Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa. 15 Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce, 16 'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi, 17 saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana. 18 Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da. 19 Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah; 20 amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe. 21 Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci." 22 Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. 23 Sai suka rubuta wasika, "Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa. 24 Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali. 25 Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba, 26 mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu. 27 Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa. 28 Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan: 29 ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya." 30 Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar. 31 Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa. 32 Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa. 33 Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su. 34 Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin. 35 Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji. 36 Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, "Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke. 37 Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus. 38 Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba. 39 Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus. 40 Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su. 41 Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.

16

1 Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne. 2 Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan. 3 Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne. 4 Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima. 5 Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana. 6 Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya. 7 Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su. 8 Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa. 9 Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. "Ka zo Makidoniya ka taimake mu". 10 Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara. 11 Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis; 12 Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama. 13 Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin. 14 Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi. 15 Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, "Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna." Sai ta rinjaye mu. 16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai. 17 Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, "Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne". 18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, "Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu". Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take. 19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta. 20 Da suka kai su Kotu, suka ce, "Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu. 21 Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa." 22 Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala. 23 Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu. 24 Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi. 25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su. 26 Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse. 27 Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu. 28 Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, "kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan". 29 Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila, 30 ya fitar da su waje ya ce, "Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?" 31 Sun ce masa, "ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira". 32 Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa. 33 Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa. 34 Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah. 35 Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila. 36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, "Ku tafi cikin salama". 37 Amma Bulus ya ce masu, "Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu. 38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne. 39 Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin. 40 Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.

17

1 Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami'ar Yahudawa a wurin. 2 Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai. 3 Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, "Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu". 4 Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa. 5 Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a. 6 Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, "Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana. 7 Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu." 8 Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu. 9 Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su. 10 A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa. 11 Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne. 12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa. 13 Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a. 14 Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna. 15 Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi. 16 Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai. 17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa. 18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, "Menene wannan sakaren ke cewa?" Wadansu kuma sun ce, "Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam," domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu. 19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, "Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka? 20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su." 21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su). 22 Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, "Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku. 23 Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, "Ga Allah wanda ba a sani ba." Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku. 24 Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu. 25 Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu. 26 Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa. 27 Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu. 28 A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'. 29 Idan mu 'ya'yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba. 30 Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko'ina ya tuba. 31 Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu". 32 Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, "Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar." 33 Bayan haka, Bulus ya bar su. 34 Amma wasu maza a cikinsu sun yarda da bisharar, sun ba da gaskiya, hade da Diyonisiyus dan Majalisar Tudun Arasa da wata mace mai suna Damaris, da wadansu tare da su.

18

1 Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti. 2 A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu. 3 Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne. 4 Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa. 5 Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne. 6 Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, "Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai." 7 Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a. 8 Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma. 9 Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, "Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru. 10 Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin." 11 Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah. 12 Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a. 13 Suna cewa, "Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu." 14 Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, "Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta. 15 Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku." 16 Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a. 17 Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba. 18 Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare. 19 Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su. 20 Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba. 21 Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, "In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana." Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa. 22 Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya. 23 Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai. 24 A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah. 25 Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai. 26 Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai. 27 Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri. 28 Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.

19

1 Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai. 2 Bulus ya ce masu, "Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?" Suka amsa, "A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba. 3 Bulus ya ce, "Wacce irin baftisma aka yi maku?" Suka ce, "Baftismar Yahaya" 4 Bulus ya amsa ya ce, "Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan." 5 Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu. 6 Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci. 7 Su wajen mutum goma sha biyu ne. 8 Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah. 9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus. 10 Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa. 11 Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus, 12 har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus. 13 Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, "Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita." 14 Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba. 15 Mugun ruhun ya amsa ya ce, "Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?" 16 Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka. 17 Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka. 18 Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata. 19 Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa. 20 Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa. 21 Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, "Bayan na je can, dole in je Roma." 22 Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci. 23 A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar. 24 Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai. 25 Ya tattara makera ya ce da su, "Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa. 26 Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu. 27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada." 28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa "Mai girma ce Dayana ta Afisa." 29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya. 30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi. 31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin. 32 Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba. 33 Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a. 34 Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, "Mai girma ce Dayana ta Afisa." 35 Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, "Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba? 36 Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce. 37 Gama kun kawo wadannan mutane a wannan dakin sharia ba a kan su mafasa ne na haikali ba ko kuma masu sabo ga allahnmu ba. 38 Saboda haka idan Damatrayas da makeran da ke tare da su na da wata tuhuma a kan wani, kotuna suna nan a bude masu shari'a kuma suna nan. Ba ri su kai karar junansu. 39 Amma idan akwai maganganu na dubawa, za a daidaita su a taronmu na lokaci lokaci. 40 Domin hakika muna cikin hatsarin zargi game da hargitsin yau. Babu dalilin wanan yamutsi domin ba mu da bayani a kansa." 41 Da ya fadi haka, sai ya sallami taron.

20

1 Bayan da rikici ya kare, Bulus ya aika a kira al'majiran, ya karfafa su. Sa'annan ya yi bankwana da su, ya tashi zai tafi Makidoniya. 2 Bayan ya ratsa cikin lardunan yana yi wa masu bi gargadi sosai, sai ya zo kasar Helenawa. 3 Sa'adda ya yi wata uku a wurin, Yahudawa suka kulla masa makirci, yayin da yake shirin hawa Jirgi zuwa Suriya, sai ya canza ra'ayi ya koma ta Makidoniya. 4 Masu yi wa Bulus rakiyar zuwa yankin Asiya sun hada da Sobatarus dan Burus daga Biriya; Gayus mutumin Derbe; Timoti da Aristakus da Sakundus, dukansu masu bi ne daga Tasalonika; da Tikikus da Trofimus daga Asiya. 5 Amma wadansu har suka rigaye mu, suka jira mu a Taruwasa. 6 Da muka shiga Jirgi daga Filibi bayan kwanakin Gurasa mara yisti; bayan kwanaki biyar muka iske su a Taruwasa; kwananmu bakwai a wurin. 7 A rana ta fari ga mako, da muka taru domin karya gurasa. Bulus ya yi wa masubi jawabi, don ya yi niyyar ya tafi da wayewar gari; jawabinsa ya kai har tsakar dare. 8 A benen da suka taru akwai fitilu da yawa. 9 Wani matashi mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, barci mai nauyi ya dauke shi; da shike Bulus ya tsawaita jawabinsa, saurayin da shike barci mai nauyi ya dauke shi sai ya fado daga kan bene na uku aka dauke shi matacce. 10 Sai Bulus ya sauka ya mike a bisansa ya rungume shi, sa'annan ya ce, "Kada kowa ya damu; domin yana darai bai mutu ba." 11 Sa'annan ya hawo kan bene domin cin gurasa tare da su, ya yi magana da su har gari ya waye daga nan ya bar su. 12 Suka kawo saurayin da rai, sun sami ta'aziya ba kadan ba. 13 Amma mu, da muka riga Bulus zuwa gun Jirgin, muka shiga zuwa Asos, mun shirya mu dauki Bulus a jirgi amma shi ya kudurta ya yi tafiya a kasa. 14 Da muka sadu a Asos, mun dauke shi a Jirgin ruwa zuwa Mitilitus. 15 Bayan tashin mu daga can, washegari muka zo tsibirin Kiyos. Washegari kuma muka zo birnin Militus. 16 Amma Bulus ya kudurta wucewa Afisa a Jirgi, don kada ya bata lokaci a Asiya, don yana sauri in ya yiwu ranar Fentekos ta same shi a Urushalima. 17 Daga Militus ya aika a kira masa dattawan iklisiyar Afisa. 18 Da suka zo wurinsa sai ya ce masu, "Ku da kanku kun san tun daga ranar da na sa kafata a Asiya, irin zaman da muka yi da kasancewar mu tare. 19 Na bauta wa Ubangiji da tawaliu har da hawaye, da wahalun da na sha saboda makircin Yahudawa. 20 Kun sani ban ji nauyin sanar da ku kowanne abu mai amfani ba, na bi ku gida gida ina koyar da ku abubuwa a sarari. 21 Kunsan yadda na gargadi Yahudawa da Hellenawa game da tuba ga Allah da bangaskiya ga Ubangiji Yesu. 22 Yanzu fa, gashi, zan tafi Urushalima, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a fili dole in je, ban san abin da zai faru da ni a can ba. 23 Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na. 24 Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah. 25 Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba. 26 Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum. 27 Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba. 28 Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29 Na sani cewa bayan tafiyata, kyarketai masu zafi za su shiga tsakaninku, kuma baza su rangwanta wa masubi ba. 30 Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su. 31 Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba. 32 Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah. 33 Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba. 34 Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana, na biya bukatu na da na wadanda ke tare da ni. 35 Na zama maku abin koyi a kowace hanya game da yadda za ku taimaka wa nakasassu ta wurin aiki, da yadda za ku tuna da maganar Ubangiji Yesu, maganar da shi da kansa ya ce: "Bayarwa tafi karba albarka." 36 Bayan da ya yi magana haka, ya durkusa ya yi addu'a tare da su duka. 37 Dukansu kuwa suka yi kuka mai tsannani, suka rungume shi kuma suka sunbace shi. 38 Suka yi bakin ciki musamman domin abin da ya ce masu, ba za su kara ganinsa ba. Sai dukansu suka yi masa rakiya zuwa wurin jirgin ruwa.

21

1 Da muka rabu da su, muka shiga jirgin ruwa muka mike hanya zuwa birnin Kos, washegari sai birnin Rodusa, daga nan sai kuma zuwa birnin Batara. 2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa Fonisiya sai muka shiga. 3 Da muka hango tsibirin Kubrus muka bar shi a hagun mu muka nufi Suriya, muka sauka a birnin Taya domin a nan ne jirgin ruwan zai sauke kayansa. 4 Bayan mun sami almajirai sai muka zauna can kwana bakwai. Al'majiran suka ce ma Bulus, ta wurin Ruhu, kada ma ya je Urushalima. 5 Bayan 'yan kwanaki muka cigaba da tafiyarmu. Dukansu da matansu da 'ya'yansu suka raka mu har bayan birnin. Sa'annan muka durkusa a bakin gacci muka yi addu'a muka yi sallama da juna. 6 Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida. 7 Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su. 8 Washegari muka tashi muka tafi Kaisariya. Muka shiga gidan Filibus mai shaida bishara, daya daga cikin bakwai din, muka zauna da shi. 9 Wannan mutum yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci. 10 Sa'anda muka zauna can 'yan kwanaki, wani annabi ya zo daga Yahudiya mai suna Agabus. 11 Ya zo wurinmu ya dauki damarar Bulus ya daure tasa kafar da hannayensa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki ya ce, 'Haka Yahudawa za su daure mai wannan damarar, zasu kuma bashe shi ga al'ummai.'" 12 Da muka ji wannan sakon, sai dukanmu da mazaunan wurin muka roki Bulus kada ya tafi Urushalima. 13 Sai Bulus ya amsa ya ce, "Me kuke yi, kuna kuka kuna karya mani zuciya? Bama a shirye don dauri kadai nake ba har ma da mutuwa a Urushalima, sabili da sunan Ubangiji Yesu." 14 Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, "Bari nufin Ubangiji ya tabbata." 15 Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima. 16 Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi. 17 Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki. 18 Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan. 19 Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa. 20 Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, "Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a. 21 An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu. 22 Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo. 23 Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi. 24 Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne. 25 Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci. 26 Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu. 27 Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi. 28 Suna ta kururuwa, "Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka." 29 Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali. 30 Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin. 31 Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma. 32 Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus. 33 Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa. 34 Wadansu cikin taron suna ta kururuwa wadansu su ce wannan, wadansu su ce, wancan. Tunda hafsan bai fahimci abin da suke fadi ba, sabo da ihunsu, ya dokaci a shigar da Bulus farfajiyar sojoji. 35 Da suka kai matakala, sojoji suka dauki Bulus sabo da tsananin husatar taron jama'a. 36 Domin taron suka biyo baya suna ihu suna cewa, "A kashe shi." 37 An kusa shigar da shi farfajiyan kenan sai Bulus ya ce wa babban hafsan, "Ko ka yarda inyi magana da kai?" Hafsan ya ce, "Ka iya Helenanci? 38 Ashe ba kai ne Bamasaren nan da kwanakin baya ka haddasa tawaye, ka dauki 'yan ta'adda dubu hudu ka kai su jeji ba?" 39 Bulus ya ce, "Ni Ba'ibrane ne daga birnin Tarsus a Kilikiya. Ni dan kasar babban birni ne. Ka amince mani in yi magana da mutanen." 40 Da hafsan ya bashi izni, Bulus ya mike a kan matakala ya daga hannayensa sama ya yi nuni su yi shuru. Da wuri ya yi tsit, Bulus ya yi masu magana da Ibraniyanci. Ya ce,

22

1 "Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu." 2 Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce, 3 Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita. 4 Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari. 5 Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su. 6 Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani. 7 Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?' 8 Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.' 9 Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba. 10 Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?" Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi. 11 Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni. 12 A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can. 13 Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi. 14 Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa. 15 Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji. 16 A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.' 17 Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi. 18 Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.' 19 Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada. 20 A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.' 21 Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.' 22 Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.' 23 Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska, 24 babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka. 25 Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, "Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?" 26 Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, "Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne." 27 Babban hafsa ya zo ya ce masa, "Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?" Bulus ya ce, "Haka ne." 28 Babban hafsan ya amsa masa, "Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa." Amma Bulus ya ce, "An haife ni dan kasar Roma. 29 "Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi. 30 Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.

23

1 Bulus ya kura wa yan majalisa ido yace, '"Yan'uwa, na yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau har wannan ranan." 2 Babban firist Hannaniya ya ba wandanda suke tsaye tare da shi urmarni su buge bakinsa. 3 Bulus ya ce, "Allah zai buge ka, kai munafiki. Kana zama domin ka shari'anta ni da shari'a, kuma ka umarce a buge ni, gaba da sharia?" 4 Wanda suka tsaya a gefe suka ce, "Kada ka zage babban firis na Allah." Bulus yace, "Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne. 5 Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba." 6 Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, '"Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni." 7 Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu. 8 Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance. 9 Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, "Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?" 10 Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya. 11 Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, "Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma." 12 Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus. 13 Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci. 14 Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, "Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus. 15 Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan. 16 Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus. 17 Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, "Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa." 18 Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, "Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka." 19 Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, "Menene kake so ka fada mani?" 20 Saurayin yace, "Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin. 21 Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini." 22 Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, "Kar ka fada wa wani al'amuran." 23 Sai ya kira jarumai biyu yace, "Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare." 24 Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna. 25 Sai ya rubuta wasika a misalin haka: 26 Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus. 27 Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne. 28 Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa. 29 Na gane cewa ana zarginsa ne a kan tambayoyi game da shari'ansu, amma ba wani zargi da ya cancanci dauri ko mutuwa. 30 Da aka sanar da ni shirin makircin, sai na tura shi wurinka ba da bata lokaci ba, na umarce masu zarginsa su kawo zarginsu wurinka. Huta lafiya." 31 Sai sojoji suka yi biyayya da umarni da aka basu: suka dauki Bulus suka kawo shi dadare a wurin Antibatris. 32 Da gari ya yawe, yan dawakai suka tafi tare da shi kuma sauran sojoji suka koma farfajiya. 33 Bayan da yandawakan suka isa Kaisiririya sun mika wasika ga gwamna, suka kuma danka Bulus a hanunsa. 34 Da gwamna ya karanta wasikar, sai ya tambaye su daga wani yanki ne Bulus ya fito; da ya ji daga yankin kilikiya ne, 35 Yace zan saurare ka sosai lokacin da masu zargin ka sun zo. Sai ya umarta a tsare shi a fadar Hiridus.

24

1 Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna. 2 Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, "Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu; 3 don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus. 4 Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan. 5 An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa. 6 Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. 1 7 Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu. 8 Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai. 9 Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne. 10 lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, "Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani. 11 Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada. 12 Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba. 13 Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau. 14 Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa. 15 Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu; 16 a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura. 17 Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai. 18 Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba. 19 Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na. 20 In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa; 21 sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'" 22 Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, "Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci." 23 Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi. 24 Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu. 25 Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, "Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka." 26 A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi. 27 Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.


1Wasu tsoffin kwafi suna ƙarawa, Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu .

25

1 Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima. 2 Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus. 3 Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya. 4 Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can. 5 "Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi." 6 Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa. 7 Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba. 8 Bulus ya kare kansa ya ce, "Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar." 9 Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, "Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?" 10 Bulus ya ce, "Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai. 11 Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar." 12 Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, "Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar." 13 Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas. 14 Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, "Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku. 15 Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi. 16 Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin. 17 Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin. 18 Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta. 19 Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai. 20 Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa. 21 Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar." 22 Agaribas yace wa Festas. "Zan so ni ma in saurari mutumin nan." "Gobe za ka ji shi," in ji Fostus. 23 Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu. 24 Festas ya ce, "Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba. 25 Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi. 26 Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi. 27 Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba."

26

1 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, "Za ka iya kare kan ka." Sai Bulus ya daga hannunsa ya fara kare kansa. 2 "Ina farinciki, ya sarki Agaribas, game da saran da Yahudawa ke kawowa a kaina yau; 3 musamman ma don kai masani ne game da al'adun Yahudawa da al'amuransu. Don haka, ina rokanka ka yi hakuri ka saurare ni. 4 Hakika, dukan Yahudawa sun san yadda na yi rayuwa ta daga kurciyata a kasa ta, da kuma Urushalima. 5 Sun san ni tun farko, kuma yakamata su yarda cewa na yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addininmu. 6 Yanzu ina tsaye a nan dominn a shari'anta ni, saboda alkawalin da Allah ya yi wa ubanninmu. 7 Domin wannan shine alkawalin da kabilunmu goma sha biyu suka sa zuciya su karba, yayin da suke yin sujada da himma ga Allah dare da rana. Saboda wanan bege, Sarki Agaribas, Yahudawa ke tuhuma ta. 8 Me ya sa wani zai yi tunani cewa abin mamaki ne Allah ya ta da mattatu? 9 Da, na yi tunanin yin abubuwa gaba da sunan Yesu Banazarat. 10 Na yi wadanan a Urshalima. Na kulle masu bi da yawa a kurkuku, sanadiyar iko da na samu daga wurin manyan firistoci, kuma da ake kashe su ma, ina ba da goyon baya. 11 Na wahalshe su sau dayawa a cikin dukan majamiu ina kuma yin kokari in tilasta masu su yi sabo. Na yi gaba mai zafi da su kuma na tsananta masu har zuwa birane na wadansu kasashe. 12 A sa'anda nake yin wannan, na tafi Dimashku da izinin manyan firistoci; 13 a cikin tafiyata kuma, da tsakar rana, ya sarki, na ga haske daga sama da ya fi rana sheki, ya haskaka kewaye da ni da kuma wadanda ke tafiya tare da ni. 14 Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.' 15 Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa. 16 Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani; 17 Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu, 18 domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.' 19 Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba; 20 amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba. 21 Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni. 22 Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru; 23 wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai." 24 Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, "Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka." 25 Amma Bulus ya ce, "Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa. 26 Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba. 27 Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta." 28 Agaribas ya ce wa Bulus, "A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?" 29 Bulus ya ce, "Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin." 30 Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su; 31 da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, "Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba." 32 Agaribas ya ce wa Fastos, "Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi."

27

1 Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas. 2 Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu. 3 Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su. 4 Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu. 5 Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya. 6 Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa. 7 Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina. 8 Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya. 9 Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su, 10 ya ce, "Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu." 11 Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi. 12 Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas. 13 Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba. 14 Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin. 15 Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa. 16 Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban. 17 Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu. 18 Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin. 19 A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu. 20 Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira. 21 Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, "Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar. 22 Yanzu fa ina karfafa ku kuyi karfin hali, domin ba wanda zai rasa ransa a cikinku, sai dai jirgin kadai za a rasa. 23 Domin daren da ya gabata mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, wanda kuma nake bautawa -mala'ikansa ya tsaya kusa dani 24 ya ce, "Kada ka ji tsoro, Bulus, dole ka tsaya gaban Kaisar, duba kuma, Allah cikin jinkansa ya baka dukan wadannan da ke tafiya tare da kai. 25 Domin haka, jama'a, kuyi karfin hali, domin na gaskanta da Allah, kamar yadda aka fada mani haka zai faru. 26 Amma lallai dole ne a jefa mu kan wani tsibiri". 27 Sa'adda dare na goma sha hudu ya yi, ana ta tura mu nan da can a cikin tekun Adriyat, wajen tsakar dare, ma'aikatan jirgin sun tsammaci sun kusanci wata kasa. 28 Da suka gwada sai suka iske kamu ashirin; bayan dan lokaci kadan, sun sake aunawa sai suka iske kamu sha biyar ne. 29 Tsoro ya kama su ko watakila a jefar da mu kan duwatsu, sai suka jefa linzami hudu daga karshen jirgin suka yi addu'a don gari ya waye da sauri. 30 Ma'aikatan jirgin ruwan suna neman hanyar da za su rabu da jirgin kuma sun jefa karamin jirgin a cikin teku. Suka yi kamar zasu jefa wasu linzamai daga gaban jirgin. 31 Amma Bulus ya ce ma jarumi da sojojin, "Idan mutanen nan ba zasu tsaya cikin jirgin ba, ba zaku tsira ba". 32 Sai sojojin suka yanke igiyoyin jirgin suka kuma barshi ya fadi. 33 Da gari ya fara wayewa, Bulus ya roke su duka su dan ci abinci, ya ce, "Yau kwana goma sha hudu kenan ba ku ci kome ba. 34 Saboda haka na roke ku ku ci abinci, domin wannan saboda lafiyarku ne; kuma ko gashin kanku daya baza ku rasa ba". 35 Da ya fadi haka sai ya dauki gurasa ya yi godiya ga Allah a idanun kowa. Sai ya gutsutsura gurasa ya fara ci. 36 Sai dukansu suka karfafu suka kuma ci abinci. 37 Mu mutane 276 (dari biyu da saba'in da shida) ne cikin jirgin. 38 Da suka ci suka koshi, suka zubar da alkamar cikin teku domin su rage nauyin jirgin. 39 Da gari ya waye, basu fahimci kasar ba, amma suka hangi wani lungu a gacci, sai suka yi shawara tsakaninsu ko su tuka jirgin zuwa cikin lungun. 40 Sai suka yanke linzaman suka bar su cikin tekun. Cikin lokaci guda suka kwance igiyoyin da ke juya jirgin, suka saki filafilan goshin jirgi suka nufi gabar tekun. 41 Da suka iso inda ruwa biyu suka hadu, sai jirgin ya tsaya kasa. Gaban jirgin ya kafe a nan, ba damar matsawa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa saboda haukan rakuman ruwa. 42 Shirin sojojin ne su kashe 'yan kurkukun domin kada su yi iyo su tsere. 43 Amma shi hafsan ya so ya ceci Bulus, sai ya tsai da shirin su, ya ba da umarni, duk masu iya iyo su yi tsalle su fada ruwa su kai gacci. 44 Sa'annan sauran mazajen su biyo baya, wadansu a kan karyayyun katakai, wadansu akan abubuwan da ke a jirgin. Ta haka ne dukanmu muka kai gacci lafiya.

28

1 Sa'adda muka sauka lafiya, sai muka ji cewa sunan tsibirin Malita. 2 Mutanen garin sun nuna mana alheri matuka don sun hura wuta don mu ji dimi, saboda ruwan sama da sanyin da ake yi. 3 Amma sa'adda Bulus ya tara kiraruwa don hura wuta, sai maciji saboda zafin wuta, ya fito ya nade hannuwansa. 4 Da mazaunan garin suka ga maciji ya nade hannuwansa, sai suka cema junansu, "Ba shakka wannan mutumin mai kisan kai ne, koda shike ya tsira daga Teku, sharia baza ta barshi da rai ba". 5 Amma ya karkade macijin cikin wuta ba tare da ya cutar da shi ba. 6 Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne. 7 A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku. 8 Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa. 9 Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa. 10 Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata. 11 Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza. 12 Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin. 13 Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli. 14 A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma. 15 Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa. 16 Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa. 17 Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, "Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma. 18 Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba. 19 Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne. 20 Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar". 21 Sai suka ce masa, "Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai. 22 Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina." 23 Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma. 24 Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba. 25 Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, "Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku. 26 Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba. 27 Amma zuciyar mutanen nan ta yi kanta, kunnuwansu sun ji da kyar, sun rufe idanunsu; don kada su gani su gane, su kuma ji da kunuwansu, kuma su fahimta da zuciyarsu, domin su juyo ni kuma in warkar da su." 28 Saboda haka, sai ku sani cewa wannan ceto na Allah an aikar da shi zuwa ga Al'ummai, za su kuma saurara." 29 1 30 Bulus ya zauna shekaru biyu a cikin gidan hayarsa, yana marabtar duk wadanda suka zo wurinsa. 31 Yana wa'azin mulkin Allah, yana koyarwa da al'amuran Ubangiji Yesu Kristi gaba gadi. Ba wanda ya hana shi.


1Ayyukan Manzanni 28: 29 - Wasu tsoffin kwafi suna da aya ta 29: Sa'adda ya fadi wannan zantattuka, Yahudawa suka tashi, suna gardama da junansu .

Romawa
Romawa
1

1 Bulus, bawan Yesu Almasihu, kirayayye ya zama manzo, kuma kebabbe domin bisharar Allah. 2 Wannan itace bisharar da ya alkawarta tuntuni ta wurin annabawansa ta wurin tsarkakakkun littattafan sa. 3 Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki. 4 Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu. 5 Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa. 6 cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu. 7 Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu. 8 Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya. 9 Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku. 10 A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah. 11 Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku. 12 Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku. 13 Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai. 14 Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima. 15 Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma. 16 Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa, 17 Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, "Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya." 18 Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su. 19 Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri. 20 Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja. 21 Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta. 22 Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye. 23 Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki. 24 Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu. 25 Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin. 26 Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace. 27 Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama. 28 Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa. 29 Suna cike da dukkan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, kuma cike da kishi, kisan kai, tarzoma, makirci, da kuma munanan manufafofi. 30 Masu gulma da kage, makiyan Allah. Masu tada zaune tsaye, masu taurin kai, da ruba, masu kaga kowadanne miyagun abubuwa, kuma masu kin yin biyayya ga iyayensu. 31 Masu duhun zuciya; masu cin amana, marasa soyayya, da kuma rashin tausayi. 32 Suna sane da tsarin Allah cewa masu yin irin wadannan al'amura sun cancanci hukuncin mutuwa. Ba kuwa yin wadannan abubuwan ka dai suke yi ba, harma goyon bayan masu yinsu suke yi.

2

1 Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa. 2 Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa. 3 Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah? 4 Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane? 5 Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah. 6 Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa: 7 Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. 8 Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu. 9 Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa. 10 Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa. 11 Domin kuwa Allah ba mai tara bane. 12 Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a. 13 Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata. 14 Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar. 15 Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu. 16 hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu. 17 Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah, 18 ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar. 19 Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu, 20 mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya. 21 ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata? 22 Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali? 23 ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a? 24 "Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku," kamar yadda aka riga aka rubuta. 25 Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya. 26 domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba? 27 Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka! 28 Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba. 29 Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.

3

1 To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya? 2 Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah. 3 Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki? 4 Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, "Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a." 5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka. 6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya? 7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi? 8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, "Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?" Hukuncin su halal ne. 9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi. 10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya. 11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah. 12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya. 13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu. 14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci. 15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini. 16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa. 17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba. 18 Babu tsoron Allah a idanunsu." 19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah. 20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo. 21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa. 22 Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci: 23 Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah, 24 Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu. 25 Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya 26 cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu. 27 To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya. 28 Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba. 29 Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma. 30 Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya. 31 Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.

4

1 Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu? 2 Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba. 3 Kuma fa me nassi ke fadi? "Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi." 4 Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa. 5 Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci. 6 Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka. 7 Sai ya ce, "Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke. 8 Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba." 9 To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, "Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi." 10 Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya. 11 Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu. 12 Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya. 13 Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne. 14 Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan. 15 Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni. 16 Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa, 17 kamar yadda aka rubuta, "Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa." Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance. 18 Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, "... Haka zuriyarka zata kasance." 19 Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba. 20 Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah. 21 Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne. 22 Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci. 23 To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa. 24 A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25 Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.

5

1 Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu. 2 . Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah. 3 Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da 4 Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba. 5 Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu. 6 Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada. 7 To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum. 8 Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu. 9 Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah. 10 Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa. 11 Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu. 12 Saboda haka, kamar yadda ta wurin mutum daya zunubi ya shigo cikin duniya, ta haka mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi. 13 Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya, amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a. 14 Duk da haka, mutuwa ta mallake tun daga Adamu har Musa, har ma wadanda basu yi zunubin keta umarni irin na Adamu ba, wanda yake misalin mai zuwan nan a gaba. 15 Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa. 16 Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa. 17 Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu. 18 Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa. 19 Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci. 20 Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi. 21 Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu.

6

1 Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita? 2 Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa? 3 Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba? 4 An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa. 5 Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa. 6 Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi. 7 Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi. 8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi. 9 Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa. 10 Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne. 11 Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu. 12 Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa. 13 Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci. 14 kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke. 15 To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba. 16 Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci. 17 Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku. 18 An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci. 19 Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci. 20 Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci. 21 A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa. 22 Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada. 23 Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

7

1 'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa? 2 Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure. 3 To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, "yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum. 4 Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya. 5 Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa. 6 Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba. 7 To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, "Kada kayi kyashi." 8 Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne. 9 Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu. 10 Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya. 11 Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni. 12 Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau. 13 To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi. 14 Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi. 15 Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa. 16 Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau. 17 Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina. 18 Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa. 19 Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa. 20 To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina. 21 Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani. 22 Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah. 23 Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina. 24 Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa? 25 Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.

8

1 Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu. 2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa. 3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki. 4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya. 5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu. 6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama. 7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya. 8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya. 9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane. 10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci. 11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku. 12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki. 13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu. 14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne. 15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, "Abba, Uba!" 16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne. 17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi. 18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba. 19 Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah. 20 Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin. 21 Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah. 22 Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu. 23 Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu--mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan. 24 Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani? 25 Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri. 26 Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa. 27 Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah. 28 Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri. 29 Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa. 30 Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka. 31 Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu? 32 Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi? 33 Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke "yantarwa. 34 Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu. 35 Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi? 36 Kamar yadda aka rubuta, "Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka." 37 A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu. 38 Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko, 39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.

9

1 Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2 cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata. 3 Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. 4 Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai. 5 Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. 6 Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba. 7 Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma "ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka." 8 Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su. 9 Wanna ce kalmar alkawari, "badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da." 10 Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku. 11 Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira-- 12 kamar yadda Ya ce, mata, "babban zaya yiwa karamin bauta," haka nassi yace, 13 "Kamar yadda aka rubuta: "Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi." 14 To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan. 15 Gama ya ce wa Musa, "Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa." 16 Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai. 17 Gama nassi ya ce da Fir'auna, "Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya." 18 Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama. 19 Za kuce mani, to don me, "Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?" 20 In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, "Don me yasa ka ginani haka?" 21 Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki? 22 In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa? 23 To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko? 24 Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai? 25 Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: "zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba. 26 Zai zama kuma a inda aka ce da su, "ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai."' 27 Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, "in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto. 28 Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba. 29 Yadda Ishaya ya rubuta ada, "In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata. 30 To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya. 31 Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba. 32 To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi. 33 Kamar yadda aka rubuta, "Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba."

10

1 'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton. 2 Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba. 3 Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba. 4 Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata. 5 Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: "mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin." 6 Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, "Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?"(don ya sauko da Almasihu kasa). 7 Kada ku ce, "Wa zai gangara zuwa kasa?" (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu). 8 Amma me yake cewa? "kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka." Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa. 9 Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto. 11 Don nassi na cewa, "Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba," 12 Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi. 13 Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto. 14 To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba? 15 Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, "Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!" 16 Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata da sakon? 17 Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu. 18 Amma na ce, "ko basu ji ba ne? I, tabbas" muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya." 19 yau, na ce, "Ko Isra'ila basu sani ba ne?" Da farko Musa ya ce, "Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali." 20 Amma Ishaya da karfin hali ya ce, "Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba. 21 "Amma ga Isra'ila kam ya ce, "na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai."

11

1 Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu. 2 Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah? 3 Ya ce, "Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni." 4 Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, "Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba." 5 Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri. 6 Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan. 7 Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare. 8 Kamar yadda yake a rubuce, "Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana." 9 Dauda kuma ya ce, "bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su. 10 Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum." 11 Na ce, "sun yi tuntube domin su fadi ne?" Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi. 12 Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala? 13 Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata. 14 Yana yiwuwa in sa "yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su. 15 Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa. 16 'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama. 17 Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din. 18 Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku. 19 Kana iya cewa, "An karye rassan domin a same ni a ciki." 20 Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro. 21 Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba. 22 Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku. 23 Hakanan, idan ba su ci gaba cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a maida su cikin itacen. Domin Allah zai iya sake maida su. 24 Idan an yanke ka daga itacen zaitun da ke na jeji, har ya yiwu an hada ka cikin itacen zaitun na ainihi, yaya kuma wadannan Yahudawa wadanda sune ainihin rassan, da za'a maido cikin zaitun da ke na ainihi? 25 Yan'uwa, ba na so ku kasance cikin duhu a game da wannan asirin, domin kada ku zama da hikima cikin tunaninku. Wannan asirin shine cewa wannan taurarewa ta faru a Isra'ila, har sai da Al'ummai suka shigo ciki. 26 Ta haka dukan Isra'ila za su tsira, kamar yadda yake a rubuce: "Daga cikin Sihiyona mai Kubutarwa zai fito; Zai kawar da kazanta daga cikin Yakubu. 27 Wannan zai zama alkawarina da su, sa'adda na kawar da zunubansu." 28 A wani bangaren kuma game da bishara, su makiya ne amamadinku, ta wani fannin kuma bisa ga zabin Allah su kaunattatu ne saboda ubanni. 29 Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa. 30 Domin ku ma da ba ku yin biyayya ga Allah, amma yanzu kun sami jinkai saboda rashin biyayyarsu. 31 Ta wannan hanyar dai, wadannan Yahudawan sun zama marasa biyayya. Sakamakon haka shine ta wurin jinkan da aka nuna maku, suma su samu jikai yanzu. 32 Domin Allah ya rufe kowa ga rashin biyayya, domin ya nuna jinkai ga kowa. 33 Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa! 34 Don wanene ya san tunanin Ubangiji? Wanene kuma ya zama mai bashi shawara? 35 Ko kuma, wanene ya fara ba Allah wani abu, domin a biya shi?" 36 Daga wurinsa ne, ta wurinsa ne kuma, a gare shi ne kuma dukan abu suka fito. A gare shi daukaka ta tabbata har abada. Amin.

12

1 Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri. 2 Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah. 3 Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya. 4 Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba. 5 haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa. 7 In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa. 8 Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya. 9 Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari. 10 Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma. 11 Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima. 12 Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace. 13 Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku. 14 Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa. 15 Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye. 16 Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa. 17 Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa. 18 Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa. 19 'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, "'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji." 20 "Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi." 21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.

13

1 Bari kowa yayi biyayya da hukuma, saboda babu wata hukuma sai dai in tazo daga Allah; mahukunta da suke nan kuwa daga Allah ne. 2 Saboda da haka duk wanda ya ja hukuma ya ja da dokar Allah; kuma dukan wadanda suka ki hukuma za su sha hukunci. 3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ne ga masu nagarta ba, amma ga masu aikata laifi. Kuna so ku zama marasa tsoron hukuma? Kuyi abu nagari, zaku sami yabo daga yin hakan. 4 Saboda shi bawan Allah ne a gare ku don nagarta. Amma in kun yi abu mara kyau, kuyi tsoro, saboda ba ya dauke da takobi ba tare da dalili ba. Don shi bawan Allah ne mai saka wa mugu da fushi. 5 Saboda haka dole kuyi biyayya, ba don fushi ba, amma saboda lamiri. 6 Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum. 7 Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa. 8 Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka. 9 To, "Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: "Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka." 10 Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a. 11 Saboda wannan, kun san lokaci yayi, ku farka daga barci. Domin cetonmu yana kusa fiye da yadda muke tsammani. 12 Dare yayi nisa, gari ya kusan wayewa. Don haka, sai mu rabu da ayyukan duhu, mu yafa makaman haske. 13 Sai muyi tafiya yadda ya kamata, kamar da rana, ba a cikin shashanci ko buguwa ba. Kada kuma muyi tafiya cikin fasikanci da muguwar sha'awa, ba kuma cikin husuma ko kishi ba. 14 Amma ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutumtaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.

14

1 Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra'ayinsa ba. 2 Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai. 3 Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara'anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi. 4 Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi. 5 Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra'ayinsa. 6 Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya. 7 Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa. 8 Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne. 9 Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu. 10 Amma ku don me kuke shara'anta yan'uwanku? kai kuma don me kake raina dan'uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari'ar Allah. 11 Domin a rubuce yake, "Na rantse, "inji Ubangiji", kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah." 12 Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah. 13 Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa. 14 Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki. 15 Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka. 16 Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu. 17 Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki. 18 Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi. 19 Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna. 20 Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi. 21 Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan'uwanka. 22 Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne. 23 Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.

15

1 Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba. 2 Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi. 3 Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, "zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina." 4 Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi. 5 Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu. 6 Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya. 7 Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah. 8 Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu. 9 Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, "Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka." 10 Kuma an ce. "Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa." 11 Kuma." Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi." 12 Kuma, Ishaya ya ce "Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa." 13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. 14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna. 15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah. 16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17 Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah. 18 Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki. 19 Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka. 20 A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani. 21 Kamar yadda yake a rubuce."Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta." 22 Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama. 23 Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku. 24 Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci. 25 Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima. 26 Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima. 27 Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa. 28 Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya. 29 Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu. 30 Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni. 31 Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya. 32 Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu. 33 Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.

16

1 Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya. 2 Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma. 3 Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu. 4 Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai. 5 Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya. 6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru. 7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni. 8 Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji. 9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena. 10 Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus. 11 Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji. 12 Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji. 13 Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni. 14 Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su. 15 Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su. 16 Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku. 17 Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su. 18 Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi. 19 Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta. 20 Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku. 21 Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana. 22 Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji. 23 Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu. 24 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin. 25 Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa, 26 amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka. 27 Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin.

1 Korintiyawa
1 Korintiyawa
1

1 Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan'uwanmu Sastanisu, 2 zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al'umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko'ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma. 3 Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu. 4 Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku. 5 Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi. 6 Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku. 7 Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8 Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9 Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu. 10 Ina rokon ku, yan'uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya. 11 Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku. 12 Ina nufin: kowannen ku na cewa, "Ina bayan Bulus," ko " Ina bayan Afollos," ko "Ina bayan Kefas," ko "Ina bayan Almasihu." 13 Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus? 14 Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus. 15 Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana. 16 (Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.) 17 Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa'azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa'azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa. 18 Gama wa'azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake, "Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira." 20 Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba? 21 Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa'azi ya ceci masu bada gaskiya. 22 Gama Yahudawa suna bidar al'ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima. 23 Amma muna wa'azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa. 24 Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa'azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi. 26 Dubi kiranku, yan'uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma'aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba. 27 Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi. 28 Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja. 29 Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa. 30 Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu. 31 A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, "Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji."

2

1 Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah. 1 2 Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye. 3 Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa. 4 Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko, 5 saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah. 6 Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. 7 Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu. 8 Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. 9 Amma kamar yadda yake a rubuce, "Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa. 10 Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah. 13 Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya. 14 Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su. 15 Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane. 16 "Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?" Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.


1Wasu 'yan mahimman da tsoffin kwafin Girkanci suna karantawa, a yayinda na bada shaida game da Allah .

3

1 Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu. 2 Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba. 3 Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane? 4 Domin in wani ya ce, "Ina bayan Bulus," wani kuma ya ce, "Ina bayan Afollos," ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba? 5 To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka. 6 Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma. 7 Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman. 8 Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa. 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma. 10 Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin. 11 Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu. 12 Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka, 13 aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi. 14 Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada; 15 amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta. 16 Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku? 17 Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke. 18 Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama" wawa" domin ya zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, "Yakan kama masu hikima a cin makircin su." 20 Har wa yau, "Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne." 21 haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne, 22 Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne, 23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

4

1 Ga yadda za ku dauke mu, kamar bayin Almasihu da kuma masu rikon asiran Allah. 2 Hade da wannan, ana bukatar wakilai su zama amintattu. 3 Amma a gare ni, karamin abu ne ku yi mani shari'a, ko a wata kotu irin ta mutane. Gama bani yi wa kaina shari'a. 4 Ban sani ko akwai wani zargi a kaina ba, amma wannan bai nuna cewa bani da laifi ba. Ubangiji ne mai yi mani shari'a. 5 Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah. 6 Yan'uwa, ina dora wadannan ka'idoji a kaina da Afollos domin ku, yadda ta wurin mu za ku koyi ma'anar maganar nan cewa, "kada ku zarce abin da aka rubuta." Ya zama haka domin kada waninku ya kumbura yana nuna fifiko ga wani akan wani. 7 Gama wa yaga bambanci tsakanin ku da wasu? Me kuke da shi da ba kyauta kuka karba ba? Idan kyauta kuka karba, don me kuke fahariya kamar ba haka ba ne? 8 Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku. 9 A tunanina, mu manzanni, Allah ya sa mu a jerin karshe kamar mutanen da aka zartar wa hukuncin mutuwa. Mun zama abin kallo ga duniya, ga mala'iku, ga mutane kuma. 10 Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ganin mu marasa daraja, ku kuwa masu daraja. 11 Har zuwa wannan sa'a, muna masu yunwa da kishi, marasa tufafi masu kyau, mun sha kazamin duka, kuma mun zama marasa gidaje. 12 Mun yi fama sosai, muna aiki da hanuwanmu. Sa'adda an aibata mu, muna sa albarka. Sa'adda an tsananta mana, muna jurewa. 13 Sa'adda an zage mu, muna magana da nasiha. Mun zama, kuma har yanzu an dauke mu a matsayin kayan shara na duniya da abubuwa mafi kazamta duka. 14 Ban rubuta wadannan abubuwa domin in kunyata ku ba, amma domin in yi maku gyara kamar kaunatattun yayana. 15 Ko da kuna da masu riko dubu goma a cikin Almasihu, ba ku da ubanni da yawa. Gama ni na zama ubanku cikin Almasihu Yesu ta wurin bishara. 16 Don haka, ina kira gare ku da ku zama masu koyi da ni. 17 Shiyasa na aiko Timoti wurin ku, kaunatacce da amintaccen dana cikin Ubangiji. Zai tunashe ku hanyoyina cikin Almasihu, kamar yadda nake koyar da su ko'ina da kowace Ikilisiya. 18 Amma yanzu, wadansun ku sun zama masu fahariya, suna yin kamar ba zan zo wurinku ba. 19 Amma zan zo gare ku ba da dadewa ba, idan Ubangiji ya nufa. Sannan zan san fiye da maganar masu fahariya, amma kuma zan ga ikonsu. 20 Gama Mulkin Allah ba magana kadai ya kunsa ba, amma ya kunshi iko. 21 Me kuke so? In zo wurin ku da sanda ne ko kuwa da kauna da ruhun nasiha?

5

1 Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa. 2 Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku. 3 Gama Kodashike ba ni tare da ku cikin jiki, amma ina tare daku a ruhu, na rigaya na hukunta wanda yayi wannan, tamkar ina wurin. 4 Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum. 5 Na yi haka ne domin in mika wannan mutum ga Shaidan domin a hallaka jikin, don ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji. 6 Fahariyarku bata yi kyau ba. Ko baku sani ba yisti dan kadan ya kan bata dukan dunkule? 7 Ku tsarkake kan ku daga tsohon yisti domin ku zama sabon dunkule, wato gurasar da ba ta da yisti. Gama an yi hadayar Almsihu, dan ragonmu na idi. 8 Don haka, bari mu yi idinmu ba da tsohon yisti ba, wato yisti irin na rashin tabi'a da mugunta. Maimakon haka, bari muyi bukin idi da gurasa marar yisti ta aminci da gaskiya. 9 Na rubuta maku a cikin wasikata cewa kada ku yi hudda da fasikan mutane. 10 Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya. 11 Amma yanzu ina rubuta maku cewa kada ku yi hudda da duk wanda ake kira dan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko in shi mai ashar ne, ko mashayi, ko dan'damfara. Kada ko abinci ku ci da irin wannan mutum. 12 Domin ta yaya zan iya shar'anta wadanda ba 'yan Ikklisiya ba? Maimakon haka, ba ku ne zaku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya ba? 13 Amma Allah ke shar'anta wadanda ke waje. "Ku fitar da mugun mutumin daga cikin ku."

6

1 Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi? 2 Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci? 3 Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai? 4 Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba? 5 Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa? 6 Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba! 7 Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba? 8 Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne! 9 Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu, 10 da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah. 11 Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu. 12 Dukkan abu halal ne a gare ni", amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. "Dukan abu halal ne a gare ni," amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba. 13 "Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne", amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji. 14 Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa. 15 Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake! 16 Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan? 17 Kamar yadda Littafi ya fadi, "Su biyun za su zama nama daya." Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan. 18 Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa. 19 Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne? 20 An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.

7

1 Game da abubuwan da kuka rubuto: "Yayi kyau ga mutum kada ya taba mace." 2 Amma Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta. 3 Kowanne maigidanci ya ba matarsa hakin ta, kuma kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna. 4 Matan ba ta da iko akan jikin ta amma maigidan ne. Haka ma, maigidan bashi da iko akan jikinsa amma matar ce. 5 Kada ku hana wa junanku saduwa, sai dai da yardar junanku domin wani dan lokaci. Kuyi haka domin ku bada kanku ga addu'a. Daganan sai ku sake saduwa, domin kada Shaidan ya jarabce ku saboda rashin kamun kanku. 6 Amma ina fada maku wadannan abubuwa ne a matsayin nuni, ba a matsayin umurni ba. 7 Na so da kowa da kowa kamar ni yake. Amma kowa na da baiwarsa daga wurin Allah. Wani na da irin wannan baiwar, wani kuma waccan. 8 Ga marasa aure da gwamraye, Ina cewa, yana da kyau a garesu su zauna ba aure, kamar yadda nike. 9 Amma idan baza su iya kame kansu ba, ya kamata su yi aure. Gama yafi masu kyau su yi aure da su kuna da sha'awa. 10 Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: "Kada mace ta rabu da mijinta." 11 Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma " Kada miji ya saki matarsa." 12 Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan'uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta. 13 Idan kuwa mace tana da miji marar bi, idan ya yarda ya zauna tare da ita, to kada ta kashe aure da shi. 14 Gama miji marar bada gaskiya ya zama kebabbe saboda matarsa, sannan mata marar bada gaskiya ta zama kebbiya saboda mijinta mai bi. In ba haka ba 'ya'yanku za su zama marasa tsarki, amma a zahiri su kebabbu ne. 15 Amma idan abokin aure marar bi ya fita, a bar shi ya tafi. A irin wannan hali, dan'uwa ko 'yar'uwa ba a daure suke ga alkawarinsu ba. Allah ya kira mu da mu zauna cikin salama. 16 Yaya kika sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? ko yaya ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka? 17 Bari dai kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kamar yadda Allah ya kirawo shi. Wannan ce ka'idata a dukkan ikilisiyu. 18 Mutum na da kaciya sa'adda aka kira shi ga bada gaskiya? Kada yayi kokarin bayyana kamar marar kaciya. Mutum ba shi da kaciya sa'adda aka kira ga bangaskiya? To kada ya bidi kaciya. 19 Gama kaciya ko rashin kaciya ba shine mahimmin abu ba. Mahimmin abu shine biyayya da dokokin Allah. 20 Kowa ya tsaya cikin kiran da yake lokacin da Allah ya kira shi ga bada gaskiya. 21 Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun 'yanci, ka yi haka. 22 Domin wanda Ubangiji ya kira shi lokacin da yake bawa, shi 'yantacce ne na Ubangiji. Hakanan kuma, wanda shike 'yantacce lokacin da aka kira shi ga bada gaskiya, Bawan Almasihu ne. 23 An saye ku da tsada, donhaka kada ku zama bayin mutane. 24 Yan'uwa, a kowace irin rayuwa kowannenmu ke ciki lokacin da aka kira mu ga bada gaskiya, bari mu tsaya a haka. 25 Game da wadanda basu taba aure ba, ba ni da wani umarni daga wurin Ubangiji. Amma ina bada ra'ayina kamar mutum wanda, ta wurin jinkan Allah, yake yardajje. 26 Don haka, Ina ganin saboda yamutsin dake tafe ba da jimawa ba, ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake. 27 Kana daure da mace? Kada ka nemi 'yanci daga gare ta. Baka daure da mace? Kada ka nemi auren mace. 28 Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su. 29 Amma wannan nike fadi ya'nuwa: lokaci ya kure. Daga yanzu, bari wadanda suke da mata suyi rayuwa kamar basu da su. 30 Masu kuka su zama kamar marasa kuka, masu farinciki kamar marasa farinciki, masu sayen abubuwa kamar marasa komai. 31 Wadanda suke harka da duniya kamar ba su harka da ita, domin ka'idar duniyan nan tana kawowa ga karshe. 32 Ina so ku kubuta daga damuwa mai yawa. Mutum marar aure yana tunani akan al'amuran Ubangiji, yadda zai gamshe shi. 33 Amma mai aure yana tunani akan al'amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa, 34 hankalinsa ya rabu. Mace marar aure ko budurwa tana tunanin al'amuran Ubangiji, yadda za ta kebe kanta a jiki da ruhu. Amma mace mai aure tana tunanin al'amuran duniya, yadda za ta gamshi mijinta. 35 Ina fadar wannan domin amfaninku ne, ba domin in takura ku ba. Na fadi wannan domin abinda ke daidai, yadda zaku bi Ubangiji ba tare da hankalinku ya rabu ba. 36 Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure. 37 Amma idan ya tsaya da karfi a zuciyarsa, idan baya shan wani matsi kuma yana iya kame kansa, har ya kudurta a zuciyarsa yayi haka, wato ya kiyaye budurwarsa da yake tashi, to hakan ya yi daidai. 38 Don haka, shi wanda ya auri budurwarsa yayi daidai, sannan shi wanda ya zabi yaki yin aure yafi yin daidai. 39 Mace tana a daure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa. Amma idan mijin ya mutu, tana da 'yanci ta auri duk wanda take so ta aura, amma a cikin Ubangiji. 40 Amma a ganina, za ta fi farinciki idan za ta zauna yadda take. Kuma ina tunanin ni ma ina da Ruhun Allah.

8

1 Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, "Dukanmu muna da ilimi." Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa. 2 Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba. 3 Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum. 4 Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, "Gunki a duniyan nan ba wani abu bane," kuma cewa" Babu wani Allah sai guda daya." 5 To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu "alloli dabam dabam a duniya ko a sama," kamar yadda akwai "alloli da iyayengiji" da yawa. 6 "Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke." 7 Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni. 8 Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba. 9 Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya. 10 Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba? 11 Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka. 12 Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu. 13 Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa.

9

1 Ni ba yantacce bane? Ni ba Manzo ba ne? Ban ga Ubangijinmu Yesu ba? ba ku ne aikin hannuna cikin Ubangiji ba? 2 Idan ni ba Manzo ba ne ga wadansu, hakika ni Manzo ne a gare ku. Ai kune shedar manzanci na cikin Ubangiji. 3 Ga kariya ta zuwa masu zargi na, 4 Ba mu da 'yanci mu ci mu sha? 5 Ba mu da 'yanci mu dauki mace mai bada gaskiya kamar sauran manzanni da Kefas da 'yan'uwan Ubangiji? 6 ko ni da Barnabas ne kawai muka cancanci aiki? 7 Wake aikin soja daga aljihunsa? Wake shuka gonar inabi baya ci daga 'ya'yan ta ba? Ko kuwa wake kiwon tumaki ba ya shan madarasu? 8 Ina wannan zance da ikon mutum ne? Doka bata fadi haka ba? 9 Gama a rubuce yake a attaura ta Musa cewa, Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi. Amma shanu ne Ubangiji ke zance a kai? 10 Ba don mu yake magana ba? An rubuta domin mu ne. Domin wanda yake noma, yayi cikin bege. mai tattake hatsi kuma yayi da begen samu. 11 Idan mun yi shuka ta ruhaniya a rayuwarku, mai wuya ne mu girbi kayan ku na jiki? 12 Idan wadansu sun mori wannan 'yanci a gurin ku, ba mu fi su cancanta ba? duk da haka bamu yi amfani da wannan 'yancin ba, maimakon haka, mun yi jimriya da duk abin da zaya hana bisharar Yesu Almasihu. 13 Baku sani ba masu bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin? Baku sani ba masu bauta a bagadi, suna da rabo daga abin da ake kawowa kan bagadin? 14 Haka kuma Ubangiji ya umarta masu aikin bishara zasu ci abincinsu ta hanyar bishara. 15 Amma ban yi amfani da wannan 'yanci ba, ba kuma ina rubuta maku domin ayi mani wani abu bane, na gwanmace in mutu maimakon wani ya hana ni wannan fahariya. 16 Ko nayi shelar bishara, ba ni da dalilin fahariya domin ya zama dole in yi. Kaito na idan ban yi shelar bishara ba 17 Idan na yi hidimar nan da yardar zuciyata, ina da sakamako, idan kuma ba da yaddar zuciyata ba, harwa yau akwai nauwaya akai na. 18 To menene sakamako na? shi ne in yi shelar bishara kyauta, da haka ba zan yi amfani the 'yanci na cikin bishara ba 19 Ko da shike ni 'yantacce ne ga duka, amma na mai da kaina bawan kowa domin in ribato masu yawa, 20 Ga yahudawa, na zama bayahude, domin in ribato yahudawa, ga wadanda ke karkashin shari'a, na maishe kaina kamarsu, domin in ribato wadanda ke karkashinta. Na aikata wannan ko da shike bana karkashin shari'a 21 Ga wadanda basu karkashin shari'a, na maishe kaina kamar su. Ko da shike ban rabu da shari'ar Allah ba. Amma ina karkashin dokar Almasihu. Na yi haka ne domin in ribato wadanda ba sa karkashin shari'a. 22 Ga marasa karfi, na maishe kaina kamar marar karfi, domin in ribato raunana. Na mai da kaina dukan abu ga dukan mutane domin in sami zarafin da zan ribato wadansu zuwa ceto. 23 Ina dukan abu sabili da bishara, domin kuma in sami albarkar da ke cikinta 24 Baku sani ba mutane da dama suna shiga tsere amma daya neke karbar sakamakon, saboda haka ku yi tsere domin ku karbi sakamako. 25 Dan wasa yana motsa jiki da kame kansa. Yana yi saboda ya karbi wannan sakamako mai lalacewa, amma muna tsere domin mu karbi sakamako marar lalacewa. 26 Saboda haka ba na tsere ko fada haka nan kamar mai bugun iska. 27 Amma ina matse jiki na in maishe shi bawa, kada bayan na yi wa wadansu wa'azi ni kuma a karshe a fitar da ni.

10

1 Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku. 2 Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku, 3 kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya. 4 Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne. 5 Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji. 6 Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi. 7 Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, "Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa." 8 Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu. 9 Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su. 10 kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa. 11 Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu. 12 Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi. 13 Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa. 14 Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka. 15 Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi. 16 Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu? 17 Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne. 18 Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba? 19 Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne? 20 Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu! 21 Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba. 22 Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne? 23 "Komai dai dai ne," amma ba komai ke da amfani ba, "Komai dai dai ne," amma ba komai ke gina mutane ba. 24 Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa. 25 Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 26 Gama "duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne." 27 Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 28 Amma idan wani ya ce maka, "Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne" To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri (gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne). 29 Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani? 30 Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa? 31 Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah. 32 Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah. 33 Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.

11

1 Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu. 2 Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku. 3 Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne. 4 Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa. 5 Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski. 6 Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta. 7 Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce. 8 Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take. 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji. 10 Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku. 11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba. 12 Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke. 13 Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude? 14 Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba? 15 Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin. 16 To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka. 17 Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce. 18 Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar. 19 Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku. 20 Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba! 21 Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu. 22 Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan. 23 Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa. 24 Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, "wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni." 25 Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, "kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni." 26 Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo. 27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa. 28 Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan. 29 In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi. 30 Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci. 31 Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba. 32 In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya. 33 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna. 34 Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.

12

1 Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci. 2 Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado. 3 Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, "Yesu la'ananne ne." Babu kuma wanda zaya ce, "Yesu Ubangili ne," sai dai ta Ruhu Mai Tsarki. 4 Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne. 5 Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne. 6 Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su. 7 To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa. 8 Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya. 9 Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun. 10 Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna. 11 Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa. 12 Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake. 13 Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya. 14 Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa. 15 Idan kafa ta ce, "tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane," wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba. 16 Kuma da kunne zaya ce, '"Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne," fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba. 17 Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna? 18 Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa. 19 Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance? 20 Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne. 21 Ba da ma ido ya fadawa hannu, "Bana bukatar ka," ko kuma kai ya fadawa kafafu, "Ba na bukatar ku." 22 Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba. 23 Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba. 24 Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba. 25 Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura. 26 Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare. 27 Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne. 28 A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban. 29 To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko? 30 Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna? 31 Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.

13

1 Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala'iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo. 2 Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne. 3 Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. (Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya). 4 Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai 5 ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka. 6 Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya. 7 Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa. 8 Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce. 9 Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa. 10 Sa'adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce. 11 Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya. 12 Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani. 13 To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.

14

1 Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci. 2 Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu. 3 Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta'azantar dasu. 4 Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa. 5 To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna (sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu). 6 Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa. 7 Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa? 8 Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma'ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki? 9 Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma'ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku. 10 Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma'ana. 11 Amma idan ban san ma'anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni. 12 haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya. 13 To wanda yake magana da harshe yayi addu'a domin ya iya fassarawa. 14 Domin idan nayi addu'a da harshe, ruhuna yayi addu'a, amma fahimtata bata karu ba. 15 To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata. 16 In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, "Amin" a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba? 17 Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba. 18 Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19 Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe. 20 'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma. 21 A rubuce yake a shari'a cewa, "zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba", in ji Ubangiji. 22 Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba. 23 Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba? 24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar, 25 asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku. 26 Sai me kuma 'yan'uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya. 27 Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada. 28 Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah. 29 Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada. 30 Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru. 31 Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa. 32 Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa, 33 domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya. 34 Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce. 35 Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya. 36 Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso? 37 In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji. 38 In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi. 39 Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna. 40 Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.

15

1 Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita. 2 Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza. 3 Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi, 4 cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi. 5 Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun. 6 Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci. 7 Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka. 8 A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini. 9 Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah. 10 Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni. 11 Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata. 12 To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu? 13 Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan. 14 idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza. 15 Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba. 16 Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan. 17 Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku. 18 To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan, 19 idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi. 20 Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu. 21 Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu. 22 Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka. 23 Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa. 24 Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko. 25 Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa. 26 Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka. 27 Domin " yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," Amma da aka ce" yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba. 28 Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai. 29 ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su? 30 Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a? 31 Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 32 Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? "bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu." 33 Kada fa a yaudare ku, domin " tarayya da mugaye takan bata halayen kirki." 34 "Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya. 35 Amma wani zaya ce, "Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi? 36 Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu. 37 Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban. 38 Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin. 39 Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi. 40 Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce. 41 Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka. 42 Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne. 43 An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko. 44 An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya. 45 Haka kuma aka rubuta, "Adamu na farko ya zama rayayyen taliki." Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai. 46 Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar. 47 Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake. 48 kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama. 49 Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama. 50 To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba. 51 Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu. 52 Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu. 53 Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa. 54 Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, "An hadiye mutuwa cikin nasara." 55 "Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?" 56 Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce. 57 Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu! 58 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.

16

1 Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi. 2 A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba. 3 Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima. 4 Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni. 5 Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya. 6 Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni. 7 Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda. 8 Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos. 9 Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa. 10 Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11 Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa. 12 Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi. 13 Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali. 14 Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna. 15 Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa, 16 kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu. 17 Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku. 18 Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane. 19 Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji. 20 Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki. 21 Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna. 22 Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo! 23 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku. 24 Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. 1


1Copiesan copiesan mahimmanci da tsoffin kwafin Girkanci da wasu tsoffin fassarorin suna da Amin a ƙarshen aya ta 24. Amma da yawa tsoffin kwafin Girkanci, da tsoffin fassarorin da yawa, ba su da Amin a karshen.

2 Korantiyawa
2 Korantiyawa
1

1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma Timoti dan'uwan mu, zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Korantus, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da kuma salama ta Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu. 3 Bari yabo ya tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine Uba na dukan jiyejiyenkai, da kuma Allah na dukan ta'aziya. 4 Allah yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da wadanda ke cikin kowace wahala. Muna ta'azantar da wasu da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu. 5 Gama kamar yadda wahalhalun Almasihu suka karu domin mu, haka kuma ta'aziyarmu ta yawaita cikin Almasihu. 6 Amma fa idan muna shan wuya, domin ta'aziyarku ne da cetonku. Haka kuma in mun ta'azantu, domin ta'aziyarku ne. Ta'aziyarku tana aiki ne sosai yayinda kuka jure da irin shan wuyar da mu ma muke sha. 7 Kuma gabagadinmu game da ku tabbatacce ne. Mun kuwa sani kamar yadda kuke tarayya cikin shan wahalhalun, haka kuma za ku yi tarayya cikin ta'aziyyar. 8 Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu. 9 Hakika, mun ji hukuncin mutuwa akan mu. Amma wannan ya faru ne domin kada mu dogara ga kanmu, sai dai ga Allah, wanda ke tada matattu. 10 Ya kubutar da mu daga wannan mummunan hatsari na mutuwa, kuma zai sake kubutar da mu. Mun kafa begenmu gare shi cewa zai sake kubutar da mu. 11 Zai aikata wannan yayinda kuka taimake mu da addu'ar ku. Sa'an nan da dama za su bada godiya a madadin mu don tagomashin alheri da aka yi mana ta wurin addu'o'in mutane masu yawa. 12 Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah. 13 Bamu rubuta maku abinda ba za ku iya karantawa ko fahimta ba. Ina fata za ku fahimce mu baki daya, 14 kamar yadda kuka fahimce mu kadan yanzu. Daganan a ranar Ubangijinmu Yesu za mu zama dalilinku na alfahari, kamar yadda za ku zama namu. 15 Saboda gabagadin da nake da shi game da haka, naso in zo gare ku da farko, domin ku amfana da ziyara sau biyu. 16 Ina da shirin ziyaratar ku a kan hanyata ta zuwa Makidoniya. Daga nan kuma ina da yi niyyar in sake ziyartar ku, a tafiya ta daga Makidoniya, domin ku aike ni a hanyata ta zuwa Yahudiya. 17 Yayinda nake irin wannan tunani, ina shakka ne? Ina shirya abubuwa ne bisa ga magwajin mutum, ta yadda har zan ce "I, i" da "A, a, a, a" a lokaci guda? 18 Amma kamar yadda Allah yake amintacce, ba ma fadin "I" da "A'a" a lokaci guda. 19 Gama Dan Allah, Yesu Almasihu, wanda Silbanus da Sila, da Ni muka shaida maku, ba "I" da "A, a" ba ne. Maimakon haka, Shi "I" ne a kodayaushe. 20 Gama dukan alkawaran Allah 'I' ne a cikin sa. Haka kuma ta wurin sa muna cewa "Amin" zuwa ga daukakar Allah. 21 Yanzu dai Allah ne ya tabbatar da mu da ku a cikin Almasihu, ya kuma kebe mu. 22 Ya sa hatiminsa a kan mu ya kuma ba mu Ruhu a zuciyar mu a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya. 23 Maimakon haka, na yi kira ga Allah ya zama shaida domina, cewa dalilin dayasa banzo Korintis ba domin in kare ku ne. 24 Ba muna kokarin mu sarrafa yadda bangaskiyar ku za ta zama ba ne. Maimakon haka, muna aiki tare da ku ne domin farincikinku, yayinda kuke tsaye cikin bangaskiyarku.

2

1 Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba. 2 Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba? 3 Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka. 4 Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku. 5 Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka. 6 Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa. 7 Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi. 8 Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili. 9 Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai. 10 Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu. 11 Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba. 12 Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can. 13 Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya. 14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina. 15 Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka. 16 Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan? 17 Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.

3

1 Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba? 2 Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa. 3 Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane. 4 Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu. 5 Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take. 6 Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa. 7 To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa. 8 Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi? 9 Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi! 10 Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi. 11 To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu! 12 Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai. 13 Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra'ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye. 14 Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa'adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi. 15 Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu. 16 Amma sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin. 17 To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci. 18 Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.

4

1 Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba. 2 Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah. 3 Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka. 4 A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah. 5 Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Gama Allah shine wanda ya ce, "Haske zai haskaka daga cikin duhu." Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu. 7 Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba. 8 Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba. 9 Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba. 10 Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma. 11 Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka. 12 Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku. 13 Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: "Na gaskata, saboda haka na furta." Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada. 14 Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa. 15 Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah. 16 Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin. 17 Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa. 18 Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne.

5

1 Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama. 2 Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya. 3 Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba. 4 Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa. 5 Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa. 6 Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji. 7 Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba. 8 Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji. 9 Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi. 10 Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau. 11 Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku. 12 Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba. 13 Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne. 14 Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu. 15 Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi. 16 Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka. 17 Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi. 18 Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu. 19 Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu. 20 Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: "ku sulhuntu ga Allah!" 21 Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.

6

1 haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah. 2 Domin ya ce, "A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku." Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto. 3 Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani. 4 Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala, 5 duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa, 6 cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna. 7 Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu. 8 Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne. 9 Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba. 10 Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai. 11 Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke. 12 Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu. 13 Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku. 14 Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu? 15 Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya? 16 ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: "Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena." 17 Sabili da haka, "Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu," in ji Ubangiji. "Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku. 18 Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni," in ji Ubangiji Mai iko duka.

7

1 Kaunatattu, da shike muna da wadannan alkawura, bari mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu. Bari mu bidi tsarki cikin tsoron Allah. 2 Ku ba mu dama! Bamu bata wa kowa rai ba. Ba mu cutar da kowa ko mu zambaci kowa ba. 3 Ba domin in kayar da ku na fadi haka ba. Domin kuwa na riga na fada muku, cewa kuna zuciyar mu, domin mu mutu tare mu kuma rayu tare. 4 Ina da muhimmin gabagadi a cikin ku, Ina fahariya da ku. Ina cike da ta'aziya. Farincikina ya cika makil duk da wahalhalunmu. 5 Yayin da muka zo Makidoniya, jikinmu bai samu hutu ba. A maimakon haka, mun shiga matsaloli ta ko wace hanya ta wurin tashin hankali a waje tsoro kuma a ciki. 6 Amma Allah, mai ta'azantar da raunana, ya ta'azantar da mu ta wurin zuwan Titus. 7 Ba ta wurin isowar sa kadai Allah ya yi mana ta'aziyya ba. Amma kuma ta wurin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin ku. Ya gaya mana irin matsananciyar kaunarku, bakincikinku, da zurfin kulawarku a kaina. Na kuwa yi farinciki sosai. 8 Kodashike wasikata, ta bata maku rai, ban yi da na sanin haka ba. Amma sa'adda na ga wasika ta ta bata maku rai, na yi da na sani. Sai dai bacin ranku, na dan lokaci ne. 9 Yanzu kuwa, ina farinciki, ba domin bacin ranku ba, amma domin bacin ranku ya kawo ku ga tuba, kun fuskanci bakinciki na ibada, donhaka ba ku yi rashi ba sabili da mu. 10 Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa. 11 Ku dubi irin kyakkyawar niyya da bakincikin nan daga Allah ya haifar a cikin ku. Ina misalin girman niyyar nan taku ta nuna cewa baku da laifi. Ina misalin girman fushinku, tsoronku, da sa zuciyarku, himmar ku, da marmarin ku na ganin cewa an yi adalci! A cikin komai, kun nuna kanku marasa laifi a cikin wannan al'amari. 12 Kodayake na rubuto maku, ban rubuto saboda mai laifin ba, ko kuma saboda wanda aka yi wa laifin. Na rubuto ne domin himmarku gare mu ta sanu gare ku a gaban Allah. 13 Dalilin haka ne muka samu karfafawa. Baya ga ta'aziyyar mu, mun kuma yi murna sosai saboda farin cikin Titus, domin ruhunsa ya wartsake ta wurin ku duka. 14 Domin kuwa idan na yi fahariya da ku a gaban sa, ban ji kunya ba. A sabanin haka, kamar yadda kowane abu da muka fada maku gaskiya ne, fahariyarmu a kan ku ga Titus ta zama gaskiya. 15 Kaunarsa a gare ku tana da girma, kamar yadda ya rika tunawa da biyayyarku duka, yadda kuka karbe shi da tsoro da rawar jiki. 16 Ina farinciki matuka domin ina da cikakken gabagadi a cikin ku.

8

1 Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya. 2 A lokacin babban gwajin wahala, yalwar farincikinsu da tsananin talaucinsu ya haifar da yalwar bayarwa hannu sake. 3 Domin ina shaida, sun yi bayarwa iya kokarinsu, fiye da abinda ma suke iyawa. Cikin yaddar ransu 4 da roko mai yawa suka nace da a ba su zarafi su yi tarayya a wannan hidima ga masu bi. 5 Haka ya auku ba kamar yadda muka yi zato ba. A Maimakon haka, sai da suka fara bada kansu ga Ubangiji. Kuma suka bada kansu gare mu bisa ga nufin Allah. 6 Sai muka karfafa Titus, wanda ya rigaya ya fara wannan aiki, domin ya kammala wannan aiki na bayarwa ta fannin ku. 7 Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa. 8 Na fadi haka ne ba kamar ina umurtar ku ba. A maimakon haka, na fadi haka ne in gwada sahihancin kaunarku ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane. 9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci, domin ta wurin talaucinsa ku yi arziki. 10 A wannan al'amari zan ba ku shawarar da za ta taimake ku. Shekarar da ta wuce, ba fara wani abu kawai kuka yi ba, amma kun yi marmarin ku yi shi. 11 Yanzu ku kammala shi. Kamar yadda kuke da niyya da marmarin yin haka a lokacin, bari ku yi kokari ku kawo shi ga kammalawa iyakar iyawar ku. 12 Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba. 13 Domin wannan aiki ba domin a nawaita maku sannan wadansu su samu sauki ba ne. A maimakon haka, ya kamata a sami daidaituwa. 14 Yalwar ku a wannan lokaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatarku, domin a sami daidaituwa. 15 Yana nan kamar yadda aka rubuta: "Wanda ke da shi dayawa bai samu raguwar komai ba, kuma wanda yake da kadan bai rasa komai ba." 16 Amma godiya ga Allah, da yasa a zuciyar Titus marmarin kulawa da ku kamar wadda nake da ita domin ku. 17 Gama ba rokon mu kadai ya karba ba, amma ya yi da gaske akan haka. Ya zo gare ku ne da yardar kan sa. 18 Mun aiko tare da shi dan'uwa da ake yaba masa a tsakanin dukan Ikkilisiyoyi domin ayyukansa a cikin shelar bishara. 19 Ba domin wannan kadai ba, amma Ikkilisiyoyi ne suka zabe shi ya tafi tare da mu a cikin yin wannan hidima ta alheri. Wannan domin girmama Ubangiji ne kansa da kuma domin aniyarmu ta taimakawa. 20 Muna gudun kada kowa ya sa mana laifi game da wannan alheri da muke dauke da shi. 21 Niyyar mu ce mu yi kyakkyawan abu, ba a gaban Ubangiji kadai ba, amma a gaban mutane ma. 22 Mun kuma aiki wani dan'uwan tare da su. Mun sha gwada shi, kuma mun same shi da himma wajen ayyuka da dama. Yanzu kuma ya kara himma, saboda amincewa mai girma da yake da ita gare ku. 23 Game da Titus, shi abokin tafiyata ne, kuma abokin aikina domin ku. Game da yan'uwanmu, an aiko su ne daga Ikkilisiyoyi. Su kuwa daraja ne ga Almasihu. 24 Don haka, ku nuna masu kaunarku, ku kuma nuna wa Ikilisiyoyi dalilin fahariyarmu game da ku.

9

1 Game da hidima domin tsarkaka, ya dace in rubuta maku. 2 Na san marmarinku, wanda na yi fahariya da shi a gaban mutanen Makidoniya. Na gaya masu Akaya sun riga sun shirya tun bara. Kwazon ku ya sa yawancin su sun shiga aiki. 3 To na aiko maku da 'yan'uwa saboda kada fahariyarmu akanku ta zama a banza, domin kuma ku zauna a shirye, kamar yadda na ce za ku yi. 4 Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku. 5 Sai na ga ya dace in turo 'yan'uwa su zo wurin ku kafin lokaci yayi suyi shirye shirye game da gudummuwar da kuka yi alkawari. Wannan ya zama haka ne domin a shirya shi a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin kwace ba. 6 Batun shine: wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka 7 Bari kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa. Kada ya bayar da bacin rai ko kamar dole. Gama Allah yana kaunar mai bayarwa da dadin rai. 8 Allah na da ikon ya sa kowace albarka ta ribanbanya domin ku, domin, a koyaushe, a cikin dukan abubuwa, ku sami duk abinda kuke bukata. Hakan zai kasance domin ku ribabbanya kowanne kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda aka rubuta, "Ya rarraba arzikinsa, ya bada shi ga matalauta. Adalcinsa ya dawwama har abada." 10 Shi wanda ke bayar da iri ga mai shuka da gurasa domin abinci, zai bayar ya kuma ribabbanya maku iri domin shuka. Zai sa girbin adalcinku ya karu. 11 Za ku wadata ta kowace hanya domin ku zama masu bayarwa, wannan kuwa zai sa a yi wa Allah godiya ta wurin mu. 12 Aiwatar da wannan hidima ba biyan bukatun tsarkaka kawai take yi ba. Tana kuma ribanbanya zuwa ayyuka masu yawa na bada godiya ga Allah. 13 Domin an gwada ku an tabbatar da ku akan wannan hidima, za ku kuma daukaka Allah ta wurin biyayyar ku ga shaidar bisharar Almasihu. Za ku kuma daukaka Allah ta wurin yalwar bayarwarku gare su da kowa duka. 14 Suna marmarin ganin ku, suna kuma yi maku addu'a. Suna yin haka saboda alherin Allah mai girma da ke bisan ku. 15 Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban bayyanawa.

10

1 Ni, Bulus, da kaina nake rokon ku, ta wurin tawali'u da nasihar Almasihu. Ina da saukin kai yayinda nake gaban ku, amma ina da gabagadi a gare ku yayinda ba na tare da ku. 2 Ina rokon ku, yayinda nake gabanku, ba ni so in zama mai tsaurin hali. Amma ina ganin zan bukaci zama mai gabagadi sa'adda nake tsayayya da su wadanda ke zaton muna zama bisa ga jiki. 3 Kodashike dai muna tafiya bisa jiki, ba ma yin yaki bisa jiki. 4 Domin makaman da muke yaki da su ba na jiki ba ne. Maimakon haka, makamai ne na Allah da ke da ikon rushe ikokin shaidan. Suna kawar da dukan gardandamin da ke kawo kaucewa. 5 Muna kuma rushe duk wani abinda ke gaba da sanin Allah. Muna kuma kama kowanne tunani zuwa biyayya ga Almasihu. 6 Muna kuma shirye mu hukunta kowanne irin aiki na rashin biyayya, da zarar biyayyarku ta tabbata. 7 Dubi abin da aka sa a bayyane a gaban ku. In har wani ya tabbata shi na Almasihu ne, bari fa ya tunatar da kansa cewa kamar yadda shi na Almasihu ne, hakanan muma muke. 8 Ko da zan yi fahariya da ikon da muke dashi, wanda Ubangiji ya ba mu domin mu inganta ku, ba domin mu rushe ku ba, ba zan ji kunya ba. 9 Ba na so ya zama kamar ina firgita ku ne da wasikuna. 10 Domin wadansu mutane na cewa, "Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne. Kalmominsa ba abin saurare ba ne." 11 Bari wadannan mutane su sani cewa abinda muke fadi a kalmomin wasikunmu lokacin da ba mu nan, haka za mu yi in muna nan. 12 Mu dai ba mu hada kanmu da kowa, ko kuma mu kwatanta kanmu da wadanda ke yabon kansu. Amma yayin da suke gwada kansu da junansu, suke kuma kwatanta kansu da junansu, ba su da ganewa. 13 Saidai, ba za mu yi fahariya fiye da yadda ya kamata ba. Maimakon haka, za mu yi haka ne gwalgwadon iyakar abinda Allah ya sa muyi, iyakar da takai gareku. 14 Gama bamu yi zarbabi ba sa'adda muka kai gareku. Mune na farko da muka kai gare ku da bisharar Almasihu. 15 Ba mu yi fahariya fiye da kima game da aikin wasu ba. Maimakon haka, muna fatan bangaskiyar ku ta karu domin bangaren aikin mu ya kara fadada kwarai, kuma a daidai iyakarsa. 16 Muna fatan haka, domin mu kai bishara zuwa yankunan da ke gaba da naku. Ba za mu yi fahariya akan aikin da aka yi a yankin wani ba. 17 "Amma bari duk wanda zai yi fahariya, ya yi ta cikin Ubangiji." 18 Domin ba wanda ya ke shaidar kansa shine yardajje ba. Maimakon haka, sai dai wanda Ubangiji ke shaidarsa.

11

1 Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni! 2 Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu. 3 Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu. 4 Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa! 5 Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni. 6 To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan. 7 Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta. 8 Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima. 9 Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka. 10 Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya. 11 Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani. 12 Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi. 13 Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu. 14 Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske. 15 Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata. 16 Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan. 17 Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa. 18 Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya. 19 Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne! 20 Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska. 21 Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya. 22 Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka. 23 Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa. 24 Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala "Arba'in ba daya". 25 Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku. 26 Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya. 27 Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici. 28 Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka. 29 Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba? 30 Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata. 31 Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba! 32 A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni. 33 Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.

12

1 Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji. 2 Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku. 3 Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani- 4 an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi. 5 A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina. 6 Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni. 7 Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa. 8 Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan. 9 Amma ya ce mani, "Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika." Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na. 10 Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma. 11 Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne. 12 Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka. 13 Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin. 14 Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi. 15 Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan? 16 Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara. 17 Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku? 18 Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba? 19 Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi. 20 Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi. 21 Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.

13

1 Wannan ne karo na uku da nake zuwa gare ku, "Ana tabbatar da kowanne zargi ta bakin shaidu biyu ko uku." 2 Na riga na yi magana a baya da wadanda suka yi zunubi da kuma sauran a lokacin da ina tare da ku karo na biyu, kuma ina sake fadi: Idan na sake zuwa, ba zan raga masu ba. 3 Ina fadi maku wannan ne domin kuna neman shaida ko Almasihu na magana ta bakina. Shi ba kasashshe bane zuwa gare ku. Maimakon haka, Shi mai iko ne a cikin ku. 4 Domin an gicciye shi cikin kasawa, amma yana da rai ta ikon Allah. Don mu ma kasassu ne a cikin shi, amma za mu rayu tare da shi cikin ikon Allah dake cikinku. 5 Ku auna kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya. Ku yi wa kanku gwaji. Ba ku lura da cewa Yesu Almasihu yana cikin ku ba? Yana cikin ku, sai dai in ba a amince da ku ba. 6 Gama ina da gabagadin cewa za ku iske an amince da mu. 7 Ina addu'a ga Allah cewa ba za a same ku da laifi ba. Ba wai ina rokon mu bayyana kamar mun ci gwadawar ba. Maimakon haka, ina addu'a ku yi abinda ke dai dai, ko dayake mun yi kamar mun fadi gwadawar. 8 Domin bamu iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya. 9 Muna farin ciki idan mun kasa ku kuma kun yi karfi. Muna addu'a kuma domin ku kammalu. 10 Na rubuta wadannan abubuwa yayinda ba ni tare da ku, saboda yayin da zan kasance da ku ba zan zamar maku mai fada ba. Ba na so inyi amfani da ikon da Ubangiji ya bani in tsattsaga ku, sai dai in gina ku. 11 A karshe, 'yan'uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku. 12 Ku gai da juna da tsattsarkar sumba. 13 Masu bi duka suna gaishe ku. 14 Bari alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.

Galatiyawa
Galatiyawa
1

1 Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu. 2 Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya. 3 Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu, 4 wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu. 5 Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin. 6 Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu. 7 Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu. 8 Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne. 9 Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, "Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne." 10 To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne. 11 Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba. 12 Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni. 13 Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita. 14 Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina. 15 Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa. 16 Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba 17 kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku. 18 Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar. 19 Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji. 20 Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku. 21 Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya. 22 Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu, 23 amma sai labari kawai suke ji, "Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa." 24 Suna ta daukaka Allah saboda ni.

2

1 Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni. 2 Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza. 3 Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya. 4 Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka. 5 Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku. 6 Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so. 7 Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya. 8 Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai. 9 Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya. 10 Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka. 11 Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure. 12 Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya. 13 Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su. 14 Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, "Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa?" 15 Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba "Al'ummai masu zunubi ba." 16 Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa. 17 Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan! 18 Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan. 19 Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah. 20 An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina. 21 Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.

3

1 Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba? 2 Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji? 3 Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki? 4 Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne? 5 To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya? 6 Ibrahim "ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci." 7 Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne. 8 Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: "A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka." 9 Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya. 10 La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, "La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka."' 11 Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin "Mai adalci zai rayu ta bangaskiya." 12 Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, "Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a." 13 Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, "La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace." 14 Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya. 15 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi. 16 Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, "ga zuriya ba" da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, "ga zuriyar ka," wanda shine Almasihu. 17 Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya. 18 Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari. 19 Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici. 20 Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne. 21 Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a. 22 A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta. 23 Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya. 24 Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya. 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora. 26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu. 27 Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu. 28 Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu. 29 Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.

4

1 Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin. 2 A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye. 3 Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya. 4 Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a. 5 Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya. 6 Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, "Abba, Uba." 7 Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah. 8 Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan. 9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko? 10 Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru. 11 Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi. 12 Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba. 13 Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko. 14 Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa. 15 Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni. 16 To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya? 17 Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su. 18 Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba. 19 'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku. 20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai. 21 Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba? 22 A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne. 23 Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne. 24 Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu. 25 Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta. 26 Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu. 27 Kamar yadda yake a rubuce, "Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji." 28 Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari. 29 A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu. 30 Amma menene nassi ya ce? "Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba." 31 Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.

5

1 Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta. 2 Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya. 3 Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a. 4 Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka "baratar" ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri. 5 Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci. 6 A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci. 7 Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya? 8 Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne 9 Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura. 10 Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi. 11 'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje. 12 Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani. 13 'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima. 14 Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; "Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka." 15 Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku. 16 Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba. 17 Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba. 18 Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a. 19 Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi, 20 bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya, 21 hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba. 22 Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya, 23 tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa. 24 Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi. 25 Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu. 26 Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.

6

1 'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji. 2 Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu. 3 Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi. 4 Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba. 5 Domin kowa zai dauki nauyin kayansa. 6 Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa. 7 Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba. 8 Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu. 9 Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba. 10 Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya. 11 Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna. 12 Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu. 13 Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku. 14 Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya. 15 Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci. 16 Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah. 17 Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina. 18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.

Afisawa
Afisawa
1

1 Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu. 2 Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu. 4 Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa. 5 Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so. 6 Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa. 7 Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa. 8 Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu. 10 Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu. 11 An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa. 12 Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu. 13 A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta. 14 Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne. 15 Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa. 16 Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina. 17 Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa. 18 Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa. 19 Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne. 20 Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai. 21 Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa. 22 Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya. 23 Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.

2

1 Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku. 2 A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. 3 Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu. 4 Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu. 5 Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu. 6 Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu. 7 Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa. 8 Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah. 9 Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya. 10 Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu. 11 Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku "marasa kaciya", abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi. 12 Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya. 13 Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu. 14 Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna. 15 Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama. 16 Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu. 17 Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa. 18 Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba. 19 Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki. 20 Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin. 21 A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji. 22 A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.

3

1 Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai. 2 Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku. 3 Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar. 4 Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu. 5 Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu. 6 Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara. 7 Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa. 8 Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka. 9 In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa. 10 Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban. 11 Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 12 Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa. 13 Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku. 14 Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba, 15 wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa. 16 Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku. 17 Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa. 18 Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu. 19 Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah. 20 Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu, 21 daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin.

4

1 Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku. 2 Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna. 3 Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama. 4 Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya. 5 Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya. 6 Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka. 7 Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu. 8 Kamar yadda nassi ya ce, "Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye. 9 Menene ma'anar, "Ya hau?" Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa. 10 Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa. 11 Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa. 12 Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu. 13 Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu. 14 Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya. 15 Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu. 16 Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna. 17 Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani. 18 Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu. 19 Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari. 20 Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba. 21 Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke. 22 Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri. 23 Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku. 24 Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya. 25 Saboda haka ku watsar da karya. "Fadi gaskiya ga makwabcin ka", domin mu gabobin juna ne. 26 "Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi." Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi. 27 Kada ku ba shaidan wata kofa. 28 Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu. 29 Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji. 30 Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa. 31 Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta. 32 Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.

5

1 Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa. 2 Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah. 3 Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi. 4 Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya. 5 Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah. 6 Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya. 7 Kada ku yi tarayya tare da su. 8 Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske. 9 Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya. 10 Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi. 11 Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su. 12 Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su. 13 Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su. 14 Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, "Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka". 15 Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima. 16 Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne. 17 Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji. 18 Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki. 19 Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba. 21 Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu. 22 Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji. 23 Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki. 24 Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu. 25 Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta, 26 Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma. 27 Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi. 28 Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa. 29 Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya. 30 Domin mu gabobin jikinsa ne. 31 "Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya". 32 Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa. 33 Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.

6

1 'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne. 2 "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka" (Doka ta fari kenan da alkawari), 3 "ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya". 4 Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa. 5 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu. 6 Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya. 7 Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba. 8 Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce. 9 Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara. 10 A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa. 11 Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan. 12 Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai. 13 Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi. 14 Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci. 15 Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama. 16 Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun. 17 Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah. 18 Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi. 19 Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara. 20 Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata. 21 Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu. 22 Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku. 23 Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. 24 Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.

Filibiyawa
Filibiyawa
1

1 Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu. 3 Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku. 4 Ko yaushe cikin addu'a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu'a. 5 Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu. 6 Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu. 7 Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara. 8 Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu. 9 Ina yin wannan addu'a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta. 10 Ina addu'a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu'a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu. 11 Wannan kuma domin a cika ku da 'ya'yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah. 12 Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske. 13 Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama'a, 14 har galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi. 15 Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa. 16 Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara. 17 Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina. 18 Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna. 19 Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu'ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20 Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa. 21 Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce. 22 Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba. 23 Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai! 24 Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku. 25 Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya. 26 Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku. 27 Ku tafiyar da al'amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara. 28 Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne. 29 Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa. 30 Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.

2

1 Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta'aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi. 2 Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya. 3 Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali'u kowa na duban wadansu fiye da kansa. 4 Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu. 5 Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu. 6 Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba. 7 Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum. 8 Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye. 9 Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna. 10 Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya. 11 Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba. 12 Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba. 13 Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi. 14 Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba. 15 Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, 'ya'yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara. 16 Ku rike kalmar rai da karfi domin in sami dalilin daukaka Almasihu a ranarsa. Sa'annan zan san cewa ban yi tseren banza ba, ban kuma yi wahalar banza ba. 17 Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka. 18 Kamar haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi farin ciki tare da ni. 19 Amma na yi niyya in aiko da Timoti wurin ku ba da dadewa ba, domin ni ma in sami karfafuwa idan na san al'amuran ku. 20 Gama bani da wani wanda halinmu yayi daidai da nasa, wanda yake juyayin ku da gaskiya. 21 Domin duka ribar kansu suke nema bata Yesu Almasihu ba. 22 Amma kun san darajar sa, kamar yadda da ke hidimar mahaifisa, haka ya bauta mani cikin bishara. 23 Shi nake sa zuciyar in aiko maku ba da dadewa ba idan naga yadda al'amura nake gudana. 24 Amma ina da gabagadi cikin Ubangiji cewa ni da kaina zan zo ba da dadewa ba. 25 Amma ina tunanin yakamata in sake aiko maku da Abafaroditus, shi dan'uwana ne, abokin aiki, da abokin yaki, manzon ku da kuma bawa domin bukatu na. 26 Da shike yana marmarin ku duka, ya damu kwarai da shike kun ji yayi rashin lafiya. 27 Da gaske yayi rashin lafiya har ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayin sa, ba shi kadai ba, amma har da ni, domin kada in yi bakin ciki kan bakin ciki. 28 Domin haka na yi niyyar aiko shi, saboda idan kun sake ganinsa za ku yi farin ciki ni kuma in kubuta daga juyayi. 29 Ku karbi Abafaroditus da dukan murna cikin Ubangiji. Ku ga darajar mutane irin sa. 30 Domin saboda aikin Almasihu ne ya kusan mutuwa. Ya sadakar da ransa domin ya bauta mani domin ya cika hidimar da ya kamata ku yi mani.

3

1 A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku. 2 Ku yi hankali da karnuka. Ku yi hankali da miyagun ma'aikata. Ku yi hankali da masu yanke-yanke. 3 Gama mune kaciyar. Don mune muke sujada ta wurin Ruhun Allah. Mune masu fahariya chikin Almasihu Yesu, kuma ba mu da gabagadi cikin jiki. 4 Ko da shike, ni kaina ina gabagadi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagadi ga jiki, ni na fi shi. 5 An yi mani kaciya a rana ta takwas, daga mutanen Israila, na kabilar Biliyaminu, Bayahuden Yahudawa; ga zancen shari'a Bafarisiye nake. 6 Wajen himma na tsanantawa ikilisiya. Ga zancen adalci cikin sharia, na zama mara abin zargi. 7 Amma duk wadannan abubuwan da suka zama riba a gare ni, na dauke su asara ne saboda Almasihu. 8 I, lallai ina lisafta dukan wadannan abubuwa asara saboda mafificin sanin Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shine na yi asarar dukan abubuwa. Na maishe su marasa amfani domin in ribato Almasihu, 9 a iske ni cikinsa. Ba ni da wani adalcin kaina ta wurin shari'a. Maimakon haka, ina da adalci ta wurin bangaskiya cikin Almasihu, adalcin dake daga wurin Allah ta wurin Bangaskiya. 10 Yanzu ina so in san shi da ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyarsa. In kuma zama kamarsa wajen mutuwarsa, 11 domin ta ko kaka in kai ga tashi daga cikin matattu. 12 Ba wai na rigaya na sami wadannan abubuwa bane, ko kuma na riga na zama cikakke. Amma ina nace bi domin in cafki wannan da Almasihu Yesu ya cafko ni dominsa. 13 'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba. 14 Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na madaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu. 15 Dukan mu wadanda muke kammalallu, sai mu yi tunani ta wannan hanyar, idan kuwa kun yi tunanin wani abu daban, to Allah zai bayyana maku wannan kuma. 16 Sai dai, in da muka rigaya muka kai, bari mu rike shi haka. 17 Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku. 18 Mutane da dama suna tafiya -sune wadanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina fada maku har da hawaye - kamar makiyan gicciyen Almasihu ne. 19 Karshen su hallaka ne. Domin allahn su ciki ne, fahariyar su kuma tana cikin kunyar su. Tunanin su na kan al'amuran duniya. 20 Amma mu 'yangarincin mu a sama yake, daga inda muke sauraron mai ceto, Ubangiji Yesu Almasihu. 21 Za ya sake jikinmu na kaskanci ya siffanta shi kamar jikin darajarsa, siffantacce ta karfin ikonsa inda ya sarayar da dukan abubuwa a gare shi.

4

1 Saboda haka, kaunatattu 'yan'uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai. 2 Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra'ayi daya cikin Ubangiji. 3 Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai. 4 Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki. 5 Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa. 6 Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu'a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah. 7 Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu. 8 A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan. 9 Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku. 10 Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba. 11 Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi. 12 Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata. 13 Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni. 14 Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na. 15 Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai. 16 Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya. 17 Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku. 18 Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah. 19 Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu. 20 Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin. 21 Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan 'yan'uwa da ke tare da ni suna gaisuwa. 22 Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar. 23 Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin

Kolosiyawa
Kolosiyawa
1

1 Bulus manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah da Timoti dan'uwanmu, 2 zuwa ga masu bada gaskiya da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Bari alheri da salama su kasance tare da ku daga wurin Allah Ubanmu. 3 Muna godiya ga Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kuma kullum muna addu'a dominku. 4 Mun ji bangaskiyar ku cikin Almasihu Yesu da kaunar da kuke da ita wa dukan kebabbu ga Allah. 5 Kuna da kaunar nan domin bege na hakika ga abin da aka tanadar maku a sama. Kun riga kun ji game da begen nan na hakika maganar gaskiya da bishara, 6 wanda ta zo maku. Wannan bishara tana ba da yaya tana kuma hayayyafa da kuma girma a cikin dukan duniya. Tana yin haka a cikinku kuma tun ranar da kuka ji ta kun kuma yi koyi game da alherin Allah cikin gaskiya. 7 Wannan itace bishara kamar yadda kuka koye ta a wurin Abafaras, kaunataccen abokin bautar mu, wanda ke amintacce mai hidimar Almasihu a madadin mu. 8 Abafaras ya bayyana mana kaunarku a Ruhu. 9 Saboda da wannan kauna, tun daga ranar da muka ji haka, ba mu fasa yi maku addu'a ba. Muna ta roko domin ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima da fahimta ta ruhaniya. 10 Muna ta addu'a domin ku yi tafiya da ta cancanci Ubangiji a kowace hanya da za ta faranta masa rai. Muna ta addu'a cewa za ku ba da 'ya'ya cikin kowanne aikin nagari kuma za ku yi girma cikin sanin Allah. 11 Muna addu'a ku karfafa a cikin kowanne iyawa bisa ga ikon daukakarsa zuwa ga matukar jimrewa da hakuri. 12 Muna addu'a za ku yi godiyar farinciki ga Uban, wanda ya sa kuka samu rabo cikin gado na masu bangaskiya cikin haske. 13 Ya kwato mu daga mulkin duhu ya kuma maishe mu ga mulkin kaunataccen Dansa. 14 Ta wurin Dan ne muka sami fansa, gafarar zunubai. 15 Dan shine surar Allah mara ganuwa. Shine farkon dukan hallitta. 16 Domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, wadanda ke sama da wadanda ke duniya, masu ganuwa da marasa ganuwa. Ko kursiyai ko mulkoki ko sarautai ko ikoki, dukan abubuwa shi ya hallice su kuma dominsa. 17 Ya kasance kafin dukan abubuwa, a cikinsa ne kuma komai yake hade. 18 Kuma shine kan jikin, ikilisiya. Shine farko da kuma dan fari daga cikin matattu, don haka yana da wuri na fari a cikin dukan abubuwa. 19 Domin Allah ya yi farinciki cewa dukan cikarsa ta kasance a cikinsa, 20 kuma ya sulhunta kowanne abu zuwa gare shi ta wurin Dan. Allah ya kawo salama ta wurin jinin giciyensa. Allah ya sulhunta duka zuwa gare shi, ko abubuwan da ke duniya ko abubuwan da ke sama. 21 Domin a da ku baki ne ga Allah, kuma makiyansa ne cikin zuciya da cikin mugun ayyuka. 22 Amma yanzu, ya sulhunta ku ta wurin mutuwarsa ta jiki. Ya yi haka domin ya mika ku tsarkakaku, marasa aibu da marasa abin zargi a gabansa, 23 idan kuka ci gaba cikin bangaskiya, kafaffu da tsayayyu, marasa kaucewa daga begen ku na hakika na bishara da kuka ji. Wannan itace bishara da aka yi wa kowanne halitaccen taliki a karkashin sama. Wannan itace bishara wadda ni, Bulus, na zama bawa. 24 Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya. 25 Saboda wannan ikilisiya na zama bawa, bisa ga haki da Allah ya ba ni domin ku, domin cika sakon Allah. 26 Wannan shine asirin gaskiya da yake a boye shekara da shekaru da zamanai. Amma a yanzu an bayyana shi ga wadanda suka gaskanta da shi. 27 A gare su ne Allah ya so ya bayyana yalwar daukakar asirin gaskiyarsa a tsakanin al'ummai. Ya nuna Almasihu ne ke cikin ku, tabbacin daukaka mai zuwa. 28 Wannan shine wanda muke shella. Muna gargadar da kowanne mutum, muna kuma koyar da kowanne mutum tare da dukan hikima, don mu mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu. 29 Domin wannan nake aiki da himma bisa ga karfinsa da yake aiki a cikina da iko.

2

1 Ina so ku san yadda na sha faman gaske dominku, domin wadanda ke a Lawudikiya, da kuma wadansu da yawa da a jiki basu taba ganin fuska ta ba. 2 Na yi aiki saboda zuciyar su ta sami karfafawa ta wurin hada su cikin kauna zuwa dukan arziki na tabbaci da fahimtar asirin gaskiya na Allah, wato Almasihu. 3 A cikinsa dukan taskar hikima da sani ke boye. 4 Na fadi haka domin kada wani ya yaudare ku da jawabi mai jan hankali. 5 Ko da yake ba na tare da ku a jiki, duk da haka ina tare da ku a cikin Ruhu. Ina murnar ganin ku a yanayi mai kyau da kuma karfin bangaskiyar ku cikin Almasihu. 6 Kamar yadda kuka karbi Almasihu Ubangiji, ku yi tafiya cikinsa. 7 Ku kafu da karfi a cikinsa, ku ginu a kansa, ku kafu cikin bangaskiya kamar yadda aka koya maku, ku yawaita cikin yin godiya. 8 Ku lura kada wani ya rinjaye ku ta hanyar ilimi da yaudarar wofi bisa ga al'adun mutane, bisa ga bin abubuwan duniya, ba na Almasihu ba. 9 A cikinsa ne dukan Allahntaka ta bayyana ta jiki. 10 Ku kuwa kun cika a cikinsa. Shine gaban kowanne iko da sarauta. 11 A cikinsa ne aka yi maku kaciya, ba kaciya irin da yan adam suke yi ba, ta cire fatar jiki, amma ta kaciyar Almasihu. 12 An binne ku tare da shi ta wurin baftisma. Kuma a cikinsa ne aka ta da ku ta bangaskiya a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga mutattu. 13 A lokacin da kuke matattu cikin laifofinku, a cikin rashin kaciyar ku ta jiki, ya rayar da ku tare da shi kuma ya yafe maku dukan laifofinku. 14 Ya share rubutattun basussukanku da ka'idodin da suke gaba da mu. Ya cire su duka ya kafa su a kan giciye. 15 Ya cire ikoki da sarautu. A fili ya falasa su ya shugabance su zuwa ga bukin nasara ta wurin giciyensa. 16 Saboda haka, kada kowa ya shari'anta ku ta wurin ci ko sha, ko kuma sabon wata, ko game da ranakun Assabaci. 17 Wadannan sune inuwar abubuwan da ke zuwa nan gaba, amma ainihin shi ne Almasihu. 18 Kada kowa wanda ke son kaskanci da sujadar mala'iku ya sharantaku ku rasa sakamakonku. Irin wannan mutum yana shiga cikin abubuwan da ya gani ya zama mai girman kai a tunaninsa na jiki. 19 Ba ya hade da kai. Daga kan ne dukan jiki da gabobi da jijiyoyi ke amfani suna kuma hade tare; yana girma da girman da Allah yake bayarwa. 20 In kun mutu tare da Almasihu ga ala'muran duniya, don me kuke rayuwa kamar kuna karkashin duniya: 21 "Kada ku rike, ko ku dandana ko ku taba?" 22 Dukan wadannan abubuwa karshen su lalacewa ne in ana amfani da su, bisa ga kaidodi da koyarwar mutane. 23 Wadannan dokoki suna da hikima ta jiki irin ta addini da aka kago na kaskanci da kuma wahalar da jiki. Amma ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.

3

1 Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah. 2 Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba. 3 Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah. 4 Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa. 5 Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka. 6 Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya. 7 A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu. 8 Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku. 9 Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa, 10 kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi. 11 A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka. 12 A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri. 13 Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku. 14 Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla. 15 Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya. 16 Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah. 17 Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji. 19 Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu. 20 Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai. 21 Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya. 22 Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji. 23 Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba. 24 Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa. 25 Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.

4

1 Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama. 2 Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya. 3 Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka. 4 Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada. 5 Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci. 6 Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum. 7 Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji. 8 Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku. 9 Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan. 10 Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi), 11 da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni. 12 Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah. 13 Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis. 14 Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku. 15 Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta. 16 Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya. 17 Ku gaya wa Arkibas, "Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi." 18 Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.

1 Tassalunikawa
1 Tassalunikawa
1

1 Bulus, Sila, da Timoti zuwa ga Ikilisiyar Tassalonikawa cikin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da Salama su kasance a gare ku. 2 Kullum muna bada godiya ga Allah domin ku dukka, kamar yadda muke ambaton ku a addu'o'in mu. 3 Muna tunawa da ku ba fasawa a gaban Allahn mu da Ubanmu kuma ayyukanku na bangaskiya, da kauna. Da hakurin bege na abinda ke gaba cikin Ubangijinmu Yesu Almasihu. 4 'Yan'uwa kaunatattu na Allah, Mun san kiran ku, 5 yadda bishararmu ta zo gare ku ba ta magana kadai ba, amma da iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa. Ta haka kuma, kun san irin mutanen da muke acikin ku kuma domin ku. 6 Kun zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji, kamar yadda kuka karbi kalmar cikin tsanani mai yawa da murna tawurin Ruhu Mai Tsaki. 7 Sakamakon haka, kuka zama abin misali ga dukkan wadanda ke Makidoniya da na Akaya wadanda suka bada gaskiya. 8 Gama daga gare kune maganar Allah ta bazu ko ina, ba kuwa Makidoniya da Akaya kadai ba. A maimako, har ma zuwa ko ina bangaskiyarku cikin Allah ta kai. Don haka, bama bukatar muce maku komai. 9 Domin su da kansu suna bada labarin irin zuwan mu gare ku. Suna fadin yadda kuka juyo ga Allah daga bautar gumaka don ku bautawa Allah mai rai. 10 Suna bayyana cewa kuna jiran bayyanar Dansa daga sama, wanda ya tasar daga matattu. Wannan shine Yesu, wanda ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.

2

1 Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba. 2 Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa. 3 Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace. 4 A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu. 5 Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu. 6 Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu. 7 A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta. 8 Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu, 9 Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah. 10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya. 11 Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida. 12 Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa. 13 Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya. 14 Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa. 15 Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane. 16 Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe. 17 Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku. 18 Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu. 19 To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a? 20 Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.

3

1 Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna. 2 Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya. 3 Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu. 4 Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani. 5 Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza. 6 Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku. 7 Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu. 8 Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji. 9 Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku? 10 Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku. 11 Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku. 12 Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku. 13 Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.

4

1 A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka. 2 Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu. 3 Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci, 4 Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa. 5 Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa (kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba). 6 Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida. 7 Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki. 8 Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku. 9 Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa. 10 Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari. 11 Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya. 12 Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai. 13 Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba. 14 Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa. 15 Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba. 16 Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi. 17 Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji. 18 Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.

5

1 Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu. 2 Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare. 3 Da suna zancen "zaman lafiya da kwanciyar rai," sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta. 4 Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo. 5 Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu, 6 Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake. 7 Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi. 8 Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba. 9 Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu. 10 Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi, 11 Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi. 12 Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku. 13 Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku. 14 Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa. 15 Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka. 16 Kuyi farin ciki koyaushe. 17 Kuyi addu'a ba fasawa. 18 A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku. 19 Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku. 20 Kada ku raina anabce anabce. 21 Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau. 22 Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta. 23 Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu. 24 Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata. 25 Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu. 26 Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba. 27 Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa. 28 Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.

2 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1

1 Bulus da Silbanus da Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasolonika cikin Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu. 3 Lallai ne mu godewa Allah kulluyaumin domin ku, yan'uwa. Domin hakan dai dai ne, saboda bangaskiyarku ta karu sosai, kuma kaunar junanku tana karuwa. 4 Mu da kanmu muna fahariya da ku a ikilisiyoyin Allah. Muna maganar hakurinku da bangaskiyarku a cikin dukkan tsananin da kuke fuskanta. Muna maganar kuncin da kuke jimrewa. 5 Wannan itace alamar shari'ar Allah ta adalci. Sakamakon haka shine za a dauke ku cancantattu na mulkin Allah wanda kuke wahala dominsa. 6 Adalci ne ga Allah ya mayar da kunci ga wadanda suke kuntata maku, 7 ya kuma baku hutu ku dake shan wuya tare da mu. Zai yi haka ne a bayyanar Ubangiji Yesu daga sama da Mala'ikun ikonsa. 8 A cikin wuta mai huruwa zai dau fansa bisa wadanda basu san Allah ba da wadanda basu karbi bisharar Ubangijinmu Yesu almasihu ba. 9 Za su sha azaba ta hallaka har abada daga fuskar Ubangiji da kuma daukakar ikonsa. 10 Zai yi wannan lokacin da yazo a wannan rana don jama'arsa su daukaka shi, kuma ya zama abin mamaki ga dukkan wadanda suka bada gaskiya. Domin kun gaskata shaidarmu a gare ku. 11 Saboda wannan muke addu'a kullum domin ku. Muna addu'a domin Allahnmu ya sa ku cancanci kiran ku. Muna addu'a ya biya ku muradin ku na yin nagarta da dukkan wani aikin bangaskiya da kuma iko. 12 Muna addu'a haka domin sunan Ubangijinmu Yesu ya sami daukaka daga gare ku. Addu'armu itace ya daukaka ku, saboda alherin Allahnmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.

2

1 Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan'uwa, 2 kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo. 3 Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka. 4 Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah. 5 Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa? 6 Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace. 7 Ko yanzu asirin take shari'a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi. 8 Sa'anan za'a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa. 9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al'ajiban karya, 10 da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto. 11 Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya. 12 Sakamakon shine dukkan su za'a yi masu shari'a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci. 13 Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan'uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya. 14 Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15 Saboda haka yan'uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al'adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu. 16 Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta'aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri, 17 ya ta'azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.

3

1 Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku. 2 Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba. 3 Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun. 4 Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta. 5 Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu. 6 Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba. 7 Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba. 8 Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi. 9 Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu. 10 Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, "Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci." 11 Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu. 12 Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su. 13 Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai. 14 In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya. 15 Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa. 16 Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka. 17 Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu. 18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.

Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
1

1 Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai cetonmu, da Almasihu Yesu begenmu, 2 zuwa ga Timoti, dana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah da Almasihu Yesu Ubangijinmu. 3 Kamar yadda na nanata maka ka yi, da zan tafi Makidoniya cewa, ka dakata a Afisa domin ka umarci wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam. 4 Kada su bata lokacinsu wajen sauraron tatsunniyoyi da kididdiga marar iyaka. Wannan yana haddasa gardandami, maimakon taimakawa shirin Allah, da ke ta wurin bangaskiya. 5 Manufar shari'a kuwa kauna ce daga tsabtacciyar zuciya, da tsatstsakan lamiri, da kuma sahihiyar bangaskiya. 6 Wadansu sun kauce daga tafarkin sun juya zuwa ga maganganun banza. 7 Suna so su zama malaman sha'ria, amma basu fahimci abin da suke fada ba ko abin da suka tsaya akai. 8 Amma mun sani shari'a tana da kyau idan an yi amfani da ita bisa ga ka'ida. 9 Gama mun san wannan, shari'a ba domin mai adalci take ba, amma domin marasa bin doka, mutane masu tawaye, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa Allah, da masu sabo. An bada shari'a domin masu kisan iyaye maza da iyaye mata, da masu kisan kai, 10 Domin fasikai da 'yan ludu, domin masu satar mutane su kai su bauta, domin makaryata, da masu shaidar zur, da kuma dukan abin da ke gaba da amintaccen umarni. 11 Wannan umarni bisa ga daukakkiyar bisharar Allah ne mai albarka, wadda aka bani amana. 12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimu. wanda ya karfafa ni, gama ya karbe ni amintacce, ya sani cikin hidimarsa. 13 Dama can ni mai sabo ne, mai tsanantawa kuma dan ta'adda. Amma duk da haka aka yi mani jinkai domin na yi su cikin jahilci da rashin bangaskiya. 14 Amma alherin Ubangijinmu ya kwararo mani tare da bangaskiya, da kauna da ke cikin Almasihu Yesu. 15 Wannan bishara amintacciya ce, ta isa kowa ya karba, cewa Almasihu Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu zunubi, a cikinsu kuwa ni ne mafi lalacewa. 16 Saboda haka ne na sami jinkai, domin ta wurina ni na farko, a nuna hakurin Yesu Almasihu. Ya yi wannan domin in zama misali ga wadanda za su bada gaskiya zuwa rai madawwami. 17 Yanzu, ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, boyayye, Allah makadaici girma, da daukaka su tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. 18 Ina danka wannan umarni gareka, dana, Timoti. Ina haka ne bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai, domin ka shiga yaki mai kyau. 19 Ka yi wannan domin ka zama da bangaskiya da kyakkyawan lamiri. Wadansu mutane sun ki sauraron wannan suka yi barin bangaskiyarsu. 20 Kamar su Himinayus da Iskandari, wadanda na bada su ga shaidan domin su horu su koyi kin yi sabo.

2

1 Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane, 2 domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja. 3 Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu. 4 Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya. 5 Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne. 6 Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci. 7 Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani. 8 Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba. 9 Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada. 10 Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka. 11 Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai. 12 Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa. 13 Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u. 14 Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi. 15 Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.

3

1 Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau. 2 Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa. 3 Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba. 4 Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma. 5 Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah? 6 Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis. 7 Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis. 8 Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba. 9 Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10 Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi. 11 Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai. 12 Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu. 13 Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu. 14 Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba. 15 Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya. 16 Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: "Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.

4

1 To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu, 2 cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta. 3 Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba. 5 Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a. 6 Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi. 7 Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah. 8 Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa. 9 Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum. 10 Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya. 11 Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa. 12 Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki. 13 Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa. 14 Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu. 15 Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa. 16 Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.

5

1 Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa. 2 Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki. 3 Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske. 4 Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka. 5 Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana. 6 Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye. 7 Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi. 8 Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi. 9 Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya. 10 A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki. 11 Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure. 12 Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari. 13 Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba. 14 Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta. 15 Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan. 16 Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske. 17 Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa. 18 Gama nassi ya ce, "Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi," kuma "Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa." 19 Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku. 20 Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro. 21 Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci. 22 Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta. 23 Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka. 24 Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya. 25 Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.

6

1 Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa. 2 Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa. 3 Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba. 4 Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da 5 yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki." Ka zame daga wadannan abubuwa. 6 Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce. 7 Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba. 8 A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura. 9 To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka. 10 Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa. 11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u. 12 Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. 13 Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti. 14 Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15 Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. 16 Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. 17 Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. 18 Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai. 20 Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace. 21 Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.

Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
1

1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai da ke cikin Almasihu Yesu, 2 zuwa ga Timoti, kaunataccen da: Alheri, jinkai, da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Ubangijinmu. 3 Na gode wa Allah, wanda na ke bautawa tun daga kakannina, da lamiri mai tsabta, sa'adda na ke tuna wa da kai cikin addu'o'ina koyaushe (dare da rana). 4 Sa'adda na tuna da hawayenka, na yi marmarin ganinka, saboda in cika da farin ciki. 5 An tunashshe ni game da sahihiyar bangaskiyarka, wadda ta samo asali daga kakarka Loyis da mahaifiyarka Afiniki. Na kuma tabbata ta na zaune a cikinka. 6 Wannan shine dalilin da ni ke tunashshe ka cewa ka sake rura baiwar Allah da ke cikinka wadda ka samu sa'adda na dibiya maka hannuwana. 7 Domin Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da kamun kai. 8 Saboda haka kada ka ji kunyar shaida ga me da Ubangijinmu, ko ni, Bulus, daurarrensa. Maimakon haka, ka zama a shirye ka sha wahala domin bishara bisa ga ikon Allah. 9 Allah ne ya cecemu kuma ya kira mu da kira mai tsarki. Ya yi wannan, ba ta wurin ayyukanmu ba, amma ta wurin shirinsa da alherinsa. Ya ba mu wadannan abubuwan a cikin Almasihu Yesu kafin farkon zamanai. 10 Amma yanzu an bayyana ceton Allah ta wurin bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu. Almasihu ne ya kawo karshen mutuwa ya kuma kawo rai marar karshe da ya bayyana ta wurin bishara. 11 Domin wannan, an zabe ni mai wa'azi, manzo da mallami zuwa ga al'ummai. 12 Domin wannan dalili na ke shan wahalar wadannan abubuwa. Amma ban ji kunya ba, domin na san shi, wanda na gaskanta. Na sakankance zai iya adana abinda na mika masa har zuwa ranan nan. 13 Ka adana misalin amintattun sakwanni da ka ji daga gare ni, ta wurin bangaskiya da kauna da ke cikin Almasihu Yesu. 14 Abu mai kyau da Allah ya danka maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da ke zaune a cikinmu. 15 Ka dai sani, dukkan wadanda su ke zama a Asiya sun juya mani baya. A cikin kungiyar akwai Fijalas da Harmajanas. 16 Bari Ubangiji ya yi wa iyalin Onisifaras jinkai, domin ya na yawan yi mani hidima, kuma ba ya jin kunyar sarkata. 17 Maimakon haka, sa'adda ya ke a Roma, ya neme ni da kokarin gaske, ya kuma same ni. 18 Bari Ubangiji ya sa, ya sami jinkai daga gare shi a wannan rana. Dukkan hanyoyin da ya taimake ni a kasar Afisa, kun sani sarai.

2

1 Domin wannan kai, dana, ka karfafa cikin alherin da ke cikin Almasihu Yesu. 2 Abubuwan da ka ji daga gare ni a bainar jama'a masu yawa, ka danka su ga mutane masu aminci da za su iya koya wa wadansu kuma. 3 Ka daure shan tsanani tare da ni, kamar amintaccen sojan Almasihu Yesu. 4 Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa. 5 Hakanan, idan wani yana gasa a matsayin dan wasa, ba zai sami rawani ba tukuna har sai in ya karasa tseren bisa ga ka'idodin gasar. 6 Wajibi ne manomi mai kwazon aiki ya fara karbar amfanin gonarsa. 7 Ka yi tunani game da abin da na ke gaya maka, gama Ubangiji zai ba ka ganewa a cikin komai. 8 Ka tuna da Yesu Almasihu, daga zuriyar Dauda, wanda a ka tayar daga matattu. Bisa ga wa'azin bisharata, 9 wanda na ke shan wahala har ya kai ga dauri kamar mai laifi. Amma maganar Allah ba a daure ta ba. 10 Saboda haka na jure wa dukkan abubuwa domin wadanda aka zaba, saboda su ma su sami ceton da ke cikin Almasihu Yesu, da daukaka madawwamiya. 11 Wannan magana tabbatacciya ce: "Idan mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi. 12 Idan mun jure, zamu kuma yi mulki tare da shi. Idan mun yi musun sa, shi ma zai yi musun mu. 13 Idan mun zama marasa aminci, shi mai aminci ne koyaushe, domin shi ba zai yiwu ya musunta kansa ba." 14 Ka yi ta tuna masu da wadannan abubuwan. Ka yi masu kashedi a gaban Allah kada su yi ta dauki ba dadi game da kalmomi. Saboda wannan bai da wani amfani. Domin wannan zai halakar da ma su sauraro. 15 Ka yi iyakacin kokarika domin ka mika kanka ma'aikacin Allah wanda aka tabbatar, wanda babu dalilin kunya a gareshi. Wanda ya ke koyar da kalmar gaskiya daidai. 16 Ka guje wa masu maganar sabo, wanda ya kan kara kaiwa ga rashin bin Allah. 17 Maganarsu za ta yadu kamar ciwon daji. Daga cikinsu akwai Himinayus da Filitus. 18 Wadannan mutanen sun kauce wa gaskiya. Sun fadi cewa an rigaya an yi tashin matattu. Suka birkitar da bangaskiyar wadansu. 19 Duk da haka, ginshikin Allah ya tabbata. Ya na da wannan hatimi: "Ubangiji ya san wadanda ke nasa," Kuma "Duk mai kira bisa ga sunan Ubangiji dole ya rabu da rashin adalci." 20 A gida mai wadata, ba kayayyaki na zinariya da azurfa ba ne kawai. Haka kuma akwai kayayyaki na itace da yunbu. Wadansu domin aikin mai daraja, wadansu kuma ga aiki mara daraja. 21 Idan wani ya tsarkake kansa daga rashin daraja, shi kayan aiki ne mai daraja. An kebe shi, abin aiki domin mai gidan, kuma a shirye domin kowanne aiki mai kyau. 22 Ka guje wa sha'awoyi na kuruciya, ka nemi adalci, bangaskiya, kauna da salama da wadanda suke kira ga sunan Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Amma ka ki tambayoyi na wauta da jahilci. Ka sani sukan haifar da gardandami. 24 Tilas bawan Ubangiji ya guje wa jayayya. A maimakon haka dole ya zama mai tawali'u ga kowa, mai iya koyarwa, kuma mai hakuri. 25 Dole ne ya koyarwa mutane da su ke jayayya da shi a cikin tawali'u. Watakila Allah ya ba su ikon tuba domin sanin gaskiyar. 26 Suna iya sake dawowa cikin hankalinsu kuma su bar tarkon Ibilis, bayan da ya cafke su domin nufinsa.

3

1 Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala. 2 Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki. 3 Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta. 4 Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah. 5 Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen. 6 A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban. 7 Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba. 8 Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya. 9 Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane. 10 Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina, 11 da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni. 12 Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani. 13 Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire. 14 Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya. 15 Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu. 16 Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci. 17 Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.

4

1 Ina bada wannan umarni a gaban Allah da Yesu Almasihu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, kuma saboda bayyanuwarsa da mulkinsa: 2 Ka yi wa'azin Kalma. Ka himmantu a kai ko da zarafi ko ba zarafi. Ka tsautar, ka kwabar, ka gargadar, da dukan hakuri da koyarwa. 3 Gama lokaci na zuwa wanda mutane ba za su jure wa koyarwar kirki ba. Maimakon haka, zasu tattara wa kansu malamai bisa ga sha'awowin zuciyarsu. Za su rika fada masu abin da kunnuwansu ke so. 4 Za su juya kunnuwansu daga koyarwar gaskiya, za su koma wa tatsunniyoyi na banza. 5 Amma kai, sai ka natsu a cikin dukan abubuwa. Ka jure wa wahala; ka yi aikin mai bishara, ka cika hidimarka. 6 Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi. 7 Na yi tsere na gaskiya; na kuma kammala tseren; na rike bangaskiya. 8 An adana mani rawani na adalci, wanda Ubangiji, alkali mai adalci, zai ba ni a ranan nan. Ba ni kadai ba, amma kuma ga dukkan wadanda suke kaunar zuwansa. 9 Ka yi iyakacin kokarinka ka zo wurina da sauri. 10 Domin Dimas ya yashe ni. Ya kaunaci wannan duniyar, ya tafi Tassalonika, Kariskis ya tafi Galatiya, Titus kuma ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kadai yake tare da ni. Ka nemo Markus ka zo tare da shi domin yana da amfani a gareni a cikin aikin. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisus. 13 Ka kawo mani mayafin da na bari a Taruwasa wurin Karbus, idan za ka zo ka taho da shi, duk da littatafan nan, musanman takardun nan. 14 Iskandari makerin dalma ya kulla mani makirci ba kadan ba. Ubangiji zai biya shi gwargwadon ayyukansa. 15 Kai ma ka yi hankali da shi, domin yana tsayyaya da maganganunmu sosai. 16 Da farkon kariyar kaina, babu wanda ya goyi bayana. Maimakon haka kowa ya guje ni. Bana so dai a lissafta wannan a kansu. 17 Amma Ubangiji ya kasance tare da ni, ya kuma karfafa ni, yadda ta wurina, shelar ta sami cika da kyau, domin dukan al'ummai su ji. An kwato ni daga bakin zaki. 18 Allah zai kubutar ni daga dukan ayyukan mugunta, ya kuma cece ni domin mulkinsa na sama. Daukaka ta tabatta a gareshi har abada abadin. Amin. 19 Ka gayar da Briskilla, da Akila, da gidan Onisifurus. 20 Arastus ya nan zaune a Korinti, amma na bar Turufimus ya na zazzabi a Militus. 21 Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa. 22 Bari Ubangiji ya kasance tare da ruhunka. Bari Alheri ya kasance da kai.

Titus
Titus
1

1 Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, ta wurin bangaskiyar zababbun mutanen Allah da sanin gaskiya da ta yadda da allahntaka. 2 Wadannan na cikin begen rai marar matuka wanda Allah, wanda babu karya a cikinsa, ya alkawarta kafin dukkan lokatan zamanai. 3 A daidai lokaci, ya bayyana maganarsa ta wurin sakonsa da ya damka mani in shelar. Zan yi wannan ta wurin umarnin Allah mai ceton mu. 4 Zuwa ga Titus, da' na gaske a cikin bangaskiyarmu. Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah Uba da Almasihu Yesu mai ceton mu. 5 Sabili da wannan ne na bar ka a Karita domin ka daidaita abubuwan da basu cika ba, ka kuma nada dattibai a dukan birane kamar yadda na umarceka. 6 Dole ne dattijo ya zama marar abin zargi, mijin mace daya, da amintattun 'ya'ya wadanda babu wani zargi na mugunta ko rashin kamun kai a kansu. 7 Wajibi ne shugaban Ikklisiya, a matsayin sa na mai kulla da haikalin Allah, ya zama marar aibi. Kada ya zama mai surutu ko rashin hakuri. Kada ya zama mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai hayaniya, ko mai handama. 8 Maimakon haka, ya zama mai karbar baki, abokin abinda ke mai kyau. Dole ne ya zama mai hankali, adali, cike da allahntaka, da kuma kamun kai. 9 Ya zama mai rike amintaccen sakon da aka koyar da karfi, yadda zai iya karfafa wasu da koyarwa mai kyau ya kuma yi wa wadanda suke hamayya da shi gyara. 10 Domin akwai kangararrun mutane dayawa, musamman masu kaciya. Maganganunsu na banza ne. Suna yaudara kuma suna badda mutane. 11 Wajibi ne mu hana su. Suna koyar da abinda bai kamata su koyar ba saboda makunyaciyar riba suna kuma rusar da iyalai dungum. 12 Daya daga cikinsu, kuma mai hikima ne daga cikinsu, yace, "Kirawa manyan makaryata ne, lalatattu kuma miyagun dabbobi, masu kyiuya da zarin cin abinci." 13 Wannan magana gaskiya ne, ka yi masu gyara da tsanani yadda zasu kafu a cikin bangaskiya. 14 Kada ka mai da hankalin ka ga tatsunniyoyi na Yahudawa ko dokokin mutane wadanda sun sauya gaskiya. 15 Ga wadanda suke da tsarki, komai mai tsarki ne. Amma wadanda suke marasa tsarki da rashin bangaskiya, komai marar tsarki ne. Domin zuciyarsu da lamirinsu sun gurbata. 16 Suna cewa sun san Allah, amma sun musanta shi ta wurin ayyukansu. Sun zama abin kyama da marasa biyayya. Ba za a iya tabbaatar dasu ba akan wani aiki maikyau.

2

1 Amma kai, ka fadi abinda yayi daidai da amintaccen umarni. 2 Dole tsofaffin mazaje su zama masu kamun kai, masu daraja kansu, masu-hankali, masu aminci cikin bangaskiya, cikin kauna da jurewa. 3 Haka ma tsofaffin mataye su kame kansu da girma, ba magulmata ba. Kada su zama bayi wajen yawan shan ruwan inabi. Su koyar da abubuwa masu kyau 4 domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu. 5 Su horar dasu su zama masu hikima da tsabtar zuci, masu tsaron gidajensu, kuma masu biyayya da mazajensu. Suyi wadannan abubuwa saboda kada maganar Allah ta sami zargi. 6 Ta haka kuma, ka karfafa samari, su zama masu hankali. 7 A kowanne fanni, ka mayar da kan ka abin koyi a cikin kyawawan ayyuka; idan kayi koyarwa, ka nuna mutunci da martaba. 8 Ka bada sako lafiyayye marar abin zargi, yadda masu hamayya da maganar Allah zasu ji kunya, domin rashin samun mugun abin fadi akan mu. 9 Bayi suyi biyayya ga iyayengijin su a cikin komai. Su faranta masu rai, ba suyi gardama dasu ba. 10 Kada suyi sata. Maimakon haka, sai su nuna dukan bangaskiya mai kyau, domin suyi wa koyarwarmu game da Allah mai cetonmu kwalliya a cikin dukan komai. 11 Domin alherin Allah ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu musanci miyagun ayyuka, da sha'awoyin duniya. Yana horar damu muyi zama cikin hankali, da adalci a cikin hanyar allahntaka a wannan zamani 13 yayin da muke cigaba da jiran karba albarkataccen begenmu, wato bayyanuwar daukakar Ubangiji Allah da kuma mai cetonmu Yesu Almasihu. 14 Yesu ya bada kansa domin mu, domin ya cece mu daga rashin kiyaye doka ya mai damu masu tsarki, domin sa, mutane na musamman wadanda suke da marmarin aikata kyawawan ayyuka. 15 Ka yi magana da karfi ka karfafawa wadannan abubuwa. Ka yi gyara da dukan iko. Kada ka bar wani ya raina ka.

3

1 Ka tuna masu su zama masu sadaukar da kai ga masu mulki da masu iko, suyi masu biyayya, su zama a shirye domin kowane kyakkyawan aiki. 2 Ka tuna masu kada su zagi kowa, su gujiwa gardama, su bar mutane su bi hanyarsu, su kuma nuna tawali'u ga dukan mutane. 3 Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu. 4 Amma da jinkan Allah mai ceton mu da kaunarsa ga 'yan Adam ta bayyana, 5 ba saboda wani aikin adalci da muka yi ba, amma sabili da jinkan sa ne ya cece mu. Ya cece mu ta wurin wankewar sabuwar haihuwa da sabuntuwar Ruhu Mai Tsarki. 6 Allah ya zubo mana Ruhu Mai Tsarki a wadace ta wurin Yesu Almasihu mai cetonmu. 7 Ya yi wannan saboda, bayan mun samu 'yantarwa ta wurin alherinsa, za mu zama magada a cikin begen rai na har abada. 8 Wannan amintaccen sako ne. Ina son kayi magana gabagadi game da wadannan abubuwa, yadda dukan wadanda suka bada gaskiya ga Allah za suyi kudirin yin kyawawan ayyuka da Allah ya mika masu. Waddannan abubuwa masu kyau ne da kuma riba ga dukan mutane. 9 Amma ka guji gardandami na wofi, da lissafin asali, da husuma da jayayya game da dokoki. Wadannan abubuwa basu da amfani kuma marasa riba. 10 Ka ki duk wani dake kawo tsattsaguwa a tsakaninku, bayan ka tsauta masa sau daya ko biyu, 11 ka kuma sani cewa wannan mutumin ya kauce daga hanyar gaskiya, yana zunubi kuma ya kayar da kansa. 12 Sa'adda na aiki Artimas da Tikikus zuwa wurin ka, kayi hanzari ka same ni a Nikobolis, a can na yi shirin kasancewa a lokacin hunturu. 13 Kayi hanzari ka aiko Zinas wanda shi gwani ne a harkar shari'a, da Afolos ta yadda ba zasu rasa komai ba. 14 Ya kamata Jama'armu su koyi yadda zasu yi ayyuka masu kyau da zasu biya bukatu na gaggawa yadda ba za suyi zaman banza ba. 15 Dukan wadanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da masu kaunar mu a cikin bangaskiya. Alheri ya kasance tare da dukan ku.

Filimon
Filimon
1

1 Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan'uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu, 2 da Afiya yar'uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka: 3 Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu. 4 Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu'oi na. 5 Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan'uwa masu bi. 6 Ina addu'a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu. 7 Na yi farinciki kwarai, na kuma ta'azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan'uwa. 8 Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi, 9 duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu. 10 Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina. 11 Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni. 12 Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai. 13 Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara. 14 Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi. 15 Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada. 16 Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji. 17 Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni. 18 Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina. 19 Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba. 20 I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu. 21 Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka. 22 Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu'oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku. 23 Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka, 24 haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina. 25 Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.

Ibraniyawa
Ibraniyawa
1

1 A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa. 2 Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama. 4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu. 5 Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, "Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?" kuma, "Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?" 6 Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, "Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada." 7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, "yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta. 8 A game da Dan, ya ce "kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya. 9 Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka." 10 "Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne. 11 Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi. 12 Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba." 13 Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, "Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?" 14 Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?

2

1 Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana. 2 Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su, 3 ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi. 4 San'nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al'ajabai, da mu'ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa. 5 Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance. 6 Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, "Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi? 7 Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta. 8 Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna. 9 Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa. 10 Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo 'ya'ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa. 11 Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa. 12 Da yace, "zan sanar da sunanka ga ya'uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka." 13 Har wa yau, yace, "Zan dogara a gare shi." Da kuma "Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni." 14 Wato tun da yake 'ya'yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis. 15 Ya kuma 'yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa. 16 Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako. 17 Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan'uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a. 18 Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa'adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.

3

1 Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu. 2 Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah. 3 Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka. 4 Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah. 5 Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba. 6 Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu. 7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: "Yau, Idan kun ji muryarsa, 8 kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji. 9 A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana. 10 Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.' 11 Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba." 12 Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai. 13 Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi. 14 Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe. 15 Game da wannan, an fadi "Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan." 16 Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne? 17 Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji? 18 Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba? 19 Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.

4

1 Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah. 2 Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba. 3 Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, "Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba." Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya. 4 Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, "Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa." 5 Ya sake cewa, "Baza su taba shiga hutu na ba." 6 Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya, 7 Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, "Yau." Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, "Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku." 8 Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba. 9 Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah. 10 Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa. 11 Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi. 12 Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta. 13 Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi. 14 Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi. 15 Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba. 16 Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

5

1 Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai. 2 Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko'ina. 3 Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kadai ba, har ma da na kansa. 4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna. 5 Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, "Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka." 6 Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, "Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak." 7 Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa. 8 Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha. 9 Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya. 10 Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak. 11 Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe. 12 Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba? 13 To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. 14 Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.

6

1 Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2 da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da dora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukuci. 3 Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4 Domin wadanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka dandana baiwar nan Basamaniya, suka kuma sami rabo na Ruhu Mai Tsarki, 5 har su ka dandana dadin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6 sa'an nan kuma suka ridda--ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da yake sake gicciye Dan Allah suke yi su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7 Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. 8 Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne. 9 Ko da yake mun fadi haka, a game da ku kam, ya kaunatattu mun tabbata kuna abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10 Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ki kula da aikinku, da kuma kaunar sunansa da kuke yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11 Muna dai bukata kwarai kowannanku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa karshe. 12 Don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da wadanda suka karbi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da hakurinsu. 13 Sa'adda Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14 Ya ce, "Hakika zan yi maka albarka, in kuma ribambamya zuriyarka." 15 Ta haka, Ibrahim bayan da ya jure da hakuri, ya karbi cikar alkawarin. 16 Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su. Rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa da kowacce magana. 17 Don haka, sa'adda Allah yake son kara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sakewa ba ne sam, sai ya hada da rantsuwa, 18 Domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sakewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi karya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu karfafa kwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19 Muna da bege, kamar yadda yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen. 20 Inda saboda mu ne Yasu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin Malkisadak.

7

1 Wannan ne Malkisadak, sarkin Salem, firist na Allah Madaukaki, wanda ya gamu da Ibrahim na dawowa daga yaki da wasu sarakuna ya kuma albarkace shi. 2 Ibrahim ya ba shi ushirin dukkan ganimar da ya samu. Sunansa," Malkisadak," ma'anar itace, "Sarkin adalci," haka ma, "sarkin salem," ma'anar iitace," Sarkin salama," 3 Bashi da uwa bashi da uba, ba shi da lissafin asalin zuriya, ba shi da farkon rayuwa ba shi da karshen rai. Shi firist ne na har abada, kamar Dan Allah. 4 Yanzu fa dubi irin girman wannan mutum. Kakan kakanninmu Ibrahim ya bada ushira ta abubuwan da ya samo na ganimar yaki gare shi. 5 Kuma hakika, zuriyar Lawi da suka karbi aikin nan na firistanci suna da umarni daga shari'ar Allah cewa su karbi zakka a gun jama'a, wato, daga yan'uwan su Isra'ilawa, koda shike suma zuriyar Ibrahim ne. 6 Amma Malkisadak, shi da ba zuriyar Lawi ba ne, ya karbi zakka daga Ibrahim, ya kuma albarkace shi, shi wanda ya ke da alkawarai. 7 Ba jayayya, karami shi ke karban albarka daga babba wanda ya girme shi. 8 A wannan tsarin mutanen da ke karban zakka wata rana sai ka ga sun mutu, amma a wani kauli mutumin da ya karbi zakka a wurin Ibrahim, ance, wanzaje ne har yau. 9 Kuma bisa ka'ida Lawi, wanda ke karban zakka, shi ma ya bada zakka ga Ibrahim, 10 Saboda kuwa Lawi na cikin tsatson Ibrahim lokacin da Malkisadak ya gamu da Ibrahim. 11 Yanzu in da mai yiwuwa ne a sami kammala cikin aikin firistanci na Lawiyawa (domin ta wurin ta ne aka bada shari'a), to ina amfanin wani firist ya zo bisa ga ka'ida irin ta Malkisadak, ba'a kuma ambaci ka'idar Haruna ba? 12 Don kuwa lokacin da aka canza firistanci, shari'a kuma dole ne a sauya ta. 13 Domin mutumin da aka fadi wadannan abubuwa a kansa na wata kabila ne, wadda ba wani mutumin da ya taba yin aiki a kan bagadi. 14 Wannan a bayyane yake Ubangijinmu ya zo ne daga zuriyar Yahuza, kabilar da Musa bai taba anbatonsu game da zancen firistanci ba. 15 Abinda muke fadi a bayyane yake cewa, idan wani firist ya taso da kamanin Malkisadak. 16 Wannan sabon firist, ba firist ne da ya taso bisa ga ka'idar zuriya ta yan'adam ba, amma ya zama firist ne ta rayuwa mai iko marar shudewa. 17 Domin a rubuce yake cikin littafi ga me da shi; "Kai firist ne na har'abada bisa ga tsari irin na Malkisadak." 18 Domin doka ta fari an ajiye ta a gefe guda saboda rarrauna ce kuma marar amfani. 19 Don kuwa shari'a ba ta iya kamalta kome. Amma fa a kwai bege mai kyau a nan gaba wanda ta gare shi ne zamu sami iso a gun Allah. 20 Kuma wannan kyakkyawan bege baya faruwa ba tare da rantsuwa ba, don kuwa su wadancan firistocin ba su dauki wata rantsuwa ba. 21 Amma Allah yayi rantsuwa game da Yesu cewa, "Ubangiji ya rantse ba kuwa zai fasa tunaninsa ba; 'Kai firist ne har'abada.'" 22 Ta wurin haka Yesu ya bada tabbatacce da kuma ingataccen alkwari. 23 Hakika, mutuwa ta hana firistoci su yi aiki har'abada. Wannan shi ya sa akwai firistoci da yawa daya bayan daya. 24 Amma da shi ke Yesu na rayuwa ne har'abada, aikinsa na firist ba a musanya shi sam sam. 25 Domin haka kuma yana da cikakken ikon ceton wadanda ke gusowa ga Allah ta wurinsa, domin kullum a raye ya ke yana kuma roko dominsu 26 . Domin irin wannan babban firist shi ne ya dace da mu. Ba shi da zunubi, marar abin zargi, tsarkakakke, kebabbe daga masu zunubi, ya na sama da sammai dukka. 27 Ba shi da bukata, kamar manyan firistoci, da ke mika hadayu kullum, da farko don zunubin kansu, sa'annan don zunubin jama'a dukka. Amma Yesu yayi wannan sau daya tak ba kari don kowa da kowa, yayin da ya mika kansa. 28 Domin shari'a na nada mutane da ke da gazawa a matsayin firistoci, amma maganar rantsuwa, wadda ta zo a bayan shari'a, ta nada Dan, wanda ya ke cikakke har'abada.

8

1 Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai. 2 Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba. 3 Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya. 4 Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan. 5 Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: "Duba" Allah ya ce, "kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse." 6 Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura. 7 Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu. 8 Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce "Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza. 9 kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su," inji Ubangiji. 10 Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata. 11 Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, "ku san Ubangiji" gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba. 12 Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba. 13 A kan fadin "sabo" ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.

9

1 To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya. 2 Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa. 3 Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki. 4 Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin. 5 A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki. 6 Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu. 7 Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba. 8 Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye. 9 Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba. 10 Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida. 11 Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa. 12 Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. 13 To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu. 14 To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai? 15 Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami. 16 Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan. 17 Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai. 18 Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini. 19 Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin. 20 Daga nan yace, "Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku." 21 Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su. 22 Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi. 23 Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau. 24 Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu. 25 Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba. 26 Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa. 27 Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a. 28 Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.

10

1 Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba. 2 In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba. 3 Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara. 4 Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai. 5 Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, "Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya. 6 Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi. 7 Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.'" 8 Da fari Yace "ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu." Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a. 9 Sa'annan sai ya ce "gani na zo domin in aikata nufinka." Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu. 10 A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari. 11 Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba. 12 A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah. 13 Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa. 14 Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah. 15 Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace, 16 "Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu. 17 Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba." 18 Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi. 19 Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu. 20 Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa. 21 Saboda muna da babban firist a gidan Allah. 22 Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta. 23 Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne. 24 Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa. 25 Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan. 26 Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa. 27 Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah. 28 Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku. 29 Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri? 30 Domin mun san wanda yace, "Ramako nawa ne; Zan yi sakayya." Sa'annan kuma, "Ubangiji zai hukumta jama'arsa." 31 Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai! 32 Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala. 33 Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki. 34 Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku. 35 Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako. 36 Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa. 37 "Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba. 38 Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba." 39 Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.

11

1 Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al'amuran da idanu basu gani. 2 Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah. 3 Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba. 4 Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu. 5 Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. "Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi." Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya. 6 Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa. 7 Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al'amuran da ba'a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya. 8 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba. 9 Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi. 10 Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah. 11 Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne. 12 Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa. 13 Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya. 14 Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu. 15 Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa. 16 Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu. 17 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya. 18 Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, "Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka." 19 Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa. 20 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba. 21 Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa'adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci 'ya'yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa. 22 Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa'adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar 'ya'yan Isra'ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa. 23 Ta dalilin bangaskiya Musa, sa'adda aka haife shi, iyayensa suka 'boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba. 24 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa'adda ya girma, yaki a kira shi 'dan diyar Fir'auna. 25 A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama'ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci. 26 Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba. 27 Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa 28 Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka 'ya'yan fari ya taba 'ya'yan fari na Isra'ila.` 29 Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa'adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su. 30 Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai. 31 Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya. 32 Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama'ila, da annabawa. 33 Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa'annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna, 34 suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa'annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al'ummai. 35 Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu. 36 Wadansu kuwa suka sha ba'a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku. 37 A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu. 38 Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka. 39 Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna. 40 Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.

12

1 Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu. 2 Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai. 4 Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya: 5 "Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa," 6 Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba. 7 Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba? 8 Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba. 9 Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba? 10 Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa. 11 Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki. 12 Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa. 13 Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke. 14 Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah. 15 Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa. 16 Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari. 17 Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye. 18 Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari. 19 Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta. 20 Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: "koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta." 21 Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, "A tsoroce nake kwarai har na firgita." 22 Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki. 23 Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake. 24 Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila. 25 Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama. 26 A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, "Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai." 27 Wannan kalma, "Harl'ila yau," ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance. 28 Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa. 29 Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.

13

1 Bari kaunar 'yan'uwa ta cigaba. 2 Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala'iku ba tare da saninsu ba. 3 Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali 4 Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar'anta fasikai da mazinata. 5 Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, "Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba." 6 Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, "Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?" 7 Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu. 8 Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada. 9 Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba. 10 Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa. 11 Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi. 12 Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13 Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa. 14 Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa. 15 Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa. 16 Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun. 17 Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba. 18 Kuyi mana addu'a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al'amura. 19 Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri. 20 To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari, 21 ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin. 22 'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku. 23 Ina so ku sani an saki dan'uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri. 24 Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. 'Yan'uwa daga can Italiya suna gaishe ku. 25 Bari alheri ya kasance tare daku dukka.

Yakubu
Yakubu
1

1 Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku. 2 Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi. 3 Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri. 4 Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai. 5 Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi. 6 Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa. 7 Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji. 8 Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa. 9 Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba, 10 amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji. 11 Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa. 12 Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah. 13 Kada wani ya ce idan aka gwada shi, "Wannan gwaji daga wurin Allah ne," domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa. 14 Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi. 15 Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa. 16 Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu. 17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi. 18 Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa. 19 Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi. 20 Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah. 21 Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku. 22 Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku. 23 Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi. 24 Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa. 25 Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi. 26 Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne. 27 Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.

2

1 Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane. 2 Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta. 3 Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, "Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau," mataulacin nan kuwa kuka ce masa, "Kai ka tsaya daga can," ko kuwa, "Zauna a nan kasa a gaba na," 4 Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba? 5 Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba? 6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba? 7 Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba? 8 Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, "Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka," to, madalla. 9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni. 10 Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan. 11 Domin wanda ya ce, "Kada ka yi zina," shi ne kuma ya ce, "Kada ka yi kisan kai." Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan. 12 Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a. 13 Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci. 14 Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya? 15 Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini. 16 Misali, idan waninku kuma ya ce masu, "Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi." Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan? 17 Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce. 18 To, wani zai ce, "Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka." Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na. 19 Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki. 20 Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce? 21 Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi? 22 Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai. 23 Nassi kuma ya cika da ya ce, "Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci." Aka kuma kira shi abokin Allah. 24 Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba. 25 Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba? 26 Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.

3

1 Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani. 2 Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa. 3 Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya. 4 Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so. 5 Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta. 6 Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi. 7 Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma. 8 Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa. 9 Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah. 10 Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba. 11 Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya? 12 "Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba. 13 Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa. 14 Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya. 15 Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu. 16 Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta. 17 Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma. 18 Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.

4

1 Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba? 2 Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba. 3 Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku. 4 Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah. 5 Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, "Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?" 6 Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, "Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu." 7 Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku. 8 Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu. 9 Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki. 10 Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku. 11 Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci. 12 Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka? 13 Saurara, ku da kuke cewa, "Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba." 14 Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace. 15 Maimakon haka, sai ka ce, "Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan." 16 Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce. 17 Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.

5

1 Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku. 2 Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne. 3 Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe. 4 Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna. 5 Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka. 6 Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba. 7 Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe. 8 Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa. 9 Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa. 10 Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji. 11 Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai. 12 Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari "I" ya zama "I", in kuwa kun ce "A'a", ya zama "A'a", don kada ku fada a cikin hukunci. 13 Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo. 14 Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji. 15 Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa. 16 Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske. 17 Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida. 18 Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta. 19 Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi, 20 wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.

Bitrus Ta Fari
Bitrus Ta Fari
1

1 Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zababbu wadanda suke baki, a warwatse cikin Buntus, Galatiya, kappadokiya, Asiya, da Bitiniya. 2 Bisa ga rigasanin Allah Uba, Ta wurin tsarkakewar Ruhu, zuwa biyayya da yayyafar jinin Yesu Almasihu. Alheri da salama su yawaita a gareku. 3 Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurin jinkansa mai girma, ya maya haihuwarmu zuwa bege mai rai ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. 4 Zuwa gado marar lalacewa, marar baci, ba kuma zai kode ba. Wanda aka kebe a sama dominku. 5 Ku da ikon Allah ya kiyaye ta wurin bangaskiya domin ceto wanda za'a bayyana a karshen zamanai. 6 Cikin wannan kuna murna da yawa, duk da ya ke ya zama wajibi gare ku yanzu ku yi bakin ciki, a cikin jarabobi iri iri. 7 Wannan kuwa da nufin a iske aunawar bangaskiyarku ne, bangaskiyar da tafi zinariya daraja, wadda takan lalace ko da an gwada ta da wuta. Wannan ya faru domin bangaskiyan nan taku ta jawo maku yabo da girma da daukaka a bayyanuwar Yesu Almasihu. 8 Wanda kuke kauna, ko da yake baku ganshi ba. Ko da yake baku ganinsa yanzu, duk da haka kun bada gaskiya gare shi murnar da ku ke yi kwarai da farin ciki wanda tafi gaban a fadi cike da daukaka. 9 Kuna karbar sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku. 10 Annabawan da su ka yi annabcin ceton da ya zama naku su ka yi bidassa suka bincike kuma da himma. 11 Sun nemi su san ko wanene da kuma kowanne lokaci ne Ruhun Almasihu da ke cikinsu yake bayyana ma su. Wannan ya faru ne sa'adda yake gaya ma su tun da wuri game da shan wahalar Almasihu da kuma daukakar da zata biyo baya. 12 An kuwa bayyana wa annabawan cewa ba kansu suke hidimtawa ba, amma ku suke yi wa hidima. Wannan shine abin da suke yi game da abin da aka rigaya aka gaya maku, ta wurin wadanda da Ruhu mai Tsarki ya bishe su. Wanda aka aiko daga sama. Wadannan sune abubuwan da mala'iku ma suka yi marmarin a bayyana masu. 13 Domin wannan fa ku natsu. Ku yi dammara a hankalinku. Ku kafa begenku sarai akan alherin da za'a kawo maku a lokacin bayyanuwar Yesu Almasihu. 14 Kamar 'ya'ya masu biyyaya, kada ku biyewa sha'awoyinku na da a zamanin jahilcinku. 15 Amma yadda shi wanda ya kira ku mai tsarki ne, kuma ku zama da tsarki cikin dukkan al'amuranku. 16 Domin a rubuce yake, "Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne." 17 Idan ku na kira bisa gare shi "Uba" shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma. 18 Kun san cewa ba da azurfa ko zinariya mai lalacewa aka fanshe ku ba, daga halinn wauta da kuka gada daga wurin iyayenku. 19 Maimakon haka an fanshe ku da jinin Almasihu mai daraja, marar aibu kamar na dan rago. 20 An zabi Almasihu tun kafin kafawar duniya, amma a karshen zamanu ya bayyanu a gare ku. 21 Ku da kuka bada gaskiya ga Allah ta wurinsa, wanda ya tashe shi daga matattu ya kuma bashi daukaka domin bangaskiyarku da begenku su kasance cikin Allah. 22 Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya. 23 da shike an sake hai'huwarku ba daga iri mai lalacewa ba amma daga iri marar rubewa, ta wurin maganar Allah wadda take rayuwa ta kuma dawwama. 24 Gama "dukkan jiki kamar ciyawa yake, dukkan darajarsa kuwa kamar furen ciyawa take. Ciyawa takan yi yaushi, furenta ya kan yankwane ya fadi, 25 amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. "Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta."

2

1 Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance. 2 Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto, 3 idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne. 4 Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah. 5 Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu. 6 Gama nassi ya ce, "Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba." 7 Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, "Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa". 8 kuma, "Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. "Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan. 9 Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi. 10 Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai. 11 Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai. 12 Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa. 13 Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba. 14 Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta. 15 Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima. 16 Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah. 17 Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki. 18 Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai. 19 Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci. 20 Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah. 21 Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa. 22 Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba. 23 Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci. 24 Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke. 25 Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.

3

1 Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba, 2 Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku. 3 Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa. 4 Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah. 5 Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu. 6 Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi "ubangiji". Yanzu ku 'ya'yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba. 7 Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu'oinku. 8 Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka. 10 "Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara. 11 Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta. 12 Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta." 13 Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari? 14 Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu. 15 Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali'u da bangirma. 16 Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne. 17 Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki. 18 Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu. 19 A Ruhu ne, ya je ya yi wa'azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku. 20 Sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa. 21 Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. 22 Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala'iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.

4

1 Saboda haka, tunda yake Almasihu ya sha wuya a jiki, muma mu sha damara da wannan ra'ayi. Duk wanda ya sha wuya a jiki ya daina aikata zunubi. 2 Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha'awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya. 3 Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al'ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama. 4 Suna tunanin bakon abu ku ke yi da ba kwa hada kai tare da su yanzu a yin wadannan abubuwa, sai suna zarginku. 5 Za su bada lissafi ga wanda yake a shirye ya shari'anta masu rai da matattu. 6 Shi yasa aka yi wa matattu wa'azin bishara, cewa ko da shike anyi masu shari'a cikin jikunan mutane, su rayu bisa ga Allah a ruhu. 7 Karshen dukkan abubuwa yana gabatowa. Saboda haka, ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku domin yin addu'oi. 8 Gaba da kome, ku himmatu wajen kaunar juna, domin kauna bata neman tona zunuban wadansu. 9 Ku yi wa juna bakunta da abubuwa nagari ba tare da gunaguni ba. 10 Yadda kowanne dayanku ya sami baiwa, kuyi amfani da su domin ku kyautata wa juna, kamar masu rikon amanar bayebaye na Allah, wanda ya ba mu hannu sake. 11 Idan wani yana yin wa'azi, ya zamana fadar Allah ya ke fadi, idan wani yana hidima, ya yi da karfin da Allah ya ba shi, domin cikin dukkan abubuwa a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Daukaka da iko nasa ne har abada abadin. Amin. 12 Ya kaunatattu, kada ku zaci cewa matsananciyar wahalar da ta zo ta gwada ku bakon abu ne, ko kuma wani bakon abu ne yake faruwa a gareku. 13 Amma muddin kuna tarayya da Almasihu cikin wahalarsa, ku yi murna, domin kuyi farin ciki da murna sa'adda za a bayyana daukakarsa. 14 Idan ana zargin ku sabili da sunan Almasihu, ku masu albarka ne, domin Ruhun daukaka da Ruhun Allah ya tabbata a kanku. 15 Amma kada kowannen ku ya sha wahala sabo da horon shi mai kisan kai ne, ko barawo, ko mamugunci, ko mai shisshigi. 16 Amma in wani yana shan wahala sabili da shi na Almasihu ne, kada ya ji kunya, amma ya daukaka Allah a wannan sunan. 17 Domin lokaci ya yi da shari'a za ta fara daga gidan iyalin Allah. Idan kuwa za a fara da mu, menene karshen wadanda suka ki biyayya da bisharar Allah? 18 Idan mutum, "mai adalci ya tsira da kyar, to, me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?" 19 Sabo da haka bari wadanda suke shan wuya bisa ga nufin Allah, su mika rayukansu ga amintaccen Mahalicci suna kuma yin ayyuka nagari.

5

1 Ina yiwa dattawan da ke cikinku gargadi, ni da nike dan'uwanku dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, ni kuma mai samun rabo ne daga cikin daukakar daza a bayyana. 2 Saboda haka na gargade ku dattawa, kuyi kiwon garken Allah dake tare da ku. Ku kula da su, ba a kan dole ba, amma domin kuna son yin haka, bisa ga yin Allah. Ku kula da su, ba don cin ribar banza ba amma sabo da yardar rai. 3 Kada ku zama kamar masu iko akan mutanen dake hannunku, amma ku zama abin koyi ga garken. 4 Sa'adda za a bayyana Sarkin Makiyaya zaku karbi rawanin da darajarsa bata dushewa. 5 Hakannan, ku kuma samari kuyi biyayya ga dattawa. Dukanku kuyi damara da tawali'u, kuna bauta wa juna, domin Allah ya na tsayayya da mai girman kai, amma yana yiwa masu tawali'u alheri. 6 Saboda haka ku kaskantar da kanku karkashin hannuwan Allah mai iko duka domin ya daukaka ku a madaidecin lokaci. 7 Ku jibga masa duk taraddadin zuciyarku, domin yana kula da ku. 8 Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku, ibilis, kamar zaki mai ruri yana zazzagawa, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayyiyar gaba da shi. Ku yi karfi cikin bangaskiyarku. Ku sani fa abokan tarayyarku da suke cikin duniya suna jimrewa da shan wuyan nan irin taku. 10 Bayan shan wuyarku na dan lokaci kadan, Allah mai alheri mara iyaka, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar daukakarsa cikin Almasihu, zai kammalaku, ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. 11 Mulki ya tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. 12 Na amince da Sila amintaccen dan'uwa ne, kuma na rubuto maku a takaice ta hannunsa. Ina yi maku gargadi ina kuma shaida maku cewa abin da na rubuto alherin Allah ne na hakika. Ku kafu a cikinsa. 13 Ita matar da ta ke a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, da Markus, dana, yana gaisheku. 14 Ku gai da juna da sumbar kauna. Salama ta tabbata a gare ku dukanku da ke cikin Almasihu.

Wasikar Bitrus Ta Biyu
Wasikar Bitrus Ta Biyu
1

1 Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu. 3 Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta. 4 Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace. 5 Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani. 6 Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah. 7 Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna. 8 Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba. 9 Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa. 10 Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba. 11 Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu. 12 Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu. 13 Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki. 14 Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani. 15 Zan yi iyakancin kokarina kulayomi domin ku rika tunawa da abubuwan, bayan kaurata. 16 Domin bamu bi labaru da aka kago na nuna wayo cikinsu ba, da muka fada maku game da iko da bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, amma mu shaidu ne na ikonsa. 17 Gama ya karbi daukaka da daraja daga wurin Allah Uba lokacin da murya ta zo daga ikon mai daukaka cewa, "Wannan shine dana, kaunataccena, wanda nake jin dadinsa kwarai." 18 Mun ji muryar nan da ta zo daga sama, lokacin da mu ke tare da shi a dutse mai tsarki. 19 Muna da wannan kalmar annabci wanda akwai tabbaci sosai, kun yi daidai idan kun mayar da hankali a kansu. Yana nan kamar fitillar da take walkiya a wuri mai duhu kafin asubahi ya zo, kuma tauraron asubahi ya tashi cikin zukatanku. 20 Ku san da wannan tun da farko, cewa babu annabci da ke bisa ga fasarar mutum. 21 Domin babu annabcin da ya taba zuwa ta wurin nufin mutum. Maimakon haka, Ruhu Mai Tsarki ne ke iza su, su fadi maganar Allah.

2

1 Annabawan karya sun zo ga mutane, hakannan kuma malaman karya suma sun zo. A asirce za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangiji da ya fanshe su. Su na jawowa kansu hallaka da sauri. 2 Da yawa za su bi gurbinsu, kuma ta wurinsu za a sabawa sahihiyar gaskiya. 3 Ta wurin hadama za su ribace ku ta wurin maganganunsu na yaudara. Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe. 4 Allah bai kebe mala'ikkun da suka yi zunubi ba. Maimakon haka ya tura su a cikin bakin duhun jahannama daure da sarkoki, har ya zuwa ranar shari'a. 5 Hakan nan kuma bai kebe duniya ta zamanin da ba. Maimakon haka, ya kebe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da mutane bakwai, lokacin da ya kawo ambaliyar ruwan Tsufana a fuskar duniyar marasa bin Allah. 6 Sa'annan Allah ya kone biranen Sadoma da Gomrata da wuta ya maishe su toka, wannan ya zama misalin abin da zai faru da marasa ibada. 7 Amma ga adalinnan Lutu, wanda ya zaku a ransa ta wurin miyagun halayen mutanen, Ubangiji kuwa ya cece shi. 8 Ga wannan mutum mai adalci, wanda yayi zama a cikinsu kowace rana ransa na baci, domin abin da yake gani yake kuma ji. 9 Saboda haka Allah ya san yadda zai ceci masu adalci daga gwaji, da yadda kuma zai kama masu rashin adalci da hukunci a ranar shari'a. 10 Wannan kuwa musamman gaskiya ce ga wadanda suka ci gaba da ayyuka na jiki suka kuma raina masu mulki. Suna da taurin kai da kuma yin ganin dama. Ba sa tsoron sabo ga wadanda aka daukaka. 11 Ko da shike mala'iku suna da karfi da iko fiye da su, amma basu kawo karar batanci a kansu a gaban Ubangiji ba. 12 Amma wadannan dabbobi marassa tunani an yi su ne musamman domin a kama a yanka. Suna sabawa abin da ba su sani ba. Zasu halaka. 13 Za su sami sakamakon mugun aikinsu. Suna tunanin yin nishadi da rana abin annashuwa ne. Su kan su tababbu ne. Suna jin dadin ayyukansu na yaudara yayin da suke liyafa tare da ku. 14 Suna da idanun sha'awace sha'awacen mata mazinata; ba sa koshi da aikata zunubi. Suna rinjayar wandanda ba su da tsayayyan hankali zuwa ga munanan ayyuka, kuma sun kafa zukatansu ga hadama, su 'ya'yan la'ana ne! 15 Sun bar bin hanyar gaskiya. Sun bijire kuma sun bi hanyar Bal'amu dan Be'or wanda yake kaunar ribar rashin adalci. 16 Amma ya karbi tsautawa domin zunubinsa. Jaki ma da baya magana ya tsauta wa haukan annabin da muryar dan adam. 17 Wadannan mutane suna kamar mabulbullai da babu ruwa. suna nan kamar gizagizai da iska ke korawa. Duhu mai tsanani yana jiransu. 18 Su masu babatu ne da girman kai. suna yadaurar mutane ta wurin sha'awowin jiki. Suna yaudarar mutane da suke kokarin su tsere daga wadanda suke rayuwa cikin kuskure. 19 Suna masu alkawarin yanci, amma su da kan su bayi ne ga zunubi. Domin mutum bawa ne ga duk abinda ya rinjaye shi. 20 Duk wanda ya kubuta daga shashanci na duniya ta wurin sanin Ubangiji da mai Ceto Yesu Almasihu, sa'annan ya koma cikin shashaci, yanayinsu na karshe ya zama da muni fiye da na farkon. 21 Da ma zai fi masu kada su san hanyar adalci da su san ta amma sa'annan su juya daga ka'ida mai tsarki wanda aka damka masu. 22 Wannan karin magana ya zama gaskiya a kan su: "Kare ya dawo yana lashe amansa. Aladen da akayi masa wanka ya koma cikin tabo."

3

1 Yanzu, ina rubata maku, kaunatattu, wannan wasika ta biyu domin in tunashe ku, in kuma zuga tunaninku na gaskiya, 2 don ku tuna da kalmomin da annabawa tsarkaka suka fada a da, kuma da umurnin Ubangijinmu da mai ceto da aka bayar ta wurin manzaninku. 3 Ku san wannan da farko, cewa masu ba'a za su zo a kwanakin karshe. Za su yi ba'a kuma su ci gaba bisa ga sha'awowinsu. 4 Za su ce, "Ina alkawarin dawowarsa? Tun lokacin da kakaninmu suka mutu, dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta." 5 Da gangan suka manta cewa sama da kasa sun kasance daga ruwa, kuma ta wurin ruwa, da dadewa ta wurin umarnin Allah, 6 kuma cewa ta wurin wadannan abubuwa duniyar wancan zamani ta halaka, da ambaliyar ruwan tsufana. 7 Amma sama da kasa na yanzu, an tanada su domin wuta ta wurin wannan umarnin. An tanada su domin ranar shari'a da halakar marassa ibada. 8 Kada ku manta da wanan, kaunatattu, cewa rana daya a gun Allah kamar shekaru dubu ne, kuma shekaru dubu kamar rana daya suke. 9 Ubangiji baya jinkiri game da alkawaransa kamar yadda wadansu ke ganin jinkiri. Maimakon haka, yana hakuri da ku. Ba ya so ko dayanku ya hallaka, amma kowanenku ya kai ga tuba. 10 Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar barawo. Sammai za su shude da kara mai karfi. Wuta zata kone komai da komai, kuma duniya da dukkan ayyukan da ke cikinta zasu bayyanu. 11 Da shike dukkan wadanan abubuwa za a hallaka su haka, wadanne irin mutane yakamata ku zama? Ya kamata kuyi rayuwar tsarki da ta ibada. 12 Ku zauna cikin bege da kuma hanzarta zuwan ranar Allah. A ranan nan, za a hallaka sammai da wuta, kuma dukkan komai da komai zai narke cikin zafi mai tsanani. 13 Amma bisa ga alkawarinsa, muna jiran sabuwar sama da sabuwar duniya, inda adalci zai kasance. 14 Saboda haka, kaunatattu, tun da kuna da begen wadannan abubuwa, ku yi iyakacin kokarinku a same ku marassa tabo da marasa aibu a gabansa, cikin salama. 15 Kuma, ku dauki hakurin Ubangiji domin ceto ne, kamar yadda kaunataccen danuwanmu Bulus ya rubuta maku bisa ga hikima da aka ba shi. 16 Bulus yayi magana akan wadanan abubuwa cikin dukkan wasikunsa, a ciki akwai abubuwa da suke da wuyar ganewa. Jahilai da mutane marassa natsuwa sukan juya ma'anarsu, kamar yadda suke yi wa sauran nassoshi, don hallakar kansu. 17 Saboda haka, kaunatattu, tun da kun san wadannan abubuwa, ku kula da kanku kada a badda ku ta wurin rudun mutanen da ba su bin doka, har ku rasa amincinku. 18 Amma ku yi girma a cikin alheri da sanin Ubangijinmu da mai ceto Yesu Almasihu. Bari daukaka ta tabbata a gare shi yanzu da har abada. Amin.

Wasikar Yahaya Ta Fari
Wasikar Yahaya Ta Fari
1

1 Abin nan da yake tun daga farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka gani hannuwanmu suka kama, a wajen maganar rai. 2 Ran kuwa aka baiyyana shi, muka gani, muka bada shaida, muka gaya maku labarin rai na har abada, wanda da yake a wurin Uba, aka kuma sanar da mu. 3 Wannan da muka gani muka ji muka baku labari, domin kuyi zumunci da mu, zumuncinmu kuwa tare da Uba yake da Dansa Yesu Almasihu. 4 Haka nan, muna rubuta maku wadannan abubuwa domin farin cikinmu ya cika. 5 Wannan shi ne sakon da muka ji daga wurinsa mu kuwa muka sanar da ku: Allah haske ne a wurinsa kuwa babu duhu ko kadan. 6 Idan mun ce muna zumunci da shi kuma muna tafiya cikin duhu, muna yin karya kuma bama aikata gaskiya. 7 Amma idan muna tafiya cikin haske kamar yadda yake cikin haske, muna zumunci da juna, jinin Yesu Dansa ya wankemu daga dukka zunubi. 8 Idan mun ce bamu da zunubi, muna rudin kanmu kenan, ba kuma gaskiya a cikinmu. 9 Amma idan mun fadi zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci da zai gafarta mana zunubanmu, ya kuma wankemu daga dukkan rashin adalci. 10 Idan mun ce bamu yi zunubi ba, mun mai da shi makaryaci kenan, maganarsa kuma bata cikinmu.

2

1 'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci. 2 Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka. 3 Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa. 4 Duk wanda yace, "Na san Allah" amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa. 6 Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi. 7 Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko. 8 Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa. 9 Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu. 10 kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa. 11 Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi. 12 Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa. 13 Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban. 14 Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun. 15 Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa. 16 Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne. 17 Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada. 18 Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce. 19 Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane. 20 Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya. 21 Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya. 22 Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan. 23 Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma. 24 A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban. 25 Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. 26 Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku. 27 Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa. 28 Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo. 29 Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.

3

1 Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu 'ya'yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba. 2 Kaunatattu, yanzu mu 'ya'yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa'adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake. 3 Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki. 4 Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari'a kenan. Gama zunubi ketare shari'a ne. 5 Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi. 6 Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi. 7 'Ya'yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali. 8 Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis. 9 Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah. 10 Ta haka ne ake bambanta 'ya'yan Allah da 'ya'yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan'uwansa. 11 Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu, 12 ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan'uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan'uwansa kuma masu adalci ne. 13 Kada kuyi mamaki 'yan'uwana, idan duniya ta ki ku. 14 Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne. 15 Dukkan wanda yake kin dan'uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai. 16 Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu. 17 Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan'uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa? 18 'Ya'yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya. 19 Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa. 20 Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome. 21 Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah. 22 Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi. 23 Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka. 24 Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.

4

1 Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya. 2 Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne, 3 kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya. 4 'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma. 5 Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu. 6 Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya. 7 Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah. 8 Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne. 9 A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10 A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu. 11 Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu. 12 Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu. 13 Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa. 14 Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya. 15 Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16 Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa. 17 Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan. 18 Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna. 19 Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu. 20 Idan wani ya ce,"Ina kaunar Allah", amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba. 21 Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.

5

1 Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa. 2 Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa. 3 Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane. 4 Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu. 5 Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne. 6 Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7 Domin akwai uku wadanda suke bada shaida: 8 Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce. 9 Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa. 10 Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba. 11 Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa. 12 Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai. 13 Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami--a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah. 14 Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu. 15 Haka kuma, in mun san yana jinmu--Duk abin da mu ka rokeshi--mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi. 16 Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17 Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba. 18 Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba. 19 Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan. 20 Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada. 21 'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.

2 Yahaya
2 Yahaya
1

1 Daga dattijon zuwa ga uwar gida zababbiya da yayanta, wadanda nake kauna da gaskiya, ba ni kadai ba, amma da dukan wadanda sun san gaskiya - 2 domin gaskiya da take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada. 3 Alheri da jinkai da salama za su kasance tare da mu, daga Allah Uba da kuma daga Yesu Almasihu Dan Uba, a cikin gaskiya da kauna. 4 Na yi murna sosai sa'anda na sami wadansu yayanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda muka karbi wannan umarni daga Uba. 5 Yanzu ina rokon ki, uwar gida, ba kamar ina rubuta maki sabon umarni ba, amma wannan da muka samu tun da can, cewa mu kaunaci junanmu. 6 Wannan kuma itace kauna, cewa mu yi tafiya bisa ga umarnin sa. Wannan shine umarnin, daidai kamar yadda kuka ji da fari, da cewa ku yi tafiya a cikinsa. 7 Gama masu yaudara sun fito a duniya, wadanda ba su yarda cewa Yesu ya zo cikin jiki ba. Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu. 8 Ku dubi kanku, domin kada ku rasa abubuwan da mu duka muka yi aiki a kansu, amma domin ku karba dukan sakamon ku. 9 Duk wanda ya ci gaba da tafiya ba cikin koyarwa Almasihu ba, ba shi da Allah. Wanda ya zauna cikin koyarwar kwa yana tare da Uban da kuma Dan. 10 Duk wanda ya zo wurinku, ba tare da wannan koyarwar ba, kar ku karbe shi cikin gidanku, kada ma ku gaishe shi. 11 Domin duk wanda ya gaishe shi ya yi tarayya da shi kenan cikin miyagun ayyukan sa. 12 Ina da abubuwa dayawa da nake so in rubuta maki amma al'kalami tawada da takarda baza su iya daukar su duka ba. Amma duk da haka ina begen zuwa gare ki domin mu yi magana fuska da fuska, domin farin cikn mu ya zama cikakke. 13 Yayan yar'uwarki zababbiya suna gaishe ki.

3 Yahaya
3 Yahaya
1

1 Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske. 2 Ya kaunatace na, ina addu'a domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya. 3 Na yi farin ciki kwarai sa'adda wadansu 'yan'uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya. 4 Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya. 5 Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baki, 6 wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada, 7 domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al'ummai. 8 Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya. 9 Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba. 10 Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya. 11 Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba. 12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce. 13 Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba. 14 Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa'annan mu yi magana ido da ido. 15 Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.

Yahuda
Yahuda
1

1 Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi: 2 bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku. 3 Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari. 4 Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu. 5 Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba. 6 Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. 7 Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. 8 Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka. 9 Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, "Bari Ubangiji ya tsauta maka!" 10 Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan. 11 Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora. 12 Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa. 13 Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. 14 Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, "Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai. 15 Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi." 16 Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu. 17 Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da. 18 Sun ce maku, "A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada," 19 Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu. 20 Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. 22 Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta. 23 Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma. 24 Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa, 25 zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin.

Wahayin Yahaya
Wahayin Yahaya
1

1 Wannan shine wahayin Yesu Almasihu da Allah ya bashi ya nuna wa bayinsa abinda zai faru ba da dadewa ba. Ya bayyana wannan ta wurin aiko da mala'ikansa ga bawansa Yahaya. 2 Yahaya yayi shaida akan abinda ya gani game da maganar Allah da kuma shaidar da aka bayar game da Yesu Almasihu. 3 Mai albarka ne wanda ke karanta littafin nan da murya mai karfi, da kuma wadanda ke sauraron kalmomin wannan annabci kuma suke biyayya da abinda aka rubuta a ciki, domin kuwa lokaci ya kusato. 4 Ni Yahaya, zuwa ga ikilisiyoyi bakwai na kasar Asiya: alheri zuwa gare ku da salama daga wanda ke yanzu, wanda ya kuma kasance a da, shi ne kuma mai zuwa nan gaba, kuma daga ruhohin nan bakwai da ke gaban kursiyinsa, 5 kuma daga Yesu Almasihu, wanda ke amintaccen mashaidi, dan fari na tashi daga cikin matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Ga wanda ya ke kaunar mu ya kuma kwance mu daga daurin zunubanmu ta wurin jininsa, 6 ya maishe mu masu mulki, firistoci na Allahnsa da Ubansa - daukaka da iko su tabbata gare shi har abada abadin, Amin. 7 Duba yana zuwa tare da gizagizai, kowane ido zai gan shi, har ma da wadanda suka soke shi. Haka kuma dukkan kabilun duniya za su yi makoki saboda da shi. I, Amin. 8 "Nine na farko da na karshe", in ji Ubangiji Allah, "Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka." 9 Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu. 10 Ina cikin Ruhu a ranar Ubangiji. Sai naji wata murya mai karfi a baya na kamar ta kaho. 11 Ta ce, "Rubuta abinda ka gani a cikin littafi, ka kuma aika wa ikilisiyoyin nan bakwai - ga Afisus, ga Simirna, ga Birgamas, ga Tayatira, ga Sardisu, ga Filadalfiya, da kuma ga Laudikiya." 12 Na juya don in ga wanda muryarsa ke magana da ni, da na juya sai na ga fitilu bakwai akan madorin su 13 A tsakiyar fitilun akwai wani mai kama da dan mutum, yana sanye da doguwar tufa har tafin sawunsa, da damara ta zinariya kewaye a kirjinsa. 14 Kansa da gashinsa fari fat kamar auduga - kamar dusar kankara, kuma idanun sa kamar harshen wuta. 15 Kafaffunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar tagullar da aka tace da wutar makera, muryar sa kuma kamar kugin ambaliyar ruwan teku ne. 16 A hannunsa na dama yana rike da taurari bakwai, daga bakinsa kuma kakkaifan takobi mai kaifi biyu ke fitowa. Fuskarsa tana haskakawa kamar sa'adda rana ke haskakawa kwarai. 17 Lokacin da na gan shi, na fadi kamar mataccen mutum a kafaffunsa. Ya dora hannunsa na dama a kaina ya ce, "Kada ka ji tsoro. Nine na farko da na karshe, 18 da kuma wanda ke raye. Na mutu, amma duba ina raye har abada! Kuma ina da mabudin mutuwa da na hades. 19 Domin haka ka rubuta abinda ka gani, abin da ke yanzu, da abin da zai faru bayan wanan. 20 Akan boyayyar ma'ana game da taurari bakwai da ka gani a hannun dama na, da madorin fitilu bakwai na zinariya: Taurarin nan bakwai mala'iku ne na ikilisiyoyi bakwai, kuma madorin fitilun nan bakwai ikilisiyoyi ne bakwai.

2

1 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Afisus, ka rubuta: 'Wadannan sune kalmomin wanda ke rike da taurari bakwai a cikin hannun damarsa. wanda yake tafiya a tsakanin zankayen fitilun zinari bakwai, 2 "Na san abubuwan da ka yi, da famar ka, da hakurinka da jimirinka. Na sani ba ka jimrewa miyagun mutane, na sani ka gwada wadanda suka ce da kansu, su manzanni ne, amma ba haka ba, ka tarar da su makaryata. 3 Na san kana da tsawon jimrewa, kuma ka sha wahala sosai sabili da sunana, kuma baka gaji ba. 4 Amma ga rashin jin dadi na da kai, ka bar kaunar ka ta fari. 5 Domin haka ka tuna daga inda ka fadi. Ka tuba ka yi abubuwan da ka yi da fari. Sai fa ka tuba, zan zo maka in kuma cire fitilar ka daga mazauninta. 6 Amma kana da wannan: Ka tsani abubuwan da Nikolatawa suka yi, wanda nima na tsana. 7 wanda yake da kunnen ji ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bashi dama ya ci daga itacen rai, wanda ke cikin firdausin Allah."" 8 Zuwa ga mala'ikan da ke Ikilisiliyar Samirna rubuta: 'Wadannan su ne kalmomin wanda yake shine farko shine karshe, wanda ya mutu ya sake rayuwa kuma. 9 "Na san wahalun ka da talaucin ka amma kana da arziki. Nasan masu bata suna wadanda suke cewa su Yahudawa ne, amma ba haka suke ba. Su majami'ar Shaidan ne. 10 Kada ka ji tsoron wahalar da zaka fuskanta nan gaba. Duba! Shaidan yana gab da jefa wadansun ku cikin kurkuku, domin a gwada ku, kuma zaku sha wahala ta kwana goma. Kuyi aminci har ga mutuwa zan baku rawanin rai. 11 wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Shi wanda yayi nasara ba zai cutu a mutuwa ta biyu ba."" 12 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Burgamas rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda ya ke da takobi mai kaifi biyu; 13 "Na san inda kake zama can inda kursiyin shaidan yake. Duk da haka ka rike sunana da karfi, na sani baka yi musun bangaskiyar ka da ni ba, ko a lokacin Antifas mashaidina, amintaccena, wanda aka kashe a tsakaninku, can inda shaidan yake zama. 14 Amma ga rashin jin dadi na kadan da kai: Kana da wadansu da suke rike da koyarwar Bil'amu kamkam, wanda ya koya wa Balak ya sa abin tuntubi gaban 'ya'yan Isra'ila, domin su ci abincin da aka mika wa gumaka kuma suyi fasikanci. 15 Hakannan kuma wasunku sun rike koyarwar Nikolatawa kamkam. 16 Sabili da haka ka tuba! Idan ka ki zan zo gare ka da sauri, kuma in yi yaki gaba da su da takobi dake cikin bakina. 17 Bari wanda yake da kunne ya sauriri abin da Ruhu yake fadawa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bada wata boyayyar manna, kuma zan bashi farin dutse da sabon suna a rubuce a kan dutsen, suna wanda ba wanda ya sani, sai shi wanda ya karbe shi."" 18 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Tiyatira rubuta: 'Wadannan sune kalamomin Dan Allah, wanda yake da idanu kamar harshen wuta; sawayen kamar gogaggiyar tagulla: 19 "Na san abin da ka yi, kaunar ka, da bangaskiya da hidima da tsawon jimrewar ka. Na san abinda ka yi bada dadewa ba ya fi abinda ka yi da fari. 20 Amma ga rashin jin dadi na da kai: Kana hakurce wa matar nan Yezebel, wadda take kiran kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta, ta rudi bayina suyi fasikanci kuma su ci abincin da aka mika wa gumaka sadaka. 21 Na bata lokaci domin ta tuba amma bata so ta tuba da fasikancin ta. 22 Duba! zan jefa ta a kan gadon jinya, wadanda kuma suka yi zina da ita za su shiga babbar wahala, sai dai in sun tuba daga ayukan ta. 23 Zan buga 'ya'yanta da mutuwa, kuma dukan ikilisiyoyi zasu san cewa nine wanda nake bincike tunani da zukata. Zan ba kowanen ku bisa ga ayyukansa. 24 Amma ga sauran ku dake cikin Tayatira, ga kowanen ku wanda bai rike wannan koyarwar ba, kuma bai san abinda wadansu suke kira zurfafan abubuwan Shaidan ba--ga ku na ce ban sa muku wata nawaya ba.' 25 Duk da haka dole ku tsaya da karfi har in zo. 26 Wanda yayi nasara da wanda ya yi abin da na yi har karshe, a gareshi zan bada iko akan al'ummai 27 Zai yi mulkin su da sandar karfe, zai farfasa su kamar randunan yumbu." 28 Kamar yadda na karba daga wurin Ubana, ni kuma zan bashi tauraron asubahi. 29 Bari wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fadawa ikilisiyioyi.""

3

1 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Sardisu rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda yake rike da ruhohi bakwai na Allah da taurari bakwai. "Na san abin da ka aikata. Ka yi suna cewa kana raye amma kai mattacce ne. 2 Ka farka ka karfafa abin da ya rage amma ya kusan mutuwa, domin ban sami ayyukanka cikakku a gaban Allahna ba. 3 Domin haka sai ka tuna, da abubuwan da ka karba kuma kaji. Ka yi biyayya da su, ka kuma tuba. Amma idan baka farka ba, zan zo maka kamar barawo, kuma ba zaka farga da sa'ar da zan zo gaba da kai ba. 4 Amma akwai sunayen mutane kadan a Sardisu wadanda basu kazantar da tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni sanye da fararen tufafi domin sun cancanta. 5 Wanda ya yi nasara za a sanya mashi fararen tufafi, kuma ba zan taba share sunansa ba daga Littafin Rai, kuma zan fadi sunansa a gaban Ubana, da kuma gaban mala'ikunsa. 6 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu ke fadawa ikilisiyoyi."'" 7 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar cikin Filadelfiya rubuta: kalmomin wanda yake maitsarki ne kuma mai gaskiya - yana rike da mabudin Dauda, yana budewa babu mai rufewa, kuma inda ya rufe ba mai budewa. 8 Na san abin da ka aikata. Duba, na sa budaddiyar kofa a gabanka wanda ba mai iya rufewa. Na san kana da karamin karfi, duk da haka ka yi biyayya da maganata kuma baka yi musun sunana ba. 9 Duba! Wadanda ke na majami'ar Shaidan, wadanda suke cewa su Yahudawa ne; amma maimakon haka karya suke yi. Zan sa su zo su rusuna a kafafunka, kuma za su san cewa ina kaunarka. 10 Tun da ka jure cikin hakuri ka kiyaye dokoki na, ni ma zan kiyaye ka daga sa'a ta gwaji da zata sauko kan dukan duniya, domin a gwada mazauna duniya. 11 Ina zuwa da sauri. Ka rike abin da kake da shi kamkam domin kada wani ya dauke maka rawani. 12 Zan sa wanda ya yi nasara ya zama ginshiki a haikalin Allahna, kuma ba zai taba fita daga cikin sa ba. Zan rubuta sunan Allahna a kansa, sunan birnin Allahna (sabuwar Urushalima, mai saukowa daga sama daga wurin Allahna), da kuma sabon sunana. 13 Bari wanda yake da kunne ya ji abin da Ruhu ke gayawa ikilisiyoyi." 14 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar da ke Lawudikiya rubuta: 'Wadannan sune kalmomin Amin, madogara da mai shaidar gaskiya, mai mulki bisa hallittar Allah. 15 Na san abin da ka aikata, ba ka sanyi ko zafi. Naso ko da kana sanyi ko zafi! 16 Amma saboda kai tsaka-tsaka ne - ba zafi ba sanyi - na kusa tofar da kai daga bakina. 17 Domin ka ce, "Ni mai arziki ne, na mallaki kadarori da yawa, ba na bukatar komai." Amma ba ka sani ba kana cike da takaici ne, abin tausayi, matalauci, makaho kuma tsirara kake. 18 Saurari shawara ta: Ka sayi zinariya a wuri na wadda aka goge da wuta domin ka zama mai arziki, domin ka suturta kanka da fararen tufafi masu kyalli domin kada ka nuna kunyar tsiraicin ka, da mai domin ka shafa wa idanunka ka sami gani. 19 Ina horar da duk wanda nake kauna, ina kuma koya masu yadda za su yi rayuwa. Saboda haka, ka himmatu ka tuba. 20 Duba, ina tsaye a bakin kofa ina kwankwasawa. Idan wani ya ji muryata ya bude kofar, zan shigo cikin gidansa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni. 21 Wanda ya ci nasara, zan bashi dama ya zauna tare da ni bisa kursiyina, kamar yadda nima na ci nasara kuma na zauna da Ubana a kan kursiyinsa. 22 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu yake fadawa wa ikilisiyoyi."

4

1 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura." 2 Nan da nan ina cikin Ruhu, sai na ga wani kursiyin da aka ajiye shi a sama, da wani zaune bisansa. 3 Shi da ke zaune a kan tana da kamanin yasfa da yakutu. Akwai Bakangizo kewaye da kursiyin kamanin bakangizon kuwa zumurudu. 4 A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da hudu, masu zama bisa kursiyoyin nan kuwa dattawa ne ashirin da hudu, sanye da fararen tufafi, da kambunan zinariya bisa kawunansu. 5 Daga kursiyin walkiya na ta fitowa, cida, da karar aradu. Fitilu bakwai na ci a gaban kursiyin, fitilun sune ruhohin Allah guda bakwai. 6 Gaban kursiyin akwai tekun gilashi, mai haske kamar karau. A tsakiyar kursiyin da kewayen kursiyin akwai rayayyun hallitu guda hudu cike da idanu gaba da baya. 7 Rayayyen hallitta na farko na da kamanin zaki, rayayyen hallitta na biyun kamanin dan maraki ne, rayayyen hailitta na uku fuskar sa kamar dan adam, kuma rayayyen hallitta ta hudu na da kamanin gaggafa mai tashi. 8 Dukan rayayyun hallittan nan hudu na da fukafukai shida shida, cike da idanu a bisa da karkashin fukafukan. Dare da rana ba sa daina cewa, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne Ubangiji Allah, mai iko duka, shine da shine yanzu shine mai zuwa." 9 A dukan lokacin da rayayyun hallittun nan suke ba da girma, daukaka, da godiya ga shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abadin, 10 sai dattawan nan ashirin da hudu suka fadi da fuskokinsu a kasa gaban shi da ke zaune bisa kursiyin. Suka yi sujada ga shi da ke rayuwa har abada abadin, suna jefar da kambinsu a gaban kursiyin, suna cewa, 11 "Ka cancanta, ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka karbi yabo da daukaka da iko. Domin kai ka hallicci dukan komai, da kuma nufinka ne, suka kasance aka kuma hallicce su.

5

1 Sa'annan na ga a cikin hannun daman wanda ke zaune a kan kursiyin, na ga littafi wanda ke da rubutu ciki da waje, an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. 2 Na kuma ga wani kakkarfan mala'ika na shela da murya mai karfi, "Wa ya isa ya bude littafin ya kuma bambare hatimin?" 3 Ba wani a sama ko a kasa ko karkashin kasa da ya iya ya bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 4 Na yi kuka mai zafi saboda ba wani da ya cancanta da zai bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 5 Amma daya daga cikin dattawan nan ya ce mani, "Kada ka yi kuka. Duba! Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda, ya yi nasara. Ya cancanci bude littafin da kuma hatimansa bakwai." 6 Na ga Dan Rago yana tsaye tsakanin kursiyin da rayayyun halittun nan guda hudu a cikin dattawa. Yana kama da wanda aka kashe. Yana da kafonni bakwai da idanuwa bakwai; wadannan sune ruhohin Allah bakwai da aka aiko zuwa dukan duniya. 7 Ya tafi ya karbi littafin daga hannun daman wanda ke zaune bisa kursiyin. 8 Lokacin da Dan Ragon ya dauki littafin, rayayyun halittun nan hudu da dattawan nan ashirin da hudu suka fadi har kasa a gaban Dan ragon. Kowannen su na dauke da molo da tasar zinariya cike da kayan kamshi, wadanda kuwa sune addu'o'in masu ba da gaskiya. 9 Suka raira sabuwar waka: "Ka cancanta ka dauki littafinka kuma bude hatimansa. Domin an yanka ka, da jininka ka saya wa Allah mutane daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma. 10 Ka maishe su mulki da firistoci su bauta wa Allanmu, kuma za su yi mulki a duniya." 11 Da na duba sai na ji karar mala'iku masu yawa kewaye da kursiyin da rayayyun halitu da kuma dattawa. Jimillarsu ya kai dubbai goma, sau dubbai goma, da dubun dubbai. 12 Suka tada murya da karfi suka ce, "Macancanci ne Dan Ragon da aka yanka ya karbi iko, wadata, hikima, karfi, girma, daukaka da yabo." 13 Na ji kowanne halittaccen abu da ke cikin sama da kasa da karkashin kasa da cikin teku - dukan abubuwan da ke cikinsu - na cewa, "Ga shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Dan Ragon, yabo, girma, daraja, da kuma ikon yin mulki, har abada abadin. 14 Sai rayayyun halittun nan hudu suka ce, "Amin!" dattawan nan kuma suka fadi da fuskokinsu suka yi sujada.

6

1 Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, "Zo!" 2 Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara. 3 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, "Zo!" 4 Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi. 5 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, "Zo!" Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa. 6 Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, "Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi." 7 Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, "Zo!" 8 Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya. 9 Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike. 10 Suka yi kuka da babban murya, "Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu? 11 Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su. 12 Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini. 13 Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada. 14 Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa. 15 Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka. 16 Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, "Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon. 17 Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?"

7

1 Bayan wannan sai na ga mala'iku hudu suna tsaye bisa kusurwoyi hudu na duniya, suka rike iskoki hudu na duniya kamkam domin kada iska ta hura a kan duniya, a kan teku, ko wani itace. 2 Sai na ga wani mala'ika na zuwa daga gabas, wanda yake da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya da mala'ikun nan hudu da aka basu dama su azabtar da duniya da teku: 3 "Kada ku azabtar da duniya, da teku, da itatuwa har sai mun sa hatimi bisa goshin bayin Allahnmu." 4 Sai naji yawan wadanda aka hatimce: 144, 000, wadanda aka hatimce daga kowacce kabilar mutanen Isra'ila: 5 dubu goma sha biyu aka hatimce daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad, 6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa. 7 Dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka, 8 dubu goma sha biyu daga kabilar zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, sai kuma dubu goma sha biyu daga kabilar Bilyaminu aka hatimce. 9 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga wani babban taro wanda ba mai iya kirgawa daga kowacce al'umma, kabila, mutane da harsuna tsaye a gaban kursiyin da gaban Dan Ragon. Suna sanye da fararen tufafi da ganyen dabino a hannuwansu, 10 kuma suna kira da murya mai karfi: "Ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune bisa kursiyi, da kuma Dan Ragon!" 11 Dukan mala'iku suna tsaitsaye kewaye da kursiyin kuma kewaye da dattawan nan da kuma rayayyun halittun nan hudu, suka kwanta rib da ciki da fuskokinsu a gaban kursiyin. Suka yi sujada ga Allah, 12 suna cewa, "Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!" 13 Sai daya daga cikin dattawan ya tambaye ni, "Su wanene wadannan, da suke sanye da fararen tufafi, kuma daga ina suka fito?" 14 Sai nace masa, "Ya shugaba, "Ka sani," sai ya ce mani, "Wadannan sune suka fito daga babban tsanani. Sun wanke tufafin su sun maida su farare cikin jinin Dan Ragon. 15 Domin wannan dalili, suke gaban kursiyin Allah, kuma suna masa sujada dare da rana cikin haikalinsa. Shi wanda ke zaune bisa kursiyin zai zama runfa a bisan su. 16 Ba za su kara jin yunwa ba, ko kishin ruwa ba. Rana ba zata buge su ba, ko kowanne zafi mai kuna. 17 Domin Dan Ragon dake tsakiyar kursiyin zai zama makiyayin su, kuma zai bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai, kuma Allah zai share dukan hawaye daga idanuwansu."

8

1 Lokacin da Dan Ragon nan ya bude hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kimanin rabin sa'a. 2 Sa'anan na ga mala'iku bakwai wadanda ke tsaye a gaban Allah, aka kuma basu kahonni bakwai 3 Wani mala'ika ya zo, rike da tasar turaren konawa na zinariya, a tsaye gaban bagadi. Turaren konawa mai yawa aka bashi saboda ya mika su tare da adu'o'in dukan masu bada gaskiya akan bagadin kona turare na zinariya a gaban kursiyin. 4 Hayakin turaren konawa, da adu'o'in masu bada gaskiya, suka tashi sama a gaban Allah daga hanun mala'ikar. 5 Mala'ikan ya dauki tasar turaren konawa ya cika ta da wuta daga bagadin. Sa'annan ya wurgo ta kasa zuwa duniya, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa. 6 Mala'ikun nan bakwai wadanda suke da kahonni bakwai suka yi shirin busa su. 7 Mala'ika na fari ya hura kahonsa, sai ga kankara da wuta a garwaye da jini. Aka jeho shi kasa zuwa duniya sai kashi daya cikin uku na duniya ya kone, daya cikin uku na itatuwa suka kone, da duk danyar ciyawa suka kone kaf. 8 Mala'ika na biyu ya busa kahonsa, sai wani abu mai kama da babban dutse mai cin wuta aka jefo shi cikin teku. Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini, 9 daya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka. 10 Mala'ika na uku ya busa kahonsa, sai gagarumin tauraro ya fado daga sama, yana ci kamar cocila, bisa kashi daya cikin uku na koguna da mabulbulan ruwa. 11 Sunan tauraron Daci. Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu domin ruwayen sun yi daci. 12 Mala'ika na hudu ya busa kahonsa, sai daya cikin kashi uku na rana ya harbu, da daya cikin kashi uku na wata da kuma daya cikin kashi uku na taurari. Sai daya cikin kashi uku nasu duka suka duhunce; daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su. 13 Da na duba sai na ji gaggafa da take shawagi a tsakiyar sararin sama tana kira da babban murya, "Kaito, kaito, kaito, ga mazaunan duniya sabili da sauran karar kahonni na mala'ikun nan uku da za su busa."

9

1 Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka. 2 Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin. 3 Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya. 4 Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu. 5 Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum. 6 A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su. 7 Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam. 8 Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki. 9 Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki. 10 Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar. 11 Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon. 12 Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa. 13 Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah. 14 Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, "Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis," 15 Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam. 16 Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su. 17 Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito. 18 Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu. 19 Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni. 20 Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya. 21 Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.

10

1 Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta. 2 Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa. 3 Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su. 4 Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, "Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi." 5 Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama. 6 Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, "Babu sauran jinkiri. 7 Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa." 8 Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: "Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa." 9 Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, "Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma." 10 Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci. 11 Wani yace mani, "Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna."

11

1 Aka bani sanda in yi amfani da ita kamar sandar awo. Aka ce mani, "Tashi ka auna haikalin Allah da bagadi, da wadanda ke sujada a cikinsa. 2 Amma kada ka auna harabar haikalin, domin an ba da shi ga Al'ummai. Za su tattake birnin mai tsarki har wata arba'in da biyu. 3 Zan ba shaidu na biyu iko su yi anabci na kwanaki dubu daya da dari biyu da sittin, sanye da tsummoki. 4 Wadannan shaidu sune itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5 Idan wani ya yi niyyar cutar da su, wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu. Duk mai son cutar da su, dole a kashe shi ta wannan hanya. 6 Wadannan shaidu suna da iko su kulle sama domin kada a yi ruwa a lokacin da suke anabci. Suna da iko su juya ruwaye su zama jini, su kuma bugi duniya da kowacce irin annoba duk lokacin da suka ga dama. 7 Sa'adda suka gama shaidarsu, dabban da ke fitowa daga rami marar iyaka zai yi yaki da su. Zai ci nasara da su ya kashe su. 8 Gawawwakinsu zasu kwanta kan hanyar babban birnin nan (wanda ma'anar sa ake kira Saduma da Masar) inda aka gicciye Ubangijinsu. 9 Wajen kwana uku da rabi wadansu daga dukan mutane, da kabila, da harshe, da al'umma za su yi kallon gawawwakinsu. Za su ki yarda a sa su cikin kabari. 10 Mazaunan duniya zasu yi murna da biki a kansu. Har za su aika wa juna kyautai saboda annabawan nan biyu da suka azabtar da mazaunan duniya. 11 Amma bayan kwana uku da rabi, numfanshin rai daga wurin Allah zai shiga cikinsu sa'annan za su tsaya a kan kafafunsu. Matsanancin tsoro zata fado kan wadanda za su gansu. 12 Sa'annan zasu ji murya mai kara daga sama tana ce masu, "Ku hauro nan!" Sa'annan za su tafi sama cikin gajimarai, makiyansu suna kallo. 13 A waccan sa'a za a yi babbar girgizar kasa, sai kashi daya cikin goma na garin ya fadi. Mutane dubu bakwai za su mutu a girgizar kasar, wadanda suka tsira kuwa za su tsorata su ba da daukaka ga Allah na sama. 14 Annoba ta biyu ta wuce. Duba! Annoba ta uku tana zuwa nan da nan. 15 Sa'annan mala'ika na bakwai ya busa kahonsa, sai muryoyi masu kara suka yi magana cikin sama cewa, "Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa. Zai yi mulki har abada abadin." 16 Sa'annan dattawan nan ashirin da hudu da ke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fadi fuskokinsu na kasa. Suka yi wa Allah sujada. 17 Suka ce, "Mun yi maka godiya, Ubangiji Allah, Madaukaki, wanda yake yanzu da wanda yake a da, saboda ka dauki ikonka mai girma ka fara mulki. 18 Al'ummai suka fusata, amma hasalar ka ta zo. Lokaci ya zo da za a yi wa mattatu sharia, da zaka ba da sakamako ga bayinka annabawa, da masu ba da gaskiya, da wadanda suka ji tsoron sunanka, karami da babba. Lokaci kuma ya yi da za ka hallaka wadanda ke hallakar da duniya." 19 Sa'annan aka bude haikalin Allah da ke sama, sai aka ga akwatin alkawarinsa a cikin haikalinsa. Sai ga hasken walkiya, da rugugi, da aradu, da girgizar kasa, da manyan duwatsun kankara.

12

1 Aka ga wata babbar alama a sama: wata mace ta yi lullubi da rana, kuma wata na karkashin kafafunta; rawanin taurari goma sha biyu na bisa kanta. 2 Tana da ciki, tana kuma kuka don zafin nakuda - a cikin azabar haihuwa. 3 Sai aka ga wata alama cikin sama: Duba! Akwai wani katon jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, sai kuma ga kambi guda bakwai bisa kawunansa. 4 Wutsiyarsa ta share daya bisa uku na taurari a sama ta zubo su kasa. Diragon nan ya tsaya a gaban matar da ta kusan haihuwa, domin lokacin da ta haihu ya lankwame yaronta. 5 Sai ta haifi da, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al'ummai da sandar karfe. Aka fizge yaron ta zuwa ga Allah da kursiyinsa, 6 matar kuwa ta gudu zuwa jeji inda Allah ya shirya mata domin a iya lura da ita kwanaki 1, 260. 7 A lokacin sai yaki ya tashi a sama. Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da diragon, sai diragon da nasa mala'iku suka yake su su ma. 8 Amma diragon ba shi da isashen karfin da zai ci nasara. Don haka, shi da mala'ikunsa ba su kara samun wuri a sama ba. 9 Sai aka jefa katon diragon nan tare da mala'ikunsa kasa, wato tsohon macijin nan da ake kira Iblis ko Shaidan wanda ke yaudarar dukan duniya. 10 Sai na ji wata murya mai kara a sama: "Yanzu ceto ya zo, karfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa. Gama an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a kasa - shi da yake sarar su a gaban Allah dare da rana. 11 Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa. 12 Don haka, yi farinciki, ya ku sammai da duk mazauna da ke cikinsu. Amma kaito ga duniya da teku saboda iblis ya sauko gare ku. Yana cike da mummunan fushi, domin ya san lokacin sa ya rage kadan. 13 Da diragon ya ga an jefar da shi kasa, sai ya fafari matar nan da ta haifi da namiji. 14 Amma aka ba matar nan fukafukai biyu na babbar gaggafa domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a jeji. A wannan wuri ne za a lura da ita na dan lokaci, da lokatai, da rabin lokaci - a lokacin da babu macijin. 15 Macijin ya kwararo ruwa daga bakin sa kamar kogi, don ya kawo ambaliyar da zai kwashe ta. 16 Amma kasa ta taimaki matar. Kasa ta bude bakinta ta hadiye kogin da diragon ya kwararo daga bakinsa. 17 Sai diragon ya fusata da matar, sai ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu. 18 Sai diragon ya tsaya a kan yashi, a gaban teku.

13

1 Sai na ga wani dabba yana fitowa daga teku. Yana da kahonni goma da kawuna bakwai. A kan kahonninsa akwai kambi goma, a kan kowanne kansa akwai suna na sabo. 2 Wannan dabban da na gani yana kama da damisa, kafafunsa kuma kamar na beyar, bakinsa kuma kamar na zaki. Wannan diragon ya ba shi karfinsa, da kursiyinsa da ikonsa mai girma na sarauta. 3 Daya daga cikin kawunan dabban ya yi kamar an kashe shi, amma rauninsa mai tsanani ya warke. Sai dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban. 4 Su ma suka yi wa diragon sujada, domin ya ba dabban ikonsa. Suka yi wa dabban sujada suna ta cewa, "Wanene kamar dabban? Wa kuma zai iya yin fada da shi?" 5 Aka ba dabban baki da zai iya fadin kalmomin fahariya da sabo. Ya sami izini na zartar da iko har wata arba'in da biyu. 6 Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama. 7 Aka yarje wa dabbar ya yi yaki da masu bi ya kuma yi nasara da su. An kuma ba shi iko bisa kowacce kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma. 8 Dukan wadanda ke zaune a duniya za su yi masa sujada, dukan wadanda tun hallitar duniya ba a rubuta sunayensu a littafin rai na Dan Rago ba, wanda aka yanka. 9 Idan wani yana da kunne, bari ya ji. Duk wanda za a dauke shi zuwa bauta, ga bauta zai tafi. 10 Duk wanda za a kashe da takobi, da takobi za a kashe shi. Wannan kira ne na dauriya, hakuri da bangaskiya ga wadanda suke da tsarki. 11 Sai na ga wani dabban na fitowa daga cikin kasa. Yana da kahonni biyu kamar na dan rago, ya kuma yi magana kamar maciji. 12 Ya zartar da dukan ikon dabban na farko a gabansa, ya kuma sa duniya da duk mazaunanta su yi wa dabban nan na farko sujada, wanda aka warkar masa da rauni mai kamar na ajali. 13 Ya yi manyan al'ajibai. Har ya sa wuta ta sauko kasa daga sama a gaban mutane. 14 Ta wurin alamu da aka yarje masa ya yi, ya yaudari mazaunan duniya. Ya ce masu su yi wata siffa don girmama dabban da yake da raunin takobi, amma duk da haka ya rayu. 15 Aka yarje masa ya ba da numfashi ga siffar dabban domin siffar ta yi magana, ta kuma sa a kashe duk wadanda suka ki yin sujada ga dabban. 16 Ya kuma tilasta kowa, kanana da manya, mawadata da matalauta, masu yanci da bayi, su karbi alama a hannun dama ko kuma a goshi. 17 Ba shi yiwuwa wani ya saya ko ya sayar sai dai yana da alamar dabban, wato lambar nan da ke wakiltar sunansa. 18 Wannan na bukatar hikima. Idan wani yana da hikima, sai ya kididdige lambar dabban nan. Gama lambar ta mutum ce. Lambarta itace 666.

14

1 Sai na duba na ga Dan Ragon yana tsaye a kan Dutsen Sihiyona. Tare da shi akwai mutum dubu dari da arba'in da hudu wadanda aka rubuta sunansa da sunan Ubansa a goshinsu. 2 Na ji wata murya daga sama mai kara kamar kogin ruwa mai gudu da kuma aradu mai kara. Muryar da na ji ta yi kama da masu molo suna kada molonsu. 3 Suka raira sabuwar waka a gaban kursiyin da kuma gaban rayayyun halittun nan hudu, da kuma dattawan. Ba mai iya koyon wakar nan sai dai mutum 144, 000 nan wadanda aka fanso daga duniya. 4 Wadannan sune wadanda basu kazantar da kansu da mata ba, gama sun kebe kansu da tsarki daga halin jima'i. Wadannan ne ke bin Dan Ragon duk inda ya tafi. Aka fanso su daga cikin mutane domin su zama nunan fari domin Allah da Dan Ragon. 5 Ba a iske karya a bakinsu ba; ba su da aibi. 6 Na ga wani mala'ika na firiya a tsakiyar sararin sama, wanda yake da madawwamin sako na labari mai dadi domin a sanar da ita ga mazaunan duniya - ga kowacce al'umma, da kabila, da harshe, da kuma jama'a. 7 Yayi kira da babbar murya, "Ku ji tsoron Allah, ku daukaka shi. Gama sa'arsa ta hukunci ta yi. Yi masa sujada, shi wanda ya yi sama da kasa, da teku, da kuma mabulbular ruwa." 8 Sai wani malai'ka, malaika na biyu, ya biyo yana cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi, wadda ta rinjayi dukan al'ummai su sha ruwan inabin fasikancinta." 9 Wani mala'ika - na uku - ya biyo su da murya mai karfi yana cewa, "Duk wanda ya yi sujada ga dabban da kuma siffarsa, ya karbi alama a goshinsa ko a hannunsa, 10 shi ma zai sha daga ruwan inabin fushin Allah, ruwan inabi da aka zuba tsantsa cikin kokon fushinsa. Wanda ya sha shi za a azabtar da shi da wuta, da farar wuta, a gaban tsarkakan mala'ikun Allah da kuma Dan Ragon. 11 Hayaki daga azabarsu yana tashi sama har abada abadin, kuma ba su da hutu dare ko rana - wadannan masu sujada ga dabban da siffarsa da kuma dukan wadanda suka karbi alamar sunansa. 12 Wannan shine kira domin hakurin jimrewa na wadanda ke da tsarki, wadanda suke biyayya ga dokokin Allah da bangaskiya cikin Yesu." 13 Na ji murya daga sama cewa, "Rubuta wannan: Masu albarka ne matattu da suka mutu cikin Ubangiji." Ruhu yace, 'I' domin sun huta daga wahalarsu, gama ayyukansu na biye da su." 14 Na duba sai ga farin gajimare. Zaune a kan gajimaren akwai wani kamar Dan Mutum. Yana da kambin zinariya a kansa da lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani malaika ya fito daga haikalin, ya yi kira da murya mai karfi ga wanda ke zaune kan gajimare: "Dauki laujenka ka fara girbi, domin lokacin girbin duniya ya yi." 16 Sai wanda ke zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa bisa kan duniya, aka kuma girbe duniya. 17 Wani mala'ika ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da kakkaifan lauje. 18 Sai wani mala'ika ya fito daga bagadin kona turare, wanda yake da iko kan wutar. Ya yi kira da murya mai karfi ga wanda yake rike da kakkaifan lauje, "Ka dauki kakkaifan laujenka ka tattara nonnan innabi daga itacen inabin na duniya, gama inabin ya nuna." 19 Mala'ikan ya jefa laujensa duniya ya tattara girbin inabin duniya. Ya zuba shi a cikin babbar taskar wurin matsar ruwan inabi na fushin Allah. 20 Aka tattake wurin matsar inabin a bayan birni, jini ya yi ta gudu daga wurin matsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil dari biyu.

15

1 Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala'iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika. 2 Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su. 3 Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: "Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al'ummai. 4 Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al'ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci." 5 Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama. 6 Daga wuri mafi tsarki mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu. 7 Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala'iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin. 8 Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala'ikun nan bakwai suka cika.

16

1 Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai'iku bakwai, "Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya." 2 Mala'ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa. 3 Mala'ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.' 4 Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini. 5 Na ji mala'ikan ruwaye ya ce, "Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari'anta wadannan abubuwa. 6 Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su. 7 Na ji bagadi ya amsa, "I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari'un ka gaskiya ne da adalci." 8 Mala'ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama'a da wuta. 9 Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi. 10 Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi. 11 Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi. 12 Mala'ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas. 13 Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi. 14 Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka. 15 ("Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.") 16 Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci. 17 Mala'ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa'annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, "An gama!" 18 Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da 'yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke. 19 Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al'ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani. 20 Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba. 21 Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.

17

1 Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, "Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa. 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu." 3 Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma. 4 Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa. 5 Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: "Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya." 6 Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske. 7 Amma mala'ikan ya ce mani, "Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma. 8 Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa. 9 Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai. 10 Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan. 11 Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka. 12 Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban. 13 Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban. 14 Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun." 15 Mala'ikan ya ce mani, "Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna. 16 Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta. 17 Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika. 18 Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya."

18

1 Bayan wadannan abubuwa sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga sama. Yana da babban iko sosai, duniya kuwa ta haskaka da daukakarsa. 2 Ya yi kira da kakkarfar murya cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi! Ta zama mazaunin aljannu, da matattarar kowanne kazamin ruhu da kuma mazaunin kowanne kazami da kyamataccen tsuntsu. 3 Gama dukan al'ummai sun sha ruwan innabin fasikancinta. Sarakunan duniya sun aikata fasikanci da ita. Attajiran duniya sun arzuta da ikon rayuwar annashuwarta." 4 Sai na ji wata murya daga sama ta ce, "Ku fito daga cikinta, mutanena, domin kada kuyi zunubi irin na ta, domin kuma kada bala'inta ya auko maku. 5 Zunubanta sun taru sun yi tsayi har sama. Allah kuma ya tuna da miyagun ayyukanta. 6 Ku saka mata gwargwadon yadda ta saka wa wadansu, ku biya ta ninki biyu na abin da ta yi; a cikin kokon da ta dama, ku dama mata ninki biyu. 7 Kamar yadda ta daukaka kanta ta yi ta annashuwa, ku wahalsheta da azaba da bakin ciki haka. Domin ta ce a zuciyarta, 'Ina zaune kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taba yin makoki ba,' 8 Saboda haka a rana daya bala'inta zai auko mata; mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta za ta kona ta kurmus, domin Ubangiji Allah mai iko ne, kuma shine mai hukuntata." 9 Sarakunan duniya da suka yi fasikanci, har suka baude tare da ita, za su yi kuka da kururuwa domin ta sa'adda suka ga hayakin kunarta. 10 Za su tsaya can nesa suna tsoron azabarta, suna cewa, "Kaito, kaiton babban birni, Babila, birni mai iko! Domin cikin sa'a guda hukuncinta ya zo." 11 Manyan 'yan kasuwan duniya za su yi kuka da bakin ciki dominta, da shike ba wanda ke sayan kayanta kuma - 12 kayan zinariya, azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'u-lu'u, da lilin mai laushi, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jar alharini da itacen kamshi iri iri, da kayan da aka sassaka da itace mai tsada, da na tagulla, da na bakin karfe, da na dutse mai sheki, 13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur da lubban, da ruwan innabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawakai, da kekunan doki, da bayi, da rayukan 'yan adam. 14 Amfanin da kika kwallafa rai da duk karfinki sun fice daga gareki. Duk annashuwarki da darajarki sun bace, ba za a kara samunsu ba kuma. 15 Manyan 'yan kasuwa na wadannan kaya da suka azurta ta wurinta, za su tsaya can nesa da ita, sabili da tsoron azabarta, kuka da kururuwar bakin ciki. 16 Za su ce, "Kaito, kaito ga babban birni da take sanye da lilin mai laushi da tufafi masu jar garura da kuma jan alharini, da ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsu masu daraja da lu'u-lu'u! 17 A cikin sa'a guda duk dukiyan nan ta lallace. Kowanne matukin jirgin ruwa, da fasinjoji, da masu tuki da duk wadanda suke samun biyan bukatun rayuwarsu daga ruwa, suka tsaya can nesa. 18 Suka yi kuka sa'anda suka ga hayakin kunarta. Suka ce, "Wanne birni ne ya yi kama da babban birnin?" 19 Suka watsa kura a kawunansu, suka yi kuka da karfi, da kururuwa da bakin ciki, "Kaito, kaiton babban birnin nan inda duk masu jiragen ruwa suka azurta daga dukiyarta. Domin a sa'a guda an hallakar da ita." 20 "Ku yi murna a kanta, sama, ku masu ba da gaskiya, manzanni, da annabawa, domin Allah ya kawo hukuncinku a kanta!" 21 Wani kakkarfan mala'ika ya dauki wani dutse mai kama da dutsen nika, ya jefa shi cikin teku yana cewa, "Ta wannan hanya, Babila, babban birnin, za a jefar da ita kasa da karfi, ba za a kara ganinsa ba. 22 Muryar masu kidar molaye, mawaka, masu busa sarewa, da na masu busa algaita, ba za a kara ji a cikinta ba. Babu wani mai kowanne irin sana'a da za a samu a cikinta. Ba za a kara jin karar nika a cikinta ba. 23 Hasken fitila ba za ya kara haskakawa a cikin ki ba. Ba za a kara jin muryoyin ango da na amarya a cikinki ba, domin attajiranki sune 'ya'yan masu mulki a duniya, kuma ta wurin sihirinki kika yaudari al'ummai. 24 A cikinta aka sami jinin annabawa da na masu ba da gaskiya, da jinin duk wadanda aka kashe a duniya."

19

1 Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, "Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu. 2 Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar." 3 Suka yi magana a karo na biyu: "Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin." 4 Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, "Amin. Halleluya!" 5 Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, "Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko." 6 Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, "Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka. 7 Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta. 8 An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi" (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka). 9 Mala'ika ya ce mani, "Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon." Ya kuma ce mani, "Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne." 10 Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci." 11 Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki. 12 Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa. 13 Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah. 14 Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta. 15 Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka. 16 Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: "Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji." 17 Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama. 18 "Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko." 19 Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa. 20 Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci. 21 Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.

20

1 Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa. 2 Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu. 3 Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci. 4 Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu. 5 Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari. 6 Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu. 7 Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa. 8 Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku. 9 Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su. 10 Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin. 11 Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi. 12 Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu. 13 Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi. 14 Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta. 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta.

21

1 Sai na ga sabuwar sama da sabuwar duniya, domin sama ta fari da duniya ta fari sun shude, ba kuma teku. 2 Na ga birni mai tsarki, sabuwar Urushalima, wadda ta sauko kasa daga sama wurin Allah, shiryayya kamar amaryar da aka yi wa ado domin mijinta. 3 Na ji babbar murya daga kursiyinta na cewa, "Duba! Mazaunin Allah yana tare da 'yan adam, zai zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kuma da kansa zai kasance tare da su ya kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu, kuma babu sauran mutuwa, ko bakinciki, ko kuka, ko azaba. Abubuwan da sun shude. 5 Shi wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce, "Duba! Na maida kome ya zama sabo." Ya ce, "Ka rubuta wannan domin wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya". 6 Ya ce mani, "Wadannan abubuwan an gama! Ni ne Alpha da Omega, farko da karshe. Ga mai jin kishi, zan bashi kyauta daga mabulbular ruwan rai. 7 Wanda ya ci nasara, zai gaji wadannan abubuwa, ni kuma zan zama Allahnsa, shi kuma ya zama da na. 8 Amma ga matsorata, da marasa bangaskiya, da masu kazanta, da masu kisan kai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da dukan makaryata, mazaunin su zai kasance cikin tafki mai ci da farar wuta. Mutuwa ta biyu kenan." 9 Daya daga cikin mala'ikun bakwai ya zo wurina, wanda yake dauke da tasoshi bakwai cike da annobai bakwai na karshe, yace, "Zo nan. Zan nuna maka amarya, matar Dan Rago". 10 Sai ya dauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsawo ya nuna mani birni mai-tsarki, Urushalima, tana saukowa daga cikin sama daga wurin Allah. 11 Urushalima tana da daukakar Allah, shekinta yana kama da dutse mai tamani, sai kace dutsen yasfa, garau kamar karau. 12 Tana da babban garu mai tsawo, da kofofi goma sha biyu, da mala'iku goma sha biyu a kofofin. Akan kofofin an rubuta sunayen kabilu sha biyu na 'ya'yan Isra'ila. 13 A gabas akwai kofofi uku, a arewa kofofi uku, a kudu kofofi uku, da kuma yamma kofofi uku. 14 Garun birnin yana da harsashin gini goma sha biyu, a bisansu akwai sunaye goma sha biyu na manzanni goma sha biyu na Dan Rago. 15 Shi wanda yayi magana dani yana da sandan awo na zinariya domin ya auna birnin, da kofofinsa, da garunsa. 16 Birnin; da tsawonsa da fadinsa iri daya ne. Ya gwada birnin da sandar awo, mil dubu sha biyu a tsaye (fadinsa, da tsawonsa, da tsayinsa duka daya ne) 17 Ya kuma gwada garunsa, kamu 144, bisa ga gwajin 'yan adam (wanda shine ma'aunin mala'ika). 18 An gina garun da Yasfa birnin kuma da sahihiyar zinariya, mai kama da madubi mai kyalli. 19 An kawata harsashin garun da kowanne irin dutse mai tamani. Na fari yasfa, na biyu saffir, na uku agat, na hudu emerald, 20 na biyar Onis, na shida sardiyus, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha daya yakinta, na sha biyu kuma ametis. 21 Kofofi goma sha biyu lu'u-lu'ai ne goma sha biyu; kowacce daya a cikin kofofin daga lu'u-lu'u daya aka yi shi. Titunan birnin kuwa zinariya ce sahihiya, sai kace madubi garau. 22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, gama Ubangiji Allah Mai iko duka da Dan Ragon su ne haikalinsa. 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi gama daukakar Allah ta haskaka shi, kuma fitilarsa Dan Rago ne. 24 Al'ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin. Sarakunan duniya kuma za su kawo daukakarsu cikinsa. 25 Kofofinsu kuma ba za a rufe su da rana ba, babu dare kuma a can. 26 Za su kawo daukaka da darajar al'ummai a cikinsa, 27 babu wani abu mai kazanta da zai taba shiga cikinsa. Ko wanda yake aikata abin kunya da karya, sai wadanda an rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Dan Rago kadai.

22

1 Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago 2 ta tsakiyar titin birnin. A kowanne gefen kogin akwai itacen rai, mai ba da 'ya'ya iri goma sha biyu, kowanne wata. Ganyayen itacen kuma domin warkar da al'ummai ne. 3 Babu sauran la'ana nan gaba. Kursiyin Allah da na Dan Rago za su kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa bauta. 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5 Babu sauran dare; ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba gama Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su yi mulki har abada abadin. 6 Mala'ika ya ce mani, "Wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya. Ubangiji, Allah na ruhohin annabawa, ya aiki mala'ikansa ya nuna wa bayinsa abin da lallai zai faru ba da dadewa ba". 7 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan." 8 Ni, Yahaya, nine na ji na kuma ga wadannan abubuwa. Sa'adda na ji na gan su, sai na fadi gaban kafaffun mala'ikan da ya nuna mani wadannan abubuwa domin in yi masa sujada. 9 Ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni abokin bauta ne tare da kai, tare da 'yan'uwanka annabawa, da wadanda ke biyayya da kalmomin littafin nan. Yi sujada ga Allah!" 10 Ya ce mani, "Kada ka rufe kalmomin anabcin littafin nan, gama lokaci ya kusa. 11 Wanda yake mara adalci, bari ya cigaba da yin rashin adalci. Wanda yake mai kazanta bari ya cigaba da kazantar da kansa. Wanda yake mai adalci bari ya cigaba da yin adalci. Wanda yake mai-tsarki, bari yaci gaba da tsarki." 12 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi. 13 Nine Alpha da Omega, farko da karshe, mafarin abu da karshensa. 14 Masu albarka ne wadanda suka wanke rigunansu domin su sami izini su ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta kofofinsa. 15 A waje akwai karnuka, masu sihiri, masu bautar gumaka, fasikai, masu kisan kai, da duk wanda yake kaunar aikata rashin gaskiya. 16 Ni, Yesu na aiko mala'ikana ya shaida maku wadannan abubuwa saboda ikilisiyoyi. Nine tushe da zuriyar Dauda, tauraron asubahi mai-haske." 17 Ruhu da Amarya suka ce, "Zo!" Bari wanda ya ji ya ce, "Zo!" Kowanne mai jin kishi, da kowanne mai bukatar ta, bari ya sami ruwan rai kyauta. 18 Ina shaida wa duk mai jin kalmomin anabcin wannan littafi: Idan wani ya kara a kansu, Allah zai kara masa annoban da ke rubuce a cikin littafin. 19 Idan wani ya rage daga kalmomin wannan littafin anabci, Allah zai rage rabonsa daga cikin itacen rai daga cikin birni mai-tsarki, wadanda aka rubuta cikin wannan littafi. 20 Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, "I! Ina zuwa ba da dadewa ba." Amin! Zo, Ubangiji Yesu! 21 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da kowanne dayanku. Amin.